ha_ulb/26-EZK.usfm

2525 lines
200 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id EZK
\ide UTF-8
\h Littafin Ezekiyel
\toc1 Littafin Ezekiyel
\toc2 Littafin Ezekiyel
\toc3 ezk
\mt Littafin Ezekiyel
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A cikin shekara ta talatin, a wata na huɗu, rana ta biyar ga wata, ya kasance kuwa ina zaune cikin 'yan bauta a bakin Kogin Keba. Sai sammai suka buɗe, kuma Na ga wahayoyin Allah.
\v 2 A rana ta biyar a wannan watan - shekara ta biyar kenan ta mijirar sarki Yehoyacin.
\v 3 Maganar Yahweh ta zo ga Ezekiyel ɗan Buzi firist, a cikin ƙasar Kaldiyawa a hanyar Kogin Keba, hannun Yahweh kuma yana kansa a wurin.
\s5
\v 4 Daga nan sai na duba, sai ga iskar hadari na tasowa daga arewa; babban girgije mai wuta na haskakawa kewaye da shi da kuma a cikinsa, haske na kewaye da shi da cikinsa, kuma wutar tana da launin rawaya cikin girgijen.
\v 5 Daga cikin tsakiyarsa siffar waɗansu masu rai huɗu. Wannan shi ne bayyanuwar su: suna da kamannin mutum,
\v 6 amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, kowacce halittar kuma nada fikafikai huɗu.
\s5
\v 7 Ƙafafunsu a miƙe suke, amma tafin sawayensu kamar kofaton ɗan maraƙi yana sheƙi kamar gogaggiyar tagulla.
\v 8 Duk da haka suna da hannayen mutane a ƙarƙashin kowanne sashi huɗu na fukafukansu, dukkan su huɗun, fuskokinsu da fukafukansu haka suke:
\v 9 fukafukansu na taɓa fukafukan ɗaya halittar, a cikin tafiyarsu ba su juyawa; maimakon haka, kowannensu a miƙe yake ɗoɗar.
\s5
\v 10 Kamannin fuskokinsu na kama da fuskar mutum. Su huɗun suna da fuskar zaki a sashin dama, su huɗun suna da fuskar bijimin sã sashin hagu. Su huɗun kuma suna da fuskar gaggafa.
\v 11 Fukafukansu haka suke, fukafukansu kuma a shimfiɗe suke a sama, domin kowacce halitta nada fiffike biyu da ke taɓa fiffiken halittar, kuma fukafukan biyu sun rufe jikkunansu.
\v 12 Kowanne ɗayansu ya tafi ɗoɗar, domin duk inda ruhu ya jagorance su suje, suna tafiya ba tare da sun juya ba.
\s5
\v 13 Game da kamannin rayayyun halittun nan kuwa, bayyanuwarsu na kama da garwashin wuta mai ci, kamar bayyanar cociloli; hasken wuta kuma na kai da komowa tsakanin halittun, kuma akwai haskawar walƙiya.
\v 14 Rayayyun halittun nan suna matsawa da sauri gaba da baya, bayyanarsu kuma kamar walƙiya take!
\s5
\v 15 Daga nan sai na dubi rayayyun halittun nan, sai ga wani gargare a ƙasa a gefen rayayyun halittun tare da fuskokinsu huɗu.
\v 16 Wannan shi ne bayyanuwa da tsarin gargarorin; kowanne gargare na kama da dutse mai tamani, dukkan su huɗun kamannin su ɗaya ne; bayyanuwarsu da ƙirarsu sai ka ce gargare mai ratsawa ta wani gargaren.
\s5
\v 17 Yayin da suke matsawa, suna tafiya ta kowanne kusurwarsu huɗu, ba tare da sun juya ba yayin da suke tafiya.
\v 18 Zancen gammon gargarensu, masu tsawo ne da kuma ban tsoro, domin gammon gargaren na cike da idanu a kewaye.
\s5
\v 19 Duk sa'ad da rayayyun halittan nan suke matsawa, gargarorin na matsawa a gefensu. Sa'ad da rayayyun halittar suka tashi daga duniya, gargarorin suma su kan tashi sama.
\v 20 Duk inda Ruhu zai tafi, sukan tafi, sai gargarorin su tashi a gefensu, gama ruhun rayayyun halittun yana cikin gargarorin.
\v 21 Duk sa'ad da halittun suke matsawa, gargarorin suma suna matsawa; idan kuma halittun suka tsaya cik, gargarorin suma sukan tsaya cik; idan halittun suka tashi daga ƙasa, gargarorin sukan tashi a gefensu, saboda ruhun rayayyun halittun yana cikin gargarorin.
\s5
\v 22 A bisa kawunan rayayyun halittun nan akwai kamannin miƙaƙƙen sarari; yana kama da abu mai banmamaki da ƙyalli a miƙe bisa kawunansu sama.
\v 23 A ƙarƙashin sararin, kowanne fukafukan halittun a miƙe suke sak kowanne yana taɓa fukafukan ɗaya rayayyen halittar. Kowannen rayayyen halittar kuma yana da fiffike biyu domin su rufe kansu; kowanne yana da biyu domin ya rufe jikinsa.
\s5
\v 24 Daga nan sai naji ƙarar fikafikansu. Kamar ƙarar ruwaye masu yawa. Kamar muryar mai Iko dukka a duk sa'ad da suke matsawa. Kamar ƙarar iskar hadari. Kamar ƙarar rundunar sojoji. Duk sa'ad da suka tsaya cik, sukan saukar da fukafukansu.
\v 25 Sai murya ta zo daga saman sararin sama da kansu duk sa'ad da suka tsaya cik suka kuma sãki fukafukansu.
\s5
\v 26 A bisa sararin nan da ke sama da kansu akwai kamannin kursiyi da ke kama da bayyanuwar dutsen tama, a bisa kamannin kursiyin kuma akwai kamannin da ya yi kama da bayyanuwar mutum.
\s5
\v 27 Na ga siffa da bayyanuwar ƙarfe mai haskakawa da wuta a cikinsa tun daga bayyanuwar kwankwasonsa har sama; naga kuma daga bayyanuwar kwankwasonsa har zuwa ƙasa sai ka ce bayyanuwar wuta da haske ko'ina kewaye.
\v 28 Kamar bayyanuwar bakangizo cikin giza-gizai a ranar da aka yi ruwa haka bayyanuwarar sheƙin hasken da ke kewaye da shi yake. Wannan kamar bayyanuwarar kamannin ɗaukakar Yahweh ne. Sa'ad da na gani, Na faɗi bisa fuskata, sai na ji murya tana magana.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ya ce mani, "Dan mutum, tashi bisa sawayenka; daga nan zan yi magana da kai."
\v 2 Daga nan, da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya shiga cikina, yasa na tsaya bisa sawayena, na kuma ji shi yana magana da ni.
\v 3 Ya ce mani, "Dan mutum, ina aiken ka zuwa wurin mutanen Isra'ila, ga al'ummai masu tayarwa, da suka tayar mani. - da su da kakanninsu sun yi mani zunubi har ya zuwa yau!
\s5
\v 4 Zuriyarsu masu tsaurin fuskoki ne zukatansu kuma kangararru ne. Ina aiken ka wurinsu, kuma za ka ce masu, 'Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya ce.'
\v 5 Ko su saurara ko kada su saurara. Gama su gida ne mai tayarwa, amma a ƙalla za su sani cewa akwai annabi a tsakiyarsu.
\s5
\v 6 Kai, ɗan mutum, kada ka ji tsoron su ko maganganunsu. Kada ka ji tsoro, koda yake kana tare da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa koda yake kuma kana zaune da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka damu da irin fuskokinsu, da shike su gida ne mai tayarwa.
\s5
\v 7 Amma za ka faɗi maganganuna a gare su, ko su ji ko kada su ji, gama suna cika da tayarwa.
\v 8 Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da nake faɗa maka. Kada kayi tayarwa kamar wannan gidan mai tayarwa. Ka buɗe bakinka kaci abin da Na ke shirin ba ka!"
\s5
\v 9 Daga nan Na duba, sai a ka miƙo mani hannu; cikin sa rubutaccen littafi ne naɗaɗɗe.
\v 10 Ya baza shi a gaba na; yana da rubutu cikinsa da bayansa, abubuwan da aka rubuta a kai sune koke-koke da makoki da kuma kaito.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka ci abin da ka samu. Ka ci littafin nan, daga nan ka tafi ka yi magana da gidan Isra'ila."
\v 2 Sai na buɗe bakina, ya kuma ciyar da ni da littafin.
\v 3 Ya ce mani, "Dan mutum, ka ciyar da tunbinka ka kuma ƙosar da cikinka da littafin da Na ba ka!" Sai na ci shi, a cikin bakina yana da zaƙi kamar zuma.
\s5
\v 4 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka tafi gidan Isra'ila ka faɗi maganganu na a gare su.
\v 5 Gama ba'a aike ka wurin mutane masu bãƙon harshe ba, ko waɗanda harshensu yake da wahala ba, amma zuwa gidan Isra'ila -
\v 6 ba wurin mutane masu yawa ba da bãƙon harshe ko waɗanda harshensu keda wuya ba, waɗanda ba za ka iya fahimtar kalmominsu ba. Tabbas idan da na aike ka wurinsu, da za su saurare ka.
\v 7 Amma, gidan Isra'ila ba za su yadda su saurare ka ba, gama ba su yadda su saurare ni ba. Gama dukkan gidan Isra'ila masu taurinkai ne masu taurin zuciya kuma.
\s5
\v 8 Duba! Na sa fuskarka ta taurare kamar fuskokinsu girarka kuma ta taurare kamar girarsu.
\v 9 Na maida girarka kamar lu'u-lu'u, yafi tsagewar dutse! kada ka ji tsoron su ko ka karaya da irin fuskokinsu, tunda gida ne mai tayarwa."
\s5
\v 10 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, dukkan kalmomin dana sanar da kai ka ɗauke su cikin zuciyarka ka kuma ji su da kunnuwanka!
\v 11 Daga nan ka tafi wurin 'yan bauta mutanenka, ka yi magana da su. Ka ce masu, 'Wannan ne abin da Ubangiji Yahweh ya ce,' ko su ji ko kada su ji."
\s5
\v 12 Daga nan sai Ruhu ya ɗaga ni sama, a baya na kuma sai na ji babbar muryar girgizar ƙasa: "Albarka ta tabbata ga ɗaukakar Yahweh daga wurinsa!"
\v 13 ƙarar fukafukan masu ran nan ne yayin da suke taɓa junansu, da ƙarar gargarorin da ke tare da su, da ƙarar babbar girgizar ƙasa.
\s5
\v 14 Sai Ruhu ya ɗauke ni sama ya tafi da ni, na kuma tafi da ɓacin rai cikin ruhuna da zafin fushi, gama hannun Yahweh yana danne ni da iko!
\v 15 Sai na tafi wurin 'yan bauta a Tel-abib waɗanda suke zama a bakin kogin Keba, na zauna cikinsu har kwana bakwai, zugum cikin mamaki.
\s5
\v 16 Daga nan ya kasance bayan kwanaki bakwai ɗin sai maganar Yahweh ta zo gare ni, tana cewa,
\v 17 "Ɗan mutum, Na maida kai mai tsaro domin gidan Isra'ila, domin haka sai ka ji maganar bakina, ka kuma ba su gargaɗi na.
\v 18 Sa'ad da na ce da mugu, 'Hakika za ka mutu' kai kuma ba ka gargaɗe shi ba ko ka yi maganar gargaɗi ga mugu a kan miyagun ayyukansa ba, domin ya rayu - mugun za ya mutu saboda zunubinsa, amma zan biɗi haƙƙin jininsa a hannunka.
\v 19 Amma idan ka gargaɗi mugun, kuma bai juya daga muguntarsa ba ko yabar miyagun ayyukansa ba, zai mutu domin zunubinsa, amma kai za ka ceci ranka.
\s5
\v 20 Kuma idan adali ya juya daga adalcinsa ya aikata ba abin da dai-dai ba, kuma na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Saboda ba kagargaɗe shi ba, zai mutu cikin zunubansa, ba kuwa zan tuna da ayyukansa na adalci da ya yi ba, amma zan biɗi haƙƙin jininsa a hannunka.
\v 21 Amma idan ka gargaɗi adalin mutum ya daina yin zunubi shi kuwa bai ƙãra yin zunubi ba, lallai zai rayu tun da shi ke an gargaɗe shi; kai kuma ka ceci ranka."
\s5
\v 22 Hannun Yahweh yana kaina a wurin, sai ya ce mani, "Tashi! Ka fita zuwa sarari, a can kuma zan yi magana da kai!"
\v 23 Sai na tashi na fita zuwa cikin sarari, a can ne ɗaukakar Yahweh na tsayawa, kamar ɗaukakar dana gani a gefen Kogin Keba; sai na faɗi a bisa fuskata.
\s5
\v 24 Sai Ruhu ya sauko mani ya tsaida ni bisa sawayena; sai ya yi magana da ni, ya ce mani, "Jeka ka kulle kanka cikin gidanka,
\v 25 domin yanzu, ɗan mutum, za su sa igiyoyi a kanka su ɗaureka domin kada ka iya fita cikinsu.
\s5
\v 26 Zan sa harshenka ya liƙe wa rufin bakinka, za ka kasa yin magana, ba za ka iya tsauta masu ba, da shi ke su gidane masu tayarwa.
\v 27 Amma sa'ad da na yi magana da kai, Zan buɗe bakinka za ka ce masu, 'Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi,' Wanda ya ji, ya ji, Wanda ya ƙi ji ya ƙi ji, gama su gida ne mai tayarwa!"
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 "Amma kai, ɗan mutum, sai ka ɗaukarwa kanka tubali ka sa a gabanka. Ka sassaƙa birnin Yerusalem a kansa.
\v 2 Daga nan kayi sansani kewaye da shi, sai ka gina kagarai gãba da ita. A kuma tayar da masu kai mata hari, a kuma sa mata sansani kewaye da ita.
\v 3 Daga nan ka ɗaukarwa kanka faifan ƙarfe ka kuma yi amfani da shi a matsayin katangar ƙarfe tsakaninka da birni ka kuma sa fuskarka gãba dashi, gama za a yi masa sansani, kuma kai zaka sa sansanin gãba dashi. Wannan zai zama alama ga gidan Isra'ila.
\s5
\v 4 Daga nan, sai ka kwanta a gefen hannunka na hagu sai ka sa zunubin gidan Isra'ila a kansa; za ka ɗauki zunubinsu bisa ga yawan kwanakin da kake kwantawa gãba da gidan Isra'ila.
\v 5 Ni da kaina na sanya maka kwana ɗaya ya wakilci shekara ta hukuncinsu: kwanaki 390! Ta haka nan, za ka ɗauki zunubin gidan Isra'ila.
\s5
\v 6 Idan ka gama waɗannan kwanaki, sai ka sake kwanciya a sashin hannunka na dama kuma, gama za ka ɗauki zunubin gidan Yahuda har kwana arba'in. Na sanya maka kwana ɗaya domin shekara guda.
\v 7 Ka sa fuskarka wajen sansanin Yerusalem, da hannunka marar rufi ka yi anabci gãba da ita.
\v 8 Duba! I na sanya maɗaurai a kanka yadda ba za ka juya daga wannan sashi zuwa wancan ba har sai lokacin da ka gama kwanakin sansaninka.
\s5
\v 9 Ka ɗaukar wa kanka alkama, bali, wake, acca, gero da maiwa; ka sa su cikin tukunya ɗaya ka yi gurasa da su bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a sashinka. Za ka ci su har kwanaki 390.
\v 10 Abincin da za ka ci zai zama bisa ga awo, shekel ashirin kowacce rana, za ka ci bisa ga lokutan da a ka ƙaiyade kowacce rana.
\v 11 Daga nan za ka sha ruwa, bisa ga aunawa sau shida bisa ga ka'ida za ka sha.
\s5
\v 12 Za ka ci a matsayin waina ta bali, amma za ka toya ta a kan idonsu da kãshin da ke fitowa daga jikin mutum!"
\v 13 Gama Yahweh ya ce, "Wato abincin da 'ya'yan Isra'ila za su ci zai zama marar tsabta, a can cikin al'ummai inda na kora su."
\s5
\v 14 Amma, Na ce, "Kaito! Ubangiji Yahweh! Ban taɓa ƙazantuwa ba! Ban taɓa cin mushe ba ko abin da namun jeji suka kashe, tun ina matashi har yanzu, kuma ba wani ƙazantaccen nama da ya taɓa shiga bakina!"
\v 15 Sai ya ce mani, "Duba, na baka kãshin shanu maimakon kãshin mutum a kansa za ka shirya abincinka."
\s5
\v 16 Ya sake ce mani, "Ɗan mutum! Duba! Ina karya sandar abincin da ke cikin Yerusalem, za su ci abinci suna aunawa cikin juyayi za kuma su sha ruwa lokacin da suke aunawa cikin rawar jiki.
\v 17 Saboda za su rasa abinci da ruwa, kowanne mutum zai dubi ɗan'uwansa da damuwa su kuma lalace saboda laifinsu."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 "Daga nan kai, Ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi kamar askar mai aski domin kanka, ka aske kanka da gemunka, daga nan ka ɗauki ma'auni ka raba gashin kanka uku.
\v 2 Ka ƙone kashi ɗaya cikin wuta a tsakiyar birnin lokacin da kwanakin yiwa birnin sansani suka cika, ka ɗauki kashi ɗaya na gashin ka buge shi da takobi ko'ina kewayen birnin. Daga nan sai ka watsar da kashi ɗaya a iska, daga nan zan zare takobi in runtumi mutanen.
\s5
\v 3 Amma ka ɗibi gashi kaɗan daga cikinsu ka ɗaure su cikin rigarka.
\v 4 Daga nan sai ka ɗebi gashi mafi yawa ka jefa cikin tsakiyar wuta; ka ƙone su cikin wuta; daga nan wuta za ta fito ta shiga dukkan gidan Isra'ila."
\s5
\v 5 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, "Wannan ita ce Yerusalem na sanya ta a tsakiyar al'ummai, na kuma kewaye ta da sauran ƙasashe.
\v 6 Amma ta ƙi shari'ata yayin da ta aikata mugunta fiye da yadda sauran ƙasashe suka yi, ta tayarwa umarnaina fiye da ƙasashen da ke kewaye da ita. Mutanen sunƙi hukuntaina ba su kuma yi tafiya cikin farillaina ba."
\s5
\v 7 Domin wannan Yahweh ya ce, "Saboda kunfi al'ummai waɗanda ke kewaye daku taurinkai ba ku yi tafiya cikin umarnaina ba kuma ba ku kiyaye dokokina ba ko ma dokokin al'umman da ke kewaye daku,"
\v 8 domin wannan Yahweh ya ce, "Duba! nima ina gãba da ke. Zan aiwatar da hukuntai a tsakiyarki domin al'ummai su gani.
\s5
\v 9 Zan yi maku abin da ban taɓa yi ba da kuma irin wanda ba zan sake yin irin sa ba, saboda dukkan ayyukan banƙyamarku.
\v 10 Domin wannan a tsakiyarki ubanni za su ci naman 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su ci naman iyayensu, da shi ke zan aikata hukunci a kanku zan kuma watsar da dukkanku da kuka rage ko ina
\s5
\v 11 Na rantse da raina - Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - hakika saboda kun tozartar da wurina mai-tsarki da dukkan kayanku na banƙyama da al'amuranku na banƙyama, domin wannan Ni da kaina zan rage yawanku; idona kuma ba zai dube ku da rahama ba, ba kuma zan bar ku ba.
\v 12 Kashi ɗaya cikin ukunku za su mutu da annoba, da yunwa kuma za su ƙare a tsakiyarku. Kashi ɗaya cikin ukunku kuma za su faɗi da kaifin takobi kewaye daku. Sulusin na ukun kuma zan watsar da su a kowanne sashi, in kuma zare takobi in fafare su.
\s5
\v 13 Daga nan fushina zai kammala, zan kuma sa zafin hasalata akansu ya huce. Zan gamsu, kuma za su sani cewa Ni, Yahweh na yi magana cikin fushina sa'ad da na gama aikin hasalata gãba da su.
\v 14 Zan maishe ku kango abin raini ga al'umman da ke kewaye daku, a kan idon duk wanda ke wucewa.
\s5
\v 15 Hakan nan Yerusalem za ta zama wani abin wulaƙantarwa da ba'a ga mutane, abin gargaɗi da tsoratarwa ga al'ummai da ke kewaye daku. Zan zartar da hukuntai gãba daku cikin fushi da hasala, da tsautawa mai zafi - Ni, Yahweh na furta wannan!
\v 16 Zan aikar da kibau masu zafi na yunwa gãba daku da za su zama dalilin da zan hallaka ku. Zan ƙara maku yunwa zan kuma datse abincin da kuke dogara da shi.
\v 17 Zan aikar da yunwa da bala'o'i gãba daku za ku zama marar 'ya'ya. Annoba da jini za su ratsa ta tsakiyarku, zan kawo takobi gãba daku - Ni, Yahweh na furta wannan."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka sa fuskarka gãba da tsaunukan Isra'ila ka yi anabci a kansu.
\v 3 Ka ce, "Tsaunukan Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji Yahweh! Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan ga tsaunuka da tuddai ga rafuffuka da kwarurruka: Duba! Zan kawo takobi gãba da ku, zan kuma hallaka wurarenku masu daraja.
\s5
\v 4 Daga nan bagadanku za su zama kangaye ginshiƙansu za a hallakar da su, zan jefar da gawarwakinku gaban gumakansu.
\v 5 Zan jera gawarwakin mutanen Isra'ila a gaban gumakansu, in warwatsar da ƙasusuwanku wajen bagadanku.
\s5
\v 6 Duk inda kuka zauna, biranen za su zama marasa amfani, wuraren bisa kuma za su zama kufai, domin bagadanku su zama kufai su zama kangaye. Daga nan za'a farfashe su kuma za su ɓace, za a datse ginshiƙanku ayyukanku kuma za a shafe su kaf.
\v 7 Matattu za su faɗi a tsakiyarku kuma za ku sani Ni ne Yahweh.
\s5
\v 8 Amma zan tsare ringi daga cikin ku, waɗansu kuma za su tsere wa takobi daga cikin al'ummai, sa'ad da aka warwatsar da ku ko'ina cikin ƙasashe.
\v 9 Daga nan su da suka tsira za su tuna da ni cikin al'ummai inda za a kai su bauta, za su tuna yadda zuciyata tayi ƙũna ta wurin zuciyarsu mazinaciya wadda ta juya daga gare ni, ta idanunsu kuma da ke ƙara sasu bin gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu suna duban dukkan muguntar da suka aikata da dukkan ƙazantarsu.
\v 10 Za su sani cewa Ni ne Yahweh. Saboda wannan dalilin Na ce Zan kawo wannan muguntar a gare su.
\s5
\v 11 Ubangji Yahweh ya ce: Ka tãɓa hannayenka ka buga ƙafarka! Ka ce, 'Kaito!' saboda dukkan miyagun ayyukan ƙazanta na gidan Isra'ila! Gama za su faɗi ta kaifin takobi da yunwa da annoba.
\v 12 Na nesa za su mutu ta annoba, na kusa zai faɗi ta wurin takobi. Waɗanda suka rage suka rayu za su mutu da yunwa. Ta haka ne zan cika hasalata a kansu.
\s5
\v 13 Daga nan za ku sani ni ne Yahweh, sa'ad da matattunsu suka kwanta wurin gumakansu, kewaye da bagadansu, a kan kowanne tudu mai bisa - kan dukkan ƙwanƙoli tsaunuka, da ƙarƙashin kowanne itace mai inuwa kuma da rimi mai kauri - da wurare inda suke ƙona turare ga dukkan gumakansu.
\v 14 Da hannuna zan kai sãra in maida ƙasar kango da kufai, tun daga jeji har zuwa Dibla, ko'ina a dukkan wuraren zamansu. Daga nan za su sani cewa Ni ne Yahweh."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Kalmar Yahweh ta zo wurina, cewa,
\v 2 "Kai, Ɗan mutum - Ubangiji Yahweh ya faɗi haka ga ƙasar Isra'ila." 'ƙarshe! ƙarshe ya zo ga iyakoki huɗu na ƙasar.
\s5
\v 3 Yanzu ƙarshenki yana kanki, gama ina aikar da fushina a kanki, zan shar'anta ki bisa ga ayyukanki; zan kuma kawo dukkanharamtattun ayyukanki a kanki.
\v 4 Gama idanuna ba za su tausaya maki ba, ba kuma zan keɓe ki ba. Maimakon haka, Zan kawo al'hakin al'amuranki a kanki, haramtattun ayyukanki kuma a cikinki, domin ki sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 5 Ubangiji Yahweh ya ce: Bala'i! Bala'i na musamman! Duba, yana zuwa.
\v 6 Lallai matuƙa tana zuwa. Matuƙa ta farka a kanki. Duba, tana zuwa!
\v 7 hukuncinku zai zo maku ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya zo; ranar hallaka ta kusa, tsaunuka kuma ba za su ƙara yin murna ba.
\s5
\v 8 Yanzu bada daɗewa ba zan zuba maku hasalata in cika fushina a kanku lokacin da nake hukunta ku bisa ga al'amuranku in kuma kawo dukkan al'hakin ƙazantarku a kanku.
\v 9 Gama idanuna ba za su tausaya ba, ba kuma zan keɓe ku ba. Kamar yadda kuka yi haka zan yi maku; haramtattun ayyukanku za su kasance a tsakiyarku domin ku sani cewa Ni ne Yahweh wanda yake hukuntaku.
\s5
\v 10 Duba, ranar! Duba, tana zuwa! hukunci ya fita waje! Sandar tayi fure, girmankai ya yi toho!
\v 11 Tashin hankali ya yi girma zuwa cikin sandar mugunta - babu wani daga cikinsu, ko wani daga cikin taronsu, ko daga cikin wadatarsu, babu wani abu nasu mai muhimmanci da zai dawwama!
\s5
\v 12 Lokaci na zuwa; lokaci ya zo kusa. Kada ka bari mai saye ya yi farinciki, ko mai sayarwa ya yi makoki, tunda fushina yana kan dukkan taronsu!
\v 13 Gama mai sayarwa ba zai dawo ƙasar da ya yi sayarwa ba muddan dukkansu suna raye, saboda wahayin game da dukkan taron ba za a sauya ba; kuma saboda zunubansu, ba waninsu da zai ƙarfafa!
\s5
\v 14 Sun busa ƙaho sun shirya komai, amma ba bu mai takawa zuwa yaƙi; tunda fushina yana kan dukkan taron jama'ar.
\v 15 Takobi na waje, yunwa kuma da annoba suna cikin ginin. Waɗanda ke cikin saura za su mutu da takobi, yayin da yunwa da annoba kuma za su cinye waɗanda ke cikin birnin.
\v 16 Amma waɗansu za su tsira daga cikinsu, za su gudu zuwa tsaunuka. Kamar kurciyoyin kwarurruwa, dukkansu za su yi makoki - kowanne mutum saboda laifinsa.
\s5
\v 17 Kowanne hannu zai zama raunanne kowacce gwiwa kuma za ta zama marar ƙarfi kamar ruwa,
\v 18 za su sa tsummoki, tsoro kuma zai rufe su; kunya za ta kasance a kowacce fuska, saiƙo kuma a dukkan kawunansu.
\v 19 Za su jefar da azurfarsu cikin karafku zinariyarsu kuma za ta zama kamar juji. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Yahweh. Rayukansu ba za su tsira ba, ba za a ƙosar da yunwarsu ba, domin laifofinsu sun zama dalilin tuntuɓe.
\s5
\v 20 A cikin taƙamarsu suka ɗauki Kyaun kayan duwatsun adonsa, da su kuma suka yi siffofinsu na gumaka da ƙazantattun abubuwansu. Domin wannan, Ina maida waɗannan abubuwa su zama marasa tsarki a gare su.
\v 21 Daga nan zan bada waɗannan abubuwa a cikin hannun bãƙi a matsayin ganima ga kuma miyagun duniya a matsayin ganima, za kuma su ƙazantar da su.
\v 22 Daga nan zan juyar da fuskata daga gare su sa'ad da suka ƙazantar da ƙaunataccen wurina; 'yan adawa za su shiga su ƙazantar da shi.
\s5
\v 23 Kayi sarƙa, saboda ƙasar ta cika da hukuncin jini, birnin kuma na cike da tashin hankali.
\v 24 Domin in kawo ƙasashe mafi mugunta, za su kuma mallaki gidajensu, zan kuma kawo ƙarshen girmankan masu ƙarfi, gama za a ƙazantar da wurarensu masu tsarki!
\v 25 Tsoro zai auko! Za su nemi salama, amma ba za a samu ba.
\s5
\v 26 Masifa biye da masifa za ta zo, kuma za a samu jita-jita bayan jita-jita. Sa'an nan za su nemi wahayi daga wurin annabi, amma shari'a za ta lalace daga Firist shawara kuma daga wurin dattawa.
\v 27 Sarki zai yi makoki yarima kuma zai rufe kansa da fargaba, yayin da kuma hannayen mutanen ƙasar makyarkyata cikin tsoro. Bisa ga hanyoyinsu zan aikata masu wannan! Zan hukunta su bisa ga matakinsu har sai sun sani cewa Ni ne Yahweh.'"
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Ana nan a shekara ta shida cikin wata na shida, a rana ta biyar ga watan, Ina zaune cikin gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, sai hannun Yahweh ya sake saukowa a kaina a wurin.
\v 2 Sai na duba, sai ga alamar wani mai kama da bayyanuwar mutum. Daga bayyanuwar ƙugunsa zuwa ƙasa akwai wuta. Daga kuma ƙugunsa zuwa sama akwai bayyanuwar wani abu mai ƙyalli, kamar ƙarfe mai sheƙi.
\s5
\v 3 Daga nan sai ya miƙa abu mai kama da hannu, ya ɗauke ni ta gashin kaina; Ruhun kuma ya ɗaga ni tsakanin duniya da sama, a kuma cikin wahayoyi daga wurin Allah, sai ya kawo ni Yerusalem, zuwa wurin shiga ƙofar arewa ta ciki, inda gunki mai cakuno babban kishi ke tsayawa.
\v 4 Daga nan duba, ɗaukakar Allah na Isra'ila na wurin, bisa ga wahayin da na gani a sarari.
\s5
\v 5 Daga nan sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka zuwa arewa." Sai na ɗaga idanuna zuwa arewa, daga arewacin ƙofar da ke bida wa zuwa bagadi, a ƙofar shigar, gunkin kishi ne.
\v 6 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga abin da suke yi? Waɗannan sune haramtattun ayyuka masu girma da gidan Isra'ila ke yi da nufin su sani in tafi nesa da wurina mai tsarki. Amma za ka juya ka ga waɗansu haramtattun ayyukan mafi girma."
\s5
\v 7 Daga nan sai ya kawo ni bakin ƙofar farfajiya, sai na duba, sai kuma ga rami a jikin bango.
\v 8 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ka yi gini cikin bangon nan" Sai na gina cikin bangon, sai ga wata ƙofa.
\v 9 Daga nan sai ya ce mani, "Je ka ka ga haramtattun ayyukan muguntar da suke yi a nan."
\s5
\v 10 Sai na shiga ciki na duba, kuma duba! Akwai kowanne abu mai rarrafe da ƙazantattun bisashe! Kowanne gunki na gidan Isra'ila an sasssaƙa siffarsa a jikin bangon kewaye ko'ina.
\v 11 Dattawa saba'in na gidan Isra'ila suna wurin, Yãzaniya ɗan Shafan kuma na tsaye a tsakiyarsu. Suna tsaye a gaban siffofin, kowanne mutum na riƙe da kaskon ƙona turare a hannunsa yadda ƙanshin girgijen turaren kuma ya hau sama.
\s5
\v 12 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga abin da dattawan gidan Isra'ila ke aikatawa a cikin duhu? Kowannesu na aikata wannan a cikin ɓoyayyen wurin ɗakin gunkinsa, gama sun ce, 'Yahweh ba ya ganin mu! Yahweh ya yi watsi da ƙasar."
\v 13 Daga nan sai ya ce mani, "Ka sake juyawa ka ga waɗansu manyan haramtattun ayyuka da suke yi."
\s5
\v 14 Gaba kuma sai ya kawo ni wajen ƙyauren ƙofar gidan Yahweh wadda ke gefen arewa, kuma duba! Mata na zaune suna makoki domin Tamuz.
\v 15 Sai ya ce mani, "Ɗan mutum, ko ka ga wannan? Ka sake juyawa za ka ga manyan haramtattun ayyuka fiye da waɗannan."
