ha_ulb/15-EZR.usfm

542 lines
35 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id EZR
\ide UTF-8
\h Littafin Ezra
\toc1 Littafin Ezra
\toc2 Littafin Ezra
\toc3 ezr
\mt Littafin Ezra
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A shekarar farko ta sarautar Sairus, sarkin Fasiya, Yahweh ya cika maganarsa wadda ta zo ta bakin Irmiya, wadda ta motsa ruhun Sairus. Muryar Sairus ta kai dukkan masarautarsa. Wannan shi ne abin da aka faɗa aka kuma rubuta:
\v 2 "Sairus sarkin Fasiya ya ce; Yahweh, Allah na Sama, ya bani dukkan mulkokin duniya, ya kuma zaɓe ni in gina masa gida a Yerusalem a Yahudiya.
\s5
\v 3 Duk wanda ya ke daga cikin mutanensa (Ubangijinsa ya kasance tare da shi) zai tafi Yerusalem ya gina gida domin Yahweh, Allah na Isra'ila, Allah da ke a Yerusalem.
\v 4 Mutanen da ke kowanne sashi na mulkin inda waɗanda suka ragu ke zama sai su basu guzirin azurfa da zinariya, da mallakoki da dabbobi, da kuma kyauta ta yardar rai domin gidan Allah a Yerusalem."
\s5
\v 5 Sai shugabannin zuriyar Yahuda da ta Benyamin, da firistoci da Lebiyawa, da duk waɗanda Allah ya iza ruhunsu su je su gina gidansa ya kafu.
\v 6 Waɗanda ke kewaye da su suka taimaki aikinsu da azurfa da zinariya da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai.
\s5
\v 7 Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin da ke gidan Yahweh waɗanda Nebukadnezza ya kwaso daga Yerusalem ya kuma ajiye a gidajen allolinsa.
\v 8 Sai Sairus ya danƙa su a hannun Miteredat ma'aji, wanda ya ƙirga su ta hannun Sheshbazza shugaban Yahudiya.
\s5
\v 9 Wannan shi ne yawansu: daro talatin na azurfa, daro dubu ɗaya na zinariya, da kuma wasu daro ashirin na sauran kayayyaki,
\v 10 Tasoshi talatin na azurfa, ƙananan tasoshi na zinariya guda 410, da kuma sauran kayayyaki guda dubu.
\v 11 Akwai a ƙalla kayayyakin zinariya da azurfa guda 5,400 da aka haɗa jimla dukka. Sheshbazza ya kawo dukkan waɗannan a lokacin da masu zaman talala suka fita daga Babila zuwa Yerusalem.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Waɗannan su ne mutanen lardin da suka fita daga bautar talalar sarki Nebukadnezza, wanda ya bautar da su a Babila, mutanen da suka koma biranensu na Yerusalem da kuma Yahudiya.
\v 2 Sun dawo tare da Zerubbabel, Yoshuwa, Nehemiya, Serayya, da Re'elaya, Modekai, Bilshan, Misfar, Bigbai, Rehum, da Bãna. Wannan shi ne lissafin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 3 Zuriyar Farosh: 2,172.
\v 4 Zuriyar Shefatiya: 372.
\v 5 Zuriyar Arak: 775.
\v 6 Zuriyar Fahat Mowab, ta wurin Yeshuwa da Yowab: 2,812.
\s5
\v 7 Zuriyar Elam: 1254.
\v 8 Zuriyar Zattu: 945.
\v 9 Zuriyar Zakkai: 760.
\v 10 Zuriyar Bani: 642.
\s5
\v 11 Zuriyar Bebai: 623.
\v 12 Zuriyar Azgad: 1,222.
\v 13 Zuriyar Adonikam: 666.
\v 14 Zuriyar Bigbai: 2,056.
\s5
\v 15 Zuriyar Adin: 454.
\v 16 Mutanen Ater, ta wurin Hezekiya: su tasa'in da takwas.
\v 17 Zuriyar Bezai: 323.
\v 18 Zuriyar Yorah: 112.
\s5
\v 19 Mutanen Hashum: 223.
\v 20 Mutanen Gibba: tasa'in da biyar.
\v 21 Mutanen Betlehem: 123.
\v 22 Mutanen Netofa: hamsin da shida.
\s5
\v 23 Mutanen Anatot:128.
\v 24 Mutanen Azmabet: arba'in da biyu.
\v 25 Mutanen Kiriyat Arim, Kefira, da Birot: 743.
\v 26 Mutanen Rama da Geba: 621.
\s5
\v 27 Mutanen Mikmas:122.
\v 28 Mutanen Betel da Ai: 223.
\v 29 Mutanen Nebo: hamsin da biyu.
\v 30 Mutanen Magbish: 156.
\s5
\v 31 Mutanen ɗayar Elam: 1,254.
\v 32 Mutanen Harim: 320.
\v 33 Mutanen Lod, Hadid, da Ono: 725.
\s5
\v 34 Mutanen Yeriko: 345.
\v 35 Mutanen Senã: 3,630.
\s5
\v 36 Sai firistoci zuriyar Yedayya na gidan Yeshuwa: 973.
\v 37 Zuriyar Immer: 1,052.
\v 38 Zuriyar Fashur: 1,247.
\v 39 Zuriyar Harim: 1,017.
\s5
\v 40 Lebiyawa zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel zuriyar Hodabiya: saba'in da huɗu.
\v 41 Mawaƙan haikali, zuriyar Asaf: 128.
\v 42 Zuriyar masu kula da ƙofa: na Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai: 139.
\s5
\v 43 Waɗanda aka sa su yi hidima a haikali: zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,
\v 44 Keros, Siyaha, Fadon,
\v 45 Lebana, Hagaba, Akkub,
\v 46 Hagab, Shalmai, da Hanan.
\s5
\v 47 Zuriyar Giddel: Gahar, Re'ayya,
\v 48 Rezin, Nekoda, Gazzam,
\v 49 Uzza, Faseya, Besai,
\v 50 Asnah, Meyunim, da Nefusim.
\s5
\v 51 Zuriyar Bakbuk: Hakufa, Harhur,
\v 52 Bazlut, Mehida, Harsha,
\v 53 Barkos, Sisera, Tema,
\v 54 Neziya, da Hatifa.
