ha_ulb/18-JOB.usfm

2072 lines
103 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id JOB
\ide UTF-8
\h Littafin Ayuba
\toc1 Littafin Ayuba
\toc2 Littafin Ayuba
\toc3 job
\mt Littafin Ayuba
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Akwai wani mutum a ƙasar Uz mai suna Ayuba; Ayuba kuwa marar laifi ne mai gaskiya, wanda ke tsoron Yahweh ya kuma juya wa mugunta baya.
\v 2 A ka haifa masa 'ya'ya bakwai maza da 'yammata uku.
\v 3 Ya mallaki tumaki dubu bakwai da raƙuma dubu uku da bijimai ɗari biyar da jakai ɗari biyar da kuma bayi masu yawan gaske. Shi ne ya fi girma a cikin dukkan mutanen Gabas.
\s5
\v 4 An keɓe rana domin kowanne ɗă, ya yi liyafa a cikin gidansa. Sukan aika a kira 'yan'uwansu mata su uku su ci su sha tare da su.
\v 5 Sa'ad da kwanakin liyafar suka ƙare, sai Ayuba ya aika su zo ya tsarkake su. Ya kan tashi da sassafe ya miƙa baye--baye na ƙonawa domin kowanne ɗaya a cikin 'ya'yansa, gama ya kan ce, "Ya yiwu yarana sun yi zunubi sun yi saɓon Yahweh a cikin zukatansu." Haka Ayuba yakan yi kullun.
\s5
\v 6 A ranar da 'ya'yan Allah maza suka zo domin su bayyana kansu a gaban Yahweh. Sai Shaiɗan ma ya biyo su. Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Daga ina ka zo?"
\v 7 Sai Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Daga garari cikin duniya da zirga--zirga a cikinta."
\v 8 Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Ka kuwa lura da Ayuba bawana? Gama babu kamar sa a duniya, marar laifi ne kuma mutum ne mai gaskiya yana tsoron Yahweh ya juya wa mugunta baya.
\s5
\v 9 Sa'annan Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Haka nan Ayuba ya ke tsoron Allah ba dalili?
\v 10 Ba ka kare shi ta kowanne gefe ba, shi da gidansa da dukkan abin da ya ke da shi? K a sawa ayyukan hannuwansa albarka da shanunsa sun yaɗu da yawa a cikin ƙasa.
\v 11 Amma yanzu ka miƙa hannunka ka taɓa abin da ya ke da shi dukka, ka gani idan bai la'ance ka kana gani ba."
\v 12 Sai Yahweh yace da Shaiɗan, "Duba, dukkan abin da ya ke da shi na hannunka." Sai dai a kansa ne kaɗai ba zaka sa hannunka ba." Sa'annan Shaiɗan ya fita daga wurin Yahweh.
\s5
\v 13 Sai ya zama a wata rana, 'ya'yansa maza da mata suna ci suna shan ruwan inabi a gidan babban wansu.
\v 14 Wani ɗan aike ya zo wurin Ayuba yace, "Bijimai suna huɗa jakai kuma suna kiwo a gefensu.
\v 15 Sai Sabiyawa suka auko ba zato suka kwashe su. Bayin kuma sun kashe su da kaifin takobi. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka."
\s5
\v 16 Yana cikin yin magana, sai wani kuma ya zo ya ce, "Wutar Allah ta sauko daga sama ta cinye tumaki duk da bayin. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka."
\v 17 Yana cikin yin magana, sai wani kuma ya zo ya ce, "Kaldiyawa sun zo a ƙungiyoyi uku, sun kawo hari a kan raƙuman sun kwashe su. Sun kuma kashe bayin da kaifin takobi. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka."
\s5
\v 18 Yana cikin yin magana, wani kuma ya zo ya ce, "Ya'yanka maza da matan suna ci suna sha a gidan babban wansu.
\v 19 Sai wata iska mai ƙarfi ta taso daga cikin jeji ta buge kusurwoyin gidan guda huɗu. Gidan ya faɗa a kan matasan, kuma sun mutu. Ni kaɗai ne na tsira don in gaya maka."
\s5
\v 20 Sai Ayuba ya tashi, ya keta tufafinsa, ya aske kansa, ya faɗi da fuskarsa a ƙasa, ya yi wa Yahweh sujada.
\v 21 Ya ce, "Sa'ad da na fito daga cikin mahaifiyata tsirara nake, kuma tsirara zan koma can. Yahweh ne ya bayar, Yahweh ne kuma ya ɗauke. Bari sunan Yahweh ya zama mai albarka."
\v 22 A cikin wannan lamari dukka, Ayuba bai yi zunubi ba, bai kuma yi zargi ga Allah kan ya yi kuskure ba.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Wata rana kuma da 'ya'yan Allah maza suka zo su baiyana kansu a gaban Yahweh. Shaiɗan ma ya biyo su don ya baiyana kansa a gaban Yahweh.
\v 2 Yahweh yace da Shaiɗan, "Daga ina ka zo?" Sai Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Daga garari cikin duniya da kai da kawowa a kanta."
\s5
\v 3 Yahweh yace da Shaiɗan, "Ka lura da bawana Ayuba? Gama babu kamar sa a duniya, marar laifi ne, mutum ne mai gaskiya, yana juya wa mugunta baya. Har yanzu yana nan riƙe da nagartarsa, duk da yake ka sa in yi gãba da shi, don in hallaka shi babu wani dalili."
\s5
\v 4 Shaiɗan ya amsawa Yahweh yace, "Jiki magayi, tabbas mutum zai iya rabuwa da dukkan abin da yake da shi domin ya ceci ransa.
\v 5 Amma ka miƙa hannunka yanzu ka taɓa ƙasusuwansa da jikinsa, ka gani idan bai la'ance ka kana gani ba."
\v 6 Yahweh yace da Shaiɗan, "Ga shi, yana hannunka; ransa ne kaɗai ba zaka taɓa ba."
\s5
\v 7 Daga nan sai Shaiɗan ya tafi daga gaban Yahweh. Ya bugi Ayuba da marurai tun daga tafin ƙafarsa har zuwa kansa.
\v 8 Ayuba ya ɗauki ɓallin kasko yana susa da shi, kuma ya zauna a cikin tsakiyar toka.
\s5
\v 9 Sai matarsa tace da shi, "Har yanzu kana nan riƙe da nagartarka? Ka la'anci Allah ka mutu."
\v 10 Amma ya ce da ita, "Kina yin magana kamar yadda gaɓuwar mace ke yi. Za mu karɓi abu mai kyau daga wurin Allah mu ƙi karɓar marar kyau"? A cikin wannan lamari dukka, Ayuba bai yi zunubi da leɓunansa ba.
\s5
\v 11 A na nan, sa'ad da abokan Ayuba uku suka ji dukkan wannan bala'in da ya same shi, kowannen su ya tawo daga garinsa: Elifaz Batemane da Bildad Bashune da Zofar Banamate. Suka sa lokaci domin suzo su makoki tare da shi su kuma ta'azantar da shi.
\s5
\v 12 Sa'ad da suka hango daga nesa, basu iya gane shi ba. Suka tada muryoyinsu suka yi kuka; kowannen su ya keta tufafinsa ya watsa ƙura a sama dakuma bisa kansa.
\v 13 Sa'an nan suka zauna a ƙasa tare da shi a ƙasa har yini uku da dare uku. Ba wanda ya yi masa magana, gama sun ga yana da baƙin ciki mai yawa.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Bayan wannan, Ayuba ya buɗe bakinsa ya la'anci ranar da aka haife shi.
\v 2 Ya ce:
\v 3 "Bari ranar da a ka haife ni ta lalace, kuma da daren aka ce, 'an ɗauki cikin yaro.'
\s5
\v 4 Bari ranar ta zama baƙa; Dãma kada Yahweh ya tuna da ita daga sama, kada ma rana ta yi haske a kanta.
\v 5 Dãma duhu da inuwar kwarin mutuwa su maishe ta tasu. Dãma girgije ya tsaya a kan ta, dãma kowanne abu mai sa rana ta yi baƙi ya ba ta tsoro da gaske.
\s5
\v 6 Wannan daren kuma, dãma baƙin duhu ya rufe shi. Dãma kada ta yi farinciki a ranakun shekara; dãma kada a lissafa ta cikin kwanakin watanni.
\v 7 Duba, dãma wannan dare ya zama wofi; kada muryar farinciki ta zo cikinsa.
\s5
\v 8 Dãma su la'anci wannan rana, waɗanda suka san yadda a ke tashin Lebiyatan.
\v 9 Dãma taurarin wayewar giri na wannan rana su yi duhu. Dãma wannan rana ta nemi haske, amma ta rasa; dãma kada ta ga ƙyallin wayewar gari,
\v 10 saboda bata rufe ƙofofin cikin uwata ba, kuma domin bata ɓoye masifa daga idanuna ba.
\s5
\v 11 Me yasa ban mutu sa'ad da na fito daga ciki ba? Me yasa ban saki ruhuna sa'ad da uwata ta haife ni ba?
\v 12 Me yasa gwiwoyinta suka marabce ni? Me yasa nonanta suka yarda na shã su?
\s5
\v 13 Gama da yanzu ina kwance shiru. Da ina barci ina hutawa
\v 14 tare da sarakuna da mashawartan duniya, waɗanda suka gina wa kansu kaburbura kuma yanzu sun ruɓe.
\s5
\v 15 Ko kuwa da yanzu ina kwance tare da sarakuna waɗanda dã suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.
\v 16 Ko kuwa ƙila da an yi ɓari na, kamar jariran da basu taɓa ganin haske ba.
\s5
\v 17 A can masu mugunta sun huta da masifa; a can masu gajjiya suna cikin hutu.
\v 18 A can 'yan kurkuku sun sami saki tare; bãsu jin muryar masu kora bayi.
\v 19 Manya da ƙananan mutane suna can; bawa yana da 'yanci daga wurin ubangijinsa a can.
\s5
\v 20 Me yasa ake ba wanda ke cikin ƙunci haske? Me yasa a ke ba wanda ke da baƙin ciki rai,
\v 21 wanda ya ƙagara yaga mutuwa bata zo ba, ga wanda yake neman mutuwa kamar ɓoyayyiyar dukiya?
\v 22 Me yasa a ke bada haske ga wanda yake farinciki ƙwarai da murna idan ya sami kabari?
\s5
\v 23 Me yasa a ke ba mutum wanda hanyarsa take a ɓoye haske, mutum wanda Allah ya kulle shi?
\v 24 Gama ajjiyar zuciya nake yi maimakon cin abinci; an zubar da gurnanina kamar ruwa.
\s5
\v 25 Gama abin da na ji tsoro ya zo kaina; abin dana tsorata yazo mani.
\v 26 Ba sauƙi a gare ni, ban yi shuru ba, kuma ban huta ba; maimakon haka masifa ce take zuwa."
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Sai Elifaz Batemane ya amsa ya ce,
\v 2 Idan wani yayi ƙoƙari ya yi magana da kai, baza ka yi haƙuri ba? Amma wa zai iya hana kansa yin magana?
\v 3 Ka ga, ka koyawa mutane da yawa; ka ƙarfafa raunanan hannuwa.
\s5
\v 4 Kalmominka sun tallafi wanda yake faɗuwa; ka sa raunanan gwiwoyi sun yi ƙarfi.
\v 5 Amma yanzu masifa ta zo kanka, kuma ka gaji; ta taɓa ka, kuma ka kaɗu.
\v 6 Tsoronka bai zama ƙarfi a gare ka ba, ammincinka bai ishe ka bege ba?
\s5
\v 7 In ka yarda yi tunanin game da wannan: Wanda ba shi da laifi ya taɓa lalacewa? Ko a ina aka taɓa datse masu adalci?
\v 8 Bisa ga abin da na gani, waɗanda suka huɗa mugunta suka shuka masifa su ke girbin ta.
\v 9 Sukan lalace ta wurin numfashi Yahweh; zafin fushinsa ya kan cinye su.
\s5
\v 10 Rurin zaki, muryar zaki mai ban tsoro, haƙoran 'yan zakuna --sukan karye.
\v 11 Tsohon zaki yakan lalace idan ba abin da zai kama; 'ya'yan zakanya sukan warwatsu ko'ina.
\s5
\v 12 An kawo mani wata matsala a asirce, kunnena ya karɓi raɗa game da ita.
\v 13 Sa'annan tunanin ruya ya zo mani cikin dare, sa'adda barci mai nauyi ya zo kan mutane.
\s5
\v 14 A cikin dare tsoro da fargaba suka zo mani, dukkan ƙasusuwana suka motsa.
\v 15 Sai wani ruhu ya wuce a gaban fuskata, gashin jikina ya tashi tsaye.
\s5
\v 16 Ruhun ya tsaya cik, amma ban iya gane baiyanuwarsa ba. Wani abu ya rufe idanuna; an yi shiru, sai na ji wata murya tace,
\v 17 "Mutum mai mutuwa ya iya fin Allah adalci? Mutum zai iya fin mahallicinsa tsarki?
\s5
\v 18 Ka gani, idan Yahweh bai amince da bayinsa ba; idan ya zargi mala'ikunsa da wawanci,
\v 19 yaya ga waɗanda ke zama a cikin gidaje na yumɓu, waɗanda tushensu yana cikin ƙasa, waɗanda a kan mutsuke su nan da nan fiye da ƙwaro.
\s5
\v 20 Tsakanin safiya zuwa yamma an hallaka su; sun lalace har abada ba abin da zai sa a tuna da su.
\v 21 Ba a kan tsinke iggiyar ransu a jikinsu ba? Su mutu; su mutu ba tare da hikima ba.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Ka yi kira yanzu; akwai wani mai ansa maka? Ga wanne cikin masu tsarkin zaka juya?
\v 2 Gama fushi ya kan kashe wawan mutum; kishi yakan kashe dolo.
\v 3 Na ga wawan mutum yana kahuwa, amma nan take na la'anci gidansa.
\s5
\v 4 Zaman lafiya yana nesa da 'ya'yansa; an murƙushe su a ƙofar birni. Ba wanda zai kuɓutar da su.
\v 5 Mayunwaci ya kan cinye anfaninsa dukka; sukan ma ɗauko shi daga cikin ƙayayuwa. Masu jin ƙishi suna hãki domin dukiyarsu.
\s5
\v 6 Gama wahala bata fitowa daga cikin turɓaya; masifa kuma bata fitowa daga cikin ƙasa.
\v 7 Maimakon haka an haifi mutum saboda masifa, kamar yadda tartsatsi yakan tashi sama.
\s5
\v 8 Amma a gare ni, zan juya wajen Allah shi da kansa; a gare shi zan danƙa al'amurana--
\v 9 shi wanda ke yin manyan al'amuran da ba a iya ganewa, abubuwan mamakin da basu lissaftuwa.
\v 10 Yakan bada ruwa a kan ƙasa, yakan aika da ruwa bisa filaye.
\s5
\v 11 Yakan yi haka ne domin ya tada ƙasƙantattu; yasa masu baƙin ciki su zauna lafiya.
\v 12 Yakan lalata shirye--shiryen masu yaudara, domin kada su kai ga cika manufarsu.
\v 13 Yakan kama mutane masu wayo cikin aikin yaudararsu; da sauri shirye--shiryen masu murɗiya sukan zo ƙarshe.
\s5
\v 14 Dare kan same su da rana, sukan yi lalube da rana sai kace dare ne.
\v 15 Amma ya kan ceci mutum matalauci da takobi cikin bakinsu mabukata kuma daga hannun ƙarfafan mutane.
\v 16 Domin mutum matalauci ya sami bege, rashin adalci kuma ya rufe bakinsa.
\s5
\v 17 Duba, mai albarka ne mutumin da Allah yakan hore shi; saboda haka kada ka rena horon Mai Iko Dukka.
\v 18 Gama yakan sa a ji ciwo yayi magani, ya kan sa a ji rauni hannunsa kuma ya warkar.
\v 19 Zai kuɓutar da kai daga masifu shida; hakika, a cikin masifu bakwai, babu muguntar da zata taɓa ka.
\s5
\v 20 A cikin yunwa zai fanshe ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma daga hannun takobi.
\v 21 Za a ɓoye ka daga la'anar harshe; ba zaka ji tsoron hallaka ba ko ta zo.
\v 22 Zaka yi dariya a kan hallakar yunwa, ba zaka ji tsoron namun jeji na duniya ba.
\s5
\v 23 Gama zaka yi alƙawari da duwatsu a gonarka, namun jeji na gona zasu yi zaman lafiya da kai.
\v 24 Zaka sani rumfarka tana lafiya; zaka ziyarci garken tumakinka ba kuwa zaka rasa kome ba.
\v 25 Zaka kuma sani irinka zai yi girma, tsatsonka zasu zama kamar ciyawa a kan ƙasa.
\s5
\v 26 Zaka je kabari da tsufanka, kamar zangarkun damin hatsi da suke tafiya a lokacinsa.
\v 27 Ka gani, mun yi binciken wannan lamari; ga kamanninsa, ka saurare shi, ka san shi kai da kanka."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Sa'an nan Ayuba ya amsa ya ce,
\v 2 "Oh, da dai an auna nauyinbaƙin cikina; da dai an sa wahalata a ma'auni!
\v 3 Gama yanzu za tafi yashin tekuna nauyi. Shi yasa nake magana barkatai.
\s5
\v 4 Gama kibawun Mai Iko Dukka suna cikina, ruhuna yana shan dafin; razana daga Yahweh ta shiryo kanta gãba da ni.
\v 5 Jakin jeji yakan yi hargowa inda yana da ciyawa? Sã yakan yi kuka ga abinci a gabansa?
\v 6 Za a iya cin abin da ba shi da ɗanɗano ba tare da an sa masa gishiri ba? Ko akwai ɗanɗano ga farin ƙwai?
\s5
\v 7 Na ƙi taɓa su; suna kama da abinci mai gundura a gare ni.
\v 8 Oh, dãmã za a amsa mani roƙona; oh, dãma Yahweh zai yarda in sami abin da nake ta nema in samu:
\v 9 dãma Yahweh zai yarda ya ruƙurƙushe ni kawai, dã zai saki hannunsa ya datse ni daga wannan rayuwa!