\s5
\v 16 Ya kawo ni cikin farfajiya ta cikin gidan Yahweh, duba kuma! A ƙofar shiga haikalin Yahweh tsakanin harabar da bagadi, akwai maza ashirin da biyar sun juyawa haikalin Yahweh baya fuskokinsu na fuskantar gabas, suna kuma yiwa rana sujada.
\s5
\v 17 Sai ya ce mani, Ɗan mutum, ka ga wannan? Wannan ƙaramin abu ne ga gidan Yahuda, su yi waɗannan haramtattun ayyuka da suke yi a nan? Gama sun cika ƙasar da tashin hankali sun sake juyawa kuma sun cakune ni ga yin fushi, suna sanya reshe cikin hancinsu.
\v 18 Ni ma zan yi aiki a cikinsu; Idanuna ba za su tausaya masu ba, ba kuwa zan raga masu ba. Koda za su yi kuka da babbar murya a kunnuwana, Ba zan ji su ba."
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Sa'an nan sai ya yi kuka da babbar murya a kunnena, ya ce, "Bari matsara su taso zuwa birni, kowanne da makamin hallakarwarsa a hanunsa."
\v 2 Daga nan duba! Mutane shida suka zo daga hanyar ƙofa ta bisa, wadda ke fuskantar arewa, kowanne mutum da makamin yankansa a hanunsa. Akwai mutum ɗaya a tsakiyarsu saye da tufafin linin a jikinsa da abin rubutu a gefensa. Suka shiga ciki suka tsaya wajen bagadi na tagulla.
\s5
\v 3 Daga nan sai ɗaukakar Allah na Isra'ila ta hau daga wurin kerubim inda take a dã har zuwa bakin ƙofar gidan. Sai ya kira mutumin da ke saye da tufafun linin wanda yake da kayan rubuta a gefensa.
\v 4 Yahweh ya ce masa, "Ka ratsa ta tsakiyar birnin - ta tsakiyar Yerusalem - ka sa shaida a goshin mutanen da ke nishi da tsaki game da dukkan haramtattun ayyukan da ake yi cikin tsakiyar birnin."
\s5
\v 5 Daga nan na ji ya yi magana da sauran ya ce, "Ku ratsa birnin ku bi bayansa ku yi kisa. Kada ku bari idanunku su tausaya, kada kuma ku raga wa kowa.
\v 6 Ko tsoho, ko saurayi, ko budurwa, ko ƙananan yara, ko mata. Ku kashe dukkan su! Amma kada ku kusanci kowanne mutum da ke da shaida a goshinsa. Ku fara daga wurina mai tsarki!" Sai suka fara da dattawa waɗanda ke a gaban gidan.
\s5
\v 7 Sai ya ce masu, "Ku ƙazantar da gidan, ku cika harabunsa da matattu. Ku zarce gaba" Sai suka fita waje suka kai wa birnin hari.
\v 8 Yayin da suke kai masa harin, sai na sami kaina ni kaɗai sai na faɗi a fuskata na yi kuka na ce, "Ah, Ubangiji Yahweh, za ka hallakar da dukkan sauran Isra'ila cikin hasalar fushin da kake zubawa kan Yerusalem?"
\s5
\v 9 Sai ya ce mani, "Zunubin gidan Isra'ila da na Yahuda ya ƙasaita ƙwarai. Ƙasar cike take da jini kuma birnin cike yake da ayyukan ƙazanta, tun da suka ce, 'Yahweh ya manta da ƙasar,' kuma Yahweh ba ya gani!'
\v 10 To daga nan, ni ma idanuna ba za su duba da tausayi ba, kuma ba zan raga masu ba. Maimakon haka, zan kawo masu duk alhakinsu a kansu."
\v 11 Duba! Mutumin da ke saye da tufafin linin wanda ke da kayan rubutu a gefensa ya dawo. Ya kawo rahoto ya ce, "Na aiwatar da dukkan abin da ka umarta."
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Da na duba ta sararin da yake bisan kawunan kerubobin; wani abu ya bayyana a samansu kamar yakutu da bayyanuwa mai kamannin kursiyi.
\v 2 Daga nan Yahweh ya yi magana da mutumin da ke saye da tufafin linin ya ce, "Jeka tsakaningargarorin da ke ƙarƙashin kerubobin, ka cika hannuwanka biyu da garwashin wuta mai zafi daga tsakanin kerubobin ka watsa su bisa birnin." Daga nan mutumin ya tafi ni yayin da nake kallo.
\s5
\v 3 Kerubobin suna tsaya a gefen dama na gidan sa'ad da mutumin ya shiga ciki, sai girgije ya cika harabar da ke can ciki.
\v 4 Ɗaukakar Yahweh ta taso daga kerubobin ta tsaya a ƙyauren gidan. ta cika gidan da girgijen, kuma harabar ta cika da hasken ɗaukakar Yahweh.
\v 5 Aka kuwa ji ƙarar fukafukan kerubobin har can wajen harabar, kamar muryar Allah maɗaukaki sa'ad da yake magana.
\s5
\v 6 Ana nan kuma, sa'ad da Allah ya umarce mutumin da ke saye da tufafin linin ya ce, "Ka ɗebi wuta daga tsakanin gargarorin da ke tsakanin kerubobin," mutumin ya je ciki ya tsaya a gefen gargare ɗaya.
\v 7 Kerubim ɗaya ya miƙa hannunsa tsakanin kerubobin zuwa wutar da ke tsakanin kerubobin, ya ɗiba ya zuba a hannun wanda ke saye da tufafin linin. Mutumin ya karɓa ya tafi waje.
\v 8 Na kuwa gani a kerubobin wani abu kamar hannun mutum a ƙarƙashin fukafukansu.
\s5
\v 9 Saboda haka na duba, sai ga! gargarori huɗu a gefen kerubobin - gargare ɗaya a gefen kowanne kerubim guda - kuma fasalin gargarorin na kamar dutse mai daraja.
\v 10 dukka huɗun fasalinsu dai-dai yake, kamar gargare na gittawa cikin wani gargaren.
\v 11 Sa'ad da suke matsawa, suna tafiya a dukkan shiyyoyi huɗun. kuma ba tare da juyawa ga wata shiyyar ba, Maimakon haka, duk inda kan yake fuskanta, nan suke bin shi. Ba su kuwa juyawa ga wata shiyya sa'ad da suke tafiya.
\s5
\v 12 Dukka jikinsu - haɗe da bayansu da hannuwansu da fukafukansu - na rufe da idanuwa, kuma idanuwan sun rufe gargarori huɗun dukka kewaye kuma.
\v 13 Sa'ad da nake saurarawa, gargarorin suna kira, "guguwa."
\v 14 Kowanne ɗayansu na da fuskoki huɗu; fuska ta fari ta Kerubim ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuma ta gaggafa ce
\s5
\v 15 Daga nan kerubobin - waɗannan ne hallitu masu rai da na gani ta Kogin Keba - suka taso.
\v 16 Duk sa'ad da Kerubobin suka matsa, gargarorin za su bi su gefensu, kuma duk sa'ad da kerubobin suka ɗaga fukafukansu su tashi daga ƙasa, gargarorin ba su juyewa. Suna dai tsaye a gefensu.
\v 17 Sa'ad da kerubobin suka tsaya cik, gargarorin suma sai su tsaya cik, kuma idan suka tashi sama, gargarorin suma sai su tashi tare da su, gama ruhun halittar mai rai na cikin gargarorin.
\s5
\v 18 Sa'an nan ɗaukakar Yahweh ta fita daga ƙyauren gidan ta tsaya a kan kerubobin.
\v 19 Kerubobin suka ɗaga fukafukansu suka tashi daga ƙasa a fuskata sa'ad da suka fita, gargarorin kuma suka yi kamarsu a gefensu. Suka tsaya a bakin kofar shiga ta wajen gabas, ta gidan Yahweh, sai ɗaukakar Allah na Isra'ila ta zo gare su daga sama.
\s5
\v 20 Waɗannan ne halittu masu rai dana gani a ƙarƙashin Allah na Isra'ila ta Kogin Keba, shi yasa na sani cewa su keruubobi ne!
\v 21 Kowannen su na da fuskoki huɗu da fukafukai huɗu, da kamannin hannuwan mutum a ƙarƙashin fukafukansu,
\v 22 kuma kamannin fuskokinsu na kama da wadda na gani a ruya a Kogin Keba, kuma kowannen su ya tafi gaba kai tsaye.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Sai Ruhun ya ɗago ni sama ya kawo ni ƙyauren gabas na gidan Yahweh, yana kuma fuskantar gabas, a bakin ƙofar akwai mutum ashirin da biyar. Na ga Yãzaniya ɗan Azzu da Felatiya ɗan Benayya shugabanin mutanen, a cikinsu.
\s5
\v 2 Allah ya ce mani, "Ɗan mutum, waɗannan ne mutanen da ke ƙirkiro zunubai da kuma yin miyagun shirye-shirye a wannan birnin.
\v 3 Suna cewa, 'Ba yanzu ne lokacin gina gidaje ba, wannan birnin shi ne tukunyar, kuma mu ne naman.'
\v 4 Saboda haka ka yi annabci gãba da su. Ɗan mutum, ka yi annabci."
\s5
\v 5 Sai Ruhun Yahweh ya sauko mani ya kuma ce mani, "Ka ce: Ga abin da Yahweh ya ce, "Gidan Isra'ila wannan shi ne abin da kuke cewa; gama na san abin da ke tafiya a zuciyarku.
\v 6 Kun yawaita mutanen da kuka kashe a wannan birnin kuma kun cika karafku da su.
\v 7 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Mutanen da kuka kashe, waɗanda kuka sa jikunansu a tsakiyar UYerusalem, su ne naman, kuma wannan birnin ne tukunyar. Amma za a fitar daku daga tsakiyar wannan birnin.
\s5
\v 8 Kun ji tsoron takobi, saboda haka ina tahowa da takobi a kanku - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.
\v 9 Zan fitar daku daga cikin birnin, in sa ku a hannun bãƙi, gama zan kawo hukunci a kanku.
\v 10 Za ku faɗi ta takobi. Zan hukunta ku a cikin iyakar Isra'ila domin ku sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 11 Wannan Birnin ba zai zama tukunyar dahuwarku ba, ko ku zama naman cikinta ba. Zan hukunta ku a kan iyakar Isra'ila.
\v 12 Sa'an nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh, wanda kuka ƙi yin tafiya bisa ga tafarkinsa wanda kuma kuka ƙi aikata umarninsa. Maimakon haka, sai kuka aikata dokokin al'umman da ke kewaye daku."
\s5
\v 13 Hakanan kuma sa'ada da nake annabci, Felatiya ɗan Benayya, ya rasu. Sai na faɗi fuskata a ƙasa na yi kuka da murya mai ƙarfi na ce, "Kash, ya Ubangiji Yahweh, za ka hallakar da ragowar Isra'ila ne kakaf?"
\s5
\v 14 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 15 "Ɗan mutum, 'yan'uwanka! 'Yan'uwanka! Mutanen danginka da dukkan gidan Isra'ila! Dukkansu ne waɗanda a ka yi magana game da su ta wurin waɗanda ke zama cikin Yerusalem, 'Su na nesa da Yahweh! Wannan ƙasar an bada ita gare mu a matsayin mallakarmu.'
\s5
\v 16 Saboda haka ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Koda shi ke na kai su nesa tsakanin al'ummai, kuma na warwatsar da su cikin ƙasahe, duk da haka na zama haikali a gare su na ɗan lokaci ƙaɗan cikin ƙasashen da suka tafi.'
\v 17 Saboda haka ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Zan tattaro ku daga mutane daban-daban, in jera ku daga ƙasashen da kuka warwatse, sai in ba ku ƙasar Isra'ila.
\v 18 Sa'an nan za su je wurin su cire dukkan abin banƙyama da dukkan ayyukan banƙyama daga wancan wurin.
\s5
\v 19 Zan ba su zuciya ɗaya, kuma zan sa sabon ruhu a cikin su. Zan ɗauke zuciyar dutse daga jikinsu in ba su zuciyar tsoƙa,
\v 20 domin su yi tafiya cikin tafarkina, za su kiyaye ka'idodina su kuma aikata su. Sa'an nan za su zama mutanena, Ni kuma in zama Allahnsu.
\v 21 Amma ga waɗanda ke tafiya tare da sha'awar abin ƙyamarsu da taƙaicinsu, Zan kawo masu ayyukansu ga kawunansu - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh."
\s5
\v 22 Kerubobin suka ɗaga fukafukansu da gargarorinsu da ke a gefensu, ɗaukakar Allah na Isra'ila kuma ta kasance a can sama bisansu.
\v 23 Sa'an nan ɗaukakar Yahweh ta fito daga cikin tsakiyar birnin ta kuma tsaya a tsauni ta gabashin birnin.
\s5
\v 24 Ruhun ya ɗago ni ya kawo ni cikin Kaldiya, gun 'yan zaman ɓauta, a wahayi daga Ruhun Allah, kuma wahayin da na gani ya fito daga gare ni.
\v 25 Sai na furtawa masu zaman bautar dukkan abubuwan Yahweh da na gani.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, kana zama a cikin gidan tayarwa, inda suna da idanuwan gani amma ba su gani; inda kuma suna da kunnuwan ji amma ba su ji. Saboda su gidan tayarwa ne.
\s5
\v 3 Saboda haka kai ma, ɗan mutum, ka shirya kayanka domin zaman bauta, kuma ka tashi da rana a fuskarsu, domin zan sa kaje zaman bauta a fuskarsu daga wurin da kake zuwa wani wurin. Watakila za su fara gani, koda shi ke su gidan tayarwa ne
\s5
\v 4 Za ka fitar da kayayyakinka na zaman bauta da rana a fuskarsu; jeka waje da yamma a fuskarsu a hanyar da kowa ke zuwa zaman bauta.
\v 5 Ka huda rami a bango a fuskarsu, kuma ka fita ta wurin.
\v 6 A fuskarsu, ka ɗauki kayayyakinka kan kafaɗarka, ka kawo su waje a cikin duhu. Ka rufe fuskarka, gama lallai ba za ka ga ƙasar ba, tunda na sa ka kamar alama ne ga gidan Isra'ila."
\s5
\v 7 Sai na yi hakan, kamar dai yadda aka umarce ni. Na kawo kayan zaman bautata da rana, kuma da yamma na huda rami da hannu a bango. Na fitar da kayana waje a duhun, sai na sa su a kafaɗata na ɗaga sama a fuskarsu.
\s5
\v 8 Sai maganar Yahweh ta zo mani da safe, cewa,
\v 9 "Ɗan mutum, ko gidan Isra'ila, gidan tayarwar nan, ba su tambaya, 'me ka ke yi?'
\v 10 Ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan aikin annabcin ya shafe ɗan sarki a Yerusalem ne, da dukkan gidan Isra'ila wanda a cikinsa suke.'
\s5
\v 11 Ka ce, 'Ni ne alama a gare ku. Kamar yadda na yi, haka za a yi masu; za su je zaman bauta da zaman talala.
\v 12 Ɗan sarkin da ke a cikinsu zai ɗauki kayansa a kafaɗarsa da duhu, kuma ya fice ta bango. Za su huda bango su fita da kayansu. Zai rufe fuskarsa domin kar ya ga ƙasar da idanuwansa.
\v 13 Zan shimfiɗa ragata a kansa kuma zai kamu a tarkona; sa'an nan zan kawo shi Babila, da ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan su ba. Zai mutu a can.
\s5
\v 14 Ta kowacce shiyya kuma zan warwatsar da dukkan waɗanda ke kewaye da shi da za su taimaka masa da dukkan sojojinsa, kuma zan aikar da takobi biye da su.
\v 15 Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, idan na warwatsar da su cikin al'umma na kuma tarwatsar da su ko'ina a ƙasashe.
\v 16 Amma zan bar kaɗan daga cikinsu daga takobin da yunwa da annoba, saboda su bada rohoton dukkan abin ƙyamar da ke cikin ƙasar inda na ɗauke su, domin su sani Ni ne Yahweh."'
\s5
\v 17 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 18 "Ɗan mutum, ka ci gurasarka a giggice, ka kuma sha ruwanka da rawar jiki da damuwa.
\s5
\v 19 Sa'an nan sai ka ce da mutanen ƙasar, ' Ubangiji Yahweh ya ce haka game da mazaunan Yerusalem, da ƙasar Isra'ila: Za su ci abincinsu da rawar jiki kuma su sha ruwa cikin fargaba, tun da za a washe ƙasar da dukkan abin da ke ciki saboda hargitsin dukkan waɗanda ke zaune a ciki.
\v 20 Domin haka Biranen da ke da mazauna za su zama kufai, kuma ƙasar za ta zama kango; To za ku sani cewa Ni ne Yahweh."'"
\s5
\v 21 Karo na biyu kuwa, maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 22 "Ɗan mutum, Mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra'ila da ke cewa, 'Kwanakin na da tsawo, kuma dukka wahayin bai gudana ba'?
\v 23 Saboda haka, ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya ce haka: Zan kawo ƙarshen wannan karin maganar, kuma mutanen Isra'ila ba za su ƙãra amfani da ita ba.' Ka ce masu, 'Kwanakin sun kusato sa'ad da dukkan wahayoyin za su cika.
\s5
\v 24 Gama ba za ƙãra samun wahayoyin ƙarya ba ko dũba ta neman suna cikin gidan Isra'ila ba.
\v 25 Gama Ni ne Yahweh! Nakan faɗa, kuma ina aikata abin da na faɗa. Ba za a ƙãra ɓata lokaci a kan batun ba. Gama zan faɗi wannan magana a kwanakinku, gidan tayarwa, kuma tabbas zan aiwatar da shi! - wannan ne Ubangiji Yahweh ke furtawa."'
\s5
\v 26 Haka kuma maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 27 "Ɗan mutum! Duba, gidan Isra'ila ya ce, 'Wahayoyin da yake gani na kwanaki da yawa ne daga yanzu, kuma yana annabcin lokutta masu nisa ne.'
\v 28 Saboda haka ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya ce: Maganganuna ba za su ƙãra yin jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta cika - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Bugu da ƙari, maganar Yahweh ta zo mani, cewa.
\v 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci gãba da annabawan da ke annabci a Isra'ila, kuma ka faɗa wa waɗanda ke annabci daga tsammace-tsammacensu, ' Ku saurari maganar Yahweh.
\v 3 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton wawayen annabawan da ke bin ruhun kansu, amma ba su ga komai ba!
\v 4 Isra'ila, annabawanki sun zama kamar diloli a watsattsun gonaki.
\s5
\v 5 Ba ku je wurin tsagogin bango da ke kewaye da gidan Isra'ila domin ku gyara shi ba, domin ku yi tsayayya a yaƙi a ranar Yahweh ba.
\v 6 Mutanen na ganin wahayoyin ƙarya kuma su na yin annabcin ƙarya, waɗanda ke cewa, "Wannan da wancan ne furcin Yahweh." Yahweh bai aike su ba, amma ko kaɗan ba su bar sanya mutane begen saƙonninsu za su zama gaskiya ba.
\v 7 Ba ku yin wahayin ƙarya da annabcin ƙarya, ku da ke cewa, "abu kaza da abu kaza ne furcin Yahweh" sa'ad da Ni kaina ban yi magana ba?
\s5
\v 8 Saboda haka Ubangiji Yaweh ya faɗi wannan, 'Domin kun yi ƙarairayi a kan karɓar wahayi - Saboda haka Ubangiji Yahweh ya yi furcin gãba da ku:
\v 9 Hannuna zai yi gãba da annabawa masu wahayoyin ƙarya da annabcin ƙarya. Ba za su kasance a taruwar jama'ata ba, ko a sa su a cikin lissafin gidan Isra'ila ba; Ba za su tafi ƙasar Isra'ila ba. Gama za ku san cewa Ni ne Ubangiji Yahweh!
\s5
\v 10 Domin wannan, kuma saboda sun sa mutanena su kauce daga hanya da cewa, "Salama!" sa'ad da babu salama, suna gini a bangon da za su shafa farar ƙasa.'
\v 11 Ka cewa waɗanda ke shafen bangon da farar ƙasar,' zai faɗo ƙasa; za a yi ruwan sama, kuma zan aiko da guguwar da za ta sa ya faɗi, da iska mai ƙarfi da za ta rushe bangon.
\v 12 Duba, bangon zai faɗo. Waɗansu ba su ce maku, "Ina farar ƙasar da kuka shafa wa bangon ba?"
\s5
\v 13 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya ce: Zan kawo guguwar iska a fushina, kuma za a samu ambaliyar ruwan sama a hasalata! ƙurar fushina za ta hallaka shi kakaf.
\v 14 Gama zan rushe bangon da kuka shafe da farar ƙasa, kuma zan ragargaza shi har ƙasa in bar ginshiƙan a fili. Domin ya faɗo, kuma ku hallaka a tsakiyarsa. Za ku kuwa sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 15 Gama cikin fushina zan hallakar da bangon da waɗanda ke shafa masa farar ƙasa.
\v 16 wato annabawan Isra'ila da ke yin annabci a kan Yerusalem waɗanda kuma ke ganin wahayoyin salama dominta. Amma babu salama!- wannan furcin Ubangiji Yaweh ne."'
\s5
\v 17 Saboda haka, ɗan mutum, ka sa fuskarka gãba da 'ya'ya mata na mutanenka da ke annabci daga nasu tunanin, kuma ka yi annabci gãba da su.
\v 18 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton matayen da ke ɗinka layun dabo a dukkan ɓangarorin hannunsu suna kuma yin gyalulluka domin kawunansu da kowanne irin fasali, suna amfani da shi a farautar mutane. Za ku farauci mutanena amma ku ceci ranku?
\s5
\v 19 Kun ɓãta ni a cikin mutanena domin a ba ku ɗan danƙin bali da gutsiren gurasa, ku kashe mutanen da bai dace su mutu ba, da kuma barin waɗanda bai dace su rayu ba su rayu, saboda karairayi da kuke yiwa mutanena da ke jinku.
\s5
\v 20 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ina gãba da dabo da layun da kuka yi aiki da su domin ku yiwa rayukan mutane tarko kamar tsuntsaye. Hakika zan yayyage su daga hannuwanku; kuma mutanen da kuka cafko kamar tsuntsaye - Zan sake su su tafi.
\v 21 Zan yayyage gyalullukanku na tsafi in ceci mutanena daga hannunku, saboda ka da su ƙara faɗawa a tarkon hannuwanku. Za ku kuwa sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 22 Saboda kun karya zuciyar mutum mai adalci da ƙarairayi, koda yake Ni ban yi niyyar karya zuciyarsa ba, kuma domin kun ƙarfafa wa mugu gwiwa domin kar ya juyo daga hanyarsa ya ceci ransa -
\v 23 to ba za ku ƙara ganin wahayoyin ƙarya ko ku ci gaba da yin annabcin ƙarya ba, gama Zan ceci mutanena daga hannunku. Za ku sani cewa Ni ne Yahweh,"'
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Waɗansu daga cikin dattawan Isra'ila suka zo wurina suka zauna a gabana.
\v 2 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 3 "Ɗan mutum waɗannan mazajen sun ɗauki gumakansu cikin zukatansu sun kuma sa tuntuɓen zunubansu a gaban fuskokinsu. Za su ma roƙe ni wani abu kuwa?
\s5
\v 4 Saboda haka ka sanar da wannan gare suka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duk mutumin gidan Isra'ila wanda ya ɗauki gumaka ya sa a zuciyarsa, ko ya sa tuntuɓen zunubansa a gaban fuskarsa, kuma ya zo gun Annabi - Ni, Yahweh, zan amsa masa bisa ga yawan gumakansa.
\v 5 Zan yi wannan domin Zan iya ɗauke gidan Isra'ila daga cikin zukatansu da ke nesa da ni ta dalilin gumakansu.'
\s5
\v 6 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila. 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ku tuba ku juyo daga gumakanku! Ku juya fuskokinku baya daga dukkan haramtattun ayyukanku.
\s5
\v 7 Domin duk wanda yake daga gidan Isra'ila da duk wanda ke cikin bãƙin da ke zaune a Isra'ila da suka rabu da ni, wanda ke ɗauke da gumaka cikin zuciyarsa ya sa abin tuntuɓe na zunubansa a furkarsa, kuma ya zo gun annabi ya roƙe ni - Ni, Yahweh, zan amsa masa da kaina.
\v 8 Saboda haka zan sa fuskata gãba da mutumin nan in maida shi alama da karin magana, gama zan yanke shi daga tsakiyar mutanena, kuma za ku sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 9 Idan a ka ruɗi annabi ya faɗi sãƙo, daga nan Ni, Yahweh, zan ruɗi annabin nan; Zan miƙa hannuna gãba da shi kuma in hallaka shi daga tsakiyar mutanena Isra'ila.
\v 10 Za su ɗauki laifofinsu; laifin annabi zai zama dai-dai da laifin wanda ke zuwa nema daga gare shi.
\v 11 Saboda wannan, gidan Isra'ila ba zai ƙara bijirewa ba daga bi na ko su ƙazamtar da kansu ta wurin bin dukkan laifofinsu. Za su zama mutanena, Ni kuma zan zama Allahnsu - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne,"'
\s5
\v 12 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 13 "Ɗan mutum, Idan ƙasa ta yi zunubi gãba da ni ta aikata laifi har Na fitar da hannuna gãba da ita na karya sandar gurasarta, kuma Na aiko yunwa a kanta kuma na datse mutum da dabba daga ƙasar;
\v 14 to ko mutanen nan guda uku - Nuhu da Daniyel da Ayuba - suna cikin tsakiyar ƙasar, za su dai iya ceton ransu ne kawai ta ayyukansu na adalci - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 15 Idan na aiko miyagun bisashe ta ƙasar na maida ita bakarariya saboda ta zama kufai inda ba mutum da zai iya wucewa saboda bisashen,
\v 16 daga nan ko waɗannan mutum ukun kuma na ciki - Muddin ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - ba za su iya su ceto ko da "ya'yansu maza ko mata ba; Rayukansu ƙadai za su iya cetowa, amma ƙasar za ta zama watsattsiya.
\s5
\v 17 Ko idan na kawo takobi gãba da ƙasar na ce, 'Takobi, je ta cikin ƙasar ki datse mutum da dabba daga cikinta,
\v 18 daga nan ko waɗannan mutane ukun suna tsakiyar ƙasar- muddin Ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - ba za su iya su ceto ko da ma 'ya'yansu maza ko mata ba; rayukansu ƙaɗai za su iya cetowa.
\s5
\v 19 Ko idan na aiko da annoba gãba da ƙasar nan kuma na zubo fushina gãba da ita ta wurin zubda jini, saboda in datse mutum da bisã,
\v 20 daga nan ko da Nuhu da Daniyel da Ayuba na cikin ƙasar - muddin ina raye, furcin Ubangiji Yahweh - Ba za su iya su ceto ko da ma 'ya'yansu maza da mata ba; rayukansu ne kawai za su iya cetowa ta wurin ayyukan adalcinsu.
\s5
\v 21 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Zan maida abubuwa su fi haka ɓaci tabbas ta wurin aikowa da hukuntaina - yunwa da takobi da namomin jeji, da annoba - gãba da Yerusalem domin in datse mutum da bisã daga cikinta.
\s5
\v 22 Duba! duk da haka, Za a bar ragowa a cikinta, waɗanda suka rayu da za su fito da 'ya'ya maza da mata. Duba Za su fita zuwa wurinku, kuma za ku ga hanyoyinsu da ayyukansu sai ku ƙarfafa game da horon da Na aiko a Yerusalem, da a kan komai da na aiko gãba da ƙasar.
\v 23 Waɗanda suka rayu za su ta'azantar da ke sa'ad da kika ga hanyoyinsu da ayyukansu, saboda ku san dukkan waɗannnan abubuwan da na yi gãba da ita, cewa ban yi su a banza ba! wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, yaya kuringar inabi ta fi kowanne itace mai rassa da ke kurmi kyau?
\v 3 Mutane na ɗaukar katako daga kuringar inabi su yi wani abu da shi? Ko kuwa su yi maratayi daga gare ta su rataya wani abu a kai?
\v 4 Duba! Idan aka jefa ta cikin wuta kuma idan wutar ta ƙone dukka sassa biyu na ƙarshenta da kuma na tsakiya, za a iya yin wani amfani?
\s5
\v 5 Duba! Sa'ad da ta kai ƙarshe, ba za ta iya yin komai ba; tabbas, sa'ad da wutar ta ƙona ta, to ba za ta yi wani abin amfani ba.
\v 6 Domin haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ba kamar itatuwan dazuzzuka ba, Na ba da kuringar inabi ta zama abin ƙonawa ga wuta; Kamar haka zan yi ga mazaunan Yerusalem.
\s5
\v 7 Gama zan sa fuskata gãba da su. koda yake sun fito daga wutar, duk da haka wutar ba za ta cinye su ba; da haka za ku sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na sa fuskata gãba da su.
\v 8 Sa'an nan zan maida ƙasar watsattsen kufai domin sun aikata zunubi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka sanar da Yerusalem game da haramtattun ayyukanta,
\v 3 ka kuma furta, 'Ubangiji Yahweh faɗi wannan ga Yerusalem: Farkonki da haihuwarki sun faru a ƙasar Kan'ana ne; Mahaifinki Ba'amore ne, mahaifiyarki Bahitiya ce.
\s5
\v 4 A ranar haihuwarki, mahaifiyarki bata yanke cibiyarki ba, balle ta tsabtace ki a ruwa ko ta shafe ki da gishiri, ko ta rufe ki da tsumma.
\v 5 Babu idon da ya tausaya maki ya yi wani abu daga cikin waɗannan domin ki, ya ji tausayinki. Aranar da aka haife ki, domin ƙin jininki, an jefa ki waje a fili.
\s5
\v 6 Amma na bi ta wurinki, kuma na ga kina motsi cikin jininki; sai Na ce da ke a cikin jininki, "Ki rayu!" Na ce da ke a cikin jininki, "Ki rayu!"
\v 7 Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yawaita kin kuma zama da girma, kika zama abin ƙauna sosai kuma kin kai ga sa kayan ado. Nonnanki sun tsaya tantsan-tantsan, kuma gashin kanki ya yi kauri, koda shi ke ki na tsirara tumɓur.
\s5
\v 8 Na bi ta wurin da kike kuma, na kuma gan ki. Duba! lokacin ƙauna ya zo maki, sai na rufe ki da bargo na rufe tsiraicinki. sa'an nan na yi maki rantsuwa na kawo ki ga alƙawari - kika kuma zama tawa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 9 Sai na wanke ki da ruwa, na kuma wanke ki daga jini, sai na shafe ki da mai.
\v 10 Na suturta ki da ɗinkakken tufafi na sa maki takalman fãta a ƙafafunki. Na naɗe ki da linin mai kyau na rufe ki da silki.
\v 11 Biye da haka na yi maki ado da sarƙoƙi masu daraja, sai na sa maki sarƙar hannu, da sarƙa kewaye da wuyanki.
\v 12 Na sa zoben hanci a hancinki, da 'yan kunne a kunnuwanki, da kambi a kanki.
\s5
\v 13 Saboda haka an yi maki ado da zinariya da azurfa, kuma an suturta ki da linin mai kyau da silki da ɗinkakkun kaya; kin ci gari mai kyau da zuma da mai, kuma kika zama kyakkyawa, sai kika zama sarauniya.
\v 14 Shahararki ta kai ga al'ummai saboda kyaunki, gama cikakkiya ce a cikin darajar da na ba ki - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 15 Amma kin dogara ga kyaunki, kuma kin yi kamar karuwa saboda shahararki; kin zubo ayyukan karuwancinki ga duk wanda ke wucewa, saboda kyaunki ya zama nasa.
\v 16 Sa'an nan kika ɗauki tufafinki kuma da su kika yiwa kanki masujadai masu ado da launuka daban-daban, a wurin kuma kika yi kamar karuwa. Bai kamata hakan ya faru ba. ko irin wannan abin ya kasance.
\s5
\v 17 Kin ɗauki kyawawan kayan adonki na zinariya da azurfa da na ba ki, sai kika yiwa kanki siffofin mazaje, sai ki ka yi da su kamar yadda karuwa ke yi.
\v 18 Kika ɗauki tufafinki da a ka yi aikin ɗinki mai kyau kika rufe su, sai kika ajiye maina da turarena a gabansu.
\v 19 Gurasata na ba ki - wanda aka yi da lallausan gari da maida zuma - kin ajiye su domin kamshi mai daɗi, gama abin da ya faru kenan - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 20 Sa'an nan kuka ɗauki 'ya'yanku maza da mata da kuka haifa mani, kuka kuma yi hadaya da su ga siffofin domin su lanƙwame kamar abinci. Ayyukan karuwancinku ƙaramin abu ne?
\v 21 Kun yanka 'ya'yana kuka sa su a cikin wutar.