\s5
\v 55 Zuriyar bayin Suleman: zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda,
\v 56 Jãla, Dakon, Giddel,
\v 57 Shefatiya, Hattil, Fokeret Hazzebem, da Ami.
\v 58 Akwai 392 jimlar zuriyar waɗanda aka sasu yi aiki a haikali da kuma zuriyar bayin Suleman.
\s5
\v 59 Waɗanda suka fita Tel Melah, Kerub, Addon, da Imma - amma basu iya gane asalinsu a Isra'ila ba -
\v 60 sun kai 652 in an haɗa da zuriyar Delayya, Tobiya, da Nekoda.
\s5
\v 61 Hakanan, daga zuriyar firistoci: da zuriyar Habayya, Hakkoz, da Barzillai (wanda ya auro matarsa daga 'ya'yan Barzillai ta Gileyed waɗanda kuma ake kiran su da sunansu).
\v 62 Sun yi ta bincika asalinsu amma basu samo su ba don haka aka cire su daga aikin firist saboda rashin tsarki.
\v 63 Don haka gwamnan ya ce da su kada su ci duk wani abu mai tsarki na hadaya har sai firist da Urim da Tummin sun amince.
\s5
\v 64 Aka haɗa jimlarsu dukka ta kai mutum 42,360,
\v 65 ba a haɗa da bayinsu ba (waɗannan sun kai 7,337) da mazansu da matansu mawaƙan haikali sun kai (ɗari biyu).
\s5
\v 66 Dawakansu: 736.
\v 67 Takarkaransu: 245. Raƙumansu: 435. Jakunansu: 6,720.
\s5
\v 68 Da suka je gidan Yahweh a Yerusalem, manyan ubanni suka yi bayarwa ta yardar rai don a gina gida.
\v 69 Sun bayar gwargwadon iyawarsu don asusun raya aikin: suka bada awon zinariya sittin da ɗaya, da azurfa jaka dubu biyar da kuma kayan sha na firistoci guda ɗari.
\s5
\v 70 To sai firistoci da Lebiyawa, da jama'a, da mawaƙan haikalin da masu tsaron ƙofofi, da waɗanda aka sa suyi hidima a haikali suka mallaki biranensu. Dukkan mutane a Isra'ila suka zauna a biranensu
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 A wata na bakwai ne bayan da mutanen Isra'ila suka dawo biranensu, inda suka tattaru a matsayin al'umma ɗaya a Yerusalem.
\v 2 Yeshuwa ɗan Yozadak da 'yan'uwansa firistoci, Zerubbabel ɗan Sheltiyyel da 'yan uwansa suka tashi don su gina bagadin haikalin Allah na Isra'ila don su miƙa hadaya ta ƙonawa kamar yadda aka umarta a shari'ar Musa mutumin Allah.
\s5
\v 3 Sai suka kafa bagadin a wurin tsayuwarsa, don sun firgita saboda mutanen ƙasar. Suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh da yammaci.
\v 4 Hakanan suka yi idin bukkoki kamar yadda ya ke a rubuce suka riƙa miƙa hadaya kowacce rana kamar yadda aka aiyana, ana yin kowanne aiki bisa ga ranarsa.
\v 5 Bisa ka'ida, akwai baye-baye na ƙonawa ta kowacce rana da kowanne wata da kuma baye-baye na kowanne idi na Yahweh da aka aiyana tare da dukkan kyautai na yardar rai.
\s5
\v 6 Suka fara miƙa baye-baye na ƙonawa ga Yahweh a rana ta farko a wata na bakwai, koda ya ke ba a kafa haikali ba tukuna.
\v 7 Don haka suka bada zinariya ga masu aikin dutse da maƙera, suka bada abinci, da abin sha, da mai ga mutanen Sidon da Taya don su kawo itacen sida ta kan teku daga Lebanon zuwa Yoffa kamar yadda sarki Sairus ya bada umarni ga sarkin Fasiya.
\s5
\v 8 Sa'an nan a wata na biyu na shekara ta biyu bayan sun zo gidan Allah a Yerusalem, sai Zerubbabel ɗan Sheltiyyel, Yeshuwa ɗan Yozadak, da sauran firistoci da Lebiyawa da waɗanda suka dawo daga bauta zuwa Yerusalem suka fara aiki. Suka sa Lebiyawa 'yan shekaru ashirin su kula da aikin gidan Yahweh.
\v 9 Yeshuwa yasa 'ya'yansa da 'yan'uwansa, Kadmiyel yasa 'ya'yansa, (da zuriyar Hodabiya), kuma 'ya'yan Henadad da 'ya'yansu da 'yan'uwansa - dukkansu Lebiyawa ne - da suka haɗu tare wajen lura da masu yin aikin gidan Allah.
\s5
\v 10 Masu ginin suka kafa harsashen ginin haikalin Yahweh. Wannan yaba firistoci da masu sa tufafinsu da kayan hurawarsu, su kuma Lebiyawa 'ya'yan Asaf suka yabi Yahweh da garaya, kamar yadda Dauda ya yi umarni.
\v 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Yahweh, Cewa "Shi nagari ne! Amintaccen alƙawarinsa mai aminci ga Isra'ila ya tabbata har abada."Dukkan mutane suka tada babbar murya da ƙarfi suna yabon Yahweh saboda kafa harsashin ginin haikalin da aka yi.
\s5
\v 12 Amma da yawa daga cikin firistoci da Lebiyawa, da manyan ubannin shugabanni, da tsofaffin mutanen da suka ga lokacin da aka kafa harsashen ginin haikali na farko suka yi kuka da ƙarfi. Amma da yawa suka rera waƙar farinciki da murna da muryoyi masu daɗi.
\v 13 A sakamakon haka mutane ba su iya tantance muryar farinciki da ta baƙinciki ba, Don mutane suna ta kuka da matuƙar farinciki, kuma an jiwo ƙararsu daga nesa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Yanzu kuwa waɗansu abokan gãba na Yahuda da Benyamin suka ji cewa mutanen da ke ƙasar bauta sun fara gina haikali domin Yahweh, Allahn Isra'ila.
