ha_ulb/19-PSA.usfm

5465 lines
240 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

This file contains Unicode characters that might be confused with other characters. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id PSA
\ide UTF-8
\h Littafin Zabura
\toc1 Littafin Zabura
\toc2 Littafin Zabura
\toc3 psa
\mt Littafin Zabura
\s5
\c 1
\cl Zabura 1
\p
\v 1 Albarka ga mutum wanda ba ya tafiya a cikin shawarar miyagu ko ya tsaya a hanyar masu zunubi ko ya zauna tare da masu ba'a.
\v 2 Amma yana jin daɗin shari'ar Yahweh, yana nazarinta dare da rana.
\s5
\v 3 Zai zama kamar itacen da aka dasa a gefen ƙorama wanda ya ke bada 'ya'yansa a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, ya kan yi nasara a dukkan abin da ya ke yi.
\s5
\v 4 Mugaye ba haka suke ba, amma suna kamar yayi wanda iska ke kwashewa.
\v 5 Saboda haka mugaye ba zasu tsaya a shari'a ba, ko masu zunubi su taru a wurin adalai ba.
\s5
\v 6 Gama Yahweh yana lura da hanyar adalai, Amma hanyar mugaye za ta lalace.
\s5
\c 2
\cl Zabura 2
\p
\v 1 Meyasa al'ummai suke shirin tayarwa, kuma don me mutane ke ƙulla shawarwarin banza?
\v 2 Sarakunan duniya ke ɗaukar matsayi tare, masu mulki kuma suna shirya maƙarƙshiya tare su yi gãba da Yahweh da kuma zaɓaɓɓensa Almasihu, cewa,
\v 3 "Bari mu tsaga karkiyar da suka ɗora a kanmu, kuma mu jefar da sarƙoƙinsu."
\s5
\v 4 Shi wanda ke zaune a sammai zai yi masu dariya; Ubangiji yana yi masu ba'a.
\v 5 Ya yi masu magana cikin fushinsa da razanar dasu da kuma hasalarsa, cewa,
\s5
\v 6 "Ni da kaina na naɗa sarkina a Sihiyona, tsattsarkan dutsena."
\v 7 Zan yi shelar abin da Yahweh ya furta. Ya ce da ni, "Kai ɗana ne! Wannan rana na zama mahaifinka.
\s5
\v 8 Ka roƙe ni, zan kuma ba ka al'ummai don gãdonka da yankunan duniya domin su zama mallakarka.
\v 9 Za ka mallake su da sandar ƙarfe; za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu, za ka ragargaza su su farfashe."
\s5
\v 10 To yanzu, ku sarakuna, ku ji gargaɗi; ku mai da hankali, ku sarakunan duniya.
\v 11 Ku bauta wa Yahweh da tsoro da kuma murna tare da rawar jiki.
\s5
\v 12 Sumbaci ɗan ko ya yi fushi da ku, zaku mutu ta hanyar fushinsa na ɗan lokaci. Albarka ta tabbata ga dukkan waɗanda ke zuwa gare shi neman mafaka.
\s5
\c 3
\cl Zabura 3
\p
\d Zabura ta Dauda, lokacin da ya guda daga ɗansa Absalom.
\p
\v 1 Yahweh, nawa ne maƙiyana! Nawa ne suka tashi suna gãba da ni.
\v 2 Da yawa suna magana a kaina, "Babu taimako dominsa daga Allah." Selah
\s5
\v 3 Amma kai, Yahweh, kai ne garkuwa a gare ni, darajata, kuma wanda ke tallafar kaina.
\v 4 Na yi kira da muryata ga Yahweh, ya kuma amsa mani daga tsattsarkan dutsensa. Selah
\s5
\v 5 Na kwanta na kuma yi barci; na farka, gama Yahweh ya tsare ni.
\v 6 Ba zan ji tsoron taron mutane waɗanda suka kewaye ni ta kowanne gefe.
\s5
\v 7 Tashi, Yahweh! Ka cece ni, Allahna! Gama zaka buga dukkan abokan gãba har ƙasa; zaka kakkarye haƙuran mugaye.
\v 8 Ceto zai zo daga wurin Yahweh. Bari ya sa wa jama'arsa albarka. Selah
\s5
\c 4
\cl Zabura 4
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; a kayayyakin kiɗa masu tsarkiya. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka amsa mani sa'ad da cikin matsuwa nayi kira, Allahna mai adalci; ba ni hutu a lokacin da nake cikin matsuwa. Ka ji tausayina ka kuma saurari addu'ata.
\s5
\v 2 Ku mutanen nan, sai yaushe zaku daina juya ɗaukakata zuwa kunya? Har yaushe zaku yi ta ƙaunar abubuwan banza kuna kuma cigaba da neman abin da ya ke na ƙarairayi? Selah
\v 3 Amma kun sani Yahweh ne ya keɓe mai tsoronsa don kansa. Yahweh zai ji idan na yi kira a gare shi.
\s5
\v 4 Ku ji tsoro, domin ku daina zunubi! Ku yi nazari a cikin zukatanku a kan gadajenku, kuma ku yi shuru. Selah
\v 5 Ku miƙa hadayun adalci kuna kuma dogara ga Yahweh.
\s5
\v 6 Da yawa sun ce, "Wane ne zai nuna mana wani abu mai kyau? Yahweh, ka ɗaga hasken fuskarka a kanmu.
\v 7 Ka ba zuciyata farinciki fiye da na waɗanda ke da wadatar hatsi da sabon ruwa inabi.
\v 8 A cikin salama zan kwanta har barci ya kwashe ni, domin kai kaɗai ne, Yahweh, ka kiyaye ni cikin lafiya sosai.
\s5
\c 5
\cl Zabura 5
\p
\d Domin shugaban mawaƙa da kayayyakin kiɗa na bushe-bushe. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka saurari kira na zuwa gare ka, Yahweh; kayi tunani a kan nishe-nishena.
\v 2 Ka saurari muryar kirana, sarkina da Allahna, gama a gare ka nake yin wannan addu'ar.
\v 3 Yahweh, da safe kaji kukana; da safe zan kawo rokona gare ka in kuma jira ka.
\s5
\v 4 Gaskiya ne kai ba Allahn dake yarda da mugunta ba ne; ko mugayen mutane su zama bãƙinka.
\v 5 Masu fahariya ba zasu tsaya a gabanka ba; kana ƙin dukkan mugaye.
\v 6 Ka kan hallakar da maƙaryata; Yahweh yakan rena masu ta da hankali da mayaudaran mutane.
\s5
\v 7 Amma ni, saboda babban alƙawarin ƙaunarka, zan zo cikin gidanka; in kuma rusuna maka da bangirma a tsattsarkan haikalinka.
\v 8 Ya Ubangiji, ka bida ni in aikata adalcinka domin abokan gãbana; ka kuma fayyace mani hanyarka a gabana.
\s5
\v 9 Gama babu gaskiya a cikin bakinsu; abubuwansu mugunta ne; harshensu kamar buɗaɗɗen kabari ya ke; suna yaudara da harshensu.
\v 10 Ka furta su masu laifi ne, Allah; bari shirye-shiryensu su zama dalilin faɗuwarsu! Ka kore su sabili da yawan zunubansu, da kuma tayarwar da suke yi maka.
\s5
\v 11 Amma bari dukkan waɗanda suka fake gare ka su yi farinciki; bari kullum su yi ta murna don kana kiyaye waɗanda ke ƙaunar sunanka.
\v 12 Gama ka sawa masu adalci albarka, Yahweh; zaka kewaye su da alheri kamar garkuwa.
\s5
\c 6
\cl Zabura 6
\p
\d Domin shugaban mawaƙa akan kayan kiɗa masu tsarkiya da aka shirya wa Sheminit. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, kada ka tsauta mani a lokacin fushinka ko ka hukunta ni da fushinka.
\v 2 Ka yi mani jinƙai, Yahweh, gama na tafke sarai, ka warkar da ni, Yahweh, domin ƙasusuwana na makyarkyata.
\s5
\v 3 Raina yana damuwa ƙwarai. Amma kai, Yahweh - har sai yaushe wannan zai ci gaba?
\v 4 Ka zo, Yahweh! ka kuɓutar da ni. Ka cece ni domin alƙawarin amincinka!
\v 5 Gama a cikin mutuwa ba a tunawa da kai. Don wane ne zai yi maka godiya a lahira?
\s5
\v 6 Na gaji tilis saboda baƙinciki. Dukkan dare gadona ya kan jiƙe da hawayena; Na jiƙa matashin kaina da hawayena.
\v 7 Idanuna sun yi kumburi saboda kuka; sun zama marasa ƙarfi saboda dukkan abokan gãbana.
\s5
\v 8 Ku tafi daga wuri na, dukkan ku masu aikin mugunta; Gama Yahweh ya ji kukana. Yahweh ya ji rokona don jinƙai;
\v 9 Yahweh ya amsa mani addu'ata.
\v 10 Dukkan abokan gãbana zasu sha kunya da babbar damuwa. Zasu juya baya tare da babban ƙasƙanci.
\s5
\c 7
\cl Zabura 7
\p
\d Haɗe-haɗen waƙoƙin Dauda wanda ya yi wa Yahweh game da maganganun Kush Benyamine.
\p
\v 1 Yahweh Allahna, na sami mafaka a wurinka! Ka cece ni daga dukkan masu nema na, ka ƙwace ni.
\v 2 Idan ba haka ba kuwa zasu ɗauke ni kamar zaki, su yayyaga ni har babu wani da zai kawo mani ceto.
\s5
\v 3 Yahweh Allahna, ban aikata abin da maƙiya suka ce nayi ba; babu rashin adalci a cikin hannuwana.
\v 4 Ban yi wani abu da ba dai-dai ga kowa ba wanda muke zaman salama dani, ko da ga wani mai gãba da ni.
\s5
\v 5 Idan ba gaskiya nake faɗa ba bari maƙiya su nemi raina har su kama shi; bari ya taka rayayyen jikina a ƙasa ya bar ni da kunyata a ƙura. Selah
\s5
\v 6 Ka tashi, Yahweh, cikin fushinka; tashi kayi gãba da hasalar abokan gãbana; ka tashi domina ka aiwatar da alƙawarin amincinka da aka sanka da shi.
\v 7 Dukkan kabilu sun taru a gabanka; ka sake ɗaukar wurinka a bisan su.
\s5
\v 8 Yahweh, kai ne alƙalin dukkan alummai; ka 'yantar da ni, Yahweh, gama ni adali ne bani da laifi, Maɗaukaki.
\v 9 Bari mugun abu na masu aikata mugunta ya zo ƙarshe, amma ka tabbatar da adalan mutane, Allah mai adalci, kai kake gwada zukata da tunane-tunane.
\s5
\v 10 Kariyata tana zuwa daga Allah, wanda ya ke ceton masu yin adalci a zuciya.
\v 11 Allah ne alƙali mai adalci, Allah wanda ya ke jin haushi a kowacce rana.
\s5
\v 12 Idan mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa ya kuma shirya bakansa don yaƙi.
\v 13 Zai shirya kayayyakin faɗa gãba da shi; zai auna kibansa masu wuta.
\s5
\v 14 Ka yi tunani akan wanda ya ɗauki ciki da mugunta, wanda ya shirya aiwatar da mugunta, wanda ya haifi cutar ƙarairayi.
\v 15 Yana haƙa rami mai zurfi har kuma ya faɗa ramin da ya gina.
\v 16 Mugun shirin da yayi ya koma a kansa kenan, don rikicin ya sauka a kansa kenan.
\s5
\v 17 Zan gode wa Yahweh saboda adalcinsa; zan raira yabo ga Yahweh Maɗaukaki.
\s5
\c 8
\cl Zabura 8
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; tsari na salon waƙar bagitte. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh Ubangijinmu, yaya girman sunanka ya ke a dukkan duniya, ka bayyana ɗaukakarka a cikin sammai.
\v 2 Daga cikin bakin yara da jarirai ka shirya yabo domin maƙiyanka, domin ka tsai da abokan gãbarka da ramako.
\s5
\v 3 Sa'ad da na duba sararin sammai, wanda yatsunka suka yi, wata da taurari, waɗanda kasa a wuraren zamansu.
\v 4 Mene ne mahimmancin 'yan adam har da kake tunawa da su, ko mutune har da kake lura da su?
\v 5 Duk da haka ka maida su ƙasa kaɗan da halittun dake sama ka kuma naɗa su da ɗaukaka da daraja.
\s5
\v 6 Ka sa shi yayi mulkin dukkan abin da kayi da hannuwanka; ka ɗora dukkan abubuwa a ƙarƙashin ƙafafuwansa:
\v 7 dukkan tumaki da shanu har ma da namomin jeji,
\v 8 tsuntsayen sammai da kifayen teku da dukkan halittun dake cikin tekuna.
\s5
\v 9 Yahweh Ubangijinmu yaya girman sunanka ya ke a cikin dukkan duniya!
\s5
\c 9
\cl Zabura 9
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsara bisa salon Mut Labben. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Zan yi maka goɗiya Yahweh da dukkan zuciyata; zan furta dukkan abubuwa masu ban mamaki da ka yi.
\v 2 Zan yi murna da farinciki da kai; zan raira waƙar yabo ga sunanka Maɗaukaki!
\s5
\v 3 Lokacin da magabtana suka ja da baya, sun faɗi sun mutu a gabanka.
\v 4 Gama kai ka tsare ni; ka zauna a kan kursiyinka, mai shari'ar adalci!
\s5
\v 5 Ka kwaɓi al'ummai, ka kuma hallakar da mugaye; ka kawar da sunayensu har abada abadin.
\v 6 An rugurguje abokan gãba kamar kangaye a lokacin da aka lalata biranensu. Dukkan tunawa dasu ya ƙare.
\s5
\v 7 Amma Yahweh ka kasance har abada; ka kafa kursiyinka domin yin shari'a.
\v 8 Zan yi mulkin dukkan duniya da adalci, kuma zai yi wa mutane shari'a da gaskiya.
\s5
\v 9 Yahweh kuma zai zama mafaka ga waɗanda ake zalunta, wurin ɓuya a lokatan wahala.
\v 10 Waɗanda suka san sunanka zasu dogara gare ka, domin kai ne, Yahweh, ba za ka yi watsi da duk wanda ya neme ka ba.
\s5
\v 11 Ku yi waƙar yabo ga Yahweh, wanda ke mulki a Sihiyona; ku faɗa wa al'ummai abin da ya yi.
\v 12 Gama Allah wanda ke ramakon jinin da aka zubar na tunawa; baya mantawa da kukan waɗanda ake cutar su.
\s5
\v 13 Ka yi mani jinƙai, Yahweh; dubi yadda waɗanda ke gãba da ni suka wulaƙanta ni, kaine wanda zai kuɓutar da ni daga ƙofofin mutuwa.
\v 14 Dãma inyi shelar dukkan yabonka. A ƙofofin budurwar Sihiyona zan yi farincikin cetonka!
\s5
\v 15 Al'ummai sun faɗa cikin ramin da suka haƙa; tarkon da suka kafa don su buya ya kama ƙafafuwansu.
\v 16 Yahweh ya bayyana kansa; ya gudanar da shari'a; mugu ya kama kansa da abubuwan da ya aikata. Selah
\s5
\v 17 An maida miyagu makomarsu a Lahira, rabon dukkan waɗanda suka manta da Allah.
\v 18 Gama ba kullum ne ake mantawa da masu buƙata ba ko masu bege waɗanda ake zalunta zasu ɓace har abada.
\s5
\v 19 Ka tashi, Yahweh; kada ka bar mutum yayi nasara da kai; bari a yiwa al'ummai hukunci a gabanka.
\v 20 Tsoratar da su, Yahweh; bari al'ummai su sani su mutane ne kawai.
\s5
\c 10
\cl Zabura 10
\p
\v 1 Yahweh don me kake tsaye, a can nesa? Me ya sa ka ɓoye kanka a lokatan wahala?
\v 2 Domin fahariyarsu, mugayen mutane na tsananta wa matalauta; amma bari tarkon da mugaye suka ɗana ya kama su.
\v 3 Gama mugun mutum yana fahariya da manufofinsa; yana albarkatar haɗamarsa har yakan zagi Yahweh.
\s5
\v 4 Mugun mutum yana ɗaga fuska; ba ya neman Allah. Ba ya tunani a kan Allah domin bai damu ya kula da dukkan al'amura a kansa ba.
\v 5 Ya kan yi nasara a dukkan lokatai, domin adalcin dokokinka sun yi masa tsada; yana furci a kan abokan gãbansa.
\s5
\v 6 Ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zan taba faɗuwa ba; a cikin dukkan tsararraki ba zan sadu da wahala ba."
\v 7 Maganganunsa suna cike da zage-zage da yaudara, da mugayen kalmomi; harshensa kuma mai hatsari ne da hallakar wa.
\s5
\v 8 Yana kwanto kusa da ƙauyuka; a ɓoyayyun wurare har ya kashe marasa laifi; idanuwansa kuma suna duban waɗanda baza su iya yin komai ba.
\v 9 Yana jira a inda ya ɓuya kamar zaki a cikin kurmi; ya kan kwanta yana fakon wanda zai kama lokacin da yasa tarkonsa.
\v 10 Kamammunsa kuma an buga su har ƙasa; suka faɗa cikin ƙaƙƙarfan ragarsa.
\s5
\v 11 Ya ce a cikin zuciyarsa, "Allah ya manta; ya rufe fuskarsa; ba zai damu ya duba ba."
\v 12 Tashi, Yahweh! Ɗaga hannunka, Allah! Kada ka manta da waɗanda ake tsanantawa.
\s5
\v 13 Me yasa mugun mutum zai ƙi Allah har ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zai kama ni da wani alhaki ba"?
\v 14 Kana kula da komai, don kullum kana ganin wanda ake sa masa damuwa da baƙinciki. Kana sa mai bukata yasa dogararsa a gare ka; kana kuɓutar da marasa iyaye.
\s5
\v 15 Ka karya hannun mugu da mai aikata mugunta. Kasa ya ɗauki laifin mugun aikinsa, kada ya yi tunanin ba za a taba ganewa ba.
\v 16 Yahweh Sarki na har abada abadin; al'ummai kuma za a kore su daga ƙasarsa.
\s5
\v 17 Yahweh, ka ji buƙatun wanda ake tsanantawa; ka karfafa zukatansu, ka saurari addu'arsu.
\v 18 Zaka kãre marasa iyaye da waɗanda ake ƙuntata masu saboda babu wani mutum a wannan duniya da zai sake jawo razana.
\s5
\c 11
\cl Zabura 11
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Na sami mafaka a wurin Yahweh; yaya zaka ce da ni, "Ka tashi kamar tsuntsu akan tsauni"?
\v 2 Amma duba! miyagu sun shirya ƙibansu a kan tsarkiya don su harba cikin duhu a zuciyar adali.
\s5
\v 3 Gama idan ginshiƙai suka lalace, mene ne adali zai iya yi?
\v 4 Yahweh yana cikin tsatsarkan haikalinsa; idanuwansa suna kallo, idanuwansa suna gwada 'ya'yan 'yan adam.
\s5
\v 5 Yahweh yana gwada masu kirki da miyagu dukka, amma yana ƙin waɗanda ke ƙaunar tashin hankali.
\v 6 Yana ruwan garwashin wuta da ƙibiritu a kan mugaye; iska zata kone rabonsu daga finjilinsa!
\v 7 Gama Yahweh mai adalci ne, yana kuma ƙaunar masu gaskiya; adalai kuma zasu ga fuskarsa.
\s5
\c 12
\cl Zabura 12
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka shirya wa Sheminit. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka yi taimako, Yahweh, saboda mutanen kirki sun ɓace; aminitattu ma sun ɓace.
\s5
\v 2 Kowanne mutum yana maganar banza ga maƙwabcinsa; kowanne yana maganar yaudara da leɓuna da zuciya biyu.
\v 3 Yahweh, ka datsa dukkan leɓunan yaudara, kowanne harshe ya riƙa faɗin manyan abubuwa.
\v 4 Waɗannan sune waɗanda suka ce, "Ta wurin harshenmu zamu rinjaya. Sa'ad da leɓunanmu suka yi magana, wane ne zai zama gwani a bisanmu?"
\s5
\v 5 "Saboda tashin hankali akan matalauta, domin nishin masu buƙata, zan tashi," inji Yahweh. "Zan basu tsaron da suka yi marmari."
\s5
\v 6 Kalmomin Yahweh kalmomi ne zalla, kamar azurfar da aka narkar a tanderun wuta, aka tace har sau bakwai.
\v 7 Kai ne Yahweh! Ka kiyaye su. Ka tsare mutanen kirki daga muguwar tsara har abada.
\v 8 Mugaye suna tafiya ko'ina a lokacin da mugunta ke ɗaukaka a cikin 'yan adam.
\s5
\c 13
\cl Zabura 13
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, har sai yaushe, za ka ci gaba da mantawa da ni? Har yaushe ne zaka ɓoye mani fuskarka daga gare ni?
\v 2 Har yaushe ne zan daina damuwa da baƙinciki a zuciyata dukkan yini? Har yaushe ne maƙiyana zasu rika cin nasara a kaina?
\s5
\v 3 Ka dube ni ka kuma amsa mani, Yahweh Allahna! Ka bani haske ga idanuwana, ko in yi barcin mutuwa.
\v 4 Kada ka bar maƙiyina ya ce, "Na ce nasara a kansa," don kada maƙiyina ya sami abin cewa, "Na yi rinjaye akan abokin gãbana;" idan ba haka ba, maƙiyina zai yi murna saboda faɗuwata.
\s5
\v 5 Amma na dogara ga amintaccen alƙawarinka; zuciyata zata yi murna da cetonka.
\v 6 Zan yi waƙa ga Yahweh domin ya yi mani abin kirki ƙwarai.
\s5
\c 14
\cl Zabura 14
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Wawa yace a cikin zuciyarsa, "Ba Allah." Sun lalace sun kuma aikata laifin ban ƙyama; babu wani wanda ya aikata nagarta.
\s5
\v 2 Yahweh ya duba ƙasa daga sama a kan 'yan adam ya gani idan ko akwai wani mai fahimta, wanda ke neman sa.
\v 3 Dukkansu sun koma baya. Ga baki ɗayansu sun zama marasa kirki. Ba wanda ya ke aikata abin da ya ke dai-dai, babu ko ɗaya.
\s5
\v 4 Sun san wani abu, waɗanda suka aikata laifi, waɗanda suke cin mutanena kamar yadda suke cin gurasa, amma wane ne ba ya kiran Yahweh?
\s5
\v 5 Sun razana tare da fargaba, gama Allah yana tare da taruwar adalai!
\v 6 Kuna so ku ci mutuncin matalaucin mutum koda ya ke Yahweh ne mafakarsa.
\s5
\v 7 Oh, dama ceton Isra'ila zai zo daga Sihiyona! Sa'ad da Yahweh ya dawo da mutanensa daga bauta, Yakubu zai yi murna, Isra'ila ma zata yi farinciki!
\s5
\c 15
\cl Zabura 15
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, wane ne zai iya tsaya wa a rumfar sujadarka? Wa zai iya zama a tudun ka mai tsarki?
\v 2 Duk wanda ba shi da laifi, wanda ke aikata abin dake dai-dai wanda kuma ya ke faɗar gaskiya daga zuciyarsa.
\s5
\v 3 Wanda baya ɓatanci da harshensa, baya cin mutuncin wasu, baya ɓatanci ga maƙwabcinsa.
\s5
\v 4 Mutumin wofi abin reni ne a idanunsa, amma yana girmama waɗanda ke tsoron Yahweh. Yana rantsuwa ba don kansa ba, kuma yana cika alƙawaran da yayi.
\v 5 Baya karɓar ruwa a kuɗin da ya bayar bashi. Baya karɓar cin hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Duk wanda ya ke yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa girgiza ba.
\s5
\c 16
\cl Zabura 16
\p
\d Salon waƙar Dauda.
\p
\v 1 Ka tsare ni, Allah, gama na zo neman mafaka a gare ka.
\v 2 Na ce da Yahweh, "Kai ne Ubangijina; nagarta ta a banza take idan bana tare da kai.
\v 3 Kamar yadda tsarkakakkun mutane waɗanda ke a duniya, su mutane masu kirki; dukkan murnata a gare su take.
\s5
\v 4 Wahalolinsu zasu ƙaru, waɗanda ke neman waɗansu gumaka. Ba zan zubo masu da baye-baye na shan jinin allolinsu ba ko in furta sunayensu da leɓuna na ba.
\s5
\v 5 Yahweh, kaine kaɗai na zaɓa da ƙoƙona. Kai ne kake riƙe da rabona.
\v 6 An ajiye ma'aunan layi domina a wuraren jin daɗi; babu shakka gãdon dake kawo jin daɗi nawa ne.
\s5
\v 7 Zan albarkaci Yahweh, wanda ke bani shawara; ko da dare ma ina tunanin umarninsa.
\v 8 Na sa kaina a wurin Yahweh a dukkan lokuta, saboda kada in girgiza daga hannun damarsa!
\s5
\v 9 Don haka cike nake da murna; ɗaukakata na farinciki. Babu shakka zan zauna a cikin tsaro.
\v 10 Saboda baza ka bar raina a Lahira ba. Ba zaka bar amintaccenka ya ga rami ba.
\s5
\v 11 Ka koya mani hanyar rai; yalwataccen farinciki na kasancewarka; murna zata zauna a hannun damarka har abada!"
\s5
\c 17
\cl Zabura 17
\p
\d Addu'ar Dauda.
\p
\v 1 Ka kasa kunne ga roƙona don adalci, Yahweh; ka saurari kirana na neman taimako! Ka kasa kunne ga addu'ata daga leɓuna marasa yaudara.
\v 2 Bari baratarwata ta zo daga wurinka; bari idanuwanka su ga abin dake dai-dai!
\s5
\v 3 Idan zaka gwada zuciyata, idan zaka zo gare ni da dare, zaka tsarkakeni ba kuma za a sami wata mugunta a shirye-shiryena ba; bakina ba zai yi saɓo ba.
\s5
\v 4 Game kuma da ayyukan mutane; sune a cikin maganar leɓunanka waɗanda na tsare kaina daga hanyoyi na marasa bin doka.
\v 5 Na yi tafiya a kan tafarkinka sosai; sawayena basu kauce ba.
\s5
\v 6 Na yi kira a gare ka, domin ka amsa mani, ya Allah; ka juyo da kunnenka gare ni ka kuma saurara a lokacin da na yi magana.
\v 7 Ka nuna mani amintaccen alƙawarinka ta hanya mai banmamaki, kai da ke yin ceto ta hannun damarka ga waɗanda ke neman mafaka a gare ka daga maƙiyansu!
\s5
\v 8 Ka tsare ni kamar ƙwayar idanunka; ka ɓoye ni a ƙarƙashin inuwar fukafukanka
\v 9 daga fuskar miyagu waɗanda ke zargi na, maƙiyana da suka kewaye ni.
\v 10 Basa jin tausayin kowa; bakunansu na magana da fahariya.
\s5
\v 11 Sun kewaye sawayena. Sun sa idanuwansu don su fyaɗa ni ƙasa.
\v 12 Su kamar zakoki ne sun ƙosa su ga abin da zasu hallaka, kamar 'ya'yan zakoki suna laɓe a ɓoyayyun wurare.
\s5
\v 13 Ka tashi, Yahweh! Ka hare su! Ka jefar da su a ƙasa a kan fuskokinsu! Ka cece raina daga takobin mugaye!
\v 14 Yahweh, ka cece ni daga gare su da hannun ka, daga mutanen wannan duniya waɗanda arziƙinsu a cikin wannan rayuwa ne kaɗai! Za ka cike wuraren ajiyar mutanenka da arziki; zasu zama da 'ya'ya dayawa kuma zasu bar wadatarsu ga 'ya'yansu.
\s5
\v 15 Amma ni, zan ga fuskarka a cikin adalci; zan gamsu, sa'ad da na farka, da ganin ka.
\s5
\c 18
\cl Zabura 18
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda, baran Yahweh, sa'ad da ya rera wa Yahweh maganganun wannan waƙa a ranar da Yahweh ya kuɓutar da shi daga hannun dukkan maƙiyansa da kuma hannun Saul. Ya raira waƙa cewa:
\p
\v 1 Ina ƙaunarka, Yahweh, ƙarfina.
\s5
\v 2 Yahweh ne dutsena, hasumiya ta, wanda ke kawo mani tsaro; shi ne Allahna, dutsena; zan ɓoye a cikinsa. Shi ne garkuwata, ƙahon cetona, shi ne kuma ƙarfina.
\v 3 Zan yi kira ga Yahweh wanda ya cancanci a yabe shi, za a kuma cece ni daga maƙiyana.
\s5
\v 4 Sarƙoƙin mutuwa sun kewaye ni, hargowar ruwaye marasa daraja sun sha kaina.
\v 5 Sarƙoƙin Lahira sun kewaye ni; tarkon mutuwa kuwa ya kama ni.
\s5
\v 6 A cikin ƙuncina na yi kira ga Yahweh; na yi kiran neman taimako ga Allahna. Ya ji muryata daga haikalinsa; kirana na neman taimako ya kai gare shi; ya shiga har cikin kunnuwansa.
\s5
\v 7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza; ginshiƙan duwatsu kuwa suka jijjigu suka kuma yi rawar jiki saboda Allah ya husata.
\v 8 Hayaƙi kuwa ya yi ta tuƙaƙowa daga kafofin hancinsa, harshen wuta ya fito daga bakinsa. Gawayin garwashi suka fita ta wurinsa.
\s5
\v 9 Ya buɗe sammai ya sauko ƙasa, duhu kuma baƙiƙƙirin na ƙarƙashin ƙafafunsa.
\v 10 Ya hau kan kerub ya tashi; ya yi tafiya a kan fikafikan iska.
\s5
\v 11 Ya maida duhu rumfa a kewaye da shi, gizagizan ruwan sama masu nauyi a sararin sama.
\v 12 Ƙanƙara da garwashin wuta sun faɗo daga walƙiya dake gabansa.
\s5
\v 13 Yahweh ya yi tsawa a cikin sammai! Muryar Maɗaukaki ta yi tsawa.
\v 14 Ya harba kibansa, ya warwatsar da magabtansa; walƙatawar walƙiyoyi ta warwatsar da su.
\s5
\v 15 Daga nan hanyoyin ruwa suka bayyana; ginshiƙan duniya dukka aka bayyana su a cikin kukan yaƙinka, Yahweh- a cikin hurawa mai ƙarfi ta numfashin kafofin hancinka.
\s5
\v 16 Ya miƙo hannunsa ƙasa daga samaniya; ya riƙe ni! Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.
\v 17 Ya kuɓutar da ni daga ƙaƙƙarfan abokin gãbata, daga waɗanda ke ƙi na, domin sun fi ni ƙarfi sosai.
\s5
\v 18 Sun tasar mani a ranar shan ƙuncina amma Yahweh ne mai taimako na!
\v 19 Ya fitar da ni daga hatsari a buɗaɗɗen wuri; ya cece ni domin yana farinciki dani.
\s5
\v 20 Yahweh ya sãka mani saboda adalcina; ya dawo da ni saboda hannuwana na da tsarki.
\v 21 Domin na kiyaye tafarkun Yahweh ban kuma juya ga mugunta daga Allahna ba.
\s5
\v 22 Gama dukkan ka'idodinsa na adalci suna gaba na; game kuma da fariilansa, ban kauce daga gare su ba.
\v 23 Na kuma zama marar laifi a gabansa, na kiyaye kaina daga zunubi.
\v 24 Domin haka Yahweh ya dawo dani saboda adalcina, domin hannuwana masu tsafta ne a idanunsa.
\s5
\v 25 Ga kowanne mai aminci, kana nuna kanka mai aminci; ga mutum marar laifi, ka nuna kanka marar laifi.
\v 26 Ga duk wani mai tsarki, ka nuna kanka mai tsarki; amma kana da dabara ga duk mai aikin mugunta.
\s5
\v 27 Gama kana ceton mutane daga wahala, amma ka kan ƙasƙantar da masu girmankai da suka ɗaga idanunsu!
\v 28 Domin ka bada haske ga fitilata; Yahweh Allahna ka haskaka duhuna.
\v 29 Gama ta wurinka zan iya tserewa maƙiyana; ta wurin Allahna zan iya tsallake saman katanga.
\s5
\v 30 Kamar yadda Allah ya ke, hanyarsa dai-dai take. Maganar Yahweh tsartsarka ce! Shi garkuwane ga duk wanda yake neman mafaka a wurinsa.
\v 31 Gama wane ne Allah sai Yahweh? Wane ne dutse in ba Allahnmu ba?
\v 32 Shi ne Allahn dake ƙarfafa ni kamar ɗammara, wanda ya ke sa mutanen da basu da aibu a kan hanyarsa.
\s5
\v 33 Yana tabbatar da lafiyar ƙafafuna kamar barewa ya kuma sa ni a bisa!
\v 34 Yakan koyar da hannuwana don yaƙi makamaina kuma za su tankware bakan tagulla.
\s5
\v 35 Kai ka bani garguwar cetona. Hannunka na dama yana ƙarfafa ni, tagomashinka kuma ya maida ni babba.
\v 36 Kayi mani buɗaɗɗen wuri don ƙafafuwana suna ƙarƙashina saboda kada santsi ya ɗauke ƙafafuwana.
\s5
\v 37 Na kori maƙiyana har na kama su; ban juya ba har sai da na lalata su dukka.
\v 38 Na buga su har ba wanda zai iya tashi; sun faɗi a ƙarƙashin ƙafafuna.
\v 39 Gama ka sa ƙarfi a kaina kamar ɗamara don yaƙi; ka sa waɗanda ke gãba da ni a ƙarƙashina.
\s5
\v 40 Ka bani nasara akan maƙiyana; zan hallaka waɗanda ke gãba da ni.
\v 41 Suna kira don taimako, amma babu wani da ya cece su; sun yi kira ga Yahweh, amma bai amsa masu ba.
\v 42 Na buge su har sun zama gutsu-gutsu kamar ƙura a fuskar iska; na jefar da su waje kamar laka a tituna.
\s5
\v 43 Ka cece ni daga mutane masu husuma. Ka maida ni shugaba a kan al'ummai. Mutanen da ban san su ba, ban ma yi masu aiki ba.
\v 44 Yayin da suka ji ni, zasu yi mani biyayya; bãƙi zasu rusuna mani dole.
\v 45 Bãƙin zasu zo da rawar jiki daga kagarunsu.
\s5
\v 46 Yahweh mai rai ne; dutsena abin yabo. Allah mai cetona a gimama shi.
\v 47 Shi ne Allah wanda ya ke ɗaukar fansa domina, yana sawa a rinjaye al'ummai a ƙarƙashina.
\s5
\v 48 Ni 'yantacce ne daga maƙiyana! Lalle, ka ɗaukaka ni sama da waɗanda suka taso suna gãba da ni! Ka cece ni daga mutane masu tawaye.
\v 49 Saboda haka zan yi yabo a gare ka, Yahweh, a cikin al'ummai; zan raira maka waƙar yabon sunanka!
\s5
\v 50 Allah yana bada babbar nasara ga sarkinsa, ya kan nuna amintaccen alƙawarinsa ga wanda ya zaɓa, ga Dauda da zuriyarsa har abada.
\s5
\c 19
\cl Zabura 19
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Sammai na bayyana ɗaukakar Allah, sararin sama kuma na bayyana ayyukan hannunsa!
\v 2 A kowacce rana ana fitar da magana; dare bisa dare na bayyana ilimi.
\v 3 Babu magana ko kalma da aka furta; ba a ji amonsu ba.
\s5
\v 4 Duk da haka maganarsu ta tafi dukkan duniya, jawabinsu kuma har ƙarshen duniya. Ya kafa rumfa domin rana a cikinsu.
\v 5 Rana kamar ango na taƙama daga kagararsa, kuma kamar ƙaƙƙarfan mutum wanda ke farinciki idan ya ƙosa ya yi tsere.
\v 6 Rana tana fitowa daga ɗaya gefen zuwa ɗaya tsallaken; ba abin da zai tsere daga zafinta.
\s5
\v 7 Dokar Yahweh cikakkiya ce, tana wartsakar da rai; shaidar Yahweh kuwa abar dogara ce, tana ba da hikima ga masu buƙata.
\v 8 Ka'idodin Yahweh dai-dai suke, tana sa zuciya ta ji daɗi; umarnin Yahweh na da kyau, yana kawo haske ga idanuwa.
\s5
\v 9 Tsoron Yahweh tsabbatacce ne, tabbatacce ne har abada; dokokin Yahweh gaskiya ne dukkansu dai-dai suke!
\v 10 Suna da girma da daraja fiye da zinariya, fiye ma da zinariyar da aka tace; sun fi zuma zaƙi, zuman dake ɗigowa daga saƙarsa.
\s5
\v 11 I, ta wurinsu bawanka ya sami gargaɗi; akwai lada mai girma idan an yi biyayya dasu.
\v 12 Wane ne zai iya rarrrabe kuskuren kansa? Ka tsabtacce ni daga ɓoyayyun laifuffuka.
\s5
\v 13 Ka tsare bawanka kuma daga zunubai marasa kangado; kada ka bari su yi mulki a kaina. Sa'an nan ne zan zama kamili, zan kuma zama mara laifi daga laifuffukana masu yawa.
\v 14 Ka sa maganar baƙina da tunanin zuciyata su zama abin karɓa a wurinka, Yahweh, dutsena da fansata.
\s5
\c 20
\cl Zabura 20
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Bari Yahweh ya taimake ka a ranar wahala; bari sunan Allah na Yakubu ya tsare ka,
\v 2 ya kuma aika taimako daga wuri mai tsarki ya kawo maka tallafi daga Sihiyona.
\s5
\v 3 Bari ya tuna da dukkanbaye-bayenka ya kuma karɓi hadayun ƙonawarka. Selah
\v 4 Ya biya maka buƙatar zuciyarka, ya kuma cika maka dukkan shirye-shiryenka.
\s5
\v 5 Sai mu yi sowa ta farinciki saboda ka ci nasara, a cikin sunan Allahnmu, zamu ɗaga tutoci. Yahweh zai biya dukkan roƙe-roƙenmu.
\v 6 Yanzu dai na sani Yahweh zai ceci zaɓaɓɓensa; zai amsa masa daga wurinsa mai tsarki a sama da iko a hannun damarsa wanda ya cece shi.
\s5
\v 7 Waɗansu sun dogara ga karusansu wasu kuma ga dawakansu, amma mu muna kira ga Yahweh Allahnmu.
\v 8 Su zasu yi tuntuɓe har su faɗi ƙasa, amma mu zamu tashi mu tsaya daram!
\s5
\v 9 Yahweh, ka ceci sarki; ka taimake mu sa'ad da muka yi kira.
\s5
\c 21
\cl Zabura 21
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Sarki na yi farinciki cikin ƙarfinka, Yahweh! Babu iyaka ga farincikinsa daga cikin ceton da ka tanada!
\v 2 Ka biya masa buƙatar zuciyarsa baka kuma hana masa roƙon leɓunansa ba. Selah.
\s5
\v 3 Gama ka kawo masa albarku masu wadata; ka sanya bisa kansa kambi na tsabar zinariya.
\v 4 Ya nemi rai daga gare ka; ka bashi; ka bashi tsawon kwanaki har abada abadin.
\s5
\v 5 Darajarsa na da girma sabili da nasarar ka; ka ɗibiya masa daraja da ɗaukaka.
\v 6 Gama ka bashi madawwaman albarku; ka sashi jin daɗi da farinciki da ke a gabanka.
\s5
\v 7 Gama sarki yana dogara ga Yahweh; ta wurin alƙawarin amincin Maɗaukaki ba zaya jijjigu ba.
\v 8 Hannunka zaya kama dukkan maƙiyanka; Hannunka na dama zaya kama waɗanda suka ƙi ka.
\s5
\v 9 A lokacin hasalarka; zaka ƙona su sarai kamar daga cikin tanderu mai ƙuna. Yahweh zai haɗiye su cikin hasalarsa, kuma wutar za ta cinye su.
\v 10 Zaka hallakar da zuriyarsu daga ƙasar kuma zuriyarsu daga cikin 'yan adam.
\s5
\v 11 Gama sun shirya yi maka mugunta; sun tsiro da shiri wanda ba za su iya yin nasara ba!
\v 12 Gama za ka sa su koma da baya; zaka jã kwarinka a fuskarsu.
\s5
\v 13 Ka ɗaukaka, Yahweh, cikin ƙarfin ka; zamu raira waƙa mu kuma yaɓi ikonka.
\s5
\c 22
\cl Zabura 22
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; an tsara bisa ga tsallen barewa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Allahna, Allahna, me yasa ka yashe ni? Me yasa ka yi nisa daga ƙubutar da ni kuma kayi nisa daga muryata ta azaba?
\v 2 Allahna, na yi kuka da tsakar rana, amma baka amsa mani ba, da dare kuma ban yi shuru ba!
\s5
\v 3 Amma kai mai tsarki ne; kana zaman sarki tare da yabon Isra'ila.
\v 4 Iyayenmu sun dogara gare ka; sun dogara gare ka, ka kuma ƙubutar da su. Sun yi kira gare ka an kuma ƙuɓutar da su.
\v 5 Sun dogara gare ka basu kuma kunyata ba.
\s5
\v 6 Amma ni tsutsa ne ba mutum ba, abin kunya ga "yan adam da kuma abin raini ga mutane.
\v 7 Dukkan waɗanda suka ganni suka cakune ni; suka yi mani haibaici; suka kaɗa mani kai.
\v 8 Suka ce, "Ya dogara ga Yahweh; bari Yahweh ya kuɓutar da shi. Bari ya kuɓutar da shi, gama yana fahariya da shi."
\s5
\v 9 Gama ka fito dani daga mahaifa; ka sa in dogara gare ka a sa'ad da nake shan nono wurin mahaifiyata.
\v 10 Tun daga mahaifa aka jefo ni gare ka; kai Allahna ne tun daga mahaifar mahaifiyata!
\s5
\v 11 Kada ka yi nisa dani, gama damuwa na kusa; babu wani mai taimako.
\v 12 Bajimai masu yawa sun kewaye ni; Bajimai masu ƙarfi na Bashan suna zagaye dani.
\v 13 Sun buɗe bakinsu da girma gãba dani kamar zaki mai ruri yana yagar abin da ya kama.