\v 22 A cikin dukkan abin ƙyamarku da ayyukan karuwancinku ba ku yi tunani a kan kwanakin kuruciyarku ba, a sa'ad da kuke tsirara tumɓur sa'ad da kuke birgima cikin jininku.
\s5
\v 23 Kaito! Kaitonki! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda haka, a kan dukkan wannan muguntar,
\v 24 kin gina wa kanki sãƙon tsafi a kowanne wurin taruwar jama'a.
\s5
\v 25 Ki ka gina wurin tsafi a kan kowacce hanya kuma kin wulaƙanta kyaunki, gama kin bada kanki ga kowanne mai wucewa kuma kika ƙara yin ayyukan karuwanci.
\v 26 Kika yi kamar karuwa tare da Masarawa, makwabtanki masu sha'awace-sha'awace, kika kuma aikata ayyukan karuwanci da yawa, ki na ta sani fushi.
\s5
\v 27 Duba! Zan cake ki da hannuna in yanke abincinki. Zan miƙa ranki ga maƙiyanki, 'yan matan Filistiyawa, waɗanda suka ji kunyar halinki na lalata.
\v 28 Kin yi kamar karuwa tare da Asiriyawa saboda ba ki ƙoshi ba. Ki ka yi kamar karuwa amma dai ba ki ƙoshi ba.
\v 29 Kin ƙara aikata ayyukan karuwanci da yawa a ƙasar attajiran Kaldiya, kuma ko wannan ma bai ƙosar da ke ba.
\s5
\v 30 Yaya ciwon zuciyarki yake - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - cewa za ki yi dukkan waɗannan abubuwan, ayyukan bankunya na karuwanci?
\v 31 Kin gina wurin tsafinki a kan dukkan tituna kuma ki ka sa sãƙon tsafinki a dukkan wurin taruwar jama'a. Duk da haka ke ba kamar karuwa ba ce saboda kin ƙi karbar biya.
\s5
\v 32 Ke mazinaciyar mace, kin amince da kwartaye a maimakon mijinki.
\v 33 Mutane na biyan kowacce karuwa, amma ke kina bada ladarki ga dukkan masoyanki kina kuma ba su cin hanci su zo wurin ki daga ko'ina domin ayyukan karuwancinki.
\v 34 Saboda haka akwai bambanci tsakaninki da waɗancan matayen, tun da ba mai zuwa wurinki ya sa ki kwana da shi, a maimakon haka kina biyan su. Babu mai biyan ki.
\s5
\v 35 Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Yahweh.
\v 36 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Saboda kin zubo sha'awace-sha'awacenki waje kika kuma buɗe tsiraicinki ta wurin ayyukan karuwanci da dukkan masoyanki da dukkan ƙazaman gumakanki, kuma saboda jinin 'ya'yanki da kika miƙawa gumakanki,
\v 37 saboda haka, Duba! Zan tara dukkan masoyanki da kika sadu da su, dukkan waanda kike so da waɗanda kike ƙi, kuma zan tara su gãba da ke a ko'ina. Zan fallasa tsiraicinki wurinsu domin su ga dukkan tsiraicinki.
\s5
\v 38 Gama zan hukunta ki saboda zina da zubda jini, kuma zan kawo maki zubda jinin fushina da shauƙi.
\v 39 Zan bada ke a hannunsu saboda su jefar da sãƙon tsafiinki ƙasa su kuma rurrushe wuraren tsafinki su kuma tuɓe maki tufafinki su ɗauki dukkan kayan adonki. Za su bar ki tsirara tumɓur.
\s5
\v 40 Sa'an nan za su tara maki jama'a gãba da ke su jejjefeki da duwatsu, kuma su daddatsa ki da takkubansu.
\v 41 Za su ƙone gidajenki su yi abubuwan hukuntawa da yawa a kanki a gaban mata da yawa, gama zan tsayar da karuwancinki, ba za ki kuma biya masoyanki ba.
\v 42 Sa'an nan ne zan kwantar da fushina a kanki; fushina zai bar ki, gama zan gãmsu, kuma ba zan ƙara yin fushi ba.
\s5
\v 43 Saboda ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba kuma kin sa na girgiza da fushi saboda dukkan waɗannan abubuwan, Domin haka, Duba! Ni kaina zan aiko hukunci a kanki domin abin da kika yi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. Ba za ki ƙara karuwanci da dukkan sauran kazamtattun ayyukanki ba?
\s5
\v 44 Duba! Duk mai faɗin karin magana game da ke zai ce, "Kamar yadda uwa take, haka ma 'yarta take."
\v 45 Ke ɗiyar mahaifiyarki ce, wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta, kuma ke 'yar'uwar 'yan'uwanki ne waɗanda suka ƙi mazajensu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahitiya ce, kuma mahaifinki Ba'amore ne.
\s5
\v 46 Yãyarki Samariya ce 'ya'yanta mata kuma su ne ke zama a Arewa, ƙanwarki kuma ita ce wadda ke zama a kudu da ke, wato Sodom da 'ya'yanta mata.
\s5
\v 47 Ba tafiya a hanyarsu da bin halayensu da ayyukansu kawai kika yi ba, amma a dukkan hanyoyinki kin zama fiye da yadda suke.
\v 48 Da dawwamata - wannan furcin Yahweh ne - Yar'uwarki Sodom da 'ya'yanta mata, ba su yi yawan mugunta kamar yadda ke da 'ya'yanki mata suka yi ba.
\s5
\v 49 Duba! Wannan ne zunubin 'yar'uwarki Sodom: ta na da kumbura kai a cikin wadataccen jin daɗi da zaman sangarcewa da rashin kulawa da komai. Ba ta ƙarfafa hannun talakawa da masu buƙata ba.
\v 50 Ta zama mai kumbura kai da aikata ayyukan ƙyama a gabana, saboda haka na ɗauke su kamar yadda kuka gani.
\s5
\v 51 Ko Samariya bata aikata rabin zunubanki ba; maimakon haka ma, kin yi ayyukan ƙyama da yawa fiye da yadda suka yi, kuma kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kirki saboda dukkan abubuwan ƙyama da kika yi!
\v 52 Ke musamman, kin nuna kunyar kanki; a wannan hanyar kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kyau, saboda laifofin da kika aikata a dukkan hanyoyin banƙyaman nan. 'Yan'uwanki yanzu sun nuna alamar fin ki kyau. Ke musamman, kin nuna kunyar kanki, gama a wannan hanyar kin nuna cewa 'yan'uwanki sun fi ki kyau.
\s5
\v 53 Gama zan komo da wadatarsu - wadatar Sodom da'ya'yanta da wadatar Samariya da 'ya'yanta; amma wadatarki zata kasance a cikinsu.
\v 54 A game da waɗannan abubuwan kuwa za ki nuna kunyarki; za a wulaƙanta ki saboda dukkan abubuwan da kika yi, kuma a sa'an nan ne za ki zama mai ta'azantarwa a gare su.
\v 55 Saboda haka 'yar'uwanki Sodom da 'ya'yanta mata za a komo da su kamar yarda suke a dã. Samariya kuma da 'ya'yanta mata za a komo masu da matsayinsu na dã.
\s5
\v 56 Ba ki ambato 'yar'uwarki Sodom da bakin ki ba a kwanakin da kike fahariya.
\v 57 kafin muguntarki ta bayyanu. Amma yanzu kin zama abar zargi ga 'ya'ya mata na Idom da kuma dukkan 'ya'ya mata na Filistiyawa kewaye da ita. Dukkan mutanen da ke kewaye na raina ki.
\v 58 Za ki nuna kunyarki da aikin banƙyamarki! wannan furcin Yahweh ne!
\s5
\v 59 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan yi da ke yadda kika cancanta, ke da kika raina rantsuwarki ta wurin karya alƙawari.
\s5
\v 60 Amma ni da kaina zan tuna da alƙawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki, kuma zan kafa madawamin alƙawari da ke.
\v 61 Sa'an nan ne za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya a sa'ad da kika ƙarɓi yãyarki da ƙanwarki. Zan ba ki su a matsayin 'ya'yanki mata, amma ba saboda alƙawarinki ba
\s5
\v 62 Ni da kaina zan ƙulla alƙawarina da ke, kuma za ki san cewa ni ne Yahweh.
\v 63 Saboda waɗannan abubuwan, za ki tuna da komai ki kuma ji kunya, saboda haka ba za ki sake buɗe bakinki ki yi magana ba saboda kunya, sa'ad da na gafarce ki a kan dukkan abin da kika yi - wannan furcin Yahweh ne."'
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, faɗi kacici-kacici da kuma misali ga mutanen Isra'ila.
\v 3 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: Wani babban gaggafa mai manyan fikafikai da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ya je Lebanon ya kama saman kan itacen sida.
\v 4 Ya karya kan tohonsa mafi tsawo ya ɗauko su zuwa ƙasar Kan'ana; ya shuka su a birnin fatake.
\s5
\v 5 Sai kuma ya ɗauki wani iri na ƙasar ya dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa kamar itacen warɗi.
\v 6 Sai ya yi toho ya zama kuringa mai yaɗuwa har ƙasa. Rassansa suka tanƙwasa wajensa, saiwoyinsa suka kama ƙasa sosai. Domin haka ya zama kuringa ya yi rassa da toho.
\s5
\v 7 Amma akwai wani babban gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuringa ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen gaggafan, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajensa tun daga inda aka dasa ta domin ya rika yi ma ta ban ruwa.
\v 8 An dasa ta a wuri mai kyau da danshi inda akwai ruwa da yawa domin ta yi rassa ta kuma ba da 'ya'ya, ta zama kuringar inabi ta ƙwarai.'
\s5
\v 9 Ka cewa mutanen, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: Ko za ta wadatu? Ba za a iya cire ta a kuma ɗebe 'ya'yanta domin kada su yi yaushi, kuma dukkan ganyayenta masu kyau su yanƙwane ba? Babu wani abu ko mutane masu yawa da a ke buƙata da su cire ta daga jijiyoyinta.
\v 10 To duba! bayan an sake dasa ta, za ta sake yin girma? Ba za ta yanƙwane ba idan iskar gabas ta hura ta? Babu shakka za ta yanƙwane ga baki ɗaya daga tushenta.'"
\s5
\v 11 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 12 "Ka yi magana da 'yan tawayen gidan, 'Ba ku san mene ne waɗannan abubuwa ke nufi ba? Duba! Sarkin Babila ya zo Yerusalem ya kuma tafi da sarkinta da yarimanta ya kai su zuwa gare shi Babila.
\s5
\v 13 Sai ya ɗauki wani daga zuriyar sarauta, ya yi alƙawari da shi, ya kuma ɗauki rantsuwa da shi. Ya ɗauke mutane na ƙasar masu iko,
\v 14 domin mulkin ya zama da rauni har ƙasar ta kasa ɗaga kanta. Ta wurin kiyayye alƙawarinsa ƙasar za ta tsira.
\s5
\v 15 Amma sarkinYerusalem ya yi masa tawaye ta wurin aikawa da jakadai zuwa Masar domin a ba shi dawakai da sojoji. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin waɗannan abubuwa zai tsira? Idan ya karya alƙawari, zai iya tsira?
\v 16 Da dawwamata -wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - babu shakka zai mutu a cikin ƙasar sarki wanda ya naɗa shi sarauta, sarkin da ya rena rantsuwarsa, wanda kuma ya karya alƙawarinsa. Zai mutu a tsakiyar Babila.
\s5
\v 17 Fir'auna da sojojinsa masu ƙarfin yaƙi da kuma jama'arsa masu yawa domin yaƙi ba za su tsare shi ba a wannan yaƙin, sa'ad da Babilawa suka gina hasumiyoyi da kagarai don su kashe rayuka masu yawa.
\v 18 Gama sarkin bai cika rantsuwar alƙawarinsa ba. Duba ya miƙa hannunsa ga yin alƙawari duk da haka ya aikata dukkan waɗannan abubuwa. Ba zai kuɓuta ba.
\s5
\v 19 Domin haka ni Ubangiji Yahweh na faɗi wannan: Da dawwamata, ba rantsuwata da alƙawarina ya rena ya kuma karya ba? Saboda ha ka zan ɗora hukuncinsa a kansa!
\v 20 Zan kafa masa tarko in kama shi, kuma za a kama shi a tarkon farautata. Sa'an nan zan kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda cin amana da kuma tayawar da ya yi mani!
\v 21 Dukkan 'yan gudun hijira cikin sojojinsa za a kashe su da takobi, sauran da suka ragu za a watsar da su ko'ina. A sa'an nan ne za su sani cewa Ni ne Yahweh; Na furta wannan zai faru."
\s5
\v 22 Ubangjji Yahweh ya faɗi wannan, 'Saboda haka ni kaina zan cire toho a kan itacen sida mai tsawo, zan kuma sake dasa shi daga sashen jikin rassansa. Zan karye shi, ni da kaina kuma zan dasa shi a tsauni mai tsayi.
\v 23 Zan dasa shi a kan tsaunukan Isra'ila domin ya fito da rassa, ya bada 'ya'ya, ya kuma zama itacen sida na gaske saboda kowanne tsuntsu mai fiffike ya zauna a ƙarƙashinsa. Za su yi sheƙa a cikin inuwar rassansa.
\s5
\v 24 Sa'an nan dukkan itatuwan jeji za su sani cewa Ni ne Yahweh. Na kan kawo manyan itatuwa ƙasa sa'an nan in tada ƙananan itatuwa sama. Zan sa ɗanyen itace ya bushe in kuma sa busashen itace ya zama ɗanye. Ni ne Yahweh, Na furta wannan zai faru; na kuma yi shi.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni, cewa,
\v 2 "Me kuke nufi, ku da kuka yi amfani da wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa, 'Mahaifa sun ci 'ya'yan inabi masu tsami, hakoran 'ya'yansu kuma sun dakushe'?
\s5
\v 3 Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba za a ƙara samun wani dalili da za ka sake amfani da wannan karin magana a Isra'ila ba.
\v 4 Ga shi! Kowanne rai nawa ne - ran mahaifi duk da na ɗan, dukka nawa ne! Wanda ya yi zunubi shi zai mutu!
\s5
\v 5 Me za a ce a kan mutum wanda yake shi adali ne yana kuma aikata shari'a da adalci--
\v 6 idan ba ya cin abinci a kan tsaunuka ko ya sa idanunsa a kan allolin da ke gidan Isra'ila, bai kuma kwana da matar maƙwabcinsa ba, ko ya Kwana da mace a lokacin hailarta, wannn mutum adali ne?
\s5
\v 7 Me za a ce a kan mutum wanda ba ya ƙuntatawa kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace amma ya kan bada abinci ga mayunwanci, yakan ba huntu tufa, wannan mutum adali ne?
\s5
\v 8 Me za a ce da mutumin da ba ya bada bashin kuɗi da ruwa; ko tare da wani ƙari a kan abin da ya sayar? Haka yake ce da shi yana goyon bayan gaskiya a tsakanin masu gaskiya, yana kuma tabbatar da adalci a tsakanin mutane.
\v 9 Amma idan mutumin yana tafiya cikin farillaina yana kuma bin ka'idodina da gaskiya, daga nan alƙawarin wannan mutum mai adalci shi ne: hakika zai rayu! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 10 Amma da a ce yana da ɗa wanda ya zama ɗan fashi mai kisankai yana kuma yin waɗannan abubuwa masu yawa kamar yadda a ka nuna su a nan,
\v 11 koda mahaifinsa ba ya yin ɗaya daga waɗannan abubuwa, amma yana cin abinci a kan tsaunuka ya kuma kwana da matar maƙwabcinsa, me za a ce game da shi?
\s5
\v 12 Wannan mutum yana cin zalin matalauta da masu buƙata, yana kuma yin ƙwace da fashi, ba ya mayar da abin da a ka jinginar masa, yana bautawa gumaka yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,
\v 13 yana bada rancen kuɗi da ruwa, yana cin riba ta fitar hankali a kan abin da ya sayar, shin wannan mutum zai rayu? Babu shakka ba zai tsira ba! Lallai ne zai mutu kuma alhakin jininsa yana a kansa domin ya yi munanan abubuwa.
\s5
\v 14 Amma idan akwai mutum da ya haifi ɗa, kuma ɗan nasa ya ga dukkan zunuban nan da mahaifinsa ya yi, koda ya gan su, amma shi bai yi waɗannan abubuwa ba.
\v 15 Wannan ɗa bai ci abinci a kan tsaunuka ba, bai kuma sa idanunsa ga gumakan gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, me za a ce game da shi?
\s5
\v 16 Wannan ɗa bai ci zalin kowa ba, ko ya ƙarbi jingina, ko ya saci wasu abubuwa, amma a maimakon haka yana bada abincinsa ga mayunwaci, yana ba huntu tufafi.
\v 17 Wannan ɗan ba ya zaluntar kowa ko ya bada bashi da ruwa ko kuma ya ci ƙazamar riba a kan bashin, amma yana bin ka'idodina, yana kuma tafiya bisa ga farillaina; wannan ɗa ba zai mutu ba saboda zunubin mahaifinsa: Lallai za ya rayu.
\s5
\v 18 Mahaifinsa kuwa, da yake ya ƙuntatawa wasu ta wurin zaluntarsu, ya yiwa ɗan'uwansa ƙwace, ya kuma aikata abubuwa marasa kyau a cikin mutanensa - zai mutu saboda muguntarsa.
\s5
\v 19 Amma kun ce, 'Me ya sa ɗa ba zai ɗauki laifin mahaifinsa ba?' Domin ɗan ya bi shari'a da adalci kuma ya bi dukkan umarnaina; ya yi su dai-dai. Babu shakka za ya rayu!
\v 20 Shi wanda ya yi zunubi, shi ne wanda zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki laifin mahaifinsa ba, haka nan mahaifi ba zai ɗauki laifin ɗansa ba. Adalcin wanda ya yi dai-dai ai nasa ne, muguntar azzalumi zata kasance a kansa.
\s5
\v 21 Amma idan mugu ya juya daga dukkan zunubansa wanda ya aikata ya kiyaye umarnaina ya bi shari'a da adalci, lallai za ya rayu ba zai mutu ba.
\v 22 Dukkan muguntar da ya aikata ba za a neme su a kansa ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi.
\s5
\v 23 Ina murna da mutuwar mugu ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba juyowa daga muguwar hanyarsa ba domin ya rayu?
\s5
\v 24 Amma idan adalin mutum ya bar yin adalcinsa, ya aikata haramtattun ayyuka kamar dukkan haramtattun ayyuka waɗanda wannan mugun mutum ya aikata, daga nan sai ya rayu? Dukkan adalcin da ya aikata ba za a tuna da su ba idan ya ci amanata da laifin da ya aikata. To zai mutu a cikin zunuban da ya aikata.
\s5
\v 25 Amma kun ce, 'Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce!' Ku ji ya ku gidan Isra'ila! Hanyata ba dai-dai ba ce? Ashe ba hanyarku ce ba dai-dai ba?
\v 26 Sa'ad da mutum adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda su, zai mutu a cikin muguntar da ya aikata.
\s5
\v 27 Amma idan mugun mutum ya bar muguntar da ya yi ya zo ya aikata gaskiya da adalci, za ya rayu.
\v 28 Domin ya gani kuma ya bar dukkan laifofin da ya aikata. Babu shakka za ya rayu, ba zai mutu ba.
\s5
\v 29 Amma gidan Isra'ila suka ce, 'Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce! Gidan Isra'ila yãyã hanyata ta zama ba dai-dai ba? Ai hanyarku ce ba dai-dai ba.
\v 30 Saboda haka zan shar'anta kowanne mutum a cikinku gwargwadon ayyukansa, ya gidan Isra'ila! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne. Ku tuba daga dukkan muguntarku domin kada su zamar maku dalilin hallaka.
\s5
\v 31 Ku rabu da dukkan laifofin da kuka aikata; ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon ruhu. Me ya sa za ku mutu, gidan Isra'ila?
\v 32 Gama ba na murna da mutuwar wanda ke mutuwa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda haka sai ku tuba domin ku rayu!"
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 "Yanzu kai, sai ka yi makoki a kan shugabanin Isra'ila
\v 2 ka ce, 'Wace ce mahaifiyarka? Zakanya, tana zaune tare da ɗan zaki; a cikin tsakiyar 'yan zakoki, ta yi renon 'ya'yanta.
\v 3 Ita ce ta goyi ɗaya daga cikin 'ya'yanta ya zama ɗan zaki wanda ya koyi kamun nama, har ya cinye mutane.
\v 4 Sai al'ummai suka ji labarinsa. Sai aka kama shi cikin tarkonsu, suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar.
\s5
\v 5 Daga nan ta ga cewa koda yake ta jira dawowarsa, sa begenta a kansa yanzu ya ƙare, sai ta ɗauki ɗaya daga cikin 'ya'yanta, ta goye shi ya zama sagari.
\v 6 Wannan sagari yana ta kai da kawowa a cikin zakoki. Ya zama sagari yana kuma koyan kamun nama; ya cinye mutane.
\v 7 Ya lalatar da kagarunsu ya kuma maida biranensu kufai. ƙasar da mazaunan cikinta an bar su saboda jin rurinsa
\s5
\v 8 Amma al'ummai suka kafa masa tarko daga kowanne waje; suka baza masa tarunsu a kansa. Suka kama shi cikin tarkunansu.
\v 9 Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka kawo shi ga sarkin Babila. Suka kawo shi cikin matsaran wurare domin kada a ƙara sake jin muryarsa a kan tsaunuka Isra'ila.
\s5
\v 10 Mahaifiyarka tana kamar kuringar inabi da aka dasa a cikin jininka a gefen ruwa. Ta yi 'ya'ya da rassa da yawa saboda isasshen ruwa.
\v 11 Tana da rassa masu ƙarfi da a ke amfani da su domin sandunan masu mulki, tsayinta zuwa sama da dukkan rassan, ta yi tsayi sosai daga nesa ana iya hangen ganyenta.
\s5
\v 12 Amma aka tumɓuke kuringar inabin da fushi aka jefar da ita a ƙasa, iskar gabas ta busar da ita. Rassanta masu ƙarfi suka kakkarye suka bushe, wuta kuwa ta cinye su.
\v 13 Yanzu an dasa ta a cikin jeji, cikin busasshiyar ƙasa mai ƙishi da fari.
\s5
\v 14 Sai wuta ta fito daga manyan rassanta ta kuwa cinye 'ya'yanta, babu reshe mai ƙarfi a kanta, babu sandar da zan yi mulki.' Wannan makoki ne, kumaza a raira shi a matsayin makoki."
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Ya zamana a kan shekara ta bakwai, a rana ta goma ga watan biyar, sai dattawan Isra'ila suka zo domin su yi roƙo a wurin Yahweh suka kuma zauna a gabana.
\s5
\v 2 Daga nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 3 "Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Kun zo ku yi roƙo a wurina? Da dawwamata, ba za ku taɓa tuntuɓa ta ba! -wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'
\s5
\v 4 Za ka shar'anta su? Za ka shar'anta, ɗan mutum? Bari su san haramtattun ayyukan da ubanninsu suka aikata.
\v 5 Ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ne ya faɗi wannan: A ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna na rantse wa zuriyar gidan Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su cikin ƙasar Masar, sa'ad da na ta da hannun rantsuwa a gare su. Na ce, "Ni ne Yahweh Allahnku"-
\v 6 a wannan rana na ta da hannuna na rantsuwar alƙawari a gare su cewa zan fito da su daga ƙasar Masar zuwa cikin ƙasar dana zaɓa dominsu. Mai malalowa da madara da zuma; tana da abubuwa masu kyau da babu irinsu a dukkan ƙasashe.
\s5
\v 7 Na ce da su, "Bari kowanne ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama daga idanunsa, da gumakan Masar. Kada ku ƙazantar da kanku; Ni ne Yahweh Allahnku."
\s5
\v 8 Amma sun yi mani tawaye, ba su da niyyar sauraro na. Kowanne mutum ya ƙi watsi da abubuwan banƙyama daga idanunsa ko ya rabu da gumakan Masar, sai na shirya zan zubo masu da fushina domin in cika hasalata a cikinsu a kuma tsakiyar ƙasar Masar.
\v 9 Amma saboda sunana ban yi haka ba a idanun al'ummai da suke zama a cikinsu. Na sanar da kaina a gare su, a idanunsu, ta wurin fito da su daga ƙasar Masar.
\s5
\v 10 Sai na fitar da su daga ƙasar Masar na kawo su cikin jeji.
\v 11 Sa'an nan na ba su farillaina na sa su san ka'idodina a gare su, waɗanda idan mutum ya kiyaye su zai rayu.
\v 12 Na kuma ba su Asabatai a matsayin alama tsakanina da su, domin kuma su sani cewa Ni ne Yahweh wanda ke tsarkake su.
\s5
\v 13 Amma gidan Isra'ila suka tayar mani a cikn jeji. Suka ƙi su yi tafiya cikin farillaina; maimakon haka, sai suka ƙi ka'idodina, waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu idan ya yi biyayya da su. Sun ɓata Asabataina ƙwarai, saboda haka na ce zan zubo masu da fushina a cikin jeji domin in ƙarar da su.
\v 14 Amma sabili da sunana ban yi haka ba saboda kada a saɓi sunana a idanun al'ummai, waɗanda a kan idanunsu ne na fitar da su daga ƙasar Masar.
\s5
\v 15 Sai na kuma tada hannuna na rantse masu a cikin jeji ba zan kai su cikin ƙasar da na ba su ba, ƙasar da ta ke cike da yalwar madara da zuma, wadda tafi kyau a cikin dukkan ƙasashe.
\v 16 Nayi rantsuwa a kan wannan domin sun ƙi ka'idodina kuma sun ƙi yin tafiya cikin farillaina, sun ɓata Asabataina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumakai.
\v 17 Amma na kawar da idanuna daga hallakasu ban kuma hallakar da su a cikin jeji ba.
\s5
\v 18 Sai na ce da 'ya'yansu a jeji, "Kada ku yi tafiya a kan farillan ubanninku; ko ku kiyaye sharuɗɗansu ko ku ɓata kanku da gumakansu.
\v 19 Ni ne Yahweh Allahnku, ku yi tafiya a kan farillaina, ku kuma kiyaye ka'idodina, ku yi biyayya da su.
\v 20 Ku kiyaye Asabataina da tsarki domin su zama alama tsakanina da ku, domin ku sani cewa Ni ne Yahweh Allahnku."
\s5
\v 21 Amma 'ya'yansu maza da mata suka tayar mani, ba su yi tafiya a cikin farillaina ko su kiyaye ka'idodina ba, ta haka idan mutum ya yi biyayya da su zai rayu. Sai kuma suka ɓata Asabataina, domin haka na yi tunani zan zubo masu da fushina a kansu in kuma huce fushina a kansu a jeji.
\v 22 Amma na yi hakuri sabili da sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban idanun al'ummai waɗanda a idanunsu ne na fito da Isra'ilawa.
\s5
\v 23 Ni da kaina na ɗaga hannuna bisa na rantse masu a jeji, zan warwatsar da su cikin al'ummai in kuma raba su a sauran ƙasashe.
\v 24 Na yi shawara zan yi wannan domin sun ƙi yin biyayya da ka'idodina, sun kuma ƙi bin farillaina, sun lalata Asabar ɗina. Idanuwansu na mamarin bauta wa gumakan kakanninsu.
\s5
\v 25 Sai kuma na ba su farillai waɗanda ba su da kyau, da ka'idodi marasa amfani da ba za susa su rayu ba.
\v 26 Na furtasu ƙazantattu ta wurin kyaututtukansu - sunyi hadayunsu na kowanne ɗan fãri daga mahaifa sunsa su ratsa ta cikin wuta - domin in cika su da fargaba su kuma sani cewa Ni ne Yahweh!"
\s5
\v 27 Saboda haka, ɗan mutum, yi magana da gidan Israila ka ce da su, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wannan kuma ubanninku suka saɓe ni ta wurin rashin aminci a gare ni.
\v 28 Sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, daga nan kuma dukkan sa'ad da suka hango wani tudu da itace mai ganye, sai su miƙa hadayunsu, suka tsokane ni ta wurin baye-bayensu, a wurin kuma suka ƙona turare mai ƙanshi da zuba baye-bayensu na sha.
\v 29 Daga nan na ce da su, "Wanne wurin ne wannan da kuke miƙa baye-baye a can?" Domin haka aka kira sunan wurin Bama har zuwa wannan rana.'
\s5
\v 30 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Me ya sa kuka ƙazantar da kanku da hanyoyin ubanninku? To me ya sa kuke haka kamar karuwai, ku na neman abubuwan banƙyama?
\v 31 Duk sa'ad da ku ke miƙa kyaututtukanku - kuma duk sa'ad da kuke sanya 'ya'yanku maza su bi ta cikin wuta - har ya zuwa wannan rana kuna ƙazantar da kanku ta wurin dukkan gumakanku. To me ya sa zan barku ku neme ni, gidan Isra'ila? Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba zan bari ku neme ni ba.
\v 32 Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku ba zai faru ba. Kuka ce, "Bari mu zama kamar sauran al'ummai, kamar dangogin sauran ƙasashe waɗanda ke bauta wa katako da dutse."
\s5
\v 33 Da dawwamata - wannan furcin Yahweh ne - tabbas zan yi mulki a bisan ku da hannu mai ƙarfi, da ɗagaggen damtse, da fushina zan zubo a kanku.
\v 34 Zan fitar da ku daga sauran mutane zan kuma tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsar da ku. Zan yi wannan da ikona ta wurin fushina mai zafi.
\v 35 Sa'an nan zan kawo ku cikin jejin mutane, a wurin ne zan yi maku shari'a fuska da fuska.
\s5
\v 36 Kamar yadda na yi wa ubanninku shari'a a jeji a ƙasar Masar, haka nan kuma zan yi maku shari'a - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 37 Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sandata, in kuma sa ku yi biyayya da abubuwan da alƙawari ya wajabta.
\v 38 Zan fitar da 'yan tawaye daga cikinku da waɗanda ke yi mani laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune kamar bãƙi, gama ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Sa'an nan ne za ku sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 39 To ku, gidan Israila, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: kowannen ku zai tafi wurin bautar gukinsa. Ku bauta ma sa tun da ya ke ba za ku saurare ni ba, amma ba za ku sake ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.
\s5
\v 40 Gama a kan dutsena mai tsarki, a bisa ƙwanƙolin dutsen Israila--wannan furcin Yahweh ne--dukkan gidan Israila za su bauta mani a ƙasar. Zan yi murna in bukaci hadayunku a wurin, da kuma nunar 'ya'yan farin gandunku na dukkan abubuwanku masu tsarki.
\v 41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fito da ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsar da ku. Zan nuna kaina mai tsarki a cikinku domin sauran al'ummai su gani.
\s5
\v 42 Gama idan na kawo ku a ƙasar Isra'ila, a ƙasar da na ɗaga hannuna sama na rantse zan bada ita ga ubanninku, za ku sani cewa Ni ne Yahweh.
\v 43 A nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da dukkan ayyukanku da kuka ɓata kanku da su, za ku ji ƙyamar kanku a idanunku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.
\v 44 Za ku sani cewa Ni ne Yahweh sa'ad da na yi maku wannan saboda sunana, ba kuma saboda gurɓatattun ayyukanku ba, ya gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'"
\s5
\v 45 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa.
\v 46 "Ɗan mutum, ka fuskanci ƙasashen kudu, ka yi maganar gãba da kudu; ka yi annabci a kan kurmin Negeb.
\v 47 Ka cewa kurmin Negeb, 'Wannan furcin Yahweh ne - Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba, zan kunna wuta a cikinka. Za ta kuwa cinye kowanne ɗanyen itace da kowanne busashen itace da ke cikinta. Ba za a iya kashe harshen wutar ba, kowacce fuska daga kudu da arewa za su ƙone.
\s5
\v 48 Gama dukkan masu rai za su sani cewa Ni ne Yahweh idan na sa wutar, ba kuma za a iya kashewa ba.
\v 49 Sai na ce, "Ya Ubangiji Yahweh, suna cewa da ni, wannan ba maganar misalai kawai yake yi ba?'"
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Sai maganar Yahweh ta zo ga gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka fuskanci Yerusalem, ka yi maganar gãba da masujadarta; ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila.
\v 3 Ka ce da ƙasar Isra'ila, 'Yahweh ya faɗi wannan: Ina gãba da ita! Zan zare takobina daga cikin kubanta in datse adalin mutum da mugun mutum daga cikinta!
\s5
\v 4 Da yake ni zan daddatse adalai da mugaye daga gare ki, takobina zata fito daga cikin kubenta gãba da dukkan mutane daga kudu da kuma arewa.
\v 5 Dukkan mutane kuwa za su sani Ni, Yahweh, na zare takobina daga kubenta. Ba kuwa za a sake mayar da ita a kubenta ba!'
\s5
\v 6 Kai kuma, ɗan mutum, sai ka yi nishi da ajiyar zuciya yayin da ƙugunka ya karye! cikin ɗacin rai kayi nishi a gaban idanunsu!