\s5
\v 10 Bari wannan ya zama abin ƙarfafa ni--ko da ciwona ya ƙaru bai ragu ba: ban yi musun maganar mai tsarki ba.
\v 11 Menene ƙarfina, da zan yi ƙoƙarin jira? mene ne ƙarshena, da zan ci gaba da rayuwa?
\s5
\v 12 Ƙarfina kamar ƙarfin dutse yake? Ko an yi jikina da tagulla ne?
\v 13 Ba gaskiya ba ne cewa ba ni da taimako a cikin kaina ba, kuma an kori hikima daga cikina?
\s5
\v 14 Mutumin da ya kusa suma, ya kamata abokansa su ji tausayinsa; ko da ya watsar da jin tsoron Mai Iko Dukka.
\v 15 Amma 'yan'uwana sun zama da aminci kamar hamadar da kan ƙafe, kamar magudanar ruwa marar anfani da ke wucewa a magudanai,
\v 16 waɗanda sukan yi duhu saboda ƙanƙara ta rufe su, kuma saboda dusar ƙanƙara da ta ke a cikin su.
\v 17 Idan su ka ji ɗumi sai su, sai su ɓace; idan zafi ya zo, sai su narke a inda suke.
\s5
\v 18 Fataken da ke bi ta wurinsu sukan ruƙa neman ruwa; sukan yi garari a busasshiyar ƙasa su lalace.
\v 19 Fatake daga Tema sun duba can, fatake daga Sheba sun sa bege a cikin su.
\v 20 Sun kunyata saboda sun gaskata zasu sami ruwa. Sun je wurin, amma an ruɗe su.
\s5
\v 21 Gama yanzu ku abokai baku da anfani a gare ni; kun ga takaicin da nake ciki kun ji tsoro.
\v 22 Nace da ku, 'ku bani wani abu ne?' Ko ku bani wani abu daga dukiyarku?'
\v 23 Ko ku cece ni daga hannun maƙiyina?' Ko ku fanshe ni daga hannun mai tsananta mani?'
\s5
\v 24 Ku koya mani, ni kuwa zan yi shiru; ku ganar da ni inda ban yi dai-dai ba.
\v 25 Gaskiya dai ɗaci gare ta! A ina gardandaminku suka ga laifina?
\s5
\v 26 Kun yi shirin ku watsar da maganata, ku ɗauki maganar mutumin da yake cikin wahala kamar iska?
\v 27 Tabbas, kun jefa ƙuri'a a kan ɗan da bashi da uba, kun mai da aboki abin samun riba.
\s5
\v 28 To, yanzu, idan kun yarda ku dube ni, gama tabbas ba zan yi ƙarya a gaban kuba ba.
\v 29 Ku dena magana haka, na roƙe ku; kada kuyi rashin gaskiya; hakika ne, ku dena yin haka, hakika ina da gaskiya a al'amarina.
\v 30 Akwai mugunta a kan harshena ne? Bakina ba zai iya ganewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Ba wani mutum da ya taɓa yin aiki mai wuya ne a duniya?
\v 2 Ashe kwanakinsa ba kamar na ɗan ƙwadago suke ba? Kamar bawan da ya ƙosa yamma ta yi, kamar ɗan ƙwadago mai neman haƙƙoƙinsa -
\v 3 don haka an sa ni in jure da watannin wahala; An ba ni kwanaki cike da wahala.
\s5
\v 4 Sa'ad da na kwanta, sai in ce da kaina, 'Yaushe zan tashi kuma yaushe gari zai waye? Ina ta juye-juye har sai gari ya waye.
\v 5 Jikina yana cike da tsutsotsi da sanyin ƙasa; gyambunan jikina sukan bushe sai kuma su fashe su zama sababbi.
\s5
\v 6 Kwanakina sun fi kibiya sauri; sukan wuce ba bege.
\v 7 Allah ya tuna raina numfashi ne kawai; idona ba zai ƙara ganin alheri ba.
\s5
\v 8 Idon Yahweh, da ke gani na, ba zai ƙara gani na ba; idanun Yahweh za su dube ni, amma ba zan kasance ba.
\v 9 Kamar yadda girgije yakan ɓace, haka wanda ya je Lahira ba zai ƙara fitowa ba.
\v 10 Ba zai ƙara dawowa gidansa ba.; wurinsa ba zai ƙara sanin sa ba.
\s5
\v 11 Saboda haka ba zan kama bakina ba; zan yi magana cikin zafin rai a ruhuna; zan yi gunaguni cikin ɗacin raina.
\v 12 Ni teku ce ko ni dorina ce da kuke tsaro na?
\s5
\v 13 Idan nace, 'gadona zai yi mani ta'aziya, shimfiɗata zata sa in ji sauƙi,'
\v 14 sai ka firgita ni da mafarkai ka sa in ji tsoro da wahayoyi,
\v 15 har na kan so a maƙare ni in mutu da a raya ƙasusuwana.
\s5
\v 16 Na rena rayuwata; bana marmarin in rayu koyaushe; ku ƙyale ni gama kwanakina basu da anfani.
\v 17 Mene ne mutum har da zaka lura da shi, da zaka sa hankalinka a kan sa,
\v 18 da zaka lura da shi kowacce safiya ka gwada shi kowanne lokaci?
\s5
\v 19 Sai yaushe zaka dena dube na, kafin ka bar ni ni kaɗai in samu in haɗiyi yawuna?
\v 20 Ko dana yi zunubi, me zaka yi da ni, kai da kake tsaron mutane? Me yasa ka sã mani ido, har da zan zama matsala a gare ka?
\s5
\v 21 Me yasa ba zaka yafe laifofina ka ɗauke muguntata ba? Gama yanzu zan kwanta a cikin turɓaya; zaka neme ni a hankali, amma ba zan kasance ba."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Sa'an nan Bildad Bashune ya amsa ya ce,
\v 2 "Har yaushe zaka yi ta faɗin waɗannan abubuwa? Har yaushe maganar bakinka zata zama iska mai ƙarfi?
\v 3 Ko Allah yana ɓata shari'a ne? Ko Mai Iko Dukka yana ɓata adalci ne?
\s5
\v 4 'Ya'yanka sun yi masa zunubi; mun san wannan, gama ya bashe su a hannun zunubansu.
\v 5 Dama ace ka jure da neman Allah da miƙa roƙonka ga Mai iko dukka.
\s5
\v 6 Idan da kana da tsarki da aminci, to da babu shakka da ya tashi da kansa a madadin ka ya dawo da kai inda ya kamace ka.
\v 7 Ko da yake ka farkonka kaɗan ne, har yanzu matsayin ƙarshenka ya fishi girma ƙwarai.
\s5
\v 8 Idan ka yarda ka tambayi mutanen dã, ka mai da hankali a kan abin da ubanninmu suka koya.
\v 9 (Jiya a ka haife mu kuma bamu san kome ba saboda kwanankinmu a duniya inuwa ne).
\v 10 Baza su gaya maka ko su koya maka ba? Baza su yi magana daga zuciyarsu ba?
\s5
\v 11 Tsire-tsire kan iya yin girma inda ba laima? Iwa ta iya yin girma ba tare da ruwa ba?
\v 12 Tun suna da korensu ba tare da an sare su ba, zasu riga kowacce shuka bushewa.
\s5
\v 13 Haka kuma hanyoyin dukkan wanda ya mance da Allah; begen wanda bashi da halin kirki zai lalace.
\v 14 Gabagaɗinsa zai lalace, bangaskiyarsa bata da ƙarfi kamar yanar gizo take.
\v 15 Ya dogara ga gidansa, amma ba zai tallafe shi ba; ya riƙe shi, amma bai tsaya ba.
\s5
\v 16 A ƙarƙashin rana kore ne shi, rassansa sukan rufe lambunsa dukka.
\v 17 Tarin duwatsu sun rufe sauyoyinsa, sukan nemi wurare masu kyau cikin duwatsu.
\v 18 Amma idan aka hallaka wannan mutum daga wurinsa, sa'an nan wannan wurin zai yi musun sa yace, 'Ban taɓa ganin ka ba.'
\s5
\v 19 Duba, wannan ne "farinciki" na mutum mai irin wannan hali; waɗansu shuke--shuken zasu fito a wannan ƙasar a wurinsa.
\v 20 Duba, Allah ba ya jefar da mutum marar laifi; kuma ba ya kama hannuwan masu aikin mugunta.
\s5
\v 21 Zaya sake cika bakinka da dariya, leɓunanka kuma da sowa.
\v 22 Kunya zata rufe maƙiyanka; rumfar masu mugunta zata lalace har abada."
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Sa'an nan Ayuba ya amsa yace,
\v 2 "Gaskiya ne haka yake na sani. Amma yaya mutum zai iya zama dai-dai wurin Allah?
\v 3 Idan yana so yayi gardama da Allah, a cikin dubu ba zai iya amsawa ko sau ɗaya ba.
\s5
\v 4 Allah mai hikima ne kuma mai ƙarfi ne; wane ne ya taɓa yin jayayya da shi yaci nasara
\v 5 shi wanda yake cire duwatsu ba tare da gargaɗi ba yakan birkice kowannen su a cikin fushinsa--
\v 6 shi wanda yake girgiza duniya daga wurinta yasa ginshiƙanta su raurawa.
\s5
\v 7 Shi ne Allahn nan wanda yakan ce da rana kada ta fito, kuma ba ta fito ba, shi wanda ya kan lulluɓe taurari,
\v 8 shi wanda yakan miƙar da sammai da kansa ya tattaka raƙuman ruwan teku,
\v 9 shi wanda ƙungiyoyin taurari da zara da gamzaki da mafarauci da kare da zomo da kuma kaza da 'yayanta, gungun taurarin kudu.
\s5
\v 10 Shi wanda ke yin manyan abubuwan da ba za a iya bincika su ba, da abubuwan mamaki da basu lissaftuwa.
\v 11 Duba, yana tare da ni kuma bana ganin sa, kuma yakan wuce, amma bana ganin sa.
\v 12 Idan ya ɗauke wani abu, wa zai iya hana shi? Wane ne zai iya cewa da shi, 'Me kake yi?'
\s5
\v 13 Allah ba zai janye fushinsa ba; masu taimakon Rahab suna sunkuya wa a ƙarƙashinsa.
\v 14 Yaya zan iya amsa masa, zan iya zaɓar kalmomin da zan iya yin nazari tare da shi?
\v 15 Ko da ace ni mai adalci ne, ba zan iya amsa masa ba; sai dai in roƙi jinƙai kaɗai daga mai yi mani hukunci.
\s5
\v 16 Ko dana yi kira ya amsa mani, ba zan gaskata cewa yana sauraren muryata ba.
\v 17 Gama ya karairaya ni da iska mai ƙarfi ya ruɓanɓanya ciwukana ba dalili.
\v 18 Ya hana ni in ja numfashi kuma; ya cika ni da baƙinciki.
\s5
\v 19 Idan maganar ƙarfi ce, duba, shi mai iko ne! Idan maganar shari'a ce, wa zai iya sashi ya zo?
\v 20 Ko da ina da gaskiya, bakina zai kãshe ni; koda ba ni da abin zargi, maganata zata nuna ni mai laifi ne.
\s5
\v 21 Bani da abin zargi, amma ban damu da kaina ba ko kaɗan; na rena raina.
\v 22 Bai bambanta da komai ba da nace yakan hallaka marar abin zargi tare da mai mugunta.
\v 23 Idan bulala tayi kisa nan da nan, sai ya yi wa al'amuran marar laifi ba'a.
\v 24 An bayar da duniya a hannun masu mugunta; Yahweh ya rufe fuskokin alƙalanta. Idan bashi ba ne, to, wane ne?
\s5
\v 25 Kwanakina sun fi ɗan aike mai gudu sauri; kwanakina suna wucewa; basu ganin alheri a ko'ina.
\v 26 Suna da sauri kamar jiragen ruwan iwa, yana sauri kamar gaggafar da ta kawo bãra a kan nama.
\s5
\v 27 Idan nace zan mance da koke--kokena, zan dena baƙinciki in yi murna,
\v 28 sai in ji tsoron dukkan wahalhaluna saboda na sani kai ba zaka dube ni a matsayin marar laifi ba.
\v 29 Tun da za a kashe ni, me kenan, zan yi ƙoƙari a wofi?
\s5
\v 30 Idan na yi wanka da ruwan ƙanƙara nasa hannuwana suka yi tsafta sosai,
\v 31 Allah zai tura ni a kwari mai taɓo, tufafina zasu zama abin ƙyama tare da ni.
\s5
\v 32 Gama Allah ba mutum ba ne, kamar yadda nake, balle in ba shi amsa, har da zamu zo kotu tare da shi.
\v 33 Ba wani alƙali a tsakanin mu wanda zai sa mana hannu mu dukka biyu.
\s5
\v 34 Ba wani alƙalin da zai iya ɗauke sandan Allah daga kaina, wanda ya hana tsoronsa ya firgitar da ni.
\v 35 Sa'an nan ba zan yi magana in ji tsoronsa ba. Amma ga yadda abubuwa suke yanzu, ba zan iya yin haka ba.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Na gaji da raina; zan yi maganar matsalata a fili; zan yi magana cikin ɗacin raina.
\v 2 Zan ce da Allah, 'Kada ka kashe ni haka kawai; ka nuna mani abin da kake zargi na a kai.
\v 3 Ya yi maka kyau ka wahalshe ni, ka rena aikin hannuwanka sa'ad da kake yin murmushi da shirye--shiryen masu mugunta.
\s5
\v 4 Ko kana da idanu na jiki ne? Kokana gani kamar mutum ne?
\v 5 Ko kwanakinka kamar na ɗan'adam ne ko shekarunka kamar na mutane ne,
\v 6 da kake yin bincike a kan muguntata kana neman zunubina,
\v 7 duk da ka san bani da laifi kuma ba wanda zai iya kuɓutar da ni daga hannunka?
\s5
\v 8 Hannuwanka ne suka sifanta ni suka tsara kome nawa, amma kana hallaka ni.
\v 9 Ina roƙon ka, ka tuna kai ne ka siffanta ni kamar yumɓu; zaka maishe ni cikin turɓaya ne kuma?
\s5
\v 10 Baka zubar da ni kamar madara ka cakuɗe ni kamar abin taunawa ba?
\v 11 Ka lulluɓe ni da fata da nama ka ɗinke ni da ƙasusuwa da guringuntsi.
\s5
\v 12 Ka bani rai da jiyejiyenƙai; taimakonka ya tsare ruhuna.
\v 13 Duk da haka ka ɓoye waɗannan abubuwaa zuciyarka--na san waɗannan abubuwan ne da kake tunaninsu:
\v 14 idan na yi zunubi zaka kula da shi; ba zaka baratar da ni daga muguntata ba.
\s5
\v 15 Idan na yi aikin mugunta, kaito na; ko da nayi aikin adalci, ba zan yi fahariya ba, da yake ina cike da kunya ka dubi wahalata!
\v 16 Idan na ɗaukaka kaina zaka bi ni kamar zaki; kuma zaka nuna kanka da ayyukan na ban mamaki na iko a kaina.
\s5
\v 17 Ka kawo mani sababbin shaidu ka ƙara fushinka a kaina; ka kawo mani hari da sababbin sojoji.
\s5
\v 18 To, me yasa ka fito da ni daga cikin ciki? Dama na saki ruhuna ba idon da ya gan ni.
\v 19 Dãma na zama kamar ban taɓa kasancewa ba; dama an ɗauke ni daga cikin ciki zuwa kabari.
\s5
\v 20 Kwanakina ba 'yan kaɗan ba ne? Tsaya haka, ka rabu da ni, domin in ɗan sami hutu
\v 21 kamin in kai inda ba zan iya dawowa ba, zuwa ƙasar duhu da inuwar mutuwa,
\v 22 ƙasa mai duhu kamar tsakiyar dare, ƙasa ta inuwar mutuwa, babu wata ka'ida, inda haske kamar tsakar dare yake.'"
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Sa'an nan Zofar Banamate ya amsa ya ce,
\v 2 "Ba za a bada amsa a kan waɗanan maganganun masu yawa ba? A gaskata da wannan mutumin, mai yawan magana?
\v 3 Fankamarka zata sa sauran mutane suyi shuru ne? Sa'ad da kayi ba'a, ba wanda zai sa ka ji kunya ne?
\s5
\v 4 Gama kace da Allah, 'Bangaskiyata sahihiya ce, bani da laifi a idanunka.'
\v 5 Amma, da Allah zai yi magana ya buɗe bakinsa gãba da kai;
\v 6 da zai nuna maka asirin hikima! Gama shi yana da fahimta mai girma. Ka sani ba kamar yadda muguntarka take Allah yake nema ba.
\s5
\v 7 Zaka iya ganewa da Allah ta wurin binciken sa? Zaka iya fahimtar Yahweh sarai?
\v 8 Matsalar tayi tsawo kamar samaniya ne; me zaka iya yi? Ta fi Lahira zurfi; me zaka iya sani?
\v 9 Ta fi duniya tsawo, kuma ta fi teku faɗi.
\s5
\v 10 Idan ya wuce ya kulle wani, ko idan ya hukunta wani, wane ne zai iya hana shi?
\v 11 Gama ya san maƙaryata; idan ya ga mugunta, baya lura da ita ne?
\v 12 Amma wawayen mutane basu ganewa; zasu same ta sa'ad da jakin jeji ya haifi ɗan mutum.
\s5
\v 13 Amma da ka tsayar da zuciyarka sosai ka miƙa hannuwanka zuwa ga Yahweh;
\v 14 da akwai mugunta a hannunka, amma daka kasa ta nesa da kai, da baka bari rashin adalci ya zauna a rumfarka ba.
\s5
\v 15 Da ka tada fuskarka ba tare da kunya ba; lallai da ka tsaya da ƙarfi ba tare da tsoro ba.
\v 16 Da ka manta da damuwarka; sai dai ka tuna da ita kamar wucewar ruwa.
\v 17 Da ranka yayi haske fiye da rana; ko da akwai duhu da ya zama kamar safiya.
\s5
\v 18 Da zaka natsu saboda akwai bege; lallai da ka sami tsaro kewaye da kai da ka huta a tsanake. Kuma da ka kwanta ka huta,
\v 19 Kuma ba wanda zai tsoratar da kai; lallai da mutane da yawa sun nemi tagomashi a wurin ka.
