ha_ulb/25-LAM.usfm

311 lines
18 KiB
Plaintext

\id LAM
\ide UTF-8
\h Littafin Makoki
\toc1 Littafin Makoki
\toc2 Littafin Makoki
\toc3 lam
\mt Littafin Makoki
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Ƙasar da dã ke cike da mutane yanzu tana zaman kaɗaici. Ta zama kamar gwauruwa ko da ya ke babbar al'umma ce dã. Dã gimbiya ce a cikin al'ummai, amma yanzu an sa ta aikin bauta na dole.
\v 2 Tana kuka da koke-koke da dare, kuma hawayenta sun rufe kumatunta. Babu masoyinta da ke yi mata taimako. Dukkan abokananta sun yashe ta. Sun zama maƙiyanta.
\s5
\v 3 Bayan talauci da ƙunci, Yahuda ta tafi zaman bauta. Tana zaune a cikin al'ummai kuma ta rasa samun hutawa. Dukkan masu korarta a guje sun wuce ta a cikin damuwarta.
\s5
\v 4 Hanyoyin Sihiyona na makoki saboda babu waɗanda suka zo bukukuwan da aka shirya. Dukkan ƙofofinta sun zama yasassu. Firistocinta na nishi. 'Yanmatanta na cikin da baƙinciki kuma ita kanta tana cikin cikakken ƙunci.
\v 5 Magabtanta sun zama iyayengijinta; maƙiyanta sun azurta. Yahweh ya ƙuntata mata domin yawan zunubanta. An kai ƙananan 'ya'yanta bauta ga magabcinta.
\s5
\v 6 Kyau ya rabu da ɗiyar Sihiyona. 'Ya'yan sarakunanta sun zama kamar bareyin da ba za su iya samun abinci ba, kuma suna tafiya da ƙyar a gaban masu farautarsu.
\s5
\v 7 A kwanakin ƙuncinta da rashin wurin zamanta, Yerusalem zata tuna da dukiyoyinta masu daraja wadda take da su a kwanakin dã. Sa'ad da mutanenta suka faɗi a hannun abokan gãba, babu wanda ya taimaketa. Abokan gãba sun gan ta sun kuma yi dariya ga hallakarta.
\s5
\v 8 Yerusalem ta yi zunubi ƙwarai, saboda haka ta zama abin ƙi kamar wani abin ƙyama. Dukkan waɗanda ke girmama ta sun yashe ta tun da suka ga tsiraicinta. Tana nishi tana ƙoƙarin juyawa.
\v 9 Ta zama marar tsabta a karkashin zannuwanta. Ba ta yi tunani a kan kwanakinta masu zuwa ba. Faɗuwarta abin takaici ne. Babu wanda zai ta'azantar da ita. Ta yi kuka cewa "Dubi wuyar da nake sha, Yahweh, gama makiyana sun ƙaru da yawa!"
\s5
\v 10 Abokin gãba yasa hannunsa a dukkan dukiyoyinmu masu daraja. Ta ga al'ummai sun shigo wurinta mai tsarki, ko da ya ke ka umarcesu kada su shiga wurin taruwar jama'arka.
\s5
\v 11 Dukkan mutanenta sun yi nishi sa'ad da suke neman abinci. Sun ba da dukiyoyinsu masu daraja domin abincin da zai rayar da su. Yahweh, ka dube ni ka kula da ni, gama na zama marar daraja.
\v 12 Wato a wurinku ba komai ba ne, dukkanku da ke wucewa? Ku duba ku gani ko akwai wani mai shan azaba kamar ni, tun da Yahweh ya azabtar da ni a ranar fushinsa mai zafi.
\s5
\v 13 Daga can bisa ya aiko da wuta a ƙasusuwana, kuma ta cinye su. Ya yafa raga domin ƙafafuwana ya kuma maida ni baya. Ya maida ni kullum a yashe da somewa. Karkiyar laifofina a ɗaure suke a hannunsa.
\v 14 An ɗaura su tare an sa su a kan wuyana. Ya sa ƙarfina ya ƙare. Ubangiji ya bashe ni a hanun maƙiyana, kuma ba zan iya tsayawa ba.
\s5
\v 15 Ubangiji ya tura majiya ƙarfina gefe waɗanda ke yi mani kariya. Ya kira taron jama'a găba da ni don su murƙushe jarumawana. Ubangiji ya tattake ɗiyar Yahuda budurwar nan, a wurin matse ruwan inabi.