\v 2 Sai suka tuntuɓi Zarubbabel da sarakunan zuriyoyin kakaninsu. Suka ce da su, "Bari mu yi gini tare da ku, gama kamar ku, muna neman Allahnku kuma mun yi hadaya gare shi tun kwanakin da Esarhadon, sarkin Asiriya, ya kawo mu nan wurin."
\s5
\v 3 Amma Zarubbabel da Yeshuwa da shugabanin dangogin kakannin suka ce, "Ba ku ba ne, amma mune waɗanda tilas ne mu gina gidan Allahnmu, gama mune waɗanda zasu yi gini domin Yahweh, Allah na Isra'ila, kamar yadda sarki Sairus na Fasiya ya umarta."
\s5
\v 4 Sai mutanen ƙasar suka sa hannuwan mutanen Yahuda suka raunana;
\v 5 Suka sa mutanen Yahuda suka tsorata da ci gaba da yin ginin. Suka kuma ba mashawartan cin hanci don su lalatar da shirin. A wannan lokacin sun yi haka a dukkan kwanakin sarki Sairus har zuwa mulkin Dariyos sarkin Fasiya.
\v 6 To sai a farkon mulkin Ahasuras suka rubuto takardar tuhuma game da mazaunan Yahuda da Yerusalem.
\s5
\v 7 A kwanakin Atazazas ne Bishilam, da Mitiredat, Tabiyel da aminansu suka rubuto wa Atazazas. An rubuta wasiƙar a harshen Aramaik aka kuma fassara.
\v 8 Rehum babban rundunan sojoji da Shimshaya marubuci sun rubuta haka ga Atazazas game da Yerusalem.
\s5
\v 9 Sai Rehum da Shimshaya da aminansu waɗanda ke Alƙalai da waɗansu hafsoshi a gwamnati, da Fasiyawa, daga mazajen Irek da Babila da mazajen Susa (wato Ilemawa) - suka rubuta wasiƙa -
\v 10 suka haɗa kai da mutane masu daraja da Ashurbanifal ya tilasta su zama a Samariya suka bi su tare da sauran waɗanda ke a Lardin Gaba da Kogin.
\s5
\v 11 Wannan ne kwafin wasiƙar da suka aika wa Atazazas: "Barorinka, mazajen Lardin Gaba da Kogin, sun rubuta wannan:
\v 12 Bari sarki ya sani cewa Yahudawan da suka tafi daga gareka sun taso mana a Yerusalem don su gina birnin tayarwa. Sun kammala garun da gyare-gyaren harsasun.
\s5
\v 13 Yanzu kuwa bari sarki ya sani cewa idan birnin nan ya ginu kuma an kammala garun, ba zasu bayar da kuɗin fito da haraji ba, amma zasu azabtar da sarakunan.
\s5
\v 14 Tabbas saboda mun ɗanɗana gishirin fãda, bai cancanci mu ga wani raini na faruwa da sarki ba. Saboda haka ne muke sanar da sarki
\v 15 ka duba daga cikin rubutun kididdiga na mahaifinka don ka tabbatar da cewa wannan birnin tayarwa ne da zai azabtar da sarakuna da lardunan. Ya sha tayar da matsaloli ga sarki da kuma larduna. Ya kuma zama cibiyar tawaye tun da daɗewa. Dalilin haka ne ma aka hallakar da birnin.
\v 16 Muna sanar da sarki cewa idan aka gina wannan birnin da garun, to babu wani abin da zai rage dominka a Lardin Gaba da Kogin."
\s5
\v 17 Sai sarkin ya aika da amsa ga Rehum da Shimshaya da aminansu a Samariya da sauran waɗanda ke a Lardin Gaba da Kogin: "Salama gareku.
\v 18 Wasiƙar da kuka aika mani an karanta an kuma fassara mani.
\v 19 Don haka nasa aka yi bincike kuma na gano cewa a kwanakin baya sun yi tayarwa da rashin hankali ga sarakuna.
\s5
\v 20 Sarakuna masu iko sun yi mulki a kan Yerusalem kuma sun kasance da iko a kan kowanne abu a Lardin Gaba da Kogin. Ana kuma biyansu haraji.
\v 21 Yanzu kuwa a yi umarni ga waɗannan mutanen su tsaya kuma kada su gina wannan birnin sai na umarta.
\v 22 Ku yi hankali kar ku yi banza da wannan. Me zai sa a bar wannan jayayyar ta yi girma ta sa mu hasara a wannan masarauta?
\s5
\v 23 Sa'ad da aka karanta umarnin sarki Atazazas a gaban Rehum, da Shimshaya da aminansu, sai suka fita da sauri zuwa Yerusalem suka sa Yahudawan su tsayar da ginin.
\v 24 Don haka aiki a gidan Allah a Yerusalem ya tsaya har zuwa shekara ta biyu ta mulkin Dariyos sarkin Fasiya.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Sai annabi Haggai da Zakariya ɗan annabi Iddo suka yi annabci da sunan Allah na Isra'ila ga Yahudawa a Yahuda da Yerusalem.
\v 2 Zarubbabel ɗan Sheltiyyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka tashi tsaye suka fara gina gidan Allah a Yerusalem tare da annabawan da suka ƙarfafa su.
\s5
\v 3 Daga nan Tattenai gwamnan Lardin Gaba da Kogin, Shetar Bozenai, da abokan aikinsa suka zo suka ce masu, "Wane ne ya baku umarni ku gina wannan gidan ku kuma ƙarasa waɗannan katangun?"
\v 4 Sai suka kuma ce, Mene ne sunayen mutanen da ke yin wannan ginin?"
\v 5 Amma idanun Allah na kan dattawan Yahudawa kuma maƙiyansu basu tsayar da su ba. Suna jiran wasiƙar da za a aika wa sarki da kuma umarnin da za a komar masu game da wannan.
\s5
\v 6 Wannan shi ne kwafin wasiƙar Tattenai wato gwamnan Lardin Gaba da Kogi, da Shetar Bozinai da tawagarsa a cikin Lardin Gaba da Kogi, wanda suka aikawa sarki Dariyos.
\v 7 Sun aika da rahoto, suka rubuta wa sarki Dariyos haka, "Bari dukkan salama ta zama taka.