\s5
\v 20 Amma idanun masu mugunta zasu kasa; ba zasu sami wurin ɓuya ba; begensu numfashin ƙarshe ne kaɗai"
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sa'an nan Ayuba ya amsa ya ce,
\v 2 "Ba shakka ku ne mutanen; hikima za ta mutu tare da ku.
\v 3 Amma ni ma ina da fahimta kamar yadda kuma kuke da shi; ni ban gaza ku ba. Hakika, waye bai san irin abubuwa kamar waɗannan ba?
\s5
\v 4 Ni wani abu ne da makwabcina zai yiwa dariya - Ni, da nake kira bisa sunan Allah wanda ya kuma amsa mani! Ni, mutum mai adalci marar aibu kuma - yanzu na zama wani abin dariya.
\v 5 A tunanin wani wanda yake zaune lafiya, akwai reni game da masifa; yakan yi tunani irin na ƙara kawo masifa kan waɗanda ƙafafunsu ke zarmewa.
\v 6 Rumfunan mafasa na azurta, waɗanda kuma ke cakunar Allah suna nan lafiya; hannunwansu ne allolinsu.
\s5
\v 7 Amma yanzu ka tambayi dabbobi, kuma zasu koya maka; ka tambayi tsuntsayen sammai, zasu kuma gaya maka.
\v 8 Ko kuma kayi wa ƙasa magana, zata kuma koya maka; kifayen teku zasu shaida maka.
\s5
\v 9 Wace dabba ce cikin dukkan waɗannan da bata sani cewa hannun Yahweh ne yayi wannan ba?
\v 10 A cikin hannunsa ran kowanne rayayyen abu yake da kuma numfashin dukkan 'yan adam.
\s5
\v 11 Ashe kunne ba yakan gwada dukkan maganganu kamar yadda baki ke ɗanɗana abinci ba?
\v 12 Hikima tana ga tsoffin mutane; a tsawon kwanaki kuma akwai fahimta.
\s5
\v 13 Hikima da iko suna ga Allah; shi ke da shawara da fahimta.
\v 14 Duba, yakan rushe, ba za a kuma iya ginawa ba, idan ya kulle mutum, ba sauran kuɓutarwa.
\v 15 Duba, idan ya janye ruwaye, sai su bushe ƙurmus; kuma idan ya aika da su, sai su malale ƙasa.
\s5
\v 16 A gunsa ƙarfi da hikima suke; mutanen da aka ruɗe su da mai ruɗin dukkansu biyu suna cikin ikonsa.
\v 17 Yakan ɓad da mashawarta zuwa baƙinciki, ya mai da alƙalai wawaye.
\v 18 Yakan tuɓe rawanin iko daga sarakuna; ya ɗaura ɗan ƙyalle a kwankwasonsu.
\s5
\v 19 Yakan ɓad da firistoci su tafi ƙafa ba takalmi cikin baƙinciki ya kuma kaɓantar da manyan mutane.
\v 20 Yakan ɗauke iya maganar mutanen da aka dogara gare su ya kuma ɗauke fahimtar dattawa.
\v 21 Yakan zuba reni a kan hakimai ya kuma kwaɓe ɗamarar mutane masu ƙarfi.
\s5
\v 22 Yakan bayyana zurfafan abubuwan duhu ya kuma kawo baƙin duhu cikin haske.
\v 23 Yakan sa al'ummai suyi ƙarfi, yakan kuma hallakasu; yakan faɗaɗa al'ummai, ya kuma bi da su kamar 'yan kurkuku.
\s5
\v 24 Yakan ɗauke fahimta daga shugabanin mutanen duniya; yasa su suyi ta yawo a jeji inda ba tafarki.
\v 25 Suyi lalube cikin duhu babu haske; yakan sa suyi tangaɗi kamar bugaggen mutum.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Duba, idona ya ga duk wannan; kunnena yaji ya kuma fahimce shi.
\v 2 Abin da kuka sani, ni ma ina sane da shi; ni ban gaza ku ba.
\s5
\v 3 Duk da haka, na gwammace in yi magana da Mai Iko Dukka; ina so in tattauna da Allah.
\v 4 Amma ku kuna lulluɓe gaskiya da ƙarereyi; ku dukka likitoci ne marasa amfani.
\v 5 Kash, dama zaku yi shuru! Wannan zai zama maku hikima.
\s5
\v 6 Ku saurari nawa hujjojin; ku kasa kunne ga ƙarar tawa leɓunan.
\v 7 Za ku yi magana marar adalci domin Allah, zaku kuma yi maganar munafunci dominsa?
\v 8 Zaku nuna masa bambanci? Zaku yi jayayya domin Allah?
\s5
\v 9 Zai zama da kyau domin ku sa'ad da ya bincike ku? Zaku iya ruɗinsa kamar yadda zaku ruɗi mutane?
\v 10 Hakika zai kwaɓe ku idan a ɓoye kuka nuna bambanci.
\s5
\v 11 Darajarsa ba zata firgita ku ba, tsoronsa kuma ya faɗo a kanku?
\v 12 Batutuwanku masu daɗin ji misalai ne da aka yi su da toka; hanzarinku hanzari ne da aka yi su da yumɓu.
\s5
\v 13 Ku riƙe salamarku, ku kyale ni kawai, domin in yi magana, bari abin da zai auko kaina ya auko.
\v 14 Zan sa namana a bakina; in ɗauki raina a hannuwana.
\v 15 Bari mu gani, ko zai kashe ni, zan zama ba sauran bege; duk da haka, zan kare hanyoyina a gabansa.
\s5
\v 16 Wannan zai zama dalilin cetona, gama ba wani mugun mutum da zai zo gabansa.
\v 17 Allah, ka kasa kunne ga furcina; bari furcina ya zo kunnuwanka.
\s5
\v 18 Duba yanzu, na shirya hanzarina sosai; na sani ba ni da aibu.
\v 19 Wane ne wannan da zai yi jayayya gãba da ni a gaban sharia? Idan kun zo ne don ku yi, idan kun tabbatar da laifina, sai in yi shuru in saki raina.
\s5
\v 20 Allah, kayi mani abu biyu kawai, sa'an nan bazan boye kaina daga fuskarka ba:
\v 21 ka janye hannunka mai azaba daga gare ni, kuma kada ka bari razanarka ta tsorata ni.
\v 22 Sa'an nan ka kira ni, zan kuma amsa; ko kuma ka bari in yi magana da kai, kai ka amsa mani.
\s5
\v 23 Laifofina da zunubaina nawa ne? Bari in san kuskurena da zunubina.
\v 24 Don me kake boye fuskarka daga gare ni ka maishe ni kamar maƙiyinka?
\v 25 Zaka tsanantawa ganyen da iska ke kora? Zaka far wa tattaka?
\s5
\v 26 Domin ka rubuta abubuwa masu ɗaci gãba da ni; kasa in gãji laifofin ƙuruciyata.
\v 27 Ka kuma sa ƙafafuna a turu; kana duba dukkan tafarkuna kurkusa; kana bincike inda sawayen ƙafafuna suka taka,
\v 28 ko da yake ni kamar ruɓaɓɓen abu ne da yake lalacewa, kamar rigar da asu suka cinye.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Mutum, da mace ta haifa, ya kan rayu 'yan kwanaki kaɗan yana kuma cike da damuwa.
\v 2 Ya kan tsiro daga ƙasa kamar fure sai kuma a datse shi; ya tsere kamar inuwa baya daɗewa.
\v 3 Kana duba kowanne su? Kana gabatar da ni a gaban shari'a tare da kai?
\s5
\v 4 Wane ne zai iya fitar da abu mai tsabta daga cikin marar tsabta? Babu ko ɗaya.
\v 5 Kwanakin mutum a ƙayyade suke. Yawan watanninsa na tare da kai; ka ƙayyade masa iyaka da ba zai iya wucewa ba.
\v 6 Ka ɗauke idonka daga gare shi domin ya huta, domin ya ji daɗin kwanansa kamar ɗan ƙwadago in ya iya.
\s5
\v 7 Mai yiwuwa ne itace na da bege; idan an sare shi, zai iya toho kuma, 'yan sabbin rassansa ba sa ɓata.
\v 8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa a ƙasa, kututturensa kuma ya mutu a ƙasa,
\v 9 amma da zarar ya ji ƙanshin ruwa, sai yayi toho ya kuma fid da rassa kamar tsiro.
\s5
\v 10 Amma mutum yakan mutu; ya zama da rauni; hakika, mutum yakan bar yin numfashi, sa'an nan fa ina yake?
\v 11 Kamar yadda ruwa ke ɓacewa a tafki, da yadda rafi ke rasa ruwa ya ƙone,
\v 12 haka mutane ke kwantawa basa sake tashi. Sai ko in sammai sun ɓace, ba zasu farka ba ko kuma a tashe su daga barcinsu.
\s5
\v 13 Kash, dama zaka ɓoye ni can Lahira nesa da wahalhalu, ka kuma a ajiye ni a ɓoye har sai fushinka ya wuce, sai kasa mani lokaci da zan kasance a can sa'an nan ka tuna da ni!
\v 14 Idan mutum ya mutu, zai sake rayyuwa kuma? Idan haka ne, zan so in jira dukkan lokacin gajiyata a can har sai 'yantarwata ta zo.
\s5
\v 15 Zaka kira, zan kuwa amsa maka. Zaka zama da marmarin aikin hannuwanka.
\v 16 Zaka ƙididdige ka kuma lura da takawata; baza ka bi diddigin zunubina ba.
\v 17 Za a ɗaure kurakuraina a jaka; zaka rufe laifofina.
\s5
\v 18 Amma har tsaunuka ma sukan faɗi su zama ba komai ba, harma duwatsu akan kawar da su daga wurinsu;
\v 19 ruwaye sukan zaizaye duwatsu; ambaliyarsu na kwashe ƙurar ƙasa. Haka nan ne, kake hallakar da begen mutum.
\s5
\v 20 Kullum kana cin nasara a kansa, sai ya rasu; ka kan sauya fuskarsa ka aike shi ya mutu.
\v 21 Idan an girmama 'ya'yansa maza, ba zai sani ba; ko kuma an wulaƙanta su, ba zai gani ba.
\v 22 Yakan ji ciwon jikinsa ne kawai, yana kuma makokin domin kansa.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Sa'an nan Elifaz Batemane ya amsa ya ce,
\v 2 "Ya kamata mutum mai hikima ya amsa da ilimin banza kuma cika kansa da iskar gabas?
\v 3 Koya kamata ya kawo hujja da magana marar amfani ko kuma furce furce waɗanda baza su amfana ba?
\s5
\v 4 Hakika, kana rushe bangirma ga Allah; kana hana sujada gare shi,
\v 5 gama ƙuraƙuranka suna koya wa bakinka; ka zaɓa ka zama da harshen mutum mai wayo.
\v 6 Bakinka da kansa ya kashe ka, ba nawa ba; hakika, leɓunanka suna shaida gãba da kai.
\s5
\v 7 Kai ne mutum na fari da aka haifa? An kawo ka cikin rayyuwa kafin tuddai ne?
\v 8 Ko ka taɓa jin asirin ilimin Allah? Ka ɗauka kai kaɗai ke da hikima?
\v 9 Me ka sani da bamu sani ba? Me ka fahimta da baya cikinmu muma?
\s5
\v 10 Tare da mu akwai masu furfura da tsoffi maza waɗanda suka girmi mahaifinka ainun.
\v 11 Ta'aziyun Allah sun yi maka kaɗan ne, maganganu masu taushi zuwa gare ka?
\s5
\v 12 Don me zuciyarka take yaudarar ka? Me yasa ka ke ruwan idanu,
\v 13 har ka mai da ruhunka gãba da Allah kana fitar da maganganu irin waɗannan daga bakinka?
\v 14 Wane ne mutum da zai zama da tsarki? Waye shi wanda mace ce ta haife shi da zai zama da tsarki?
\s5
\v 15 Duba, Allah ba ya amincewa da tsarkakansa; hakika, sammai basu da tsarki a idanunsa;
\v 16 ballantana wanda ya gaza a tsarki ƙazantacce lalatacce kuma, mutum wanda yake shan laifi kamar ruwa!
\s5
\v 17 Zan nuna maka; ka kasa kunne gare ni; zan yi maka shelar abubuwan da na gani,
\v 18 abubuwan da masu hikima suka gãda daga ubanninsu, abubuwan da kakannisu basu ̀ɓoye ba.
\s5
\v 19 Waɗannan su ne kakanninsu, waɗanda su kaɗai aka ba ƙasar, wanda ba wani baƙo da ya taɓa ratsawa.
\v 20 Mugun mutum yana murmurɗewa don zafin ciwo dukkan kwanakinsa, shekarun da aka aza wa azalumi yasha azaba.
\v 21 Ƙarar firgitarwa na cikin kunnuwansa; sa'ad da yake cikin wadata, mai hallakarwa zai auka masa.
\s5
\v 22 Baya tunani cewa zai komo daga cikin duhu; takobi na jiransa.
\v 23 Sai ya tafi wurare da bam da ban domin abinci, yana cewa, 'Ina yake?' Ya sani ranar duhu ta gabato.
\v 24 Ƙunci da raɗaɗi sukan tsoratar da shi; su ci nasara a kansa, kamar sarkin da ya shirya domin yaƙi.
\s5
\v 25 Domin ya miƙa hannunsa gãba da Allah, ya kuma nuna girman kai gãba da Mai Iko Dukka,
\v 26 wannan mugun mutum yana gudu zuwa ga Allah da taurararriyar zuciya, da garkuwa kakkaura.
\s5
\v 27 Wannan gaskiya ne, ko da yake ya rufe fuskarsa da kitsensa ya kuma tara kitse a kwiɓinsa,
\v 28 ya kuma zauna a rusassun birane; a gidajen da ba mazauna yanzu kuma suna shirye su zama tsibi.
\s5
\v 29 Ba zai yi arzaki ba; arzaƙinsa ba zai daɗe ba kuma mallakarsa baza ta yaɗu a ƙasar ba.
\v 30 Ba zai fita daga duhu ba; harshen wuta zai ƙona karmaminsa; numfashi daga bakin Allah zai kora shi ya tafi..
\s5
\v 31 Kada ya dogara ga abubuwa marasa amfani, yana ruɗin kansa; gama abubuwa marasa amfani zasu zama ladansa.
\v 32 Zai faru kafin lokacin mutuwarsa yazo; reshensa ba zai zama kore ba.
\v 33 Zai kakkaɓe ɗanyun inabinsa kamar kuringar inabi; zai zubar da furanninta kamar itacen zaitun.
\s5
\v 34 Gama tawagar marasa tsoron Allah ba zasu zama da zuriya ba; wuta zata cinye rumfar masu cin hanci.
\v 35 Sukan ɗauki cikin ƙeta su haifi zunubi; mahaifarsu na ɗaukar cikin rikirkicewa.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Sa'an nan Ayuba ya amsa yace,
\v 2 "Na sha jin abubuwa da yawa kamar haka; ku dukka masu ta'aziyar ma abin ban tausai ne.
\v 3 Maganganu marasa amfani basu da ƙarshe ne? Me ya dame ku da kuke amsawa haka?
\s5
\v 4 Nima zan iya magana kamar yadda kuke yi, in da kuna gurbina; zan iya tattara maganganu in haɗa su tare gãba da ku kuma in girgiza kaina a gabanku don reni.
\v 5 Zan ƙarfafa ku da bakina, ƙaɗawar leɓunana zasu kawo maku sauƙi.
\s5
\v 6 Idan na yi magana wannan ba zai sauƙaƙe baƙincikina ba; idan na yi shiru, ƙaƙa wannan zai taimake ni?
\v 7 Amma yanzu, Allah, ka sani na gaji; ka mai da dukkan iyali na wofi.
\v 8 Ka sa na ƙeƙashe, wannan ma shaida ce gãba da ni; ƙeƙashewar jikina ya tashi gãba da ni, yana kuma shaida gãba da ni a fuskata.
\s5
\v 9 Allah ya kekketa ni cikin hasalarsa ya kuma tsananta mani; Yana tauna haƙoransa cikin zafin fushi; magabcina ya kafa idanunsa a kaina sa'ad da ya kekketa ni.
\v 10 Mutane sun buɗe bakinsu suna mani gwalo; sun buge ni ba dalili a kunci; sun taru gaba ɗaya gãba da ni.
\s5
\v 11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefar da ni cikin hannun mugayen mutane.
\v 12 Ina zaune lau, sai ya kakkarya ni. Hakika, ya kama ni a wuya ya jefar ya jefar da ni gutsu-gutsu; ya kuma tsai da ni daf a gabansa.
\s5
\v 13 Maharbansa dukka sun kewaye ni; Allah ya sossoke ka'idojina bai yi mani rangwame ba; ya zubar da matsarmamata a ƙasa.
\v 14 Yana bubbuga bangona akai akai; yana gudu a kaina kamar mayaƙi.
\s5
\v 15 Na ɗaura tsumma a fatata; na soka ƙaho na cikin ƙasa.
\v 16 Fuskata tayi jawur da kuka; a kan girata akwai inuwar mutuwa
\v 17 ko da yake ba ta'addanci a hannuwana, addu'ata mai tsarki ce.
\s5
\v 18 Ƙasa, kada ki rufe jinina; kada kukana ya sami wurin hutawa.
\v 19 Ko yanzu ma, duba, shaidata tana cikin sama; wanda yake lamuni domina yana sama.
\s5
\v 20 Abokaina suna yi mani ba'a, amma idona yana zubar da hawaye ga Allah.
\v 21 Ina roƙo domin wannan mashaidi a cikin sama yayi muhauwara da Allah kamar yadda mutum zai yi da makwabcinsa!
\v 22 Domin bayan 'yan shekaru sun wuce, zan tafi wurin da bazan komowa daga can ba.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 An cinye ruhuna, kwanakina sun ƙare; kabari na shirye domina.
\v 2 Lallai da akwai masu ba' a tare da ni; idona dole kullum ya ga cakunar su.
\v 3 Ka bani shaida, kayi mani lamuni da kanka; wane ne kuma ke nan da zai taimake ni?
