ha_ulb/17-EST.usfm

355 lines
29 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id EST
\ide UTF-8
\h Littafin Esta
\toc1 Littafin Esta
\toc2 Littafin Esta
\toc3 est
\mt Littafin Esta
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A kwanakin Ahasuros (wannan shi ne Ahasuros wanda yayi mulki daga Indiya har zuwa Kush, bisa larduna 127),
\v 2 a kwanakin nan Sarki Ahasuros ya zauna bisa kursiyin sarautarsa a fadar Susa.
\s5
\v 3 A shekara ta uku ta sarautarsa, yayi wa dukkan sarakunansa da barorinsa biki. Mayaƙan Fasiya da Midiya da manyan sarakuna da hakimai da gamnonin larduna duk suna gabansa.
\v 4 Ya nuna darajar arziƙin mulkinsa da bangirman ɗaukakar ƙasaitarsa kwanaki da yawa, har kwanaki 180.
\s5
\v 5 Da kwanakin nan suka cika, sarki yayi biki kuma na kwana bakwai. Yayi bikin ne saboda dukkan mutanen da suke a fadar Susa, manya da ƙanana. Anyi wannan a farfajiyar lambu da ke a fãdar sarki.
\v 6 Anyi wa farfajiyar lambun ado da labulai farare da shunayya, aka ratayesu bisa kirtani na lallausar lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa aka ɗaure ajikin ginshiƙan duwatsu masu daraja. Akwai kujeru na zinariya, dana azurfa da suke a shirayin da aka daɓe da duwatsun ado masu daraja kamar su fofari mabil, fiyel da duwatsun dakali masu launi.
\s5
\v 7 Aka bada abin sha a moɗayen zinariya, kowacce moɗa daban take, kuma ga ruwan inabin sarakai a yalwace saboda tsabar alfarmar sarki.
\v 8 An shayar ne bisa ga umarni, "Kada a tilasa wa kowa." Sarki ya ba fadawan fadarsa umarni suyi wa kowa yadda yake so.
\s5
\v 9 Har wayau, Sarauniya Bashti ta yawa mata biki a fadar Sarki Ahasuros.
\v 10 A rana ta bakwai da sarki ke jin daɗi a zuciyarsa saboda ruwan inabi, ya cewa Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar, da Karkas (shugabanni bakwai da ke masa hidima),
\v 11 su kawo Sarauniya Bashti a gabansa da kambin sarauta a kanta. Yana so ya nuna wa mutane da fadawansa ƙyanta, gama tana da ƙyaƙƙyawan fasali.
\s5
\v 12 Amma Sarauniya Bashti taƙi zuwa bisa ga faɗar sarki sa'ad da fadawa suka je suka faɗa mata. Sai sarki ya husata ƙwarai; fushinsa yayi ƙuna a ransa.
\s5
\v 13 Sai sarki yayi shawara da waɗanda aka san su masu hikima ne, sun fahimci lokatai (domin haka sarki ya saba yi ga waɗanda suka ƙware a shari'a da hukunci).
\v 14 Na kusa da shi su ne Karshina, Shetar, Admata, Tashish, Meres, Marsina, da Memukan, sarakuna bakwai na Fasiya da Midiya. Suna da 'yancin shiga gun sarki, suke da mafifitan muƙamai a mulkin.
\v 15 "Bisa ga shari'a me za a yiwa Sarauniya Bashti saboda taƙi yin biyayya da umarnin Sarki Ahasuros wanda ya aika mata ta hannun shugabanni?'
\s5
\v 16 Sai Memukan yace a gaban sarki da fadawansa, "Ba ga sarki ne kaɗai Sarauniya Basti tayi laifi ba, amma ga dukkan fadawa da dukkan mutanen da ke a lardunan Sarki Ahasuros.
\v 17 Gama wannan al'amari da sarauniya ta aikata zai zama sananne ga dukkan mata. Zai sasu rena mazajensu. Zasu ce, 'Sarki Ahasuros ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa amma taƙi.
\v 18 Kafin faɗuwar ranar yau manyan matan Fasiya da Midiya da suka ji al'amarin sarauniya zasu maimaita wa dukkan hakiman sarki haka. Wannan zai kawo reni da fushi mai yawa.
\s5
\v 19 Idan ya gamshi sarki bari a aika dokar sarauta daga gareshi, a kuma rubuta a shari'ar Fasiyawa da Midiyawa da bata canzawa, cewa Bashti ba zata ƙara zuwa gaban sarki ba. Bari sarki ya bada matsayin ta ga wacce ta fita.
\v 20 Sa'ad da dokar sarki ta kai ko'ina a faɗin masarautarsa, dukkan mata zasu girmama mazansu, daga manyansu har zuwa ƙananansu."
\s5
\v 21 Sarki da hakimansa sun gamsu ƙwarai da wannan shawara. Sarki kuwa yayi yadda Memukan ya shawarta.