\s5
\v 14 An kwararo ni kamar ruwa, kuma dukkan ƙasusuwana sun goce. Zuciyata kamar kitse; ta narke daga cikin cikina.
\v 15 Ƙarfina ya bushe kaf kamar fasasshiyar tukunya; harshena ya manne sama a bakina. Ka kwantar da ni a cikin ƙurar mutuwa.
\s5
\v 16 Gama karnuka suka zagaye ni; taron masu aikata mugunta suka kewaye ni; suka huda hannuwana da ƙafafuna.
\v 17 Zan iya ƙirga ƙasusuwana. Suka duba suka kuma zura mani ido.
\s5
\v 18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu, suka jefa ƙuri'a a bisa kayana.
\v 19 Kada ka yi nisa, Yahweh; ina roƙon ka kayi sauri domin ka taimake ni, ƙarfina!
\s5
\v 20 Ka kuɓutar da raina daga takobi, raina ɗaya daga hannuwan karnukan daji.
\v 21 Ka cece ni daga bakin zaki; ka kuɓutar dani daga ƙahonni na shanun daji.
\s5
\v 22 Zan furta sunanka ga 'yan'uwana; a tsakiyar taruwar jama'a zan yabe ka.
\v 23 Ku da kuke tsoron Yahweh, yabe shi! Dukkan ku zuriyar Yakubu, girmama shi! Ku tsaya cik cikin tsoronsa, dukkan ku zuriyar Isra'ila!
\s5
\v 24 Gama baya rena ko yayi banza da wahalar ƙuntattu ba; Yahweh baya ɓoye fuskarsa daga gare shi ba; a lokacin da ƙuntacce yayi kira gare shi, ya ji.
\v 25 Yabona zai zama sabili da kai a cikin babban taron jama'a; Zan cika wa'adina a gaban waɗanda ke tsoron sa.
\s5
\v 26 Tsanantattu za su ci su ƙoshi; Waɗanda suka nemi Yahweh zasu yabe shi. Bari zukatanku su rayu har abada.
\v 27 Dukkan mazamnan duniya zasu tuna su kuma juyo ga Yahweh; dukkan iyalan al'ummai zasu durƙusa a gabanka.
\s5
\v 28 Gama mulki na Yahweh ne; shi yake mulki bisa al'ummai.
\v 29 Dukkan mawadatan mutanen duniya za su yi buki su kuma yi sujada; dukkan su masu gangarawa zuwa turɓaya zasu durƙusa a gabansa, su waɗanda baza su iya adana rayyukansu ba.
\s5
\v 30 Tsara mai zuwa zata yi masa hidima; zasu gaya wa tsara ta gaba game da Ubangiji.
\v 31 Zasu zo su kuma yi magana game da adalcinsa; zasu faɗi abin da yayi ga mutanen da ba a haife su ba.
\s5
\c 23
\cl Zabura 23
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh makiyayina ne; ba zan rasa komai ba.
\v 2 Yana sa ni in kwanta a cikin korayen makiyayu; yana bi da ni kurkusa da kwantaccen ruwa.
\s5
\v 3 Ya maido da raina; yana bishe ni ta tafarku madaidaita domin sunansa.
\s5
\v 4 Ko da ina tafiya ta cikin kwari na inuwa mafi duhu, ba zan ji tsoron cutarwa ba tun da kana tare da ni; sandarka da kerenka na ta'azantar da ni.
\s5
\v 5 Ka shirya teburi a gabana a fuskar maƙiyana; ka shafe kaina da mai; ƙoƙona ya cika har yana zuba.
\s5
\v 6 Tabbas nagarta da amintaccen alƙawari zasu bi ni dukkan kwanakin raina; zan kuma zauna a cikin gidan Yahweh na lokaci mai tsawo sosai!
\s5
\c 24
\cl Zabura 24
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ƙasa ta Yahweh ce, da dukkan cikarta, duniyar, da dukkan mazauna cikinta.
\v 2 Gama ya gina ta a bisa tekuna ya kuma ƙafa ta a bisa koguna.
\s5
\v 3 Wane ne zai haura tudun Yahweh? Wane ne zai tsaya a cikin wurinsa mai tsarki?
\v 4 Shi wanda ke da hannuwa masu tsarki da kuma zuciya mai tsabta; wanda baya faɗar ƙarya, ba ya kuma yin rantsuwa domin yayi yaudara.
\s5
\v 5 Zai karɓi albarka daga wurin Yahweh da kuma adalci daga Allah na cetonsa.
\v 6 Haka ya ke ga tsarar masu neman sa, masu neman fuskar Allah na Yakubu. Selah
\s5
\v 7 Tãda kanku, ku ƙyamare; ku tashi, madawwaman ƙofofi, domin Sarkin daraja ya shigo ciki!
\v 8 Wane ne wannan Sarkin daraja? Yahweh, mai ƙarfi da girma; Yahweh, mai girma cikin yaƙi.
\s5
\v 9 Tãda kanku, ku ƙyamare; ku tashi, madawaman ƙofofi, domin Sarki na daraja ya shigo ciki!
\v 10 Wane ne wannan Sarkin daraja? Yahweh mai runduna, shi ne Sarkin daraja. Selah
\s5
\c 25
\cl Zabura 25
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 A gare ka, Yahweh, na miƙa raina!
\v 2 Allahna, Na dogara gare ka. Kar ka bari a wulaƙanta ni; kar ka bari maƙiyana suyi farincikin nasara a kaina.
\v 3 Duk wanda yasa begensa a kan kada shi kunyata bari waɗanda suke aikata makirci babu dalili su ji kunya!
\s5
\v 4 Ka bayyana mani hanyarka, Yahweh; koya mani tafarkinka.
\v 5 Bishe ni cikin gaskiyarka ka kuma koyar dani, gama kai ne Allah na cetona; na sa begena bisan ka a koda yaushe.
\s5
\v 6 Ka tuna, Yahweh, ayyukanka na tausayi da kuma amintaccen alƙawari; gama sun kasance tun tuni.
\v 7 Kada kayi tunanin zunubaina na ƙuruciyata ko tayarwata; ka tuna da ni game da amintaccen alƙawarinka sabili da alherinka, Yahweh!
\s5
\v 8 Yahweh yana da nagarta kuma yana da alheri saboda haka yana koyawa masu zunubi tafarki.
\v 9 Yana bi da kamili ga abin da ke dai-dai kuma yana koya masu hanyarsa.
\s5
\v 10 Dukkan tafarkun Yahweh na dawwamammiyar ƙauna ne da kuma aminci ga waɗanda ke kiyaye alƙawarinsa da kuma umarnansa tabbatattu.
\v 11 Sabili da sunanka, Yahweh, ka gafarta zunubina, gama yana da girma sosai.
\s5
\v 12 Wane ne mutumin dake tsoron Yahweh? Ubangiji zaya umarce shi a hanyar da zaya zaɓa.
\v 13 Rayuwarsa zata bi ta hanya mai kyau; kuma zuriyarsa zasu gaji ƙasar.
\s5
\v 14 Abokantakar Yahweh na ga waɗanda ke girmama shi, kuma yana sanar da alƙawarinsa gare su.
\v 15 Idanuna suna bisa Yahweh koda yaushe, gama zaya ƙuɓutar da sawayena daga tarko.
\v 16 Ka juyo gare ni kayi mani jinƙai; gama ni kaɗai ne kuma cikin ƙunci.
\s5
\v 17 Damuwoyin zuciyata sun yawaita; ka tsamo ni daga nawayata!
\v 18 Ka dubi wahalata da kuma matsalolina; ka gafarta zunubaina.
\v 19 Ka dubi maƙiyana, gama suna da yawa; suna ƙina da ƙiyayya mai zafi.
\s5
\v 20 Ka kare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari a wulaƙanta ni, gama ina samun mafaka a wurinka!
\v 21 Bari nagarta da aminci su kiyaye ni, gama begena a cikinka ya ke.
\s5
\v 22 Ka kuɓutar da Isra'ila, Allah, daga dukkan wahalolinsa!
\s5
\c 26
\cl Zabura 26
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yi mani shari'a, Yahweh, gama nayi tafiya da aminci; na dogara ga Yahweh babu ja da baya.
\v 2 Ka gwada ni, Yahweh, ka kuma jaraba ni; jaraba tsabtar cikin raina da zuciyata!
\v 3 Gama amintaccen alƙawarinka na gaban idanuna, kuma ina tafiya cikin amincinka.
\s5
\v 4 Ban yi hurɗa da mutane marasa gaskiya ba, ko in yi cuɗanya da mutane macuta ba.
\v 5 Na ƙi jinin taruwar masu aikata mugunta, ban kuma zauna da mugaye ba.
\s5
\v 6 Na wanke hannuna cikin rashin laifi, ina kuma zagaya bagadinka, Yahweh,
\v 7 domin in raira waƙar yabo da ƙarfi in kuma shaida dukkan ayyukanka masu ban girma.
\v 8 Yahweh, ina ƙaunar gidan da kake zama, inda ɗaukakarka take!
\s5
\v 9 Kada ka kawar dani tare da masu zunubi, ko raina tare da mutane masu marmarin shan jini,
\v 10 waɗanda a cikin hannuwansu akwai mugun shiri, kuma hanunsa na dama ke cike da rashawa.
\s5
\v 11 Amma ni, zan yi tafiya cikin aminci; ka fanshe ni ka kuma yi mani jinƙai.
\v 12 Sawayena suna tsaye a shimfiɗarɗiyar ƙasa; a cikin taruwa zan albarkaci Yahweh!
\s5
\c 27
\cl Zabura 27
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh ne haske na da cetona; wane ne zan ji tsoro? Yahweh ne mafakar raina; wane ne zai razana ni?
\s5
\v 2 Lokacin da masu aikata mugunta suka taso mani domin su cinye namana, magabtana da maƙiyana suka yi tuntuɓe suka kuma faɗi.
\v 3 Koda runduna zasu zagaye ni da gãba, zuciyata baza ta ji tsoro ba; koda yaƙi zai taso gãba dani, duk da haka zan kasance da ƙarfin hali.
\s5
\v 4 Abu guda ɗaya nayi roƙo ga Yahweh, zan kuma biɗi wannan; shi ne in zauna a cikin gidan Yahweh dukkan kwanakin raina, in dubi kyawun Yahweh in kuma yi bimbini a cikin haikalinsa.
\s5
\v 5 Gama a ranar wahala zaya ɓoye ni a cikin fukafukansa; a ƙarƙashin inuwar rumfarsa zaya suturce ni. Zaya ɗaukaka ni a bisa dutse mai tsawo!
\v 6 Sa'an nan za a ɗaukaka kaina fiye da maƙiyana dake kewaye dani, zan kuma miƙa hadayu na farinciki a cikin rumfarsa! Zan raira waƙa in kuma yi waƙoƙi ga Yahweh!
\s5
\v 7 Yahweh ka ji, muryata a lokacin da nayi kuka! Kayi mani jinƙai, ka kuma amsa mani!
\v 8 Zuciyata na ce da kai, "Nemi fuskarsa!" Na nemi fuskarka, Yahweh!
\s5
\v 9 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni; kada ka juyar da bawanka daga gare ka cikin fushi! Tun dama kaine mai taimakona; kada ka yashe ni ko kayi banza dani, Allah na cetona!
\v 10 Koda mahaifina ko mahaifiyata sun yashe ni, Yahweh zaya karɓeni.
\s5
\v 11 Ka koya mani tafarkinka, Yahweh! Ka bishe ni a daidaitacciyar hanya saboda maƙiyana.
\v 12 Kada ka bayar da ni ga nufin maƙiyana, gama shaidun ƙarya sun tashi gãba dani, suna kuma huro da ta'addanci!
\s5
\v 13 Da mene ne zai faru dani da ba domin na yarda cewa zan ga alherin Yahweh a cikin ƙasar masu rai ba?
\v 14 Ka jira ga Yahweh; yi ƙarfi, bari zuciyarka ta ƙarfafa! Saurari Yahweh!
\s5
\c 28
\cl Zabura 28
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 A gare ka, Yahweh, nayi kuka; dutsena, kada kayi banza da ni. Idan baka amsa mani ba, zan harɗe da waɗanda ke gangarawa zuwa kabari.
\v 2 Kaji ƙarar roƙona a lokacin da nayi kira domin taimako daga gare ka, a lokacin da na tãda hannuwa na zuwa wurinka mai tsarki!
\s5
\v 3 Kada ka kawar dani tare da masu aikata mugunta, su masu aikata laifuffuka, su dake faɗin alheri da maƙwabtansu da baki amma zuciyarsu cike take da mugunta.
\v 4 Ka basu dai-dai abin da ayyukansu ya dace dasu da kuma abin da muguntarsu ta wajaba, ka biya su bisa ga aikin hannuwansu ka kuma mayar masu bisa ga ladarsu.
\v 5 Domin basu gane da ayyukan Yahweh ba ko ayyukan hannuwansa, zaya buga su ƙasa baza a ƙara gina su ba.
\s5
\v 6 Albarka ga Yahweh domin ya ji muryar kukana!
\v 7 Yahweh ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta dogara gare shi, na kuma sami taimako. Saboda haka zuciyata tayi farinciki ƙwarai, zan kuma yabe shi da raira waƙoƙi.
\v 8 Yahweh ne karfin mutanensa, kuma shi ne maɓoyar ceto na shafaffensa.
\s5
\v 9 Ka ceci mutanenka ka kuma albarkaci gãdonka. Ka zama makiyayinsu ka kuma ɗauke su har abada.
\s5
\c 29
\cl Zabura 29
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Bada yabo ga Yahweh, ku 'ya'yan Allah! Bada yabo ga Yahweh domin ɗaukakarsa da ƙarfinsa.
\v 2 Ba Yahweh ɗaukakar da ta cancanci sunansa. Durƙusa ƙasa ga Yahweh cikin jamalin tsarkinsa.
\s5
\v 3 An ji muryar Yahweh har bisa ruwaye; Allah maɗaukaki ya yi tsawa, Yahweh na tsawa bisa ruwaye masu yawa.
\v 4 Muryar Yahweh na da cikakken iko; Muryar Yahweh mai daraja ne.
\v 5 Muryar Yahweh na fasa itatuwan sida; Yahweh na fasa gutsu-gutsu itatuwan sida na Lebanon.
\s5
\v 6 Yana sa Lebanon tayi tsalle kamar ɗan maraki da kuma Dutsen Hamon kamar ɗan shanu.
\v 7 Muryar Yahweh na aikar da harshen wuta.
\v 8 Muryar Yahweh na girgiza hamada; Yahweh na girgiza hamadar Kadesh.
\s5
\v 9 Muryar Yahweh nasa rimaye su tanƙware tana kuma kware daji a fili. Kowanne a cikin haikali na cewa, "Daukaka!"
\v 10 Yahweh na zaman sarki a bisa ruwa mai ambaliya; Yahweh na zaman sarki har abada.
\s5
\v 11 Yahweh yana bada karfi ga mutanensa; Yahweh yana albarkatar mutanensa da salama.
\s5
\c 30
\cl Zabura 30
\p
\d Zabura; waƙar da aka yi a keɓewar haikali. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Zan girmama ka, Yahweh, gama ka tã dani sama kuma baka bari maƙiyana sun yi farinciki bisa na ba.
\v 2 Yahweh Allahna, nayi kuka gare ka domin taimako, ka kuma warkar dani.
\v 3 Yahweh, ka tsamo raina daga Lahira; ka adana ni da rai kada in gangara ƙasa zuwa kabari.
\s5
\v 4 Raira yabbai ga Yahweh, ku amintattunsa! Ku bada godiya a lokacin da kuka tuna da tsarkinsa.
\v 5 Gama fushin sa na lokaci kaɗan ne; amma tagomashinsa na har abada ne. Kuka na zuwa da dare ne, amma farinciki na zuwa da safe.
\s5
\v 6 Da ƙarfin hali nace. "Ba zan jijjigu ba."
\v 7 Yahweh, da tagomashinka ka kafa ni kamar ƙaƙƙarfan tsauni; amma daka ɓoye fuskarka, na shiga damuwa.
\v 8 Nayi kira gare ka, na kuma nemi tagomashi daga wurin Ubangijina!
\s5
\v 9 Wacce riba ce ke cikin mutuwata, idan na gangara cikin kabari? Ko turɓaya zata yabe ka? Zata furta tabbatattun amincinka?
\v 10 Ka saurara, Yahweh, kayi mani jinƙai! Yahweh, ka zama mai taimakona.
\s5
\v 11 Ka juyar da makokina zuwa rawa; ka cire mani tsumma ka kuma sanya mani rigar farinciki.
\v 12 Yanzu ɗaukakata zata yi maka waƙar yabo kuma ba zata yi shuru ba; Yahweh Allahna, zan yi maka godiya har abada!
\s5
\c 31
\cl Zabura 31
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 A cikin ka, Yahweh, na sami mafaka; kada ka barni in wulaƙanta. Ka kuɓutar dani cikin adalcinka.
\v 2 Ka saurare ni; Ka kuɓutar dani da sauri; ka zama dutsen mafakata, ƙaƙƙarfar maɓoya domin cetona.
\s5
\v 3 Gama kai ne dutsena da kuma mafakata; Saboda haka sabili da sunanka, ka shugabance ni ka kuma bishe ni.
\v 4 Ka ƙwato ni daga cikin tãrun da suka ɓoye domi na, gama kai ne maɓuyata.
\s5
\v 5 A cikin hannuwanka nake bada ruhuna; zaka fanshe ni, Yahweh, Allah madogarata.
\v 6 Na ƙi jinin waɗandɑ suke bautawa gumakan banza, amma na dogara ga Yahweh.
\v 7 Zan yi murna da kuma farinciki cikin amintaccen alƙawarinka, gama ka ga ƙuncina; ka san matsalar raina.
\s5
\v 8 Baka miƙa ni a cikin hannuwan maƙiyana ba. Ka kafa ƙafafuwana a buɗaɗɗen wuri mai faɗi.
\v 9 Kayi mani jinƙai, Yahweh, gama ina cikin ƙunci; idanuna sun yi nauyi da azaba tare da raina da jikina.
\s5
\v 10 Gama raina yayi nauyi da makoki kuma shekaruna na cike da nishe-nishe. Ƙarfina ya gaza sabili da zunubina, ƙasusuwana suna lalacewa sarai.
\v 11 Sabili da maƙiyana, mutane sun yi banza dani; maƙwabtana suka gaji da yanayina, kuma waɗanda suka san ni suka tsorata. Waɗanda suka gamu dani a hanya suka gudu daga gare ni.
\s5
\v 12 An manta da ni kamar mataccen mutum wanda babu wanda ke tunaninsa. Ina kama da fasasshiyar tukunya.
\v 13 Gama na ji raɗe-raɗe masu yawa, labarai masu ban tsoro daga kowanne sashe sa'ad da suke shiri gãba da ni. Sun yi shiri domin su ɗauke raina.
\s5
\v 14 Amma na dogara gare ka, Yahweh; Na ce, "Kai ne Allahna."
\v 15 Ƙaddarata na cikin hannuwanka. Ka kuɓutar dani daga hannuwan magabtana daga kuma waɗanda suke fafarata.
\v 16 Bari fuskarka ta haskaka bisa bawanka; ka cece ni cikin amintaccen alƙawarinka.
\s5
\v 17 Kada ka bar ni in wulaƙantu, Yahweh; gama na yi kira gare ka! Bari mugu ya wulaƙanta! Bari suyi shuru a cikin Lahira.
\v 18 Bari harsuna masu ƙarya suyi shuru su dake magana gãba da mai adalci da renin girma da kuma tozartarwa.
\s5
\v 19 girman alherinka da ka shirya wa masu girmama ka, abin da kake aiwatar wa domin waɗanda suka yi mafaka a cikinka a gaban dukkan 'ya'yan talikai!
\v 20 A cikin mahallin bayyanuwarka, ka ɓoye su daga makircin mutane. Ka ɓoye su a cikin mahalli daga ta'addancin harsuna.
\s5
\v 21 Mai albarka ne Yahweh, gama ya nuna mani amintaccen alƙawarinsa mai ban mamaki a lokacin da nake a cikin birnin kwanto.
\v 22 Ko da ya ke na faɗa cikin gaggawata, "An datse ni daga fuskarka," duk da haka ka ji roƙona domin taimako lokacin da nayi kuka gare ka.
\s5
\v 23 Oh, ƙaunaci Yahweh, dukkan ku amintattun mabiya. Yahweh yana tsare amintattu, amma yana sãka wa masu girman kai.
\v 24 Ku ƙarfafa kuyi ƙarfi, dukkan ku dake dogara cikin Yahweh domin taimako.
\s5
\c 32
\cl Zabura 32
\p
\d Zabura ta Dauda. Waƙar hikima.
\p
\v 1 Mai albarka ne taliki wanda an gafarta masa kurakuransa, wanda aka rufe zunubinsa.
\v 2 Mai albarka ne mutum wanda Yahweh ba ya lisafta laifi bisansa kuma wanda babu algus cikin ruhunsa.
\s5
\v 3 Da na yi shuru, ƙasusuwana suna lalacewa sa'ad da nake nishe-nishe dukkan yini.
\v 4 Gama rana da dare hannunka na da nauyi bisana. ƙarfina ya gaza kamar lokacin fãrin kaka.
\s5
\v 5 Sa'an nan na furta zunubi na gare ka, ban kuma ƙara ɓoye laifi na ba. Na ce, "Zan furta kurakuraina ga Yahweh," ka kuma gafarta mani ladar zunubina.
\v 6 Saboda wannan, dukkan waɗanda ke na allahntaka suna adu'a a gare ka a lokacin gwagwarmaya mai girma. Sa'an nan lokacin da ruwaye masu hauka suka taso, baza su cimma waɗannan mutane ba.
\s5
\v 7 Kai ne maɓuyata; zaka tsare ni daga wahala. Zaka zagaye ni da waƙoƙin nasara.
\v 8 Zan umarce ka in koya maka hanyar da zaka bi. Zan umarce ka da idanuna a bisanka.
\s5
\v 9 Kada ka zama kamar doki ko kamar alfadari, wanda ba shi da fahimta; sai tare da linzami da ragama domin a bi da su inda ake so su tafi.
\v 10 Mugu yana da baƙinciki mai yawa, amma amintaccen alƙawarin Yahweh zai zagaye wanda ya dogara gare shi.
\s5
\v 11 Yi murna cikin Yahweh, da farinciki, ku adalai; yi sowa ta farinciki, dukkan ku masu tsabta cikin zuciya.
\s5
\c 33
\cl Zabura 33
\p
\v 1 Yi farinciki cikin Yahweh, ku adalai; Yin yabo ya dace ga adalai.
\v 2 Kuyi godiya ga Yahweh da molo; yi waƙoƙin yabo gare shi da molo mai tsarkiya goma.
\v 3 Raira sabuwar waƙa gare shi; ku yi kiɗa da ƙwarewarku kuna raira waƙa tare da farinciki.
\s5
\v 4 Gama maganar Yahweh mai adalci ce, kuma dukkan abin da ya aikata dai-dai ne.
\v 5 Yana ƙaunar adalci da shari'a. Duniya na cike da amintaccen alƙawarinsa.
\v 6 Da maganar Yahweh aka hallici sammai, kuma dukkan taurari sun kasance ne ta numfashin bakinsa.
\s5
\v 7 Yana tara ruwayen teku wuri ɗaya kamar tudu; ya ajiye tekuna cikin ɗakunan ajiya.
\v 8 Bari dukkan ƙasar taji tsoron Yahweh; Bari dukkan mazaunan duniya su tsaya cik a gabansa.
\v 9 Gama ya yi magana, aka kuma aikata; ya umarta, ya kuma tabbata.
\s5
\v 10 Yahweh yana lalatar da ƙawancen al'ummai; yana mulki akan shirye-shiryen mutane.
\v 11 Shirin Yahweh ya tsaya har abada, shirye-shiryen zuciyarsa ga dukkan tsararraki.
\v 12 Mai albarka ce al'ummar da Yahweh ne Allahnta, mutanen da ya zaɓa abin gãdonsa.
\s5
\v 13 Yahweh yana gani daga sama; yana ganin dukkan mutane.
\v 14 Daga wurin da ya ke zama, yana duban dukkan masu zama cikin ƙasar.
\v 15 Shi wanda ya ke shirya zuciyarsu dukka yana la'akari da ayyukansu.
\s5
\v 16 Babu sarkin da zai tsira sabili da yawan runduna; jarumi baya tsira ta dalilin ƙarfinsa.
\v 17 Doki tsaro ne na banza domin nasara; duk da ƙarfinsa, ba zai iya ƙubutarwa ba.
\s5
\v 18 Duba, idanun Yahweh na bisan waɗanda ke tsoronsa, a bisa waɗanda suka dangana bisa amintaccen alƙawarinsa
\v 19 domin ya kuɓutar da rayukansu daga mutuwa ya kuma kiyaye su da rai a lokacin yunwa.
\s5
\v 20 Muna jiran Yahweh; shi ne taimakonmu da kuma garkuwarmu.
\v 21 Zuciyarmu tayi farinciki cikinsa, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
\s5
\v 22 Bari amintaccen alƙawarinka, Yahweh, ya kasance da mu a lokacin da muka kafa begenmu cikinka.
\s5
\c 34
\cl Zabura 34
\p
\d Zabura ta Dauda; lokacin da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, wanda ya kore shi waje.
\p
\v 1 Zan yabi Yahweh a dukkan lokaci, Yabonsa zai kasance a bakina koda yaushe.
\s5
\v 2 Zan yabi Yahweh! Bari ƙuntattu su ji su kuma yi farinciki.
\v 3 Ku yabi Yahweh tare da ni, bari mu ɗaukaka sunansa tare.
\s5
\v 4 Na nemi Yahweh kuma ya amsa mani, ya kuma ba ni nasara bisa dukkan tsorona.
\v 5 Waɗanda ke duban sa suna haskakawa, kuma fuskarsu ba ta ji kunya ba.
\v 6 Wannan matsattsen mutum yayi kuka Yahweh kuma ya ji ya kuma cece shi daga dukkan matsalolinsa.
\s5
\v 7 Mala'ikan Yahweh na zagaye waɗanda ke tsoronsa ya kuma ƙubutar da su.
\v 8 Ku ɗanɗana ku kuma gani cewa Yahweh na da kyau. Mai albarka ne mutum wanda ke ɓuya cikinsa.
\v 9 Ku ji tsoron Yahweh, ku mutanensa masu tsarki. Babu rashi ga waɗanda ke tsoronsa.
\s5
\v 10 'Ya'yan zakuna wasu lokuttan suna rasa abinci su kuma ji yunwa, amma waɗanda suka nemi Yahweh baza su rasa kowanne abu mai kyau ba.
\v 11 Ku zo, 'ya'ya maza, ku saurare ni. Zan koya maku jin tsoron Yahweh.
\s5
\v 12 Wanne mutum ne mai biɗar rai ya ke kuma ƙaunar ranaku masu yawa, domin ya ga alheri?
\v 13 To, sai ka tsare harshenka daga faɗin mugunta leɓunanka kuma daga faɗin ƙarya.
\v 14 Ka juyo daga barin mugunta ka kuma aikata nagarta. Nemi salama ka kuma bi ta.
\s5
\v 15 Idanun Yahweh suna bisa masu adalci kuma kunnuwansa suna karkatawa zuwa ga kukansu.
\v 16 Fuskar Yahweh na gãba da waɗanda ke aikata mugunta, domin a datse tunawa da su daga duniya.
\v 17 Masu adalci sun yi kira Yahweh kuma yana kuɓutar da su daga dukkan matsalolinsu.
\s5
\v 18 Yahweh yana kurkusa da masu karyayyar zuciya, kuma yana ceton waɗanda aka ƙuntatawa a cikin ruhu.
\v 19 Da yawa suke matsalolin masu adalci, amma Yahweh yana ƙubutar da su daga dukkan su.
\v 20 Ya kare dukkan ƙasusuwansa, babu ko ɗaya daga cikinsu da za a karya.
\s5
\v 21 Mugunta zata kashe mai mugunta. Waɗanda suka ƙi masu adalci za a hallakar da su.
\v 22 Yahweh yana ƙubutar da rayukan bayinsa. Babu ɗaya daga cikin waɗanda ke neman mafaka wurinsa da za a kayar.
\s5
\c 35
\cl Zabura 35
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, ka yi gãba da waɗanda ke aiki gãba da ni; ka yaƙi waɗanda ke yaƙi da ni.
\v 2 Ka ɗauki garkuwarka ƙarama da babba; tashi ka taimake ni.
\v 3 Yi amfani da mashi da gatarin yaƙin ka gãba da waɗanda ke runtuma ta; ka ce da raina, "Ni ne cetonka."
\s5
\v 4 Bari su waɗanda ke neman raina su ji kunya su kuma faɗi. Bari waɗanda ke shirin cuta na a juyar da su a kuma hargitsa su.
\v 5 Bari su zama kamar ƙaiƙayi a fuskar isaka, a sa'ad da mala'ikan Yahweh ke korar su.
\v 6 Bari hanyar su ta duhunta tana kuma zamewa, a sa'ad da mala'ikan Yahweh ke runtumar su.
\s5
\v 7 Babu dalili suka shirya mani tarkonsu; Babu dalili suka haƙa rami domin raina.
\v 8 Bari halakarwa ta auko masu ba zato. Bari tarkon da suka ɗana ya kama su. Bari su faɗa ciki, ga hallakarsu.
\s5
\v 9 Amma zan yi farinciki cikin Yahweh in kuma yi murna cikin cetonsa.
\v 10 Dukkan ƙasusuwana za su ce, "Yahweh, wane ne kamar ka, wanda ke ƙuɓutar da ƙuntattu daga waɗanda suka fi ƙarfinsu da kuma matalauta da kuma mabuƙata daga waɗanda ke ƙoƙarin yi masu fashi?"
\s5
\v 11 Shaidu marasa adalci sun tashi; sun yi mani zargin ƙarya.
\v 12 Sun sãka mani nagarta da mugunta. Ina cike da ɓacin rai.
\s5
\v 13 Amma a lokacin da suke ciwo, na sanya tsummokara; na yi azumi a madadinsu da kaina sunkuye ga ƙirjina.
\v 14 Na yi tafiya cikin ƙunci domin ɗan'uwana; Na durƙusa cikin makoki domin mahaifiyata.
\s5
\v 15 Amma da nayi tuntuɓe, suka yi murna suka taru wuri ɗaya; suka taru wuri ɗaya gãba da ni, kuma suka bani mamaki. Suka kawo mani farmaƙi babu fasawa.
\v 16 Da rashin girmamawa samsam suka yi mani ba'a; suka tauna mani haƙoransu.
\s5
\v 17 Ubangiji, har yaushe zaka duba? Ka ƙuɓutar da raina daga farmaƙinsu mai hallakarwa, raina daga zakuna.
\v 18 Sa'an nan zan gode maka a babban taro mai girma; Zan yabe ka a cikin mutane masu yawa.
\s5
\v 19 Kada ka bar maƙiyana masu ƙarya su yi murna a kaina; kada ka barsu su aiwatar da mugun shirinsu.
\v 20 Gama basu maganar salama, amma suka shirya maganganun ƙarya gãba da waɗanda ke zaman salama cikin ƙasar.
\s5
\v 21 Sun buɗe bakunansu da girma gãba da ni; suka ce, "Aha, Aha, idanunmu sun gan shi."
\v 22 Ka gan shi, Yahweh, kada ka yi shuru; Ubangiji, kada kayi nisa dani.
\v 23 Ka tãda kanka ka kuma farka domin ka kare ni; Allahna da Ubangijina, ka kare bukatata.
\s5
\v 24 Ka kãre ni, Yahweh Allahna, sabili da adalcinka; kada ka bar su suyi murna a kaina.
\v 25 Kada ka bari su faɗa a cikin zuciyarsu, Aha, mun sami abin da muke nema." Kada ka bar su su ce, "Mun haɗiye shi."
\v 26 Ka basu kunya ka kuma ruɗar da waɗanda ke niyyar cutar da ni. Bari waɗanda ke cakuna ta a rufe su da kunya da ƙasƙanci.
\s5
\v 27 Bari su dake marmarin kuɓutata suyi sowa ta murna su kuma ji daɗi; bari koyaushe su ce, "Bari Yahweh ya ɗaukaka, shi da ya ke jin daɗi cikin wadatar bawansa."
\v 28 Sa'an nan zan faɗi game da shari'arka in kuma yabe ka dukkan yini.
\s5
\c 36
\cl Zabura 36
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda bawan Yahweh.
\p
\v 1 Mugun mutum yana zancen kurakuransa daga cikin zuciyarsa, babu tsoron Allah a idanunsa.
\v 2 Gama yana yiwa kansa ta'aziya, da tunanin cewar zunubansa ba zasu tonu ba ko kuma a ƙi su.
\s5
\v 3 Maganganunsa na zunubi ne da yaudara; ba ya son ya zama mai hikima ya kuma aikata nagarta.
\v 4 A lokacin da ya ke kwance a gado, yana shirya yadda zai yi zunubi; ba ya ƙin mugunta.
\s5
\v 5 Amintaccen alƙawarinka, Yahweh, na kaiwa har zuwa sammai; amincinka na kaiwa zuwa cikin giza-gizai.
\v 6 Adalcinka na kama da duwatsun Allah; shari'unka na kama da manyan zurfafa. Yahweh, ka kare talikai da dabbobi.
\s5
\v 7 Yaya darajar amintaccen alƙawarinka ya ke, Allah! Bil'adama na fakewa a ƙarƙashin inuwar fukafukanka.
\v 8 Zasu ƙoshi daga yalwar abincin gidanka; zaka sa su sha daga cikin koginka mai manyan albarku.
\v 9 Domin a gare ka akwai maɓulɓular rai; cikin haskenka zamu ga haske.
\s5
\v 10 Ka kawo gare ni amintaccen alƙawarinka cikakke ga waɗanda suka san ka, kariyarka zuwa ga kamilai a zuci.
\v 11 Ka da ka bar ƙafafun mai girman kai shi zo kusa dani. Ka da ka bar hannun mugaye su kore ni da nisa.
\v 12 A can mugaye suka faɗi; aka buga su ƙasa basu kuma iya tashi ba.
\s5
\c 37
\cl Zabura 37
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Kada ka damu da masu mugunta; kada ka ji ƙyashin waɗanda ke ayyukan rashin adalci.
\v 2 Gama zasu bushe da wuri kamar ciyawa, su kuma yanƙwane kamar korayen tsire-tsire.
\s5
\v 3 Ka dogara ga Yahweh kuma ka yi abin da ke nagari; ka zauna a ƙasar ka yi kiwo cikin aminci.
\v 4 Sa'an nan ka yi murna da al'amuran Yahweh, kuma zai biya maka buƙatun zuciyarka.
\s5
\v 5 Ka miƙa hanyoyinka ga Yahweh; ka dagara gare shi, kuma zai yi abu a madadinka.
\v 6 Zai nuna aɗalcinka kamar hasken rana da rashin laifinka kamar rana tsaka.
\s5
\v 7 Ka natsu a gaban Yahweh kuma kayi jira da haƙuri domin sa. Kada ka ji haushi idan wani ya yi nasara da abin da ya ke yi, ko sa'ad da ya ke ƙulla mugunta.
\s5
\v 8 Kada ka ji haushi da takaici. Kada ka damu. Wannan na bada damuwa ne kawai.
\v 9 Za a datse miyagu, amma waɗanda ke jiran Yahweh zasu gãji ƙasar.
\v 10 A ɗan lokaci ƙaɗan mugun mutum zai ɓace; zaka dubi wurinsa, amma ba zai kasance ba.
\s5
\v 11 Amma masu tawali'u zasu gãji ƙasar kuma zasu yi murna da gagarumar wadata.
\v 12 Mugun mutum yana shirya maƙarƙashiya gãba da adali yana kuma cizon haƙora gãba da shi.
\v 13 Ubangiji yana yi masa dariya, gama yana ganin zuwan ranarsa.
\s5
\v 14 Mugaye sun zare takubbansu suka kuma tanƙware bakkunansu don su kãda waɗanda ake masu danniya da masu buƙata, su kashe waɗanda ke da nagarta.
\v 15 Takkubansu zasu soke zukatansu, kuma bakkunansu zasu kakkarye.
\s5
\v 16 Gara ƙanƙanen abin da mutumin kirki ya ke da shi da yawan abubuwan mugayen mutane.
\v 17 Gama za a ƙarɓe ƙarfin mugayen mutane, amma Yahweh zai taimaki adalai
\s5
\v 18 Yahweh yana lura da marasa abin zargi a kowacce rana, kuma gãdonsu zai kasance har abada.
\v 19 Ba za su ji kunya a lokacin masifa ba. Sa'ad da Yunwa tazo, zasu samu isasshen abinci.
\s5
\v 20 Amma mugaye zasu lalace. Maƙiyan Yahweh za su zama kamar darajar ciyawa; za a cinye su su ɓace kamar hayaƙi.
\v 21 Mugu yakan ci bashi amma ba ya biya, amma adali yana bayarwa hannu sake.
\s5
\v 22 Waɗanda Allah ya sawa albarka zasu gãji ƙasar; waɗanda ya la'anta zasu zama korarru.
\v 23 Ta wurin Yahweh ne hanyoyin mutum ke kafuwa, mutumin da hanyarsa amintacciya ce a fuskar Allah.
\v 24 Ko da ya ke yana tuntuɓe, ba zai faɗi ba, gama Yahweh na riƙe shi da hannunsa.
\s5
\v 25 Dã ni yaro ne kuma yanzu na tsufa; ban taɓa ganin an yashe da adali ba ko kuma 'ya'yansa na roƙon abinci.
\v 26 Dukkan yini yana yin alheri yana ba da rance, kuma 'ya'yansa sun zama albarka.
\v 27 Ka bar mugunta kayi abin da ke dai-dai; zaka cetu har abada.
\s5
\v 28 Gama Yahweh yana ƙaunar adalci kuma baya rabuwa da amintattun masu binsa. Yana kiyaye su har abada, amma zuriyar mugaye zasu zama korarru.
\v 29 Adalai zasu gãji ƙasar su zauna ciki har abada.
\v 30 Bakin adali yana maganar hikima da kuma ƙara adalci.
\s5
\v 31 Shari'ar Allahnsa na zuciyarsa; ƙafafunsa ba za su yi santsi ba.
\v 32 Mugu yakan yi fakon adali ya nemi hanyar kashe shi.
\v 33 Yahweh ba zai bar shi a hannun mugun ba ko kuwa ya yanke masa hukunci sa'ad da ya ke masa shari'a.
\s5
\v 34 Ka jira Yahweh ka kuma kiyaye hanyoyinsa, zaya kuma ɗaga ka sama ka mallaki ƙasar. Za ka gani sa'ad da ake korar mugaye.
\s5
\v 35 Na ga mugu da azzalumin taliki ya baje kamar koren itace a ƙasarsa ta asali.
\v 36 Amma sa'ad da na sãke wucewa kuma, bai kasance a wurin ba. Na neme shi, amma ba ya samuwa.
\s5
\v 37 Dubi mutumin kirki, ka kuma lura da adali; gaba zai zama da kyau ga mutumin salama,
\v 38 Masu zunubi kuwa za a hallaka su ƙaƙaf; za a kuma share zuriyar mugun mutum.
\s5
\v 39 Ceton adalai yakan zo daga Yahweh ne; yakan kiyaye su a lokatan damuwa.
\v 40 Yahwe ya taimake su ya kuɓutar da su, Ya kuɓutar dasu daga mugaye ya cece su saboda sun sami garkuwa a cikinsa.
\s5
\c 38
\cl Zabura 38
\p
\d Zabura ta Dauda, domin ya kawo tunawa.
\p
\v 1 Yahweh, kada ka tsauta mani a cikin fushinka; kada ka hukunta ni a cikin hasalarka.
\v 2 Gama kibiyoyinka suna sukana, kuma hannunka na matse ni har ƙasa.
\s5
\v 3 Dukkan jikina na ciwo saboda hasalarka; babu lafiya a ƙasusuwana saboda laifina.
\v 4 Gama zunubaina sun fi ƙarfina; sun zamar mani kaya mai nauyi da yawa.
\s5
\v 5 Raunukana sun harbu suna wari saboda wawancin zunubaina.
\v 6 Ana dakatar dani ana wulaƙanta ni kowacce rana; Ina ta makoki dukkan tsawon rana.
\s5
\v 7 Gama daga ciki, ina cike da zafin ciwo; babu lafiya a jikina.
\v 8 An sandare ni an ragargaza ni; ina gunaguni saboda fushin zuciyata.
\s5
\v 9 Ubangiji kana sane da buƙatar zuciyata, kuma gunagunina basa ɓoyu ba daga gare ka.
\v 10 Zuciyata na bugawa, ƙarfina na ƙarewa, bana kuma gani sosai.
\s5
\v 11 Abokaina da aminai sun ƙaurace mani saboda yanayina; maƙwabtana na tsaye daga nesa.
\v 12 Waɗanda ke so su kashe ni sun ƙafa mani tarko. Su waɗanda ke neman yi mani rauni suna maganar hallakarwa da faɗin kalmomin ruɗu dukkan tsawon rana.
\s5
\v 13 Amma ni, ina kamar kurman mutum kuma bana jin komai; ina kamar beben da ba ya iya faɗin komai.
\v 14 Ina kamar mutumin da ba ya ji kuma ba shi da amsa.
\s5
\v 15 Tabbas ina jiranka, Yahweh; zaka amsa, Ubangiji, Allahna.
\v 16 Na faɗi haka saboda maƙiyana ba zasu yi murna a kan damuwata ba. Idan tafin ƙafata ya zame, zasu yi mani mugayen abubuwa.
\s5
\v 17 Gama ina gab da mutuwa, kuma ina cikin wahala kowacce sa'a.
\v 18 Na furta laifofina; na kuma damu da zunubina.
\s5
\v 19 Amma maƙiyana na da yawa; waɗanda suka ƙi ni cikin kuskure na da yawa.
\v 20 Suna rama mani nagarta da mugunta; suna ta tuhuma ta koda ya ke ina neman abin da ke nagari.
\s5
\v 21 Kada ka yashe ni, Yahweh; Allahna, kada ka tsaya nesa dani.
\v 22 Ka zo da sauri ka taimakeni, Ubangiji, cetona.
