ha_ulb/23-ISA.usfm

2880 lines
191 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id ISA
\ide UTF-8
\h Littafin Ishaya
\toc1 Littafin Ishaya
\toc2 Littafin Ishaya
\toc3 isa
\mt Littafin Ishaya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Wahayin Ishaya ɗan Amoz, wanda ya gani game da Yahuda da Yerusalem, a kwanakin Uziya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuda.
\s5
\v 2 Ku saurara, ku sammai, ke duniya, ki kasa kunne; gama Yahweh ya yi magana: "Na yi renon 'ya'ya na girmar da su, amma sun tayar mani.
\v 3 Sã ya san mai shi, jaki kuma ya san inda ubangijinsa ke ciyar da shi, amma Isra'ila ba ta sanni ba, Isra'ila ba ta fahimta ba,"
\s5
\v 4 Kaito! Al'umma, masu zunubi, mutanen da zunubi ya danne su ƙasa, zuriyar masu aikata mugunta, 'ya'ya masu aikin lalata! Sun yi watsi da Yahweh, sun rena Mai Tsarki na Isra'ila, sun ware kansu daga gare shi.
\s5
\v 5 Donme a ke ta dukan ku har yanzu? Me ya sa kuke ta tayarwa akai akai? Dukkan kai yana ciwo, dukkan zuciya kuma ta yi rauni.
\v 6 Tun daga tafin sawu har zuwa kai ba inda ba ciwo; sai ciwuka ne da ƙoƙƙojewa, da sababbin raunuka; ba'a rufe su ba, ba'a tsabtace su ba, ba'a naɗe su ba, ko kuma a sa masu mai.
\s5
\v 7 Ƙasarku ta zama kufai; an ƙone biranenku; filayenku - a idonku, bãƙi na hallaka su - an yi watsi da su, an yi kaca-kaca da su ta hannun bãƙi.
\v 8 Ɗiyar Sihiyona an barta kamar 'yar bukka a garkar inabi, kamar 'yar rumfa a lambun kukumba, kamar birnin da aka yiwa sansani.
\s5
\v 9 Idan dã Yahweh mai runduna bai bar mana ragowa ƙalilan ba, da mun zama Sodom, mun kuma zama kamar Gomora.
\s5
\v 10 Ku ji maganar Yahweh, ku shugabannin Sodom; ku saurari shari'ar Allahnmu, ku mutanen Gomora:
\v 11 "Mene ne yawan hadayunku a gare ni?" in ji Yahweh. Ina da isassun baye-bayen ƙonawa na raguna, da kitsen manyan dabbobi; da jinin bijimai, da raguna, ko awaki waɗanda bana jin daɗi.
\s5
\v 12 Lokacin da kuka zo gare ni wa ya buƙaci wannan daga gare ku, don ku tattaka harabaina?
\v 13 Kada ku ƙara kawo baye-bayenku marasa ma'ana, na ƙi ƙonennan turare, ba zan yarda da bukukuwanku na sabon wata ba da na Asabaci - Ba zan yarda da wannan taron ba.
\s5
\v 14 Na ƙi bukukuwanku na sababbin watanni da keɓaɓɓun ranaku; sun zama nawaya a gare ni; Na gaji da jurewa da su.
\v 15 Don haka lokacin da kuka buɗe hannuwanku kuna addu'a na ɓoye fuskata daga gare ku; koda ya ke kun yi addu'o'i da yawa, Ba zan ji ba; hannuwanku sun cika da jini.
\s5
\v 16 Yi wanka ku tsabtace kanku; ku cire mugayen ayyukanku daga fuskata, ku dena mugunta;
\v 17 Ku koyi yin abin kirki; ku nemi adalci, ku dena danniya, ku yi adalci ga marayu, ku kare gwauraye."
\s5
\v 18 Sai ku zo mu tattauna tare," in ji Yahweh; koda zunubanku sun yi kamar jangarura za su yi fari kamar ƙanƙara; koda sun yi jawur kamar jini, za su zama kamar ulun auduga.
\s5
\v 19 In kun yarda kuka yi biyayya za ku ci mafi kyau daga cikin ƙasar,
\v 20 Amma idan kuka ƙi kuka yi tayarwa, to takobi zata haɗiye ku," domin bakin yahweh ne ya furta haka.
\s5
\v 21 Yadda birni mai aminci ya zama karuwa! Ita da dã take cike da adalci, amma yanzu ta cika da masu kisan kai.
\v 22 Zinariyarki ta zama marar tsarki, ruwan inabinki ya gauraye da ruwa.
\s5
\v 23 Sarakunanki masu tayarwa ne da kuma abokan ɓarayi; kowa na ƙaunar cin hanci, yana gudu domin ya ci haram. Ba su kare marayu ba, ba su kuma yiwa gwauruwa shari'ar adalci ba a lokacin da ta zo gare su.
\s5
\v 24 Saboda haka sai ku ji abin da Yahweh mai runduna ya faɗi, Mai Iko na Isra'ila: "Kaiton su! Zan ɗauki fansa a kan maƙiyana, in kuma nuna ramuwata a kan magabtana;
\v 25 Zan juya hannuna gãba daku, zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe in kawar da ƙazantarku dukka.
\s5
\v 26 Zan maido da mahukuntanku kamar farko, mashawartanku kuma kamar na can farko; bayan wannan za a kira ku birnin adalci, gari kuma mai aminci."
\s5
\v 27 Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma ta wurin adalci.
\v 28 Masu tayarwa da masu zunubi za a murje su tare, waɗanda suka yi watsi da Yahweh kuma za a kawar dasu.
\s5
\v 29 Don za ku ji kunyar wurare masu tsarki na itatuwan rimi da kuke marmari, za a kuma kunyata ta wurin lambun da kuka zaɓa.
\v 30 Gama za ku zama kamar itacen rimi wanda ya kaɗe, kamar kuma lambun da ba ruwa.
\s5
\v 31 Ƙaƙƙarfan mutum zai zama kamar ƙeƙasesshe, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duk za a ƙone su tare, ba kuma mai kashe su."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Abubuwan da Ishaya ɗan Amoz ya ji a wahayi game da Yahuda da Yerusalem.
\v 2 Zai zamana a kwanaki na ƙarshe za a kafa tsaunin gidan Yahweh a can ƙololuwar tsaunuka, za a tada shi bisa dukkan tuddai, dukkan al'ummai kuma za su kwararo gare shi.
\s5
\v 3 Mutane da yawa za su zo su ce, "Ku zo mu je kan tsaunin Yahweh, zuwa gidan Allah na Yakubu, don ya koya mana waɗansu hanyoyinsa, mu kuma yi tafiya cikin tafarkunsa." Gama daga Sihiyona shari'a za ta fito maganar Yahweh kuma daga Yerusalem.
\s5
\v 4 Zai hukunta tsakanin al'ummai ya kuma yanke shawara ga mutane da yawa; za su mayar da takkubansu garemani, mãsunsu kuma su maida su almakashin yanke rassa; al'umma ba za ta sake tayar da takobi gãba da al'umma ba, ko kuma su sake horar da kansu don yaƙi.
\s5
\v 5 Gidan Yakubu, ku zo, sai muyi tafiya cikin hasken Yahweh.
\v 6 Gama ka yi watsi da mutanenka, gidan Yakubu, saboda sun cika da al'adu daga gabas suna kuma karatun sihiri kamar Filistiyawa, suna kuma shan hannuwa da 'ya'yan băƙi.
\s5
\v 7 Ƙasarsu ta cika da zinariya da azurfa, kuma wadatarsu ba ta da iyaka; ƙasarsu kuma ta cika da dawakai, karusarsu ba ta da iyaka.
\v 8 Hakannan kuma ƙasarsu ta cika da gumaka; suna bautawa aikin hannun mutum na hannuwansu, abubuwan da yatsunsu suka yi.
\s5
\v 9 Za a sunkuyar da mutane ƙasa, mutum zai faɗi ƙasa; don haka kada ka tada su tsaye.
\v 10 Ku je wurare masu duwatsu ku ɓuya a ƙarƙashin ƙasa don ku ɓoye wa hukuncin Yahweh daga kuma ɗaukakar ikonsa.
\v 11 Za a ƙasƙantar da kallon girman kan mutum, fahariyar mutune kuma za a ƙasƙantar da ita, Yahweh kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
\s5
\v 12 Gama akwai ranar Yahweh mai runduna găba da duk masu girman kai da masu kumbura, găba kuma da duk marasa kunya -
\v 13 kuma da dukkan itatuwan Labanon waɗanda suka yi girma sosai da kuma găba da dukkan itatuwan rimi na Bashan.
\s5
\v 14 Waccan ranar ta Yahweh mai runduna za ta yi găba da dukkan dogayen tsaunuka, da tuddai da suka yi tsayi,
\v 15 gãba kuma da doguwar hasumiya, gãba kuma da kowacce katanga marar gwami,
\v 16 gãba kuma da dukkan jiragen ruwa na Tarshish, gãba kuma da dukkan kyawawan abubuwan tafiya a ruwa.
\s5
\v 17 Za a saukar da girman kan mutum ƙasa, taƙamar mutum kuma zata fãɗi; Yahweh kaɗai za a ɗaukaka a waccan rana.
\v 18 Gumakan za su shuɗe ɗungum.
\v 19 Mutane za su shiga kogonnin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa, domin ɓuya daga razanar Yahweh, da kuma darajar ɗaukakarsa, a lokacin daya tashi domin ya razana duniya.
\s5
\v 20 A ranar nan mutane za su watsar da gumakansu na azurfa da zinariya da suka yiwa kansu domin su bauta masu - za su watsar da su a gidan mujiya da jemagu.
\v 21 Mutane za su shiga cikin matsin duwatsu da kuma cikin tsagar fasassun duwatsu domin su ɓuya daga hasalar Yahweh, kuma daga darajar martabarsa, a lokacin da ya tashi domin ya razana duniya.
\v 22 Ku dena dogara ga mutum, wanda numfashinsa a ƙofofin hancinsa ya ke, domin kuwa wacce daraja ya ke da ita?
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Duba, Ubangiji Yahweh mai runduna, yana gab da ya kawar da Yerusalem da kuma goyon bayansa daga Yahuda, da samar da gurasa da kuma ruwa,
\v 2 mutum mai iko da mayaƙi, da mai hukunci, da annabi da masu dubarsu, da dattijo;
\v 3 jagoran hamsin, da mazaunan birnin da ake girmamawa, da mashawarci, da shahararen masassaƙi, da gwanayen masu sihirinsu.
\s5
\v 4 Zan sa matasa kawai su zama shugabanninsu, matashi kuma zai mulke su.
\v 5 Za a tsanantawa mutane, za su tsananta wa junansu da kuma maƙwabtansu; yaro zai wulaƙanta dattijo, ƙasƙantattu kuma su ƙalubalanci masu martaba.
\s5
\v 6 Mutum zai sami ɗan'uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, 'Kana da riga; ka yi mulkin mu, kuma bari wannan kangon ya kasance a hannuwanka,'
\v 7 Ranar zai yi ihu ya ce, 'Ba zan iya zama mai warkarwa ba; ba ni da gurasa ko sutura. Ba za ku mai da ni shugaban mutane ba,'"
\s5
\v 8 Gama Yerusalem ta yi tuntuɓe, Yahuda kuma ta faɗi, saboda maganganunsu da ayyukansu na gãba da Yahweh, suna rena idanunsa na ɗaukaka
\v 9 Suka duba shaidunsu a fuskarsu suna gãba da su; suna maganar zunubansu kamar Sodom; ba su ɓoye shi ba. Kaiton su! Gama sun kammalawa kansu bala'i.
\s5
\v 10 Faɗawa mai adalci cewa komai zai yi dai-dai, domin za su ci 'ya'yan ayyukansu.
\v 11 Kaiton mugu! abin zai yi masa muni sosai, gama za'a sãka masa abin da ya aikata.
\v 12 Mutanena 'ya'yansu su ne masu wahalshe su, mata ne kuma ke mulkinsu. Mutanena masu yi maku jagora suna ɓatar da ku suna kuma rikitar da hanyar tafarkinku.
\s5
\v 13 Yahweh na tsaye domin ya faɗi laifin mutanensa; yana tsaye domin ya zarge su.
\v 14 Yahweh zai zo da hukunci gãba da dattawan mutanensa da kuma shugabanninsu: "Kun lallatar da garkar inabi; ganimar matalauci na gidajenku.
\v 15 Donme kuke ƙuje mutanena, kuke kuma musgunawa matalauta?" Wannan furcin Ubangiji Yahweh mairunduna ne.
\s5
\v 16 Yahweh yace saboda 'yan matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya suna ɗaga wuya sama, suna kuma jujjuya idanunsu, suna rangwaɗa a lokacin da suke tafiya kayan adon ƙafafunsu na ƙãra.
\v 17 Saboda haka Ubangiji zai saukar masu da ciwon ƙuraje a bisa kawunan 'yan matan Sihiyona, Yahweh kuma zai sa su yi saiƙo.
\s5
\v 18 A wannan ranar Ubangiji zai cire masu kyawawan kayan adonsu na ƙafa, da maɗaurin kansu, da kayan adonsu masu siffofin wata,
\v 19 da 'yankunne, da abin hannu, da kayan lulluɓi;
\v 20 'yankwalaye, da sarkar ƙafa, da ɗamara; da akwatunan turare, da layunsu na neman sa'a.
\s5
\v 21 Zai cire zobba da kayan adon hanci;
\v 22 da suturun bukukuwa, da alkyabbobi, da mayanai, da jakkunan hannu;
\v 23 da madubai na hannu, da linin mai kyau, da ƙyallayen kai, da kuma zannuwa.
\s5
\v 24 A maimakon ƙanshin turare za su yi wari; a maimakon sarƙa kuma igiya; a maimakon gyararriyar suma kuma saiƙo, a maimakon sutura mai ƙawa kuma kayan makoki; tsaga maimakon kyau.
\v 25 Mazajenku za su fãɗi da takobi, jarumawanku kuma za su fãɗi a wurin yaƙi.
\v 26 Ƙofofin Yerusalem za su yi makoki da baƙinciki; za ta kuma zauna a ƙasa a kaɗaice.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 A wannan rana mata bakwai za su riƙe namiji ɗaya su ce, "Mă ciyar da kanmu, mu yiwa kanmu suturar da za mu sa. Amma ka yarda a kira mu da sunanka domin a kawar mana da kunya."
\v 2 A wannan ranar rassan Yahweh za suyi kyau da kuma ɗaukaka, 'ya'yan itatuwan ƙasar kuma za su yi zaƙi, da kuma jin daɗi ga waɗanda suka ragu a Isra'ila.
\s5
\v 3 Zai kasance a wannan ranar da wanda ya ragu a Sihiyona da kuma wanda ya ragu a Yerusalem za a kira shi mai tsarki, da kuma duk wanda aka rubuta sunansa a matsayin mazaunin Yerusalem.
\v 4 Wannan zai faru a lokacin da Ubangiji zai share tsaurin idon 'yan matan Sihiyona, ya kuma goge jinin da ya manne daga tsakiyar Yerusalem, ta wurin ruhun hukunci da kuma ruhun harshen wuta.
\s5
\v 5 Sa'an nan dukkan sassan Tsaunin Sihiyona da kuma kan wuraren taruwarta, Yahweh zai yi girgije da hayaƙi da rana, da kuma hasken harshen wuta da dare; zai zama inuwa a kan dukkan ɗaukaka.
\v 6 Za ta bada inuwa da rana daga zafi, da kuma mafaka da kuma maɓoya daga hadari da ruwan sama.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Sai in raira waƙa ga ƙaunataccena, waƙar ƙaunataccena game da garkar inabinsa. Wadda nake ƙauna sosai yana da garka a tudu mai dausayi.
\v 2 Ya gyara ta, ya cire duwatsu, ya kuma shuke ta da irin inabi mai matuƙar daraja. Ya gina hasumiya a tsakiyar gonar, ya kuma kafa wurin matse ruwan inabi. ya jira ta bada 'ya'ya amma sai 'ya'yan inabin jeji kawai ta yi.
\s5
\v 3 To yanzu, mazauna Yerusalem da mutanen Yahuda, ku yi hukunci tsakanina da garkar inabita.
\v 4 Me kuma zan ƙara yi wa garkar inabita, da ban taba yi mata ba? Lokacin da na dube ta ta bada 'ya'ya me yasa ta bada 'ya'yan inabin jeji?
\s5
\v 5 Yanzu zan fada maku abin da zan yi da garkata: Zan cire shingen, zan mayar da ita makiyaya, zan rushe garunta, za a kuma tattaketa ƙasa
\v 6 Zan watsar da ita, ba zan yi mata noma ko kaftu ba. A maimakon haka ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro a cikin ta. Zan kuma umarci giza-gizai kada su yi ruwa a kanta.
\s5
\v 7 Domin garkar inabin Yahweh mai runduna ita ce gidan Isra'ila, mutanen Yahuda kuma dashensa ne da ya ke jin daɗi; ya jiraci adalci, a maimakon haka sai kisa; a maimakon adalci kuma, sai ihun neman taimako.
\s5
\v 8 Kaiton su masu yawo gida gida, waɗanda ke haɗa wurare daga wannan wuri zuwa wancan wuri, har sai ba ɗakunan da suka ragu sai kai kaɗai za a bari a cikin ƙasar!
\v 9 Yahweh mai runduna ya faɗa mani, gidaje da yawa za su zama kufai, har ma da manyan gidajen nan masu ban sha'awa, ba mazauna.
\v 10 Domin kadada goma ta garkar inabi za ta bada garwa ɗaya ne kacal, sannan mudun iri zai bada ɗangongoni ne kawai.
\s5
\v 11 Kaiton masu tashi da asuba domin neman ƙaƙƙarfan ruwan inabi, waɗanda ba su kwantawa da wuri har sai ruwan inabi ya bugar da su.
\v 12 Suna shagali da sarewa da garaya da tambari da algaita da ruwan inabi, amma ba su fahimci aikin Yahweh ba Ba su kuma yi la'akari da aikin hannuwansa ba.
\s5
\v 13 Saboda haka mutanena suka tafi bautar talala saboda rashin fahimta; Shugabaninsu masu daraja suka zauna a cikin yunwa, talakawansu kuma ba su da wani abin sha.
\v 14 Domin haka Lahira ta maida marmarinta babba ta kuma buɗe bakinta sosai; da masanansu da mutanensu da shugabanninsu da masu duba na cikinsu da kuma waɗanda ke murna a cikin su, sun ɗunguma Lahira.
\s5
\v 15 Za a tilastawa mutum ya sunkuya ƙasa, Za'a ƙasƙantar da mutum; idanun masu taƙama za su wulaƙanta.
\v 16 Yahweh mai runduna zai ɗaukaka cikin adalcinsa, Allah Mai Tsarki nan zai nuna kansa da tsarki cikin adalcinsa.
\v 17 Bayan wannan sai tumakai su yi kiwo kamar a makiyayarsu, a kuma cikin kangaye, 'yan raguna za su yi kiwo kamar bãƙi.
\s5
\v 18 Kaiton masu cire laifofinsu da sarƙoƙi marasa amfani da masu birgima cikin zunubi kamar an ɗaure su da igiya.
\v 19 Kaiton masu cewa, "Bari Allah ya yi sauri, bari ya hanzarta ya yi aikinsa, domin mu ga ya faru; kuma bari shirye-shiryen Mai Tsarki na Isra'ila su zo, domin mu sansu."
\s5
\v 20 Kaiton masu kiran mugunta nagarta, nagarta kuma mugunta; waɗanda suka mai da duhu haske, haske kuma duhu; suka kuma mai da ɗaci zaƙi, zaki kuma ɗaci!
\v 21 Kaiton masu hikima a fuskarsu, masu daraja kuma a cikin fahimtarsu!
\s5
\v 22 Kaiton shahararrun shan ruwan inabi, da waɗanda s ka shahara a wajen gauraya ruwan inabi mai ƙarfi;
\v 23 Waɗanda suka ƙyale mugu saboda a biya su, suka kuma zalunci marar laifi a kan hakinsa!
\s5
\v 24 Saboda haka kamar yadda harshen wuta ke lanƙwame kututture, kamar kuma yadda busasshiyar ciyawa ke shiga harshen wuta haka saiwarsu za ta mutu, kyansu kuma ya gushe kamar ƙura. Wannan zai faru saboda sun ƙi shari'un Yahweh mai runduna, saboda kuma sun rena maganar Mai Tsarki na Isra'ila.
\s5
\v 25 Saboda haka fushin Yahweh yana kan mutanensa. Ya miƙa hannusa gãba da su ya kuma hore su. tsaunuka sun razana, gawawwakinsu sun zama kamar sharar da a ka zubar a bakin hanyonyi. A cikin duk waɗannan abubuwa fushinsa bai sauka ba; a maimakon haka hannunsa har yanzu yana miƙe.
\s5
\v 26 Zai ɗaga alama ta tuta don al'ummai masu nisa zai kuma yi fĩto ga waɗanda ke ƙarshen duniya. Ku duba, za su zo a guje a kan lokaci kuma.
\s5
\v 27 Ba yagewa ko tuntuɓe a cikinsu; babu masu rurrumi ko bacci. Ba su kuma kwance ɗammararsu ba, ko kuma shimfiɗar takalmansu da ta yage.
\v 28 Kibawunsu na da tsini kuma dukkan bakkunansu a tanƙware; kofatan dawakansu kuma kamar curin dutse, gargaren karusarsu kuma kamar hadari ya ke.
\s5
\v 29 Gurnaninsu kuma kamar na zãki; za su yi ruri kamar matasan zãki. Za su yi ruri su fizge abin da suka farauto su kuma ja shi su tafi, ba kuma wanda zai kuɓutar da su.
\v 30 A wannan ranar za su yi ruri kamar yadda tekuna ke ruri. In wani ya dudduba ƙasar zai ga duhu da shan wuya; ko ma da haske za a mai da shi duhu ta wurin giza-gizai.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 A cikin shekarar da sarki Uziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kursiyi; yana da tsayi da kuma martaba, gezar tufarsa kuma ta cika haikalin.
\v 2 A sama da shi kuma da serafim; kowannen su yana da fuka-fukai shida; kowannen su yana rufe fuska da guda biyu, ya kuma rufe ƙafafu da guda biyu, yana kuma shawagi da guda biyu.
\s5
\v 3 Suna kiran juna suna cewa, "Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki," shi ne Yahweh mai runduna! Dukkan duniya ta cika da ɗaukakarsa."
\s5
\v 4 Harsashen ginin ƙofofinsa sun girgiza a lokacin da suka tada murya, sai kuma hayaƙi ya cika gidan.
\v 5 Sa'an nan na ce "kaitona! Gama na hallaka domin ni mutum ne dake da leɓuna marasa tsarki, ina kuma rayuwa a cikin mutane marasa tsarkin leɓuna, saboda idanuna sun ga Sarki, Yahweh, Yahweh mai runduna!"
\s5
\v 6 Daga nan sai ɗaya daga cikin serafim ɗin yawo shawagi wurina; yana da garwashi jawur a hannunsa, wanda ya ɗauko daga bagadi.
\v 7 Sai ya taɓa bakina da shi ya kuma ce, "Duba wannan ya taɓa leɓunanka; an kawar da laifofinka, an kuma gafarta zunubanka."
\s5
\v 8 Na ji muryar Ubangiji tana cewa, "Wa zan aika; wa kuma zai tafi dominmu?" Daga nan sai na ce, "Ga ni; ka aike ni."
\v 9 Ya ce ka je ka faɗawa mutanen nan, za ku ji amma ba za ku gane ba; za ku gani amma ba za ku sani ba.'
\s5
\v 10 Mai da zuciyarsu ta zama marar tunani, kunnuwansu kuma su kurmance, idanunsu kuma su makance. A maimakon haka za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su kuma fahimta da zuciyarsu, kuma daga nan su juyo su kuma warke."
\s5
\v 11 Sai na ce Ubangiji har tsawon wanne lokaci? '"Ya amsa "Har sai birane sun zama kangaye ba mazauna a ciki, gidaje kuma sun zama ba mutane, ƙasar kuma ta zama yasasshiya,
\v 12 Har sai Yahweh ya kora mutanen waje, kaɗaicin ƙasar kuma ya haɓaka.
\s5
\v 13 Koda kashi ɗaya cikin goma na mutanen suka ragu a cikinsa, duk da haka za a ƙara hallaka shi; zai zama kamar ranar da aka datse itacen rimi wanda gungumensa ya ragu, iri mai tsarki na cikin kututture."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 A kwanakin Ahaz ɗan Yotam ɗan Uziya, sarkin Yahuda, Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya da sarkin Isra'ila, suka je Yerusalem domin su yaƙe ta, amma ba su iya yin nasara da ita ba.
\v 2 Sai aka sanar da gidan Dauda cewa Aram ya haɗa kai da Ifraim. Sai ya tsorata, haka ma zuciyar mutanensa, kamar yadda itatuwan jeji ke kaɗawa a cikin iska.
\s5
\v 3 Sai Yahweh yace da Ishaya, "Ka tafi tare da ɗanka Shiya-Yashub ku sadu da Ahaz a ƙarshen kwararon babban wurin da aka datse ruwa, a kan hanya zuwa Filin masu wanki da guga.
\v 4 Ka ce da shi, 'Ka lura, ka tsaya a natse, kada ka ji tsoro ko ka razana saboda waɗannan 'yan guma-gumai na wuta, ta wurin zafin fushin Rezin da Aram, da Feka ɗan Remaliya.
\s5
\v 5 Aram, Ifraim da ɗan Remaliya sun ƙulla mugun abu găba da kai; sun ce,
\v 6 "Bari mu kai wa Yahuda hari mu firgita ta, mu kuma fasa cikinta mu naɗa sarkinmu a can, wato ɗan Tabil."
\s5
\v 7 Ubangiji Yahweh yace, "Ba zai faru ba; ba zai faru ba,
\v 8 saboda shugabar Aram ita ce Damaskus, shugabar Damaskus kuma ita ce Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar, za'a watsa Ifraim kuma ba za su zama al'umma ɗaya ba
\v 9 Shugabar Ifraim ita ce Samariya, shugaban Samariya kuma shi ne ɗan Remaliya. Idan ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya ba, tabbas ba za ku zama da kariya ba.""'
\s5
\v 10 Sai Ubangiji ya sake yin magana da Ahaz,
\v 11 "Ka roƙi alama daga Yahweh Allahnka; ka yi roƙonta ko a cikin zurfafa ko a can sama."
\v 12 Amma Ahaz yace "ba zan yi tambaya, ko kuma in gwada Yahweh ba."
\s5
\v 13 Domin haka Ishaya ya amsa, "Ku saurara, gidan Dauda. Ya ku mutane ashe bai isheku ba ku gwada haƙurin jama'a? Dole ne kuma ku gwada haƙurin Allahna?
\v 14 Saboda haka Ubangiji da kansa zai ba ku alama, duba budurwa za ta yi juna biyu za ta haifi ɗa, za a kira sunansa Imanuwel.
\v 15 Zai ci fãra da ruwan zuma a lokacin da ya ƙi mugunta ya kuma zaɓi nagarta.
\s5
\v 16 Gama kafin yaron ya san ƙin mugunta da zaɓar nagarta, ƙasar sarakunan nan guda biyu da kuka ji tsoronsu za ta zama kufai.
\v 17 Yahweh zai sauko maku da wata rana a kan mutanenku da gidan mahaifanku ranar da ba a taɓa ganin ta ba tun da Ifraim ya bar Yahuda - zai aiko maku da sarkin Asiriya."
\s5
\v 18 A wannan lokacin Yahweh zai yi kira na tashi daga ƙoramu masu nisa na Masar, kuma da na zuma daga ƙasar Asiriya.
\v 19 Duk za su zo su zauna a dukkan kwazazzabai, a cikin kogonnin duwatsu, a kan dukkan ƙayayuwa, da a kan dukkan makiyaya.
\s5
\v 20 A wannan lokacin Ubangiji zai yi aski da rezar da aka yi haya daga hayin Kogin Yuferitis - sarkin Asiriya - da kai da gashin ƙafafu; za a kuma share gemu.
\v 21 A wannan rana mutum zai yi kiwon 'yar karsana da tumaki guda biyu,
\v 22 Kuma saboda yalwar madarar da za su bayar, zai ci cuku, ga duk waɗanda suka ragu a ƙasar za su ci cuku da ruwan zuma.
\s5
\v 23 A wannan lokacin, a inda a kwai dubu na inabi da ya kai azurfa dubu, a wurin ba za a ga komai ba sai sarƙarƙiya da ƙayayuwa.
\v 24 Mutane za su fita farauta da bãka, saboda dukkan ƙasar za ta cika da ƙaya da sarƙaƙiya.
\v 25 Za su tsaya nesa da dukkan tuddan da aka nome da fartanya, domin tsoron sarƙaƙiya da ƙayayuwa; amma zai zama wurin da dabbobi da tumaki za su yi kiwo.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Yahweh yace mani, "Ka ɗauki babban allo ka yi rubutu a kansa, 'Maha-Shalal-Hash-Baz.'
\v 2 Zan kira amintattun shaidu su tabbatar mani, Yuriya Firist, da Zakariya ɗan Yebirekiya."
\s5
\v 3 Na je wurin annabiya, ta kuwa yi juna biyu ta haifi ɗa. Sai Yahweh yace mani, "Ka kira sunansa 'Maha-Shalal-Hash-Baz.'
\v 4 Gama kafin yaron ya san yin kuka har ya furta, 'Babana da Mamata,' sarkin Asiriya zai kwashe dukiyar Damaskus da ganimar Samariya."
\s5
\v 5 Sai Yahweh ya sake yi mani magana,
\v 6 "Saboda waɗannan mutanen sunƙi tausassun ruwayen Shilowa, amma suna murna kan Rezin da ɗan Remaliya,
\v 7 don haka Ubangiji ya kusa kawo ruwayen Kogi a kansu, masu ƙarfi da yawa, sarkin Asiriya da dukkan ɗaukakarsa. Za ya hau kan dukkan magudanansa ya yi ambaliya kan iyakokinsa.
\s5
\v 8 Rafin zai shafe har zuwa cikin Yahuda, ambaliyar zata ratsa, har sai ta kai wuyanka. Miƙawar fikafikansa zai cika iya faɗin ƙasarka, Imanuwel."
\s5
\v 9 Ku mutanen za a daddatsa ku gunduwa-gunduwa. Ku saurara, dukkan ku manisantan ƙasashe: ku yi ɗammara domin yaƙi za a kuwa daddatse ku, ku yi shiri za a kuwa gutsuttsuraku.
\v 10 Ku yi shiri, amma bãza ku iya aiwatarwa ba; ku ba da umarni, ba za a kiyaye ba, gama Allah yana tare da mu.
\s5
\v 11 Yahweh ya yi magana da ni, da hannunsa mai ƙarfi a kaina, ya dokace ni kada in yi tafiya cikin tafarkin mutanen nan.
\v 12 Kada ku kira maƙida akan kowanne abin da mutanen nan suke kira maƙida, kada ku ji tsoron abin da suke tsoro, kada ku firgita kuma.
\v 13 Amma Yahweh mai runduna za ku girmama a matsayin maitsarki; shi ne wanda dole za ku ji tsoro, shi ne dole zai zama abin razanar ku.
\s5
\v 14 Zai zama wuri maitsarki; amma zai zama dutse abin bugu da pã abin sa tuntuɓe ga dukan gidajen Isra'ila, zai zama tarko da azargiya ga mutanen Yerusalem.
\v 15 Mutane da yawa za su yi tuntuɓe a kansa su faɗi su karye, su zama azargiya kuma su kamu.
\s5
\v 16 Ka ɗaure shaida ta, ka hatimce umarni na musamman, ka kuma bada su ga alma'jiraina.
\v 17 Zan jira Yahweh, wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yakubu; Zan jira shi.
\v 18 Duba, Ni da 'ya'yan da Yahweh ya bani domin alamu ne da al'ajibai cikin Isra'ila daga Yahweh mai runduna, wanda ya ke zaune akan Tsaunin Sihiyona.
\s5
\v 19 Za su ce maku, "Ku tuntuɓi mãsu duba da bokaye" waɗanda suke kashe murya suna surkulle. Shin ko mutane ba za su tuntuɓi Allahnsu ba? za su tuntuɓi matattu a madadin masu rai?
\v 20 Ga shari'a da kuma shaida! idan ba su faɗi waɗannan abubuwan ba, saboda ba bu hasken wayewar gari a garesu.
\s5
\v 21 Za su ratsa ta cikin ƙasa da babbar damuwa da yunwa. Idan suna jin yunwa, za su yi fushi su la'anta sarkinsu da Allahnsu, yayin da suka ɗaga fuskokinsu sama.
\v 22 Za su du bi duniya kuma za su ga wahala, duhu, da azabtarwa. Za a koresu zuwa cikin ƙasar duhu.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Amma za a kawar da baƙin duhun daga wurin ta wadda take cikin azaba a dã. A kwanakin da ya ƙasƙantar da ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, amma cikin kwanaki na ƙarshe zai ɗaukakata, ta hanyar teku, ƙetaren Yodan, Galili ta al'ummai.