\v 22 Ya aika wasiƙu zuwa dukkan lardunansa, kowanne lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane da harshensu. Ya umarta kowanne namiji ya zama shugaban gidansa. Wannan doka an bada ita a cikin harshen kowaɗanne mutane da ke cikin masarautarsa.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da fushin Sarki Ahasuros ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da tayi. Ya kuma tuna da dokar da ya zartar akanta.
\v 2 Sai samari waɗanda ke wa sarki hidima suka ce, "Bari a madadin sarki a binciko kyawawan budurwai masu tãshe."
\s5
\v 3 Bari sarki yasa shugabanni a dukkan lardunan mulkinsa, su tara dukkan kyawawan budurwai ma su tãshe a gidan mata a cikin masarauta a Susa. A sasu a ƙarƙashin shugabancin Hegai, hakimin sarki, wanda shi ne mai lura da mata, ya kuma basu kayan kwalliyarsu.
\v 4 Bari yarinyar data gamshi sarki ta zama sarauniya a madadin Bashti." Wannan shawarar ta gamshi sarki, sai yayi haka.
\s5
\v 5 Akwai wani Bayahude a fadar Susa mai suna Modakai ɗan Yair ɗan Shimeya ɗan Kish ɗan Benyamin.
\v 6 An ɗauko shi ne daga Yerusalem tare da 'yan bautar talala waɗanda aka kwasosu tare da Yehoiachin, sarkin Yahuda, su ne Nebukadnezza sarkin Babila ya kwashe.
\s5
\v 7 Yayi ta lura da Hadassa, wato Esta ɗiyar kawunsa, domin bata da uba ko uwa. Yarinyar tana da kyan fasali tana kuma da kyan fuska. Modakai ya ɗauketa a matsayin 'yarsa.
\s5
\v 8 Sa'ad da aka yi shelar umarni da dokar sarki, aka kawo 'yan mata da yawa a masarautar Susa. Sai aka sasu a hannun Hegai ya kula dasu. Esta ma aka kaita fadar sarki aka sata a ƙarƙashin Hegai mai lura da mata.
\v 9 'Yar yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashi a wurinsa. Sai nan da nan ya tanada mata kayan kwalliyarta da kuma abincinta. Ya tanada mata kuyangi bakwai daga fadar sarki, ya kuma kaita da ita da kuyanginta wuri mafi kyau a gidan mata.
\s5
\v 10 Esta bata gayawa kowa su wane ne mutanenta da danginta ba, gama Modakai ya umarce ta kada ta faɗa.
\v 11 Kowacce rana Modakai yana kai da kawowa a shirayin gidan da aka sa mata, domin ya san lafiyar Esta, da kuma ko me za ayi da ita.
\s5
\v 12 Da lokaci yayi da kowacce yarinya zata shiga wurin Sarki Ahasuros - bisa ga ƙa'idar da ke na mata, kowacce yarinya sai ta cika watanni goma sha biyu na kwalliyar mata, wata shida tana shafe jikinta da man mur, wata shida tana shafa turare da mai -
\v 13 sa'ad da yarinya mace ta shiga wurin sarki, duk abin da ranta yaso sai a bata daga cikin gidan matayen domin ta kai fãda.
\s5
\v 14 Da yamma zata shiga ciki, da safe zata koma gidan matayen na biyu, a hannun Sha'ashigaz, shugaba na sarki wanda shi ke lura da ƙwaraƙwarai. Ba zata ƙara komawa wurin sarki ba sai in ko yaji daɗinta a ransa kamin ya sake kiranta.
\s5
\v 15 Sa'ad da lokacin Esta ('yar Abihel kawun Modakai wanda ya ɗauke ta a matsayin 'yarsa) yazo da zata shiga wurin sarki, bata roƙi komai ba sai abin Hegai bafaden sarki, wanda shi ke kula da matayen, ya bata. A yanzu Esta ta sami farin jini wurin dukkan waɗanda suka dube ta.
\v 16 Aka kai Esta wurin Sarki Ahasuros a masarautar fãda a wata na goma, wanda shi ne watan Tebet a shekararsa ta bakwai da mulki.
\s5
\v 17 Sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukkan sauran matayen ta kuma sami karɓuwa da tagomashi daga gare shi, fiye da dukkan sauran budurwan. Sai ya ɗibiya mata kambin sarauta a kanta ya maisheta sarauniya a madadin Bashti.
\v 18 Sai sarki ya yi ƙasaitaccen biki domin dukkan hakimansa da kuma barorinsa, wato, "Bikin Esta'," kuma ya tsaida biyan haraji a duk lardunansa. Ya kuma bada kyautai bisa ga falalar yalwar mulkinsa.
\s5
\v 19 Ananan sa'ad da aka tara budurwai karo na biyu, Modakai ya zauna a ƙofar sarki.
\v 20 Esta ba ta rigaya ta faɗa wa kowa game da 'yan uwanta ko mutanenta ba, domin Modakai ya umarceta. Ta ci gaba da bin shawarar Modakai, kamar yadda tayi lokacin daya reneta.
