ha_ulb/16-NEH.usfm

783 lines
54 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id NEH
\ide UTF-8
\h Littafin Nehemiya
\toc1 Littafin Nehemiya
\toc2 Littafin Nehemiya
\toc3 neh
\mt Littafin Nehemiya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Maganar Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan: A wata na Kislif, a shekara ta ashirin, a lokacin da nake a fãdar Shusha,
\v 2 Sai wani daga cikin 'yan'uwana mai suna Hanani ya zo tare da waɗansu mutane daga Yahuda, sai na tambaye su labarin Yahudawan da suka tsira, da kuma sauran Yahudawan da ke a can, waɗanda ke a Yerusalem.
\s5
\v 3 Suka ce da ni "waɗanda suka kuɓuta daga zaman bauta suna cikin babbar damuwa da wulaƙanci, saboda ganuwar Yerusalem ta karye ta faɗi, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta"
\s5
\v 4 Nan da nan bayan na ji waɗannan maganganu sai na zauna na yi kuka, har tsawon kwanaki ina damuwa da azumi a gaban Yahweh na sama.
\v 5 Sai na ce Yahweh "kai ne Ubangiji Allah na sama, Allah wanda ya ke da girma da nagarta, mai cika alƙawari, mai kuma madawammiyar ƙauna ga masu ƙaunarsa da kuma kiyaye dokokinsa.
\s5
\v 6 Ka ji addu'ata ka kuma buɗe idanunka, don ka ji addu'o'in bayinka da nake yi a gare ka dare da rana, don mutaten Isra'ila bayinka. Ina furta zunuban mutanen Isra'ila, waɗanda suka yi maka. Duk da ni da gidan ubana mun yi zunubi.
\v 7 Mun yi aikin mugunta sosai a gabanka kuma bamu kiyaye dokokinka da farillanka waɗanda ka ba mu ba, da kuma ƙa'idojin da ka umarci bawanka Musa.
\s5
\v 8 Ka tuna da abin da ka umarci bawanka Musa, cewa "In kun yi rashin biyayya, zan warwatsa ku cikin al'ummai,
\v 9 amma in kun komo gare ni kuka kuma bi umarnina kuka aikata su, to ko da ya ke an warwatsa mutanenku a faɗin duniya, zan tattaro su daga can zan kuma kawo su wurin nan da na zaɓa domin sunana ya zauna."
\s5
\v 10 Yanzu su bayinka ne da kuma mutanenka, waɗanda ka kuɓutar da ƙarfin ikonka da kuma ƙarfin dantsenka.
\v 11 Yahweh ina roƙon ka, ka saurari addu'ar bayinka yanzu, kuma addu'ar bayinka waɗanda ke son yi maka biyayya, yanzu ka ba bawanka nasara, ka kuma ba shi tagomashi a gaban wannan mutum." Ni mai aikin shayar da sarki ne.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 A watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar Atazazas sarki, ya zaɓi ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin na ba sarki. Sai ya zamana fuskata ta ɓaci a gaban sarki kuma ban taba ɓata fuska a gabansa ba.
\v 2 Amma sarki ya ce mani " me ya sa fuskarka ta ɓaci haka? Kuma gashi ba ciwo kake yi ba. Hakika wannan damuwar zuciya ce "Daga nan sai na tsorata sosai.
\s5
\v 3 Na ce da sarki "Ran sarki ya daɗe! me zai hana ni baƙinciki? Da ya ke birni da maƙabartar iyayena sun zama kufai, kuma an ƙone ƙofofinta da wuta."
\s5
\v 4 Sai sarki ya ce mani "Me kake so in yi?" Sai na yi addu'a ga Allah na sama.
\v 5 Sai na amsa wa sarki" Idan ya gamshi sarki, in kuma na sami tagomashi a idon sarki, sai ka aike ni Yahudiya, garin maƙabartar iyayena, don in sake gina shi."
\v 6 Sai sarki ya amsa mani (sarauniya kuma tana zaune a gefen sarki), "Har zuwa yaushe za ka ɗauka, kuma yaushe za ka dawo?" Bayan na faɗawa sarki lokacin da zan dawo sai ya yi farincikin aike na.
\s5
\v 7 Sai na ce da sarki "Idan ya gamshi sarki, ina roƙo a ba ni wasiƙu domin gwamnonin lardin da ke gefen rafi don su bani damar wucewa ta yankunansu a kan hanyata ta zuwa Yahuda.
\v 8 Kuma ina roƙo a bani wasiƙa domin in ba Asaf mai kula da mashigin dajin sarki don ya ba ni katakan da zan yi madogarai na mashigin kusa da haikalin, da kuma ganuwar birnin, da kuma ɗakin da zan zauna." To da ya ke hannun Allah na tare da ni, sai sarki ya yarda da buƙatuna.
\s5
\v 9 Sai na zo wurin gwamnoni a cikin Lardi Gaba da Kogin na basu wasiƙun sarki. Sarki kuma ya haɗa ni tare da waɗansu jarumawa na sojojin dawakai.
\v 10 Lokacin da Samballat Bahorine da kuma Tobiya Ba'amone bayi suka ji wannan, sai suka da mu sosai cewa wani ya zo don ya taimaki mutanen Isra'ila.
\s5
\v 11 Sai na zo Yerusalem na zauna a can har kwana uku.
\v 12 Sai na tashi da dare ni da mutane kima da ke tare da ni. Ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi domin Yerusalem ba. Ba dabba tare da ni, in ban da wacce na ke hawa ba.
\s5
\v 13 Da duhu sai na bi ta Ƙofar Kwari, kusa da Rijiyar Dila zuwa Ƙofar Kashin Shanu, na dudduba ganuwar Yerusalem, an rushe ta kuma a buɗe take, aka kuma ƙone ƙofofinta na katakai da wuta.
\v 14 Daga nan sai na je ƙofar ƙorama da kuma Madatsin ruwan Sarki. Wurin yana da matsi sosai ga dabbar da nake a kai har da za ta iya wucewa ta ciki.
\s5
\v 15 To sai na tafi da duhu ta kwari na dudduba ganuwar, sai na dawo na shiga Ƙofar Kwari, ta haka na dawo.
\v 16 Shugabanni basu san inda na je da kuma abin da na yi ba, kuma ban sanar da Yahudawa ba tukuna, ban kuma faɗa wa firistoci ba, hakanan ma manyan mutanen garin, da kuma sauran mutanen da suka yi aikin.
\s5
\v 17 Sai na ce da su, "Kun ga masifar da muke ciki, yadda Yerusalem ta zama kufai kuma an ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sake gina ganuwar Yerusalem, don kada mu ƙara zama abin wulaƙanci."
\v 18 Na faɗa masu cewa hannun Allah na tare da mu da kuma maganar da sarki ya faɗa mani. Sai suka ce "Mu tashi mu kama ginin." Sai suka ƙarfafa hannuwansu don wannan aiki nagari.
\s5
\v 19 Amma lakacin da Samballat Bahorine, da Tobiya bawan nan Ba'amone, da Geshem Balarabe suka ji labarin aikin, sai suka yi mani ba'a da reni, suka ce, "Me ku ke yi? Kuna yiwa sarki tayarwa ne?"
\v 20 Sai na amsa masu na ce, "Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa ne kuma za mu tashi muyi ginin. Amma ku baku da gãdo, ko iko, kuma baku da tarihin da zaku ce naku ne a Yerusalem".
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Eliyashib ya tashi tare da 'yan'uwansa firistoci, sai suka gina Ƙofar Tumaki. Suka keɓe ta suka sa ƙofofinta a inda suke. Suka keɓe ta har zuwa Hasumiyar Ɗari da kuma Hasumiyar Hananel.
\v 2 A gaba da shi sai mutanen Yeriko suka yi aiki, a gaba da su kuma Zakkur ɗan Imri ne ya yi aiki.
\s5
\v 3 'Ya'yan Hassina'a ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka sa mata madogarai, da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta.
\v 4 Meremot ne ya gyara sashi na gaba. Shi ɗan Yuriya ne ɗan Hakkoz. Gaba da su sai Meshullam ya gyara. Shi ɗan Berekiya ne ɗan Meshezabel. Gaba da su sai Zadok ya gyara. Shi ɗan Ba'ana ne.
\v 5 Gaba da su sai Tikoyitawa suka gyara, amma shugabanninsu suka ƙi yin aikin da masu duba aikinsu suka umarce su.
\s5
\v 6 Yohaida ɗan Fasiya da Meshullam ɗan Besodeiya ne suka gyara Tsohuwar Ƙofa. Suka sa mata madogarai, da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta.
\v 7 Gaba da su sai Melatiya mutumin Gibiyon da Yadon mutumin Meronot, su mutanen Gibiyon da Mizfa ne, suka yi gyare-gyaren inda gwamnan Lardin Gaba da Kogi ke zama.
\s5
\v 8 Gaba da shi sai Uziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin maƙeran zinariya, ya yi gyara, Gaba da shi kuma sai Hananiya mai yin turare. Su ne suka sake gina Yerusalem da Babban Garun.
\v 9 Gaba da su kuma sai Refayiya ɗan Hur ya gyara. Shi ke mulkin rabin gundumar Yerusalem.
\v 10 Gaba da su sai Yedayiya ɗan Harumaf ya gyara kusa da gidansa. Gaba da shi sai Huttush ɗan Hashabniya ya gyara.
\s5
\v 11 Malkiya ɗan Harim da Hasshub ɗan Fahat- Mowab suka gyara ɗaya sashin tare da Hasumiyar Matoya.
