ha_ulb/21-ECC.usfm

494 lines
32 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id ECC
\ide UTF-8
\h Littafin Mai Wa'azi
\toc1 Littafin Mai Wa'azi
\toc2 Littafin Mai Wa'azi
\toc3 ecc
\mt Littafin Mai Wa'azi
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Waɗannan ne maganganun malami, zuriyar Dauda kuma sarki a Yerusalem.
\v 2 Malami ya faɗi wannan. "Kamar turirin hayakin raɓa, kamar hurawa a cikin iska, komai na ɓacewa, su na barin tambayoyi masu yawa.
\v 3 Wacce riba ce 'yan'adam suke samu daga dukkan aikin da suke yin aiki tuƙuru akai a ƙarƙashin rana?
\s5
\v 4 Tsara ɗaya ta tafi, wata tsarar kuma ta zo, amma duniya ta tabbata har abada.
\v 5 Rana na fitowa, kuma tana faɗuwa, tana kuma sake saurin komawa wurin da ta fito.
\v 6 Iska na hurawa kudu tana kuma zagayawa kewaye zuwa arewa, koyaushe ta na tafiya kewaye bisa tafarkinta ta kuma sake dawowa.
\s5
\v 7 Dukkan koguna suna gangarawa zuwa teku, amma teku bai taɓa cika ba. Inda koguna su ke tafiya, a can kuma suke sake tafiya.
\v 8 Komai ya zama a gajiye, ba bu kuma wanda zai iya yin bayani. Ido bai ƙoshi da abin da ya ke gani ba, ko kuma kunne ya wadatu da abin da ya ke ji ba.
\s5
\v 9 Duk abin da ya kasance shi ne zai kasance, duk kuma abin da aka taɓa yi shi ne za'a yi. Ba bu wani abu sabo a ƙarƙashin rana.
\v 10 Akwai wani abu game da abin da za'a ce, 'Duba, wannan sabo ne'? Duk abin da ya wanzu ya riga ya wanzu da daɗewa, a lokacin shekarun da suka zo da daɗewa kafin mu.
\v 11 Babu wanda ya ke kamar ya tuna da abubuwan da suka faru a zamanin dã, da abubuwan da suka faru daga bisani sosai da abin da zai faru a nan gaba bai yi kama da za'a tuna da shi ba ma."
\s5
\v 12 Ni ne Malamin, kuma ni ne nake sarki a bisa Isra'ila a Yerusalem.
\v 13 Na miƙa raina ga bincike da nemowa ta wurin hikima duk abin da ake yi a ƙarƙashin sama. Cewa nema gajiyayyen aiki ne da Allah ya ba 'ya'yan ɗan'adam suyi ta aiki da shi.
\v 14 Naga dukkan ayyukan da ake yi a ƙarƙashin rana, kuma duba, dukkan su ɗungum turirin hayaƙi ne da bin iska.
\v 15 Murɗaɗɗe ba za a iya miƙar da shi ba! Abin da ya ɓace ba za a iya ƙidaya wa ba!
\s5
\v 16 Nayi magana da zuciyata cewa, "Duba, na sami hikima fiye da waɗanda suke kafin ni a Yerusalem. Raina yaga babbar hikima da ilimi."
\v 17 Sai na miƙa zuciyata in san hikima da kuma hauka da wawanci. Sai na kai ga fahimtar cewa wannan ma wani yunƙuri ne na kiwon iska.
\v 18 Gama a cikin yalwar hikima akwai ruɗewa sosai, shi kuma wanda ke ƙara ilimi yana ƙara baƙinciki.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Na cewa zuciyata, "Zo yanzu, zan gwada ki da murna. Sai ki more jin daɗinki." Amma duba, wannan ma 'yar taƙaitacciyar iska ce.
\v 2 Game da dariya na ce, "Taɓin hankali ce," game da jin daɗi kuma, "Ina amfanin shi?"
\s5
\v 3 Na nemo a zuciyata yadda zan biya buƙatar marmarina da ruwan inabi. Na bar raina ya bishe ni da hikima kodaya ke har wa yau ina riƙe da wawanci. Na so in samo abu mai kyau da mutane za suyi a ƙarƙashin sama a lokacin kwanakin rayuwarsu.
\s5
\v 4 Na aiwatar da manyan abubuwa. Na gina gidaje domin kaina na kuma dasa garkunan inabi.
\v 5 Na ginawa kaina lambuna da tashoshin shaƙatawa; na dasa dukkan ire-iren itatuwa masu ba da 'ya'ya a cikin su.
\v 6 Na ƙirƙiro tafkunan ruwa domin su bada ruwa ga jejin da ake renon itatuwa.
\s5
\v 7 Na sawo bayi maza da bayi mata; An haifa ma ni bayi a fãdata. Kuma ina da manyan garkunan shanu da garkunan tumaki da awaki, fiye da duk wani sarki da ya yi mulki kafin ni a Yerusalem.
\v 8 Na kuma tarawa kaina azurfa da zinariya, dukiyar sarakuna da larduna. Na samar wa kai na mawaƙa maza da mata - abin farincikin 'ya'yan 'yan'adam - da ƙwaraƙwarai masu yawa.
\s5
\v 9 Sai na zama mafi girma da dukiya fiye da dukkan waɗanda suke kafin ni a Yerusalem, kuma hikimata ta kasance tare da ni.
\v 10 Duk abin da idanuna suka yi marmari, ban hana masu ba. Ban hana wa zuciyata duk wani jin daɗi ba, saboda zuciyata na farinciki cikin dukkan aikin ƙarfina kuma jin daɗi shi ne ladata domin dukkan aikina.
