ha_ulb/14-2CH.usfm

1686 lines
136 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 2CH
\ide UTF-8
\h Littafin Tarihi Na Biyu
\toc1 Littafin Tarihi Na Biyu
\toc2 Littafin Tarihi Na Biyu
\toc3 2ch
\mt Littafin Tarihi Na Biyu
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Aka ƙarfafa Suleman ɗan Dauda a cikin mulkinsa, Yahweh Allahnsa na tare da shi ya kuma sa shi ya zama da iko sosai.
\s5
\v 2 Suleman ya yi magana da dukkan Isra'ila, hafsoshi dubu-dubu dana ɗari-ɗari, da mahukunta da dukkan sarakuna a Isra'ila, da shugabannin gidajen ubanni.
\v 3 Suleman da dukkan taro suka tafi babban tudu a Gibiyon, domin a can ne rumfar taruwa ta Allah take, wadda Musa bawan Yahweh ya yi a cikin jeji.
\v 4 Amma Dauda ya kawo akwatin alƙawari na Allah daga Kiriyat Yerim zuwa wurin da ya keɓe dominsa. Domin ya kafa mata rumfa a Yerusalem,
\v 5 Bugu da ƙari bagadin jan ƙarfen da Bezalel ɗan Uri ya yi yana wurin a gaban rumfar taruwa ta Yahweh; Suleman da dukkan taron suka tafi wurinta.
\s5
\v 6 Suleman ya tafi can wurin bagadi na tagulla a gaban Yahweh, wadda take a rumfar taruwa, ya miƙa baye-bayen ƙonawa guda dubu a kansa.
\v 7 Allah ya bayyana ga Suleman a wannan dare ya cemasa, "ka tambaya! Me zan baka?"
\s5
\v 8 Suleman ya ceda Allah, '"Ka nuna babban amintaccen alƙawari ga Dauda mahaifina, kuma ka maida ni sarkin mutanensa a madadin sa.
\v 9 Yanzu, Yahweh Allah, sai ka cika alƙawarin da kayi wa mahaifina Dauda, domin ka maida ni sarki kan mutane masu ɗumbin yawa kamar ƙasa.
\v 10 Yanzu sai ka bani hikima da ilimi domin in iya jagorancin mutanen nan, domin wane ne zai iya yiwa mutanenka hukunci, su da keda yawa sosai?"
\v 11 Allah ya ceda Suleman, "Saboda wannan ne yake zuciyarka, kuma domin baka roƙi wadata ba, ko kuɗi, ko girma, ko kuma ran waɗanda ke ƙinka, ko kuma tsawon ranka ba, amma ka roƙi hikima da ilimi domin kanka, domin ka iya mulkin mutanena, waɗanda na maishe ka sarki a kansu, to wannan shi ne abin da zan yi.
\s5
\v 12 Yanzu zan baka hikima da ilimi. Hakannan zan baka arziki da wadata da girma, da ba a taɓa samun sarki kamarka a baya ba, ba kuma za a samu a bayan ka ba."
\v 13 To sai Suleman ya komo Yerusalem wuri mai tudu da kea Gibiyon, daga wurin rumfar taruwa; ya yi sarauta akan Isra'ila.
\s5
\v 14 Suleman ya tattara karusai da mahayan dawakai, yana da karusai 1,400 da mahayan dawakai dubu goma sha biyu waɗanda yasa a biranen karusai da kuma tare da shi sarki, a Yerusalem.
\v 15 Sarki ya samar da zinariya da azurfa birjik kamar duwatsu a Yerusalem, ya kuma samar da itacen sida sosai kamar itacen ɓaure da ke cikin kwaruruka.
\s5
\v 16 Game da sayo dawakai daga Masar da Kuye domin Suleman, fatakensa ne suka sayo su daga Kuye cikin rahusa.
\v 17 Suka sayo karusa daga Masar a awo ɗari shida na zinariya, da kuma doki akan shekel 150. Suka kuma sayar da wasu ga sarakunan Hitiyawa da Aremiyawa.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Suleman kuma ya bada umarni domin ginin gida saboda sunan Yahweh da kuma gina fãda domin masarautarsa.
\v 2 Suleman yasa mutune dubu saba'in su kwaso kayayyaki, mutane dubu tamanin masu saran duwatsu a cikin tsaunuka, da kuma mutane dubu 3,600 su dinga kula da su.
\v 3 Suleman ya aika da saƙo zuwa sarki Hiram na Taya cewa "Kamar yadda ka yi ga mahaifina Dauda, kana aiko masa da itacen sida domin ya gina gidan da zai zauna, to sai kayi mani haka.
\s5
\v 4 Duba ina gab da gina gida saboda sunan Yahweh Allahna, in keɓe shi dominsa, in ƙona turare mai ƙamshi a gabansa, in kuma kawo gurasa ta kasancewarsa da kuma hadaya ta ƙonawa safe da yamma, da ranakun asabarci da sabobbin watanni, da kuma ayyanannun bukukuwa domin Yahweh Allahnmu. Wannan na har abada ne, domin Isra'ila.
\v 5 Gidan da zan gina zai zama da girma sosai, domin Allahnmu mai girma ne fiye da dukkan wasu alloli.
\s5
\v 6 Amma wane ne zai iya gina gida domin Allah, da yake duniya da dukkan sammai da kansu basu ishe shi ba? Wane ni da zan gina masa gida, ba sai dai kawai in ƙona masa hadaya ba?
\v 7 To sai ka aiko mani da mutum da ya ƙware a aikin zinariya, azurfa, tagulla, jan ƙarfe, da shunayya, da ja, da shuɗin u'lu, mutum wanda ya iya dukkan ingantattatu sassaƙa. Zai kasance tare da ƙwararrun mutane waɗanda ke tare da ni a Yahuda da Yerusalem, wanda Dauda mahaifina ya yi tanadi.
\s5
\v 8 Ka aiko mani da itacen sida dana sifires da algun daga Lebanon. Duba barorina zasu tafi tare da barorinka,
\v 9 domin a samar da katakai sosai, domin gidan da nake shirin ginawa zai zama babba da kuma ban mamaki.
\v 10 Duba zan ba barorinka mutanen da zasu saro katakan, da kuma awo dubu ashirin na niƙaƙƙiyar alkama, da awo dubu ashirin na sha'ir, da salkunan ruwan inabi dubu ashirin, da kuma santulan mai guda dubu ashirin."
\s5
\v 11 Sai Hiram, sarkin Taya ya amsa a rubuce ya aika wa Suleman: "Saboda Yahweh yana ƙaunar mutanensa, sai ya naɗa ka sarki a kansu."
\v 12 Bugu da ƙari Hiram yace, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda ya hallici sama da duniya, wanda ya ba sarki Dauda ɗa mai hikima, da baiwa da kirki da fahimi, wanda zai gina gida domin Yahweh, da kuma fãda domin kansa.
\s5
\v 13 Yanzu na aiko da mutum mai fasaha, da baiwa da fahimi, shi ne Huram-Abi.
\v 14 Shi ɗan wata mata ne a cikin 'ya'yan Dan. Mahaifinsa ya zo ne daga Taya. Shi ƙwararre ne a aikin zinariya da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da duwatsu, da katakai, da shunayya, da shuɗi, da jan ulu, da lilin mai kyau. Hakannan kuma ƙwararre ne a fannin kowacce irin sassaƙa da zãne. Sai a samar masa wuri a cikin mutanenka ƙwararru da keyi maka aiki, da kuma na shugabana, Dauda, mahaifinka.
\s5
\v 15 Yanzu kuma da alkama da riɗi, da maida ruwan inabi, wanda shugabana ya yi magana, sai ya aiko da waɗannan abubuwan ga bayinsa.
\v 16 Zamu saro katako daga Lebanon, gwargwadon yawan katakon da kake bukata. Zamu kawo maka har zuwa tekun Yoffa, sai ka ɗauke su zuwa Yerusalem."
\s5
\v 17 Suleman ya ƙirga dukkan baƙi da kea ƙasar Isra'ila, ya bi irin fasahar da Dauda mahaifinsa ya mora, ya ƙirga su aka sami mutum 153,600.
\v 18 Yasa dubu saba'in daga cikinsu su suke ɗaukar kaya, dubu tamanin kuma masu saro katako a kan duwatsu, sai 3,600 su zama masu duba aikin da kuma sa mutanen suyi aikin
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Sai Suleman ya fara gina gidan Yahweh a Yerusalem akan Tsaunin Moriya, inda Yahweh ya bayyana ga Dauda mahaifinsa. Ya shirya wurin da Dauda ya tsara dominsa, a masussukar Ornan na Yebusiya.
\v 2 Ya fara ginin a rana ta biyu ta watan, a shekara ta huɗu ta mulkinsa.
\v 3 Wannan shi ne fasalin ginshiƙin da Suleman ya kafa domin gidan Allah. ya yi amfani da tsohon salon awo, tsawonsa kamu sittin ne, sai faɗinsa kamu ashirin ne.
\s5
\v 4 Awon harabar daga gaban gidan ya kai kamu ashirin, dai-dai da faɗin ginin. Tsayinsa kuma kamu ashirin ne, Suleman kuma ya dalaye cikin ginin da tsantsar zinariya.
\v 5 ya yi wa rufin ainihin cikin harabar ado da sifires, waɗanda ya dalaye da zinariya mai kyau, waɗanda ya sassaƙa da itatuwan dabino da sarƙoƙi.
\s5
\v 6 ya yi wa gidan ado da duwatsu masu daraja; zinariyar an samo ta ne daga Farbayim.
\v 7 Hakannan ya yi daɓen ƙasa da bango, da ƙofofin da zinariya; da sassaƙaƙƙun kerubim a jikin bangayensa.
\s5
\v 8 Ya gina wuri mafi tsarki. Tsawonsa ya kai awo ashirin dai-dai da faɗin ginin, haka kuma faɗin gidan shi ma kamu ashirin ne. Ya shafe shi da tsantsar zinariya dai-dai da yawan talanti dubu ɗari shida.
\v 9 Nauyin awon ƙusa ya kai awo hamsin na zinariya. Ya shafe shi har sama da zinariya.
\s5
\v 10 Ya yi siffofin kerubim guda biyu domin wuri mafi tsarki; masu aikin sassaƙa suka dalaye su da zinariya.
\v 11 Faɗin fuka-fukan kerubobin kamu ashirin ne tsawonsu gaba ɗaya; Fuffuken kerub ɗin ya kai awo biyar a tsawo, wanda ya kai har bangon ɗakin; shi ma ɗaya fuffuken kamu biyar ne, yana taɓa fuffuken ɗaya kerub ɗin na farko.
\v 12 Fuffuken ɗaya kerub ɗin ma kamu biyar ne, ya kai har bangon ɗakin; ɗayan fuffuken ma kamu biyar ne, yana taɓa fuffuken kerub na farko.
\s5
\v 13 Fuka-fukan waɗannan kerubobin sun kai faɗin awo ashirin. Kerubobin suka tsaya kan ƙafafunsu, fuskokinsu na fuskantar babban ɗakin taron.
\v 14 Ya mayar da labulen shuɗi, da shunayya, da jan ulu, ya sassaƙa zãnen kerubobi a kansa.
\s5
\v 15 Hakannan Suleman ya kafa ginshiƙai guda biyu kowanne tsawonsa ya kai kamu talatin da biyar a tsawo, domin a gaban, abubuwan da kekansu sun kai kamu biyar na tsawo.
\v 16 Ya yi sarƙoƙi domin ginshiƙan ya kuma dora su a kansu; hakannan yasa turaren ƙanshi ya haɗa su a jikin sarƙar.
\v 17 Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya daga hannun hagu, ɗaya kuma daga hannun dama, yasa wa ginshiƙan hannun dama suna Yakin, na hannun hagun kuma Bo'aza.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Hakanan ya yi bagadi na tagulla; tsawonsa kamu hamsin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin ne, tsawonsa kuma goma ne.
\v 2 Hakannan ya yi wani kewayayyen tafki na ƙarfe, kamu goma daga baki zuwa baki. Tsawonsa kamu biyar ne, tafkin kuma a kewaye kamu talatin ne.
\v 3 A ƙarƙashin bakin tafkin akwai bijimai kewaye, kowanne awo goma, aka yi zuɓin ɗaya tare da tafkin sa'ad da aka yi zuɓin tafkin kansa.
\s5
\v 4 Babban madatsar da ake kira "Tafkin" aka ɗora shi bisa bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku yamma, uku kudu, uku kuma gabas. Aka ɗora "Tafkin" a bisansu kuma gadon bayansu na fuskantar ciki.
\v 5 "Bangajin" ya yi kaurin damtsen hannu, kuma aka goge bakinsa kamar bakin kofi, kamar buɗewar fure. "Tafkin" yana ɗaukar kimanin garwa dubu uku ta ruwa.
\v 6 Hakannan ya yi tafkuna goma domin wankin abubuwa; yasa biyar daga ɓangaren kudu, biyar kuma daga arewa; za a dinga wanke kayayyakin miƙa baiko na ƙonawa a cikinsu. Babban madatsar da aka fi sani da "Tafki" firistoci ne suke amfani da ita domin wanke-wanke.
\s5
\v 7 ya yi sandunan zinariya na ajiye fitilu guda goma kuma an tsara su ne kamar yadda aka umarta; ya ajiye su a cikin haikali, biyar a hannun dama biyar a hannun hagu.
\v 8 ya yi tebura goma yasa su a cikin haikalin, biyar a bangon dama, biyar a bangon hagu. Ya yi kwanonin na zinariya guda ɗari.
\s5
\v 9 Bugu da ƙari ya yi harabar firistoci, da babbar haraba da kuma ƙofofi domin harabar ya kuma dalaye ƙofofinsu da tagulla.
\v 10 Ya ajiye madatsar da aka sani da "Tafki" a gefen gabas na haikalin, daga gabas kuma na haikalin, yana fuskantar kudu.