\v 12 Gaba da su sai Shallum ɗan Hallohesh, shugaban sashin gundumar Yerusalem, ya yi gyara tare da 'ya'yansa mata.
\s5
\v 13 Hannun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sake gina ta suka sa ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. Suka yi gyara har zuwa kamu dubu tun daga Ƙofar Kashin Shanu.
\s5
\v 14 Malkiya ɗan Rekab, shugaban gundumar Bet Hakkerem, ya gyara Ƙofar Kashin Shanu. Ya gina ta ya sa ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta.
\v 15 Shallun ɗan Kol-Hozeh, shugaban gundumar Mizfa, ya sake gina Ƙofar Ruwa. Ya gina ta ya sa murfi akan ta da ƙyamarenta, da sakatunta, da mãkarenta. Hakanan ya sake gina Shirayin Siloyam a lambun sarki, tun daga ƙasa har ya zuwa birnin Dauda.
\s5
\v 16 Nehemiya ɗan Azbuk, shugaban rabin gundumar Bet Zur, ya yi gyara har zuwa wurin kabarin Dauda, zuwa madatsar ruwan da mutum ya yi, har ya kai gidan manyan mutane.
\v 17 Bayansa sai Lebiyawa suka yi gyara, tare da Rehum ɗan Bani, gaba da shi kuma sai Hashabiya, shugaban rabin gundumar Keilah don gundumarsa.
\s5
\v 18 Bayansa sai jama'ar ƙasarsu suka yi gyara, suka haɗa da Binuyi ɗan Henadad, shugaban rabin gundumar Keilah.
\v 19 Gaba da shi sai, Ezar ɗan Yeshuwa, shugaban Mizfa, ya gyara ɗaya sashin da ke fuskantar ƙurya har kwanar garun.
\s5
\v 20 Bayansa sai Baruk ɗan Zabbai ya ba da kansa domin gyaran ɗaya gefen, tun daga kwanar garun har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.
\v 21 Bayansa sai Meremot ɗan Yuriya ɗan Hakkoz ya gyara ɗaya gefen ƙofar gidan Eliyashib har zuwa ƙarshen gidan Eliyashib.
\s5
\v 22 Gaba da shi sai firistoci, da sauran mutane daga yankin Yerusalem suka yi gyara.
\v 23 Gaba da su Benyamin da Hasshub suka gyara gefen gidajensu. Gaba da su Azariya ɗan Ma'asiya ɗan Hananiya ya gyara kusa da gidansa.
\v 24 Gaba da shi Binuyi ɗan Henadad ya gyara ɗaya gefen daga gidan Azariya zuwa kwanar garun.
\s5
\v 25 Falal ɗan Uzai ya yi gyaran wajen kwanar bango, da kuma hasumayar da ta kai har dogon gidan sarki a fãdar tsaro. Gaba da shi sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyara.
\v 26 Barorin da ke zama a Ofel suka yi gyara har kusa da Ƙofar Ruwa a wajen gabas da kuma bangon da ya haɗe garin.
\v 27 Daga shi sai Tekoyawa suka yi gyaran ɗaya gefen da ke kusa da babbar hasumaya har zuwa garun Ofel.
\s5
\v 28 Sai firistoci suka gyara sama da Ƙofar Doki, kowanne kusa da gidansa.
\v 29 Bayansu sai Zadok ɗan Immar ya gyara wajen sashen gidansa. Daga bayansa sai Shemaiya ɗan Shekaniya mai tsaron ƙofar gabas ya yi gyara.
\v 30 Bayansa Hananiya ɗan Shelemiya da Hanun ɗan Zalaf na shida, ya gyara ɗaya ɓangaren. Bayansa sai Meshullam ɗan Berekiya ya gyara kusa da ɗakin da ya ke zama.
\s5
\v 31 Bayansa sai Malkiya, ɗaya daga cikin maƙeran azurfa, ya yi gyara har zuwa gidan masu hidima a haikali da kuma na fataken dake haɗe da ƙofa da kuma ɗakin fira na kan kwana
\v 32 Maƙeran zinariya da kuma fatake suka gyara sama da ɗakin fira da ke kwanar Ƙofar Tumaki.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Da Sanballat ya ji muna yin ginin ganuwar, sai abin ya dame shi, ya fusata sosai, ya yi wa Yahudawa ba'a.
\v 2 A gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya, sai ya ce, mene ne waɗannan kumaman Yahudawan ke yi? Ko zasu iya dawo da birni don kansu? Ko zasu miƙa hadayu? Ko zasu iya gama aikin a rana ɗaya? Ko zasu iya samun duwatsu daga tarin matattun duwatsu da aka ƙone?
\v 3 Tobiya Ba'amone na tare da shi, sai ya ce, "Ai ganuwar da suke ginawa dila ma kawai in ya bi ta kan abin da suke ginawa zai rushe ganuwarsu ta dutse!"
\s5
\v 4 Ya Allahnmu, ka ji yadda aka rena mu. Ka mayar masu da reninsu a kansu, ka sa a kwashe su suzama ganimar yaƙi zuwa ƙasar da zasu yi zaman jarun.
\v 5 Kada ka rufe laifofinsu, kada ka shafe zunubansu daga fuskarka, don sun sa maginan sun yi fushi,
\v 6 To sai muka gina katangar kuma katangar ta haɗu har ta kai rabin tsawonta, don jama'ar na da marmarin aiki.
\s5
\v 7 Amma bayan Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Amoniyawa, da kuma Ashdodiyawa suka ji yadda ake yin gyaran katangar Yerusalem da kuma yadda aka gyaggyara wuraren da suka lalace, sai matsanancin fushi ya kama su.
\v 8 Sai duk suka haɗa baki, suka fito don su yaƙi Yerusalem, da kuma kawo rikici a cikinta.
\v 9 Amma muka yi addu'a ga Allahnmu kuma muka sa masu tsaronsu dare da rana, saboda wannan maƙarƙashiyar tasu.
\s5
\v 10 Daga nan sai mutanen Yahuda suka ce, "Ƙarfin ma'aikatan yana kasawa. Akwai kayayyaki da yawa da za a kwashe, kuma ba zamu iya ci gaba da ginin ganuwar ba".
\v 11 Maƙiyanmu suka ce, "Ba za su gan mu ko su san lokacin da zamu auko masu mu kashe su ba, mu tsayar da aikin."
\s5
\v 12 A lokacin, Yahudawan da ke zama kusa da su ne suka zo ta ko'ina suka yi magana da mu sau goma, suka gargaɗe mu akan maƙarƙashiyar da suke shirya mana.
\v 13 Sai na sa mutane a gangaren ganuwar a wuraren da ke da hatsari nasa kowanne iyali da takobinsu, mãshi, da kibiya.
\v 14 Daga nan sai na miƙe na duba, sai na ce da manyan mutane da shugabanni, da sauran mutanen, "Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda ya ke da girma da kuma ban razana. Ku yi yaƙi domin iyalinku da 'ya'yanku maza da mata da matayenku da kuma gidajenku."
\s5
\v 15 Sai ya kasance bayan maƙiyanmu sun ji mun san shirye-shiryensu, Allah kuma ya rikirkita shirye-shiryensu, sai kowa ya koma ya kama aikin garun, kowa ga nasa aikin
\v 16 Tun daga rabin barorina suka koma aikin katanngar, rabinsu kuma suka riƙe mãsu da kwalkwali da kwari, suka kuma sa sauran kayan yaƙi, shugabanni kuma na bayan mutanen Yahuda.
\s5
\v 17 Mutanen dai dake aikin ginin katangar da kuma ɗauko kaya, suke kuma tsaron in da suke. Sai kowannen su ya kama aiki da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma yana riƙe da makami.
\v 18 Kowanne mai gini kuma yana rataye da takobinsa a kwiɓi, yadda suka yi aikin kenan, mai busa ƙaho kuma yana gefena.
\s5
\v 19 Sai na ce da manyan mutane da shugabannin, "Aikin babba ne kuma yanzu ya yi fãɗi, kuma mun rabu a kan garun, mun kuma yi wa juna nisa
\v 20 To dole ne ku ruga inda kuka ji ƙarar ƙaho sai ku tattaru a can. Allahnmu zai yi yaƙi a madadinmu."
\s5
\v 21 Da haka muka yi aiki. Rabinsu na riƙe da mãshi tun daga safe har fitowar taurari.
\v 22 Hakannan sai na ce da mutanen a wancan lokacin, "Sai kowanne mutum da baransa su kwana a tsakiyar Yerusalem, don su zama masu gadi, da dare da kuma ma'aikata da rana."
\v 23 To ko ni ko 'yan'uwana, ko bayina, ko masu gadi dake tare da mu ba wanda ya canza tufafin da yasa, kuma kowannen mu ya ɗauki makaminsa, ko dama ya tafi ɗebo ruwa ne.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Daga nan sai mazaje da matansu suka yi babban kuka kan 'yan'uwansu Yahuduwa.
\v 2 akwai waɗanda suka ce "Mu da 'ya'yanmu maza da mata muna da yawa. To sai mu sami hatsin da za mu ci mu rayu."
\v 3 Akwai waɗanda suka ce, muna jinginar da filayenmu da kuringar inabinmu, da gidajenmu don mu sami abinci a lokacin yunwa."
\s5
\v 4 Hakannan waɗansu suka ce. '"Mun ranci kuɗi don mu biya harajin sarki saboda gonakin inabinmu.