\v 21 A kwanakin da Modakai ke zama a ƙofar sarki, hakiman sarki guda biyu, Bigtan da Teres, masu tsaron ƙofa, suka fusata suka nema su cuci Sarki Ahasuros.
\s5
\v 22 Da aka bayyana wa Modakai al'amarin sai ya gaya wa Sarauniya Esta, Esta ta faɗa wa sarki a sunan Modakai.
\v 23 Aka bincika rahoton aka tabbatar haka yake, sai aka rataye dukkansu biyun a bisa gungume. Aka rubuta wannan al'amari a Littafin Tarihi a gaban sarki.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Bayan waɗannan abubuwa, Sarki Ahasuros ya ɗaukaka Haman ɗan Hamedata Ba'agage, ya fifita matsayin ikonsa bisa kan dukkan shugabanni da ke tare da shi.
\v 2 Dukkan barorin sarki da ke ƙofar sarki kulluyomi sukan durƙusa su rusuna wa Haman, gama sarki ya umarta suyi haka. Amma Modakai bai durƙusa masa ba ko kuma ya rusuna masa ba.
\s5
\v 3 Sai barorin sarki da ke a kofar sarki suka cewa Modakai, "Me yasa kake rashin biyayya da dokar sarki?"
\v 4 Suka yita masa magana kowacce rana, amma yaƙi ya cika burinsu. Saboda haka suka gaya wa Haman domin suga ko za a bar al'amarin game da Modakai ya zama haka, gama ya gaya musu shi Bayahude ne.
\s5
\v 5 Da Haman yaga Modakai baya durƙusa ko ya rusuna masa ba, sai Haman ya cika da hasala.
\v 6 Sai ya ƙudurta ba Modakai kaɗai zai kashe ba, gama barorin sarki sun gaya masa irin mutanen Modakai. Haman yana so ya hallakar da dukkan Yahudawa, mutanen Modakai, waɗanda suke cikin dukkan masarautar Ahasuros.
\s5
\v 7 A cikin wata na fari (wanda shi ne watan Nisan), a shekara ta goma sha biyu ta mulkin Sarki Ahasuros, aka jefa Fur - wato ƙuri'a - a gaban Haman, domin a zaɓi rana da wata. Suka yita jefa ƙuri'a akai akai har sai data faɗa akan watan goma sha biyu (wato watan Ada).
\s5
\v 8 Sa'an nan Haman ya cewa Sarki Ahasuros, "Akwai waɗansu mutane a warwatse an kuma baza su a dukkan lardunan masarautarka. Shari'arsu daban take data sauran mutane, basa kuma kiyaye dokokin sarki, sabili da haka bai kyautu ba sarki ya bar su da rai.
\v 9 Idan sarki ya amince, ya bada umarni a kashe su, ni kuma zan bada talanti dubu goma na azurfa a hannun waɗanda ke tafiyar da cinikaiyar sarki, domin susa a cikin baitulmalin sarki."
\s5
\v 10 Sai sarki ya tuɓe zobensa daga yatsansa ya ba Haman ɗan Hamedata Ba'agagite, maƙiyin Yahudawa.
\v 11 Sarki ya cewa Haman, "Zan tabbatar an mayar maka da kuɗin da kuma mutanenka. Za ka yi abin daka gadama da su."
\s5
\v 12 Sai aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari, aka rubuta doka game da dukkan umarnin da Haman ya bayar zuwa ga masu mulkin lardunan sarki, waɗanda suke bisa dukkan larduna, zuwa ga gwamnonin dukkan al'umma, da shugabannin dukkan mutane, ga kowanne lardi bisa ga irin rubutunsa, da kowacce al'umma kuma bisa ga harshenta. Da sunan Sarki Ahasuros aka rubuta, aka kuma hatimce shi da zobensa.
\v 13 Aka aika da takardun hannu da hannu ta wurin manzanin zuwa ga dukkan lardunan sarki, domin a shafe su, a kashe, a kuma hallaka dukkan Yahudawa, samari da tsofaffi, yara da mata, rana ɗaya - a rana ta goma sha uku a watan goma sha biyu (wato watan Ada) - a kuma washe mallaƙarsu.
\s5
\v 14 Sai aka sanar kowanne lardi takardar data zama shari'a. Aka sanar da dukkan mutane a kowanne lardi cewa su shirya domin wannan rana.
\v 15 Manzanin suka tafi da hanzari domin su baza umarin sarki. Aka baza umarnin kuma a fadar Susa. Da sarki da Haman suka zauna domin su sha, amma birnin Susa ya ruɗe.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Da Modakai ya ji dukkan abin da aka riga aka yi, sai ya kyekketa tufafinsa yasa rigar makoki da toka. Ya fita waje ya je tsakiyar birni, ya yita rusa kuka da bacin rai mai tsanani.
\v 2 Iyakarsa bakin ƙofar sarki kaɗai, domin ba a yardar wa kowa ya wuce wurin sanye da tsummoki ba.