\v 2 Mutanen da suka yi tafiya cikin duhu sun ga babban haske; waɗanda suka zauna cikin ƙasa ta inuwar mutuwa, haske ya haskaka bisansu.
\s5
\v 3 Ka riɓanya al'umma; ka ƙara farincikin su. Suna murna gaban ka kamar murna a lokacin girbi, kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke raba ganima.
\s5
\v 4 Gama karkiyar kayansa, katakon dake gicciye da kafaɗarsa, sandar mai azabta masa, ka rafke su kamar a ranar Midiyan.
\v 5 Gama dukkan takalman mayaƙa cikin hayaniyar yaƙi da tufafi mirginannu cikin jini za a ƙone su, su zama abin rura wuta.
\s5
\v 6 Gama a gare mu an haifi yaro, a gare mu an bada ɗa; mulki kuma zai kasance a kafaɗarsa; za a kira sunansa Al'ajibi Maishawara, Allah maigirma, Uba Madawwami, Sarkin Salama.
\v 7 Ƙaruwar mulkinsa da salama bata da iyaka, ya yin da ya ke mulki kan kursiyin Dauda, da bisa mulkinsa, a kafa shi a kuma tabbatar dashi cikin gaskiya da adalci daga wannan lokaci har abada kuma. Himmar Yahweh Mairunduna zai yi wannan.
\s5
\v 8 Sai Ubangiji ya aika da magana gãba da Yakubu, sai ta faɗo kan Isra'ila.
\v 9 Dukkan mutane za su sani, har Ifraim da mazaunan Samariya, waɗanda suke magana cikin girmankai da taurin zuciya,
\v 10 "Tubala sun faɗi, amma za mu sake gini da sassaƙaƙƙun duwatsu; an sare durumi ƙasa, amma zamu sa itatuwan sidas amadadinsu."
\s5
\v 11 Domin haka Yahweh zai tayar masa da Rezin, abokin gabarsa, zai harzuƙa maƙiyansa,
\v 12 Suriyawa daga gabas, da kuma Filistiyawa daga yamma. Da baki buɗe za su cinye Isra'ila. A cikin waɗannan duka, fushinsa bai juya ba; maimakon haka, hannunsa har yanzu a miƙe ya ke.
\s5
\v 13 Duk da haka mutane ba za su juya wajen shi wanda ya buge su ba, ba kuwa za su nemi Yahweh mai runduna ba.
\v 14 Domin haka Yahweh zai datse ma Isra'ila kai da wutsiya, reshen dabino da gazarinsa, cikin rana ɗaya.
\v 15 Shugaba da mutum maidaraja su ne kai; da annabi mai koyar da ƙarya shi ne wutsiya.
\s5
\v 16 Waɗanda ke shugabantar jama'ar nan sun karkataddasu, waɗanda suke binsu kuma an haɗiye su.
\v 17 Domin wannan Ubangiji ba za ya yi murna da majiya karfinsu ba ba kuma zai tausayawa marayunsu da gwaurayensu ba, domin kowannensu marasa allahntaka ne da masu aikata mugunta, kowanne baki kuma yana faɗin wauta. Cikin waɗannan duka fushinsa ba zai juya ba; maimakon haka, hannunsa har yanzu a miƙe ya ke.
\s5
\v 18 Mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa; tana ƙone ƙungurmin daji, wanda ke tashi cikin tuƙuƙin hayaƙi.
\v 19 Ta wurin hasalar Yahweh mairunduna ƙasa ta ƙone, mutane kuma sun zama kamar abin rura wuta. Ba mutumin daya bar ɗan'uwansa.
\s5
\v 20 Za su fizge abinci a hannun dama duk da haka za su ji yunwa, za su ci abinci a hannun hagu duk da haka ba za su ƙoshi ba. Kowanne zai ci naman dantsen hannunsa.
\v 21 Manasse zai lanƙwame Ifraim, Ifraim kuma Manasse, tare kuma za su kaima Yahuda farmaki. Cikin waɗannan duka, fushinsa yana nan, maimakon haka, har yanzu hannunsa a miƙe ya ke.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Kaitonsu waɗanda ke zartar da hukuncin zalunci suke rubuta umarnan rashin gaskiya.
\v 2 Suna hana wa mabuƙata adalci, mutanena suna yi masu ƙwace su hana masu haƙƙinsu, gwamraye sun zama ganimarsu, sun maida marayu ganimarsu!
\s5
\v 3 Me za kuyi a ranar hukunci lokacin da hallakarwa ke zuwa daga nesa? wurin wa za ku gudu domin neman taimako, kuma ina za ku bar dukiyarku?
\v 4 Ba abin daya rage, za ku laɓe ƙarƙashin 'yan sarƙa, ko ku faɗi tsakanin kisassu. Cikin dukkan waɗannan abubuwa, fushinsa ba zai sauka ba; maimakon haka, har yanzu hannunsa a miƙe ya ke.
\s5
\v 5 Kaiton Asriyen, kulkin fushina, sandar hannunka a bin harzuƙata ne!
\v 6 Na aike shi gãba da al'umma mai girmankai, gãba da mutane masu ɗauke da ambaliyar fushina. Na umarce shi ya ɗauki ɓãtattu, ya kwashi ganima, ya tattake su kamar laka cikin tituna.
\s5
\v 7 Amma ba haka ya ke nufi ba, bai kuma yi tunanin haka ba. Amma shi a cikin zuciyarsa ne ya kawar da al'umma masu yawa.
\v 8 Gama ya ce, "Shugabannina ba sarakuna ba ne dukkansu?
\v 9 Kalno ba kamar Karkemish ba ce? Hamat ba kamar Arfad ba ce? Samariya ba kamar Damaskus ba ce?
\s5
\v 10 Kamar yadda hannuna ya yi nasara da mulkokin tsafi, wanda ƙerarrun gumakansu sun fi na Yerusalem da Samariya,
\v 11 kamar yadda na yi da Samariya da gumakanta marasa amfani, ba zan yi irin wannan kuma ga Yerusalem da gumakanta ba?"
\s5
\v 12 Sa'ad da Ubangiji ya gama aikin sa akan Tsaunin Sihiyona da bisa Yerusalem, zan hukunta jawabin faɗin ran sarkin Asiriya da homarsa.
\v 13 Domin yace, "Da karfina da hikimata Na yi aiki. Ina da fahimta, na kuma kawas da iyakoki na mutane. Na sace taskokin su, kamar sã na nakasadda mazauna nan wurin.
\s5
\v 14 Hannuna ya tsaya, kamar sheƙa, dukiyar dangogi, kuma kamar wanda ya tattara ƙwan da aka ƙyale. Na tattaro dukkan duniya. Ba bu wanda ya motsa fiffike, ko ya buɗe baki balle suyi ƙara."
\s5
\v 15 Ko gatari zai iya yiwa mai sara da shi alfahari? ko zarto zai iya ɗaukaka kansa bisa wanda ya ke yanka da shi? sai kace sanda zata iya ɗaga mai ɗaukar ta, ko kuma kulkin katako zai ɗaga mutum.
\v 16 Domin haka Yahweh mai runduna zai aiko da ramewa cikin jarumawansa; ƙarƙashin ɗaukakarsa kuma za a kunna ƙonewa kamar wuta.
\s5
\v 17 Hasken Isra'ila kuma zai zama wuta, Mai Tsarkin nasa kuma harshen wuta, za ya ƙone ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ya cinye su rana ɗaya.
\v 18 Yahweh kuma zai cinye darajar kurminsa da gonarsa mai albarka, rai duk da jiki; zai zama kamar lokacin da ran marar lafiya ya suma.
\v 19 Sauran itatuwan kurmin za su zama 'yan kaɗan, ƙaramin yaro zai iya ƙirga su.
\s5
\v 20 A wannan rana, ringin Isra'ila, da iyalin Yakubu waɗanda suka tsira, ba za su dogara ga wanda ya ci nasara da su ba, amma lallai za su dogara ga Yahweh, MaiTsarkin nan na Isra'ila.
\v 21 Ringi na Yakubu za su juya zuwa ga Allah mai iko.
\s5
\v 22 Ko da shike mutanenka, Isra'ila, suna kama da yashin teku, sai ringi daga cikin su za su komo. An zartar da dokar Hallakarwa, kamar yadda adalci mai malalowa ya wajabta.
\v 23 Gama Yahweh mai runduna, daf ya ke da hallakar da dukkan ƙasar kamar yadda ya ayyana.
\s5
\v 24 Domin wannan Ubangiji Yahweh mai runduna yace, "Mutanena da suke zaune cikin Sihiyona, kada ku ji tsoron Asiriyen. Zai buge ku da sanda ya ɗaga kerensa ga bada ku, kamar yadda Masarawa suka yi.
\v 25 "Kada ku ji tsoron sa, gama a cikin ɗan lokaci kaɗan fushina a kanku zai ƙare, fushi na zai kai ga hallakarwarsa."
\s5
\v 26 Daga nan Yahweh mai runduna zai tayar da bulala akansu, kamar yadda ya fatattaki Midiyan a Tsaunin Oreb. Zai ɗaga sandarsa bisa teku ya ɗaga ta sama kamar yadda ya yi a Masar.
\v 27 A wannan rana, nauyin kayansa an ɗauke shi daga kafaɗarki kuma karkiyarsa an ɗauke daga wuyanki, kuma karkiyarki zata lalace saboda ƙibar.
\s5
\v 28 Maƙiyi ya zo Ayiyat ya ratsa ta Migron; a Mikmash ya ajiye abubuwan daya tanada.
\v 29 Sun ƙetare suka sauka a Geba. Rema tana rawar jiki Gibiya ta Saul kuma ta gudu.
\s5
\v 30 Ki yi kuka da ƙarfi, ɗiyar Galim! ki saurara, Laisha! ke talautattar Anatot!
\v 31 Madmena tana gudu, mazaunan Gebim sun gudu domin su ɓuya.
\v 32 A wannan rana zai sauka a Nob zai girgiza damtsensa a tsaunin ɗiyar Sihiyona, tudun Yerusalem.
\s5
\v 33 Duba, Ubangiji Yahweh mai runduna zai sassare rassa da ban razana; itatuwan da suka fi tsawo za'a sare su, maɗaukaka kuma za'a ƙasƙantar dasu.
\v 34 Za ya sassare kuramen jeji da gatari, Lebanon kuma cikin ɗaukakarsa zata faɗi.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Zai toho daga cikin kututturen Yesse, reshe kuma daga cikin sa zai bada 'ya'ya.
\v 2 Ruhun Yahweh kuma zai zauna bisansa, Ruhun hikima da fahimta, da Ruhun umarni da iko, da Ruhun sani dana tsoron Yahweh.
\s5
\v 3 Marmarin sa zai kasance tsoron Ubangiji; ba zaiyi shari'a bisa ga abin da idanunsa suka gani ba, ba kuwa zai yi hakunci bisa ga abin da kunnensa ya ji ba.
\v 4 Maimakon haka zai shar'anta talakwa bisa ga adalci bisa ga dai-daita kuma zai yanke shawara ga masu tawali'u na duniya. Zai bugi duniya da sandar bakinsa, da numfashin leɓunansa kuma zai kashe miyagu.
\v 5 Adalci zai zama ɗammarar ƙugunsa, aminci kuma ɗammara kewaye da kwatangwalonsa.
\s5
\v 6 Kyarkeci zai zauna tare da rago, damisa kuma zata kwanta tare da ɗan'akuya, ɗan maraki da ɗan zaki tare da kiwataccen ɗan maraƙi, za su zauna tare, ɗan yaro kuwa zai bishe su.
\v 7 Saniya da kerkeci za su yi kiwo tare, 'ya'yansu za su kwanta wuri ɗaya. Zaki zai ci ciyawa kamar sã.
\s5
\v 8 Jariri zai yi wasa a bakin ramin maciji, yayayyen yaro kuma zai sa hannunsa a kogon maciji.
\v 9 Ba za su cutar ko hallakar ba a ko'ina kan tsaunina mai tsarki; gama duniya za ta cika da sanin Yahweh, kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
\s5
\v 10 A wannan rana, tushen Jesse zai tsaya a matsayin tuta ga mutane. Al'ummai za su neme shi, wurin hutun sa kuma zai zama abin ɗaukaka.
\v 11 A wannan rana, Ubangiji zai sake sa hannunsa domin ya fanshi sauran mutanensa da suka rage a Asiriya, Masar, Fatros, Kush, Ilam, Shina, Hamat, da tsibirai na teku.
\s5
\v 12 Zaya kafa tuta domin al'ummai ya tattara korarru na Isra'ila warwatsattsu na Yahuda daga kusurwoyi huɗu na duniya.
\v 13 Zai juyar da kishin Ifraim, masu azabtar da Yahuda kuma zai datse su. Ifraim ba zai yi kishin Yahuda ba, Yahuda kuma ba zai ƙara kishin Ifraim ba.
\s5
\v 14 Maimakon haka zasu sauko bisa tuddan Filistiyawa a wajen yamma, tare za su washe 'ya'yan gabas. Za su kai hari ga Idom da Mowab Mutanen Ammon kuma za su yi masu biyayya.
\v 15 Yahweh zai hallakar da dukkan kwarurruka na Tekun Masar. Da iskarsa mai ƙonewa zai karkaɗe hannunsa bisa kan Kogin Yufiretis zai raba su zuwa rafuffuka bakwai, domin a iya ƙetarewa da takalmi a ƙafa.
\s5
\v 16 Zai kasance akwai karabka domin sauran mutanensa, waɗanda suka ragu za su dawo daga Asiriya, kamar yadda akayi ga Isra'ila cikin ranar da suka taso daga ƙasar Masar
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 A wannan rana za ka ce, "Zan gode maka, Yahweh. Koda shike ka yi fushi da ni, fushinka ya juya, ka kuwa yi mani ta'aziya.
\v 2 Duba, Allah shi ne cetona; zan dogara, ba kuwa zan ji tsoro ba, gama Yahweh, hakika, ƙarfina ne da waƙata. Ya zama cetona,"
\s5
\v 3 Da farinciki za ku ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.
\v 4 A wannan rana za ku ce, "Kuyi godiya ga Yahweh ku kuma kira ga sunansa; ku bayyana ayyukan sa a wurin al'ummai, ku yi shelar sunansa maɗaukaki ne.
\s5
\v 5 Ku raira ga Yahweh, gama ya aikata al'amura mafifita, bari wannan ya zama sananne ko'ina a duniya.
\v 6 Ku tada murya ku yi sowa ta murna, ku mazaunan Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra'ila dake tsakiyarku mai girma ne."
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Kenan game da Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa:
\v 2 A bisa buɗaɗɗen tsauni ku ɗaga tutar alama, ku tada murya gare su, ku kaɗa hannu gare su domin su shigo ƙofofin hakimai.
\v 3 Na umarci tsarkakana, I, Na kira masu iko na su aiwatar da fushina, su waɗanda nake fahariya da su da waɗanda aka ɗaukaka.
\s5
\v 4 Hayaniyar mutane cikin duwatsu, sai kace na mutane da yawa! Hayaniya ta mulkokin al'ummai a tattare! Yahweh mai runduna yana tattara runduna domin yaƙi.
\v 5 Sun zo daga ƙasa mai nisa, tun daga iyakacin sama. Yahweh kenan da kayan yakinsa na hukunci, domin hallaka dukkan ƙasa.
\s5
\v 6 Ku yi kuka, gama ranar Ubangiji ta kusa; zata zo da hallakrwa daga Mai iko.
\v 7 Domin haka dukkan hannuwa za su maƙale, kowacce zuciya kuma za ta narke.
\v 8 Za su firgita; zafi da baƙinciki za su kama su, kamar mace cikin naƙuda. Za su dubi junansu cikin mamaki, fuskokinsu za su zama kamar gaushen wuta.
\s5
\v 9 Duba, ranar Yahweh tana zuwa da hasala da fushi mai zafi, za'a maida ƙasar kango, za'a hallakar da masu zunubin daga cikin ta.
\v 10 Taurarin sama ba za su bada haskensu ba. Rana za ta duhunta a lokacin fitowarta, wata kuma ba zai haskaka ba.
\s5
\v 11 Zan hori duniya domin muguntarta da Miyagu domin zunubansu. Zan kawo ƙarshen alfarmar masu girmankai in ƙasƙantar da alfarmar mutane masu ban tsoro.
\v 12 Zan sa maza su yi ƙaranci fiye da zinariya mai daraja, samun mutum kuma ya zama da wuya fiye da tsattsarkar zinariya ta Ofir
\s5
\v 13 Domin wannan zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuma za ta girgiza ta gusa daga wurinta, ta wurin hasalar Yahweh mai runduna, da cikin ranar fushinsa mai zafi.
\v 14 Kamar barewar da aka farauto ko tumakin da ba su da makiyayi, kowanne mutum ya juya ga bin mutanensa, zai gudu zuwa ƙasarsa.
\s5
\v 15 Duk wanda aka samu za a kashe shi, duk wanda aka kama kuma zai mutu da kaifin takobi.
\v 16 Jariransu kuma za a yayyanka su akan idanunsu. Gidajensu za a washesu, matan su kuma za a yi masu fyaɗe.
\s5
\v 17 Duba, Ina gab da tayar da Medes domin su kai masu hari, waɗanda ba za su kula da azurfa ba, ba kuma za su yi murna saboda zinariya ba.
\v 18 Mãsunsu za su soki samari. Ba za su tausayawa jarirai ba kuma ba zasu bar yara ba.
\s5
\v 19 Daga nan Babila, mafi daraja a mulkoki, jamalin fahariyar Kaldiyawa, Allah zai juyadda su kamar yadda ya yi da Sodom da Gomora.
\v 20 Ba za a zauna ciki ko rayuwa a ciki ba daga tsara zuwa tsara. Balarabe ba zai kafa rumfarsa a can ba, makiyaya kuma ba za su bar garken su su huta a can ba.
\s5
\v 21 Amma namomin jeji za su kwanta a wurin. Gidajensu za su cika da mujiyoyi; Jiminai da Gadai za su yi ta tsalle can.
\v 22 Kuraye za su yi kuka a cikin kagarorinsu, diloli kuma a cikin fadodinsu masu kyau. Lokacinta ya kusa, kwanakinta kuma ba za a jinkirtasu ba.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Yahweh zai ji tausayin Yakubu; zai sake zãɓen Isra'ila ya sake dawo da su cikin ƙasarsu, bãƙi za su haɗa kai da su, za su haɗa kansu da gidan Yakubu.
\v 2 Al'ummai za su ɗauke su su kai su garinsu. Gidan Isra'ila zai ɗauke su ya kai su ƙasar Yahweh a matsayi bayi maza da mata. Za su bautadda waɗanda suka kwashe a dã, za su yi mulkin waɗanda suka ƙuntata masu.
\s5
\v 3 A wannan rana Yahweh ya ba ku hutu daga baƙinciki da wahalarku kuma daga aiki mai wahala wanda aka sa ku yi,
\v 4 za ku raira wannan waƙar ta habaici gãba da sarkin Babila, "Yadda ƙarshen mai azabtarwa ya zo, fushin masu girmankai ya ƙare!
\s5
\v 5 Yahweh ya karya sandar mugu, ikon masu mulkin nan,
\v 6 wanda ya bugi mutane cikin fushi da naushi kowanne lokaci, ya mallaki al'ummai da fushi, da harin da ba mai hanawa.
\s5
\v 7 Dukkan duniya tana zaune cikin hutu kuma shiru; sun fara biki da raira waƙa.
\v 8 Har itatuwan sayfres suna murna da kai tare da Sidas na Lebanon; suka ce, 'Tunda aka ƙasƙantar da kai, ba bu wani mai saran itace da ya zo ya sare mu ƙasa.'
\v 9 Lahira daga ƙasa na marmarin saduwa da kai idan ka je can. Ta tayar da mattatu domin ka, dukkan sarakunan duniya an sa sun tashi daga kursiyinsu, dukkan sarakunan al'ummai.
\s5
\v 10 Dukkansu za su yi magana su ce maka, 'Ka zama marar ƙarfi kamar mu.
\v 11 Ka zama irin mu. An yi ƙasa da alfarmarka har Lahira duk da ƙarar amon tamburanka. An shimfiɗa tsutsotsi ƙarƙashinka, tsutsotsi sun rufe ka.'
\s5
\v 12 Yadda ka faɗo daga sama, tauraron rana, ɗan asubahi! Yadda aka sãre ka ƙasa, kai wanda kayi nasara da al'ummai!
\v 13 Sai ka ce a cikin zuciyarka, 'Zan hau cikin sama, Zan ɗaukaka kursiyina bisan taurarin Allah, zan zauna bisa tsaunin taruwar jama'a, cikin ƙarshen arewa.
\v 14 Zan hau can bisa maɗaukakan gajimarai; Zan maida kaina kamar Allah Mai Iko.'
\s5
\v 15 Yanzu angangaradda kai zuwa Lahira, zuwa ƙarshen rami.
\v 16 Waɗanda suka ganka za su zuba maka ido kuma za su saurare ka. Za su ce, 'Ko shi ne mutumin da ya sa duniya ta yi rawa, wanda ya girgiza mulkoki,
\v 17 wanda ya mai da duniya kamar jeji, wanda ya juyadda biranenta ya kuma hana 'yan yãrinsa komawa gida?'
\s5
\v 18 Dukkan sarakunan al'ummai, dukkan su cikin daraja suke kwance, kowannen su cikin kabarinsa.
\v 19 Amma kai an jefar da kai can waje da kushewarka kamar reshen da a ka jefar. Mattatu sun rufe ka kamar riga, waɗanda a ka sara da takobi, masu gangarowa zuwa ramin duwatsu.
\v 20 Ba za ka bi su cikin jana'iza ba, saboda ka hallaka ƙasarka kuma ka kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaton zuriyar masu mugunta ba har abada."
\s5
\v 21 Ka shira yanka domin 'ya'yansa, saboda zunubin kakanninsu, don kada su tashi su mallaki duniya su cika dukkan duniya da birane.
\v 22 "Zan tashi in yi gãba da su"-wannan furcin Yahweh mai runduna ne. Zan datse wa Babila sũna, zuriya da tsãra" - wannan furcin Yahweh ne.
\v 23 Zan maishe ta mallakar mujiyoyi, da kuma tabkunan ruwa, kuma zan share ta tsintsiyar hallakarwa" - wannan shi ne furcin Yahweh mai runduna.
\s5
\v 24 Yahweh mai runduna ya rantse ya ce, "Hakika, kamar yadda na ayyana, haka zai faru; kamar yadda na shirya haka zai faru:
\v 25 Zan karya mutumin Asiriya cikin ƙasa ta kuma bisa kan duwatsu zan tattake shi ƙarƙashin sawu. Daga nan za a kawar da karkiyarsa daga gare su kayansa kuma daga kafaɗarsu."
\s5
\v 26 Wannan shi ne shirin da a ka ƙadartawa dukkan duniya, wannan kuma shi ne hannun da a ka miƙar kan dukkan al'ummai.
\v 27 Gama Yahweh mai runduna ya shirya haka; wa zai hana shi? hannun Sa a miƙe ya ke, wa za ya juyadda shi?
\s5
\v 28 A cikin shekarar da sarki Ahaz ya mutu wannan furcin yazo:
\v 29 Kada ku yi murna, dukkan ku Filistiyawa, cewa sandar da ya buge ki ya karye. Gama daga cikin tsatson maciji ƙasa mai dafi za ta fito, zuriyarsa kuma za ta zama wuta mai firiyar maciji.
\v 30 Ɗan farin talaka zai yi kiwon tumaki a makiyayata, mabuƙaci kuma zai kwanta cikin tsaro. Zan kashe tsatsonka da yunwa dukkan waɗanda suka tsira za su mutu.
\s5
\v 31 Ki yi kururuwa, ƙofa, ki yi kuka, birni, dukkan ku za ku narke, Filistiya. Gama daga arewa girgije mai hayaƙi ke fitowa, ba kuma mai ratsewa cikin dagarsa.
\v 32 Ta yaya za a amsa wa 'yan saƙon al'umman nan? Wato Yahweh ne ya kafa Sihiyona, daga cikin ta ne raunanan mutanensa za su sami mafaka.
\s5
\c 15
\cl Sura 25
\p
\v 1 Furci game da Mowab. Lallai, a dare ɗaya Ar ta Mowab ta zama marar amfani an hallaka ta, Lallai, a dare ɗaya Kir ta Mowab ta zama marar amfani an hallaka ta.
\v 2 Sun hau saman masujada, mutanen Dibon sunje sammai don su yi kuka; Mowab na makoki kan Nebo da Medeba. Duk kawunansu an aske su kwal duk gemunsu kuma an yanke su.
\s5
\v 3 A cikin titunansu suna saye da tsummoki; a kan benayen su da dandalinsu kowannensu yana koke-koke, sun narke da hawaye.
\v 4 Heshbon da Ileyale sun yi kira domin taimako; a na jin muryarsu har Yahaz. Domin haka mayaƙa na Mowab suna kira domin neman taimako; su kadai suna rawar jiki.
\s5
\v 5 Zuciyata tana kuka domin Mowab; sanannun ta suna gudu zuwa Zowa da Iglat Shelishiya. Sun hau zuwa wajen Luhit suna kuka; hanyar zuwa Horonayim sun tada murya da ƙarfi kan hallakarsu.
\v 6 Ruwayen Nimrim sun bushe; ciyawa ta yi yaushi, sabuwar ciyawa ta mutu, ba sauran ɗanyen abu.
\v 7 Yalwar abin da suka samar da wanda suka ajiye, za su ɗauka su haye kwazazzabon foflas.
\s5
\v 8 Kukan ya zaga wajen iyakar Mowab; kuwwarta har ta fi Iglaim da Biya Ilim.
\v 9 Domin ruwayen Dimon cike suke da jini; amma zan kawo wanda ya fi zafi akan Dimon. Zaki zai kai hari ga waɗanda suka tsira a Mowab da kuma sauransu da suka rage a cikin ƙasar.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Ku aika da raguna domin mulkin ƙasa daga Selah cikin jeji; zuwa tsaunin ɗiyar Sihiyona.
\v 2 Kamar tsuntsaye masu yawo, kamar sheƙar da aka warwatsar haka matan Mowab a mishigan Kogin Arnon.
\s5
\v 3 "Ka bada umarni, ka tabbatar da adalci; ka sa inuwa ta zama dare a cikin tsakiyar rana; ka ɓoye yasassu; kada ka bashe da waɗanda ba kome ba.
\v 4 Ka barsu su zauna a cikin ku, 'yan gudun hijira daga Mowab; ka zama maɓuya gare su daga mai lalatarwa." Gama zalunci zai tsaya, hallakarwa kuma zata tsaya, waɗannan da suke tattaka mutane za su ɓace a ƙasar.
\s5
\v 5 A cikin alƙawarin aminci kuma za'a kafa kursiyi, ɗaya kuma daga cikin rumfar Dauda da aminci zai zauna can, zai yi shari'a yana neman adalci, yana aikata gaskiya.
\s5
\v 6 Mun ji labarin girmankan Mowab, girmankansa da fahariyarsa da fushinsa. Amma taƙamarsa duk bakomai ba ne.
\v 7 Sai Mowab tayi koke-koke domin Mowab - dukkan su suna makoki, ku da a ka lalatar ɗungum, domin wainar kauɗar inabin Kir Hareset.
\s5
\v 8 Gonakin Heshbon sun bushe duk da kuringar inabin Sibma. Sarakunan al'ummai sun tattake zaɓaɓɓun inabin da suka kai zuwa Yaza, da suka yaɗu zuwa cikin jeji. Rassanta sun yaɗu waje; sun fita zuwa ƙetaren teku.
\s5
\v 9 Domin wannan zan yi kuka tare da Yaza domin kuringar Sibma. Zan dausayar da ku da hawaye na, Heshbon da Ileyale. Gama na kawo ƙarshen farincikinku game da amfanin gonakinku damina da na kaka.
\v 10 Murna da farincikinku an ɗauke su daga 'ya'yan itatuwan kuramenku, ba sauran waƙa, ba sowa cikin gonakinku. Ba mai taka ruwan inabi a wurin matsewa, gama na kawo ƙarshen sowa ga mai takawar.
\s5
\v 11 Domin haka zuciyata na tsãki kamar girayar Mowab, can cikina kuma domin Kir Hareset.
\v 12 Sa'ad da Mowab ya gajiyar da kansa a wuri mai bisa kuma ya shiga masujada ya yi addu'a, addu'o'insa ba za su yi komai ba.
\s5
\v 13 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗi game da Mowab da farko.
\v 14 Yahweh ya sake yin magana, "Cikin shekara uku, ɗaukakar Mowab za ta ɓace; duk da yawan mutanensa, sauran da za su ragu za su zama 'yan kaɗan marasa amfani."
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Furci game da Damaskus.
\v 2 Biranen Arowa za su zama kufai. Za su zama inda garkuna za su riƙa kwanciya, ba kuwa mai tsoratar dasu.
\v 3 Biranensu masu kagara za su ɓace daga Ifraim, mulki kuma daga Damaskus, da ringin Aram - za su zama kamar ɗaukakar mutanen Isra'ila - wannan furcin Yahweh mai runduna ne.
\s5
\v 4 Zai zama kuma a ranar nan darajar Yakubu zata zama 'yar siririya, ƙibar jikinsa zata saɓe.
\v 5 Zai zama kamar kwanakin da maigirbi ya tattara hatsin dake tsaye, hannunsa kuma yana yankan zangarku. zai zama kamar lokacin da mutum ke kalar zangarku cikin kwarin Refayim.
\s5
\v 6 Za'a bar kala, duk da haka, kamar lokacin da itacen zaitun ke kakkaɓewa: biyu ko uku cikin reshe mafi bisa, huɗu ko biyar a cikin rassa mafi bisa na itace mai 'ya'ya - wannan furcin Yahweh ne, Allah na Isra'ila.
\v 7 A wannan rana mutane za su dubi mahaliccinsu, idanunsu za su dubi Mai Tsarki na Isra'ila.
\s5
\v 8 Za su dubu bagadai, aikin hannuwansu, ba kuwa za su dubi abin da yatsunsu suka yi ba, sandunan Ashera ko siffofin rana.
\v 9 A wannan rana ƙarfafan biranensu za su zama kamar wuraren da aka bar su kufai cikin kurmi a ƙwanƙolin tsaunuka, da aka bar su saboda mutanen Isra'ila wannan zai zama hallaka.
\s5
\v 10 Domin kun manta da Allah mai cetonku, kun kuma yi watsi da dutsen ƙarfinku. Kuna dasa tsire-tsiren da suka gamshe ku, kuna dasa rassan inabi da kuka karɓa wurin baƙo,
\v 11 A cikin rana kayi dashe da shinge da noma. Bada daɗewa ba irinka zai yi girma, amma girbinka zai gaza a cikin ranar baƙinciki da matsananciyar azaba.
\s5
\v 12 Kaito! ga hayaniyar mutane da yawa, wannan ruri na kama da rurin tekuna, da gudun al'ummai, suna gudu kamar gudun ruwaye masu girma!
\v 13 Al'ummai za su yi ruri kamar gudun ruwaye masu yawa, amma Allah zai tsauta masu. Za su gudu nesa za'a runtume su kamar ƙai-ƙai a kan tsaunuka gaban iska, kamar guguwa kuma gaban hadari.
\v 14 Da yamma, ga, razana! Kafin safiya kuma za su tafi! wannan shi ne rabon waɗanda suke yi mana sata, rabon waɗanda suke yi mana fashi.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Kaiton ƙasa ta motsin fukafukai wadda, take rafukan Kush.
\v 2 Wadda take aika jakadu ta hanyar teku, a cikin ruwaye ta jiragen iwa Ku tafi ku, jakadu masu sauri, wurin dogayen al'ummai masu taushin fata, wurin mutanen da a ke tsoron su nesa da kusa, al'umma mai ban razana mai tattakewa, wadda ruwaye sun raba ƙasarta.
\s5
\v 3 Dukkan ku mazaunan duniya da waɗanda ke zaune a duniya, idan kuka ga alama a kan duwatsu, ku duba; idan aka busa ƙaho, ku saurara.
\s5
\v 4 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi mani, "A hankali zan lura daga gidana, kamar gumi cikin hasken rana, kamar hazon ƙyasashi a lokacin girbi.
\v 5 Kafin girbi, ya zo sa'ad da fure ya kaɗe, huda tana zama nunannun 'ya'yan inabi, zai datse maɓulɓula da ƙugiya mai tsini, zai sare ya kuma kwashe rassan da suka barbaje.
\s5
\v 6 Za a bar su tare saboda tsuntsayen duwatsu da dabbobin duniya. Tsuntsaye za su yi damina a kansu, kuma dukkan dabbobin duniya za su yi lokacin sanyi a kansu."
\v 7 A wancan lokacin dogayen mutane masu taushin jiki za su kawo hadaya ga Yahweh, daga mutanen da a ke tsoro nesa da kusa, ƙarfafan al'ummai masu ban razana, waɗanda rafuka suka raba ƙasarsu, zuwa wurin da ya ke na sunan Yahweh mai runduna, zuwa Tsaunin Sihiyona.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Furci game da Masar. Duba, Yahweh ya hau girgije mai sauri ya taho Masar; gumakan Masar za su razana a gabansa, zuciyar masarawa za ta narke a cikin su.