\v 5 Yanzu kuma jikkunanmu da jininmu dai-dai ya ke da na 'yan'uwanmu, 'ya'yanmu kuma dai-dai da nasu 'ya'yan. An tilasta mana mu sayar da 'ya'yanmu su zama bayi. Tuni ma aka bautar da 'ya'yanmu mata. Amma mu ba mu da iko mu yi komai sabada gonakinmu na inabi suna hannun waɗansu mutane"
\s5
\v 6 Bayan na ji wannan kuka nasu da waɗannan maganganu sai na fusata sosai
\v 7 Sai na yi tunani na kuma ba manyan mutane da shugabanni laifi. Na ce da su, "Kowa na neman riba a kan ɗan'uwansa." Sai na jagoranci babban taron gãba da su,
\v 8 sai na faɗa masu cewa, "Mun sha fama kafin mu fito daga ƙangin bauta musamman 'yan'uwanmu Yahudawa da aka sayar a cikin al'ummai, amma sai ga shi kuna sake sayar da 'yan'uwanmu don a sake sayar da su a gare mu kuma!" Sai suka yi shiru ba wanda ya ce uffan.
\s5
\v 9 Hakanan na ce da su abin da kuke yi ba shi da kyau. A she ba za ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu ba, don kada mu zama abin ba'a ga al'umman da ke gãba da mu ba?
\v 10 Ni da 'yan'uwana da bayina ne ke basu rancen kuɗi da hatsi. Amma dole ne mu dena sa ruwa a kan wannan bashin.
\v 11 Sai ku mayar masu da filayensu, da gonakin inabinsu. Da na zaitun ɗinsu, da gidajensu da kuma ƙiyasin kuɗi da na hatsi, da sabon ruwan inabi, da kuma man da kuka karɓa daga gare su."
\s5
\v 12 Daga nan sai suka ce. "Za mu mayar da abin da muka karɓa daga wurinsu, kuma ba za mu karɓi komai daga wurinsu ba. Za mu yi kamar yadda ka faɗi. 'Daga nan sai na kira firistoci, na sa su rantse cewa zasu yi kamar yadda suka alƙawarta.
\v 13 Sai na kakkaɓe tufafina na ce, "Ubangiji ya kakkaɓe dukiya da gidan duk wanda bai cika alƙawaransa ba. Da ma a kakkaɓe shi ya zama fanko sai taron suka amsa, "Amin," sai suka yabi Yahweh jama'ar kuma suka aikatata kamar yadda suka yi alƙawari.
\s5
\v 14 To, tun daga lokacin da aka naɗa ni na zama gwamnan a ƙasar Yahuda, daga shekara ta ashirin har ya zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Atazazas, ko kuma in ce shekaru sha biyu ba mu taɓa cin abincin da ake ba gwamna ba.
\v 15 Amma su tsofaffin gwamnoni da suka gabace ni suka ɗora wa jama'ar ɗawainiya mai nauyi, suka kuma karɓi awo, da zinariya da kuma abincin yau da kullum, da ruwan inabi. Har ma bayinsu suka dinga ƙuntatawa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda tsoron Allah.
\s5
\v 16 Na kuma ci gaba da aikin ganuwar, ba mu kuma sayi ƙasa ba, duk barorina suka taru a can don wannan aiki.
\v 17 A kan teburi kuma inda Yahudawa da shugabaninsu, su 150 suke, in ban da sauran waɗanda suka zo tare da mu daga al'umman dake kewaye da mu.
\s5
\v 18 Kuma kowacce rana akwai sã da aka shirya, zaɓaɓɓun tumaki guda shida, da tsuntsaye, kuma bayan kwana goma a kan kawo kowanne irin ruwan inabi, kuma duk da haka ban taɓa karɓar kuɗin abincin gwamna ba, don buƙatu sun yi wa mutane yawa.
\v 19 Ka tuna da ni ya Allahna, saboda duk abin da na yi domin mutanen nan.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 To, bayan Sanballat da Tobiya da Geshem Balarabe da sauran maƙiyanmu suka ji labarin na sake gina ganuwar, ba kuma inda ya ragu a buɗe, duk da ya ke ban sa ƙyamare a ƙofofin ba,
\v 2 sai Sanballat da Geshem suka aiko mani da saƙo cewa, "Ka zo mu haɗu a wani wuri a filin Ono." Amma so suke su cutar da ni.
\s5
\v 3 Na aika masu da 'yan'saƙo, cewa, "Ina yin babban aiki, kuma ba zan sauko ƙasa ba. Donme aiki zai tsaya a lokacin da na bar shi na gangaro wurinku?"
\v 4 Sai suka sake aiko mani da dai irin wannan saƙon har sau huɗu kuma na dinga ba su amsa da irin amsar da na saba basu a kullum.
\s5
\v 5 Sanballat ya aiko bawansa gare ni da dai irin wannan saƙon a karo na biyar, da rubutu a buɗe a hannunsa.
\v 6 A cikin sa aka rubuta cewa, "An ba da rahoto cikin al'ummai hakannan Geshem shi ma ya faɗa cewa, kai da Yahudawa kuna so kuyi tayarwa, don wannan ya sa kuke sake gina ganuwar. Daga cikin abin da rahoton ya ce har ma ka kusa zama sarkinsu.
\s5
\v 7 Kuma ka zaɓi annabawa su yi wannan shela game da kai a Yerusalem, cewa, 'Akwai sarki a Yahuda!' Kuma ka tabbata sarki zai ji waɗannan saƙonnin. Don haka ka zo muyi magana da juna."
\s5
\v 8 Sai na aika da saƙo gare shi cewa, "Ba wani abu kamar irin abin da ka ce ya faru, amma ka ƙago su ne daga cikin zuciyarka."
\v 9 Don dukkansu sun so su tsoratar da mu, suna tunanin, "Za su sa hannunsu su tsai da aikin, don kada a kammala shi." Amma ya Allah ka ƙarfafa hannuwana.
\s5
\v 10 Na je gidan Shemaiya ɗan Delaiya ɗan Mehetabel, wanda a gidansa aka ƙulla maƙarƙashiyar. Ya ce, "Sai mu je gidan Allah tare a cikin haikali, sai mu kulle ƙofofin haikalin don suna zuwa don su kashe ka. Da dare suna son su kashe ka."
\v 11 Na ba su amsa cewa, "Ko namiji kamar ni zai iya guduwa? Ko namiji kamar ni zai iya zuwa haikali don ya tsirar da ransa? Ba za ni ciki ba."
\s5
\v 12 Na gane cewa ba Allah ne ya aiko shi ba, amma ya yi anabci ne gãba da ni. Tobiya da Sanballat ne suka yi hayar sa.
\v 13 Sun yi hayar sa don ya tsoratar da ni, don in yi abin da ya ce in yi zunubi, don su bani laifi har su wulaƙanta ni.
\v 14 Ya Allahna ka tuna da Tobiya da Sanballat, da duk abin da suka yi. Hakannan ka tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawan da suka so su sa in tsorata.
\s5
\v 15 Da haka aka kammala ginin garun a ranar ashirin da biyar ga watan Elul, bayan kwana hamsin da biyu.
\v 16 Bayan duk maƙiyanmu sun ji labarinsa, sai dukkan al'umman da ke kewaye da mu suka ji tsoro sosai duk fuskarsu ta yanƙwane. Don sun san an kammala aikin ne ta wurin taimakon Allahnmu.
\s5
\v 17 A wannan lokaci sai masu daraja na Yahuda suka aika da wasiƙu masu yawa ga Tobiya, wasiƙun Tobiya kuma suka zo masu.
\v 18 Don akwai waɗanda ke yi masa alƙawari, don shi surukin Shekaniya ne, ɗan Ara. Ɗansa Yehohanan ya auri 'yar Meshullam ɗan Berekiya ta zama matarsa.
\v 19 Sun faɗa mani labarin ayyukansa masu kyau nima kuma na bashi nawa rahoton. Tobiya ya aika mani da wasiƙu don ya firgita ni.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Bayan an gama ganuwar na kuma sa ƙofofin a wurarensu, na kuma zaɓi masu tsaron ƙofofin da mawaƙa da Lebiyawa,
\v 2 na ba ɗan'uwana Hanani iko kan Yerusalem, tare da Hananiya muka kula da masarautar, don shi amintacce ne, kuma mai tsoron Allah fiye da masu yawa daga cikinsu.
\s5
\v 3 Na ce da su, "Ka da ku buɗe ƙofofin Yerusalem har sai rana ta yi zafi. Lokacin da masu tsaron ƙofofin ke tsaro, zaku kulle ƙofofin kusa mãkaransu. Ku zaɓi masu gadi daga cikin mazaunan Yerusalem, waɗansu a bayan gidajensu, waɗansu kuma su tsaya inda aka sa su gadin."
\v 4 Yanzu birnin yana da faɗi da kuma girma, amma kuma waɗanda ke ciki basu da yawa, kuma ba'a gama sake gina gidaje ba tukuna.
\s5
\v 5 Ya Allahna ka ba ni iko in tattara mutane masu girma da shugabanni da dukkan jama'a in sa su bisa ga iyalansu. Sai na samo littafin asalin waɗanda suka dawo daga farko sai na samo wannan rubutun a cikinsa.
\s5
\v 6 Waɗannan sune mutanen lardin da suka fito daga bautar talala waɗanda sarki Nebukadnezza sarkin Babila ya kwasa zuwa bauta. Sun dawo zuwa Yerusalem da Yahuda, zuwa birninsa.