\s5
\v 11 Huram ya yi tukwanen, cebura na ƙarfe da kwanoni na yayyafa ruwa. Da haka Huram ya kammala aikin da ya yi wa Suleman a cikin gidan Allah:
\v 12 ginshiƙai guda biyu, gammunan biyu masu fasalin kwano da kebisa ginshiƙin biyu, tsare-tsaren aikin ado biyu da aka yi domin rufe gammunan biyu masu fasalin kwano waɗanda ke bisa ginshiƙan.
\v 13 Ya kuma yi siffofin ruman guda ɗari huɗu domin suturta waɗannan kayayyakin: ya kawo dozin biyu na kayan kyalli domin a adana bangazan da kekan ginshiƙan.
\s5
\v 14 Hakannan ya yi matokarai domin kawo tafkunan su zauna a matokaran;
\v 15 tafki ɗaya bijimai sha biyu a ƙarƙashinsa,
\v 16 Hakannan da tukwanen, da ceburan, cokulan nama masu yatsu, da dukkan sauran kayayyaki da Huram-Abi ya ƙera daga gogaggiyar tagulla domin Sarki Suleman, domin gidan Yahweh.
\s5
\v 17 Sarki ya ajiye su a filin Yodon filin yumɓu tsakanin Sukkot da Zaretan.
\v 18 Da haka Suleman ya yi dukkan waɗannan kayyayaki cikin babbar yalwa. Hakika ba a san nauyin tagullar da aka yi aiki da ita ba.
\s5
\v 19 Suleman ya yi dukkan kayan ƙawa da kecikin haikalin Allah da kuma bagadi na zinariya, da kuma teburi inda ake ajiye gurasa;
\v 20 Sandunan ajiye fitilu da fitilun da aka yi domin ƙona hadaya a gaban ɗakin ƙurya - waɗannan anyi su da tsantsar zinariya ne;
\v 21 Hakannan furannin, da fitilun bangazan, da cokulan da abin ƙona turare duk da zinariya tsantsa, aka yi su.
\s5
\v 22 Haka kuma abin gyara fitilu, da cokula, da bangazai da abin ƙona turare duk da tsantsar zinariya aka yi su. Game kuma da ƙofar gidan, da ƙofofinsu na ciki zuwa wuri mafi tsarki da kuma ƙofofin gidan, dake, na haikalin, duk da zinariya aka yi su.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Bayan Suleman ya kammala waɗannan ayyukan domin gidan Yahweh, Suleman ya kawo kayayyakin da Dauda mahaifinsa ya keɓe saboda wannan dalilin, haɗe da zinariya da azurfa, da dukkan kayayyakin ado - ya ajiye su a ma'ajin gidan Allah.
\s5
\v 2 Daga nan Suleman ya tattaro dukkan dattawan Isra'ila, da dukkan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalai na mutanen Isra'ila, a Yerusalem domin su kawo akwatin alƙawari na Yahweh daga birnin Dauda, wato Sihiyona.
\v 3 Dukkan mutanen Isra'ila suka tattaru a gaban sarki a wurin bikin, wanda aka yi a wata na bakwai.
\s5
\v 4 Dukkan dattawan Isra'ila suka zo, Lebiyawa kuma suka ɗauko akwatin alƙawari.
\v 5 Suka kawo akwatin, da rumfar taruwa, da dukkan kayayyakin da kecikin rumfar. Sai firistoci waɗanda ke daga kabilar Lebiyawa suka kawo waɗannan abubuwa
\v 6 Sarki Suleman da dukkan taron mutanen Isra'ila suka taru a gaban akwatIn, suka yi hadaya da shanu har da ba za'a iya ƙirgawa ba.
\s5
\v 7 Sai firistoci suka kawo akwatin alƙawari na Yahweh a wurinsa, a can ɗaki na ƙurya na gidan, zuwa wuri mafi tsarki, a ƙarƙashin fuka-fukan kerubim.
\v 8 Domin kerubim sun buɗe fuka-fukansu a kan wurin akwatin sun kuma rufe akwatin da kuma sanduna da aka ɗauko shi da su.
\s5
\v 9 Sandunan suna da tsawo sosai ana ganin ƙarshensu daga wuri mai tsarki a gaban ɗaki na can ciki, amma ba za a iya ganinsu daga waje ba. Suna nan a wurin har ya zuwa yau.
\v 10 Ba komai a cikin akwatin sai allunan guda biyu da Musa ya saka a Tsaunin Horeb, a lokacin da Yahweh ya ƙulla alƙawari da Isra'ila, bayan sun fito daga Masar.
\s5
\v 11 Sai ya zamana bayan firistoci sun fito daga wuri mai tsarki. Dukkan firistocin da kewurin suka tsarkake kansu ga Yahweh, basu bi tsarinsu na rabe-rabensu ba.
\v 12 Hakannan Lebiyawa da kemawaƙa, dukkansu har da Asaf da Heman da Yedutun da 'ya'yansu da 'yan'uwansu suka yi ado da kaya masu kyau suna kaɗa molo da garayu, da goge, sarewa, suna tsaye a gabas da bagadin. Tare da su akwai firistoci 120 suna hura kakakai.
\s5
\v 13 Sai ya zamana da masu hura kakakin da mawaƙan suna waƙa tare, suna fitar da murya ɗaya domin yabo da godiya ga Yahweh. Sun tada muryoyinsu da kakakinsu da molonsu da kayan kaɗe-kaɗensu, suka kuma yabi Yahweh. Suka rera waƙa cewa, "Domin shi managarci ne domin alƙawarinsa mai aminci ya tabbata har abada." Daga nan sai gidan, wato gidan Yahweh, ya cika da girgije.
\v 14 Firistoci basu iya tsayawa suyi hidima ba saboda girgijen, domin daukakar Yahweh ta cika gidan.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Daga nan sai Suleman ya ce"Yahweh ya cezai zauna a cikin duhu baƙi ƙirin,
\v 2 amma na gina maka wurin zama mai dacewa, wurin da zaka zauna har abada."
\v 3 Bayan wannan sai sarki ya juya ya albarkaci dukkan taron mutanen Isra'ila a lokacin da taron Isra'ila ke tsaye.
\s5
\v 4 ya ce dãma a yabi Yahweh na Isra'ila, wanda ya yi magana da mahaifina Dauda, ya kuma cika shi da hannunsa, cewa,
\v 5 'Tun daga ranar dana fito da mutanena daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani wuri a cikin dukkan kabilun Isra'ila domin in gina gida saboda sunana a can ba. Ban kuma zaɓi wani mutum ya zama sarkin mutanena Isra'ila ba.
\v 6 Duk da haka na zaɓi Yerusalem, domin sunana ya kasance a can, na kuma zaɓi Dauda ya zama sarkin mutanena Isra'ila,'
\s5
\v 7 To a cikin zuciyar mahaifina Dauda ya ƙudurta ya gina gida domin Yahweh Allah na Isra'ila.
\v 8 Amma Yahweh ya cewa Dauda mahaifina in har ka ƙudurta ka gina gida domina ka kyauta daka sa wannan a zuciyarka.
\v 9 Duk da haka ba kaine zaka gina gidan ba; amma ɗanka ne, wanda zai fito daga tsatsonka, shi ne zai gina gida domin sunana.'
\s5
\v 10 Yahweh ya cika maganar da ya faɗa, domin ina tsayawa a maimakon Dauda mahaifina, na kuma zauna a kan gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya alƙawarta. Na kuma gina gida domin sunan Yahweh, Allah na Isra'ila.
\v 11 Na ajiye akwatin alƙawari a can, wanda shi ne alƙawarin Yahweh, wanda ya yi da mutanen Isra'ila."
\s5
\v 12 Suleman ya tsaya a gaban bagadi na Yahweh a gaban dukkan taron Isra'ilawa ya buɗe hannuwansa.
\v 13 Domin ya yi dakali na tagulla, tsawo kamu biyar, fãɗi kamu biyar, bisansa kamu biyar. Ya ajiye shi a tsakiyar harabar haikalin. Ya tsaya a kansa ya kuma durƙusa a gaban dukkan taron Isra'ila, daga nan sai ya buɗe hannuwansa zuwa sammai.
\s5
\v 14 Yace, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a ƙasa, wanda ke cika alƙawari da madawwamiyar ƙauna ga bayinka da suka yi tafiya a gabanka da dukkan zuciyarsu;
\v 15 kai wanda ka riƙe alƙawari da bawanka Dauda mahaifina, abin daka alƙawarta masa. I, kayi magana da bakinka ka kuma cikata da kanka kamar yadda ya ke a yau.
\s5
\v 16 Yanzu Yahweh, Allah na Isra'ila, sai ka cika abin daka alƙawarta wa bawanka Dauda mahaifina, lokacin da kace 'Baza ka taɓa rasa wani mutun a gabana da zai zauna a kan gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka suka lura suyi tafiya bisa shari'ata, kamar yadda kayi tafiya a gabana.'
\v 17 Yanzu, Yahweh, Allah na Isra'ila, ina roƙonka cewa ka tabbatar da alƙawarin da kayi wa bawanka Dauda.
\s5
\v 18 Amma ko Allah zai yi rayuwa da mutum a duniya? duba, duniya ma kanta da sama basu isheka ba, balle kuma wannan haikalin dana gina!
\v 19 Amma duk da haka ina roƙo ka girmama wannan addu'a ta bawanka, da kuma roƙonsa Yahweh Allahna; ka ji addu'a da kuma kukan da bawanka ke yi a gabanka.
\v 20 Dama idanunka da kunnuwanka su kasance a buɗe rana da dare ga wannan haikalin. Wurin da kayi alƙawarin sa sunanka. Dama ka saurari addu'ar bayinka da zasu yi a wannan wurin.
\s5
\v 21 To sai ka saurari roƙe-roƙen bawanka da mutanenka Isra'ila a lokacin da suka yi addu'a suna fuskantar wannan wuri. I, ka saurara daga wurin da kake zaune, daga sammai kuma bayan ka saurara, ka yi gafara.
\s5
\v 22 In mutun ya yi laifi gãba da ɗan'uwansa in an bukace shi da ya rantse a gaban bagadinka a wannan gida,
\v 23 to sai kaji daga sammai ka kuma hukunta bayinka, kayi wa mugu sakaiya, ka kuma ɗora masa hakinsa a kansa. Ka kuma shaida mai adalci mara laifi, ka bashi ladar aikinsa na adalci.
\s5
\v 24 A lokacin da aka ci nasara kan mutanenka Isra'ila ta hannun maƙiya saboda sunyi maka zunubi, in sun juyo wurinka, suka kuma furta sunanka, suka yi addu'a, suka roƙi gafara a gabanka a wannan wuri-
\v 25 to ina roƙo kaji daga sammai ka gafarta zunubin mutanenka Isra'ila; ka komo da su ƙasar daka basu, su da kakaninsu.
\s5
\v 26 Idan sammai suka rufe kuma aka sami fãri saboda mutane sun yi maka zunubi - in sun yi addu'a suna fuskantar wannan wuri, suka furta sunanka, suka kuma juyo daga zunubinsu bayan ka hore su -
\v 27 to sai kaji su a sama ka gafarta zunubin bayinka da mutanenka Isra'ila, lokacin daka bi da su ta hanya mai kyau da zasu bi. Ka aiko da ruwan sama a kan ƙasarka, wadda ka ba mutanenka gãdo.
\s5
\v 28 Ko kuma ace ana yunwa a ƙasar, ko kuma akwai cuta, ko annoba, ko darɓa, ko funfuna; ko kuma ace a kwai magafta da suka kawo hari a ƙofofin birnin ƙasar, ko kuma wata masifa ta afko wa ƙasar ko rashin lafiya_
\v 29 ko kuma ace an yi adduo'i da roƙe-roƙe ta wurin mutum ɗaya ko kuma dukkan mutanenka Isra'ila-ko kuma na sane da annobar da kuma baƙincikin a zuciyarsa lokacin da ya buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali.
\v 30 sai ka saurara daga sama, a wurin da kake zama; ka gafarta ka kuma sãka wa kowanne mutum gwargwadon aikinsa; ka san zuciyarsa, domin kai kaɗai ne kasan zukatan mutane.
\v 31 Kayi wannan domin su ji tsoronka, domin suyi tafiya bisa tafarkunka a cikin dukkan kwanakin da suke a wannan ƙasa daka ba kakaninsu.
\s5
\v 32 Game kuma da băƙi da ba mutanenka Isra'ila ba, amma saboda girman sunanka, da hannunka mai iko, da kuma damtsenka daka miƙa - suka zo suka yi addu'a suna fuskantar wannan wuri,
\v 33 to ina roƙo ka saurara daga sama, wurin da kake zama, ka kuma yi duk abin da băƙin suka roƙe ka, domin dukkan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar mutanenka Isra'ila, domin kuma su san wannan gidan dana gina ana kiransa da sunanka.
\s5
\v 34 Ko kuma in mutanenka suka tafi yaƙi gãba da maƙiyansu, ta kowacce hanya da zaka aike su, sai kuma suka yi addu'a gare ka suna fuskantar wannan birni daka zaɓa, suna kuma fuskantar wannan wuri dana gina domin sunanka.
\v 35 To sai ka saurari addu'arsu da roƙonsu ka taimake su daga sammai.
\s5
\v 36 Ko kuma in sunyi maka zunubi_ tunda ya ke ba wanda baya yin zunub i- ko kuma in kayi fushi da su ka kuma miƙa su ga maƙiya, domin maƙiya su kwashe su su kaisu bauta a ƙasarsu, ko kusa ko nesa.
\v 37 Daga nan a misali in sun gane cewa suna ƙasar bauta, kuma a misali in sun tuba suka kuma nemi tagomashi daga wurinka a ƙasar da suke bauta. A misali kuma idan suka ce, 'Mun yi wauta mun yi zunubi. Mun yi halin mugunta.'
\v 38 A misali idan suka juyo gare ka da dukkan zuciyarsu da ransu a ƙasar da suke bauta, inda suka ɗauke su a matsayin bautar talala, a misali kuma in sun yi addu'a suna fuskantar ƙasarsu, wadda ka ba kakaninsu, da kuma birni daka zaɓa, da kuma gidan da na gina domin sunanka.