\v 2 "Zan haɗa masarawa gãba da masarawa: Mutum zai yi faɗa gãba da ɗan'uwansa, mutum gãba da maƙwabcinsa; birni kuma gãba da birni, mulki kuma gãba da mulki.
\s5
\v 3 Ruhun Masar zai karaya daga ciki. Zan rushe shawararsa, koda ya ke sun nemi shawarar gumakai, da ruhun matattu, da masu duba, da masu aiki da ruhohi.
\v 4 Zan bada masarawa a hannun mugun shugaba, sarki mai ƙarfi zai yi mulkin su - wannan shi ne furcin Yahweh Ubangiji mai runduna."
\s5
\v 5 Ruwayen teku za su bushe, rafi zai bushe ya zama ba komai.
\v 6 Rafuka za su yi wari; ƙoramun Masar kuma za su shanye su bushe; iwa da jema za su yi yaushi.
\s5
\v 7 Iwar dake kusa da Nilu, da bakin gãɓar Nilu, da dukkan gonakin da a ka shuka a gefen Nilu za su bushe, za a kore su, kuma ba za su kasance ba.
\v 8 Masunta za su yi kuka su yi makoki, da dukkan masu jefa ƙugiya cikin Nilu za su yi makoki, kuma masu jefa tãru za su yi baƙinciki.
\s5
\v 9 Masu aikin tsifar zare da waɗanda ke saƙar farar tufa za su rame.
\v 10 Za a murƙushe masu aikin tufafi na Masar; masu aikin lada za su yi baƙinciki a cikin su.
\s5
\v 11 Sarakunan Zowan wawaye ne gaba ɗaya. Shawarar mashawartan Fir'auna mafiya wayo ta zama rashin hankali. Yaya za ka iya cewa da Fir'auna, "Ni ɗan mutane masu hikima ne, ni ɗan sarakunan dã ne?"
\v 12 Ina mazajenka masu wayau suke? Bari su gaya maka su kuma sanasshe ka abin da Yahweh mai runduna ke shiryawa game da Masar.
\s5
\v 13 Sarakunan Zowan sun zama wawaye, an ruɗi sarakunan Memfis; sun sa Masar ta bauɗe, su da suke duwatsun kusurwar kabilunta.
\v 14 Yahweh ya sa ruhun lalacewa cikin tsakiyarta, suka kuma sa Masar ta bauɗe cikin dukkan abin da take yi, kamar mashayi mai tangaɗi cikin amansa.
\v 15 Ba abin da wani zai iya yi domin Masar, ko kai ko wutsiya, ko rassan dabino ko iwa.
\s5
\v 16 A wannan rana, Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki da tsoro saboda ɗagaggen hannun Ubangiji mai runduna a kansu.
\v 17 Ƙasar Yahuda za ta zama sanadin tangaɗin Masar. Dukkan sa'ad da wani ya tuna masu da ita, za su ji tsoro, saboda shirin Yahweh, kan abin da ya ke shiryawa gãba da su.
\s5
\v 18 A wannan rana za a sami birane biyar cikin ƙasar Masar da za su yi magana da harshen Kan'ana su yi rantsuwa su yi amana da Yahweh mai runduna. Ɗaya daga waɗannan za a kira shi Birnin Rana.
\s5
\v 19 A wannan rana za a sami bagadin Yahweh a tsakiyar ƙasar Masar, da dutsen daya zama ginshiƙi na kan iyakar Yahweh.
\v 20 Zai zama kamar alama da shaida ga Yahweh mai runduna a cikin ƙasar Masar. Idan suka yi kuka ga Yahweh saboda mai tsananta masu, zai aiko masu da mai ceto da mai kariya, zai kuma cece su.
\s5
\v 21 Yahweh zai zama sananne a Masar, a wannan rana Masarawa za su san da kasancewar Yahweh. Za su yi sujada da hadayu da baye-baye, za su yi wa'adodi ga Yahweh, su cika su kuma.
\v 22 Yahweh zai azabci Masar, yana azabtarwa da warkarwa kuma. Za su juyo ga Yahweh; zai ji addu'arsu ya warkar dasu.
\s5
\v 23 A wannan rana za a sami karabka tsakanin Masar da Asiriya, Asiriye zai zo Masar, Bamasare kuma zai je Asiriya; Masarawa kuma za su yi sujada tare da Asiriyawa.
\s5
\v 24 A cikin wannan rana, Isra'ila za ta zama ta uku tare da Masar da Asiriya, za su zama albarka a tsakiyar duniya;
\v 25 Yahweh mai runduna zai albarkace su ya ce, "Mai albarka ce Masar, jama'ata; Asiriya, aikin hannuwana; da Isra'ila, abin gãdona."
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 A cikin shekarar da Tartan ya zo Ashdod, sa'ad da Sargon sarkin Asiriya ya aiko shi, ya yi faɗa gãba da Ashdod ya amshe ta.
\v 2 A wannan lokaci Yahweh ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz yace, "Ka je ka tuɓe tsummokara daga ƙugunka, ka tuɓe takalma daga ƙafafunka." Ya yi haka, ya yi tafiya huntu ba takalma a ƙafafunsa.
\s5
\v 3 Yahweh yace, "Kamar yadda bawana Ishaya ya yi tafiya huntu ba takalma a ƙafafunsa shekara uku, wannan alama ce da al'ajibi dangane da Masar da Kush -
\v 4 ta haka sarkin Asiriya zai tafi da kamammu na Masar, da korarru na Kush, tsoho da yaro, huntu ba takalmi, da ɗuwawunsu a waje, domin Masar ta kunyata.
\s5
\v 5 Za su karaya su ji kunya, saboda Kush begensu da Masar darajarsu.
\v 6 Mazaunan wannan yanki a cikin wannan rana za su ce, 'Hakika, wannan shi ne tushen begenmu, inda mu kan ruga neman taimako domin a cece mu daga sarkin Asiriya, to yanzu, ta yaya za mu tsira?"'
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Furci game da hamada ta wajan teku. Kamar guguwa mai sharewa ta bi ta Negeb, ta zo tana wucewa ta cikin jeji, daga ƙasa mai ban tsoro.
\v 2 An ba ni ruya mai ban razana: mutum marar imani yana yin rashin imani, mai hallakarwa yana hallakarwa. Jeka ka kai hari, a kan Ilam; yi sansani, Midiya; zan tsaida dukkan rurinta.
\s5
\v 3 Saboda haka kwankwasona ya cika da ciwo; ciwo kamar irin ciwon mace mai naƙuda ya kama ni; abin da na ji ya durƙusar da ni; abin da na gani ya tada hankalina.
\v 4 Zuciyata tana bugawa; na kaɗu da tsoro. Hasken asuba lokacin da nike so, amma ya kawo razana a gare ni.
\s5
\v 5 Sun shirya teburi, sun shimfiɗa dardumai, sun ci sun sha; ku tashi, yarimai, ku shafe garkuwoyinku da mai.
\s5
\v 6 Gama abin da Yahweh yace da ni ke nan, "Jeka, ka sa mai tsaro; dole ya faɗi abin da ya gani.
\v 7 Sa'ad da ya ga karusa, da tagwayen mahaya, a kan jakuna, da raƙuma, sai ya natsu ya yi lura sosai."
\s5
\v 8 Mai tsaron ya yi kuka, "Ubangiji, a kan kagara nike tsaye dukkan yini, kullum, a kan aikina nike dukkan dare."
\v 9 Ga karusa tana zuwa da mutum da tagwayen mahaya. Ya yi kira, "Babila ta faɗi, ta faɗi, dukkan sassaƙaƙƙun siffofin allolinta kuma sun ragargaje har ƙasa."
\s5
\v 10 Masussukaina da sheƙaƙƙu, yaran masussukata! Abin da na ji daga Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, shi na furta maku.
\s5
\v 11 Furci game da Duma. Wani ya kira ni daga Siya, "Mai tsaro, me ya rage na dare?" Mai tsaro, me ya rage na dare?"
\v 12 Mai tsaro ya ce, "Safiya ta kan zo haka ma dare. Idan kana so ka yi tambaya, sai ka yi tambaya; ka sake dawowa kuma."
\s5
\v 13 Furci game da Arebiya. A cikin jejin Arebiya za ku kwana, ku fataken Dedaniyawa.
\v 14 Ku kawo ruwa saboda masu jin ƙishi; mazauna ƙasar Tema, ku kawo gurasa ga masu gudun hijira.
\v 15 Gama sun gudo daga takobi, daga takobin da a ka zaro, daga bakan da ke a ɗane, kuma daga nawayar yaƙi.
\s5
\v 16 Gama abin da Yahweh ya faɗa mani ke nan, "A cikin shekara ɗaya, kamar yadda ma'aikacin da a ka ɗauka domin shekara ɗaya zai gani, dukkan darajar Keda za ta ƙare.
\v 17 Maharba kaɗan kawai, da jarumawan Keda 'yan kaɗan za su rage," gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Furci game da Kwarin Wahayi: Mene ne dalilin da ya kai dukkan ku bisan gidaje?
\v 2 Shi ne domin ka ji birni cike da hargowa, birni cike da bukukuwa? Matattunka bada takobi a ka kashe su ba, kuma ba a dãgar yaƙi suka mutu ba.
\s5
\v 3 Dukkan masu mulkinku sun gudu tare, amma an kamo su ba tare da an yi amfani da baka ba; dukkan su an kamo su tare, koda ya ke sun gudu nesa.
\v 4 Saboda haka sai na ce, "Kada ku dube ni, zan yi kuka mai zafi; Kada ku yi ƙoƙarin ta'azantar da ni game da hallakar ɗiyar mutanena."
\s5
\v 5 Gama akwai ranar hargitsi, tana tattakowa, da ruɗami domin Ubangiji Yahweh mai runduna, a Kwari na Wahayi, da rushewar ganuwoyi, da mutane suna kuka ga duwatsu.
\v 6 Ilam ya ɗauki kwãri, da mahayan karusai da mahayan dawakai, Kir kuma ya ajiye garkuwa a fili.
\v 7 Zai zama zaɓaɓɓun kwarurrukan ku za su cika da karusai, masu hawan dawaki kuma za su ja dãgarsu a ƙofa.
\s5
\v 8 Ya ɗauke kariyar Yahuda; a cikin wannan rana ka duba kayan yaƙi a Fada wadda ke Jeji.
\v 9 Kun ga tsagogin birnin Dauda, suna da yawa, ku ka kuma ɗebo ruwa daga tafki na gangare.
\s5
\v 10 Kun ƙirga gidajen Yerusalem, kun fasa gidaje domin ku ƙara ƙarfin ganuwa.
\v 11 kun gina wurin tãra ruwa a tsakanin ganuwowin biyu na tsohon tafki. Amma ba ku kula da wanda ya yi birnin ba, wanda ya shirya shi tun da daɗewa.
\s5
\v 12 Ubangiji Yahweh mai runduna ya yi kira a wannan rana domin kuka, domin makoki, domin aske kawuna, da sanya tsummokara.
\v 13 Amma duba, maimakon haka, sai buki da annashuwa, da yanka shanu da tumaki, da cin nama da shaye-shayen ruwan inabi; bari mu ci mu sha, gama gobe za mu mutu.
\v 14 An bayyana mani haka a kunnuwana daga wurin Yahweh mai runduna: "Babu shakka ba za a gafarta maku wannan muguntar ba, ko kun mutu," inji Ubangiji Yahweh mai runduna.
\s5
\v 15 Ubangiji Yahweh mai runduna, yace, "Jeka wurin shugaban nan, wurin Shebna, mai lura da gidan, ka ce,
\v 16 "Me ka ke yi a nan, wane ne ya ba ka izini ka gina kabari domin kanka, sassaƙa kabari ya ke yi a wurare masu tsawo, yana sassaƙawa kansa wurin hutawa a cikin dutse?"'
\s5
\v 17 Duba, Yahweh ya kusa jefar da kai, ƙaƙƙarfan mutum, ya kusa jefar da kai ƙasa; zai cafke ka da ƙarfi.
\v 18 Ba shakka zai yi majaujawa da kai, kamar ƙwallo zai wurga ka a cikin ƙasa mai girma. Can za ka mutu, can kuma karusanka masu daraja za su kasance; za ka zama abin kunyar gidan shugabanka!
\v 19 Zan tumɓuke ka daga matsayin ka daga wurin da kake aiki. Zan jawo ka har ƙasa.
\s5
\v 20 Zai zama a wannan rana zan kira bawana Iliyakim ɗan Hilkiya.
\v 21 Zan tufasantar da shi da alkyabbarka in ɗaura masa ɗamararka, zan maida muƙaminka a hannunsa. Za ya zama uba ga mazaunan Yerusalem da gidan Yahuda.
\v 22 Zan ɗora mabuɗin gidan Dauda a kafaɗarsa; zai buɗe, kuma ba mai kullewa; zai kulle, kuma ba mai buɗewa.
\s5
\v 23 Zan kafa shi, kamar ƙusa a wuri mai tsaro, zai zama mazaunin ɗaukaka domin gidan ubansa.
\v 24 Za su rataya masa dukkan ɗaukakar gidan ubansa, 'ya'ya da zuriya-zuriya, kowanne ƙaramin wurin ajiya daga ƙoƙuna zuwa dukkan moɗaye.
\s5
\v 25 A wannan rana - wannan furcin Yahweh mai runduna ne - ƙusar da a ka kafa a wuri mai ƙarfi za ta cire, ta karye, ta kuma faɗi, nauyin dake kanta kuma zai yanke - Gama Yahweh ya furta.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Furci game da Taya: Ku yi ruri, ku jiragen Tarshish; domin babu gida ko wurin tsayawa; daga ƙasar Sifuros an bayyana masu.
\v 2 Ku yi shiru, ku mazauna bakin teku; 'yan kasuwar Sidon, masu tafiya kan teku, sun cika ku.
\v 3 A kan manyan ruwaye ga hatsin Shiho, girbin Nilu ne amfaninta; kuma ta zama wurin cinikin al'ummai.
\s5
\v 4 Ki ji kunya, ke Sidon; gama teku ya yi magana, babba na teku. Ya ce, "Ban yi naƙuda ba ban haihu ba, ban yi renon samari ba, ban tarbiyantar da 'yammata ba."
\v 5 Sa'ad da rahoton ya zo ga Masar, za su yi baƙinciki saboda Taya.
\s5
\v 6 Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka, ku mazauna bakin teku.
\v 7 Wannan ya faru da ku ne, birni mai farinciki, wanda tushenta tun daga zamanin dã ne, wadda ƙafafunta sun kai ta can nesa zuwa bãƙin wurare ta zauna?
\s5
\v 8 Wane ne ya shirya wa wannan gãba da Taya haka, mai bada rawwuna ce, wadda 'yan cinikinta yarimai ne, wanda dillalanta masu daraja ne na duniya?
\v 9 Yahweh mai runduna ne ya shirya haka domin ya ƙasƙantar da girman kanta da dukkan darajarta, ya kunyatar da dukkan masu martabarta a duniya.
\s5
\v 10 Ki nome gonarki, kamar mai noma a Nilu, ke ɗiyar Tarshish. Ba sauran wurin kasuwanci a Taya.
\v 11 Yahweh ya kai hannunsa bisa teku, ya girgiza mulkoki; ya bada umarni game da Fonisiya, ta rushe ƙarfafan wurarensu.
\v 12 Ya ce, "Ba za ki ƙara yin farinciki ba, ke mai shan tsanani ɗiyar budurwa ta Sidon; ki tashi, ki wuce zuwa Sifuros; Amma ko can ma ba za ki sami hutu ba."
\s5
\v 13 Dubi ƙasar Kaldiyawa. Waɗannan mutane yanzu ba su; Asiriyawa sun maida ita daji domin dabbobin jeji. Sun kafa hasumiyoyin sansaninsu; sun rushe fãdojinta; sun maida ita tsibin kufai.
\v 14 Ku yi ruri, ku jiragen Tarshish; gama an rushe mafakarku.
\s5
\v 15 A wannan rana, za a manta da Taya har shekara saba'in, kamar kwanakin sarki. Bayan shekara saba'in ɗin wani abu zai faru da Taya kamar yadda ya ke a cikin waƙar karuwa.
\v 16 Ɗauki molo, ki zagaya birnin, ke karuwar da a ka manta da ita; ki kaɗa su da kyau, ki yi waƙoƙi masu yawa, domin a tuna dake.
\s5
\v 17 Zai zama bayan shekara saba'in, Yahweh zai taimaki Taya, za ta fara samun kuɗi ta wurin aikin karuwanci, za ta bada hidimarta ga dukkan mulkokin duniya.
\v 18 Ribarta da abin da take samu za a keɓe shi ga Yahweh. Ba za a tara su ko a ajiye su a ma'aji ba, gama za a bada ribarta ga waɗanda suke zama a gaban Yahweh domin ayi amfani da su a ba su abinci isashshe saboda su sami tufafi mafi daraja.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Duba, Yahweh ya kusa mayar da duniya kango, ya lalata ta, ya ɓata fuskarta, ya watsar da mazauna cikinta.
\v 2 Za ya zama cewa, kamar yadda ya ke da mutane, haka kuma firist; kamar yadda iyayengiji suke haka bayi za su zama, kamar yadda uwargijiya take, haka kuyangarta za ta zama, kamar yadda mai sayarwa ya ke, haka mai saye za ya zama; kamar yadda mai bada bashi ya ke, haka mai karɓar bashin za ya zama; kamar yadda mai karɓar bashi da ruwa ya ke, haka mai bada wa da ruwa.
\s5
\v 3 Duniya za ta zama kango ta zama huntuwa sarai; gama Yahweh ya faɗi wannan magana.
\v 4 Ƙasa za ta yanƙwane ta bushe, duniya za ta koɗe ta watse, sanannun mutane na duniya za su lalace.
\v 5 Duniya ta ƙazamtu daga mazaunanta saboda sun karya dokoki, sun wofinta farillai, sun karya alƙawari na har abada.
\s5
\v 6 Saboda haka, la'ana ta cinye duniya, an sami mazaunan ta da laifi. Mazauna duniya sun ƙone, mutane kuma kaɗan suka rage.
\v 7 Sabon ruwan inabi ya bushe, kuringar ta yi yaushi, dukkan masu farinciki a zuciya suna nishi.
\s5
\v 8 Ƙarar murna ta kacau-kacau ta ƙare, bukukuwan waɗanda suke farinciki; murnar masu garaya ta ƙare.
\v 9 Ba sa shan ruwan inabi su yi waƙa, kuma barasa ta yi ɗaci ga masu shan ta.
\s5
\v 10 An rushe birni mai ruɗani; an rufe kowanne gida ba kowa a ciki.
\v 11 Ana kuka a kan hanyoyi saboda ruwan inabi; dukkan farinciki ya duhunta, murnar birnin ta shuɗe.
\s5
\v 12 A cikin birnin sai kufai, an rushe birnin, an ɓalle ƙofarsa zuwa kango.
\v 13 Domin haka zai kasance a dukkan duniya cikin al'ummai, kamar yadda a ke bugun itacen zaitun, kamar yadda a ke kãlar inabi bayan an gama girbi.
\s5
\v 14 Za su tada muryoyi su yi sowa ga darajar Yahweh, kuma za su yi sowa ta murna daga teku.
\v 15 Saboda haka daga gabas ku ɗaukaka Yahweh, a cikin tsibiran teku ku ɗaukaka sunan Yahweh, Allah na Isra'ila.
\s5
\v 16 Mun ji waƙoƙi daga wuri mafi nisa na duniya, "Ɗaukaka ga mai tsarki!" Amma na ce, "Kaito na, na lalace, na lalace! Mazambata sun yi zamba; i, mazambata sun yi zamba ƙwarai."
\s5
\v 17 Razana, da rami da tarko suna kanku, mazaunan duniya.
\v 18 Shi wanda ya gudu saboda jin ƙarar razana zai faɗa rami, kuma shi wanda ya fito daga tsakiyar rami tarko zai kama shi. Tagogin sama za su buɗe, tussan duniya kuma za su girgiza.
\s5
\v 19 Za a rushe duniya sarai, duniya zata tsage, duniya zata girgiza ƙwarai.
\v 20 Duniya zata yi tangaɗi kamar mutum mashayi ta yi tangaɗi gaba da baya kamar bukka. Zunubinta zai yi mata nauyi zata faɗi ba zata ƙara tashi ba.
\s5
\v 21 Zai zama a wannan rana, Yahweh zai hukunta rundunar sama a can sammai, sarakunan duniya kuma a duniya.
\v 22 Za a tattara su tare, 'yan sarƙa a cikin rami, za a rufe su a cikin kurkuku; bayan kwanaki da yawa zai yi masu hukunci.
\v 23 Sa'an nan rana zata ƙasƙanta wata kuma ya ji kunya, gama Yahweh zai yi mulki a Tsaunin Sihiyona da cikin Yerusalem a gaban dattawansa cikin daraja.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Yahweh, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka, zan yabi sunanka; saboda ka yi abubuwan ban mamaki, abubuwan da a ka shirya tun dã, cikin cikakken aminci.
\v 2 Gama ka mayar da birnin juji, birni mai daraja ya zama kufai, wurin zaman baƙi ya zama ba birni ba kuwa.
\v 3 Saboda haka ƙarfafan mutane za su ɗaukaka ka; birnin al'ummai 'yan ta'adda zai ji tsoronka.
\s5
\v 4 Gama ka zama mafaka ga wanda ya ke matalauci, mafaka ga fakirai mabuƙata - wurin fakewa daga hadari, wurin fakewa daga zafin rana. Sa'ad da hucin marasa hankali ya ke kamar haɗari mai buga bango,
\v 5 kamar zafi a busasshiyar ƙasa, ka sha ƙarfin hayaniyar bãƙi, kamar yadda inuwar giza-gizai sukan sha ƙarfin zafi, haka aka amsa waƙar 'yan ta'adda.
\s5
\v 6 A kan wannan tsaunin Yahweh mai runduna zai yiwa dukkan mutane liyafa da abubuwa masu ƙiba, zaɓaɓen ruwan inabi, da nama mai taushi, liyafar ruwan 'ya'yan itace.
\v 7 A kan wannan tsaunin zai rushe abin da ya rufe dukkan mutane, saƙaƙƙen mayafin lulluɓe dukkan al'ummai.
\v 8 Zai haɗiye mutuwa har abada, Ubangiji Yahweh zai share hawaye daga dukkan fuskoki; zai ɗauke ƙasƙancin mutanensa daga duniya dukka, gama Yahweh ya faɗe shi.
\s5
\v 9 A wannan rana za a ce, "Duba, wannan shi ne Allahnmu, mun jira shi, shi kuma zai cece mu. Wannan shi ne Yahweh, mun jira shi, za mu yi murna da farinciki cikin cetonsa."
\v 10 Gama a wannan tsaunin Yahweh zai ɗora hannunsa; za a tattake Mowab daga wurinsa, kamar yadda ake tattake ciyawa cikin ramin dake cike da taki.
\s5
\v 11 Za su buɗe hannuwansu a tsakiyarsa, kamar yadda mai iyo ya kan buɗe hannunsa ya yi iyo.
\v 12 Amma Yahweh zai ƙasƙantar da girman kansu, duk da hikimar hannuwansu. Zai rushe hasumiyoyinsu mai tsawo har ƙasa ta zama turɓaya.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 A wannan rana za a yi wannan waƙar a ƙasar Yahuda: Mu na da birni mai ƙarfi; Yahweh yasa ceto ya zama ganuwarsa da kagararsa.
\v 2 A Buɗe ƙofofin, domin al'umma mai adalci da take riƙe gaskiya ta shiga ciki.
\s5
\v 3 Wanda ya tsayar da hankalinsa a kanka, za ka riƙe shi cikin cikakkiyar salama, domin ya dogara gare ka.
\v 4 Ku sa dogara cikin Yahweh, har abada; gama cikin Yah, Yahweh, dutse ne na har abada.
\s5
\v 5 Gama waɗanda suke zama cikin girman kai zai ƙasƙantar da su; zai rushe tsararren birni, zai rushe shi har ƙasa; ya mayar da shi turɓaya.
\v 6 Fakirai da matalauta za su tattake shi da ƙafafunsu har ƙasa.
\s5
\v 7 Hanyar mai adalci an shirya ta, Mai Adalcin nan; ka shirya tafarkin mai adalci ka maishe ta miƙaƙƙa.
\v 8 I, a tafarkin hukuncinka, Yahweh, za mu jira ka; sunanka da ɗabi'arka su ne marmarinmu.
\v 9 Na ji marmarinka cikin dare; i, ruhuna a cikina ya neme ka da gaske. Gama sa'ad da hukucinka ya zo duniya, mazaunan duniya suna koyo game da adalci.
\s5
\v 10 Bari a nuna wa mai mugunta tagomashi, amma ba zai koyi adalci ba. A cikin ƙasar masu tafiya dai-dai, shi mugunta ya ke yi kuma darajar Yahweh shi bai san ta ba.
\s5
\v 11 Yahweh, an tada hannunka sama, amma su ba su lura ba, amma za su ga himmar ka domin mutane za su ji kunya, saboda wutar magabtanka za ta cinye su.
\v 12 Yahweh, za ka kawo mana salama; gama hakika ka cika dukkan ayyukanmu domin mu.
\s5
\v 13 Yahweh Allahnmu, waɗansu shugabanni baya ga kai sun yi mulki a kanmu; amma sunan ka kaɗai muke yabo.
\v 14 Sun mutu, ba za su tsaya ba sun shuɗe, ba za su tashi ba. Hakika, ka zo cikin hukunci, ka hallaka su, ko tunawa da su ba a yi.
\s5
\v 15 Ka sa al'umma ta ƙaru, Yahweh, al'umma ta ƙaru ta wurin ka; ka ɗaukaka, an darjantaka; ka faɗaɗa dukkan iyakokin ƙasar.
\s5
\v 16 Yahweh, a cikin matsala suka dube ka, sai da horon ka ya zo kansu sa'an nan suka yi addu'a.
\v 17 Kamar mace mai juna biyu sa'ad da lokacin haihuwar ta ya yi kusa, tana zafin ciwon naƙuda ta kuma yi kuka gare ka, haka muke a gaban ka, Ubangiji.
\s5
\v 18 Muna da juna biyu, muna cikin naƙuda, amma ya zama kamar mun haifi iska. Ba mu kawo ceto ga duniya ba, kuma mazaunan duniya ba su faɗi ba.
\s5
\v 19 Matattun ka za su rayu; jukkunan su da suka mutu za su tashi. Ku farka ku raira waƙar farinciki, ku mazauna cikin ƙura; gama raɓarku raɓar haske ce, ƙasa kuma za ta fito da matattunta.
\s5
\v 20 Ku tafi ku mutanena, ku shiga ɗakunanku ku rufe ƙofofi; ku ɗan ɓoye kaɗan, har sai hasalar ta wuce.
\v 21 Gama, duba, Yahweh ya kusa fitowa daga wurinsa ya hori mazaunan duniya saboda muguntarsu; ƙasa za ta buɗe zubar da jinin da ta yi, ba zata ƙara ɓoye waɗanda ta kashe ba.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 A wannan rana Yahweh zai hori Lebiyatan macijin nan mai gudu da takobinsa mai girma, mai karfi, mai ban tsoro, Lebiyatan macijin nan mai tafiya a shagide, zai kashe babban dodon ruwa dake cikin teku.
\v 2 A wannan rana: kuringar inabi, ta yi masa waƙa.
\v 3 "Ni, Yahweh, ni ne mai kare shi; zan yi masa banruwa kowanne lokaci. zan yi tsaron sa dare da rana yadda ba wanda zai cuce shi.
\s5
\v 4 Ban ji haushi ba, Oh, dãma akwai sarƙaƙiya da ƙaya! Zan far masu a filin daga in ƙone su tare duka;
\v 5 sai dai idan sun nemi kariyata, sun nemi salama da ni; bari su nemi salama da ni.
\s5
\v 6 A rana mai zuwa, Yakubu zai yi sauya; Isra'ila zaya bunƙasa ya yi fure; su cika sararin ƙasa da 'ya'ya."
\s5
\v 7 Yahweh, ya kaiwa Yakubu da Isra'ila hari kamar yadda ya kaiwa al'umman da suka kai masu hari? An kashe Yakubu da Isra'ila kamar yadda aka kashe al'umman da suka kashe su?
\v 8 Ka yi fama bisa mizanin da ya yi dai-dai, ka sallami Yakubu da Isra'ila suka tafi; ka kore su da iska mai ƙarfi sun tafi, a wannan rana ta iskar gabas.
\s5
\v 9 Haka a wannan rana, za a rufe muguntar Yakubu, wannan shi ne cikakken 'ya'yan kawar da zunubi: sa'ad da zai farfasa duwatsun bagadi ya yi masu gutsu-gutsu kamar alli, ba za a sami sifofin Asheran ko bagadin turarenta a tsaye ba.
\s5
\v 10 Gama birni mai ganuwa ya zama kufai, an watsar da mazauna a ciki an yashe su kamar jeji. A can ɗan maraƙi ya ke kiwo yana cin rassansa.
\v 11 Sa'ad da ƙiraruwan suka bushe, za a kakkarye su. Mataye za su hura wuta da su, gama mutane ne marasa fahimta. Wanda ya yi su ba za ya ji tausayin su ba, shi wanda ya yi su ba za ya nuna masu jinƙai ba.
\s5
\v 12 Rana zata zo inda Yahweh zai yi shiƙa tun daga Kogin Yuferitis har zuwa Wadi ta ƙasar Masar, ku kuma mutanen Isra'ila za a tattaro ku ɗai-ɗai da ɗai-ɗai.
\v 13 A wannan rana za a busa babban ƙaho; lalatattu na ƙasar Asiriya za su zo, da yasassu na ƙasar Masar, cikin Isra'ila za su yi sujada ga Yahweh a kan tsauni mai tsarki cikin Yerusalem.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Kaiton rawanin girman kai na fure da kowanne mashayan Ifraim ke sanye da shi, kyaun darajarsu na dushewa kamar yadda kyaun fure ke dushewa, haka ma rawanin dake kan waɗanda suka bugu da ruwan inabi a Kwari mai tãki, inda ruwan inabi ya rinjayi wasu!
\v 2 Duba, Ubangiji yana aiko da wani babba, kuma ƙaƙƙarfa; kamar hadari mai ƙanƙara, da iska mai lalatarwa, kamar ruwan sama mai kwararowa da ambaliyar ruwaye; zai jefar da kowanne rawanin fure a ƙasa.
\s5
\v 3 Masu rawanin girman kai na fure mashaya na Ifraim za a tattake a ƙarƙashin sawu.
\v 4 Furen ɗaukakarsa mai ƙyau, dake kan kwari mai arziki, zai zama kamar nunannen ɓaure na fãri da damuna, zai zamana, sa'ad da wani ya dube shi, tun yana hannunsa, zai haɗiye su.
\s5
\v 5 A ranar nan Yahweh mai runduna zai zama rawani mai daraja da kambi mai kyau ga sauran mutanensa da suka rage,
\v 6 ruhun adalci ga mahukunta, ƙarfi kuma ga waɗanda suka kori abokan gãba daga ƙofofinsu.
\s5
\v 7 Amma har ma waɗannan suna tangaɗi da ruwan inabi mai ƙarfi. Da firist da annabi suna tangaɗi da ruwa mai ƙarfi, ruwan inabi ya haɗiye su. Suna tangaɗi da ruwan inabi mai ƙarfi, suna tangaɗi a wahayi da rashin sanin abin yi.
\v 8 Hakika duk teburorin sun ƙazantu da haraswa, har ma babu tsabtaccen wuri.
\s5
\v 9 Su waye zai koya wa sani, kuma ga suwa zai fasara saƙon? Ga waɗanda aka yaye daga nono, ko kuma waɗanda a ka cire daga mama?
\v 10 Gama doka ce bisa doka, doka bisa doka; ka'ida bisa ka'ida; nan ɗan-kaɗan can ɗan-kaɗan.
\s5
\v 11 Hakika, da leɓunan ba'a da kuma bãƙon harshe zai yiwa mutanen nan magana.
\v 12 A dã ya ce masu, "Wannan shi ne hutu, a bada hutu ga wanda ya gaji; wannan shi ne wartsakewa ɗin," amma ba za su kasa kunne ba.
\s5
\v 13 Haka maganar Yahweh za ta zama ma su doka bisa doka, doka bisa doka; ka'ida bisa ka'ida, ka'ida bisa ka'ida; nan ɗan kaɗan, can ɗan kaɗan; domin su tafi da baya su faɗi, a karya su, a sa masu tarko, a kama.
\s5
\v 14 Ku saurari maganar Yahweh, ku masu ba'a, ku da ke mulki bisa waɗannan mutane dake Yerusalem.
\v 15 Wannan zai faru domin kun ce, "Mun yi alƙawari da mutuwa, da muka ƙulla yarjejeniya. Saboda haka lokacin da babbar bulala mai bin kan kowa zata ratsa, ba zai iso wurin mu ba. Gama mun mai da ƙarya mafaƙarmu, mun sami mafaka a rumfa cikin ƙarya."
\s5
\v 16 Saboda haka Ubangiji Yahweh yace, "Duba: Zan kafa harsashin dutse a Sihiyona, dutsen da aka jaraba, dutsen kusurwa mai daraja, tabbataccen harsashi, duk wanda ya gaskata ba za ya kunyata ba.