\s5
\v 16 Saboda waɗannan abubuwa na yi kuka. Idanuwana, ruwa na zubowa ƙasa daga Idanuwana tun da mai ta'azantar da ni wanda zai 'yantar da raina yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace saboda maƙiyin ya yi nasara.
\v 17 Sihiyona ta shinfiɗa hannuwanta da făɗi; ba wanda zai ta'azantar da ita. Yahweh ya umarci waɗanda ke kusa da Yakubu su zama abokan găbarsa. Yerusalem ta zama abin rashin tsabta a garesu.
\s5
\v 18 Yahweh mai adalci ne, gama na tayar wa dokokinsa. Ku ji, dukkan mutane, ku kuma ga damuwata. Budurwaina da jarumawana sun tafi bauta.
\v 19 Na yi kira ga abokaina, amma sun zama maciya amana a gareni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin, sa'ad da suke neman abinci na ceton ransu.
\s5
\v 20 Duba, Yahweh, gama ina cikin kunci; cikina ya ɗuri ruwa, sai na damu a cikin zuciyata, gama ni mai tayarwa ne sosai. A waje, takobi ya sa uwa makoki, a cikin gida kuma babu kome sai mutuwa.
\s5
\v 21 Sun ji nishina, amma ba mai ta'azantar da ni. Dukkan maƙiyana sun ji batun matsalata kuma sun yi murna cewa kai ka yi haka. Kã kawo ranar da ka alƙawarta; yanzu bari su zama kamar ni.
\v 22 Bari dukkan muguntarsu ta zo gabanka. Ka yi masu yadda ka yi mani saboda laifofina. Nishe-nishe na da yawa kuma zuciyata ta some.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ubangiji yã rufe ɗiyar Sihiyona a karkashin gizagizan fushinsa. Ya jefar da darajar Isra'ila ƙasa daga sama zuwa duniya. Bai tuna da matashin sawunsa a ranar fushinsa ba.
\v 2 Ubangiji yã haɗiye yã kuma ƙi jin tausayin dukkan garurruwan Yakubu. A ranar fushinsa ya jefar da ƙayatattun biranen ɗiyar Yahuda a ƙasa; a cikin rashin girmamawa ya saukar da mulkin da shugabaninsa ƙasa.
\s5
\v 3 Da zafin fushinsa ya datse kowanne ƙaho na Isra'ila. Ya cire hannun damansa daga gaban maƙiyi. Ya ƙone Yakubu kamar harshen wuta da ke cinye dukkan abin da ke kewaye da shi.
\v 4 Kamar maƙiyansa ya ɗana bakansa gare mu, ya yi shirin harbi da hannun damansa. Ya yayyanke dukkan masu faranta masa rai a rumfar ɗiyar Sihiyona; Ya zuba fushinsa kamar wuta.
\s5
\v 5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi. Ya haɗiye Isra'ila. Ya haɗiye dukkan fadodinta. Ya hallakar da wuraren mafakarta. Ya ƙara baƙinciki da makoki cikin ɗiyar Yahuda.
\v 6 Ya kai wa rumfar sujadarsa hari kamar bukkar gona. Ya rusa wurin tsattsarkan taron jama'a. Yahweh yasa a mance da tattsarkar Asabar da taron jama'a a Sihiyona, gama ya wofintar da sarki da firist cikin zafin fushinsa.
\s5
\v 7 Ubangiji ya ƙi bagadinsa ya kuma musanci tsarkakan haikalinsa. Ya ba da bangayen fadodinta ga hannun maƙiyi. Sai suka ta da ihu a gidan Yahweh, kamar ranar ayyanannen idi.
\s5
\v 8 Yahweh ya ƙudura ya hallakar da garun birnin ɗiyar Sihiyona. Ya miƙar da igiyar gwaji kuma bai ɗauke hannunsa daga rusar da garun ba. Ya sa kagara da garu suyi makoki; ya wofintar da su tare.
\v 9 Ƙofofinta sun lume cikin ƙasa; ya rusar ya kuma karya shingayen kofofinta. Sarkinta da 'ya'yan sarkinta na cikin al'ummai, babu doka kuma, har anabawanta sun rasa wahayi daga Yahweh.
\s5
\v 10 Dattawan ɗiyar Sihiyona na zaune shiru a ƙasa. Sun watsa ma kawunansu ƙasa suna kuma sanye da tufafin makoki. 'Yan matan Yerusalem sun russunar da kawunansu ƙasa.