\v 7 Sun zo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra'amiya, da Nahamani, da Modakai, da Bilshan, da Misferet, da Bigbai, da Nehum, da Ba'ana. Yawan mazajen mutanen Isra'ila ya haɗa da waɗannan.
\s5
\v 8 Zuriyar Farosh, 2,172.
\v 9 Zuriyar Shefatiya, 372.
\v 10 Zuriyar Ara, 652.
\s5
\v 11 Zuriyar Fahat-Mowab, zuwa zuriyar Yeshuwa da Yowab, 2,818.
\v 12 Zuriyar Elam, 1,254.
\v 13 Zuriyar Zattu, 845.
\v 14 Zuriyar Zakkai, 760.
\s5
\v 15 Zuriyar Binuyi, 648.
\v 16 Zuriyar Bebai, 628.
\v 17 Zuriyar Azgad, 2,322.
\v 18 Zuriyar Adonikam, 667.
\s5
\v 19 Zuriyar Bigbai, 2,067.
\v 20 Zuriyar Adin, 655.
\v 21 Zuriyar Ater na Hezekiya, 98.
\v 22 Zuriyar Hashum, 328.
\s5
\v 23 Zuriyar Bezai, 324.
\v 24 Zuriyar Harif, 112.
\v 25 Zuriyar Gibiyon, 95.
\v 26 Mutane daga Betlehem da Netofa, 188.
\s5
\v 27 Mazaje daga Anatot, 128.
\v 28 Mutane daga Bet Azmabet, 42.
\v 29 Mutanen daga Kiriyat Yeriyim, da Kefira, da Birot, 743.
\v 30 Mutanen daga Rama da Geba, 621.
\s5
\v 31 Mutanen Mikmas,122.
\v 32 Mutanen Betal da Ai, 123.
\v 33 Mutanen Nebo, 52.
\v 34 Mutanen wancan Elam, 1,254.
\s5
\v 35 Mutanen Harim, 320.
\v 36 Mutanen Yeriko, 345.
\v 37 Mutanen Lod, Hadid, da Ono, 721.
\v 38 Mutanen Sena'a, 3,930.
\s5
\v 39 Sai firistoci: Zuriyar Yedayya (na gidan Yeshuwa), 973.
\v 40 Zuriyar Immer, 1,052.
\v 41 Zuriyar Fashur, 1,247.
\v 42 Zuriyar Harim, 1,017.
\s5
\v 43 Sai Lebiyawa: Zuriyar Yeshuwa, na Kadmiyel, na Binuyi, da Hodiba, 74.
\v 44 Mawaƙa: Zuriyar Asaf, 148.
\v 45 Masu tsaron ƙofa na zuriyar Shallum, da zuriyar Ater, da zuriyar Talmon, da zuriyar Akkub, da zuriyar Hatita, da kuma zuriyar Shobai, 138.
\s5
\v 46 Masu hidimar haikali: Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot,
\v 47 da zuriyar Keros, da zuriyar Siya, da zuriyar Fadon,
\v 48 da zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Shalmai,
\v 49 da zuriyar Hanan, da zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar.
\s5
\v 50 Da zuriyar Riyayya, da zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda,
\v 51 da zuriyar Gazzam, da zuriyar Uzza, da zuriyar Faseya,
\v 52 da zuriyar Besai, da zuriyar Mewunim, da zuriyar Nefushesim.
\s5
\v 53 Da zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa, da zuriyar Harhur,
\v 54 da zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha,
\v 55 da zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Timah,
\v 56 da zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa.
\s5
\v 57 Da zuriyar bayin Suleman: da zuriyar Sotai, da zuriyar Soferet, da zuriyar Ferida,
\v 58 da zuriyar Ya'ala, da zuriyar Darkon, da zuriyar Giddel,
\v 59 da zuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret Hazzebayim, da zuriyar Amon.
\v 60 Dukkan masu hidimar haikali, da zuriyar bayin Suleman, 392.
\s5
\v 61 Waɗannan su ne mutanen da suka tafi daga Tel Mela, Telkasha, Kerub, Addon, da Imma. Amma ba zasu iya ba da shaida cewa iyayensu zuriyar Isra'ila ba ne:
\v 62 da zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda, 642.
\v 63 Waɗanda ke daga firistoci: zuriyar Habaiya, da Hakkoz, da Barzilai (wanda ya auro matarsa daga mutanen Barzillai na Giliyad ake kuma kiran su da sunansu).
\s5
\v 64 Waɗannan sun binciko rubutaccen tarihinsu a cikin waɗanda aka karɓo tarihinsu bisa ga asalinsu, amma ba'a samu ba, don haka aka cire su daga aikin firist don ba su da tsarki.
\v 65 Daga nan sai gwamna ya ce da su ba za a barsu su ci rabon firistoci ba na abinci daga cikin abincin hadaya har sai an sami firist tare da Urim da Tummim.
\s5
\v 66 Dukkan taron baki ɗaya shi ne 42,360,
\v 67 ban da barorinsu maza da mata, waɗanda daga cikinsu aka sami 7,337. Suna da mawaƙa maza da mata da suka kai 245.
\s5
\v 68 Dawakansu guda 736, bijimansu 245,
\v 69 raƙumansu, 435, da jakunansu, 6,720.
\s5
\v 70 Waɗansu daga cikin shugabannin iyaye suka bada kyautai domin aikin. Gwamna ya bada awo dubu na zinariya, da bangaji 50, da suturar firistoci guda 530.
\v 71 Waɗansu daga cikin shugabannin iyalai suka bayar da awo dubu ashirin na zinariya da awon azurfa 2,200.
\v 72 Sauran jama'a suka bayar da awo dubu ashirin na zinariya, da kuma awo dubu biyu na azurfa, da suturar firistoci guda sittin da bakwai,
\s5
\v 73 To sai firistoci da Lebiyawa, da masu tsaron ƙofa da mawaƙa, da waɗansu mutane da masu hidima a haikali da dukkan Isra'ila dake cikin birane. A wata na bakwai sai mutanen Isra'ila suka zauna a biranensu."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Sai dukkan mutane suka taru a matsayin mutum ɗaya a fili a gaban Ƙofar Ruwa. Sai suka tambayi Ezra marubuci ya kawo Littafin Shari'a na Musa, wanda Yahweh ya umarci Isra'ila.
\v 2 A rana ta fari a wata na bakwai, Ezra firist ya kawo shari'a a gaban taron mutanen maza da mata, da duk waɗanda zasu iya ji su kuma fahimta.
\v 3 Sai ya fuskanci filin Ƙofar Ɍuwa, sai ya yi karatu daga cikinsa tun daga asubahi har zuwa tsakar rana, a gaban dukkan maza da mata waɗanda zasu ji su kuma fahimta, kuma dukkan mutanen suka saurari karatun littafin shari'a a hankali.
\s5
\v 4 Sai Ezra marubuci ya tsaya a kan dogon dakali na katako wanda mutane suka shirya saboda wannan dalilin. Waɗanda ke tsaye a gefansa su ne Mattitiya, Shema, Ananiya, Yuriya, Hilkiya, da Ma'aseiya, a gefen damarsa; da Fedaiya, Mishyel, Malkiya, Hashun, Hashbaddana, Zakariya, da Meshullum suna gefensa na hagu.
\v 5 Sai Ezra ya buɗe littafin a gaban dukkan mutane, don yana tsaye ne a saman mutanen, sa'ad da ya buɗe littafin sai dukkan mutane suka miƙe tsaye.
\s5
\v 6 Sai Ezra ya yi godiya ga Yahweh, Allah mai girma, sai dukkan mutane suka ɗaga hannuwansu sama suka amsa, "Amin! Amin!" Sai suka sunkuyar da kansu suka yi sujada ga Yahweh da fuskokinsu a ƙasa.
\v 7 Hakannan Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma'aseiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan, da Felaiya - Lebiyawa - suka taimaki mutane su fahimci shari'ar, a sa'ad da mutane suke a wurarensu.
\v 8 Sun karanta daga cikin littafin, Shari'ar Allah, suka faiyace ta a fili suka kuma fassarata suka bada ma'anarta ga mutane don mutane su fahimci karatun.
\s5
\v 9 Nehemiya gwamna, da Ezra firist da marubuci, da kuma Lebiyawa da ke yiwa mutane fassara suka ce da dukkan mutanen, "Wannan rana ce mai tsarki ga Yahweh Allanku. Kada ku yi baƙinciki ko kuka." Don dukkan mutanen sun yi kuka bayan da suka ji manganganun shari'a.
\v 10 Sai Nehemiya ya ce da su, "Kuje ku ci kitse ku kuma sami abu mai zaƙi ku sha, ku kuma aikawa waɗanda basu da abin yin bikin, don wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi alhini, don farincikin Yahweh shi ne ƙarfinku."
\s5
\v 11 Sai Lebiyawa suka sa mutane su yi shiru, suna cewa, "Ku natsu! Don wannan rana mai tsarki ce. Kada ku yi baƙincikin."
\v 12 Daga nan sai mutane suka tafi don su ci, su sha, su kuma yi zumunci, suyi biki cikin murna sosai saboda sun fahimci maganar da aka koyar da su.
\s5
\v 13 A rana ta uku sai shugabannin iyalai da iyaye daga dukkan mutane, da firistoci, da Lebiyawa, suka taru a wurin Ezra marubuci don su sami fahimta daga manganganun shari'a.
\v 14 Sai suka ga wani wuri inda Yahweh ya umarta ta wurin Musa cewa 'ya'yan Israi'la su taru a cikin bukkoki a lokacin bikin watan bakwai.