\v 39 Daga nan sai kaji addu'oinsu da roƙe-roƙensu ka kuma taimake su, daga sammai a wurin da kake zama ka taimaki al'amarinsu. Ka gafarta wa mutanenka, da suka yi maka zunubi.
\s5
\v 40 Yanzu, Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kuma sa kunnuwanka suji addu'ar da za a yi a wannan wuri.
\v 41 Yahweh Allah, sai ka tashi daga wurin hutawarka, kai da akwatin ƙarfinka. Yahweh kasa firistocinka su rufa da cetonka, ka kuma sa tsarkakanka suyi murna kan alheranka.
\v 42 Yahweh Allah, kada ka juyar da fuskar keɓaɓɓunka daga wurinka. Ka tuna da abubuwan daka alƙawarta na yin aminci ga bawanka Dauda."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Da Suleman ya gama addu'a sai wuta ta sauko daga sama ta cinye baye-baye na ƙonawa da hadayu, sai ɗaukakar Yahweh ta cika gidan.
\v 2 Firistoci basu iya samun damar shiga gidan Yahweh ba, saboda ɗaukakarsa ta cika gidansa.
\v 3 Duk mutanen Isra'ila sun ga yadda wutar tazo daga sama ɗaukakar Yahweh kuma ta sauko a kan gidan, sai suka sunkuyar da kawunansu ƙasa a kan keɓaɓɓen dutse na sujada suka bada godiya ga Yahweh. Suka ce, "Domin shi nagari ne, domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada."
\s5
\v 4 Sai sarki da dukkan mutanen suka miƙa hadaya ga Yahweh.
\v 5 Sarki Suleman ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin, da tumaki da awaki 120,000. Sai sarki da dukkan mutanen suka keɓe gidan Allah.
\v 6 Sai firistoci suka tsaya, kowanne ya tsaya a inda ya ke hidima, hakannan Lebiyawa suna ɗauke da kayan kiɗa na Yahweh, wanda sarki Dauda ya yi domin ya riƙa yin godiya ga Yahweh ta wurin waƙa, "Domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada." Sai dukkan firistoci suka hura kãkãki a gabansu, kuma sai dukkan Isra'ila suka miƙe tsaye.
\s5
\v 7 Sai Suleman ya keɓe tsakiyar haikalin a gaban gidan Yahweh. A can ya miƙa baye-baye ta ƙonawa da kuma kitse na baye-baye na zumunci, domin wannan bagadi na tagulla da ya yi ya gaza ɗaukar baye-baye na ƙonawa, baye-baye ta hatsi, da kitsen.
\s5
\v 8 Sai Suleman da ya yi bukin a wancan lokacin har na kwana bakwai tare kuma da dukkan Isra'ilawa, babban taro ne tun daga Lebo Hamat har zuwa iyakar Masar.
\v 9 A rana ta takwas suka yi taron murna domin sun yi taron keɓe bagadi na kwana bakwai.
\v 10 A rana ta ashirin da uku a wata na bakwai, Suleman ya sallami taron mutanen suka koma gidajensu da murna da farin ciki saboda alheran Yahweh daya nuna ga Dauda da Suleman da kuma Isra'ila, mutanensa.
\s5
\v 11 Da haka Suleman ya kammala gidan Yahweh da kuma gidansa. Duk abin da yazo zuciyar Suleman game da gidan Yahweh da kuma gidansa ya yi su dukka.
\v 12 Sai Yahweh ya bayyana ga Suleman da dare ya kuma ce da shi, "Na ji addu'arka na kuma zaɓi wannan wurin domin kaina domin ya zama gidan miƙa hadaya.
\s5
\v 13 A misali da ace na rufe sammai domin kada ayi ruwa, ko kuma in umarci fări su cinye ƙasar, ko kuma idan na aiko da cuta cikin mutanena,
\v 14 To indan mutanena da ake kira da sunana, zasu yi tawali'u su yi addu'a, su biɗi fuskata, su kuma juya daga mugayen hanyoyinsu, to zan ji daga sama, zan kuma gafarta zunubinsu, in kuma warkar da ƙasarsu.
\v 15 Yanzu idanuna zasu zama a buɗe kunnuwana kuma zasu ji addu'o'in da za ayi a wannan wurin.
\s5
\v 16 Domin yanzu na zaɓa na kuma keɓe wannan gida domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata zasu kasance a can kullum.
\v 17 Kai kuma in zaka yi tafiya a gabana kamar yadda mahaifinka Dauda ya yi, ka kuma yi biyayya da duk abin da na umarce ka ka kuma kiyaye sharuɗana da farillaina,
\v 18 To zan kafa gadon sarautarka, kamar yadda na faɗa a alƙawarina da Dauda mahaifinka, lokacin da nace, 'Ba za a taɓa rasa wani daga cikin zuriyarka ba wanda zai yi mulki a Isra'ila.'
\s5
\v 19 Amma in ka juya, kayi watsi da farillaina da dokokina dana sa a gabanka, kuma idan ka juya ka bautawa gumaka ka russuna masu,
\v 20 To zan tunɓuke su daga ƙasar dana basu. Wannan gidan kuma dana keɓe domin kaina zan kawar da shi daga gare ni, zan kuma maida shi abin habaici da ba'a ga dukkan al'ummai.
\s5
\v 21 Koda ya ke wannan haikalin ya ƙayatu yanzu, duk wanda ya wuce ta gefensa zai razana ya yi tsaki. Zasu ce 'Me yasa Yahweh ya yi haka ga wannan gida da kuma wannan ƙasa?'
\v 22 Sauran zasu amsa suce saboda sun yashe da Yahweh Allahnsu ne, wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, sai kuma suka kakkafa waɗansu gumaku suka russuna masu suka yi masu sujada. Shi yasa Yahweh ya aukar masu da duk wannan masifa."'
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Sai ya kasance a karshen shekaru ashirin da Suleman ya gina gidan Yahweh da kuma gidansa,
\v 2 sai Suleman ya sake gina garuruwan da Hiram ya bayar gare shi, ya kuma zaunar da mutanen Isra'ila a cikinsu.
\s5
\v 3 Sai Suleman ya kai wa Hamatzoba hari ya kuma cinye ta.
\v 4 Ya gina biranen ajiya a cikin hamada, da dukkan birane ƙayatattu da ya gina a Hamat.
\s5
\v 5 Haka kuma sai ya gina Bet Horon na Sama da Bet Horon na Ƙasa, birane masu tsaro mai ƙarfi tare da katangai, ƙofofi, da ƙyamare.
\v 6 Ya gina Balat da dukkan biranen ma'aji da ya mallaka, da dukkan biranem domin karusansa da kuma biranen domin mahayansa, kuma ko mene ne ya yi niyar ginawa domin jin daɗinsa a cikin Yerusalem, cikin Lebanon, da kuma cikin dukkan ƙasashen da keƙarƙashin mulkinsa.
\s5
\v 7 Amma game da dukkan mutanen da aka rage na wajen su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da kuma Yebusiyawa, waɗanda ba daga Isra'ila suke ba,
\v 8 zuriyarsu da aka bari a bayansu cikin ƙasar, waɗanda mutanen Isra'ila basu hallakar ba - Suleman ya maishe su masu aikin tilas, haka suke har wa yau.
\s5
\v 9 Duk da haka, Suleman bai ɗora wa jama'ar Isra'ila aikin tilas ba. A maimakon haka, suka zama sojojinsa, kwamandojinsa, da hafsoshinsa, da kuma kwamandojin karusan jarumawansa da kuma mahaya dawakansa.
\v 10 Waɗannan kuma su ne manyan hafsoshin masu tafiyar da al'amuran masu kula waɗanda ke na Sarki Suleman, 250 ne suke, waɗanda suka kula da mutanen da suka yi aiki.
\s5
\v 11 Sai Suleman ya fito da ɗiyar Fir'auna daga birnin Dauda zuwa gidan da ya gina mata, gama yace, "Matata bazata zauna a gidan Dauda sarkin Isra'ila ba, domin duk inda akwatin alƙawarin Yahweh ya shiga mai tsarki ne."
\s5
\v 12 Sai Suleman ya miƙa baye-baye na ƙonawa ga Yahweh a bisa bagadin Yahweh daya gina a gaban Haikalin.
\v 13 Ya miƙa hadayu kamar yadda ya wajaba cikin shirin kowacce rana; ya miƙa su, yana koyi da yadda aka shimfiɗa su a cikin umurnan Musa, a ranakun Asabaci, sabobbin watanni, da kuma kafaffun bikin sau uku kowacce shekara: Bikin Gurasa Mara Gami, Bikin Mako, da kuma Bikin Bukkoki.
\s5
\v 14 Bisa ga dokokin mahaifinsa Dauda, Suleman ya naɗa ƙungiyoyin firistoci ga aikinsu, Lebiyawa kuma ga matsayinsu, domin suyi yabo ga Allah su kuma yi hidima a gaban firistoci, kamar yadda ya wajaba a kowacce rana. Ya kuma sa matsaran ƙofofi bisa ga tsarinsu a kowacce ƙofa, gama Dauda, mutumin Allah, ya umarta wannan.
\v 15 Waɗannan mutane basu kauce daga dokokin sarki ga firistoci da Lebiyawa ba game da kowanne al'amari, ko game da ɗakunan ajiya.
\s5
\v 16 Dukkan aikin da Suleman ya umartar aka gama, daga ranar da aka kafa harsashen gidan Yahweh har aka gama shi. Gidan Yahweh ya kammalu.
\s5
\v 17 Sai Suleman ya tafi Eziyon Geba daga nan zuwa Elat a gaɓar teku, a ƙasar Idom.
\v 18 Sai Hiram ya aika mashi da jirage da hafsoshinsa suka umarta, mazajen da suka ƙware a sha'anin teku, kuma tare da bayin Suleman suka tafi Ofir suka kuma ɗauka daga nan talanti 450 na zinariya suka kawo wurin Sarki Suleman.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Da sarauniyar Sheba taji game da girman Suleman, sai tazo Yeruslem domin ta gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da doguwar tawaga, tare da raƙuma ɗauke da kayayyakin ƙamshi, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja dayawa. Da ta iso wurin Suleman, sai ta gaya masa dukkan abin da kecikin zuciyarta.
\v 2 Suleman ya bata amsar dukkan tambayoyinta; babu komai mai wuya ga Suleman; babu tambayar da bai bada amsar ta ba.
\s5
\v 3 Da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Suleman da kuma fãdar da ya gina,
\v 4 abincin teburinsa, da yanayin zaman bayinsa, aikin bayinsa da kuma tufafinsu, har da masu ba shi abin sha da irin tufafinsu, da kuma baye-baye na ƙonawa daya miƙa a gidan Yahweh, sai kuma babu sauran hanzari a cikinta.
\s5
\v 5 Ta cewa sarkin, "Gaskiya ne, labarin da naji cikin ƙasata game da maganganunka da hikimarka.
\v 6 Ban yarda da abin da naji ba har sai da nazo nan, kuma da idanuwana na gani. Ko rabi ba a gaya mani ba game hikima da wadatarka! Ka zarce girman da naji game da kai.
\s5
\v 7 Mutanenka masu albarka ne, bayinka kuma waɗanda ke tsayawa gaban ka koyaushe masu albarka ne, domin suna sauraran hikimarka.
\v 8 Mai albarka ne Yahweh Allahnka, wanda ya ke jin daɗinka, wanda ya ɗora ka a bisa kursiyinsa, ka zama sarki domin Yahweh Allahnka. Domin Allahnka na ƙaunar Isra'ila, domin ya kafa su har abada, ya maishe ka sarki bisansu, domin ka aikata gaskiya da adalci!"
\s5
\v 9 Sai ta ba sarki talanti 120 na zinariya da kayan ƙamshi mai yawa da kuma duwatsu masu daraja. Babu kayan ƙamshi mai yawa haka kamar wannan da sarauniyar Sheba ta ba Sarki Suleman da aka ƙara kawo masa kuma.
\s5
\v 10 Bayin Hiram da bayin Suleman, waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kawo kuma katakon algum da duwatsu masu daraja.
\v 11 Da katakan algum ɗin, sarki ya yi matakalai na gidan Yahweh da kuma domin fadarsa, har kuma da garayu da molaye domin mawaƙa. Ba a taɓa ganin irin wannan katakon a ƙasar Yahuda ba.
\v 12 Sarki Suleman ya ba sarauniyar Sheba dukkan abin da ta tambaya; ya bata fiye da abin da ta kawo wa sarki. Sai ta tafi ta koma ƙasarta, ita da bayinta.
\s5
\v 13 Yanzu nauyin zinariyan da yazo wurin Suleman a cikin shekara ɗaya talanti 666 na zinariya ne,
\v 14 ban da zinariyar da 'yan kasuwa da fatake suka kawo. Dukkan sarakunan Arabiya da gwamnoni a cikin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa ga Suleman.
\s5
\v 15 Sarki Suleman ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na bugaggar zinariya. Awo ɗari shida na zinariya ne ya shiga kowacce ɗaya.
\v 16 Ya kuma yi garkuwoyi na bugaggar zinariya guda ɗari uku. Minas uku na zinariya ne ya shiga kowacce garkuwa; sarki ya ajiye su a cikin Gida na Jejin Lebanon.
\s5
\v 17 Sa'an nan sarki ya gina babban kursiyi na hauren giwa ya kuma dalaye ta da zinariya mafi kyau.
\v 18 Da akwai matakalai guda shida na hawan kursiyin, kuma da kujeran ɗora ƙafa harɗe da mazamnin sarautar. A kowanne ɓangaren kursiyin akwai abin ɗora hannu da zakuna biyu tsaye kusa da kowannen su.
\s5
\v 19 Zakuna goma sha biyu suna tsaye a matakalun, ɗaya a kowanne gefe na matakalai shidan. Babu wata masarautar da keda irin wannan kursiyin.
