ha_ulb/22-SNG.usfm

305 lines
16 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id SNG
\ide UTF-8
\h Waƙar Suleman
\toc1 Waƙar Suleman
\toc2 Waƙar Suleman
\toc3 sng
\mt Waƙar Suleman
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Waƙar Waƙoƙi ta Suleman ce. Matar tana magana da kanta ne
\v 2 Oh, da ma zai sumbace ni da sumbatar bakinsa, matar kuma tana yin magana da mutumin, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi.
\v 3 Manka na shafawa yana da ƙanshi mai daɗi, sunanka na kama da turare mai kwararowa, zuwa ga 'yammatan da kake ƙauna.
\v 4 Ka ɗauke ni mu yi gudu tare. Matar tana yin magana da kanta. Sarkin ya kawo ni cikin ɗakunansa. Matar tana yin magana da mutumin. Muna yin murna; muna farinciki game da kai; bari muyi bukin ƙaunarka; ta fi ruwan inabi. Dai-dai ne waɗansu mata su yi sha'awar ka. Matar tana magana da waɗansu matan.
\s5
\v 5 Ni baƙa ce amma kyakkawa, ku 'yammatan Yerusalem - baƙaƙe kamar rumfunan Kedar, kyawawa kamar labulen Suleman.
\v 6 Kada ku ƙyale ni saboda ni baƙa ce, saboda rana ta gasa ni. 'Ya'yan mahaifiyata suna fushi da ni; sun maida ni mai tsaron garka, amma ban iya tsare tawa garkar ba. Matar tana magana da mutumin.
\s5
\v 7 Ka gaya mani, wanda raina ya ke ƙauna, ina kake kiwon garkenka? Ina kake sa garkenka su huta da tsakiyar rana? Me yasa zan zama kamar wadda take kai da kawo wa a kusa da garkunan abokanka?
\s5
\v 8 Mutumin yana magana da matar. Idan baki sani ba, wadda ta fi sauran mataye kyau, ki bi sawun garkena, ki kiwaci 'yan awakinki kusa da rumfar makiyaya.
\s5
\v 9 Ƙaunatacciyata, ina kwatanta ki da goɗiya a cikin dawakin karusar Fir'auna.
\v 10 Kumatunki kyawawa ne masu ban sha'awa, wuyanki da sarƙoƙin lu'uluai.
\v 11 Zamu yi maki kayan ado na zinariya da azurfa. Matar tana magana da kanta.
\s5
\v 12 Sa'ad da sarkin ya ke kwance a kan shimfiɗarsa, yana jin daɗin ƙanshin turaren.
\v 13 Ƙaunataccena yana kama da jakar mur sa'ad da ya kwanta a tsakanin nonnana.
\v 14 Ƙaunataccena kamar fure ya ke a garkar En Gedi. Mutumin yana magana da matar.
\s5
\v 15 Ki saurara, kina da kyau, ƙaunatacciyata; ki saurara, kina da kyau; idanunki suna sheki.
\s5
\v 16 Matar tana magana da mutumin. Ka saurara, kana da kyau, ƙaunataccena. Shuke-shuke masu taushi sune gadonmu.
\v 17 Kalankuwar gidanmu ta al'ul ce, raftarmu ta fir ce.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Ni furen kallo ce ta Sharon, fure na bakin kwari. Mutumin yana magana da matar.
\v 2 Kamar fure a cikin ƙayoyi, haka ƙaunatacciyata take a cikin 'yammata.
\s5
\v 3 Matar tana magana da kanta. Kamar itacen tsada a cikin itatuwan jeji, haka ƙaunataccena ya ke a cikin samari. Na kan zauna a cikin inuwarsa da jin daɗi mai yawa, ina jin daɗin 'ya'yan itatuwansa.
\v 4 Ya kawo ni gida mai ruwan inabi, tutarsa a kaina ƙauna ce. Matar tana magana da mutumin.
\s5
\v 5 Ka farfaɗo dani da waina ka wartsakar da ni da 'ya'yan tsada, gama ƙaunata ta kasa. Matar tana magana da kanta.
\v 6 Na yi matashin kai da hannunsa na hagu, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
\s5
\v 7 Matar tana magana da sauran mata. Ku 'yammatan Yerusalem, ina so ku yi rantsuwa, da bareyi da batsiyoyi na jeji, ba zaku farka da ƙauna ba sai ta gamsu.
\s5
\v 8 Matar tana magana da kanta. Akwai motsin ƙaunataccena! Saurara, gashi yana zuwa, yana sassarfa a kan duwatsu, yana tsalle a kan tuddai.