\v 3 A kowanne lardi, duk inda umarnin da dokar sarki ya kai, Yahudawa suka yi ta makoki ƙwarai, tare da azumi, kuka da makoki. Da yawa kuma suka zauna cikin tsummoki da toka.
\s5
\v 4 Da kuyangun Esta da barorinta suka zo suka faɗa mata, sarauniya ta damu ƙwarai. Ta aika wa Modakai tufafin sawa (domin ya tuɓe tsummokaransa), amma ya ƙi karɓarsu.
\v 5 Sai Esta ta kira Hatak, ɗaya daga cikin wakilan sarki wanda aka sasu yi mata hidima. Ta umarce shi ya je wajen Modakai ya binciko abin daya faru da kuma ma'anar al'amarin.
\s5
\v 6 Sai Hatak ya tafi wurin Modakai a dandalin birnin da ke gaban ƙofar sarki.
\v 7 Modakai ya gaya masa dukkan abin daya faru da shi, da kuma jimillar azurfar da Haman ya alƙawarta zai auna ya sa a baitulmalin sarki domin a kashe Yahudawa.
\v 8 Ya kuma ba shi takardar umarnin bugu na biyu a Susa domin hallaka Yahudawa. Yayi haka ne domin Hatak ya nuna wa Esta, ya kuma ba ta nawaiyar tafiya wurin sarki don ta roƙi tagomashi ta kuma nemi alfarma daga gare shi game da mutanenta.
\s5
\v 9 Sai Hatak ya tafi ya faɗa wa Esta abin da Modakai yace.
\v 10 Sai Esta ta yi magana da Hatak cewa ya koma wurin Modakai.
\v 11 Ta ce, "Dukkan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani cewa duk wani namiji ko mace wanda ya shiga cikin farfajiyar sarki ba tare da an kira shi ba, doka ɗaya ce tak: wato dole a kashe shi - sai ko wanda sarki ya miƙa wa sandar zinariya kaɗai domin ya rayu. Ba a kira ni in je wurin sarki ba kwanakin nan talatin."
\v 12 Sai Hatak ya tafi ya faɗa wa Modakai abin da Esta ta ce.
\s5
\v 13 Modakai ya mayar da wannan saƙo: "Kada ki yi tsammanin saboda kina gidan sarki zaki kuɓuta fiye da sauran Yahudawa.
\v 14 Idan kika yi shiru a wannan lokaci, to gudunmawa da tsira zasu zo wa Yahudawa daga wani wuri, amma ke da gidan mahaifinki zaku hallaka. Wa ya sani ko kin sami wannan matsayin mulkin saboda makamancin lokaci irin wannan?"
\s5
\v 15 Sa'an nan Esta ta aika wa Modakai wannan saƙo,
\v 16 "Kaje ka tattara dukkan Yahudawan da ke zaune a Susa, kuyi azumi domina. Kada ku ci ko ku sha har kwana uku, rana ko dare. Ni da 'yan matana ma zamu yi haka. Sa'an nan zan je wajen sarki, koda yake yin hakan ya saɓa wa shari'a, idan na hallaka, na hallaka."
\v 17 Modakai ya tafi yayi duk abin da Esta ta faɗa masa yayi.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Bayan kwana uku, sai Esta ta saka rigunan sarauta ta tafi ta tsaya a shirayin ciki na fadar sarki, a gaban gidan sarki. Sarki yana zaune a kan kursiyinsa a masarautar gidansa, yana fuskantar kofar shiga gidan.
\v 2 Lokacin da sarki ya ga sarauniya Esta tana tsaye a shirayi, sai ta sami amincewa a idanunsa. Sai ya miƙa mata sandar zinariya da ke hannunsa. Sa'an nan Esta ta matso ta taɓa kan sandar.
\s5
\v 3 Sa'an nan sarki yace mata, "Mene ne kike so Sarauniya Esta? Mene ne roƙon ki? Har ma rabin masarautata, za a ba ki."
\v 4 Esta tace, "Idan sarki ya yarda, bari sarki da Haman su zo yau wurin liyafar dana shirya domin sa."
\s5
\v 5 Sa'an nan sarki yace, "Ku kawo Haman nan da nan, yayi abin da Esta ta ce." Sai sarki da Haman suka tafi liyafar da Sarauniya Esta ta shirya.
\v 6 Lokacin da ana raba ruwan inabi a liyafar, sai sarki ya cewa Esta, "Me kike so? Za a baki. Mene ne kike roƙo? Har ma rabin masarautar, za a baki ita."
\s5
\v 7 Esta ta amsa, "Abin da nike so da kuma roƙona shi ne,
\v 8 idan na sami tagomashi a idanun sarki kuma idan ya gamshi sarki ya amsa roƙona kuma ya girmama roƙona, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan shirya maka gobe, sa'an nan zan amsa tambayar sarki."