\v 15 Sai suyi shela a cikin dukkan biranensu, da Yerusalem, cewa, "Kuje can ƙasa mai duwatsu, ku kawo rassan zaitun da zaitun na daji, da tuwon-biri, da na dabino, da durumi da sauran itatuwa masu rassa don ku yi bukkoki, kamar yadda ya ke a rubuce."
\s5
\v 16 To sai mutanen suka fita suka samo rassan suka yi wa kansu bukkoki, dukkansu kowa da nasa rufe-rufen, da harabunsu, da kuma harabar gidan Allah, a fili a gaban Ƙofar Ruwa da kuma dandalin dake ƙofar Efiraim.
\v 17 Dukkan mutanen da suka dawo daga bautar talala suka kakkafa bukkoki suka zauna a cikinsu. Don tun daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har ya zuwa wannan rana mutanen Isra'ila ba su yi wannan biki ba, don haka suka yi murna sosai.
\s5
\v 18 Hakanan rana bayan rana, daga rana ta fari zuwa rana ta ƙarshe, Ezra ya karanta littafin shari'ar Allah. Su kan yi bikin a kwanaki bakwai a rana ta takwas sai ayi babban taro, don nuna biyayya ga wannan umarni.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 A rana ta ashirin da huɗu a wannan watan dai sai mutanen Israi'la suka taru suna kuma yin azumi, suna sanye da tufafin makoki, suka kuma baɗa toka a kawunansu.
\v 2 Zuriyar Israi'la suka keɓe kansu daga dukkan bãƙi. Suka tsaya, suka furta zunubansu, da kuma ayyukan mugunta na kakaninsu.
\s5
\v 3 Suka tsaya a wurarensu, har kusan faɗuwar rana suna karanta littafin shari'ar Yahweh Allahnsu. Har kusan rabin ɗaya ranar suna ta furta zunubansu suna sunkuyawa a gaban Yahweh Allahnsu.
\v 4 Sai Lebiyawa, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani, da Kenani, suka tsaya a filin suka yi kuka ga Yahweh Allahnsu.
\s5
\v 5 Sai Lebiyawa, Yeshuwa, da Kadmiyel, Bani, Hashabneyya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya, da Fetahiya, suka ce, "Ku miƙe tsaye ku yabi Yahweh Allahnku har abada abadin." Dama su yabi sunanka maɗaukaki, kuma ya ɗaukaka fiye da dukkan albarku da yabo.
\v 6 Kai ne Yahweh. Kai kaɗai. Ka yi samaniya da sammai mafiya nisa, da dukkan rundunoninsu, da duniya da duk abin da ke cikinta, da tekuna da duk abin da ke cikinsu. Ka ba dukkan su rai, kuma dukkan rundunar sama na yi maka sujada.
\s5
\v 7 Kai ne Yahweh, Allahn da ya zaɓi Abram, ya kawo shi daga Ur ta Kaldiyawa ya bashi suna Ibrahim.
\v 8 Ka gane cewa yana da aminci a gare ka, ka kuma yi masa alƙawari zaka bada ƙasar Kan'aniyawa, da Hitiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Yebusiyawa, da Girgashiyawa, ga zuriyarsa. Ka kiyaye alƙawarinka saboda kai adali ne.
\s5
\v 9 Ka ga ƙuncin kakanninmu a Masar ka kuma ji kukansu a bakin Tekun Iwa.
\v 10 Ka bada alamu da al'ajibai gãba da Fir'auna da dukkan bayinsa da dukkan mazaunan ƙasarsa don ka san Masarawa sun yi masu mugun hali sosai. Amma ka samarwa kanka suna wanda ya ke nan har ya zuwa yau.
\s5
\v 11 Kai ne kuma ka raba teku biyu a gabansu, don su bi ta cikin tsakiyar teku a kan sandararriyar ƙasa; ka kuma kora masu runtumarsu cikin zurfafa kamar dutse a cikin ruwaye zurfafa.
\s5
\v 12 Ka bida su ta wurin ginshiƙin girgije da rana, da kuma ginshiƙin wuta da dare don ta nuna masu hanyar da za su bi.
\v 13 A kan Dutsen Sinai ka sauko ƙasa ka yi magana da su daga sama ka kuma ba su ka'idojinka na adalci da kuma shari'arka ta gaskiya, da farillanka da dokokinka masu kyau.
\s5
\v 14 Ka koyar da su game da Asabar ɗinka mai tsarki, ka basu dokoki da farillai da shari'u ta wurin Musa bawanka.
\v 15 Ka basu gurasa daga sama saboda yunwarsu, da kuma ruwa daga dutse saboda ƙishinsu, ka kuma ce da su ku shiga ku mallaki ƙasar da ka rantse za ka basu.
\s5
\v 16 Amma su da kakaninmu suka nuna rashin girmamawa, suka yi taurin kai, basu saurari dokokinka ba,
\v 17 Suka ƙi su saurara, kuma suka ƙi tunani a kan al'ajibanka da kayi a cikinsu, amma suka yi tayarwa, saboda tayarwarsu suka zaɓi shugaba don su koma zaman bautarsu. Amma kai Allah ne wanda ya ke cike da gafara, da alheri da tausayi, mai jinkirin fushi, mai madawwamiyar ƙauna. Baka yashe su ba.
\s5
\v 18 Ko ma a lokacin da suka kafa ɗan maraƙin daga narkakken ƙarfe suka ce, 'Wannan Allahnku wanda ya fitar da ku daga ƙasar Masar,' suka kuma yi babban saɓo,
\v 19 kai, cikin tausayinka, baka yashe su ba a cikin jeji. Ginshiƙin girgijen ya bi da su akan hanya bai kuma rabu da su ba da rana, hakama ginshiƙin wutar bai rabu da su ba da dare don ya haskaka masu hanyar da zasu bi.
\s5
\v 20 Ruhunka manargaci ka basu don ya gargaɗe su, Baka janye mannarka daga bakunansu ba, ka kuma basu ruwa saboda ƙishinsu.
\v 21 Har shekaru arba'in ka yi masu tanadi a cikin jeji, kuma basu rasa komai ba. Suturunsu basu koɗe ba ƙafafunsu kuma ba su kumbura ba.
\s5
\v 22 Ka basu mulkoki da al'ummai ka ba kowannesu lungu-lungu na ƙasar. Sa'an nan suka mallaki ƙasar Sihon da sarkin Heshbon da kuma ƙasar Og sarkin Bashan.
\s5
\v 23 Ka sa 'ya'yansu su yawaita kamar taurarin sama, ka kuma kawo su ƙasar da ka faɗawa ubanninsu su je su mallake ta.
\v 24 Sai mutanen suka je suka mallaki ƙasar ka kuma kori mazauna ƙasar a idonsu, wato Kan'aniyawa. Ka ba da su a hannuwansu, tare da sarakunansu da mutanensu na ƙasar, don Isra'ila su yi yadda suka so da su.
\s5
\v 25 Suka kame ƙayatattun birane da kuma ƙasa mai bada abinci, sun kuma mamaye gidaje cike da abubuwa kyawawa da rijiyoyin da tuni aka haƙa, da garkar inabi da ta zaitun, da itatuwa masu bada 'ya'ya sosai. Da suka ci suka ƙoshi suka yi ƙiba suka ji daɗin kansu a cikin babbar nagartarka.
\s5
\v 26 Daga nan suka yi rashin biyayya a gare ka. Suka yi watsi da dokokinka. Suka karkashe annabawanka da suka gargaɗe su su komo gare ka, sun kuma yi babban aikin saɓo.
\v 27 Don haka sai ka ba da su a hannun maƙiyansu, waɗanda suka wahalashe su. A cikin wahalarsu, suka yi kuka gare ka, ka kuwa ji su daga sama, Kuma saboda babban jinƙanka ka aika masu da masu kuɓutarwa waɗanda suka kuɓutar da su daga ƙasar maƙiyansu.
\s5
\v 28 Amma bayan sun huta, sai suka ƙara yin aikin mugunta a gabanka, sai ka yashe su a hannun maƙiyansu suka mulke su. Duk da haka sa'ad da suka juyo suka yi kuka gare ka, ka ji su daga sama, da kuma a lokuta da yawa saboda yawan jinƙanka ka 'yanto su.
\v 29 Ka gargaɗe su da su juyo ga dokokinka. Duk da haka suka yi husuma kuma ba su saurari umarnanka ba. Suka yi zunubi kan sharuɗan da ke bada rai ga wanda ya kiyaye su. Sun miƙa kafaɗunsu na taurin kai suka ƙi sauraro.
\s5
\v 30 Ka yi ta watsi da su da kuma yi masu gargaɗi ta wurin Ruhunka ta hannun annabawanka. Duk da haka ba su saurara ba. Don haka sai ka miƙa su ga magabtan ƙasashensu
\v 31 Amma a cikin jinƙanka mai girma baka hallakar da su dukka ba, ko kuma ka yashe su, Don kai Allah ne mai yawan jinƙai da alheri.
\s5
\v 32 Yanzu saboda haka ya Allahnmu - kai mai girma ne, maɗaukaki, managarci wanda ka riƙe alƙawarinka da kuma ƙaunarka madauwamiya - kar ka bari duk wannan wahalar da ta same mu ta zama kamar 'yar ƙarama a gare ka, ga sarakunanmu, ga masu mulkinmu, da kuma firistocinmu, da annabawanmu, da iyayenmu, da dukkan mutanenka tun daga kwanakin sarakunan Asiriya har ya zuwa yau.