\s5
\c 39
\cl Zabura 39
\p
\d Domin shugaban mawaƙa, domin Yedutan. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Na yi shiri, "Zan lura da furcin da zan yi saboda kada in yi zunubi da harshe na. Zan sa wa bakina takunkumi a lokacin da nake wurin da mugu ya kasance."
\s5
\v 2 Na yi shiru; Na riƙe maganganuna daga faɗin wani abu koda nagari ne, shanwuta kuma ta ƙaru.
\v 3 Zuciyata ta yi zafi; sa'ad da nayi tunani a kan abubuwan nan, yana ci kamar wuta. Sa'an nan a ƙarshe nayi magana.
\s5
\v 4 "Yahweh, kasa in san yaushe ne ƙarshen rayuwata da tsawon kwanakina. Ka nuna mani ina kurkusa da matuwa.
\v 5 Duba, kã maida kwanakina kamar tsawon hannuna, kuma rayuwata kamar ba komai take ba a wurinka. Hakika kowanne mutum lumfashi ɗaya ne. Selah
\s5
\v 6 Hakika kowanne mutum yana tafiya kamar inuwa. Hakika dukkan kowa yana hanzari ya tattara arziki ko da yake basu san wanda zai karbe su ba.
\v 7 Yanzu, Ubangiji, domin me nake jira? Kai ƙaɗai ne begena.
\s5
\v 8 Ka cece ni daga zunubaina; kada ka bari in zama abin ba'a ga wawaye.
\v 9 Na yi shiru kuma bazan iya buɗe bakina ba, saboda kai ne kayi haka.
\s5
\v 10 Ka daina yi mani rauni; na karaya ta wurin bugun hannunka.
\v 11 Sa'ad da kake horar da mutane don zunubi, kakan cinye abubuwan da suke marmari kamar asu; hakika dukkan mutane ba komai bane banda tururi kawai. Seleh
\s5
\v 12 Ka ji addu'ata, Yahweh, ka saurare ni; ka saurari kukana! Kada ka zama kurma a gare ni, gama ni kamar baƙo ne tare da kai, ɗan gudun hijira kamar yadda dukkan kakannina suke.
\v 13 Ka juyar da harararka daga gare ni domin in sake yin murmushi kafin in mutu,"
\s5
\c 40
\cl Zabura 40
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Na jira Yahweh da haƙuri; ya saurare ni ya ji kukana.
\v 2 Ya fitar dani daga rami mai furgitarwa, daga taɓo, ya sa ƙafafuna a kan dutse ya tsare takawata.
\s5
\v 3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina, yabo ga Allahnmu. Da yawa zasu gani su kuma girmama shi su dogara ga Yahweh.
\v 4 Mai albarka ne mutumin da ya maida Yahweh madogararsa kuma baya girmama masu fahariya ko waɗanda suka juya daga gare shi zuwa ƙarairayi.
\s5
\v 5 Da yawa suke, Yahweh Allahna, ayyukan al'ajiban da ka yi, kuma babu wanda zai iya ƙirga abubuwan da kake tunani gme da mu; Idan na yanke shawara in yi magana a kan su, za su fi abin da za a iya ƙirgawa.
\v 6 Ba ka buƙatar hadaya ko baiko, amma ka buɗe kunnuwana; ba ka buƙatar baye-baye na ƙonawa ko baye-baye na zunubi.
\s5
\v 7 Sa'an nan na ce, "Duba, Na zo; a rubuce ya ke a game dani cikin littafin Yahweh.
\v 8 Ina jin daɗin yin nufinka, Allahna, shari'unka na cikin zuciyata."
\v 9 Na yi shelar nagartattun labaran ayyukanka na adalci a babban taron jama'a; Yahweh, ka san leɓunana basu dena yin wannan ba.
\s5
\v 10 Ban ɓoye ayyukan adalcinka a zuciyata kaɗai ba; Na furta amincinka da cetonka; Ban ɓoye amintaccen alƙawarinka ko madawwamiyar ƙaunarka daga babban taron jama'a ba.
\v 11 Kada ka yi jinkirin yi mani ayyukan jinƙai; ka bar amintaccen alƙawarinka da madawwamiyar ƙaunarka su kiyaye ni.
\s5
\v 12 Damuwoyin da basu ƙidayuwa sun kewaye ni; alhakin zunubaina ya tarar da ni har yasa bana iya ganin wani abu; Sun fi gashin kaina yawa, kuma zuciyata ta karaya.
\v 13 In ka yarda, Yahweh, ka cece ni; ka yi hanzari ka taimake ni, Yahweh.
\s5
\v 14 Ka sa waɗanda suke son kashe ni su sha kunya da yawa. Kasa su koma baya a ci nasara a kansu, ka kawo waɗanda ke murna saboda wahalar da nake sha, cikin ƙasƙanci.
\v 15 Kasa su razana saboda kunya, su waɗanda ke yi mani ba'a, "
\s5
\v 16 Amma bari dukkan waɗanda ke neman ka su yi farinciki da murna a cikinka; ka sa duk mai ƙaunar cetonka ya ci gaba da cewa, "A yabi Yahweh."
\v 17 Na talauce na zama mabuƙaci; duk da haka Ubangiji yana tunani a kai na. Kai ne mai taimako na kuma ka zo domin ka cece ni; kada ka yi jinkiri, Allahna.
\s5
\c 41
\cl Zabura 41
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Mai albarka ne wanda ke kulawa da marasa ƙarfi; a ranar masifa, Yahweh zai 'yantar da shi.
\v 2 Yahweh zai kiyaye shi ya kare shi, kuma zai zama da albarka a duniya; Yahweh ba zai bar shi ga nufin maƙiyansa ba.
\v 3 Yahweh zai yi masa gudummawa a gadon wahalarsa; zaka maida gadonsa na ciwo zuwa gadonsa na warkarwa.
\s5
\v 4 Na ce, "Yahweh, ka yi mani jinƙai! Ka warkar dani, gama na yi maka laifi."
\v 5 Maƙiyana suna muguwar magana gãba da ni, cewa, 'Yaushe ne zai mutu kuma sunansa ya lalace?'
\v 6 Idan maƙiyina ya zo gani na, ya furta maganganun banza; zuciyarsa na ƙoƙarin sanin dukkan matsalolina; sa'ad da ya tafi daga gare ni, sai ya gaya wa kowa game da su.
\s5
\v 7 Dukkan waɗanda ke ƙi na na raɗa da juna gãba da ni; gãba da ni suna fatan shan wahalata.
\v 8 Suna cewa, "Mugun ciwo ya make shi; yanzu da ya ke kwance ƙasa, ba zai ƙara tashi ba."
\v 9 Lallai, ko abokina na ƙut da ƙut, da na yarda da shi, wanda ya ci gurasata, ya juya mani baya.
\s5
\v 10 Amma kai, Yahweh, ka yi mani jinƙai ka ɗaga ni sama saboda in mai da martani.
\v 11 Ta wannan na san kana farinciki dani, gama maƙiyina bai yi murna a kaina ba.
\v 12 Amma ni, ka tallefe ni cikin aminncina kuma zaka kiyaye ni a fuskarka har abada.
\s5
\v 13 Bari Yahweh, Allah na Isra'ila a yabe shi daga dawwama zuwa dawwama. Amin da Amin. Littafi Biyu
\s5
\c 42
\cl Zabura 42
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. 'Salon waƙa ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Kamar yadda mariri ke marmarin rafukan ruwa, haka nake ƙishinka, Allah.
\v 2 Ina ƙishin Allah, Allah mai rai, yaushe zan zo in bayyana a gaban Allah?
\s5
\v 3 Hawayena sun zama abincina dare da rana, lokacin da maƙiyana kullum suna cewa dani, "Ina Allahnka?"
\v 4 Waɗannan abubuwan nake tunawa da su yayin da nake zubo raina: yadda na tafi tare da taron mutane na jagorance su zuwa gidan Allah tare da muryar jin daɗi da yabo, babban taro na shagalin buki.
\s5
\v 5 Me yasa ka rusuna ƙasa, raina? Me yasa kake damuwa daga can ciki? Yi bege ga Allah, gama zan ƙara yabonsa wanda shi ne cetona.
\v 6 Allahna, raina ya rusuna ƙasa a can ciki, don haka na tuna da kai daga ƙasar Yordan, daga ƙololuwar Dutsen Hamon, kuma daga tudun Miza.
\s5
\v 7 Zurfi na kira ga zurfi da jin ƙarar kwararowar ruwanka; dukkan raƙuman ruwanka da matsirgan ruwanka sun mamaye ni.
\v 8 Duk da haka Yahweh zai umarci amintaccen alƙawarinsa da rana; da dare waƙarsa zata kasance tare da ni, addu'a ce ga Allah na rayuwata.
\s5
\v 9 Zan yi magana ga Allah, dutsena, "Me yasa ka mance da ni" Me yasa nake makoki saboda danniyar maƙiyina?"
\v 10 Kamar da takobi a ƙasusuwana, maƙiyana ke yi mani zargi, yayin da kullum suke cewa dani, "Ina Allahnka?"
\s5
\v 11 Me yasa kake rusuna a ƙasa, raina? Me yasa kake damuwa can ciki? Yi bege cikin Allah, gama kuma zan yabe shi wanda shi ne cetona da Allahna.
\s5
\c 43
\cl Zabura 43
\p
\v 1 Kawo mani adalci, Allah, kayi mani taimakon kãriya a kan al'umma marasa tsoron ka.
\v 2 Gama kai ne Allah na ƙarfina. Meyasa ka yashe ni? Me yasa nake tafiya cikin makoki saboda muzgunawar maƙiya?
\s5
\v 3 Oh, ka aiko da haskenka da gaskiyarka, su jagorance ni. su kawo ni ga tudunka mai tsarki da wurin zamanka.
\v 4 Sa'an nan zan yi tafya zuwa ga bagadin Allah, ga Allah matuƙar jin daɗina. Zan yabeka da garaya, Allah, Allahna.
\s5
\v 5 Me yasa ka rusuna ƙasa, raina? Me ya sa kake damuwa can ciki? Yi bege cikin Allah, gama zan ƙara yabonsa wanda shi ne cetona da Allahna.
\s5
\c 44
\cl Zabura 44
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Salon waƙa ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Mun ji da kunnuwanmu, Allah, Kakanninmu suka faɗa mana irin aikin da ka yi a kwanakinsu, a kwanakin dã.
\v 2 Ka kore al'ummai da hannunka, amma ka dasa mutanenmu; ka azabci mutane, amma ka baza mutanenmu cikin ƙasar.
\s5
\v 3 Gama basu samu mallakar ƙasar ta takobin kansu ba, ba kuma ƙarfin kansu ba ne ya cece su; amma hannun damanka da ƙarfinka da hasken fuskarka ne, saboda yi tagomashi gare su.
\v 4 Allah, kai ne sarkina; ka umarta nasara domin Yakubu.
\s5
\v 5 Da taimakonka zamu tura maƙiyanmu; da sunanka za mu tattakesu, waɗanda suka tashi gãba da mu.
\v 6 Gama ba zan dogara ga bakana ba, takobina kuma ba zai cece ni ba.
\s5
\v 7 Amma ka cece mu daga maƙiyanmu, ka ba masu ƙinmu kunya.
\v 8 A cikin Allah muke fahariya a kullum, kuma za mu yi godiya ga sunanka har abada. Selah
\s5
\v 9 Amma yanzu ka ƙi mu ka kawo mu ga kunya, kuma baka yi tafiya tare da mayaƙanmu ba.
\v 10 Ka sa muka juya baya daga maƙiyin; kuma waɗanda suka ƙi mu suna ɗibi ganima domin kansu.
\v 11 Ka maida mu kamar tumakin da aka ƙaddara don abinci ka warwatsar da mu cikin al'ummai.
\s5
\v 12 Ba a bakin komai ka sayar da mutanenka ba; ba ka ƙara wadatarka ta yin haka ba.
\v 13 Ka maida mu abin zargi ga maƙwabtanmu, waɗanda ke kewaye da mu suna yi mana reni da ba'a.
\v 14 Ka sa mun zama abin zãgi cikin al'ummai, abin girgiza kai cikin tarrukan mutane.
\s5
\v 15 A dukkan tsawon rana ƙasƙancina na gabana, kuma kunyar fuskata ta rufe ni
\v 16 saboda muryar wanda ke tsautarwa da zage-zage, saboda maƙiyi da mai ɗaukar fansa.
\v 17 Dukkan waɗannan sun zo a kanmu; duk da haka ba mu mance da kai ba ko kuwa mu yi aiki cikin rahin gaskiya da alƙawaranka.
\s5
\v 18 Zuciyarmu bata juya ba; ƙafafunmu ba su yi nisa daga hanyarka ba.
\v 19 Duk da haka ka kakkarya mu a wurin diloli ka rufe mu da inuwar mutuwa.
\v 20 Idan mun mance da sunan Allahnmu ko kuwa muka buɗe hannuwanmu ga wani bãƙon allah,
\v 21 Allah ba zai bincika haka ba? Gama ya san asiran zuciya.
\v 22 Hakika, ta dalilinka ake karkashe mu dukkan rana; ana yi mana kallon tumaki domin yanka.
\s5
\v 23 Farka, me yasa kake barci, Ubangiji? Tashi, kada ka jefar da mu da daɗewa.
\v 24 Me yasa ka ɓoye fuskarka ka mance da matsananciyar azabarmu da wahalarmu?
\s5
\v 25 Gama mun narke mun zama ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.
\v 26 Tashi tsaye domin taimakonmu ka 'yantar da mu ta dalilin amintaccen alƙawarinka.
\s5
\c 45
\cl Zabura 45
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; an shirya domin shoshanayim. Zabura ta 'ya'yan Kora. Salon waƙa. Waƙar ƙauna.
\p
\v 1 Zuciyata na jin daɗi da nagartaccen zance; Zan karanta kalmomin da na harhaɗo a kan sarki da ƙarfi; harshena shi ne al'ƙalamin shiryayyen marubuci.
\v 2 Ka fi 'ya'yan ɗan Adam kyau; an zuba alheri a leɓunanka; saboda haka mun san Allah ya albarkaceka har abada.
\s5
\v 3 Kasa takobinka a gefenka, mai girma, cikin ɗaukakarka da martabarka.
\v 4 Cikin darajarka ka hau dokinka cikin murna saboda yarda da tawali'u da ayyukan adalci; hannun damanka zai koya maka abubuwan bantsoro.
\s5
\v 5 Kibawunka na da ƙaifi; mutane sun faɗa ƙarƙashinka; kibawunka na cikin zukatan maƙiyan sarki.
\v 6 Kursiyinka, Allah, yana nan har abada, sandar adalci shi ne sandar mulkinka.
\v 7 Kana ƙaunar ayyukan adalci kuma kana ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya shafe ka da mai na murna fiye da abokan taraiyarka.
\s5
\v 8 Dukkan tufafinka na ƙamshin turaren mur da aloyes da ƙahonnin da aka samo; daga kowacce fadar hauren giwa kayyakin busa da kiɗe-kiɗe sun saka murna.
\v 9 'Ya'ya mata na sarakuna na cikin matayenka masu martaba; sarauniya na tsaye da tufafin zinariya da Ofir a hannun damanka,
\s5
\v 10 Saurara, ɗiya, ki maida hankali ki buɗe kunne, ki mance da mutanenki da gidan mahaifinki.
\v 11 Ta haka sarkin zai yi marmarin kyanki; shi shugabanki ne; ki girmama shi.
\s5
\v 12 Ɗiyar Taya zata kasance a wurin da kyauta; masu arziki cikin mutanen za su nemi alfarmarku.
\v 13 Ɗiya gimbiya a fãda tana cikin dukkan ɗaukaka; an yi aikin tufafinta da zinariya.
\s5
\v 14 Za a kaita wurin sarki cikin kyawawan tufafi masu ado kala-kala; budurwai, ƙawayenta dake binta, za a kawo maka.
\v 15 Za a jagorance su da murna da farinciki; za su shiga cikin fadar sarki.
\s5
\v 16 A fãdar ubanninka 'ya'yanka zasu kasance, waɗanda zaka maida su yarimai a dukkan duniya.
\v 17 Zan sa sunanka ya dawwama a dukkan tsararraki; saboda haka mutanen zasu yi maka godiya har abada abadin.
\s5
\c 46
\cl Zabura 46
\p
\d Domin shugaban mawaka. Zabura ta 'ya'yan Kora; shirin Alamot. Waƙa.
\p
\v 1 Allah shi ne mafakarmu da ƙarfinmu, Mai matuƙar taimako a lokacin wahala.
\v 2 Domin haka ba za mu ji tsoro ba, ko duniya zata canza, ko an girgiza duwatsu har cikin tekuna,
\v 3 ko ruwayenta sun yi ruri da tangaɗi, duwatsu kuma suna motsi saboda kumburinsu. Selah
\s5
\v 4 Akwai kogi, da ƙoramu waɗanda ke sa birnin Allah farinciki, wuri mai tsarki na shirayi na Maɗaukaki.
\v 5 Allah yana cikin tsakiyarta; ba zata kawu ba; Allah zai taimake ta, kuma zai yi haka da sassafen safiya.
\s5
\v 6 Al'ummai suka fusata kuma mulkoki suka girgiza; ya tayar da muryarsa, kuma duniya ta narke.
\v 7 Yahweh mai runduna na tare da mu; Allah na Yakubu shi ne mafakarmu. Selah
\s5
\v 8 Zo, dubi ayyukan Yahweh, hallakar da ya kawo wa duniya.
\v 9 Ya sa yaƙe-yaƙe su ƙare har zuwa iyakar duniya; ya kakkarya baka ya daddatsa mãsu gutsu--gutsu; ya ƙone garkuwoyi.
\s5
\v 10 Ku yi shiru ku sani Ni ne Allah; Zan sami ɗaukaka a cikin al'ummai; Za a ɗaukaka ni a duniya.
\v 11 Yahweh mai runduna na tare da mu; Allah na Yakubu ne mafakarmu. Saleh
\s5
\c 47
\cl Zabura 47
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Ku tafa hannuwanku, ku dukkan mutane; ku yi sowa ga Allah da muryar nasara.
\v 2 Gama Yahweh Maɗaukaki abin tsoro ne; shi Sarki ne mai girma bisa dukkan duniya.
\s5
\v 3 Ya mayar da mutane ƙarƙashinmu, ya sa al'ummai a ƙarƙƙashin ƙafafunmu.
\v 4 Ya zaɓi gãdonmu dominmu, ɗaukakar Yakubu wanda ya ke ƙauna. Selah
\v 5 Allah ya tafi sama da sowa, Yahweh da ƙarar kakaki.
\s5
\v 6 Raira waƙoƙin yabo ga Allah. raira waƙoƙin yabo; raira waƙoƙin yabo ga Sarkinmu, raira waƙoƙin yabo.
\v 7 Gama Allah Sarki ne a kan dukkan duniya; raira woƙoƙin yabo da ganewa.
\s5
\v 8 Allah yana mulki a kan al'ummai; Allah na zaune a tsattsarkan kursiyinsa.
\v 9 'Ya'yan sarakuna sun tattaru wurin mutanen Allah na Ibrahim; gama garkuwoyin duniya na Allah ne; yana da ɗaukaka mai girma.
\s5
\c 48
\cl Zabura 48
\p
\d Waƙa; zabura ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Yahweh mai girma ne kuma a yabe shi da girma, cikin birnin Allahnmu a tsauni mai tsarki.
\v 2 Mai kyakkyawan tsawo, farincikin duk duniya, shi ne Tsaunin Sihiyona, a kusurwoyin arewa, birnin sarki mai girma.
\v 3 Allah ya maida kansa sananne a cikin fadodinta a matsayin mafaka.
\s5
\v 4 Gama, duba, sarakuna sun tattaro kansu; suna wucewa tare.
\v 5 Suka gan ta, sa'an nan suka yi mamaki; suka damu ƙwarai, sai suka wuce da sauri.
\v 6 Firgici ya mamaye su a wurin, da azaba kamar ta mace mai naƙuda.
\s5
\v 7 Da iskar gabas ka karya jiragen ruwan Tarshish.
\v 8 Kamar yadda muka ji haka muka gani a birnin Yahweh mai runduna, a birnin Allahnmu; Allah zai kafa shi har abada. Selah
\s5
\v 9 Mun yi tunanin amintaccen alƙawarinka, Allah. a tsakiyar haikalinka.
\v 10 Kamar yadda sunanka ya ke, Allah, haka yabonka har ga iyakar duniya; hannun damanka na cike da ayyukan adalci.
\s5
\v 11 Tsaunin Sihiyona yi murna, bari 'ya'ya mata na Yahuda su yi farinciki saboda shari'unka masu adalci.
\s5
\v 12 Yi tafiya a kewayen Dutsen Sihiyona, je ka kewaya ta, harabarta da hasumiyarta,
\v 13 lura da bangayenta sosai kuma ka duba fãdodinta da kyau, don ka faɗa wa tsara mai zuwa.
\s5
\v 14 Gama wannan Allahn shi ne Allahnmu har abada abadin; shi zai bi damu har mutuwa.
\s5
\c 49
\cl Zabura 49
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Ku ji wannan, dukkanku mutane; ku kasa kunne, dukkanku mazaunan duniya, ƙanana da manya,
\v 2 masu arziki da matalauta dukka.
\s5
\v 3 Bakina zai yi maganar hikima kuma nazarin zuciyata zai zama na ganewa.
\v 4 Zan sa kunnena ga misali; zan fara misalina da molo.
\v 5 Me zai sa in ji tsoron kwanakin mugunta, sa'ad da zunuban maƙiyana suka kewaye ni.
\s5
\v 6 Me zai sa in ji tsoron waɗanda suka dogara ga wadatarsu suke kuma yin fahariya game da arzikinsu?
\v 7 Tabbas babu wanda zai iya fansar ɗan'uwansa ko ya ba Allah fansa dominsa,
\v 8 Gama 'yantar da ran wani na da tsada, kuma ba wanda zai iya biyan bashinmu.
\s5
\v 9 Babu wanda zai dawwama da har jikinsa ba zai ruɓe ba.
\v 10 Gama zai ga ruɓa. Masu hikima na mutuwa; wawaye da sakarkaru ma na lalacewa su kuma bar wadatarsu ga waɗansu.
\s5
\v 11 Tunaninsu na can ciki shi ne iyalansu zasu cigaba har abada, wuraren da suke zama kuma, su cigaba har dukkan tsararraki; suna kiran gonakinsu da sunayensu.
\s5
\v 12 Amma mutum, mai arziki ba shi rayuwa har abada; yana kamar dabbobi dake mutuwa.
\v 13 Wannan, hanyarsu, ita ce wautarsu; duk da haka bayansu, mutane suna amincewa da maganganunsu.
\s5
\v 14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga Lahira, kuma mutuwa zata zama mai kiwon su. Adalai zasu yi mulki a kansu da safe, kuma jikunansu zasu hallaka a Lahira, tare da rashin wurin zama dominsu.
\v 15 Amma Allah zai 'yantar da rai na daga ikon lahira; zai karɓe ni. Selah
\s5
\v 16 Kada ka ji tsoro sa'ad da wani ya yi arziki, kuma darajar gidansa ta ƙaru.
\v 17 Gama sa'ad da ya mutu ba zai tafi da komai ba; darajarsa ba zata tafi tare da shi ba sa'ad da ya mutu.
\s5
\v 18 Ko da mutum yana farinciki da nasararsa saboda arzikinsa yayin da ya ke raye- kuma mutane na yabonka sa'ad da kake rayuwa don kanka-
\v 19 zai tafi zuwa tsarar ubanninsa kuma ba za su ƙara ganin haske kuma ba.
\v 20 Mai wadata amma ba shi da ganewa yana kamar dabbobi, dake lalacewa.
\s5
\c 50
\cl Zabura 50
\p
\d Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Maɗaukaki, Allah, Yahweh, ya yi magana yana kiran duniya daga fitar rana zuwa faɗuwarta.
\v 2 Daga Sihiyona, wuri mafi kyau, Allah yana haskakawa.
\s5
\v 3 Allahnmu ya zo kuma ba ya tsaye shiru; wuta na ci a gabansa, kuma babban hadari na kewaye da shi.
\v 4 Ya kira sammai da duniya domin ya shar'anta mutanensa.
\v 5 Tattaro mani amintattuna dukka gare ni, waɗanda suka yi alƙawari dani ta miƙa hadaya."
\s5
\v 6 Sammai zasu yi shelar ayyukan adalcinsa, gama Allah da kansa alƙali ne. Selah
\s5
\v 7 Ku ji, mutanena, kuma zan yi magana; Ni ne Allah, Allahnku.
\v 8 Ba zan kwaɓe ku domin hadayunku ba; hadayunku na ƙonawa na gabana kullum.
\s5
\v 9 Ba zan ƙarɓi bijimi daga gidanku ba, ko kuwa bunsurai daga garkenku ba.
\v 10 Gama kowanne naman jeji nawa ne da shanun kan tuddai dubu.
\v 11 Na san dukkan tsuntsayen duwatsu, kuma namomin jeji na fili nawa ne.
\s5
\v 12 Idan ina jin yunwa, ba zan faɗa maku ba; gama duniya tawa ce, da dukkan abin da ke cikinta.
\v 13 Ko zan ci naman bijimai ko in sha jinin awakai?
\s5
\v 14 Ku miƙa wa Allah hadayar godiya, kuma ku bada alƙawaranku ta rantsuwa ga Mai iko dukka.
\v 15 Ku yi kira gare ni a ranar damuwa; Zan cece ku, kuma zaku girmama ni."
\s5
\v 16 Amma ga mugaye Allah yace, "Me zaku yi da furtawar farillaina, har da zaku ɗauki alƙawarina a bakinku,
\v 17 tunda kun ƙi umarnina kuma kun jefar da maganganuna?
\s5
\v 18 Sa'ad da kuka ga barawo, kuka yarda da shi; kuna ayyuka tare da waɗanda ke yin zina.
\v 19 Kun bada bakinku ga mugunta, kuma harshenku na fitar da ruɗu.
\v 20 Ka zauna kana magana gãba da ɗan'uwanka; ka na saran ɗan mahaifiyarka.
\s5
\v 21 Kun aikata waɗannan abubuwan, amma na yi shiru, sai kuka zata cewa Ni kamarku nake. Amma zan kwaɓe ku in kawo a gaban idanuwanku, dukkan abubuwan da kuka yi.
\v 22 Ku lura da wannan da kulawa, ku da kuka mance da Allah, ko kuma zan yayyaga ku gutsu-gutsu, kuma babu wanda zai zo ya taimake ku!
\s5
\v 23 Wanda ya ke miƙa hadayar godiya yana yabona ne, kuma ga duk wanda ya ke rayuwarsa a hanyar da ta dace zan nuna masa ceton Allah."
\s5
\c 51
\cl Zabura 51
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda; Sa'ad da annabi Natan ya je gunsa bayan da ya kwanta da Batsheba.
\p
\v 1 Ka yi mani jinƙai, Allah, saboda amintaccen alƙawarinka; saboda kana yin ayyukan jinƙai masu yawa, ka tsige kurakuraina.
\v 2 Ka wanke ni sosai daga zunubina ka share mani laifina.
\s5
\v 3 Gama na san kurakuraina, kuma laifina yana gabana kullum.
\v 4 Gãba da kai, kai kaɗai, na yiwa laifi kuma na yi abin mugunta a fuskarka; ka yi dai-dai sa'ad da kayi magana; baka yi kuskure ba sa'ad da ka shar'anta.
\s5
\v 5 Duba, An haife ni a cikin zunubi; tun daga cikin mahaifiyata, ina cikin zunubi.
\v 6 Duba, kana so in yi marmarin aminci cikin zuciyata; a cikin zuciyata zaka sa in san hikima.
\s5
\v 7 Ka tsarkake ni da abin tsarkakewa, zan kuwa tsarkaka; ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
\v 8 Ka sa in ji daɗin rai da murna saboda ƙasusuwan da ka karya suyi farinciki.
\v 9 Ka ɓoye fuskarka daga laifofina ka hure dukkan zunubaina.
\s5
\v 10 Ka sa in so yi maka biyayya kullum, Allah, ka sa kullum in so yin abin da ke dai-dai.
\v 11 Kada ka kore ni daga gare ka, kar kuma ka ɗauke mani Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
\s5
\v 12 Ka maido mani da farincikin cetonka, ka riƙe ni da ruhun yin biyayya.
\v 13 Sa'an nan zan koya wa masu zunubi hanyoyinka, masu laifi kuma zasu komo gare ka
\s5
\v 14 Ka gafarce ni domin zub da jini, Allahn cetona, sai in yi sowa domin farincikin ayyukan adalcinka.
\v 15 Ubangiji, ka buɗe leɓunana, sai bakina ya furta yabonka.
\v 16 Gama baka murna da sadaka, da zan bada ita; Baka jin daɗin baye-bayen ƙonawa.
\s5
\v 17 Hadayu na Allah sune karyayyen ruhu. Kai, Allah, baza ka ƙi zuciya mai tuba da kuma tawali'u ba.
\v 18 Kayi nagarta cikin managarcin jin daɗinka ga Sihiyona; ka sake gina garun Yerusalem.
\v 19 Sa'an nan zaka yi murna da sadakokin ayyukan aɗalci da baye-bayen ƙonawa da ainihin baye-yen ƙonawa; sa'an nan mutanenmu zasu miƙa bijimai a bagadinka.
\s5
\c 52
\cl Zabura 52
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Salon waƙar Dauda; lokacin da Dowaj Ba'idome yazo ya faɗawa Saul, ya ce da shi, "Dauda ya zo gidan Ahimelek."
\p
\v 1 Meyasa kuke taƙama da tada fitina, ku manyan mutane? Alƙawarin Allah mai aminci yana zuwa kullum.
\v 2 Harshenku yana shirya hallakarwa kamar reza mai kaifi, kuna aikata yaudara.
\s5
\v 3 Kuna ƙaunar mugunta fiye da nagarta ƙarya kuma fiye da maganar adalci. Selah
\s5
\v 4 Ka na ƙaunar maganar da zata hallaka waɗansu, kai harshe mai yaudara.
\v 5 Haka Allah zai hallaka ka har abada, zai ɗauke ka daga rumfarka ya tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Selah.
\s5
\v 6 Masu adalci zasu gani su ji tsoro; su yi masa dariya su ce,
\v 7 "Ku dubi mutumin da bai mayar da Allah wurin fakewarsa ba, amma ya dogara ga dukiya da yawa, kuma yana da ƙarfi sa'ad da ya hallaka waɗansu."
\s5
\v 8 Amma ni, ina kama da itacen inabi mai sheƙi a cikin gidan Allah; zan dogara ga alƙawarin Allah mai aminci har abada.
\v 9 Zan yi godiya gare ka har abada saboda abin da kayi. Zan jira ga sunanka, saboda yana da kyau a cikin taron jama'arka masu tsoron ka.
\s5
\c 53
\cl Zabura 53
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Mahalat. Salon waƙar Dauda.
\p
\v 1 Wawa a zuciyarsa yace, "Babu wani Allah." Dukkan su sun gurɓace sun yi aikin mugunta; babu ko ɗaya dake aikata abin kirki.
\v 2 Allah ya dubo 'yan Adam daga sama, ya gani ko akwai wani mai fahimta, wanda ke neman sa.
\v 3 Dukkan su sun fanɗare. Gabaɗayan su sun gurɓace. Ba wani mai aikata abin kirki, babu ko guda ɗaya.
\s5
\v 4 Waɗanda ke aikata mugunta basu da fahimta ne--waɗanda ke cin naman mutanena kamar suna cin gurasa kuma ba su kira ga Allah ba?
\v 5 Suna cikin tsoro mai yawa ko da ya ke ba wani abin tsoratarwa; gama Allah zai tarwatsa duk wanda ya yi maku kwanto; irin waɗannan mutane zasu sha kunya gama Allah ya ƙi su.
\s5
\v 6 Oh, dama ceton Isra'ila ya zo daga Sihiyona! Sa'ad da Allah ya dawo da mutanensa daga bauta, Yakubu zai yi farinciki, Isra'ila kuma zai yi murna!
\s5
\c 54
\cl Zabura 54
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; Akan kayan kaɗe-kaɗe. Salon Dauda; lokacin da Zifaniyawa suka zo suka ce da Saul, "Ashe ba Dauda na ɓoye a cikinmu ba?"
\p
\v 1 Ka cece ni ya Allah, ta wurin sunanka, ka yi mani shari'a cikin ƙarfin ikonka.
\v 2 Allah, ka ji addu'ata, ka saurari kalmomin bakina.
\v 3 Gama bãƙi sun afko mani, lalatattun mutane na neman raina, basu sa Allah a gabansu ba. Selah.
\s5
\v 4 Duba, Allah shi ne mai taimako na, Ubangiji shi ne mai tallafa ta.
\v 5 Zai saka wa maƙiyana da mugunta; cikin amincinka, ka hallaka su!
\s5
\v 6 Zan baka hadaya ta yardar rai, zan yi godiya ga sunanka, Yahweh gama haka na da kyau.
\v 7 Gama ya kuɓutar dani daga kowacce damuwa; idona na duban nasara a kan maƙiyana.
\s5
\c 55
\cl Zabura 55
\p
\d Domin shugaban mawaƙa akan kayan kiɗa na tsarkiya. Salon Dauda.
\p
\v 1 Allah, ka ji addu'ata, kada ka ɓoye kanka daga roƙona.
\v 2 Ka saurare ni ka amsa mani, gama bani da hutu cikin wahaluna,
\v 3 saboda muryar maƙiyana, saboda matsin masu mugunta, gama suna tsananta mani cikin fushi.
\s5
\v 4 Zuciyata tana kiɗima a cikina, tsoron mutuwa ya faɗo kaina.
\v 5 Firgita da razana sun zo kaina, kuma fargaba ya sha kaina.
\s5
\v 6 Na ce, "Oh, dãma ina da fukafukai kamar kurciya! Da na tashi in je in huta.
\v 7 Da zan tafi can nesa in zauna a cikin jeji. Selah
\s5
\v 8 Da zan yi hanzari in sami mafaka daga hadari mai iska da guguwa.
\v 9 Ka haɗiye su, Ubangiji, kasa ruɗami cikin harsunansu! Gama na ga ta'addanci da hargitsi a cikin birnin.
\s5
\v 10 Suna ta yawo a kan ganuwarsa dare da rana. Mugunta da lalata suna cikin tsakiyarsa.
\v 11 Aikin mugunta na cikin tsakiyarsu; Tsanani da zamba ba su bar hanyoyinsu ba.
\s5
\v 12 Gama da maƙiyi ne ke tsauta mani, da na iya jurewa; ba kuma wanda ya ke gaba dani ne ya tada kansa gaba dani ba, da na ɓoye kaina daga wurin sa.
\v 13 Amma kai ne mutum kamar ni, abokina, da aminina kuma.
\v 14 Mun yi zumunci mai kyau tare, mun je gidan Yahweh tare da ƙarfafa.
\s5
\v 15 Bari mutuwa ta afko masu, bara su gangara lahira, gama mugunta ce kaɗai rayuwarsu, haka suke.
\s5
\v 16 Ni kuwa zan kira ga Allah, Yahweh zai cece ni.
\v 17 Ko da yamma ko da rana ko da safe, idan na yi ƙara da nishi zai ji muryata.
\v 18 Zai kuɓutar da raina daga masu kawo mani hari, gama waɗanda ke faɗa dani suna da yawa.
\s5
\v 19 Yahweh, wanda ya ke mulki tun daga farko, zai ji su ya ƙasƙantar dasu. Ba zasu taɓa canzawa ba, kuma ba sa tsoron Yahweh.
\s5
\v 20 Abokina ya tada hannuwansa gaba da waɗanda ke zaman salama dani. Bai cika alƙawarin da ya yi ba.
\v 21 Bakinsa yana da taushi kamar mai, amma zuciyarsa tana da hasala; kalmominsa suna da taushi kamar mai, amma a gaskiya takubba ne zararru.
\s5
\v 22 Ka ɗora wa Yahweh matsalolinka, shi zai riƙe ka, ba zai bari adalai su lalace ba.
\v 23 Amma kai Allah, za ka kawo miyagu cikin ramin hallakarwa. Masu shan jini da mayaudaran mutane ba za su rayu koda kamar na rabin sauran mutane ba, amma zan dogara gare ka.
\s5
\c 56
\cl Zabura 56
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Yanat elem rehokim. Zabura ta Dauda. Kewa; lokacin da Filistiyawa suka ɗauke shi zuwa Gat.
\p
\v 1 Ka ji ƙaina ya Allah, gama mutane na kawo mani hari! Dukkan yini suna tsananta ɓatancin da suke yi mani.
\v 2 Maƙiyana na musguna mani dukkan yini, gama waɗanda ke yin faɗa dani cikin wauta suna da yawa.
\s5
\v 3 Sa'anda na ji tsoro, zan dogara gare ka.
\v 4 Ina jin daɗin maganar Allah, ga Allah zan dogara; ba zan ji tsoro ba; me mutum kawai zai iya yi ma ni?
\s5
\v 5 Juya maganata suke yi dukkan yini, dukkan tunaninsu a kaina na mugunta ne.
\v 6 Sun tattara kansu, sun yi kwanto, suna bin sawuna, suna neman raina.
\s5
\v 7 Kada ka bari su dena yin mugunta. Ya Allah, ka kayar da su a cikin fushinka.
\v 8 Ka lissafa yawace-yawacena ka kuma sa hawayena cikin kwalba; ko ba a cikin littafinka suke ba?
\s5
\v 9 Sa'ad da na kira ka, maƙiyana zasu koma da baya, abin da na sani kenan, Allah yana tare da ni.
\v 10 A cikin Allah --wanda maganarsa nake yabo, a cikin Yahweh--
\v 11 a cikin Allah na dogara, bazan ji tsoro ba. Me wani zai iya yi mani?
\s5
\v 12 Aikina shi ne in cika wa'adina gare ka, Yahweh. Zan miƙa baye-baye na godiya a gare ka.
\v 13 Gama ka kuɓutar da raina daga mutuwa, ka tsare ƙafafuna daga faɗuwa, domin in yi tafiya a gaban Allah a cikin masu rai.
\s5
\c 57
\cl Zabura 57
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa; lokacin da ya gudu daga wurin Saul a cikin kogo.
\p
\v 1 Ka yi mani jinƙai, Yahweh, ka yi mani jinƙai, gama na fake wurin ka har sai waɗannan wahalu sun wuce. Na tsaya a ƙarƙashin inuwar fukafukanka har sai wannan hallaka ta ƙare.
\s5
\v 2 Zan yi kuka ga Allah Maɗaukaki, ga Allah, wanda ya ke yi mani komai.
\v 3 Zai aiko da taimako daga sama ya cece ni, yana jin haushin waɗanda ke ƙuje ni. Allah zai aiko mani da jinƙansa da amincinsa.
\s5
\v 4 Raina yana cikin zakuna, ina cikin waɗanda suke a shirye su cinye ni. Ina cikin mutanen da haƙoransu mãsu ne da kibau, haƙoransu kuma kamar takubba masu kaifi.
\v 5 Ya Yahweh, ka ɗaukaka a bisa sammai, bari ɗaukakarka ta zama a bisa duniya.
\s5
\v 6 Sun baza taru saboda ƙafafuna; Na shiga cikin ƙunci. Sun gina rami a gabana. Amma su da kansu ne suka faɗa a cikin tsakiyarsa! Selah
\s5
\v 7 Zuciyata ta kafu, Allah, zuciyata a kafe take; Zan raira, I, zan raira yabbai.
\v 8 Tashi, ke zuciyata mai daraja, tashi, ke sarewa da molo, nima tun da asuba zan tashi.
\s5
\v 9 A cikin jama'a zan yi maka godiya, ya Ubangiji; zan raira yabo gare ka a cikin al'ummai.
\v 10 Gama ƙaunarka tana da girma ƙwarai, ta kai har sama, amincika kuma ya kai gizagizai.
\v 11 Ka ɗaukaka ya Allah, sama da sammai, darajarka ta ɗaukaka bisa dukkan duniya.
\s5
\c 58
\cl Zabura 58
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsara ga salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa.
\p
\v 1 Ku shugabanni kuna faɗin gaskiya? Ku jama'a kuna yin shari'ar gaskiya?
\v 2 Babu, kun yi aikin mugunta cikin zuciyarku; kun baza tashin hankali da hannuwanku a cikin ƙasar dukka.
\s5
\v 3 Tun daga cikin ciki, masu mugunta ke fanɗarewa, tun daga haihuwarsu suke ratsewa, suna faɗin ƙarya.
\v 4 Dafinsu kamar dafin maciji ya ke, suna kama da kurmar ƙasa wadda take toshe kunnuwanta,
\v 5 wadda bata jin muryar masu layu, komai gwanintarsu.
\s5
\v 6 Ka karairaya haƙoransu a cikin bakunansu, ya Allah; ka ciccire manyan haƙoran 'yan zakuna, ya Yahweh.
\v 7 Bari su narke kamar ruwan dake gangarewa; idan suka harba kibansu, bari su zama kamar basu yi saiti ba.
\v 8 Bari su zama kamar dodon koɗi wanda ke narkewa ya lalace, kamar jaririn da mace ta haifa kafin lokacinsa yayi wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
\s5
\v 9 Kafin tukunyarka ta ji zafin wuta, zai kwashe su da guguwa, da ɗanye da wanda a ke ƙonawa dukka.
\v 10 Mai adalci zai yi farinciki sa'ad da ya ga ramako daga Allah, zai wanke ƙafafunsa da jinin masu mugunta,
\v 11 domin mutane su ce, "Gaskiya ne akwai lada ga mutum mai adalci, gaskiya ne akwai Allah wanda ke shar'anta duniya.
\s5
\c 59
\cl Zabura 59
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; wadda aka tsarawa salon murya. Zabura ta Dauda. Salon waƙa lokacin da Saul ya aika, suka kuma yi fakon gidan domin su kashe shi.
\p
\v 1 Ka kuɓutar dani daga maƙiyana, ya Allahna; ka ɗora ni can sama nesa daga waɗanda suke taso mani.
\v 2 Ka tsare ni daga waɗanda suke aikata mugunta, ka cece ni daga mutane waɗanda suke zubar da jini.
\s5
\v 3 Gama, duba, sun yi kwanto domin su ɗauki raina. Manya manyan masu aika mugunta sun tattara kansu gãba dani, amma ba saboda nayi kuskure ko zunubi ba, Yahweh.