\s5
\v 11 Daga nan na duba dukkan ayyukan da hannuwa na suka aiwatar, da aikin da nayi, amma kuma, kowanne abu turiri ne da yunƙurin kiwon iska. A ƙarƙashin rana babu wata riba a cikin su.
\v 12 Daga nan na juya in yi la'akari da hikima, da kuma hauka da wawanci. Gama me sarki na gaba zai yi wanda zai zo bayan sarki, wanda ba a riga anyi ba?
\s5
\v 13 Daga nan na fãra fahimtar cewa hikima na da daraja bisa wawanci, kamar yadda haske yafi duhu.
\v 14 Mutum mai hikima ya kan yi amfani da idanunsa cikin kansa ya ga inda ya ke tafiya, amma wawa yana tafiya cikin duhu, ko da ya ke na san al'amura iri ɗaya ne ke faruwa da dukkan su.
\s5
\v 15 Daga nan na ce a cikin zuciyata, "Abin da ya fãru da wawa, ni ma zai fãru da ni. To ina ban-banci idan ina da wayau sosai?" Sai na kammala a cikin zuciyata, "Wannan ma turirin hayaƙi ne kawai."
\v 16 Domin mutum mai hikima, kamar wawa, ba a tunawa da shi har dogon lokaci sosai. A cikin kwanaki masu zuwa an riga an manta da komai. Mai wayau na mutuwa kamar yadda wawa ke mutuwa.
\s5
\v 17 Sai rayuwa ta gundure ni saboda dukkan aikin da ake yi a ƙarƙashin rana mugunta ce a gare ni. Wannan kuwa saboda komai turiri ne kawai da yunƙurin kiwon iska.
\v 18 Na ƙi jinin dukkan abin da na aiwatar wanda na aikata a ƙarƙashin rana saboda tilas in bar su baya ga mutumin da zai zo bayana.
\s5
\v 19 Gama wa ya sani ko zai zama mutum mai hikima ko wawa? duk da haka zai zama shugaba bisa komai ƙarƙashin rana wanda aikina da hikimata suka gina. Wannan ma turirin hayaƙi ne.
\v 20 Saboda haka zuciyata ta fãra razana bisa dukkan aikin da nayi a ƙarƙashin rana.
\s5
\v 21 Domin za a sami wanda ya ke aiki tare da hikima, tare da ilimi, da ƙwarewa, amma zai bar duk abin da ya ke da shi ga mutumin da bai yi wani abu kamar sa ba. Wannan ma turirin hayaƙi ne da tsautsayi mai girma.
\v 22 Domin wacce riba taliki ya samu wanda ya yi aiki tuƙuru kuma ya yi ƙoƙari a zuciyarsa ya kammala aikin ƙarfinsa a ƙarƙashin rana?
\v 23 Kowacce rana aikin shi cike da ciwo da gajiya, sa'an nan da dare ransa ba ya samun hutawa. Wannan ma turirin hayaƙi ne.
\s5
\v 24 Babu wani abin da ya fiye wa kowa baya ga ya ci ya sha ya ƙoshi da abin da ke mai kyau cikin aikinsa. Naga cewa wannan gaskiyar ta zo daga hannun Allah ne.
\v 25 Gama wane ne zai iya ci ko ya sami wani irin jin daɗi idan ba daga Allah ba?
\s5
\v 26 Domin ga dukkan wanda ya ke faranta masa rai, Allah na bayar da hikima da ilimi da farinciki. Duk da haka, ga mai zunubi yana bayar da aikin tattarawa da adanawa domin ya bayar da su ga wanda ya ke farantawa Allah rai. Wannan ma ɗungum turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Game da kowanne abu akwai tsaidajjen lokaci, da zamani domin kowanne dalili ƙarƙashin sama.
\v 2 Akwai lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin dasawa da lokacin tuge dashe-dashen,
\v 3 lokacin kashewa da lokacin warkarwa, lokacin yagawa da lokacin ginawa.
\s5
\v 4 Akwai lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa,
\v 5 lokacin zubar da duwatsu da lokacin tattara duwatsu, lokacin rungume wasu mutane da lokacin janyewa daga rungumewa.
\s5
\v 6 Akwai lokacin dubawa domin abubuwa da lokacin tsayawa daga dubawar, lokacin ajiye abubuwa da lokacin zubar da abubuwa,
\v 7 lokacin yaga sutura da lokacin gyara sutura, lokacin yin shiru da lokacin magana.
\s5
\v 8 Akwai lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
\v 9 Wacce riba ma'aikaci ke ci cikin aikin ƙarfinsa?
\v 10 Naga aikin da Allah yaba talikai su kammala.
\s5
\v 11 Allah ya yi kowanne abu ya dace domin nasa lokaci. Ya sa madawwamin lokaci a zukatansu. Amma 'yan'adam ba zasu fahimci ayyukan da Allah ya yi ba, daga farkonsu har ya zuwa ƙarshensu.
\s5
\v 12 Nasan babu abin da ya fiye wa kowa baya ga ya yi farinciki ya kuma yi abin da ke mai kyau dukkan tsawon rayuwarsa -
\v 13 kowa kuma ya ci ya sha, ya kuma fahimci yadda zai ji daɗin abin da ke zuwa daga dukkan aikinsa. Wannan kyauta ce daga Allah.
\s5
\v 14 Nasan cewa dukkan abin da Allah ya yi yana dawwama har abada. Babu abin da za a ƙãra akai ko a ɗauke, saboda Allah ne ya yi domin mutane su kusance shi tare da girmamawa.