\s5
\v 8 Bari sarki ya sani cewa mun je Yahuda gidan Allah mai Girma. Ana gininta da manyan duwatsu da katakan da aka shirya a ganuwar. Wannan aikin kuwa ana yin sa sosai da sosai, kuma yana tafiya dai-dai a hannuwansu.
\v 9 Muka tambayi dattawan, 'Wa ya baku umarni ku gina wannan gida da wannan ganuwar?'
\v 10 Mun kuma tambayi sunayensu domin ka iya sanin sunan kowanne mutum da ya jagorance su.
\s5
\v 11 Suka amsa suka ce, 'Mu barorin wanda shi ne Allah na sama da ƙasa, kuma muna ginin wannan gida wanda aka gina a shekarun baya masu yawa a sa'ad da sarki mai girma na Isra'ila ya gina, ya kuma ƙarasa shi.
\s5
\v 12 Koda ya ke, Sa'ad da kakaninmu suka sa Allah na sama ya yi fushi, sai ya bada su ga hannuwan Nebukadnezza, sarkin Babila, wanda ya rushe wannan gidan ya kuma ɗauke mutanen zuwa ɓauta a Babila.
\v 13 Duk da haka, a shekara ta fari sa'ad da Sairus ya ke sarkin Babila, Sairus ya bada umarni a gina gidan Allah.
\s5
\v 14 Sarki Sairus ya kuma mayar da kayayyakin zinariya da azurfa na gidan Allah da Nebukadnezza ya kawo daga haikali a Yerusalem zuwa ga haikali na Babila. Ya mayar da su ga Sheshbazza, wanda yasa ya zama gwamna.
\v 15 Ya ce da shi, "Ɗauki waɗannan kayayyakin. Tafi ka aje su a haikali a Yerusalem. Bari a sake gina gidan Allah a wurin."
\s5
\v 16 Sai Sheshbazza yazo ya ƙafa harsashe domin gidan Allah a Yerusalem; kuma ana kan yi, amma ba a ƙarasa shi ba.'
\s5
\v 17 Yanzu kuwa, idan sarki ya yarda, sai a bincika a gidan ajiyar rahotonin dã a Babila koda akwai huƙunci daga Sarki Sairus game da gina gidan Allah a Yerusalem. To sai sarki ya aiko da ra'ayinsa gare mu.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Sai sarki Dariyos ya bada umarni a yi bincike a gidan ajiyar rahotanin dã a Babila.
\v 2 A ƙasaitaccen birnin Ikbatana a Midiya aka sami takarda; wannan ne abin da aka rubuta a cikinta:
\s5
\v 3 A shekara ta farko ta Sarki Sairus, Sairus ya bada umarni game da gidan Allah a Yerusalem: 'Bari gidan ya sake ginuwa domin ya zama wurin hadaya, bari a kafa harsasunsa, bari tsawonsa ya zama kamu 27, faɗinsa kamu 27,
\v 4 da layin manyan duwatsu guda uku da layi ɗaya na sababbin katakai, kuma bari gidan sarki ya biya duk kuɗin da aka kashe.
\v 5 Yanzu a dawo da kayayyakin zinariya da azurfa na gidan Allah wanda Nebukadnezza ya kawo Babila daga haikali a Yerusalem sai a aika da su kuma ga haikali a Yerusalem. Zaku kuwa aje su a gidan Allah.'
\s5
\v 6 Yanzu Tattenai, gwamnan Lardin Gaba da Kogi da Shetar Bozinai da tawagar da ke Lardin Gaba da Kogi, ku rabu da su!
\v 7 Ku bar aikin gidan nan na Allah yadda ya ke. Gwamna da dattawan Yahudawa zasu gina wannan gidan Allah a wancan wurin.
\s5
\v 8 Ina umarta cewa tilas ne kuyi wannan domin waɗannan dattawan Yahudawan da suka gina wannan gida na Allah: Kuɗi daga asusun sarkin gaba da Kogi za a yi amfani da su a biya waɗannan mutanen don kada su tsayar da aikinsu.
\v 9 Ko mene ne ake bukata - bijimai, ko raguna, ko 'yan raguna domin hadaya ga Allah na Sama, ko hatsi, ko gishiri, ko ruwan inabi, ko mai bisa ga umarnin firistocin Yerusalem - ku ba su waɗannan abubuwa kowacce rana babu fasawa.
\v 10 Ku yi wannan domin su kawo bayarwarsu ga Allah na Sama kuma ku yi mani addu'a, sarki, da 'ya'yansa.
\s5
\v 11 Ina umarta cewa duk wanda ya taka wannan doka, za a ciro ginshiƙi daga gidansa a soke shi da shi. Gidansa kuwa tilas ne a mayar da shi juji saboda wannan.
\v 12 Bari Allah wanda yasa sunansa ya zauna a wurin ya cisge kowanne sarkin ko mutanen da suka ɗaga hannu su canza wannan doka, ko su lalata wannan gidan na Allah a Yerusalem. Ni, Dariyos, nake umarta wannan. Bari a yi tare da kula!"
\s5
\v 13 To saboda umarnin da sarki Dariyos ya aika, Tattenai, gwamnan Lardin Gaba da Kogi da Shetar-Bozinai da abokan aikinsa, suka yi dukkan abin da Sarki Dariyos ya umarta.
\v 14 Saboda haka dattawan Isra'ila suka yi ginin kamar yadda Haggai da Zakariya suka umarta ta wurin annabci. Suka gina shi bisa ga dokar Allah na Isra'ila da Sairus da Dariyos da Atazazas, sarakuna Fasiya
\v 15 An kammala gidan a rana ta uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta mulkin sarki Dariyos.
\s5
\v 16 Mutanen Isra'ila da firistoci da Lebiyawa da sauran masu zaman bauta suka yi bukin keɓe gidan Allah tare da jin daɗi.
\v 17 Suka ba da bijimai ɗari da raguna ɗari da 'yan raguna ɗari huɗu domin keɓe gidan Allah. Awaki goma sha biyu aka bayar a matsayin bayarwa ta wanke zunubi domin dukkan Isra'ila, ɗaya domin kowacce kabilar Isra'ila.