\v 4 Sun shirya domin su tattake ni ba tare da laifina ba, duba, tashi ka taimake ni.
\s5
\v 5 Kai Yahweh, Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, tashi ka hori dukkan al'ummai. Kada ka ji tausan wani mai laifin aika mugunta ko ɗaya.
\s5
\v 6 Sukan dawo da yamma, su zagaya birnin suna haushi kamar karnuka.
\v 7 Duba suna yin gyatsa da bakunansu, takubba suna kan leɓunansu, suna cewa, "Wane ne ya ke sauraren mu?"
\s5
\v 8 Amma kai, Yahweh, kana yi masu dariya, dukkan al'ummai ba a bakin komai suke a gare ka ba.
\v 9 Allah, ƙarfina, zan kasa kunne gare ka, kaine hasumiyata mai tsawo.
\s5
\v 10 Allahna zai same ni da alƙawarin amincinsa, Yahweh, zai biya muradina a kan maƙiyana.
\v 11 Kada ka kashe su domin kada jama'ata su mance. Yahweh, garkuwarmu, ka warwatsa su, ka sa su faɗi.
\s5
\v 12 Saboda kalmomin bakinsa, da maganar leɓunansu, ka bari a kwashe su cikin girman kansu, kuma saboda la'ana da ƙarairayin da suka bayyana.
\v 13 Ka hallaka su cikin hasalarka, ka hallaka su domin kada su ƙara kasancewa. Bari su sani, Allah ne ke mulki cikin Yakubu kuma har iyakar duniya. Selah
\s5
\v 14 Sukan dawo da yamma, su zagaya birnin suna haushi kamar karnuka.
\v 15 Sukan yi yawo suna neman abinci, sukan yi gurnani idan ba su ƙoshi ba.
\s5
\v 16 Amma zan yi rairawa game da ƙarfinka, da safe kuma zan yi rairawa saboda ƙaunarka madawwamiya! Gama ka zama hasumiyata mai tsawo, mafaka a lokacin dani ke cikin matsala.
\v 17 A gare ka ƙarfina zan raira yabo, gama Yahweh ne hasumiyata mai tsawo, Allah mai amincin alƙawari.
\s5
\c 60
\cl Zabura 60
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Shushan Idut. Salon waƙar Dauda, domin koyarwa. Lokacin da ya yi faɗa da Aram Naharayim da kuma Aram Zoba da Yowab ya dawo daga kisan Idomawa dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.
\p
\v 1 Yahweh, ka yashe mu, ka kutsa cikin matsararmu, ka yi fushi, ka dawo da mu.
\s5
\v 2 Kasa ƙasar ta girgiza, ka ɓarke ta; tana girgiza, ka warkar da ɓarakarta.
\v 3 Kasa mutanenka su ga abubuwa masu wuya, kasa mun sha ruwan inabin tangaɗi.
\s5
\v 4 Saboda waɗanda ke darjantaka, kasa an tada tuta gãba da masu ɗaukar baka.
\v 5 Saboda waɗanda kake ƙauna su kuɓuta, ka amsa mani ka kuɓutar da mu da hannun damanka.
\s5
\v 6 Allah ya yi magana cikin tsarkinsa, "Zan yi farinciki, zan raba Shekem, zan karkasa Kwarin Sukot.
\v 7 Giliyad tawa ce Manasse ma tawa ce, Ifraim kuma hular kwanona ce, Yahuda kuma sandar girmana ce.
\s5
\v 8 Mowab bangajin wankina ne, zan ajiye takalmina a kan Idom, zan yi sowa ta murna saboda Filistiya."
\v 9 Wa zai kawo ni birni mai ƙarfi? Wa zai kai ni Idom?
\s5
\v 10 Amma kai Yahweh, ba ka yashe mu ba? Gama ba ka tafi yaƙi tare da sojojinmu ba.
\v 11 Ka taimake mu gãba da maƙiyanmu gama taimakon mutum banza ne.
\v 12 Da taimakon Allah za mu yi nasara; shi zai tattake maƙiyanmu.
\s5
\c 61
\cl Zabura 61
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; akan kayan kiɗa na tsarkiya. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka ji kukana Yahweh, ka amsa addu'ata.
\v 2 Daga iyakar duniya zan kira gare ka lokacin da zuciyata ta ruɗe, ka kai ni wurin dutsen da ya fi ni tsawo.
\v 3 Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi daga maƙiyana.
\s5
\v 4 Ka bar ni in zauna a shirayinka har abada! Ka bar ni in ɓoye cikin inuwar fukafukanka. Selah
\v 5 Gama kai Allah, ka ji wa'adina, ka bani gãdon waɗanda suke darjanta sunanka.
\s5
\v 6 Za ka sa ran sarki ya yi tsawo, shekarunsa kuma kamar tsararraki da yawa.
\v 7 Zai kasance a gaban Yahweh har abada.
\s5
\v 8 Zan raira yabo ga sunanka har abada, domin in cika wa'dina gare ka kowacce rana.
\s5
\c 62
\cl Zabura 62
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; bisa ɗabi'ar Yedutun. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Na yi shiru a gaban Yahweh kaɗai, daga wurin sa cetona ya ke zuwa.
\v 2 Shi kaɗai ne cetona, shi ne hasumiyata mai tsawo, ba zan girgiza ba sosai.
\s5
\v 3 Har yaushe ku dukka, zaku kai hari ga mutum ɗaya? Domin ku rufe shi kamar bangon da a ke jigina da shi, shinge mai rawa?
\v 4 Suna shawara da shi ne domin su ture shi daga matsayinsa mai daraja kaɗai; su na ƙaunar faɗin ƙarya, suna sa masa albarka da bakinsu, amma cikin zuciyarsu suna la'antar sa. Selah
\s5
\v 5 Ga Allah kaɗai nake saurare, gama shi ne begena.
\v 6 Shi kaɗai ne dutsena da cetona, shi ne hasumiyata mai tsawo ba zan jijjigu ba.
\s5
\v 7 Allah ne cetona da ɗaukakata, dutsen ƙarfina da mafakata a cikin Allah suke.
\v 8 Ku dogara gare shi kowanne lokaci, ku mutane, ku kafa zuciyarku a gaban sa, Allah shi ne mafakarmu. Selah
\s5
\v 9 Ba shakka mutanen da basu da matsayi ba komai bane, waɗanda ke da matsayin kuma ƙarya ne. Idan a ka auna su a ma'auni ba su da nauyi, inda za a haɗa su a auna ba su da nauyin komai.
\v 10 Kada ku dogara ga aikin zalunci ko ƙwace, kada ku sa begenku ga dukiyar wofi, gama ba su da amfanin komai, kada ku sa zuciya gare su.
\s5
\v 11 Allah ya yi magana sau ɗaya, sau biyu kuwa na ji wannan: iko na Allah ne.
\v 12 Kuma Ubangiji, a gare ka alƙawarin gaskiya yake. Gama kana ramawa kowanne mutum bisa ga abin da ya yi.
\s5
\c 63
\cl Zabura 63
\p
\d Zabura ta Dauda, lokacin da ya ke a cikin dajin Yahuda.
\p
\v 1 Allah, kai ne Allahna, da gaske raina ya ke neman ka, raina yana ƙishin ka, jikina ya ƙagara ya gan ka, a cikin ƙasa da turɓaya in da babu ruwa.
\v 2 Na dubo zuwa gare ka a cikin mutane masu tsarki domin in ga ikonka da ɗaukakarka.
\s5
\v 3 Saboda alƙawarin ka mai aminci yafi rai, leɓunana zasu yabe ka.
\v 4 Zan albarkace ka sa'ad da nake da rai, a cikin sunanka zan tada hannuwana.
\s5
\v 5 Zai zama kamar na ci abinci mai ɓargo da kitse, zan yabe ka da leɓuna masu farinciki,
\v 6 sa'ad da ni ke tunaninka a kan gadona, sa'ad da nake nazarin ka a cikin dare.
\s5
\v 7 Gama kai ne taimakona, a ƙarƙashin inuwar fukafukanka nake yin farinciki.
\v 8 Na manne maka hannun damanka yana tallafa ta.
\s5
\v 9 Amma waɗanda ke nema su hallaka raina, zasu faɗa cikin wuri mai zurfi na duniya;
\v 10 za a bashe su ga hannun masu aiki da takobi, zasu zama abicin diloli.
\s5
\v 11 Amma sarki zai yi farinciki cikin Allah, dukkan wanda ya rantse da shi, zai yi fahariya da shi kuma, amma bakin masu faɗin ƙarya za a kwaɓe shi.
\s5
\c 64
\cl Zabura 64
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka ji muryata, Allah, ka saurari ƙarata; ka tsare raina daga tsoron maƙiyana.
\v 2 Ka ɓoye ni daga shirin miyagu, daga hargowar masu aika mugunta.
\s5
\v 3 Sun wasa harsunansu kamar takubba, sun haro kibansu, wato maganganu masu ɗaci,
\v 4 domin su harbi wanda ba shi da laifi daga wurin da suke ɓoye, nan da nan suka harbe shi ba tare da sun ji tsoro ba.
\s5
\v 5 Suna ƙarfafa kansu cikin shirya mugunta, suna shawara a asirce domin su ɗana tarkuna, suna cewa, "Wa zai gan mu?"
\v 6 Suna ƙulla mugunta; "Mun gama" suka ce, "Natsastsen shiri" Tunanin ciki da zuciyar mutum suna da zurfi.
\s5
\v 7 Amma Yahweh, zai harbe su, nan da nan kibau zasu ji masu ciwo.
\v 8 Zasu yi tuntuɓe tun da ya ke harshensu yana gãba da su; dukkan waɗanda suka gan su zasu kaɗa kansu.
\v 9 Dukkan mutane zasu ji tsoro su bayyana ayyukan Allah. Cikin hikima zasu yi tunani a kan abin da ya yi.
\s5
\v 10 Masu adalci zasu yi murna da Yahweh, zasu sami mafaka a wurinsa. Dukkan waɗanda ke tafiya dai-dai zasu yi fahariya a cikin sa.
\s5
\c 65
\cl Zabura 65
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura. Waƙar Dauda.
\p
\v 1 Domin kai Allah a Sihiyona ne, yabonmu; da wa'adodinmu, za a kawo maka su a cikin Sihiyona.
\v 2 Kai da kake jin addu'a, a gare ka dukkan mutane za su zo.
\v 3 Laifofi sun yi mana tsayayya, amma za ka gafarta zunubanmu, za ka kuma gafarta su.
\s5
\v 4 Mai albarka ne mutumin daka zaɓa ya zo ya zauna a kusa da kai a cikin harabarka. Za mu gamsu da kyawawan abubuwan dake a gidanka, haikalinka mai tsarki.
\s5
\v 5 Cikin adalci za ka amsa mana ka yi abubuwan mamaki, kai Allah na cetonmu, Kai wanda dukkan mutane ke dagara gake ka har da waɗanda ke a can hayin teku.
\s5
\v 6 Gama kai ne ka kafa duwatsu suka yi ƙarfi, kai wanda ka yi ɗamara da iko.
\v 7 Kai ne ka kwantar da rurin tekuna da balalloƙansu da hargowar mutane
\s5
\v 8 Su waɗanda ke zama a can ƙarshen duniya suna jin tsoron alamun ayyukanka, kasa gabas da yamma suna farinciki.
\v 9 Ka zo domin ka taimaki duniya; ka yi mata banruwa, kasa ta yi arziki, kogin Allah na cike da ruwa; tun da ka hallicci duniya ka tanadawa ɗan Adam hatsi.
\s5
\v 10 Ka jiƙe kwarin kunyai a wadace, ka dai-daita kwarin kunyai sosai, kakan sa su yi taushi, kasa albarka a kan yabanyarsu.
\v 11 Ka yi wa shekara dajiyar alherai, sawayen karusanka suka zubo da kitse a kan duniya.
\v 12 Wuraren kiwo a jeji sun jiƙe da raɓa, ka sa tsire--tsire suyi farinciki.
\s5
\v 13 Wuraren kiwo sun cika da garkuna, kwarurruka sun cika da hatsi, suna shewa ta farinciki, suna rairawa.
\s5
\c 66
\cl Zabura 66
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Waƙa ta Zabura.
\p
\v 1 Ku yi sowa ta farinciki ga Yahweh, ku duniya dukka.
\v 2 Ku raira ɗaukakar sunansa, ku sa yabonsa ya zama ɗaukakakke.
\s5
\v 3 Ku ce da Allah, "Ayyukanka suna da ban tsoro! Da girman ikonka kasa maƙiyanka su yi ladabi a gabanka.
\v 4 Dukkan duniya zasu bauta maka su raira yabo gare ka, zasu yi rairawa ga sunanka." Selah
\s5
\v 5 Ku zo ku ga ayyukan Yahweh, ayyukansa na da ban mamaki ga 'yan Adam.
\v 6 Ya mayar da teku busasshiyar ƙasa; sun bi ta cikin teku da ƙafa; can muka yi farinciki a cikin sa.
\v 7 Da ikonsa ya ke mulki har abada, idanunsa suna lura da al'ummai; kada masu tawaye su ɗaukaka kansu. Selah
\s5
\v 8 Ku albarkaci Allah, ku mutane, bari a ji amon yabonsa.
\v 9 Ya bar mu cikin masu rai, bai bari ƙafafunmu suka yi tuntuɓe ba.
\s5
\v 10 Gama kai Yahweh ka gwada mu, ka gwada mu kamar yadda a ke gwada azurfa.
\v 11 Ka kawo mu cikin taru, ka ɗora mana kaya mai nauyi a kanmu.
\v 12 Ka bari mutane su tattaka mu, mun shiga cikin wuta da ruwa, amma ka kawo mu cikin wuri mai faɗi.
\s5
\v 13 Zan zo cikin gidanka da baiko na ƙonawa, zan cika wa'adodina gare ka,
\v 14 waɗanda leɓunana suka yi alƙawarin su, bakina kuma ya furta, sa'ad da nake cikin wahala.
\v 15 Zan kawo maka baiko na ƙonawa da dabbobi masu ƙiba da ƙamshin raguna; zan miƙa bijjimai da awaki.
\s5
\v 16 Ku zo ku saurara, dukkan ku dake tsoron Allah, zan bayyana abin da ya yi domin raina.
\v 17 Na yi kuka gare shi da bakina, harshena kuma ya yabe shi.
\v 18 Idan dana dubi zunubi a cikin zuciyata, da Ubangiji bai saurare ni ba.
\s5
\v 19 Amma da gaske Allah ya ji; ya kula da muryar addu'ata.
\v 20 Albarka ta tabbata ga Allah, wanda bai yi watsi da addu'ata ba ko ya ɗauke alƙawarinsa mai aminci daga gare ni ba.
\s5
\c 67
\cl Zabura 67
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; a kan kayan kiɗa na tsarkiya. Zabura, waƙa.
\p
\v 1 Bari Allah ya yi mana jinƙai, yasa fuskarsa ta haskaka wajenmu. Selah
\v 2 domin a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma cikin al'ummai dukka.
\s5
\v 3 Bari mutane su yabi Allah, dukkan mutane su yabe ka.
\v 4 Oh, bari al'ummai suyi murna su raira domin farinciki, gama za ka hukunta mutane cikin adalci, ka shugabanci mutanen duniya. Selah
\s5
\v 5 Bari mutane su yabe ka Allah, bari dukkan mutane su yabe ka.
\v 6 Ƙasa ta ba da amfaninta kuma Allah, Allahnmu ya albarkace mu.
\s5
\v 7 Allah ya albarkace mu kuma dukkan ƙarshen duniya na darjanta shi.
\s5
\c 68
\cl Zabura 68
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; Zabura ta Dauda, waƙa.
\p
\v 1 Bari Allah ya tashi, bari maƙiyansa su warwatse, bari kuma waɗanda ke ƙin sa su gudu daga gabansa.
\v 2 Ka kore su kamar yadda hayaƙi ke watsewa, kamar yadda saƙar zuma kan narke a gaban wuta, haka masu mugunta zasu lalace a gaban Allah.
\v 3 Amma bari masu adalci suyi murna, su ɗaukaka a gaban Allah; bari su yi farinciki su kuma ji daɗi.
\s5
\v 4 Ku raira ga Allah! Ku raira yabbai ga sunansa! Ku yabe shi wanda ke ratsawa ta filin kwarin Kogin Yodan! Yahweh ne sunansa! Ku yi farinciki a gabansa!
\v 5 Uban marar uba, alƙali saboda gwauraye, shi ne Allah daga wurin zamansa mai tsarki.
\v 6 Allah yakan sa masu kaɗaici cikin iyali, ya kan fito da 'yan kurkuku cikin waƙa, amma 'yan tawaye suna zama a faƙo.
\s5
\v 7 Allah idan da kayi tafiya a gaban mutanenka, idan ka bi ta cikin jeji, Selah
\v 8 Ƙasa takan girgiza, sama kan zubo da ruwa a gaban Allah, a gaban Allah sa'ad da ya zo Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra'ila.
\s5
\v 9 Kai, Allah, ka aiko da ruwa isasshe, ka ƙarfafa abin gãdonka sa'ad da suka gaji.
\v 10 Mutanenka suka zauna a ciki; kai, Allah, daga cikin alherinka ka bayar ga matalauta.
\s5
\v 11 Ubangiji ya bada umarnai, waɗanda suka sanar da su kuwa manyan sojoji ne.
\v 12 Sarakunan sojoji sun gudu, suka gudu, matayen dake zama a gida kuwa suka raba ganima.
\v 13 Kurciyoyi rufe da azurfa, da fukafukan zinariya rawaya. Sa'ad da waɗansu ku mutane kuka tsaya a garkunan tumaki, me ya sa kuka yi haka?
\s5
\v 14 Mai iko dukka ya tarwatsa sarakuna a wurin, sai ya zama kamar dusar ƙanƙara a Dutsen Zalmon.
\v 15 Babban dutse shi ne tudun ƙasar Bashan, dutse mai tsawo shi ne tudun ƙasar Bashan.
\v 16 Me yasa ki ke ƙyashi ke ƙasar kan tudu, a kan dutsen da Allah ya zaɓi ya zauna a wurin? Tabbas, Yahweh zai zauna a cikinta har abada.
\s5
\v 17 Karusan Allah dubu ashirin ne, dubbai bisa dubbai; Ubangiji na cikinsu a wuri mai tsarki, kamar a Sinai.
\v 18 Ka haye sama, ka kwashi 'yan bauta, ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga waɗanda suka yi faɗa da kai, domin kai Yahweh Allah, ka zauna a can.
\s5
\v 19 Albarka ga Ubangiji, wanda kullum ya ke kula da mu, Allah wanda shi ne cetonmu.
\v 20 Allahnmu, Allah ne wanda ke yin ceto. Yahweh, Ubangiji, shi ne kaɗai wanda zai iya kuɓutar da mu daga mutuwa.
\v 21 Amma Allah zai rotsa kan maƙiyansa, ta wurin fatar kai mai gashi ta waɗanda ke tafiya cikin yi masa laifi.
\s5
\v 22 Ubangiji yace, "Zan dawo da maƙiyana daga Bashan, zan dawo da su daga cikin zurfin teku
\v 23 domin ka ragargaza maƙiyanka, kana tsoma ƙafarka cikin jini, domin harsunan karnukanka su sami rabo daga cikin maƙiyanka."
\s5
\v 24 Sun ga shigowar ka, Allah, shigowar Allahna, Sarkina cikin wuri mai tsarki.
\v 25 Mawaƙa suka fara yin gaba, masu busa na bin baya, a tsakiya kuwa 'yammata na kaɗa molo.
\s5
\v 26 Ku albarkaci Allah a cikin taro, ku yabi Yahweh, ku zuriyar Isra'ila na gaskiya.
\v 27 Da fari akwai Benyamin, kabila mafi ƙanƙanta, sai kuma shugabannin Yahuda da jama'arsu, shugabannin Zebulun da shugannin Naftali.
\s5
\v 28 Allahnka, ya Isra'ila ya umarta ƙarfinka, ka nuna ikonka, Allah, kamar yadda ka nuna shi a lokacin dã.
\v 29 Ka nuna mana ikonka daga Yerusalem inda sarakuna ke kawo maka kyautai.
\s5
\v 30 Yi ruri cikin yaƙi gãba da namomin jejin dake zama cikin iwa, a kan mutane, da bijimai masu yawa da 'yan maruƙa. Kunyatar dasu kasa su kawo maka kyautai, ka tarwatsa mutanen dake ƙaunar yin yaƙi.
\v 31 Sarakuna zasu fito daga Masar; Itofiya zata yi sauri ta kawo hannuwanta ga Allah.
\s5
\v 32 Ku raira yabbai ga Allah ku mulkokin duniya; Selah ku raira yabbai ga Yahweh.
\v 33 Gare shi wanda ke sukuwa kan saman sammai, shi wanda ya kasance tun zamanin dã; duba, ya tada muryarsa da iko.
\s5
\v 34 Ku furta ƙarfi ga Allah, darajarsa tana kan Isra'ila, ikonsa na cikin sararin sama.
\v 35 Allah, kai abin tsoro ne a cikin wurinka mai tsarki, Allah na Isra'la yana ba da ƙarfi da iko ga mutanensa. Albarka ga Allah.
\s5
\c 69
\cl Zabura 69
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; da aka tsarawa Shoshanayim. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka cece ni Allah, gama ruwaye sun sa raina cikin hatsari.
\v 2 Na nutse cikin laka, mai zurfi inda ba wurin tsayawa; na zo cikin ruwa mai zurfi, rigyawa ta sha kaina.
\s5
\v 3 Na gaji da kuka, maƙogwarona ya bushe, idanuna sun dishe sa'ad da nake jiran Allahna.
\v 4 Waɗanda ke ƙi jinina ba dalili sun fi gashin kaina yawa, su waɗanda zasu datse ni saboda dalilan da ba dai-dai ba, suna da ƙarfi, abin da ban sata ba, sai na mayar.
\s5
\v 5 Allah, ka san wawancina, zunubaina kuma ba ɓoye suke a gare ka ba.
\v 6 Kada waɗanda ke jiran ka su ji kunya saboda ni, Ubangiji Yahweh Mai Runduna, kada masu neman ka su ƙasƙanta saboda ni, Allah na Isra'ila.
\s5
\v 7 Saboda kai na jure da tsautawa; kunya ta rufe fuskata.
\v 8 Na zama bãƙo ga 'ya'uwana, bare kuma ga 'ya'yan mahaifiyata.
\v 9 Gama niyyar zuwa gidanka ta ɗauke hankalina, tsautawar waɗanda ke tsauta maka ta faɗo kaina.
\s5
\v 10 Idan na yi kuka na ƙi cin abinci, sai su zage ni.
\v 11 Idan kayan makoki suka zama kayan sawata, sai in zama abin misali gare su.
\v 12 Waɗanda ke zama a ƙofar birni magana suke yi a kaina, mashaya waƙa su ke yi a kaina.
\s5
\v 13 Amma ni addu'ata gare ka take, Yahweh, sa'ad da ka ga yayi dai-dai, ka amsa mani cikin aminci cetonka.
\v 14 Ka tsamo ni daga cikin laka, kada ka bari ni nutse; bari a ɗauke ni daga waɗanda ke ƙina, a kuma tsamo ni daga cikin ruwaye masu zurfi.
\v 15 Kada ka bari rigyawa ta sha kai na, kada ka bari zurfi ya haɗiye ni. Kada ka bari rami ya rufe bakinsa a kaina.
\s5
\v 16 Ka amsa mani Yahweh, gama alƙawarin amincinka yana da kyau; domin jiye-jiyen ƙanka suna da yawa zuwa gare ni, ka juyo wajena.
\v 17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka, gama ina cikin wahala, ka amsa mani da sauri.
\s5
\v 18 Ka zo wuri na ka cece ni, saboda maƙiyana ka fanshe ni.
\v 19 Ka san tsautawar da a ke yi mani, ka san kunyata, ka san ƙasƙancin da nake sha; dukkan magabtana a gabana suke.
\s5
\v 20 Tsautawa ta karya zuciyata; cike nake da nauyi; na duba ko wani zai ji tausayi na, amma ban samu ba.
\v 21 Sun ba ni dafi shi ne abincina, cikin ƙishina kuma sai suka ba ni ruwan tsami domin in sha.
\s5
\v 22 Bari teburin gabansu ya zama tarko, sa'ad da suke tsammanin suna lafiya bari ya zama tarko a gare su.
\v 23 Bari idanunsu su dishe yadda ba zasu iya gani ba; bari kwankwasonsu su riƙa yin rawa.
\s5
\v 24 Ka zuba masu hasalarka, bari zafin fushinka ya yi ƙuna a kan su.
\v 25 Bari wurin zamansu ya zama kufai; kada kowa ya zauna a rumfunansu.
\s5
\v 26 Gama sun tsanantawa wanda ka fyaɗe ƙasa. Sun ƙarawa waɗanda suka ji rauni zafin ciwo.
\v 27 Ka zarge su a kan aikata mugunta a kan mugunta; kada ka bari su zo cikin nasararka mai adalci.
\s5
\v 28 Bari a shafe su daga cikin lattafin rai, kada a rubutasu tare da tsarkaka.
\v 29 Amma ni matalauci ne mai baƙinciki, bari cetonka; Allah, ya sanya ni can sama.
\s5
\v 30 Zan yabi sunan Allah da waƙa, zan ɗaukaka shi da shaidar godiya.
\v 31 Wannan zai gamshi Yahweh fiye da sã da bijimi mai ƙahonni da kofatai.
\s5
\v 32 Masu taushin zuciya za su gani suyi murna, ku da kuke neman Yahweh, zukatanku zasu rayu.
\v 33 Gama Yahweh na sauraron mabuƙata, ba ya kuma raina 'yan sarƙarsa.
\s5
\v 34 Bari sama da ƙasa su yabe shi da tekuna da dukkan abubuwan dake iyo a cikinsu.
\v 35 Gama Allah zai ceci Sihiyona, zai sake gina biranen Yahuda; mutane zasu zauna a can ya zama nasu.
\v 36 Zuriyar bayinsa zasu gaje shi, waɗanda ke ƙaunar sunansa zasu zauna a can.
\s5
\c 70
\cl Zabura 70
\p
\d Domin shugaban mawaƙa Zabura ta Dauda; ta kawo tunawa.
\p
\v 1 Ka cece ni ya Allah, Yahweh, ka zo da sauri ka taimake ni.
\v 2 Bari waɗanda ke so su ɗauki raina su ji kunya su ƙasƙanta; bari su koma baya a wulaƙance, su waɗanda ke murna da raɗaɗina.
\v 3 Bari su koma baya cikin kunya, su waɗanda ke cewa, "Aha, aha."
\s5
\v 4 Bari dukkan waɗanda ke neman ka suyi farinciki, suyi murna a cikin ka, bari waɗanda ke ƙaunar cetonka koyaushe su ce, "A yabi Allah."
\v 5 Amma ni matalauci ne mai bukata, ka yiwo sauri wurina Allah, kai ne taimakona ka kuɓutar dani, Yahweh, kada ka yi jinkiri.
\s5
\c 71
\cl Zabura 71
\p
\v 1 Yahweh, a gare ka nake samun mafaka, kada ka taɓa bari in ji kunya.
\v 2 Ka kuɓutar da ni ka sa in zauna lafiya cikin adalcinka.
\v 3 Ka zama dutsen fakewa a gare ni inda zan zo ko yaushe, ka bada umarni a cece ni, gama kai ne dutsena da kagarata.
\s5
\v 4 Ka cece ni, Allahna daga hannun miyagu, daga masu shirya mugunta.
\v 5 Gama kai ne begena, Ubangiji Yahweh. Na dogara gare ka tun ina yaro.
\s5
\v 6 Kai ne kake ta taimako na tun daga cikin ciki; kai ne ka fito dani daga cikin mahaifiyata; yabona a gare ka ya ke koyaushe.
\v 7 Na zama misali ga mutane da yawa, kai ne mafakata mai ƙarfi.
\s5
\v 8 Bakina zai cika da yabonka, da ɗaukakarka dukkan yini.
\v 9 Kada ka yashe ni a lokacin dana tsufa, kada ka manta dani lokacin da ƙarfina ya ƙare.
\s5
\v 10 Gama maƙiyana maganata, waɗanda ke neman raina suna shiri tare.
\v 11 Sun ce, "Allah ya yashe shi, ku bi ku ɗauko shi, gama ba wanda zai cece shi."
\s5
\v 12 Allah, kada ka yi nisa dani, Allahna, ka yi sauri ka taimake ni.
\v 13 Bari su sha kunya su hallaka su waɗanda suka hasalar da raina; su ji kunya su hallaka. bari zarga da raini su rufe su, su waɗanda ke so su lahanta ni.
\s5
\v 14 Amma zan sa begena a gare ka, zan yabe ka gaba-gaba.
\v 15 Bakina zai yi maganar adalcinka da cetonka dukkan yini, koda yake ba zan iya gane shi ba.
\v 16 Zan zo da manyan ayyukan Ubangiji Yahweh, zan faɗi adalcinka, naka kaɗai.
\s5
\v 17 Allah, ka koya mani tun ina saurayi, har yanzu ina shelar ayyukanka na ban mamaki.
\v 18 I, ko lokacin da kaina ya yi furfura, Allah, kada ka yashe ni, ina ta shelar ƙarfinka ga tsara mai zuwa, ikonka kuma ga kowanne mai zuwa.
\s5
\v 19 Adalcinka kuma, ya Allah yana da tsawo ƙwarai, kai da ka yi manyan abubuwa, Allah, wane ne kamar ka?
\v 20 Kai da ka nuna mana wahalhalu da yawa masu tsanani, za ka farfaɗo damu, ka fito damu daga ƙarƙashin ƙasa.
\s5
\v 21 Ka ƙara mani martaba, ka juyo ka ƙarfafa ni.
\v 22 Zan kuma yi maka godiya da molo saboda amincinka, Allahna; gare ka zan yi yabo da molo, mai tsarki na Isra'ila.
\s5
\v 23 Leɓunana zasu yi sowa ta farinciki, sa'ad da nake raira yabo a gare ka-har da raina, wanda ka fanso.
\v 24 Harshena kuma zai yi maganar adalcinka dukkan yini; gama sun ji kunya sun rikice, su waɗanda ke nema su lahanta ni.
\s5
\c 72
\cl Zabura 72
\p
\d Zabura ta Suleman.
\p
\v 1 Ka ba sarki dokokinka masu adalci, Allah, adalcinka kuma ga ɗan sarkin.
\v 2 Dãma ya hukunta jama'arka da adalci, matalautanka kuma da adalci.
\v 3 Dãma duwatsu su fito da salama saboda mutanenka; dãma tuddai kuma su fito da adalci.
\s5
\v 4 Dãma ya hukunta mutane matalauta; dãma ya ceci 'ya'yan mabuƙata, ya ragargaza azzalumi.
\v 5 Dãma su ba ka daraja muddin rana tana haskakawa, wata kuma yana nan har zuwa tsararraki dukka.
\s5
\v 6 Dãma ya sauko kamar ruwan sama a kan ciyawar da a ka tattake, kamar zubowar ruwan sama a kan ƙasa.
\v 7 Dãma masu adalci su yalwata a kwanakinsa, dãma kuma a sami salama a yalwace har sai wata ya shuɗe.
\s5
\v 8 Dãma ya yi mulki daga teku zuwa teku, daga kogi har zuwa ƙarshen duniya.
\v 9 Dãma waɗanda ke zama a jeji su rusuna a gabansa; dãma maƙiyansa kuma su lashi turɓaya.
\v 10 Dãma sarkunan Tarshish da na tsibirai su kawo gaisuwa a gare shi, dãma sarakunan Sheba da Seba su ba shi kyautai.
\s5
\v 11 I, dãma dukkan sarakuna su rusuna a gabansa, dãma kuma dukkan al'ummai su bauta masa.
\v 12 Gama ya kan taimaki mabuƙacin da yayi kuka da matalaucin da ba shi da mai taimako.
\s5
\v 13 Ya ji tausayin mabuƙata da matalauta, ya kuma ceci ran mabuƙata.
\v 14 Ya fanshi rayukansu daga wahala da kuma wulaƙanci, jininsu kuma yana da daraja a idanunsa.
\s5
\v 15 Dãma ya rayu! Dãma a ba da zinariyar Sheba a gare shi. Bari mutane su yi masa addu'a koyaushe; dãma Yahweh ya albarkace shi dukkan yini.
\v 16 Dãma a sami hatsi a yalwace a cikin ƙasa, na kan tudu kuma amfaninsu ya yi yabanya. Dãma kawunan hatsinsu ya zama kamar Lebanon, dãma jama'a su sami albarka kamar ciyawa ta saura.
\s5
\v 17 Dãma sunansa ya kasance har abada, dãma sunansa ya ci gaba muddin rana ta nan; dãma jama'a su sami albarka ta wurinsa; dãma dukkan al'ummai su kira shi mai albarka.
\s5
\v 18 Dãma Allah Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zama mai albarka; wanda shi kaɗai ne ke yin abubuwan ban mamaki.
\v 19 Dãma sunansa mai daraja ya zama mai albarka har abada, dãma kuma dukkan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin -- Amin.
\v 20 Dauda ɗan Yesse ya gama yin addu'o'insa. Littafi na Uku.
\s5
\c 73
\cl Zabura 73
\p
\d Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Hakika Allah mai alheri ne ga Isra'ila, gare su da suke da tsabtar zuciya.
\v 2 Amma a gare ni kafafuna sun kusa su zame; kafafuna sun kusa su zame waje daga karkashina.
\v 3 saboda na ji kishin masu girmankai sa'ad da na ga wadatar masu mugunta.
\s5
\v 4 Gama basu da raɗaɗi har ranar mutuwarsu, amma suna da ƙarfi kuma suna ci da kyau. Basu da nawayar sauran mutane;
\v 5 Basu da masifu kamar na sauran mutane.
\s5
\v 6 Girmankai na rataye a wuyansu kamar sarƙa; tashin hankali ya rufe su kamar riga.
\v 7 Daga irin wannan makantar zunubi ke zuwa; mugayen tunani sun ratsa zukatansu
\s5
\v 8 Suna ba'a kuma suna magana cikin mugunta; cikin fankamarsu suna yin kurarin zalunci.
\v 9 Suna magana gãba da sammai, harsunan su kuma na tattaki a ƙasa.
\s5
\v 10 Domin haka mutanensa sun juya gare su isassun ruwaye sun cika kwararo.
\v 11 Suka ce, "Ta yaya Allah ya sani? Akwai wani sani a wurin maɗaukaki?"
\v 12 Kula: waɗannan mutane mugayene; a koyaushe a huce suke, sai ƙara zama mawadata suke yi.
\s5
\v 13 Lallai a banza na kiyaye zuciyata kuma na wanke hannuwana cikin rashin laifi.
\v 14 Kowacce rana ina shan azaba da horo kowacce safiya.
\v 15 Idan nace, "Zan faɗi waɗannan abubuwa," da naci amanar wannan tsarar ta 'ya'yanka.
\s5
\v 16 Ko da shike na yi ƙoƙarin fahimtar waɗannan abubuwa, ya zama da wahala a gare ni.
\v 17 Daga nan sai na tafi cikin wuri mai tsarki na Allah daga nan na fahimci makomarsu.
\s5
\v 18 Hakika ka sanya su a wurare masu santsi; ka kawo su ƙasa ga hallaka.
\v 19 Yadda suka zama jeji farat ɗaya! ƙarshensu yazo sun ƙarasa cikin babban tsoro.
\v 20 Sun zama kamar mafarki bayan da mutum ya farka; Ya Ubangiji, sa'ad da ka tashi, ba zaka yi tunanin komai game da waɗannan mafarkan ba.
\s5
\v 21 Gama zuciyata ta damu, a cikina nayi rauni. Na zama jahili na kuma rasa basira;
\v 22 Na zama kamar dabba marar tunani a gabanka.
\s5
\v 23 Duk da haka kullum ina tare da kai; Ka riƙe hannuna na dama.
\v 24 Zaka bishe ni da shawarar ka bayan wannan ka karɓe ni zuwa ɗaukaka.
\s5
\v 25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba wani a duniya da nake marmari in ba kai ba.
\v 26 Jikina da zuciyata sun yi sanyi, amma Allah shi ne ƙarfin zuciyata har abada.
\s5
\v 27 Waɗanda suke nesa da kai zasu lalace; zaka hallaka dukkan marasa aminci gare ka.
\v 28 Amma ni, abin da nake bukata shi ne in kusanci Allah. Na mai da Ubangiji Yahweh mafakata. Zan bayyana dukkan ayyukanka.
\s5
\c 74
\cl Zabura 74
\p
\d Salon waƙar Asaf.
\p
\v 1 Ya Allah, don me ka yashe mu har abada? Don me fushin ka yayi ƙuna a kan tumakin makiyayarka?
\v 2 Ka da tuna mutanenka, waɗanda ka saya a zamanin dã, kabila wadda ka fãnsa su zama abin gãdonka, da Tsaunin Sihiyona, inda kake zama.
\s5
\v 3 Kazo ka dubi dukkan hallakarwa, dukkan ɓarnar da maƙiyi yayi a cikin wuri mai tsarki.
\v 4 Abokan gãbar ka sun yi ruri a tsakiyar zaɓaɓɓen wurinka; sun kafa tutocin yaƙinsu.
\v 5 Sun sassare ruƙuƙin kurmi da gatura.
\v 6 Sun ragargaza sun kuma sassake su dukka; sun karya su da gatura da gudumai.
\s5
\v 7 Sun kunna wa wurinka mai tsarki wuta; sun tozarta wurin zaman ka, sun buga shi har ƙasa.
\v 8 A cikin zuciyarsu suka ce, "Zamu hallakar dasu dukka," Sun ƙone dukkan wuraren taruwarka cikin ƙasar.
\s5
\v 9 Bamu ga wasu alamu ba; ba sauran wani annabi, ba wani a cikin mu da yasan har yaushe wannan zai ƙare.
\v 10 Ya Allah, har yaushe maƙiyi zai yi ta cin mutuncin ka? Maƙiyi zai yi ta saɓon sunanka har abada?
\v 11 Donme ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fito da hannunka na dama daga cikin rigarka ka hallaka su.
\s5
\v 12 Duk da haka Allah sarkina ne tun zamanun dã, mai kawo ceto a duniya.
\v 13 Ka raba teku da ƙarfinka; ka farfasa kawunan dodannin teku cikin ruwaye.
\s5
\v 14 Ka murƙushe kan Lebiyatan; ka ciyar da waɗanda suke zama cikin jeji da shi.
\v 15 Ka karya buɗaɗɗun maɓuɓɓulai da ƙoramai; kasa koguna masu gudu su ƙafe.
\s5
\v 16 Yini naka ne, dare kuma naka ne; kaine ka sanya rana da wata.
\v 17 Kaine ka sanya dukkan iyakokin duniya; kayi damina da rani.
\s5
\v 18 Yahweh, Ka tuna yadda maƙiyi yayi ta jefa maganganun banza a kanka, wawayen mutanen nan sun yi saɓon sunanka.
\v 19 Kada ka miƙa ran kurciyarka ga naman jeji. Kada ka manta da ran mutanenka da ake zalunta har abada.
\s5
\v 20 Katuna da alƙawarinka, gama wurare masu duhu na ƙasa suna cike da tashin hankali.
\v 21 Kada ka bari waɗanda ake zalunta su dawo cikin kunya; bari talakawa da waɗanda ake zalunta su yabi sunanka.
\s5
\v 22 Ka tashi, ya Allah; ka kãre mutuncinka; ka tuna yadda wawaye suke zaginka dukkan yini.
\v 23 Kada ka manta da muryar magabtanka ko hargowar waɗannan da suke ci gaba da adawa da kai.
\s5
\c 75
\cl Zabura 75
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; ga Salon murya. Zabura ta Asaf, waƙa.
\p
\v 1 Muna yi maka godiya, ya Allah; muna godiya, domin ka bayyana kasancewarka; mutane suna faɗin ayyukanka na al'ajabi.
\v 2 A ƙayyadajjen lokaci zanyi hukunci da dai-daita.
\v 3 Koda ya ke duniya da mazauna cikinta sun girgiza cikin tsoro, na kafa wa duniya ginshiƙai. Selah
\s5
\v 4 Nace wa masu girmankai, "Kada kuyi girmankai," ga masu mugunta kuma, "Kada ku ɗaga ƙaho;
\v 5 kada ku ɗaga ƙahonku ga sammai; kada kuyi magana da ɗaga wuya na rashin mutuntawa."
\v 6 Ba daga gabas bane ko daga yamma, kuma ba daga jeji bane ɗaukaka take fitowa ba.
\s5
\v 7 Amma Allah ne mai shari'a; yakan ƙasƙantar yakan kuma ɗaukaka sama.
\v 8 Gama Yahweh ya riƙe ƙoƙon inabi cikin hannunsa mai sa buguwa, wanda yake gauraye da kayan yaji, yana tsiyayar da shi. Hakika dukkan miyagun duniya zasu shanye shi dukka.
\s5
\v 9 Amma zan ci gaba da faɗin abin da kayi; Zan raira yabbai ga Allah na Yakubu.
\v 10 Yace, zan datse dukkan ƙahonnin miyagu, amma ƙahonnin masu adalci zasu ɗaukaka."
\s5
\c 76
\cl Zabura 76
\p
\d Domin shugaban mawaƙa, a bisa kan girayu. Zabura ta Asaf, waƙa.
\p
\v 1 Allah ya sanar da kansa cikin Yahuda; sunansa mai girma ne cikin Isra'ila.
\v 2 Rumfarsa cikin Salem take; wurin zaman sa cikin Sihiyona ya ke.
\v 3 A can ya kakkarya kibawu na baka, garkuwa da takobi da sauran kayan yaƙi. Selah
\s5
\v 4 Ka haskaka da sheƙi kuma ka bayyana ɗaukakarka, daka sauka daga duwatsu, wurin daka kashe masu azabtar da kai.
\v 5 Masu ƙarfin zuciya an washe su; an kashe su. Dukkan jarumawa sun rasa mai taimako.
\s5
\v 6 Bisa ga tsautawarka, Allah na Yakubu, doki da mahayinsa sun faɗi sun mutu.
\v 7 Kai, I kaine za a ji tsoro; wa zai tsaya gabanka lokacin da kayi fushi?