\v 15 Kowanne abu da ke wanzuwa ya rigaya ya wanzu; kowanne abu da zai wanzu ya rigaya ya wanzu. Allah ya sa talikai su nemi ɓoyayyun abubuwa.
\s5
\v 16 Na kalli muguntar da ke ƙarƙashin rana, inda ya kamata a yi hukunci, a gurbin adalci, mugunta ce ke wurin.
\v 17 Na ce a zuciyata, "Allah zai shar'anta mai adalci da mugu a lokacin da ya dace domin kowanne al'amari da kowanne aiki."
\s5
\v 18 Na ce a zuciyata, "Allah na gwada talikai ya nuna masu cewa kamar dabbobi suke."
\s5
\v 19 Gama ƙaddarar ɗan'adam da ƙaddarar dabbobi ƙaddara ce iri ɗaya domin su. Mutuwar ɗaya kamar mutuwar ɗayan ce. Lumfashin iri ɗaya ne domin dukkan su. Babu wata daraja game da ɗan'adam fiye da ta dabbobi. Domin kowanne abu ba lumfashi ne kawai ba?
\v 20 Kowanne abu na tafiya wuri ɗaya. Kowanne abu ya zo daga turɓaya, kuma kowanne abu zai koma ga turɓaya.
\s5
\v 21 Wa ya sani ko ruhun ɗan'adam na tafiya sama kuma ruhun dabbobi na tafiya ƙasa cikin ƙasa?
\v 22 Sai kuma na gane cewa babu abin da ya fiye wa kowa banda ya ji daɗin aikinsa, domin wannan ne hidimarsa. Wa zai maido da shi baya yaga abin da ke fãruwa bayansa?
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Na sake yin tunani game da cutarwar da ke faruwa a ƙarƙashin rana. Duba kuma, hawayen mutanen da aka cuta, babu kuma wanda zai ta'azantar da su! Iko na hannun masu cutar da su, babu kuma wanda zai ta'azantar da su!
\s5
\v 2 Sai na yi la'akari da cewa waɗanda suka mutu sun fi waɗanda ke da rai morewa, waɗanda har yau suna raye.
\v 3 Duk da haka, wanda ya fisu dukka morewa shi ne wanda bai riga ya rayu ba, wanda bai riga ya ga ayyukan muguntar da ake yi ba ƙarƙashin rana.
\s5
\v 4 Daga nan naga cewa kowanne aikata aiki da aikin ƙwarewa ya zama kishin maƙwabcin wa ni. Wannan shi ma turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.
\s5
\v 5 Wawa yana naɗe hannuwansa kuma baya aiki, domin wannan abincinsa jikinsa ne.
\v 6 Amma gwamma riba kaɗan tare da aikin natsuwa da hannuwa biyu cike da aikin ƙoƙarin kiwon iska.
\s5
\v 7 Daga nan na sake yin tunani game da ƙarin aikin wofi, ƙarin turirin hayaƙi mai ɓacewa a ƙarƙashin rana.
\v 8 Akwai wani irin mutum da ya ke shi kaɗai. Bai da kowa, ba ɗa ko ɗan'uwa. Babu ƙarshe ga dukkan aikinsa, idanunsa ba su ƙoshi da neman wadata. Yana mamaki, "Domin wa nake wahala ina hana wa kaina jin daɗi?" Wannan ma turirin hayaƙi ne, al'amari marar kyau.
\s5
\v 9 Mutum biyu za su yi aiki fiye da ɗaya; tare za su sami biya mai kyau game da aikinsu.
\v 10 Domin idan ɗaya ya fãɗi, ɗayan zai iya ɗaga abokinsa. Duk da haka, baƙinciki na biye da wanda ke shi kaɗai sa'ad da ya fãɗi idan babu wanda zai iya ɗaga shi.
\v 11 Idan biyu suka kwanta tare, za su iya jin ɗumi, amma ta yaya ɗaya zai ji ɗumi shi kaɗai?
\s5
\v 12 Za a iya fin ƙarfin mutum ɗaya shi kaɗai, amma biyu za su iya yin tsayayya da hari, igiya uku a murɗe ba za su yi saurin tsinkewa ba.
\s5
\v 13 Gwamma wani ya zama matashi talaka amma mai wayau da tsohon sarki wawa wanda ya daina sanin yadda ake sauraron kashedi.
\v 14 Wannan gaskiya ne koda saurayin ya zama sarki daga kurkuku, ko kuma an haife shi talaka a masarautarsa.
\s5
\v 15 Na kalli kowa wanda ya ke da rai kuma yana yawonsa a ƙarƙashin rana, tare da matashin da ke tasowa ya maye gurbinsa.
\v 16 Babu ƙarshen dukkan mutanen da suke so suyi biyayya da sabon sarki, amma daga ba ya yawancin su ba zasu sake yabonsa ba. Tabbas wannan al'amari turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Ka kiyaye takawarka sa'ad da ka je gidan Allah. Ka matsa kusa ka saurara fiye da miƙa hadayar wawaye, waɗanda basu fahimci cewa suna yin abin da ba dai-dai ba.
\s5
\v 2 Kada ka yi saurin magana da bakinka, kada kuma ka yi saurin barin zuciyarka ta fito da wani al'amari a gaban Allah. Allah na sama, amma kai ka na duniya, sai ka bari maganganunka su zama kaɗan.
\v 3 Idan kana da abubuwa da yawa da za ka yi kuma ka da mu a kai, zai yiwu ka sami miyagun mafarkai. Kana ƙara yawan maganganun da zaka furta, kana ƙara yawan abubuwan shirme da zaka iya faɗa.