\v 20 Dukkan abubuwan shan ruwan Sarki Suleman na zinare ne, kuma dukkan moɗayen shan ruwa da kea Gida na Jejin Lebanon duk na zallar zinare ne. Babu wadda suke daga azurfa domin azurfa ba abin daraja bane a kwanakin Suleman.
\v 21 Sarkin yana da jiragen ruwa masu tafiya cikin teku, tare da jiragen na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku jiragen sukan tafi su kawo zinariya, azurfa, da kuma hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.
\s5
\v 22 Saboda haka sarki Suleman yafi dukkan sarakunan duniya arziki da kuma hikima.
\v 23 Dukkan sarakunan duniya suka nemi su ga Suleman domin su saurari hikimarsa, wadda Allah yasa cikin zuciyarsa.
\v 24 Waɗanda suka kawo ziyara suka zo masa da kyautai, kayayyaki na azurfa dana zinariya, riguna, kayan yaƙi, da kayan ƙanshi, da kuma dawakai da alfadarai, shekara bayan shekara.
\s5
\v 25 Suleman yana da ɗakunan dawakai har dubu huɗu da karusai, da mahayan dawakai dubu sha biyu, waɗanda ya sanya su cikin birnin karusai tare da shi kuma a cikin Yerusalem.
\v 26 ya yi mulki bisa dukkan sarakuna daga Kogin Yufiretis zuwa ƙasar Filistiyawa, zuwa iyakar Masar.
\s5
\v 27 Sarkin yana da azurfa cikin Yerusalem, yawansu kamar duwatsun ƙasa. Ya maida itacen sida kamar itacen durumi mai yawa da suke ƙauyuka.
\v 28 Aka kawo wa Suleman dawakai daga Masar da kuma daga dukkan ƙasashe.
\s5
\v 29 Game da waɗansu batutuwa game da Suleman, farko da ƙarshe, ba an rubuta su cikin Tarihi na Nathan annabi ba, cikin Annabci Ahiya Ba-shiloni, kuma a cikin Wahayin Iddo Mai duba (wanda ya sami labari game da Yerobowam ɗan Nebat)?
\v 30 Suleman ya yi mulki cikin Yerusalem bisa dukkan Isra'ila har shekara arba'in.
\v 31 Ya yi barci tare da kakanninsa kuma mutanen suka binne shi a cikin birnin Dauda mahaifinsa. Rehobowam, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukkan Isra'ila na zuwa Shekem domin a naɗa shi sarki.
\v 2 Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (domin yana cikin Masar, inda ya guje wa sarki Suleman), sai ya dawo daga Masar.
\s5
\v 3 Sai suka aika aka kirawo shi, kuma Yerobowam da dukkan Isra'ila suka zo; suka yi magana da Rehobowam suka kuma ce,
\v 4 "Mahaifinka yasa karkiyarmu da wuya. Yanzu kuwa, kasa aikin mahaifinka mai wuya ya zama da sauƙi, ka kuma sauƙaƙa karkiya mai nauyin da ya ɗora mana, mu kuma mu bauta maka."
\v 5 Sai Rehobowam yace masu, "Ku komo gare ni bayan kwana uku." Sai mutanen suka tafi.
\s5
\v 6 Sai sarki Rehobowam ya nemi shawara a wurin dattawa waɗanda suka tsaya a gaban Suleman mahaifinsa sa'ad da ya ke raye; yace, "Ta yaya zaku shawarce ni in bada amsa ga waɗannan mutanen?"
\v 7 Suka yi magana da shi suka ce, "Idan kayi alheri ga waɗannan mutanen ka kuma kyauta masu, ka kuma faɗi masu maganganun alheri, sa'annan zasu zama bayin ka koyaushe."
\s5
\v 8 Amma Rehobowam ya yi watsi da shawarar da dattawan suka bashi, amma ya nemi shawara daga matasa waɗanda suka girma tare dashi, waɗanda suka tsaya gabansa.
\v 9 Yace masu, "Wacce shawara zaku bani, domin mu amsa ma mutanen da suka yi magana da ni suka ce, 'Ka rage mana nauyin karkiyar da mahaifinka ya ɗora mana'?"
\s5
\v 10 Samarin da suka yi girma tare da Yerobowam suka yi magana dashi, cewa, "Ga yadda zaka yi magana da mutanen da suka ce maka mahaifinka Suleman yasa ƙarkiyarsu tayi nauyi, amma wai dole kasa ta zama da sauƙi. Ga abin da zaka ce masu, 'Ɗan ƙaramin yatsana yafi ƙugun mahaifina kauri.
\v 11 Don haka yanzu, ko da ya ke mahaifina ya tsananta maku da karkiya mai nauyi, ni zan daɗa bisa karkiyarku. Mahaifina ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunnamai."
\s5
\v 12 Sai Yerobowam da dukkan mutanen suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗi, "Ku dawo wurina a rana ta uku."
\v 13 Sai Rehobowam ya yi masu magana da zafi, ya yi banza da shawarar dattawan.
\v 14 ya yi masu magana bisa ga shawarar Samarin, cewa, "Mahaifina yasa ƙarkiyarku tayi nauyi, amma zan daɗa bisanta. Mahaifina ya yi maku horo da bulala, amma ni zanyi maku horo da kunamai."
\s5
\v 15 Sarki kuwa bai saurari mutanen ba, gama al'amari ne wadda ke faruwa yadda Allah ya shirya, domin Yahweh ya aiwatar da maganarsa wadda Ahiya Bashilone ya faɗi ga Yerobowam ɗan Nebat.
\s5
\v 16 Lokacin da dukkan Isra'ila suka ga cewa sarki bai saurare su ba, sai mutanen suka amsa masa suka ce, "Wanne rabo muke da shi a cikin Dauda? Bamu da gãdo a cikin ɗan Yesse! Kowannenku ya koma ga rumfarsa, Isra'ila. Yanzu ka kula da naka gidan, Dauda." Sai dukkan Isra'ila suka koma rumfunansu.
\s5
\v 17 Amma game da mutanen Isra'ila waɗanda ke zaune cikin biranen Yahuda, Rehobowam ya yi mulki bisansu.
\v 18 Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, wanda ke lura da aikin tilas, amma mutanen suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam ya tsere da sauri cikin karusansa zuwa Yerusalem.
\v 19 Don haka Isra'ila ke tayarwa gãba da gidan Dauda har wa yau.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Da Rehobowam ya isa Yerusalem, ya tattaro gidan Yahuda da Benyamin, 180,000 zaɓaɓɓun mutane waɗanda suke sojoji, suyi yaƙi gãba da Isra'ila, su maido da masarautar ga Rehobowam.
\s5
\v 2 Amma maganar Yahweh tazo wa Shamayya mutumin Allah, cewa,
\v 3 "Ka cewa Rehobowan ɗan Suleman, sarkin Yahuda, da dukkan Isra'ila cikin Yahuda da Benyamin,
\v 4 Yahweh ya faɗi wannan, "Kada ku kai hari ko kuyi yaƙi gãba da 'yan'uwanku. Kowanne dole ya koma ga nasa gidan, domin na sanya wannan ya faru."'" Sai suka yi biyayya da maganganun Yahweh suka kuma juya baya daga harin Yerobowam.
\s5
\v 5 Rehobowam ya zauna cikin Yerusalem ya kuma gina birane domin tsaro.
\v 6 Ya gina Betlehem, Itam, Tekoya,
\v 7 Betzur, Soko, Adullam,
\v 8 Gat, Maresa, Zif,
\v 9 Adorayim, Lakish, Azeka,
\v 10 Zora, Ayyalon, da kuma Hebron. Waɗannan tsararrun birane ne cikin Yahuda da Benyamin.
\s5
\v 11 Ya ƙarfafa wuraren tsaronsu ya sanya ofisoshi a cikinsu, tare da tanadin abinci, da mai, da inabi.
\v 12 Ya sanya garkuwoyi da mãsu a cikin dukkan biranen ya kuma maida su masu ƙarfi sosai. Haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
\s5
\v 13 Firistoci da Lebiyawa daga cikin dukkan Isra'ila suka ƙetara zuwa gare shi daga cikin kan iyakokinsu.
\v 14 Domin Lebiyawan suka bar gonakinsu na noma da kiwo da kaddarorinsu domin su zo Yahuda da Yerusalem, domin Yerobowam da 'ya'yansa maza sun kore su, don kada su sake aiwatar da ayyukan firistoci domin Yahweh.
\v 15 Yerobowam ya naɗa wa kansa firistoci domin wuraren masujadai da kuma gumakan akuya da na maraƙi da ya yi.
\s5
\v 16 Mutane daga dukkan kabilun Isra'ila suka biyo shi, waɗanda suka tsaida zukatansu su biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila; suka zo Yerusalem suyi hadaya ga Yahweh. Allahn Ubanninsu.
\v 17 Sai suka ƙarfafa masarautar Yahuda suka kuma sa Rehobowam ɗan Suleman ya yi ƙarfi lokacin shekaru uku, suka kuma yi tafiya shekaru uku cikin hanyar Dauda da Suleman.
\s5
\v 18 Rehobowam ya ɗaukar wa kansa mata: Mahalat, ɗiyar Yerimot, ɗan Dauda, da Abihayil, ɗiyar Eliyab, ɗan Yesse.
\v 19 Ta haifa masa 'ya'ya maza: Yewush, Shemariya, da Zaham.
\s5
\v 20 Bayan Mahalat, Rehobowam ya ɗauki Ma'aka, ɗiyar Absalom; ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza, da Shelomit.
\v 21 Rehobowam yana ƙaunar Ma'aka, ɗiyar Absalom, fiye da dukkan matansa da ƙwaraƙwaransa (ya ɗauki mata sha takwas da ƙwaraƙwarai sittin, ya kuma zama mahaifin 'ya'ya maza ashirin da takwas da 'ya'ya mata sittin).
\s5
\v 22 Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma'aka ya zama basarake, shugaba a tsakanin 'yan'uwansa; yana tunanin maida shi sarki.
\v 23 Rehobowam ya yi mulki da hikima; ya baza dukkan 'ya'yansa maza cikin dukkan ƙasar Yahuda da Benyamin zuwa kowanne tsararren birni. Ya kuma basu abinci a yalwace ya kuma nemo mataye da yawa domin su.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sai ya kasance, da mulkin Rehobowam ya kafu ya kuma yi ƙarfi, sai ya watsar da shari'ar Yahweh - da dukkan Isra'ila tare da shi.
\s5
\v 2 Ya faru a shekara ta biyar na sarki Rehobowam, Shishak, sarkin Masar, yazo gãba da Yerusalem, saboda mutanen sun yi rashin aminci ga Yahweh.
\v 3 Yazo da karusai ɗari sha biyu da mahaya dawakai dubu sittin. Sojoji babu iyaka suka zo tare da shi daga Masar: Libiyawa, Sukkiyawa, da Kushiyawa.
\v 4 Ya ƙwaci tsararrun birane da kena Yahuda ya kuma zo Yerusalem.
\s5
\v 5 Yanzu Shemayya annabi yazo wurin Rehobowam da shugabannin Yahuda da suka tattaru tare a Yerusalem saboda Shishak. Shemayya yace masu, "Wannan ne abin da Yahweh ya faɗa: Kun yashe ni, don haka nima na bayar daku cikin hannun Shishak."
\v 6 Daga nan shugabannin Isra'ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka kuma ce, "Yahweh mai adalci ne."
\s5
\v 7 Da Yahweh yaga cewa sun ƙasƙantar da kansu, maganar Yahweh tazo ga Shemayya, cewa, "Sun ƙasƙantar da kansu. Ba zan rusa su ba; zan ƙubutar da su na wani matsayi, fushina kuma ba zai zubo bisa Yerusalem ta hannun Shishak ba.
\v 8 Duk da haka, zasu zama bayinsa, domin su fahimci bambanci tsakanin yi mani bauta da kuma bauta wa shugabannin sauran ƙasashen."
\s5
\v 9 Sai Shishak sarkin Masar yazo gãba da Yerusalem ya kuma ɗauke taskokin cikin gidan Yahweh, da taskokin cikin gidan sarki. Ya ɗauke komai da komai; ya ɗauke garkuwoyi ta zinariya da Suleman ya yi.
\v 10 Sarki Rehobowam ya yi garkuwoyi na tagulla a mamadinsu ya miƙa su kuma cikin hannuwan ofisoshin tsaro, waɗanda ke tsaron ƙofofin zuwa gidan sarki.
\s5
\v 11 Sai ya kasance duk sa'ad da sarki ya shiga gidan Yahweh, matsaran zasu ɗauke su; daga nan zasu maido da su cikin gidan tsaro.
\v 12 Da Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, fushin Yahweh ya juya daga gare shi, domin kada a lalatar da shi ɗungun; baya da haka, akwai sauran wasu abubuwan nagarta da ake samu cikin Yahuda.
\s5
\v 13 Sai sarki Rehobowam yasa sarautarsa tayi ƙarfi a Yerusalem, haka kuma ya yi mulki. Rehobowam na da shekaru arba'in da ɗaya sa'ad da ya fara mulki, ya kuma yi mulki shekaru sha bakwai a Yerusalem, birnin da Yahweh ya zaɓa daga dukkan kabilun Isra'ila saboda yasa sunansa a wurin. Sunan mahaifiyarsa Na'ama, Ba'ammoniya.
\v 14 Ya aikata abin da ke mugunta, saboda bai kafa zuciyarsa ba domin ya biɗi Yahweh.
\s5
\v 15 Sauran al'amura kuwa game da Rehobowam, farko da ƙarshe, ba a rubuce suke ba a cikin rubuce-rubucen Shemayya annabi da Iddo mai dubawa, waɗanda kuma suke da lissafe - lissafen asaloli da ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam?
\v 16 Rehobowam ya yi barci da kakanninsa aka kuma binne shi cikin birnin Dauda; Abiya ɗansa ya zama sarki a gurbinsa.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 A cikin shekara ta sha takwas ta sarki Yerobowam, Abiya ya fara mulki bisa Yahuda.