\v 9 Ƙaunataccena yana kama da barewa ko ɗan kishimi; duba, ga shi a tsaye bayan katangarmu, yana leƙowa ta taga, yana kallo cikin assabari.
\s5
\v 10 Ƙaunataccena yayi magana da ni yace, "Tashi, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, ki zo mu fita.
\v 11 Duba, hunturu ya wuce, ruwa ya ɗauke kuma ya tafi.
\s5
\v 12 Furanni sun fito a kan ƙasa; lokacin aske itatuwa da kukan tsuntsaye ya zo, kuma an ji motsin kurciyoyi a ƙasarmu.
\v 13 'Ya'yan ɓaure sun nuna, inabi kuma yana sheƙi; sun bayar da ƙanshinsu. Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, mu fita.
\s5
\v 14 Kurciyata a kogon dutse, a cikin wani asirtaccen kogon dutse, bari in ga fuskarki. Bari in ji muryarki, gama muryarki tana da zaƙi, kuma fuskarki abin ƙauna ce." Matar tana magana da mutumin.
\s5
\v 15 Ka kamo mana diloli, 'yan dilolin da suke ɓata gonaki, gama gonarmu tana sheƙi.
\s5
\v 16 Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce; yana kiwo a cikin furanni na annashuwa. Matar tana magana da mutumin.
\v 17 Ka tafi, ƙaunataccena, kafin iskar asubahi ta buso inuwoyi kuma su ɓace. Ka zama kamar barewa ko kamar 'yar batsiya a kan dutse mara laushi.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Ina jiran sa da dare a bisa gadona wato shi wanda raina ya ke ƙauna, na neme shi, amma ban same shi ba.
\v 2 Na ce da kaina, "Zan tashi in shiga cikin birni, a kan hanyoyi da wuraren shaƙatawa; zan neme shi wato shi wanda raina ya ke ƙauna." Na neme shi amma ban same shi ba.
\s5
\v 3 Masu gãdi suka same ni sa'ad da suke aikinsu na zagayawa a cikin birni. Na tambaye su, "Ko kun gan shi wanda raina ya ke ƙauna?
\v 4 Na wuce su kenan sai na sami shi wanda raina ya ke ƙauna. Sai na riƙe shi na hana shi ya tafi sai da na kawo shi gidan su mahaifiyata, a cikin ɗakin wadda ta ɗauki cikina.
\s5
\v 5 Matar tana magana da waɗansu matayen. Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, da bareyi da batsiyoyin jeji, ba zaku tashi ku nuna ƙauna ba sai ta yarda.
\s5
\v 6 Matar tana magana da kanta. Mene ne wancan mai tahowa daga jeji kamar umudin hayaƙi, tare da kayan ƙanshi masu ƙăwa, tare da dukkan hodar da 'yan kasuwa ke sayarwa?
\v 7 Duba, gadon Suleman ne; kewaye da mayaƙa sittin, sojoji sittin na Isra'ila.
\s5
\v 8 Dukkan su gwanayen mãshi ne ƙwararru a wajen yaƙi. Kowanne mutum yana da mashinsa a gefe, shiryayye saboda ta'adanci cikin dare.
\v 9 Sarki Suleman yayi wa kansa kujera ta alfarma da itacen Lebanon.
\s5
\v 10 An yi ginshiƙanta da azurfa; bayanta kuma an yi shi da zinariya, da wurin zama na ƙyallen shunayya. Daga ciki 'yammatan Yerusalem sun yi mata ado na ƙauna. Matar tana magana da matayen Yerusalem.
\v 11 Ku je waje, ku 'yammatan Sihiyona, ku hangi Sarki Suleman, yana ɗauke da rawani wanda mahaifiyarsa ta naɗa masa a ranar aurensa, a cikin ranar da ya ke farinciki a zuciyarsa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Oh, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata; kina da kyau. Idanunki suna kama da kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki kamar garken awaki suna gangarowa daga Dutsen Giliyad.
\s5
\v 2 Haƙoranki kamar kazganyar da a ka yi wa sabon aski, tana fitowa daga wurin yi mata wanka. Kowanne da na kusa dashi, ba wani a cikin su da ya faɗi.
\s5
\v 3 Leɓunanki kamar jan zare; bakinki abin ƙauna ne. Kumatunki suna sheƙi da santsi a cikin lulluɓinki.
\s5
\v 4 Wuyanki yana kama da hasumiyar Dauda da a ka gina da jerin duwatsu, wadda a ka rataye garkuwoyi dubu a kanta, dukkan garkuwoyin sojoji ne.