\s5
\v 4 Sa'ad da ka ɗauki alƙawari ga Allah, kada ka yi jinkirin aikatawa, domin Allah ba ya jin daɗin wawaye. Ka yi abin da ka yi alƙawarin za ka yi.
\v 5 Gwamma kada ka ɗauki alƙawari da ka ɗauki wanda ba ka aiwatar ba.
\s5
\v 6 Kada ka bar bakinka yasa jikinka ya yi zunubi. Kada ka cewa manzon firist, "Wannan alƙawari kuskure ne." Meyasa za ka ba Allah haushi ta wurin alƙawarin ƙarya, kana tunzura Allah ya rushe aikin hannuwanka?
\v 7 Gama a cikin yawan mafarkai, kamar a cikin yawan maganganu, akwai turirin hayaƙi marar ma'ana. Sai ka ji tsoron Allah.
\s5
\v 8 Sa'ad da kaga ana zaluntar matalauci kuma ana karɓe masa hakkinsa da ke dai-dai a cikin lardinka, kada ka yi mamaki kamar cewa babu wanda ya sani, saboda akwai mutane da ke kan mulki waɗanda ke lura da waɗanda ke ƙarƙashinsu, akwai kuma waɗanda suka fisu iko sama da su.
\v 9 Bugu da ƙari, amfanin ƙasar domin kowa ne, sarki kuma kansa yana ɗaukar amfani daga gonakin.
\s5
\v 10 Duk wanda ke ƙaunar azurfa ba zai ƙoshi ba da azurfa, duk kuma wanda ke ƙaunar dukiya a koyaushe yana son ƙãri. Wannan, shi ma, turirin hayaƙi ne.
\v 11 Yadda wadata ke ƙaruwa, haka ma mutanen da ke cin ta. Ina amfanin dukiya ga mai ita baya ga ya yi ta kallon ta da idanunsa?
\s5
\v 12 Barcin ma'aikaci mai daɗi ne, ko ya ci kaɗan ko da yawa, amma dukiyar mai arziki bata barin shi ya yi barci sosai.
\s5
\v 13 Akwai muguntar da na gani a ƙarƙashin rana: dukiyar da mai ita ya ɓoye, ita ce sakamakon azabarsa.
\v 14 Sa'ad da mai arziki ya rasa dukiyarsa ta wurin rashin sa'a, ɗansa, wanda ya haifa, za a bar shi ba komai a hannuwansa.
\s5
\v 15 Yadda mutum ya zo daga mahaifar mahaifiyarsa, haka ma zai tafi tsirara. Ba zai tafi da ko ɗaya daga cikin aikin ƙarfinsa ba cikin hannunsa.
\v 16 Wani mugun abin kuma shi ne yadda mutum ya zo, haka ya ke tafiya. To wacce riba ce ke akwai game da shi wanda ya ke aiki domin iska?
\v 17 A lokacin kwanakinsa ya ci tare da duhu kuma ya ƙuntata kwarai tare da ciwo da fushi.
\s5
\v 18 Duba, abin da na ga yafi kyau da dacewa kuma shi ne mu ci mu sha mu kuma ji daɗin riba daga dukkan aikinmu, yayin da muke aiki tuƙuru ƙarƙashin rana a lokacin kwanakin rayuwarmu wadda Allah ya ba mu. Gama wannan ne hidimar mutum.
\s5
\v 19 Duk wanda Allah ya ba arziki da dukiya da ikon karɓar rabonsa ya kuma yi farinciki cikin aikinsa - wannan kyauta ce daga Allah.
\v 20 Domin ba ya yawan tunawa da kwanakin rayuwarsa, saboda Allah ya sa yana ta hidima da abubuwan da ya ke jin daɗin aiwatarwa.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Akwai wata mugunta da na gani a ƙarƙashin rana, kuma ta yi babban nauyi bisa mutane.
\v 2 Allah zai iya ba mutum arziki, dukiya, da daraja yadda bai rasa wani abin da ya ke marmari ba domin kansa, amma daga nan Allah bai bashi ikon jin daɗin su ba. Maimako, wani daban ke amfani da abubuwansa. Wannan turirin hayaƙi ne, muguwar azaba.
\s5
\v 3 Idan mutum ya zama mahaifin 'ya'ya ɗari kuma ya rayu shekaru masu yawa, yadda kwanakin shekarunsa masu yawa ne, amma idan zuciyarsa bata ƙoshi da abu mai kyau ba kuma ba a bizne shi ba, daga nan na ce gwamma jaririn da aka haifa matacce da shi.
\v 4 Wannan irin jariri ma an haife shi a wofi kuma ya wuce cikin duhu, sunansa kuma ya rage ɓoyayye.
\s5
\v 5 Ko da ya ke wannan ɗan bai ga rana ba ko kuma ya san wani abu, ya huta koda ya ke wancan mutum bai huta ba.
\v 6 Koda mutum zai yi rayuwa shekaru dubu biyu amma bai koyi ya ji daɗin abubuwa masu kyau ba, yana tafiya wuri guda kamar kowa da kowa.
\s5
\v 7 Dukkan aikin mutum domin bakinsa ne, duk da haka ɗanɗanonsa ba ya ƙoshi.
\v 8 Tabbas, wacce moriya mai wayau ya ke da ita bisa wawa? Wacce moriya matalauci ya ke da ita koda ya san yadda zai aiwatar a gaban sauran mutane?
\s5
\v 9 Gwamma a ƙoshi da abin da idanu ke gani da ayi marmarin abin da ɗanɗano ke sha'awa barkatai, wanda shi ma turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska.