\s5
\v 9 A wannan rana Haman ya tafi gida da murna da farinciki, a zuciyarsa. Amma da Haman ya ga Modakai a bakin ƙofar sarki, kuma Modakai bai tashi tsaye ba balle yayi rawar jiki a gabansa da ko wani tsoro, sai ya cika da hasala găba da Modakai.
\v 10 Duk da haka Haman ya kame kansa ya tafi gidansa. Ya aika aka kira abokansa, ya kuma tattarosu da matarsa Zeresh.
\v 11 Haman ya rattaba masu darajar wadatarsa, yawan "ya'yansa maza, da dukkan yawan matsayi da sarki ya girmama shi da su, da yadda yake da fifikon daya zarce na dukkan shugabanni da barorin sarki.
\s5
\v 12 Haman yace, "Sarauniya Esta bata gayyaci kowa ba sai ni zan je da sarki liyafar data shirya. Har ma gobe ta sake gayyata ta in zo tare da sarki.
\v 13 Amma ban ɗauki duk wannan a bakin komai ba a gareni muddin in na ganin Modakai zaune a bakin ƙofar sarki."
\s5
\v 14 Sai Zeresh matarsa ta cewa Haman da dukkan abokansa. Bari a kafa wani gungume mai tsawon ƙafa hamsin. Da safe sai ka yi magana da sarki domin su rataye Modakai a kai. Sa'an nan ka tafi da murna tare da sarki wurin liyafar." Wannan ya gamshi Haman sai yasa aka kafa gungumen.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 A daren nan sarki ya kasa barci. Sai ya umarci barori su kawo tarihin ayyukan mulkinsa, aka kuma riƙa karanta wa sarki da murya.
\v 2 Sai aka tarar a rubuce a wurin cewa Modakai ya faɗi game da Bigtana da Teresh, fadawan sarki biyu da ke tsaron ƙofa, da suka yi ƙoƙarin su cuci Sarki Ahasuros.
\v 3 Sarki ya tambaya, "Me aka yi don a bashi girma ko a maida Modakai sananne saboda yayi wannan abu?" Sai samari matasa na sarki da ke masa hidima suka ce, "Ba a yi masa komai ba."
\s5
\v 4 Sarki yace, "Wa ke a shirayi?" Yanzu fa Haman ya rigaya ya shigo shirayin gidan sarki na waje domin yayi masa magana game da rataye Modakai a kan gungumen daya kafa masa.
\v 5 "Barorin sarki suka ce masa, Haman yana tsaye a shirayi." Sarki yace bari ya shigo ciki."
\v 6 Da Haman ya shigo, sarki yace masa, "Me za a yiwa mutumin da sarki yake jin daɗin ya girmama shi?" Sai Haman yace a zuciyarsa, "Wane ne kuwa sarki zai ji daɗin girmama shi fiye da ni?"
\s5
\v 7 Haman ya cewa sarki, "Saboda mutumin da sarki ke jin daɗin girmama shi,
\v 8 bari a kawo rigunan sarauta, waɗanda sarki ya taɓa sawa, da dokin da sarki ya taɓa hawa, kuma a sa masa kambin sarauta.
\v 9 Sa'an nan da rigunan da dokin a ba da su ga ɗaya daga cikin manyan shugabanni. Bari su sa wa mutumin da sarki ke so ya girmama rigunan, bari kuma su bishe shi a kan dokin, a titunan birni. Bari kuma su yi shela a gabansa, "Wannan shi ne abin da ake yi wa wanda sarki ke jin daɗin girmama shi!'"
\s5
\v 10 Sai sarki ya cewa Haman, "Yi hanzari ka ɗauki rigunan da dokin, kamar yadda ka faɗi kayi wa Modakai Bayahude wanda ya kan zauna a ƙofar sarki. Kada ka kasa yin ko abu ɗaya daga abin da ka faɗa."
\v 11 Sai Haman ya ɗauki rigunan da dokin. Ya sanya wa Modakai rigunan ya bishe shi bisa dokin a dukkan titunan birnin. Yayi ta shela a gabansa, '"Haka ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗin girmama shi."
\s5
\v 12 Modakai ya dawo ƙofar sarki. Amma Haman ya gaggauta zuwa gidansa, yana makoki, da kansa a lulluɓe.
\v 13 Haman ya gaya wa matarsa Zeresh da dukkan abokanansa duk abubuwan da suka faru da shi. Sai mutanensa sanannu domin hikimarsu, da Zeresh matarsa suka ce masa, "Idan dai Modakai, wanda ka fara faɗuwa a gabansa Bayahude ne, ba zaka ci nasara a kansa ba, amma hakika zaka faɗi a gabansa."
\v 14 Suna cikin magana da shi haka, sai ga hakiman sarki sun iso. Suka gaggauta suka tafi da Haman wurin liyafar da Esta ta shirya.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Sai sarki da Haman suka tafi su yi liyafa da Sarauniya Esta.