\v 5 Nonnanki kamar bareyi biyu, tagwayen bareyi, suna kiwo cikin furanni.
\s5
\v 6 Sai asuba ta yi inuwa ta ɓace, zan je dutsen mur da tudun kayan ƙanshi.
\v 7 Ke kyakkyawa ce a kowanne sashi, ƙaunatacciyata babu inda kike da cikas.
\s5
\v 8 Mu tafi tare daga Lebanon, amaryata. Mu tafi tare daga Lebanon; ki tawo daga ƙololuwar Dutsen Amana, daga ƙololuwar Dutsen Senir da Harmon daga kogon zakuna, daga kogon dutsen damisoshi.
\s5
\v 9 'Yar'uwata, kin sace zuciyata, amaryata, kin sace zuciyata, da kika dube ni sau ɗaya kawai, da abin wuyanki guda ɗaya kaɗai.
\s5
\v 10 'Yar'uwata, ƙaunarki tana da kyau, amaryata! Ƙaunarki ta fi ruwan inabi, ƙanshin turarenki yafi kowanne kayan ƙanshi.
\v 11 Amaryata, leɓunanki suna ɗigo da zuma; zuma da madara suna ƙarƙashi harshenki; ƙanshin tufafinki yana kama da ƙanshin Lebanon.
\s5
\v 12 'Yar'uwata, amaryata tana kama da lambun da a ka kulle, kullallen lambu, maɓulɓula wadda a ka hatimce.
\v 13 Rassanki suna kama da rukunin itatuwa masu bada 'ya'ya na musamman, da itacen lalle da nardi,
\v 14 Nardi da saffron da man ƙanshi da kalamus da kirfi da kayan yaji iri-iri da aloyis da dukkan kayan ƙanshi mafi kyau.
\s5
\v 15 Ke maɓulɓular lambu ce, rijiya mai sabon ruwa, ƙorama mai gangarowa daga Lebanon. Matar tana magana da mutumin.
\v 16 Ki taso iskar arewa; ki zo iskar kudu; ki busa a kan lambuna domin kayan yaji suba da ƙanshinsu. Dămă ƙaunataccena zai zo cikin lambunsa yaci zaɓaɓɓun 'ya'yan itatuwa.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Na shigo cikin lambuna, 'yar'uwata, amaryata; na tattaro mur da kayan ƙanshina. Ina shan zumana da saƙarsa; na sha ruwan inabina da madarata. Abokai suna yin magana da mutumin da matar, Ku ci, abokai, ku sha ku bugu da ƙauna. Matar tana magana da kanta.
\s5
\v 2 Ina barci, amma zuciyata ba barci take yi ba. Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa yana cewa, "Ki buɗe mani, 'yar'uwata, abin ƙaunata, kurciyata, ke tawa marar cikas, gama kaina ya jiƙa da raɓa, sumata kuma da danshin dare."
\s5
\v 3 Na tuɓe rigata; in sake maida ita ne? Na wanke ƙafafuna; in sake sawa su yi dauɗa?"
\v 4 Ƙaunataccena yasa hannunsa a kan marfin ƙofa, kuma zuciyata tana wajensa.
\s5
\v 5 Na tashi in buɗe ƙofa saboda ƙaunataccena; hannuwana nashe-nashe da mur, yatsuna da danshin mur, a kan mariƙin ƙofa.
\s5
\v 6 Na buɗe ƙofar saboda ƙaunataccena, amma ƙaunataccena ya juya ya tafi. Zuciyata ta nutsa sa'ad da yayi magana. Na neme shi, amma ban same shi ba; na kira shi amma bai amsa mani ba.
\s5
\v 7 Masu gadi suka tarar dani sa'ad da suke aikinsu na zagaya birni. Suka buge ni suka ji mani ciwo; masu gadin da ke kan ganuwa suka ɗauke gyalena daga gare ni. Matar tana magana da matan birni.
\s5
\v 8 Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, idan kuka haɗu da ƙaunataccena - Me zaku sanar da shi? - ina ciwon ƙauna. Matan birni suna magana da matar.
\s5
\v 9 Da me ƙaunataccenki ya fi wani ƙaunataccen, ke mafi kyau a cikin mata? Me yasa ƙaunataccenki ya fi wani ƙaunataccen, da kika ce mu ɗauki alkawari kamar wannan?
\s5
\v 10 Matar ta na magana da matan birni. Ƙaunataccena wankan tarwaɗa ne yana sheƙi, fitacce ne shi a cikin dubu.
\v 11 Kansa zinariya ce mai tsaftar gaske; sumarsa nannaɗe take baƙa wulik kamar hankaka.