\s5
\v 8 Daga sama kasa aji hukuncinka; duniya ta ji tsoro tayi shiru
\v 9 lokacin da kai, Allah, ka tashi don tabbatar da hukunci kuma ka ceci dukkan waɗanda ake zalunta na duniya. Selah
\s5
\v 10 Hakika fushin hukuncin ka akan ɗan adam zai kawo maka yabo; ka yiwa kanka ɗamara da sauran abin da ya ragu na fushinka.
\s5
\v 11 Kayi alƙawura ga Yahweh Allahnka ka kumaa cika su. Bari duk waɗanda suke kewaye da shi su kawo kyautai gare shi wanda ya isa a ji tsoronsa.
\v 12 Ya datse ruhun 'ya'yan sarakai; sarakunan duniya sun ji tsoron sa.
\s5
\c 77
\cl Zabura 77
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; kamar na Yedutun. Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Da muryata zan yi kira ga Allah; Zan yi kira da muryata ga Allah, Allah zai ji ni.
\s5
\v 2 A cikin ranar masifata na biɗi Ubangiji; da dare na miƙar da hannuwana waje, ba kuwa zasu gaji ba. Raina yaƙi ta'azantuwa.
\v 3 Na tuna da Allah yayin da nayi nishi; Nayi tunaninsa yayin dana sụma. Selah
\s5
\v 4 Ka riƙe idanuna a buɗe; na damu ƙwarai na kasa magana.
\v 5 Na tuna da kwanakin dã, game da lokuttan da suka wuce tun-tuni.
\s5
\v 6 A cikin dare na tuna da waƙar dana taɓa rairawa. Nayi tunani a hankali kuma nayi ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru.
\v 7 Ko Ubangiji zai ƙini har abada? Ba zai ƙara nuna cewa ya ji ɗaɗi na ba?
\s5
\v 8 Amintaccen alƙawarinsa ya tafi har abada? Ko alƙawarinsa ya tsinke har abada?
\v 9 Ko Allah ya manta zama mai alheri? Ko fushinsa ya kulle jinƙansa ne? Selah
\s5
\v 10 Nace, "Wannan baƙinciki na ne: Canjin hannun dama na Maɗaukaki a kanmu."
\s5
\v 11 Amma zan tuna da ayyukanka; Zan yi tunani game da ayyukanka na al'ajabi na dã.
\v 12 Zan yi bin-binin dukkan ayyukanka kuma in yi tunani a kansu.
\s5
\v 13 Hanyarka, ya Allah, mai tsarki ce, ba wani allah da za a kwatanta shi da Allahnmu babba?
\v 14 Kaine Allah wanda kake aikata al'ajibai; ka bayyana ƙarfinka tsakanin dangogi.
\v 15 Ka ba mutanenka nasara ta wurin girman ikonka - zuriyar Yakubu da Yosef. Selah
\s5
\v 16 Ruwaye sun ganka, ya Allah; ruwaye sun ganka, kuma sunji tsoro; zurfafa sun raurawa.
\v 17 Giza-gizai sun zubo da ruwa ƙasa; hadarin sammai sun yi tsawa; hasken walƙiyarka sun tashi kamar kibau.
\s5
\v 18 Muryar tsawarka an ji ta cikin guguwa; hasken ya ɗaga duniya; duniya ta raurawa ta girgiza kuma.
\v 19 Hanyarka tabi ta teku tafarkin ka kuma ta manyan ruwaye, amma ba a ga sawayenka ba.
\v 20 Ka bi da mutanenka kamar garken tumaki ta hannun Musa da Haruna.
\s5
\c 78
\cl Zabura 78
\p
\d Salon waƙar Asaf.
\p
\v 1 Ku ji koyarwata, ya mutanena, ku saurari maganar bakina.
\v 2 Zan buɗe bakina cikin misalai; Zan raira game da ɓoyayyun abubuwa na dã.
\s5
\v 3 Waɗannan sune abubuwan da muka ji muka kuma koya, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana. Ba zamu ɓoye su daga zuriyarsu ba.
\v 4 Zamu sanar da tsara mai zuwa game da yabban ayyukan Yahweh, ƙarfinsa, da al'ajiban da ya aikata.
\s5
\v 5 Gama ya tabbatadda shaidar alƙawari cikin Yakubu ya sanya shari'a cikin Isra'ila. Ya umarci kakanninmu cewa su koyar dasu ga 'ya'yansu.
\v 6 Ya umarta wannan domin tsara mai zuwa ta iya sanin umarnansa, 'ya'yan da ba a haifa ba, su kuma su faɗi wa 'ya'yansu.
\s5
\v 7 Daga nan sai su sa zuciyarsu ga Allah kada su manta da ayyukansa amma su kiyaye dokokinsa.
\v 8 Daga nan ba zasu zama kamar kakanninsu ba, da suka zama da taurin kai da tsara mai tayarwa, tsarar da zukatansu ba dai-dai suke ba, waɗanda ruhohinsu basu tsaya sun yi aminci ga Allah ba.
\s5
\v 9 'Ya'yan Ifraim sun riƙe makamai tare da bakukkuna, amma suka juya baya a ranar yaƙi.
\v 10 Basu kiyaye alƙawari da Allah ba, suka ƙi yin biyayya da dokarsa.
\v 11 Suka manta da ayyukansa, ayyukan al'ajiban daya nuna masu.
\s5
\v 12 Sun manta da ayyukan mamaki da yayi a idanun kakanninsu a cikin ƙasar masar, cikin ƙasar Zowan.
\v 13 Ya raba teku ya ƙetaradda su; ya sa ruwa ya tsaya kamar bangaye.
\v 14 Da rana ya bishe su da girgije dukkan dare kuma da hasken wuta.
\s5
\v 15 Ya tsaga duwatsu cikin jeji, ya basu ruwa a yalwace, isasshe dake iya cika zurfafan teku.
\v 16 Yasa rafuffuka su malala daga cikin dutse ya kuma sa ruwan ya gudana kamar koguna.
\s5
\v 17 Duk da haka suka ci gaba da yi masa zunubi, suna tayar wa Maɗaukaki cikin ƙasa busasshiya.
\v 18 Suka ƙalubalanci Allah cikin zukatansu ta wurin tambayar abinci domin ƙosar da marmarinsu.
\s5
\v 19 Sun yi wa Allah baƙar magana; suka ce, "Zai yiwu Allah ya shirya teburi a cikin jeji?
\v 20 Duba, lokacin da ya bugi dutsen, ruwaye suka ɓullo rafuffuka suka yi ambaliya. Amma zai yiwu ya bada gurasa kuma? Zai iya tanada nama domin mutanensa?"
\s5
\v 21 Lokacin da Yahweh ya ji wannan, yayi fushi; wutarsa tayi ƙuna akan Yakubu, fushinsa kuma ya hari Isra'ila,
\v 22 saboda basu gaskata Allah ba basu kuma dogara ga cetonsa ba.
\s5
\v 23 Duk da haka ya umarci sammai a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sararin sama.
\v 24 Ya zuba masu manna su ci, ya kuma basu hatsi daga sama.
\v 25 Mutane suka ci abincin mala'iku. Ya aika masu da abinci isasshe.
\s5
\v 26 Yasa iskar gabas ta hura cikin sama, ta wurin ikonsa kuma ya jagoranci iskar kudu.
\v 27 Ya zuba masu nama kamar ƙura, tsuntsaye da yawa kamar yashin teku.
\v 28 Suka faɗo a tsakiyar sansaninsu, ko'ina kewaye da rumfunansu.
\s5
\v 29 Suka ci suka ƙoshi sosai. Ya basu abin da suke marmari.
\v 30 Amma duk da haka basu cika ba; tun abincinsu na cikin bakinsu.
\s5
\v 31 Daga nan fushin Allah ya buge su ya kashe mafi ƙarfin su. Majiya ƙarfin Isra'ila ya buga su ƙasa.
\v 32 Duk da wannan, sun ci gaba da yin zunubi kuma basu gaskata ayyukan al'ajabansa ba.
\s5
\v 33 Domin haka Allah ya taƙaita kwanakin su; shekarunsu suna cike da razana.
\v 34 Duk sa'ad da Allah ya buge su, sai su fara neman sa, za su juyo su neme shi da gaske.
\s5
\v 35 Zasu tuna cewa Allah ne dutsensu Allah maɗaukaki kuma shi ne mai fansarsu.
\v 36 Amma suka yi masa daɗin baki suka kuma yi masa ƙarya da maganganunsu.
\v 37 Gama zukatansu basu dogara gare shi ba, basu yi aminci ga alƙawarinsa ba.
\s5
\v 38 Amma shi, mai tausayi ne, ya gafarta laifofinsu bai hallaka su ba. I, lokuta da yawa yakan janye fushinsa bai tayar da dukkan hasalarsa ba.
\s5
\v 39 Ya tuna cikin jiki aka yi su, iska mai wucewa da bata dawowa.
\v 40 Sau nawa suka yi ta tayar masa cikin jeji suka ɓata masa rai cikin hamada!
\v 41 Akai akai suka tuhunci Allah suka cakuni Mai tsarki na Isra'ila.
\s5
\v 42 Ba su tuna da ikonsa ba, yadda ya fanso su daga abokin gaba.
\v 43 Lokacin da ya aikata alamominsa masu tsoratarwa cikin Masar da al'ajabansa cikin yankin Zowan.
\s5
\v 44 Ya juyarda kogunan Masarawa su zama jini don kada su sha daga rafuffukansu.
\v 45 Ya aika da cincirindon ƙudaje da suka cinye su da kwaɗi da suka mamaye ƙasar.
\v 46 Ya bada amfaninsu ga fãra aikin hannun su kuma ga babe.
\s5
\v 47 Ya lalata inabinsu da ƙanƙara itatuwansu masu bada 'ya'ya ga jaura.
\v 48 Ya saukar da ƙanƙara ga garkunansu aradu kuma ta fãɗa akan dabbobinsu.
\v 49 Ya zuba masu zafin fushinsa. Ya aika da fushi, hasala, da wahala kamar wakili mai kawo masifa.
\s5
\v 50 Ya baje wa fushinsa hanya; bai barsu su rayu ba amma ya ba she su ga annoba.
\v 51 Ya kashe dukkan 'ya'yan fari cikin Masar, ɗan farin ƙarfinsu cikin rumfunan Ham.
\s5
\v 52 Ya fitar da mutanensa waje kamar tumaki ya bishe su cikin jeji kamar garke.
\v 53 Ya kare su kuma ba su ji tsoro ba, amma teku ya dulmiyadda abokan gabarsu.
\s5
\v 54 Daga nan ya kawo su kan iyakar ƙasarsa mai tsarki, zuwa tsaunin nan da hannun damansa ya saya.
\v 55 Ya kori al'ummai daga gaban su ya raba masu gadonsu. Ya sa kabilun Isra'ila suka zauna cikin rumfunansu.
\s5
\v 56 Duk da haka suka ƙalubalanci da tozartar da Allah Maɗaukaki kuma ba su kiyaye umarnansa ba.
\v 57 Sun yi rashin aminci suka yi yaudara kamar ubanninsu; suka zama marasa abin dogaro kamar tanƙwararren baka.
\s5
\v 58 Gama sun sa shi fushi da masujadansu kuma suka harzuƙa shi ga yin kishi da gumakansu.
\v 59 Sa'ad da Allah ya ji wannan, ya hasala ya ƙi Isra'ila gaba ɗaya.
\s5
\v 60 Ya yashe da wuri mai tsarki na Shilo, rumfar in da ya zauna a tsakiyar mutane.
\v 61 Ya bari a ƙwace ƙarfinsa ya bada ɗaukakarsa a cikin hannun abokan gãba.
\s5
\v 62 Ya miƙa mutanensa ga takobi, yayi fushi da abin gãdonsa.
\v 63 Wuta ta cinye majiya ƙarfinsu, "yanmatansu kuma ba su sami waƙar aure ba.
\s5
\v 64 Firistocinsu sun faɗi ta kaifin takobi, gwaurayensu kuma suka kasa yin kuka.
\v 65 Sa'an nan sai Ubangiji ya farka sai ka ce mai tashi daga barci, kamar jarumi wanda ya fasa kuwwa saboda buguwa da ruwan inabi.
\v 66 Ya kori magabtansa baya; ya sa su cikin kunya ta har abada.
\s5
\v 67 Ya ƙi rumfar Yosef, bai kuma zaɓi kabilar Ifraim ba.
\v 68 Ya zaɓi kabilar Yahuda da Tsaunin Sihiyona wanda yake ƙauna.
\v 69 Ya gina tsatsarkan wurinsa kamar sammai, kamar duniya wadda ya kafa ta har abada.
\s5
\v 70 Ya zaɓi Dauda, bawansa, ya ɗauke shi daga wurin tsaron tumaki.
\v 71 Ya ɗauke shi daga bin tumaki da ƙananan su, ya kawo shi ya zama makiyayin Yakubu, mutanensa, da Isra'ila, abin gãdonsa.
\v 72 Dauda yayi kiwonsu da mutuncin zuciyarsa, ya bishe su da gwanintar hannuwansa.
\s5
\c 79
\cl Zabura 79
\p
\d Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Ya Allah bãƙin alummai sun zo cikin gãdonka; sun kazantar da haikalinka maitsarki; sun maida Yerusalem ta zama tsibin kangaye.
\v 2 Sun bada gawawwakin bayinka a matsayin abinci ga tsuntsayen sararin sama, jikkunan amintattun mutanenka ga dabbobin duniya.
\v 3 Sun zubar da jininsu kamar ruwa kewaye da Yerusalem, ba wanda zai yi jana'izar su.
\s5
\v 4 Mun zama abin ba'a ga makwabtanmu, ba'a da reni ga waɗanda ke kewaye damu. Har yaushe, Yahweh? Zaka yi ta fushi har abada?
\v 5 Har yaushe kishin fushinka zai yi ta ci har abada?
\s5
\v 6 Ka zubo da fushinka kan al'umman da basu san ka ba da bisa mulkokin da basu kira bisa sunanka ba.
\v 7 Gama sun cinye Yakubu sun hallaka ƙauyukansa.
\s5
\v 8 Kada kayi ta tunawa da zunubin kakanninmu har su shafe mu; bari ayyukan jinƙanka su zo kanmu, gama mun yi sanyi ƙwarai.
\v 9 Ka taimake mu, ya Allah na cetonmu, domin ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka yafe zunubanmu sabili da sunanka.
\s5
\v 10 Don me al'ummai zasu ce, "Ina Allahn su?" Bari jinin bayinka da aka zubar yayi ramako akan al'ummai a idanunmu.
\v 11 Bari nishin ɗaurarru ya zo gabanka; da girman ikonka ka tsare 'ya'yan waɗanda aka yanke wa mutuwa da rai.
\s5
\v 12 Ya Ubangiji. Ka maida zagin da ƙasashe maƙwabtanmu suka zazzageka ka sau bakwai bisa cinyoyinsu.
\v 13 Don haka mu mutanenka da tumakin makiyayarka zamu yi maka godiya har abada. Za mu faɗi yabbanka ga dukkan tsararraki.
\s5
\c 80
\cl Zabura 80
\p
\d Domin shugaban mawaƙa shiryayyen salo domin Shoshanayim. Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Ka kasa kunne, Ya Makiyayi na Isra'ila, kai mai bida Yosef kamar tumaki; kai mai zama bisan Kerubim, ka haskaka a bisanmu!
\v 2 A idon Ifraim da Benyamin da Manasse, ka motsa ikon ka; zo ka cece mu.
\v 3 Ya Allah, ka maishe mu; ka sa fuskarka ta haskaka a bisanmu, mu kuwa zamu tsira.
\s5
\v 4 Ya Yahweh Allah mai runduna, har yaushe zaka yi fushi da addu'ar mutanenka?
\v 5 Ka ciyar dasu da gurasar hawaye ka basu hawaye mai yawa su sha.
\v 6 Kasa mana wani abin da zamuyi jayayya da maƙwabtanmu a kansa, maƙiyanmu kuma suna yi mana dariya tsakaninsu.
\s5
\v 7 Ya Allah mai runduna; ka dawo damu; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu tsira.
\v 8 Ka fito da kuringa daga Masar; Ka kori al'ummai ka dasa ta.
\s5
\v 9 Ka gyara kasa domin ta; ta kafa saiwa ta cika ƙasa.
\v 10 Duwatsu sun rufe ta da inuwarta, Rassanta suna kama da itacen sida na Allah.
\v 11 Ta miƙa rassanta har bakin teku tohonta kuma har bakin Kogin Yuferitis.
\s5
\v 12 Don me ka rushe garunta har dukkan masu wucewa ta hanyar zasu tsinki 'ya'yanta.
\v 13 Aladun kurmi sun batata, namomin jeji kuma suna kiwo cikin ta.
\s5
\v 14 Ya Allah mai runduna; ka juyo, ka duba daga sama kayi la'akari ka kula da wannan kuringar.
\v 15 Wannan itace sauyar daka dasa da hannunka na dama, reshen da kasa ya girma.
\v 16 An ƙone shi da wuta an sare shi ƙasa; sun hallaka saboda tsautawarka.
\s5
\v 17 Bari hannunka ya kasance bisa mutumin hannunka na dama, bisa ɗan mutum wanda kasa ya zama da karfi domin kanka.
\v 18 Daga nan ba zamu juya daga gare ka ba; ka farkar da mu, mu kuwa zamu kira bisa sunanka.
\s5
\v 19 Ya Yahweh, Allah mai runduna, ka dawo damu; kasa fuskarka ta haskaka a kanmu, ta haka zamu tsira.
\s5
\c 81
\cl Zabura 81
\p
\d Domin shugaban mawaƙa bisa ga salon Gitit. Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Ku raira da ƙarfi ga Allah karfinmu; ku tada muryar farinciki ga Allah na Yakubu.
\v 2 Ku raira waƙa ku kaɗa ganga, garaya mai daɗi da molo.
\v 3 Ku busa ƙahon rago a ranar tsayawar sabon wata, a ranar cikar wata, ranar da bukukuwanmu ke farawa.
\s5
\v 4 Gama farilla ce ga Isra'ila, sharia da Allah na Yakubu ya bayar.
\v 5 Ya bada ita a matsayin doka cikin Yosef lokacin da ya tafi gãba da kasar Masar, in da naji muryar da ban fahimta ba.
\s5
\v 6 Na kawar da nauyin daga kafaɗarsa; an raba hannunsa daga ɗaukar kwando.
\v 7 A cikin masifa ka yi kira, na taimake ka; Na amsa maka daga duhun tsawar girgije. Na gwada ka a bakin ruwayen Meriba. Selah
\s5
\v 8 Ku saurara, mutanena, gama zan gargaɗe ku, zan so da kun saurare ni!
\v 9 Kada wani bãƙon allah ya kasance a cikinku; baza kuyi sujada ga wani bãƙon allah ba.
\v 10 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga kasar Masar. Ku wage bakinku, ni ma in cika shi.
\s5
\v 11 Amma mutanena basu saurara ga maganata ba; Isra'ila bata yi mani biyayya ba.
\v 12 Domin haka na bar su da taurinkansu domin suyi abin da suka ga dama.
\s5
\v 13 Ina ma, mutanena zasu saurare ni; ina ma, mutanena zasu yi tafiya cikin tafarkuna.
\v 14 Dana hanzarta mamaye abokan gabarsu in kuma juya hannuna akan masu zaluntar su.
\s5
\v 15 Dama waɗanda suka ƙi Yahweh su faɗi cikin tsoro gabansa! Dama su ƙasƙanta har abada. Zan ciyar da Isra'ila da alkama mai kyau;
\v 16 Zan ƙosarda ku da zuma daga cikin dutse."
\s5
\c 82
\cl Zabura 82
\p
\d Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Allah yana tsaye cikin taron jama'ar Allah; cikin tsakiyar alloli yana zartar da hukunci.
\v 2 Har yaushe zaka yi hukuncin rashin gaskiya ka nuna kana goyon bayan masu mugunta? Selah
\s5
\v 3 Ka kare talakawa da marasa mahaifa; ka kare hakkin masu shan azaba da marasa galihu.
\v 4 Ka ceci fakirai da mabukata; ka fisshe su daga hannun mugu.
\s5
\v 5 Basu da sani basu kuwa da fahimta; suna kai da komowa cikin duhu; dukkan harsasun duniya sun rugurguje.
\s5
\v 6 Na ce, ku alloline, dukkan ku kuma 'ya'yan Maɗaukaki ne.
\v 7 Duk da haka za ku mutu kamar mutane kuma ku faɗi kamar ɗaya daga cikin sarakuna."
\s5
\v 8 Ya Allah, ka tashi, ka shar'anta duniya, gama kana da gãdo cikin dukkan al'ummai.
\s5
\c 83
\cl Zabura 83
\p
\d Waƙa. Zabura ta Asaf.
\p
\v 1 Ya Allah, kada kayi shiru! Kada ka manta damu kada kuma kaƙi taimakon mu, ya Allah.
\v 2 Duba, abokan gabarka suna tada hankali, su da suka ƙi ka sun tada kansu.
\s5
\v 3 Sun shirya wa mutanenka makirci suna ƙulli gaba da waɗanda ka kãre.
\v 4 Suka ce, "Ku zo mu hallaka su a matsayin al'umma. Daga nan ba za'a ƙara tunawa da sunan Yahweh ba.
\v 5 "Sun ƙulla Makirci tare dabararsu ɗaya ce; don suyi gãba dakai suka yi ƙawance.
\s5
\v 6 Wannan ya haɗa da rumfunan Idom da na Ishma'ilawa, da mutanen Mowab da Hagarawa, waɗanda suka ƙulla tare da
\v 7 Gebal, Ammon, Amalek; ya kuma haɗa da Filistiya da mazaunan Taya.
\s5
\v 8 Assuriya kuma ta hada kai dasu; suna taimakon zuriyar Lot. Selah
\s5
\v 9 Kayi masu kamar yadda kayi wa Midiyan kamar yadda kayi da Sisera da Yabin a Kogin Kishon.
\v 10 Suka hallaka a Endo suka zama kamar taki domin ƙasa.
\s5
\v 11 Ka sa shugabanninsu sun zama kamar Oreb da Zib, da dukkan sarakunansu kamar Ziba da Zalmunna.
\v 12 Suka ce, "Bari mu ɗaukar wa kanmu makiyayar Allah."
\s5
\v 13 Ya Allahna, ka maishe su kamar ƙurar guguwa, kamar ƙaiƙai gaban iska,
\v 14 kamar wuta mai cin kurmi, kamar harshen wuta mai kama duwatsu.
\v 15 Ka koresu da iskarka mai ƙarfi, ka razanar dasu da guguwar hadari.
\s5
\v 16 Ka cika fuskokinsu da kunya domin su nemi sunanka, Ya Yahweh,
\v 17 bari su sha kunya su firgita har abada; dama su lalace cikin kunya.
\s5
\v 18 Daga nan zasu sani kai kaɗai ne, Yahweh, kai ne Maɗaukaki bisa dukkan duniya.
\s5
\c 84
\cl Zabura 84
\p
\d Domin shugaban mawaƙa; Bisa ga salon Gitit. Zabura ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Ina misalin ƙaunar wurin da kake zaune, Yahweh mai runduna!
\v 2 Ina marmarin harabun Yahweh, marmarin da nake da shi dominsa yasa na suƙe. Zuciyata da dukkan kome nawa ya kira ga Allah mai rai.
\s5
\v 3 Har tsaddu ta samar wa kanta gida mashillira ta yi wa kanta sheka inda zata ajiye 'ya'yanta kusa da bagadanka, Yahweh mai runduna, sarkina, Allahna kuma.
\v 4 Masu albarkane waɗanda suka zauna cikin gidanka, zasu yita ci gaba da yabonka. Selah
\s5
\v 5 Mai albarkane mutumin da ƙarfinsa yana cikinka, wanda zuciyarsa ke marmarin zuwa Sihiyona.
\v 6 Cikin ratsawa zuwa kwarin Hawaye, sun iske maɓulɓulan ruwa domin sha. Ruwan farko ya rufe shi da albarku.
\s5
\v 7 Suna tafiya daga karfi zuwa karfi; kowanne ɗayan su ya bayyana gaban Allah cikin Sihiyona.
\v 8 Yahweh Allah mai runduna, kaji addu'ata; Allahn Yakubu, ka saurari abin da nake cewa! Selah
\v 9 Ya Allah, ka duba garkuwarmu; ka nuna damuwarka ga shafaffenka.
\v 10 Gama yini ɗaya cikin harabunka ya fi dubu a wani wuri. Na gwammace in zama mai tsaron ƙofa cikin gidan Allahna, da in zauna tsakanin rumfuna na masu mugunta.
\s5
\v 11 Gama Yahweh Allah shi ne ranar mu da garkuwa;
\v 12 Yahweh zai bada alheri da ɗaukaka; ba ya hana wani abu mai kyau ga waɗanda suke tafiya cikin gaskiya. Yahweh mai runduna, mai albarkane mutumin da ya ke dogara gare ka.
\s5
\c 85
\cl Zabura 85
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta 'ya'yan Kora.
\p
\v 1 Yahweh ka nuna wa ƙasarka tagomashi; ka dawo da lafiya da arzikin Yakubu.
\v 2 Ka yafe zunubin mutanenka; ka rufe dukkan zunubinsu.
\s5
\v 3 Ka janye dukkan fushinka; ka juya baya daga zafin fushinka.
\v 4 Ka dawo damu, Allahn cetonmu, kasa rashin jindaɗinka tare da mu ya wuce.
\v 5 Zaka yi ta fushi da mu har abada? Zaka yi ta yin fushi har ga tsararraki masu zuwa?
\s5
\v 6 Ba zaka sake falkar damu ba? Daga nan mutanenka za suyi murna a cikin ka.
\v 7 Ka nuna ma na amincin alƙawarinka ya Yahweh, ka bamu cetonka.
\s5
\v 8 Zan saurari abin da Yahweh Allah zai ce, gama zai kawo salama ga mutanensa, amintattun mabiyansa. duk da haka ba zasu koma ga bin hanyoyinsu na wauta ba.
\v 9 Hakika cetonsa yana kusa da masu tsoronsa; daga nan ɗaukaka zata zauna cikin ƙasarmu.
\s5
\v 10 Alƙawarin aminci da gaskiya sun haɗu tare; adalci da salama sun yi wa juna sumba.
\v 11 Gaskiya tana tsirowa daga ƙasa, adalci yana kallo daga sama.
\s5
\v 12 I, Yahweh zai ba da albarku masu kyau, ƙasarmu zata bada amfaninta.
\v 13 Adalci zai tafi gabansa kuma zai yi hanya domin sawayensa.
\s5
\c 86
\cl Zabura 86
\p
\d Addu'ar Dauda.
\p
\v 1 Ka saurara, Yahweh, ka kuma amsa mani, domin ni matalauci ne, wanda aka tsanantawa.
\v 2 Ka kare ni domin ina biyayya, ya Allahna, ka ceci bawanka wanda ya ke dogara a gare ka.
\s5
\v 3 Ka yi mani jinƙai, ya Ubangiji, don a gare ka nake kuka dukkan yini.
\v 4 Kasa bawanka yayi murna domin a gare ka nayi addu'a ya Ubangiji.
\s5
\v 5 Ubangiji, kai nagari ne, kuma kana shirye kayi gafara. Kana kuma nuna jinƙai ga duk waɗanda suka yi kuka gare ka.
\v 6 Yahweh, ka ji addu'ata, ka kuma ji muryar roƙona.
\v 7 A ranar masifata nayi kira gare ka, domin zaka amsa mani.
\s5
\v 8 Ya Ubangiji ba wanda za a kwatanta shi da kai a cikin alloli, ba ayyukan da za a kwatanta su da naka.
\v 9 Dukkan al, umman da kayi zasu zo su rusuna maka. Za su girmama sunanka.
\s5
\v 10 Domin kana da girma kana kuma yin abubuwan al'ajabi, kai kaɗai ne Allah.
\v 11 Ka koya mani tafarkinka Yahweh. Sa'an nan zan yi tafiya cikin gaskiyarka. Ka haɗa zuciyata ta girmamaka.
\v 12 Ubangiji Allahna zan yabe ka da dukkan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada.
\s5
\v 13 Domin alƙawarinka mai aminci yana da girma a gare ni, domin ka ceto raina daga zurfafan Lahira.
\v 14 Ya Allah marasa hankali sun tasar mani. Ƙungiyar masu husuma sun tasar mani suna neman raina, ba su kula da kai ba.
\s5
\v 15 Amma kai, Ubangiji, Allah ne mai jinƙai da alheri, mai jinkirin fushi, mai mayalwacin alƙawari mai aminci da kuma madogara.
\v 16 Ka juyo wurina kayi mani jinƙai; ka bada ƙarfinka ga bawanka; ka ceci ɗan baiwarka.
\v 17 Ka nuna mani alamar jinƙanka. Sa'an nan waɗanda ke ƙi na zasu gani su kunyata saboda kai, Yahweh, ka taimake ni ka kuma ta'azantar dani.
\s5
\c 87
\cl Zabura 87
\p
\d Zabura ta 'ya'yan Kora; waƙa.
\p
\v 1 Akan dutse mai tsarki birninsa da ya samo ya tsaya;
\v 2 Yahweh yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da rumfuna na Yakubu.
\v 3 An faɗi maɗaukakan abubuwa game da kai birnin Allah. Selah.
\s5
\v 4 Na ambaci Rahab da Babila ga masu bi na. Duba, akwai Filistiya, da Taya, tare da Itofiya- kuma zasu ce, 'Wannan an haife shi a can.'"
\s5
\v 5 Ga Sihiyona za'a ce, "Dukkan wɗannan an haife su a cikinta, kuma Mafi Girma dukka da kansa zai kafa ta."
\v 6 Yahweh ya rubuta a cikin littafin ƙidaya na al'ummai, "Wannan an haife shi a can." Selah
\s5
\v 7 Haka kuma mawaƙa da masu rawa suka faɗa tare, "Dukkan maɓulɓulaina suna cikinka."
\s5
\c 88
\cl Zabura 88
\p
\d Waƙar zabura ta 'ya'yan Kora; domin shugaban mawaƙa; da aka shirya bisa ga salon Mahalat Leyanot. Salon Heman Ezrahiye.
\p
\v 1 Yahweh, Allah na cetona, Na yi kuka a gabanka dare da rana.
\v 2 Ka ji addu'ata, ka saurari kukana.
\s5
\v 3 Domin na cika da damuwoyi, raina kuma ya kai Lahira.
\v 4 Mutane sun ɗauke ni kamar waɗanda suka faɗa rami; Mutumin da ba shi da ƙarfi.
\s5
\v 5 An yi watsi da ni a cikin matattu; Ina kama da matacce dake kwance a kabari, game da wanda ka daina kula da shi saboda an datse su daga ikonka.
\v 6 Ka ajiye ni a wuri mafi ƙasƙanci na cikin rami, a wuri mai zurfi da kuma duhu.
\s5
\v 7 Fushinka yayi nauyi a kaina, kuma dukkan rigyawarka tabi ta kaina. Selah
\s5
\v 8 Saboda kai, abokan tarayyata suka yashe ni. Ka maishe ni abin rawar jiki a gare su. An shinge ni a ciki ba kuma zan tsira ba.
\s5
\v 9 Idanuna sun gaji da damuwa; Dukkan yini ina kira gare ka, Yahweh; na buɗe hannuwana gare ka.
\v 10 Ko zaka yi mu'ujuzai ga matattu? Ko waɗanda suka mutu zasu tashi su yabe ka? Selah
\s5
\v 11 Ko za'a yi shelar alƙawarin amincinka a kabari, amincinka kuma a wurin matattu?
\v 12 Ko za'a san ayyukanka na al'ajibai a cikin duhu, ko kuma adalcinka a wurare na mantuwa?
\s5
\v 13 Amma nayi kuka gare ka, Yahweh; da safe addu'ata tana zuwa gare ka.
\v 14 Yahweh me yasa ka ƙi ni? Me yasa ka ɓoye fuskarka daga gare ni?
\s5
\v 15 Har kullum an tsananta mani kamar a hallaka ni tun daga ƙuruciyata. Na sha hukuncin horonka ina cikin fargaba.
\v 16 Ayyukanka na fushi sun bi ta kaina, kuma ayyukanka masu ban razana sun kawar da ni.
\s5
\v 17 Sun kewaye ni kamar ruwa a dukkan yini; dukkan su sun kewaye ni.
\v 18 Ka kawar da abokaina da duk waɗanda suka shaƙu dani daga gare ni. Wanda ya shaƙu dani duhu ne kaɗai.
\s5
\c 89
\cl Zabura 89
\p
\d Salon Etan Ezrahiye.
\p
\v 1 Zan raira yabon ayyukan alƙawarin amincin Yahweh na har abada, Zan yi shelar gaskiyarka ga tsararraki masu zuwa.
\v 2 Domin na ce "Anyi amintaccen alƙawari na har abada; ka kuma kafa gaskiyarka a cikin sammai."
\s5
\v 3 Na yi alƙawari da zaɓaɓɓena, nayi alƙawari ga Dauda bawana.
\v 4 Zan kafa zuriyarka har abada, kuma zan kafa kursiyinka a dukkan tsararraki." Selah
\s5
\v 5 Sammai na yabon al'ajibanka, Yahweh; a na yabon gaskiyarka a taron tsarkaka.
\v 6 Domin da wane ne za a kwatanta shi da Yahweh a sammai? Wane ne za a kwatanta shi da Yahweh?
\s5
\v 7 Shi Allah ne dake da girmamawa a taron tsarkaka yana kuma da kwarjini ga dukkan waɗanda suka kewaye shi.
\v 8 Yahweh Allah mai runduna, wa keda ƙarfi kamar ka? amincinka ya kewaye ka.
\s5
\v 9 Kana mulkin haukan teku; lokacin da ambaliyoyi su ka tashi ka kwantar da su.
\v 10 Ka buge Rahab kamar wadda aka kashe. Ka warwatsa maƙiyanka da ƙarfin damtsenka.
\s5
\v 11 Sammai naka ne, haka kuma duniya. Ka hallici duniya da dukkan abin da ke cikin ta.
\v 12 Ka hallici arewa da kudu. Tabor da Harmon na murna a cikin sunanka.
\s5
\v 13 Kana da damtse mai iko da kuma hannu mai ƙarfi, hannunka na dama kuma yana da tsayi.
\v 14 Aikin adalci da adalci su ne ginshiƙan mulkinka. Alƙawari mai aminci da kuma dogara daga gare ka suke zuwa.
\s5
\v 15 Masu albarka ne waɗanda ke yi maka sujada! Yahweh, suna tafiya a cikin hasken fuskarka,
\v 16 Suna murna da sunanka dukkan yini. Ayyukan adalcinka kuma sun ɗaukaka ka.
\s5
\v 17 Kai ne ƙarfin ikonsu, ta wurin jinƙanka kuma mun yi nasara.
\v 18 Domin garkuwoyinmu na Yahweh ne; sarkinmu kuma na Mai tsarki na Isra'ila ne.
\s5
\v 19 Tun da daɗewa kayi magana da tsarkakanka ta wurin wahayi; kace "Na sa kambi bisa mai iko; Na tayar da wani da aka zaɓa daga cikin mutane.
\v 20 Na zaɓi Dauda bawana, da maina na keɓe shi.
\v 21 Hannuna zai taimake shi. Damtsena kuma zai ƙarfafa shi.
\v 22 Ba maƙiyin da zai yaudare shi; ba kuma ɗan magabcin da zai ƙuntata masa.
\v 23 Zan buge maƙiyansa a gabansa, masu ƙin sa kuma zan hallaka su.
\s5
\v 24 Gaskiyata da alƙawarin amincina zai kasance tare da shi, ta wurin sunana zai yi nasara.
\v 25 Zan ɗora hannunsa a kan teku, hannunsa na dama kuma bisa koguna.
\v 26 Zai yi kira gare ni yace kai ne ubana, 'Kai ne Ubana kuma Allahna, da kuma dutsen cetona.'
\s5
\v 27 Zan ɗora shi a matsayin ɗan farina, mafi ɗaukaka a cikin sarakunan duniya.
\v 28 Zan tsawaita alƙawarin amincina a gare shi har abada; zan kuma riƙe alƙawarina da shi.
\v 29 Zan kafa zuriyarsa har abada, mulkinsa kuma zai kai har sammai.
\s5
\v 30 Idan 'ya'yansa suka yi watsi da shari'una suka kuma yi rashin biyayya ga sharuɗɗana,
\v 31 idan kuma sun karya dokokina basu kuma kiyaye umarnaina ba,
\v 32 to sai in hori rashin biyayyarsu da sandar ƙarfe laifofinsu kuma da nushe-nushe.
\s5
\v 33 Amma ba zan janye madawammiyar ƙaunata ba daga gare shi ko kuma in yi rashin aminci a kan alƙawarina ba,
\v 34 Ba zan karya alƙawarina ba ko kuma in canza maganganun leɓuna na ba.
\s5
\v 35 Sau ɗaya tak na rantse da tsarkina-Ba zan yiwa Dauda ƙarya ba:
\v 36 zuriyarsa zata ɗore har abada mulkinsa kuma zai zama kamar rana a gabana.
\v 37 Za a kafa shi har abada kamar wata, amintaccen mashaidi a sararin sama." Selah
\s5
\v 38 Amma ka ƙi ka kuma yi watsi; kana kuma fushi da shafaffen sarki.
\v 39 Ka kuma musunta alƙawarin bawanka. Ka ƙazamtar da rawaninsa a ƙasa.
\v 40 Ka kuma rushe katangunsa dukka. Ka kuma mayar da ƙarfafan kagarunsa kufai.
\s5
\v 41 Duk masu wucewa suka yi masa ƙwace. Ya zama abin ƙyama a cikin maƙwabta.
\v 42 Ka tayar da hannun damar maƙiyansa; ka kuma sa dukkan maƙiyansa suyi farinciki.
\v 43 Ka juya takobinsa ka kuma hana shi ya tsaya a lokacin yaƙi.
\s5
\v 44 Ka kawo ƙarshen martabarsa; ka kuma karya mulkinsa
\v 45 Ka gajarta kwanakin ƙuruciyarsa. Ka kuma rufe shi da kunya. Selah
\s5
\v 46 Yahweh har yaushe? Ko zaka ɓoye kanka, har abada? Har yaushe zaka bar fushinka yayi ta ƙuna kamar wuta?
\v 47 Oh, ka yi tunanin yadda gajartar lokacina ya ke, da kuma rashin amfanin yadda ka hallici dukkan mutane!
\v 48 Wane ne zai rayu ba zai mutu ba, ko kuma ya iya kuɓutar da ransa daga Lahira? Selah
\s5
\v 49 Ya Ubangiji, ina ayyukanka na dã a kan alƙawarin amincinka da ka rantsewa Dauda a cikin gaskiyarka?
\v 50 Ka tuna ya Ubangiji da rainin da aka yi wa bayinka da kuma yadda na ji a zuciyata ire-iren cin mutunci daga al'ummai.
\v 51 Maƙiyanka suna nuna wulaƙanci, Yahweh; suna wulaƙanta sawayen keɓaɓɓenka.
\s5
\v 52 Albarka ta tabbata ga Yahweh har abada. Amin da Amin. Littafi na Huɗu
\s5
\c 90
\cl Zabura 90
\p
\d Addu'ar Musa mutumin Allah.
\p
\v 1 Ubangiji kai ne mafakarmu a dukkan tsararraki.
\v 2 Kafin a kafa duwatsu, ko kuma ka hallici duniya da abin dake cikinta, har abada abadin, kai Allah ne.
\s5
\v 3 Ka kan komar da mutum ƙura, ka ce "ku koma ku zuriyar ɗan adam."
\v 4 Domin shekaru dubu a gare ka kamar jiya ne data wuce, kamar kuma sa'ar tsaro ce ta dare.
\s5
\v 5 Ka share su kamar da rigyawa sun kuma yi barci; da safe suna kama da ciyayi da suka yi girma.
\v 6 Da safe sukan yi yabanya suyi girma; da yamma kuma su kan yanƙwane su bushe.
\s5
\v 7 Hakika, an cinye mu a cikin fushinka, a cikin fushinka kuma mun gigice.
\v 8 Ka jejjera zunubanmu a gabanka, laifofinmu na ɓoye kuma kasa su a hasken gabanka.
\s5
\v 9 Ran mu yana shuɗewa a ƙarƙashin fushinka;
\v 10 shekarunmu kuma sun wuce da sauri kamar ajiyar zuciya. Shekarunmu saba'in ne, ko kuma tamanin in muna da lafiya; amma koma da shekarunmu mafiya kyau suna cike da damuwa da baƙinciki. Hakika, sukan wuce da sauri sai kuma mu ɓace.
\s5
\v 11 Wa ya san ƙarfin fushinka, da kuma fushinka da ke dai-dai da tsoronka?
\v 12 ka koya mana yadda zamu yi la'akari da rayuwarmu domin mu yi rayuwa cikin hikima.
\v 13 Juya, Yahweh! Har yaushe zai zama? Ka ji tausayin bayinka.
\s5
\v 14 Ka ƙosar da mu da alƙawarin amincinka da safe domin muyi farinciki a cikin dukkan kwanakinmu.
\v 15 Ka samu muyi murna gwargwadon kwanakin daka azabtar damu da kuma shekarun da muka fuskanci matsala.
\v 16 Ka bar bayinka suga aikinka, kuma ka bar 'ya'yanmu suga darajarka.
\s5
\v 17 Da ma jinƙan Ubangiji Allahnmu ya zama namu; ka wadata aikin hannuwanmu; hakika, ka wadata aikin hannuwanmu.
\s5
\c 91
\cl Zabura 91
\p
\v 1 Wanda ya ke rayuwa a bukkar Mafi Ɗaukaka zai zauna a inuwar Mai Iko Dukka.
\v 2 Zan ce da Yahweh, "Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda na dogara a gare shi."
\s5
\v 3 Domin zai kuɓutar da kai daga wayon tarkon maharbi kuma daga annoba mai hallakarwa.
\v 4 Zai rufe ka da fukafukansa, kuma a ƙarƙashin fukafukansa zaka sami mafaka. Madogararsa garkuwa ce da kuma kariya.
\s5
\v 5 Ba za ka ji tsoron masifa ba da dare, ko kuma kibiyoyin dake shawagi da rana.
\v 6 Ko kuma annobar dake aukowa da dare ba.