\v 2 A kan rana ta biyu, da ake bada ruwan inabi, sarki ya cewa Esta, "Mene ne roƙonki, Sarauniya Esta? Za a biya maki. Me kike tambaya? Har ma rabin masarautar ma, za a kuma baki."
\s5
\v 3 Sai Sarauniya Esta ta amsa, "Idan na sami tagomashi a idanun ka, idan kuma ka yarda, bari a barni da raina - wannan shi ne roƙona, ina kuma roƙon wannan domin mutanena.
\v 4 Gama an sayar damu - ni da mutanena, domin a hallaka mu, a kashe, a kuma shafe mu gaba ɗaya. Dama a ce an sayar damu ga bauta, maza da mata bayi, dana yi shuru, gama ba wani ƙunci makamancin haka da zai bada dalilin damun sarki."
\v 5 Sai Sarki Ahasuros ya cewa Sarauniya Esta, "Wa ye shi? Ina za a sami wannan mutum daya ƙudurta a zuciyarsa yayi makamancin abu haka?"
\s5
\v 6 Esta tace, "Mafaɗacin mutumin, wannan maƙiyi shi ne mugun nan Haman!" Sai Haman ya firgita a gaban sarki da sarauniya.
\v 7 Sarki ya miƙe tsaye cikin hasala wurin shan ruwan inabin liyafar ya tafi cikin lambun fãda, amma Haman ya jira ya roƙi ransa daga Sarauniya Esta. Ya lura sarki yana niyyar zartar da hallakarwa gãba da shi.
\s5
\v 8 Sarki ya komo daga lambun fãda zuwa cikin ɗakin da aka shayar da su ruwan inabi. Haman ya faɗi a kan kujerar da Esta take. Sai sarki yace, "Zai ci mutuncin sarauniya a gabana a cikin gidana?" Da zarar fitar wannan magana daga bakin sarki, sai barorin suka lulluɓe fuskar Haman.
\s5
\v 9 Sai Harbona, ɗaya daga cikin hakimai da ke wa sarki hidima, ya ce, "Akwai wani gugume mai tsawon kamu hamsin kusa da gidan Haman. Ya kafa shi ne saboda Modakai, wanda yayi magana domin a kare sarki." Sarki yace, "A rataye shi a kai."
\v 10 Sai suka rataye Haman bisa gungumen da ya shirya saboda Modakai. Sai hasalar sarki ya huce.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 A wannan ranar Sarki Ahasuros ya bai wa Sarauniya Esta mallakar Haman, maƙiyin Yahudawa, sai kuma Modakai ya fara hidima a gaban sarki, gama Esta ta gaya wa sarki dangartakarta da Modakai.
\v 2 Sai sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓe daga wurin Haman, sai ya ba da shi ga Modakai. Esta ta sa Modakai ya zama mai lura da gidagen Haman.
\s5
\v 3 Sai Esta ta sake yin magana da sarki. Ta kwantar da fuskartar a ƙasa tana kuka yayinda take roƙo gareshi ya kawo ƙarshen mugun shirin Haman Ba'agage, da maƙarkashiyar daya ƙulla wa Yahudawa.
\v 4 Sai sarki ya miƙo sandar zinariya na sarauta ga Esta, ta tashi ta tsaya a gaban sarki.
\s5
\v 5 Sai ta ce, "Idan ya gamshi sarki, kuma idan na sami tagomashi a wurinka, idan abin yayi dai-dai a ganin sarki, kuma idan na sami tagomashi a idanunka, bari a bada rubutaccen umarni da zai soke wasiƙun da Haman ɗan Hamedata Ba'agage, ya rubuta domin ya hallakar da Yahudawa waɗanda suke warwatse cikin lardunan sarki.
\v 6 Gama yaya zan jimre da ganin masifar da za ta faɗo wa mutanena? Ta yaya zan iya daure wa ganin hallakarwar dangina?"
\s5
\v 7 Sarki Ahasuros ya cewa Sarauniya Esta da kuma Modakai Bayahude, "Duba, na miƙa wa Esta gidan Haman, kuma sun rataye shi a bisa gungume, domin yayi shirin kaiwa Yahudawa farmaki.
\v 8 Rubuta wani umarni domin Yahudawa a cikin sunan sarki a kuma hatimce shi da zoben sarki. Gama umarnin da aka riga aka rubuta da sunan sarki aka kuma hatimce shi da zoben sarki ba za a iya soke shi ba."
\s5
\v 9 Sai aka kirawo magatakardan sarki a wannan lokaci, a cikin wata na uku, wanda shi ne watan Siban, a ranar ashirin da uku ga wata. Aka rubuta umarni ɗauke da dukkan abin da Modakai ya umarta game da Yahudawa. Aka rubuta zuwa ga gwamnonin larduna, su gwamnoni da shugabannin lardunar da ke zaune daga Indiya zuwa Kush, larduna 127, ga kowanne lardi aka rubuta da irin rubutunsu, da kuma ga kowaɗanne mutane cikin yarensu, da kuma ga Yahudawa da rubutunsu da yarensu.