\s5
\v 17 Zan sa gaskiya ta zama sandar gwaji, adalci kuma igiyar awo. Ƙanƙara za ta share mafaƙar ƙarairayi, kuma rigyawa zai sha kan maɓuya.
\s5
\v 18 Za a tada alƙawarin ku da mutuwa, yarjejeniyar da ku ka ƙulla da Lahira za a soke. Sa'ad da rigyawa mai ruri ke wucewa, za a sha kanku.
\v 19 Duk lokacin da za su wuce, za su sha kanku, daga safiya zuwa safiya za su yi ta aukowa, kuma dare da rana za su wuce kuma da rana da dare zai zo. Sa'ad da aka fahimci saƙon, zai sa firgita.
\s5
\v 20 Gama gadon ya gajarce da mutum ya miƙe a bisansa, bargon kuma bashi da fãɗin da zai isa ya rufe kansa."
\v 21 Yahweh zai miƙe kamar a kan Dutsen Ferazim, zai tashi kansa kamar a cikin Kwarin Gibiyan domin ya yi aikinsa, bãƙon aikinsa, ya kuma yi bãƙon aikinsa.
\s5
\v 22 Saboda haka kada ku yi ba'a, domin kada a karfafa sarƙarku. Na ji daga wurin Ubangiji Yahweh mai runduna, dokar hallaka a kan duniya.
\s5
\v 23 Ku natsu ku saurari muryata; ku natsu ku saurari maganganuna.
\v 24 Manomin dake huɗa dukkan rana domin shuka, ya kanyi huɗar ƙasar ne kawai? Zai yi ta huɗa ne kawai yana fasa ƙasa?
\s5
\v 25 Lokacin da ya shirya ƙasar, ba yakan yafa tamba ba, ya warwatsa riɗi, sai ya sa alkama a jere, da bali a inda ya kamata, da kuma wasu irin a gefuffuka?
\v 26 Allahnsa yana gaya masa abin yi; yana koya masa da hikima.
\s5
\v 27 Bugu da ƙari 'ya'yan tamba ba a sussukasu da haƙoran ƙarfe, ba a kuma bin kan riɗi da tayar karusa; amma akan buga tamba da 'gora, riɗi kuma da sanda.
\v 28 Akan niƙa tsaba domin abinci amma bada laushi ba, koda shike ƙafafun kekensa dana dawakansa sukan warwatsar da shi, dawakansa ba sa murƙushesu.
\s5
\v 29 Wannan ma daga Yahweh mai runduna ya ke fitowa, shi kuwa mai al'ajibi ne a cikin bishewa mafifici cikin hikima.
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Kaiton Ariyel, Ariyel birnin da Dauda ya kafa zango! A ƙara shekara kan shekara; bari bukukuwa su kewayo.
\v 2 Amma zan kafa wa Ariyel dãga, zata yi ta makoki da kururuwa; kuma zata zamar mani kamar Ariyel.
\s5
\v 3 Zan kafa dãga gãba dake in kewaye ki, zan yi maki kwanto gãba dake da kuma soro, zan kafa wuraren faƙo gãba dake.
\v 4 Za a jawo ki ƙasa za ki yi magana daga ƙasa; muryarki zata dushe a cikin ƙura. Muryar ki zata zama kamar ta ruhu dake fitowa daga ƙasa, maganar ki kuma zata zama rarrauna daga cikin ƙura.
\s5
\v 5 Yawan masu kawo maki hari za su zama kamar 'yar ƙura, ɗunbin mugayen nan kamar dusa dake wucewa. Zai faru, ba zato ba tsammani, farat ɗaya.
\v 6 Yahweh mai runduna zai zo maki, da tsawa, da raurawar ƙasa, da ƙara mai tsanani, da babbar iska, da gawurtaccen hadari, da harshen wuta mai hallakarwa,
\s5
\v 7 Zai zama kamar mafarki, wahayi da dare: Taron dukkan al'ummai za su yaƙi Ariyel da kagararta. Za su hare ta da ita da garunta domin su matsa mata.
\v 8 Zai zama kamar lokacin da mayunwacin mutum ya ke mafarki yana cin abinci, amma da ya farka, cikininsa ba komai. Zai zama kamar lokacin da wani mutum yana jin kishin ruwa, sai ya yi mafarki yana shan ruwa, amma lokacin da ya farka, yana suma, kishin ruwansa ba a kashe ba. I, haka zai zama ga dukkan al'umman da za su yaƙi Dutsen Sihiyona.
\s5
\v 9 Ku jiwa kanku mamaki, ku kuma yi mamaki; ku makantar da kanku, ku zama makafi! Ku bugu, amma bada ruwan inabi ba, amma bada giya ba.
\v 10 Gama Yahweh ya kwararo maku ruhun barci mai nauwi. Ya rufe maku idanu, ku annabawa, ya lulluɓe kawunanku, masu gani.
\s5
\v 11 Dukkan wahayi ya zamar maku kamar maganganun littafin da a ka kulle, wanda mutane za su ba masani, su ce, "Karanta wannan." Shi kuma zai ce, "Ba zan iya ba gama an kulle."
\v 12 Idan an bada littafin ga wanda bai iya karatu ba, cewa,"Karanta wannan," zai ce, "Ban iya karatu."
\s5
\v 13 Ubangiji yace, "Waɗannnan mutane suna kusatowa gare ni da bakunansu, suna kuma girmamani da leɓunansu, amma zuciyarsu tana nesa da ni. Girman da suke ba ni na dokokin mutane ne da a ka riga a ka koya.
\v 14 Saboda haka, duba, zan ci gaba in yi abin ban mamaki cikin mutanen nan, al'ajibi kan al'ajibi. Hikimar masanansu zata lalace kuma fahimtar masu tattalinsu zasu ɓace."
\s5
\v 15 Kaiton waɗanda suke ɓoye wa Yahweh shirye-shiryensu, waɗanda ayyukansu suke cikin duhu. Suna cewa, "Wa ke ganinmu, wa kuma ya san mu?"
\s5
\v 16 Kuna juya abubuwa na sama zuwa ƙasa! Za a kwatanta mai ginin tukwane kamar yumɓu, har da abin da a ka yi zai ce game da wanda ya yi shi, "Ba shi ya yi ni ba," ko abin da a ka sarrafa ya cewa wanda ya sarrafa shi, "Bai fahimta ba"?
\s5
\v 17 A ɗan lokaci kaɗan, za a maida Lebanon fili, filin kuma zai zama kurmi.
\v 18 A ranar nan kurma zai ji maganganun littafi, idanun makafi kuma za su gani daga cikin duhu baƙiƙƙirin,
\v 19 Waɗanda a ka murƙushe za su sake yin murna a cikin Yahweh, matalauta kuma a cikin mutane za su yi farinciki cikin Mai Tsarkin na Isra'ila.
\s5
\v 20 Gama miyagu za su ƙare, masu ba'a za su ɓace. Za a datse dukkan masu ƙaunar aikata mugunta,
\v 21 waɗanda ta wurin magana su kan maida mutum mai laifi. Suna kafa tarko ga mai neman a yi mashi adalci a ƙofa su kuma kãda mai adalci da holoƙan ƙarairayi.
\s5
\v 22 Saboda haka ga abin da Yahweh ya faɗi game da gidan Yakubu - Yahweh wanda ya fanshi Ibrahim, "Yakubu ba zai ƙara jin kunya ba, ko kuma fuskarsa ta turɓune.
\v 23 Amma sa'ad da zai dubi 'ya'yansa, aikin hannuwana, za su tsarkake sunana. Za su tsarkake sunan Mai Tsarki na Yakubu za su kafu cikin tsoron Allah na Isra'ila.
\v 24 Waɗanda suka ɓata cikin ruhaniya za su sami fahimta, masu gunaguni za su koyi ilimi."
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 "Kaiton 'ya'yan tawaye," wannan ne furcin Yahweh. Suna shirye-shirye, amma ba daga gare ni ba; suna ƙulla yarjejeniya da wasu al'ummai, amma ba Ruhuna ya bishe su ba, saboda haka suna ƙara zunubi kan zunubi.
\v 2 Sun kama hanya su gangara zuwa Masar, amma ba su nemi bishe wa daga gare ni ba. Suna neman kariya daga Fir'auna, sun nemi mafaƙa a inuwar Masar.
\s5
\v 3 Saboda haka kariyar Fir'auna zata zama abin kunyarku, fakewa a inuwar Masar, zai zama ƙasƙancinku,
\v 4 koda shike hakimansu suna Zowan, jakadunsu sun iso Hanes.
\v 5 Dukkansu za su ji kunya domin mutanen da ba za su iya taimakonsu ba, waɗanda ba taimako ba ne ko tallafawa, amma abin kunya ne, har ma abin ƙasƙanci."
\s5
\v 6 Furci game da dabbobin Negeb: Cikin ƙasar wahala da hatsari, da zakanya da kuma zaki, da kububuwa da miciji mai dafi yana shawagi, su kan labta arzikinsu bisa jakkai, da kayayyakinsu masu daraja bisa doron raƙuma, su kaiwa mutanen da ba za su iya taimaka masu ba. Gama taimakon
\v 7 Masar na banza ne; Saboda haka na kirata Rahab, wadda ta zauna shuru.
\s5
\v 8 Yanzu ka tafi, ka rubuta shi a gabansu a kan allo, ka maka shi a kan allon fata, domin a adana shi da kyau saboda lokaci mai zuwa ya zama shaida.
\v 9 Gama mutanen nan 'yan tawaye ne, 'ya'ya maƙaryata, waɗanda ba za su ji umarnin Yahweh ba.
\s5
\v 10 Sukan cewa masu duba, "Kar ku gani," ga kuma annabawa, "Kada ku faɗa mana annabcin gaskiya; ku faɗa mana maganganun wãsawa, annabcin ruɗami,
\v 11 Kun kauce daga hanya, kun saki tafarki; kun sa Mai Tsarkin na Isra'ila ya daina magana a fuskarmu."
\s5
\v 12 Saboda haka Mai Tsarki na Isra'ila yace, "Domin kun ƙi wannan magana, kun dogara ga zilama da ruɗi, kun jingina gare shi,
\v 13 saboda haka wannan zunubi zai zamar maku kamar ɓangaren shashe dake shirin faɗuwa, kamar curi a kan bango mai tsayi wanda faɗuwarsa zata zo nan da nan, farat ɗaya."
\s5
\v 14 Zai fasa shi kamar yadda tukunyar magini ke farfashewa; ba zai ƙyale ta ba, don kada a sami cikin farfasassun koda ɗan kaskon da za a ɗauko ɗan garwashin wuta daga sauran garwashin, ko a kwarfo ruwa daga cikin randa.
\s5
\v 15 Gama wannan shi ne Ubangiji Yahweh, Mai Tsarki na Isra'ila yace, "Cikin komowa da hutu za ku tsira; cikin natsuwa da dogara ƙarfin ku zai tabbata. Amma ba ku yarda ba,
\v 16 Kuka ce, 'A a, za mu gudu a kan dawakai,' haka za ku gudu; kuma, 'Za mu hau kan dawakai masu zafin gudu,' haka masu bin ku za su yi sauri.
\s5
\v 17 Dubu za su gudu a tsoratawar mutum ɗaya; a tsoratawar biyar za ku gudu har sai sauranku da suka rage sun zama kamar sandar tuta a kan tsauni, ko kamar 'yar tuta a kan tudu."
\s5
\v 18 Duk da haka Yahweh yana jira ya yi maku alheri, saboda haka a shirye ya ke ya nuna maku jinƙai. Gama Yahweh Allah ne mai adalci; masu albarka ne dukkan waɗanda suke jiransa.
\v 19 Gama waɗansu mutane za su zauna a cikin Sihiyona, cikinYerusalem, ba za su ƙara yin kuka kuma ba. Hakika zai yi maku alheri da ya ji ƙarar kukan ku. Idan ya ji shi, zai amsa maku.
\s5
\v 20 Koda shike Yahweh yana ba ku gurasar wahala da ruwan matsaloli, haka kuma, malaminku ba zai ƙara ɓoye kansa ba, amma za ku ga malamin ku da idanunku.
\v 21 Kunnuwan ku za su ji magana a bayan ku, cewa, "Wannan ita ce hanya, yi tafiya a cikinta," sa'ad da kuka juya zuwa dama ko kuka juya zuwa hagu.
\s5
\v 22 Za ku tozartar da sassaƙaƙƙun siffofin ku da a ka dalaye da azurfa da kuma sarrafaffun siffofinku na zinariya. Za ku zubar da su kamar ƙazamtattun tsunmokaran al'ada. Za ku ce masu, "Ku fita daga nan."
\s5
\v 23 Zai bada ruwan sama domin iri lokacin da kuka yi shuka a ƙasa, da gurasa tare da yalwa daga ƙasa, amfani kuma zai zama da yawa. A ranar nan shanunku za su yi kiwo a makiyaya mai fãɗi.
\v 24 Shanun noma da jakkai, da suke huɗa, za su ci gyararren abinci wanda aka sheƙe da cebur da matankaɗi.
\s5
\v 25 Bisa kowanne dogon tsauni, da bisa kowanne dogon tudu, za a sami maɓuɓɓugai da rafuka masu gudanar da ruwa, a ranar gawurtaccen kisa sa'ad da hasumiyoyi za su faɗi.
\v 26 Hasken wata zai zama kamar hasken rana, hasken rana zai ninka sau bakwai, kamar hasken kwana bakwai. Yahweh zai ɗaure karayar mutanensa ya warkar da ƙujewar raunin da ya yi masu.
\s5
\v 27 Duba, sunan Yahweh ya zo daga wuri mai nisa, yana ƙũna da fushinsa kuma a cikin turmuƙin hayaƙi. Leɓunansa suna cike da zafi, harshensa kuma na kama da wuta mai cinyewa.
\v 28 Numfashinsa yana kama da ambaliya wanda ruwansa ya kai har tsakiyar wuya, domin ya rairaye al'ummai da matankaɗin hallakarwa. Numfashinsa linzami ne a muƙamuƙan mutane yasa su warwatse.
\s5
\v 29 Za ku sami waƙa da dare sa'ad da kuke biki mai tsarki, da murna a zuciya, kamar yadda wani zai tafi da sarewa bisa tsaunin Yahweh, zuwa ga Dutsen Isra'ila.
\s5
\v 30 Yahweh zai sa aji muryarsa mai daraja, ya nuna motsin hannunsa cikin zafin fushinsa da harshen wuta, tare da guguwa, hadari, da ƙanƙara.
\s5
\v 31 Gama da jin muryar Yahweh, Asiriyawa za su razana; zai fyaɗe su da sanda.
\v 32 Kowanne dukkan sanda da Yahweh ya ƙaddara masu za a bi bayansa da waƙoƙin tambura da molo sa'ad da ya ke yaƙi da faɗa da su.
\s5
\v 33 Domin an shirya wurin ƙũna tuntuni. Hakika, an shirya shi domin sarki, Allah ya shirya shi da zurfi da kuma faɗi. Tarin kuwa a shirye ne da wuta da kuma itace da yawa. Numfashin Yahweh, kamar rafin ƙibiritu ne da zai cinna masa wuta.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Kaiton waɗanda suke gangarawa zuwa Masar domin neman gudummuwa suna jingina ga dawakai, suna dogara ga karusai, (domin suna da yawa), da kuma mahayan dawakai (domin sun zarce ƙididdiga). Amma ba su damu da Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su kuma neman Yahweh!
\v 2 Duk da haka yana da hikima, zai kuwa kawo masifa ba zai janye maganarsa ba. Zai tashi gãba da gidan mugunta, gãba kuma da kai gudummuwa ga masu aikata zunubi.
\s5
\v 3 Masar mutum ne ba Allah ba, dawakansu kuma jiki ne ba ruhu ba. Lokacin da Yahweh zai miƙar da hannunsa, dukka da wanda ya yi gudummuwar zai yi tuntuɓe, wanda kuma a ka yiwa gudummuwar zai faɗi; su biyun za su hallaka tare.
\s5
\v 4 Ga abin da Yahweh yace mani, "Kamar yadda zaki, har ma ɗan zaki ya kan yi ruri a kan dabbar da ya kashe, sa'ad da a ka kira ƙungiyar makiyaya a kansa, amma ba ya rawar jiki saboda muryoyinsu, ko ya sulale domin ƙararsu; haka Yahweh mai runduna zai sauko ya yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona, a kan tudun nan.
\s5
\v 5 Kamar tsuntsaye masu shawagi bisa sheƙarsu, haka Yahweh mai runduna zai tsare Yerusalem; zai tsare ya kuma cece ta sa'ad da ya ke wuce wa bisanta ya kare ta.
\v 6 Ki komo wurinsa shi wanda kika juya nesa daga gare shi, mutanen Isra'ila.
\v 7 Domin a cikin wannan rana kowanne zai jefar da gumakansa na azurfa da gumakansa na zinariya wanɗanda hannuwanku ne cikin zunubi suka yi su.
\s5
\v 8 Asiriya zata faɗi da kaifin takobi, takobin da ba mutum ne ya ke wurgawa ba zata hallaka shi. Zai gujewa takobi, matasanta za su yi aikin tilas.
\v 9 Za su karai saboda razana, sarakunansu za su tsorata idan sun ga tutar yaƙin Yahweh - wannan furcin Yahweh ne - wanda wutarsa ke cikin Sihiyona, tanderun wutarsa kuma tana cikin Yerusalem.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Duba, wani sarki zai yi sarauta cikin adalci, yarimai kuma za su yi mulki da gaskiya.
\v 2 Kowanne ɗayansu zai zama kamar wurin faƙewa daga iska da kuma mafaka daga hadari, kamar rafukan ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa, kamar inuwar babban dutse a ƙasar gajiya.
\v 3 Sa'an nan idanun waɗanda suke gani ba za su dushe ba, kuma kunnuwan waɗanda suke ji za su ji sarai.
\s5
\v 4 Mai saurin baki zai yi tunani da kyau tare da ganewa, mai nauyin baki kuma zai yi magana da kyau da sauƙi kuma.
\v 5 Ba za a ƙara kiran wawa nagari ba, ko a ce da mayaudari mai aminci.
\v 6 Domin wawa yakan faɗi wauta, zuciyarsa takan shirya mugunta da mugayen ayyuka, yana kuma faɗar ƙarya akan Yahweh. Yakan tsiyatar da mayunwata, masu jin ƙishirwa kuma ya sa su rasa abin sha.
\s5
\v 7 Dabarun mayaudari mugaye ne. Yakan ƙago mugayen shirye-shirye, domin ya lalatar da matalauta da ƙarairayinsa, koda matalaucin ya faɗi abin dake dai-dai.
\v 8 Amma nagarin mutum yakan yi shiri nagari; kuma saboda nagargarun ayyukansa zai tsaya.
\s5
\v 9 Ku tashi, ku matan dake zaman sake, ku saurari murya ta; ku 'ya'ya mata 'yan ba ruwanmu, ku saurare ni.
\v 10 Gama nan gaba kaɗan da shekara guda ƙarfin halinku za a karya, ku mata masu zaman sake, gama ba za a sami girbin inabi ba, kuma ba amfanin da za a tattara a rumbuna.
\s5
\v 11 Ku yi rawar jiki don tsoro, ku mata masu zaman sake; ku yi damuwa, ku masu ƙarfin hali; ku tuɓe ƙyawawan tufafinku, ku tsirance kanku; ku ɗaura tsummokin makoki a kwankwasonku.
\v 12 Za kuyi kururuwa domin gonakinku masu yalwa, da inabinku masu 'ya'ya.
\v 13 Ƙasar mutanena zata cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya, har ma a cikin dukkan gidaje da aka taɓa yin farinciki a birnin bukukuwa.
\s5
\v 14 Gama za a yasar da fãda, birnin mai cincirindon mutane zai koma kango; da tudu da benen tsaro za su zama kogonni har abada, abin murna ga jakan jeji, wurin kiwo domin garkuna;
\v 15 har sai an kwararo Ruhu a kanmu daga bisa, jeji kuma ya zama gonaki masu bada amfani, gonaki masu bada amfani kuma su zama kamar kurmi.
\s5
\v 16 Sa'an nan hukunci za ya kasance a jeji; adalci kuma ya kasance a gonaki masu amfani.
\v 17 Aikin adalci zai zama salama; sakamakon adalci, kwanciyar hankali da gabagaɗi har abada.
\v 18 Mutanena za su zauna a cikin mazauni na salama, a cikin tsararrun gidaje, da natsattsun wuraren hutawa.
\s5
\v 19 Amma koda an yi ƙanƙara ko kuma jeji duk ya ƙone, aka kuma rushe birnin gaba ɗaya,
\v 20 ku da kuka yi shuka a bakin rafuffuka za a albarkace ku, da dukkan ku da kuke aika shanunku da jakai su yi kiwo.
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Kaiton ka, mai ɓatawa ba a ɓata ka ba! Kaiton ka mai cin amanar waɗanda ba su ci amanarka ba! Lokacin da ka bar ɓatawa, za a ɓata ka. Lokacin da ka daina cin amana, za a ci amanar ka.
\s5
\v 2 Yahweh, ka yi mana alheri; muna jiranka; ka zama damtsenmu kowacce safiya, cetonmu kuma a lokacin wahala.
\s5
\v 3 Da jin ƙararka mai amo mutanen suka gudu; lokacin da ka tashi, al'ummai sai su watse.
\v 4 Akan tara ganimarka kamar yadda fãri ke taruwa, kamar yadda fãri ke tsalle haka mutane ke tsalle a kanta.
\s5
\v 5 Daukaka ga Yahweh, yana zaune a mafificin wuri. Zai cika Sihiyona da gaskiya da adalci.
\v 6 Shi zai zama kafuwarmu a lokatanki, ceto a yalwace, hikima, da ilimi; da tsoron Yahweh shi ne dukiya mai tamani.
\s5
\v 7 Duba, manzannin suna kuka a tituna; 'Jakadun masu begen salama, suna kuka mai zafi.
\v 8 An yasar da karabku; ba bu sauran matafiya. Ana ta tada alƙawari, an wofintar da shaidu, kuma ba nuna bangirma ga ɗan adam.
\s5
\v 9 Ƙasar tana makoki, duk ta yi yaushi; Lebanon ta kunyata ta kuma yi yaushi; Sharon kamar ƙasar filin hamada take; Bashan kuma da Kamel sun kakkaɓe ganyayensu.
\s5
\v 10 "Yanzu ne zan tashi," inji Yahweh; "Yanzu ne za a ɗagani sama; yanzu za a fifita ni.
\v 11 Kun ɗauki cikin ƙai-ƙai, kun haifi ciyawa; numfashinku wuta ce da zata cinye ku.
\v 12 Mutanen za a ƙona su su zama danƙo, kamar yadda a ke sassare sarƙaƙƙiya a ƙone ta.
\s5
\v 13 Ku da kuke nesa, ku ji abin da na yi; kuma ku da ke kusa, ku shaidi ƙarfina."
\v 14 Masu zunubi a Sihiyona sun tsorata; makyarkyata ta kama marasa tsoron Allah. Wane ne a cikin mu zai iya zama da wuta mai ruruwa? Wane ne a cikin mu zai iya zaunawa da madawwamin ƙone-ƙone?
\s5
\v 15 Shi wanda ya ke tafiya bisa adalci yana magana da gaskiya; wanda ke ƙin ribar zilama, yana ƙin karɓar toshi, ba ya shirye-shiryen ta'addanci; ba ya duban mugunta -
\v 16 zai kafa gidansa a kan tuddai; Mafaƙarsa zai zama kagarar duwatsu; zai dinga samun abincinsa da ruwan shansa a kan kari.
\s5
\v 17 Idanunku za su ga sarki cikin jamalinsa; za su ga babbar ƙasa.
\v 18 Zuciyarka zata tuna da razanar da ta faru; ina magatakarda, ina mai auna kuɗi? Ina ya ke mai ƙididdiga hasumiyoyi?
\v 19 Ba za ku ƙara ganin mutanen nan masu tawaye ba, mutane masu baƙon harshe, waɗanda ba ku fahimce su ba.
\s5
\v 20 Dubi Sihiyona, birnin bukukuwanmu; idanunku za su ga Yerusalem kamar mazauni mai lafiya, rumfar da ba za a kawas ba, ƙusoshin ta ba za a tumbuƙe su ba, kuma igiyoyinta ba za a katse su ba.
\v 21 Maimakon haka, Yahweh cikin daraja zai kasance tare damu, a wuri mai manyan koguna da rafuffuka. Ba jirgin ruwan yaƙi da zai bi ta cikinsa, ba kuma manyan jiragen da za su bi ta wurin.
\s5
\v 22 Domin Yahweh ne alƙalinmu, Yahweh ne mai bamu shari'a; Yahweh ne sarkinmu; shi zai cece mu.
\s5
\v 23 An kwance maɗaurinka, ba za su iya riƙe tirken tutar jirgin ruwa da ƙarfi ba; ba za su iya baza tutar jirgin ruwa ba; sa'ad da za a raba babbar ganima, har gurgu ma zai sami rabo.
\v 24 Mazaunan wurin ba za su ce, "Ba ni da lafiya ba," mutanen dake zaune a can za a gafarta zunubansu.
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Ku matso kusa, ku al'ummai, ku saurara; ku natsu, ku mutane! Duniya da dukkan cikarta dole su saurara, duniya, da dukkan abin da ke fitowa a cikinta.
\v 2 Gama Yahweh yana fushi da dukkan al'ummai, da hasala ga dukkan rundunar yaƙin su; ya hallakar da su gaba ɗaya, ya bashe su ga yanka.
\s5
\v 3 Za a jefar da gawawwakin matattunsu waje. Warin gawawwakin su zai bazu ko'ina; duwatsu kuma za su shanye jininsu.
\v 4 Dukkan taurarin sama za su dushe, za a naɗe sammai kamar naɗaɗɗen littafi; dukkan taurarinsu za su dushe, kamar yadda ganyayen inabi suke karkaɗewa su faɗi daga itacen, kuma kamar yadda nunannun ɓaure ke faɗuwa daga jikin itacensa.
\s5
\v 5 Sa'ad da takobina ya sha ya ƙoshi a sama; duba, yanzu zai gangara a kan Idom, akan mutanen da na keɓe domin hallakarwa.
\v 6 Takobin Yahweh na ɗiɗɗigar da jini da kitse, tana ɗiɗɗigar da jinin 'yan raguna da na awaki, rufe da kitsen ƙodojin raguna. Gama Yahweh yana da hadaya a Bozra da kuma babban yanka a ƙasar Idom.
\s5
\v 7 Za a kashe bijiman jeji tare da su, ƙananan bijimai tare da manyansu. Ƙasarsu za ta bugu da jini, ƙurarsu za ta yi ƙiba da kitse.
\s5
\v 8 Gama zata zama ranar sãkayya ga Yahweh da shekarar kuma da zai sãka masu sabili da Sihiyona.
\v 9 Kogunan Idom za a mai da su baƙin danƙo, ƙurarta kuma ta zama ƙibiritu, ƙasarta kuma ta zama baƙin danƙo mai cin wuta.
\v 10 Zata ci wuta dare da rana; hayaƙinta zai tashi sama har abada; daga tsara zuwa tsara zata zama yasasshiyar ƙasa; ba wanda zai ratsa ta tsakiyarta har abada abadin.
\s5
\v 11 Tsuntsaye jeji da dabbobi za su zauna a wurin; mujiya da hankaka za su yi sheƙar su a cikin ta. Kamar yadda mai gini ya ke amfani da igiyar gwaji haka zai auna ƙasar domin rusarwa da hallakarwa.
\v 12 Ba za a bar wa shugabaninta komai da za su kira masarauta ba, kuma dukkan hakimanta ba za su zama komai ba.
\s5
\v 13 Ƙayayuwa za su cika fãdodinta, tsidau da dundu a wuraren tsaronta. Zai zama mazaunin diloli, farfajiyar jiminai.
\v 14 Dabbobin jeji da kuraye za su tattaru a can, awakan jeji za su kira junansu da kuka. Dabbobin jeji masu yawon dare za su tare a nan su kuma samar wa kansu wurin hutawa.
\v 15 Mujiyoyi za su yi sheƙa, za su nasa ƙwayayensu su ƙyanƙyashe, su ƙyanƙyashe su kuma tsare 'yan ƙananansu. I, a can hankaki za su taru, kowanensu da abokin tarayyarsa.
\s5
\v 16 Ku binciko daga naɗaɗɗen littafin Yahweh; ba ko ɗayansu da za a rasa. Ba wanda zai rasa ɗan'uwan tarayyarsa; gama bakinsa ya umarta shi, ruhunsa kuma ya tattara su.
\v 17 Ya jefa ƙuri'a domin mazaunansu, hannunsa kuwa ya auna masu shi da igiya. Za su mallaketa har abada; daga tsara zuwa tsara za su zauna a can.
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Jeji da Hamada za su yi farin ciki; hamada kuma za ta yi murna ta faso da fure. Kamar tsire-tsire,
\v 2 zata faso da furanni ainun ta yi murna da farin ciki da waƙa; za a ba shi darajar Lebanon, da kuma ɗaukakar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Yahweh, mafificiyar ɗaukakar Allahnmu.
\s5
\v 3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku tsaida gwiwoyin masu kaɗuwa.
\v 4 Ku ce wa matsorata, "Ku ƙarfafa, kada ku ji tsoro! Duba, Allahnku zai zo da ramako, da kuma sakamakon Allah. Zai zo kuwa ya cece ku."
\s5
\v 5 Sa'an nan idanun makafi za su gani, kunnuwan kurame kuma za su ji.
\v 6 Sa'an nan gurgu zai yi tsalle kamar barewa, bebe zai raira waƙa, gama ruwa zai malalo daga cikin Hamada, koguna kuma cikin jeji.
\v 7 Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙasa mai ƙishin ruwa kuma zata zama maɓuɓɓugar ruwa; a mazaunin diloli, inda dă suka kwanta, za a tarar da ciyawa da iwa.
\s5
\v 8 Wata karafka zata kasance a wurin ana kiran ta Hanya Mai Tsarki. Marar tsarki ba zai bi ta kanta ba. Amma zata kasance domin wanda ya yi tafiya a cikinta. Ba wawan da zai bi ta kanta.
\v 9 Ba zakin da zai kasance a wurin, ba wata muguwar dabba da zata kasance a kanta; ba za a same su ba a can, amma fansassu ne za su yi tafiya a can.
\s5
\v 10 Baratattun Yahweh za su komo za su taho suna waƙa zuwa Sihiyona, madawwamin farinciki zai kasance a kansu; murna da farinciki za su mamaye su; baƙinciki da ajiyar zuciya za su shuɗe.
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 A shekara ta goma sha huɗu ta sarki Hezekiya, Senakerib sarkin Asiriya, ya tasar wa dukkan biranen Yahuda da kagararsu ya kuma kame su.
\v 2 Sai sarkin Asiriya ya aika da babban shugaban soja daga Lakish zuwa Yerusalem ga sarki Hezekiya tare da babban soja. Ya gabaci dai-dai magudanar kwarin da ya ke kawo ruwa, a babbar hanyar filin da masu wankin tufafi suka tsaya a kanta.
\v 3 Shugabannin Isra'ilawa waɗanda suka fito wajen birnin su yi magana da su su ne Hilkiya ɗan Iliyakim, shugaba mai kula da fãda, Shebna sakataren sarki, da Yowa ɗan Asaf, wanda ke rubuta matakan gwamnati.
\s5
\v 4 Sai shugaban sojoji yace da su, "Ku faɗawa Hezekiya babban sarki, sarkin Asiriya, yace, 'Me kake dogara da shi?
\v 5 Ka na maganganun wofi marar amfani, cewa akwai shawara da ƙarfin yaƙi. To yanzu ga wa kake dogara? Wane ne ya baka ƙarfin zuciya da za ka yi mani tawaye?
\s5
\v 6 Duba, kana dogora da Masar, da tsabgar da kake amfani da ita a matsayin sandar tafiya, amma duk mutumin da ya dogara da ita, zai karye ya soke hannunsa. Wannan shi ne Fir'auna sarkin Masar zai yiwa dukkan wanda ya dogara gare shi.
\v 7 Amma idan ka ce da ni, "Mu na dogara ga Yahweh Allahnmu," ba shi ne wanda ya ke a manyan wurare da bagadai Hezekiya ya ɗauke, ya kuma ce Yahuda da Yerusalem, '"Dole ku yi sujada a wannan bagadi a Yerusalem ba"?
\s5
\v 8 Saboda haka yanzu, zan ba ka abu mai kyau daga maigidana sarkin Asiriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, idan har za ka iya samin masu hawansu.
\s5
\v 9 Ya ya zaka iya kaucewa ko ɗaya daga cikin barorin shugabana? Kana sa dogara ga karusai da mahaya dawakai na Masar!
\v 10 To yanzu, na tafi can ba tare da Yahweh ba in tasar wa wannan ƙasar, har in lalatar da ita? Yahweh yace da ni, "Ka faɗawa wannan ƙasar har ka lalatar da ita.'""
\s5
\v 11 Sa'an nan Iliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce da babban shugaba, "Ka yi magana da barorinka a cikin harshen Aremiyanci, Aremaik, domin muna gane shi. Kada ka yi magana da mu da harshen Yahuda a kunnuwan mutane waɗanda suke a kan garu."