\s5
\v 4 Domin kai, Allah, ka hana wa zuciyarsu fahimta; saboda haka, ba zaka ɗaukaka su a bisa na ba.
\v 5 Wanda yaci amanar abokansa domin ya sami lada, idanun 'ya'yansa zasu dushe.
\s5
\v 6 Amma ya maishe ni abin karin magana ga mutane; suna tofa mani miyau a fuska.
\v 7 Idona ya sace saboda baƙin ciki; dukkan gaɓaɓuwan jikina sun ƙanjame kamar inuwa.
\v 8 Mutane masu adalci zasu yi mamaki da wannan; mutum marar aibu zai husata kansa gãba da mugayen mutane.
\s5
\v 9 Mutum mai adalci zai kiyaye hanyarsa; wanda ya ke da hannuwa mararsa laifi zai yi ta ƙaruwa da ƙarfi.
\v 10 Amma game da dukkanku, kuzo yanzu; ba zan sami wani mai hikima a cikinku ba.
\s5
\v 11 Shekaruna sun wuce; shirye shiryena sun watse, haka kuma marmarin zuciyata.
\v 12 Waɗannan mutane, waɗannan masu reni, suna sauya dare zuwa rana; haske ya fi kusa da duhu.
\s5
\v 13 Idan gidan da nake bege Lahira ne kaɗai; idan na baza shimfiɗata cikin duhu;
\v 14 idan kuma na cewa rami, 'Kai ne mahaifina,' da kuma tsutsa, 'Ke ce mahaifiyata ko kuma 'yar'uwata,'
\v 15 to ina begena ya ke? A game da begena, wa ya iya ganin ko da ɗan kaɗan?
\s5
\v 16 Bege zai tafi tare da ni zuwa ƙofar Lahira ne sa'ad da zamu gangara cikin turɓaya?
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Sai Bildad Bashune ya amsa ya ce,
\v 2 "Shin yaushe zaka dena maganarka? Kayi tunani, daga bayan haka zamu yi magana.
\s5
\v 3 Don me za a ɗauke mu dabbobi, marasa wayo a ganinka?
\v 4 Kai da ka ke yayyage kanka a cikin fushinka, ya kamata a kawar da duniya domin ka ko kuma ya kamata a tumbuƙe duwatsu daga wurarensu?
\s5
\v 5 Hakika, za a ɓice hasken mugun mutum; tarwatsun wutarsa ba za ta haskaka ba.
\v 6 Haske zai zama duhu a rumfarsa; fitilar da ke bisansa za a ɓice ta.
\s5
\v 7 Takawar ƙarfinsa zata ragu; shirye shiryen kansa zasu kada shi.
\v 8 Gama za a jefa shi cikin raga da ƙafarsa; zai yi tafiya zuwa cikin tarko.
\s5
\v 9 Tarko zai kama diddigensa; ashibta zata riƙe shi.
\v 10 An binne masa igiyar zarmewa a ƙasa a ɓoye; tarko ne dominsa akan hanya.
\v 11 Banrazana zai sa shi tsoro a kowanne gefe; zasu fafari digadigansa.
\s5
\v 12 Arzikinsa zai juya ya zama yunwa, kuma masifa na shirye a gefensa.
\v 13 Gaɓaɓuwan jikinsa zasu mutu; hakika, ɗan farin mutuwa zai ci gaɓaɓuwansa.
\s5
\v 14 Za a fizge shi daga rumfarsa da yake zaune lafiya a kora shi zuwa ga sarkin razanai.
\v 15 Mutanen da ba nasa ba zasu zauna a rumfarsa bayan da suka ga wutar ƙibiritu ta bazu cikin gidansa.
\s5
\v 16 Saiwowinsa zasu bushe daga ƙasa; a sama za a daddatse rassansa.
\v 17 Ba sauran tunawa da shi a duniya; ba zai sami suna a titi ba.
\s5
\v 18 Za a kora shi daga haske zuwa cikin duhu kuma za a kore shi daga wannan duniya.
\v 19 Ba zai zama da ɗa namiji ko jikoki maza a cikin mutanensa ba, ko ragowar dangi inda dã ya zauna.
\v 20 Waɗanda ke zaune a kudu zasu tsorata da abin da ya faru da shi wata rana; waɗanda ke zaune a gabas zasu firgita da wannan.
\s5
\v 21 Tabbas haka gidan marasa adalci yake, wuraren waɗanda basu san Allah ba."
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Sai Ayuba ya amsa ya ce,
\v 2 "Har yaushe zaku sa ni cikin wahala kuma ku daddatse ni gutsu gutsu da maganganu?
\s5
\v 3 Sau goma ɗin nan kun zarge ni; baku ji kunya ba cewa kun wulaƙanta ni ainun.
\v 4 Idan lallai gaskiya ne nayi kuskure, to kuskurena ya zama abin da ni kaina zan yi tunani sa.
\s5
\v 5 Idan hakika zaku ɗaukaka kanku fiye da ni ku kuma yi amfani da ƙasƙancina gãba da ni,
\v 6 sai ku sani Allah bai yi mani dai-dai ba ya kuma kama ni cikin ragarsa.
\s5
\v 7 Duba, na ƙwala ihu, "Ta'adanci!" amma ban sami amsa ba. Na yi kira domin neman taimako, amma babu adalci.
\v 8 Yasa katanga a hanyata domin kada in iya wucewa, ya kuma sa duhu a tafarkina.
\v 9 Ya tuɓe mani darajata, ya kuma ɗauke kambi daga kaina.
\s5
\v 10 Ya kakkarya ni ta kowanne gefe, na kuma ƙare; ya janye begena kamar itace.
\v 11 Ya kuma kunna wutar hasalarsa gãba da ni; ya maishe ni ɗaya daga cikin abokan gabarsa.
\v 12 Rundunarsa sun tashi gaba ɗaya; sun tula tsibin shara gãba da ni kuma sun kewaye rumfata.
\s5
\v 13 Ya nisantar da 'yan'uwana maza daga gare ni; sanin idona an ware su gaba ɗaya daga gare ni.
\v 14 Dangina sun yashe ni; aminaina na kurkusa sun manta da ni.
\s5
\v 15 Waɗanda dã na saukar baƙi a gidana da barorina mata sun maishe ni kamar baƙo; ni bare ne a idanunnunsu.
\v 16 Na kira barana, amma bai ba ni amsa ba ko da yake na roƙe shi da bakina.
\s5
\v 17 Numfashina ya dunguri matata; har ta maishe ni abin watsi ga waɗanda mahaifiyarmu ɗaya.
\v 18 Har ma 'yan yara ƙanana sun rena ni; idan na tashi zan yi magana, sai suyi magana gãba da ni.
\v 19 Dukkan idon sani abokanaina sun kyamace ni; Waɗanda nake ƙauna suna gãba da ni.
\s5
\v 20 Ƙasusuwana sun manne wa fatata da kuma naman jikina; ina raye da ƙyar.
\v 21 Ku ji tausayina, ku ji tausayi na, abokaina, gama hannun Allah ya taɓa ni.
\v 22 Me yasa kuke farautata kamar yadda Allah ke yi? Zaku taɓa ƙoshi da naman jikina?
\s5
\v 23 Kash, da ma za a rubuta maganganuna! Aiya, dama za a rubuta su a cikin littafi!
\v 24 Kash, dama da alƙalamin ƙarfe da tamã aka sassaƙa rubutun akan dutse har abada!
\s5
\v 25 Amma a gare ni, na sani mai fansata yana raye, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya;
\v 26 bayan fatata, watau, wannan jiki, an hallaka shi, sa'an nan a cikin jiki zan ga Allah.
\v 27 Zan gan shi da idanuna-ni, ba kuma wani da bam ba. Zuciyata ta karai a cikina.
\s5
\v 28 Idan kun ce, 'Yaya zamu tsananta masa! Tushen matsalarsa tana cikinsa,'
\v 29 sai ku ji tsoron takobi, domin hasala na kawo hukuncin takobi, domin ku sani a kwai shari'a."
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sa'an nan Zofar Banamate ya amsa ya ce,
\v 2 "Tunane tunanena suna sa ni in amsa da garaje saboda damuwar da ke cikina.
\v 3 Ina jin zargi da ke kunyatar da ni, amma wani ruhu daga fahimtata yana amsa mani.
\s5
\v 4 Baka san wannan abu tun daga zamanan dã ba, da Allah ya ajiye mutum a duniya:
\v 5 cin nasarar mugun mutum na gajeren lokaci ne, kuma murnar marar tsoron Allah daɗewarta kamar ƙiftawar ido ne?
\s5
\v 6 Ko da tsayinsa ya kai sammai, kuma kansa ya taɓa gizagizai,
\v 7 duk da haka irin mutumin nan zai lalace tuttur kamar najasarsa; waɗanda suka gan shi zasu ce, 'Ina yake?'
\s5
\v 8 Zai yi firiya ya ɓace kamar mafarki ba za a kuma same shi ba; hakika, za a fafare shi kamar wahayin dare.
\v 9 Idon da ya ganshi ba zai ƙara ganin sa ba; mazauninsa ba zai ƙara ganinsa ba.
\s5
\v 10 'Ya'yansa zasu roƙi gafarar matatalauta; hannuwansa zasu mayar da dukiyarsa.
\v 11 Ƙasusuwansa suna cike da ƙarfin ƙuruciya, amma zai kwanta tare da shi cikin turɓaya.
\s5
\v 12 Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa, ko da yake ya ɓoye shi ƙarƙashin harshensa,
\v 13 ko da yake ya riƙe shi a can bai bari ya fita ba amma ya riƙe ya gama cikin bakinsa -
\v 14 abincin da ke cikin hanjinsa zai juya ya zama da ɗaci; ya zama dafin maciji a cikinsa.
\s5
\v 15 Yakan haɗiye arziki, amma sai ya haras da su kuma; Allah zai tutturo su waje daga cikinsa.
\v 16 Zai sha dafin maciji; harshen kububuwa zai kashe shi.
\s5
\v 17 Ba zai ji daɗin rafuffuka ba, yalwar zuma da madara.
\v 18 Zai mayar da rabon wahalar aikinsa kuma ba zai iya ya cin sa ba; ba zai ji daɗin dukiyar da ya samu ta wurin cinikaiyarsa ba.
\v 19 Gama ya wulaƙanta matalauta ya kuma yashe su; ya ƙwace gidajen da bai gina ba ƙarfi da yaji.
\s5
\v 20 Domin bai san ƙoshi ba, ba zai iya tanada wani abin da yake marmari ba.
\v 21 Ba wani abin da ya rage da bai cinye shi ba; saboda haka arzikinsa ba zai daɗe ba.
\v 22 A cikin yalwar wadatarsa zai faɗa cikin wahala; hannun kowanne matalauci zai yi tsayayya da shi.
\s5
\v 23 Sa'ad da yake gaf da cika cikinsa, Allah zai jeho masa fushinsa mai ƙuna a kansa; Allah zai kwararo masa shi sa'ad da yake cin abinci.
\v 24 Ko da yake mutumin nan ya guje wa makamin ƙarfe, bakan tagulla zai harbe shi.
\v 25 Idan ya cire shi a bayansa sai bakin mai tsini ya shiga hantarsa. Razana zata faɗo masa.
\s5
\v 26 Duhu ne baƙi ƙirin ke ajiye domin kayansa masu daraja; wutar da ba a izawa zata cinye shi; zata cinye ragowar abin da ke rumfarsa.
\v 27 Sammai zasu bayyana zunubansa, ƙasa kuma zata miƙe gãba da shi ta zama shaida.
\s5
\v 28 Dukiyar gidansa zata ɓace; kayayyakinsa zasu gudu a ranar hasalar Allah.
\v 29 Wannan shi ne rabon mugu daga Allah, gadon da Allah ya ajiye masa kenan."
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Sai Ayuba ya amsa ya ce,
\v 2 "Ku kasa kunne da kyau ga maganganuna, kuma bari wannan ya zama ta'aziyar da kuke yi mani.
\v 3 Ku daure da ni, ni kuma zan yi magana; bayan nayi magana, sai ku cigaba da ba'a.
\s5
\v 4 Ni dai kam, ƙarata ga mutum ne? Don mene ne bazan yi rashin haƙuri ba?
\v 5 Ku duba ni kuyi mamaki, ku ɗibiya hannuku a kan bakinku.
\v 6 Sa'ad da nayi tunani akan wahaluna, nakan tsorata, makyarkyata sai ta kama jikina.
\s5
\v 7 Me yasa mugayen mutane suke a rayuwa, su tsufa, su girma su ƙasaita a iko?
\v 8 Zuriyarsu ta kafu tare da su a kan idanunsu, kuma jikokinsu su da su a idanunsu.
\v 9 Gidajensu lafiya ba tsoro; kuma babu hukuncin Allah a kansu.
\s5
\v 10 Bijiminsu na barbara; baya fasa yi; shanunsu suna haifuwa basa yin ɓarin 'yan maruƙansu'
\v 11 Sukan aika da 'yan maruƙansu kamar garke, 'ya'yansu suna rawa.
\v 12 Suna waƙa da kuge da molo kuma suna farinciki da waƙar sarewa.
\s5
\v 13 Suna zaman kwanakinsu cikin wadata, su gangara shuru zuwa Lahira.
\v 14 Sai su cewa Allah, 'Ka rabu da mu domin ba ma son wani fahimta game da hanyoyinka.
\v 15 Wanene Mai Iko Dukka, da zamu yi masa sujada? Wace riba ce zamu samu idan muka yi addu'a gare shi?'
\s5
\v 16 Duba, arzikinsu ba a hannunsu yake ba? Ba ruwana da shawarar mugayen mutane.
\v 17 Sau nawa fitilar mugayen mutane ana hure ta, ko kuma masifarsu ta auka masu? Sau nawa yakan faru sai Allah ya rarraba ma su baƙin ciki cikin fushinsa?
\v 18 Sau nawa su ke zama kamar tattaka cikn iska ko kamar ƙaiƙai da iskar hadari ke kwashewa.
\s5
\v 19 Kun ce, 'Allah yana tara alhakin mutum domin 'ya'yansa su biya.' Bari shi da kansa ya biya, domin ya san laifinsa.
\v 20 Bari idanunsa su ga hallakarsa, kuma bari ya sha hasalar Mai Iko Dukka.
\v 21 Gama me ya dame shi da iyalinsa da ya bari bayan an datse kwanakinsa?
\s5
\v 22 Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da shima yana shari'anta har waɗanda suke sama?
\v 23 Wani mutum yakan mutu cikin goshin ƙarfinsa, ya yi shuru a natse.
\v 24 Jikinsa na cike da madara, kuma ɓargon ƙashinsa da danshi.
\s5
\v 25 Wani mutum kuma ya mutu cikin ɓacin zuciya, wanda bai taɓa ɗanɗana wani abin kirki ba.
\v 26 Dukkan su sukan kwanta a cikin turɓaya; tsutsotsi su mamayesu.
\s5
\v 27 Duba, na san tunaninku, kuma da hanyoyin da ku ke so ku aibata ni.
\v 28 Domin kun ce, 'Ina yanzu gidan ɗan sarki? Ina rumfar da mugun mutumin nan ya zauna a ciki?'
\s5
\v 29 Baku taɓa tambayar mutane matafiya ba? Ko ba ku san shaidar da zasu iya faɗi ba,
\v 30 cewa mugun mutum an keɓe shi daga ranar masifa, an kuma janye shi daga ranar hasala?
\s5
\v 31 Wane ne zai zargi hanyoyin mugun mutum a fuskarsa? Wane ne zai sãka masa domin abin da ya yi?
\v 32 Duk da haka za a kai shi kabari; mutane zasu yi ta kiyaye kushewarsa.
\v 33 Ƙurar kabarinsa da aka tula a kansa zata zama masa da daɗi; dukkan mutane za su bi bayansa, kamar yadda mutanen ba su ƙidayuwa sun sha gabansa.
\s5
\v 34 To ƙaƙa zaku ta'azantar da ni da rashin hankali, tun da cikin amsoshinku babu komai sai ƙarairayi?"
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Sai Elifaz Batemane ya amsa, yace,
\v 2 "Mutum zai zama da amfani ga Allah? Mutum mai wayau zai zama da amfani ga gare shi?
\v 3 Zai zama da jin daɗi ga Mai Iko idan ka zama mai adalci? Zai zama da wata riba gare shi idan hanyoyinsa marasa laifi ne?
\s5
\v 4 Ai ba domin kana tsoronsa ba ne ya kwaɓe ka, ko kuma ka ɗauki shari'a?
\v 5 Ba babbar muguntarka ba ce? Ashe babu ƙarshen muguntarka?
\s5
\v 6 Domin ka bukaci a ba ka bashin da ke daga wurin ɗan'uwanka ba tare da wani dalili ba, ka kuma ƙwace tufafi daga wurin wanda ba shi da komai.
\v 7 Ka hana ruwa ga mutane masu ƙishinruwa su sha; ka hana abinci ga mutane masu jin yunwa
\v 8 ko da ya ke kai mutum ne mai iko, kana da kayan duniya, ko da ya ke kai, mutum ne mai girma, kana rayuw a cikinta.
\s5
\v 9 Ka kori mata da mazajensu suka mutu ba tare da komai ba; hannuwan marayu sun karye.
\v 10 Saboda haka, ramummuka a ko'ina kewaye da kai, sun kuma kawo maka tsoron damuwa.
\v 11 Akwai duhu, saboda har baza ka iya gani ba; ruwaye masu yawa sun sha kanka.
\s5
\v 12 Ashe Allah ba a saman sammai yake ba? Dubi taurare a sama, yaya nesan su a can!
\v 13 Kace, 'Me Allah ya sani? Zai iya shari'a a cikin baƙin duhu?
\v 14 Gizagizai masu duhu sune ke rufe shi, saboda haka ba ya ganin mu; yana tafiya a kan iyakar sararin sama.'
\s5
\v 15 Kana bin tsohowar hanyar da mugayen mutane suke tafiya a kai--
\v 16 waɗanda aka ƙwace kafin lokacinsu, waɗanda tuwasunsu suka shafe kamar rafi,
\v 17 sune waɗanda suka ce da Allah, 'Tafi daga wurin mu,' su ne suka ce, 'Mene ne Mai Iko zai yi da mu?'