\v 7 Ko cutar dake samuwa da tsakar rana ba. Dubu zasu faɗi a gefenka dubu goma kuma a hannunka na dama, amma ba zasu iso wurinka ba.
\s5
\v 8 Zaka duba ne kawai kaga hukuncin da za'a yiwa miyagu,
\v 9 Domin Yahweh ne mafakata! Kuma ka maida Maɗaukaki mafakarka.
\s5
\v 10 Ba mugun abin da zai same ka; ba wani abu mai cutarwa da zai kusanci gidanka.
\v 11 Domin zai umarci mala'ikunsa su kare ka, su kuma yi tsaronka a cikin dukkan hanyoyinka.
\s5
\v 12 Zasu tayar da kai tsaye da hannunsu domin kada kayi tuntuɓe a kan dutse.
\v 13 Zaka hamɓare zãkuna da damisoshi a ƙarƙashin ƙafafunka; zaka tattake 'yan zãkoki da kuma macizai.
\s5
\v 14 Saboda ya sadaukar da kansa gare ni, zan cece shi. Zan kare shi saboda yana yi mani biyayya.
\v 15 Sa'ad da yayi kira gare ni zan amsa masa. Zan kasance tare da shi a cikin masifa; Zan ba shi nasara zan kuma girmama shi.
\v 16 Zan ƙosar da shi da tsawon rai in kuma nuna masa cetona.
\s5
\c 92
\cl Zabura 92
\p
\d Zabura. Waƙar ranar Asabaci.
\p
\v 1 Abu mai kyau ne a yi godiya ga Yahweh, a kuma yi waƙar yabo ga sunanka, Maɗaukaki,
\v 2 a kuma yi shelar alƙawarin amincinka da safe gaskiyarka kuma kowanne dare,
\v 3 da garaya mai tsarkiya goma da kuma kayan kaɗe-kaɗe masu daɗi.
\s5
\v 4 Domin kai, Yahweh, kasa ni murna ta wurin ayyukanka. Zanyi waƙar farinciki saboda ayyukan hannuwanka.
\v 5 Ina misalin girman ayyukanka, Yahweh! Tunane-tunanenka suna da zurfi.
\s5
\v 6 Daƙiƙin mutun bai sani ba, haka ma wawa bai fahimci wannan ba:
\v 7 Lokacin da miyagu suka firfito kamar ciyawa, ko ma a lokacin da miyagu suka taru, duk da haka an miƙa su ga hallaka ta har abada.
\s5
\v 8 Amma kai Yahweh zaka yi mulki har abada.
\v 9 Hakika ka duba maƙiyanka, Yahweh! Hakika ka duba maƙiyanka. Hakika zasu hallaka! Duk masu aikin mugunta za'a warwatsa su.
\s5
\v 10 Ka tada ƙahona kamar na bijimin sã; An keɓe ni da sabon mai.
\v 11 Idanuna sun ga faɗuwar maƙiyana; kunnuwana kuma sun ji hallakar miyagun maƙiyana.
\s5
\v 12 Masu adalci zasu yi yaɗo kamar gazarin dabino; zasu yi girma kamar itacen sida na Lebonon.
\v 13 An dasa sune a gidan Yahweh; Suna sheƙi a harabar Allahnmu.
\s5
\v 14 Suna ba da 'ya'ya har ma a kwanakin tsufansu; suna nan kore shar,
\v 15 Don ayi shela cewa Yahweh mai adalci ne. Shi ne dutsena, ba kuma rashin adalci a cikinsa.
\s5
\c 93
\cl Zabura 93
\p
\v 1 Yahweh yana mulki; Yana saye da daraja; Yahweh yasa sutura ya kuma yiwa kansa ɗammara da ƙarfi. An kafa duniya daram; kuma ba zata gusa ba.
\v 2 Kursiyinka ya kafu tun zamanin dã can; kana nan tun fil azal.
\s5
\v 3 Tekuna suka tashe, Yahweh; sun ta da muryarsu; raƙuman tekuna sunyi tumbotso sunyi ruri.
\v 4 Sun fi dukkan sauran ambaliyoyi masu ikon karya teku, Yahweh na sama maigirma ne.
\s5
\v 5 Manyan umarnanka abin dogara ne na hakika; Yahweh, tsarki ya ƙayata gidanka, har abada.
\s5
\c 94
\cl Zabura 94
\p
\v 1 Yahweh, Allah mai sakayya, Allah mai sakayya ka haskaka a bisan mu.
\v 2 Ka tashi tsaye mai shari'ar duniya ka ba masu girman kai abin da ya kamance su.
\s5
\v 3 Har yaushe miyagu, Yahweh har yaushe miyagu za suyi farinciki
\v 4 Dukkan masu aikin mugunta suna ta yin maganganunsu na wauta; Duk masu mugunta suna fahariya.
\s5
\v 5 Yahweh; sun buge mutanenka, Sun ƙuntata wa al'ummarka.
\v 6 Sun kashe gwauruwa da bãƙon dake zaune a ƙasarsu, sun kuma kashe marayu.
\v 7 Suka ce, "Allah ba zai gani ba, Yahweh na Yakubu bai kula da abin ba."
\s5
\v 8 Ku lura mutane marasa hankali! Ku wawaye, har sai yaushe zaku koyi darasi?
\v 9 Shi wanda yayi kunne ashe ba zai ji ba? Shi wanda yayi ido ba ya gani ne?
\s5
\v 10 Shi dake horon al'ummai, ashe ba zai tsautar ba? Shi ne mai ba da ilimi ga mutum.
\v 11 Yahweh ya san tunanin mutane, cewa turiri ne kawai.
\s5
\v 12 Mai albarka ne wanda ka yiwa gargaɗi, Yahweh wanda ka koyar daga cikin shari'arka
\v 13 Ka bashi hutu a lokutan damuwa har sai da aka gina rami domin miyagu.
\s5
\v 14 Domin Yahweh ba zai yashe da mutanensa ba ko kuma yayi watsi da abin gãdonsa ba.
\v 15 Domin hukunci zai sake zama da adalci; kuma dukkan masu tsarkin rai zasu bi shi.
\v 16 Wa zai tashi ya kuɓutar dani daga masu mugunta?
\s5
\v 17 In da ba domin Yahweh ya taimake ni ba da yanzu ina can kwance a lahira.
\v 18 Lokacin dana ce ƙafafuna na barci," Yahweh alƙawarin amincinka ya ɗaga ni sama.
\v 19 Lokacin da fargaba ya cika ni ta'aziyarka ta kan sani in cika da murna.
\s5
\v 20 Ko akwai hurɗa tsakaninka da mulkin hallakarwa da ya kafa rashin adalci?
\v 21 Sun shirya maƙarƙashiya tare domin su kashe mai adalci sun kuma hukuntawa marar laifi mutuwa.
\s5
\v 22 Amma Yahweh ne babbar hasumiyata, Allahna kuma shi ne dutsen fakewa ta.
\v 23 Zai saukar masu da laifofinsu zai kuma daddatsa su a cikin aikin muguntarsu. Yahweh Allahnmu zai daddatse su.
\s5
\c 95
\cl Zabura 95
\p
\v 1 Ku zo mu raira yabo ga Yahweh, Sai mu raira waƙar farinciki ga dutsen cetonmu.
\v 2 Sai mu zo gabansa da godiya, sai mu raira masa yabo da waƙoƙin zabura.
\v 3 Domin Yahweh Allah ne mai girma, sarki ne mai girma da yafi dukkan alloli.
\s5
\v 4 Zurfafan duniya dukka a hannunsa suke; Duwatsu masu tsawo kuma nasa ne.
\v 5 Teku tasa ce, shi ne yayi ta. Hannuwansa kuma suka yi busasshiyar ƙasa.
\s5
\v 6 Ku zo muyi sujada mu durƙusa ƙasa, sai mu durƙusa a gaban Yahweh mahallicinmu;
\v 7 Domin shi ne Allahnmu, mu mutanen makiyayarsa ne, tumakin hannunsa kuma. Yau ace dai za ku ji muryarsa!
\s5
\v 8 Kada ku taurare zuciyarku, kamar a Meriba, ko kuma kamar ranar Massa a cikin jeji,
\v 9 inda ubanninku suka gwada ni suka kuma jaraba ni, koda ya ke sun ga aikina.
\s5
\v 10 Shekaru arba'in ina fushi da waccan tsarar na ce, "Waɗannan mutane ne da zuciyarsu ta karkace; basu san hanyoyina ba.
\v 11 'Domin haka cikn fushina na rantse cewa ba zasu taɓa shiga wurin hutu na ba
\s5
\c 96
\cl Zabura 96
\p
\v 1 Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh; ku raira waƙa ga Yahweh, dukkan duniya.
\v 2 Ku raira waƙa ga Yahweh, ku albarkaci sunansa; kuyi shelar cetonsa a kowacce rana.
\s5
\v 3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al'ummai, ayyukansa na ban mamaki a cikin al'ummai.
\v 4 Domin Yahweh yana da girma ya kuma isa yabo sosai. A ji tsoron sa fiye da dukkan sauran alloli.
\s5
\v 5 Saboda allolin al'ummai gumaka ne, amma Yahweh ne ya hallici sammai, martaba da wadata suna gabansa.
\v 6 Jamali da ƙarfi suna cikin wurinsa mai tsarki.
\s5
\v 7 Kuyi yabo ga yahweh ku dukkan kabilu na mutane, ku yabi Yahweh sabili da ɗaukakarsa da ƙarfinsa.
\v 8 Ku ba yahweh ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo baiko a haikalinsa.
\s5
\v 9 Ku durƙusa a gaban Yahweh saye da tufafin dake girmama tsarkinsa. Yi rawar jiki a gabansa, dukkan duniya.
\v 10 Ku faɗa a cikin al'ummai cewa,"Yahweh ne ke mulki." Hakannan kuma aka kafa duniya; ba kuma zata jijjigu ba. Yana yiwa mutane shari'ar dake dai-dai.
\s5
\v 11 Sai sammai suyi murna, sai duniya kuma ta yi farinciki; sai teku yayi ruri abin da ke cikinsa kuma su cika da murna.
\v 12 Filaye suyi murna da duk abin da ke cikin su. Sa'an nan kuma dukkan bishiyoyin duniya su ɓarke da yabo
\v 13 a gaban Yahweh, domin yana tafe. Yana zuwa domin ya shar'anta duniya. Zai shar'anta duniya da adalci da mutane kuma cikin amincinsa.
\s5
\c 97
\cl Zabura 97
\p
\v 1 Yahweh na mulki sai duniya ta yi murna, sai dukkan ƙasashe masu nisa suyi murna.
\v 2 Gizagizai da duhu na kewaye da shi. Adalci da gaskiya ne harsashen kursiyinsa.
\s5
\v 3 Wuta na tafe a gabansa tana cinye magafta ko ina
\v 4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta furgita.
\v 5 Duwatsu kuma sun narke kamar tufa a gaban Yahweh Ubangijin dukkan duniya.
\s5
\v 6 Sararin sama na shaida adalcinsa, dukkan al'ummai kuma sun ga ɗaukakarsa.
\v 7 Duk waɗanda ke bauta wa abin da hannu ya sassaƙa zasu kunyata, masu taƙama da gumaka marasa amfani- ku rusuna masa da dukkan allolinku!
\v 8 Sihiyona taji sai tayi farinciki, biranen Yahuda kuma suka yi murna saboda dokokinka na adalci, Yahweh.
\s5
\v 9 Domin kai, Yahweh, kafi kowa ɗaukaka a cikin dukkan duniya. An ɗaukaka ka fiye da dukkan alloli.
\v 10 Ku dake ƙaunar Yahweh ku ƙi mugunta! Yana kare ran tsarkakansa, ya karɓo su daga hannun mugun.
\v 11 An shuka haske domin adalai farinciki kuma domin masu zukata masu aminci.
\s5
\v 12 Kuyi murna cikin Yahweh ku adalai; ku kuma yi masa godiya lokacin da kuka tuna da tsarkinsa.
\s5
\c 98
\cl Zabura 98
\p
\d Zabura.
\p
\v 1 Oh, ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh domin yayi ayyuka masu ban mamaki; hannunsa na dama da damtsensa sun ba shi nasara.
\v 2 Yahweh ya sa cetonsa ya sanu; ya nuna adalcinsa a fili ga dukkan al'ummai.
\s5
\v 3 Ya tuna da alƙawarinsa mai aminci da gaskiya ga gidan Isra'ila; dukkan iyakokin duniya zasu ga nasarar Allahnmu.
\v 4 Ku raira waƙar farinciki ga Yahweh, dukkan duniya ku ɓarke da waƙa, kuyi waƙa domin murna, kuyi waƙoƙin yabo.
\s5
\v 5 Ku raira yabo ga Yahweh da garaya, tare da garaya haɗe da waƙoƙi masu daɗi.
\v 6 Tare da kakaki da ƙarar ƙaho, ku tada muryoyi masu daɗi a gaban Sarki, Yahweh.
\s5
\v 7 Sai teku yayi ihu da dukkan abin dake cikinsa!
\v 8 Sai rafuffuka su tafa hannuwansu, sai duwatsu kuma su raira waƙar yabo.
\v 9 Yahweh yana zuwa domin ya yi wa duniya shari'a da adalci da kuma al'ummai tare da gaskiya.
\s5
\c 99
\cl Zabura 99
\p
\v 1 Yahweh na mulki; bari al'ummai suyi rawar jiki, yana zaune kan kursiyi sama da Kerubim, duniya ta girgiza,
\v 2 Yahweh yana da girma a Sihiyona yana da ɗaukaka fiye da dukkan al'ummai.
\v 3 Sai a yabi sunanka mai jamali da girma; yana da tsarki.
\s5
\v 4 Sarki yana da ƙarfi, yana kuma ƙaunar adalci. ka kafa gaskiya; ka aikata adalci akwai adalci kuma a cikin Yakubu.
\v 5 A yabi Yahweh Allahnmu a kuma yi sujada a digadigansa. Ya na da tsarki.
\s5
\v 6 Musa da Haruna na cikin firistocinsa, Sama'ila kuma na cikin waɗanda suka yi addu'a gare shi. Sun yi addu'a ga Yahweh, ya kuma amsa masu.
\v 7 Ya yi masu magana daga ginshinƙin girgije. Sun kiyaye tsattsarkan umarninsa da farillan da ya basu.
\s5
\v 8 Ka amsa masu, Yahweh Allahnmu. Kai Allah ne mai gafara a gare su, amma kuma kana horon ayyukansu na zunubi.
\v 9 Ku yabi Yahweh Allahnmu, ku kuma yi sujada akan tudunsa mai tsarki, gama Yahweh Allahnmu yana da tsarki.
\s5
\c 100
\cl Zabura 100
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Kuyi ihu da farinciki ga Yahweh ku dukkan duniya,
\v 2 Ku bautawa yahweh da farar zuciya, kuzo gabansa da waƙoƙin farinciki.
\s5
\v 3 Ku sani Yahweh Allah ne; yayi mu, mu kuma nasa ne. Tumakin makiyayarsa kuma.
\s5
\v 4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya cikin gidansa da yabo. Kuyi masa godiya ku albarkaci sunansa.
\v 5 Domin Yahweh nagari ne; alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada gaskiyarsa kuma har dukkan tsararraki ne.
\s5
\c 101
\cl Zabura 101
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Zan raira alƙawarin aminci da gaskiya; a gare ka, Yahweh, zan raira yabbai.
\s5
\v 2 Zan yi tafiya cikin aminci. Oh, yaushe zaka zo wurina ne? Ni da gidana za muyi tafiya cikin nagarta.
\v 3 Ba zan ƙyale mugunta a idanuna ba; Na ƙi mugun aiki marar cancanta; ba zai manne mani ba.
\s5
\v 4 Ɓatattun mutane zasu rabu dani; bana yin biyayya ga mugunta.
\v 5 Zan hallaka duk wanda ya yiwa maƙwabcinsa yanke a asirce. Ba zan ƙyale duk wani mai fankama da rashin hankali ba.
\v 6 Zan nemi masu aminci na ƙasar su zauna a gefena. Masu tafiya cikin gaskiya da riƙon amana ne zasu bauta mani.
\s5
\v 7 Mayaudara ba zasu kasance a gidana ba; maƙaryata bazan marabce su a idona ba.
\v 8 Duk safiya zan hallakar da miyagu dukka daga ƙasar; Zan kawar da dukkan miyagu daga birnin Yahweh.
\s5
\c 102
\cl Zabura 102
\p
\d Addu'ar wanda ya ke cikin ƙunci sa'ad da yake cikin damuwa ya kuma zuba makokinsa gaban Yahweh.
\p
\v 1 Yahweh ka ji addu'ata, Yahweh ka ji kukana dana keyi gare ka.
\v 2 Kada ka ɓoye mani fuskarka a lokacin da nake damuwa. Ka ji ni. A lokacin da nayi kira gare ka, ka amsa mani da sauri.
\s5
\v 3 Gama kwanakina sun wuce kamar hayaƙi, ƙasusuwana kuma na ƙuna kamar wuta.
\v 4 An buge zuciyata na zama kamar ciyawar data bushe. Na manta in ci wani abinci.
\s5
\v 5 Da nishe-nishena na kullum, na rame.
\v 6 Na zama kamar zalɓe a hamada; na zama kamar mujiya a kufai.
\s5
\v 7 Na kwanta ba tare da yin barci ba, kamar tsuntsun dake kaɗaici, shi kaɗai a bisa kan gida.
\v 8 Maƙiyana nayi mani ba'a; masu yi mani habaici na la'anta sunana.
\s5
\v 9 Toka ce abincina kuma gurasa abin shana ya gauraye da hawaye na.
\v 10 Saboda fargaban fushinka ka ɗaga ni sama domin ka fyaɗa ni ƙasa.
\s5
\v 11 Kwanakina sun zama kamar inuwar data gushe, na kuma yanƙwane kamar ciyawa.
\v 12 Amma kai Yahweh, kana raye har abada, kuma shahararka ta dukkan tsararraki ce.
\s5
\v 13 Zaka tashi kayi jinƙai ga Sihiyona. Yanzu ne lokacin nuna mata jinƙai; lokacinta da kasa yayi.
\v 14 Domin bayinka sun riƙe duwatsunta ƙaunatacce ka ji tausayi saboda ƙurar kufanta.
\v 15 Al'ummai zasu girmama sunanka, Yahweh, kuma dukkan sarakunan duniya zasu girmama ɗaukakarka.
\v 16 Yahweh zai sake gina Sihiyona ya kuma bayyana a cikin ɗaukakarsa.
\s5
\v 17 A wancan lokacin, zai amsa addu'ar wulaƙantattu; ba zai ƙi addu'arsu ba.
\v 18 Za a rubuta wannan saboda tsararraki masu zuwa, da mutanen da ba'a haifa ba tukuna zasu yabi Yahweh.
\s5
\v 19 Domin ya dubo ƙasa daga can sammai; Daga samaniya Yahweh ya dubi duniya,
\v 20 domin ya ji nishe-nishen 'yan sarƙa, ya kuɓutar da waɗanda aka hukuntawa mutuwa.
\s5
\v 21 Mutane zasu yi shelar sunan Yahweh a Sihiyona da kuma yabonsa a Yerusalem
\v 22 lokacin da mutane da mulkoki suka tattaru tare su bauta wa yahweh.
\s5
\v 23 Ya ɗauke ƙarfina a tsakiyar rayuwata. Ya gajarta kwanakina.
\v 24 Na ce Allahna kada ka kawar dani a tsakiyar rayuwa; kana nan a dukkan tsararraki.
\s5
\v 25 A can lokacin dã ka kafa duniya a wurinta; sammai kuma aikin hannuwanka ne.
\v 26 Zasu lalace amma kai zaka dawwama; duk zasu tsufa kamar sutura; kamar tufafi, zaka cire su, zasu kuma ɓace.
\v 27 Amma kai kana nan yadda kake, shekarunka kuma basu da iyaka.
\s5
\v 28 'Ya'yan bayinka zasu rayu, zuriyarsu kuma zasu rayu a gabanka."
\s5
\c 103
\cl Zabura 103
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ina godiya ga Yahweh da dukkan raina, da dukkan abin da ke cikina, Ina yabon sunansa mai tsarki.
\v 2 Ina godiya ga Yahweh da dukkan raina, na kuma tuna da dukkan ayyukansa nagari.
\s5
\v 3 Ya gafarta dukkan zunubanka, ya kuma warkar da dukkan cututtukanka.
\v 4 Ya ceci ranka daga hallaka yayi maka rawani da alƙawarin aminci da ayyukan jinƙai.
\v 5 Ya ƙosar da ranka da abubuwa masu kyau domin haka ƙuruciyarka ta sabunta kamar gaggafa.
\s5
\v 6 Yahweh yakan yi abin dake dai-dai da adalci ga duk waɗanda aka tsanantawa.
\v 7 ya sanar da hanyoyinsa ga Musa, ayyukansa kuma ga zuriyar Isra'ila.
\v 8 Yahweh mai jinƙai ne da alheri; yana da haƙuri; yana da matuƙar amincin alƙawari.
\s5
\v 9 Ba kullum ya kanyi horo ba; ba kullum kuma ya kanyi fushi ba.
\v 10 Baya yi mana bisa ga gwargwadon zunubanmu ko ya saka mana kan hukuncin zunubanmu ba.
\s5
\v 11 Domin kamar yadda sammai ke nesa da duniya, to haka girman alƙawarinsa ya ke ga masu girmama shi.
\v 12 Kamar yadda gabas tayi nisa da yamma hakannan ya kawar da laifofin zunubanmu daga gare mu.
\v 13 Kamar yadda mahaifi ke tausayin 'ya'yansa, haka Yahweh ke tausayin masu girmama shi.
\s5
\v 14 Domin yasan yadda aka yi mu; ya sani cewa mu ƙura ne.
\v 15 mutum kwanakinsa kamar ciyawa ce yakan yi yabanya kamar furen saura.
\v 16 Iska ta kan hura ta kansa, sai kuma ya ɓace kuma ba wanda zai san yadda yayi girma.
\s5
\v 17 Amma alƙawarin Yahweh mai aminci har abada abadin ne ga masu girmama shi. Adalcinsa ya kai har ga zuriyar su.
\v 18 Sun kiyaye alƙawarinsa sun kuma tuna su yi biyayya da dokokinsa.
\v 19 Yahweh ya kafa kursiyinsa a sammai, masarautarsa kuma na mulkin kowa.
\s5
\v 20 A yi yabo ga Yahweh, ku mala'ikunsa, ku masu iko dukka dake yin biyayya da maganarsa.
\v 21 Ku yabi Yahweh, dukkan rundunoninsa, ku bayinsa ne dake yin nufinsa.
\v 22 A yabi Yahweh, dukkan halittunsa, a dukkan wuraren da ya ke mulki. Zan yabi Yahweh da dukkan raina.
\s5
\c 104
\cl Zabura 104
\p
\v 1 Na bada yabo ga Yahweh da dukkan raina, Yahweh Allahna, kai mai girma ne da ƙawa; Kayi sutura da martaba da daraja.
\v 2 Ka rufe kanka da haske kamar da sutura; ka shimfiɗa sammai kamar yadda ake simfiɗa labulen rumfa.
\v 3 Ka shimfiɗa katakan fadodinka a kan gajimarai; ka mai da gajimarai karusanka; kana tafiya akan fika-fikan iska.
\s5
\v 4 Ya mai da iskoki manzanninsa, harsunan wuta kuma bayinsa.
\v 5 Ya kafa tushen duniya ba kuma zata jijjigu ba.
\s5
\v 6 Ka rufe duniya da ruwa kamar sutura; ruwa ya rufe duwatsu.
\v 7 Tsautawarka nasa ruwaye su janye; da jin ƙarar tsawarka sai suka gudu.
\s5
\v 8 Duwatsu sun tashi, kwarurruka kuma suka bazu zuwa wuraren da ka shirya masu.
\v 9 Ka yi masu iyakar da ba zasu tsallake ba; ba zasu ƙara rufe duniya ba.
\s5
\v 10 Yasa maɓuɓɓugan ruwa su gudana zuwa kwarurruka; maɓulɓulan sun kwarara tsakanin duwatsu.
\v 11 Suna bayar da ruwa ga dukkan dabbobin saura; jakunan jeji a wurin ne suke kashe ƙishinsu.
\v 12 A bakin kogunan ruwa tsuntsaye suka yi sheƙunansu; suna raira waƙa a cikin rassa.
\s5
\v 13 Ya shayar da duwatsu daga ruwansa ya kafa kursiyinsa a sammai. Duniya ta cika da 'ya'yan aikinsa.
\v 14 Yasa ciyawa ta fito domin dabbobi da kuma tsire-tsire domin mutum ya nome ya sami abinci daga ƙasa.
\v 15 Yayi inabi domin mutum yayi murna, mai kuma domin fuskarsa tayi haske, abinci kuma domin rayuwarsa.
\s5
\v 16 Itatuwan Yahweh suna samun ruwa; Sidar Lebanon da ya dasa
\v 17 Acan tsuntsaye ke yin sheƙunansu. Shamuwa ta mai da itacen sifurus gidanta.
\v 18 Awakin jeji kuma suna zama a kan duwatsu; rimaye kuma sun mayar da ƙonƙolin duwatsu mafakarsu.
\s5
\v 19 Yasa wata ya nuna lokuta; rana kuma ta san lokacin faɗuwarta.
\v 20 Ka yi duhun dare lokacin da duk daji ke fitowa waje.
\s5
\v 21 Sagarun zakuna kan yi gurnani domin neman abincinsu daga wurin Allah.
\v 22 Lokacin da rana ta fito sai su koma suyi barci a kogunansu.
\s5
\v 23 Hakanan mutane kan je waje wurin aikinsu suyi ta aiki har yamma.
\v 24 Yahweh ayyukanka iri-iri guda nawa ne! Da hikima kayi su dukka; duniya ta cika maƙil da ayyukanka.
\s5
\v 25 A can kuma sai teku, mai zurfi da faɗi cike da manya da ƙananan hallitu marasa ƙidayuwa,
\v 26 Jiragen ruwa sukan je can, Lebiyatan kuma a can ya ke, wanda ka yi domin yayi wasa a cikin teku.
\s5
\v 27 Duk waɗannan gare ka suke zuba ido domin samun abinci a kan lokaci
\v 28 Lokacin da ka basu, su kan tara; lokacin daka buɗe hannunka, sukan ƙoshi.
\s5
\v 29 Lokacin da ka ɓoye fuskarka, sukan shiga damuwa; in ka ɗauke numfashinsu sukan mutu su koma ƙura.
\v 30 Lokacin da ka aiko Ruhunka, aka hallice su, ka kuma sabunta gefen ƙasarsu.
\s5
\v 31 Dãma ɗaukakar Yahweh ta dawwama har abada; dãma Yahweh ya ji daɗin hallitarsa.
\v 32 Ya dubi duniya, sai ta girgiza; yakan taɓa duwatsu suyi hayaƙi.
\s5
\v 33 Zan raira yabo ga Yahweh a dukkan kwanakin raina; zan raira waƙar yabo ga Allah muddin ina raye.
\v 34 Dãma tunane-tunanena su zama da zaƙi a gare shi; Zan yi murna cikin Yahweh.
\s5
\v 35 Dãma masu zunubi su hallaka daga duniya, dãma miyagu su ɓace daga duniya. Ina yabon Yahweh dukkan kwanakin raina. A yabi Yahweh.
\s5
\c 105
\cl Zabura 105
\p
\v 1 Ku bada godiya ga Yahweh, ku kira bisa sunansa; ku sanar da ayyukansa cikin al'ummai.
\v 2 Ku raira gare shi, ku raira yabbai gare shi; kuyi maganar dukkan ayyukansa na ban mamaki.
\v 3 Kuyi taƙama cikin sunan sa mai tsarki; bari zuciyar waɗanda ke biɗar Yahweh ta yi farinciki.
\s5
\v 4 Ku biɗi Yahweh da ƙarfinsa kuma; ku biɗi bayyanuwarsa ba fasawa.
\v 5 Ku tuna da abubuwan ban mamaki da yayi, al'ajibansa da kuma dokoki daga bakinsa,
\v 6 ku zuriyar Ibrahim bawansa, ku mutanen Yakubu, zaɓaɓɓunsa.
\s5
\v 7 Shi ne Yahweh, Allahnmu. Dokokin sa suna bisan dukkan duniya.
\v 8 Cikin ransa yana ajiye alƙawarinsa har abada, maganarsa da ya umarta domin dubun tsararraki.
\s5
\v 9 Yana tunawa a cikin ransa alƙawarin da yayi da Ibrahim da kuma rantsuwarsa ga Ishaku.
\v 10 Wannan ne abin da ya tabbatar wa Yakubu a matsayin farilla da Isra'ila a matsayin madawwamin alƙawari.
\v 11 Ya ce, "Zan baku ƙasar kan'ana a matsayin kasonku na gãdonku."
\s5
\v 12 Ya faɗi wannan sa'ad da suke kaɗan a lissafi, 'yan kima sosai, kuma suna baƙi a ƙasar.
\v 13 Suka tafi daga al'umma zuwa al'umma kuma daga masarauta zuwa wata.
\s5
\v 14 Bai bar wani ya tsananta masu ba; ya tsautawa sarakuna sabili da su.
\v 15 Ya ce, "Kada ku taɓa shafaffuna, kada kuma ku yi lahani ga annabawana."
\s5
\v 16 Yayi kira domin yunwa bisa ƙasar; ya yanke dukkan biyan buƙatar gurasa.
\v 17 Ya aika da mutum gaba da su; Yosef a ka sayar da shi a matsayin bawa.
\s5
\v 18 Aka ɗaure ƙafafunsa da sarƙoƙi; a bisa wuyansa aka sa maɗaurin ƙarfe,
\v 19 har sai lokacin da maganganun sa suka zama gaskiya, kuma maganar Yahweh ta gwada shi.
\s5
\v 20 Sarki ya aika da bayi su sake shi; shugaban mutanen ya 'yantar da shi.
\v 21 Ya sanya shi lura da gidansa a matsayin shugaban dukkan mallakarsa
\v 22 ya bayar da umarni ga shugabanninsa yadda ya so ya kuma koyar da dattawansa hikima.
\v 23 Daga nan Isra'ila ya zo cikin Masar, Yakubu kuma ya zauna na wani lokaci a cikin ƙasar Ham.
\s5
\v 24 Yahweh yasa mutanen sa suka yi 'ya'ya, ya kuma sa suka yi ƙarfi fiye da maƙiyansu.
\v 25 Ya kuma sa maƙiyansa suka ƙi Jinin mutanensa, suka muzguna wa bayinsa.
\v 26 Ya aika da Musa, bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.
\v 27 Suka aikata alamunsa a tsakiyar masarawa, al'ajibansa a ƙasar Ham.
\s5
\v 28 Ya aika da duhu ya maida ƙasar duhu, amma mutanen ta basu yi biyayya da umarninsa ba.
\v 29 Ya maida ruwansu ya zama jini ya kuma kashe kifinsu.
\v 30 Ƙasar ta cika da gungun kwaɗi, har ma cikin ɗakunan shugabanninsu.
\s5
\v 31 Yayi magana, kuma gungun ƙudaje da ƙwari suka zo cikin dukkan ƙasar.
\v 32 Ya maida ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da wuta mai ci balbal bisa ƙasarsu.
\v 33 Ya lalata kuringun inabinsu da itatuwan ɓaurensu; ya karya itatuwan ƙasarsu.
\s5
\v 34 Yayi magana, fãri suka zo, fãri masu yawan gaske.
\v 35 Fãrin suka cinye dukkan ganyayyaki a ƙasar; suka cinye dukkan amfanin gona.
\v 36 Ya kashe kowanne ɗan fãri a cikin ƙasar, 'ya'yan fãrin dukkan ƙarfinsu.
\s5
\v 37 Ya fito da Isra'ilawa tare da azurfa da zinariya; babu wani cikin kabilunsa da yayi tuntuɓe a hanya.
\v 38 Masar ta yi farinciki da suka tafi, domin masarawa sunji tsoronsu.
\v 39 Ya shimfiɗa girgije a matsayin abin rufa ya kuma yi wuta ta haskaka dare.
\s5
\v 40 Isra'ilawa suka yi roƙon abinci, ya kuma kawo makwarwa ya kuma ƙosar da su da gurasa daga sama.
\v 41 Ya fasa dutse ruwa kuma ya ɓulɓulo daga gare shi; ya malala cikin jeji kamar kogi.
\v 42 Domin ya tuna a ransa da alƙawarin sa mai tsarki wanda yayi wa Ibrahim bawansa.
\s5
\v 43 Ya bida mutanen sa suka fita da farinciki, zaɓaɓɓunsa da sowace-sowace fiye da gaban masu nasara.
\v 44 Ya basu ƙasashen al'ummai; suka ɗauki mallakar dukiyar mutanen
\v 45 domin su kiyaye farillansa su kuma yi biyayya da shari'unsa. A yabi Yahweh.
\s5
\c 106
\cl Zabura 106
\p
\v 1 A yabi Yahweh. A bada girma ga Yahweh, domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\v 2 Wa zai lissafa manyan ayyukan Yahweh ko yayi cikakken shelar dukkan ayyukansa da suka cancanci yabo?
\s5
\v 3 Masu albarka ne waɗanda suke yin abin dake dai-dai, waɗanda kuma a koyaushe ayyukansu baratattu ne.
\v 4 Ka tuna dani a rai, Yahweh, sa'ad da ka nuna tagomashi ga mutanenka; ka taimake ni sa'ad da ka cece su.
\v 5 Daga nan zan ga wadatar zaɓaɓɓun ka, in yi farinciki cikin murnar ƙasarka, da ɗaukaka tare da gãdonka.
\s5
\v 6 Mun yi zunubi kamar Kakanninmu; mun yi laifi, mun kuma aikata mugunta.
\v 7 Ubanninmu basu yaba wa ayyukanka masu ban mamaki ba a Masar; suka yi banza da ayyukanka masu yawa na alƙawarin aminci; suka yi tawaye a bakin teku, Tekun Iwa.
\s5
\v 8 Duk da haka, ya cece su domin sunansa saboda ya bayyana ikonsa.
\v 9 Ya tsautawa Tekun Iwa, ya kuwa bushe. Daga nan ya bida su ta cikin zurfafan, kamar ta cikin jeji.
\s5
\v 10 Ya cece su daga hannun waɗanda suka ƙi su, ya kuma ƙwato su daga hannun maƙiyansu.
\v 11 Amma ruwayen suka rufe magaftansu; babu wanin su da ya tsira.
\v 12 Daga nan suka gaskata maganganunsa, kuma suka raira yabonsa.
\s5
\v 13 Amma nan da nan suka manta da abin da yayi; ba su jira umarninsa ba.
\v 14 Suka yi kwaɗayi marar ƙosarwa a jeji, kuma suka ƙalubalanci Allah a cikin hamada.
\v 15 Ya basu abin da suka roƙa, amma ya aika da cuta wadda ta cinye jikkunansu.
\s5
\v 16 A sansanin suka zama masu kishin Musa da Haruna, firist mai tsarki na Yahweh.
\v 17 Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta kuma rufe mabiyan Abiram.
\v 18 Wuta ta ɓarke a tsakaninsu; wutar ta cinye mãsu mugunta.
\s5
\v 19 Suka yi maraƙi a Horeb suka kuma yi sujada ga sarrafaffar siffar ƙarfe.
\v 20 Suka musanya ɗaukakar Allah domin siffar maraƙi mai cin ciyawa.
\v 21 Suka manta da Allah Maicetonsu, wanda yayi manyan ayyuka a Masar.
\s5
\v 22 Yayi abubuwan ban mamaki a ƙasar Ham ya kuma yi ayyuka masu iko a Tekun Iwa.
\v 23 Da ya zartar da dokar hallakar dasu, inda ba domin Musa, zaɓaɓɓensa, ya shiga tsakaninsu da shi ba ya juya fushinsa daga hallakar dasu.
\s5
\v 24 Daga nan suka raina ƙasa mai bayar da amfani; ba su gaskata da alƙawarinsa ba,
\v 25 amma suka yi gunaguni a rumfunansu, ba su kuma yi biyayya da Yahweh ba.
\s5
\v 26 Saboda haka ya ɗaga hannunsa kuma ya rantse masu cewa zai barsu su mutu a hamada,
\v 27 ya warwatsa zuriyarsu cikin al'ummai, ya kuma warwatsa su cikin bãƙin ƙasashe.
\s5
\v 28 Suka yi sujada ga Ba'al na fowa suka kuma ci hadayun da a ke miƙawa ga matattu.
\v 29 Suka cakune shi ya yi fushi da ayyukansu, annoba kuwa ta faso a tsakaninsu.
\s5
\v 30 Daga nan Fenihas ya tashi ya kai ɗauki, annobar kuwa ta tsagaita.
\v 31 Aka lissafa masa shi a matsayin aikin adalci ga dukkan tsara har abada.
\s5
\v 32 Suka kuma ba Yahweh haushi a ruwayen Meriba, Musa kuma ya sha wahala saboda su.
\v 33 Suka sa Musa ya ji haushi, ya kuma yi magana da fushi.
\v 34 Basu hallakar da al'ummai ba kamar yadda Yahweh ya dokace su,
\v 35 amma suka gauraye da al'ummai suka kuma koyi hanyoyinsu
\v 36 kuma suka yi sujada ga gumakansu, waɗanda suka zamar masu tarko.
\s5
\v 37 Suka yi hadayar 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata ga aljanu.
\v 38 Suka zubar da jini marar laifi, jinin 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata, waɗanda suka yi hadaya dasu ga gumakan Kan'ana, suka ƙazantar da ƙasar da jini.
\v 39 Suka ɓãci da ayyukansu; cikin ayyukansu suka zama kamar karuwai.
\s5
\v 40 Saboda haka Yahweh ya yi fushi da mutanensa, ya kuma rena nasa mutanen.
\v 41 Ya bayar dasu cikin hannun al'ummai, waɗanda kuma suka ƙi su suka yi mulki a kansu.
\s5
\v 42 Maƙiyan su suka tsananta masu, aka kuma kawo su ƙarƙashin hukuncinsu.
\v 43 Lokutta da yawa yazo ya taimake su, amma suka ci gaba da yin tawaye aka kuma kawo su ƙasa ta wurin zunubinsu.
\s5
\v 44 Duk da haka, ya lura da ƙuncin su sa'ad da ya ji kukansu domin taimako.
\v 45 Ya tuna a ransa da alƙawarin sa tare dasu ya kuma yi jinkiri saboda matuƙar ƙaunarsa.
\v 46 Ya sa dukkan waɗanda suka yi nasara dasu suka ji tausayin su.
\s5
\v 47 Ka cece mu, Yahweh, Allahnmu. Ka tattaro mu daga cikin al'ummai domin mu ba da godiya ga sunan ka mai tsarki mu kuma yi ɗaukaka cikin yabban ka.
\v 48 Bari Yahweh, Allah na Isra'ila, ya sami yabo daga matuƙa zuwa matuƙa. Dukkan mutane sukace, "Amin." A yabi Yahweh. Littafi na Biyar
\s5
\c 107
\cl Zabura 107
\p
\v 1 Ku ba da godiya ga Yahweh, domin shi nagari ne, kuma alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\v 2 Bari fansassun Yahweh suyi magana, waɗanda ya cafko daga hannun maƙiyi.
\v 3 Ya tattaro su daga bãƙin ƙasashe, daga gabas daga kuma yamma, daga arewa daga kuma kudu.
\s5
\v 4 Suka yi yawo a jeji bisa hanyar hamada ba su kuma sami birnin da zasu zauna ba.
\v 5 Saboda sunji yunwa da ƙishi, suka some cikin gajiya.
\v 6 Daga nan suka yi kira ga Yahweh cikin damuwarsu, ya kuma ceto su daga ƙuncinsu.
\v 7 Ya bida su ta miƙaƙƙen tafarki saboda su tafi cikin birnin da zasu zauna.
\s5
\v 8 Da ma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da yayi domin 'yan adam!
\v 9 Domin ya biya buƙatun begen masu jin ƙishi, da marmarin masu jin yunwa ya cika da abubuwa masu kyau.
\v 10 Waɗansu suka zauna cikin duhu da ɓoyewa, 'yan kurkuku cikin ƙunci da sarƙoƙi.
\s5
\v 11 Wannan kuwa saboda sun yi tawaye gãba da maganar Yahweh suka kuma yi watsi da umarnin Maɗaukaki.
\v 12 Ya ƙasƙantar da zukatansu ta wurin shan wuya; suka yi tuntuɓe kuma babu wanda zai taimake su ya ɗaga su.
\v 13 Daga nan suka yi kira ga Yahweh a cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncinsu.
\s5
\v 14 Ya fito dasu daga cikin duhu da ɓoyewa ya kuma karya karkiyarsu.
\v 15 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da ya yi domin 'yan adam!
\v 16 Domin ya karya ƙofofin tagulla ya kuma datse ginshiƙan ƙarfe.
\s5
\v 17 Sun yi wawanci a cikin hanyoyinsu na tawaye suka kuma ƙuntata saboda zunubansu.
\v 18 Marmarinsu na cin abinci ya ɓace, suka kuma zo kusa da ƙofofin mutuwa.
\v 19 Daga nan suka yi kira ga Yahweh a cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncin su.
\s5
\v 20 Ya aika da maganarsa ya warkar da su, ya kuma ceto su daga hallakarsu.
\v 21 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da yayi domin 'yan adam!
\v 22 Bari su miƙa hadayun godiya su kuma yi shelar ayyukansa cikin waƙa.
\s5
\v 23 Waɗansu suka yi tafiya bisa teku cikin jiragen ruwa suka kuma yi sana'o'i bisa tekuna.
\v 24 Waɗannan sun ga ayyukan Yahweh da al'ajibansa bisa tekuna.
\s5
\v 25 Domin ya bada umarni ya kuma zuga iskar guguwa dake motsa tekuna.
\v 26 Suna kaiwa ga sararin sama; su tafi ƙasa cikin zurfafa. Rayuwar suna narkewa cikin ƙunci.
\v 27 Suna gushewa suyi tangaɗi kamar bugaggu waɗanda kuma suka kawo ga ƙarshen iyawarsu.
\s5
\v 28 Daga nan suka yi kira ga Yahweh cikin damuwarsu, ya kuma fito dasu daga cikin ƙuncinsu.