\v 2 ya yi mulki shekaru uku a Yerusalem; sunan mahaifiyarsa Ma'aka, ɗiyar Yuriyel na Gibiya. Aka yi yaƙi tsakanin Abiya da Yerobowam.
\v 3 Abiya ya tafi cikin yaƙin da mayaƙa ƙarfafa, sojoji masu ƙarfin hali, zaɓaɓɓun mutane 400,000. Yerobowam yaja dagar yaƙi gãba da shi tare da zaɓaɓɓun mutane 800,000, ƙarfafa, sojoji masu ƙarfin hali.
\s5
\v 4 Abiya ya tsaya a tsaunin Zemarayim, wanda ke ƙasar tudu ta Ifraim, ya kuma ce, "Ku saurare ni, Yerobowam da dukkan Isra'ila!
\v 5 Baku san cewa Yahweh, Allah na Isra'ila, ya bayar da mulki bisa Isra'ila ga Dauda ba har abada, gare shi da 'ya'yansa bisa tsararren alƙawari?
\s5
\v 6 Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, bawan Suleman ɗan Dauda, ya tashi da tawaye gãba da ubangijinsa.
\v 7 Mutane marasa amfani, ƙasƙantattun jama'a, suka tattaru gare shi. Sun zo gãba da Rehobowam ɗan Suleman, duk da cewa Rehobowam yaro ne kuma bai da ƙwarewa kuma ba zai iya tsayayya da su ba.
\s5
\v 8 Yanzu kunce wai zaku iya ƙin ikon mulkin Yahweh cikin hannun zuriyar Dauda. Ku mayaƙa ne masu yawa, tare daku kuma akwai maruƙan zinariya da Yerobowam ya yi a matsayin alloli dominku.
\v 9 Ba ku kuka kori firistocin Yahweh, zuriyar Haruna, da Lebiyawa ba? Ba kun naɗa wa kanku firistoci bisa ga ɗabi'ar mutanen sauran ƙasashe ba? Duk wanda yazo ya keɓe kansa da ɗan maraƙi da raguna bakwai zai zama firist na abubuwan da ba alloli ba.
\s5
\v 10 Amma mu kam, Yahweh ne Allahnmu, kuma bamu yashe shi ba. Muna da firistoci, zuriyar Haruna, suna bautar Yahweh, da Lebiyawa, waɗanda ke kan aikinsu.
\v 11 Kowacce safiya da maraice suna ƙona wa Yahweh baye-baye na ƙonawa da turaren ƙamshi. Suna kuma shirya gurasar miƙawa a bisa tsastsarkan teburi; suna kuma lura da mazaunin fitila na zinariya tare da fitilunsu, domin su riƙa ci kowacce safiya. Muna kiyaye dokokin Yahweh, Allahnmu, amma kun yashe shi.
\s5
\v 12 Duba, Allah yana tare da mu a bisa kanmu, kuma firistocinsa suna nan tare da kãkãki domin su busa ƙara gãba daku. Mutanen Isra'ila, kada kuyi faɗa gãba da Yahweh, Allah na kakanninku, domin baza kuyi nasara ba."
\s5
\v 13 Amma Yerobowam ya shirya kwanto a bayansu; mayaƙansa suna gaban Yahuda, masu kwanton kuma a bayansu.
\v 14 Da Yahuda suka waiga baya, duba, yaƙin yana gabansu kuma yana bayansu. Suka yi kuka ga Yahweh, firistocin kuma suka busa kãkãki.
\v 15 Dagana mutanen Yahuda suka yi kuwwa; yayin da suka yi kuwwar, sai Allah ya mazge Yerobowam da dukkan Isra'ila a gaban Abiya da Yahuda.
\s5
\v 16 Mutanen Isra'ila suka guje daga gaban Yahuda, Allah kuma ya bayar da su cikin hannun Yahuda.
\v 17 Abiya da mayaƙansa suka kashe su da babban yanka; zaɓaɓɓun mutane 500,000 na Isra'ila suka fãɗi matattu.
\v 18 Ta wannan hanya, mutanen Isra'ila aka kayar da su a wannan lokaci; mutanen Yahuda suka yi nasara saboda sun dogara ga Yahweh, Allah na kakanninsu.
\s5
\v 19 Ya runtumi Yerobowam; Ya ɗauke birane daga gare shi: Betel da kauyukanta, Yeshana da ƙauyukanta, da Efron da ƙauyukanta.
\v 20 Yerobowam bai taɓa sake samun iko ba a lokacin kwanakin Abiya; Yahweh ya buge shi, kuma ya mutu.
\v 21 Amma Abiya ya zama cike da iko; ya ɗaukar wa kansa mata sha huɗu ya kuma zama mahaifin 'ya'ya maza ashirin da biyu da 'ya'ya mata sha shida.
\v 22 Sauran ayyukan da Abiya ya aiwatar, ɗabi'arsa da maganganunsa an rubuta a cikin taƙaitaccen labarin Annabi Iddo.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Abiya ya yi barci tare da kakanninsa, aka kuma bizne shi a cikin birnin Dauda. Asa, ɗansa, ya zama sarki a gurbin sa. A kwanakin sa ƙasar ta kasance shiru na shekaru goma.
\v 2 Asa ya yi abin da kemai kyau da dai-dai a idanun Yahweh Allahnsa,
\v 3 domin ya ɗauke bãƙin bagadai da wuraren tuddai. Ya farfasa ginshiƙan dutse ya kuma datse kafe-kafen Astarot.
\v 4 Ya dokaci Yahuda su biɗi Yahweh, Allah na kakanninsu, su kuma aiwatar da shari'ar da dokokin.
\s5
\v 5 Haka kuma ya ɗauke wuraren tuddai da bagadan turare daga dukkan biranen Yahuda. Masarautar ta sami hutawa a ƙarƙashin sa.
\v 6 Ya gina tsararrun birane a Yahuda, domin ƙasar ta kasance shiru, kuma ba shi da yaƙi a waɗannan shekaru, saboda Yahweh ya ba shi salama.
\s5
\v 7 Domin Asa ya cewa Yahuda, "Bari mu gina waɗannan birane muyi katangai kewaye da su, da hasumiyoyi, da ƙofofi, da ƙarafuna; ƙasar har wayau tamu ce, saboda mun biɗo Yahweh Allahnmu. Mun biɗo shi, kuma ya bamu salama ta kowanne gefe." Sai suka yi gini kuma suka yi nasara.
\v 8 Asa na da mayaƙa da ke ɗaukar garkuwoyi da mãsu; daga Yahuda yana da mutane 300,000, daga kuma Benyamin, mutane 280,000 waɗanda ke ɗauke da garkuwoyi suna kuma jan bakkuna. Dukkan waɗannan ƙarfafa ne, mutane masu ƙarfin hali.
\s5
\v 9 Zera Bakushe yazo gãba da su tare da mayaƙa sojoji miliyan ɗaya da karusai ɗari uku; yazo Maresha.
\v 10 Daga nan Asa ya fita domin ya gamu da shi, suka kuma kafa dãgar yaƙi a kwarin Zefata a Maresha.
\v 11 Asa ya yi kuka ga Yahweh, Allahnsa, ya kuma ce, "Yahweh, babu wani sai kai da zai taimaki wanda ba shi da ƙarfi yayin da ya ke fuskantar masu yawa. Ka taimake mu, Yahweh Allahnmu, domin mun dogara gare ka, kuma a cikin sunanka munzo gãba da wannan babban taro. Yahweh, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum ya yi nasara da kai."
\s5
\v 12 Yahweh ya buge Kushiyawa a gaban Asa da Yahuda; Kushiyawa suka tsere.
\v 13 Asa da sojojin da ketare da shi suka runtume su zuwa Gera. Kushiyawa da yawa suka fãɗi yadda basu iya murmurowa ba, domin an lalatar da su gaba ɗaya a gaban Yahweh da mayaƙansa. Mayaƙan suka kwashe ganima mai yawa.
\s5
\v 14 Mayaƙan suka hallakar da dukkan ƙauyukan da ke kewaye da Gera, domin fargaban Yahweh ya sauko bisa dukkan mazaunansu. Mayaƙan suka washe dukkan ƙauyukan, kuma akwai ganima da yawa a cikin su.
\v 15 Mayaƙan kuma suka hallakar da rumfar zaman makiyaya mayawata; suka kwashe ganimar tumaki masu yawa, tare da raƙuma, sa'an nan suka koma Yerusalem.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Ruhun Allah yazo bisa Azariya ɗan Oded.
\v 2 Ya fita ya sami Asa ya kuma ce masa, "Ka saurare ni, Asa, da dukkan Yahuda da Benyamin: Yahweh yana tare da kai, yayin da kake tare da shi. Idan ka biɗe shi, zaya samu gare ka; amma idan ka yashe shi, zai yashe ka.
\s5
\v 3 Yanzu lokaci mai tsawo, Isra'ila basu tare da Allah na gaskiya, babu firist mai koyarwa, babu kuma shari'a.
\v 4 Amma idan a cikin ƙuncinsu suka juya ga Yahweh, Allahnsu, suka kuma biɗe shi, sai ya samu a gare su.
\v 5 A waɗannan lokuta babu salama ga wanda ya yi tafiyarsa zuwa wani wuri, ko wanda ya yi tafiya zuwa nan; maimako, manyan matsaloli na bisa dukkan mazauna ƙasashen.
\s5
\v 6 Aka karya su gutsu-gutsu, al'umma gãba da al'umma, birni kuma gãba da birni, domin Allah ya azabtar da su da dukkan wahalu iri - iri.
\v 7 Amma ka ƙarfafa, kada kuma ka bar hannunka ya zama kasasshe, domin aikin ka zai sami sakamako."
\s5
\v 8 Sa'ad da Asa yaji waɗannan maganganu, anabcin Oded annabi, sai ya yi ƙarfin hali ya kori ƙazantattun abubuwa daga dukkan ƙasar Yahuda da Benyamin, daga kuma biranen da ya kame daga ƙasar tudu ta Ifraimu, ya kuma sake gina bagadin Yahweh, wanda ke gaban rumfar gidan Yahweh.
\v 9 Ya tattaro dukkan Yahuda da Benyamin, da waɗanda ke zama tare da su - mutane daga na Ifraim da Manasse, daga kuma Simiyon. Domin sunzo daga Isra'ila zuwa gare shi babban taro, da suka ga cewa Yahweh Allahnsa na tare da shi.
\s5
\v 10 Sai suka tattaru tare a Yerusalem a cikin wata na uku, a cikin shekara ta sha biyar na mulkin Asa.
\v 11 Suka yi hadaya ga Yahweh a wannan rana daga cikin ganimar da suka kawo: shanu ɗari bakwai da tumaki da awaki dubu bakwai.
\s5
\v 12 Suka shiga cikin alƙawari su biɗi Yahweh, Allah na kakanninsu, da dukkan zuciyarsu kuma da dukkan ransu.
\v 13 Suka yarda da cewa duk wanda ya ƙi ya biɗi Yahweh, Allah na Isra'ila, za a kashe shi, ko da ƙarami ne ko babba, ko namiji ko mace.
\s5
\v 14 Suka yi rantsuwa ga Yahweh da babbar murya, tare da sowa, kuma da kãkãki da ƙahonni.
\v 15 Dukkan Yahuda suka yi farinciki da alƙawarin, domin sun yi rantsuwa da dukkan zuciyarsu, suka kuma biɗi Allah da dukkan buƙatunsu, kuma ya samu a gare su. Yahweh ya basu salama a dukkan kewayensu.
\s5
\v 16 Ya kuma cire Ma'aka, kakarsa, daga zama sarauniya, domin tayi ƙazantaccen siffa daga wani ƙarfen Ashera. Asa ya datse ƙazantaccen siffar, ya niƙe shi zuwa turɓaya ya kuma ƙone shi a magudanar Kidron.
\v 17 Amma bisan wurare ba a ɗauke su ba daga Isra'ila. Duk da haka Asa ya sadaukar da zuciyarsa gaba ɗaya dukkan kwanakinsa.
\s5
\v 18 Ya kawo cikin gidan Allah abubuwan mahaifinsa da abubuwansa wanda ke na Yahweh: Kayayyakin azurfa da zinariya.
\v 19 Babu sauran yaƙi kuma har shekara talatin da biyar na mulkin Asa.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Cikin shekara ta talatin da shida na mulkin Asa, Ba'asha, sarkin Isra'ila, ya nuna tsageranci gãba da Yahuda ya kuma gina Rama, domin kada ya bar wani ya tashi ko ya tafi ƙasar Asa, sarkin Yahuda.
\s5
\v 2 Daga nan Asa ya fito da azurfa da zinariya daga ɗakunan ajiya na cikin gidan Yahweh da gidan sarki, ya kuma aika su ga Ben Hadad sarkin Aram, wanda ke zama a Damaskus. Yace,
\v 3 "Bari alƙawari ya kasance tsakani na da kai, kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifi na da mahaifin ka. Duba, na aiko maka da azurfa da zinariya. Ka karya alƙawarinka da Ba'asha, sarkin Isra'ila, saboda ya rabu da ni."
\s5
\v 4 Ben Hadad ya saurari sarki Asa ya kuma aika da shugabannin mayaƙansa gãba da biranen Isra'ila. Suka kai hari ga Iyon, Dan, Abelmayim, da dukkan biranen ajiya na Naftali.
\v 5 Sai ya kasance da Ba'asha yaji wannan, sai ya dena ginin Rama, ya kuma bar aikinsa ya tsaya.
\v 6 Daga nan Asa sarki ya ɗauki dukkan Yahuda tare da shi. Suka ɗauke duwatsu da katakai daga Rama wanda Ba'asha ke ginin birnin da su. Daga nan nan sarki Asa ya ɗauki waɗannan kayan gini ya yi amfani da su ya gina Geba da Mizfa.