\v 33 Kai mai adalci ne a cikin duk abin da ya same mu, don da amincinka ka bi da mu, amma muka yi aikin mugunta.
\v 34 Sarakunanmu da masu mulkinmu, da firistocinmu da iyayenmu, ba mu kiyaye shari'arka ba, ko mu saurari dokokinka ko sharuɗɗan da ka gindaya mana waɗanda kuma ka gargaɗe su ba.
\s5
\v 35 Koma da a cikin mulkinsu, sa'ad da suka ji daɗin babban alherinka a gare su, a wannan babbar ƙasa mai yalwa da ka basu, ba su bauta maka ba ko kuma su juyo daga mugayen hanyoyinsu ba.
\s5
\v 36 Yanzu mu bayi ne a ƙasar da ka ba iyayenmu su ji daɗin yalwarta da dukkan abubauwa masu kyau da ke cikinta, yanzu mun zama bayi a cikinta!
\v 37 Dukkan wadatar da ka ba mu tana hannun sarakunan da ka ɗora a kanmu saboda zunubanmu. Suna mulkin jikkunanmu da dabbobinmu yadda suka so. Muna cikin babban ƙunci.
\s5
\v 38 Saboda dukkan wannan, muka yi dauwamammen alƙawari a rubuce. A kan littafin da aka hatimce akwai sunayen shugabanninmu, da Lebiyawa da firistoci."
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 A bisa takardu masu tambari akwai Nehemiya, wanda ya ke gwamna, ɗan Hakaliya da Zedekiya,
\v 2 Sera'iya, Azariya, Irmiya,
\v 3 Fashhur, Amariya, Malkiya,
\s5
\v 4 Hattush, Shebaniya, Malluk,
\v 5 Harim, Meremot, Obadiya,
\v 6 Daniyel, Ginneton, Baruk,
\v 7 Meshullam, Abiya, Miyamin,
\v 8 Ma'aziya, Bilgai, da kuma Shemaiya. Waɗannan su ne firistocin.
\s5
\v 9 Lebiyawan su ne: Yeshuwa ɗan Azaniya, Binuyi na iyalin Henadad, Kadmiyel,
\v 10 da kuma sauran yan'uwansu Lebiyawa, Shebaniya, Hodiya, Kelita, Felaiya, Hanan,
\v 11 Mika, Rehob, Hashabiya,
\v 12 Zakkur, Sherebiya, Shebaniya,
\v 13 Hodiya, Bani, da kuma Beninu.
\v 14 Shugabannin mutanen su ne: Farosh, Fahat-Mowab, Ilam, Zattu, da Bani,
\s5
\v 15 Bunni, Azgad, Bebai,
\v 16 Adoniya, Bigbai, Adin,
\v 17 Atar, Hezekiya, Azzur,
\v 18 Hodiya, Hashum, Bezai,
\v 19 Harif, Anatot, Nebai,
\v 20 Magfiyash, Meshullam, Hezir,
\v 21 Meshezabel, Zadok, da Yadduwa,
\s5
\v 22 Felatiya, Hanan, Anaya,
\v 23 Hoshiya, Hananiya, Hasshub,
\v 24 Hallohesh, Filha, Shobek,
\v 25 Rehum, Hashabna, Ma'aseiya
\v 26 Ahiya, Hanan, Anan,
\v 27 Malluk, Harim, da kuma Ba'ana.
\s5
\v 28 Game da sauran mutanen kuwa, waɗanda suke firistoci, Lebiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, da masu hidimar haikali, da kuma dukkan waɗanda suka keɓe kansu daga mutanen ƙasashen maƙwabta suka kuma miƙa kansu ga shari'ar Allah, har da matayensu, da 'ya'yansu maza da mata, dukkan waɗanda suke da ilimi da kuma fahimta,
\v 29 suka haɗu tare da 'yan'uwansu, da sarakunansu, kuma suka ɗaure kansu da la'ana da kuma alƙawarin yin tafiya bisa shari'un Allah, wadda Musa bawan Allah ya bayar, su kuma kula su kuma yi biyayya da dukkan dokokin Yahweh Ubangijinmu da kuma umarnai da kuma farillunsa.
\s5
\v 30 Mun yi alƙawari ba zamu ba da 'ya'yanmu mata aure ga mazaunan ƙasar ba ko mu auro 'yan matansu ga 'ya'yanmu maza.
\v 31 Mun kuma yi alƙawari idan mazaunan ƙasar suka kawo kayayyaki ko wani hatsi domin sayarwa a ranar Asabarci, ba zamu saya daga gare su ba a ranar Asabaci ko wata rana mai tsarki. Kowacce shekara ta bakwai zamu bar filayenmu su huta, kuma zamu ṣoke dukkan basusuwan da aka yi.
\s5
\v 32 Mun yi na'am da dokokin bayar da ɗaya cikin uku na awo a shekara domin hidimar gidan Allahnmu,
\v 33 domin tanadin gurasar wuri-mai tsarki, da kuma hatsin baiko na kullum, baye-baye na ƙonawa a ranakun Asabaci, bukukuwan sabon wata da kuma shiryayyar liyafa, da kuma baye-baye masu tsarki, da kuma baye-baye na zunubi domin yi wa Isra'ila kaffara, haka kuma domin dukkan ayyukan gidan Allahnmu.
\s5
\v 34 Da firistoci da Lebiyawa da mutane suka jefa ƙuri'u domin itacen yin baiko. Ƙuri'un zasu zaɓi wane ne daga cikin iyalanmu zai kawo itace zuwa gidan Allahnmu a sanyayyun lokatai kowacce shekara, domin ƙonawa a bisa bagadin Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya ke a rubuce cikin shari'a.
\v 35 Mun yi alƙawari mu kawo nunar fari da aka shuka a ƙasarmu cikin gidan Yahweh, da kuma nunar fari na kowanne itace duk shekara.
\v 36 Kamar yadda aka rubuta a shari'a, mun yi alƙawari mu kawo cikin gidan Allah da kuma ga firistoci masu hidima a can, ɗan fari cikin 'ya'yanmu da kuma na garkunan shanunmu da garkunan tumakinmu.
\s5
\v 37 Zamu kawo cụrinmu na fari da kuma baye-bayenmu na hatsi, da kuma 'ya'yan kowacce itaciya, da kuma sabon inabi da kuma mai zamu kawo su ga firistoci, ga rumbunan gidan Allahnmu. Zamu kawo wa Lebiyawa zakka daga ƙasarmu domin su Lebiyawa na karɓar ɗaya daga goma daga dukkan garuruwan da muke aiki.
\v 38 Firist, zuriyar Haruna, dole yana tare da Lebiyawa sa'ad da suke karɓar ɗaya daga goma. Su Lebiyawa dole su kawo ɗaya daga goma ga gidan Allahnmu zuwa cikin runbunan ma'aji.
\s5
\v 39 Gama mutanen Isra'ila da kuma zuriyar Lebi zasu kawo gudumuwoyin na hatsi, da sabon inabi, da kuma mai zuwa ga runbuna inda ake ajiyar santalolin wuri mai tsarki inda firistoci masu hidima suke, da kuma matsaran ƙofa, da kuma inda mawaƙa ke zama. Ba za mu yi watsi da gidan Allahnmu ba.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Shugabannin mutanen suka zauna cikin Yerusalem, sai kuma sauran mutanen suka jefa ƙuri'u domin kawo ɗaya daga cikin goma ya zauna a Yerusalem, birni mai tsarki, sai kuma sauran kashi taran a bar su a wasu garuruwan.
\v 2 Sai mutanen suka albarkaci dukkan waɗanda suka yarda su zauna a Yerusalem.
\s5
\v 3 Waɗannan su ne shuagabannin lardin dake zama Yerusalem. Duk da haka, a cikin garuruwan Yahuda kowanne na zama a ƙasarsa, harma da waɗansu Isra'ilawa, firistoci, Lebiyawa, masu hidimar haikali, da zuriyar bayin Suleman.
\v 4 A Yerusalem akwai mazauna waɗanda suke na zuriyar Yahuda da kuma zuriyar Benyamin. Mutanen Yahuda su ne: Atayya ɗan Uzziya ɗan Zakariya ɗan Amariya ɗan Shefatiya ɗan Mahalalel, na zuriyar Ferez.
\s5
\v 5 Akwai Ma'aseiya ɗan Baruk ɗan Kol-Hoze ɗan Hazayya ɗan Adayya ɗan Yoyarib ɗan Zakariya, ɗan Bashiloni.
\v 6 Dukkan 'ya'yan Ferez da suka zauna cikin Yerusalem 468 ne. Su zama shahararrun mutane.
\s5
\v 7 Waɗannan su ne zuriyar Benyamin: Sallu ɗan Meshullam ɗan Yoyed ɗan Fedayya ɗan Kolayya ɗan Ma'aseyya ɗan Itiyel ɗan Yeshayya,
\v 8 da waɗanda suke binsa, da Gabbai da Sallai, mutane 928.
\v 9 Yowel ɗan Zikri shi ne mai kula da su, da kuma Yahuda ɗan Hassenuwa shi ya zama na biyu a shugabanci bisa birnin.
\s5
\v 10 Daga firistocin: Yedayya ɗan Yoyarib, Yakin,
\v 11 Serayya ɗan Hilkiya ɗan Meshullam ɗan Zadok ɗan Merayot ɗan Ahitub, babban mai kula da gidan Allah,
\v 12 da kuma abokan aikinsu waɗanda suka yi aikin gidan Allah, mutane 822, tare da Adayya ɗan Yeroham ɗan Felaliya ɗan Amzi ɗan Zakariya ɗan Fashhur ɗan Malkiya.