\v 10 Duk abin da ya wanzu an riga an ba shi sunansa, kamannin mutum kuma an riga an san shi. Sai ya zama marar amfani ayi saɓani da babban mai hukunta kowa.
\v 11 Ana ƙãra maganganun da ake faɗa, ana ƙãra yawan aikin wofi, to ina moriyar wannan ga mutum?
\v 12 Gama wa yasan abin da ke mai yau domin mutum a cikin rayuwarsa a lokacin, lissafin kwanakinsa na wofi ta inda ya ke wucewa kamar inuwa? Wa zai gayawa mutum abin da zai fãru a ƙarƙashin rana bayan da ya mutu?
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Suna mai kyau ya fi turare mai tsada, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.
\v 2 Gwamma a je gidan makoki da a je gidan biki, domin makoki yana zuwa ga dukkan mutane a ƙarshen rayuwa, to mutanen da ke raye tilas su ɗauki wannan a zuciya.
\s5
\v 3 Ɓacin rai ya fi dariya, domin bayan baƙinciki a fuska sai farinciki a zuciya ya zo.
\v 4 Zuciyar mai hikima na gidan makoki, amma zuciyar wawaye na gidan biki.
\s5
\v 5 Gwamma a saurari tsautawar mai hikima da a saurari waƙar wawaye.
\v 6 Domin kamar ƙarar ƙayoyin da ke ƙonewa a ƙarƙashin tukunya, haka ma dariyar wawaye. Wannan, ma, turirin hayaƙi ne.
\s5
\v 7 Babu shakka ƙwace na sa mutum mai hikima ya zama wawa, kuma cin hanci na ɓãta zuciya.
\s5
\v 8 Gwamma ƙarshen al'amari da farkonsa; kuma mutane masu haƙuri a ruhu sun fi mutane masu girman kai a ruhu.
\v 9 Kada ka yi saurin fushi a ruhunka, domin fushi na zama cikin zukatan wawaye.
\s5
\v 10 Kada ka ce, "Me ya sa kwanakin dã suka fi waɗannan?" Domin ba saboda hikima ka yi wannan tambaya ba.
\s5
\v 11 Hikima, kamar gãdo, mai kyau ce, waɗanda ke ganin rana na moriyar ta.
\v 12 Domin hikima na bada kariya kamar yadda kuɗi ke bada kariya, amma darajar ilimi shi ne hikima na ba da rai ga duk wanda ke da ita.
\s5
\v 13 Yi la'akari da ayyukan Allah: Wa zai miƙar da duk abin da ya tanƙwarar?
\s5
\v 14 Sa'ad da lokutta ke da kyau, ka zauna da murna cikin kyaun nan, amma sa'ad da lokutta suka ɓaci, yi la'akari da wannan: Allah ya bar dukkan su su wanzu gefe da gefe. Domin wannan dalili, babu wanda zai san wani abu da ke zuwa bayansa.
\s5
\v 15 Naga abubuwa masu yawa a cikin kwanakina marasa ma'ana. Akwai mutane masu adalci da ke hallaka duk da adalcinsu, akwai kuma mutane masu mugunta da ke yin tsawon rai duk da muguntarsu.
\v 16 Kada ka zama mai adalcin kai, mai hikima a idanunka. Meyasa za ka hallakar da kanka?
\s5
\v 17 Kada ka zama mai yawan mugunta ko wawanci. Meyasa za ka mutu kafin lokacinka?
\v 18 Yana da kyau ka riƙe wannan hikimar, kuma kada ka saki adalci. Domin talikin da ke da tsoron Allah zai kiyaye dukkan farillansa.
\s5
\v 19 Hikima na da ƙarfi sosai a cikin mutum mai wayau, fiye da shugabanni goma a cikin birni.
\v 20 Babu mutum mai adalci a duniya da ke aikata nagarta kuma bai taɓa yin zunubi ba.
\s5
\v 21 Kada ka saurari dukkan maganar da aka furta, saboda kana iya jin bawanka na la'antar ka.
\v 22 Haka nan kuma, ka sani da kanka cewa a cikin zuciyarka kana yawan la'antar wasu.
\s5
\v 23 Dukkan waɗannan na tabbatar ta wurin hikima, na ce, "Zan yi wayau," amma ya fi abin da zan iya zama.
\v 24 Hikima na nesa kuma da zurfi sosai. Wa zai same ta?
\v 25 Na juya zuciyata in koya kuma in jaraba kuma in biɗi hikima da bayanan zahiri, in kuma fahimci cewa mugunta sakarya ce kuma wawanci hauka ne.
\s5
\v 26 Na gano cewa abin da yafi mutuwa ɗaci shi ne ko wacce mata wadda zuciyarta ke cike da tarkuna da tãrurruka, wadda kuma hannuwanta sarƙoƙi ne. Duk wanda ya gamshi Allah zai kucce daga gare ta, amma zata ɗauke mai zunubi.
\s5
\v 27 "Yi la'akari da abin da na gãno," cewar Malamin. "Ina ta tãra gãnowa bisa gãnowa domin in samo bayanin zahiri.
\v 28 Wannan ne har yanzu nake nema, amma ban same shi ba. A cikin dubu na sami namiji ɗaya mai adalci, amma a cikin dukkan waɗannan ban sami mace ɗaya ba.
\s5
\v 29 Wannan ne kawai na gãno: Cewa Allah ya halicci 'yan'adam dai-dai, amma suka tafi neman wahalhalu da yawa."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Wane ne mutum mai hikima? Wanda ya san abin da al'amuran rayuwa ke nufi? Hikima a cikin mutum nasa fuskarsa ta haskaka, kuma taurin fuskarsa ya canza.