\v 12 Amma babban kwamanda ya ce, "Babban sarki ya aiko ni ga shugabanku kuma ya faɗi waɗannan maganganu? Ba ya aiko ni ga jama'ar da suke a kan garu ba, waɗanda za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu tare da ku ba?"
\s5
\v 13 Sai shugaban sojoji ya tsaya ya tada murya da ƙarfi a cikin Yahudanci, cewa, "Ku saurari magana daga babban sarki, sarkin Asiriya.
\v 14 Sarki yace, 'Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, shi ba zai iya cetonku ba.
\v 15 Kada kuma ku bari Hezekiya ya saku ku dogara ga Yahweh, cewa, '"Yahweh zai tabbatar da cetonku; wannan birni ba za a bada shi a hannun sarkin Asiriya ba.'"
\s5
\v 16 Kada ku saurari Hezekiya, domin wannan shi ne abin da sarkin Asiriya yace: 'Ku nemi salama tare da ni kuma ku fito wuri na. Sai kowannenku ya ci daga cikin 'ya'yan inabin gonarsa, daga kuma itacen ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga rijiyon kansa.
\v 17 Za ku yi wannan har saina zo na ɗauke ku zuwa wata ƙasa mai kama da irin ta ku, ƙasa mai hatsi da sabuwar inabi, ƙasa ta gurasa da kuringar inabi.'
\s5
\v 18 Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, cewa, 'Yahweh zai kuɓutar da ku.' Ko akwai wasu allolin mutanen da suka cece su daga hannun sarkin Asiriya?
\v 19 Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarwayim? Sun ceci Samariya daga ikona?
\v 20 A cikin dukkan allolin waɗannan ƙasashe, akwai wani da ya ceci ƙasarsa daga ikona, ya ya kuke ganin kamar Yahweh zai ceci Yerusalem daga ikona?
\s5
\v 21 Amma mutane suka tsaya tsit ba bu kuma wanda ya maida martani, don umarnin sarki, "Kada ku amsa masa."
\v 22 Sai Iliyakim ɗan Hilkiya, wanda ya ke bisa iyalin, Shebna marubuci, da Yowa ɗan Asaf mai kula da tarihi, suka zo wurin Hezekiya da tufaffinsu a kekkece, kuma suka faɗa masa maganganun da shugaban mayaƙa ya faɗa.
\s5
\c 37
\cl Sura 37
\p
\v 1 Ya zamana a lokacin da sarki Hezekiya ya ji abin da suka faɗa, ya kekkece tufafinsa, ya rufe jikinsa da tsummoki, ya kuma shiga gidan Yahweh.
\v 2 Ya aika Iliyakim, mai kula da fada, da Shebna marubucin shari'a, da dattawa firistoci, dukkansu suka rufe jikinsu da tsummoki, zuwa wurin Ishaya ɗan Amoz, annabi.
\s5
\v 3 Suka ce da shi, "Hezekiya yace, 'Wannan rana ce ranar wahala da wulaƙanci da kunya, mun zama kamar lokacin da za a haifi yaro, amma uwar ba ta da ƙarfin da zata haifi yaron.
\v 4 Watakila Yahweh Allahnka zai ji maganganun shugaban mayaƙansa, wanda sarkin Asiriya uban gidansa ya aiko domin ya wulaƙanta Allah mai rai, ya kuma tsawata wa maganganu waɗanda Yahweh Allahnka ya ji. Yanzu sai ka yi addu'a domin ringin da har yanzu suna nan.'"
\s5
\v 5 Sa'ad da barorin sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,
\v 6 sai Ishaya yace da su, "Ku faɗawa ubangidanku: 'Yahweh yace, "Kada ku ji tsoron irin maganganun da kuka ji, waɗanda dasu barorin sarkin Asiriya suka wulaƙanta ni.
\v 7 Duba, zan sa ruhu a cikinsa, zai kuma ji jita-jitar da zata sa ya koma ƙasarsa. Zan sa shi ya faɗi ƙasa da takobi a cikin ƙasarsa.'"'
\s5
\v 8 Sai shugaban mayaƙan ya koma ya kuma sami sarkin Asiriya yana yaƙi da Libna, domin ya ji sarki ya tafi daga Lakish.
\v 9 Sa'ad da Senakerib ya ji Tirhaka sarkin Kush da Masar sun haɗu domin su yi yaƙi da shi, sai kuma ya aika da manzanni zuwa wurin Hezekiya tare da saƙo:
\v 10 "Ka ce da Hezekiya, sarkin Yahuda, 'Kada ka bari Allahnka wanda kake dogara da shi ya ruɗe ka, cewa, 'Yerusalem ba zata faɗa hannun sarkin Asiriya ba."
\s5
\v 11 Ku gani, ku kuma ji abubuwan da sarakunan Asiriya suka yiwa dukkan ƙasashe ta wurin lalata su ga baki ɗaya. Kuna tsammani za ku kuɓuta?
\v 12 Ko allolin al'ummai sun kuɓutar da su, al'umman da ubannina suka lalata akwai Gozan, da Haran, Rezef, da kuma mutanen Iden a Tel-assa?
\v 13 Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin biranen Sefarwayim, da Hena, da kuma Iwwa?'"
\s5
\v 14 Hezekiya ya karɓi wannan wasiƙar daga hannun manzannin ya kuma karanta ta. Sai ya shiga gidan Yahweh ya baza ta gabansa.
\v 15 Hezekiya ya yi addu'a ga Yahweh:
\v 16 "Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, kai da ka zauna a sama da kerubim, kai kaɗai ne Allah a kan dukkan mulkokin duniya. Kai ka yi sammai da duniya.
\s5
\v 17 Ka juyo da kunnuwanka, Yahweh, ka ji mu. Buɗe idanuwanka, Yahweh, ka gani, ka kuma ji maganar Senakerib, wanda ya aika don ya yi ba'a ga Allah mai rai.
\v 18 I' gaskiya ne, Yahweh, sarakunan Asiriya sun lalata dukkan al'ummai da ƙasashensu.
\s5
\v 19 Suka sa allolinsu a cikin wuta, domin su ba alloli ba ne amma ayyukan hannunwan mutane ne, itace da dutse ne kawai.
\v 20 Saboda haka Asiriyawa sun lalata su. Yanzu dai, Yahweh Allahnmu, ka cece mu daga ikonsa, saboda dukkan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Yahweh."
\s5
\v 21 Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wurin Hezekiya, cewa, "Yahweh, Allah na Israila yace, 'Domin ka yi addu'a gare ni a kan Senakerib sarkin Asiriya,
\v 22 wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗa a kansa: "Akwai budurwar yariya ta Sihiyona ta rena ka kuma tana yi maka dariyar ba'a; budurwar Yerusalem tana girgiza kanta gare ka.
\v 23 Wa ka rena ka kuma ci mutunci sa? Gãba da wa ka ɗaga muryarka, ka kuma ɗaga idanuwanka na girmankai? Gãba da Mai Tsarki na Isra'ila.
\s5
\v 24 Ta wurin barorinka ka rena Ubangiji ka kuma ce, 'Da yawan karusaina har na kai ƙololuwar duwatsu, zuwa tsayin Lebanon. Zan sare dogayen itatuwan sida dana sifuros zaɓuɓɓu, na kuma kai wurare mafi nisa, na jeji mafi 'ya'ya.
\v 25 Na gina rijiyoyi na kuma sha ruwa; Na busar da dukkan kogunan Masar ƙarƙashin sawayena.'
\s5
\v 26 Baka ji yadda na ƙudura a yi haka tuntuni kuma na aiwatar tun zamanin ḍã? Yanzu ne nake cikawa. Kana nan ne domin ka mai da birane gagara-shiga zuwa tulin kango.
\v 27 Mazaunan su, masu ƙaramin ƙarfi, sun warwatse da kunya. Sun zama tsire-tsire a gona, ɗanyar ciyawa, ciyawar dake kan rufi ko a fili, kafin iskar gabas.
\s5
\v 28 Amma na san zaman ka, da fitar ka, da kuma zuwan ka, na san yadda ka harzuƙa gãba da ni.
\v 29 Domin harzuƙar ka ta gãba da ni, kuma don girmankanka ya iso kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka, linzami na kuma a bakinka; zan komar da kai hanyar da ka biyo."
\s5
\v 30 Wannan ita ce zata zama alama domin ka: A wannan shekara zaku ci gyauro, a kuma shekara ta biyu zaku shuka daga abin da ya tsiro daga gauron. Amma a shekara ta uku dole zaku yi shuka ku kuma girɓe shi, ku dasa kuringar inabi ku kuma ci 'ya'yanta.
\s5
\v 31 Su da suke ringi na gidan Yahuda da waɗanda kuma suka tsira za su sake kafuwa su haifi 'ya'ya.
\v 32 Domin daga Yerusalem ringin za su fito; daga Dutsen Sihiyona waɗanda suka tsira za su zo. Himmar Yahweh mai runduna zai yi wannan.'"
\s5
\v 33 Saboda Yahweh ya faɗi wannan a kan sarkin Asiriya: "Ba zai shiga wannan birnin ba kuma ba zai harba kibiya a nan ba. Ba zai zo gare shi ba tare da garkuwa ko ya kafa sansanin tudu gãba da ita.
\v 34 Ta hanyar da ya zo ta hanyar kuma zai koma; ba zai shiga wannan birni ba - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 35 Zan kare wannan birnin zan kuma ceto shi, domin ni kaina da kuma bawa na Dauda."
\s5
\v 36 Sai mala'ikan Yahweh ya fito ya fãɗa wa sansanin Asiriyawa, ya kashe sojoji 185,000. Da mutanen suka tashi da sassafe, sai suka ga jukunan matattu a kwakkwance ko'ina.
\v 37 Senakerib sarkin Asiriya ya ƙyale Isra'ila ya koma gida ya zauna a Nineba.
\s5
\v 38 Daga bisani, yayin da ya ke sujada a gidan Nisrok allahnsa, 'ya'yansa Adramelek da Shareza suka kashe shi da takobi. Sai suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Isahadon ɗansa ya yi sarauta a matsayinsa.
\s5
\c 38
\cl Sura 38
\p
\v 1 A kwanakin da Hezekiya ya ke ciwo har ya kusa mutuwa. Sai Ishaya ɗan Amoz, annabi, ya zo wurinsa, ya ce masa, "Yahweh yace, 'Ka kintsa komai dai-dai a gidanka; gama mutuwa za ka yi, ba za ka rayu ba,'"
\v 2 Sai Hezekiya ya juya ya sa fuskarsa a bango ya yi addu'a ga Yahweh.
\v 3 Ya ce, "Idan ka yarda Yahweh, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da dukkan zuciyata da aminci, yadda na yi abin da ke dai-dai a idanunka." Sai Hezekiya ya yi kuka da ƙarfi.
\s5
\v 4 Sai maganar Yahweh ta zo wurin Ishaya, cewa,
\v 5 "Tafi ka ce da Hezekiya, shugaban mutanena, 'Wannan shi ne abin da Yahweh, Allah na Dauda kakanka, ya ce: Na ji addu'arka, na kuma ga hawayenka. Duba, ina shirin ƙara maka shekaru goma sha biyar nan gaba.
\v 6 Daga nan zan cece ka da wannan birnin daga hannun sarkin Asiriya, kuma zan kãre wannan birni.
\s5
\v 7 Wannan zai zama alama a gare ka daga Yahweh, zan yi abin da na alƙawarta.
\v 8 Duba, zan komar da inuwa baya da taki goma na hawan benen Ahaz. Saboda haka inuwa ta koma baya da taki goma a kan hawan benen inda ta yi gaba.
\s5
\v 9 Wannan ita ce rubutacciyar addu'ar Hezekiya sarkin Yahuda, lokacin da ya ke rashin lafiya daga nan kuma ya warke:
\v 10 "Na ce tsakanin ƙarshen rayuwata zan koma daga ƙofofin Lahira; zan ƙarashe sauran shekaru a can.
\v 11 Na ce ba zan ƙara ganin Yahweh, Yahweh a cikin ƙasar rayayyu ba; ba kuma zan ƙara duban wani mutum ko mazaunan duniya ba.
\s5
\v 12 An datse raina an kuma tafi da shi daga gare ni kamar rumfar makiyayin tumaki; na naɗe raina kamar gado; kana sare ni daga masaƙa; tsakanin rana da dare zaka ƙarar da raina.
\v 13 Na yi ta kuka har gari ya waye; kamar zaki yana kakkarya dukkan ƙasussuwana. Tsakanin rana da dare kana ƙarashe raina.
\s5
\v 14 Kamar muryar ƙaramin tsuntsu; na yi kuka kamar kurciya; idanuna sun gaji don dubar sama. Ubangiji, an matsa mani; ka taimake ni.
\v 15 Me zan iya faɗa? Ya yi magana da ni, ya yi haka, zan yi tafiya a hankali dukkan shekaruna sabili da baƙinciki ya rinjaye ni.
\s5
\v 16 Ubangiji, wahalolin daka aiko suna da kyau a gare ni; ka dawo mani da raina; ka maido mani da raina da kuma lafiyata.
\v 17 Domin amfani na ne na ji irin wannan baƙincikin. Ka cece ni daga kududufin hallaka; domin ka jefar da dukkan zunubaina bayanka.
\s5
\v 18 Gama Lahira ba ta yi maka godiya; mutuwa ba ta yabonka; waɗanda suka tafi can cikin rami ba za su bege cikin amincinka ba.
\v 19 Mutum mai rai, mutum mai rai, shi ne zai iya yi maka godiya, kamar yadda na ke yi a wannan rana, uba yana bayyanawa 'ya'ya irin amincinka.
\s5
\v 20 Yahweh yana kusa da ceto na, za mu kuma yi buki tare da kaɗe-kaɗe da waƙoƙi dukkan ƙwanakin ranmu cikin gidan Yahweh."
\s5
\v 21 Yanzu Ishaya yace, "Bari su ɗauki 'ya'yan ɓaure su cura a kuma sa shi akan marurun, zai kuma warke."
\v 22 Hezekiya kuma ya ce, "Me zai zama alama da yasa zan iya zuwa gidan Yahweh?"
\s5
\c 39
\cl Sura 39
\p
\v 1 A wannan lokacin sai Maduk-Baladan ɗan Baladan, sarkin Babila, ya aika da wasiƙu tare da kyauta ga Hezekiya; domin ya ji cewa Hezekiya ya yi ciwo ya kuma sami lafiya.
\v 2 Hezekiya kuwa ya ji daɗin waɗannan abubuwa; har ya kuma nuna wa manzannin ɗakin dukiyarsa - wato su azurfa, da zinariya, da kayan yaji, da mai mai daraja, da daƙin kayayyakinsa na yaƙi, da dukkan abin da ke cikin gidansa. Babu sauran wani abu da ya ke da shi a gidansa, ko cikin dukkan mulkinsa, wanda Hezekiya bai nuna masu ba.
\s5
\v 3 Sai Ishaya annabi ya zo wurin sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi, "Me waɗannan mutane suka ce da kai? Daga ina suka zo?" Hezekiya yace, "Sun zo wuri na daga ƙasa mai nisa ta Babila."
\v 4 Ishaya ya yi tambaya, "Me suka gani a gidanka?" Hezekiya ya amsa, "Sun ga dukkan abin da ya ke a gidana. Babu wani abu mai daraja da ban nuna masu ba."
\s5
\v 5 Sai Ishaya yace da Hezekiya, "Saurari maganar da Yahweh mai runduna:
\v 6 'Duba, ranaku sun kusa zuwa da za a kwashe komai a fadarka, abubuwan da kakaninka suka tara har ya zuwa yau, za a ɗauke su zuwa Babila. Ba abin da za a rage, in ji Yahweh.
\s5
\v 7 'Ya'ya da aka haifa maka, waɗanda kai ka haife su - za a ɗauke su, kuma za su zama bãbãnni a fadar sarkin Babila.'"
\v 8 Sai Hezekiya ya cewa Ishaya, "Maganar Yahweh wadda ka faɗa tana da kyau." Domin ya yi tunani, "Za a sami salama da kwanciyar rai a zamanina."
\s5
\c 40
\cl Sura 40
\p
\v 1 "Ta'aziya, ta'azanta mutanena," in ji Allahnka.
\v 2 "Yi magana mai taushi ga Yerusalem; ka yi mata shela cewa yaƙinta ya zo ƙarshe, laifofinta kuma an gafarta mata, za ta sami ruɓi biyu daga hannun Yahweh domin dukkan zunubanta."
\s5
\v 3 Wata murya ta koka, "A cikin jeji shirya hanyar Yahweh; a shirya ta miƙaƙƙiya a cikin Hamada doguwar hanya domin Allahnmu."
\v 4 Kowanne kwari zai cika, za a baje kowanne tsauni da tudu; ƙasa mai kwazazzabai kuwa za ta zama sumul, wurare kuma masu gargada za su zama sarari;
\v 5 kuma ɗaukakar Yahweh zata bayyana, dukkan mutane kuwa za su gan shi tare; gama bakin Yahweh ne ya faɗi haka.
\s5
\v 6 Wata murya na cewa, "Yi kuka." Wata ta amsa, "Kukan me zan yi?" "Dukkan yan adam ciyawa ne, dukkan alƙawarinsu da amincinsu kamar furannin jeji.
\v 7 Ciyawa ta kan bushe, furanni kuma su yanƙwane sa'ad da numfashin Yahweh ya hura a kansu; ba bu shakka mutane ciyawa ne.
\v 8 Hakika ciyawa ta kan bushe, furanni kuwa kan yi yaushi, amma maganar Allahnmu zata tsaya har abada."
\s5
\v 9 bisa tsauni mai tsayi, Sihiyona, mai ɗauke da labari mai daɗi. Ki yi kuwwa da ƙarfi, yaYerusalem. Ke da kika kawo labari mai daɗi, daga muryarki, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa biranen Yahuda, "Ga Allahnku!"
\v 10 Duba, Ubangiji Yahweh yana zuwa kamar mayaƙi mai nasara, damtsensa mai ƙarfi zai yi masa mulki. Ga shi, da sakamako tare da shi, kuma waɗanda ya ceto sun sha gabansa.
\s5
\v 11 Zai ciyar da garkensa kamar makiyayi, zai tattara 'yan tumakin a damtsensa, ya kuma ɗauke su kusa da zuciyarsa, kuma a hankali zai bida tumaki masu shayar da nono.
\s5
\v 12 Wa ya taɓa auna ruwaye da tafin hannunsa, ko ya auna sararin sama da tafin hannunsa, ko ya iya riƙe ƙurar duniya a kwando, ko ya iya auna nauyi tsaunika a sikeli, ko tuddai a ma'auni?
\s5
\v 13 Akwai wanda zai iya fahimtar tunanin Yahweh, ko ya ba shi umarni a matsayin mashawarcinsa?
\v 14 Daga wurin wa ya taɓa karɓar umarni? Wane ne ya koya masa yadda zai yi abubuwa, ya kuma koya masa sani, ko ya nuna masa hanyar fahimta?
\s5
\v 15 Duba, al'ummai na kamar digon ruwa a bokiti, kuma suna kama da ƙura a sikeli; duba, yana auna tsibirai kamar ɗan ɗigo.
\v 16 Lebanon bata da isasshen fetur, ko dabbobin dajinta ba su isa baikon konawa ba.
\v 17 Dukkan al'ummai ba isassu ba ne a gare shi; an ɗauke su ba a bakin komai bane a gare shi.
\s5
\v 18 Da wa za ka iya ƙwatanta Allah? To da wanne gunki za ka kamanta da shi?
\v 19 Gunki! Masassaƙi ne ya yi shi: makera suka dalaye da zinariya kuma suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.
\v 20 Domin miƙa baiko wani ya zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba; ya nemi ƙwararren maƙeri da zaya yi masa siffar gunkin da ba zaya fãɗi ba.
\s5
\v 21 Ashe ba ka sani ba? Ashe ba ka ji ba? Ba a faɗa maka ba tun daga farko? Ba ka fahimta ba tun daga fara kafa harsashin duniya?
\v 22 Shi wanda ya ke zaune a bisa bangon duniya; mazaunanta suna kama da fãri a gabansa. Ya miƙar da sammai kamar labule kuma ya baza su kamar rumfa domin a zauna ciki.
\s5
\v 23 Yana maida masu mulki ba komai ba kuma yana maida masu mulkin duniya yadda ba a san da zamansu ba.
\v 24 Suna kama da dashe kasafai, dashen da a ka shuka kasafai, dashen da bai yi ko saiwar da ta shiga ƙasa ba, sa'ad da ya hura a kansu sai su yi yaushi, kuma iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.
\s5
\v 25 "To, da wane ne za a kwatanta ni, ko akwai wani mai kama da ni?" in ji shi Mai Tsarki.
\v 26 Dubi sararin sama a bisa! Wane ne ya halicce dukkan waɗannan taurarin? Shi ne wanda ya ke masu jagora kuma ya kira su bisa ga sunan kowa. Ta wurin ikonsa da girmansa da kuma ta wurin karfi da iko, ba ko ɗayansu da ya ɓace.
\s5
\v 27 Me ya sa kuka ce, Yakubu, kuma kuka ce, Isra'ila, "Hanya ta a ɓoye take daga Yahweh, kuma Allahna bai damu da baratarwata ba"?
\v 28 Ba ku sani ba? Ba ku kuma ji ba? Madawwamin Allah, Yahweh, shi ne mahaliccin ƙarshen duniya, ba ya taɓa jin gajiya ko kasala ba; ba shi da iyakar fahimta.
\s5
\v 29 Yana ƙarfafa masu jin gajiya; masu kasala kuma ya kan sabunta ƙarfinsu.
\v 30 Duk da matasa ma sukan ji kasala da gajiya, samari kuma sukan yi tuntuɓe su faɗi:
\v 31 Amma waɗanda suke dogara ga Yahweh zai sabunta ƙarfinsu; za su tashi da fikafikai kamar gaggafa; za su yi gudu kuma ba za su gaji ba; za su yi tafiya amma ba za su suma ba.
\s5
\c 41
\cl Sura 41
\p
\v 1 "Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe; bari ƙasashe su sabunta ƙarfinsu; bari su matso kusa su yi magana; bari mu taru ga yin jayayya a kan saɓanin.
\v 2 Wane ne wannan da ya motso wani daga gabas, ana kiransa cikin adalci ga aikinsa? Ya bada ƙasashe a gare shi ya kuma taimaka masa har ya yi nasara a kan sarakuna. Ya maida su ƙura da takobinsa, kamar ciyawar da iska ta hure da bakansa.
\s5
\v 3 Yana biye da su har ma ya wuce lafiya, da sauri ƙwarai da ƙyar ƙafarsa take taɓa ƙasa.
\v 4 Wane ne yasa wannan ya faru kuma su wane ne suka yi waɗannan ayyuka? Wane ne ya kirawo tsararraki tun daga farko? Ni, Yahweh, na farko, da na ƙarshe, Ni ne shi.
\s5
\v 5 Tsibirai sun gani kuma sun ji tsoro; ƙarshen duniya ta girgiza; sun nufo har sun zo.
\v 6 Kowanne ya taimaki makwabcinsa, kowanne kuma ya cewa ɗayan, 'Yi ƙarfin hali.'
\v 7 Masassaki yana ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma wanda ya ke aiki da guduma yana ƙarfafa shi wanda ya ke aiki da tubalin ƙarfe, haka nan ya ke cewa mai walda, yana da kyau.' Suna buga ƙusoshi masu ƙarfi domin kada su tuntsure,
\s5
\v 8 Amma kai, Isra'ila, bawana, Yakubu wanda na zaba, zuriyar Ibrahim abokina,
\v 9 kai wanda na kawo ka daga maƙurar duniya, kuma wanda na kira daga wurare masu nisa, wanda na ce, 'kai ne bawana,' Na zaɓe ka ban kuma ƙi ka ba.
\s5
\v 10 Kada ka ji tsoro, ina tare da kai. Kada ka damu da komai, ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka, zan kuma taimake ka, zan tallafe ka da hannunna na dama mai adalci.
\s5
\v 11 Duba, za su ji kunya da ƙasƙanci, dukkan su da suke fushi da kai; za su zama ba komai ba za su kuma lalace, waɗannan da suke gãba da kai.
\s5
\v 12 Za ka neme su amma ba za ku same su ba; wato waɗanda suke gãba da kai; za su zama kamar ba komai ba, ba bu shakka za su zama ba komai ba.
\v 13 Gama Ni, Yahweh Allahnku, zan riƙe ka da hannun dama, ina faɗi maka, 'Ka da ka ji tsoro; ina taimakonka.'
\s5
\v 14 Kada ka ji tsoro, kai tsutsa Yakubu, da ku mutanen Isra'ila; zan taimake ku - wannan furcin Yahweh ne, mai fansarku, Mai Tsarki na Isra'ila.
\v 15 Duba, zan sa ku zama kamar ceburin sussuka mai kaifi, sabo mai baki biyu; za ku sussuke tsaunuka ku lalatar da su; za ku niƙe tuddai kamar ƙaiƙayi.
\s5
\v 16 Za ku sheƙesu, iska kuma zata hure su; iska kuma zata warwatsa su. Za ku yi murna cikin Yahweh, za ku yi murna a cikin Mai Tsarki na Israi'la.
\s5
\v 17 Waɗanda ake takurawa da mabuƙata za su nemi ruwa, amma ba bu, harsunansu za su bushe da ƙishi; Ni Yahweh, zan amsa addu'arsu; Ni Allah na Isra'ila, ba zan yashe su ba.
\v 18 Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga gangare, maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a tsakiyar kwarurruka; zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.
\s5
\v 19 Zan sa itatuwan sida, da gawo su tsiro a jeji, da itacen ci-zaƙi, da itacen zaitun. Zan dasa siferas a hamada, tare da marke da wuraren renon itacen siferas.
\v 20 Zan yi wannan domin mutane su gani, su sani, su kuma fahimta tare, hannun Yahweh ya yi wannan, Mai Tsarki na Isra'ila ya halitta shi.
\s5
\v 21 "Faɗi maganarka," Inji Yahweh, "Faɗi jayayyarka mai kyau don gumakunka," inji Sarkin Yakubu.
\v 22 Bari ku kawo ma na jayayyarku; ku zo ga ba ku furta ma na abin da da zai faru, saboda mu san waɗannan abubuwa sosai. Ku sa su faɗa mana yadda furcin za su zama, domin mu yi tunani a kansu mu kuma san yadda su ka cika.
\s5
\v 23 Ku faɗa game da abubuwan da za su faru nan ga ba, domin mu san ko ku alloli ne; ku yi wani abu mai kyau ko bala'i, ko ma cika da jin tsoro ya kuma burgemu.
\v 24 Ku duba, ku allolin wofi ne kuma ayyukan kuma na wofi ne; wanda ya zaɓe ku ma abin ƙyama ne.
\s5
\v 25 Na ta da wani daga arewa, kuma ya zo; daga fitowar rana na kira shi wanda ya yi kira bisa sunana, wanda zai tattake masu mulki kamar laka, kamar yadda maginin tukwane ya ke tattake yumɓu.
\v 26 Wa ne ne ya faɗa ma na wannan tun daga farko, ko ma sani? Kafin wannan lokaci, ko mu ce, "Ya yi dai-dai"? Babu ɗayansu da ya yi dokar haka, i, ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu.
\s5
\v 27 Ni ne na farko da na ce da Sihiyona, "Duba ga su a nan;" Na aika manzo zuwa Urshalima.
\v 28 Sa'ad da na duba, ba bu wani, ko ma a cikinsu wanda zai ba da shawara mai kyau, wanda idan Na yi tambaya, zai iya amsawa da magana.
\v 29 Duba, dukkansu a wofi su ke, ayyukansu na wofi ne; zubin siffofinsu na ƙarfe adadin iska su ke, wofi ne kuma.
\s5
\c 42
\cl Sura 42
\p
\v 1 Duba, bawana, wanda na riƙe; zaɓaɓɓena, wanda na ke jindaɗin sa. Na sa Ruhuna a bisansa; za ya kawo hukunci ga al'ummai.
\v 2 Ba za ya yi kuka ko sowa ba, ko ya sa a ji muryarsa a tituna ba.
\s5
\v 3 Murzajjen kara ba za ya karya shi ba, lagwanin da ba ya ci sosai ba za ya ɓice shi ba: a cikin aminci za ya zartar da hukunci.
\v 4 Ba za ya suma ba ko ya karaya har sai ya kafa hukunci a duniya; Ƙasashen tsibirai kuma suna jiran shari'arsa.
\s5
\v 5 Ga abin da Allah Yahweh ya faɗa - shi wanda ya halicci sammai kuma ya shimfiɗasu, shi wanda ya yi duniya da dukkan abin da take fitarwa, shi wanda ya ke bayar da numfashi ga mutanen dake cikin ta da kuma rai ga waɗanda ke zaune a cikin ta:
\v 6 "Ni, Yahweh, na kira ka cikin adalci kuma zan ri ƙe hannunka. Zan kiyayeka in sanya ka alƙawari domin mutane, haske kuma ga al'ummai,
\s5
\v 7 Domin a buɗe idanun makafi, za a sako da 'yan kurkuku daga can cikin kogo da kuma waɗanda aka tsare a gidan tsaro waɗanda ke zaune a cikn duhu.
\s5
\v 8 Ni ne Yahweh, sunana kenan; bazan raba ɗaukakata da wani ba ko yabona da sassaƙaƙƙun gumaka.
\v 9 Duba, abubuwan da suka wuce sun faru, yanzu ina gaf da furta sabobbin al'amura. Kafin su fara afkuwa zan gaya maku game da su."
\s5
\v 10 Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh, da kuma yabonsa daga ƙarshen duniya; ku waɗanda ke gangarawa zuwa teku, da dukkan abin da ke ciki, ƙasashen tsibirai da dukkan mazaunan cikin su.
\v 11 Bari hamada da biranenta su koka, ƙauyuka kuma inda keda ke zaune, ku yi sowa ta farinciki! bari mazauna Sela su raira; bari su yi sowa daga ƙololuwar tsaunuka.
\s5
\v 12 Bari su bada ɗaukaka ga Yahweh su kuma furta yabonsa a ƙasashen tsibirai.
\v 13 Yahweh za ya fita a matsayin mayaƙi; a matsayin mutumin yaƙi za ya motsa himmarsa. Za ya yi sowa, I, za ya yi kururuwar koke-koken yaƙinsa; za ya nuna wa maƙiyansa ikonsa.
\s5
\v 14 Na yi shiru na dogon lokaci; na tsaya cik na hana kaina; yanzu zan yi kuka kamar macen dake cikin naƙuda; zan yi nishi da huci.
\v 15 Zan rusar da tsaunuka da tuddai in kuma sa ganyayensu su bushe; zan maida koguna tsibirai in kuma sa lakarsu su bushe.
\s5
\v 16 Zan kawo makafi bisa hanyar da ba su sani ba; bisa tafarkun da ba su san zan bi da su ba. Zan mayarda duhu ya zama haske a gabansu, zan sa karkatattun wurare su miƙe. Zan yi waɗannan abubuwa, ba kuma zan yashe su ba.
\s5
\v 17 Za a komar da su baya, za a san ya su cikin kunya gabaɗaya, wato su waɗanda suka sa dogararsu ga sassaƙaƙƙun siffofi, su waɗanda suke cewa sarrafaffun siffofin ƙarfe, "Ku ne allolinmu."
\s5
\v 18 Ka saurara, kai kurma; ka duba, kai makaho, domin ka sami gani.
\v 19 Wane ne makaho idan ba bawana ba? ko kurma kamar manzona wanda na aika? Wane ne ya yi makantar abokin alƙawarina, ko makaho kamar bawan Yahweh?
\s5
\v 20 Kana ganin abubuwa da yawa, amma baka fahimta; kunnuwa a buɗe, amma ba bu mai ji.
\v 21 Ya gamshi Yahweh ya yabawa hukuncinsa kuma yasa shari'arsa a bar ɗaukaka.
\s5
\v 22 Amma waɗannan mutane ne waɗanda a ka yiwa fashi a ka kuma washe su; an datse su dukka a ramuka, sun zama abin washe wa ba bu kuma mai fansarsu, ba bu wanda kuma ya ce, "A maido da su!"
\s5
\v 23 Wane ne a cikin ku za ya saurari wannan? Wane ne za ya saurara kuma ya ji a nan gaba?
\v 24 Wane ne ya miƙa Yakubu ga ɗan fashi, Isra'ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Yahweh bane, wanda muka yiwa zunubi, wanda suka ƙi tafiya cikin hanyoyinsa, wanda kuma suka ƙi yin biyayya da shari'arsa?
\s5
\v 25 Domin wannan ya zubo da fushinsa mai zafi a bisansu, da masifar yaƙi. Ya haska kewaye da su, amma ba su lura ba; ya ƙona su, amma ba su yi hattara ba a zukatansu.
\s5
\c 43
\cl Sura 43
\p
\v 1 Amma yanzu ga abin da Yahweh ya faɗa, shi wanda ya halicceka, Yakubu, shi wanda ya yi ka, Isra'ila: "Kada ka ji tsoro, gama na fansheka; na kiraka da sunanka, kai nawa ne.