\v 18 Suka kuma sa firistoci da Lebiyawa su rarraba wa mutanen aiki domin sujada ga Allah a Yerusalem, kamar yadda aka rubuta a Littafin Musa.
\s5
\v 19 Saboda haka waɗanda suke cikin bauta suka yi bukin idin Ƙetarewa a watan huɗu.
\v 20 Firistocin da Lebiyawa dukka suka tsarkake kansu suka kuma yanyanka hadayun idin Ƙetarewa domin dukkan waɗanda suka yi bauta, har da su kansu.
\s5
\v 21 Mutanen Isra'ila da suka ci kaɗan daga cikin naman idin Ƙetarewa su ne waɗanda suka dawo daga bauta suka kuma raba kansu daga rashin tsarkin mutanen ƙasar suka kuma biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 22 Cikin jin daɗi kuwa suka sha shagulgulan bukin gurasa marar gami har kwanaki bakwai, gama Yahweh ya kawo masu jin daɗi ya kuma juya zuciyar sarkin Asiriya ta ƙarfafa hannunsu a cikin aikin gidansa, gidan Allah na Isra'ila.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Yanzu bayan wannan, a zamanin mulkin Atazazas sarkin Fasiya, Ezra ya dawo daga Babila. Kakannin Ezra su ne kamar haka, Seraiya, Azariya, Hilkiya,
\v 2 Shallum, Zadok, Ahitub,
\v 3 Amariya, Azariya, Merayot,
\v 4 Zerahiya, Uzzi, Bukki,
\v 5 Abishuwa, Fenihas, Eliyeza, wanda shi ne ɗan Haruna babban firist.
\s5
\v 6 Ezra ya dawo daga ƙasar Babila kuma ƙwararren marubuci ne cikin shari'ar Musa wanda Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bayar. Sarki ya ba shi dukkan abin da ya ke buƙata domin hannun Yahweh na tare da shi.
\v 7 Wasu daga cikin zuriyar Isra'ila da kuma firistoci, da Lebiyawa, da mawaƙan haikali, da masu tsaron ƙofa da kuma waɗanda aka shirya domin hidima a haikali suma suka tafi Yerusalem a cikin wata na bakwai na mulkin Atazazas.
\s5
\v 8 Ya isa Yerusalem a wata na biyar na wannan shekara.
\v 9 Ya baro Babila a rana ta ɗaya na watan farko. A rana ta ɗaya ne na watan biyar ya isa Yerusalem, tun da hannun Allah mai kyau na tare da shi.
\v 10 Ezra ya kafa zuciyarsa domin ya yi bincike, ya aikata, ya kuma koyar da farillai da hukumtai da dokokin Yahweh.
\s5
\v 11 Wannan shi ne umarnin da sarki Atazazas ya ba Ezra firist da kuma marubucin dokoki da farillun Yahweh domin Isra'ila.
\v 12 "Sarkin sarakuna Atazazas, zuwa ga firist Ezra, marubuci na dokokin Allah na sama:
\v 13 Ina bada umarni cewa kowannene daga Isra'ila cikin harabar mulkina tare da firistocinsu da Lebiyawa da ya ke da niyar tafiya zuwa Yerusalem, zaya iya tafiya da kai.
\s5
\v 14 Ni, sarki, tare da mashawartana guda bakwai, muna aiken ku dukka ku bincika game da Yahuda da kuma Yerusalem bisa ga dokokin Allah, wanda ke cikin hannuwanku.
\v 15 Ku dawo da azurfa da zinariyar da suka bayar da yardar rai zuwa ga Allah na Isra'ila, wanda mazauninsa ke a Yerusalem.
\v 16 Ku bayar hannu sake dukkan azurfa da zinariya da dukkan Babila ta bayar kuma da dukkan abin da mutane da firistoci suka bayar hannu sake domin gidan Allah a Yerusalem.
\s5
\v 17 Saboda haka ku saya da farashi cikakke shanun, da ragunan, da 'yan tumakin, da hatsi da baye-baye na sha. Ku miƙa su a bisa bagadin da ke cikin gidan Allahnku a Yerusalem.
\v 18 Ku yi haka da sauran azurfar da zinariyar dukkan abin da kuka ga ya dace maku da 'yan'uwanku, domin ku gamshi Allahnku.
\s5
\v 19 Ku ɗibiya kayayyakin da aka yi maku kyautarsu a gabansa domin hidima cikin gidan Allahnku a Yerusalem.
\v 20 Duk wani abin da ake buƙata domin gidan Allahnku da za kuyi bukatarsa, sai a biya daga cikin ma'ajina.
\s5
\v 21 Ni, sarki Atazazas, na yi umarni ga dukkan masu ajiya cikin Lardin Gaba da Kogi, da cewa dukkan abin da Ezra zai yi buƙata daga gareku bari a ba shi a cike,
\v 22 har sama da talantai na azurfa ɗari, tuli buhu ɗari na hatsi, da ruwan inabi gallan ɗari, da gallan ɗari na mai, da kuma gishiri babu iyaka.
\v 23 Dukkan abin da suka fito daga umarnin Allah na Sama, ka aikata da kuzari, domin gidansa. Donme ne ne hasalarsa za ta yi ƙuna a bisa masarauta ta da 'ya'yana?
\s5
\v 24 Muna sanar da su game da ku da kada su ɗora maku wata tãra ko haraji ga kowanne firistoci, ko Lebiyawa, ko mawaƙa, ko masu tsaron ƙofa, ko ga mutanen da aka ba hidimar haikalin da kuma bayin gidan wannan Allah.
\s5
\v 25 Ezra, ta wurin hikimar da Allah ya baka, dole ka naɗa alƙalai da masanan hikima su yiwa mutane hidima a cikin dukkan Lardin Gaba da Kogi, su kuma yi hidima ga kowannene da ya san shari'ar Allahnka. Dole kuma ka koyar da shari'ar ga dukkan waɗanda basu san dokar ba.
\v 26 Ku hori duk wanda ba ya yi cikakkiyar biyayya ga shari'ar Allah ba ko shari'ar sarki ba, ko ta mutuwa, ko kora daga ƙasa, ko a ƙwace mallakarsu, ko jefawa cikin kurkuku.