\s5
\v 2 Ina ba ka shawara da ka yi biyayya da dokar sarki saboda rantsuwar Allah na kiyaye shi.
\v 3 Kada ka yi garajen barin gabansa, kada kuma ka goyi bayan abin da ba dai-dai ba, domin sarki na yin abin da ya so.
\v 4 Maganar sarki ke mulki, to wane ne zai ce masa, "Me ka ke yi?"
\s5
\v 5 Duk wanda ke kiyaye dokar sarki yana kaucewa cutarwa. Zuciyar mutum mai hikima takan gane dai-dai lokacin daya dace a aiwatar da abu.
\v 6 Domin ga kowanne al'amari akwai yadda ya dace da lokacin da ya dace, saboda matsalolin mutum manya ne.
\v 7 Babu wanda ya san abin da ke zuwa a gaba. Wane ne zai gaya mashi abin da ke zuwa?
\s5
\v 8 Babu wanda ke mulki bisa lumfashinsa yadda zai tsaida lumfashin, babu kuma wanda ke da iko bisa ranar mutuwarsa. Babu wanda ake sallama daga bataliyar sojoji a lokacin yaƙi, kuma mugunta ba ta kuɓutar da waɗanda ke bayinta.
\v 9 Na gãno dukkan wannan; Na sanya zuciyata ga kowanne irin aiki da ake yi a ƙarƙashin rana. Akwai lokacin da wani taliki ke muzgunawa wani talikin domin cutarwar wannan taliki.
\s5
\v 10 Sai naga ana bizne miyagu a sarari. An ɗauke su daga wuri mai tsarki aka kuma bizne su mutane kuma suka yabe su a cikin birni inda suka aiwatar da ayyukan muguntarsu. Wannan ma wofi ne.
\v 11 Sa'ad da zartar da hukunci gãba da aikin mugunta ba a aiwatar dashi ba da sauri, yana jarabtar zukatan 'yan'adam da su aikata mugunta.
\s5
\v 12 Koda ya ke mai zunubi yana aikata mugunta sau ɗari kuma duk da haka ya yi tsawon rai, duk da haka na sani cewa zai fi kyau ga waɗanda ke girmama Allah, ga waɗanda ke tsayawa a gabansa suna kuma nuna masa girma.
\v 13 Amma ba zai zama da lafiya ba game da mugun mutum; rayuwarsa ba za tayi tsawo ba. Kwanakinsa kamar inuwa ce mai wucewa saboda ba ya darjanta Allah.
\s5
\v 14 Akwai wani turirin hayaƙi marar amfani - wani abun kuma da ake yi a duniya. Abubuwa na faruwa da mutane masu adalci yadda suke faruwa da mutane masu mugunta, kuma abubuwa na faruwa da mutane masu mugunta yadda suke faruwa da mutane masu adalci. Na ce shi ma wannan turirin hayaƙi ne marar amfani.
\v 15 Sai na shawarta murna, saboda mutum ba ya da wani abu a ƙarƙashin rana fiye da ya ci ya sha ya kuma yi murna. Murna ce za ta yi masa rakiya cikin aikin ƙarfinsa domin dukkan kwanakin rayuwarsa waɗanda Allah ya bashi a ƙarƙashin rana.
\s5
\v 16 Sa'ad da na bada zuciyata in san hikima in kuma fahimci aikin da ake yi a duniya, aikin da yawanci ake yi ba bu barci domin idanu koda rana ko da dare,
\v 17 daga nan na yi la'akari da dukkan ayyukan Allah, kuma da cewar mutum ba zai iya fahimtar aikin da ake yi ba a ƙarƙashin rana. Ko ta yaya mutum ya yi aiki tuƙuru domin ya sami amsoshi, ba zai same su ba. Koda ya ke mutum mai hikima zai bada gaskiyar cewa ya sani, lallai bai sani ba.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Gama na yi tunani game da dukkan wannan a raina in sami fahimta game da mai adalci da mutane masu hikima da ayyukansu. Dukkan su suna cikin hannuwan Allah. Babu wanda ya sani wataƙila ƙauna ko ƙiyayya zata zo ga wani.
\s5
\v 2 Kowa na fuskantar ƙaddara ɗaya. Ƙaddara ɗaya ce ke jiran mutane masu adalci da miyagu, masu kyau, masu tsarki da marasa tsarki, da mai miƙa hadayu da wanda ba ya hadaya. Kamar yadda masu kyau suke mutuwa, haka kuma mai zunubi. Kamar yadda mai rantsuwa zai mutu, haka kuma mutumin da ke jin tsoro ya ɗauki wa'adi.
\s5
\v 3 Akwai muguwar ƙaddara ga kowanne abu da ake yi a ƙarƙashin rana, al'amari ɗaya ne ke faruwa da su dukka. Zukatan 'yan'adam na cike da mugunta, kuma hauka na cikin zukatansu yayin da suke raye. Sai bayan wannan su tafi wurin matattu.
\s5
\v 4 Domin duk wanda ya ke tare da dukkan masu rai, akwai bege, kamar yadda kare mai rai yafi mataccen zaki.
\v 5 Domin mutane masu rai sun san cewa za su mutu, amma matattu basu san komai ba. Basu da wani sakamako kuma saboda an manta da tunawa da su.
\s5
\v 6 Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu, da kishinsu, sun ɓace da daɗewa. Ba za su sake samun wuri ba kuma cikin kowanne abu da ake yi ƙarƙashin rana.