\s5
\v 2 Sa'ad da ka bi ta cikin ruwaye, zan kasance tare da kai; ta cikin koguna kuma, ba za su sha kanka ba. Sa'ad da ka yi tafiya ta cikin wuta ba za ka ƙone ba, harsashen wutar kuwa ba za ya lalatar da kai ba.
\v 3 Gama ni ne Yahweh Allahnka, mai tsarki na Isra'ila, mai cetonka. Na ba da Masar diyya a kanka, Itiyofiya da Seba misanya dominka.
\s5
\v 4 Tunda kana da tamani da muhimmanci a idanuna, ina ƙaunarka; saboda haka zan bayar da mutane misanya dominka, wasu mutanen kuma misanya domin rayuwarka.
\v 5 Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; zan kawo zuriyarka daga gabas, in tattaro ka daga yamma.
\s5
\v 6 Zan cewa arewa, 'Miƙosu,' kudu kuma, 'Kada ka riƙesu,' A kawo 'ya'yana maza daga ne sa, 'ya'yana mata kuma daga lungun sassan duniya,
\v 7 dukkan wanda ake kira da sunana, wanda na halitta domin ɗaukakata, wanda na yi, I, wanda na halitta.
\s5
\v 8 Fito da mutane makafi, koda ya ke suna da idanu, da kuma kurame, koda ya ke suna da kunnuwa.
\v 9 Dukkan al'ummai ku tattaru wuri ɗaya, dukkan mutane kuma ku taru. Wane ne a cikinsu za ya furta wannan, ya kuma yi mana shelar al'amuran farko? Bari su kawo shaidunsu su tabbatar da gaskiyarsu, bari su saurara su kuma tabbatar, 'Gaskiya ne.'
\s5
\v 10 Ku ne shaiduna," Yahweh ya furta, "Bawana kuma wanda na zaɓa, domin ku sani ku kuma gaskata da ni, ku kuma fahimci cewa ni ne shi. Kafin ni babu wani allah da a ka yi, kuma ba za ayi wani ba bayana.
\v 11 Ni, ni ne Yahweh, kuma babu wani mai ceto sai ni.
\s5
\v 12 Na furta, na ceto, kuma na yi shela, kuma babu wani allah a tsakaninku. Kune shaiduna," Yahweh ya furta, '"Ni ne Allah.
\v 13 Daga wannan rana har zuwa nan gaba ni ne shi, kuma babu wanda za ya ceci wani daga hannuna. Na aikata, wane ne za ya canza?"
\s5
\v 14 Wannan ne abin da Yahweh yace, Mai fansarku, Mai tsarki na Isra'ila: "Sabili da ku na yi aike a Babila na turasu dukka zuwa gudun hijira, na maida farincikin Babiloniyawa zuwa waƙoƙin makoki.
\v 15 Ni ne Yahweh, Mai tsarkinku, Mahaliccin Isra'ila, Sarkinku."
\s5
\v 16 Wannan shi ne abin da Yahweh yace (Wanda ya buɗe hanya ta cikin teku da kuma tafarki ta cikin manyan ruwaye,
\v 17 wanda ya bida karusa da doki, sojoji da babbar runduna. Suka faɗi tare; ba za su sake tashi ba; an kawar da su, aka ɓice su kamar lagwanin da ke ci.)
\s5
\v 18 Kada ku yi tunani akan waɗannan abubuwa da suka wuce, ko ku kula da abubuwan dã can.
\v 19 Duba, ina gaf da yin sabon abu; yanzu ya fara faruwa; ba ku yi la'akari ba? zan yi hanya a hamada da magudanan ruwa a cikin jeji.
\s5
\v 20 Dabbobin jeji za su girmamani, diloli da jiminai, saboda na bayarda ruwa a jeji, da koguna a hamada, domin zaɓaɓɓun mutanena su sha,
\v 21 waɗannan mutane waɗanda na yi su domin kaina, domin su maimaita yabbaina.
\s5
\v 22 Amma ba ku yi kira gare ni ba, Yakubu; kun gaji da ni, Isra'ila.
\v 23 Ba ku kawo mani ko ɗaya daga cikin tumakinku ba a matsayin baye-bayen ƙonawa, ko kuka girmamani da hadayunku ba. Ban ɗora maku nauyin baye-bayen hatsi ba, ko na gajiyar daku da kawo turare.
\s5
\v 24 Ba ku sawo mani ƙiraren ƙanshi da kuɗi ba, ko kuwa ku zubo mani kitsen hadayunku ba; amma kuna ɗoramani nauyin zunubanku, kun gajiyar da ni da miyagun ayyukanku.
\s5
\v 25 Ni, I, Ni, Ni ne wanda na ke share kurakuranku sabili da ni; kuma bazan sake tunawa da zunubanku ba.
\v 26 Ku tuna mani da abin da ya faru, bari mu yi mahawara tare; ku kawo ƙararku, domin a tabbatar da ku marasa laifi.
\s5
\v 27 Ubanku na farko ya yi zunubi, kuma shugabanninku sun yi mani laifi.
\v 28 Saboda haka zan gurɓata tsarkakan shugabanni; zan miƙa Yakubu ga lalacewa ɗungum, Isra'ila kuma ga wulaƙantaccen ƙasƙanci."
\s5
\c 44
\cl Sura 44
\p
\v 1 Ka saurara yanzu, bawana Yakubu, da Isra'ila, wanda na zaɓa:
\v 2 Ga abin da Yahweh yace, shi wanda ya yi ka ya kuma nasa ka cikin mahaifa wanda kuma za ya taimake ka: "Kada ka ji tsoro, bawana Yakubu; da kai kuma, Yeshurun, wanda na zaɓa.
\s5
\v 3 Gama zan zubo da ruwa a bisa ƙasa mai ƙishi, da magudanan ruwa a bisa busasshiyar ƙasa; zan zubo da Ruhuna a bisa zuriyarku, da albarkata a bisa 'ya'yanku.
\v 4 Za su tsiro daga cikin ciyawa, kamar itatuwan kurmi dake gefen magudanan ruwa.
\s5
\v 5 Wani za ya ce, 'Ni na Yahweh ne,' wani kuma za ya yi kira ga sunan Yakubu, wani kuma zaya rubuta a kan hannunsa, 'Na Yahweh ne,' ya kuma raɗawa kansa suna da sunan Isra'ila."
\s5
\v 6 Wannan ne abin da Yahweh yace - Sarkin Isra'ila da mai fansarsa, Yahweh mai runduna: "Ni ne farko, ni ne kuma ƙarshe; babu kuma wani Allah sai ni.
\s5
\v 7 Wane ne kamar ni? bari ya yi shela kuma ya yi mani bayanin al'amuran da suka afku tunda na kafa mutanen dã, bari kuma su yi bayanin al'amuran da za su zo.
\s5
\v 8 Kada ku ji tsoro ko ku firgita. Ba na furta maku ba tuntuni, na kuma shelarda shi? Ku ne shaiduna: Akwai wani Allah baya gare ni? Babu wani Dutse; bansan da wani ba."
\s5
\v 9 Dukkan masu sarrafa gumakai ba komai bane; abubuwan da suke jiwa daɗi wofi ne; shaidunsu basu gani ko sanin wani abu, kuma za a sa su sha kunya.
\v 10 Wane ne za ya yi allah ko ya sarrafa gumaka da ke wofi?
\s5
\v 11 Duba, dukkan abokan tarayyar shi za su sha kunya; masu sassaƙa shi mutane ne kawai. Bari su ɗauki matsayinsu tare; za su noƙe kuma za a sa su sha kunya.
\s5
\v 12 Maƙeri na aiki da kayan aikinsa, ya yi su, ya zuga su a garwashi. Ya siffantashi da guduma ya aikatashi da ƙarfin damtsensa. Ya ji yunwa, ƙarfinsa ya ƙare; bai sha ruwa ba sai ya sume.
\s5
\v 13 Kafinta yana gwada katako da abin gwaji, za ya yi mashi zane-zane da abin salo. Da kayan aikinsa zai yi masa siffofi, ya zãne shi da abin zãne. zai yi shi siffa-siffa bisa ga siffar mutum, kamar mutum mai ban sha'awa, domin ya zauna a cikin gida.
\s5
\v 14 Yana saro itatuwan sida, ko ya zaɓo itatuwan sifares ko itacen rimi. Yana ɗaukowa kansa itatuwa daga jeji. Za ya dasa itacen fir ruwan sama kuma za ya sa ya yi girma.
\s5
\v 15 Sai mutum ya yi amfani da shi ya kunna wuta kuma ya ji ɗumi. I, yana kunna wuta ya gargasa gurasa. Daga ciki kuma yana ɗauka ya yi wa kansa allah sai ya rusuna masa; ya yi wa kansa gumaka kuma ya rusuna masa.
\v 16 Daga cikin katakan yana yin amfani da wasu ya kunna wuta, ya kuma gasa nama a kai. Ya ci ya ƙoshi. yana ɗunɗuma kansa sai ya ce, "Ah, na ji ɗumi, na ga wutar."
\s5
\v 17 Sauran itatuwan da suka rage kuma sai ya yi allah da su, siffar da ya sassaƙa kuma; sai ya rusuna masa yana ba shi girma, sai ya yi addu'a gare shi yana cewa, "Cece ni, gama kai ne allahna."
\s5
\v 18 Ba su sani ba, balle kuma su fahimta, domin idanunsu makafine ba su kuma gani, kuma zukatansu ba su ganewa.
\s5
\v 19 Babu mai yin tunani, ko su yi nazari su ce, "Daga cikin katakon na yi abin wuta da wasu; I, kuma na gasa gurasa bisa garwashin. Na gasa nama bisa garwashin na ci. To ya ya zan ɗauki sauran katakon da ya rage in yi abin ƙazanta da shi domin sujada? Ya ya zan rusuna ga wani kututturen katako?"
\s5
\v 20 Ya yi kamar toka ya ke ci; ruɗaɗɗiyar zuciyarsa ta sa ya kauce. Baya iya ceton kansa, ko kuwa ya ce, "Wannan abin da ke hannun damana ba allahn gaskiya ba ne."
\s5
\v 21 Yi tunani a kan waɗannan abubuwa, Yakubu, da Isra'ila, domin kai bawana ne: na yi ka, kai bawana ne; Isra'ila bazan manta da kai ba.
\v 22 Na share, ayyukan tawayenka sarai, kamar girgije mai kauri, kamar girgije kuma, zunubanka sun dawo mani, gama na fanshe ka.
\s5
\v 23 Ku raira, ku sammai, gama Yahweh ya yi wannan; ku yi sowa, ku zurfafan duniya. Ku fashe da waƙa, ku tsunuka, kai daji da duk itatuwan da ke cikinka; gama Yahweh ya fanshi Yakubu, kuma za ya nuna ɗaukakarsa a Isra'ila.
\s5
\v 24 Wannan ne abin da Yahweh yace, mai fansarka, wanda ya yi ka daga cikin mahaifa: "Ni ne Yahweh, wanda ya yi dukkan abubuwa, wanda shi kaɗai ya shimfiɗa sammai, shi kaɗai ya sarrafa duniya.
\v 25 Ni wanda na lalata kayan tsafin masu maganar wofi na kuma wulaƙanta masu karanta kayan tsafin; Ni wanda na juyarda hikimar masu hikima na kuma maida shawararsu wawanci.
\s5
\v 26 Ni, Yahweh, wanda ke tabbatarda maganganun bawansa wanda kuma ke sa hasashen manzanninsa su afku, wanda ya cewa Yerusalem, 'Za a sake zaunawa a cikinki,' da kuma garuruwan Yahuda, 'Za a sake ginaku, kuma zan ɗaga rusassun wurarensu';
\v 27 wanda ya ke cewa teku mai zurfi, 'Ki bushe, kuma zan busar da igiyoyinki.'
\s5
\v 28 Yahweh ne ya faɗa game da Sairus, 'Makiyayina ne shi, za ya aiwatar da dukkan nufina; za ya zartar da doka game da Yerusalem, 'Za a sake ginata,' game da haikalin, 'Bari a sake kafa harsashensa.'"
\s5
\c 45
\cl Sura 45
\p
\v 1 Ga abin da Yahweh ya faɗi wa shafaffensa, ga Sairus, wanda nake riƙe da hannun damansa, domin inci ƙarfin al'ummai a gabansa, in tuɓe makaman sarakuna, in kuma buɗe ƙofofi a gabansa, domin ƙofofin su zauna a buɗe:
\s5
\v 2 Zan shiga gabanka in rusar da duwatsu; zan farfasa ƙofofin tagullar in kuma dardatse sandunan ƙarfensu,
\v 3 zan baka taskokan duhu da kuma dukiyoyin da a ka ɓoye, domin ka sani cewa Ni ne, Yahweh, wanda ya kira ka da sunanka, Ni, Allah na Isra'ila.
\s5
\v 4 Saboda Yakubu bawana, da Isra'ila zaɓaɓɓena, na kira ka da sunanka: Ina baka daraja kaɗan, koda ya ke ba ka sanni ba.
\v 5 Ni ne Yahweh, babu wani kuma; babu wani Allah sai ni. zan shirya ka domin yaƙi, koda ya ke ba ka sanni ba;
\v 6 domin mutane susan cewa daga tasowar rana, daga kuma yamma, cewa babu wani allah sai ni: Ni ne Yahweh, babu kuma wani.
\s5
\v 7 Ni na yi haske kuma na halicci duhu; Ina kawo salama in kuma ƙirƙiro bala'i; Ni ne Yahweh, wanda ke yin dukkan waɗannan abubuwa.
\v 8 Ku sammai, ku kwararo ruwa daga sama! bari sararin sammai su kwararo da adalci. Bari duniya ta shanyesu, domin ceto ya tsiro, da adalci kuma su yi girma tare. Ni, Yahweh, na halicce su dukka.
\s5
\v 9 Kaiton duk wani wanda ke gardama da wanda ya halicce shi, ga wanda ya ke kamar kowacce tukunyar yunɓu a cikin tukwanen yunɓu a ƙasa! yunɓun za ya iya cewa mai yin tukwanen, 'Me kake yi?' ko 'Aikin naka baya da abin riƙewa a jikinsa'?
\s5
\v 10 Kaiton wanda za ya cewa Mahaifi, 'Mahaifin wa kake yi?' ko kuwa ga mace, 'Me kike haihuwa?'
\s5
\v 11 Ga abin da Yahweh yace, Mai Tsarki na Isra'ila, Mahaliccinka: 'Me yasa kake tambayoyi game da abin da zan yi domin 'ya'yana? zaka gaya mani abin da zan yi game da aikin hannuwana?'
\s5
\v 12 Ni na yi duniya kuma na halitta mutum a kanta. Hannuwana ne suka shimfiɗa sammai, kuma na umarci dukkan taurari su bayyana.
\s5
\v 13 Na motsa Sairus cikin adalci, kuma zan miƙar da tafarkunsa dukka. Zai gina birnina; za ya bar mutanena 'yan gudun hijira su koma gida, ba kuma da farashi ba ko cin hanci,'" Yahweh mai runduna ya faɗa.
\s5
\v 14 Ga abin da Yahweh ya faɗa, "Za a kawo maku cinikayyar Masar da fataucin Itiyofiya tare da Sabiyawa, mutane masu doguwar siffa. Za su zama naku. Za su biyo ku, tafe cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku suna roƙonku suna cewa, 'Tabbas Allah na tare daku, babu kuma wani sai dai shi.'"
\v 15 Hakika kai ne Allah wanda ka ɓoye kanka, Allah na Isra'ila, Mai ceto.
\s5
\v 16 Dukkansu za su kunyata su wulaƙanta tare; masu sassaƙa gumakai za su yi tafiya cikin ƙasƙanci.
\v 17 Amma Yahweh za ya ceci Isra'ila da madawwamin ceto; ba za ku sake shan kunya ba ko ƙasƙanci.
\s5
\v 18 Ga abin da Yahweh ya faɗa, shi wanda ya halicci sammai, Allahn gaskiya wanda ya ƙirƙiro duniya, ya halittata, ya kafa ta. Ya halittata, ba a matsayin jujiba, Ya zãna ta domin a zauna a cikinta: "Ni ne Yahweh, babu wani kuma.
\s5
\v 19 Ban yi magana a asirce ba, a wani ɓoyayyen wuri; Ban cewa zuriyar Yakubu, 'Ku neme ni a wofi ba!' Ni ne Yahweh, Mai yin magana a gaskiya; Ina furta abubuwan da ke dai-dai.
\s5
\v 20 Ku tattaro kanku ku zo! ku taru wuri ɗaya, ku 'yan gudun hijira daga cikin al'ummai! basu da Ilimi, su waɗanda ke ɗaukar sassaƙaƙƙun siffofi su kuma yi addu'a ga allolin da ba su iya ceto.
\s5
\v 21 Ku zo kusa ku furta mani, ku kawo shaida! bari su yi mugun shirinsu tare. Wane ne ya nuna wannan tundã can? Wane ne ya yi shelar shi? Ba Ni ne ba, Yahweh? Babu wani Allah sai dai ni, Allah baratacce Mai ceto kuma; babu wani baya gare ni.
\s5
\v 22 Ku juyo gare ni ku sami ceto, ku dukkan ƙarshen duniya; gama Ni ne Allah, babu wani kuma.
\v 23 Na yi rantsuwa da kaina, maganar dokar adalci tawa, kuma ba za ta koma baya ba: 'A gare ni kowacce gwiwa zata durƙusa kuma kowanne harshe za ya rantse.
\s5
\v 24 Za su ce mani, "A cikin Yahweh ne kawai akwai ceto da ƙarfi kuma.""' Ma su jin haushina kuma za su sha kunya.
\v 25 A cikin Yahweh dukkan zuriyar Isra'ila za su barata; za su yi taƙama a cikinsa.
\s5
\c 46
\cl Sura 46
\p
\v 1 Bel ta rusuna, Nebo ta sunkuya; an ɗauke gumakansu a bisa dabbobi da bisashen ɗaukar kaya. Waɗannan gumakai da kuka ɗauko kaya ne masu nauyi a bisa dabbobin da suka gaji.
\v 2 Gaba ɗaya sun sunkuya ƙasa, durƙushe a ƙasa; basu iya fanso siffofin, su kansu kuma sun tafi cikin bauta.
\s5
\v 3 Ku saurareni, gidan Yakubu, dukkanku ragowar gidan Isra'ila, waɗanda nake ɗauke daku tun kafin a haifeku, a ɗauke tun daga mahaifa.
\v 4 Har zuwa tsufanku Ni ne shi, kuma zan ɗaukeku har sai gashinku ya zama furfura. Na halicceku kuma zan riƙeku; zan ɗaukeku kuma zan fansheku.
\s5
\v 5 Da wa za ku kwatantani? da wa kuke tunanin na yi kama, domin ku kwatantamu?
\v 6 Mutane sukan zubo da zinari waje daga Jaka sukan kuma gwada azurfa a bisa ma'auni. Sai su yi hayar maƙeri, sai ya narka ya yi masu allah; sai su rusuna su kuma yi mashi sujada.
\s5
\v 7 Za su ɗagashi su ɗora a kafaɗa su ɗaukeshi; sai su ajiye a wurin zamansa, zai tsaya a wurin zamansa ba kuma zai matsa daga wurin ba. Za su yi kuka zuwa gare shi, amma ba za ya iya amsawa ba ko kuwa ya ceci wani daga matsalarsa.
\s5
\v 8 Ku yi tunani game da waɗannan abubuwa; kada ku yi watsi dasu, ku fitsararru!
\v 9 Ku yi tunani game da abubuwan farko, na lokutan da suka wuce, gama Ni ne Allah, babu wani kuma, Ni ne Allah, babu wani kama da ni.
\s5
\v 10 Ina sanar da ƙarshen tun daga farko, tukunna kuma abin da bai riga ya faru ba; Na faɗa, "Shirina za ya faru, kuma zan yi yadda nake so."
\v 11 Na kira tsuntsun ganima daga gabas, mutumin dana zaɓa kuma daga ƙasa mai nisa; I, na faɗa; Zan kuma aiwatar da shi; ina da manufa, zan kuma aikata.
\s5
\v 12 Ku saurareni, ku mutane marasa ji, waɗanda ke nesa da yin abin dake dai-dai.
\v 13 Ina kawo adalcina kusa; baiyi nisaba, kuma cetona baya jira; zan bada ceto kuma ga Sihiyona kyauna kuma ga Isra'ila.
\s5
\c 47
\cl Sura 47
\p
\v 1 Sauko ki zauna cikin turɓaya, ke budurwa ɗiyar Babila; zauna ƙasa babu kursiyi, ɗiyar Kaldiyawa. Baza a sake kiranki mai kwarjini da taushi ba.
\v 2 Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; kware lulluɓinki, ki tuɓe doguwar rigarki, buɗe ƙafafunki, ki tsallake rafuffuka.
\s5
\v 3 Za a buɗe tsiraccinki, I, za a ga kunyarki: I zan ɗauki fansa kuma bazan bar kowa ba.
\v 4 Mai fansarmu, Yahweh mai runduna sunansa, Mai tsarki na Isra'ila.
\v 5 Ki zauna shiru ki tafi cikin duhu, ke ɗiyar Kaldiyawa; domin ba za a sake kiranki sarauniyar masarautai ba.
\s5
\v 6 Na yi fushi da mutanena; na lalata gãdona na miƙasu cikin hannunki, amma ba ki nuna masu jinƙai ba; ki ka ɗora kaya mai nauyi bisa tsofaffin mutanen.
\v 7 Ki ka ce, "Zan yi mulki har abada a matsayin sarauniya ni kaɗai." ba ki yi la'akari da abubuwannan ba a zuciyarki, ba ki kuwa duba yadda za su kasance ba.
\s5
\v 8 To yanzu saurari wannan, ke da kika ƙaunaci annashuwa kika zauna a tsare; ke da kika ce a zuciyarki, "Zan wanzu, babu kuma wani kamar ni; Bazan taɓa zaunawa kamar gwauruwa ba, ko in taɓa fuskantar rashin 'ya'ya ba."
\v 9 Amma abubuwan nan biyu za su zo maki a lokaci guda a rana ɗaya: rashin 'ya'ya da gwauranci; da cikakken ƙarfi za su afko maki, duk da sihirinki da surkullen ki masu yawa da layunki.
\s5
\v 10 Kin dogara ga muguntarki; ki ka ce, "Babu mai gani na"; hikimarki da iliminki sun kai ki ga hallaka, amma kika ce a zuciyarki, "Na wanzu, babu kuma wani kama da ni."
\v 11 Bala'i za ya afko maki; ba za ki iya korar shiba da surkullenki. Lalacewa zata faɗo maki; ba za ki iya kawar da ita ba. Babbar hasara zata afko maki nan da nan, kafin ki farga.
\s5
\v 12 Ki yi naciya wurin zuba magungunanki da sihirorinki mãsu yawa waɗanda kika yi aminci wurin nanatawa tun cikin kuruciyarki; watakila za ki yi nasara, watakila za ki kori bala'in.
\v 13 Kin gaji da yawan zuwa wurin bokayenki; bari su waɗannan mutanen su tashi su ceceki - su waɗanda ke shawagi a sammai suna duba taurari, waɗanda ke furta sabobbin watanni - bari su ceceki daga abin da zaya faru dake.
\s5
\v 14 Duba, za su zama kamar haki, wuta za ta cinye su. Ba za su ceci kan su ba daga cikin harsashen. Babu garwashin da za su ji ɗumi dashi babu kuma wutar da za su zauna a gefe!
\v 15 Ga abin da za su zama a gare ki, su waɗanda kika yi aiki tare da su, kika yi saye da sayarwa tare da su da ki na yarinya, dukkansu kuma su ka ci gaba da aikata abubuwansu na wawanci; da kika yi kukan neman taimako kuma, ba bu wanda zai iya ƙwato ki."
\s5
\c 48
\cl Sura 48
\p
\v 1 Ku saurara, ya gidan Yakubu, waɗanda a ke kira da suna Isra'ila, waɗanda kuma kuka fito daga tsatson Yahuda; ku da kuka yi rantsuwa da sunan Yahweh kuka kuma tono Allahn Isra'ila, amma bada gaske ba ko kuma ta hanyar adalci.
\v 2 Domin suna kiran kansu mutanen birni mai tsaki masu dogara kuma ga Allahn Isra'ila. Yahweh mai runduna ne sunansa.
\s5
\v 3 Na furta abubuwa tunda daɗewa; sun fito daga bakina, na sa a sansu, sai nan da nan kuma na yi su, su ka kuma kasance.
\v 4 Saboda na sani ku masu taurinkai ne, tsokar wuyanku ta cije kamar karfe, goshinku kuma kamar tagulla,
\v 5 domin wannan na furta waɗannan abubuwa tuntuni; kafin su faru na sanardaku, domin kada ku ce, 'Gunkina ya yi wannan,' ko kuwa 'Sassaƙaƙƙen siffana ko sarrafaffen siffar ƙarfena ya ƙaddara waɗannan abubuwa.'
\s5
\v 6 Kun ji game da waɗannan abubuwa; ku duba dukkan alamunnan; kuma ku, ba za ku yarda da cewa abin da na faɗi gaskiyane ba? Daga yanzu zuwa nan gaba, zan nunamaku sabobbin abubuwa, ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
\v 7 Yanzu, ba daga baya ba, za su kasance, kuma kafin yau ba ku taɓa ji game da su ba, saboda haka ba za ku iya cewa, 'I, na san da su ba.
\s5
\v 8 Ba ku taɓa ji ba; ba ku sani ba; ba a bayyana abubuwan nan a kunnuwanku ba kafin yanzu. Domin na san ku macutane sosai, kuma ku masu taurinkai ne tunda a ka haife ku.
\s5
\v 9 Sabili da sunana zan yi jinkirin fushina, domin darajata kuma zan dakata daga lalatar daku.
\v 10 Duba, na tãce ku, amma ba kamar azurfa ba; Na tsarkakeku cikin garwashin azaba.
\v 11 Sabili da kaina, sabili da kaina zan aiwatar; domin tayaya zanbar sunana ya wulaƙanta? ba zan bayar da ɗaukakata ga wani dabam ba.
\s5
\v 12 Ku saurareni, Yakubu, da Isra'ila, wanda na kira: Ni ne shi; Ni ne farko, Ni ne kuma ƙarshe.
\v 13 I, hannuna ya kafa harsashen duniya, hannun damana kuma ya shimfiɗa sammai; Idan na yi kira gare su, suna tashi tsaye tare.
\s5
\v 14 Ku tattara kanku, dukkanku, ku saurara! wane ne a cikinku ya yi shelar waɗannan abubuwa? Wanda Yahweh ya zaɓa za ya cika nufinsa a kan Babila. Za ya aiwatar da nufin Yahweh a kan Kaldiyawa.
\v 15 Ni, na faɗa, I, na kiraye shi, na kawo shi, kuma za ya yi nasara.
\s5
\v 16 Ku zo kusa da ni, ku saurari wannan: Tun daga farko ban yi magana a asirce ba; sa'ad da ya faru, ina nan." Yanzu Ubangiji Yahweh ya aike ni, da Ruhunsa kuma.
\s5
\v 17 Ga abin da Yahweh, Mai fansarku, Mai tsarki na Isra'ila ya faɗa, "Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ke koya maku yadda za ku yi nasara, wanda ke bida ku a hanyar da za ku bi.
\v 18 Inda ace kawai kunyi biyayya da dokokina! da salamarku da wadatarku sun malala kamar kogi, cetonku kuma kamar raƙuman teku.
\s5
\v 19 Da yawan zuriyarku yakai kamar rairayi, 'ya'ya kuwa daga mahaifarku kamar ƙwayoyin rairayi; da baza a datse sunansu ba ko kuwa a gogesu daga gabana.
\s5
\v 20 Ku fito daga Babila! ku tsere daga Kaldiyawa! da ƙarar kuka mai ƙaraurawa ku yi shelar shi! ku sanar da wannan, ku sa ya bazu zuwa iyakar duniya! Ku ce, 'Yahweh ya fanshi bawansa Yakubu.'
\s5
\v 21 Ba su ji ƙishi ba da ya bida su ta cikin jeji; Ya sa ruwa ya kwararo daga dutse dominsu; Ya fasa dutse, ruwayen kuwa suka ɓulɓulo.
\v 22 Babu salama ga mugu - inji Yahweh."
\s5
\c 49
\cl Sura 49
\p
\v 1 Ku saurare ni, ku dake gaɓar tekuna! ku kasa kunne gare ni, ku manisantan mutane. Yahweh ya kira ni tun da a ka haife ni da suna na, sa'ad da mahaifiyata ta kawo ni cikin duniya.
\v 2 Ya maida bakina kamar takobi mai kaifi; ya ɓoye ni a inuwar hannunsa; ya maida ni gogaggiyar kibiya; a cikin kwarinsa ya ɓoye ni.
\s5
\v 3 Ya ce mani, "Kai bawana ne, Isra'ila, wanda ta wurinka ne na nuna ɗaukakata."
\v 4 Amma sai na ce, "Koda ya ke nayi zaton nayi aiki a banza, na ɓata karfina a banza, duk da haka adalcina yana ga Yahweh, kuma sakamakona na gun Allahna."
\s5
\v 5 Yanzu Yahweh ya yi magana - wanda ya sifanta ni daga haihuwata in zama bawansa, za ya maida Yakubu kuma gare shi, domin a tattaro Isra'ila zuwa gare shi, gama an ɗaukaka ni a gaban Yahweh, kuma Allahna ya zama ƙarfina -
\v 6 sai ya ce, "Abu mafi ƙanƙanta kai ka zama bawana da zan sa ya sake kafa kabilun Yakubu, ya kuma farfaɗo da tsirarrun Isra'ila. Zansa ka zama haske ga Al'ummai, domin ka zama cetona ga duk karshen duniya."
\s5
\v 7 Wannan ne abin da Yahweh yace, mai 'Fansar Isra'ila, Mai Tsarkin Nan nasu, gare shi wanda a ka rena ransa, al'ummai suka ƙi shi, da kuma barorin masu mulki, "Sarakuna za su ganka su miƙe, kuma "hakimai za su ganka su rusuna, saboda Yahweh mai aminci ne, wato Mai Tsarkin nan na Isra'ila, wanda ya zaɓe ka."
\s5
\v 8 Ga abin da Yahweh ya faɗi, "A lokacin dana shirya nuna tagomashina zan ba ka amsa, kuma a ranar ceto zan taimake ka; zan yi maka kariya, in kuma bada kai a matsayin alƙawari domin mutanen, domin a sake gina ƙasar, a kuma sake raba gãdon da ya lalace.
\s5
\v 9 Za ka cewa 'yan kurkuku, 'Ku fito waje;' ga waɗanda ke ramuka masu duhu, 'Ku nuna kanku.' Za su yi kiwo a hanyoyi, kuma dukkan sararin gangare zai zama makiyayarsu.
\s5
\v 10 Ba za su ji yunwa ko ƙishi ba, ko kuwa zafi ko rana ta buge su, domin shi mai yi masu jinƙai zai jagorance su; zai bishe su har ga maɓulɓulan ruwa.
\v 11 Daga nan zan sa dukkan tsaunuka su zama hanya, in kuma sa karafku su zama miƙaƙƙu."
\s5
\v 12 Duba, waɗannan za su zo daga nesa, waɗansu daga arewa da yamma; waɗansu kuma daga ƙasar Sinim.
\v 13 Ku yi waƙa, sammai, da murna, duniya; fashe da waƙoƙi ku duwatsu! Gama Yahweh zai ta'azantar da mutanensa, ya kuma ji tausayin nãsa masu tsanancin wahala.
\s5
\v 14 Amma Sihiyona ta ce, "Yahweh ya yashe ni, kuma Ubangiji ya manta da ni."
\v 15 Mace za ta iya mantawa da jaririnta, da ke shan nononta, har ta rasa jin tausayin ɗan da ta haifa? I, za su iya mantawa, amma Ni ba zan manta daku ba.
\s5
\v 16 Duba, na zana sunanki a tafin hannuwa na; katangunki na gabana a kowanne lokaci.
\v 17 'Ya'yanki suna dawowa da sauri, yayin da waɗanda suka lalatar dake suna watsewa.
\v 18 Duba kewaye ki gani, suna tattarowa suna zuwa gare ki. Lallai hakika idan ina raye - wannan Yahweh ne ya faɗa -za ki sa su kamar kayan ado, ki kuma sanya su kamar amarya.
\s5
\v 19 Koda shi ke ke lalatacciya ce kuma kufai, ƙasa ce da dã a ka hallakar, yanzu za ki yiwa mazaunan ƙasar ƙanƙanta, kuma masu takura maki za su yi nisa dake.
\v 20 'Ya'yan da a ka haifa a lokacin da a ka yi maki rashi za su faɗa a kunnuwanki, 'Wurin ya yi mana ƙanƙanta, a yi mana ƙãri, saboda mu zauna a nan.'
\s5
\v 21 Sa'an nan za ki tambayi kanki, 'Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'yan domina? An yi mani rashi kuma ni bakarariya ce, mai gudun hijira da sakakkiya ni ke. Wane ne ya yi renon waɗannan yaran? Duba, ni kaɗai a ka bari; daga ina waɗannan suke?"'