\v 29 Ya tausar da guguwar, kuma raƙuman suka yi tsit.
\v 30 Daga nan suka yi farinciki saboda tekun ya tausu, ya kuma kawo su in da suke so su sauka.
\s5
\v 31 Dãma mutane su yabi Yahweh domin alƙawarin amincinsa domin kuma abubuwan ban mamaki da ya yi domin 'yan adam!
\v 32 Bari su ɗaukaka shi a cikin taron mutane su kuma yabe shi a majalisar dattawa.
\s5
\v 33 Ya maida koguna suka koma jeji, maɓulɓulan ruwa suka koma busasshiyar ƙasa,
\v 34 da ƙasa mai bada 'ya'ya zuwa bakararen wuri saboda muguntar mutanenta.
\v 35 Ya maida jeji kuma ya zama tafkin ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulan ruwa.
\s5
\v 36 Ya wadatar da masu jin yunwa a wurin, suka kuma gina birni su zauna a ciki.
\v 37 Suka gina birni su dasa gonaki a ciki, su dasa garkunan inabi, su kuma kawo yalwar kaka.
\v 38 Ya albarkace su suka zama fiye da lissafi sosai. Bai bar garken dabbobinsu ba su ragu a lissafi.
\s5
\v 39 Suka ragu aka kuma ƙasƙantar dasu ta wurin ƙunci mai zafi da wahala.
\v 40 Ya zubo raini bisa shugabanninsu yasa kuma suka yi yawo cikin jeji, in da babu hanyoyi.
\s5
\v 41 Amma ya kiyaye mabuƙata daga ƙunci ya kuma lura da iyalinsa kamar garken tumaki.
\v 42 Masu adalci zasu dubi wannan suyi farinciki, dukkan mugunta kuma ta rufe bakinta.
\v 43 Duk mai hikima ya yi la'akari da waɗannan abubuwa ya kuma yi tunani bisa ayyukan Yahweh na alƙawarin aminci.
\s5
\c 108
\cl Zabura 108
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Zuciyata ta kafu, Allah; zan raira, I, zan raira yabbai kuma tare da zuciyata ta girmamawa.
\v 2 Ku tashi, sarewa da garaya; zan tashi da asuba.
\s5
\v 3 Zan bada godiya gare ka, Yahweh, a tsakanin mutane; zan raira yabbai gareka a tsakanin al'ummai.
\v 4 Domin alƙawarin amincinka mai girma ne sama da sammai; amincin ka kuma ya kai sararin sama.
\s5
\v 5 Ka ɗaukaka, Allah, sama da sammai, bari kuma darajarka ta ɗaukaka sama da dukkan duniya.
\v 6 Domin waɗanda kake ƙauna su sami ceto, ka ceto mu da hannunka na dama ka kuma amsa mani.
\s5
\v 7 Allah yayi magana cikin tsarkinsa; "Zan yi farinciki; zan raba Shekem in kuma yi kason kwarin Sukkot.
\v 8 Giliyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Ifraim ma ƙwalƙwali nane; Yahuda kuma sandar sarautana ne.
\s5
\v 9 Mowab kwanon wankina ne; bisa Idom zan jefa takalmina; Zanyi sowa cikin nasara saboda Filitiya.
\v 10 Wa zai kawo ni ckin birni mai karfi? Wa zai bida ni zuwa Idom?"
\s5
\v 11 Allah, baka watsar damu ba? Baka tafi cikin yaƙi tare da mayaƙanmu ba.
\v 12 Ka ba mu taimako gãba da maƙiyinmu, domin taimakon mutum wofi ne.
\v 13 Zamu yi nasara da taimakon Allah; zaya tattake maƙiyanmu.
\s5
\c 109
\cl Zabura 109
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Allah wanda nake yabo, kada ka yi shiru,
\v 2 Domin miyagu da macuta sun kawo mani hari; sun faɗi ƙarairayi game dani.
\v 3 Sun kewaye ni kuma sun faɗi abubuwan ƙiyayya, kuma sun kawo mani hari babu dalili.
\s5
\v 4 A ramuwar ƙaunata sun kawo mani sãra, amma nayi addu'a domin su.
\v 5 Sun biya nagarta ta da mugunta, kuma sun ƙi ƙauna ta.
\s5
\v 6 Ka naɗa mugun mutum bisa irin waɗannan maƙiya kamar waɗannan mutanen; ka naɗa mai sãra ya tsaya a hannun damansa.
\v 7 Idan aka shar'anta shi, bari a same shi mai laifi; bari addu'arsa a ɗauke ta zunubi.
\s5
\v 8 Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani ya ɗauki gurbinsa.
\v 9 Bari 'ya'yansa su zama marasa mahaifi, matar sa kuma gwauruwa.
\v 10 Bari 'ya'yan sa su tafi gantali da bara. Suna roƙon abin da aka rage yayin da suka bar rusassun gidajensu.
\s5
\v 11 Bari mai bin bashi ya ɗauke dukkan abin da ya mallaka; bari bãƙi su washe abin da ya ke samu.
\v 12 Kada wani ya miƙa wani halin kirki gare shi; kada wani ya ji tausayin 'ya'yansa marasa mahaifi.
\v 13 Bari a datse 'ya'yan sa; bari a share sunansu daga tsara ta gaba.
\s5
\v 14 Bari a faɗi zunuban kakanninsa ga Yahweh; bari kuma kada a manta da zunubin mahaifiyarsa.
\v 15 Bari laifinsu a koyaushe ya kasance a gaban Yahweh; Bari Yahweh ya datse tunawa dasu daga duniya.
\v 16 Bari Yahweh yayi haka saboda mutumin nan bai kula daya nuna wani alƙawarin aminci ba, amma a maimako ya firgitar da masu shan tsanani, masu buƙata, da masu ɓacin zuciya har ga mutuwa.
\s5
\v 17 Yana ƙaunar la'ana; bari ta dawo kansa. Yaƙi albarka; bari kada albarka ta zo gareshi.
\v 18 Ya lulluɓe kansa da la'ana kamar tufafi, kuma la'anarsa ta shiga cikin sa kamar ruwa, kamar mai cikin ƙasusuwansa.
\s5
\v 19 Bari la'anoninsa su zame masa kamar suturar da ya ke sanyawa ya rufe kansa, kamar ɗamarar da ya ke sanyawa koyaushe.
\v 20 Bari wannan ya zama rabon masu zargina daga Yahweh, ga waɗanda ke faɗin miyagun abubuwa game dani.
\s5
\v 21 Yahweh Ubangijina, ka yi mani alheri sabili da sunanka. Saboda alƙawarin amincinka nagari ne, ka cece ni.
\v 22 Domin ni mai shan tsanani ne mai buƙata kuma, zuciya ta kuma taji ciwo a cikina.
\v 23 Ina ƙarewa kamar inuwar maraice; Ina kakkaɓewa kamar fãra.
\s5
\v 24 Gwiwowina sun rasa ƙarfi daga azumi; Ina komawa fata da ƙasusuwa.
\v 25 Na zama wulaƙantacce wurin masu zargina; idan suka ganni, suna girgiza kawunansu.
\s5
\v 26 Ka taimake ni, Yahweh Allahna; ka cece ni ta wurin alƙawarin amincin ka.
\v 27 Bari su san cewa wannan yinka ne, cewa kai, Yahweh, ka yi wannan.
\s5
\v 28 Koda ya ke sun la'ance ni, ina roƙon ka ka albarkace ni; Idan suka kawo hari, bari su sha kunya, amma bari bawanka yayi farinciki.
\v 29 Bari magafta na suyi sutura da kunya; bari su sanya kunyar su kamar alkyabba.
\s5
\v 30 Da bakina na bada babbar godiya ga Yahweh; Zan yabe shi a tsakiyar taro.
\v 31 Domin zai tsaya a hannun daman wanda keda buƙata; ya cece shi daga waɗanda ke shar'ianta shi.
\s5
\c 110
\cl Zabura 110
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh ya cewa ubangijina, "Ka zauna hannun damana har sai na maida maƙiyanka abin takawar ka."
\s5
\v 2 Yahweh zai riƙe sandar mulkin ƙarfin ka daga Sihiyona; kayi mulki a tsakiyar maƙiyanka.
\v 3 Mutanenka zasu bi ka cikin tsarkakan tufafi da nufin kansu ranar ikonka; daga mahaifar asubahi ƙuruciyar ka zata zame maka a kamar raɓa.
\s5
\v 4 Yahweh yayi rantsuwa, kuma ba zai canza ba: "Kai firist ne na har abada, bisa ga ɗabi'ar Melkizadek."
\s5
\v 5 Ubangiji yana hannun damanka. Zai kashe sarakuna a ranar fushinsa.
\v 6 Zai shar'anta al'ummai; zai cika filin yaƙi da gawarwaki; zai kashe shugabanni a ƙasashe masu yawa.
\s5
\v 7 Zai sha daga rafin bakin hanya, daga nan kuma zai ɗaga kansa sama bayan nasara.
\s5
\c 111
\cl Zabura 111
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Zan bada godiya ga Yahweh da dukkan zuciyata a cikin taron masu adalci, a cikin tattaruwarsu.
\v 2 Ayyukan Yahweh masu girma ne, ana jira da ɗoki ga dukkan waɗanda ke marmarin su.
\v 3 Aikin sa mai daraja ne cike da ɗaukaka, adalcinsa kuma ya dawwama har abada.
\s5
\v 4 Yana yin abubuwan ban mamaki daza a tuna; Yahweh cike da alheri ya ke cike kuma da jinƙai.
\v 5 Yana bayar da abinci ga amintattun mabiyansa. Za ya tuna a ransa koyaushe da alƙawarinsa.
\v 6 Ya nuna ayyukansa a cike da iko ga mutanensa inda ya basu gãdon al'ummai.
\s5
\v 7 Ayyukan hannuwansa sun isa amincewa da hukunci; dukkan umarninsa abin dogara ne.
\v 8 An kafa su har abada, domin a kiyaye su da aminci a dai-dai kuma.
\v 9 Ya bada nasara ga mutanensa; ya naɗa alƙawarinsa har abada; tsarki da ban mamaki ne sunansa.
\s5
\v 10 Girmama Yahweh shi ne farkon hikima; waɗanda suke aikata umarninsa suna da fahimta mai kyau. Yabonsa ya dawwama har abada.
\s5
\c 112
\cl Zabura 112
\p
\v 1 A yabi Yahweh. Mai albarka ne mutumin dake biyayya da Yahweh, wanda ya ke jin daɗin dokokinsa sosai.
\v 2 Zuriyarsa zasu zama cike da iko a duniya; zuriyar mutum mai tsoron Allah masu albarka ne.
\s5
\v 3 Dukiya da arziki suna cikin gidansa; adalcinsa zai dawwama har abada.
\v 4 Haske yana haskaka wa cikin duhu domin taliki mai tsoron Allah; yana cike da alheri, cike da jinƙai, da hukunci.
\v 5 Yana tafiya lafiya ga mutumin dake aikata alheri da bayar da rancen kuɗi, wanda ke tafiyar da al'amuransa tare da gaskiya.
\s5
\v 6 Domin ba zai taɓa gusawa ba; mai adalci za a tuna da shi har abada.
\v 7 Baya jin tsoron mugun labari; yana da ƙarfin hali, dogara ga Yahweh.
\s5
\v 8 Zuciyar sa lif, ba tare da tsoro ba, har sai ya duba cikin nasara bisa magabtansa.
\v 9 A yalwace ya ke bayar wa ga talakawa; adalcinsa ya dawwama har abada; za a ɗaukaka shi da girmamawa.
\s5
\v 10 Wanda ke mugu zai duba wannan kuma ya ji haushi; zai ciza haƙoransa ya kuma narke; marmarin miyagun mutane zaya lalace.
\s5
\c 113
\cl Zabura 113
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Ku yabe shi ku bayin Yahweh; ku yabi sunan Yahweh.
\v 2 Albarka ta tabbata ga sunan Yahweh, duk da yanzu da har abada abadin.
\s5
\v 3 Daga tasowar rana har zuwa faɗuwarta, sunan Yahweh ya sami yabo.
\v 4 Yahweh ya ɗaukaka sama da dukkan al'ummai, darajarsa kuma ta wuce gaban sararin sammai.
\s5
\v 5 Wane ne kamar Yahweh Allahnmu, wanda keda mazauninsa a sama,
\v 6 wanda ke duba sararin sama da duniya?
\s5
\v 7 Yana taso da talaka daga datti kuma ya ɗaga mabuƙaci daga tarin toka,
\v 8 domin ya zaunar da shi tare da shugabanni, tare da shugabannin mutanensa.
\s5
\v 9 Yana bayar da gida ga bakarariyar macen gidan, yana mayar da ita uwar 'ya'ya cike da farinciki. A yabi Yahweh!
\s5
\c 114
\cl Zabura 114
\p
\v 1 Da Isra'ila suka bar Masar, gidan Yakubu daga waɗannan bãƙin mutane,
\v 2 Yahuda ya zama wurinsa mai tsarki, Isar'ila masarautarsa.
\s5
\v 3 Teku ya duba kuma ya gudu; Yodan ya juya baya.
\v 4 Duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai suka yi tsalle kamar 'yan raguna.
\s5
\v 5 Me yasa ka gudu, teku? Yodan, me yasa ka juya baya?
\v 6 Duwatsu, me yasa kuka yi tsalle kamar raguna? Ku ƙananan tuddai, me yasa kuka yi tsalle kamar 'yan raguna?
\v 7 Yi rawar jiki, duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allahn Yakubu.
\s5
\v 8 Ya juya dutse ya zama tafkin ruwa, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓular ruwa.
\s5
\c 115
\cl Zabura 115
\p
\v 1 Ba gare mu ba, Yahweh, ba gare mu ba, amma ga sunanka ka kawo daraja, domin alƙawarin amincinka domin kuma isar amincewarka.
\v 2 Me yasa al'ummai zasu ce, "Ina Allahnsu?"
\s5
\v 3 Allahnmu yana sama; yana yin abin daya so.
\v 4 Gumakan al'ummai azurfa ne da zinariya, aikin hannuwan mutane.
\s5
\v 5 Waɗannan gumakai suna da baki, amma ba su magana; suna da idanu, amma basu gani;
\v 6 suna da kunnuwa, amma basu ji; suna da hanci, amma basu sunsuna wa.
\s5
\v 7 Waɗannan gumakai suna da hannuwa, amma basu taɓa wa; suna da tafin ƙafafu, amma basu tafiya; ko kuwa suyi magana daga bakunansu.
\v 8 Waɗanda suka yi su kamar su suke, haka ma duk wanda ya dogara gare su.
\s5
\v 9 Isra'ila, ku dogara ga Yahweh; shi ne taimakonku da garkuwarku.
\v 10 Gidan Haruna, ku dogara ga Yahweh; shi ne taimakonku da garkuwarku.
\v 11 Ku waɗanda ke girmama Yahweh, ku dogara gare shi; shi ne taimakonku da garkuwarku.
\s5
\v 12 Yahweh yana la'akari damu kuma zai albarkace mu; zai albarkaci iyalin Isra'ila; zai albarkaci iyalin Haruna.
\v 13 Zai albarkaci waɗanda ke girmama shi, yara da tsofaffi.
\v 14 Bari Yahweh ya ƙara lissafin ku ƙari da ƙari, naku dana zuriyarku.
\s5
\v 15 Bari ku yi albarka ta wurin Yahweh, wanda yayi sama da duniya.
\v 16 Sammai na Yahweh ne; amma duniya ya bayar ga 'yan adam.
\s5
\v 17 Matattu basu yabon Yahweh, ko kuwa wani wanda ya gangara cikin shiru;
\v 18 Amma zamu albarkaci Yahweh yanzu da har abada abadin. A Yabi Yahweh.
\s5
\c 116
\cl Zabura 116
\p
\v 1 Ina ƙaunar Yahweh saboda yana jin murya ta da kuma roƙe-roƙe na domin jinƙai.
\v 2 Saboda yana saurare na, zan yi kira a gare shi muddan ina da rai.
\s5
\v 3 Sarƙoƙin mutuwa sun kewaye ni, tarkon Lahira kuma ya fuskance ni; naji ƙunci da baƙinciki.
\v 4 Daga nan nayi kira ga sunan Yahweh: "Ina roƙon ka Yahweh, ka ceto rai na."
\s5
\v 5 Yahweh yana cike da jinƙai da adalci; Allahnmu mai tausayi ne.
\v 6 Yahweh yana kiyaye marasa sani; an kawo ni ƙasa, kuma ya cece ni.
\s5
\v 7 Raina zai koma wurin hutawarsa, domin Yahweh yana yi mani da kyau.
\v 8 Domin ka ceto raina daga mutuwa, idanu na daga hawaye, tafin ƙafafuna kuma daga tuntuɓe.
\s5
\v 9 Zan bauta wa Yahweh a ƙasar masu rai.
\v 10 Na bada gaskiya a gare shi, ko sa'ad da nace, "Ina cikin babban ƙunci."
\v 11 Nayi garejen cewa, "Dukkan mutane maƙaryata ne."
\s5
\v 12 Yaya zan biya Yahweh domin dukkan jiyejiyenƙansa zuwa gare ni?
\v 13 Zan ɗaga ƙoƙon ceto, in kuma yi kira ga sunan Yahweh.
\v 14 Zan cika alƙawaraina ga Yahweh a gaban dukkan mutanensa.
\v 15 Abu mai daraja a gaban Yahweh shi ne mutuwar tsarkakansa.
\s5
\v 16 Yahweh, tabbas, ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ɗauke tsarƙoƙina.
\v 17 Zan miƙa maka hadayar godiya in kuma yi kira ga sunan Yahweh.
\s5
\v 18 Zan cika alƙawaraina ga Yahweh a gaban dukkan mutanensa,
\v 19 cikin harabun gidan Yahweh, a tsakiyarki, Yerusalem. A yabi Yahweh.
\s5
\c 117
\cl Zabura 117
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh, dukkan ku al'ummai; ku ɗaukaka shi, dukkan ku mutane.
\v 2 Domin alƙawarin amincinsa mai girma ne zuwa gare mu, isar amincin Yahweh kuma ya dawwama har abada. A yabi Yahweh.
\s5
\c 118
\cl Zabura 118
\p
\v 1 Ku bada godiya ga Yahweh, domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\v 2 Bari Isra'ila su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada."
\s5
\v 3 Bari gidan Haruna su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada."
\v 4 Bari amintattun masu bin Yahweh su ce, "Alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada."
\s5
\v 5 A cikin ƙuncina nayi kira ga Yahweh; Yahweh ya amsa mani ya kuma 'yantar dani.
\v 6 Yahweh yana tare dani; ba zan ji tsoro ba; me mutum zai yi mani?
\v 7 Yahweh yana gefe na a matsayin mai taimako na; zan duba cikin nasara bisa waɗanda suka ƙi ni.
\s5
\v 8 Ya fi kyau a ɗauki mahalli cikin Yahweh da a sa dogara cikin mutum.
\v 9 Gwamma a ɗauki mafaka cikin Yahweh da wani yasa dogararsa cikin sarakuna.
\s5
\v 10 Dukkan al'ummai sun kewaye ni; a cikin sunan Yahweh na datse su.
\v 11 Sun kewaye ni; I, sun kewaye ni; a cikin sunan Yahweh na datse su.
\v 12 Sun kewaye ni kamar zuma; sun ɓace da sauri kamar wuta a tsakiyar sarƙaƙiya; a cikin sunan Yahweh na datse su.
\s5
\v 13 Sun kawo mani hari saboda su mãke ni ƙasa, amma Yahweh ya taimake ni.
\v 14 Yahweh ne ƙarfina da farincikina, shi ne kuma ya ceto ni.
\s5
\v 15 Sowar farinciki ta nasara aka ji a cikin rumfunan adalai; hannun dama na Yahweh ya ci nasara.
\v 16 Hannun dama na Yahweh ya ɗaukaka; hannun dama na Yahweh yaci nasara.
\s5
\v 17 Ba zan mutu ba, amma zan rayu kuma inyi shelar ayyukan Yahweh.
\v 18 Yahweh ya horar da ni da zafi; amma bai miƙa ni ga mutuwa ba.
\s5
\v 19 Ka buɗe mani ƙofofin adalci; zan shige su kuma zan bada godiya ga Yahweh.
\v 20 Wannan ce ƙofar Yahweh; adali yana bi ta ciki.
\v 21 Zan bada godiya a gare ka, domin ka amsa mani, kuma ka zama cetona.
\s5
\v 22 Dutsen da magina suka watsar ya zama dutsen kusurwa.
\v 23 Wannan yin Yahweh ne; mai ban mamaki ne a idanunmu.
\s5
\v 24 Wannan ce ranar da Yahweh ya yi aiki; za muyi farinciki da murna a cikin ta.
\v 25 Ina roƙon ka, Yahweh, ka bamu nasara! Ina roƙon ka, Yahweh, ka bamu ci gaba!
\s5
\v 26 Mai albarka ne wanda ya zo cikin sunan Yahweh; mun albarkace ka daga gidan Yahweh.
\v 27 Yahweh Allahn ne, ya kuma bamu haske; ku ɗaure hadaya da igiyoyi a ƙahonnin bagadi.
\v 28 Kai Allahna ne, kuma zan bada godiya a gare ka; kai Allahna ne; zan ɗaukaka ka.
\s5
\v 29 Oh, ku bada gadiya ga Yahweh; domin shi nagari ne; domin alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\c 119
\cl Zabura 119
\p
\d ALEPH
\p
\v 1 Masu albarka ne waɗanda hanyoyinsu basu da laifi, waɗanda ke tafiya cikin shari'ar Yahweh.
\v 2 Masu albarka ne waɗanda suka kiyaye umarnansa masu tsarki masu neman sa da dukkan zuciyarsu.
\s5
\v 3 Sun yi abin da ke dai-dai; suna tafiya cikin hanyoyinsa.
\v 4 Ka umarce mu mu kiyaye dokokinka, domin muyi lura mu kiyaye su,
\s5
\v 5 Kash, ina ma zan ɗore a cikin lura da farillanka!
\v 6 To da ba za a kunyata ni ba a lokacin da nayi tunanin dukkan dokokinka.
\s5
\v 7 Zan yi maka godiya da zuciya mai tsarki a lokacin dana koyi sharuɗɗanka.
\v 8 Zan kiyaye farillanka; kar ka barni ni kaɗai.
\d BETH
\s5
\p
\v 9 Yaya matashi zai tsare tafarkinsa da tsabta? Ta wurin kiyaye maganarka.
\v 10 Da dukkan zuciyata na neme ka; Kar ka barni in kauce wa umarnanka.
\s5
\v 11 Na adana maganarka a cikin zuciyata domin kada in yi maka zunubi.
\v 12 Yahweh kai mai albarka ne, ka koya mani farillanka.
\s5
\v 13 Da bakina na furta dukkan ayyukanka na jinƙai da ka bayyana mani.
\v 14 Ina murna da umarnanka fiye da dukkan wadata.
\s5
\v 15 Zan yi ta nazarin dokokinka in kuma saurari sharuɗɗanka.
\v 16 Ina jin daɗin farillanka; ba kuma zan manta da maganarka ba.
\d GIMEL
\s5
\p
\v 17 Yiwa bawanka kirki domin in rayu in kiyaye maganarka.
\v 18 Buɗe idanuna domin in ga ayyukan al'ajibi a cikin shari'arka.
\s5
\v 19 Ni bãƙo ne a cikin ƙasar; kada ka ɓoye umarnanka daga gare ni.
\v 20 An rushe marmarina ta wurin jimirin sanin umarnanka masu adalci a kowanne lokaci.
\s5
\v 21 Ka tsauta wa masu fahariya, waɗanda aka la'anta, Waɗanda suka bauɗe wa dokokinka.
\v 22 Kãre ni daga wulaƙanci da cin mutunci, domin na kiyaye sharuɗɗan alƙawarinka.
\s5
\v 23 Koda ya ke shugabanni sun ƙudurta suka yi mani maƙarƙashiya, ni bawanka ina binbinin farillanka.
\v 24 Alƙawaran farillanka sune nake jin daɗi, sune kuma ke yi mini jagora.
\d DALETH
\s5
\p
\v 25 Raina yana birgima a ƙura! Ka bani rai ta wurin maganarka.
\v 26 Na faɗa maka hanyoyina, ka kuma amsa mani; ka koya mani farillanka.
\s5
\v 27 Ka sani in fahimci tafarkin umarninka, domin in yi ta nazarin koyarwarka mai al'ajibi.
\v 28 Baƙinciki ya cika ni! Ka ƙarfafa ni ta wurin maganarka.
\s5
\v 29 Ka jutar daga gare ni hanyar yaudara; ta wurin alheri ka koya mani shari'arka.
\v 30 Na zaɓi hanyar aminci; Har kullum na kiyaye farillanka masu adalci daka sa a gabana.
\s5
\v 31 Na manne wa umarnin alƙawarinka; Yahweh kada ka bar ni in ji kunya.
\v 32 Zan bi hanyoyin dokokinka da gudu, gama ka faɗaɗa zuciyata tayi haka.
\d HE
\s5
\p
\v 33 Ka koya mani, Yahweh, hanyar umarnanka, kuma zan kiyaye su har ga ƙarshe.
\v 34 Ka bani ganewa, kuma zan kiyaye shari'arka; Zan lura da ita da dukkan zuciyata.
\s5
\v 35 Ka bishe ni ta tafarkin dokokinka, gama ina fahariya in yi tafiya cikinta.
\v 36 Ka jagoranci zuciyata ga alƙawarin umarnanka da kaucewa daga ƙazamar riba.
\s5
\v 37 Ka juya idanuwana daga duban wofintattun abubuwa; ka rayar da ni cikin hanyoyinka.
\v 38 Ka cika wa bawanka alƙawarin da kayi ga waɗanda ke girmama ka.
\s5
\v 39 Ka ɗauke zage-zagen da nake tsoro, gama hukuncin adalcinka na da kyau.
\v 40 Duba, na jira umarnanka; ka farkar dani cikin sanin gaskiyarka.
\d VAV
\s5
\p
\v 41 Yahweh, ka ba ni madawwamiyar ƙaunarka- cetonka bisa ga alƙawarinka;
\v 42 sa'an nan zan sami amsa domin duk mai yi mani ba'a, gama na amince da maganarka.
\s5
\v 43 Kada ka ɗauke maganar gaskiya daga bakina, gama Na yi jira domin umarnan sanin gaskiyarka.
\v 44 Zan kiyaye dokarka babu fasawa, har abada abadin.
\s5
\v 45 Zan yi tafiya cikin kwanciyar hankali, gama ina neman ka'idodinka.
\v 46 Zan yi magana a kan hakikanin umarninka a gaban sarakuna kuma ba zan ji kunya ba.
\s5
\v 47 Ina murna da dokokinka, waɗanda nake ƙauna sosai.
\v 48 Zan ɗaga hannuwana ga dokokinka, waɗanda nake ƙauna; Zan yi nazari a kan farillanka.
\d ZAYIN
\s5
\p
\v 49 Ka tuna da alƙawarinka zuwa ga bawanka domin ka ba ni bege.
\v 50 Wannan itace ta'aziyata a cikin ƙuncina: cewa alƙawarinka ya kiyaye ni da rai.
\s5
\v 51 Mai girman kai ya yi mani gwalo, duk da haka ban juya daga dokarka ba.
\v 52 Nayi tunanin umarnanka masu adalci dake tun zamanun dã, Yahweh, kuma sai na yi wa kaina ta'aziya.
\s5
\v 53 Fushi mai ƙuna ya riƙe ni sabili da mugu da ya ƙi dokarka.
\v 54 Farillannka sun zama waƙoƙina a cikin gidan da nake zama na ɗan lokaci.
\s5
\v 55 Na yi tunanin sunanka a cikin dare, Yahweh, na kuma riƙe dokarka.
\v 56 Wannan ya zama abin da na ke yi domin na kula da umarnanka.
\d HETH
\s5
\p
\v 57 Yahweh ne rabona; nayi ƙudirin kula da maganganunka.
\v 58 Nayi matuƙar neman tagomashinka da dukkan zuciyata; ka yi mani jinƙai, kamar yadda maganarka tayi alƙawari.
\s5
\v 59 Nayi la'akari da tafarkina na kuma juyar da ƙafafuna zuwa ga umarnan alƙawarinka.
\v 60 Nayi sauri ban kuma ɓata lokaci ba domin in kiyaye dokokin ka.
\s5
\v 61 Igiyoyin mai mugunta suka nannaɗe ni; Ban manta da shari'arka ba.
\v 62 Cikin dare na tashi domin inyi maka godiya sabili da dokokinka masu adalci.
\s5
\v 63 Ni abokin dukkan waɗanda ke girmamaka ne, da dukkan waɗanda ke kula da umarnanka.
\v 64 ƙasar, Yahweh, tana cike da amintaccen alƙawarinka; ka koya mani farillanka.
\d TETH
\s5
\p
\v 65 Kayi abin alheri ga bawanka, Yahweh, ta wurin maganarka.
\v 66 Ka koya mani sasancewa da fahimta, gama na gaskata da dokokinka.'
\s5
\v 67 Kamin a wahalshe ni sai da na bijire, amma yanzu ina kula da maganarka.
\v 68 Kana da kyau, kuma kai ne mai aikata abu mai kyau; ka koya mani farillanka.
\s5
\v 69 Mai girman kai ya rufe ni da ƙarairayi, amma na adana umarninka da dukkan zuciyata.
\v 70 Zuciyarsu ta taurare, amma ina fahariya da shari'arka.
\s5
\v 71 Ya dace dani dana sha wahala domin in koyi farillanka.
\v 72 Umarni daga bakinka ya fiye mani daraja fiye da dubban zinariya da azurfa.
\d YOD
\s5
\p
\v 73 Hannayenka sunyi ni ka ƙera ni; ka ba ni fahimta domin in koyi dokokinka.
\v 74 Waɗanda suke yi maka biyayya za suyi murna idan suka ganni saboda na sami bege cikin maganarka.
\s5
\v 75 Yahweh, Na sani, dokokinka masu adalci ne, cikin amincinka kuma ka hukunta ni.
\v 76 Bari alƙawarin amincinka ya ta'azantar dani, kamar yadda ka alƙawarta wa bawanka.
\s5
\v 77 Ka nuna mani jinƙai domin in rayu, gama shari'arka ita ce jin daɗina.
\v 78 Bari masu girmankai su sha kunya, gama sun ɓata sunana; amma zan yi nazarin umarnanka.
\s5
\v 79 Bari masu darjanta ka su juyo gare ni, su da suka san alƙawaran dokokinka.
\v 80 Bari zuciyata ta zama da rashin laifi da darjanta farillanka domin kada in sha kunya.
\d KAPH
\s5
\p
\v 81 Na suma domin sauraron cetonka! Na sa zuciya cikin maganarka.
\v 82 Idanuna na jiran ganin alƙawarinka; yaushe za ka ta'azantar dani?
\s5
\v 83 Gama na zama kamar salka cikin hayaƙi; Ban manta da farillanka ba.
\v 84 Har yaushe bawanka zai jiure da wannan; yaushe zaka hukunta waɗanda suke tsananta mani?
\s5
\v 85 Masu girmankai sun haƙa ramuka domina, suna rena shari'arka.
\v 86 Dukkan dokokinka abin dogaro ne; waɗannan mutanen suna tsananta mani cikin kuskure; ka taimake ni.
\s5
\v 87 Saura kaɗan su kawo ƙarshena a duniya, amma ban ƙi umarnanka ba.
\v 88 Ta wurin tsayayyar ƙaunarka, ka kiyaye ni a raye, domin inyi biyayya da umarnanka.
\d LAMEDH
\s5
\p
\v 89 Yahweh, maganarka ta tsaya har abada; maganarka ta kahu da ƙarfi a cikin sama.
\v 90 Amincinka ya dawwama ga dukkan tsararraki; ka kafa duniya, ta kuwa tsaya.
\s5
\v 91 Dukkan abubuwa sun ci gaba har yau, kamar yadda ka faɗi cikin amintattun umarnanka, gama dukkan abubuwa bayinka ne.
\v 92 Da shari'arka ba jin daɗina ba ce, da na hallaka a cikin ƙuncina.
\s5
\v 93 Ba zan taɓa mantawa da umarnanka ba, gama ta wurinsu ka kiyaye ni da rai.
\v 94 Ni naka ne; ka cece ni, gama na nemi umarnanka.
\s5
\v 95 Masu mugunta sunyi shirin hallakar dani, amma zan nemi in san alƙawarin umarnanka.
\v 96 Naga cewa dukkan abu yana da iyakarsa, amma dokokinka suna da fãɗi, basu da iyaka.
\d MEM
\s5
\p
\v 97 Oh ina ƙaunar shari'arka! ita ce abin bin-binina dukkan yini.
\v 98 Dokokinka sun sani na zama da hikima fiye da maƙiyana, gama dokokinka kullum suna tare dani.
\s5
\v 99 Ina da sani fiye da dukkan malamaina, gama ina tunani akan alƙawaran umarnanka.
\v 100 Ina da sani fiye da waɗanda suka girmeni; wannan ya faru domin na kiyaye umarnanka.
\s5
\v 101 Na kiyaye sawayena daga hanyar mugaye saboda in lura da maganarka.
\v 102 Ban juya daga dokokin adalcinka ba, saboda kai ne ka bani umarni.
\s5
\v 103 Ya ya zaƙin maganarka ga ɗanɗanona, I, tafi zuma zaƙi a bakina!
\v 104 Ta wurin umarninka na ƙaru da basira; saboda haka ina ƙin kowacce hanyar ƙarya.
\d NUN
\s5
\p
\v 105 Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma ga hanyata.
\v 106 Na rantse na kuma tabbatar da ita, saboda haka zan kula da adalcin dokokinka.
\s5
\v 107 Ina shan azaba; ka bar ni a raye, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta a cikin maganarka.
\v 108 Yahweh, idan ka yarda karɓi shaidar godiyar bakina, ka koya mani adalcin dokokinka.
\s5
\v 109 Raina kullum yana hannuna, duk da haka ban manta da shari'arka ba.
\v 110 Mugaye sun ɗana tarko domina, amma ban ratse daga umarninka ba.
\s5
\v 111 Na nemi alƙawaran dokokinka a matsayin gãdona har abada, gama su ne murnar zuciyata.
\v 112 Zuciyata a shirye take don biyayya da farillanka har abada, har kuma zuwa ƙarshe.
\d SAMEKH
\s5
\p
\v 113 Ina ƙin waɗanda ba sa son yi maka biyayya, amma ina ƙaunar shari'arka.
\v 114 Kai ne kake tsare ni da garkuwarka; ina jiran maganarka.
\s5
\v 115 Ku tafi daga gare ni, ku masu aikata mugunta, domin in kiyaye dokokin Allahna.
\v 116 Ka ƙarfafa ni ta wurin maganarka saboda in rayu ba domin inji kunyar sa begena ba.
\s5
\v 117 Ka ƙarfafa ni, zan kuma tsira. Zan yi ta nazari a kan umarninka.
\v 118 Ka ƙi dukkan waɗanda suka ratse daga umarninka, domin waɗancan mutanen masu yaudara ne kuma ba abin dogara ba ne.
\s5
\v 119 Ka cire dukkan mugayen duniya kamar dattin maƙera; saboda haka ina ƙaunar mahimman umarninka.
\v 120 Na cika da tsoronka, kuma ina jin tsoron adalcin ka'idodinka.
\d AYIN
\s5
\p
\v 121 Na yi abin da ke na gaskiya da adalci, kada ka bashe ni a wurin masu yi mani tsanani.
\v 122 Ka tsare lafiyar bawanka, kada ka bari masu girman kai su wahallar da shi.
\s5
\v 123 Idanuna sun gaji sa'ad da nake jiran cetonka da maganarka mai adalci.
\v 124 Ka nuna wa bawanka amincin alƙawarinka, ka koya mani farillanka.
\s5
\v 125 Ni bawanka ne, ka bani fahimta domin in sa alƙawarin farillanka.
\v 126 Lokaci ya yi da Yahweh zai yi aiki, domin mutane sun karya shari'arka.
\s5
\v 127 Gaskiya ne ina ƙaunar dokokinka fiye da zinariya, fiye da zinariya mai kyau.
\v 128 Saboda haka na bi umarninka a hankali, na tsani kowacce hanya ta ƙarya.
\d PE
\s5
\p
\v 129 Ka'idojinka suna da ban mamaki, shi yasa nake yin biyayya dasu.
\v 130 Buɗewar maganarka tana bada haske, tana bada ganewa ga wanda ba koyayye ba.
\s5
\v 131 Na buɗe bakina ina haki, saboda na ƙagara domin maganarka.
\v 132 Ka juyo wajena ka yi mani jinƙai kamar yadda ka ke yiwa waɗanda ke ƙaunar sunanka.
\s5
\v 133 Ka bida ƙafafuna da maganarka, kada ka bari wani zunubi yayi mulki a kaina.
\v 134 Ka fanshe ni daga hannun masu zalunci domin in lura da umarninka.
\s5
\v 135 Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka, ka koya mani farillanka.
\v 136 Ƙoramun ruwaye suna gudu daga idanuna saboda mutane ba sa lura da shari'arka ba.
\d TSADHE
\s5
\p
\v 137 Mai adalci ne kai, Yahweh, dokokinka kuma dai-dai suke.
\v 138 Ka bada dokokinka na alƙawari masu adalci kuma amintattu.
\s5
\v 139 Fushi ya hallaka ni saboda maƙiyana sun manta da maganganunka.
\v 140 An jaraba maganarka sau da yawa, bawanka kuma yana ƙaunar su.
\s5
\v 141 Ni ba komai bane an kuma rena ni, duk da haka ban manta da umarninka ba.
\v 142 Adalcinka dai-dai ya ke har abada, shari'arka madogara ce.
\s5
\v 143 Koda ya ke wahala da azaba sun afko mani, duk da haka dokokinka suna faranta mani rai.
\v 144 dokokinka na alƙawari masu adalci ne har abada.; ka bani fahimta domin in rayu.
\d QOPH
\s5
\p
\v 145 Nayi kuka da dukkan zuciyata, "Ka amsa mani, Yahweh, zan yi biyayya da farillanka.
\v 146 Na kira ka; ka cece ni, zan kuwa aikata dokokinka na alƙawari.
\s5
\v 147 Da asussuba nake tashi in yi kukan neman taimako. Na sa begena a cikin maganarka.
\v 148 Na kan farka kafin masu gadin dare suyi sauyi domin in yi bin-binin maganarka.
\s5
\v 149 Ka saurari muryata a cikin alƙawarin amincinka; ka barni da rai, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta a cikin dokokinka na adalci.
\v 150 Su waɗanda suke tsananta mani suna matsowa kusa dani, amma suna nesa da shari'arka.
\s5
\v 151 Kana kusa, Yahweh, kuma duk umarnanka amintattu ne.
\v 152 Tun dã can na koya daga dokokin alƙawaranka cewa ka tsaida su har abada.
\d RESH
\s5
\p
\v 153 Ka dubi ƙunci na kayi mani taimako, gama ban manta da shari'arka ba.
\v 154 Ka tsaya mani ka kuma fanshe ni; ka riƙe ni, kamar yadda ka alƙawarta a maganarka.
\s5
\v 155 Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa ƙaunar farillanka.
\v 156 Ayyukanka na jinƙai masu girma ne, Yahweh; ka kiyaye ni da rai, kamar yadda ka saba yi.
\s5
\v 157 Masu zaluntata da maƙiyana suna da yawa, duk da haka ban bar bin dokokinka na alƙawari ba.
\v 158 Ina duban maciya amana a ƙyamace domin ba sa biyayya da maganarka.
\s5
\v 159 Dubi yadda nake ƙaunar umarninka; ka kiyaye ni da rai, Yahweh, kamar yadda ka alƙawarta ta wurin alƙawarinka mai aminci.
\v 160 Cibiyar maganarka ita ce gaskiya; kowanne ɗaya daga cikin dokokinka na adalci ne sun tabbata har abada.
\d SHIN
\s5
\p
\v 161 Sarakuna suna tsananta mani ba dalili; zuciya ta ta karai, gama ina jin tsoron karya maganarka.
\v 162 Ina farinciki da maganarka kamar wanda ya sami ɗumbin ganima.
\s5
\v 163 Ina ƙin ƙarairayi ina kuma wofintar dasu, amma ina ƙaunar shari'arka.
\v 164 Ina yabon ka sau bakwai a rana sabili da dokokinka na adalci.
\s5
\v 165 Masu ƙaunar shari'arka, suna da babbar salama; ba abin da zai sasu suyi tuntuɓe.
\v 166 Ina jiran cetonka, Yahweh, ina kuma biyayya da dokokinka.
\s5
\v 167 Ina aikata dokokinka tabbatattu, ina kuma ƙaunarsu ƙwarai.
\v 168 Ina biyayya da umarninka da kuma dokokinka tabbatattu, gama kana sane da duk abin da nake yi.
\d TAV
\s5
\p
\v 169 Ka saurari kukana na neman taimako, Yahweh; ka bani fahimtar maganarka.
\v 170 Bari roƙona ya zo gaba gare ka; ka taimake ni, kamar yadda ka alƙawarta a maganarka.
\s5
\v 171 Bari leɓunana su cika da yabo, gama kana koya mani farillanka.
\v 172 Bari harshena yayi waƙa akan maganarka, gama dukkan dokokinka dai-dai suke.
\s5
\v 173 Bari hannunka ya taimake ni, gama na zaɓi umarnanka.
\v 174 Ina marmarin cetonka, Yahweh, shari'arka ce farincikina.
\s5
\v 175 Ka rayar dani don in yabe ka, bari dokokinka na adalci su taimake ni.
\v 176 Nayi makuwa kamar ɓatacciyar tunkiya; ka nemi bawanka, gama ban manta da dokokinka ba.
\s5
\c 120
\cl Zabura 120
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 A cikin ƙuncina nayi kira ga Yahweh, ya kuma amsa mani.
\v 2 Ka ƙwato raina, Yahweh, daga waɗanda ke ƙarya da leɓunansu da ruɗi da harsunansu.
\s5
\v 3 Ta yaya zai hore ka, mene ne kuma zai ƙara yi maka, kai wanda ke da harshe na ƙarya?
\v 4 Zai hore ka da kibiyoyin mayaƙi da aka wãsa bisa garwashin wutar ƙiraren itace.