\v 7 Idan har za su tambaye ka, 'Donme ya sa kake nishi?' Sai ka ce masu, 'Saboda labarin abin da ke zuwa, domin kowacce zuciya za ta narke, kuma kowanne hannu zai yi lakwas! Kowanne ruhu zai some, kuma kowace gwiwa zata malale kamar ruwa. Duba! Abin yana zuwa kuma zai kasance kamar haka! - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'"
\s5
\v 8 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 9 "Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji ya faɗi haka: "Ka ce Takobi! Takobi! Za a wãsa ta sosai a kuma goggoge ta!
\s5
\v 10 Za a wãsa ta domin a yi babban kisa, an goge ta domin ta yi walwal kamar walƙiya! Shin mũyi murna a kan sandar girma ta ɗana? Takobi mai zuwa na gãba da kowacce sanda!
\v 11 Saboda haka za a bada takobin a goge ta, sa'an nan a cafke ta da hannu! Takobin an wãsa ta an kuma goge ta za a kuma bada ita a hannun wanda ke yin kisa!""'
\s5
\v 12 Ɗan mutum ka yi kiran neman taimako da makoki! Gama takobi ta zo ta yi gãba da mutanena! Ta na gãba da dukkan shugabannin Isra'ila. An bada su ga takobi tare da mutanena. Saboda haka, ka buga cinyarka!
\v 13 Gama akwai gwaji, amma idan sandar girman bata daɗe ba fa? - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 14 Yanzu kai, ɗan mutum, ka yi annabci ka buga hannuwanka biyu tare, don takobi zata kai hari har sau uku! Takobi domin waɗanda za a yanka! Ita ce takobin da zata datse mutane da yawa, za a yi masu gunduwa-gunduwa a ko'ina!
\s5
\v 15 Domin a narkar da zukatansu a kuma ruɓanya faduwarsu, na aika da takobi domin yanka a ƙofofinsu. Ah! An yi ta kamar walƙiya, an cafko ta domin yanka!
\v 16 Ke, takobi! ki sara dama! ki kuma sara hagu! Ki kuma je duk inda kika juya fuskarki.
\v 17 Gama ni ma zan buga hannuwana biyu, Sa'an nan kuma zan kwantar da fushina, Ni, Yahweh na furta haka.
\s5
\v 18 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni, cewa,
\v 19 "Yanzu kai, ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu domin takobin sarkin Babila ta zo. Hanyoyin biyu kuwa za su fara a ƙasar, alama kuma za ta nuna ɗaya daga ckinsu da ke kaiwa zuwa birnin.
\v 20 Ka kuma sa alamar ɗaya hanyar domin sojojin Babila da za su zo Rabba, birnin Ammonawa. Ka kuma sa ɗaya alamar ta kai sojoji Yahuda da kuma birnin Yerusalem, wadda aka katange.
\s5
\v 21 Gama sarkin Babila zai tsaya a mararrabar hanyoyi, inda hanyar ta rabu biyu, domin ya yi tsãfi. Yana girgiza waɗansu kiɓau yana kuma neman bayani daga waɗansu gumaka zai kuma binciki hanta.
\v 22 A hannun damarsa zai riƙe wani abun sihiri game da Yerusalem, zai kafa mata dundurusai, ya buɗe bakinsa domin ya bada umarnin yanka, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta ya kuma gina mahaurai da gina hasumiyoyin sansani.
\v 23 Zai kasance kamar abin banza ne a idanuwan waɗanda suke a Yerusalem, waɗanda suka rantse ga Babiloniyawa! Amma sarkin zai zarge su da karya yarjejeniyarsu domin mamaye su!
\s5
\v 24 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Saboda kun sa a tuna da laifinku, kuka kuma sa a bayyana kurakuranku, domin a ga zunubanku a dukkan ayyukanku - saboda kun yi haka za a kame ku a hannu.
\s5
\v 25 Kai kuma, ƙazantacce da mugun shugaban Isra'ila, wanda ranar hukuncinsa ta zo, wanda kuma lokacin aikata laifofinsa ya zo karshe,
\v 26 Ubangiji Yahweh ne ya faɗi haka zuwa gare ka: Ka cire rawani ka kuma cire kambi! Abubuwa ba za su sake zama dai-dai ba! A ɗaukaka marasa martaba a kuma ƙasƙantar da masu girmankai!
\v 27 Kufai! Kufai! Zan maida ita kufai! ba za a komar da ita ba, har sai shi wanda aka sa ya zartar da hukunci ya zo.
\s5
\v 28 To Kai, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan ga mutanen Ammonawa a kan zuwan kaskancinsu: Takobi! an zare takobi! An wãsa ta domin yanka domin ta lanƙwame, haka zata zama kamar walƙiya!
\v 29 Annabawa kuma suna ganin holoƙan wahayoyi domin ku, sa'ad da suke yin bukukuwan addini domin su zo maku da karairayi, wannan takobin zata kwanta a wuyan mai mugunta wanda aka kusan kashewa, wanda ranar hukuncinsa ta zo wanda kuma lokacin zunubinsa ya kusa ƙarewa.
\s5
\v 30 Maida takobi a cikin kubenta. A wurin da aka hallice ka, a cikin ƙasarka ta ainihi, zan hukunta ka!
\v 31 Zan zubo da hasalata a kanka! Zan kunna wutar fushina gãba da kai in kuma sa ka a cikin hannun mugayen mutane masu dabarar hallakarwa!
\s5
\v 32 Za ka zama abincin wuta! Jininka zai kasance a tsakiyar ƙasar. Ba za a tuna da kai ba, gama Ni, Yahweh na furta wannan!'"
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa
\v 2 "Yanzu, kai ɗan mutum, za ka shar'anta? Za ka shar'anta birni mai jini? Kasa ta san dukkan ayyukanta na banƙyama.
\v 3 Dole ne ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan shi ne birnin da ke zubar da jini a tsakiyarsa domin lokacinsa ya zo; birnin da ya yi gumaka domin ya kazantar da kansa.
\s5
\v 4 Ka zama mai laifi ta wurin jinin da ka zubar, ka ƙazantar da kanka ta wurin gumakan da ka yi. Domin ka jawo kwanakinka kusa, ƙarshen shekarunka kuma ya zo. Domin haka zan maida kai abin reni ga dukkan al'ummai, abin ba'a kuma a dukkan ƙasashe.
\v 5 Da waɗanda ke kusa da waɗanda ke nesa da kai za su yi maka ba'a, kai ƙazantaccen birni - da aka sani a ko'ina cike da rudami.
\s5
\v 6 Duba! Masu mulki na Isra'ila, kowannen su da ikonsa, ya zo wurin ka domin ya zubar da jini.
\v 7 Sun rena ubanni da uwaye a cikin ka, kuma suka yiwa baƙi danniya a cikin tsakiyar ka.
\v 8 Sun wulaƙanta marayu da gwauraye a cikinka ka rena abubuwana masu tsarki, ka tozarta Asabataina.
\v 9 Masu yankan baya sun zo cikin ka domin su zubar da jini, kuma sun ci abinci a kan tsaunuka. Sun yi mugunta a tsakiyarka.
\s5
\v 10 Mazaje sun buɗe tsiraicin mahaifinsu a cikin ka. Sun kuma tozarta mata masu haila a cikin ka a lokacin hailarsu.
\v 11 Mutanen da suka yi aikin kazanta da matan makwabtansu, mutanen da suka sa surukansu cikin kunya da kazanta; mazajen da suka ɓata 'yan'uwansu mata - 'ya'ya matan ubanninsu - dukkan waɗannan suna cikin ka.
\v 12 Waɗannan mutane sun karɓi toshi a cikin ka domin su zubar da jini. Ka karɓi kuɗinka da ruwa, kaci riba mai yawa, ka ɓata maƙwabtanka da danniya, ka mance da ni - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 13 Duba! Da hannuna na bugi kazamar ribar da kaci, da kuma zubar da jinin da ke a tsakiyarka.
\v 14 Zuciyarka zata tsaya, hannuwanka suyi ƙarfi a kwanakin da ni da kaina zan ɗauki mataki a kan ka? Ni Yahweh ni ne ke furta wannan, kuma zan aikata.
\v 15 Zan watsar da kai cikin al'ummai in sa ka ɗaiɗaice cikin ƙasashe. Ta haka zan wanke ƙazantarka.
\v 16 Ta haka za ka zama mai ƙazanta a cikin al'ummai. Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."
\s5
\v 17 Sai kuma maganar Yahweh ta zo gare ni cewa,
\v 18 "Ɗan mutum, gidan Isra'ila sun zama a yamutse a gare ni. Dukkan su sun zama ragowar tagulla da tãma da ƙarfe da dalma a cikin tsakiyar ka. Za su zama kamar gurɓatacciyar azurfa a cikin kaskonka.
\v 19 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya ce, 'Saboda ku dukka kun zama kamar gauraye, duba, saboda haka na kusa tattara ku a cikin tsakiyar Yerusalem.
\s5
\v 20 Kamar yadda mutane ke tara azurfa da tagulla da ƙarfe da tãma da dalma a maƙera su narke, su kuma hura wuta a kan su domin su narkar da su, to haka zan tattara ku cikin fushina da hasalata, zan kuma sa ku a wurin in narkar da ku.
\v 21 Zan tattara ku in hura wutar hasalata a kanku, za ku kuma narke a cikin tsakiyarta.
\v 22 Kamar yadda a ke narka azurfa a cikin tsakiyar maƙera, za ku narke a cikin ta, sa'an nan za ku sani cewa Ni, Yahweh na zubo da hasalata a kan ku.
\s5
\v 23 Maganar Yahweh ta zo gare ni cewa,
\v 24 "Ɗan mutum ka ce da ita ke ƙasa ce wadda ba a tsabtace ba. Ba ruwan sama a cikin ranar hasala!
\v 25 Akwai haɗaɗɗiyar maƙida ta annabawanta a cikinta kamar zaki mai ruri yana yaga nama. Suna kashe rai su kwashi dukiya mai daraja, suka sa gwauraye su yi yawa a cikin ta!
\s5
\v 26 Firistocinta suna yiwa shari'ata tayarwa, sun ɓata abubuwa masu tsarki. Ba su banbanta abu mai tsarki da lalatacce ba, bãsa koyar da banbanci tsakanin abu mai tsabta da marar tsabta. Sukan kawar da idanunsu daga ranakun Asabar ɗina, saboda haka suka tozarta ni a cikin su.
\v 27 Hakiman da ke cikin ta kamar kerketai suke lokacin da suke yayyaga nama. Sukan kashe rai, su zubar da jini domin suci riba ta rashin gaskiya.
\v 28 Annabawanta sun shafe su da farar ƙasa; suna ganin wahayoyin ƙarya suna kuma faɗa masu ƙarya. Sukan ce, "Ubangiji Yahweh ya faɗi haka" Sa'ad da Yahweh bai yi magana ba.
\s5
\v 29 Mutanen ƙasar suna yin zalunci, suna karɓar toshi, suna yin fashi, suna wulaƙanta mabuƙata da masu talauci, suna ƙwarar bãƙo da rashin adalci.
\s5
\v 30 Sai na nemi mutum ɗaya a cikin su wanda zai gina ganuwa, ya tsaya a gabana a cikin tsagar domin kada in hallaka ta, amma ban samu ba.
\v 31 Saboda haka zan zuba fushin hasalata a kan su. Zan gama da da su da fushin hasalata in maida masu ayyukansu a kansu - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, akwai mata guda biyu, mahaifiyarsu kuma ɗaya.
\v 3 Sun yi aikin karuwanci a Masar sa'ad da suke matasa. Sun yi aikin karuwanci a can. A can aka lagwaigwaita nonnansu, aka daƙuna kan nonnan budurcinsu.
\v 4 Sunayensu su ne Ohola - ita ce babba - da Oholiba kuma ƙanwarta. Daga nan suka zama nawa suka haifi 'ya'ya maza da mata. Ga ma'anar sunayensu: Ohola tana nufin Samariya, Oholiba tana nufin Yerusalem.
\s5
\v 5 Ohola ta yi karuwanci ko sa'ad da take tawa; ta yi sha'awar masoyanta, su Asiriyawa waɗanda suke da yawa a wurin.
\v 6 Gwamna mai saye da shuɗi, da jami'ansa kyawawa majiya ƙarfi, da dukkan waɗanda ke a kan dawakai.
\v 7 Ta bayar da kanta karuwa a gare su, da dukkan mahimman mazaje na Asiriya, ta ƙazantar da kanta da dukkan waɗanda ta yi sha'awar su - da dukkan gumakansu.
\s5
\v 8 Gama ba ta bar halinta na karuwanci a Masar ba, sa'ad da suka kwana da ita lokacin da take yarinya, sa'ad da suke taɓa nonnanta na kuruciya, lokacin da suka fara zuba mata halinsu na lalata.
\v 9 Saboda haka na miƙa ta a hannun masoyanta, a hannun Asiriyawa waɗanda ta yi sha'awar su.
\v 10 Suka yi mata tsirara sun kwashe 'ya'yanta maza da mata, kuma suka kashe ta da kaifin takobi, ta zama abin kunya ga sauran mata, suka yi mata hukunci.
\s5
\v 11 Oholiba 'yar'uwarta ta ga haka, amma ta yi sha'awa fiye da ita, ta yi aikin karuwanci fiye da 'yar'uwarta.
\v 12 Ta yi sha'awar Asiriyawa da gwamnoni da jami'ai waɗanda suke sa kaya masu kyau, masu hawan dawaki. Dukkan su kyawawa ne kuma ƙarfafan mutane ne.
\v 13 Na ga ta kazamtar da kanta. Dukkan su sun zama ɗaya.
\s5
\v 14 Sai kuma ta ƙaru cikin karuwancinta, ta ga sifofin mazaje a kan ganuwa, waɗanda a ka zãna da siffar Kaldiyawa da jar kala,
\v 15 suna ɗaure da ɗamara a gindinsu, da rawunna masu lilo a kansu. Dukkan su sun yi kama da jami'ai masu karusai, kamanninsu na 'ya'yan Babiloniyawa ne, waɗanda asalin ƙasarsu Kaldiya ce.
\s5
\v 16 Da dai idanunta suka gan su, sai ta yi sha'awar su, sai ta aiki waɗansu wurin su a cikin Kaldiya.
\v 17 Sai Babiloniyawa suka zo wurin ta, wurin gadon sha'awarta, suka kazantar da ita da lalatarsu. Abin da ta yi ya kazantar da ita, sai ta ɓatar da kama ta rabu da su.
\s5
\v 18 Ta bayyana aikin karuwancinta ta nuna tsiraicinta, raina ya yi ƙyamar ta kamar yadda raina ya yi kyamar 'yar'uwarta.
\v 19 Sa'an nan ta ƙara tunawa da aikin karuwanci, kamar yadda ta yi kwanakin ƙuruciyarta, sa'ad da ta zama kamar karuwa a cikin ƙasar Masar.
\s5
\v 20 Ta yi sha'awar masoyanta waɗanda mazakuttarsu ke kamar na jakuna, waɗanda kuma maniyinsu kamar na dawaki ne.
\v 21 Haka ki ka yi aikin kunya a lokacin ƙuruciyarki, sa'ad da Masarawa suka taɓa kan nonnanki suka lagwaigwaita nonnanki da ke tsaye.
\s5
\v 22 Saboda haka, Oholiba, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Duba! Zan sa mãsu ƙaunar ki su yi gãba da ke. Waɗanda kika gudu daga wurin su, za su taso maki daga kowanne sashi:
\v 23 Babiloniyawa da dukkan Kaldiyawa da Fekod da Shoya da Koya da dukkan Asiriyawa tare da su da ƙarfafa da kyawawan mutane da gwamnoni da jami'ai, dukkan su jami'ai ne da mazaje masu muƙami, dukkan su suna kan dawakai.
\s5
\v 24 Za su auko maki da kayan yaƙi, da karusai da kekuna da taron mutane da yawa. Za su ta da garkuwoyi manya da ƙanana da hulunan ƙarfe kewaye da ke ko'ina. Zan ba su zarafi su hore ki, za su hore ki da ayyukansu.
\v 25 Gama zan sa kishin fushina a kan ki, za su lallasa ki da fushinsu. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka tsira kuma za su faɗi da kaifin takobi. Za su kwashe 'ya'yanki maza da mata, waɗanda suka tsira kuma wuta za ta cinye su.
\s5
\v 26 Za su tuɓe kayanki su bar ki tsirara, su kwashe kayan adonki dukka.
\v 27 Ta haka zan cire halinki na abin kunya da aikin karuwancinki daga ƙasar Masar. Ba za ki ƙara ɗaga idonki wajen su da marmarin ki gan su ba, ba za ki ƙara yin tunanin Masar ba.
\s5
\v 28 Gama Ubangiji ya faɗi haka. Duba! zan bayar da ke a hannun waɗanda kika ƙi su, ki koma hannun waɗanda kika juyawa baya.
\v 29 Za su azabtar da ke cikin zafin ƙiyayya, za su ɗauke dukkan kayayyakinki su bar ki huntuwa. Huntancinki na karuwanci zai bayyana, halinki na kunya da lalatarki za su bayyana.
\s5
\v 30 Za a yi maki waɗannan abubuwa saboda aikinki na karuwanci, sha'awarki ta al'ummai wadda ta ƙazamtar da ke da gumakansu.
\v 31 Kin yi tafiya cikin hanyar 'yar'uwarki, saboda haka zan sa ƙoƙon horona a cikin hannunki.'
\s5
\v 32 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Za ki sha ƙoƙon 'yar'uwarki mai faɗi da zurfi. Za ki zama abin dariya da abin ba'a - cikin wannan ƙoƙon akwai abubuwa da yawa.
\s5
\v 33 Za ki cika da maye da baƙinciki, ƙoƙon fargaba da lalacewa; ƙoƙon 'yar'uwarki Samariya.
\v 34 Za ki shanye shi dukka ki farfasa shi ki tsattsaga nononki da gutsattsarinsa. Gama na furta shi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 35 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Saboda kin manta da ni kin jefar da ni bayanki, ke kuma za ki ɗauki alhakin halinki na kunya da lalata."
\s5
\v 36 Yahweh ya ce da ni, "Ɗan mutum, za ka hukunta Ohola da Oholiba? To ka nuna masu ayyukansu na banƙyama,
\v 37 tun da yake sun yi zina, tun da yake akwai jini a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu, sun sa 'ya'yansu cikin wuta, a matsayin abinci ga gumakansu.
\s5
\v 38 Sa'an nan sun ci gaba da yi mani haka, sun ɓata gidana mai tsarki, sun tozarta Asabataina.
\v 39 Gama sa'ad da suka yanka 'ya'yansu ga gumakansu, rannan kuma suka zo gidana mai tsarki suka ɓata shi! To duba! Wannan shi ne abin da suka yi a tsakiyar gidana.
\s5
\v 40 Kin yi aike wurin mutanen da suka zo daga nesa, an aika manzanni - duba yanzu. To sun zo su waɗanda kika yi wanka domin su, kin yi wa idanunki kwalliya kin sa kayan adonki.
\v 41 Can kika zauna a kan gado mai kyau wanda aka shirya teburi a gabansa inda kika ajiye turarena da maina.
\s5
\v 42 To ga hayaniyar babban taro kewaye da ita; ciki akwai mutane iri-iri har da masu maye daga cikin jeji, sun sa sarƙoƙi a hannuwansu da kambuna kyawawa a kawunansu.
\s5
\v 43 Sa'an nan na ce da ita, ita wadda ta tsofe a wurin karuwanci, 'Yanzu za su ƙazantu da zinarta, ita kuma da su.'
\v 44 Suka je wurin ta suka kwana da ita kamar yadda mutum zai je wurin karuwa. Ta wannan hanya suka kwana da Ohola da Oholiba, kazantattun mata.
\v 45 Amma mazaje masu adalci za su yi masu hukuncin mazinata, kuma za su yi masu hukunci na mãsu zubar da jini, saboda su mazinata ne kuma jini yana hannuwansu.
\s5
\v 46 To Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: zan sa taron mutane su auko masu da ta'addanci su washe su.
\v 47 Sa'an nan waɗannan mutane za su jejjefe su da duwatsu su daddatsu da takubbansu. Za su karkashe 'ya'yasu maza da mata, su ƙone gidajensu.
\s5
\v 48 Gama zan cire halayen kunya daga ƙasar, in hori dukkan mataye domin kada su ƙara yin rayuwa kamar karuwai.
\v 49 Haka za su sa maki halinki na kunya. Za ki ɗauki hakin zunubanki da gumakanki, ta haka za ki sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni a cikin shekara ta tara, a cikin wata na goma, a kan rana ta goma ga watan, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka rubuta wa kanka sunan wannan rana, ranar nan ta yau, gama a dai-dai wannan ranar ne sarkin Babila ya ƙwace Yerusalem.
\s5
\v 3 To sai ka yi magana da misali gãba da wannan gida mai tayarwa, a misali. Ka ce da su Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ɗora tukunyar girki. Ɗora ta ka zuba ruwa a cikin ta.
\v 4 Ka tattara gutsattsarin abinci a cikin ta, kowanne yanka mai kyau - kamar su cinya da karfata - ka cika ta da ƙasusuwa zaɓaɓɓu.
\v 5 A cikin garke ka ɗauki dabba zaɓaɓɓiya ka jera kasusuwan a ƙarƙashin ta. Ka sa ta tafasa ka dafa ƙasusuwan a cikin ta.
\s5
\v 6 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Kaiton birni mai jini, tukunyar girki mai tsatsa kuma tsatsar ba za ta fita daga cikin ta ba. Ka ɗauki yanka bayan yanka daga cikin ta, amma kada ka jefa ƙuri'a kan ta.
\s5
\v 7 Gama jininta yana cikin tsakiyarta, ta sa shi a kan dutse mai laushi; ba ta zubar da shi a ƙasa ta rufe shi da turɓaya ba,
\v 8 ta kawo hasala dai-dai ta ɗaukar fansa. Na sa jininta a kan dutse mai laushi domin kada ya rufu.
\s5
\v 9 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Kaiton birni mai jini. Zan ƙara sa itace da yawa.
\v 10 Iza itacen ka sa wuta. Ka dafa naman ya dafu sosai ka gauraye da kayan yaji ka kuma bari kasusuwan su gashe.
\s5
\v 11 Sa'an nan ka ɗora tukunyar a kan garwashi ba komai a ciki, domin ta yi zafi tagullarta ta rikiɗe, domin ƙazantar da ke cikinta ta narke, tsatsarta ta ƙone.
\v 12 Ta zama gajiyayya saboda aiki, amma tsatsarta ba ta fita daga cikin ta da wuta ba.
\s5
\v 13 Halinki na kunya yana cikin ƙazantarki. Saboda nayi ƙoƙari in tsabtace ki amma har yanzu ba ki tsabtatu daga ƙazantarki ba, ba za ki sake tsabtatuwa ba sai na ƙosar da fushina a kan ki.
\s5
\v 14 Ni, Yahweh, na furta, kuma zan aikata. Ba zan janye ba, ba zan huta ba. Yadda hanyoyinki suke, yadda kuma ayyukanki suke, su za su hukunta ki! - Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\v 15 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 16 "Ɗan mutum! Duba zan ɗauke maka muradin idanunka daga gare ka da annoba, amma kada ka yi baƙinciki ko kuka, kada hawayenka su zubo.
\v 17 Ka yi nishi a hankali. kada kayi jana'izar matattu. Ka ɗaura rawaninka a jikinka ka sa takalmanka a ƙafafunka, amma kada ka lulluɓe gashin bakinka, kada ka ci gurasar waɗanda ke makoki saboda sunyi rashin matayensu."
\s5
\v 18 Domin haka na yiwa mutane magana da safe, da yamma kuma matata ta mutu. Da safe na yi abin da aka umarce ni in yi.
\s5
\v 19 Mutanen suka tambaye ni, "Ba za ka gaya mana ma'anar waɗannan abubuwa ba, abubuwan da kake yi?"
\v 20 To sai na ce da su, "Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 21 'Ka ce da gidan Isra'ila, ga abin da Ubangiji Yahweh ya fadi: Duba! Zan ƙaskantar da gidana mai tsarki - girmankan ikonku da muradin idanunku, da marmarin ranku da na 'ya'yanku maza da mata da kuka baro, za su faɗi da kaifin takobi.
\s5
\v 22 Sa'an nan za ku yi dai-dai yadda na yi: Ba za ku lulluɓe kanku ba, ba za kuci gurasar mazajen da ke yin makoki ba!
\v 23 Maimakon haka rawunanku za su kasance a kan ku takalmanku kuma a ƙafafunku; ba za ku yi baƙinciki ka kuka ba, gama za ku narke cikin muguntarku, kowanne mutum zai yi nishi saboda ɗan'uwansa.
\v 24 Domin haka Ezekiyal za ya zamar maku misali, yadda idan wannan abu ya zo za ku yi dukkan abin da ya yi. Sa'an nan za ku sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."
\s5
\v 25 "Amma kai ɗan mutum, ran da na ƙwace haikalinsu, wanda shi ne farincikinsu, da fahariyarsu da abin da suke gani suna jin daɗi - sa'ad da kuma na ɗauke 'ya'yansu maza da mata -
\v 26 a wannan rana mai gudun hijira zai zo ya ba ka labari!
\v 27 A wannan rana ne bakinka zai buɗe ga wannan mai gudun hijira za ka yi magana - ba za ka ƙara yin shiru ba. Za ka zama misali a gare su domin su sani cewa Ni ne Yahweh."
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka sa fuskar ka gãba da mutanen Amon ka yi anabci gãba da su.
\s5
\v 3 Ka ce da mutanen Amon, 'Ku ji maganar Yahweh. Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi: Saboda kun ce, "Aha!" a kan wurina mai tsarki sa'ad da aka ɓata shi, da kuma gãba da ƙasar Isra'ila sa'ad da ta zama kango, da kuma gidan Yahuda sa'ad da suka tafi bauta,
\v 4 saboda haka, duba, zan bashe ku ga mutanen gabas su mallake ku. Za su kafa sansani gãba da ku su kafa rumfuna a cikin ku. Za su ci 'ya'yan itatuwanku su sha madararku.
\v 5 Zan maida Rabba wurin kiwon raƙuma mutanen Amon kuma saura domin garkuna. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 6 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Da yake kun tafa hannuwanku kun buga ƙafafunku kun yi farinciki da ƙiyayya a cikin ku gãba da ƙasar Isra'ila.
\v 7 Saboda haka, duba! Zan buge ku da hannuna in bashe ku ganima ga al'ummai. Zan datse ku daga cikin mutane in sa ku lalace daga cikin al'ummai! Zan hallaka ku, kuma za ku sani cewa Ni ne Yahweh.'
\s5
\v 8 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Saboda Mowab da Siya sun ce, "Duba! Gidan Yahuda ya zama kamar kowacce al'umma."
\v 9 Saboda haka, Duba! Zan buɗe magangarin Mowab in fara daga biranensa a kan iyaka - martabar Bet Yeshimot, Ba'al Miyon da Kiriyattayim -
\v 10 domin mutanen gabas waɗanda ke gãba da mutanen Amon. Zan bayar da su a mallake su yadda ba za a ƙãra tunawa da mutanen ba a cikin al'ummai.
\v 11 Haka zan yi hukunci a kan Mowab, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 12 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Idom ta ɗauki fansa a kan gidan Yahuda kuma ba ta yi dai-dai ba da ta yi haka.
\v 13 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan bugi Idom da hannuna in hallaka kowanne mutum da kowacce dabba a can. Zan maida su kufai, yasasshen wuri tun daga Teman har zuwa Dedan. Za su faɗi da kaifin takobi.
\s5
\v 14 Zan ɗora ramakona a kan Idom ta hannun mutanena Isra'ila, za su yi wa Idom bisa ga fushina da hasalata, kuma za su gane ramako na ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'
\s5
\v 15 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Tun da Filistiyawa sun ɗauki fansa da reni a cikin su, sun yi ƙoƙari su rushe Yahuda ba sau ɗaya ba.
\v 16 To ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Zan kai hannuna a kan Filistiyawa, zan datse Keretiyawa in hallaka waɗanda suka rage a gefen teku.
\v 17 Gama zan ɗauki fansa a kan su da fushi mai zafi da horo, saboda su sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na ɗauki fansata a kan su."
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Ya zama a cikin wata na goma sha ɗaya, a kan rana ta fari ga watan, Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, saboda Taya ta ce, 'Aha! A kan Yerusalem, ƙofofin mutanen yanzu an ɓalle su! ta dawo wurina; zan cika saboda ta zama kango.'
\s5
\v 3 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka, 'Duba! Ina gãba da ke Taya, zan taso da al'ummai da yawa a kan ki kamar yadda teku ya kan tada raƙuman ruwansa.
\v 4 Za su rushe ganuwoyin Taya, su farfasa hasumiyoyinta. Zan share ƙurarta in sa ta zama kamar huntun dutse.
\s5
\v 5 Za ta zama wurin da a ke shimfiɗa taru ya bushe a tsakiyar teku, tun da shi ke na furta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - kuma za ta zama ganima ga al'ummai.
\v 6 'Ya'yanta waɗanda suke cikin gona za a datse su da takobi; kuma za su sani cewa Ni ne Yahweh.'
\s5
\v 7 Gama wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi: Duba, daga arewa zan kawo Nebukadnezza sarkin Babila, sarkin sarakuna gãba da Taya, da dawakai da karusai da masu hawan dawakai da mutane da yawa.
\v 8 Za ya kashe 'ya'yanki mata a gona. Ya kafa sansani ya gina wuraren hawan ganuwarki ya tada garkuwoyi gãba da ke.
\s5
\v 9 Zai sa mabugi ya bubbuge ganuwarki, ya rushe hasumiyoyinka da kayan aikinsa.
\v 10 Dawakinsa za su yi yawa har ƙurar su za ta rufe ki. Ganuwarki za ta girgiza da ƙarar mahayan dawakai da kekunan yaƙi da karusai. Sa'ad da zai shiga ƙofofinki zai shiga kamar yadda mutane ke shiga birnin da aka rushe ganuwarsa.
\v 11 Kofatun dawakinsa za su yi tafiya a cikin dukkan hanyoyinki. Zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki na dutse masu ƙarfi za su faɗi har ƙasa.
\s5
\v 12 Za su kwashe dukiyarki da kayan cinikinki, za su farfasa ganuwarki su rushe gidajenki na jin daɗi. Duwatsunki da katakonki da ɓaragwazanki za su zubar da su a cikin ruwaye.
\v 13 Zan tsayar da ƙarar waƙoƙinki. Ba za a ƙara jin ƙarar molayenki ba.
\v 14 Zan maida ke huntun dutse, za ki zama wurin da za a shanya taru ya bushe. Ba za a sake gina ki ba, gama Ni, Ubangiji Yahweh na faɗi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 15 Ubangiji Yahweh ya faɗawa Taya haka, 'Tsibirai ba za su girgiza ba da ƙarar faɗuwarki, da nishin waɗanda aka yiwa rauni sa'ad da wannan kisa mai muni ya zo cikin ki?
\v 16 Sa'an nan dukkan yarimai na bakin teku za su sauka daga mulkokinsu su tuɓe tufafinsu, su jefar da rigunansu masu aiki. Za su rufe kansu da rawar jiki, za su zauna a ƙasa suna rawar jiki kowanne lokaci, kuma za su yi nukura saboda ke.
\s5
\v 17 Za su yi makoki a kanki su ce da ke, yaya haka, ke da kike wurin zaman masu tukin jirgin ruwa aka rushe ki. Sanannen birni mai ƙarfin gaske - yanzu ba shi a bakin teku. Su da suke zaune cikin ta suka baza labarin fargabarsu ga waɗanda ke zaune kusa da su.
\v 18 Yanzu ƙasashen tudu sun girgiza da ranar faɗuwarki. Tsibirai na cikin teku sun firgita saboda kin rabu da wurin ki..
\s5
\v 19 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Sa'ad da na mayar da ke kangon birni, kamar biranen da ba kowa. Sa'ad da na taso da zurfafa a kan ki, sa'ad da manyan ruwaye suka rufe ki,
\v 20 sa'ad da zan saukar da ke wurin mutanen dã, kamar waɗanda suka gangara cikin rami; gama zansa ki zauna can ƙarƙashin ƙasa kamar irin kango na zamanin dã. Saboda haka ba za ki ƙara dawowa ki tsaya a cikin ƙasar masu rai ba.