\s5
\v 22 Wannan ne abin da Ubangiji Yahweh yace, "Duba, Zan tayar da hannuna ga al'ummai; Zan tayar da tutar alamata ga mutane. Za su zo da 'ya'yanki maza a hannuwansu su kuma taho da 'ya'yanki mata a kafaɗunsu.
\s5
\v 23 Sarakuna za su zama kamar ubanninki, kuma sarauniyoyinsu kamar masu renonki; za su rusuna maki da fuskokinsu ƙasa suna lasar ƙurar ƙafafunki; kuma za ki san cewa ni ne Yahweh; waɗanda suke jira na ba za su kunyata ba."
\s5
\v 24 Za a iya karɓe ganima daga jarumi, ko a ƙubutar da kamammu daga 'yan ta'adda?
\v 25 Amma ga abin da Yahweh yace, "I, za a karɓe kamammun daga jarumi, kuma a washe ganimar; Gama zan yi tsayayya da magabcinki in kuma ceci 'ya'yanki.
\s5
\v 26 Zan ciyar da masu tsananta maku da naman jikinsu; kuma za su bugu da jininsu, kamar a ce ruwan inabin ne. Sai dukkan 'yan adam su sani cewa Ni, Yaweh, ne mai cetonku da mai fansarku, Maɗaukaki na Yakubu."
\s5
\c 50
\cl Sura 50
\p
\v 1 Wannan ne abin da Yahweh ya faɗi, "Ina takardar saki da na saki mahaifiyarku? ga waɗanne masu bina bashi na sayar daku? Duba, an sayar daku domin laifofinku ne, domin kuma tayarwarku, a ka kori mahaifiyarku.
\s5
\v 2 Me yasa na zo amma babu kowa a wurin? Me yasa na yi kira amma babu wanda ya amsa? Hannu na ya gajarce ga fansar ku ne? Ko babu iko a gare ni da zan ƙuɓutar da ku? Duba, ga tsautawata na busar da teku; na maida koguna hamada; kifayensu suka mutu domin rashin ruwa suka ruɓe.
\v 3 Na suturtar da sararin sama da duhu; Na rufe shi da tsummoki."
\s5
\v 4 Ubangiji Yahweh ya bani harshe kamar na ɗaya daga cikin waɗanda a ka koyar dasu, saboda in yi maganar ƙarfafawa ga gajiyayyu; yana farkar da ni daga safiya zuwa safiya; ya kan tasar da kunnena ga saurarawa kamar waɗanda a ka koyar dasu.
\s5
\v 5 Ubangiji Yahweh ya buɗe kunne na, kuma ban zama mai tayarwa ba, ban kuma koma baya ba.
\v 6 Na bada bayana ga masu bugu na, kuncina kuma ga masu tuge mani gemu; ban ɓoye fuskata ba daga ayyukan ban kunya da tofa miyau ba.
\s5
\v 7 Gama Ubangiji Yahweh zai taimake ni; saboda haka ba zan wulaƙanta ba; don haka na maida fuskata kamar dutsen ƙyastawa, domi na san ba zan kunyata ba.
\s5
\v 8 Shi wanda zai yi mani adalci yana kusa, Wane ne zai yi jayayya da ni? Bari mu tsaya mu fuskanci juna. Wane ne mai tuhuma ta? Bari ya zo kusa da ni.
\v 9 Duba, Ubangiji Yahweh zai taimake ni. Wane ne zai furta ni mai laifi ne? Duba za su koɗe kamar tufafi; ƙwaro mai cin kaya zai cinye su ɗungum.
\s5
\v 10 Wane ne a cikinku ke tsoron Yahweh? Wane ne ke biyayya da muryar bawansa? Wa ke tafiya a cikin zurfafan duhu ba tare da haske ba? Sai ya dogara da sunan Yahweh ya kuma jingina ga Allahnsa.
\s5
\v 11 Ku duba, dukkan ku masu kunna wuta, masu tanadawa kansu cociloli: ku yi tafiya cikin hasken wuta da harsunan wutar da kuka kunna. Wannan ne abin da ku ka karɓa daga gare ni: za ku kwanta a wurin azaba.
\s5
\c 51
\cl Sura 51
\p
\v 1 Ku saurare ni, ku da ke biɗar ayyukkan adalci, ku dake neman Yahweh: Ku dubi dutsen da aka sassaƙo ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka yanko ku.
\s5
\v 2 Ku duba Ibrahim, mahaifinku, da Saratu wadda ta haife ku; gama tun yana mutum guda, na kirawo shi, na albarkace shi na maida shi mai yawa.
\s5
\v 3 I, Yahweh zai ta'azantar da Sihiyona; zai ta'azantar da dukkan kufanta; jejinta ya maida kamar gonar Iden, kuma sararin hamadarta a gefen kogin Yodan ya maida kamar lambun Yahweh; za a sami farinciki da murna a cikinta, godiya, da ƙarar waƙa.
\s5
\v 4 Ku kasa kunne gare ni, mutane na; ku kuma saurare ni mutane na. Gama zan zartar da doka, kuma zan sa hukuncina ya zama haske domin al'ummai.
\v 5 Adalci na ya kusato; ceto na zai fito, kuma hannu na zai hukunta al'ummai; ƙasashen kurmi za su jira ni; domin damtsena za su jira ni da ɗoki.
\s5
\v 6 Ku ɗaga idanuwanku ga sararin sama, sai ku kalli duniya a ƙasa, gama sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za ta shuɗe kamar tufa, kuma mazaunanta za su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai ci gaba har abada, gama adalcina ba zai taɓa daina aiki ba.
\s5
\v 7 Ku saurare ni, ku da kuka san abin da ya ke dai-dai, ku dake da dokokina a zukatanku: kada ku ji tsoron zage-zagen mutane, ko ku karaya saboda wulaƙancinsu.
\v 8 Gama ƙwaro mai cin kaya zai cinye su kamar tufafi, tsutsa kuma ta cinye su kamar ulu; amma adalci na zai dawamma har abada, cetona kuma ga dukkan tsararraki."
\s5
\v 9 Farka, farka, ka suturtar da kanka da ƙarfi, damtsen Yahweh. Tashi kamar kwanakin dã, tsararraki na zamanan dã. Ba kai ba ne ka ragargaza Rahab, kai da ka soke dodon ruwa?
\v 10 Ba kai ka busar da teku ba, ruwayen manyan zurfafa, ka kuma maida tsakiyar teku hanya domin wucewar tsararraki?
\s5
\v 11 Waɗanda Yahweh ya fansa za su dawo su zo Sihiyona tare da kukan farinciki tare kuma da murna har abada a kawunansu; kuma murna da farinciki za su mallake su, baƙinciki da makoki za su tsere daga gare su.
\s5
\v 12 Ni, Ni, ne shi wanda ke ta'azantar da ku. Me ya sa kuke tsoron mutane, waɗanda za su mutu, da 'ya'yan ɗan Adam, wanɗanda aka yi su kamar ciyawa?
\s5
\v 13 Donme ku ka mance da Yahweh wanda ya yi ku, wanda ya miƙar da sammai ya kuma kafa harsasan duniya? Kun kasance a cikin fargaba kowacce rana saboda zafin fushin mai zalunci sa'ad da ya shirya ya yi hallaka. Ina hasalar mai zaluncin?
\s5
\v 14 Wanda ya rusuna ƙasa, Yahweh zai hanzarta 'yantar da shi; ba zai mutu kuma ya je rami ba, ko ya rasa gurasa ba.
\v 15 Gama Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ke motsa teku saboda raƙuman ruwa su yi ruri - Yahweh mai runduna ne sunan sa.
\s5
\v 16 Na sa maganata a bakinka, kuma na rufe ka da inuwar hannuna, domin in dasa sammai, in kafa harsasan duniya, in kuma cewa Sihiyona, 'ku mutanena ne.'"
\s5
\v 17 Farka, farka, tashi tsaye Yerusalem, ke da kika bugu a hannun Yahweh daga kwanon fushinsa; ke da kika bugu daga kwanon, har zuwa dago-dago daga ƙoƙon tangadi.
\v 18 Babu kowa a cikin dukkan 'ya'yanta maza da ta haifa da zai yi mata jagora; babu kowa kuma daga cikin 'ya'yanta maza waɗanda ta rayar da su da zai riƙe hannunta.
\s5
\v 19 Waɗannan matsalolin biyu sun faru dake - wa zai yi makoki tare dake? - kaɗaici da hallaka, da yunwa da takobi. Wane ne zai ta'azantar dake?
\v 20 'Ya'yanki maza sun some; suna kwance a kowacce kwanar tituna, kamar barewa a tarko; suna cike da fushin Yahweh, da tsautawar Allahnki.
\s5
\v 21 Amma yanzu ki ji wannan, ke da a ke muzguna wa ke bugaggiyar nan amma bada ruwan inabi ba
\v 22 Ubangijinki Yahweh, Allahnki wanda ke kãriyar ki ya ce, "Duba, na ɗauki ƙoƙon tangaɗi daga hannun ki -kwanon, wadda shi ne ƙoƙon fushi na. domin kada ki sake shan sa kuma.
\s5
\v 23 Zan sa shi a hannun masu ba ki wuya, waɗanda suka ce maki, 'Ki kwanta a ƙasa don mu yi tafiya bisan ki; kin maida bayanki kamar ƙasar da a ke takawa, kamar kuma tituna domin su yi tafiya akai."
\s5
\c 52
\cl Sura 52
\p
\v 1 Farka, farka, ki sa ƙarfinki, Sihiyona; ki sa sababbin tufafinki, Yerusalem, Birni mai tsarki, gama marasa kaciya da kazamtattu ba za su sake shigar ki ba.
\s5
\v 2 Girgiza kanki daga ƙura; tashi ki zauna, Yerusalem; cire sarƙa daga wuyanki, ɗaurarriya, ɗiyar Sihiyona.
\v 3 Gama ga abin da Yahweh ya faɗi, "An sayar dake a banza, kuma za a fanshe ki ba tare da ƙuɗi ba."
\s5
\v 4 Gama ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi, "Da farko mutane na zun je can Masar domin zama na 'yan kwanaki; Asiriya bada dadewa ba ta muzguna masu.
\s5
\v 5 Yanzu me nake da shi a nan - wannan furcin Yahweh ne - ganin an ɗauke mutane na babu dalili,? Waɗanda suke mulkinsu suka yi ba'a - Wannan furcin Yahweh ne - kuma aka ci gaba da saɓon suna na dukkan rana.
\v 6 Saboda haka mutane na za su san sunana; za su sani a ranan nan cewa ni ne wanda ya ce, "I, Ni ne!"
\s5
\v 7 Yaya kyaun sawayen manzo mai kawo labarai ma su daɗi ya ke akan duwatsu, wanda ke shelar salama. wanda ke riƙe da saƙonni masu daɗi, wanda ya shelar ceto, wanda ya cewa Sihiyona, "Allahnki na mulki!"
\v 8 Ki saurara! masu tsaronki sun ɗaga muryoyinsu, tare suna sowa don murna, gama za su gani, kowanne idonsu, dawowar Yahweh zuwa Sihiyona.
\s5
\v 9 Ku fashe da waƙoƙin farinciki tare, ku duk kufan Yerusalem; Gama Yahweh ya ta'azantar da mutanensa; ya fanso Yerusalem,
\v 10 Yahweh ya buɗe damtsensa mai tsarki a gaban dukkan al'ummai; dukkan duniya za su ga ceton Allahnmu.
\s5
\v 11 Tafi, tafi, fita daga nan; kar ki taɓa wani kazamtaccen abu; tafi daga cikinta; ku tsarkake kanku, ku da ke ɗauke da taskokin Yahweh.
\v 12 Gama ba za ku tafi a cikin hanzari ba, ko ku tafi a cikin fargaba ba; gama Yahweh zai tafi gabanku; kuma Allah na Isra'ila zai kasance a bayanku.
\s5
\v 13 Duba, bawana zai yi aiki da hikima; za ya zama da ɗaukaka sosai, kuma za a ɗaukaka shi,
\v 14 Kamar yadda da yawa suka yi fargaba da kai - kamanninsa ya lalace fiye da kowanne mutum, kuma fasalinsa bai sake yin kama da wani abu na mutum ba.
\s5
\v 15 Duk da haka, bawa na zai yayyafa al'ummai masu yawa sarakuna kuma za su rufe bakunansu saboda shi. Gama abin da ba a taɓa faɗa masu ba, za su gani, kuma abin da ba su taɓa ji ba, za su gane.
\s5
\c 53
\cl Sura 53
\p
\v 1 Wane ne ya gaskata da abin da ya ji daga gare mu, kuma ga wane ne aka bayyana hannun Yahweh?
\v 2 Gama ya yi girma a gaban Yahweh kamar 'yar itaciya, kuma kamar tsiro daga cikin busasshiyar ƙasa; ba shi da wani kyakkyawan jamali ko daraja; sa'ad da muka ganshi, babu wani kyau da zai rinjaye mu.
\s5
\v 3 Mutane suka rena shi suka kuma ƙi shi; mutumin baƙinciki, kuma wanda ya saba da raɗaɗi. Kamar wanda mutane ke ɓoye fuskarsu daga gare shi; aka rena shi; muka kuma ɗauke shi ba a bakin komai ba.
\s5
\v 4 Amma tabbas ya sungumi cututtukanmu ya kuma ɗauke baƙincikinmu; duk da haka mun yi zaton cewa Allah ne ke hukunta shi, Allah ya mazge shi, ya kuma azabta.
\s5
\v 5 Amma an soke shi saboda ayyukan tayarwarmu; aka ragargaje shi saboda zunubanmu. Hukunci domin salamarmu ya kasance a kansa, kuma ta wurin raunukansa muka warke.
\s5
\v 6 Dukkanmu kamar tumaki muka bijire; kowannenmu ya juya zuwa hanyarsa, kuma Yahweh ya ɗora masa laifuffukanmu dukka.
\s5
\v 7 An muzguna masa; duk da haka sa'ad da ya ƙasƙantar da kansa, bai buɗe bakinsa ba; kamar ɗan ragon da za'a kai yanka, kuma kamar tumakin dake tsaye shiru a gaban masu sausaya, haka shi ma bai buɗe bakinsa ba.
\s5
\v 8 Ta wurin wulaƙantarwa da hukuntawa aka kayar da shi; wane ne daga wancan tsara ya sake yin tunani a kansa? Amma an datse shi daga ƙasar masu rai; saboda laifuffukan mutanena aka yanke masa hukunci.
\v 9 Suka sa kabarinsa tare da ma 'yan ta'adda, tare da mai arziki a mutuwarsa, koda ya ke bai yi tawaye ba, ko kuwa wata ruɗarwa a bakinsa.
\s5
\v 10 Duk da haka, nufin Yahweh ne a murkushe shi a sa shi ciwo. Sa'ad da ya mai da kansa baiko domin zunubi, zai ga 'ya'yansa, zai daɗa tsawon kwanakinsa, kuma dalilin Yahweh zai cika ta wurinsa.
\v 11 Bayan wahalar rayuwarsa, zai ga haske kuma ya gamsu da saninsa. Bawana mai adalci zai baratar da mutane da yawa; zai ɗauki laifuffukansu.
\s5
\v 12 Saboda haka zan ba shi nasa kason a cikin yawan mutane, kuma zai raba ganimar da mutane da yawa, domin ya sa kansa ga mutuwa, aka kuma ƙidaya shi tare da masu kurakurai. Ya ɗauki zunuban mutane da yawa ya kuma yi roƙo domin masu kurakurai.
\s5
\c 54
\cl Sura 54
\p
\v 1 "Yi waƙa, ke bakarariya, ke da ba ki haihu ba; ki fashe da waƙar farinciki ki yi kuka da karfi, ke da ba ki taɓa yin naƙudar haihuwa ba. Gama 'ya'yan yasassa sun fi na matar da aka aura," inji Yahweh.
\s5
\v 2 Ki faɗaɗa girman rumfarki, ki baza labulen rumfarki da faɗi; bada ƙwauro ba; ki daɗa tsawon igiyoyinki; ki miƙar da dirkokinki,
\v 3 Gama za ki bazu ta hannun dama da ta hagu, har sai zuriyarki sun mamaye al'ummai sun kuma sake kafa yasassun birane.
\s5
\v 4 Kada ki ji tsoro domin ba za ki ji kunya ba, ko ki karaya ba gama ba za a wulaƙanta ki ba; za ki mance da abin kunyar kuruciyarki da wulaƙancin yashewarki.
\s5
\v 5 Gama wanda ya Yiki shi ne mijinki; Yahweh mai runduna shi ne sunansa. Mai Tsarkin nan na Isra'ila shi ne mai Fansarki; Shi a ke kira Allahn dukkan duniya.
\v 6 Gama Yahweh ya sake kirawo ki a matsayin matar da aka yasar da take kuma cikin ƙunci a ruhu. Kamar matar da a kuruciyarta aka aurota sa'an nan aka ƙi ta," inji Allahnki.
\s5
\v 7 Gama na yashe ki na ɗan lokaci kaɗan, amma da tausayi mai girma zan tattara ki.
\v 8 A sa'ad da na yi fushi mai zafi, na ɓoye fuskata daga gare ki na wani lokaci; amma da madawwamin alƙawari aminci zan yi maki jinƙai - inji Yahweh, wanda ya ƙubutar dake.
\s5
\v 9 Gama wannan kamar ruwayen Nuhu ne a gare ni: kamar yadda na rantse cewa ruwayen Nuhu ba za su sake shan kan duniya ba, saboda haka na rantse cewa ba zan yi fushi dake ko in kwaɓe ki ba.
\v 10 Koda shi ke tsaunuka za su iya faɗuwa kuma tuddai su girgizu, duk da haka madawwamiyar ƙauna ta ba zata rabu da ke ba, ko alƙawarin salamata ya girgiza ba - inji Yahweh, wanda ke yi maki jinƙai.
\s5
\v 11 Mai ƙunci, wanda guguwa ke kora kuma marar ta'aziyya, ku duba, zan sa shiryayyar hanya da dutsen tukoyis, in kuma kafa harsashenki da saffiyes.
\v 12 Zan sa sorayenki da duwatsu masu ƙawa ƙofofinki kuma da duwatsu masu walƙiya, da kuma katangarki ta waje da kyawawan duwatsu.
\s5
\v 13 Sa'an nan Yahweh zai koyar da dukkan 'ya'yanku; kuma salamar 'ya'yanku zata yi yawa.
\v 14 A cikin adalci zan sake kafa ku. Ba za ku ƙara fuskantar tsanantawa ba, gama ba za ku ji tsoro ba; kuma ba abin ban tsoro da zai yi kusa da ku ba.
\s5
\v 15 Duba, idan wani ya tada rikici, ba zai zama daga gare ni ba, duk wanda ya tada rikici da ku, za ku yi nasara a kansa.
\v 16 Duba na halici maƙeri, mai hura garwashin wuta ya ƙera makamai na aikinsa, Ni kuma na hallici mai hallakarwa domin ya hallakar.
\s5
\v 17 Babu makamin da aka ƙera gãba da kai da zai yi nasara; kuma zan kayar da duk wanda ya tuhume ka. Wannan shi ne gădon bayin Yahweh, kuma kariyarsu daga gare ni take. wannan furcin Yahweh ne."
\s5
\c 55
\cl Sura 55
\p
\v 1 Ku zo, kowannen ku dake jin kishin ruwa, ku zo wurin ruwan, ku da baku da kuɗi, ku zo, ku saya, ku ci, ku zo ku sayi ruwan inabi da madara kyauta da arha kuma.
\s5
\v 2 Me ya sa kuke auna azurfa domin abin da ba abinci ba, kuma me yasa kuke aiki domin abin da ba ya ƙosarwa? Ku saurare ni sosai ku ci abin dake da kyau, ku kuma yi farinciki cikin ƙoshi.
\s5
\v 3 Ku juyo da kunnuwanku ku zo gare ni! Ku saurara, domin ku rayu! Zan yi madawwamin alƙawari da ku - ingantacce, amintacciyar ƙauna dana alƙawarta wa Dauda,
\v 4 Duba, na sashi a matsayin shaida ga al'ummai, a matsayin shugaba da mai ba da umarni ga mutane.
\s5
\v 5 Duba, za ku kira ga al'umman da baku san su ba; kuma al'umman da basu san ku ba za su rugo gunku saboda Yahweh Allahnku, Mai Tsarki na Isra'ila wanda ya ɗaukaka ku."
\s5
\v 6 Ku nemi Yahweh tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.
\v 7 Bari mai mugunta ya bar tafarkinsa, haka nan mai zunubi ya bar tunane-tunanensa. Bari ya komo wurin Yahweh, sai ya yi masa jinƙai, da kuma Allahnmu wanda zai gafarta masa a yalwace.
\s5
\v 8 Gama tunane-tunanena ba dai-dai ne da tunane-tunanenku ba, kuma hanyoyinku ba dai-dai da nawa ba - wannan furcin Yahweh ne -
\v 9 gama kamar yadda sammai ke nesa da duniya, haka hanyoyina ke nesa da taku, haka kuma tunane-tunanena ke nesa da tunane-tunanenku.
\s5
\v 10 Gama kamar yadda ruwa da ƙanƙara ke saukowa daga sama, kuma basu komawa sai sun jiƙa ƙasa, susa amfaninta su tsiro su bada 'ya'ya ga manomin da ya yi shuka ya kuma bada abinci ga mai ci,
\v 11 haka nan ne maganata wadda ta fito daga bakina zata kasance - ba za ta komo gare ni a banza ba, amma zata yi nasara a kan abin da na aike ta ta aiwatar.
\s5
\v 12 Gama za ku fita da farinciki, a kuma jagorance ku a cikin salama; Tsaunuka da tuddai za su farfashe da murnar ihu a gabanku, kuma dukkan itatuwan filaye za su tafa hannuwansu.
\v 13 A maimakon ƙayoyin saura, itatuwa masu ganyaye za su fito; kuma a maimakon itacen ƙaya, itacen ganye mai kyau zai fito, kuma zai zama domin Yahweh, domin sunansa, kamar madawwamiyar alama da ba za a tsige ba."
\s5
\c 56
\cl Sura 56
\p
\v 1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi, "Ku yi abin dake dai-dai; ku yi abin da ya kamata; gama cetona ya yi kusa, kuma adalcina na gaf da bayyana.
\v 2 Mai albarka ne mutumin dake yin wannan, wanda kuma ya riƙe shi kam-kam. Ya kiyaye ranar Asabaci, ba ya ƙazamtata, yana kuma kiyaye hannunsa daga aikin mugunta."
\s5
\v 3 Kada bãƙon da ya zama mai bin Yahweh yace, "Yahweh zai tuge ni daga cikin mutanensa." Kada bãbã yace, "Duba, ni busasshen itace ne."
\s5
\v 4 Gama wannan ne abin da Yahweh yace, "Ga bãbãnni da ke kiyaye Asabataina kuma suna zaɓen abin dake faranta mani rai, su kuma riƙe alƙawaraina kam-kam,
\v 5 dominsu ne zan kafa alama a cikin gidana da ganuwata abin tunawa da yafi samun 'ya'ya maza da mata. Zan ba su madawwamin abin tunawa da ba za a taɓa datsewa ba.
\s5
\v 6 Haka ma bãƙin da suka haɗa kansu da Yahweh - su ɓauta masa, waɗanda kuma suke son sunan Yahweh, su ɓauta masa, duk wanda ke lura da Asabaci, da wanda ke kãre kansa daga ƙazamta, da wanda ya riƙe alƙawari na kam-kam
\v 7 - zan kawo su ga tsarkakken tsaunina in sa su yi farinciki a gidan addu'a ta; baye-bayensu na ƙonawa da hadayunsu za su samu karɓuwa a bagadina. Gama za'a kira gidana gidan addu'a domin dukkan al'ummai,
\s5
\v 8 Wannan ne furcin Ubangiji Yahweh, wanda ya tattara korarrun Isra'ila - Zan sake tattaro waɗansu in haɗa tare da su."
\s5
\v 9 Dukkanku namomin jeji na saura, ku zo ku lanƙwame, dukkan ku dabbobin cikin kurmi!
\v 10 Dukkan matsaransu maƙafi ne, ba su fahimta ba. Su dukka karnuka dake shiru ne waɗanda ba su iya yin haushi. Suna mafarki, kuma a kwance suna ƙaunar yin barci.
\s5
\v 11 Karnukan na da babban marmarin ci; Ba za su taba samun abin da ya ishe su ba; su makiyaya ne da ba su da ganewa; dukkansu sun juya ga ta su hanya, kowannensu na ƙyashin mugun ribar kansa.
\v 12 "Zo," suka ce "bari mu sha ruwan inabi da barasa mai karfi," Gobe zai zama kamar yau, rana mai girma fiye da yadda a ke tsammani."
\s5
\c 57
\cl Sura 57
\p
\v 1 Adali ya hallaka, babu wanda ya kula, kuma mutanen amintaccen alƙawari sun taru a can, amma ba wanda ya gane cewa an ɗauke mai adalici ne daga mugunta.
\v 2 Ya shiga cikin salama; suna hutawa a cikin gadajensu, waɗanda ke tafiya a cikin kamilcinsu
\s5
\v 3 Amma ku zo nan, ku 'ya'yan masu sihiri, 'ya'yan mazinaciya da matar da ta karuwantar da kanta. Wane ne kuke yi masa ba'a da murna?
\v 4 Gãba da wa kuke buɗe bakunanku kuke gwalo? Ku ba 'ya'yan tayarwa ba ne, 'ya'yan zamba?
\s5
\v 5 Kuna ɗuma kanku ku da kuke kwance tare ƙarƙashin itacen rimi, ƙarƙashin kowanne koren itace, ku dake kashe 'ya'yanku a cikin rafuffukan da suka ƙone da ƙarƙashin duwatsu masu maratayi
\s5
\v 6 A cikin abubuwa masu laushi na rafin gangare su ne aka ba ku. Wato kayan ibadarku. Kun zuba ruwan baikon abin sha gare su kuka kuma ɗaga baikon hatsi. A waɗannan abubuwan ne ya kamata in ji daɗi?
\s5
\v 7 Kun shirya gadonku a ƙwanƙwolin tsauni; kun kuma tafi sama can domin ku miƙa hadayu.
\v 8 A bayan ƙofa da ƙyaurayen kuka shirya alamunku; kun yashe ni, kun yi wa kanku tsiraici, sai kuka haura sama; kuka yi gadonku da faɗi. Kuka yi yerjejeniya da su; kuka ƙaunaci gadajensu; kuka ga tsiraicinsu.
\s5
\v 9 Kun tafi wurin Molek da mai; kun ruɓanɓanya turare. Kun aika jakadunku nesa; kun gangara zuwa Lahira.
\v 10 Kun gaji saboda doguwar tafiyarku, amma ba ku taɓa cewa, "babu bege ba." Kun sami rai a hannuwanku; saboda haka ba ku karaya ba.
\s5
\v 11 Wane ne kuke damuwa dominsa? Wane ne kuke jin tsoronsa da yawa har ya sa kuka aikata abin ruɗi, harma kun manta da ni ko ku yi tunani akai na? Saboda na yi shiru na dogon lokaci, harma yanzu kun dena jin tsoro na.
\v 12 Zan sanar da dukkan ayyukan adalcinku in kuma faɗi dukkan abin da kuka yi, amma ba za su taimake ku ba.
\s5
\v 13 Sa'ad'da kuka yi kũka, bari tarin gumakanku su 'yantar daku. Maimakon haka iska za ta ɗauke su dukka, wani numfashi zai ɗauke su dukka. Duk da haka wanda ya yi mafaka a cikina zai gaje ƙasar ya kuma mallaki tsarkakken tsaunina.
\s5
\v 14 Zai ce, 'Gina, gina! A shãre hanya! Cire dukkan abin sa tuntuɓe a hanyar mutanena!'"
\v 15 Gama ga abin da mai girma maɗaukaki Kaɗai yace, wanda ke zaune har abada, wanda sunansa tsarki ne, "Ina zaune a maɗaukakin wuri mai tsarki, tare da shi kuma mai karyayye da ƙasƙantaccen ruhu, in falkar da ruhun masu ƙasƙantar da kai, in farkar da zuciyar masu tawali'u.
\s5
\v 16 Gama ba zan yi zargi har abada ba, ko in yi fushi har abada ba, domin ruhun mutum zai some a gabana, rayyukan dana halitta,
\v 17 Saboda da zunubinsa na ribar ƙwãce, Na yi fushi, Na kuma hukunta shi; Na ɓoye fuskata na kuma yi fushi, amma ya koma da baya cikin hanyar zuciyarsa.
\s5
\v 18 Na ga hanyoyinsa, amma zan warkar da shi. Zan jagorance shi in kuma ta'azantar da shi in kuma ƙarfafa waɗanda ke makoki dominsa,
\v 19 kuma ni na hallici diyan lebuna. Salama, salama, ga waɗanda ke nesa da na kusa - inji Yahweh - Zan warkar da su.
\s5
\v 20 Amma miyagu suna kama da haukan teku, wanda ba zai huta ba, kuma ruwayen suna amayar da taɓo da laka.
\v 21 Babu salama domin mugu - inji Allah."
\s5
\c 58
\cl Sura 58
\p
\v 1 Yi kuka da ƙarfi; kada ku dena. Ku ɗaga muryarku kamar kakaki. Ku ta'azantar da mutanena a kan tayarwarsu, da kuma gidan Yakubu a kan zunubansu.
\v 2 Duk da haka suna nema na kullum suna kuma fahariya a sanin hanyoyina, kamar al'umma dake yin aɗalci da ba su yashe da dokokin Allahnsu ba. Suna tambayata hukuncin aɗalci; Suna jin daɗin tunani a kan Allah ya kusance su.
\s5
\v 3 Me yasa muka yi azumi,' suka ce, 'amma ba ka gani ba? Me yasa muka ƙasƙantar da kanmu, amma ba ka kula ba?' Duba, a ranar azuminku, kuna neman jin daɗinku kuna kuma danne dukkan ma'aikatanku,
\s5
\v 4 Duba, kuna azumi ku yi faɗace-faɗace, kuma ku bugu da hannun mugunta; ba za ku yi azumi yau wanda za ku sa a ji muryarku a sama ba.
\v 5 Wannan shi ne lallai irin azumin da zan so: Ranar da wani zai ƙasƙantar da kansa, ya sunkuyar da kansa kamar ciyawa, kuma ya yafa tsummokara da toka a ƙarƙashinsa? Kun tabbata za ku kira wannan azumi, rana wadda ta gamshi Yahweh?
\s5
\v 6 Wannan ba shi ne azumin dana zaɓa ba: A saki miyagun sarƙoƙi, a kwance igiyoyin karkiya, a sa waɗanda aka ragargaza su sami 'yanci, a kuma karya kowacce karkiya?
\v 7 Ko kuma ku raba gurasarku da mayunwata ku kuma shigo da marasa mazauni cikin gidanku ba?" Idan ku ka ga wani tsirara, sai ku suturtar da shi; kuma kada ku ɓoye kanku daga 'yan'uwa.
\s5
\v 8 Sa'an nan hasken ku zai faso a buɗe kamar fitowar rana, kuma warkewarku zata tsiro nan da nan; adalcinku zai sha gabanku, kuma ɗaukakar Yaweh zata biyo bayanku.
\s5
\v 9 Sa'an nan ne za ku yi kira, kuma Yahweh zai amsa; za ku yi kukan neman taimako, kuma zai ce, "Ga ni nan." Idan har kuka ɗauke daga tsakiyarku karkiya, da zargi, da maganganun mugunta,
\v 10 idan ku da kanku kuka tanada wa mayunwata kuma kuka biya buƙatun gajiyayyu; sa'an nan ne haskenku zai keto daga cikin duhu, kuma duhunku zai zama kamar rana tsaka.
\s5
\v 11 Sa'an nan Yahweh zai jagoranceku a kullum kuma ya ƙosar da ku a wuraren da babu ruwa, ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambu mai laima, kuma kamar maɓulɓular ruwa, wanda ruwansa ba ya ƙarewa.
\s5
\v 12 Waɗansunku za su sake gina lalatattun kufaye; za ku tada kufayen tsararraki da yawa; za a kira ku "Masu gyaran Garu," "Masu maido da titunan da za a zauna."
\s5
\v 13 Dãma a ce kun juyo da ƙafafunku daga tafiya a ran Asabaci, kuma daga yin abin son ranku a ranata mai tsarki. Dãma a ce kun kira ranar Asabaci abin farinciki, kuma harma ku kira sha'anin Yahweh tsarki da martaba. Dãma a ce kun girmama ranar Asabacina wurin barin sha'anin kanku, ku kuma bar neman jin daɗin kanku da kuma kun ƙi faɗar maganganun kanku.
\s5
\v 14 Sa'an nan za ku yi farinciki cikin Yahweh; kuma zan sa ku yi yawo a ƙwalƙwolin duniya; zan ciyar daku daga gãdon Yakubu mahaifinku - gama bakin Yahweh ya faɗa."
\s5
\c 59
\cl Sura 59
\p
\v 1 Duba, hannun Yahweh bai gajarce bada ba zai iya ceto ba; kunnensa bai kurmance ba, da ba zai iya ji ba.
\v 2 Ayyukanku na zunubi, duk da haka, su suka raba ku daga Allahnku, kuma zunubanku sun sashi ya ɓoye fuskarsa daga gare ku daga kuma sauraronku.