\s5
\v 13 Yan'uwansa ne shugabannin zuriya, mutane 242; da kuma Amashsai ɗan Azarel ɗan Ahzai ɗan Meshillemot ɗan Immer,
\v 14 da kuma yan'uwansu, mutane 128 masu ƙarfin halin yaƙi; mai kula da su shi ne Zabdiyel ɗan Hagedolim.
\s5
\v 15 Daga Lebiyawa: Shemayya ɗan Hashub ɗan Azrikam ɗan Hashabiya ɗan Bunni,
\v 16 da kuma Shabbetai da Yozabad, su da ke daga wajen shugabannin Lebiyawa kuma su ne ke da haƙin aikin waje da gidan Allah.
\s5
\v 17 Akwai Mattaniya ɗan Mika ɗan Zabdi, na zuriyar Asaf, shi ne jagora da ya fara bada godiya cikin addu'a, da kuma Bakbukiya, shi ne na biyu cikin yan'uwansa, da kuma Abda ɗan Shammuwa ɗan Galal ɗan Yedutun.
\v 18 Dukkan Lebiyawa da ke cikin birni mai tsarki lissafinsu 284 ne.
\s5
\v 19 Masu kula da ƙofa: Akkub, Talmon, kuma sauran abokan hurɗarsu, da suke kula da ƙofofi, mutane 172.
\v 20 Sauran Isra'ila da kuma sauran firistoci da Lebiyawa suna cikin dukkan garuruwan Yahuda. Kowannen su na zaune a wurinsa na gãdo.
\v 21 Ma'aikatan haikali suna zaune cikin Ofel, da Ziha da Gishfa su ne masu kula da su.
\s5
\v 22 Babban shugaba a bisa Lebiyawan da ke a Yerusalem shi ne Uzzi ɗan Bani ɗan Hashabiya ɗan Mattaniya ɗan Mika, daga zuriyar Asaf, mawaƙa a bisa aikin cikin gidan Allah.
\v 23 Suna a ƙarƙashin umarnai masu girma daga wurin sarki, kuma an bada umarnai masu tsanani ga mawaƙa yadda kowacce rana ke bukata.
\v 24 Sai Fetaniya ɗan Meshezabel, daga zuriyar Zera ɗan Yahuda, ya zauna a ɓarayin sarki a game da kowanne al'amari da ya shafi mutane.
\s5
\v 25 A game da ƙauyuka da kuma filayensu, wasu mutanen Yahuda sun zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da kuma cikin Dibon da ƙauyukanta, da kuma cikin Yekabzil da ƙauyukanta,
\v 26 da cikin Yeshuwa, Molada, Bet Felet,
\v 27 Hazar Shuwal, da kuma Biyasheba da ƙauyukanta.
\s5
\v 28 Wasu daga mutanen Yahuda sun zauna cikin Ziklag, Mekona da kuma ƙauyukanta,
\v 29 Enrimmon, Zora, Yamut,
\v 30 Zanowa, Adullam, da kuma ƙauyukanta, da cikin Lakish da filayenta, da Azeka da ƙauyukanta. Sai suka zauna daga Biyasheba zuwa Kwarin Hinnom.
\s5
\v 31 Benyamin suka zauna daga Geba, a Mikmash da Aiya, a kuma Betel da ƙauyukanta,
\v 32 Anatot, Nob, Ananiya,
\v 33 Ramah, Gittayim,
\v 34 Hadid, Zeboyin, Neballat,
\v 35 da kuma Ono kwarin maƙera.
\v 36 daga cikin Lebiyawa dake zama cikin Yahuda aka sanya su kan mutanen Benyamin.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Waɗannan su ne firistoci da Lebiyawa da suka fito tare da Zerubbabel ɗan Sheltiyel da kuma tare da Yeshuwa: Serayya, da Irmiya, Ezra,
\v 2 Amariya, Malluk, Hattush,
\v 3 Shekaniya, Rehum, da kuma Meremot.
\s5
\v 4 Akwai su Iddo, Ginneton, Abiya,
\v 5 Miyamin, Mowadiya, Bilga,
\v 6 Shemayya, da Yoyarib, Yedayya,
\v 7 Sallu, Amok, Hilkiya, da Yedayya. Waɗannan ne shugabannin firistoci da mataimakansu a kwanakin Yeshuwa.
\s5
\v 8 Lebiyawan su ne Yeshuwa, Binuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da Mattaniya, wanda shi ne shugaban waƙoƙin godiya, tare da abokan aikinsa.
\v 9 Bakbukiya da Unni, su ne abokan aikinsu, suka tsaya daura da su lokacin yin sujada.
\s5
\v 10 Yeshuwa shi ne mahaifin Yowakim, Yowakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib ne Mahaifin Yowada,
\v 11 Yowada ne mahaifin Yonatan, kuma Yonatan shi ne mahaifin Yadduwa.
\s5
\v 12 A zamanin Yowakim waɗannan su ne firistoci, su ne shugabannin iyalai: Merayya ne shugaban Serayya, Hananiya ne shugaban Irmiya,
\v 13 Meshullam shi ne shugaban Ezra, Yehohanan shi ne shugaban Amariya,
\v 14 Yonatan ne shugaban Malluk, kuma Yosef shi ne shugaban Shebaniya.
\s5
\v 15 Adna ne shugaban Harim, Helkai shugaban Merayot,
\v 16 Zakariya shi ne shugaban Iddo, Meshullam shi ne shugaban Ginneton
\v 17 Zikri shi ne shugaban Abiya. ... na Miniamim. Filtai shi ne shugaban Mowadiya.
\v 18 Shammuwa shi ne shugaban Bilga, Yehonatan shi ne shugaban Shemayya,
\v 19 Mattenai shi ne shugaban Yoyarib, Uzzi shi ne shugaban Yedayya,
\v 20 Kallai shi ne shugaban Sallai, Eba shi ne shugaban Amok,
\v 21 Hashabiya shi ne shugaban Hilkiya, da Netanel shi ne shugaban Yedayya.
\s5
\v 22 A kwanakin Eliyashib, Lebiyawa Eliyashib, Yowada, Yohanan, da Yadduwa aka lisafta su a matsayin shugabannin iyalai, kuma aka lisafta firistocin a zamanin mulkin Dariyos na Fasiya.
\v 23 Su zuriyar Lebi, shugabannin iyalansu aka lisafta su a cikin littafi na tarihi har zuwa kwanakin Yohanan ɗan Eliyashib.
\s5
\v 24 Su shugabannin Lebiyawan su ne Hashabiya, Sherebiya, da Yeshuwa ɗan Kadmiyel, tare da abokan tarayyarsu, suna zaune daura da su domin raira waƙoƙin yabo da kuma bada godiya, suna aikinsu cikin ka'ida, suna biyayya da umarnin Dauda, mutumin Allah.
\v 25 Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon, da Akkub su ne matsaran ƙofofi masu tsaro a tsaye a ɗakunan ajiya dake gefen ƙofofin.
\v 26 Sun yi hidima a cikin kwanakin Yoyakim ɗan Yeshuwa ɗan Yozadak, da kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma Ezra firist da marubuci.
\s5
\v 27 A lokacin keɓewar ganuwar Yerusalem, mutane suka nemi firistoci dukkan inda suke zama, suka kawo su Yerusalem su yi bikin keɓewar tare da farinciki, da godiya da kuma waƙoki tare da kuge, da molo, da giraya, da tsarkiyoyi.
\v 28 Zumuntar mawaƙa suka tattaru tare daga garuruwa kewaye da Yerusalem daga kuma ƙauyuka na Netofatiyawa.
\s5
\v 29 Sun kuma fito daga Bet Gilgal daga kuma filin Geba da Azmabet, domin mawaƙa sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Yerusalem.
\v 30 Su firistoci da Lebiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake mutanen, da ƙofofin, da kuma ganuwar.
\s5
\v 31 Sai na sa shugabannin Yahuda suka hau kan ganuwar, na kuma shirya manyan ƙungiyoyin mawaƙa guda biyu domin su yi waƙoƙin godiya. Sashi ɗaya suka yi dama bisa ganuwar ta sashen Ƙofar Kashin Shanu.
\s5
\v 32 Hoshayya da rabin shugabannin Yahuda suka tafi tare da su,
\v 33 bayan su Azariya, Ezra, Meshullam,
\v 34 Yahuda, Benyamin, Shemayya, da Irmiya,
\v 35 da wasu 'ya'yan firistoci ɗauke da algaitu, da kuma Zekariya ɗan Yonatan ɗan Shemayya ɗan Mattaniya ɗan Mikayya ɗan Zakkur ɗan Asaf.
\s5
\v 36 Da akwai waɗansu cikin 'yan'uwan Zakariya, Shemayya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma'ai, Netanel, Yahuda, Hanani, suna ɗauke da kayayyakin kiɗe-kiɗen Dauda mutumin Allah. Ezra marubuci na tsaye gabansu.
\v 37 Daga Ƙofar Maɓulɓula suka haura kai tsaye zuwa matakalar birnin Dauda, daga matakala zuwa ganuwa a bisa fãdar Dauda, zuwa wajen Kofar Ruwa daga gabas.