\s5
\v 27 Yi yabo ga Yahweh, Allahn kakanninmu, wanda ya sanya dukkan wannan cikin zuciyar sarki ya ɗaukaka gidan Yahweh cikin Yerusalem,
\v 28 kuma wanda ya nuna amincin alƙawarinsa gareni a gaban sarki, da mashawartansa, da kuma dukkan majalisarsa masu iko. Na sami ƙarfafawa daga hannun Yahweh Allahna, sai na tara shugabanni daga Isra'ila su tafi tare da ni.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Waɗannan su ne shugabanni na kakannin iyalansu waɗanda suka baro Babila tare da ni a zamanin mulkin sarki Atazazas.
\v 2 Na zuriyar Fenihas, Geshom. Na zuriyar Itamar, Daniyel. Na zuriyar Dauda, Hattush,
\v 3 wanda ya zama na zuriyar Shekaniya, wanda ya zama daga zuriyar Farosh; da kuma Zakariya, kuma tare da shi akwai mazaje 150 da aka lisafta su cikin rubutattun tarihin zuriyarsu.
\s5
\v 4 Na zuriyar Fahat Mowab, Elihonai ɗan Zerahiya kuma tare da shi akwai mazaje ɗari biyu.
\v 5 Na zuriyar Zatti, Ben Yahaziyel kuma tare da shi akwai mazaje ɗari uku.
\v 6 Na zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan kuma tare da shi an lisafta mazaje hamsin.
\v 7 Na zuriyar Ilam, Yeshayya ɗan Ataliya kuma tare da shi an lisafta mazaje saba'in.
\s5
\v 8 Na zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mikayel kuma tare da shi an lisafta mazaje tamanin.
\v 9 Na zuriyar Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel kuma tare da shi aka lisafta mazaje 218.
\v 10 Na zuriyar Bani, Shelomit ɗan Yesofiya kuma tare da shi aka lisafta mazaje 160.
\v 11 Na zuriyar Bebai, Zakariya ɗan Bebai kuma tare da shi aka lisafta mazaje ashirin da takwas.
\s5
\v 12 Na zuriyar Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan kuma tare da shi aka lisafta mazaje 110.
\v 13 Waɗanda suke daga zuriyar Adonikam suka zo daga baya. Waɗannan su ne sunayensu: Elifelet, Yewuyel, tare da Shemayya kuma mazaje sittin ne suka zo tare da su.
\v 14 Na zuriyar Bigbai, Uttai da Zakku kuma tare da shi aka lisafta mazaje saba'in.
\s5
\v 15 Na tara matafiyan a mashigin daya tafi har zuwa Ahaba, kuma muka yi sansani a nan kwana uku. Na bincike mutanen da kuma firistoci, amma babu wani daga zuriyar Lebi a nan.
\v 16 Sai na aika a kirawo mani Eliyeza, da Ariyel, da Shemayya, da Elnatan, da Yarib, da kuma Elnatan da Natan, da Zakariya da kuma Meshullam - waɗanda su ne shugabanni - da kuma Yoyarib tare da Elnatan waɗanda su ne masu koyarwa.
\s5
\v 17 Daga nan sai na aike su wurin Iddo, shugaban da ke a Kasifiya. Na faɗa masu abin da zasu faɗawa Iddo da kuma danginsa, su bayi na haikali da ke zaune a Kasifiya, wato, su aika mana da bayi domin gidan Allah.
\s5
\v 18 Sai suka aika mana ta hannun Allahnmu mai nagari mutum mai suna Sherebiya, mutum mai tattali. Shi daga zuriyar Mahali ne ɗan Lebi ɗan Isra'ila. Ya zo da 'ya'ya sha takwas da 'yan'uwa.
\v 19 Hashabiya ya zo tare da shi. Haka kuma akwai Yeshayya, ɗaya daga cikin 'ya'yan Merari, da ɗan'uwansa tare da 'ya'yansu, dukkan su mazaje ashirin.
\v 20 Cikin waɗanda aka ɗaurawa hidimar haikali, waɗanda Dauda da bayinsa suka ɗora wa haƙin yiwa Lebiyawa hidima: 220, kowanne ɗayansu aikinsa bisa ga sunansa.
\s5
\v 21 Sai nayi shelar azumi a mashigin Ahaba domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu biɗi hanya madaidaiciya dominmu, domin ƙanananmu, da dukkan mallakarmu.
\v 22 Na ji kunyar tambayar sarki sojoji ko dawakai da zasu yi tsaronmu daga maƙiya a hanya, gama mun gaya wa sarki, 'hannun Allah na bisa dukkan waɗanda suka neme shi da gaskiya, amma ƙarfinsa da fushinsa na bisa dukkan waɗanda suka manta da shi.'
\v 23 Sai muka yi azumi muka nemi Allah game da wannan, muka yi roko gare shi.
\s5
\v 24 Daga wannan sai na zaɓi mazaje guda sha-biyu daga cikin shugabannin firistoci: Sherebiya, Hashabiya, da kuma yan'uwansu guda goma.
\v 25 Na auna masu azurfa goma, da zinariya, da kayayyaki da baye-baye na gidan Allah da sarki, da mashawartansa da kuma shugabanninsu, da dukkan Isra'ila suka bayar hannu sake.
\s5
\v 26 Sai na auna cikin hannunsu azurfa talanti 650, talanti ɗari na kayayyakin azurfa, talanti ɗari na zinariya,
\v 27 kwanonin zinariya guda ashirin waɗanda aka haɗa su dukka aka ƙimanta farashinsu akan sulallan zinari dubu ɗaya, da kuma a kan gogaggun tagulla biyu masu daraja kamar zinariya.
\s5
\v 28 Sa'an nan na ce masu, "An keɓe ku ga Yahweh, da waɗannan kayayyakin, kuma azurfar da zinariyar dukka baiko ne na yardar rai ga Yahweh, Allah na kakaninku.
\v 29 Ku kula da su ku kuma adanasu, har sai kun auna su a gaban shugabannin firistoci, da Lebiyawa, da kuma shugabannin kakannin zuriyar Isra'ila a Yerusalem cikin ɗakunan gidan Allah."
\v 30 Su firistoci da kuma Lebiyawa suka yi na'am da azurfa, da zinariya da kuma kayayyakin da aka auna domin su tafi da su Yerusalem, zuwa gidan Allahnmu.