\v 21 Zan saukar maki da masifa, kuma ba za ki ƙara wanzuwa ba har abada. Sa'an nan za a neme ki, kuma ba za a ƙara samun ki ba - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Kuma maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni cewa,
\v 2 "Yanzu kai, ɗan mutum, sai ka soma makoki game da Taya,
\v 3 ka kuma cewa Taya, wadda take zama kurkusa da ƙofofin teku, masu kasuwancin mutane ne ga Tsibirai da yawa, Ubangiji Yahweh ya faɗa maki haka: Taya, Kin ce, 'Ni kammalalliya ce mai kyau.'
\s5
\v 4 Iyakokinki suna cikin tsakiyar zuciyar tekuna; maginanki sun kamalla kyaunki;
\v 5 Sun yi katakan ki da siferas daga Tsaunin Hamon; sun ɗauko sida daga Lebanon domin su yi maki sandar tukin jirgi.
\s5
\v 6 Sun sarrafa sandar tukin jirginki da itace na Bashan; suka yi matakalar ki da katakan siferas daga Saifrus, suka kuma lulluɓe ta da hauren giwa.
\v 7 Mayafanki mayafai masu ƙawa ne daga Masar da ke a matsayin tutarki; launin shuɗi da shunayya daga gaɓar Elisha a na amfani da su domin kare jirgin ruwanki.
\s5
\v 8 Waɗanda suka zauna cikin Sidon da Abad su ne matuƙanki; masu hikima na Taya na cikin ki; su ne masu yi maki jagora.
\v 9 Ƙwararru masana masu aikin hannu daga Baibilos sun gyarta tsagaggun wurarenki; dukkan jiragen teku da matuƙansu da ke cikin ki suna ɗaukar kayan fatauci domin kasuwanci.
\s5
\v 10 Fãsha da Lidiya da kuma Libiya suna cikin rundunarki, mayaƙãnki sun rataye garkuwa da ƙwalƙwali a cikin ki; suka bayyana darajarki.
\v 11 Mazajen Abad da Helek da ke cikin rundunarki sun zama katanga zagaye da ke, kuma mutanen Gammad su ne hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu a kan katangu zagaye da ke! Suka kammala kyaunki.
\s5
\v 12 Tarshish abokiyar kasuwancinki ce saboda yawan wadatar dukiyarki ta sayarwa: da azurfa, da baƙin ƙarfe, da tãma, da dalma. Suka saya suka kuma sayar da kayayyakin ki!
\v 13 Yaban da Tubal da kuma Meshek-sun sayar da bayi da kuma kayayyaki na tagulla. Suka sarrafa kayan fataucinki.
\s5
\v 14 Bet Togama ta tanadi dawakai, da dawakan yaƙi da alfadarai a matsayin kayan fataucinki.
\v 15 Mazajen Rodes suka zama yan kasuwarki a tsibirai masu yawa. Fatauci na cikin hannunki; suka kuma aiko maki ƙaho da hauren giwa da katakai masu ƙarfi a matsayin kyautai.
\s5
\v 16 Aram babbar 'yar kasuwa ce da kayayyakin ki masu yawa; suka tanada koren dutse mai daraja da shunayya, kaya mai launuka, da yãdi mai kyau da tsakiya da sauran kayan ado a matsayin kayan fataucinki.
\v 17 Yahuda da Isra'ila abokan kasuwancin ki ne. Suka tanada alkama daga Minit, waina da zuma, da mai, da ƙãro a matsayin kayan fataucinki.
\v 18 Dimaskus dillaliyar dukkan kayayyakin da kika sarrafa ce, ta hamshaƙiyar dukiyarki, da kuma ruwan inabi na Helbon da ulun Zaha.
\s5
\v 19 Dan da Yaban daga Izal suka yi maki fataucin ɗanyen ƙarfe da ɓawon ƙirya, da ƙansa-ƙansa. Wannan ya zama abin fatauci domin ki.
\v 20 Dedan ce mai samar maki da mashinfiɗai na sirdin dawakai masu kyau.
\v 21 Arebiya da dukkan shugabannin Keda suna ciniki da ke; sun samo maki 'yan raguna da raguna da awaki.
\s5
\v 22 'Yan kasuwa na Sheba da Rama suka zo su sayar maki da kowanne irin kayan ƙamshi mafiya daraja da kowanne irin dutse mai daraja; suka yi safarar zinariya domin fataucinki.
\v 23 Haran da Kane da Iden su ne abokan kasuwancinki, tare da Sheba da Ashu da kuma Kilmad.
\s5
\v 24 Waɗannan su ne dillalanki waɗanda ke sayar da kayan ƙawa (kayayyaki masu daraja na sãƙaƙƙun kayan ãdo), da kuma cikin barguna masu zane iri-iri da sãƙaƙƙun kaya a cikin kasuwannin ki.
\v 25 Jiragen ruwa na Tarshish su ne masu kawo maki kayayyakin fataucinki! Domin haka ki ka cika, aka loda maki kaya masu nauyi a tashoshin jiragen ruwanki.
\s5
\v 26 Matuƙan jiragen ruwanki suka kawo ki ga manyan tekuna; iskar gabas ta karya ki a tsakiyar su.
\v 27 Dukiyarki, da abin fataucinki da kuma kayan kasuwancinki; matuƙan jiragenki, da mãsassaƙa jiragen ruwa; abokan cinikinki da dukkan mayaƙan da ke cikin ki da dukkan ma'aikatan jiragenki- za su nutse cikin zurfin teku a ranar hallakarki.
\s5
\v 28 Biranen kusa da teku za su yi rawar jiki da jin ƙarar kukan masu yin jagoran jiragen ruwanki;
\v 29 Dukkan matuƙan jiragen za su sauko daga jiragensu; ma'aikata da majayan hanya za su sauka su tsaya kan ƙasa.
\v 30 Sa'an nan za susã ki saurari muryarsu za su kuma yi kuka mai zafi; za su watsa ƙura a kawunansu. Za su kwanta suna birgima cikin toka.
\s5
\v 31 Za su aske sumar kansu dominki su kuma ɗaure kansu da tsummokin makoki, kuma za su yi kuka mai zafi su kuma tãda murya ƙwarai.
\v 32 Za su tãda muryarsu ta makoki mai zafi dominki su kuma furta kalamai na habaici a kanki, wane ne kamar Taya, wadda yanzu aka sa tayi shiru a tsakiyar teku?
\v 33 A lokacin da fataucinki ya kai bakin teku, yana biyan buƙatar mutane masu yawa; kin azurtar da sarakunan duniya da dukiyarki da fataucinki!
\s5
\v 34 Amma lokacin da teku ya ragargaza ki, ta zurfafan ruwaye, fataucinki da dukkan ma'aikatanki suka nutse!
\v 35 Mazaunan tsibirai suka gan ki suka tsorata da ke, kuma sarakunansu suka yi rawar jiki mai ban razana! Fuskokinsu suka gigice!
\v 36 Fatake suka yi maki tsãki, kin zama abin razana, kuma ba za a sake ganin ki ba har abada."
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Sai maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka yi magana da shugaban Taya, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zuciyarka tunƙaho! Kãce, 'Ni allah ne! zan zauna a cikin mazaunin alloli a tsakiyar tekuna!" koda shi ke kai mutum ne ba allah ba, ka maida zuciyarka kamar ta allah;
\v 3 kana tunanin ka fi Daniyel hikima, kuma babu asirin da ke ba ka mamaki!
\s5
\v 4 Ka maishe da kanka mawadaci da hikima da fasaha, ka kuma tara zinariya da azurfa cikin ma'ajin ka!
\v 5 Ta wurin babbar hikima da kuma kasuwanci, ka ruɓanɓanya wadatarka, sai zuciyarka ta kumbura saboda dukiyarka.
\s5
\v 6 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: domin ka maida zuciyarka kamar zuciyar allah,
\v 7 Zan kawo bãƙi gãba da kai, Mazaje masu ban razana daga waɗansu al'ummai. Za su kawo takubba gãba da kyakkawar hikimarka, kuma za su wulaƙanta darajarka.
\s5
\v 8 Za su tura ka cikin rami, kuma za ka mutu mutuwa irin ta masu mutuwa cikin tsakiyar tekuna.
\v 9 Ka iya cewa, 'Ni allah ne' a fuskar mai kashe ka? Kai mutum ne ba Allah ba, kuma za ka zama a hannun wanda yake caccakar ka.
\v 10 Za ka yi mutuwar marasa kaciya ta hannun bãƙi, gama na furta haka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\v 11 Maganar Yahweh ta sake zuwa gare ni karo na biyu, cewa,
\v 12 "Ɗan mutum, ka tãda makoki domin sarkin Taya kace da shi, "Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: ka zama misalin kammala, cike da hikima da kammalanlen kyau.
\v 13 Kana cikin Iden, lambun Allah. Kowanne dutse mai daraja ya rufeka; da rubi, da tofaz, da imeral, da kiraisolet, da oniks, da yasfa, da saffiya, da tokwayis, da beril. Tsare-tsarenka da haɗuwarka anyi su ne da zinariya. A ranar da aka hallice ka ne aka shirya su.
\s5
\v 14 Na ajiye ka a bisa tsauni mai tsarki na Allah a matsayin kerubim da na shafe domin ya yi tsaron 'yan adam. Kana cikin tsakiyar dutse ma wuta inda ka yi yawo.
\v 15 Kana da aminci a tafarkunka tun daga ranar da aka hallice ka har sai da aka sami rashin adalci cikin ka.
\s5
\v 16 Ta wurin girman kasuwancinka ka cika da ta'addanci, domin haka ka yi zunubi. Saboda haka sai na jefar da kai daga tsaunin Allah, kamar wadda ya ƙazanta, kuma sai na hallakar da kai, kerubim mai tsaro, na kore ka daga cikin duwatsu masu wuta.
\v 17 Zuciyarka ta cika da tunƙaho domin kyaunka; ka wofintar da hikimarka saboda darajarka. Na koro ka ƙasa. Na sanya ka a gaban sarakuna domin su gan ka.
\s5
\v 18 Saboda zunubanka masu yawa da kuma rashin amincin kasuwancinka, ka ƙazantar da wurarenka masu tsarki. Domin haka na sa wuta ta fito daga gare ka; zata cinye ka. Zan maishe ka toka a fuskar dukkan waɗanda suke kallon ka.
\v 19 Dukkan waɗanda suka san ka cikin mutanen za su girgiza kai; za su yi fargaba, kuma ba za a sake ganinka ba har abada."'
\s5
\v 20 Sai maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 21 "Ɗan mutum, ka sa fuskar ka gãba da Sidon ka kuma yi annabci gãba da ita.
\v 22 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Ina gãba da ke, Sidon! Gama za a ɗaukaka Ni a tsakiyarki domin mutanenki su sani cewa Ni ne Yahweh a lokacin da zan zartar da adalci a cikin ki. Za a nuna ni mai tsarki cikin ki.
\s5
\v 23 Zan aika da annoba cikin ki da jini cikin titunanki, kuma waɗanda aka kashe za su faɗi a tsakiyarki. A lokacin da takobin zata tashi gãba da ke ta ko'ina, sa'an nan za ki sani cewa Ni ne Yahweh.
\v 24 Daga nan ba za a sami wata sarƙaƙiya da ƙaya mai azaba domin gidan Isra'ila ba daga dukkan waɗanda ke zagaye da ita waɗanda ke raina mutanenta ba, haka za su sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh!'
\s5
\v 25 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan, 'Lokacin da na tara gidan Isra'ila daga cikin mutane waɗanda aka tarwatsa su, kuma lokacin da na keɓe cikin su, domin al'ummai su gani, sa'an nan za su gina gidajensu a cikin ƙasar da zan ba bawana Yakubu.
\v 26 Sa'an nan za su zauna lafiya cikin ta su kuma gina gidaje, su shuka gonakin inabi, su kuma zauna lafiya a lokacin da zan shar'anta dukkan waɗanda suka rena su yanzu daga dukkan kewaye; Da haka za su sani Ni ne Yahweh Allahnsu!"'
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 A cikin shekara ta tara, a watan goma a ran sha biyu ga wata, maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka juya fuskar ka gãba da Fir'auna, sarkin Masar; ka yi annabci gãba da shi da kuma gãba da dukkan Masar.
\v 3 Ka furta ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Ina gãba da kai, Fir'auna, sarkin Masar. Kai, babbar dabbar teku da ke ɓuya cikin tsakiyar kogi, da ke cewa, "Kogi nawa ne. Na yi shi domin kaina."
\s5
\v 4 Gama zan sa ƙugiya a cikin bakinka, kuma kifaye na cikin Nilunka za su liƙe bisa ɓawonka; Zan tãda kai sama tare da dukkan kifayen kogin da suka manne wa ɓawonka.
\v 5 Zan jefar da kai cikin hamada, kai da dukkan kifaye daga koginka. Zaka faɗi a buɗaɗɗen fili; ba za a tãra ka ko a tãda kai sama ba. Zan bada kai abinci ga hallitun ƙasa da kuma tsuntsayen sammai.
\s5
\v 6 Sa'an nan dukkan mazaunan Masar za su sani cewa Ni ne Yahweh, domin sun zama sandar matsala ga gidan Isra'ila.
\v 7 A lokacin da suka riƙe ku da hannunsu, kun karye kun kuma yage kafaɗarsu; da suka jingina a kanku, sai kuka karye, sai kuma kuka sa ƙafafunsu suka kasa tsayawa.
\s5
\v 8 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! Zan kawo takobi gãba da kai. Zan datse mutum da dabba daga gare ka.
\v 9 Sai ƙasar Masar ta zama yasasshiya da kuma kufai. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, domin dabbar teku ta ce, "Kogin nawa ne, gama ni na yi shi."
\v 10 Domin haka, duba! Ina gãba da kai kuma ina gãba da koginka, don haka zan bayar da ƙasar Masar ga hallakarwa da lalacewa, kuma za ta zama lalatacciyar ƙasa daga Migdol zuwa Sãyin da kuma iyakokin Kush.
\s5
\v 11 Babu ƙafafun mutum da za shi wuce ta cikin ta, kuma babu ƙafar naman jeji da za shi wuce cikin ta. Ba za a zauna cikin ta ba har shekaru arba'in.
\v 12 Gama zan maida Masar ƙango a tsakiyar ƙasar da ba a zama cikin ta, kuma biranenta a tsakiyar lalatattun birane za su zama kufai har shekaru arba'in; sa'an nan zan tarwatsa Masar cikin al'ummai, in kuma watsa su cikin ƙasashe.
\s5
\v 13 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: a ƙarshen shekara arba'in zan tara Masar daga cikin mutanen da aka watsar da su.
\v 14 Zan dawo da abin da ke na Masar in kuma dawo da su zuwa ga yankin Fatros, zuwa ga ƙasar su ta asali. Sa'an nan za su zama masarauta marar muhimmanci a can.
\s5
\v 15 Zata zama ƙasƙantacciyar masarauta cikin masarautu, kuma ba za a ɗaga ta sama ba cikin al'ummai. Zan ƙasƙantar da su domin kada su yi mulkin al'ummai.
\v 16 Masarawa ba za su ƙara zama dalilin ƙarfin zuciya ga gidan Isra'ila ba. Maimakon haka, za su zama abin tunawa da zunubin da Isra'ila ta aikata a lokacin da suka juya ga Masar neman taimako. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Ubangiji Yahweh."'
\s5
\v 17 Sai ya zama a cikin shekara ta ashirin da bakwai a ranar farko ta watan ɗaya, maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 18 "Ɗan mutum, Nebukadneza sarkin Babila ya shirya rundunarsa su yi aiki mai wuya gãba da Taya. Kowanne kai an murje shi har sai ya yi saiƙo, kuma kowacce kafaɗa ta gogu. Duk da haka shi da rundunarsa ba su karɓi lada daga wurin Taya domin aiki mai wuyar da ya yi gãba da ita ba.
\s5
\v 19 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: 'Duba! Ina bayar da Masar ga sarki Nebikadneza sarkin Babila, kuma zai kwashe dukiyarta, ya kwashe mallakarta, ya tafi da duk abin da ya iske a can; wannan zai zama ladar rundunarsa.
\v 20 Na ba shi ƙasar Masar domin aikin da suka yi mani - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 21 A wannan rana zan sa ƙaho ya taso domin gidan Isra'ila, kuma na sa ku yi magana a tsakiyarsu, domin su san cewa Ni ne Yahweh."
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ku yi kururuwa, "Kaiton ranar mai zuwa."
\v 3 Ranar ta kusa. Ranar ta gabato domin Yahweh. Za ta zama rana ce ta hadarai, lokaci na masifa ga al'ummai.
\s5
\v 4 Sa'an nan takobi zata zo gãba da Masar, kuma za a yi ƙunci a cikin Kush a lokacin da mutanen da aka kashe suka fǎɗi a Masar - a lokacin da suka ɗauki dukiyarsu, da kuma lokacin da ginshiƙanta aka warwatsar.
\v 5 Kush da Libiya, da kuma Lidiya, da dukkan Arebiya, tare da mutanen da ke na alƙawari - dukkan su za su fãɗi ta dalilin takobi.
\s5
\v 6 Yahweh ya faɗi wannan: Waɗanda suka tsaya tare da Masar za su fǎɗi, kuma girman ƙarfin ta zai fǎɗi ƙasa. Daga Migdol zuwa Siyen sojojinsu za su fǎɗi da takobi - wannan furcin Yahweh ne.
\v 7 Za su zama wofi a tsakiyar yasassun ƙasashen, kuma biranen su za su zama cikin dukkan rusassun biranen.
\s5
\v 8 Sa'an nan za su san cewa Ni ne Yahweh, yayin da na cinna wuta cikin Masar, kuma lokacin da aka hallaka dukkan mataimakanta.
\v 9 A wannan ranar 'yan saƙo za su fito daga gare ni cikin jirage su addabi tsararrar Kush, kuma za a yi azaba a cikin su a wannan rana ta azabar Masar. Duba! Tana zuwa.
\s5
\v 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Zan kawo ƙarshen taron jama'ar Masar ta hannun Nebukadneza, sarkin Babila.
\v 11 Shi da rundunarsa tare, ta'addar al'ummai, za a hallakar da ƙasar; za su zare takobinsu gãba da Masar su kuma cika ƙasar da gawawwakin mutane.
\s5
\v 12 Zan maishe da rafuffuka busassun ƙasa, zan kuma sayar da ƙasar cikin hannun mugayen mutane. Zan maishe da ƙasar da dukkan cikarta kufai ta hannun bãƙi- Ni, Yahweh, na yi magana.
\s5
\v 13 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zan hallakar da gumaka, kuma zan kawo iyakar gumakan Memfis marasa amfani. Ba za a sake samun yarima cikin ƙasar Masar ba, kuma zan sa ta'adda a bisa ƙasar Masar.
\v 14 Sa'an nan zan sa Fatros ta zama kufai in kuma cinna wuta a Zowan, kuma zan aiwatar da ayyukan shari'a a kan Tebes.
\s5
\v 15 Gama zan zubo da fushi na a bisa Felusiyom, kangararren wuri na Masar, in kuma datse taron jama'ar Tebes.
\v 16 Sa'an nan zan cinna wuta a Masar; Felusiyom za ta zama da azaba mai tsanani, Tebes za ta kakkarye, Memfis kuma za ta fuskanci magabta a kowacce rana.
\s5
\v 17 Majiya ƙarfi cikin Heliyofolis da Bubastis za su fǎɗi ta takobi, kuma birninsu zai tafi bauta.
\v 18 A Tafahes, rana za ta ƙi bada haskenta sa'ad da na karya karkiyar Masar a nan, za a ƙarar da alfarmar ikonta. Girgije zai rufe ta, kuma 'ya'yanta mata za su tafi bauta.
\v 19 Zan aiwatar da ayyukan shara'a a Masar, domin su sani cewa Ni ne Yahweh.'"
\s5
\v 20 Sai ya kasance a cikin shekara ta sha ɗaya, cikin wata na farko, a cikin kwana na bakwai na watan, da maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 21 "Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, sarkin Masar. Duba! Ba a rigaya an ɗaure masa ciwon ba, ko a shirya shi ya warke da bandeji, saboda ya yi ƙarfi ya kama takobi.
\s5
\v 22 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: 'Duba, ina gãba da Fir'auna, sarkin Masar. Gama zan karya hannunsa, da mai ƙarfin da wanda aka karye, kuma zan sa takobin ya fǎɗi daga hannunsa.
\v 23 Sa'an nan zan tarwatsa su cikin Masar cikin al'ummai in kuma watsa su cikin ƙasashe.
\v 24 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila in kuma ɗibiya takobina a cikin hannunsa domin in hallaka hannun Fir'auna. Zai yi nishi a gaban sarkin Babila da nishi kamar na mutum mai mutuwa.
\s5
\v 25 Gama zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila, amma hannun Fir'auna zai faɗi. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh, a lokacin da zan sa takobina cikin hannuwan sarkin Babila; gama zai kai wa Masar farmaki da ita.
\v 26 Don haka zan watsar da Masar cikin al'ummai In kuma tarwatsa su a cikin ƙasashe. Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh."'
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Sai ya zama a cikin shekara ta sha ɗaya, a wata na uku, a rana ta farko ta watan, da maganar Yahweh ta zo mani, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka ce da Fir'auna, sarkin Masar, da kuma ga taron jama'arsa da ke kewaye da shi, 'girman kujerarka, kama da wa kake?
\s5
\v 3 Duba! Asiriya ta zama sida a cikin Lebanon da kyawawan rassa, ta na bada inuwa ga jejin, kuma doguwa ce, kuma rassanta suka zama ƙoƙuwar itace.
\v 4 Ruwaye masu yawa suka sa tayi tsayi; zurfafan ruwaye suka sa tayi faɗi. Rafuka suka gangara dukka kewaye da sashenta, gama hanyoyinsu sun bi ta dukkan hanyoyi zuwa ga dukkan itatuwan fili.
\s5
\v 5 Tsawonsa mai girma yafi sauran itatuwa da ke a filin, kuma rassanta sun zama da yawa; rassanta suka yi tsayi sabili da ruwaye masu yawa sa'ad da suke girma.
\v 6 Kowanne tsuntsun sammai na zama cikin rassanta, haka kuma kowacce halita mai rai na cikin filin suna haifar 'ya'yansu a ƙarƙashin inuwarsa. Dukkan al'ummai masu yawa suna zama a ƙarƙashin inuwarsa.
\v 7 Gama yana da kyau a cikin girmansa da kuma tsayi a rassansa, gama saiwarsa na cikin ruwaye masu yawa.
\s5
\v 8 Sida na cikin gonar Allah ba su kai shi ba. A cikin itatuwan gora babu waɗanda suka kai rassansa, kuma itacen durumi bai kai shi rassa ba. Babu wani itace a cikin lambun Allah da ke kamar sa cikin kyaunsa.
\v 9 Na yi shi da kyau da rassansa masu yawa kuma dukkan itatuwan Iden da ke cikin lambun Allah suka yi kishinsa.
\s5
\v 10 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Saboda yana da tsawo, kuma ya sa dogayen rassansa a tsakanin rassansa, ya ɗaukaka zuciyarsa sabili da tsawonsa.
\v 11 Na rigaya na bayar da shi cikin hannuwan jarumi na al'ummai, ya yi masa dai-dai da muguntarsa. Na wurga shi waje.
\s5
\v 12 Bãƙi waɗanda ke ta'addanci a dukkan al'ummai suka datse shi suka bar shi ya mutu. Rassansa suka fãɗi a kan tsaunuka da kuma dukkan kwari, rassansa suka kakkarye a cikin dukkan magudanun ruwaye na ƙasar. Sai dukkan al'ummai na duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka kuma tafi suka bar shi.
\s5
\v 13 Dukkan tsuntsayen sararin sama suka sauka bisa tushen itacen da ya fãɗi, kuma kowacce dabba ta fili ta zo rassansa.
\v 14 Wannan ya faru ne domin kada wata itaciyar ta tsiro kusa da ruwayen ta ɗaga ganyayesu zuwa ga itatuwa mafiya tsawo, kuma kada waɗansu itatuwa su yi girma gefen ruwayen su kai tsayinta. Dukkan su an sa sun mutu, a can ƙasa, a cikin 'ya'yan mutane, tare da waɗanda suka gangara cikin rami.
\s5
\v 15 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A ranar da sida ya gangara zuwa Lahira na kawo makoki cikin duniya. Na rufe zurfafan ruwaye bisanta, na kuma tsayar da ruwayen teku. Na tsai da ruwaye masu girma, na kuma kawo makoki ga Lebanon dominsa. Saboda haka dukkan itatuwan saura suka yi makoki sabili da shi.
\s5
\v 16 Na kawo rawar jiki ga al'ummai ta dalilin ƙarar faɗuwarsa, a lokacin da na wurga shi cikin lahira tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin rami. Sai na ta'azantar da dukkan itatuwan da ke a Iden a cikin wuraren duniya a ƙasa. Waɗannan su ne da zaɓaɓɓu da kuma mafi kyaun itatuwa na Lebanon; itatuwan da suka sha ruwan.
\s5
\v 17 Gama suma suka gangara tare da shi zuwa Lahira, zuwa ga waɗanda aka kashe da takobi. Waɗannan su ne ƙarfin hannunsa, waɗannan al'umman da suka zauna cikin inuwarsa.
\v 18 Wacce itaciya ce dai-dai da ke a ɗaukaka da girma? Gama za a kawo ki ƙasa tare da itatuwan Iden zuwa ƙarkashin ƙasa a tsakanin marasa kaciya; za ka zauna tare da waɗanda aka kashe da takobi.' Wannan shi ne Fir'auna tare da dukkan taronsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Sa'an nan ya kasance a cikin wata na sha biyu ta shakara ta sha biyu, a rana ta farko ga watan, da maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, tãda makoki domin Fir'auna sarkin Masar; ka ce masa, 'Ka na kamar ɗan zaki a cikin al'ummai, amma ka zama kama da dodon ruwa na cikin teku; ka na dama ruwa, ka na dãma ruwaye da ƙafafunka ka kuma yamutsa ruwayensu.
\s5
\v 3 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Haka zan warwatsa tãruna bisan ka cikin mutane da yawa, kuma za su ɗaga ka cikin tãruna.
\v 4 Zan yashe ka cikin ƙasar. Zan wurga ka cikin fili in kuma sa dukkan tsuntsayen sammai su zauna bisanka; yunwar dukkan dabbobi masu rai a duniya za su ƙoshi ta wurin ka.
\s5
\v 5 Gama zan sa naman ka a bisa tsaunuka, zan kuma cika kwarurruka da gawarka cike da tsutsotsi.
\v 6 Sa'an nan zan watsar da jininka a bisa tsaunuka, ruwayen ƙarƙarshin ƙasa za su cika da jininka.
\s5
\v 7 Bayan na katse ka, Zan rufe sammai in kuma baƙantar da taurarinsu; Zan rufe rana da giza-gizai, wata kuma ba zai bada haskensa ba.
\v 8 Dukkan haske masu haskakawa a sammai zan baƙanta su bisan ka, zan kuma sa duhu bisa ƙasarka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 9 Da haka zan tsoratar da zuciyar mutane da yawa a cikin ƙasashen da ba ka sani ba, a lokacin da na kawo rushewarka a tsakiyar al'ummai, cikin ƙasashen da ba ka sani ba.
\v 10 Zan firgita mutane da yawa saboda kai; sarakunansu za su girgiza cikin tsoro saboda kai a lokacin da zan jujjuya takobina a gabansu. A kowacce sa'a kowa zai yi rawar jiki saboda kai, a ranar faɗuwar ka.
\s5
\v 11 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Takobin sarkin Babila zai auko gãba da kai.
\v 12 Zan sa taron jama'arka mutanenka su faɗi ta hannun takobin jarumi - kowanne jarumi ɗan ta'adda ne ga al'ummai. Waɗannan jarumawa za su lalatar da fahariyar Masar su kuma lalata dukkan tarurrukanka.
\s5
\v 13 Gama zan lalatar da dukkan garkunan da ke a bakin magudanun ruwaye masu yawa; tafin ƙafar mutum ba zai ƙara dãma ruwan ba, ko kuma kofatun dabbobi su dãma su.
\v 14 Sa'an nan zan kwantar da ruwansu in sa ƙogunansu su zubo kamar mai - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 15 A sa'ad da na maida Masar yasasshiyar ƙasa, lokacin da aka maida ƙasar abin wofi sarai da dukkan cikarta, bayan na kai hari ga mazaunanta, za su san cewa Ni ne Yahweh.
\v 16 Za a yi makoki; 'ya'ya mata na al'ummai za su yi makoki domin ta; za su yi makoki domin Masar, domin dukkan taruwar jama'arta za su yi makoki - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."'
\s5
\v 17 Hakanan ya faru a cikin shekara ta sha biyu, a ranar sha biyar ga wata, da maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 18 "Ɗan mutum, ka yi kuka domin taron jama'ar Masar ka kuma jawo su ƙasa - ita da 'ya'yanta mata masu daraja na al'ummai-- zuwa cikin ƙarƙashin ƙasa tare da sụ waɗanada suke gangarawa cikin rami.
\s5
\v 19 'Ki na da kyau fiye da wani? Je ƙasa ki kwanta da marasa kachiya.'
\v 20 Za su faɗi daga cikin waɗanda aka kashe da takobi. An zare takobin! An miƙa ki ga takobin; za su kama ta tare da taron jama'arta.
\v 21 Mafi ƙarfi daga cikin jarumawa a Lahira zai yi magana game da Masar da kuma abokan amanarta. Sun gangaro zuwa nan! Za su kwanta tare da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.'
\s5
\v 22 Asiriya ta na can tare da dukkan jama'arta. Kaburburanta suna zagaye da ita; dukkansu an kashe su da takobi.
\v 23 Su waɗanda kaburburansu na can cikin wuri mai zurfin rami su na can, da dukkan jama'arta. Kaburburanta sun zagaye dukkan waɗanda aka kashe, su da suka faɗi ta wurin takobi, su da suka jawo masifa a bisa ƙasar masu rai.
\s5
\v 24 Ilam na wurin tare da dukkan taron. kaburburanta na zagaye da ita; dukkan su aka kashe su. Waɗanda suka faɗi ta wurin takobi, su da suka gangara ƙasa babu kaciya zuwa wurin zurfafa na iyakar ƙasa, su da suka kawo ta'addancin su bisa ƙasar masu rai kuma su waɗanda suke ɗauke da kunyarsu, tare da waɗanda suke gangarawa cikin rami.
\v 25 Suka shirya wa Ilam makara da dukkan taron ta cikin tsakiyar waɗanda aka kashe; kaburburanta sun zagaye ta. Dukkan su marasa kaciya ne, an sha zararsu da takobi, domin sun kawo ta'addancinsu cikin ƙasar masu rai. Domin haka suna ɗauke da kunyarsu, tare da su waɗanda suke gangarawa zuwa cikin rami a tare da dukkan waɗanda aka kashe, waɗanda suke gangarawa zuwa cikin rami. Ilam na cikin dukkan waɗanda aka kashe.
\s5
\v 26 Meshek, Tubal, da dukkan taron suna wurin! Kaburburansu na kewaye da su. Dukkansu marasa kaciya ne, aka kashe da takobi, domin sun kawo ta'addancinsu cikin ƙasar masu rai.
\v 27 Ba su kwanta da jarumawan da suka faɗi na marasa kaciya waɗanda suka gangara zuwa Lahira da dukkan makamansu na yaƙi ba, kuma da dukkan makamansu ƙarƙashin kawunansu da kuma kurakuransu bisa ƙasusuwansu. Gama su ne 'yan ta'adda na jarumawa a cikin ƙasar masu rai.
\s5
\v 28 To ke, Masar, za a kakkarya ki a cikin takiyar marasa kaciya! Za ki kwanta tare da waɗanda aka sare su da takobi.
\v 29 Idom na wurin tare da sarkinta da kuma dukkan shugabanninta. An sanya su cikin ƙarfinsu tare da waɗanda aka kashe da takobi. Tare da marasa kaciya suka kwanta, tare da waɗanda suka gangara cikin rami.
\s5
\v 30 Sarakunan arewa suna wurin - dukkansu da kuma dukkan Sidoniyawa waɗanda suka gangara ƙasa tare da waɗanda aka sare su. Suna da matuƙar karfi kuma suka sanya waɗansu jin tsoro, amma yanzu suna wurin cikin kunya, marasa kaciya tare da waɗanda aka sare da takobi. Sun ji kunyarsu, tare da waɗanda suke gangarawa cikin rami.
\s5
\v 31 Fir'auna zai gani ya kuma karfafa game da dukkan taron jama'arsa waɗanda aka sare da takobi - Fir'auna tare da dukkan sojojinsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 32 Na sa shi a matsayin mai ban tsoro a cikin ƙasar masu rai, amma za a ajiye shi ƙasa a tsakiyar marasa kaciya, cikin waɗanda aka sare da takobi, Fir'auna da dukkan taron jama'arsa - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Dan mutum, ka faɗa wa mutanenka wannan; ka ce masu, 'Sa'ad da na kawo takobi gãba da wata ƙasa, sai mutanen wannan ƙasar suka ɗauki ɗaya da ga cikin su suka maishe shi mai tsaro domin su.