\s5
\v 11 Hawayen idanuwana sun gaji da zubowa; cikina ya kiɗime, dukkan raina na cike da baƙinciki saboda rushewar ɗiyar mutanena, yara da jarirai sun some a titunan birnin.
\v 12 Suka cewa uwayensu, "Ina hatsi da ruwan inabi?" sa'ad da suka some kamar mutumin da ya ji ciwo a titunan birnin, rayukansu suka kasance cikin baƙinciki a hannuwan uwayensu
\s5
\v 13 Me zan ce maki, ɗiyar Yerusalem? Me zan kwatanta ta'aziyar da zan yi maki 'yar Sihiyona? Ciwonki na da girma kamar teku. Wa zai iya warkar da ke?
\v 14 Anabawanki sun gano wahayin ƙarya dana wofi domin ki. Ba su fallasar da laifofinki har da farfaɗo da ke daga hasarar bauta ba, amma suka fitar da maganganun ƙarya dana kaucewa daga hanya.
\s5
\v 15 Dukkan waɗanda suka wuce a hanya suna tafa maki hannuwansu. Suna tsãki suna kaɗa kai gãba da 'yar Yerusalem suna cewa, "Ba wannan ne birnin da ake kira 'Cikakken Kyau,' 'Farin Cikin dukkan Duniya' ba?"
\v 16 Dukkan maƙiyanki sun buɗe bakunansu suna maki ba'a. Suna gwalo da cizon baki da cewa, "Mun haɗiye ta! Wannan ce ranar da muke jira! Muna jiran ganinta!"
\s5
\v 17 Yahweh ya aikata abin da ya shirya zai yi. Ya cika maganarsa. Ya tumɓuke ki da rashin tausayi, gama ya bai wa maƙiya dama su yi farinciki a kan ki; ya ɗaga ƙahon maƙiyanki.
\s5
\v 18 Zuciyarsu ta yi kuka ga Ubangiji, garun 'yar Sihiyona! Ki sa hawayenki su kwararo ƙasa kamar kogi dare da rana. Kar ki ba kanki da idanunki hutu,
\v 19 Tashi, yi kuka da dare, sau da yawa da almuru! Ki zubo da zuciyarki kamar ruwa a gaban fuskar Ubangiji. Ki ɗaga hannuwanki gareshi domin rayukan 'ya'yanki waɗanda suka some da yunwa a kowanne gefen titi.
\s5
\v 20 Duba, Yahweh, ka kula da waɗanda ka yi masu haka. Shin mata zasu iya cinye 'ya'yan cikinsu, 'ya'yan da suka yi renonsu? Yana yiwuwa a kashe firist da annabi a rumfar sujada ta Ubangiji?
\s5
\v 21 Matasa da tsofaffi na kwance a ƙurar titunan. "Yan mata da samari sun făɗi ta takobi; kã yanka su ba tare da tausayinsu ba.
\v 22 Kã yi kira, kamar yadda kake kiran mutane a ranar idi, ina fargaba a kowanne gefe, a ranar fushin Yahweh, babu wanda zai kuɓuta ko ya rayu; waɗanda na lura na kuma tasar da su, maƙiyana sun hallakar da su.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Ni ne mutumin da yaga wuya a ƙarƙashin sandar fushin Yahweh.
\v 2 Ya kore ni waje ya kuma sanya ni in yi tafiya cikin duhu a maimakon haske.
\v 3 Hakika ya juye hannuwansa gãba da ni ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba a dukkan rana.
\v 4 Ya maida naman jikina da fatar jikina banza; ya karya kassusuwana.
\s5
\v 5 Ya kewaye ni kamar birnin da aka kawo masa hari, ya kuma kewaye ni da baƙinciki da matsananciyar wahala.
\v 6 Yasa na zauna a wurare masu duhu, kamar waɗanda suka mutu da daɗewa.
\v 7 Ya gina garu kewaye da ni kuma ba zan iya kuɓuta ba. Yasa sarƙoƙina sun nawaita
\v 8 kuma ko da na yi kiran neman taimako, sai ya ƙi jin addu'ata
\s5
\v 9 Ya tare hanyata da garun sassaƙaƙƙun duwatsu; ya maida hanyoyina karkatattu.