\s5
\v 38 Ɗaya ƙungiyar mawaƙan masu bada godiya suka tafi zuwa wancan sashen. Na bi su a bisa ganuwar tare da rabin mutanen, sama da Hasumiyar Murahu, zuwa kan Ganuwa Mai Faɗi,
\v 39 da bisa Kofar Ifraim, da kuma daga Tsohuwar Ƙofa, da kuma daga Ƙofar Kifi da kuma Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiyar Ɗari, zuwa ga Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Matsara.
\s5
\v 40 Da haka dukkan mawaƙa suka bada godiya suka ɗauki wurinsu a cikin gidan Allah, nima na ɗauki wurina tare da rabin ma'aikatan da ke tare da ni.
\v 41 Sai su firistoci suka ɗauki wurin zamansu: Eliyakim, Ma'aseyya, Miniyamin, Mikayya, Elihonai, Zakariya, da kuma Hananiya, tare da ƙahonni,
\v 42 da kuma Ma'aseyya, Shemayya, Eliyaza, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam, da kuma Eza, sai kuma mawaƙan suka sa aka ji su Jezrahiya kuma shi ne shugabansu.
\s5
\v 43 Suka bada manyan hadayu a wannan rana, da farinciki kuma, gama Allah ya sa suka yi farinciki da murna mai girma. Haka mataye da kuma yara suka yi murna. Da haka aka ji farincikin Yerusalem daga nesa.
\s5
\v 44 A wannan rana aka naɗa mutane su shugabanci ɗakunan ajiya domin gudumuwa, nunar fari, da zakka, domin su tara adadin da aka shirya bisa ga shari'a a cikinsu domin firistoci da kuma Lebiyawa. Kowannen su aka ba shi aikin noma filayen da ke kusa da garuruwan. Domin Yahuda sun yi farinciki da firistoci da kuma Lebiyawa waɗanda ke tsaye a gabansu.
\v 45 Suka yi hidimar Allahnsu, da kuma hidimar tsarkakewa, haka kuma mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, domin kiyaye umarnan Dauda da na Suleman ɗansa.
\s5
\v 46 A tun zamanin dã, cikin kwanakin Dauda da Asaf, akwai shugabannin mawaƙa, aka yi waƙokin yabo da godiya ga Allah.
\v 47 A zamanin Zerubbabel da kuma zamanin Nehemiya, dukkan Isra'ilawa suka kawo rabonsu na kowacce rana ga mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi. Suka keɓe wa Lebiyawa rabonsu na kowacce rana, su kuma Lebiyawa suka keɓe wa 'ya'yan Haruna nasu rabon.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 A wannan rana suka karanta Littafin Musa mutane na saurare. Aka iske a rubucce a cikinsa cewa kada wani Ba'ammone ko mutumin Mowab ya shigo cikin taron jama'ar Allah, har abada.
\v 2 Dalili kuwa shi ne domin basu taryi mutanen Isra'ila da gurasa da ruwan sha ba, amma suka yiwo hayar Bala'am domin ya la'anci Isra'ila. Duk da haka, Allahnmu ya juyar da la'anar zuwa albarka.
\v 3 Da dai suka ji shari'ar, sai suka ware kowanne baƙo daga Isra'ila.
\s5
\v 4 Yanzu dai kafin wannan aka sa Eliyashib firist ya zama shugaban ɗakunan ajiya na gidan Allahnmu. Yana da dangantaka da Tobiya.
\v 5 Eliyashib ya shirya wa Tobiya babban ɗaki na ajiya, inda dã aka ajiye hadayar gari, da ta turare, da tasoshi, da kuma zakkar hatsi, da sabon inabi, da mai, wanda aka keɓe domin Lebiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofofi, da kuma gudumuwa domin firistocin.
\s5
\v 6 Amma cikin dukkan wannan lokacin ba na cikin Yerusalem. Gama a cikin shekara ta talatin da biyu ta sarautar Atazazas sarkin Babila na tafi wurin sarki. Bayan lokaci kaɗan sai na nemi izinin tafiya daga wurin sarki
\v 7 sai kuma na komo Yerusalem. Na fahimci muguntar da Eliyashib ya aikata da ya ba Tobiya ɗakin ajiya a cikin haikali na gidan Allah.
\s5
\v 8 Na fusata ƙwarai sai na watsar da kayan ɗakin Tobiya zuwa waje daga ɗakin ajiya.
\v 9 Na umarta a tsabtace ɗakunan ajiyar, na sake zuba kayayyakin gidan Allah a cikinsu, wato baye-bayen hatsi, da kuma turare.
\s5
\v 10 Sai na fahimci cewa ba a ba wa Lebiyawa rabonsu ba, kuma duk sun gudu, kowannen su zuwa ga gonarsa, su Lebiyawa da mawaƙa waɗanda suka yi aikin.
\v 11 Sai na yiwa shugabannin faɗa na ce, "Me ya sa aka yi watsi da gidan Allah?" Na tara su tare kowannen su a wurin aikinsa.
\s5
\v 12 Sa'annan dukkan Yahuda suka kawo zakkar hatsi, sabon inabi, da kuma mai cikin ɗakunan ajiya.
\v 13 Sai naɗa ma'aji bisa gidajen ajiya su Shelemiya firist da Zadok marubuci, kuma daga wurin Lebiyawa, Fedayya. Na kusa da su shi ne Hanan ɗan Zakkur ɗan Mattaniya, gama an iske su amintattu ne. Aikinsu shi ne su rarraba ragowar kayayyakin ga abokan aikinsu.
\v 14 Ka tuna da ni, Allahna, game da wannan, kuma kada ka shafe sarai ayyukan alherin da na aikata sabili da gidan Allahna da kuma hidimarsa.
\s5
\v 15 A waɗannan kwanakin na gani a Yahuda mutane na matsar inabi a ranar Asabaci suna kuma kawo tulin hatsi da ɗauro su bisa jakkai, da kuma inabi, da zaitun, da ɓaure, da kuma kowanne kayan nauyi, wanda suka kawo cikin Yerusalem a ranar Asabaci. Na yi tsayayya da su ganin cewar suna sayar da abinci a wannan rana.
\s5
\v 16 Mutanen Tiya masu zama cikin Yerusalem suka kawo kifi da dukkan kowanne kayayyaki, suka sayar a ranar Asabaci ga mutanen Yahuda da kuma cikin birnin!
\v 17 Sai na fuskanci shugabannin Yahuda kai tsaye, "Wacce irin mugunta ce haka kuke yi, ku na mai da ranar Asabaci wofi?
\v 18 Ba abin da iyayenku suka yi ba kenan? Ba Allahnmu ya aiko da dukkan wannan masifar a bisanmu da kuma wannan birni ba? Yanzu kuna ƙara kawo wata hasala kan Isra'ila ta wofintar da Asabaci."
\s5
\v 19 Daga nan da zarar dare ya yi a bakin ƙofofin Yerusalem kafin Asabaci, na ba da umarni a kulle ƙofofin kada kuma a buɗe su har sai bayan Asabaci. Na sanya wasu bayina a bakin ƙofofin don kada a iya shigo da kaya ciki ranar Asabaci.
\v 20 'Yan kasuwa da masu sayar da kowanne irin tufafi suka taru a wajen Yerusalem sau ɗaya ko biyu.
\s5
\v 21 Amma na yi masu kashedi, "Donme ku ke taruwa a wajen ganuwa? Idan kuka ƙara yin haka, zan kore ku da hannuna!" Daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabaci ba.
\v 22 Sai na dokaci Lebiyawa su tsabtace kansu, su kuma zo su tsare ƙofofin, a tsarkake ranar Asabacin. Ka tuna da ni game da wannan kuma, Allahna, ka kuma yi mani jinƙai sabili da amintaccen alƙawarinka zuwa gare ni.
\s5
\v 23 A waɗannan kwanaki na kuma ga Yahudawan da suka auro matan Ashdod, da Ammon, da kuma Mowab.
\v 24 Rabin 'ya'yansu na magana da yaren Ashdod. Babu waninsu da zai iya magana da harshen Yahuda, amma sai ɗaya daga cikin harshen sauran mutanen kawai.
\s5
\v 25 Na fuskance su kai tsaye, na kuma la'anta su, na kuma bugi wasu daga cikinsu har na tsige sumar kansu. Na sa suka yi rantsuwa ga Allah, cewa, "Ba za ku bada 'ya'yanku mata ga samarinsu ba, ko ku ɗauko wa 'ya'yanku maza 'yanmatansu, ko don kanku.
\v 26 Ba haka Suleman sarkin Isra'ila ya yi zunubi ta dalilin waɗannan matayen ba? A cikin al'ummai masu yawa babu sarki kamarsa, kuma Allahnsa ya ƙaunace shi, kuma Allah ya maishe shi sarki bisa dukkan Isra'ila. Duk da haka, matayensa bãƙi suka sa yayi zunubi.
\v 27 Ƙaƙa zamu saurare ku mu aikata dukkan wannan babbar mugunta, mu kuma yi rashin aminci ga Allahnmu ta wurin auro mataye bãƙi?"
\s5
\v 28 Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yowada ɗan Eliyashib babban firist surukin Sanballat Bahorone ne. Saboda haka na sa shi ya gudu daga fuskata.
\v 29 Ka tuna da su, Allahna, domin sun ƙazantar da firistanci, da kuma alƙawarin firistanci da kuma Lebiyawa.
\s5
\v 30 Da haka na tsabtace su daga duk abin da da ke na bãƙunci, na kuma kafa ayyukan firistoci da na Lebiyawa, kowanne ga aikinsa.
\v 31 Na yi tanadi domin baikon itace a lokatansu da na nunar fari. Ka tuna da ni, Allahna, domin alheri.