\s5
\v 5 Kaito na saboda ina zaune jim kaɗan cikin Meshek; Dã na zauna a rumfunan Keda.
\v 6 Har dogon lokaci na zauna tare da waɗanda suka ƙi salama.
\v 7 Ni domin salama nake, amma idan na yi magana, domin yaƙi suke.
\s5
\c 121
\cl Zabura 121
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Zan ɗaga idanu na ga duwatsu. Daga ina taimakona zai zo?
\v 2 Taimakona na zuwa daga Yahweh, wanda yayi sama da duniya.
\s5
\v 3 Ba zai bar sawunka ya zãme ba; shi wanda ya ke kiyaye ka ba zai yi gyangyaɗi ba.
\v 4 Duba, mai lura da Isra'ila ba zai taɓa gyangyaɗi ba ko barci.
\s5
\v 5 Yahweh shi ne mai lura da kai; Yahweh shi ne inuwa a hannun damanka.
\v 6 Rana ba zata cutar da kai ba da rana, ko kuma wata da daddare.
\s5
\v 7 Yahweh zai kiyaye ka daga dukkan cutarwa, kuma zai kiyaye ranka.
\v 8 Yahweh zai kiyaye ka cikin dukkan abin da kake yi yanzu da har abada abadin.
\s5
\c 122
\cl Zabura 122
\p
\d Waƙar takawa sama, ta Dauda.
\p
\v 1 Nayi farinciki da suka ce mani, "Bari mu tafi gidan Yahweh."
\v 2 Yerusalem, sawayenmu na tsaye cikin ƙofofinki!
\v 3 Yerusalem, an gina ki birnin da aka yiwa shiri a hankali!
\s5
\v 4 Kabilun suna tafiya Yerusalem - kabilun Yahweh - a matsayin shaida ga Isra'ila, su bada godiya ga sunan Yahweh.
\v 5 An kafa kursiyoyin hukuncinsu, kursiyoyin gidan Dauda.
\s5
\v 6 Kuyi addu'a domin salamar Yerusalem! "Bari masu ƙaunar ki su sami salama.
\v 7 Bari salama ta kasance cikin katangogin dake kãre ki, bari kuma su sami salama cikin ƙarfafan wurin tsaronki."
\s5
\v 8 Domin albarkacin 'yan'uwana da abokaina zan ce, "Bari salama ta kasance a cikin ki."
\v 9 Domin albarkacin gidan Yahweh Allahnmu, zan biɗi alheri game dake.
\s5
\c 123
\cl Zabura 123
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 A gare ka na ɗaga idanuna, kai wanda kake bisa kursiyi a sammai.
\v 2 Duba, kamar yadda idanun bãyi ke duban hannun ubangijinsu, kamar yadda idanun baiwa ke duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu ke duban Yahweh Allahnmu har sai ya nuna mana jinƙai.
\s5
\v 3 Kayi mana jinƙai, Yahweh, kayi mana jinƙai, domin cike muke da wulaƙanci.
\v 4 Mun ma fi cike da ba'ar masu ba'a da kuma renin masu fahariya.
\s5
\c 124
\cl Zabura 124
\p
\d Waƙar takawa sama, ta Dauda.
\p
\v 1 "Idan da ba don Yahweh yana gefenmu ba," bari Isra'ila suce yanzu,
\v 2 "Idan da ba don Yahweh yana gefenmu ba sa'ad da mutane suka taso gãba da mu,
\v 3 daga nan da sun haɗiye mu ɗungum da rai sa'ad da fushin su ya wo hauka gãba da mu.
\s5
\v 4 Da ruwa ya share mu; igiyoyin da sun sha ƙarfinmu.
\v 5 Daga nan haukan ruwayen da ya shanye mu."
\s5
\v 6 Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda bai bari haƙoran sa suka yayyage mu ba.
\v 7 Mun kucce kamar tsuntsu daga tarkon mafarauta; tarkon ya karye, mun kuma kucce.
\s5
\v 8 Taimakonmu yana cikin Yahweh, wanda ya yi sama da ƙasa.
\s5
\c 125
\cl Zabura 125
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Waɗanda suka sa dogararsu ga Yahweh suna kama da Tsaunin Sihiyona, marar jijjiguwa, mai dawwama har abada.
\v 2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Yerusalem, haka Yahweh ya kewaye mutanensa yanzu da har abada.
\v 3 Sandar mulkin mugunta ba za tayi mulki ba a ƙasar mai adalci. Idan ba haka ba mai adalci zai iya yin abin da ba dai-dai ba.
\s5
\v 4 Kayi da kyau, Yahweh, ga waɗanda suke yi da kyau waɗanda kuma suke masu adalci a zukatansu.
\v 5 Amma ga waɗanda suka kauce gefe ga karkatattun hanyoyinsu, Yahweh zai kawar dasu tare da masu aikata mugunta. Bari salama ta kasance a Isra'ila.
\s5
\c 126
\cl Zabura 126
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Sa'ad da Yahweh ya maido da kadarorin Sihiyona, mun zama kamar masu mafarki.
\s5
\v 2 Daga nan bakunanmu suka cika da dariya harsunanmu kuma da waƙa. Daga nan suka ce a tsakanin al'ummai, "Yahweh ya yi masu manyan abubuwa."
\v 3 Yahweh ya yi mana manyan abubuwa; mun kuwa yi murna!
\s5
\v 4 Ka maido da kadarorinmu, Yahweh, kamar rafuffukan Negeb.
\v 5 Su waɗanda suka yi shuka cikin hawaye zasu yi girbi tare da sowace-sowacen farinciki.
\v 6 Shi wanda ya fita da kuka, yana ɗauke da irin shuka, zai sake dawowa da sowace-sowacen farinciki, yana kawo dammunansa tare da shi.
\s5
\c 127
\cl Zabura 127
\p
\d Waƙar takawa sama, ta Suleman.
\p
\v 1 Sai idan Yahweh ne ya gina gida, sun yi aikin banza, su waɗanda ke ginin. Sai idan Yahweh ne yayi tsaron birni, masu tsaron suna tsayawa tsaro a banza.
\v 2 Aikin banza ne a gare ka ka tashi da wuri, ka dawo gida da latti, ko ka ci gurasar aiki tuƙuru, domin Yahweh yana biyan buƙatun masu ƙaunarsa yayin da suke barci.
\s5
\v 3 Duba, 'ya'ya gãdo ne daga Yahweh, kuma ɗiyan mahaifa lada ne daga gare shi.
\v 4 Kamar kibiyoyi a hannun mayaƙi, haka nan 'ya'yan ƙuruciyar mutum.
\v 5 Yaya albarkar mutumin da yake da kwarinsa cike da su. Ba zai sha kunya ba sa'ad da ya fuskanci maƙiyansa a ƙofa.
\s5
\c 128
\cl Zabura 128
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Mai albarka ne duk wanda ya girmama Yahweh, wanda ya ke tafiya cikin hanyoyinsa.
\v 2 Abin da hannuwanka suka wadatar, zaka ji daɗin sa; zaka yi albarka da wadata.
\s5
\v 3 Matarka zata zama kamar inabi mai bada 'ya'ya a cikin gidanka; 'ya'yanka zasu zama kamar itatuwan zaitun yayin da suka zauna kewaye da teburinka.
\v 4 I, tabbas, mutumin zai zama mai albarka wanda ya ke girmama Yahweh.
\v 5 Bari Yahweh ya albarkace ka daga Sihiyona; bari kaga wadatar Yerusalem dukkan kwanakin rayuwarka.
\v 6 Bari ka rayu ka ga 'ya'yan 'ya'yanka. Bari salama ta kasance bisa Isra'ila.
\s5
\c 129
\cl Zabura 129
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 "Sau da yawa tun ƙuruciya ta suke kawo mani hari," bari Isra'ila yace.
\v 2 "Sau da yawa tun ƙuruciya ta suke kawo mani hari, duk da haka ba su kayar dani ba.
\v 3 Masu huɗa suna huɗa bisa bayana; sunyi kuyyoyinsu da tsawo.
\s5
\v 4 Yahweh mai adalci ne; ya datse igiyoyin mai mugunta."
\v 5 Bari dukkan su su sha kunya su kuma koma baya, su waɗanda suka ƙi jinin Sihiyona.
\s5
\v 6 Bari su zama kamar ciyawar dake bisa rufin gida wadda ke yaushi kafin ta girma,
\v 7 wadda ba zata cika hannun mai girbi ba ko ƙirjin mai ɗaure dammuna.
\v 8 Bari waɗanda ke ratsawa su wuce kada su ce, "Bari albarkar Yahweh ta kasance a kan ka; mun albarkace ka a cikin sunan Yahweh."
\s5
\c 130
\cl Zabura 130
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Daga zurfafa nayi kuka gare ka, Yahweh.
\v 2 Ubangiji, ka ji murya ta; bari kunnuwanka su saurari roƙe-roƙe na domin jinƙai.
\s5
\v 3 Idan kai, Yahweh, zaka kula da kurakurai, Ubangiji, wane ne zai iya tsayawa?
\v 4 Amma akwai gafartawa tare da kai, saboda a girmama ka.
\s5
\v 5 Nayi jira domin ka Yahweh, raina yana jira, kuma a cikin maganarsa nake da bege.
\v 6 Raina yana jira domin Ubangiji fiye da yadda masu tsaro ke jira domin safiya.
\s5
\v 7 Isra'ila, kuyi bege cikin Yahweh. Yahweh yana cike da jinƙai, kuma yana da nufin gafartawa sosai.
\v 8 Shi ne wanda zai fanshi Isra'ila daga dukkan zunubansa.
\s5
\c 131
\cl Zabura 131
\p
\d Waƙar takawa sama; ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, zuciyata ba tayi fahariya ba ko idanuna suyi tsauri. Bani da manyan bege domin kaina ko in dami kaina da abubuwan da suka sha kaina.
\s5
\v 2 Tabbas na tsaida kuma na tausar da raina; kamar ɗan da aka yaye tare da mahaifiyarsa, raina a ciki na kamar ɗan yaye ya ke.
\v 3 Isra'ila, kasa bege cikin Yahweh yanzu da har abada.
\s5
\c 132
\cl Zabura 132
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Yahweh, albarkacin Dauda ka tuna da dukkan ƙuncinsa.
\v 2 Ka tuna da yadda ya rantse wa Yahweh, yadda yayi wa'adi ga Mai Iko Dukka na Yakubu.
\s5
\v 3 Yace, "Ba zan shiga gidana ba ko in kwanta a kan gadona ba,
\v 4 ba zan ba idanuna barci ba ko kuma in rintsa
\v 5 sai na samawa Yahweh wuri, rumfar sujada domin Maɗaukaki na Yakubu."
\s5
\v 6 Duba, munji haka a Ifrata; mun same shi a jejin Yayir.
\v 7 Zamu shiga rumfar sujada ta Allah; zamu yi sujada a ƙafafunsa.
\v 8 Tashi, Yahweh, zuwa wurin hutawarka, kai da akwatin alƙawarinka mai nuna ƙarfinka!
\s5
\v 9 Bari firistocinka su suturta da adalci; bari amintattunka suyi ihu don murna.
\v 10 Saboda bawanka Dauda, kada ka juya wa zaɓaɓɓen sarkinka baya.
\s5
\v 11 Yahweh ya rantse da tabbatacciyen wa'adi ga Dauda, tabbataccen wa'adi da ba zai janye ba: "Zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyarka in sa shi bisa gadon sarautarka.
\v 12 Idan 'ya'yanka sun yi biyayya da umarnina da kuma dokokin da zan koya masu, 'ya'yansu zasu zauna a gadon sarautarka har abada."
\s5
\v 13 Hakika Yahweh ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa.
\v 14 "Nan ne wurin hutawana har abada. Zan zauna a nan, gama ina marmarinta.
\s5
\v 15 Zan albarkaceta da yalwar abin da take buƙata, zan ƙosar da matalautanta da abinci.
\v 16 Zan suturta firistocinta da ceto, amintattunta zasu yi sowa da ƙarfi don murna.
\s5
\v 17 Can zan sa ƙaho ya toho domin Dauda zan kuma kafa fitila domin zaɓaɓɓena.
\v 18 Zan suturta maƙiyansa da kunya, amma a kansa kambinsa zai yi walƙiya."
\s5
\c 133
\cl Zabura 133
\p
\d Waƙar takawa sama, ta Dauda.
\p
\v 1 Duba, yadda ya ke da kyau da kuma daɗi idan 'yan'uwa suka zauna tare!
\s5
\v 2 Wannan yana kama da mai mai kyau a kai dake gangarowa zuwa gemu - gemun Haruna, yana kuma gangarowa har kan wuyar rigarsa.
\v 3 Kamar raɓar Hermon da take fadowa bisa duwatsun Sihiyona. Gama a nan ne Yahweh ya umarta albarka - rai na har abada.
\s5
\c 134
\cl Zabura 134
\p
\d Waƙar takawa sama.
\p
\v 1 Ku zo, ku albarkaci Yahweh, dukkanku bayin Yahweh, ku da kuke wa Yahweh hidima da dare a haikalinsa.
\v 2 Ku ɗaga hannunwanku zuwa wuri mai tsarki ku albarkaci Yahweh.
\s5
\v 3 Bari Yahweh ya albarkace ku daga Sihiyona, Shi da yayi sama da ƙasa.
\s5
\c 135
\cl Zabura 135
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi sunan Yahweh. Ku yabe shi, ku barorin Yahweh,
\v 2 ku da kuke tsayawa a cikin haikalinsa, cikin harabun gidan Allahnmu.
\s5
\v 3 Ku yabi Yahweh, gama shi nagari ne; ku raira waƙoƙin yabo ga sunansa, gama yana da ƙyau a yi haka.
\v 4 Gama Yahweh ya zaɓi Yakubu domin kansa, Isra'ila abin mallakarsa.
\s5
\v 5 Na sani Yahweh mai girma ne, kuma Ubangijinmu yafi dukkan alloli.
\v 6 Ko mene ne Yahweh ya ke marmari, yakan yi shi a cikin sama, da ƙasa, a cikin ruwaye da dukkan zurfafan tekuna.
\s5
\v 7 Yakan kawo gizagizai daga nesa, yakan sa walƙiya da ruwan sama su taho tare, ya kuma fito da iska daga rumbunsa.
\s5
\v 8 Ya kashe ɗan farin Masar, na mutum dana dabbobi.
\v 9 Ya aika da alamu da al'ajibai a tsakiyarsu, Masar, gãba da Fir'auna da dukkan barorinsa.
\s5
\v 10 Ya hari al'ummai da yawa ya kuma kashe manyan sarkuna,
\v 11 Sihon sarkin Amoriyawa da Og sakin Bashan da dukkan mulkokin Kan'ana.
\s5
\v 12 Ya ba mu ƙasarsu abin gãdo, gãdo ga Isra'ila mutanensa.
\v 13 Sunanka, Yahweh, ya dawwama har abada; ka shahara, Yahweh, dawwamamme har tsararraki dukka.
\s5
\v 14 Gama Yahweh zai kare mutanensa, yana juyayin barorinsa.
\v 15 Allolin al'ummai azurfa ne da zinariya, aikin hannuwan mutane.
\v 16 Waɗannan allolin suna da bakuna, amma ba su yin magana; suna da idanu, amma ba sa gani;
\v 17 suna da kunnuwa, amma ba sa ji, babu kuma numfashi a bakunansu.
\v 18 Waɗanda suka siffanta su kamar su suke, haka kuma wanda ya dogara gare su.
\s5
\v 19 Zuriyar Isra'ila, ku albarkaci Yahweh; ku zuriyar Haruna, ku albarkaci Yahweh.
\v 20 Ku zuriyar Lebi, ku albarkaci Yahweh; ku da kuke girmama Yahweh, ku albarci Yahweh.
\v 21 Mai albarka ne Yahweh a cikin Sihiyona, shi wanda da ya ke zaune cikin Yerusalem. Ku yabi Yahweh.
\s5
\c 136
\cl Zabura 136
\p
\v 1 Oh, kuyi godiya ga Yahweh; gama nagari ne, gama alƙawarin amincisa ya dawwama har abada.
\v 2 Oh, kuyi godiya ga Allahn alloli, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\v 3 Oh, ku yi godiya ga Ubangiji iyayengiji, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 4 Kuyi godiya ga wanda shi ƙaɗai ya ke manyan mu'ujizai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 5 ga shi wanda ta wurin hikima yayi sammai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 6 Ku yi godiya ga shi wanda ya shinfiɗa ƙasa da sama da ruwaye, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 7 ga shi wanda yayi manyan haske, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 8 Kuyi godiya ga wanda ya bada rana yayi mulkin yini, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 9 wata da taurari suyi mulki da dare, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 10 Kuyi godiya ga wanda ya karkashe 'ya'yan fari na Masar, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 11 ya fitar da Isra'ila daga tsakiyarsu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 12 da ƙarfin hannunsa ba janyewa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 13 Ku yi godiya ga wanda ya tsaga Tekun Iwa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 14 yasa Isra'ila suka wuce ta tsakiyarsa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 15 amma ya dulmayar da Fir'auna da rundunarsa cikin Tekun Iwa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 16 Kuyi godiya ga wanda ya bida mutanensa cikin jeji, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 17 ga shi wanda ya kashe manyan sarakuna, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 18 Kuyi godiya ga wanda ya kashe shahararrun sarakuna, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 19 Sihon sarkin Amoriyawa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 20 da Og sarkin Bashan, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 21 Kuyi godiya ga shi wanda ya bada ƙasarsu abin gado, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 22 abin gado ga Isra'ila bawansa, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 23 ga wanda ya tuna damu ya kuma taimake mu cikin ƙasƙancinmu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\v 24 Kuyi godiya ga shi wanda ya bamu nasara bisa maƙiyanmu, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada -
\v 25 ga wanda ke bada abinci ga dukkan masu rai, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\v 26 Oh, sai ku yi godiya ga Allah na sama, gama alƙawarin amincinsa ya dawwama har abada.
\s5
\c 137
\cl Zabura 137
\p
\v 1 Muka zauna a bakin kogunan Babila muka yi ta kuka da muka tuna da Sihiyona.
\v 2 Muka rataye garayunmu akan itatuwa.
\s5
\v 3 A can waɗanda suka bautar damu suka roƙa muyi masu waƙoƙi, kuma waɗanda suka yi mana ba'a suka matsa mana muyi farinciki, suna cewa, "Ku raira mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona."
\v 4 Ƙaƙa zamu raira waƙa kan Yahweh a baƙuwar ƙasa?
\s5
\v 5 Idan na ƙyale tunawa dake, Yerusalem, bari hannun damana ya manta da iya kaɗa garaya.
\v 6 Bari harshena ya manne a rufin bakina, idan na dena tunaninki, idan ban fi son Yerusalem da abin da nafi jin daɗi ba.
\s5
\v 7 Ka tuna, Yahweh, abin da Idomawa suka yi a ranar da Yerusalem ta faɗi. Suka ce, "A ragargazata, a ragargazata har harsashenta."
\s5
\v 8 Ɗiyar Babila, an kusa hallaka ki - bari mutumin nan ya zama da albarka, ko ma wane ne wanda ya sãka maki domin abin da kika yi mana.
\v 9 Bari mutumin nan ya sami albarka, duk wanda ya kwashe 'ya'yanki ƙanana ya fyaɗa su kan duwatsu.
\s5
\c 138
\cl Zabura 138
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Zan yi maka godiya da dukkan zuciyata; a gaban alloli zan raira yabbai gare ka.
\v 2 Zan rusuna ina fuskantar haikalinka mai tsarki in kuma bada godiya ga sunanka sabili da amincinka na alƙawarinka domin kuma amincewarka. Ka fifita maganarka da sunanka da muhimmanci fiye da komai.
\s5
\v 3 A ranar dana kira ka, ka amsa mani; ka ƙarfafa ni ka bani karfin zuciya.
\v 4 Dukkan sarakunan duniya zasu yi maka godiya, Yahweh, gama zasu ji maganganun bakinka.
\s5
\v 5 Hakika, zasu raira waƙoƙi akan abubuwan da Yahweh yayi, gama ɗaukakar Yahweh mai girma ce.
\v 6 Gama ko da ya ke Yahweh mafifici ne, duk da haka yana kula da masu kaɗaici, amma ya san masu girman kai tun daga nesa.
\s5
\v 7 Koda ya ke ina tafiya a tsakiyar hatsari, zaka tsare raina; zaka miƙa hannunka gãba da hushin maƙiyana, hannun damanka zai cece ni.
\v 8 Yahweh yana tare da ni har ƙarshe; alƙawarin amincinka, Yahweh, dawwamamme ne har abada. Kada ka yasar da waɗanda hannuwanka suka yi.
\s5
\c 139
\cl Zabura 139
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, ka jaraba ni, ka kuma sanni.
\v 2 Ka san lokacin da zan zauna da lokacin da zan tashi; ka san tunanina tun daga nesa.
\s5
\v 3 Kana lura da tafarkina da kwanciyata; hanyoyina sanannu ne dukka a gareka.
\v 4 Gama kafin magana ta kasance a kan harshena, ka sani sarai.
\v 5 Ka kewaye ni gaba da baya kuma ka ɗibiya hannunka a kaina.
\v 6 Wannan sani ya fi ƙarfina ƙwarai; yayi mani zurfi, ba zan iya fahimtar sa ba.
\s5
\v 7 Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan guje wa fuskarka?
\v 8 Idan na hau cikin sammai, kana can; Idan na tafi na zauna cikin Lahira, to duba, kana can.
\s5
\v 9 Idan nayi asubanci na tashi sama akan fukafukai na tafi na zauna can nesa a ƙurewar teku,
\v 10 ko can ma hannunka zai bishe ni, hannun damanka zai riƙe ni.
\s5
\v 11 Idan nace, "Hakika duhu zai rufe ni, haske kuma ya zama dare kewaye dani,"
\v 12 ko duhunma ba zai zama duhu a gare ka ba. Daren zai haskaka kamar rana, gama da duhu da haske duk ɗaya suke a gare ka.
\s5
\v 13 Kai ka yi gaɓaɓuwan cikin cikina; kai ka siffanta ni a cikin mahaifiyata.
\v 14 Zan yabe ka, gama an yini da ƙyan gaske. Raina ya tabbatar da wannan sosai.
\s5
\v 15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke ba gare ka sa'ad da aka siffanta ni a ɓoye, sa'ad da aka hallita ni a can cikin zurfin ƙasa.
\v 16 Ka ganni a cikin mahaifa; dukkan kwanakin da an ƙaddara mani suna rubuce cikin littafinka tun kafin na farkon ya faru.
\s5
\v 17 Tunaninka yana da daraja a guna, Allah! Tarinsu da yawa basu lisaftuwa.
\v 18 Idan na yi ƙoƙarin ƙididdiga su, zasu fi yashi yawa. Sa'ad da na farka, ina tare da kai.
\s5
\v 19 Dãma zaka kashe mugaye, ya Allah; ku rabu dani, ku 'yan ta'adda.
\v 20 Suna yi maka tawaye suna aikata munafunci, maƙiyanka suna faɗar ƙarairayi.
\s5
\v 21 Ba na ƙi waɗanda suka ƙi ka ba, Yahweh? Ba ina rena waɗanda suka tashi gãba da kai ba?
\v 22 Na ƙi su fau-fau; sun zama maƙiyana.
\s5
\v 23 Ka jaraba ni, ya Allah, ka san zuciyata; ka gwada ni ka san tunanina.
\v 24 Ka duba ko akwai muguwar hanya a cikina, ka kuma bishe ni a madawwamiyar hanya.
\s5
\c 140
\cl Zabura 140
\p
\d Domin shugaban mawaƙa. Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, ka cece ni daga mugaye; ka kiyaye ni daga mutane masu zafin rai.
\v 2 Sukan shirya mugunta a zuciyarsu; sukan sa yaƙi kowacce rana.
\v 3 Harsunansu suna sara kamar maciji; dafin kububuwa na leɓunansu. Selah
\s5
\v 4 Ka tsare ni daga hannuwan mugaye, Yahweh; ka tsare ni daga mutane masu zafin rai waɗanda suka shirya su kada ni ƙasa.
\v 5 Masu fariya sun ɗana mani tarko; sun baza taru; sun shirya mani tarko. Selah
\s5
\v 6 Na cewa Yahweh, "Kai ne Allahna; ka kasa kunne ga koke-kokena na neman jinƙai.
\v 7 Yahweh, Ubangijina, kai mai iko ne ka iya ceto na; kana kare kaina a lokacin yaƙi.
\v 8 Yahweh, kada ka biya buƙatun mugaye; kada ka bari shirye-shiryensu yayi nasara. Selah
\s5
\v 9 Waɗanda suka ɗaga kansu sun kewaye ni; bari makircin leɓunansu ya rufe su.
\v 10 Bari garwashin wuta su afko masu; ka jefa su cikin wuta, cikin rami marar matuƙa, kada su ƙara tashi.
\v 11 Kada mutane masu mugun harshe su sami kwanciyar rai a duniya; bari bala'i ya farauci ɗan ta'adda ya buge shi ya mutu.
\s5
\v 12 Na sani Yahweh zai kyautata wa mai shan ƙunci a shari'a kuma zai yi adalci ga matalauci.
\v 13 Hakika mutane masu adalci zasu bada godiya ga sunanka; mutanen dake yin gaskiya zasu kasance a gabanka.
\s5
\c 141
\cl Zabura 141
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Yahweh, ina kuka gare ka; ka zo wurina da sauri. Ka saurare ni sa'ad da na kira ka.
\v 2 Bari addu'ata ta zama kamar turare a gaban ka; bari tãda hannuwana sama ya zama kamar hadayar maraice.
\s5
\v 3 Yahweh, kasa mai tsaro a bakina; ka kiyaye ƙofar leɓunana,
\v 4 Kada ka bari zuciyata ta yi marmarin wani mugun abu ko in haɗa kai cikin ayyukan zunubi tare da mutanen dake aikata mugunta. Kada ma in ci wani kayan lashe-lashensu.
\s5
\v 5 Bari adilin mutum ya buge ni; zai zamar mani alheri. Bari ya tsauta mani; zai zama kamar mai a kaina; bari kada in ƙi karɓar wannan. Amma addu'ata kullum gãba take da ayyukan muguntarsu.
\v 6 Za a jefar da shugabanninsu daga kan duwatsu; zasu ji cewa maganganuna masu daɗi ne.
\v 7 Tilas zasu ce, "Kamar yadda mutum yakan yi huɗa ya rugurguza ƙasa, haka suka warwatsar da ƙasusuwanmu a ƙofar Lahira."
\s5
\v 8 Hakika idanuna suna kanka, Yahweh, Ubangiji; a cikinka zan fake; kar ka bar raina ba tsaro.
\v 9 Ka tsare ni daga tarkunan da suka ɗana mani, daga tarkunan masu mugun aiki.
\v 10 Bari mugaye su faɗa cikin tarkonsu ni kuwa in kubce.
\s5
\c 142
\cl Zabura 142
\p
\d Salon waƙa ta Dauda, lokacin da ya ke cikin kogo; addu'a.
\p
\v 1 Da muryata nayi kuka domin neman taimako daga Yahweh; da muryata na roƙi Yahweh tagomashi.
\v 2 Na zuba masa koke-kokena a gabansa; na gaya masa wahaluna.
\s5
\v 3 Sa'ad da ruhuna ya raunana a cikina, ka san tafarkina. Sun ɗana ɓoyayyen tarko domina a hanyar da nake bi.
\v 4 Na duba hannun damana sai na ga babu wanda ya kula dani. Ba mafita domina, ba wanda ya kula da rayuwata.
\v 5 Na kira gare ka, Yahweh; nace, "Kai ne mafakata, rabona kuma a ƙasar rayayyu.
\s5
\v 6 Ka kasa kunne ga kirana, gama an ƙasƙantar dani; ka cece ni daga masu tsananta mani, gama sun fi ƙarfi na,
\v 7 Ka fitar da raina daga kurkuku domin in yi godiya ga sunanka. Masu adalci zasu tattaru kewaye dani domin ka yi mani alheri."
\s5
\c 143
\cl Zabura 143
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Ka ji addu'ata, Yahweh; ka ji roƙona. Saboda amincinka da adalcinka, ka amsa mani!
\v 2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari'a gama a gabanka babu mai adalci ko ɗaya.
\s5
\v 3 Maƙiyina ya hari raina; ya ture ni ƙasa; ya sãni in zauna cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun-tuni.
\v 4 Ruhuna ya karaya a cikina; babu sauran bege a raina.
\s5
\v 5 Idan na tuna kwanakin dã; na kan yi bin-bini akan ayyukanka; ina tunani akan nasararka.
\v 6 Na tada hannuwana zuwa gare ka cikin addu'a; raina yana da ƙishinka cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa. Selah
\s5
\v 7 Ka amsa mani da wuri, Yahweh, saboda ruhuna ya some. Kada ka ɓoye mani fuskarka, domin kada in zama kamar masu gangarawa cikin rami.
\v 8 Bari inji alƙawarinka na aminci da safe, gama na dogara gare ka. Ka nuna mani tafarkin da zan bi, gama nasa zuciyata a gare ka.
\s5
\v 9 Ka cece ni daga maƙiyana, Yahweh; ina gudu gare ka domin in ɓoye.
\v 10 Ka koya mani in aikata nufinka, gama kai ne Allahna. Bari Ruhunka mai kyau ya bishe ni cikin ƙasar da ake adalci.
\s5
\v 11 Yahweh, sabili da sunanka, ka barni da rai; cikin adalcinka ka fitar da raina daga wahala.
\v 12 Cikin alƙawarin amincinka ka datse maƙiyana kuma ka hallaka dukkan maƙiyan rayuwata, gama ni baranka ne.
\s5
\c 144
\cl Zabura 144
\p
\d Zabura ta Dauda.
\p
\v 1 Mai albarka ne Yahweh, dutsena, wanda ya ke horar da hannuwana domin yaƙi da yatsuna domin faɗa.
\v 2 Kai nawane mai amintaccen alƙawari da mafakata, kaine hasumiyata mai tsawo wanda ya ke ceto na, garkuwata wanda a cikinsa nake fakewa, shi ya ke sarayar da al'ummai ƙarƙashina.
\s5
\v 3 Yahweh, wane ne mutum har da kake kula shi ko ɗan mutum da kake tunani a kansa?
\v 4 Mutum kamar huci ya ke; kwanakinsa kamar inuwa mai wucewa ne.
\s5
\v 5 Ka sa sararin sama ya tsage ka sabko ƙasa, Yahweh; ka taɓa duwatsu ka sa suyi hayaƙi.
\v 6 Ka aika walƙiyar tsawa ka warwatsar da maƙiyana; ka harba kibanka ka kore su su sheƙa a ruɗe.
\s5
\v 7 Ka miƙo hannunka daga sama; ka cece ni daga ɗumbin ruwaye; daga hannun baƙi.
\v 8 Bakunansu suna faɗar ƙarairayi, komai kuma dake hannunsu sun samu ne daga rashin gaskiya.
\s5
\v 9 Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah; akan garaya mai igiya goma zan raira maka yabo,
\v 10 kai wanda ke bada ceto ga sarakai, wanda ya tsirar da Dauda bawanka daga mugun takobi.
\v 11 Ka cece ni ka 'yantar dani daga hannun baƙi. Bakunansu suna faɗar ƙarairayi, a hannun damansu kuma akwai rashin gaskiya.
\s5
\v 12 Bari 'ya'yanmu maza su zama kamar dashe-dashen da suka yi girma suka ƙosa a samartakarsu 'ya'yanmu mata kuma kamar sassaƙaƙƙun ginshiƙan fãda masu kyan fasali.
\v 13 Bari rumbunanmu su cika da kowanne irin amfani, bari kuma tumakinmu su hayayyafa dubbai kan dubbai har sau goma a saura.
\s5
\v 14 Sa'an nan shanunmu zasu haifi 'yan maruƙa da yawa. Ba wanda zai hudo ta katangunmu; baza a tafi bautar talala ba ko a ji koke-koke a tituna.
\v 15 Masu albarka ne mutanen dake da waɗannan albarku; masu farinciki ne mutanen da Allahnsu shi ne Yahweh.
\s5
\c 145
\cl Zabura 145
\p
\d Zabura ta yabo. Ta Dauda.
\p
\v 1 Zan ɗaukaka ka, ya Allah, Sarki; zan albarkaci sunanka har abada abadin.
\v 2 Kowace rana zan albarkace ka; zan albarkaci sunanka har abada abadin.
\v 3 Yahweh Mai Girma ne, ƙasaitarsa ta cancanci yabo; Girmansa ba ya bincikuwa.
\s5
\v 4 Daga wata tsara zuwa wata tsara za a yabi ayyukanka kuma za a labarta manyan ayyukanka.
\v 5 Zan yi bin-bini akan martabar ɗaukakarka da kuma ayyukanka masu ban mamaki.
\s5
\v 6 Zasu yi magana akan ikon manya-manyan ayyukanka, ni kuwa zan yi shelar girmanka.
\v 7 Zasu yi shelar ayyukanka nagari masu yawa, kuma zasu raira yabo akan adalcinka.
\s5
\v 8 Yahweh mai alheri ne kuma mai jinƙai ne, mai jinkirin fushi amincinsa kuma cikin alƙawari ba iyaka.
\v 9 Yahweh yana yi wa kowa kirki; jinƙansa na bisa dukkan aikin hannunsa.
\s5
\v 10 Dukkan abubuwan da kayi zasu yi maka godiya, Yahweh; amintattunka zasu sa maka albarka.
\v 11 Amintattunka zasu yi magana akan darajar mulkinka, zasu faɗi ikonka.
\v 12 Zasu sanar da 'yan adam ayyukan Allah masu girma da kuma ɗaukakar darajar mulkinka.
\s5
\v 13 Mulkinka, dawwamammen mulki ne, masarautarka ta dawwama har tsararraki dukka.
\s5
\v 14 Yahweh yakan tallafa wa dukkan waɗanda suke faɗuwa ya kuma tãda dukkan waɗanda ke a wulaƙance.
\v 15 Idanun kowa na jiranka; ka kan basu abincinsu a madai-daicin lokaci.
\v 16 Ka kan buɗe hannuwanka ka biya buƙatun kowanne abu mai rai.
\s5
\v 17 Yahweh mai adalci ne a dukkan tafarkunsa mai alheri ne a dukkan abin da ya ke yi.
\v 18 Yahweh na kusa da dukkan waɗanda suke kira gareshi, ga dukkan waɗanda suke kiransa da amincewa.
\v 19 Yana biyan buƙatun waɗanda suke girmama shi; yana jin kukansu sai kuma ya cece su.
\s5
\v 20 Yahweh yana lura da dukkan waɗanda ke ƙaunarsa, amma zai hallaka duk mugaye.
\v 21 Bakina zai furta yabon Yahweh; bari duk 'yan adam su albarkaci sunansa mai tsarki har abada abadin.
\s5
\c 146
\cl Zabura 146
\p
\v 1 Ka yabi Yahweh, Yabi Yahweh, ya raina.
\v 2 Ina ba da yabo ga Yahweh a dukkan rayuwata; Zan raira yabo ga Allahna muddin ina raye.
\s5
\v 3 Kada ka dogara ga sarakuna ko ga ɗan adam, waɗanda babu ceto gare su.
\v 4 Sa'ad da ran mutum ya dena numfashi, sai ya koma turɓaya; a ranan nan shawarwarinsa zasu watse.
\s5
\v 5 Mai albarka ne wanda mataimakinsa Allahn Yakubu ne, wanda begensa na cikin Yahweh Allahnsa.
\v 6 Yahweh ne yayi sama da ƙasa, da teku, da dukkan abubuwan dake cikinsu; yana kiyaye gaskiya har abada.
\s5
\v 7 Yana zartar da hukunci domin dukkan waɗanda ake zalumta kuma yana bada abinci ga mayunwata. Yahweh yakan 'yantar da ɗaurarru;
\v 8 Yahweh yana ba makafi ganin gari; Yahweh yana tãda waɗanda an tanƙwaresu; Yahweh yana ƙaunar mutane masu aikata adalci.
\s5
\v 9 Yahweh yana kãre bãƙin dake cikin ƙasa; yana agajin marayu da gwauraye, amma yana tsayayya da mugaye.
\v 10 Yahweh zai yi mulki har abada, Allahnki, Sihiyona, domin dukkan tsararraki. Mu yabi Yahweh.
\s5
\c 147
\cl Zabura 147
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh gama yana da kyau a raira yabo ga Allahnmu, yana da daɗi, ya dace a yi yabo.
\s5
\v 2 Yahweh zai sake gina Yerusalem, zai sake tattaro warwatsatsun mutanen Isra'ila.
\v 3 Yana warkar da masu karyayyar zuciya ya ɗaure raunukansu.
\s5
\v 4 Yana ƙididdiga taurari, ya ba dukkansu sunaye.
\v 5 Mai girma ne Ubangijinmu mai daraja a iko, saninsa ya zarce gaban aunawa.
\s5
\v 6 Yahweh yana tãda waɗanda aka wulaƙantasu, yakan jawo miyagu ƙasa.
\v 7 Ku raira waƙa ga Yahweh tare da godiya, mu raira yabbai ga Allahnmu da garaya.
\s5
\v 8 Yakan rufe sammai da gizagizai ya shirya ruwan sama domin ƙasa, ya sa ciyayi su tsiro bisa duwatsu.
\v 9 Yana ba dabbobi abincinsu da kuma 'ya'yan hankaki lokacinda suka yi kuka.
\s5
\v 10 Ba ya jin daɗin ƙarfin doki, ba ya dogara ga ƙarfin mutum.
\v 11 Yahweh yana jin daɗin waɗanda suke girmama shi, waɗanda suka kafa begensu akan amintaccen alƙawarinsa.
\s5
\v 12 Ku yabi Yahweh, Yerusalem, ki yabi Allahnki, Sihiyona.
\v 13 Gama yana ƙarfafa ƙarafun ƙofofinki, yana albarkatar 'ya'yanki a cikinku.
\v 14 Yana kawo wadata cikin iyakar ƙasarki, yana ƙosar dake da kyakkyawar alkama.
\s5
\v 15 Yana aika dokokinsa cikin duniya, dokokinsa yakan sheƙa da gudu.
\v 16 Yakan yin ƙanƙara kamar ulu, ya baza dusarta kamar toka.
\s5
\v 17 Yakan aiko da ƙanƙara kamar 'yan gutsittsire, wa zai iya jure sanyin da ya ke aikowa?
\v 18 Ya aika dokokinsa ya narkar dasu, yakan sa iska ta buga su sai ruwan ya kwarara.
\s5
\v 19 Ya yi shelar maganarsa ga Yakubu, farillansa da dokokinsa masu adalci ga Isra'ila.
\v 20 Bai taɓa yin haka ba da wata al'umma, game da dokokinsa ma, basu san su ba. Mu yabi Yahweh.
\s5
\c 148
\cl Zabura 148
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi Yahweh, ku dake cikin sammai; ku yabe shi, ku dake can tuddan sama.
\v 2 Ku yabe shi, dukkanku mala'ikunsa; ku yabe shi, dukkan rundunarsa.
\s5
\v 3 Ku yabe shi, rana da wata; ku yabe shi, dukkanku taurari masu ƙyalli.
\v 4 Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi daku ruwayen dake sama da sarari.
\s5
\v 5 Bari su yabi sunan Yahweh, gama ya bada umarnj, sai aka hallicesu.
\v 6 Ya kuma kafasu har abada abadin; ya zartar da doka da bazata taɓa canzawa ba.
\s5
\v 7 Ku yabe shi daga duniya, ku dodannin ruwa, da dukkan zurfafan teku,
\v 8 wuta da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da giza-gizai, iskar hadari masu biyayya da maganarsa.
\s5
\v 9 Ku yabe shi, duwatsu, da dukkan tuddai, itatuwa masu bada 'ya'ya, da duk itatuwan sida,
\v 10 namun jeji da na gida, hallitu masu rarrafe da tsuntsaye.
\s5
\v 11 Ku yabi Yahweh, sarakunan duniya da dukkan al'ummai, hakimai da dukkan masu mulki a duniya,
\v 12 samari da 'yan mata, dattawa da yara.
\s5
\v 13 Bari dukkansu su yabi sunan Yahweh, gama sunansa kaɗai aka fiffita, ɗaukakarsa kuma ta mamaye duniya da sammai.
\v 14 Ya ɗaga ƙahon mutanensa domin yabo daga dukkan amintattunsa Isra'ilawa. Mutanen dake kurkusa da shi. Ku yabi Yahweh.
\s5
\c 149
\cl Zabura 149
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Ku raira wa Yahweh sabuwar waƙa; ku raira yabonsa cikin taron amintattunsa.
\s5
\v 2 Bari Isra'ila su yi murna cikin wannan daya yi su; bari mutanen Sihiyona su yi murna da sarkin sarkinsu.
\v 3 Bari su yabi sunansa suna rawa; bari su raira masa yabo da bandiri da molo.
\s5
\v 4 Gama Yahweh yana jin daɗin mutanensa; yana ɗaukaka masu tawali'u da cetonsa.
\v 5 Bari masu tsoronsa su yi murna cikin nasara; bari su yi waƙa don murna bisa gadajensu.
\s5
\v 6 Bari yabon Allah ya kasance a bakinsu da takkuba masu kaifi biyu a hannunsu
\v 7 domin su maida martani kan al'ummai da ayyukan hukunci akan mutane.
\s5
\v 8 Zasu ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi shugabanninsu kuma da baƙin ƙarfe.
\v 9 Zasu aiwata hukunci da aka rubuta. Wannan ne zai zama ɗaukaka domin dukkan amintattunsa. Ku yabi Yahweh.
\s5
\c 150
\cl Zabura 150
\p
\v 1 Ku yabi Yahweh. Ku yabi Allah cikin wurinsa mai tsarki; ku yabi ƙarfinsa cikin sammai.
\v 2 Ku yabe shi saboda manyan ayyukansa; ku yabe shi saboda fiffikon girmansa.
\s5
\v 3 Ku yabe shi da ƙarar ƙaho; ku yabe shi da garayu da molaye.
\v 4 Ku yabe shi da bandiri da rawa; ku yabe shi da garayu da sarewa.
\v 5 Ku yabe shi da kuge masu ƙara; ku yabe shi da kuge masu amo.
\s5
\v 6 Bari dukkan abin dake da numfashi su yabi Yahweh. Ku yabi Yahweh.