\s5
\v 3 Gama hannayenku sun haramtu da jini kuma yatsunku da zunubi. Leɓunanku na faɗin ƙarya kuma harsunanku na faɗin tsokana.
\v 4 Babu mai kira cikin aɗalci, kuma babu mai gudanar da ƙararsa cikin gaskiya. Suna dogara da maganganun wofi, suna faɗin ƙarairayi; Suna ɗaukar cikin masifa su kuma haifi zunubi.
\s5
\v 5 Suna ƙyanƙyashe ƙwayayen maciji mai dafi su kuma sãƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci daga ƙwansu zai mutu, kuma idan aka fasa ƙwan, zai ƙyanƙyashe maciji mai dafi.
\v 6 sãƙarsu ba za a iya yin tufafi da su ba, kuma ba za su iya rufe kansu da ayyukansu ba. Ayyukansu ayyukan zunubi ne, kuma ayyukan ta'addanci na cikin hannayensu.
\s5
\v 7 Kafafunsu na gudu gun mugunta, kuma suna gudu domin su zubar da jini. Tunaninsu tunanin zunubi ne; ta'addanci da hallakarwa ne hanyoyisu.
\v 8 Ba su san tafarkin salama ba, kuma babu adalci a tafarkinsu. Sun ƙago karkatattun tafarkuna; Duk wanda ya yi tafiya kan waɗannan tafarku ba zai san salama ba.
\s5
\v 9 Saboda haka adalci ya yi nesa daga gare mu, kuma ayyukan adalci ba su kai wurinmu ba. Mun jira haske, amma muna ganin duhu; muna neman haske amma muna tafiya a duhu.
\v 10 muna laluɓar bango kamar maƙafi, kamar waɗanda basu gani. Mu na yin tuntuɓe da rana kamar da asussuba; a cikin jarumai muna kama da matattun mutane.
\s5
\v 11 Muna ihu kamar damusai da makoki kamar kurciyoyi; muna jiran adalci amma babu ko ɗaya, domin kuɓutarwa, amma tana nesa da mu.
\s5
\v 12 Gama yawan zunubanmu suna gabanmu, kuma zunubanmu na shaida gãba damu; gama laifofinmu na tare damu, kuma mun san zunubanmu.
\v 13 Mun yi tayarwa, muna musanta Yahweh kuma mun juya daga bin Allahnmu. Mun faɗi yaudara da juyin baya, mun ɗauki cikin gunaguni daga zuciya da maganganun ƙarya.
\s5
\v 14 An kori adalci baya, kuma ayyukan adalci sun tsaya nesa; gama gaskiya ta yi tuntuɓe a dandali, na gaske ba zai iya zuwa ba.
\v 15 Aminci ya tafi, kuma wanda ya juya ga barin mugunta ya maida kansa abin zargi. Yahweh ya gani kuma bai ji daɗi ba cewa babu adalci.
\s5
\v 16 Ya ga babu wani mutum, ya kuma yi mamakin cewa babu wanda zai shiga tsakani. Saboda haka damtsensa ya kawo ceto dominsa, kuma ayyukan adalcinsa suka tallafe shi.
\s5
\v 17 Yasa ayyukan adalci su zamar masa sulke da ƙwalƙwalin ceto a kansa. Ya suturta kansa da rigunan ɗaukar fansa ya yafa himma ya zama alkyabbarsa.
\v 18 Ya biya su gwargwadon abin da suka yi, hunkuncin fushi ga maƙiyansa, da ramako ga magabtansa, da kuma horo ga tsibirai wannan ne ladarsu.
\s5
\v 19 Saboda haka za su ji tsoron sunan Yahweh daga yamma, da ɗaukakarsa daga fitowar rana; gama zai zo kamar rafi mai kwararowa, wand numfashin Yahweh ke tunkuɗawa.
\v 20 Mai fansa zai zo Sihiyona, da kuma ga waɗanda suka juyo daga ayyukan tayarwarsu cikin Yakubu - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 21 Ni dai, wannan shi ne alƙawari na da su - inji Yahweh - ruhuna wanda ya ke bisanku, da maganganuna waɗanda na sa a bakinku, ba za su bar bakinku ba, ko su fita daga bakin 'ya'yanku, ko su fita daga bakin 'ya'yan 'ya'yanku ba - inji Yahweh - daga wannan lokaci zuwa har abada."
\s5
\c 60
\cl Sura 60
\p
\v 1 Tashi, haskaka; gama haskenki ya iso, kuma ɗaukakar Yahweh ta taso a bisanki.
\s5
\v 2 Koda shi ke duhu zai rufe duniya, kuma duhu mai kauri ga al'ummai; duk da haka Yahweh zai tashi bisanki, kuma za a ga ɗaukakarsa a bisanki.
\v 3 Al'ummai za su zo ga haskenki, sarakuna kuma ga sheƙin haskenki dake tashi.
\s5
\v 4 Duba ko'ina ki gani. Suna tattarowa domin su zo gare ki. 'Ya'yanki maza za su zo daga nesa, kuma 'ya'yanki mata za su ɗaukosu a hannuwansu.
\v 5 Sa'an nan za ki duba ki cika da farinciki, kuma zuciyarki zata yi ambaliya, domin za a zuba maki yalwar teku, kuma arzikin al'ummai za su zo gare ki.
\s5
\v 6 Ayarin raƙuma za su rufe ki, takarkaran Midiyan da Ifa; dukkansu za su zo daga Sheba; za su kawo zinari da kayan ƙanshi, kuma za su raira waƙar yabon Yahweh.
\v 7 Dukkan garkunan Kedar za a tara maki, ragunan Nebayot za su biya buƙatunki; za su zama karɓaɓun baiko a kan bagadina; kuma zan darjanta gidana mai daraja.
\s5
\v 8 Su wane ne waɗannan dake shawagi kamar girgije, kuma kamar kurciyoyi da za su mafaƙarsu?
\v 9 Ƙasashen gãɓar tekuna suna nema na, kuma jiragen ruwa na Tarshish suna jagoranci, domin su kawo 'ya'yanki maza daga nesa, zinariyarsu da azurfarsu na tare da su, domin sunan Yahweh Allahnki, da kuma domin Mai Tsarkin Nan na Isra'ila, saboda ya daukaka ki.
\s5
\v 10 'Ya'ya maza na bãƙi za su gina garunki, kuma sarakunanki za su yi maki bauta; koda ya ke a cikin fushina na hore ki, duk da haka a cikin alheri na zan yi maki jinƙai.
\v 11 Ƙofofinki ma zasu kasance a buɗe kullum; ba za a rufe su da rana koda dare ba, saboda a kawo arzikin al'ummai da sarakunansu dake masu jagora.
\s5
\v 12 Hakika, al'ummai da masarautu da ba za su ɓauta maki ba za su lalace; waɗannan al'umman za su hallaka kakaf.
\v 13 Ɗaukakar Lebanon za ta zo gare ki, itatuwan fir da makamantansu za su ƙawata masujadata; kuma zan darjanta wurin sa ƙafafuna.
\s5
\v 14 Za su zo gare ki su yi rusuna, 'ya'yan ki maza waɗanda suka ƙasƙantar dake; za su rusuna a ƙafafunki; za su kira ki Birnin Yahweh, Sihiyona ta Mai Tsarkin Nan na Isra'ila.
\s5
\v 15 A maimakon ki ci gaba da zaman wadda aka yashe ta aka ƙita, ba kuma wanda ya wuce ta wurinki, zan maishe ki abin fahariya na har abada, abin murna daga tsara zuwa tsara.
\v 16 Za ki kuma sha madarar al'ummai, kuma za a rene ki a kirjin sarakuna; za ki sani cewa Ni, Yahweh, ni ne Mai cetonki da mai Fansarki. Mai Girman nan na Yakubu.
\s5
\v 17 A maimakon tagulla zan kawo maki zinariya, a maimakon ƙarfe zan kawo azurfa; a maimakon katako, tagulla, kuma a maimakon duwatsu, karfe. Zan sa salama ta zama gwamnoninki, adalci kuma masu mulkinki.
\v 18 Ba za a ƙara jin tashin hankali a ƙasarki ba, ko hallakarwa ko aukawar ɓarna a yankin; amma za ki kira garunki Ceto, ƙofofinki kuma Yabo.
\s5
\v 19 Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba, ko hasken wata ya haskaka a kanki; amma Yahweh zai zama haskenki na har abada, Allahnki kuma shi ne darajarki.
\v 20 Ranarki ba za ta ƙara faɗuwa ba, ko watanki ya dushe ya ɓace ba; Gama Yahweh zai zama haskenki har abada, kuma ranakun makokinki za su ƙare.
\s5
\v 21 Dukkan mutanenki za su zama adalai; za su karɓi mallakar ƙasar na dukkan lokaci, reshen shuka ta da aikin hanuwana, domin a ɗaukaka Ni
\v 22 Ƙarami ɗaya zai zama dubu, mafi ƙanƙanta guda kuma al'umma mai ƙarfi; Ni, Yahweh, zan aiwatar da waɗannan abubuwa da sauri idan lokacin ya yi.
\s5
\c 61
\cl Sura 61
\p
\v 1 Ruhun Ubangiji Yahweh na bisana, domin Yahweh ya shãfe ni in yi shelar labari mai daɗi ga ƙuntattu. Ya aike ni in warkar da waɗanda suka karye a zuci, in yi shelar 'yanci ga kamammu, da kuma buɗewar kurkuku domin waɗanda suke a ɗaure.
\s5
\v 2 Ya aike ni in yi shelar shekarar tagomashi ta Yahweh, ranar ramuwar gayya ta Allahnmu, in kuma ta'azantar da dukkan masu makoki.
\s5
\v 3 Ya aike ni - in ba masu makoki cikin Sihiyona - in ba su rawani a maimakon toka, mai na farinciki a maimakon makoki, alƙyabba ta yabo a maimakon ruhun baƙinciki, domin a kira su rimayen adalci, dashen Yahweh, domin ya sami ɗaukaka.
\s5
\v 4 Za su sạke gina rusassun birane nadã; za su gyara lalatattun wurare. Za su gyara rusassun birane, lalatattu tun daga tsararrakin da suka rigaya suka wuce.
\v 5 Bãƙi za su tsaya su ciyar da garkunanki, 'ya'yan baƙi kuma za su yi maki aiki a gonakinki dana garkunan inabinki.
\s5
\v 6 Za a kira ku firistocin Yahweh; za su kira ku bayi na Allahnmu. Za ku ci wadatar al'ummai, kuma za ku yi fahariya cikin arzikinsu.
\v 7 A maimakon kunyar ki zaki sami riɓi biyu; kuma a maimakon ƙasƙanci za su yi farinciki da rabonsu. Haka za su sami riɓi biyu na rabon ƙasarsu; murna zata zama tasu har abada.
\s5
\v 8 Gama Ni, Yahweh, ina kaunar shari'ar gaskiya, kuma na ƙi fạshi da shari'ar zalunci. Na tabbata zan sạka masu, kuma zan yi madawwamin alƙawari dasu.
\v 9 Zuriyarsu za su zama sanannu a cikin dukkan al'ummai, kuma 'ya'yan tsatsonsu cikin mutane. Dukkan wanda ya gan su zai tabbatar da su, cewa su ne mutanen da Yahweh ya sawa albarka.
\s5
\v 10 Zan yi farinciki sosai cikin Yahweh; cikin Allahna zan yi murna sosai. Gama ya suturce ni da mayafan ceto; ya suturceni da rigar adalci, kamar yadda ango ke ƙawata kansa da rawani, kuma kamar yadda amarya takan ƙawata kanta da kayan ado.
\v 11 Gama kamar yadda ƙasa take fito da dashe-dashenta, kuma kamar yadda gona takan sa shuke-shukenta su tsiro, haka Ubangiji Yahweh zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukkan al'ummai.
\s5
\c 62
\cl Sura 62
\p
\v 1 Saboda Sihiyona ba zan yi shuru ba, saboda da kuma Yerusalem ba zan yi tsit ba, har sai adalcinta ya bayyana da haske sosai, kuma cetonta kamar fitila mai ci bal-bal.
\v 2 Al'ummai za su ga adalcinki, dukkan sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki. Za a kira ki da sabon suna wanda Yahweh zai zaɓa.
\s5
\v 3 Za ki zama kambi mai daraja cikin hannun Yahweh, kuma rawanin sarauta a cikin hannun Allahnki.
\v 4 Ba za a ƙara ce dake, "Yasasshiya" ba; ko ƙasarki ba za a ce da ita, "Watsattsiya ba." Hakika, za a ce dake "Farincikina na cikin ta," ƙasarki kuma "Aurarra," gama Yahweh na farinciki dake, kuma ƙasarki za ta yi aure.
\s5
\v 5 Hakika, kamar yadda saurayi matashi yakan auri 'yar budurwa, haka 'ya'yanki za su aure ki, kuma kamar yadda ango ke farinciki da amaryarsa, Allahnki zai yi farinciki dake.
\s5
\v 6 Na sa masu tsaro a bisa ganuwarki, Yerusalem; ba za su yi shuru ba dare da rana. Ku da kuke tunasshe da Yahweh, kada ku tsagaita.
\v 7 Kada ku ba shi hutu har sai ya sake kafa Yerusalem ya kuma maishe ta abin yabo a duniya.
\s5
\v 8 Yahweh ya yi rantsuwa da hannunsa na dama da kuma hannunsa mai iko, "Hakika ba zan ƙara bada hatsinki ya zama abinci ga maƙiyanki ba. Bãƙi ba za su sha sabon ruwan inabinki ba, wanda ke kika aikinta ba.
\v 9 Gama waɗanda suka yi girbin hatsinsu za su ci su kuma yabi Yahweh, kuma waɗanda suka tsinke 'ya'yan inabisu za su sha ruwan inabin a cikin wurarena masu tsarki."
\s5
\v 10 Ku shigo, ku shigo ta cikin ƙofofi! Ku shirya hanya domin mutane! Ku gina, ku gina babbar hanya! Ku tattara duwatsu! Ku tada tutar alama sama domin al'ummai!
\s5
\v 11 Duba, Yahweh yana sanarwa zuwa ga iyakar duniya, "Ku cewa ɗiyar Sihiyona: Duba, Mai cetonki yana zuwa! Ki gani, ladarsa na tare da shi, kuma sakamakonsa ya sha gabansa."
\v 12 Za su kira ki, "tsarkakakkiyar jama'a; fansassu na Yahweh," kuma za a kira ki "Biɗaɗɗiya; birnin da ba a yashe shi ba."
\s5
\c 63
\cl Sura 63
\p
\v 1 Wane ne wannan da ya ke zuwa daga Idom, yafe da jar tuffa daga Bozara? Wane ne shi cikin kayan sarauta, yana takawa da ƙarfin hali sabili da girman ƙarfinsa? Ni ne, ina maganar adalci da kuma ikon yin ceto.
\v 2 Me yasa kayayyakinka suka yi jạ, kuma me yasa suka yi kamar ka daɗe kana tattaka 'ya'yan inabi a wurin matatsar inabi?
\s5
\v 3 Na tattaka 'ya'yan inabi a matatsar inabi ni kaɗai, kuma babu wani daga cikin al'ummai da ya yi tare da ni. Na tattakesu a cikin fushina na kuma rugurgujesu cikin hasalata. Jininsu ya ɗiɗɗiga a kan kayana kuma ya ɓaɓɓata tufafina.
\v 4 Gama ina hangen ranar ramuwa, kuma shekara domin fansata ta rigaya ta zo.
\s5
\v 5 Na duba, kuma babu wani da zai yi taimako. Na yi mamaki cewa babu mai taimako, amma hannuna ya kawo mani nasara, kuma fushina mai tsanani ya iza ni.
\v 6 Na tattake mutanen a cikin fushina na kuma sa sun bugu cikin hasalata, na kuma zubar da jininsu a fuskar ƙasa.
\s5
\v 7 Zan faɗi amincin ayyukan alƙawarin Yahweh, ayyukan yabo na Yahweh. Zan faɗi dukkan abin da Yahweh ya yi mana, da kuma manyan alherinsa zuwa gidan Isra'ila. Wannan tausayi da ya nuna mana sabili da jinƙansa, da kuma ayyuka masu yawa na amintaccen alƙawarinsa.
\v 8 Gama ya ce, "Hakika sụ mutanena ne, 'ya'ya masu biyayya." Ya zama Mai cetonsu.
\s5
\v 9 Cikin dukkan wahalarsu, shima ya wahala, sai mala'ika daga gare shi ya cecesu. Cikin ƙaunarsa da jinƙansa ya cecesu, ya kuma ɗagasu sama ya kuma bishesu a cikin dukkan zamanan dã.
\s5
\v 10 Amma suka yi tayarwa suka ɓata wa Ruhunsa Mai Tsarki rai. Saboda haka yạ zama abokin gạbarsu ya kuma yaƙesu.
\s5
\v 11 Mutanensa suka yi tunani game da kwanakin dã na Musa. Suka ce, "Ina Allah, wanda ya fito da su daga teku da makiyayin garkensa? Ina Allah, wanda ya sanya Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu?
\s5
\v 12 Ina Allah, wanda yasa darajar ikonsa ya tafiya tare da hannun daman Musa, ya kuma raba ruwa a gabansu, domin ya yiwa kansa suna na har abada?
\v 13 Ina Allah, wanda ya bi da su ta cikin ruwa mai zurfi? Kamar doki mai gudu a hanya mai kyau, ba su yi tuntuɓe ba.
\s5
\v 14 Kamar shanu da suke gangarawa zuwa cikin kwari, Ruhun Yahweh ya ba su hutuwa. Sai ka bida da mutanenka, domin ka yiwa kanka suna mai yabo.
\s5
\v 15 Ka duba daga sama ka kuma kula daga wurinka mai tsarki da kuma maɗaukakin mazauni. Ina himmarka da kuma manyan ayyukanka? Tausayinka da ayyukan juyayinka an hana mana su.
\v 16 Gama kai ne ubanmu, ko da shi ke Ibrahim bai sanmu ba, kuma Isra'ila bai fahimcemu ba, kai, Yahweh, kai ne ubanmu. 'Mai fansarmu' sunanka kenan tun zamanan dã.
\s5
\v 17 Yahweh, me yasa ka sạmu muka bijire daga hanyoyinka ka kuma taurare zukatanmu, har ba mu yi maka biyayya ba? Ka dawo ta dalilin bayinka, kabilun gãdonka.
\s5
\v 18 Mutanenka sun mallaki wurinka mai tsarki na ƙaramin lokaci, amma maƙiyanmu suka tattake ta.
\v 19 Muka zama kamar waɗanda ba ka taɓa mulkinsu ba, kamar waɗanda ba a taɓa kiransu da sunanka ba."
\s5
\c 64
\cl Sura 64
\p
\v 1 Ai ya, dãma ace ka tsaga sammai ka sauko ƙasa! Da tsaunuka sun girgiza a gabanka,
\v 2 kamar yadda wuta ke chinye ƙananan kurmi, ko wuta tasa ruwa ya tafasa. Ai ya, dãma dai sunanka ya zama sananne a wurin magabtanka, domin al'ummai su yi rawar jiki a gabanka!
\s5
\v 3 A dã, da kayi abubuwan ban mamaki waɗanda ba mu zata ba, kạ sauko ƙasa, kuma tsaunuka suka girgiza a gabanka.
\v 4 Tun a zamanin dã ba wanda ya taɓa ji ko ya fahimta ko ya gani da ido wani Allah in banda kai, wanda ya ke yin abubuwa ga wanda ya jira gare shi.
\s5
\v 5 Ka kan zo ka taimaki waɗanda suke farinciki da aikata abin dake na adalci, su dake tunawa da hanyoyinka suna kuma yin biyayya dasu. Kạ yi fushi a lokacin da muka yi zunubi. Ta hanyoyinka kullum za a cecemu.
\s5
\v 6 Gama dukkan mu mun zama kamar wanda ya ƙazamtu, kuma dukkan aikin adalcinmu kamar tsumman jinin haila. Dukkanmu mun yi yaushi kamar ganyaye; kurakuranmu, kamar iska, sun kwashe mu nesa.
\v 7 Babu ko ɗaya mai kira bisa sunanka, wanda ya ke ƙoƙarin ya kama ka. Gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace a cikin hannun kurakuranmu.
\s5
\v 8 Duk da haka, Yahweh, kai ne ubanmu; mu ne yimɓu. Kai ne maginin tukunya; kuma dukkanmu aikin hannunka ne.
\v 9 Kada ka yi fushi sosai, Yahweh, kada koyaushe ka tuna da zunubanmu gãba damu. In ka yarda ka dube mu dukka, jama'arka.
\s5
\v 10 Biranenka masu tsarki sun zama jeji; Sihiyona ta zama jeji, Yerusalem kuma kango.
\v 11 Haikalinmu mai tsarki mai kyau, inda dã ubanninmu suka yabe ka, an rusar da su da wuta, kuma dukkan abin dake da muhimmanci yạna a lalace.
\v 12 Ta ƙaƙa za ka jure wannan, Yahweh? Ta ƙaƙa za kayi shuru ka kuma ci gaba da ƙasƙantar damu?
\s5
\c 65
\cl Sura 65
\p
\v 1 "Na shirya da su same ni su waɗanda ba su tambaya ba; Na shirya domin su same ni su waɗanda ba su neme ni ba. Na ce, 'Ga ni nan! Ga ni nan!' ga al'ummar da ba su kira bisa sunana ba.
\v 2 Na miƙa hannayena dukkan yini zuwa ga mutane masu taurin zuciya, masu tafiya a cikin tafarkin da ba dai-dai ba, waɗanda suka yi tafiya bisa ga tunaninsu da shirye-shiryensu!
\s5
\v 3 Sụ jama'ane dake tozartani a koyaushe, suna miƙa hadayu a cikin gonaki, suna kuma ƙona turare bi sa ginin tuballa.
\v 4 Sukan zauna cikin maƙabarta suna tsaro dukkan dare, suna kuma cin naman alade tare da romon ruɓaɓɓen nama a cikin kwanoninsu.
\s5
\v 5 Suna cewa, "Tsaya nesa, kada ka zo kusa da ni, gama nafi ka tsarki.' Waɗannan abubuwa hayaƙi ne cikin hancina, wutar da take ƙonewa duk yini.
\s5
\v 6 Duba, a rubuce ya ke a gabana: Ni ba zan yi shuru ba, gama zan yi masu sãkayya; zan sãka masu a cikin cinyarsu,
\v 7 domin zunubansu da zunuban ubanninsu tare," Yahweh ya faɗa. "Zan sãka masu domin ƙona turare a bisa tsaunuka da kuma ba'ar da suke yi mani a bisa tuddai. Saboda haka zan auna masu ayyukansu na dã a cikin cinyarsu."
\s5
\v 8 Ga abin da Yahweh ke cewa, "Kamar yadda a ke samun ruwan inabi daga nonon 'ya'yan inabi, lokacin da wani na cewa, 'Kada ka lalata shi, gama akwai abu mai kyau a cikinsa; Ga abin da zan yi domin barorina: Ba zan lallatar da su dukka ba.
\s5
\v 9 Zan fito da zuriya daga Yakubu, kuma daga Yahuda waɗanda za su mallaki tsaunukana. Zaɓaɓɓuna za su mallaki ƙasar, kuma bayina za su zauna a wurin.
\v 10 Sharon zata zama makiyaya domin garkena, kuma Kwarin Ako wurin hutawar garkuna, domin mutanena masu nema na.
\s5
\v 11 Amma ku da kuka yashe da Yahweh, waɗanda suke mantawa da tsaunina mai tsarki, masu shirya teburi domin allahn Sa'a, su kuma cika moɗar ruwan inabi mai gauraye domin Ƙaddara.
\s5
\v 12 Zan ƙaddara ku ga takobi, kuma dukkanku za ku rusuna ga kisa, domin a lokacin da nayi kira, ba ku amsa ba; da nayi magana, ba ku saurara ba. Amma ku ka aikata abin dake mugu a gabana kuka kuma zaɓi ku aikata abin da ba zan ji daɗinsa ba."
\s5
\v 13 Wannan shi ne abin da Ubangiji Yahweh ke faɗi, "Duba, bayina za su ci, amma ku za ku ji yunwa; duba, bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; duba, bayina za su yi murna, amma ku za ku kunyata.
\v 14 Duba, bayina za su yi sowa da farinciki domin murnar zuciya, amma ku za ku yi kuka saboda da zafin zuciya, kuma za ku yi makoki saboda karayar ruhu.
\s5
\v 15 Za ku bar sunanku abin la'antawa domin zaɓaɓɓuna su yi managa; Ni, Ubangiji Yahweh, zan kasheku; Zan kira bayina da wani suna.
\v 16 Duk wanda ya furta albarka ga ƙasar zaiyi albarka ta wurina, Allah na gaskiya. Duk wanda ya yi rantsuwa a duniya zai rantse da ni, Allah na gaskiya, gama matsalolin dã za a manta da su, gama za su ɓoye daga idanuna.
\s5
\v 17 Gama duba, ina dab da halitta sabobbin sammai da kuma sabuwar duniya; kuma al'amuran dã ba za a tuna dasu ba ko su zo ga rai.
\v 18 Amma ku za kuyi murna da farinciki har abada a cikin abin da zan hallita. Ga shi, ina dab da halitta Yerusalem abin farinciki, mutanenta kuma abin fahariya.
\v 19 Zan yi murna bisa Yerusalem in kuma ji daɗi bisa mutanena; kuka da ihu saboda matsala ba za a ƙara ji a cikinta ba.
\s5
\v 20 Ba zai ƙara faruwa ba ɗan jinjiri ya rayu kwanaki kaɗan; ko tsohon mutum ya mutu kafin lokacinsa. Wanda ya mutu yana shekara ɗari za a ce da shi matashi. Duk wanda ya kãsa kaiwa shekara ɗari za a ɗauke shi la'ananne ne.
\v 21 Za su gina gidaje su kuma zauna ciki, kuma za su shuka garkunan inabi su ci amfaninsu.
\s5
\v 22 Ba za su ƙara gina gida wani daban ya zauna ciki ba; ba za su shuka, wani ya ci ba; gama kamar kwanakin itatuwa haka zai zama kwanakin jama'ata. Zaɓaɓɓuna za su kere ayyukan hannuwansu a shekaru.
\v 23 Ba za su yi aiki a banza ba, ko su haifi kaito. Gama sụ 'ya'yan waɗanda Yahweh yasa masu albarkata ne, kuma da zuriyarsu tare da su.
\s5
\v 24 Kafin su kira, Zan amsa; kuma a lokacin da suke magana, Zan ji.
\v 25 Damisa da ɗan rago za su yi kiwo tare, kuma zaki zai ci ciyawa kamar sã; amma ƙura ce za ta zama abincin maciji. Ba za su ƙara cutarwa ko su hallakar a kan dukkan tsaunina mai tsarki," inji Yahweh.
\s5
\c 66
\cl Sura 66
\p
\v 1 Wannan shi ne abin da Yahweh ya ke cewa, "Sama kursiyina ne, ƙasa kuma matashin sawuna. To ina gidan da za ku gina mani? Ina wurin da zan iya hutawa?
\s5
\v 2 Hannuwana suka yi dukkan waɗannan abubuwa; haka waɗannan abubuwa suka zo suka kasance - wannan shi ne abin da Yahweh ya furta. Wannan shi ne mutumin dana zaɓa, karyayye da tawali'u a ruhu, kuma wanda ya ke rawar jiki ga maganata.
\s5
\v 3 Shi wanda ya yanka rago ya kuma kashe mutum; shi wanda ya yi hadayar ɗan rago ya kuma karya wuyan kare; shi wanda ya miƙa baikon hatsi ya miƙa jinin alade; shi wanda ya miƙa turare na tunawa shima yasa wa mugunta albarka. Sun zaɓi hanyoyin kansu, kuma suna fahariya da aikin ƙazamtarsu.
\s5
\v 4 Ni ma haka zan zaɓi masu horonsu; zan kawo a bisansu abin nan da suke tsoro, domin a lokacin dana yi kira, ba bu wanda ya amsa; dana yi magana, ba bu wanda ya saurara. Suka aikata abin da ke mugu a gabana, suka zaɓi su yi abin dake ɓata mani rai."
\s5
\v 5 Ku saurara ga maganar Yahweh, ku da kuke rawar jiki da maganarsa, "Yan'uwanku da suka ƙi ku suka ware ku sabili da sunana suka ce, 'Bari Yahweh ya ɗaukaka, sa'an nan za mu ga murnar ku'; amma za a kunyatar dasu.
\s5
\v 6 Hayaniyar yaƙi na fitowa daga birnin, hayaniya daga haikali, hayaniyar Yahweh yana sãka wa maƙiyansa.
\s5
\v 7 Kafin ta shiga naƙuda, ta haihu; kafin zafi ya abko mata, ta haifi ɗa namiji.
\v 8 Wane ne ya taɓa jin abu kamar haka? Wane ne ya taɓa ganin abubuwa kamar haka? Ana iya haihuwar al'umma a rana ɗaya? Al'umma tana iya haihuwa a ɗan ƙanƙanin lokaci? Duk da haka da Sihiyona ta shiga naƙuda, nan da nan ta haifi 'ya'yanta.
\s5
\v 9 Zan kawo jinjiri a cikin ƙofar fita in kuma hana a haifi jaririn?- Yahweh yana tambaya. Ko ina kawo jariri lokacin haihuwa amma sai in hana shi fitowa?- Allahnka na tambaya."
\s5
\v 10 Ku yi farinciki da Yerusalem ku yi murna dominta, dukkanku masu ƙaunarta; ku yi farinciki da ita, dukkanku da kuke makoki a kanta!
\v 11 Gama za kuyi reno ku kuma ƙoshi; da nonnanta za ku ta'azantu; Gama za ku sha ku ƙoshi ku kuma ji daɗin yalwar ɗaukakarta.
\s5
\v 12 Wannan shi ne abin da Yahweh yace, "Ina gab da zubo wadata bisanta kamar kogi, kuma arzikin al'ummai kamar ambaliyar kogi. Za kuyi reno kusa da ita, a ɗauke ku cikin hannuwanta, a karkaɗa ku da murna a gwuiwarta.
\v 13 Kamar yadda mahaifiya ke ta'azantar da ɗanta, haka ni ma zan ta'azantar daku, kuma za ku ta'azantu a cikin Yerusalem."
\s5
\v 14 Za ku ga wannan, kuma zuciyarku za tayi farinciki, kuma ƙasusuwanku za su tsiro kamar 'yan ciyayi. Za a bayyana hannun Yahweh ga bayinsa, amma zai nuna fushinsa gãba da maƙiyansa.
\s5
\v 15 Gama duba, Yahweh yana zuwa da wuta, kuma karusansa suna zuwa kamar guguwar iska domin ta kawo zafin fushinsa da kwaɓarsa tare da harshen wuta.
\v 16 Gama Yahweh yana shar'anta 'yan adam da wuta da kuma takobinsa. Waɗanda Yahweh ya kashe za su yi yawa.
\s5
\v 17 Sun keɓe kansu suna tsabtace kansu, domin su shiga gonaki, suna bi ta tsakiyar waɗanda suke cin naman alade da abubuwan ban ƙyama kamar kũsu. "Za su kawo ga ƙarshe - wannan shi ne furcin Yahweh.
\s5
\v 18 Gama na san ayyukansu da tunaninsu. Lokaci na zuwa da zan tara dukkan al'ummai da yarurruka. Za su zo su ga ɗaukakata.
\v 19 Zan sa gaggarumar alama a tsakaninsu. Sa'an nan zan aiko da masu tsira daga gare su zuwa ga al'ummai: Zuwa ga Tarshish, Fut, da Lud, masu harbi da suke jan bakansu, zuwa ga Tubal, da Yaban, da kuma zuwa iyakar ƙasashen bakin ruwa da ke nesa inda ba su taɓa ji game da ni ko suka ga ɗaukakata ba. Za su furta ɗaukakata a tsakiyar al'ummai.
\s5
\v 20 Za su dawo da dukkan 'yan'uwanku daga cikin al'ummai, abin baiko ga Yahweh. Za su zo bisa dawakai, da karusai, da cikin kekunan shanu, da bisa jakuna, da kuma bisa raƙuma, zuwa ga tuduna mai tsarki Yerusalem - inji Yahweh. Gama jama'ar Isra'ila za su kawo baiko na hatsi a cikin kwanuka masu tsabta cikin gidan Yahweh.
\v 21 Zan zaɓi wasu daga cikinsu su a matsayin firistoci da kuma Lebiyawa - inji Yahweh
\s5
\v 22 Gama kamar yadda sabuwar sammai da sabuwar duniya da zan halitta za su dawwama a gabana - wannan shi ne furcin Yahweh - haka zuriyarku za su dawwama.
\v 23 Daga wata ɗaya zuwa na gaba, kuma daga wannan Asabaci zuwa na gaba, dukkan mutane za su zo su rusuna mani - inji Yahweh.
\s5
\v 24 Za su fito waje su dubi gawawakin jama'ar da su ka yi mani tayarwa, gama tsutsotsin da za su ci su ba za su mutu ba, kuma wutar da za ta haɗiyesu ba za ta ɓice ba; kuma za su zama abin ƙi ga dukkan masu rai."