\s5
\v 10 Modakai yayi rubutu da sunan sarki Ahasuros ya kuma hatimce shi da zoben hatimin sarki. Ya aika takardun ta hannun 'yan kada ta kwana mahaya doki masu gudu sosai da ake yin anfani da su a hidimar sarki, wanda aka yi renon su daga masarauta.
\v 11 Sarki ya baiwa Yahudawa na kowanne birni izinin taruwa tare a kuma yi tsayayya don kariyar rayukarsu: su shafe su gaba ɗaya, su kashe, su kuma hallakar da kowacce taruwar masu makamai daga kowaɗanne mutane, ko lardin da ke niyyar kawo masu farmaki, da yaransu da kuma matayensu, ko su kwashi dukiyoyinsu ganima.
\v 12 Wannan za a aiwatar cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, a ranar sha uku na watan sha biyu, wanda shi ne watar Ada.
\s5
\v 13 Takardar dokar za a miƙa ta a matsayin shari'a kuma za a bayyana ta a fili ga dukkan mutane. Yahudawa sai su zauna da shiri a wannan rana don ɗaukar fansa kan maƙiyansu.
\v 14 Sai 'yan kada ta kwana suka hau dawakan masarauta da ake amfani dasu a hidimar sarki. Suka tafi babu ɓata lokaci. Dokar sarki kuwa aka miƙa ta daga fada a Susa.
\s5
\v 15 Sai Modakai ya tashi daga gaban sarki sanye da rigunan sarauta na shuɗi da fari, tare da gagarumin kambi na zinariya da kuma alkyabba ta lillin mai ruwan shunayya, sai birnin Susa tayi sowa da kuma farinciki.
\v 16 Yahudawa suka sami sauƙi da kuma farinciki, da kuma murna da kuma daraja.
\v 17 A kowanne lardi da cikin kowanne birni, dukkan inda umarnin sarki ya kai, aka yi farinciki da kuma murna a tsakanin Yahudawa, aka yi biki da kuma hutu. Dayawa daga cikin mutane daban-daban a ƙasar suka zama Yahudawa, domin tsoron Yahudawa ya faɗo masu.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Yanzu a cikin watan sha biyu, wanda shi ne watan Ada, a ranar sha uku, lokacin da za a aiwatar da shari'a da kuma dokar sarki, a ranar da makiyan Yahudawa ke sa ran zasu sha karfinsu, aka juyad da yanayin. Yahudawa suka sha karfin waɗanda suka tsane su.
\v 2 Yahudawa suka tattaru a biranensu cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, su tayar wa waɗanda suka so su kawo masu bala'i. Babu wanda ya iya tsayayya dasu, gama tsoronsu ya abko wa dukkan mutanen.
\s5
\v 3 Dukkan shugannin lardunar, da gwamnonin lardunar, su gwamnoni, da ma'aikatan sarki, suka taimaka wa Yahudawa domin tsoron Modakai ya abko masu.
\v 4 Gama Modakai ya zama mutum mai girma a gidan sarki, kuma labarinsa ya bazu a dukkan larduna, domin mutumin Modakai ya zama mai girma.
\v 5 Yahudawa suka kai hari ga makiyansu da takobi, suna kisansu da hallakar da su, kuma suka yi masu yadda suka ga dama ga waɗanda suka ƙisu.
\s5
\v 6 A cikin fãdar Susa da kanta Yahudawa suka kashe da kuma hallakar da mutum ɗari biyar.
\v 7 Suka kashe Farshandata, Dalfon, Asfata,
\v 8 Forata, Adaliya, Aridata,
\v 9 Farmashta, Arisai, Aridai, da Baizata,
\v 10 da kuma 'ya'ya maza na Haman ɗan Hamedata su goma, maƙiyin Yahudawa. Amma basu kwashi ganima ba.
\s5
\v 11 A wannan rana jimillar waɗanda aka kashe cikin fãdar Susa, aka faɗa wa sarki.
\v 12 Sai sarki ya cewa Sarauniya Esta, "Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar cikin fãdar Susa, har da 'ya'ya maza na Haman su goma. Mene ne kuma suka aiwatar cikin sauran lardunar sarki? Yanzu mene ne roƙonki? Za a baki. Mene ne bukatarki? Za a biya maki."
\s5
\v 13 Esta tace, "Idan ya dace a ganin sarki, bari a baiwa Yahudawan da ke cikin Susa izinin aiwatar da dokar yau a gobe kuma, bari kuma a rataye gawawakin 'ya'ya maza na Haman su goma a bisa gumagumai."
\v 14 Sai sarki ya umarta da a yi haka. Aka zartar da dokar a cikin Susa, aka kuma rataye 'ya'ya maza goma na Haman.
\s5
\v 15 Yahudawa da ke a Susa suka taru tare a rana ta sha huɗu a watan Ada, suka kashe mutum ɗari uku cikin Susa, amma ba su kwashi ganima ba.