\s5
\v 12 Idanunsa kamar kurciyoyi a bakin ƙoramar ruwa, sun yi wanka da madara, sun tsaya kamar lu'ulu'ai.
\s5
\v 13 Kumatunsa suna kama da kwamin kayan ƙanshi, yana bada ƙanshi mai gamsarwa. Leɓunansa abin kallo ne, nashe-nashe da ruwan mur.
\s5
\v 14 Hannayensa kamar zinariyar da a ka yi wa dajiya da lu'ulu'ai; kwankwasonsa kamar hauren giwar da a ka dalaye da duwatsun saffayar.
\s5
\v 15 Ƙafafunsa kamar ginshiƙan da a ka yi da zinariya tsantsa, fitowarsa kamar Lebanon, zaɓabbe kamar itacen sidar.
\s5
\v 16 Bakinsa yana da zaƙin gaske; shi cikakkaken abin ƙauna ne. Wannan shi ne Ƙaunataccena, kuma wannan shi ne abokina, 'yammatan Yerusalem.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Ina ƙaunataccenki ya tafi, ke mafi kyau a cikin mata? Wacce hanya ƙaunataccenki ya bi, domin mu neme shi tare da ke? Matar tana magana da kanta.
\s5
\v 2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, wurin kwamin kayan ƙanshi, domin yayi kiwo a lambu kuma ya ɗebo furen kallo.
\v 3 Ni ta ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; yana kiwo a cikin furanni da farinciki. Mutumin yana magana da matar.
\s5
\v 4 Kina da kyau kamar Tirzah, abin ƙaunata, ƙauna kamar Yerusalem, mai ban sha'awa da gamsarwa kamar tutocin nasara na sojoji.
\s5
\v 5 Ki juyar da idanunki daga wajena, gama suna ɗaukar mani hankali. Gashinki yana kama da garken awakin da ke gangarowa daga magangarin Giliyad.
\s5
\v 6 Haƙoranki suna kama da tumakin da a ka yi wa aski suna fitowa daga wurin da a ka yi masu wanka. Kowacce da 'ya'uwarta ba wadda take baƙinciki.
\v 7 Kumatunki sumul-sumul a cikin lulluɓinki. Mutumin yana magana da kansa.
\s5
\v 8 Akwai sarauniyoyi sittin, ƙwaraƙwarai tamanin, 'yammata kuwa sun fi a ƙirga.
\v 9 Kurciyata, marar aibi, ita kaɗai ce; ita kaɗai ce ɗiya a wurin mahaifiyarta; tana da tagomashi a wurin matar da ta haife ta. 'Yammata sun gan ta sun kira ta mai albarka; sarauniyoyi da ƙwaraƙwarai ma sun ganta sun yabe ta: Ga abin da sarauniyoyin da ƙwaraƙwaran suka ce,
\s5
\v 10 "Wace ce wannan da ta fito kamar tauraron asubahi, kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai ban sha'awa kamar sojoji da tutocinsu?" Mutumin yana magana da kansa.
\s5
\v 11 Na gangara cikin rukunin itatuwa domin in ga waɗanda suke yin girma a cikin kwari, in gani ko inabi sun yi lingaɓi, in gani ko itatuwan rumman suna yin fure.
\v 12 Na yi murna sosai na ji kamar ina cikin karusar sarki. Ƙawayen matar suna magana da ita.
\s5
\v 13 Ki dawo, ki dawo, ke sahihiyar mata; ki dawo, ki dawo domin mu kalle ki. Matar tana magana da ƙawayenta. Me yasa kuke kallon sahihiyar mata, kamar rawa a tsakanin sojoji biyu?
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Ƙafafunki sun yi kyau sosai a cikin takalmanki, ɗiyar sarki! Tsarin cinyoyinki sun yi kama da lu'ulu'ai, aikin ƙwararre a sassaƙa.
\s5
\v 2 Cibiyarki tana kama da bangaji; dãma kada ta rasa gaurayayyen ruwan inabi. Cikinki yana kama da tarin alkama kewaye da furen kallo.
\s5
\v 3 Nonnanki biyu suna kama da tagwayen bareyi.
\v 4 Wuyanki yana kama da hasumiyar hauren giwa, idanunki tafki ne cikin Heshbon a ƙofar Bat Rabbim. Hancinki kamar hasumiya ce cikin Lebanon wadda ta ke fuskantar Damaskus.
\s5
\v 5 Kanki yana bisanki kamar Karmel; gashin kanki shunayya ne mai duhu-duhu. Kitsonki ya ɗauke hankalin sarki.