\s5
\v 7 A wannan lokaci Hanani mai gani ya tafi wurin Asa, sarkin Yahuda, ya kuma ce ma shi, "Saboda ka dogara ga sarkin Aram baka kuma dogara ga Yahweh Allahnka ba, mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.
\v 8 Kushiyawa da Libiyawa ba manyan mayaƙa ba ne, tare da karusai masu yawa da mahaya dawakai? Duk da haka, saboda ka dogara ga Yahweh, ya baka nasara a bisansu.
\s5
\v 9 Gama idanun Yahweh na dubawa ko'ina cikin dukkan duniya, domin ya nuna kansa mai karfi a madadin waɗanda zukatansu ke shiryayyu zuwa gare shi. Amma ka aikata wawanci a cikin wannan al'amari. Daga yanzu zuwa nan gaba, zaka sami yaƙi."
\v 10 Daga nan Asa ya fusata da mai ganin; ya sanya shi cikin kurkuku, domin ya yi fushi da shi game da wannan al'amari. A dai-dai wannan lokacin kuma, Asa ya tsananta wa wasu daga cikin mutanen.
\s5
\v 11 Duba, ayyukan Asa, daga farko zuwa karshe, duba, an rubuta su cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila.
\v 12 A cikin shekara ta talatin da tara na mulkinsa, Asa ya kamu da cuta a ƙafafunsa; cutarsa kuwa ta yi tsanani sosai. Duk da haka, bai nemi taimako ba daga Yahweh, amma daga masu magani kaɗai.
\s5
\v 13 Asa ya yi barci tare da kakanninsa; ya mutu a shekara ta arba'in da ɗaya na mulkinsa.
\v 14 Suka bizne shi a nasa kabarin, wanda ya haƙa domin kansa a cikin birnin Dauda. Aka kwantar da shi cikin maɗauki da ke cike da ƙanshi mai daɗi da kayan ƙanshi daban-daban da ƙwararrun masu haɗa turare suka haɗa. Daga nan suka haɗa babbar wuta domin girmama shi.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarki a gurbinsa. Yehoshafat ya ƙarfafa kansa gãba da Isra'ila.
\v 2 Ya sanya 'yan doka a cikin dukkan ƙarfafan biranen Yahuda, ya kuma kafa sansanai a cikin ƙasar Yahuda da cikin biranen Ifraim, waɗanda Asa mahaifinsa ya kame.
\s5
\v 3 Yahweh yana tare da Yehoshafat saboda ya yi tafiya cikin hanyoyin farko na mahaifinsa Dauda, bai kuma biɗi ba'aloli ba.
\v 4 Maimako, ya dogara ga Allah na mahaifinsa, ya kuma yi tafiya cikin dokokinsa, ba bisa ga ɗabi'ar Isra'ila ba.
\s5
\v 5 Sai Yahweh ya tabbatar da mulkin a hannunsa; dukkan Isra'ila suka kawo haraji ga Yehoshafat. Yana da dukiya da daraja a yalwace.
\v 6 Zuciyarsa ya sadaukar ga hanyoyin Yahweh. Ya cire wuraren tuddai da kafe-kafen Ashera daga Yahuda.
\s5
\v 7 A cikin shekara uku na mulkinsa ya aika da ofisoshinsa Benhayin, Obadiya, Zakariya, Netanel, da Mikaya, su koyar a cikin biranen Yahuda.
\v 8 Tare da su kuma akwai Lebiyawa: Shemayya, Nataniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya, da Tobadoniya; tare da su kuma akwai firistoci Elishama da Yehoram.
\v 9 Suka koyar a Yahuda, suna da littafin shari'ar Yahweh tare da su. Suka yi yawo cikin dukkan biranen Yahuda suka kuma yi koyarwa a cikin mutanen.
\s5
\v 10 Fargabar Yahweh ya sauko bisa dukkan masarautun ƙasashen da kekewaye da Yahuda, har da ba su iya yaƙar Yehoshafat ba.
\v 11 Wasu daga cikin Filistiyawa suka kawo kyautai ga Yehoshafat, da azurfa a matsayin haraji. Larabawa kuma suka kawo masa garkuna, raguna 7,700, da awaki 7,700.
\s5
\v 12 Yehoshafat ya zama cike da iko sosai. Ya gina tsararrun birane da wuraren ajiya a Yahuda.
\v 13 Yana da kayan biyan buƙatu masu yawa a cikin biranen Yahuda, da sojoji - ƙarfafa, mutane masu ƙarfin hali - a Yerusalem.
\s5
\v 14 Ga lissafinsu an tsãra bisa ga sunayen gidajen ubanninsu: Daga Yahuda, shugabannin dubbai; Adna shugaba, tare da shi kuma mutanen yaƙi 300,000;
\v 15 gaba da shi kuma Yehohanan shugaba, tare da shi kuma mutane 280,000;
\v 16 gaba da shi kuma Amasiya ɗan Zikri, wanda ya miƙa kansa ya bautawa Yahweh da yardan ransa; tare da shi kuma mutanen yaƙi 200,000.
\s5
\v 17 Daga Benyamin: Eliyada cike da iko mutum mai ƙwazo, tare da shi kuma 200,000 shiryayyu da bakkuna da garkuwoyi;
\v 18 gaba da shi kuma Yehozabad, tare da shi kuma 180,000 a shirye shiryayyu domin yaƙi.
\v 19 Waɗannan ne waɗanda suka bauta wa sarki, baya ga waɗanda sarki ya sanya a tsararrun birane a cikin dukkan Yahuda.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Yanzu Yehoshafat yana da dukiya da yawa da kuma girma; sai ya haɗa kai da Ahab ta wurin miƙa ɗaya daga cikin iyalinsa ya auri 'yarsa.
\v 2 Bayan 'yan shekaru sai ya tafi wurin Ahab a Samariya. Ahab ya yanyanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanensa da ketare da shi. Ahab yasa shi ya kai wa Ramot Giliyad hari tare da shi.
\v 3 Ahab sarkin Isra'ila yace da Yehoshafat, sarkin Yahuda, "Ko za ka bini zuwa Ramot Giliyad?" Yehoshafat ya amsa masa, ni kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne; zamu kasance tare da kai a cikin yaƙin."
\s5
\v 4 Sai Yehoshafat yace da sarkin Isra'ila, "Na roƙe ka ka fara neman maganar Yahweh domin amsarka."
\v 5 Daga nan sai sarki ya tattara dukkan annabawa tare har su ɗari huɗu sai yace da su, "Ko ma iya zuwa Ramot Gileyad yaƙi, ko kuwa kada mu je?" Suka ce, "Ka kai hari, domin Allah zai bada ita a hannun sarki."
\s5
\v 6 Amma Yehoshafat yace, "Babu wani annabin Yahweh da ba shi nan da zamu nemi shawara?"
\v 7 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Har yanzu akwai wani da zamu nemi shawarar Yahweh, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa domin bai taɓa yi mini wani anabci mai kyau ba, amma kullum na mugunta ne." Amma Yehoshafat yace, "Bai kamata sarki ya faɗi haka ba."
\v 8 Sai sarkin Israila ya kira hafsa yace, "Ka yi hanzari ka kawo Mikaiya ɗan Imla."
\s5
\v 9 To Ahab sarkin Isra'ila da Yehoshafat sarkin Yahuda na zaune a kujerar mulki kowannensu ya yi adonsa na sarauta a filin Allah a ƙofar shiga Yerusalem, kuma dukkan annabawa na zaune a gabansu.
\v 10 Sai Zedekiya ɗan Kena'ana ya yi wa kansa ƙaho na ƙarfe ya ce"Yahweh ya faɗi wannan. Da wannan zaka rarraki Aremiyawa har sai an haɗiye su.
\v 11 Duk annabawan suka yi annabci iri ɗaya suna cewa ka kai hari kan Ramot Gileyad kayi nasara, gama Yahweh ya bayar da ita a hannun sarki."
\s5
\v 12 Manzon da aka aika wurin Mikaiya ya yi magana da shi yace, "Duba, dukkan annabawa sun faɗi maganganu masu kyau game da sarki. Ina roƙonka kaima maganarka ta zama kamar tasu, ka faɗi abubuwa masu kyau."
\v 13 Mikaiya ya amsa, "Na rantse da Yahweh abin da Allah ya faɗi shi zan faɗa."
\v 14 Sa'ad da yazo wurin sarki, sarki ya ceda shi, "Mikaiya, ma iya zuwa Ramot Gileyad yaƙi, ko a'a?" Mikaiya ya amsa masa, "Ka kai hari ka kuma yi nasara! Domin zata zama babbar nasara."
\s5
\v 15 Sai sarki ya ceda shi, "Har sau nawa zan buƙace ka da ka rantse ka faɗa mini gaskiya da sunan Yahweh?"
\v 16 To sai Mikaiya yace, "Na ga dukkan Isra'ila a warwatse a kan tuddai, kamar tumakin da basu da makiyayi, Yahweh kuma yace, 'Waɗannan basu da makiyayi. Bari kowanne mutum ya koma gidansa cikin salama.'"
\s5
\v 17 To sai sarkin Isra'ila ya ceda Yehoshafat, "Ashe ban faɗa maka cewa ba zai yi annabci mai kyau game da ni ba, amma sai na masifa?"
\v 18 Sai Mikaiya ya ce yanzu dukkan ku sai ku ji maganar Yahweh: Na ga Yahweh zaune kan kursiyinsa, kuma dukkan rundunar sama na tsaye a gefen damansa da hagunsa.
\s5
\v 19 Yahweh yace, Wane ne zai yaudari Ahab, sarkin Isra'ila, domin ya haura ya faɗi a Ramot Gileyad?' Wannan ya ce haka wani kuma ya ce wancan.
\s5
\v 20 Daga nan sai wani ruhu ya sauko daga wurin Yahweh yace, 'zan ruɗe shi. 'Yahweh ya ceda shi ta yaya?'
\v 21 Sai ruhun ya amsa, 'Zan je in zama ruhun ƙarya a bakin annabawansa dukka. Yahweh ya amsa, 'Zaka ruɗe shi, kuma zaka yi nasara. To yanzu sai ka tafi ka yi haka.'
\s5
\v 22 Yanzu duba, Yahweh yasa ruhun ƙarya a bakin annabawan nan naka, Yahweh kuma ya umarta masifa dominka."
\s5
\v 23 Sai Zedekiya ɗan Kena'aya, yazo gaba, ya mari Mikaiya a kunci, yace, "Ta wacce hanya Ruhun Yahweh ya barni har ya yi magana da kai?"
\v 24 Mikaiya yace, "Duba za ka san haka a waccan ranar, lokacin da ka shiga lungun ɗaki domin ka ɓuya."
\s5
\v 25 Sarkin Isra'ila ya ceda wanɗansu bayi, "Ku je ku kama Mikaiya ku kai shi wurin Amon gwamnan birnin, da kuma Yowash, ɗana.
\v 26 kuce da shi, 'Sarki ya ceka sa wannan mutum a kurkuku ka kuma ciyar da shi da 'yar gurasa da ɗan ruwa, har sai na dawo lafiya.'"
\v 27 Sai Mikaiya ya cein har ka dawo lafiya to ba Yahweh ne ya yi magana ta wurina ba." Ya ƙara da cewa, dukkan ku mutane ku ji wannan."
\s5
\v 28 To sai Ahab, sarkin Isra'ila, da Yehoshafat, sarkin Yahuda, suka tafi yaƙi a Ramot Gileyad.
\v 29 Sarkin Isra'ila ya ceda Yehoshafat, "Zan yi ɓadda kama in tafi yaƙin, amma kai sai ka sa rigunanka na sarauta." Sai sarkin Isra'ila ya yi ɓadda kama suka tafi yaƙin.
\v 30 Shi kuma sarkin Aram ya bada umarni ga shugaban mayaƙan karusai cewa "Kada ya hari ƙananan mayaƙa sai dai sarkin Isra'ila kaɗai."
\s5
\v 31 Sai ya kasance bayan shugaban mayaƙan ya ga Yehoshafat sai yace, "Wancan sarkin Isra'ila ne." Sai suka juya domin su kai masa hari, amma Yehoshafat ya ƙwala ihu, Yahweh kuma ya taimake shi. Allah ya juyar da su daga binsa.
\v 32 Bayan da shugabannin yaƙin suka gane ba sarkin Isra'ila bane sai suka juya suka dena fafararsa.
\s5
\v 33 Amma wani mutum ya ciro bakansa ya yi harbi a iska sai ya bugi sarkin Isra'ila a mahaɗar makamansa. Sai Ahab ya ceda mai tuƙa karusarsa, ka juya ka fitar da ni daga filin dãga, domin na sami mummunan rauni sosai."
\v 34 Yaƙi ya yi zafi sosai a wannan rana, ana kuma riƙe da sarkin Isra'ila a cikin karusarsa da kefuskantar Aremiyawa har yamma. Can kusan faɗuwar rana, sai ya mutu.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Yehoshafat sarkin Yahuda ya koma gidansa a Yerusalem lafiya.
\v 2 Sai Yehu ɗan Hanani, mai duba yaje ya tare shi ya cewa sarki Yehoshafat, "Ko zaka dinga taimakon mugaye? Ko zaka ƙaunaci maƙiyan Yahweh? Domin wannan, fushi daga Yahweh na kanka.
\v 3 Duk da haka akwai 'yan waɗansu halaye nagari a cikinka, domin kã kawar da sandunan Ashera daga ƙasar, ka kuma sa zuciyarka ga neman Allah."
\s5
\v 4 Yehoshafat ya zauna a Yerusalem; ya kuma sake yin tafiya cikin mutanen Biyarsheba zuwa ƙasar duwatsu ta Ifiraimu ya kuma komo da su ga Yahweh, Allah na ubanninsu.
\v 5 Ya sa mahukunta a cikin ƙasar a cikin dukkan tsararrun biranen Yahuda, daga birni zuwa birni.
\s5
\v 6 ya ceda mahukuntan, "Ku yi la'akari da abin da zaku yi, domin ba saboda mutum kuke yin hukuncin ba, amma saboda Yahweh; yana tare daku a cikin zartar da hukunci.