\s5
\v 18 Duk da haka ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, shirye-shiryen mugayen mutane suna nesa daga gare ni.
\v 19 Adalan mutane su na ganin kaddararsu suna murna; mutane marasa laifi kuma suna dariyarsu.
\v 20 Sun ce, 'Babu shakka waɗanda suka taso gãba da mu an yanke su, wuta kuwa ta lashe mallakarsu.'
\s5
\v 21 Yanzu ka yarda da Allah salama ta kasance tare da kai; ta wannan hanya, abu mai kyau zai zo gare ka.
\v 22 Karɓi, ina rokon ka, ka koya daga bakinsa; ka riƙe kalmominsa a zuciyarka.
\s5
\v 23 Idan zaka juyo ga Mai Iko, za a sake gina ka, idan za ka ajiye rashin adalci nesa daga gidanka.
\v 24 Ka ajiye dukiyarka can cikin ƙura, zinariya daga ofir a cikin duwatsun rafuffuka,
\v 25 Mai Iko zai zama dukiyarka, da azurfa mai daraja ga gare ka.
\s5
\v 26 Sa'an nan zaka sami farin ciki a wurin Mai Iko, za ka tada fuskarka ga Allah.
\v 27 Za ka yi addu'a gare shi, shi kuma zai ji ka; zaka kiyaye alkawaran da ka yi masa.
\v 28 Za ka kuma hurta komai, za a kuma tabbatar maka, haske zai haskaka a hanyoyinka.
\s5
\v 29 Allah yakan ƙasƙantar da mutum mai girmankai, yakan ceci mai tawali'u.
\v 30 Zai ceci kowane mutum wanda ke da laifi; wanda za a ceta ta wurin abin da hannuwansa ke yi dai-dai."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Sai Ayuba amsa ya ce,
\v 2 "Har yau ƙarata nada zafi, hannuna yayi nauyi saboda gunagunina.
\s5
\v 3 Oh, dama na san inda zan same shi! Oh, da sai in tafi wurinsa!
\v 4 Da zan kai ƙarata a gabansa, da na cika bakina da muhawara.
\v 5 Zan koyi kalmomi waɗanda zaya amsa mani, yadda zan san abin da zai ce da ni.
\s5
\v 6 Zaya yi gardamar gãba da ni duk da ƙarfin ikonsa? A'a, zai saurare ni.
\v 7 Akwai amintaccen mutum da zai yi gardama da shi. Ta wannan hanyar zan tabbatar da aminci har abada ta wurin shari'a ta.
\s5
\v 8 Duba, na tafi gabashi, amma baya can, yammaci, amma ban same shi ba.
\v 9 A arewa, a wurin yake aiki, duk da haka ban gan shi ba, a kudu, a wurin ya ɓoye kansa domin kada in gan shi.
\s5
\v 10 Gama ya san hanyar da na ɗauka; ya jarraba ni, zan fito kamar zinariya.
\v 11 Ƙafata tana bin sawun ƙafarsa; ina bin hanyarsa ban kuma kauce wani gefen ba.
\v 12 Ban kuma koma da baya ba daga umarnin leɓunansa; na ajiye kalmomin baƙinsa sun zama abinci na.
\s5
\v 13 Gama yana ɗaya daga cikin masu kirki, wa zai iya juyar da shi? Abin da yake so ya aikata.
\v 14 Gama ya ɗauki ka'ida gãba da ni; akwai da yawa kamar su.
\s5
\v 15 Saboda haka, ina rawar jiki a gabansa; duk lokacin da nake tunani a kansa.
\v 16 Domin Allah ya sa zuciyata tayi sanyi; Mai Iko ya tsorata ni.
\v 17 Amma duhu bai kawo ni ƙarshe ba, ko da yake baƙin duhu ya rufe mani fuskata.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Meyasa Mai Iko bai tsaida lokatan shari'ar mugayen mutane ba? Meyasa bai tsayar wa waɗanda suke adalai ga Allah suga kwanakinsa na shari'a ya zo?
\s5
\v 2 Akwai mugayen mutane da yawa da suke kawar da iyaka; akwai mugayen mutane waɗanda suke ɗaukan garke da tsiya su zuba cikin makiyayarsu.
\v 3 Sukan saci jakin marayu; su kama takarkarin gwauruwa a matsayin jingina.
\v 4 Sukan tilastawa mutane masu bukata su bar masu hanya; mutane matalauta na ƙasa dukka su ɓoye kansu daga gare su.
\s5
\v 5 Duba, waɗannan mutane matalauta su fita daga wurin ayyukansu kamar jakunan daji a jeji, suna bi hankali su na neman abinci; me yiwuwa Arabah zai ba su abinci domin 'ya'yansu.
\v 6 Matalautan mutane na girbi da dare a gonakin wasu mutanen, su na tattara 'ya'yan inabi daga gonakin waɗannan mugayen mutanen.
\v 7 Su na kwance tsirara dukkan dare ba tare da tufa ba, basu da abin da zai hana su jin sanyi.
\s5
\v 8 Suna jike sharkaf da ruwa da ke kwararowa daga kan duwatsu; suna kwance kusa da manyan duwatsu domin basu da mafaka.
\v 9 Akwai mugayen mutane waɗanda suke figar marayu daga nonon iyayansu mata, mugayen mutane waɗanda suke ɗaukan yara a matsayin jingina daga matalautan mutane.
\v 10 Amma matalautan mutane suna tafiya babu kaya a jikinsu; suna tafiya da yunwa, suna ɗauke da damunan hatsi na waɗansu mutane.
\s5
\v 11 Matalautan mutane na matse mai a katangar mugayen mutane; suna kuma matsar ruwan inabin mugayen mutane, amma su da kansu suna fama da ƙishi.
\v 12 Daga cikin birni ana jin nishin masu mutuwa, makogwaron masu rauni na kukan neman taimako. Amma Allah bai kula da masu laifin ba.
\s5
\v 13 Wasu daga cikin waɗannan mugayen mutanen suna ƙin haske; basu san hanyarsa ba, ko su tsaya a hanyarsa.
\v 14 Kafin hasken rana mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci da mutane masu bukata; da dare kuma ya kan zama kamar ɓarawo.
\s5
\v 15 Har yau, idon mazinaci yakan jira sai da magariba; ya faɗa, 'Babu idon da zai gan ni.' Yana ɓoye fuskarsa.
\v 16 A cikin duhu mugayen mutane sukan kutsa kai cikin gidaje; amma suna ɓoye kansu da rana; basu damu da haske ba.
\v 17 Gama dukkan su, mattsanancin duhu ne kamar duhun safiya; domin su abokan "yan ta'addar baƙin duhu ne.
\s5
\v 18 Suna wucewa da sauri, duk da haka, kamar kumfa a kan fuskar ruwaye; ƙasar da suka mallaka an la'anta ta; babu wanda zai tafi yayi aiki a cikin gonar inabi.
\v 19 Kamar dusar ƙanƙara take narkewa, iska mai laima cikin ruwaye, haka Lahira ke ɗaukan waɗanda suka yi zunubi.
\s5
\v 20 Cikin da ya haife shi ba zai tuna da shi ba; macijin ciki zai ji daɗin ƙoshi a kansa; ba za a ƙara tunawa da shi ba; ta wannan hanya, miyagu zasu lalace kamar itace.
\v 21 Mugun da ya lanƙwame matan da basu haifi yara ba; bai kuma nuna alheri ga matar da ke gwauruwa ba.
\s5
\v 22 Duk da haka Allah yakan ja mutane masu iko ta wurin ikonsa; yakan ɗaga ya kuma hana su ƙarfi a rayuwarsu.
\v 23 Allah ya kan bar su da tunanin sun tsira, suna murna a kan haka, amma idanuwansa na kan hanyoyinsu.
\s5
\v 24 An ɗaukaka waɗannan mutane; a ɗan lokaci kaɗan, zasu ɓace; za a ƙasƙantar da su; za a tattara su wuri ɗaya kamar sauran; za a hallaka su kamar karan dawa da aka yanke.
\v 25 Idan ba haka ba, wane ne ya tabbatar ni maƙaryaci ne; wa zai ce kalmomina ba gaskiya ba ne?"
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Sai Bildad Bashune ya amsa ya ce,
\v 2 "Mulki da tsoro suna tare da shi, yayi samaniya wurarensa.
\v 3 Akwai ƙarshen jimilar yawan sojojinsa? A kan wane ne haskensa yaƙi haskakawa?
\s5
\v 4 Yaya mutum zai zama adali tare da Allah? Yaya shi wanda mace ta haifa zai zama da tsabta, ƙarɓaɓɓe gare shi?
\v 5 Duba, ko da wata bashi da haske gare shi, taurari ma basu da tsarki a gabansa.
\v 6 Yaya kuma mutum, wanda aka haifa--ɗan mutum, wanda aka haife shi!"
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Sai Ayuba ya amsa ya ce,
\v 2 "Yaya ka taimakawa wanda bashi da ƙarfi! Ka cece hannun da bashi da ƙarfi!
\v 3 Yaya kake ba wanda bashi da hikima shawara, kana sanar da amon ilimi!
\v 4 Ta wurin wa ka sami taimako ka ke yin maganar waɗannan kalmomi? Wanne ruhu ne ya fito daga gare ka?
\s5
\v 5 Matattu suna rawar jiki, su waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukkan waɗanda su ke zama da su.
\v 6 Lahira ta na tsirara gaban Allah; hallakarwa da ke kanta ba rufe take ba a gare shi.
\s5
\v 7 Ya shimfiɗa arewa a sarari a kan abin da ke fili, ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.
\v 8 Ya ɗaure ruwaye a gizagizai, amma gizagizan ba a ƙarƙashinsu suke ba.
\s5
\v 9 Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa girgije a kanta.
\v 10 Ya zana kewayanta a kan iyakar fuskar ruwaye kamar layi tsakanin haske da duhu.
\s5
\v 11 Ginshiƙan samaniya sun girgiza, sun firgice sakamakon tsautawarsa.
\v 12 Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku; ta wurin saninsa ya hallakar da Rahab.
\s5
\v 13 Ta wurin numfashinsa yasa sararin sama yayi garau; da hannunsa ya sha zarar macijin nan mai gudu.
\v 14 Duba, amma waɗannan su ne yatsun hanyoyinsa; yaya ƙanƙantar raɗa da muke ji a gare shi! Wane ne ya gane tsawar ikonsa?"
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Ayuba ya fara magana, ya ce,
\v 2 "Yadda Allah na raye, wanda ya ɗauke mani adalci, Mai Iko, wanda yasa rayuwata ɗaci,
\v 3 har yanzu raina baya tare da ni, numfashi daga Allah ya cika hancina, wannan shi ne abin da zan yi.
\s5
\v 4 Leɓena ba zai faɗi mugunta ba, ko harshena ya hurta maganganun yaudara;
\v 5 ba zan taɓa yarda cewa ku ukun kun yi dai-dai ba; har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
\s5
\v 6 Ina rike da adalcina ba kuwa zan sake shi ba ya tafi; tunanina ba zai zarge ni ba idan dai ina raye.
\v 7 Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum; bari wanda ya ke gãba da ni ya zama kamar mutum marar adalci.
\s5
\v 8 Gama wacce sa zuciya ke ga mutum marar tsoron Allah sa'ad da Allah ya datse shi, sa'ad da Allah ya ɗauke ransa?
\v 9 Allah kuwa zai ji kukansa a lokacin da wahala ta same shi?
\v 10 Zai yi farinciki da kansa a wurin Mai Iko, zai yi kira ga Allah a dukkan lokatai?
\s5
\v 11 Zan koya maka game da hannun Allah; ba zan ɓoye tunanin Mai Iko ba.
\v 12 Duba, dukkan ku kun ga wannan da kanku; me yasa kuke yin wannan magana ta wawanci?
\s5
\v 13 Wannan shi ne rabon mugun mutum a wurin Allah, gãdo ne kuma wanda azzalumi zai karɓa daga wurin Mai Iko:
\v 14 Idan 'ya'yansa sun riɓamɓanya, zasu zama rabon takobi; zuriyarsa kuwa ba zata sami isasshen abinci ba.
\s5
\v 15 Duk wanda ya tsira za a bizne shi da annoba, gwaurayensu ba zasu yi makoki domin su ba.
\v 16 Ko da yake mugun mutum ya tsibe azurfa kamar turɓaya, tarin tufafi kamar laka,
\v 17 zai iya tara tufafi, amma adalan mutane zasu zuba a kai, mutanen kirki zasu raba azurfar a tsakaninsu.
\s5
\v 18 Ya gina gidansa kamar saƙar gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.
\v 19 Ya kwanta a gadon mai arzaki, amma ba zai ci gaba da yin haka ba, zai buɗe idanunsa, yaga komai ya tafi.
\s5
\v 20 Razana zata auko masa kamar ruwaye; iska zata tafi da shi da dare.
\v 21 Iskar gabas zata fyauce shi, zai tashi; zata share shi daga wurinsa.
\s5
\v 22 Zata jefar da kanta a kansa, babu tsayawa; zai yi ƙoƙari ya tsere daga hannunsa.
\v 23 Zata tafa hannuwanta a kansa domin ba'a; zata yi masa ƙara daga wurinsa.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Babu shakka akwai ma'adani na azurfa, a wurin da ake tace zinarya.
\v 2 Ana samun ƙarfe daga cikin ƙasa; a kuma narkar da tagulla daga dutse.
\s5
\v 3 Mutum ya kan kawar da duhu, ya kuma bincike zuzzurfar iyaka, ya haƙo duwatsun a lunguna masu sulɓi da ke cikin duhu baƙi ƙirin.
\v 4 Ya kan buɗe ƙyaure daga wurin da mutane ke zama, wuraren da ƙafar wani ba zata manta ba. Yakan kafa abin lilo nesa da mutane; yayi ta lilo zuwa da komawa.
\s5
\v 5 Daga cikin ƙasa ake samun abinci, takan juyo ƙarƙashinta kamar ta wurin wuta.
\v 6 Duwatsu ne wurin da ke samun shudin yakutu, zinariya ɗauke da ƙurarta.
\s5
\v 7 Tsuntsu mai cin nama bai san hanyarta ba, shaho ma da idanuwansa bai ganta ba.
\v 8 Namomi masu fahariya basu taɓa bin irin hanyar ba, ko zaki mai zafi ma bai taɓa wucewa can ba.
\s5
\v 9 Mutum yasa hannunsa a kan ƙanƙarar dutse, yana kuma iya tunɓuke tushen duwatsun daga saiwoyinsu.
\v 10 Yana kuma iya sarar magudanar ruwa cikin duwatsu; idannunsa kan ga kowanne abu mai daraja a can.
\v 11 Yana iya datse rafuffuka ya hana su gudu; ya binciko abin da ke ɓoye a can ya kawo shi a sarari.
\s5
\v 12 Daga ina za a samo hikima? Ina ne wurin haziƙanci?
\v 13 Mutum bai san darajarta ba; ko a samo ta a ƙasar masu rai.
\v 14 Zurfafan ruwaye a ƙarƙashin ƙasa sun ce, 'Bata cikina,' teku ta faɗa, 'Bata tare da ni.'
\s5
\v 15 Ba zata iya samuwa daga zinariya ba; ko azurfa bata yi nauyi kamar tamaninta ba.
\v 16 Ba zata yi kimanin zinariyar Ofir, tare da darajar baƙin dutse mai daraja ba ko saffir.
\v 17 Zinariya da madubi ba zasu yi dai-dai da tamaninta ba; ko kuma a musanyata da murjanin da aka yi da zinariya mai kyau.
\s5
\v 18 Kada ma a ambaci darajar murjani ko dutse mai walkiya; lallai tamanin hikima yafi shi.
\v 19 Duwatsu masu darajar Kush ba za a dai-dai su da tamaninta ba; ko kuma darajar tamaninta yafi na zinariya tsantsa.
\s5
\v 20 Daga ina hikima take fitowa? A wanne wuri kuma hazaƙa take?
\v 21 Hikima a ɓoye take daga idon dukkan abubuwa masu rayuwa, haka nan yake a ɓoye ga tsuntsaye da ke tashi a sammai.
\v 22 Hallaka da mutuwa sun ce, 'Mun ji ƙishin-ƙishin a kanta a kunnuwanmu.'
\s5
\v 23 Allah ya fahimci hanyar zuwa gare ta; ya san wurinta.
\v 24 Saboda yana ganin ƙarshen duniya, yana duban ƙarƙashin dukkan sammai.
\v 25 Yasa iska mai ƙarfi da ƙunshi daga ciki ta wurin auna ruwaye.
\s5
\v 26 Yayi ka'ida domin ruwan sama da hanya domin tsawa.
\v 27 Sai ya ga hikima, ya sanar da ita; ya tabbatar da ita; ya gwada ta.
\v 28 Ga mutane yace, 'Duba, tsoron Ubangiji -- shi ne hikima; rabuwa daga mugunta kuma ita ce hazaƙa.'"
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Ayuba yaci gaba da magana yace,
\v 2 "Oh, dama ina ma yadda nake a watanin da suka wuce ne? lokacin da Allah yake lura da ni,
\v 3 sa'ad da fitilarsa take haska mani kai, da kuma lokacin da nake tafiya cikin duhu ta wurin haskensa.
\s5
\v 4 Kash, dãma na tsaya yadda nake cikakke a kwanakina, sa'ad da abokantaka da Allah ke kan gidana,
\v 5 lokacin da Mai Iko ke tare da ni, 'ya'yana ke kewaye ni,
\v 6 sa'ad da aka rufe hanyata da madara, duwatsu kuma na fito mani da rafuffukan mai!
\s5
\v 7 A lokacin da nakan fito ƙofar birni, sa'ad da na zauna a wurin zamana a dandali,
\v 8 da samari sukan gan ni, sai su kawar da kansu daga gare ni don girmamawa, tsofaffi mutane kuma su miƙe tsaye domi na.
\s5
\v 9 Sarakuna na yin shiru da magana sa'ad da nazo; sai su ɗora hannuwansu a kan bakinsu.
\v 10 Muryoyin manyan mutane sun yi tsit, harshensu ya liƙe a dasashin bakunansu.