\v 6 Ke kyakkyawa ce kuma abin ƙauna, ƙaunatacciyata, tare da jin daɗi!
\s5
\v 7 Kina da tsawo kamar itacen dabino, nonnanki suna kama da kurshen 'ya'yan itace.
\v 8 Na ce, "Ina so in hau wannan itacen dabino; zan kama rassansa." Dãmã nonnanki su zama kamar kurasan zaitun, damã ƙanshin hancinki ya zama kamar 'ya'yan tsada.
\s5
\v 9 Dãmã kitsonki ya zama kamar ruwan inabi mafi kyau, ya malala a hankali domin ƙaunataccena, ya gangara leɓunan waɗanda suke yin barci.
\s5
\v 10 Matar tana magana da mutumin. Ni ta ƙaunataccena ce, yana marmari na.
\v 11 Kazo, ƙaunataccena, bari mu je ƙauye; bari mu kwana a can cikin ƙauyuka.
\s5
\v 12 Bari mu tashi da sassafe mu tafi gonaki; bari mu gani ko inabi sun yi lingaɓi, ko furanninsu sun buɗe, mu gani ko itatuwan rumman sun yi fure. A can zan baka ƙaunata.
\s5
\v 13 Tsiretsire suna ba da ƙanshinsu; akwai dukkan zaɓaɓɓun 'ya'yan itatuwa a ƙofar wurin da mu ke tsaye, da sabo da tsoho, waɗanda na ajiye saboda kai, ƙaunataccena.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Dãmã kai ɗan'uwana ne, wanda a ka yi renon sa da nonnan mahaifiyata. Daga nan duk inda na ganka a waje, sai na sumbace ka, kuma ba wanda zai rena ni.
\s5
\v 2 Zan yi maka jagora in kawo ka gidan mahaifiyata - ita wadda ta koyar da ni. Dã na baka ruwan inabi mai ƙanshi ka sha da wani abin sha daga itatuwan rumman. Matar tana magana da kanta.
\v 3 Na tãda kai da hannun hagunsa hannun damansa kuma yana rungume da ni.
\s5
\v 4 Matar tana magana da waɗansu mata. Ina so ku yi rantsuwa, ku 'yammatan Yerusalem, ba zaku shiga tsakani ku dame mu ba sai mun gama ƙaunarmu.
\s5
\v 5 Matan Yerusalem suna magana. Wace ce wannan da ke fitowa daga cikin jeji, tana jingina da ƙaunataccenta? Matar tana magana da mutumin. Na tashe ka a ƙarƙashin itacen tsada; a can mahaifiyarka ta ɗauki cikin ka; a can ta haife ka, ita ta haife ka.
\s5
\v 6 Ki sani kamar hatimi a zuciyarki, kamar hatimi a hannunki, gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa. Ƙarfin kishi kamar Lahira; harshensa yana ƙonewa; harshen wuta ne mai ci, harshen wutar ya fi kowacce wuta zafi.
\s5
\v 7 Ruwa mai yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, ko rigyawa ma ba zata iya share ta ba. Koda mutum zai bayar da dukkan abin da ya mallaka a gidansa saboda ƙauna, za a rena abin da ya bayar.
\s5
\v 8 'Yan'uwan matar suna magana da junansu. Muna da 'yar'uwa ƙarama, nonnanta ko fitowa basu yi ba. Me zamu yi wa 'yar'uwarmu sa'ad da za a ba da ita aure?
\s5
\v 9 Inda ita ganuwa ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Inda ita ƙofa ce, da sai mu yi mata ado da katakon al'ul.
\s5
\v 10 Matar tana magana da kanta. Ni ganuwa ce, amma nonnana yanzu suna kama da hasumiya ƙayatacciya; Ina kama da mai kawo salama a idanunsa. Matar tana magana da kanta.
\s5
\v 11 Suleman yana da gona a Ba'al Hamon. Ya sa waɗansu su kula da ita. Kowannen su zai kawo masa kuɗi azurfa dubu daga 'ya'yan itatuwanta.
\v 12 Gonata, tawa ce sosai, tana gabana; Suleman, kuɗi azurfa dubu naka ne, azurfa ɗari biyu kuma na masu kula da 'ya'yan itatuwan gonar ne.
\s5
\v 13 Mutumin yana magana da matar. Ke da kike zaune a cikin lambuna, abokaina suna sauraren muryarki; bari nima in ji muryarki.
\s5
\v 14 Matar tana magana da mutumin. Ka yi hanzari ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko batsiya a kan duwatsu inda kayan ƙanshi suke.