\v 16 Sauran Yahudawa da ke a lardunan sarki suka taru tare don su kare rayukansu, sun kuma ƙuɓuta daga makiyansu suka kuma kashe mutum dubu saba'in da biyar daga waɗanda suka tsanesu, amma basu ɗibiya hannunsu bisa dukiyan waɗanda suka kashe ba.
\s5
\v 17 Wannan ya faru ne a ranar sha uku na watan Ada. A rana ta sha huɗu sai suka huta suka maishe ta ranar shagali da kuma murna.
\v 18 Amma Yahudawan da ke a Susa suka taru tare a ranakun sha uku da sha huɗu. A rana ta sha biyar suka ka huta suka maishe ta ranar shagali da kuma murna.
\v 19 Shi yasa Yahudawan da ke ƙauyuka, waɗanda suka yi gidajensu a ƙauyukan karkara, suka maida rana ta sha huɗu na watan Ada ranar murna da kuma shagali, da kuma ranar da zasu aika wa juna kyaututtukan abinci.
\s5
\v 20 Modakai ya rubuta waɗannan abubuwan ya kuma aika wasiƙu zuwa ga dukkan Yahudawan da ke cikin dukkan lardunan sarki Ahasuros, na kusa dana nesa,
\v 21 yana umurtansu dasu kula su kuma kiyaye ranakun sha huɗu da kuma sha biyar na Ada a kowacce shekara.
\v 22 A wannan kwanaki ne Yahudawa suka kuɓuta daga maƙiyansu, da kuma watan da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, kuma ranar makoki ta zama ranar shagali. Zasu maishe su ranakun shagali da kuma murna, da kuma aikar da kyaututtukan abinci ga juna, da kuma kyaututtuka ga talakawa.
\s5
\v 23 Sai Yahudawa suka cigaba da shagali kamar yadda suka fara, suna aiwatar da abin da Modakai ya rubuta garesu.
\v 24 A wannan lokacin da Haman ɗan Hamedata Ba'agage, maƙiyin dukkan Yahudawa, ya shirya wa Yahudawa makirci don ya hallakar dasu, ya kuma jefa Fur (wato, ya jefa ƙuri'u), don ya hargitsa su ya hallakar da su.
\v 25 Amma da zancen ya kai ga sarki, sai ya bada umarnai ta wasiƙu domin makircin da Haman ya ƙulla gãba da Yahudawa shi koma kansa, da kuma a rataye shi da 'ya'yansa maza a bisa gumagumai.
\s5
\v 26 Saboda haka aka kira waɗannan ranakun sunan Furim, bisa ga sunan Fur. Saboda dukkan abubuwan da aka rubuta cikin wannan wasiƙa, da dukkan abin da suka gani da idanunsu ta kuma same su,
\v 27 Yahudawa suka yi na'am da sababbin ranaku da al'ada. Wannan ranaku zasu zama dominsu, da kuma zuriyarsu, da kuma dukkan wanda zai haɗa kai da su. Ya kuma zama cewa za su tuna da waɗannan ranakun biyu sau biyu a kowacce shekara. Zasu kula da waɗannan ranakun a hanyoyi na musamman da kuma a lokaci ɗaya kowacce shekara.
\v 28 Waɗannan ranaku za a yi bukukuwa a kuma kula dasu a kowacce tsara, da kowanne iyali, da kowanne lardi, da kowanne birni. Waɗannan Yahudawan da kuma zuriyarsu ba zasu dena tunawa da waɗannan ranakun Furim cikin aminci ba, domin kada su manta da su.
\s5
\v 29 Sarauniya Esta ɗiyar Abihel da Modakai Bayahude suka yi rubutu da cikakken iko suka kuma tabbatar da wannan wasika ta biyu game da Furim.
\s5
\v 30 Aka aika wasiƙu zuwa ga dukkan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Ahasuros, ana yi wa Yahudawa barka na salama da gaskiya.
\v 31 Waɗannan wasiƙu suka tabbatar da ranakun Furim cikin lokacinsu, kamar yadda Modakai Bayahude da Sarauniya Esta suka dokaci Yahudawa. Yahudawa suka yi na'am da wannan doka domin kansu da kuma zuriyarsu, kuma kamar yadda suka yi na'am da lokacin azumi da makoki.
\v 32 Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan sharuɗɗai game da Furim, an kuma rubuta su cikin littafi.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Sa'an nan Sarki Ahasuros yasa dokar haraji a ƙasar da kuma kasashen tuddai na bakin teku.
\v 2 Dukkan aikin ci gaba na iko dana karfi, tare da cikakken tarihin girman Modakai ta yadda sarki ya darajartar da shi, aka rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Midiya da kuma Fasiya.
\s5
\v 3 Modakai Bayahude ya zama na biyu bayan sarki Ahasuros ta fannin mulki. Mai girma ne cikin Yahudawa da kuma sananne cikin 'yan'uwansa Yahudawa masu yawa, gama yana kula da lafiyar mutanensa yana yin maganar salama domin dukkan mutanensa.