\v 7 Ka yi tafiyar ka, ka ci gurasarka da farinciki, ka kuma sha ruwan inabinka da zuciya mai murna, domin Allah ya tabbatar da shagalin ayyuka masu kyau.
\v 8 Bari suturunka koyaushe su zama farare kanka kuma shafaffe da mai.
\s5
\v 9 Ka zauna da murna tare da matar daka ke ƙauna dukkan kwanakin rayuwarka marasa amfani, kwanakin da Allah ya baka a ƙarƙashin rana a zamanin kwanakinka marasa amfani. Wannan ne sakamakonka a rayuwa domin aikinka a ƙarƙashin rana.
\v 10 Duk abin da hannunka ya samu ya yi, ka aikata shi da dukkan ƙarfinka, saboda babu aiki ko bayani ko ilimi ko hikima a Lahira, in da kake tafiya.
\s5
\v 11 Na ga wasu abubuwa na burgewa a ƙarƙashin rana: Tseren ba na mutane masu sauri ba ne. Yaƙin ba na mutane masu ƙarfi ba ne. Gurasa ba ta mutane masu hikima ba ce. Arziki ba na mutane masu fahimta ba ne. Tagomashi ba na mutane masu ilimi ba ne. Maimako, lokaci da sarari ke shafar su dukka.
\v 12 Tabbas, babu wanda ya san sa'ad da lokacinsa zai zo. Kamar yadda ake kama kifi cikin tãru mai haɗari, ko ake kama tsuntsaye cikin tarko, a na yi wa 'ya'yan 'yan'adam tarko da miyagun lokutta da ke faɗowa bisan su farat ɗaya.
\s5
\v 13 Na kuma ga hikima a ƙarƙashin rana ta hanyar da na kalle ta babba a gare ni.
\v 14 Akwai wani ƙaramin birni mai mutane ƙalilan a ciki, wani babban sarki kuma ya zo gãba da shi ya yi masa sansani ya kuma gina manyan ramukan sansani gãba da shi.
\v 15 To a cikin birnin an sami matalauci, mutum mai wayau, wanda ta wurin hikimarsa ya ceci birnin. Duk da haka daga baya, babu wanda ya tuna da wannan mutum matalauci.
\s5
\v 16 Sai na kammala, "Gwamma hikima da ƙarfi, amma aka rena hikimar mutumin nan matalauci, maganganunsa kuma ba a ji su ba."
\s5
\v 17 Maganganun mutane masu hikima da aka furta a hankali an fi jin su fiye da kururuwar duk wani sarki cikin wawaye.
\v 18 Hikima tafi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya zai lalata abubuwan nagarta masu yawa.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Kamar yadda mataccen ƙuda yana sa turare ya yi wãri, haka wawanci ƙarami zai iya shan ƙarfin hikima da daraja.
\v 2 Zuciyar mai hikima na gusawa dãma, amma zuciyar wawa na gusawa hagu.
\v 3 Sa'ad da wawa ke tafiya akan hanya, tunaninsa kasasshe ne, yana tabbatar wa da kowa cewa shi wawa ne.
\s5
\v 4 Idan hankalin mai mulki ya tashi gãba da kai, kada ka bar aikinka. Natsuwa na iya kwantar da fushi mai girma.
\s5
\v 5 Akwai muguntar da na gani a ƙarƙashin rana, wani irin kuskure da ke zuwa daga shugaba:
\v 6 A na ba wawaye matsayin shugabanci, yayin da mutane na ƙwarai ake basu ƙasƙantattun matsayi.
\v 7 Na ga bayi na hawa dawakai, kuma mutane na ƙwarai na tafiya kamar bayi bisa ƙasa.
\s5
\v 8 Duk wanda ya ke ginin rami zai iya faɗawa a ciki, duk kuma sa'ad da wani ya fasa katanga, maciji na iya sarar sa.
\v 9 Duk wanda ke yankan duwatsu za su iya ji masa rauni, kuma mutumin da ke sarar katako yana cikin haɗari dashi.
\s5
\v 10 Idan bãkin ƙarfe ya dushe, kuma mutum bai wãsa shi ba, daga nan tilas ya yi amfani da ƙarfi sosai, amma hikima na bayar da mafita domin nasara.
\v 11 Idan maciji ya yi sara kafin a yi masa makari, daga nan babu wani amfani domin mai makarin.
\s5
\v 12 Maganganun bãkin mutum mai hikima na cike da alheri, amma leɓunan wawa na lanƙwame shi.
\s5
\v 13 Sa'ad da maganganu suka fãra kwararowa daga bãkin wawa, wawanci na fitowa, a ƙarshe kuma bãkinsa na kwararowa da haukan mugunta.
\v 14 Wawa yana ruɓanɓanya maganganu, amma babu wanda ya san abin da ke zuwa. Wane ne ya san abin da ke zuwa bayansa?
\s5
\v 15 Aikin wawaye na gajiyar da su, yadda ba zasu san ma hanyar zuwa gari ba.
\s5
\v 16 Kaiton ki, ƙasa, idan sarkin ki ƙaramin yaro ne, idan kuma shugabanninki suka fara shagali da safe!
\v 17 Amma mai albarka ce ke, ƙasa, idan sarkin ki ɗa ne na ƙwarai, idan kuma shugabannin ki na cin abinci lokacin da ya dãce, domin ƙarfi, kuma ba domin buguwa ba!
\s5
\v 18 Saboda ƙyuya rufin gida na ruftawa, kuma saboda hannaye marasa aiki gida na zuba.
\v 19 Mutane na shirya abinci domin dariya, ruwan inabi yana kawo jin daɗi ga rayuwa, kuɗi kuma na cika buƙata domin komai.