\v 10 Ya yi kamar damisa da ke mani kwanto, Zaki na boyewa;
\v 11 ya bauɗar da hanyoyina, ya yashe ni.
\s5
\v 12 Ya ja bakansa ya sa na zama abin da kibiyarsa zata harba.
\v 13 Ya soke ƙodojina da kiɓiyoyin kwarinsa.
\v 14 Na zama abin dariya ga dukkan mutane, wani abin yi wa zambo a dukkan yini.
\v 15 Ya cika ni da ɓacin rai ya kuma tilasta ni sha ruwan ɗaci.
\s5
\v 16 Ya haƙorana niƙa da tsakuwa; ya tura ni ƙasa cikin ƙura.
\v 17 An raba raina da salama; Na mance da mene ne ma farinciki.
\v 18 Saboda haka na ce, "jimirina ya ƙare haka kuma begena ga Yahweh"
\s5
\v 19 Tuna da azabata da yawace-yawacena, ɗacin rai da baƙinciki.
\v 20 Ina ci gaba da tunawa da ita ina kuma russunawa ƙasa a cikin rai na.
\v 21 Amma ina nazarin wannan a zuciyata saboda haka ina da bege:
\s5
\v 22 Kaunar Yahweh madawwamiya ba ta ƙarewa kuma tausayinsa baya zuwa ga ƙarshe,
\v 23 suna sabuntuwa kowacce safiya; amincinka mai girma ne.
\v 24 "Yahweh ne gãdona". Na ce, saboda haka zan yi bege a cikinsa.
\s5
\v 25 Yahweh managarci ne ga waɗanda ke jiransa, kuma ga mai nemansa.
\v 26 Ya yi kyau a yi shiru a jira ceton Yahweh.
\v 27 Abu nagari ne mutum ya jure karkiya a cikin ƙuruciyarsa.
\v 28 Bari ya zauna shiru shi kaɗai sa'ad da aka ɗora masa shi.
\v 29 Bari ya sa bakinsa a ƙura - mai yiwuwa akwai bege.
\s5
\v 30 Bari ya ba da kuncinsa ga mai marinsa, kuma bari ya cika da abin kunya.
\v 31 Gama Ubangiji ba zai ƙi mu har abada ba,
\v 32 Amma koda ya ke ya jawo ɓacin zuciya, zai ji tausayinmu bisa ga yawan kaunarsa marar ƙarewa,
\v 33 Gama ba ya ƙuntatawa daga zuciyarsa, ko cakuna ga 'yan adam.
\s5
\v 34 Domin a rugurguza a karkashin kafafunsa dukkan ɗaurarrun duniya,
\v 35 a hana yiwa mutum adalci a gaban maɗaukaki,
\v 36 a hana adalci ga mutum - Ubangiji ba zai amince da abubuwa haka ba.
\s5
\v 37 Wa ya yi magana kuma ta cika, idan ba Ubangiji ya umarta ta ba?
\v 38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne masifu da nagargarun abubuwa ke fitowa ba?
\v 39 Ta yaya wani rayayye zai yi gunaguni? Ta yaya mutum zai yi gunaguni game da hukuncin zunubansa?
\s5
\v 40 Bari mu auna hanyoyinmu mu gwada su, mu kuma juyo ga Yahweh.
\v 41 Bari mu daga zukatanmu da hannuwanmu ga Allah a sammai.
\v 42 "Mun yi laifofi da tayarwa, kuma baka gafarta ba.
\v 43 Ka rufe kanka da fushi ka kuma kore mu, ka kashe kuma ba ka keɓe mu ba.
\s5
\v 44 Ka rufe kanka da giza-gizai yadda babu addu'ar da zata wuce ciki.
\v 45 Ka maishe mu kamar ƙazantaccen juji na wofi a cikin al'ummai.
\v 46 Dukkan maƙiyanmu sun la'anta mu,
\v 47 fargaba da tsoro da lalacewa da hallaka sun auko mana.
\s5
\v 48 Idanuwana na fitar da maɓulɓulan hawaye saboda mutanena da aka hallaka.
\v 49 Idanuwana za su zubar da hawaye marar ƙarewa; babu tsayawa,
\v 50 har sai ya dubo ƙasa kuma Yahweh zai duba daga sama.
\s5
\v 51 Idanuwana sun sa ni matsananciyar wahala saboda dukkan 'yan matan birnina.