\v 7 Yanzu dai, sai ku bar tsoron Yahweh ya zauna a bisanku. Ku yi hankali a lokacin da kuke yin hukunci, domin babu laifofi ga Yahweh Allahnmu, kuma babu wata tara ko karɓar rashawa."
\s5
\v 8 Bugu da ƙari, a Yerusalem Yehoshafat ya naɗa waɗansu daga cikin Lebiyawa da firistoci da waɗansu shugabannin kakanni na gidajen Isra'ila, da su gudanar da hukunci domin Yahweh, da kuma sasanta saɓani. Suka zauna a Yerusalem.
\v 9 Ya umarce su, da cewa, "Dole ku yi hidima cikin girmamawa ga Yahweh, da kuma aminci, da kuma dukkan zuciyarku.
\s5
\v 10 Duk inda akwai wani saɓani da ya zo gare ku daga ɗan'uwa da kezaune a birninsu, ko dai game da zubar da jini, ko game da dokokin da aka umarta, da sharuɗa da farillai, dole ku gargaɗe su kada su zama da laifi a gaban Yahweh, ko kuma fushi ya sauko maku daku da "yan'uwanku. Wannan zaku yi kuma ba zaku zama da laifi ba.
\s5
\v 11 Duba, Amariya babban firist shi ne shugabanku a kan dukkan al'amuran Yahweh. Zebadiya ɗan Isma'ila, shugaban gidan Yahuda, shi ne ke da ragamar duk abin da ya shafi sarki. Hakannan Lebiyawa zasu zama hafsoshi suna yi maku hidima. Ku yi ƙarfin hali ku kiyaye dokokin ku, Bari Yahweh kuma ya kasance da masu aikata nagarta."
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sai ya kasance bayan wannan, sai mutanen Mowab da Ammon, da waɗansu Meyunawa suka kawo wa Yehoshafat yaƙi.
\v 2 Sai waɗansu suka faɗa wa Yehoshafat cewa, "Babbar runduna na zuwa găba da kai daga hayin Mataccen Teku, daga Idom. Duba suna nan a Hazezon Tamar," wato Engedi.
\s5
\v 3 Sai Yehoshafat ya tsorata ya kuma ƙudurta ya nemi Yahweh. ya yi shelar azumi a cikin dukkan Yahuda.
\v 4 Yahuda ta taru domin neman Yahweh; Suka zo su nemi Yahweh daga dukkan biranen Yahuda.
\s5
\v 5 Yehoshafat ya miƙe a cikin taron mutanen Yahuda da Yerusalem, a gidan Yahweh, a gaban sabon harabar.
\v 6 ya ce"Yahweh Allah na ubanninmu, ba kai bane Allah a sama? Ba kai bane mai mulkin dukkan mulkokin al'ummai? Ƙarfi da iko naka ne, domin haka ba wanda zai iya yin tsayayya da kai.
\v 7 Allahnmu ashe ba kai ka kori mazaunan wannan ƙasa ba daga gaban mutanen ka Isra'ila, ka kuma bada ita har abada ga zuriyar Ibrahim?
\s5
\v 8 Sun zauna a cikinta suka gina maka wuri mai tsarki a cikinsa da sunanka cewa,
\v 9 'In wata masifa ta taso a kanmu - ko takobin hukunci, ko cuta, ko yunwa - zamu tsaya a gaban wannan gida, da kuma gabanka (domin sunanka na a cikin wannan gida), kuma zamu yi kuka zuwa gare ka a cikin ƙuncinmu, zaka kuma jimu ka kuma cece mu.'
\s5
\v 10 Duba yanzu, ga mutanen Ammon, da Mowab, da Tsaunin Seyir waɗanda baka bari mu hallakar da su ba a lokacin da suka fito daga ƙasar Masar; a maimakon haka, Isra'ila suka juya daga wurinsu basu kuma hallaka su ba.
\v 11 Dubi yadda suke sãka mana; suna tafe domin su kore mu daga ƙasar da ka bamu gãdo.
\s5
\v 12 Allahnmu, ba zaka hukunta su ba? Domin bamu da ikon yin yaƙi da wannan babbar rundunar da kezuwa domin su yaƙe mu. Ba mu san abin da zamu yi ba, amma mun zuba ido gare ka."
\v 13 Dukkan Yahuda suka tsaya a gaban Yahweh, duk da ƙananansu da matayensu, da yaransu.
\s5
\v 14 To a cikin tsakiyar tattaruwar, sai Ruhun Yahweh ya zo kan Yahaziyel, ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yeyel, ɗan Mataniya, Balebi, ɗaya daga cikin 'ya'yan Asaf.
\v 15 Yahaziyel yace, "Ku saurara, ku dukkan Yahuda da mazaunar Yerusalem, da sarki Yehoshafat. Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa maku, ' Kada kuji tsoro; kada ku karaya saboda girman wannan babbar rundunar, domin yaƙin ba naku bane na Allah ne.
\s5
\v 16 Dole ne kuje ku yaƙe su gobe. Duba suna zuwa ta mashigin Ziz. Zaku same su a ƙarshen kwari kafin hamadar Yeruwel.
\v 17 Ba zaku bukaci ku yi faɗa ba a wannan yaƙin. Ku tsaya a wurarenku, ku tsaya ku jira, ku ga ceton Yahweh tare daku, Yahuda da Yerusalem. Kada ku tsorata ko ku karaya. Kuje ku hare su gobe, domin Yahweh yana tare daku.'"
\s5
\v 18 Yehoshafat ya sunkuyar da kansa ƙasa. Dukkan Yahuda da mazauna Yerusalem suka faɗi a gaban Yahweh, suna yi masa sujada.
\v 19 Da Lebiyawa, na zuriyar Kohatiyawa, suka miƙe suka yabi Yahweh, Allah na Isra'ila, da babbar murya.
\s5
\v 20 Da sassafe suka tashi suka tafi hamadar Tekowa. A lokacin da suka fita, Yehoshafat ya tashi tsaye yace, "Ku saurare ni Yahuda da ku mazauna Yerusalem! Ku dogara ga Yahweh Allahnku, zaku sami kafuwa. Ku dogara ga annabawansa, zaku yi nasara."
\v 21 Bayan da ya tuntuɓi mutane, sai ya naɗa waɗanda zasu raira yabo ga Yahweh su ba shi waƙar yabo domin ɗaukakarsa mai tsarki, a lokacin da suka tafi suna tunkarar sojoji, suka ce, "Ku yi godiya ga Yahweh, domin alƙawarin amincinsa ya tabbata har abada."
\s5
\v 22 Sa'ad da suka fara waƙar yabo, sai Yahweh yasa masu kwanto gãba da mutanen Ammon, da Mowab, da Tsaunin Seyir waɗanda ke zuwa domin su kawo hari ga Yahuda, aka yi nasara da su.
\v 23 Domin mutanen Ammon da Mowab suka fita suka yaƙi mazaunan Tsaunin Seyir, suka karkashe su suka hallakar da su. Bayan sun hallaka mazaunan Tsaunin Seyir. Sai duk suka taimaka wajen hallaka junansu.
\s5
\v 24 Sa'ad da Yahuda suka zo su dudduba hamada sai suka dubi sojojin. Duba, sun fãɗi ƙasa matattu; ba wanda ya tsira.
\s5
\v 25 Yehoshafat da dukkan mutanensa suka zo domin su kwashi ganima daga gare su, sai suka sami kayayyakin da aka yi watsi da su, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka ɗebar wa kansu, fiye da yadda zasu iya ɗauka. Ya ɗauke su kwana uku kafin su iya kwashe ganimar, domin akwai ta birjik.
\v 26 A rana ta huɗu sai suka taru a kwarin Beraka. A can suka yabi Yahweh, domin haka ake kiran sunan wurin "Kwarin Beraka" har ya zuwa yau.
\s5
\v 27 Daga nan sai suka juya, dukkan mutanen Yahuda da na Yerusalem, Yehoshafat kuma yana yi masu jagora, suka sake koma Yerusalem da farinciki, domin Yahweh ya sake sa su suyi murna a kan maƙiyansu.
\v 28 Suka zo Yerusalem zuwa gidan Yahweh da garayu, da molo, da kãkãki.
\s5
\v 29 Razanar Allah ta kama dukkan mulkokin al'ummai sa'ad da suka ji Yahweh ya yaƙi maƙiyan Isra'ila.
\v 30 Ta haka mulkin Yehoshafat ya zama da kwanciyar hankali, domin Allahnsa ya ba shi salama a dukkan yankunansa.
\s5
\v 31 Yehoshafat ya yi mulkin Yahuda: Yana da shekaru talatin da biyar a lokacin da ya fara sarauta, ya kuma yi mulkin Yerusalem na tsawon shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba, 'yar Shilhi.
\v 32 ya yi tafiya bisa tafarkin Asa, mahaifinsa, bai kuma juya ya barsu ba; ya yi abin da keda kyau a gaban Yahweh.
\v 33 Duk da haka, ba a ɗauke wuraren tuddai ba. Mutanen basu juyar da zukatansu ga Allah na kakanninsu ba.
\s5
\v 34 A kan kuma sauran abubuwa game da Yehoshafat, farko da ƙarshe, duba an rubuta su a cikin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a cikin littafin sarakunan Isra'ila.
\s5
\v 35 Bayan wannan Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya haɗa kai da Ahaziya, sarkin Isra'ila, wanda ya yi aikin ƙeta sosai.
\v 36 Ya haɗa kai da shi domin ya yi jiragen ruwa domin zuwa Tarshish. Sun kafa jiragen a Eziyon Geba.
\v 37 Daga nan sai Eliyeza ɗan Dodabahu na Maresha, ya yi annabci gãba da Yehoshafat; ya ce"Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Yahweh ya rushe ayyukanka." Sai aka ragargaje jiragen domin kada a iya tafiya.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Yehoshafat ya yi barci tare da kakanninsa aka binne shi tare da su a birnin Dauda; Yehoram, ɗansa, ya zama sarki a madadin sa.
\v 2 Yehoram na da 'yan'uwa, ga 'ya'yan Yehoshafat: Azariya, Yehiyel, Zekariya, Azariyahu, Mika'ilu da Shefatiya. Dukkan waɗannan 'ya'yan Yehoshafat ne sarkin Isra'ila.
\v 3 Mahaifinsu ya basu kyautar zinariya da azurfa masu ɗumbin yawa da sauran kayayyaki masu daraja, da ƙayatattun birane a Yahuda, amma sai ya bada gadon sarauta ga Yehoram, saboda shi ne ɗan fari.
\s5
\v 4 To lokacin da Yehoram ya gãji mahaifinsa a sarauta ya kuma kafa kansa sosai a matsayin sarki, sai ya karkashe dukkan 'yan'uwansa da takobi, haka kuma da shugabannin Isra'ila da ban da ban.
\v 5 Yehoram na da shekaru talatin da biyu lokacin da ya fara mulkin, ya kuma yi mulki a Yerusalem na tsawon shekaru takwas.
\s5
\v 6 ya yi tafiya bisa tafarkin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, domin ya auri ɗiyar Ahab ta zama matarsa sai ya yi mugun abu a gaban Yahweh.
\v 7 Duk da haka Yahweh bai so ya hallakar da gidan Dauda ba saboda alƙawarin da ya yi da Dauda; ya yi alƙawarin cewa kullum zai ba da rai a gare shi da kuma zuriyarsa.
\s5
\v 8 A kwanakin Yehoram, Idom ta ɓalle daga mulkin Yahuda, suka kuma naɗawa kansu sarki.
\v 9 Daga nan sai Yehoram da jarumawansa suka ƙetara da karusansa. Da duhu ya tashi ya yaƙi Idomawan da suka kewaye shi da dukkan jarumawan karusansa.
\v 10 Ta haka Idom ta ci gaba da tayar wa Yahuda har wa yau. Libna ita ma sai ta tayar a lokaci guda, domin Yehoram ya rabu da Yahweh, Allah na kakanninsa.
\s5
\v 11 Haka kuma, Yehoram ya gina manyan wurare a duwatsun Yahuda yasa mazaunan Yerusalem su yi rayuwa kamar karuwai, ya kuma karkatar da Yahuda.
\s5
\v 12 Wasiƙa daga annabi Iliya ta zo ga Yehoram. Cewa, "Wannan shi ne abin da Yahweh, Allah na Dauda mahaifinka, ya ce: Saboda baka yi tafiya bisa tafarkin Yehoshafat mahaifinka ba, baka kuma bi tafarkin Asa sarkin Yahuda ba,
\v 13 amma ka bi tafarkin sarakunan Isra'ila, ka kuma sa Yahuda da mazauna Yerusalem su zama kamar karuwai, kamar yadda gidan Ahab suka yi-saboda kuma ka kashe 'yan'uwanka a cikin iyalin mahaifinka ko mariƙa takobi da suka fi ka shahara-
\v 14 Duba, Yahweh zaya kawo wa mutanenka da matanka da 'ya'yanka da mallakarka babbar annoba.
\v 15 Kai kuma da kanka ka zama da matsananciyar cuta saboda cutar da kecikin hanjinka, har sai hanjinka ya fito waje saboda cutar, kwana bayan kwana."
\s5
\v 16 Yahweh ya tayar da ruhun Filistiyawa da na Larabawa gãba da Yehoram waɗanda ke kusa da Kush.
\v 17 Suka kawo wa Yahuda hari, suka washe ta, suka kwashe dukkan wadatarta da suka samu a gidan sarki. Suka kuma kwashe 'ya'yansa da matansa. Basu bar masa ko ɗa ɗaya ba sai dai Yehowahaz, ƙaramin ɗansa.
\s5
\v 18 Bayan duk waɗannan, Yahweh ya buge shi a hanjinsa da cuta mara warkewa.
\v 19 Sai ya kasance a lokacin a ƙarshen shekaru biyu, sai hanjinsa ya fito saboda rashin lafiyarsa, sai ya mutu ta wurin matsananciyar cuta. Mutanensa basu yi wata wata domin girmama shi ba kamar yadda suke yi wa kakanninsa.