\v 3 Zai riƙa duba idan takobi ya taso wa ƙasar sai ya busa ƙahonsa ya faɗakar da mutane!
\v 4 Idan mutanen suka ji ƙarar ƙaho amma ba su yi lura ba, idan kuma takobi ya zo ya kashe su, to kowanne ɗayansu alhakin jininsa na kansa.
\s5
\v 5 Idan wani ya ji ƙarar ƙaho amma ya ƙyale, alhakin jininsa na kansa; amma idan ya kula, zai ceci na sa ran.
\v 6 Idan kuwa, mai tsaro ya ga takobi yana tasowa, amma bai busa ƙaho ba, sakamakon bai faɗakar da mutane ba, takobi ya zo ya ɗauki ran wani, wannan mutum ya mutu cikin zunbinsa, zan biɗi alhakin jininsa daga hannun mai tsaro.'
\s5
\v 7 Yanzu kai da kanka, ɗan mutum! Na saka ka zama mai tsaron gidan Isra'ila; za ka ji maganganu daga bakina kayi gargaɗi a madadi na.
\v 8 Idan na cewa mugun mutum, 'Kai mugu, hakika za ka mutu!' Amma idan ba ka faɗakar da wannan ba domin a gargaɗi mugu game da hanyarsa, mugun nan zai mutu cikin zunubinsa, amma zan biɗi alhakin jininsa a hannun ka!
\v 9 Amma idan kai, ka gargaɗi mugu game da hanyarsa, domin ya juyo ya bar ta, idan bai juyo yabar hanyarsa ba, to zai fa mutu cikin zunubinsa, amma kai da kanka ka riga ka ceci ranka.
\s5
\v 10 Saboda haka, ɗan mutum, ka cewa gidan Isra'ila, 'Kuna cewa haka, 'Kurakuranmu da zunubanmu suna kanmu, muna kuma ruɓewa a cikin su! Ƙaƙa za mu rayu?'"
\v 11 Ka ce masu, 'Muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - ba na farinciki da mutuwar mugu, domin idan mugu ya tuba daga hanyarsa, zai rayu! Ku Tuba! Ku Tuba daga mugayen hanyoyinku! Donme ne ne za ku mutu, gidan Isra'ila?'
\s5
\v 12 Yanzu kai, ɗan mutum, ka cewa mutanenka, 'Ayyukan adalcin adali ba zai cece shi ba idan ya yi zunubi! Muguntar mugun mutum ba za ta sa shi ya hallaka ba, idan ya tuba daga zunubinsa! Domin mai adalci ba zai iya rayuwa ba saboda adalcinsa idan ya yi zunubi.
\v 13 Idan na cewa adali, "Ba shakka za ka rayu!" idan kuwa ya dogara ga adalcinsa sa'an nan ya aikata rashin gaskiya, ba zan tuna da adalcinsa ba ko guda ɗaya. Zai mutu saboda muguntar da ya yi.
\s5
\v 14 Idan na cewa mugu, "Ba shakka za ka mutu," amma kuma sai ya tuba daga zunubinsa ya aikata abin adalci da gaskiya -
\v 15 idan ya mayar da ƙwacen da ya yi da sunan jingina, ko kuma ya mayar da abin da ya sata, kuma idan ya yi tafiya a cikin farillan rai ya dena yin laifi - ba shakka zai rayu. Ba zai mutu ba.
\v 16 Ba za a kuma tuna masa da laifofinsa waɗanda ya aikata ba. Gama ya aikata gaskiya da adalci, saboda haka, zai rayu!
\s5
\v 17 Amma mutanenka suka ce, "Hanyar Ubangiji ba dai-dai take ba!" alhali hanyoyinku ne ba dai-dai ba!
\v 18 Sa'ad da adali ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu cikinsa!
\v 19 Sa'ad da mugu ya juya ya bar muguntarsa ya yi abin da ke gaskiya da adalci, zai rayu saboda waɗannan abubuwa!
\v 20 Amma ku mutane kun ce, '"Hanyar Ubangiji ba dai-dai ba ce!" Zan shar'anta kowannenku bisa ga hanyarsa, gidan Isra'ila.'"
\s5
\v 21 Wannan ya faru a shekara ta goma sha biyu, a rana ta biyar ga watan goma na bautar talalarmu, wani ɗan gudun hijira ya zo guna da ga Yerusalem ya ce, "An ci birnin!"
\v 22 Hannun Yahweh yana bisana da maraice kafin ɗan gudun hijiran ya zo, bakina kuma ya rigaya ya buɗe kafin lokacin zuwansa da safe. Bakina kuwa ya buɗe; ban ƙara yin shuru ba!
\s5
\v 23 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 24 "Ɗan mutum, waɗanda suke zaune cikin kango a ƙasar Isra'ila suna magana suna cewa, 'Ibrahim kaɗai ne ya gaji ƙasar, amma mu, muna da yawa! An riga an ba mu ƙasar a matsayin mallaka.'
\s5
\v 25 Saboda haka ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi: Kuna cin nama da jini, kuna bautar gumakanku sa'an nan kuna zubda jinin mutane. Lallai sai kun mallaki ƙasar?
\v 26 Kun kafa dogararku ga takubba, kunyi abubuwan banƙyama; kowannenku yana zina da matar maƙwabcinsa. Ya kamata ku mallaki ƙasar kenan?'
\s5
\v 27 Za ka faɗa masu haka, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Muddin ina raye, 'hakika waɗanda ke kufai za a kashe su da takobi, zan kuma bada waɗanda ke jeji ga hallitu masu rai su zama abincinsu, waɗanda ke cikin kagaru da koguna annoba za ta kashe su.
\v 28 Sa'an nan zan maida ƙasar kufai da kuma abin tsoro, ƙarfinta na taƙama zai ƙare, gama za a bar duwatsun Isra'ila, ba wanda zai ratsa ta cikinsu.'
\v 29 Gama za su sani Ni ne Yahweh, sa'ad da na maida ƙasar kufai a lalace saboda dukkan abubuwan banƙyamar da suka aikata.
\s5
\v 30 Yanzu kai, ɗan mutum - mutanenka suna faɗin abubuwa game da kai a jikin garu da ƙofofin gidaje, suna cewa junansu - kowanne mutum ga ɗan'uwansa, 'Bari mu je mu saurari maganar annabi wadda ta zo daga Yahweh!'
\v 31 Mutanena za su zo wurinka, kamar yadda suka saba yi, za su zauna a gabanka su saurari maganganunka, amma ba za su yi biyayya da su ba. Maganganu masu kyau suna bakinsu, amma zukatansu na bin ƙazamar riba.
\s5
\v 32 Gama kai kamar waƙa mai daɗi ne a gare su, ƙyakkyawar murya da a ke rairawa a kan garaya, lallai za su kasa kunne ga maganarka, amma ba ko ɗaya da zai yi biyayya da ita.
\v 33 Saboda haka idan duk waɗannan sun faru - duba! haka kuwa zai faru! - sa'an nan ne za su sani annabi ya kasance a tsakanin su."
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Sai maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 "Ɗan mutum, ka yi annabci gãba da makiyayan Isra'ila. Yi annabci ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya cewa makiyaya: Kaiton makiyayan Isra'ila masu kiwon kansu. Bai kamata masu kiwo su tsare garke ba?
\v 3 Kuna cin rabo mai tsoka kuna kuma sa tufafi na ulu. Kuna yanka masu ƙiba cikin garke. Baku yin kiwo ko kaɗan.
\s5
\v 4 Ba ku ƙarfafa waɗanda ke da cututtuka ba, ko ku warkar da marasa lafiya. Waɗanda suka karye, ba ku ɗori su ba, waɗanda aka kora ba ku dawo da su ba ko ku nemo ɓatattu. Maimakon haka, kun mallaƙesu ƙarfi da yaji.
\v 5 Sai suka warwatse saboda ba makiyayi, suka zama nama ga kowanne mai rai a jeji bayan an warwatsar da su.
\v 6 Tumakina suka yi makuwa a kan duwatsu da tsaunuka, suka kuma warwatsu a dukkan faɗin duniya. Duk da haka ba wanda ya ke neman su.
\s5
\v 7 Saboda haka, makiyaya, ku ji maganar Yahweh:
\v 8 Da dawwamata - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - saboda tumakina sun zama ganima da abinci ga kowanne naman jeji, saboda rashin makiyayan kirki, kuma masu kiwon garkena ba su nemo tumakin ba, amma makiyayan sun kãre kansu, ba su yi kiwon garkena ba.
\s5
\v 9 Saboda haka, makiyaya, ku ji maganar Yahweh:
\v 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ina găba da masu kiwon tumakina, zan nemi tumaki na a hannunsu. Sa'an nan zan sallame su daga kiwon garkena; makiyayan ba za su ƙara kiwon kansu ba tunda zan ƙwace garkena daga bãkinsu, domin kada tumakina su ƙara zama abincinsu.
\s5
\v 11 Gama Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ni da kaina zan nemo garkena in kuma lura da su,
\v 12 kamar yadda makiyayi yakan nemi tumakinsa da suka watse daga cikin garkensa. Haka zan nemo tumakina, zan kuma cecesu daga dukkan wuraren da aka warwatsa su a ranar hadari da duhu.
\v 13 Sa'an nan zan fito da su daga cikin al'ummai; zan tattaro su daga ƙasashe dabam dabam in kawo su ƙasarsu. Zan saukar da su a wurin kiwo mai dausayi a gefen duwatsu na Isra'ila, a maɓugɓugai, a dukkan wuraren da mutane ke zaune a ƙasar.
\s5
\v 14 Zan sa su a makiyaya mai kyau; manyan duwatsun Isra'ila za su zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, inda akwai ciyawa da yawa, za su yi kiwo a tsaunukan Isra'ila.
\v 15 Ni da kai na zan yi kiwon garkena, Ni da kaina kuma zan sa su kwanta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne -
\v 16 Zan nemo ɓatattu in kuma dawo da waɗanda aka watsar da su. Zan ɗora karyayyun tumaki, in warkar da marasa lafiya amma masu ƙiba da ƙarfafa zan hallaka su. Zan yi kiwo da adalci.
\s5
\v 17 Yanzu dai ku, garkena - ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗa - duba, zan shar'anta tsakanin tunkiya da tunkiya, tsakanin raguna da bunsurai.
\v 18 Bai isa ba ku ci ciyawa mai ƙyau, sai kun tattake ragowar da ƙafafunku; ku kuma sha ruwa mai kyau, sai kuma kun gurɓata rafin dukka da ƙafafunku?
\v 19 Dole ne tumakina suci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku?
\s5
\v 20 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗa masu haka: Duba! Ni da kaina zan shar'anta tsakanin tumaki masu ƙiba da ramammu,
\v 21 domin kun tunkuɗe su da kwankwasonku da kuma kafaɗunku, kun kuma tunkuɗe dukkan marasa ƙarfi da ƙahonninku har sai da kuka warwatsar da su daga ƙasar.
\s5
\v 22 Zan ceci garkena ba za su ƙara zama ganima ba, zan shar'anta tsakanin tunkiya da tunkiya!
\v 23 Zan ɗora makiyayi guda a bisansu, bawana Dauda. Shi zai yi kiwon su, zai ciyar da su, zai kuma zama makiyayinsu.
\v 24 Gama Ni, Yahweh, zan zama Allahnsu, kuma bawana Dauda zai zama sarki a cikin su - Ni, Yahweh, na furta wannan.
\s5
\v 25 Sa'an nan zan yi alƙawarin salama da su in fitar da mugayen dabbobi a ƙasar, domin su zauna lafiya a jeji su kuma yi barci lafiya a kurmi.
\v 26 Zan kuma kawo albarku a bisan su da kuma wurare kewaye da tuddaina, domin zan aiko da ruwan sama a lokacinsa. Zai zama ruwan albarka.
\v 27 Sa'an nan itatuwan saura za su bada 'ya'yansu, ƙasa za ta bada amfaninta. Tumakina za su zauna lafiya a ƙasarsu; sa'an nan ne za su sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da zan karya gungumen kãrkiyarsu, in kuma cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.
\s5
\v 28 Ba za su ƙara zama ganima ga al'ummai ba, mugayen namomin jeji a bisa ƙasa ba za su cinye su ba. Gama za su zauna lafiya, ba kuma wanda zai tsoratasu.
\v 29 Gama zan ƙebe masu mazaunin salama domin kada a ƙara zama da yunwa a cikin ƙasar, al'ummai kuma ba za su kawo zargi a kansu ba.
\s5
\v 30 Sa, an nan za su sani cewa Ni, Yahweh Allahnsu, ina tare da su. Su jama'ata ne, gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 31 Gama ku tumakina ne, garken makiyayata, mutanena, ni kuma Allahnku ne - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'"
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 'Ɗan mutum, kasa fuskarka gãba da Tsauna Seyir ka yi annabci gãba da shi.
\v 3 Ka ce masa, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi: Duba! Ina gãba da kai, Tsauni Seyir, kuma zan buge ka da hannuna in maishe ka kufai abin watsarwa.
\s5
\v 4 Zan maida biranenka kufai, kai kuma da kanka za ka zama kango; sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh.
\v 5 Domin kullum kana ƙiyayya da mutanen Isra'ila, kuma domin ka bashesu a hannun takobi a lokacin ƙuncinsu, a lokacin da hukuncinsu yake da zafi.
\v 6 Saboda haka, Muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zan shiryaka domin zubar da jini, alhakin jini zai bi ka! Tun da ba ka ƙi zubar da jini ba, alhakin jini zai bi ka.
\s5
\v 7 Zan maida Tsaunin Seyir kufai gaba ɗaya sa'ad da na datse mai shiga cikinsa da mai fita.
\v 8 Sa'an nan zan cika duwatsunsa da gawawwakinsa. Da tuddansa da kwarurukansa da dukkan rafuffukansa, waɗanda aka kashe da takobi za su fǎɗa.
\v 9 Zan sa ka yi ta zama kufai. Ba za a zauna cikin biranenka ba, amma za ka sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 10 Ka ce, "Waɗannan al'ummai biyu da ƙasashen nan biyu za su zama nawa, zan kuma mallakesu," koda yake Yahweh yana tare da su.
\v 11 muddin ina raye - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zan sãka maka gwargwadon fushinka da gwargwadon kishi da ƙiyayyar da ka yiwa Isra'ila, kuma zan bayyana kaina gare su sa'ad da na shar'anta ka.
\s5
\v 12 Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh. Na ji ɓatancin da ka yi gãba da duwatsun Isra'ila, sa'ad da ka ce, "An lalatar da su; an rigaya an ba mu su mu cinye."
\v 13 Ka ɗaukaka kanka gãba da ni da abin da ka faɗa, ka yi maganganu da yawa gãba da ni; na kuma ji su dukka.
\s5
\v 14 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Zan maishe ka kufai, dukkan duniya za suyi murna.
\v 15 Kamar yadda ka yi murna da gãdon mutanen Isra'ila saboda ta zama kufai, kai ma zan yi haka da kai. Za ka zama kufai, Tsaunin Seyir da dukkan Idom - dukkanta! Sa'an nan za ka sani cewa Ni ne Yahweh."'
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Yanzu dai, ɗan mutum, ka yi annabci ga tsaunukan Isra'ila ka ce, "Tsaunukan Isra'ila, ku saurari maganar Yahweh.
\v 2 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Magabci ya ce a kanka, "Aha!" kuma "Daɗaɗɗun tuddai na dã sun zama mallakarmu.'"
\v 3 Saboda haka ka yi annabci kace, Ubangiji Yahweh ya ce: Saboda an maishe ka kufai an kuma murƙushe ka ta kowacce fuska, ka zama abin mallaka ga sauran al'ummai; ka zama abin ɓatanci a leɓuna da harsuna, a kuma labaran mutane.
\s5
\v 4 Saboda haka, Tsaunukan Isra'ila, ku kasa kunne ga maganar Ubangiji Yahweh: Ubangiji Yahweh ya faɗi haka ga tsaunuka, da tuddai, da rafuffuka da kwarurruka, da kufafan da ba kowa da yasassun biranen da aka washe su sun zama ganima da abin ba'a ga sauran al'umman da ke kewaye da su -
\v 5 saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Hakika nayi magana cikn zafin fushina da hasalata gãba da sauran al'ummai, gãba da Idom da dukkan waɗanda suka ƙwace ƙasata suka maisheta mallakarsu, gãba da dukkan masu murna a zuciyarsu ko reni a ruhunsu, yadda suka ƙwace ƙasata domin su mallaki wuraren kiwo su zama nasu.'
\v 6 Saboda haka, ka yi annabci a kan ƙasar Isra'ila ka cewa tsaunuka da kuma tuddai, da rafuffuka da kwarurruka, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duba! A cikin fushina da hasalata nake furta wannan domin ka jure da zage-zagen al'ummai.
\s5
\v 7 Saboda haka, Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ni da kaina zan ɗaga hannuna in rantse cewa al'ummai da ke kewaye daku tabbas za su sha tasu kunyar.
\s5
\v 8 Amma ku, tsaunuka Isra'ila, za ku yi rassa ku haifi 'ya'ya domin mutanena Isra'ila, domin bada daɗewa ba za su komo wurinku.
\v 9 Ku duba, Ni naku ne, na yi maku tagomashi; za a huɗe ku a kuma shuke ku da iri.
\s5
\v 10 Saboda haka zan ruɓanya maku yawan mutanenku, koda dukkan gidan Isra'ila ne. Birane za su kasance da mazauna, za a sake gina rusassun wurare.
\v 11 Zan riɓaɓɓanya mutum da dabba a kanku ku tsaunuka saboda su ruɓaɓɓanya su hayayyafa. Sa'an nan Zan sa a zauna a cikin ku kamar yadda kuke dã, zan sa ku yalwata fiye da dã, domin ku sani cewa Ni ne Yahweh.
\v 12 Zan kawo mutane, jama'ata Isra'ila, su tattaka ku. Za su mallakeku, za ku zama gãdonsu, ba za ku ƙara sa 'ya'yansu su mutu ba.
\s5
\v 13 Ubangiji Yaweh ya faɗi haka: Saboda suna ce maku, "Ku na cinye mutane, kuna sa 'ya'yan al'ummarku suna mutuwa,"
\v 14 saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba za ku ƙara sa al'ummarku ta yi makokin mutuwarsu ba. Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 15 Ba zan ƙara bari ku sake sauraren zage-zagen al'ummai ba, ba za ku ƙara jin kunyan mutane ba ko ku sa al'ummarku ta faɗi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'"
\s5
\v 16 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo wuri na, cewa,
\v 17 "Ɗan mutum, sa'ad da gidan Isra'ila suka gaji ƙasarsu, suka ƙazamtar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Hanyoyinsu a gabana kamar ƙazantar hailar mace suke.
\v 18 Saboda haka na zuba hasalata gãba da su, domin zubar da jini da suka yi a ƙasar da kuma ƙazantarsu ta wurin gumakansu.
\s5
\v 19 Na warwatsa su cikin al'ummai; suka warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon hanyoyinsu da ayyukansu.
\v 20 Sai suka tafi cikin al'ummai, duk inda suka tafi, sai suka ɓata sunana mai tsarki sa'ad da mutane suka ce masu: 'Da gaske waɗannan mutanen Yahweh ne? Gama an fitar da su daga ƙasarsa.'
\v 21 Amma ina da juyayi saboda sunana mai tsarki wanda gidan Isra'ila ya ƙazantar cikin al'ummai lokacin da suka tafi can.
\s5
\v 22 Saboda haka ka cewa gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: 'Ba saboda ku nake wannan ba, gidan Isra'ila, amma saboda sunana mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al'ummai dukkan inda kuka tafi.
\v 23 Gama zan sa sunana mai girma ya zama da tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al'ummai - a tsakiyar al'ummai, kuka ɓata shi. Sa'an nan al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh - wannan furcin Ubagiji Yahweh ne - sa'ad da za ku ga Ni mai tsarki ne.
\s5
\v 24 Zan kwasoku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga kowacce ƙasa, zan kawo ku ƙasarku.
\v 25 Sa'an nan zan yayyafa maku tsabtataccen ruwa domin ku tsarkaka daga dukkan ƙazantarku, zan kuma tsarkake ku daga gumakanku.
\s5
\v 26 Zan ba ku sabuwar zuciya da sabon ruhu a cikinku, zan ɗauke zuciyar dutse daga cikinku. Gama zan ba ku zuciyar tsoka.
\v 27 Zan sa Ruhuna a cikinku in sa ku kuyi tafiya a cikin farillaina da kiyaye umarnaina, domin ku yi su.
\v 28 Sa'an nan za ku zauna a ƙasar da na ba kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku.
\s5
\v 29 Gama zan ceceku daga dukkan ƙazantarku. Zan sa hatsi ya yawaita. Ba zan ƙara nawaitaku da yunwa ba.
\v 30 Zan yawaita 'ya'yan itatuwa da amfanin gona domin kada ku ƙara jin kunya a wurin al'ummai saboda yunwa.
\v 31 Sa'an nan za ku yi tunani a kan mugayen hanyoyinku da ayyukanku masu banƙyama, za ku nuna naɗama a fuskokinku sabili da zunubanku da kuma mugayen ayyukanku.
\s5
\v 32 Ba dominku nake yin wannan ba - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - yakamata ku san wannan. Saboda haka, ku kunyata ku ƙasƙanta, saboda hanyoyinku ku gidan Isra'ila.
\v 33 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: A ranar da na tsarkake ku daga dukkan kurakuranku, zan sa ku zauna a birane, ku kuma gina rusassun wurare.
\v 34 Gama za ku noma ƙasa wadda take kufai a dã masu wucewa wurin ba za su gane ta ba.
\s5
\v 35 Sa'an nan za su ce, "Wannan ƙasa wadda dă kufai ce yanzu ta zama kamar lambun Iden; rusassun birane da rusassun wurare waɗanda suka zama kufai an yi masu garu a na kuma zama a cikin su."
\v 36 Sa'an nan sauran al'ummai da ke kewaye daku za su sani cewa Ni ne Yahweh, mai gina rusassun wurare da mai zaunar da mutane a yasassun wuri. Ni ne Yahweh. Ni na faɗi haka, zan kuma aiwatar da shi.
\s5
\v 37 Ubangiji Yahweh ya faɗi: Gidan Isra'ila za su roƙe ni in yi masu haka, in riɓaɓɓanya su kamar garken mutane.
\v 38 Kamar garken da aka keɓe domin hadayu, kamar garke a Yerusalem a lokacin bukukuwan idi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh."'
\s5
\c 37
\cl Sura 37
\p
\v 1 Hannun Yahweh yana bisa na, ya fito da ni waje ta wurin Ruhun Yahweh kuma ya zaunar da ni a tsakiyar wani kwari; yana cike da ƙasusuwa.
\v 2 Daga nan ya sani na bi ta tsakiyar su ina ta zagayawa, Duba! Da yawansu birjik suna cikin kwarin. Duba! Ga su busassu ƙayau.
\v 3 Sai ya ce mani, "'Dan mutum, ƙasusuwan nan za su iya rayuwa kuma?" Sai na ce, "Ubangiji Yahweh, kai kaɗai ka sani."
\s5
\v 4 Daga nan ya ce mani, "'Ka yi annabci a kan waɗannan ƙasusuwa ka ce masu, 'Busassun ƙasusuwa. Ku saurari maganar Yahweh.
\v 5 Ubangiji Yahweh ya cewa ƙasusuwan nan: Duba! Zan sa numfashi a cikinku, za ku kuma rayu.
\v 6 Zan sa jijiyoyi a jikkunanku in kuma sa tsoka. Zan rufe ku da fata in hura numfashi a cikinku domin ku rayu. Daga nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh.'"
\s5
\v 7 Sai na yi anabci kamar yadda ya umarce ni; da na ke anabcin, duba, sai wata ƙara ta fito, mai girgiza. Sai ƙasusuwan suka marmatso ga junansu - ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu.
\v 8 Da na duba, ai kuwa, sai ga jijiyoyi a kansu, tsoka kuma ta fito fata kuma ta rufe su. Amma ba numfashi a cikinsu tukuna.
\s5
\v 9 Daga nan Yahweh ya ce mani, "Yi anabci a kan numfashi, yi anabci, ɗan mutum, ka ce da numfashi, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Numfashi, ka zo daga kusurwai huɗu, ka hura a kan waɗannan da aka kashe, domin su rayu.'"
\v 10 Sai na yi anabci kamar yadda aka umarce ni; numfashi ya shiga cikinsu suka rayu. Daga nan suka miƙe a kan ƙafafunsu, babbar rundunar mayaƙa.
\s5
\v 11 Daga nan Yahweh ya ce da ni, "Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwan gidan Isra'ila ne dukka. Duba! Suna cewa, 'Kasusuwanmu sun bushe, zuciyarmu ta karai. An datse mu.'
\v 12 Saboda haka ka yi anabci ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Duba! Zan buɗe kabarbarunku in tashe ku daga cikinsu, ya ku mutane na. Zan dawo daku ƙasar Isra'ila.
\s5
\v 13 nan za ku sani cewa Ni ne Yahweh, sa'ad da na buɗe kabarbarinku na tashe ku daga cikin su, mutane na.
\v 14 Zan sa Ruhuna a cikin ku domin ku rayu, zan sa ku huta a ƙasarku sa'ad da kuka sani ni ne Yahweh. Ni na faɗa kuma zan aikata - wannan furcin Yahweh ne.'"
\s5
\v 15 Sa'an nan maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 16 "Yanzu dai, ɗan mutum, ka ɗauki sanda guda domin kanka ka yi rubutu a kan sa, 'Domin Yahuda da mutanen Isra'ila abokan tarayya.' Sa'an nan ka ɗauki wata sandar ka yi rubutu a kansa, 'Domin Yosef reshen Ifraim kuma domin dukkan mutanen Isra'ila, abokan tarayya.'
\v 17 Haɗa biyun su zama sanda guda, domin su zama ɗaya a hannunka.
\s5
\v 18 Sa'ad da mutanenka za su yi maka magana, su ce, 'Ba za ka gaya mana abin da kake nufi da waɗannan ba?'
\v 19 sai ka ce masu, 'Ubangiji Yahweh ya ce: Duba! Ina ɗauke reshen Yosef da ke hannun Ifraim da kabilar Isra'ila abokan tarayyarsa domin in haɗa shi da Yahuda, domin su zama sanda guda, za su kuma zama ɗaya a hannuna.'
\v 20 Ka riƙe sandunan da ka yi rubutu a kansu a hannunka a kan idanunsu.
\s5
\v 21 Ka furta masu, Ubangiji Yahweh yafaɗi wannan: Duba! Ina gab da fitar da mutanen Isra'ila daga cikin al'ummai inda suka tafi. Zan tattaro su daga ƙasashen kewaye in kuma dawo da su ƙasarsu.
\v 22 Zan tattaro su al'umma ɗaya a ƙasar, a kan tsaunukan Isra'ila, sarki guda ne zai yi sarauta bisansu dukka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba. Ba za a ƙara raba su zuwa masarautai biyu ba.
\v 23 Daga nan ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumakansu ba, da abubuwansu na ban ƙyama, ko kowanne irin zunubansu ba. Gama zan cece su daga dukkan ayyukan rashin aminci waɗanda da su suka yi mani zunubi, zan kuma tsarkake su, domin su zama mutanena ni kuma in zama Allahnsu.
\s5
\v 24 Bawana Dauda zai zama sarki bisansu. Domin su kasance da makiyayi ɗaya a bisansu dukka, za su yi tafiya bisa ga dokokina su kuma kiyaye farillaina su yi biyayya da su.
\v 25 Za su zauna a ƙasar da na ba bawana Yakubu, inda ubanninku suka zauna. Za su zauna cikin ta har abada - da su, da 'ya'yansu, da jikokinsu, gama bawana Dauda zai zama sarkinsu har abada.
\s5
\v 26 Zan kafa alƙawarin salama da su. Zai zama madawwamin alƙawari ne da su. Zan kafa su in ruɓanɓanya su, in kuma kafa wurina mai tsarki a tsakaninsu har abada.
\v 27 Mazaunina zai kasance tare da su; zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.
\v 28 Daga nan al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh da na ƙeɓe Isra'ila da bam, sa'ad da wurina mai tsarki yana cikinsu har abada.'"
\s5
\c 38
\cl Sura 38
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo gare ni, cewa,
\v 2 Ɗan mutum, ka juya ka fuskanci Gog, ƙasar Magog, babban yariman Meshek da Tubal; ka kuma yi anabci gãba da shi.
\v 3 Ka ce, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! ina gãba da kai, Gog, babban yariman Meshek da Tubal.
\s5
\v 4 Domin in juya ka in kuma sa maka ƙugiya a muƙamuƙinka; Zan fitar da kai da dukkan sojojinka, da dawakai, da mahaya dawakan, dukkansu sun sa kayan yaƙi sosai, babbar runduna da manyaan garkuwoyi da ƙananan garkuwoyi, dukkan su suna riƙe da takubba!
\v 5 Fasiya, Kush, da Libiya suna tare da su, dukkan su da garkuwoyi da hulunan kwano!
\v 6 Goma da dukkan rundunarta, da Bet Togama, daga arewa mafi nisa, da dukkan rundunarta! Mutane da yawa na tare da kai!
\s5
\v 7 shiri!, ka shirya kanka da tawagarka da suka yi layi tare kai, ka zama kwamandansu.
\v 8 Bayan waɗansu kwanaki da waɗansu za a kiraka, kuma bayan waɗansu shekaru za ka je wata ƙasa da ta farfaɗo daga takobi wadda kuma aka tattaro daga mutane masu yawa, tattare aka koma tsaunin Isra'ila wanda ya ci gaba da zama kango. Amma mutanen ƙasar za a fito da su daga mutanen, kuma za su zauna cikin tsaro, dukkan su!
\v 9 Saboda za ka tashi sama kamar yadda hadari ke yi; za ka zama kamar girgijen da yake rufe ƙasar, da duk rundunar sojojinka, da sojoji masu yawa da ke tare da kai.
\s5
\v 10 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: zai kuma faru a wannan ranar da aka tsara wannan shiri a zuciyarka, kuma za ka ɓata mugayen shirye-shirye.'
\v 11 Daga nan za ka ce, zan je can buɗaɗɗiyar ƙasa; zan je wurin mutane masu natsuwa da ke zama cikin tsaro, dukkan su da ke rayuwa a inda babu garu ko danga, inda babu ƙofofin birane.
\v 12 Zan kwaso kayayyaki in saci ganima, domin in kawo hannuna gaba da kangayen da yanzu mutane suka fara zama, da kuma gaba da al'ummai waɗanda ke samun dabbobi da kayayyaki, waɗanda kuma ke zama a tsakiyar duniya.'
\s5
\v 13 Sheba da Dedan, da 'yan kasuwar Tarshish haɗe da matasan mayaƙanta za su ce da kai, Kun zo ne domin ku kwashi ganima? Kun tattara sojoji ne domin ku kwashi ganima, domin ku kwashi azurfa da zinariya, ku kuma kwashi dabbobinsu da kayayyaki ku kuma kwashi garar ganimar yaƙi?'
\s5
\v 14 Saboda haka, ɗan mutum ka yi anabci, ka ce da Gog, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wannan rana, lokacin da mutanena Isra'ila na zama cikin tsaro, ba za ku koyi wani abu ba game da su?
\v 15 Za ku fito daga wurarenku a can arewa mafi nisa tare da babbar rundunar sojoji, dukkan su suna kan dawakai, babbar runduna, manyan mayaƙa.
\v 16 Za ka kai hari ga mutanena Isra'ila kamar girgijen da ya rufe ƙasar. A kwanaki masu zuwa zan kawo ka gãba da ƙasata, domin ƙasashe su san ni a lokacin da na nuna kaina ta wurinka, Gog, ka zama da tsarki a idanunsu.
\s5
\v 17 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ba ku ba ne waɗanda na yi magana a kan ku a waɗancan kwanaki ta hannun bayina, annabawan Isra'ila, waɗanda suka yi anabci a nasu lokuttan game da shekarun da zan kawo ku gãba da su?
\v 18 Haka zai faru a waɗancan kwanaki bayan Gog ya kai hari ƙasar Isra'ila - wannan furcin Yahweh ne - fushina zai yi ƙuna a cikin hasalata.
\s5
\v 19 A cikin himmata da kuma cikin wutar fushina, na furta cewa za'a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra'ila.
\v 20 Za su girgiza a gabana - da kifayen teku da tsuntsayen sama, da dabbobin saura, da dukkan dabbobi masu rarrafe a duniya, da kowanne mutum da ke a doron ƙasa. Za'a ragargaza duwatsu ɓallin zai faɗi, har sai kowacce kusurwa ta faɗi a kan duniya.