\v 52 Maƙiyana na farauta ta kamar waɗanda ke kamun tuntsu; suna ta farauta ta ba dalili.
\v 53 Sun jefa ni cikin rami suka kuma jefe ni da dutse,
\v 54 har ruwa ya zuba a bisa kaina. Na ce, "An datse ni!'
\s5
\v 55 Yahweh, na kira sunanka daga rami mai zurfi.
\v 56 Ka ji muryata sa'ad da na ce, 'Kada ka rufe kunnuwanka ga kukana na neman taimako.'
\v 57 Ka zo kusa a ranar da na kira ka; ka ce, 'kada kaji tsoro.'
\s5
\v 58 Ubangiji, ka yi mani kariya, ka cece ni!
\v 59 Yahweh, ka ga abu marar kyau da aka yi mani; ka zama alƙalina.
\v 60 Ka ga zagi da ƙulle-ƙullen da suke yi mani.
\v 61 Ka ji reninsu, Yahweh, da dukkan shirin da suke yi a kai na.
\s5
\v 62 Leɓunan waɗanda suke yi mani tayarwa, da zarginsu sun zo gãba da ni dukkan rana.
\v 63 Duba yadda suke zama da tashi; suna yi mani ba'a da waƙoƙinsu.
\s5
\v 64 Yahweh, ka rama mani bisa ga abin da suka yi.
\v 65 Za ka bar zukatansu a rashin kunya! Da ma hukuncinka ya auka masu!
\v 66 Ka rarakesu a cikin fushinka ka hallaka su daga ƙarƙashin sammai, Yahweh!"
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Zinariyar ta zama gurbatacciya; tatacciyar zinariyar ta sake kamanni! An watsar da tsarkakakkun duwatsu a kwanar kowanne titi.
\v 2 'Yan mazan Sihiyona masu daraja sun cancanci nauyin tacacciyar zinariya, amma yanzu ba suma cancanci tulunan yumɓu ba, aikin hannuwan maginin tukwane!
\s5
\v 3 Har ma diloli kan iya ba 'ya'yansu nono amma ɗiyar mutanena ta zama mai mummunan hali irin na garken jiminai da ke hamada.
\s5
\v 4 Harshen jariri saboda ƙishin ruwa ya liƙe a dasashinsa; yaran na neman abinci amma babu kome dominsu.
\v 5 Waɗanda suka saba da idin abinci mai tsada sun gamu da yunwa a tituna; waɗanda aka san su da sa kyawawun kaya, yanzu suna kwance a juji wofi.
\s5
\v 6 Hukuncin ɗiyar mutanena ya fi na Sodom, wadda aka kawar da ita a ɗan lokaci kaɗan kuma babu wanda ya tada hannu na taimakonta
\s5
\v 7 Shugabaninta sun ɗara dusar ƙanƙara rashin aibi, sun kuma fi madara fari; jikunansu sun fi murjani kyau, fasalinsu kamar shudin saffiya.
\v 8 Yanzu kammaninsu yafi kunkunniya baƙi. Ba sa ganuwa a tituna. Fatarsu ta liƙe a kasusuwansu; ta zama busasshiya kamar katako.
\s5
\v 9 Waɗanda aka kashe su da takobi suna da farinciki fiye da waɗanda aka kashe da yunwa, wanɗanda su ne suka zama lalatattun da aka sokesu da rashin wani girbi daga gona.
\v 10 Hannuwan mata masu tausayi sun dafa 'ya'yansu; suka zamar masu abinci a lokacin da ake hallakar da ɗiyar mutanena.
\s5
\v 11 Yahweh ya nuna dukkan fushinsa; ya zubo zafin fushinsa. Ya kunna wuta a Sihiyona da ta cinye tushenta.
\s5
\v 12 Sarakunan duniya, ba su amince ba, da haka ma dukkan mazaunann duniya ba su amince ba cewa maƙiyan ko masu adawa za su iya shiga ƙofofin Yerusalem.
\v 13 Wannan ya faru ne saboda zunuban annabawanta da laifofin firistocinta waɗanda suka zubar da jinin adalai a cikinta.
\s5
\v 14 Sun yi ta gararamba cikin makanta a tituna. Sun zama ƙazantattu sosai ta wurin jini da babu wanda aka yarda ya taba tufafinsu.
\v 15 "Fita! Marar tsabta!" mutane na ta ihun kiransu. "Fita! Fita! Kar ku taɓa!" Haka suke gararamba; mutane faɗi a cikin al'ummai, "Ba za su ƙara zama a nan kuma ba."