\s5
\v 31 Muka fito daga mashigin Ahaba a rana ta sha biyu na watan farko domin mu tafi Yerusalem. Hannun Allahnmu na a bisanmu; ya kare mu daga hannun maƙiyanmu da kuma waɗanda suka yi niyyar yi mana kwanto a kan hanya.
\v 32 Sai muka shiga Yerusalem muka kwana uku a cikinta.
\s5
\v 33 Daga nan a rana ta huɗu aka auna azurfa, da zinariya, da kuma kayayyakin cikin gidan Allahnmu ta hannun Meremot ɗan Yuriya firist, kuma tare da shi akwai su Eliyeza ɗan Fenihas, Yozabad ɗan Yeshuwa, da kuma Nodiya ɗan Binnui Balebi.
\v 34 Aka tabbatar da jimilla da nauyin komai. Dukkan nauyin komai aka rubuta a wannan lokacin.
\s5
\v 35 Waɗanda suka komo daga bautar talala, su mutanen 'yan gudun hijira, suka miƙa ƙonannun baye-baye zuwa ga Allah na Isra'ila: raguna goma sha biyu, awakai tasa'in da shida, tumaki guda saba'in da bakwai, da kuma tunkiyoyi goma sha biyu domin hadayar zunubi. Dukkansu hadayu ne na ƙonawa na Yahweh.
\v 36 Sa'an nan suka ba da umarnai na sarki ta hannun manyan shugabannin sarki da kuma gwamnonin Lardin Gaba da Kogi. Sai kuma suka taimaki jama'ar da kuma gidan Allah.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Bayan waɗannan abubuwa sun faru, shugabanni suka same ni suka ce, "Mutanen Isra'ila, da firistoci da Lebiyawa basu keɓe kansu daga mutanen sauran ƙasashe ba da kuma abin ƙyamarsu: Kan'aniyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Yebusiyawa da Ammoniyawa da Mowabiyawa da Masarawa da kuma Amoriyawa.
\v 2 Domin sun ɗauki wasu daga cikin 'yan matansu da samarinsu, kuma sun hada mutane masu tsarki da sauran mutanen ƙasashen, shugabanni da magabata su ne na farko ga wannan rashin bangaskiya."
\s5
\v 3 Lokacin da na ji wannan, na yayyage rigata da alkyabbata na kuma tsittsige gashin kaina da gemuna, sai na zauna a ruɗe.
\v 4 Sai dukkan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra'ila saboda wannan rashin aminci da suka same ni lokacin da nake zaune ina jin kunya har baikon yamma.
\s5
\v 5 Amma a lokacin baikon yamma sai na tashi daga matsayin ƙasƙanci a cikin rigata da alkyabbata a yayyage, na russuna da gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Yahweh Allahna.
\v 6 Na ce, "Ya Allahna, ina jin kunya da takaici in ɗaga fuskata gare ka, muguntarmu ta ƙaru a kanmu, kuma zunubanmu sun yi girma har sun kai sammai.
\s5
\v 7 Tun daga lokacin kakanninmu har yanzu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu sun bada mu a hannun sarakunan wannan duniya, ga takobi, ga bauta, da ganima da kuma kunyatar da mu, kamar yadda muke a yau.
\s5
\v 8 Amma yanzu a ƙaramin lokaci, alheri daga Yahweh Allahnmu ya zo ya bar mana ringi ya kuma bamu wuri a wurinsa mai tsarki. Wannan yasa Allahnmu ya buɗe mana idanu, ya kuma bamu 'yar wartsakewa daga bautarmu.
\v 9 Domin mu bayi ne, amma duk da haka Allahnmu bai manta da mu ba amma ya cika alƙawarinsa da amincinsa a gare mu. Ya yi wannan ta wurin sarkin Fasiya domin ya bamu ƙarfi, don mu sake gina gidan Allahnmu mu kuma sake gyaransa. Ya yi wannan saboda ya bamu tsaron gina garu a Yahuda da Yerusalem.
\s5
\v 10 Amma yanzu, Allahnmu, me zamu ce bayan wannan? Mun manta da umarnanka,
\v 11 umarnan daka ba bayinka annabawa, daka ce, "Wannan ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta ƙazamtaciyar ƙasa ce. Ta ƙazamtu ta wurin mutanen ƙasar da abubuwan ƙyamarsu. Sun cikata daga ƙarshe zuwa ƙarshe da abubuwansu na ban ƙyama.
\v 12 Saboda haka, kada ku bada 'ya'yanku 'yan mata su auri 'ya'yansu maza; kada ku ɗauki 'ya'yansu mata don 'ya'yanku maza, kuma kada ku nemi salamarsu da jin daɗi, don zaku yi ƙarfi ku ci abu mai kyau a ƙasar, domin zaku sa 'ya'yanku su gaje ta a dukkan lokaci."
\s5
\v 13 Bayan da dukkan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa - tun da kai, Allanmu, ka ɗauke dukkan laifoffinmu ka kuma bar mana ringi -
\v 14 ko zamu sake karya umarninka mu kuma yi auratayya tare da waɗannan mutane da ke ƙazamtattu? Ba zaka yi fushi da mu ka shafe mu don kada a sami wani da ya rage, har babu wani da zai tsira ba?
\s5
\v 15 Yahweh, Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama mun zama 'yan ringi da suka tsira a wannan rana. Duba! Ga mu nan gabanka da zunubanmu, don ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Sa'ad da Ezra ya ke yin addu'a da roƙon gafara, ya yi kuka har yasa kansa ƙasa a gaban gidan Allah. Sai babban taron jama'a maza da mata da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa, don mutane na kuka mai zafi sosai.
\v 2 Shekaniya ɗan Yehiyel na zuriyar Elam ya ce da Ezra, "Mun yiwa Allahnmu rashin aminci har mun auri mata bãƙi daga mutanen ƙasar waje. Amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila.
\s5
\v 3 Saboda haka yanzu bari muyi alƙawari da Allahnmu mu kori dukkan matan da 'ya'yansu bisa ga umarnin shugabanni da waɗanda suke rawar jiki don umarnin Allahnmu, bari a yi haka bisa ga doka.