\s5
\v 21 Zan kawo takobi a kansu a kan dukkan duwatsu -wannan shi ne furcin Ubangiji Yahweh - kowanne mutum zai juya takobinsa gãba da ɗan'uwansa.
\v 22 Bayan wannan zan hukunta shi da annoba da jini; da kuma ambaliyar ruwa da aman duwatsu da tattatsin wuta zan saukar a kansa shi da rundunarsa da dukkan al'umman da ke kewaye da shi.
\v 23 Domin zan nuna girmana da tsarkina zan kuma sa al'ummai da yawa su san ni, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh.'"
\s5
\c 39
\cl Sura 39
\p
\v 1 "Yanzu, kai ɗan mutum, ka yi annabci gãba da Gog ka ce, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Duba! ina gãba da kai Gog, sarkin Meshek da Tubal.
\v 2 Zan juya ka in bi da kai; Zan kawo ka daga can arewa in kawo ka tsaunukan Isra'ila.
\v 3 A sa'an nan ne zan bugi bakanka daga hannunka na hagu in kuma sa kibiya ta faɗi daga hannunka na dama.
\s5
\v 4 Za ka fãɗi ƙasa matacce a kan tsaunukan Isra'ila -kai da tawagar da ke tare da kai da kuma sojojin da ke tare da kai. Zan miƙa ka ga tsuntsayen sama da dabbobin dawa ka zama abincinsu.
\v 5 Za ka faɗi ƙasa a saura, domin ni da kaina na furta haka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 6 Daga nan zan aika da wuta a kan Magog a kan kuma masu zama cikin tsaro a wurare masu nisa, za su kuma sani cewa Ni ne Yahweh.
\s5
\v 7 Domin zan sa su san sunana mai tsarki a tsakiyar mutanena Isra'ila, kuma ba zan taɓa yadda sunana ya ɓaci ba; al'ummai za su sani cewa Ni ne Yahweh, mai Tsarki na Isra'ila.
\v 8 Duba! Rana na zuwa, kuma za ta zo - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 9 Masu zama a biranen Isra'ila za su fita za su mori makamai su kunna wuta su ƙone su - ƙananan garkuwoyi, da manyan garkuwoyi, da bakkuna, da kibau, da kwarin mashi; za su wuta da su har tsawon shekaru bakwai.
\v 10 Ba za su tattara itatuwa daga saura ba ko su sassaro bishiyoyi daga dawa, tun da ya ke za su ƙona makamansu; za su ɗauka daga wurin waɗanda ke son su ɗauka daga gare su; za su baje waɗanda suka so su baje su - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\v 11 Kuma zai zamana a wannan rana zan tanada wuri domin Gog - maƙabarta a Isra'ila, kwari ga waɗanda ke tafiya cikin gabashin kwarin teku. Zai toshe waɗanda ke son ƙetarewa su haye. A can za su binne Gog da dukkan mutane masu yawa da ke tare da shi. Za su kira shi kwarin Hamon Gog.
\s5
\v 12 Har tsawon watanni bakwai gidan Isra'ila za su binne su domin su tsarkake ƙasar.
\v 13 Domin dukkan mutanen ƙasar za su binne su; za su zama abin tunawa a gare su a lokacin da na sami ɗaukaka - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 14 A sa'an nan ne za su keɓe mutanen da za su ci gaba da tafiya a cikin ƙasar, domin su sami waɗanda ke tafiya a ciki, amma waɗanda suka mutu gangar jukkunansu kuma na waje a ƙasar za su iya su binne su, domin su tsarkake ƙasar. A ƙarshen shekarun nan bakwai za su fara bincikensu.
\v 15 A lokacin da mutanen nan ke tafiya a cikin ƙasar, bayan sun ga ƙashin mutum za su sa alama a gefenta, har sai masu haƙar kabari sun zo domin su binne su a kwarin Hamon Gog.
\v 16 Za'a sami wani birni a can ta wurin sunan Hamona. A wannan hanya za su tsarkake ƙasar.
\s5
\v 17 Yanzu a gare ka, ɗan mutum, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ka faɗi wannan ga dukkan tsuntsayen sama da dukkan dabbobin daji, 'Ku taru wuri ɗaya ku zo. Ku tattaru daga ko'ina ku kewaye hadayar da ni kaina nake miƙawa a kan tsaunukan Isra'ila, domin ku ci gangar jiki ku kuma sha jini.
\v 18 Za ku ci jikkunan mayaƙa ku kuma sha jinin shugabannin duniya; za su zama raguna, da 'yan raguna, da awaki. da bijimai, duk sun yi ƙiba a Bashan.
\s5
\v 19 Daga nan za ku ci wadataccen kitse ku ci ku ƙoshi; ku kuma sha jini har sai kun bugu; wannan ita ce hadayar da zan yanka dominku.
\v 20 A kan teburina za ku ƙoshi da dawakai, da karusai, da mayaƙi, da dukkan jaruman yaƙi - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.'
\s5
\v 21 Zan sa ɗaukakata a cikin al'ummai, kuma dukkan al'ummai za su ga hukuncina da nayi da kuma hannuna da na sa nake gãba da su.
\v 22 Gidan isra'ila za su sani cewa Ni ne Yahweh Allansu daga wannan rana zuwa gaba.
\s5
\v 23 Al'ummai za su sani cewa gidan Isra'ila sun je bauta saboda laifofinsu wanda ta wurinsu suka bashe ni, domin haka na ɓoye fuskata daga gare su, na kuma miƙa su ga abokan gãbarsu domin a hallaka dukkan su da takobi.
\v 24 Na yi masu gwargwadon ƙazantarsu da zunubansu, a lokacin da na kawar da fuskata daga gare su.
\s5
\v 25 Saboda haka Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan; Yanzu zan komo da damar Yakubu, kuma zan ji tausayin dukkan gidan Is'raila, a lokocin da na yi haka da himmar sunana mai tsarki.
\v 26 A lokacin za su sha kunyarsu a cikin dukkan cin amanar da suka bashe ni. Za su manta da duk wannan a lokacin da suka huta a cikin ƙasarsu cikin tsaro, inda ba wanda zai firgita su.
\v 27 lokacin da na komo da su daga cikin jama'a na kuma tattaro su daga ƙasar maƙiyansu, zan nuna kaina a matsayin mai tsarki a idon al'ummai masu yawa.
\s5
\v 28 Sa'an nan za su sani cewa Ni ne Yahweh Allahnsu, domin na aika su zuwa bauta a cikin al'ummai, amma zan sake tattara su a ƙasarsu. Ba zan rage ko ɗaya daga cikinsu ba a cikin al'ummai.
\v 29 Ba zan sake ɓoye fuskata daga garesu ba a lokacin da na huro Ruhuna a kan gidan Isra'ila - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 40
\cl Sura 40
\p
\v 1 A cikin shekara ta ashirin da biyar ta bautar talalarmu a farkon shekara a rana ta goma ga wata, A shekara ta sha huɗu bayan an kame birnin a wannan dai ranar, hannun Yahweh na bisana ya kuma ɗauke ni zuwa can.
\v 2 A cikin wahayai daga Allah sai ya kawo ni zuwa ƙasar Isra'ila. Ya kawo ni in huta a kan tsauni mai tsawo sosai; a ɓangaren kudu inda abin da ya bayyana ya zama gine-ginen birni.
\s5
\v 3 Sai ya kawo ni can. Sai ga wani mutum! Bayyanuwarsa kamar bayyanuwar tagulla. Yana ɗauke da igiyar linin da sandar awo a hannunsa, sai ya tsaya a bakin ƙofar birnin. Mutumin ya ce da ni,
\v 4 "Dan mutum, ka duba da idanunka ka kuma saurara da kunnuwanka, ka kuma maida hankali ga dukkan abin da nake bayyana maka, domin an kawo ka nan ne domin in bayyana maka su. Ka bada rahoton duk abin da za ka gani ga gidan Isra'ila."
\s5
\v 5 Akwai katangar da ta kewaye haikali. Tsawon sandar awon a hannun mutumin kamu shida ne. Dukkan mizanan tsawonsu iri ɗaya. Sai ya auna katangar; ta kai kamu ɗaya da rabi na tsawon sandar awon.
\v 6 Daga nan sai ya tafi ƙofar haikali da ke fuskantar gabas. Sai ya hau kan matakansa ya auna ginshiƙin ƙofar tsawonsa shi ne dai-dai tsawon sandar gwajin a zurfi.
\v 7 Ɗakunan tsaron dukkan su kamun sandar awon ɗaya a tsawo kuma ɗaya ne a fãɗi; akwai tsawon kamu biyar a tsakanin kowanne ɗakuna biyu, kuma daga dankarin shirayin haikalin akwai kwararo mai tsayi da aka kafa ƙasa.
\s5
\v 8 Sai ya auna kwararon ƙofar; faɗinsa ya kai kamu guda na sandar awon.
\v 9 Ya auna kwararon ƙofar. Zurfinsa ya kai kamu guda na sandar awo. Madogaran ƙofofin sun kai kamu biyu a fãɗi. Wannan shi ne kwararon ƙofar da ke fuskantar haikali.
\v 10 Akwai ɗakunan tsaro guda uku a kowacce kwana a ɓangaren gabas, kuma dukkan su suna da awo iri ɗaya ne, kuma katangar da ta raba su ita ma awo iri ɗaya ne.
\s5
\v 11 Daga nan mutumin ya auna faɗin ƙofar shiga - aka sami kamu goma; kuma faɗin ƙofar shiga - ya kai kamu goma sha uku.
\v 12 Sai ya auna katangar da ke iyaka da ɗakuna na gaba - tsayinta kamu guda ne. Aka auna ɗakunan kowannen su ya kai kamu shida a kowanne gefe.
\v 13 Daga nan sai ya auna ƙofar shiga daga rufin ɗaya daga cikin ɗakin har zuwa ɗaki na gaba - aka sami kamu ashirin da biyar, daga ƙofar farko ta shiga ɗakin har ya zuwa ta biyun.
\s5
\v 14 Daga nan ya auna katangar da ta bi ta tsakanin ɗakunan tsaron - tsawonsu ya kai kamu sittin; ya auna har ya zuwa kwararon ƙofar.
\v 15 Mashigi daga ƙofar gaba har ya zuwa kwararon ƙofar ƙarshen kamu hamsin.
\v 16 Akwai kullallun tagogi a kusa da ɗakunan da kuma kusa da madogaran da ke cikin dukkan ƙofofin da ke kewayen; hakannan kuma zaurukan. Akwai tagogin da ke kewaye a ciki, kuma kowanne ƙyaure an yi masa ado da itacen kwakwa.
\s5
\v 17 Sai mutumin ya kawo ni harabar waje da haikalin. Duba, ga ɗakuna, akwai gefen hanya a harabar, da kuma ɗakuna sittin a gaban harabar, da ɗakuna talatin gaba da gefen hanyar.
\v 18 Gefen hanyar ya bi ta gefen ƙofofin, kuma fasalinsu ɗaya ne da tsawon ƙofofin. Wannan shi ne gefen hanya mafi kwari.
\v 19 Sai mutumin ya auna nisan daga gaban ƙaramar ƙofa zuwa gaban ƙofofi na ƙurya; kamu ɗari ne daga bangon gabas, haka kuma yake a bangon arewa.
\s5
\v 20 Daga nan sai ya auna tsawo da fadin ƙofar da ke arewa a can cikin harabar waje
\v 21 Akwai ɗakuna guda uku a kowanne gefe na ƙofar, ƙofar da kwararonta duk suma an auna su kamar yadda aka auna babbar ƙofar - tsawonta dukka kamu hamsin ne sai fadinta kuma kamu ashirin da biyar ne
\s5
\v 22 Tagogin, da kwararon, da ɗakunan, da bishiyoyin dabinon da aka sa a ƙofar da ke fuskantar gabas. Taki bakwai su ne suka kai kwararonsa.
\v 23 Akwai kuma wata ƙofar daga ciki wadda ke fuskantar arewa, kamar dai yadda akwai ƙofa a gabas; mutumin ya auna daga ƙofa ɗaya zuwa ƙofa ɗaya - ya sami kamu dari na nisa.
\s5
\v 24 A gaba sai mutumin ya kawo ni ƙofar shiga ta kudu, kusurwarta da tsawonta suma ya auna su kamar yadda ya auna sauran ƙofofin.
\v 25 Akwai tagogi da ke a kulle a kan hanyar ƙofar da kwararonta kamar dai irin na waccan ƙofar. Kofar kudu da kwararonta tsawonta kamu hamsin ne faɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne.
\s5
\v 26 Akwai kuma ƙofa zuwa can ƙuryar harabar daga bangon kudu tsawonta kamu ɗari ne.
\v 27 Akwai matakai bakwai da ake hawa zuwa ƙofar da kwararonta akwai kuma itacen dabino da aka kewaye katangar da su a kowanne gefe.
\s5
\v 28 Sai mutumin ya kawo ni ƙuryar harabar ta hanyar ƙofarsa ta kudu, wadda ke da awo irin na sauran ƙofofin.
\v 29 da bangayen, da kwararon duk awonsu dai-dai ne da na sauran ƙofofin; kuma akwai tagogi a ko'ina a kwararon. ƙofar ciki da girmanta kamu hamsin ne na tsawo kuma faɗinta kamu ashirin da biyar ne.
\v 30 Kuma akwai kwararo da suka kewaye katangar ta ta ciki a ko'ina; waɗannan ne ma su kamu ashirin da biyar a tsawo da kuma kamu biyar na faɗi.
\v 31 Wannan kwararo ya fuskanci harabar waje da aka kewaye da sassaƙaƙƙun itatuwan dabino a bangonta kuma akwai matakai takwas da a ke takawa a hau samanta.
\s5
\v 32 Daga nan sai mutumin ya kawo ni cikin haraba ta ƙurya ta bangon gabas ya kuma auna ƙofar, ita ma awonsu ɗaya da sauran ƙofofin.
\v 33 Ɗakunansa, da bangayen, da kwararon suma an auna su kamar yadda aka auna sauran ƙofofin, kuma awonsu dai-dai, kuma akwai tagogi a kewaye a ko'ina. Ƙofar ciki da kwararonta an auna tsawonsu kamu hamsin, faɗinsu kuma kamu ashirin da biyar.
\v 34 Kwararonta na fuskanci harabar waje; kuma tana da itatuwan dabino a kowanne gefe kewaye da matakai takwas na hawa bisansa.
\s5
\v 35 A gaba sai mutumin ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta; awonta dai-dai ne da sauran ƙofofin.
\v 36 Ɗakunanta, da bangayenta, da kwararonta duk ɗaya suke da sauran ƙofofin, akwai kuma tagogi a kewaye a ko'ina. ƙofar shiga da kwararonta an auna kamu hamsin na tsawo, sai kamu ashirin da biyar na faɗi.
\v 37 Kwararonta na fuskantar harabar waje; tana kuma da itatuwan dabino a kowacce kusurwarsa da kuma matakai takwas na hawa samansa.
\s5
\v 38 Akwai ɗaki da ƙofa a kowanne gefe na hanyoyin shiga da ke ciki. Wannan ne wurin da suke ɗauraye baye-baye na ƙonawa.
\v 39 Da tebura guda biyu a kowanne gefen kowanne kwararo, inda a ke yanka baikon ƙonawa a kai, haka kuma baiko na zunubi da kuma baiko na laifi.
\s5
\v 40 Bangon harabar, da ya bi ta ƙofa zuwa arewa, akwai tebura guda biyu. Hakan nan a ɗaya gefen shi ma akwai tebura guda biyu a kwararon ƙofar.
\v 41 Akwai kuma tebura guda huɗu a kowanne gefe wurin ƙofa; su na yanka dabbobi a kan teburan nan guda takwas.
\s5
\v 42 Akwai kuma tebura huɗu na yakkakken dutse domin baye-baye na ƙonawa, tsawonsu kamu ɗaya da rabi, sanan faɗinsa rabin kamu ne, tsayinsa kuma kamu guda ne. A kansu suke ɗora kayayyakin da suke yanka baye-baye na ƙonawa da su.
\v 43 Aka kakkafa matsirai guda biyu tsawonsu kamun hannu ne a kwararon kewaye da ko'ina, domin a dinga ƙyafe naman baye-bayen da za'a miƙa a kan teburan.
\s5
\v 44 A waje da ƙofar ciki, a cikin harabar ciki, akwai ɗakuna na mawaƙa, ɗaya daga gefen arewa yana fuskantar kudu, ɗayan kuma daga gefen kudu yana fuskantar arewa.
\v 45 Bayan haka sai mutumin ya ce da ni, "Wannan ɗakin da ke fuskantar kudu domin firistoci ne waɗanda ke kan aiki a cikin haikali.
\s5
\v 46 Ɗakin da ke duban arewa na firistocin da ke kan aiki ne a bagadi. Waɗannan sune 'ya'yan Zadok da suka zuwa kusa da Yahweh domin su bauta masa; suna cikin 'ya'yan Lebi."
\v 47 A gaba sai ya auna harabar - tsawo kamu dari faɗi kuma kamu ɗari ne, tare da bagadi a gaban gidan.
\s5
\v 48 Sai mutumin ya ɗauko ni ya kawo ni kwararon gidan ya kuma auna madogaran ƙofofin - kaurinsu ya kai kamu biyar a kowanne gefe. Hanyar shiga ita kanta kuma sha huɗu ne a faɗi, kuma bangayen kowanne gefe faɗinsu kamu uku ne.
\v 49 Tsawon kwararon ya kai kamu ashirin, kuma zurfinsa ya kai kamu sha ɗaya. Akwai matakai da suka nufe shi sama da lungunan da ke a kowanne gefen gini.
\s5
\c 41
\cl Sura 41
\p
\v 1 Sai mutumin ya kawo ni cikin wuri mai tsarki na haikali, sai ya auna madogaran ƙofofin - faɗinsa kamu shida ne ta kowanne gefe.
\v 2 faɗin hanyar ƙofar ya kai kamu goma; bagon a kowanne gefe ya kai kamu biyar a tsawo. Daga nan sai mutumin ya auna fasalin wuri mai tsarki - tsawonsa kamu arba'in da faɗinsa kamu ashirin.
\s5
\v 3 Daga nan mutumin ya tafi ya shiga wuri mafi tsarki ya auna madogaran hanyar ƙofar - aka sami awo biyu, hanyar ƙofar kuma kamu shida ne faɗinsa. Bangayen ta kowanne gefe kamu bakwai ne a faɗi.
\v 4 Daga nan sai ya auna tsawon ɗaki - awo ashirin ne. Faɗinsa kuma - kamu ashirin ne zuwa gaban sararin haikalin. Daga nan sai ya ce mani, "Wannan shi ne wuri mafi tsarki."
\s5
\v 5 Sai mutumin ya auna bangon gidan - kaurinsa kamu shida ne. Faɗin kowanne gefen ɗaki kewaye da gidan kamu huɗu ne a faɗi.
\v 6 Akwai ɗakuna a gefe bisa hawa ku, ɗaki ɗaya bisa ɗaya, akwai ɗakuna talatin a kowanne hawa. Akwai ginshiƙai kewaye da bangon gidan, domin su zama makarai na dukkan ɗakunan da ke gefe, domin babu makarin da aka sa a bangon gidan.
\v 7 To ɗakunan gefen suka faɗaɗa suka kewaya suka nufi sama, domin gidan ya zama bene kan bene a kewaya; ɗakunan suna faɗaɗa yayin da gida ke yin sama, hawan benen ya hau zuwa mataki mafi bisa, ta cikin mataki na tsakiya.
\s5
\v 8 Sa'an nan na ga sashen da aka ɗaga dukkan kewayen gidan, da harsashe domin ɗakunan gefe; an auna shi kamun tsayin sanda - wato awo shida.
\v 9 Faɗin bangon ɗakunan gefe ta waje awo biyar ne. Akwai kuma wuri buɗaɗe a wajen waɗannan ɗakunan a masujada.
\s5
\v 10 A ɗaya gefen na wannan buɗaɗɗen fili akwai ɗakunan firistoci da ke waje; wannan filin faɗinsa ya kai awo ashirin a dukkan kewayen masujadar.
\v 11 Akwai ƙofofi a cikin ɗakunan gefe daga wani buɗaɗɗen filin -akwai kuma wata hanyar ƙofar daga bangon arewa, da kuma wata daga kudu. Faɗin wannan buɗɗaɗen fili dukka kamu biyar ne.
\s5
\v 12 Ginin da ya fuskanci harabar daga yamma ya kai kamu saba'in a faɗi. Bangonsa kuma da aka auna ya kai kamu biyar a kauri a kewaye da ko'ina, tsawonsa kuma ya kai kamu tasa'in.
\v 13 Daga nan sai mutumin ya auna masujadar - tsawonsa kamu ɗari ne. Ginin da ke ware, da bangonsa, da harabar duk suma an auna su tsawonsu kuma ya kai kamu ɗari.
\v 14 Faɗin gaban harabar a gaban masujadar shi ma kamu ɗari ne.
\s5
\v 15 Sai mutumin ya auna tsawon ginin da ke bayan masujadar, zuwa yammacinsa, da ɗakunan ajiya da ke a dukkan gefen - aka sami awo ɗari. Wuri mai tsarki da kwararon,
\v 16 da bangayen ciki da tagogi da duk da ƙananan tagogi, da ɗakunan ajiya kewaye da dukkan hawa ukunnan, duk an ƙayata su da katako
\v 17 A saman hanyar shiga zuwa masujada ta ciki da kuma filin da ke wurin shi ma duk an auna shi.
\s5
\v 18 An yi masa ado da kerubim da itatuwan dabino a tsakanin kowanne kerubim da kerubim, kuma kowanne kerubim na da fuskoki biyu:
\v 19 fuskar mutum na duban itacen dabino ta gefe ɗaya da kuma fuskar sagarin zaki da ke duban ɗaya gefen. Sun kewaye ko'ina na gidan,
\v 20 Doga ƙasa har zuwa saman hanyar ƙofa, an kewaye shi da kerubim da kuma itatuwan dabino a dukkan bangon gidan
\s5
\v 21 Madogaran ƙofar wuri mai tsarki an yi masu zagaye. Kammanninsu kamar kamannin
\v 22 bagadin katako ne a gaban wuri mai tsarki, wanda bisansa kamu uku ne, tsawonsa kuma kamu biyu ne ta kowanne gefe. Madogaran kusurwa, da harsashen, da matokaranta, da katako aka yi su. Sai mutumin ya ce da ni, "Wannan shi ne teburin da ke tsaye a gaban Yahweh."
\v 23 Akwai ƙofofi ruɓi biyu manne domin wuri mai tsarki da kuma wuri mafi tsarki.
\v 24 Waɗannan ƙofofin suna da maƙalatun ƙofa guda biyu, maƙalatun ƙofa biyu domin kowacce ƙofa.
\s5
\v 25 Aka sassaƙa a kansu - a kan ƙofofin wuri mai tsarki - kerubim ne da itatuwan dabino, kamar dai yadda aka yi wa bango ado, kuma an yi rufin katako a kan kwararon daga gaba.
\v 26 Akwai kuma tagogi da itatuwan dabino a gefen kwararon waɗannan su ne ɗakunan da ke gefen gidan, suma kuma suna da rufi a sama.
\s5
\c 42
\cl Sura 42
\p
\v 1 A gaba sai mutumin ya aike ni waje zuwa harabar ciki daga wajen arewa, sai ya kawo ni ɗakuna a gaban harabar waje da kumabangon waje daga kudu.
\v 2 Waɗannan ɗakunan sun kai kamu ɗari a tsawonsa a gaba sai kuma kamu hamsin na faɗi.
\v 3 Waɗansu daga cikin ɗakunan sun fuskanci harabar ciki nisansu daga masujadar ya kai kamu ashirin. Akwai ɗakuna hawa uku waɗanda ke sama suna duban ƙasa na waɗanda ke ƙasa da su, an kuma bubbuɗe masu ƙofofin da a ke bi. Waɗansu ɗakunan kuma suna duban haikalin.
\s5
\v 4 Sararin wucewa kamu goma ne na faɗi da kuma kamu ɗari na tsawo su ne a gaban ɗakunan. Ƙofofin ɗakunan na duban arewa.
\v 5 Amma ɗakunan taro na sama ƙanana ne daga nan ne a ke samun hanyar wucewa, ƙofofin suna da faɗi fiye da filin da ke a ƙasa da kuma tsakiyar matakai na ginin.
\v 6 Domin ɗakunan taron da ke hawa na uku ba su da shingaye. Ba kamar harabar ba, da ke da shingaye. To benayen da ke can sama ƙanana ne in kwatanta da girman ɗakunan da ke ƙarƙas da kuma benaye na hawan tsakiya.
\s5
\v 7 Bangon da ke waje ya bi ta kusa da harabar ciki, harabar da ke gaban ɗakunan. Wannan bangon ya kai kamu hamsin a tsayi.
\v 8 Tsawon ɗakunan ya kai kamu hamsin, ɗakunan da ke fuskantar masujada kamunsu kamu ɗari ne a tsawo.
\v 9 Akwai hanyar shiga ta ɗakunan da ke kwari da ke gefen gabas, da suka fito daga wajenharabar waje.
\s5
\v 10 A gefen bangon harabar waje da ke gefen gabas da harabar waje, a gaban harabar ciki na masujada, akwai kuma waɗansu ɗakunan
\v 11 da hanyar wucewa a gabansu. Suna kama da bayyanuwar ɗakunan a gefen arewa. Suna da tsawo da faɗi iri ɗaya kuma kasancewar iri ɗaya ne da jerin da ƙofofin.
\v 12 A gefen kudu akwai ƙofofin zuwa cikin ɗakuna waɗanda suke dai-dai da da na gefeb arewa. Sararin wucewa daga ciki yana da ƙofa bisa kansa, kuma sararin wucewar ya buɗe zuwa cikin ɗakuna daban-daban. A gefen gabas akwai hanya da ke zuwa sararin wucewar a ƙarshe ɗaya.
\s5
\v 13 Daga nan sai mutumin ya ce da ni, "Ɗakunan da ke arewa da kuma ɗakunan da ke kudu waɗanda ke a gaban harabar waje ɗakuna ne masu tsarki inda firistocin da ke aiki kusa da Yahweh za su iya cin abinci mafi tsarki. Za su ajiye abubuwa mafiya tsarki a can - baiko na abinci, da baiko na zunubi, dabaiko na laifi - domin wannan wuri mai tsarki.
\v 14 Sa'ad da firistoci suka shiga can, ba za su fita daga wuri mai tsarki ba zuwa harabar waje, ba tare da sun ajiye tufafin da suea yin hidima da su ba, tun da ya ke waɗannan masu tsarki ne. To dole ne su sa waɗansu tufafin na da ban kafin su kusanci mutane."
\s5
\v 15 Mutumin ya gama auna gida na ciki daga nan sai ya ɗauke ni zuwa waje zuwa ƙofar da ke duban gabas ya auna dukkan filayen da ke kewaye a can.
\s5
\v 16 Ya auna gefen gabas da sandar awo - ya sami kamu ɗari biyar da sandar awon.
\v 17 Ya auna gefen arewa - awo ɗari biyar da sandar awo.
\v 18 Hakannan ya auna gefen kudu - awo ɗari biyar da sandar awo.
\v 19 Ya kuma juya ya auna gefen yamma - awo ɗari biyar da sandar awo.
\s5
\v 20 Ya auna sassan guda huɗu. Akwai bango a kewaye da shi tsawonsa kamu ɗari biyar, da kuma kamu ɗari biyar a faɗi, domin ya raba tsakanin wuri mai tsarki da kuma dandali.
\s5
\c 43
\cl Sura 43
\p
\v 1 Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da ta buɗe zuwa gabas.
\v 2 Duba! ɗaukakar Allah na Isra'ila na zuwa daga gabas; muryarsa kamar rurin ruwaye masu yawa, duniya kuma ta haskaka da ɗaukakarsa.
\s5
\v 3 Bisa ga bayyanuwar wahayin dana gani ne, bisa ga wahatin dana gani sa'ad da yazo domin ya lalatar da birnin, wahayoyin kuma sun yi kama da wahayin dana gani a Kogin Keba - sai na faɗi da fuskata.
\v 4 Sai ɗaukakar Yahweh ta zo gidan daga ƙofar da ta buɗe zuwa gabas.
\v 5 Sai Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin harabar ciki. Duba! ɗaukakar Yahweh ta cika gidan.
\s5
\v 6 Mutumin na tsaye a gefena, sai na ji muryar wani mutumin da ban na magana da ni daga gidan.
\v 7 Ya ce mani, "Ɗan mutum, wannan ne wurin kursiyina da kuma wurin sawayen ƙafafuna, inda zan zauna a tsakiyar mutanena Isra'ila har abada. Gidan Isra'ila ba za su ƙara rena sunana mai tsarki ba - su ko sarakunansu - da rashin amincinsu ko kuma da gawayen sarakunansu bisa dogayen wurarensu ba.
\v 8 Ba za su sake rena sunana mai tsarki ba ta wurin kafa dankarin gidansu, da dankarin gidana ba, da kuma madogaran ƙofofinsu da madogaran ƙofofina ba, babu wani abu sai katanga kawai tsakanina da su. Suka rena sunana mai tsarki da ayyukansu na ƙazanta, sai na cinye su cikin fushina.
\s5
\v 9 Yanzu bari su kawar da rashin amincinsu da gawarwakin sarakunansu daga gabana, daga nan in zauna a tsakiyarsu har abada.
\s5
\v 10 Ɗan mutum, kai da kanka dole ka gaya wa gidan Isra'ila game da wannan gida domin su ji kunyar kurakuransu. Su yi tunani game da wannan kwatancin.
\v 11 Gama idan suka ji kunyar abin da suka yi, dagaan sai ka bayyana masu zanen gidan, da dukkan abin da ya ƙunsa, da wanzuwarsa, da hanyoyin shiga cikinsa, dukkan dokoki da ka'idodinsa. Daga nan sai ka rubuta wannan a gaban idanunsu domin su kiyaye dukkan tsarinsa da dukkan dokokinsa, domin su yi biyayya da su.
\s5
\v 12 Wannan ne ka'idar gidan: Daga ƙololuwar tudu zuwa dukkan kewayen kan iyakar da ta kewaye shi, za ya zama mafi tsarki. Duba! wannan ce ka'idar gidan.
\s5
\v 13 Waɗannan ne za su zama gwaje-gwajen bagadin bisa ga kamu-kamun kuwa dai-dai kamun tafin hannu a tsawonsa. To ramin da ke kewaye da bagadin zurfinsa za ya zama kamu ɗaya, faɗin sama kamu ɗaya. Kan iyakar da ke kewaye da gefensa zaya zama taƙi daya. Wannan ne za ya zama ƙasan bagadin.
\v 14 Daga ramin daɓen ƙasa zuwa hawa na farko na bagadin kamu biyu ne, hawa na farkon kansa faɗinsa kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin hawan kuma zuwa babban hawan bagadin kamu huɗu ne, babban hawan kuma faɗinsa kamu ɗaya ne.
\s5
\v 15 Murhun bagadin kuma domin baye-baye na ƙonawa bisansa kamu huɗu ne, akwai kuma ƙahonni huɗu da suka fuskanci sama a bisa murhun.
\v 16 Tsawon murhun kamu sha biyu ne faɗinsa kuma kamu sha biyu ne, a kewaye.
\v 17 Kan iyakarsa kuma tsawonsa kamu sha huɗu fadinsa kamu sha huɗu a fannoninsa huɗu, gefensa kuma rabin kamu a faɗi. Ramin kuwa faɗinsa kamu ɗaya ne a dukkan kewayen da matakalunsa na fuskantar gabas.
\s5
\v 18 Daga nan sai ya ce mani, "Ɗan mutum, Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Waɗannan ne ka'idoji domin bagadi a ranar da aka yi su, domin ɗaga baikon ƙonawa a kansa, da kuma yayyafa jini a kansa.
\v 19 Za ku bada maraƙi daga cikin garken shanu a matsayin baikon zunubi domin Lebiyawa firistoci waɗanda ke na zuriyar Zadok, waɗanda ke zuwa kusa da ni su yi mani bauta - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 20 Sai ka ɗauki jinin ka sa a ƙahonnin huɗu na bagadin, da fannoni huɗu na hawan da kewayen gefen kuma; za ka tsaftace shi ka kuma yi kaffara domin sa.
\v 21 Sai ka ɗauki maraƙin baikon zunubin ka ƙona a wurin da aka zaɓa a sashen harabar haikalin da ke waje da masujadar.
\s5
\v 22 A rana ta biyu sai ka miƙa bunsuru marar aibi daga garken awaki a matsayin baikon zunubi; Firistocin za su tsaftace bagadin da shi kamar yadda suka tsaftace shi da maraƙin.