\s5
\v 11 Gama bayan da kunnuwansu suka ji ni, sai su albarkace ni; bayan da idanuwansu suka gan ni, sai su ba da shaida a kaina su kuma amince da ni
\v 12 domin nakan ceci duk matalauci sa'ad da yayi kuka, da kuma wanda bashi da uba kuma bashi da wanda zai taimake shi.
\v 13 Albarka ga wanda yake bakin mutuwa idan yazo gare ni; nakan sa zuciyar gwauraye ta yi waƙar murna.
\s5
\v 14 Na sa sutura ta adalci, ta rufe ni; gaskiyata ita ce kamar suturata da rawanina.
\v 15 Ni ne idon makafin mutane; ni ne ƙafaffun guragun mutane.
\v 16 Ni mahaifi ne ga mutane masu bukata; nakan yi bincike don in warware al'amari harma wanda ban san shi ba.
\s5
\v 17 Nakan karya muƙamuƙan mutum marar adalci; in fisge wanda aka zalunta daga cikin tsakanin haƙoransa.
\v 18 Sa'an nan nace, 'Zan mutu cikin gidana; zan riɓaɓɓanya kwanakina kamar tsabar yashi.
\v 19 Saiwoyina suna shimfiɗe cikin ruwaye, raɓa na sauka a dukkan dare a rassana.
\s5
\v 20 Daraja a gare ni kullum garau take, baka shi ne ƙarfina kullum sabo yake a hannuna.
\v 21 A gare ni mutane ke saurare; suna jira na, sun tsaya shiru su ji shawarata.
\v 22 Bayan na gama magana ba wanda ya sake wata magana kuma; maganata tana sauka kamar ruwa a kansu.
\s5
\v 23 Suna jira na kullum kamar yadda ake jiran ruwan sama; sun buɗe bakinsu sosai don su sha daga kalmomina, kamar yadda suke jiranruwan bazara.
\v 24 Na yi masu murmushi sa'ad da basu sa tsammaninsaba; ba su yi watsi da fara'ar fuskata ba.
\s5
\v 25 Nakan zaɓar masu hanya, in zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin sojojinsa, kamar wanda yake ta'azantar da masu makoki.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Yanzu waɗanda na girme su, sai ba'a kaɗai suke yi mani -- waɗannan matasa maza waɗanda iyayensu ban ma yarda in bar su suyi aiki tare da karnukan da suke kiwon garke tumakina ba.
\v 2 Lallai, ƙarfin hannuwan iyayensu maza, ba zasu iya taimako na ba--mutanen waɗanda ƙarfin balagarsu yake lalacewa?
\v 3 Sun rame daga talauci da yunwa; sai gaigayar ƙasa suke yi da duhu, cikin jeji da kufai.
\s5
\v 4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, doyar jeji ita ce abincinsu.
\v 5 Aka kore su daga cikin mutane ana bin su da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo ihu.
\v 6 Sai a kwazazzaban rafi suke zama, ramummukan ƙasa da kogwannin duwatsu.
\s5
\v 7 A cikin jeji suke ta kuka kamar jakai, sukan taru tare a ƙarƙashin sarƙaƙiya.
\v 8 Su 'ya'yan wawaye ne, lallai, 'ya'ya maza marasa suna a mutane! Aka kore su daga ƙasar tare da tsumagu.
\s5
\v 9 Amma yanzu na zama abin yiwa zambo, na zama abin magana a gare su.
\v 10 Suna ƙyamata ta, sun tsaya da nisa daga gare ni; basu daina tofa mani yawu a fuskata ba.
\v 11 Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙantar da ni, waɗanda suka yi mani ba'a sun hana ni sakewa in yi wani abu.
\s5
\v 12 A hannun damana 'yan iska sun taso mani; sun kore ni suna gãba da ni sun tura ni hanyarsu ta hallaka.
\v 13 Sun lalata hanyata, sun jawo bala'i domi na, ba wanda ya hana su.
\s5
\v 14 Sun zo suna gãba da ni kamar soja wanda yabi ta babbar kafar bangon birni; a tsakiyar hallaka sun naɗa kansu a kaina.
\v 15 Babban tsoro ya faɗo mani; an kore darajata kamar iska; wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.
\s5
\v 16 Yanzu raina yana kwararowa daga gare ni; kwanakin wahala sun same ni.
\v 17 A cikin dare ƙasusuwana na karkaɗawa; azaba tana gaigaya ta ba hutawa.
\s5
\v 18 Ƙarfin girman Allah yaci wuyan rigata; ya kuma kewaye ni kamar ƙarfin taguwata.
\v 19 Ya jefar da ni cikin laka; na zama kamar ƙura da toka.
\s5
\v 20 Na yi kuka a gare ka, Allah, amma ba ka amsa mani ba; na tashi tsaye, ka dai kalle ni kawai.
\v 21 Ka canja sai ka zama mara tausayi a gare ni; da ƙarfin hannunka ka tsananta mani.
\s5
\v 22 Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ta kora ni; ka jefa ni baya da gaba a cikin hadari.
\v 23 Gama na sani zaka kai ni ga mutuwa, a gidan da aka ƙaddara wa kowanne mai rai.
\s5
\v 24 Duk da haka, ba wanda ya isa ya miƙa hannunsa ya roƙi taimako idan ya faɗi? Babu wani da zai nemi taimako idan ya shiga cikin wahala?
\v 25 Ashe ban yi kuka saboda shi wanda yake cikin wahala ba? Ashe ban yi ɓacin rai saboda mutum mai bukata ba?
\v 26 Sa'ad da nasa bege don abin kirki, sai ga mugunta ta zo; sa'ad da nake jiran haske, sai duhu ya zo.
\s5
\v 27 Zuciyata tana cikin damuwa, bata huta ba; kwanakin wahala ya zo a kaina.
\v 28 Na tafi kamar wanda ke rayuwa cikin duhu, amma ba domin rana ba, na tsaya a gaban taron jama'a ina kukan neman taimako.
\v 29 Na zama ɗan'uwan dila, aminin jiminai.
\s5
\v 30 Fatata baƙa ce, ta faɗi daga gare ni; ƙasusuwana suna ƙuna da zafi.
\v 31 Saboda haka garayata ta juya ga waƙar makoki, sarewata kuma ta zama waƙoƙi ga waɗanda ke kuka.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Na yi alƙawari da idanuna; me zai sa in dubi budurwa har in yi sha'awa?
\v 2 Gama wanne irin rabo zan samu daga wurin Alla a sama, gãdon me kuma zan samu daga wurin Mai Iko a samaniya?
\s5
\v 3 Na kan yi tunanin masifa daga wurin mutane mara sa adalci, bala'i na masu aikata mugunta ne.
\v 4 Ko Allah ba ya ganin hanyoyina da dukkan matakallaina?
\s5
\v 5 Idan ina tafiya da rashin gaskiya, idan kafata tana hanzarin aikata yaudara,
\v 6 bari a auna ni da ma'aunin yadda Allah zai san halayena na kwarai.
\s5
\v 7 Idan ƙafata ta kauce daga hanya, idan kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna, idan akwai wani aibi ya wuce ta hanuwana,
\v 8 to bari na shuka, bari wani yaci, bari kuma amfanina ya tumɓuke.
\s5
\v 9 Idan zuciyata tayi sha'awar wata mace, idan har naje na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
\v 10 to bari matata tayi niƙan hatsi domin wani, bari waɗansu su kwanta a kanta.
\s5
\v 11 Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai; lallai, alƙalai ne zasu hukunta.
\v 12 Domin wuta mai ci zata hallaka, zata cinye har zuwa Abaddon, zata kone dukkan girbina har saiwa.
\s5
\v 13 Idan naƙi kulawa da roƙo domin adalci daga barorina maza da mata sa'ad da suka kawo koke-kokensu a kaina,
\v 14 to me zan yi lokacin da Allah ya tashi don ya hukuntar da ni? Sa'ad da yazo yi mani shari'a, ya ya zan amsa masa?
\v 15 Ai shi wanda yayi ni a mahaifa shi ne ya yi su kuma? Ba shi ne dai ya siffata mu dukka a cikin mahaifa ba?
\s5
\v 16 Idan na taɓa hana matalautan mutane daga sha'awarsu, ko idan nasa gwauruwar da mijinta ya mutu idanunta su dushe da kuka,
\v 17 ko kuwa naci ɗan abincina ni kaɗai ban bar waɗanda basu da iyaye maza suma su ci abincina ba--
\v 18 gama tun daga yarintaka marayu suka yi girma tare da ni kamar mahaifi, na lura da mahaifiyarsa, gwauruwa, daga cikin mahaifiyata.
\s5
\v 19 Idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura; ko idan naga wani mutum da bukata na rashin sutura;
\v 20 idan zuciyarsa bata albarkace ni ba domin bai ji dumi da ulun tumakina ba,
\v 21 idan na daga hannuna gãba da marayun mutane, don naga taimakona a ƙofar birni, sai a kawo ƙara a kaina!
\s5
\v 22 Idan na yi waɗannan abubuwa, bari kafaɗata ta ɓaɓɓalle daga in da su ke, bari hannuna ya karye daga mahadarsa.
\v 23 Gama firgici da bala'i daga wurin Allah; saboda ɗaukakarsa, ba zan iya yin kome a kan waɗannan abubuwa ba.
\s5
\v 24 Idan nasa zinariya abin fatana, idan nace ina da zinariya mai kyau, 'Kana nan yadda na ke da aminci;
\v 25 idan ina murna saboda dukiyata ta na da girma, ko saboda abin da na mallaka ne, sai su kawo s̀̀̀u a kaina!
\s5
\v 26 Idan na ga rana tana haske, ko wata yana tafiya da haskensa,
\v 27 idan zuciyata jarabtu a asirce, yadda bakina zai sumbace hannun a sujadarsu--
\v 28 wannan ma zai zama laifi wanda shari'a zata hukunta, gama na musanta Allah wanda ke sama.
\s5
\v 29 Idan ina murna saboda hallaka ta sami wanda ya ke maƙiyina, ko zan yiwa kaina barka ne, idan wahala ta same shi, zai kawo ƙarata!
\v 30 Lallai, ban ma yarda in bar bakina ya yi zunubi ta wurin tambaya don ransa tare da la'ana.
\s5
\v 31 Idan a rumfata akwai mutanen da suka ce, 'Wane ne zai sami wanda bai ƙoshi da abincin Ayuba ba?"
\v 32 (ko da baƙon da baya zama a dandalin birni, domin kullum ina buɗe ƙofufina ga mai tafiya), idan ba haka ba ne, sai a kawo ƙarata!
\s5
\v 33 Idan, kamar 'yan adam, na ɓoye zunubai na ta wurin ɓoye laifi a cikina
\v 34 (saboda ina jin tsoron babban taron jama'a, domin tsoron rainin iyalai gare ni, na yi shuru, ban ma iya fita waje ba), sai a kawo ƙarata!
\s5
\v 35 Oh, idan za a sami wani shi kaɗai ya ji ni! Duba a nan ga sa hannuna; bari Mai Iko ya amsa mani! Idan ni kaɗai na yi ƙarar maƙiyana a rubuce!
\v 36 Babu shakka zan ɗauke ta a buɗe a kan kafaɗata; zan sa ta kamar rawani.
\v 37 Zan furta a kansa lissafin takawa ta; a matsayin asirin sarki zan tafi wurinsa.
\s5
\v 38 Idan ƙasata tana kuka da ni, tare da ƙungiyoyinta,
\v 39 idan na ci amfaninta ba tare da biya ba, ko na yi sanaɗin mutuwar masu ita,
\v 40 bari ƙayayuwa su tsiro maimakon alkama, tsire tsire marasa amfani kuma maimakon bali." Maganganun Ayuba sun kare.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Sai mutanen uku suka daina ba Ayuba amsa saboda yana ganin kansa shi adali ne.
\v 2 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz daga iyalin Arama, ya husata da fushi a kan Ayuba saboda ya baratar da kansa maimakon Allah ya baratar da shi.
\s5
\v 3 Elihu ya fusata da fushi a kan abokansa uku saboda sun rasa amsawa Ayuba, duk da haka sun gani Ayuba ne ke da laifi.
\v 4 Yanzu Elihu ya jira ya yi magana da Ayuba, don sauran mutanen uku sun girme shi da shekaru.
\v 5 Sa'ad da Elihu ya ga babu wata amsa a bakunan waɗannan mutanen uku, har fushinsa ya yi ƙuna.
\s5
\v 6 Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya yi magana ya ce, "Ni yaro ne, ku manya ne sosai. Wannan ya sa na yi shuru, ban iya faɗa maku ra'ayina ba.
\v 7 Na ce, "Yawan kwana su yi magana; yawan shekaru kuma su koyar da hikima.
\s5
\v 8 Amma akwai ruhu a cikin mutum; numfashin Mai Iko ya ke ba da sani da basira.
\v 9 Ba manyan mutane ne kaɗai waɗanda suke da wayo da hankali ba, ko tsofaffin mutane kaɗai suke da sanin adalci da gaskiya.
\v 10 Don haka nace da ku, 'Ku saurare ni; zan kuma faɗa maku ta wa fahintar.'
\s5
\v 11 Duba, na jira domin inji maganarku; na kasa kunne da jin muhawararku, tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.
\v 12 Lallai, na saurare ku, amma duba, babu wanda ya kada Ayuba ko wanda ya bashi amsar maganganunsa.
\s5
\v 13 Ku yi hankali kada wani ya ce, "Mun sami hikima! Allah ne zai ci nasara a kan Ayuba; mutum mai mutuntaka ba zai iya ba.
\v 14 Gama Ayuba ba da ni ya ke magana ba, saboda haka ba zan amsa da irin amsarku ba.
\s5
\v 15 Waɗannan mutane uku abin ya cika masu ciki, ba su ƙara amsawa Ayuba ba; ba su da sauran abin da za su ce kuma.
\v 16 Ni kuma zan tsaya don su basu ce kome ba, don sun tsaya a wurin shiru, basu da wata amsa kuma?
\s5
\v 17 A'a, ni kuma zan ba da ta wa amsa; zan kuma faɗa masu na wa sanin.
\v 18 Gama ina cike da magana, ruhu da ke ciki na ya iza ni.
\v 19 Duba, kirjina ya na kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska. kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda ya ke shirin ya fashe.
\s5
\v 20 Zan yi magana saboda in huce, zan buɗe lebuna na in ba da amsa.
\v 21 Ba zan nuna san zuciya ba, ko kuma in yi wa wani mutum fadanci.
\v 22 Gama ni ban san yadda zan iya yi fadanci ba; idan nayi haka kuwa Mahaliccina zai ɗauke ni nan da nan.
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Amma yanzu, kai Ayuba, ina roƙon ka, ka saurari abin da zan ce, ka saurari dukkan maganganuna.
\v 2 Duba yanzu, na buɗe bakina; harshena ya yi magana da bakina.
\v 3 Kalmomina sun zo da gaskiyar zuciyata; leɓuna suna faɗar ilimi tsantsa.
\s5
\v 4 Ruhun Allah ne yayi ni; numfashin Mai Iko ne ya bani rai.
\v 5 Idan za ka iya ka amsa mani; ka shirya kalmominka dai-dai a gabana, kayi tsaye a kansu.
\s5
\v 6 Duba, ni kamar ka mu ke a wajen Allah; ni kuma daga yumɓu aka siffanta ni.
\v 7 Duba, razanata ba zata sa ka ji tsoro ba, ko matsawata ta zama da nauyi a kanka.
\s5
\v 8 Babu shakka maganar da ka yi na ji ta; na kuwa ji amon maganganunka,
\v 9 ni tsabtattace ne, ba wani laifi, bani da laifi, kuma ba wani zunubi a gare ni.
\s5
\v 10 Duba, Allah ya sami damar zargi na, ya ɗauke ni tankar maƙiyinsa.
\v 11 Ya sa ƙafaffuna a turu, ya na lura da dukkan hanyoyina.'
\v 12 Duba, a wannan kayi kuskure--zan baka amsa, gama Allah ya fi kowane mutum girma.
\s5
\v 13 Me yasa kake yi masa gunaguni? Baya lissafin kowanne abu da yayi.
\v 14 Gama Allah yakan yi magana sau ɗaya ne--i, har sau biyu, duk da haka mutum baya kula da ita.
\v 15 Cikin mafarki, ko cikin wahayi da dare, a sa'ad da dogon barci ya faɗo wa mutane, ana barci a kan gado--
\s5
\v 16 sai Allah ya buɗe kunnuwan mutane, ya tsorata su da faɗakarwarsa,
\v 17 don ya kawar da mutum daga zunubinsa da yayi nufi, ya kuma kawar da girmankai daga gare shi.
\v 18 Allah yakan hana ran mutum daga faɗawa rami, rayuwarsa daga haurawa zuwa mutuwa.
\s5
\v 19 A kan hori mutum kuma da cuta mai zafi a gadonsa, yayi ta fama da azaba a cikin ƙasusuwansa,
\v 20 saboda da ransa ya kyamaci abinci, kurwarsa ta ƙyamaci daɗinsa.
\s5
\v 21 Tsokar jikinsa ta rame ƙangayau yadda ba za a iya ganinta ba, ƙasusuwansa baza a iya gani ba, yanzu sun zama waje.
\v 22 Lallai, ranna yasa gab da shiga rami, ransa yana wurin waɗanda suke so su hallaka shi.
\s5
\v 23 Amma idan a ce akwai wani mala'ika wanda zai yi sulhu dominsa, mai sulhu, ɗaya daga cikin duban mala'iku, zai nuna masa abin da ke dai-dai da zai yi,
\v 24 idan mala'ikan da zai yi masa alheri ya faɗa wa Allah, 'Cece wannan mutum daga gangarawa zuwa cikin ramin; dana sami abin da zai fansa domin sa,'
\s5
\v 25 Naman jikinsa zai koma fiye da na yaro, zai komo irin kwanakin ƙarfin ƙuruciyarsa.
\v 26 Zai yi addu'a ga Allah, Allah kuma zai yi masa alheri, saboda ya ga fuskar Allah da murna. Allah zai ba mutumin nasararsa.
\s5
\v 27 Sai wannan mutum ya raira waƙa a gaban sauran mutane yace, 'Na yi zunubi, ban yi dai-dai ba, amma zunubi bai sa a hore ni ba.