\v 4 Tashi, domin wannan hakinka ne ka aiwatar, mu kuma muna tare da kai. Ka yi ƙarfin hali, ka yi wannan."
\s5
\v 5 Ezra kuwa ya tashi, yasa shugabannin firistoci, Lebiyawa, da dukkan Isra'ila su yi alƙawarin aiki ta wannan hanyar. Saboda haka dukkansu suka ɗauki alƙawarin rantsuwa.
\v 6 Sai Ezra ya tashi daga gidan Allah, ya tafi ɗakunan Yehohanan ɗan Eliyashib. Bai ci ko da gurasa ba bai kuma sha ruwa ba, tun da ya ke yana baƙinciki a kan rashin amincin waɗanda suka yi a zaman talala.
\s5
\v 7 Saboda haka suka aika da magana a Yahuda da Yerusalem ga dukkan mutane da suka komo daga zaman talala su kasance a Yerusalem.
\v 8 Duk wanda bai zo ba a cikin kwana uku bisa ga umarni daga shugabanni da dattawa zai rasa dukkan abin da ya mallaka za a kuma ware shi daga cikin babban taron mutanen da suka dawo daga zaman talala.
\s5
\v 9 Sai dukkan mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Yerusalem a cikin kwana uku. A ranar ashirin ga watan tara. Dukkan mutanen suka tsaya a dandalin gidan Allah, suna kuma rawar jiki saboda maganar da kuma ruwan sama.
\v 10 Ezra firist kuma ya miƙe tsaye ya ce, "Ku kunyi rashin aminci. Kun zauna da mata bãƙi ta haka kuka ƙarawa Isra'ila laifi.
\s5
\v 11 Amma yanzu sai ku bada yabo ga Yahweh, Allah na kakanninku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware daga mutanen ƙasar da mata bãƙi.
\s5
\v 12 Dukkan taron suka amsa da babbar murya, '"Za muyi kamar yadda ka ce.
\v 13 Amma, akwai mutane da yawa, kuma lokacin marka ne. Ba mu da ƙarfin tsayawa a waje, kuma wannan ba aikin da za ayi shi a kwana ɗaya ko biyu bane, tun da mun yi babban laifi a wannan al'amari.
\s5
\v 14 Saboda haka bari shugabanninmu su wakilci dukkan taron. Bari dukkan waɗanda suka bar baƙin mata su zauna a biranenmu su zo su sa lokaci tare da dattawan birni da kuma alƙalan birnin har sai fushin Allah ya huce daga kanmu.
\v 15 Yonatan ɗan Asahel da Yazeyya ɗan Tikba ne basu yarda da wannan ba, da Meshullam da Shabbetai Balebi suka goyi bayansu.
\s5
\v 16 Saboda haka mutane waɗanda suka komo daga zaman talala suka yi wannan. Ezra firist ya zaɓi maza, da dattawa kakanin zuriyarmu da gidaje - dukkansu kuwa ta wurin sunaye, sai suka duba al'amarin a kan rana ta farko ga wata na goma.
\v 17 Sun gama binciken a rana ta farko a wata na farko ga mazajen da suke zama tare da baƙin mata.
\s5
\v 18 A cikin zuriyar firistoci ma akwai waɗanda suke zama da bãƙin mata. A cikin zuriyar Yeshuwa ɗan Yehodak da ɗan'uwansa su ne Mãseyya, Eliyeza, Yarib da Gedaliya.
\v 19 Suka yi niyyar sakin matansu. Tun da su masu laifi ne, suka bada baikon rago daga cikin garkensu don laifinsu.
\s5
\v 20 A cikin zuriyar Imma akwai Hanani da Zebadiya.
\v 21 A cikin zuriyar Harim akwai Mãseyya da Iliya da Shemayya da Yehiyel da Uzziya.
\v 22 A cikin zuriyar Fashu akwai Elihonai da Mãseyya, Isma'il da Netanel da Yozabad da Elasa.
\s5
\v 23 A cikin Lebiyawa akwai Yozabad da Shimei da Kelayya - wato Kelita, Fetahiya, Yahuda da Eliyeza.
\v 24 a cikin mawaƙa akwai Eliyashib.
\v 25 A cikin masu tsaron ƙofa akwai Shallum, Telem da Uri. A cikin sauran Isra'ilawa - a cikin zuriyar Farosh akwai Ramiya, Izziya, Malkiya, Miyamin, Eliyeza, Malkiya da Benayya.
\s5
\v 26 A cikin zuriyar Elam akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot da Iliya.
\v 27 A cikin zuriyar Zattu akwai Elihonai, Eliyashib, Mattaniya, Yeremot, Zabad da Aziza.
\v 28 A cikin zuriyar Bebai akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai da Atlai.
\v 29 A cikin zuriyar Bani akwai Meshullam, Malluk, Adayya, Yashub da Shil Yeremot.
\s5
\v 30 A cikin zuriyar Fahat Mowab akwai Adana, Kelal, Benayya, Mãseyya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi da Manasse.
\v 31 A cikin zuriyar Harim akwai Eliyeza, Ishiya, Malkiya, Shemayya, Shimiyon,
\v 32 Benyamin, Malluk da Shemariya.
\s5
\v 33 A cikin zuriyar Hashum akwai Mattenai, Matatta, Zabad, Elifelet, Yeremai, Manasse, Shimei.
\v 34 A cikin zuriyar Bani akwai Mãdai, Amram, Uwel,
\v 35 Benayya, Bedeya, Keluhi,
\v 36 Waniya, Meremot, Eliyashib,
\s5
\v 37 Mattaniya, Mattenai, da Yãsu.
\v 38 A cikin zuriyar Binnuyi akwai Shimei,
\v 39 Shelemiya, Natan, Adayya,
\v 40 Maknadebai, Shashai, Sharai,
\s5
\v 41 Azarel, Shelemiya, Shemariya,
\v 42 Shallum, Amariya da Yosef.
\v 43 A cikin zuriyar Nebo: Yehiyel, Matitiya, Zabad, Zebina, Yaddai da Yowel da Benayya.
\v 44 Dukkan waɗannan sun auro mata bãƙi kuma suna da 'ya'ya tare da wasun su.