\v 23 Idan kuka gama tsaftace shi, sai ku miƙa maraƙi marar aibi daga garken shanu da rago marar aibi daga garken tumaki.
\v 24 Ku miƙa su a gaban Yahweh; Firistocin za su barbaɗa masu gishiri su ɗaga su sama a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh.
\s5
\v 25 Dole ku shirya bunsuru a matsayin baikon zunubi kullum har kwanaki bakwai, Firistoci kuma dole su shirya maraƙi marar aibi daga garken shanu da rago marar aibi daga garken tumaki.
\v 26 Dole su yi kaffara ta kwana bakwai domin bagadin su tsarkake shi, ta wannan hanya dole su keɓe shi.
\v 27 Dole su kammala waɗannan kwanaki, a rana ta takwas kuma da nan gaba za ya kasance Firistocin za su shirya baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a kan bagadin, kuma zan karɓe ku - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 44
\cl Sura 44
\p
\v 1 Sai mutumin ya dawo da ni ƙofar masujadar da ke fuskantar gabas; an rufe ta gam.
\v 2 Yahweh ya ce mani, "An datse wannan ƙofar gam; ba za a buɗe ta ba. Babu wanda za ya bi ta cikin ta, gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bi ta cikin ta, domin haka an rufe ta gam.
\v 3 Shugaban Isra'ila za ya zauna a kai ya ci abinci a gaban Yahweh. Za ya shiga ta rumfar ƙofar ya kuma fita ta cikin ta."
\s5
\v 4 Daga nan sai ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa da ke fuskantar gidan. Sai na gani na kuma duba, ga ɗaukakar Yahweh ta cika gadan Yahweh, sai na faɗi bisa fuskata.
\v 5 Sai Yahweh ya ce mani, "Ɗan mutum, ka shirya zuciyarka ka kuma duba da idanunka ka saurara kuma da kunnuwanka dukkan abin da na ke furta maka. Ga dukkan farillai na gidan Yahweh da dukkan ka'idodin. Yi tunani game da ƙofofin shiga gidan dana fitarsa.
\s5
\v 6 Sai ka faɗa wa kangararrun nan, gidan Isra'ila, 'Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Bari dukkan ayyukanku na ƙazanta su ishe ku, gidan Isra'ila -
\v 7 Da kuka kawo baƙi marasa kaciyar zuciya da kaciyar jiki su kasance a Haikalina, suna rena gidana, yayin da kuke miƙa mani abinci, kitse da Jini - Kun karya alƙawarina da dukkan ayyukanku na ƙazanta.
\s5
\v 8 Ba ku aiwatar da ayyukanku ba game da abubuwana masu tsarki, amma kuka zaɓi wasu suyi ayyukanku, kuka kuma sanyasu su lura da wurina maitsarki.
\v 9 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ba bu wani baƙo, marar kaciyar zuciya da jiki, a cikin dukkan waɗanda ke zaune tare da mutanen Isra'ila, da za ya shiga wurina mai tsarki.
\s5
\v 10 Amma Lebiyawa suka tafi nesa da ni - suka kauce daga gare ni, suka tafi ga gumakansu - amma za su biya domin zunubinsu.
\v 11 Su bayi ne a haikalina, suna lura da ƙofofin gidan suna kuma yin bauta a cikin gidan suna kuma yanka baye-baye na ƙonawa da hadayun mutane, za su tsaya a gaban mutane su bauta masu.
\v 12 Amma saboda sun miƙa hadayu ga gumakansu, sai suka zama abin sa tuntuɓe domin zunubi ga gidan Isra'ila. Saboda haka zan ɗaga hannuna in furta rantsuwa game da su - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne - zasu ɗauki nauyin horonsu.
\s5
\v 13 Ba za su zo kusa da ni ba su yi aikin firistoci ko kuma su kusanci abubuwana masu tsarki, abubuwa mafi tsarki ba. Maimako haka, za su ɗauki zarginsu da laifofinsu domin ayyukan ƙazanta da suka aiwatar.
\v 14 Amma zan maishe su masu tsaron aikin cikin gidan, domin dukkan ayyukansa da dukkan abin da a ke yi a cikinsa.
\s5
\v 15 Daga nan su Lebiyawa firistoci, su waɗannan 'ya'ya maza na Zadok waɗanda suka cika ayyukan masujadata sa'ad da mutanen Isra'ila suke bauɗewa daga gare ni - za su zo kusa da ni su yi mani sujada. Za su tsaya a gabana su miƙa mani kitse da jini - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\v 16 Za su zo masujadata; za su kusanci teburina su yi mani sujada su kuma cika ayyukansu a gare ni.
\s5
\v 17 Hakanan za ya kasance sa'ad da suka zo ƙofofin harabar ciki, dole su yi sutura da kayan linin, dole ne kuma ba za su zo cikin ƙofofin harabar ciki da gidansa ba a cikin suturar ulu.
\v 18 Za su sa rawwunan linin a kawunansu da kuma bujen linin a kwankwasonsu. Ba za su yi sutura da kayan da za susa su yi zufa ba.
\s5
\v 19 Idan suka fita zuwa harabar waje, zuwa harabar waje domin suje wurin mutanen, dole su tuɓe kayan da suka sa sa'ad da suke yin hidima; dole su tuɓe su su kuma ajiye su a cikin ɗaki mai tsarki, domin kada su maida sauran mutane masu tsarki ta wurin shafar suturarsu ta musamman.
\s5
\v 20 Dole ne kuma ba za su aske kawunansu ba ko su bar gashinsu a rataye ba yana lilo, amma dole su yiwa gashin kawunansu saisaya.
\v 21 Kada wani firist ya sha ruwan inabi idan za ya shiga harabar ciki,
\v 22 ko kuma ya ɗaukarwa kansa gwauruwa ko bazawara a matsayin matar aure, sai dai budurwa kaɗai daga zuriyar gidan Isra'ila ko kuma gwauruwar da ta auri firist.
\s5
\v 23 Gama za su koyawa mutanena bambanci tsakanin abu mai tsarki da abun reni; za su sanya su su san abu mai tsafta daga marar tsafta.
\v 24 A wurin saɓani za su tsaya su yi hukunci da dokokina; dole su kasance masu adalci. Za su kiyaye shari'ata da farillaina a cikin kowanne buki, kuma su yi shagalin Asabataina masu tsarki.
\s5
\v 25 Ba za su je ga wanda ya mutu ba domin su zama marasa tsarki, sai dai ko mahaifinsu ne ko mahaifiyarsu, ko ɗa ko ɗiya, ko ɗan'uwa ko 'yar'uwar da ba ta taɓa kwana da namiji ba; idan kuwa ba haka ba, za su zama marasa tsafta.
\v 26 Bayan da firist ya zama marar tsafta, za su lissafa warewar tsawon kwana bakwai domin sa.
\v 27 A ranar da za ya shiga wuri mai tsarki, a cikin harabar ciki domin ya yi bauta a wuri mai tsarki, dole ne ya kawo baikon zunubi domin kansa - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.
\s5
\v 28 Wannan za ya zama gãdonsu: Ni ne gãdonsu, tilas kuma ba za ku ba su kaddara ba a Isra'ila; Ni ne zan zama kaddararsu!
\v 29 Za su ci baye-baye na abinci, da baye-baye na zunubi, da kuma baye-baye na laifi, da kuma dukkan abin da aka keɓe domin Yahweh a Isra'ila, za ya zama nasu.
\s5
\v 30 Mafi kyau na 'ya'yan fari na dukkan abubuwa da kuma dukkan baiko, kowanne abu daga dukkan baye-baye za ya zama na firistoci, za ku kuma bayar da mafi kyau na baye-bayen abincinku ga firistoci domin albarka ta sauka bisa gidanku.
\v 31 Firistoci kuma ba za su ci wani mushe ba ko dabbar da naman daji ya yaga, ko tsuntsu ne ko bisa ne.
\s5
\c 45
\cl Sura 45
\p
\v 1 Idan kuka jefa ƙuri'u domin raba ƙasar a matsayin gãdo, dole ku bayar da baiko domin Yahweh; wannan baiko za ya zama fanni mai tsarki na ƙasar, kamu dubu ashirin da biyar a tsawonsa, faɗinsa kuma kamu dubu goma. Za ya zama mai tsarki, da dukkan lardin da ke kewaye da shi.
\v 2 Daga wannan za a ɗibi wuri kamu ɗari biyar na tsawo da kamu ɗari biyar na faɗi a kusurwa huɗu kewaye da wuri mai tsarki, da kuma kewayen kan iyakarsa kamu hamsin a faɗinsa.
\s5
\v 3 Daga wannan lardin za ka ɗibi wuri kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kamu dubu goma a faɗi; shi ne za ya zama masujada, wuri mafi tsarki.
\v 4 Za ya zama wuri mai tsarki a ƙasar domin firistoci da ke yiwa Yahweh bauta, waɗanda ke zuwa kusa da Yahweh su bauta masa. Za ya zama wuri domin gidajensu da kuma lardi mai tsarki domin wuri mai tsarki.
\v 5 Saboda haka za ya zama kamu dubu ashirin da biyar a tsawonsa da kamu dubu goma a faɗinsa, za ya kuma zama garurruka domin Lebiyawa da ke bauta a gidan.
\s5
\v 6 Zaku keɓe lardi domin birnin, kamu dubu biyar a faɗi da kamu dubu ashirin da biyar a tsawo, wanda zaya zama a gaba da lardin da aka keɓe domin wuri maitsarki; wannan birni zaya zama na dukkan gidan Isra'ila.
\v 7 Ƙasar shugaban zata kasance a ɓarayi biyu na lardin da aka keɓe domin wuri maitsarki da kuma birnin. Zaya zama a yamma da su da kuma gabas da su. Tsawonsa zaya zama dai-dai da tsawon ɗaya daga cikin wuraren da aka keɓe, daga yamma zuwa gabas.
\s5
\v 8 Wannan ƙasa zata zama kaddarar shugaba a Isra'ila. Shugabannina ba zasu sake muzgunawa mutanenaba; Maimako, zasu bayar da ƙasar ga gidan Isra'ila, domin kabilunsu.
\s5
\v 9 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Ya isheku, shugabannin Isra'ila! Ku kawar da ta'addanci da rigima; kuyi hukunci da adalci! ku daina kawar da mutanena! - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.
\v 10 Dole kuyi ma'aunai na gaskiya, da jarka ta gaskiya, da daro na gaskiya!
\v 11 Awon jarkar da daron su zama ɗaya, saboda daro ɗaya ya zama kashi ɗaya cikin goma na durom; jarkar kuma ta zama kashi ɗaya cikin goma na durom. Ma'auninsu zaya zama dai-dai da durom.
\v 12 Shekel zaya zama gerori ashirin; shekel sittin zaya zama maina a gare ku.
\s5
\v 13 Wannan ne baikon da ya zama tilas ku gabatar: kashi shida na jarka domin kowanne durom na alkama, zaku kuma bayar da kashi shida na jarka domin kowanne durom na bãli.
\v 14 Baikon ka'ida na mai zaya zama kashi goma na daro wanda ya ke durom ɗaya (wanda ya ke darurruka goma), ko kuma kowanne durom, tunda ya ke durom ɗinma darurruka goma ne.
\v 15 Tunkiya ɗaya ko akuya ɗaya daga cikin garken kowanne dabbobi ɗari biyu daga shiyyoyin ruwa na Isra'ila za a yi amfani da su domin baikon ƙonawa da baikon salama ayi kaffara domin mutanen - wannan ne furcin Ubangiji Yahweh.
\s5
\v 16 Dukkan mutanen ƙasar zasu bayar da wannan baiko ga shugaban Isra'ila.
\v 17 Zaya zama aikin shugaban ya shirya dabbobin domin baye-baye na ƙonawa, da baye-baye na hatsi, da baye-baye na abin sha a lokacin shagulgula da bukukuwan sabon wata, da ranakun asabaci - dukkan kafaffun shagulgulan gidan Isra'ila. Zaya bayar domin baye-baye na zunubi, da baye-baye na hatsi, da baye-baye na ƙonawa, da baye-baye na salama domin kaffara a madadin gidan Isra'ila.
\s5
\v 18 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: A wata na farko, a rana ta farko ga watan, zaku ɗauki maraƙi marar cikas daga garke kuyi baikon zunubi domin masujadar.
\v 19 Firist zaya ɗiba daga cikin jinin baikon zunubin sai ya sanya a dawakan ƙofar gidan da kuma kusurwa hudu na kan iyakar bagadin, da kuma dawakan ƙofar shiga harabar ciki.
\v 20 Zakuyi wannan a rana ta bakwai na watan domin zunubin kowanne mutum da a kayi cikin kuskure ko jahilci; ta wannan hanya zakuyi kaffara domin haikalin.
\s5
\v 21 A cikin wata na farko a rana ta sha huɗu ga watan, akwai shagali dominku, shagali na kwana bakwai. Za kuci gurasa marar gami.
\v 22 A wannan rana, shugaban zaya shiryawa kansa da dukkan mutanen maraƙi a matsayin baikon zunubi.
\s5
\v 23 A kwanaki bakwai na bukin, shugaban zaya shirya baiko na ƙonawa ga Yahweh: maraƙai bakwai da raguna bakwai marasa cikas kowacce rana har ranaku bakwai, da kuma bunsuru kowacce rana a matsayin baikon zunubi.
\v 24 Daga nan shugaban za ya yi baikon abinci na jarka ɗaya domin kowanne maraƙi da kuma jarka ɗaya domin kowanne rago da gwajin mai domin kowacce jarka.
\s5
\v 25 A cikin wata na bakwai a rana ta sha biyar ga watan, a wurin shagalin, shugaban za ya yi baye-baye cikin waɗannan kwanaki bakwai: baye-baye na zunubi, baye-baye na ƙonawa, baye-baye na abinci, da baye-baye na mai.
\s5
\c 46
\cl Sura 46
\p
\v 1 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: Ƙofar harabar ciki, da ke fuskantar gabas, za a rufe ta a cikin kwanaki shida na aiki, amma a ranar Asabaci za a buɗe ta, ranar sabon wata kuma za a buɗe ta.
\v 2 Shugaban za ya shiga harabar waje ta hanyar ƙofar da rumfarta da ke waje, za ya kuma tsaya a dawakan ƙofa na ƙofar ciki yayin da firistocin ke shirya masa baikon ƙonawa da baikon salama. Daga nan sai ya yi sujada a dankarin ƙofar ciki sai ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma.
\s5
\v 3 Mutanen ƙasar kuma za suyi sujada a gaban Yahweh a wurin shiga wannan ƙofa a ranakun asabaci da sabobbin watanni.
\v 4 Baikon ƙonawa da shugaban zaya miƙa ga Yahweh a ranar asabaci zaya zama 'yan tumaki shida marasa cikas da kuma rago ɗaya marar cikas.
\v 5 Baikon hatsi tare da ragon zaya zama jarka ɗaya, baikon hatsin dana 'yan ragunan zaya bayar bisa ga ra'ayinsa, da kuma gwajin mai ga kowacce jarkar hatsin.
\s5
\v 6 A ranar sabon wata tilas ne ya miƙa maraƙi marar cikas daga garke, 'yan tumaki shida, da rago marar cikas.
\v 7 Tilas ya miƙa baikon hatsi na jarka ɗaya domin maraƙin da kuma jarka ɗaya domin ragon, da abin da ya yi niyyar bayar wa domin 'yan tumakin, da kuma gwajin mai ga kowacce jarkar hatsi.
\v 8 Idan shugaban ya shiga ta hanyar ƙofar da rumfarta, tilas ya fita ta hakan.
\s5
\v 9 Amma idan mutanen ƙasar suka zo gaban Yahweh a lokacin shagulgulan da aka kafa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa domin ya yi sujada tilas ya fita ta ƙofar kudu; duk kuma wanda ya shiga ta ƙofar kudu tilas ya fita ta ƙofar arewa. Babu wanda za ya koma baya ta ƙofar da ya shiga, tilas ya miƙe ya fita ta gabansa.
\v 10 Tilas shugaban ya kasance a tsakanin su; yayin da suke shiga, tilas ya shiga, yayin da suke fita, tilas ya fita.
\s5
\v 11 A lokacin shagulgulan, baikon hatsin tilas ya zama jarkar hatsi ɗaya domin maraƙin da jarka ɗaya domin ragon, da kuma duk abin da ya yi niyyar bayarwa domin 'yan tumakin, da gwajin mai domin kowacce jarka.
\v 12 Idan shugaban ya bayar da baikon yaddar rai, kodai baiko na ƙonawa ko baiko na salama ga Yahweh, za a buɗemashi ƙofar da ke fuskantar gabas. Zaya miƙa baikonsa na ƙonawa da baikonsa na salama kamar yadda ya ke yi a ranar asabaci. Daga nan tilas ya fita, bayan kuma daya fita sai a kulle ƙofar.
\s5
\v 13 Bugu da ƙari, za ku bayar da ɗan rago marar cikas ɗan shekara ɗaya a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh kullum; za ku yi wannan safiya bayan safiya.
\v 14 Za ku bayar da baikon hatsi tare da shi safiya bayan safiya, ka shi shida na garwar da kashi uku na gwajin mai domin a murtsike garin baikon hatsin ga Yahweh, bisa ga madawwamin farilla.
\v 15 Za su shirya ɗan ragon, da baikon hatsin, da kuma mai safiya bayan safiya, baikon ƙonawa madawwami.
\s5
\v 16 Ubangiji Yahweh ya faɗi wannan: idan shugaban ya bayar da kyauta ga ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza, gãdonsa ne. Za ya zama kadarar 'ya'yansa maza, gãdo ne.
\v 17 Amma idan ya bayar da kyauta daga gãdonsa ga ɗaya daga cikin bayinsa, za ya zama na bawannan har zuwa shekarar 'yantarwa, sai kuma a maida shi ga shugaban. Gãdonsa lallai za ya zama na 'ya'yansa maza ne.
\v 18 Shugaban ba za ya ɗauke gãdon mutanen daga kadararsu ba; dole ya bayar ga 'ya'yansa maza daga kadararsa domin kada mutanena su warwatse, kowanne mutum daga kadararsa."'
\s5
\v 19 Daga nan sai mutumin ya kawo ni ta hanyar shiga ɗakuna masu tsarki domin firistoci, masu fuskantar arewa duba kuma! Akwai wani wuri kuma zuwa yamma.
\v 20 Ya ce mani, "Wannan ne wurin da tilas firistoci su dafa baikon laifofi da baikon zunubi inda kuma tilas su gasa baikon hatsi. Tilas kuma ba za su kawo baye-bayen ba zuwa harabar waje, domin mutanen za su zama keɓaɓɓu."
\s5
\v 21 Daga nan ya kawo ni harabar waje ya bida ni na bi ta kusurwoyi huɗu na harabar, sai kuma na ga cewa a kowacce kusurwar harabar akwai wata harabar.
\v 22 A kusurwoyi huɗu na harabar waje akwai waɗansu ƙananan harabai huɗu, kamu arba'in a tsawo da kamu talatin a faɗi. Dukkan harabobin huɗu gwajinsu ɗaya ne.
\v 23 Akwai layin da aka yi da dutse kewaye da dukkan su huɗun, kuma murahun girki na ƙarƙashin dutsen.
\v 24 Sai mutumin ya ce mani, "Waɗannan ne wuraren da bayin haikali za su dafa hadayun mutane."
\s5
\c 47
\cl Sura 47
\p
\v 1 Sai mutumin ya maida ni baya hanyar shiga haikalin, sai ga ruwa na ɓulɓulowa daga ƙarƙashin dankarin haikalin gidan zuwa gabas - gama gaban haikalin na fuskantar gabas - kuma ruwan na ɓulɓulawa ɓangaren kudu na haikalin, zuwa dama da bagadin.
\v 2 Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa ya kuma bi da ni zagaye da ƙofar da ke fuskantar gabas, a nan ruwan yana ta malalawa daga wannan ƙofa zuwa kudu da ita.
\s5
\v 3 Yayin da mutumin ke tafiya zuwa gabas, yana riƙe da magwaji a hannunsa; sai ya gwada kamu dubu ya kuma kawo ni ta cikin ruwan inda zurfinsa ya kai idon ƙafa.
\v 4 Ya sake gwada kamu dubu ya kuma kawo ni ta cikin ruwan inda zurfinsa yakai gwiwa; ya sake gwada kamu dubu ya kuma kawo ni inda zurfin ruwan ya kai kwankwaso.
\v 5 Sai ya sake gwada wani kamu dubu, amma ruwan ya zama kogi wanda bazan iya bi ta cikin ba gama ruwan ya taso sama zurfinsa kuma ya isa ayi iwo a ciki - ya zama kogin da ba a iya ƙetarewa.
\s5
\v 6 Daga nan mutumin ya ce mani, "Ɗan mutum, ka ga wannan?" sai ya fito da ni waje ya kuma sa na tafi na koma baya ina tafiya ta gefen kogin.
\v 7 Yayin da nake komawa baya sai na ga gefen kogin nada itatuwa da yawa a wannan gefe da kuma wancan gefe.
\v 8 Mutumin ya ce mani, "Wannan ruwan na tafiya lardin gabas ne da ƙasa zuwa Araba; wannan ruwan yana gudu ne zuwa cikin tekun gishiri za ya kuma sabunta ta.
\s5
\v 9 Za ya zama kuma duk wata halitta mai rai da ke iwo za ta kasance inda ruwan ya tafi; za ayi kifaye masu yawa, gama wannan ruwan za ya malala zuwa can. Za ya maida ruwan gishirin mai daɗi. Komai za ya rayu a duk inda ruwan ya je.
\v 10 Daga nan za ya kasance masu kamun kifi na Engedi za su tsaya bakin ruwan, za a sami wurin shanya tarurrukan kamun kifin su bushe a En Egilayim. Za a sami kifaye daban-daban a Tekun Gishiri, kamar kifayen babbar teku domin tsananin yawansu.
\s5
\v 11 Amma kududdufai da tafkunan Kogin Gishirin ba za a maida su masu daɗi ba; za su zama wurin samun gishiri.
\v 12 Gefen wannan kogin a bakunansa, a gefensa biyu, itatuwa daban-daban masu bada abinci za su fito. Ganyayensu ba za su yi yaushi ba kuma ba za su taɓa dena bada 'ya'ya ba. Kowanne wata itatuwan za su bada 'ya'ya, saboda ruwa daga haikalin yana malalawa zuwa gare su. 'Ya'yansu za su zama domin abinci, ganyayensu kuma za su zama domin warkaswa.
\s5
\v 13 Ubangiji Yahweh ya faɗi haka: Wannan ce hanyar da za ku raba ƙasar ga kabilu sha biyu na Isra'ila: Yosef za ya sami kaso biyu.
\v 14 Za ku raba dai-dai abin da na ɗaga hannu na rantse wa ubanninku zan ba su. Wannan ƙasa za ta zo maku a matsayin gãdo.
\s5
\v 15 Wannan ne za ya zama kan iyakar ƙasar a gefen arewa dagaBabbar Teku zuwa hanyar Hetlon, daga nan kuma zuwa Zedad.
\v 16 Daga nan kan iyakar za ya tafi Berota, da Sibirayim, wadda ke tsakanin Damaskus da Hamat, daga nan kuma zuwa Haza Hattikon, wadda ke gefen kan iyakar Hauran.
\v 17 Saboda haka kan iyakar za ya tafi daga teku zuwa Haza Enan kan iyaka da Damaskus da Hamat zuwa arewa. Wannan ne za ya zama ɓarayin arewa.
\s5
\v 18 A gefen gabas, a tsakanin Hauran da Damaskus da kuma tsakanin Giliyad da ƙasar Isra'ila za ya zama Kogin Yodan. Tilas ka gwada daga kan iyaka zuwa tekun gabas; dukkan wannan za ya zama kan iyakar gabas.
\v 19 Daga nan gefen kudu kan iyakar zai kama daga Tama zuwa ruwayen Meriba Kadesh, gulbin Masar zuwa BabbarTeku. Wannan zai zama kan iyakar gefen kudu.
\v 20 Daga nan kan iyakar yamma za ya zama daga BabbarTeku zuwa inda ya tafi daura da Hamat. Wannan ne za ya zama gefen yamma.
\s5
\v 21 Ta wannan hanyar za ku raba ƙasar a tsakaninku, domin kabilun Isra'ila.
\v 22 Sai ku rarraba gãdon domin ku da kuma baƙin da ke zaune a tsakanin ku, su waɗanda suka haifi 'ya'ya a tsakanin ku, tare daku, kamar haihuwar 'yan asalin mutanen Isra'ila. Za ku jefa ƙuri'u domin gãdo a tsakanin kabilun Isra'ila.
\v 23 Daga nan za ya zama cewa baƙo za ya kasance tare da kabilar da ke zaune tare da su. Tilas ku ba shi gãdo - wannan furcin Ubangiji Yahweh ne."
\s5
\c 48
\cl Sura 48
\p
\v 1 Waɗannan ne sunayen kabilun. Kabilar Dan za su karɓi kaso ɗaya na ƙasar; Kan iyakarsu za ya tafi dai-dai da kan iyakar Isra'ila ta arewa ta hanyar Hetlon da Lebo Hamat. Kan iyakar za ya tafi har zuwa Hazar Enan ya kuma tafi kan iyaka da Damaskus zuwa arewa daga nan har zuwa Hamat. Kan iyakar Dan za ya tafi daga gabas har zuwa Babbar Teku.
\v 2 Haɗe da kan iyakar Dan, daga gefen gabas zuwa yamma, Asha za ya sami kaso ɗaya.
\v 3 Haɗe da kan iyakar Asha, daga gefen gabas zuwa yamma, Naftali za ya sami kaso ɗaya.
\s5
\v 4 Haɗe da kan iyakar Naftali daga gefen gabas zuwa yamma, Manasse za ya sami kaso ɗaya.
\v 5 Haɗe da kan iyakar Manasse daga gefen gabas zuwa yamma, Ifraim za ya sami kaso ɗaya.
\v 6 Haɗe da kan iyakar Ifraim daga gefen gabas zuwa yamma, Ruben za ya sami kaso ɗaya.
\v 7 Haɗe da kan iyakar Ruben daga gefen gabas zuwa yamma, Yahuda za ya sami kaso ɗaya.
\s5
\v 8 Baikon ƙasa da zaku bayar za ya kasance daga kan iyakar Yahuda ya zarce daga gefen gabas zuwa gefen yamma; Faɗin ta za ya zama kamu dubu ashirin da biyar. Tsawonta kuma za ya zama dai-dai da kason kabila ɗaya daga gefen gabas zuwa gefen yamma, Haikalin kuma za ya kasance a tsakiyarsa.
\v 9 Wannan ƙasa da za ku miƙa baiko ga Yahweh za ta zama kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kuma kamu dubu goma a fãɗi.
\s5
\v 10 Waɗannan ne za su zama ayyukan kason wannan ƙasa mai tsarki: za a ɗeba wa firistoci ƙasar a gwada kamu dubu ashirin da biyar bisa gefen arewa; kamu dubu goma a fãɗi bisa gefen yamma; kamu dubu goma a fãɗi bisa gefen gabas; kamu dubu ashirin da biyar kuma bisa gefen kudu, tare da wuri mai tsarki na Yahweh a tsakiyarta.
\v 11 Wannan za ya zama domin keɓewar firistoci zuriyar Zadok, waɗanda suka bauta mani da aminci ba su kuma kauce ba a lokacin da mutanen Isra'ila suka kauce, yadda Lebiyawa suka yi.
\v 12 Baiko dominsu za ya kasance kason wannan ƙasa mafi tsarki, ya zarce zuwa kan iyakar Lebiyawa.
\s5
\v 13 Ƙasar Lebiyawa da ke kan iyaka da ƙasar firistoci za ta kasance kamu dubu ashirin da biyar a tsawo da kamu dubu goma a fãɗi. Tsawon gabaɗaya na tsagawar ƙasar biyu za ya kasance kamu dubu ashirin da biyar da kuma kamu dubu ashirin a fãɗi.
\v 14 Dole ba za su sai da ba ko su yi musanya da ita; 'Ya'yan fari na ƙasar Isra'ila dole ba za a taɓa ware su ba daga waɗannan karkasawar, gama dukkan ta mai tsarki ce ga Yahweh.
\s5
\v 15 Sauran ƙasar, kamu dubu biyar a fãɗi da kamu dubu ashirin da biyar a tsawo, za ta zama abin amfanin birnin gabaɗaya, da gidajen, da saurar kiwo, birnin za ya kasance a tsakiya.
\v 16 Waɗannan ne za su zama gwaje-gwajen birnin: Gefen arewa za ya zama kamu 4,500 a tsawo; gefen kudu za ya zama 4,500 a tsawo; gefen gabas za ya zama 4,500 a tsawo; gefen yamma za ya zama 4,500 a tsawo.
\s5
\v 17 Za a fidda saura domin birnin wajen arewa, kamu 250 a zurfi; wajen kudu, kamu 250 a zurfi; wajen gabas, kamu 250 a zurfi; wajen yamma, kamu 250 a zurfi.
\v 18 Sauran lardin domin baiko mai tasrki za ya zarce ya kai kamu dubu goma zuwa gabas da kamu dubu goma zuwa yamma. Za ta zarce har zuwa kan iyaka da baiko mai tsarki, amfanin ta kuma za ya zama abinci domin masu aiki cikin birnin.
\s5
\v 19 Mutanen da ke aiki cikin birnin, mutanen da suka fito daga dukkan kabilun Isra'ila, za su noma wannan ƙasar.
\v 20 Dukkan ƙasar baikon za a gwada kamu dubu ashirin da biyar da kamu dubu ashirin da biyar. Ta wannan hanyar za ku bada baikon mai tsarki da ƙasa, domin birnin.
\s5
\v 21 Sauran ƙasar daga kowanne gefe na baiko mai tsarki da lardin birnin za ya zama domin shugaban. Tsagin ƙasar shugaban zuwa gabas za ta zarce ta kai kamu dubu ashirin da biyar daga kan iyakar baiko mai tsarki zuwa gabashin kan iyakar - tsagin nasa kuma daga yamma za ta zarce ta kai kamu dubu ashirin da biyar zuwa yammacin kan iyakar. Tsakiyar za ta zama baiko mai tsarki, wuri mai tsarki kuma na haikalin za ya kasance a tsakiyarta.
\v 22 Ƙasar za ta zarce daga kadarar Lebiyawa da kuma lardin birnin da ke tsakiya zaya zama na shugaban; za ta kasance tsakanin kan iyakar Yahuda da kuma kan iyakar Benyamin - wannan ƙasa za ta zama ta shugaban.
\s5
\v 23 Sauran kabilun kuwa, na su kashi-kashinsu ma za ya fara daga gefen gabashi zuwa gefen yamma. Benyamin za ya karɓi kaso ɗaya.
\v 24 Haɗe da kan iyakar Benyamin daga gefen gabas zuwa yamma, Simiyon za ya sami kaso ɗaya.
\v 25 Haɗeda kan iyakar Simiyon daga gefen gabas zuwa yamma, Issaka za ya sami kaso ɗaya.
\v 26 Haɗe da kan iyakar Issaka daga gefen gabas zuwa yamma, Zebulun za ya sami kaso ɗaya.
\s5
\v 27 Daga kudancin kan iyakar Zebulun, ya kamo daga gefen gabas zuwa yamma, za ya zama ƙasar Gad - kaso ɗaya.
\v 28 Kan iyakar kudancin Gad za ya zarce daga Tama zuwa Meriba Kadesh da kuma nesa daga tafkin Masar, daga nan kuma zuwa babbar teku.
\v 29 Wannan ce ƙasar da za ku jefa ƙuri'u; za ta zama gadon kabilun Isra'ila. Waɗannan ne za su zama rabonsu. Wannan furcin Ubangiji Yahweh ne.
\s5
\v 30 Waɗannan ne za su zama wuraren fita daga birnin: a gefen arewa, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo,
\v 31 za ya zama ƙofofi uku, waɗanda za a yi wa suna domin kabilun Isra'ila: ƙofa ɗaya domin Ruben, ƙofa ɗaya domin Yahuda, ƙofa ɗaya kuma domin Lebi.
\v 32 A gefen gabas, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Yusufu, ƙofa ɗaya domin Benyamin, ƙofa ɗaya kuma domin Dan.
\s5
\v 33 A bangon kudu, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Simiyon, ƙofa ɗaya domin Issaka, ƙofa ɗaya kuma domin Zebulun.
\v 34 A gefen yamma, wanda za a gwada kamu 4,500 a tsawo, za ya zama ƙofofi uku: ƙofa ɗaya domin Gad, ƙofa ɗaya domin Asha, ƙofa ɗaya kuma domin Naftali.
\v 35 Tazarar kewaye da birnin za ya zama kamu dubu sha takwas; daga ranar nan zuwa nan gaba, sunan birnin za ya zama "Yahweh yana wurin."