\s5
\v 20 Kada ka la'anci sarki, ko a tunaninka ma, kada kuma ka la'anci mutane masu arziki a cikin ƙuryar ɗakinka. Domin tsuntsuwar sararin sama na iya ɗaukar maganganunka; duk abin da ke da fukafukai zai iya baza al'amarin.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Ka aika da gurasar ka bisa ruwaye, domin za ka same ta kuma bayan kwanaki masu yawa.
\v 2 Ka raba da bakwai, har ma da mutane takwas, domin baka san bala'o'in da ke zuwa bisa duniya ba.
\v 3 Idan giza-gizai suka cika da ruwa, suna juye kansu bisa duniya, idan kuma itace ya fãɗi zuwa kudu ko zuwa arewa, inda itacen ya fãɗi, nan zai tsaya.
\s5
\v 4 Duk wanda ke kallon iska ba zai yi shuka ba, duk kuma wanda ke kallon giza-gizai ba zai yi girbi ba.
\v 5 Kamar yadda ba ka san tafarkin iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri ke girma a cikin mahaifar mai ciki, haka nan kuma ba za ka gãne aikin Allah ba, wanda ya halicci komai.
\s5
\v 6 Da safe ka shuka irinka; har yamma, ka yi aiki da hannuwanka bisa ga buƙata, domin ba ka san wanda zai wadata ba, ko safe ko yamma, ko wannan ko wancan, ko dukkan su biyu zasu yi kyau.
\v 7 Gaskiya haske yana da daɗi, kuma abu mai gamsarwa ne ga idanu su kalli rana.
\v 8 Idan wani ya rayu shekaru masu yawa, bari ya yi murna cikin dukkan su, amma bari ya yi tunani game da kwanakin duhu masu zuwa, domin zasu zama da yawa. Kowanne abu da ke zuwa turirin hayaƙi ne mai wucewa.
\s5
\v 9 Ka yi farinciki, saurayi, a cikin ƙuruciyarka, bari kuma zuciyarka ta yi farinciki cikin kwanakin ƙuruciyarka. Ka runtumi sha'awoyi masu kyau na zuciyarka, da duk abin da ke cikin ganin idanunka. Duk da haka, ka sani cewa Allah zai kawo ka cikin hukunci domin dukkan waɗannan abubuwa.
\v 10 Ka kori fushi daga zuciyarka, ka kuma yi watsi da duk wani zafi a cikin jikinka, saboda ƙuruciya da ƙarfinta turirin hayaƙi ne.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Ka kuma tuna da mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin kwanaki masu wuya su zo, kafin kuma shekarun su iso waɗanda za ka ce, "Ba ni da marmari a cikin su,"
\v 2 ka yi wannan kafin hasken rana da na wata da na taurari su duhunta, baƙaƙen giza-gizai kuma su dawo bayan ruwan sama.
\s5
\v 3 Wannan lokacin ne sa'ad da masu tsaron făda zasu yi rawar jiki, kuma a tanƙwarar da mazaje masu ƙarfi, mataye masu niƙa kuma su tsaya saboda basu da yawa, waɗanda kuma su ke dubawa ta taga sun dena gani sosai.
\s5
\v 4 Wannan lokacin ne sa'ad da aka kulle ƙofofi cikin tituna, ƙarar niƙa kuma ta tsaya, sa'ad da mazaje ke firgicewa ta muryar tsuntsu, kuma muryoyin waƙoƙin 'yanmata suka dushe.
\s5
\v 5 Wannan lokacin ne sa'ad da mazaje suka zama masu jin tsoron tuddai da haɗarorin da ke bisa hanya, sa'ad da kuma itacen almon ke yaɗo, sa'ad da kuma fãri suke jan kansu tare, sa'ad da kuma marmari na ɗabi'a ya karye. Daga nan mutum ya tafi madawwamin gidansa masu makoki kuma su gangara bisa tituna.
\s5
\v 6 Ka tuna da mahaliccinka kafin a datse igiyar azurfa, ko a kwankwatse kwanon zinariya, ko tulu ya farfashe a rafi, ko gargaren murɗo ruwa ya fashe a rijiya,
\v 7 kafin turɓaya ta koma ƙasa in da ta fito, kuma ruhu ya koma ga Allah wanda ya bayar dashi.
\s5
\v 8 "A tsakiyar turirin hayaƙi," a faɗar Malamin, "komai turirin hayaƙi ne mai bajewa."
\v 9 Malamin mai hikima ne kuma ya koyar da mutane ilimi. Ya yi bincike kuma ya yi juyayi kuma yasa misalai masu yawa a jere.
\s5
\v 10 Malamin ya nemi ya rubuta kuma yana amfani da zahirin, cikakkun maganganun gaskiya.
\v 11 Maganganun mutane masu hikima kamar zugazugai suke. Kamar ƙusoshin da ake bugawa da zurfi haka nan maganganun gwanayen da suka ƙware wajen tattara misalansu, wanda makiyayi ɗaya ya koyar.
\s5
\v 12 Ɗana, ka zama a faɗake game da wani abin kuma: yin litattafai da yawa, wanda bai da ƙarshe da yawan bincike yana kawo gajiyarwa ga jiki.
\s5
\v 13 Ƙarshen al'amari bayan an ji komai, shi ne tilas ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye dokokinsa, domin wannan gabaɗaya shi ne aikin ɗan'adam.
\v 14 Domin Allah zai kawo kowanne aiki zuwa hukunci, tare da duk wani ɓoyayyen abu, ko mai kyau ne ko mugu.