\v 28 Allah ya fanshi raina daga tafiya can cikin rami, raina zai cigaba da ganin haske.
\s5
\v 29 Duba, Allah yayi dukkan waɗannan abubuwa ga mutum harma sau biyu, i, harma lokatai uku,
\v 30 ya komo da ransa daga rami, don a haskaka shi da hasken rai.
\s5
\v 31 Ka yi lura Ayuba, ka saurare ni, kayi shiru, zan yi magana.
\v 32 Idan kana da wani abu da zaka ce, ka amsa mani, yi magana, don in tabbatar maka kana dai-dai.
\v 33 Idan ba haka ba, sai kayi shiru ka ji ni, ka zauna shiru, zan kuwa koya maka hikima."
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Hakanan, Elihu ya ci gaba da magana:
\v 2 "Ku saurari kalmomina, ku masu hikima; ku ji ni, ku masu ilimi.
\v 3 Domin kunnuwa na gwada kalmomi kamar yadda faranti ke ɗanɗana abinci.
\s5
\v 4 Bari mu zaɓar wa kanmu abin da ke na adalci, mu kuma yiwa kanmu abin da ke mai kyau.
\v 5 Domin Ayuba yace ni adali ne, amma Allah ya ɗauke abin da ke dai-dai.
\v 6 Ba a ma la'akari da adalcina, sai aka ɗauke ni maƙaryaci, raunukana kuma basu warkuwa duk da yake bani da zunubi.
\s5
\v 7 Wanne irin mutum ne Ayuba wanda ke shan ba'a kamar ruwa,
\v 8 wanda ke tafiya da ma su yin mugunta, wanda kuma ke rayuwa tare da miyagu.
\v 9 Domin ya ce ba amfani mutum yayi abin da ke mai kyau a gaban Allah
\s5
\v 10 Ku saurare ni ku mutane masu fahimta Allah ya sauƙaƙe ace Allah yayi aikin mugunta, kuma Allah ya sha ƙarfin ace yayi zunubi,
\v 11 Domin yana sakawa kowanne mutum gwargwadon aikinsa, kowanne mutum kuma gwargwadon abin da ya aikata.
\v 12 Hakika Allah ba ya aikata mugunta, kuma mai iko dukka bai taɓa watsi da adalci ba
\s5
\v 13 Wane ne ya ɗora shi bisa duniya? Wane ne kuma ya ɗora duniya a ƙarƙashinsa?
\v 14 Shi kaɗai ne yasan abin da yake so ya aikata, in har ya taɓa tattaro ruhunsa da numfashinsa,
\v 15 daga nan sai dukkan talikai su lalace mutum kuma ya koma ƙura.
\s5
\v 16 I kuna da fahimta yanzu sai ku saurari wannan ku saurari ƙarar kalmomina.
\v 17 Ko wanda yaƙi adalci zai iya yin shugabanci? Ko zaku iya shari'anta Allah? Wanda ke da adalci da kuma girma?
\s5
\v 18 Allah wanda ke cewa da sarki kai ɗan tawaye ne? ko kuma ya ce da masu daraja ku miyagu ne'?
\v 19 Allah wanda baya nuna tara ga shugabanni kuma baya la'akari da mawadata fiye da matalauta, domin dukkansu aikin hannunsa ne.
\v 20 A cikin ɗan lokaci sukan mutu; da tsakar dare za a girgiza mutane zasu kuwa shuɗe; za a kwashe ƙarfafan mutane, amma ba ta hannuwan mutum ba.
\s5
\v 21 Domin idanun Allah suna bisa hanyoyin mutum; yana ganin dukkan sawayensa.
\v 22 Babu duhu, ko dishi-dishi inda ƙofofin laifofi zasu ɓoye kansu,
\v 23 Domin Allah baya bukatar ya sake yiwa mutum ƙwanƙwanto; babu bukatar kowanne mutum yaje gabansa domin alƙalanci.
\s5
\v 24 Ya kakkarya mutane masu girma gunduwa-gunduwa domin tafarkinsu da ke bukatar ƙarin bincike; ya ɗora waɗansu a madadinsu.
\v 25 Ta wannan fannin yasan abin da suke yi; ya kaɓantar da waɗannan mutane da dare an kuma hallakar da su.
\s5
\v 26 A idon sauran, ya karkashe su saboda miyagun ayyukansu kamar masu aikata miyagun laifofi,
\v 27 saboda sun juya masa baya sun kuma ƙi yin la'akari da dukkan tafarkunsa.
\v 28 Ta wannan hanya, suka sa kukan mutane matalauta yazo gare shi; yaji kukan waɗanda ake zalunta.
\s5
\v 29 In ya yi shiru wane ne zai bashi laifi? in ya ɓoye fuskarsa, wane ne zai ji shi? Yana mulkin al'uma haka kuma kowa,
\v 30 domin kada mutum marar tsoron Allah ya yi mulki, domin kada a sami wanda zai jefa mutane cikin tarko.
\s5
\v 31 A misali in a ce wani zai ce da Allah, ' Hakika nayi laifi, amma bazan ƙara yin laifi ba,
\v 32 koya mani abin da bazan gani ba; Nayi zunubi, amma bazan ƙara yinsa ba.'
\v 33 Kana tunanin cewa Allah zai hori zunubin na wancan mutum, tun da yake kun ƙi abin da Allah ke yi? Dole ne kuyi zaɓi, ba ni ba. To sai ku faɗi abin nan da kuka sani.
\s5
\v 34 Mutane masu fahimta zasu ce da ni-hakika, duk mutum mai fahimta da ya ji ni zai ce,
\v 35 Ayuba na yin magana ba tare da sani ba; kalmominsa kuma basu da hikima.'
\s5
\v 36 In da za a sa Ayuba a ma'auni na ɗan lokaci saboda maganarsa kamar ta miyagun mutane.
\v 37 Domin ya ƙara tawaye a kan zunubinsa; ya tafa hannuwansa cikin zagi a tsakiyarmu; ya jera kalmomi gãba da Allah."
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Bugu da ƙari Elihu ya ƙara cewa,
\v 2 "Kana tunanin hakan dai-dai ne a lokacin da kayi magana, 'Hakina a gaban Allah'?
\v 3 Domin kayi tambaya, cewa wanne amfani yake da shi a gare ni?' kuma 'Ashe bai fi ba in da a ce nayi zunubi?'
\s5
\v 4 Zan amsa maka kai da abokanka.
\v 5 Ka dubi rana a sama, ka gan ta; ka dubi sararin sama wanda ya fi ka tsayi.
\s5
\v 6 In ka yi zunubi a ina ka sa Allah ya ji zafi? In laifofinka su jeru zuwa sama, me zaka yi masa?
\v 7 In kana da adalci me zaka iya bashi? Me zai karɓa daga hanunka?
\v 8 Aikin muguntarka na iya cutar da mutum, kamar yadda kake mutum, aikin adalcinka kuma na iya amfanar wani ɗan mutum.
\s5
\v 9 Sabo da ayyukana na tsanantawa, mutane suka yi kuka; suka nemi taimako daga damatsan ƙarfafan mutane.
\v 10 Amma ba wanda yace ina Allah mahallicina, wanda ke bada waƙoƙi da dare,
\v 11 wanda ke koyar damu fiye da yadda yake koyar da dabbobin duniya, wanda kuma yasa muka fi tsuntsayen sararin sama hikima?'
\s5
\v 12 Suka yi kuka a can amma Allah bai amsa ba saboda girman kan miyagun mutane.
\v 13 Hakika Allah ba zai ji kuka na wawanci ba, maɗaukaki ba zai saurare shi ba.
\v 14 Yaya kuma zai ƙi amsa maka in ka ce baka ganinsa, cewa kuma ƙararka na gabansa, da kuma cewa kana jiransa!
\s5
\v 15 Yanzu kuma kuka ce fushinsa baya yin hukunci, kuma baya ko ɗan kula da laifofi.
\v 16 To Ayuba ya buɗe bakinsa domin kawai ya faɗi maganar; ya jera kalmomi ba tare kuma da sani ba."
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Elihu yaci gaba ya ce,
\v 2 Bani dama in yi magana 'yar kaɗan, zan kuma nuna maka wani abu domin ina da ɗan sauran abin faɗi domin in kare Allah.
\v 3 Zan sami fahimtata daga can nesa; Zan yi la'akari da adalcin da ke na Mahallicina.
\s5
\v 4 Domin hakika kalmomina baza su zama ƙarya ba; wani wanda yayi girma cikin sanina tare da kai.
\v 5 Duba Allah mai iko ne, kuma baya rena kowa; yana da ƙarfi cikin ikon fahimta.
\s5
\v 6 Baya kiyaye rayukan miyagun mutane, amma a memakon haka ya kan yi abin da ke dai-dai ga waɗanda ke shan wahala.
\v 7 Baya kawar da idanunsa daga adalan mutane amma yakan ɗora su a kursayi kamar sarakuna har abada, kuma sun ɗaukaka sosai.
\s5
\v 8 In an ɗaure su da sarƙoƙi da karkiya ta wahala,
\v 9 to sai ya baiyana musu abin da suka yi, da laifofinsu da girman kansu.
\s5
\v 10 Hakannan ya buɗe kunnuwansu ga umarnansa, da dokokinsa ya kuma gargaɗe su da su juyo daga aikata laifofi.
\v 11 In sun saurare shi sun kuma yi masa sujada, zasu yi kwanakinsu cikin wadata, shekarunsu kuma cikin wadar zuci.
\v 12 Duk da haka, in basu saurare shi ba, zasu hallaka ta wurin takobi; zasu mutu saboda basu da sani.
\s5
\v 13 Marasa tsoron Allah a zuciya na ajiye wa kansu fushi; basu yi kukan neman temako ba koma da a lokacin da Allah ya ɗaure su.
\v 14 Sun mutu cikin ƙuruciyarsu; rayukansu sun kai ga ƙarshe a cikin ɗabi'ar karuwanci.
\s5
\v 15 Allah na kuɓutar da waɗanda ake tsananta wa, ya buɗe kunnuwansu ta wurin tsananinsu.
\v 16 Hakika zai so ya jawo ka daga cikin tsanani zuwa wuri inda ba ƙunci, kuma inda za a shirya teburinka da abinci mai cike da kitse.
\s5
\v 17 Amma ka cika da hukunci ga miyagun mutane; hukuncisu ne ke riƙe ka.
\v 18 Kar ka yarda fushinka ya ruɗe ka ga yin zagi, ko kuwa girman fansa yasa ka ka kauce.
\s5
\v 19 Ko wadatarka zata amfane ka, domin kada ka shiga damuwa, ko kuwa ƙarfinka zai taimake ka?
\v 20 Kada kayi marmarin da zaka yi zunubi ga waɗansu, lokacin da a ka kama mutane a cikin wurarensu.
\v 21 Ka lura domin kada ka koma ga yin zunubi saboda an gwada ka da tsanani domin kada kayi zunubi.
\s5
\v 22 Duba Allah ya sami ɗaukaka cikin ikonsa, wane ne mai koyarwa kamarsa?
\v 23 Wa ya taɓa bashi umarni game da tafarkinsa? Wane ne zai iya cewa da shi, ka aikata rashin adalci?
\v 24 Tuna ka yabi ayyukansa, wanda mutane suka rera waƙarsu.
\s5
\v 25 Dukkan mutane sun duba waɗannan ayyukan, amma daga nesa ne kawai suke ganin su.
\v 26 Duba Allah nada girma, amma bamu fahimce shi sosai ba; yawan shekarunsa basu ƙidayuwa.
\s5
\v 27 Domin ya jawo ɗigon ruwa wanda yasa ya zama ruwan sama daga taskarsa,
\v 28 wanda giza-gizai ke sheƙowa daga sama cikin wadatuwar mutum.
\v 29 Hakika ko akwai wanda zai iya fahimtar yawan faɗin yadda giza-gizai suke da kuma yadda tsawa take daga gare shi?
\s5
\v 30 Duba ya shimfiɗa walƙiyarsa a kewaye da shi ya rufe sauyoyin teku.
\v 31 A wannan hanya ya hukunta mutane kuma yana bada abinci a yalwace.
\s5
\v 32 Ya cika hannuwansa da walƙiya har sai da ya umarce ta takai iyakarta.
\v 33 Tsawarta takan gargaɗi hadari, dabbobima kan ji tana zuwa.
\s5
\c 37
\cl Sura 37
\p
\v 1 Hakika zuciyata ta firgita a kan wanan; an cire shi daga wurinsa.
\v 2 Ku saurara, i ku saurari ƙarar muryarsa, ƙarar da ke fita daga bakinsa.
\v 3 Ya fitar da ita waje a ƙarƙashin dukkan sararin sama, ya kuma aika da walƙiyarsa zuwa iyakokin duniya.
\s5
\v 4 Sai wata murya tayi ruri a bayansa, yayi tsawa da muryar darajarsa; bai hana mariƙin walƙiya ba a lokacin da aka ji muryarsa.
\v 5 Allah yayi tsawa mai ban mamaki da muryarsa; yayi manyan abubuwa da ba zamu iya bada da bayaninsu ba.
\v 6 Domin yace da ƙanƙara, 'faɗo a duniya', haka nan ruwan sama shima ya sheƙo, 'Ya zama babbar mafitar ruwa.'
\s5
\v 7 Ya dakatar da hanun kowa daga aiki, domin dukkan mutanen daya hallitta suga ayyukansa.
\v 8 Sai dabbobi su gudu zuwa maɓoya su kuma zauna a kogonninsu.
\v 9 Hadari yakan zo daga mazauninsa a kudu kuma sanyi ya tattaru daga iskar da ta warwatsu a arewa.
\s5
\v 10 Ta wurin numfashin Allah a ka bayar da ƙanƙara; sai ruwa ya daskare kamar ƙarfe.
\v 11 Hakika ya kan tarwatsa baƙin girgije da ikonsa; ya warwatsa walƙiyarsa a cikin giza-gizai.
\s5
\v 12 Yakan sarrafa giza-gizai ta wurin bishewarsa, domin su yi duk abin da ya umarce su a sararin duniya.
\v 13 Yasa duk wannan ya faru; waɗansu lokutan yana faruwa domin gyara, waɗansu lokutan domin ƙasarsa, waɗansu lokutan su zama ayyukan amintaccen alkawari.
\s5
\v 14 Ayuba ka saurari wannan; ka dena kayi tunani kan al'amuran Allah masu girma.
\v 15 Ko ka san yadda Allah ya shimfiɗa giza-gizai ya kuma sa walƙiya ta haskaka a cikin su
\s5
\v 16 Ko ka fahimci tashin giza-gizai, da ayyukan ban mamaki na Allah, wanda ke da cikakken sani?
\v 17 Ko ka fahimci yadda tufafinka suka zama da zafi lokacin da ƙasar ta tsaya saboda iska ta taso daga kudu?
\s5
\v 18 Zaka iya shimfiɗa rana kamar yadda zai yi, wadda keda ƙarfi kamar madubi an kuma zuba shi kamar ƙarfe?
\v 19 Koya mana abin da za mu ce da shi, domin ba zamu iya shimfiɗa gardamarmu bisa tsari ba saboda duhun tunaninmu.
\v 20 Ko za a faɗa masa abin da naso yi masa magana? Ko mutum zai so a haɗiye shi?
\s5
\v 21 Yanzu kuma mutane baza su iya duban rana ba lokacin da tayi zafi a sararin sama ba bayan iska ta wuce ta share giza-gizanta.
\v 22 Daga cikin arewa ake samun wadatar zinariya-a sama Allah ya isa aji tsoronsa cikin daraja.
\s5
\v 23 Ga mai iko dukka, ba zamu iya samunsa ba! Yana da girma cikin iko; baya ƙuntatawa adalci da cikakakken adalci.
\v 24 Saboda haka mutane ke tsoronsa. Baya sauraron waɗanda ke da hikima a cikin tunaninsu."
\s5
\c 38
\cl Sura 38
\p
\v 1 Sai Yahweh ya kira Ayuba ta cikin gawurtacciyar guguwa yace,
\v 2 "Wane ne wannan da ke kawo duhu domin shirye shirye ta wurin kalmomin da ba ilimi?
\v 3 Yanzu sai ka yi ɗammara kamar namiji domin zan tambaye ka, kuma dole ne ka ba ni amsa.
\s5
\v 4 Ina ka ke sa'ad da na shimfiɗa ginshiƙan duniya? Faɗa mini, in kana da isarshiyar ganewa.
\v 5 Wane ne ke aiyana inda iyakokinta? Faɗa mini, in ka sani. Wane ne ya miƙa fitaccen layi a kan ta?
\s5
\v 6 A kan me a ka kafa ginshiƙanta? wane ne ya ɗora dutsen kan kusurwarta?
\v 7 lokacin da taurarin asubahi suka rera waƙa tare kuma dukkan 'ya'yan Allah suka yi sowa domin farinciki?
\s5
\v 8 Wane ne ya kulle tekuna da ƙofofi lokacin da suka tumbatsa, inda ta zama kamar tazo daga mahaifa-
\v 9 lokacin da nayi giza-gizai su zama suturarta, kuma baƙin duhu ya zama babbar iyakokinta?
\s5
\v 10 Cewa lokacin da nasa alamomi a kan tekuna da kuma iyakokina,
\v 11 da kuma lokacin dana sa kuryoyin ƙofofinta, lokacin kuma da nace da ita, 'Zaki iya zuwa daga wannan nisan, amma ba ci gaba; nan ne zan sa iyakoki ga wannan fahariyar ta raƙuman ruwanki.'
\s5
\v 12 Ka taɓa ba da umarni ga safiya, ko ka sa faɗuwar rana ta san wurinta,
\v 13 domin ta jira iyakokin duniya ta kuma kakkaɓe miyagu daga cikin ta?
\s5
\v 14 An canja fasalin duniya kamar yadda yunɓu ke canjawa a ƙarƙashin hatimi; dukkan abubuwa sukan tsaya a kanta a sarari kamar gezar sutura.
\v 15 Daga miyagu sai aka ɗauke haskensu; dantsensu da ya ɗaukaka sai aka kakkarya shi.