\s5
\v 16 Yahweh da kansa ya watsar da su; bai sake kula da su kuma ba. Ba su girmama firistoci ba, kuma ba su nuna wani alheri ga dattawa ba.
\s5
\v 17 Idanuwanmu sun gaji da neman taimako a banza; daga wurin duban maƙiyanmu mun dubi al'ummar da ba za ta iya kuɓutar da mu ba.
\v 18 Suka bi duk inda muka nufa, bamu iya tafiya a titunanmu ba. Ƙarshenmu ya kusato kuma an lisafta kwanakinmu, ƙarshenmu ya zo.
\s5
\v 19 Masu fafarar mu sun fi gaggafan sararin sama sauri. Suna korar mu zuwa duwatsu kuma suna yi mana kwanton ɓauna a cikin jeji.
\v 20 Numfashin hancinmu - keɓaɓɓu na Yahweh - shi ne wanda aka cafko a ramukansu; wanda aka ce game da shi, "a ƙarkashin inuwarsa ne za mu zauna cikin al'ummai."
\s5
\v 21 Ki yi farinciki da murna, ɗiyar Idom, ke da kike zaune a ƙasar Uz. Amma a gare ki kuma za a fara shan ƙoƙon; za ki bugu har sai kin tuɓe kanki tsirara.
\v 22 Ɗiyar Sihiyona, hukuncinki zai kawo ga ƙarshe, ba zai ƙara kwanakin bautarki ba. Amma zai hukunta ɗiyar Idom, zai hukunta; zai buɗe zunubanki
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Tuna, Yahweh, da abin da ya same mu. Ka duba ka ga abin ban kunyarmu.
\v 2 Gãdonmu an bayar ga bãƙi, gidajenmu ga bãƙi.
\v 3 Mun zama marayu, marasa ubanni, kuma waɗanda uwayensu sun zama kamar gwauraye.
\v 4 Dole mu biya zinariya don ruwan shanmu, kuma dole mu biya zinariya kafin mu samu abincinmu.
\s5
\v 5 Waɗanda suke rarakarmu sun matso kusa da mu. mun gaji kuma ba mu samu hutu ba.
\v 6 Mun ba da kanmu ga Masar da Asiriya don mu samu isasshen abinci.
\v 7 Ubanninmu sun yi zunubi, kuma yanzu basu nan, kuma muna ɗaukar alhakin laifofinsu.
\s5
\v 8 Bãyi suna mulki a kanmu, kuma babu wanda zai kuɓutar da mu daga hannunsu.
\v 9 Muna samun abincinmu ta sadaukar da ranmu ne kawai, saboda takobin cikin jeji.
\v 10 Zafin fatarmu kamar zafin tanderu don tsananin yunwa.
\s5
\v 11 Ana yi wa mata fyaɗe a Sihiyona, har da 'yan mata ma a biranen Yahuda.
\v 12 'Ya'yan sarakuna na rataya kansu da hannuwansu, kuma ba a nuna girmamawa ga dattawa.
\s5
\v 13 An sa samari su yi niƙan hatsi dole da dutsen niƙa, samari kuma suna jiri da kayan itace masu nauyi.
\v 14 Dattawa sun bar kofar birnin kuma samarin sun bar raira waƙoƙinsu.
\s5
\v 15 Farincikinmu ya ƙare kuma rawarmu ta koma makoki.
\v 16 Rawani ya faɗo ƙasa daga kanmu; kaiton mu, don mun yi zunubi!
\s5
\v 17 Domin wannan, zuciyarmu ta kamu da ciwo, kuma idanuwanmu sun dushe, saboda wannan idanuwanmu sun rage ƙarfi.
\v 18 gama Tsaunin Sihiyona ya zama ƙango, diloli ke yawo a kansa.
\s5
\v 19 Amma kai, Yahweh, mulkinka har abada ne, kuma za ka zauna a kan kursiyinka daga tsara zuwa tsara.
\v 20 Meyasa ka mance da mu har abada? Meyasa ka bar mu har tsawon kwanaki da yawa?
\v 21 Ka komo da mu zuwa gare ka ya Yahweh, kuma zamu komo. ka sabunta kwanakinmu kamar yadda suke a dã -
\v 22 har sai in ka ƙi mu ɗungum kuma ka yi fushi da mu fiye da misali.