\s5
\v 16 Ka taɓa zuwa maɓɓuɓɓugan ruwan tekuna? ka taɓa yin tafiya a wuri mafi zurfi?
\v 17 Ko an taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa, ka taɓa ganin ƙofofin inuwar mutuwa?
\v 18 Ko ka fahimci duniya da duk cikarta? faɗa mini in ka san ta dukka.
\s5
\v 19 Ina hanyar da haske ke bi domin hutawa-game da dare kuma ina nasa wurin?
\v 20 Zaka iya yi wa haske da dare jagora zuwa wuraren aikinsu? Zaka iya samun hanya domin su bi su koma gidajensu!
\v 21 Babu shakka ka sani, domin an haife ka a lokacin; shekarunka kuma suna da yawa!
\s5
\v 22 Ka taɓa zuwa ma'ajiyar sino, ko ka taɓa ganin ma'ajiyar ƙanƙara,
\v 23 waɗannan abubuwan da na adana na tsawon lokaci saboda masifa, domin ranar hargitsi da yaƙe-yaƙe?
\v 24 Ina ne sashen da walƙiya ke warwatsuwa ko kuma inda ake warwatsa iska daga gabas akan duniya?
\s5
\v 25 Wane ne ya yi kwazazzaban da ruwan damina ke bi, ko kuma wane ne ya yi wa aradu hanya,
\v 26 yasa tayi ruwa a bisa ƙasa inda ba wani mutum da ke wurin, da kuma jeji, inda ba kowa,
\v 27 don ƙosar da yasassun wurare ya kuma sa ciyayi su firfito?
\s5
\v 28 Ko ruwan sama yana da uba, ko kuma wane ne ya zama uba ga raɓa?
\v 29 Daga mahaifar wa ƙanƙara ke zuwa? Wane ne ya kafa daɓen hasken sararin sama?
\v 30 Ruwaye kan ɓoye kansu su zama kamar dutse; cikin zurfafa kuma ya zama daskararru
\s5
\v 31 Zaka iya kafa sarƙoƙi kan taurari na musamman ko ka datse sarƙar Oriyon?
\v 32 Za ka iya yiwa dandazon taurari jagora su baiyana a lokutan da suka dace? Zaka iya yi wa damisa da 'ya'yanta jagora?
\v 33 Ko ka san sharruɗan sararin sama? Zaka iya saita wurin da sararin sama ke mulki a kan duniya?
\s5
\v 34 Zaka iya tada murya har zuwa cikin giza-gizai, domin ruwa mai yawa ya rufe ka?
\v 35 Zaka iya aika cincirindon walƙiya domin su fita, domin suce da kai, ga mu nan'?
\s5
\v 36 Wane ne ya bayar da hikima a cikin giza-gizai ko kuma ya bada fahimta ga masu tatsuniya?
\v 37 Wane ne zai iya ƙirga giza-gizai ta wurin fasaharsa? Wane ne zai iya kwararo ruwan sararin sama,
\v 38 lokacin da ƙura ta murtuke ƙasa kuma ta murtuke tare?
\s5
\v 39 Zaka iya kamo abin da zakanya zata ci? ko kuma ka iya ƙosar da marmarin 'ya'yan zaki,
\v 40 lokacin da suke kuyakuyai a cikin kogonninsu suke kuma cikin inuwa a ɓoye suna fako?
\s5
\v 41 Wake bada kamammu ga hankaki lokacin da ƙananansu suka yi kuka ga Allah suka kuma yi yako saboda ƙarancin abinci?
\s5
\c 39
\cl Sura 39
\p
\v 1 Ko ka san lokacin da awakin jeji ke renon ƙananansu a cikin duwatsu? Zaka iya jira lokacin da kishimai ke maza?
\v 2 Zaka iya ƙirga watannin da suke kammala ɗaukan ciki? Ka san lokacin da suke renon 'ya'yansu?
\s5
\v 3 Sukan durƙusa su haifi 'ya'yansu, daga nan su gama zafin naƙudarsu.
\v 4 'Ya'yansu kan yi ƙarfi su yi girma a cikin saura, sai su tafi ba su kuma ƙara dawowa.
\s5
\v 5 Wane ne ke 'yantar da jakin jeji? wane ne ke kwance dabaibayin jaki,
\v 6 gidan wa na yi a Arabah, gidansa a ƙasa mai gishiri.
\s5
\v 7 Sai ya yi dariyar reni ga hayaniyar cikin birni; ba ya jin tsawar mai tuƙi.
\v 8 Ya yi ta gararanba a kan duwatsu a matsayin makiyayarsa; a can ya yi ta neman koren tsiron da zai ci.
\s5
\v 9 Ko takarkarin jeji zai yi murna ya bauta maka? Ko zai so ya tsaya a wurin kwaminka?
\v 10 Za ka iya riƙe jakin jeji da igiya lokacin da ya fusata? Za ka iya baje kwarurruka a lokacin da ya rarake ka?
\s5
\v 11 Ka iya amincewa da shi domin yana da ƙarfi sosai? Zaka iya bar masa aikinka yayi maka?
\v 12 Zaka iya dogara gare shi domin ya kawo maka hatsinka gida, ya tattara hatsi domin masussukarka?
\s5
\v 13 Fukafukan jimina na da faɗi sosai, to amma ko dogayen gashin fuka-fukan da kuma ƙananan gasusuwan zasu iya kare ta?
\v 14 Domin ta kan bar ƙwaiƙwayenta a ƙasa, ta kan barsu su sha ɗumi a cikin ƙura,
\v 15 takan manta cewa sawaye zasu iya farfasa su ko kuma dabbobin jeji su tattake su.
\s5
\v 16 Takan azabtar da 'ya'yanta kamar ba ita ta haife su ba; bata jin tsoro kada naƙudarta ta zama a banza,
\v 17 domin Allah bai bata hikima ba kuma bai bata wani fahimta ba.
\v 18 Lokacin da take gudu takan yi dariyar wulaƙanci ga doki da kuma mahayin dokin.
\s5
\v 19 Ka ba doki ƙarfinsa ne? kai ne ka yiwa wuyansa ado da dogon gashi mai sheƙi?
\v 20 Ka taɓa sa shi ya yi tsalle kamar bãbe? Girman haniniyarsa abin tsoro ne.
\s5
\v 21 Yana haniniya da ƙarfi, yana kuma murna da ƙarfinsa; yakan fita domin ya tunkari makamai.
\v 22 Ya kan rena tsoro kuma baya alhini; baya kafcewa takobi.
\v 23 Kwari da bãka na hararsa, tare da sheƙin mãshi da dogon ƙarfe mai tsini.
\s5
\v 24 Yana haɗiye ƙasa cikin ƙarfi ya murtuke ta a lokacin da ya ji ƙarar ƙaho, baya tsayuwa wuri ɗaya.
\v 25 Duk lokacin da ya ji ƙarar ƙaho, yakan ce, Aha! Ya kan sunsini yaƙi daga nesa-ƙara mai ƙarfi da ihun kwamandoji da hayaniyarsu.
\s5
\v 26 Ta wurin hikimarka ne shaho ke miƙar da fuka-fukansa ya fuskanci kudu da su?
\s5
\v 27 Ko ta wurin umarninka ne gaggafa ke yin sheƙarta a can ƙonƙoli?
\v 28 Yakan zauna a can ƙonƙolin itace yakan yi sheƙarsa a reɗimar rassa, ya zama mafakarsa.
\s5
\v 29 Daga can yake duban abincinsa idanunsa na hangen su daga can nesa, hakanan
\v 30 'Ya'yanta kan sha jini a inda aka karkashe mutane, a can yake.
\s5
\c 40
\cl Sura 40
\p
\v 1 Yahweh yaci gaba da yiwa Ayuba magana cewa,
\v 2 "Ko duk wani da ke ƙoƙarin ganin laifi zai iya ƙoƙarin yi wa Mafi iko dukka gyara? Shi wanda ke gardama da Allah sai ya amsa."
\s5
\v 3 Sai Ayuba ya amsawa Yahweh cewa,
\v 4 "'Duba ni da ban can-canta ba; yaya zan amsa maka? Na sa hanunna a kan bakina.
\v 5 Sau ɗaya na yi magana, kuma ba zan amsa ba; hakika sau biyu ne, amma ba zan ci gaba da yi ba."
\s5
\v 6 Sai Yahweh ya amsawa Ayuba daga cikin hadari yace,
\v 7 "Yanzu sai ka yi wa kanka ɗammara kamar jarumi, domin zan tambaye ka tambayoyi, kuma dole ne ka amsa mini.
\s5
\v 8 Ko hakika za ka ce ba ni da adalci, ko za ka hukunta ni domin ka nuna mini cewa ka yi dai-dai?
\v 9 Ko kana da damatsa kamar na Allah? Ko za ka iya yin tsawa da murya kamar sa?
\s5
\v 10 To ka yi wa kanka sutura cikin ɗaukaka da ƙima, ka yi wa kanka kwalliya da daraja.
\v 11 Ka baje kewaye da fushinka, ka dubi kowanne mai fahariya ka ƙasƙantar da shi.
\s5
\v 12 Ka duba duk mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake miyagu a inda suke tsayiwa.
\v 13 Ka bisne su tare a ƙasa, ka kulle su a ɓoyayyen wuri,
\v 14 Daga nan zan yi la'akari da kai da kuma sanin cewa hannunka na dama zai cece ka.
\s5
\v 15 Yanzu ka duba dodon ruwa, lokacin da nayi a lokacin da na halice ka, yana cin ciyawa kamar takarkari,
\v 16 Yanzu duba, ka ga yadda ƙarfinsa ke ƙirjinsa, ikonsa kuma yana cikin tumbinsa.
\s5
\v 17 Ya mayar da bindinsa kamar sidar, haƙoransa a haɗe suke.
\v 18 Ƙasusuwansa kamar cikin ƙarfe suke, ƙafafunsa kuma kamar makaran ƙarfe suke.
\s5
\v 19 Shi ne sarki a cikin hallitar Allah. Allahn da ya yi shi ne kawai ke iya kayar da shi,
\v 20 Domin tuddai ne ke ba shi abinci, sauran dabbobi kuma na kusa da wurin suna wasa a kusa.
\v 21 Yana kwance can cikin lollokin ganyaye.
\s5
\v 22 Ganyaye masu toho sun rufe shi da inuwarsu duhuwar itatuwa ta shinge shi. Duba
\v 23 Idan rafi yayi ambaliya ba ya fIrgita, yana da ƙarfin hali ko da ruwan Yodan zai kawo masa iya bakinsa.
\v 24 Ko wani zai iya kama shi da ashifta, ko ya iya huda hancinsa ta wurin yaudara?
\s5
\c 41
\cl Sura 41
\p
\v 1 Ko za ka iya jawo Lebiyatan da ƙugiyar kamun kifi? za ka iya ɗaure wuyanta da sarƙa?
\v 2 Za ka iya sa igiya a hancinta? ko ka iya huda cikin bakinta da ƙugiya? lokacin da ta ke yi maka gurnani
\v 3 Ko za ta ji daɗinka? Ko za ta yi maka magana mai lumana?
\s5
\v 4 Kuna da yarjejeniya da ita kan cewa ba za ka mai da ita baiwarka ba har abada?
\v 5 ko za ka iya wasa da ita kamar yadda zaka yi da tsuntsu? Za ka iya ɗaure ta kamar bayinka mata?
\v 6 Ko masunta zasu iya ƙulla wata yarjejeniya dominta? Ko zasu iya yin fataucinta a cikin fatake?
\s5
\v 7 Za ka cika maɓoyarsa da ƙayayuwa, Ko kansa da mãsun kamun kifi?
\v 8 Ka ɗora hanunka bisansa sau ɗaya tak daga nan za ka san yaƙi ba kuma za ka ƙara yinsa ba.
\v 9 Duba duk mai begen yin hakan ƙarya yake yi; ba wanda za a jefa masa a gabansa da ba zai tattake ba.
\s5
\v 10 Ba wanda zai iya tarar dorinar ruwa ba tare da ya furgita ba?
\v 11 Wane ne ya fara ba ni wani abu domin in biya shi? Duk abin da ke ƙarƙashin sararin sama nawa ne.
\v 12 Ba zan yi shiru ba game da ƙafafun dorinar ruwa, da kuma game da al'amarin ƙarfinta ba, ba kuma game da tagomashin hallitar da take da ita ba.
\s5
\v 13 Wane ne zai iya yaye masa wannan lulluɓin na samansa? Wane ne zai iya ratsa garkuwoyinsa masu ninki biyu?
\v 14 Wane ne zai iya buɗe ƙofofin fuskarsa-zagaye da haƙoransa masu banrazana?
\v 15 bayansa an yi shi ne da garkuwoyi aka harhaɗa su wuri ɗaya, kamar da wata rufarfiyar alama.
\s5
\v 16 Suna marmatse da juna domin kada iska ta iya ratsa su, suna harhaɗe da juna.
\v 17 Suna manne da juna, domin kada a ɓamɓare su.
\v 18 Haske na walƙatawa daga gurnaninsa; haskensa kamar na hasken fitowar rana.
\s5
\v 19 Daga cikin bakinsa tartsatsin wuta na fita.
\v 20 Daga cikin hancinsa kuma hayaƙi na fita kamar na matoyar tukunya da ta toyu ta yi zafi sosai.
\v 21 Numfashinsa ne ke samar da gawayin wutar; wuta na fita daga bakinsa.
\s5
\v 22 Wuyansa na da ƙarfi, masifa na rawa a gabansa.
\v 23 Maɗaukan jikinsa a harhaɗe suke tare, suna kafe a jikinsa; baza su iya ciruwa ba.
\v 24 Zuciyarsa na da ƙarfi kamar dutse, hakika tana da tauri kamar dutsen niƙa.
\s5
\v 25 Sa'ad da ya miƙar da kansa tsaye alloli ma kan firgita saboda tsoro, sukan ja baya.
\v 26 In takobi ya sare shi, ba ya yi masa komai- hakama mãsu da sauran makamai duk ba su yi masa komai.
\v 27 Ya na ganin kibiya kamar rauga ce kawai, namijin ƙarfe kuma kamar abin da tsatsa ta riga ta cinye.
\s5
\v 28 Kibiya ba ta sa shi gudu; a gare shi duwatsu masu sulɓi kamar ƙaiƙai suke.
\v 29 Rundunoni kuma kamar tattakar ciyawa; ya kan yiwa walƙiyar kibiya dariya.
\v 30 Ƙananan sassansa kamar rusarshiyar masana'antar tukwane ce, yakan bar wuri a damalmale kamar wurin da a ka yi kwaɓar fitar da zinariya da azurfa.
\s5
\v 31 Ya kan haƙa wuri ya yi zurfi ya zama kamar tukunyar dafa ruwa; ya kan mayar da teku ta zama kamar tukunyar mai.
\v 32 Ya kan sa haske ya haskaka bayansa; wani zai yi tunanin yadda zurfin suma mai furfura take.
\s5
\v 33 A cikin duniya babu wanda ke dai-dai da shi, wanda aka yi shi ya zama da rashin tsoro.
\v 34 Yana ganin duk wani abu da ke taƙama; shi sarki ne a kan dukan 'ya'yan masu taƙama.
\s5
\c 42
\cl Sura 42
\p
\v 1 Daga nan sai Ayuba ya amsawa Yahweh ya ce,
\v 2 "Na sani zaka iya yin komai, kuma ba wani nufi naka da ba zai cika ba.
\v 3 Wane ne wannan da ke ɓata shiri ba tare da ilimi ba? Hakika, na faɗi abubuwan da ban fahimta ba, abubuwan da ke da wahalar fahimta a gare ni, waɗanda ban sani ba.
\s5
\v 4 Ka ce da ni, 'Yanzu ka saurara, zan yi magana; zan tambaye ka abubuwan da za ka faɗa mini'.
\v 5 Na ji labarinka da jin kunnuwana, amma yanzu na ganka.
\v 6 Domin haka na rena kaina ina hurwa cikin toka da ƙura.
\s5
\v 7 Sai ya zamana bayan ya faɗi waɗannan maganganu ga Ayuba, sai Yahweh yace da Elifhas Batishmine, fushina yayi ƙuna a kanka da kai da abokanka guda biyu, domin ba ku yi mani maganar da ta dace ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi ba.
\v 8 To yanzu sai ku tanada wa kanku shanu bakwai da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa baiko na ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi muku addu'a, zan kuma amsa addu'arsa, domin kada in yi fushi da ku saboda wawancinku, domin ba ku faɗi abin da ya dace game da ni kamar yadda Ayuba bawana ya yi ba."
\v 9 Sai Elifas da Bildad Bashune, da Zofar Bana'ame suka je suka yi kamar yadda Yahweh ya umarce su, Yahweh kuma ya karɓi Ayuba.
\s5
\v 10 Bayan Ayuba ya yi addu'a domin abokansa, Yahweh ya komo masa da wadatarsa. Yahweh ya ninka wa Ayuba wadatarsa fiye da ta dã.
\v 11 Daga nan 'yan'uwan Ayuba mata, da duk waɗanda suka san shi a dã suka zo suka ci abinci tare da shi a gidansa. Suka nuna tausayinsu da kuma ta'aziya a gare shi kan duk asarar da Yahweh ya aukar masa, kowanen su kuma ya ba shi zoben zinariya da kuma azurfa.
\s5
\v 12 Yahweh ya albarkaci ƙarshen rayuwar Ayuba fiye da lokacin farko, yana da tumaki dubu goma sha huɗu, raƙuma dubu shida, bijimai dubu ɗaya, da matan jakuna ɗari.
\v 13 Haka nan ya sake samun 'ya'ya bakwai maza da 'ya'ya mata uku.
\v 14 Ya raɗa wa ta fari suna Yemima ta biyun kuma Keziya, ta ukun kuma Keren-Haffuk.
\s5
\v 15 A cikin dukkan ƙasar babu matan da aka samu kyawawa da suka kai su kyau, mahaifinsu ya ba su gãdo tare da 'yan'uwansu maza.
\v 16 Bayan wannan Ayuba ya rayu shekaru 140; ya ga 'ya'yansa da kuma jikokinsa. Har zuwa tsara ta huɗu.
\v 17 Bayan nan Ayuba ya mutu cikin tsufa da kuma cikakkun kwanaki.