\v 20 Ya fara sarauta a lokacin da yake da shekaru talatin da biyu; ya yi mulkin Yerusalem na tsawon shekaru takwas, sai ya mutu ba tare da makoki ba. Suka binne shi a birnin Dauda, amma ba a maƙabartar sarakuna ba.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Mazauna Yerusalem suka naɗa Ahaziya sarki, wato ƙaramin ɗan Yehoram sarki, a madadinsa, domin rundunonin Larabawa sun kashe dukkan manyan 'ya'yansa. Domin haka Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya zama sarki.
\v 2 Ahaziya na da shekaru ashirin da biyu a lokacin da ya fara sarauta; ya yi mulkin Yerusalem shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya; ita 'yar Omri ce.
\v 3 Shi ma ya bi tafarkin Ahab domin mahaifiyarsa ce ke ba shi shawara a cikin yin ayyukan mugunta.
\s5
\v 4 Ahaziya ya yi abin mugunta a gaban Yahweh, kamar yadda gidan Ahab suka yi, domin su ne mashawartansa bayan mutuwar mahaifinsa zuwa hallakarsa.
\v 5 Hakanan ya bi shawararsu; ya yi tafiya tare da Yerom ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, domin su kai hari ga Hazzaiyel, sarkin Aram, a Ramot Gileyad. Aremiyawa suka yi wa Yoram rauni. `
\s5
\v 6 Yoram ya komo domin ya warke daga raunukan da suka ji masa a Rama, lokacin da ya fita ya yi yaƙi da Hazeyel, sarkin Aram. Domin haka Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya tafi can Yezril domin ya ga Yoram ɗan Ahab, domin an raunata Yoram.
\s5
\v 7 To an kawo hallakar Ahaziya daga Allah a ziyarar da Ahaziya ya kai wa Yoram. A lokacin da ya isa, sai ya tafi tare da Yehoram domin su kai hari ga Yehu ɗan Nimshi, wanda Yahweh ya zaɓa ya hallakar da gidan Ahab.
\v 8 A lokacin da Yehu ke aiwatar da hukuncin Allah a kan gidan Ahab, sai ya tarar da shugabannin Yahuda da kuma 'ya'yan ɗau'uwan Ahaziya suna yi wa Ahaziya hidima. Sai Yehu ya kashe su.
\s5
\v 9 Yehu ya nemi Ahaziya, suka kama shi yana ɓoye a Samariya, sai suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi. Sai suka binne shi, domin sun ce, "Shi ɗan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Yahweh da dukkan zuciyarsa." Domin haka gidan Ahaziya ba shi da sauran iko yin sarautar mulkin.
\s5
\v 10 Yanzu bayan Ataliya, ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta kashe dukkan 'ya'yan sarauta a cikin gidan Yahuda.
\v 11 Amma Yehosheba, ɗiyar sarki, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya a asirce ta ware shi da ban da sauran 'ya'ya maza na sarki waɗanda ake shirin kashewa. Ta sa shi da kuma mai renon shi a ɗakin kwana. Da haka Yehosheba 'yar sarki Yehoram, matar Yehoida firist (domin ita 'yar'uwar Ahaziya ce) sai ta ɓoye shi daga Ataliya domin kada Ataliya ta kashe shi.
\v 12 Yana tare da su a gidan Allah har tsawon shekaru shida, bayan Ataliya ta yi mulkin ƙasar.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 A shekara ta bakwai, Yehoyida ya nuna ƙarfinsa ya shiga alƙawari da shugabannin ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, da Isma'ila ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, Ma'asiya ɗan Adayiya, da Elishafat ɗan Zikri.
\v 2 Suka zazzaga Yahuda suka tattara Lebiyawa daga dukkan biranen Yahuda, da kuma shugabannin kabilu na gida-gidan Isra'ila sai suka zo Yerusalem.
\v 3 Dukkan taron mutanen suka yi alƙawari da sarki a gidan Allah. Yehoyida ya ce da su, Duba ɗan sarki ne zai yi mulki, kamar yadda Yahweh ya faɗi game da zuriyar Dauda.
\s5
\v 4 Wannan ne abin da dole zaku yi: kashi uku na firistoci da Lebiyawa da suka zo yin hidima a ranar Asabar, zasu zama masu tsaro a ƙofofi.
\v 5 Kashi uku kuma su tsaya a fadar sarki, kashi uku kuma a wurin da aka kafa harsashin ƙofa. Dukkan mutane zasu kasance a harabar gidan Yahweh.
\s5
\v 6 Kada ku bar kowa ya shiga haikalin Yahweh sai dai firistoci da Lebiyawan da keyin hidima kai ɗai. Zasu shiga domin an keɓe su, amma sauran dole ne su yi biyayya da umarnin Yahweh.
\v 7 Dole ne Lebiyawa su kewaye sarki, kowanne na riƙe da makami a hannunsa. Duk wanda ya shigo gidan kuma sai a kashe shi. "Ku tsaya wurin sarki a lokacin da ya shigo da kuma lokacin da ya fita."
\s5
\v 8 To sai Lebiyawa da dukkan Yahuda suka yi kamar yadda Yehoyida firist ya umarta. Kowannen su ya ɗauki mutanensa, masu zuwa domin su yi hidima a ranar Asabar, da kuma waɗanda ba zasu yi hidima a ranar Asabar ba, domin Yehoyida firist bai sallami kowacce runduna ba tukuna.
\v 9 Sai Yehoyida firist ya kawo masu da manya da ƙananan garkuwoyi da sarki Dauda ya ajiye a gidan Allah ya ba kwamandojin.
\s5
\v 10 Yehoyida ya sanya dukkan sojojin, kowanne mutum da makaminsa a hannusa, daga sashen dama na haikalin zuwa sashen hagu na haikalin, kusa da bagadin da kuma haikalin, zagaye da sarkin.
\v 11 Sai suka fito da ɗan sarki suka sa masa rawani suka kuma bashi kundin dokoki na alƙawari, suka naɗa shi sarki daga nan sai Yehoyida firist da 'ya'yansa suka keɓe shi ya zama sarki suka ce, "Ranka ya daɗe sarki."
\s5
\v 12 Lokacin da Ataliya ta ji hayaniyar mutanen suna yabon sarki sai ta zo cikin mutane ta shiga haikalin,
\v 13 ta na dubawa sai ga sarki tsaye kan dakalin sarauta riƙe da sandar sarauta a ƙofar shiga, ga kuma kwamandoji da masu hura kakaki kewaye da sarki. Dukkan mutanen ƙasar na murna suna busa kakaki, mawaƙa suna kaɗa kayan kaɗe-kaɗe suna kuma bida waƙoƙin yabo. Sai Ataliya ta keta tufafinta tana cewa, "Cin amana! Cin amana!"
\s5
\v 14 Daga nan sai Yehoyida ya ce da kwamandojin ɗari-ɗari su zo su fito da ita a kashe ta da takobi tare da duk waɗanda suka biyo ta. domin firist ya ce, "Kada ku kashe ta a cikin gidan Yahweh".
\v 15 To sai suka buɗa mata hanya ta bi ta Ƙofar Doki zuwa gidan sarki a can suka kashe ta.
\s5
\v 16 To sai Yehoaida da sarki da dukkan mutanen suka yi alƙawari cewa za su zama mutanen Yahweh.
\v 17 Sai dukkan mutanen suka tafi gidan Ba'al suka rushe shi, suka ɓaɓɓalle bagadin Ba'al da kuma gunkinsa. Suka kashe matan firist na Ba'al a gaban waɗanan bagadan.
\s5
\v 18 Yehoyida ya zaɓi shugabannin haikalin Yahweh ta wurin jagorancin firistoci, da ke Lebiyawa waɗanda Dauda ya sa domin su yi hidima a gidan Yahweh, domin su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh tare da farinciki kamar yadda Dauda ya yi umarni, kamar yadda ya ke a rubuce a shari'ar musa.
\v 19 Yehoyida ya sa 'yan tsaro a ƙofar haikalin Yahweh, domin kada duk wani marar tsarki ta kowanne fanni ya shiga.
\s5
\v 20 Yehoyida ya kwashi kwamandoji da mutane ma su daraja da gwamnoni tare da shi da dukkan mutanen ƙasar. Ya kawo sarki daga gidan Yahweh, mutane suka shiga ta babbar ƙofa zuwa gidan sarki daga gidan suka zaunar da sarki akan gadon sarauta.
\v 21 domin haka dukkan mutanen ƙasar suka yi murna birnin kuma ya sami kwanciyar hankali. Ataliya kuma aka kashe ta da takobi.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Yowash yana da shekaru bakwai lokacin da ya fara mulki, ya yi mulki na tsawon shekaru arba'in a Yerusalem, sunan mahaifiyarsa Zibiya, daga Biyasheba.
\v 2 Yoash ya yi abin da kenagari a gaban Yahweh a dukkan kwankin Yehoyida, firist.
\v 3 Yehoyida ya aura masa mata biyu, sai ya zama uba na 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 4 Bayan wannan Yowash ya yanke shawarar gyara gidan Yahweh.
\v 5 Sai ya tara firistoci da Lebiyawa ya ce da su, "Kowacce shekara sai ku je cikin dukkan biranen Yahuda ku tattaro kuɗin da za a gyara gidan Allahnku daga dukkan mutanen Isra'ila. Ku tabbata kun fara yanzu." Lebiyawa basu yi komai ba da farko.
\s5
\v 6 Sai sarki ya kirawo Yehoyida babban firist ya ce da shi, "Meyasa baka bukaci Lebiyawa su kawo haraji daga Yahuda da kuma Yerusalem ba kamar yadda Musa bawan Yahweh da kuma taron Isra'ila suka yi ba domin rumfar alƙawarin dokoki ba?"
\v 7 Domin 'ya'ya maza na Ataliya wannan muguwar mata, sun rushe gidan Allah suka kuma kwashe dukkan kayayyaki masu tsarki na gidan Yahweh suka kai suka bayar ga Ba'al.
\s5
\v 8 To sai sarki ya umarta, suka yi taska suka sa ta daga wajen ƙɔfar shiga gidan Yahweh.
\v 9 Sai suka yi shela a cikin dukkan Yahuda da Yerusalem domin mutane su biya haraji domin gidan Yahweh harajin da Musa bawan Allah ya sa wa Isra'ila a jeji.
\v 10 Dukkan shugabanni da dukkan mutane suka yi murna suka kawo kuɗi suka sa a taska har sai da suka cika ta.
\s5
\v 11 To bayan an kawo taskar wurin fadawan sarki ta hannun Lebiyawa duk lokacin da suka ga taskar ta cika da kuɗi sosai a cikinta, marubutan sarki da manyan firistoci su kan zo, su ɗauke ta su kwashe sai su mayar da ita wurin da ta ke. Haka suka dinga yi kowacce rana, suka dinga tara kuɗaɗe masu yawa.
\v 12 Sai sarki da Yehoyida suka ba da kuɗaɗen ga masu yin aikin hidima a gidan Yahweh. Waɗannan mutanen suka yi hayar masu aikin dutse da masu aikin katako domin su komo da gidan Yahweh, haɗe da masu aikin ƙarfe da tagulla.
\s5
\v 13 To sai ma'aikatan, suka gudanar da aikin ta hannuwansu; suka tayar da gidan Yahweh suka komar da shi kamar yadda ya ke da farko, suka kuma ƙarfafa shi.
\v 14 Bayan sun gama sai suka mayar da sauran kuɗin ga sarki da kuma Yehoyida. Wannan kuɗin da shi aka yi aikin kujerun gidan Yahweh, da kayayyaki wanda aka mora domin karɓar baiko- cokula da kayayyaki na zinariya da azurfa. Suka yi ta miƙa baye-baye na ƙonawa a gidan Yahweh a dukkan kwanakin Yehoyida.
\s5
\v 15 Yehoyida ya tsufa yana da cikkakun kwanaki, ya mutu yana da shekaru 130.
\v 16 Suka binne shi a birnin Dauda a cikin sarakuna, saboda ya yi abu mai kyau a Isra'ila, a gaban Allah da kuma gidan Allah.
\s5
\v 17 To yanzu kuma bayan mutuwar Yehoyida, mutanen Yahuda suka zo domin su nuna karramawa ga sarki. Sai sarki ya saurare su.
\v 18 Suka yi watsi da gidan Yahweh, Allah na kakanninsu suka bautawa gumakan Ashera da siffofinta. Fushin Allah ya auko kan Yahuda da Yerusalem saboda wannan aikin na su mara dacewa.
\v 19 Duk da haka ya aiko annabawa gare su domin su sake komo da su gare shi, annabawan suka ce Yahweh na gãba da mutanen, amma suka ƙi saurara.
\s5
\v 20 Sai Ruhun Allah ya zo kan Zakariya ɗan Yehoyida, firist; Zakariya ya miƙe a sama da mutanen ya ce da su, "Allah ya faɗi wannan: Me yasa ku ke aikata laifofi ga dokokin Yahweh, domin kada ku azurta? Da yake kun yi watsi da Yahweh, shima ya yi watsi da ku.
\v 21 "Amma suka yi masa maƙarƙarshiya; sarki ya umarta a jejjefe shi da duwatsu a dandalin gidan Yahweh.
\v 22 Ta irin wannan hali Yowash, sarki, ya jahilci kirkin da Yehoyida mahaifin Zakariya ya yi masa. A memakon haka ya kashe ɗan Yehoyida. Lokacin da Zakariya ke mutuwa ya faɗi cewa, "Dãma Yahweh ya ga wannan ya kuma sa ka bada lissafi."
\s5
\v 23 To bayan kusan ƙarshen shekara, sai sojojin Aram suka tasarwa Yowash. Suka zo Yahuda da Yerusalem; suka kashe dukkan shugabannin mutane suka kuma kwashe dukkan ganimarsu zuwa ga sarkin Damaskus.
\v 24 Sojojin Armeniyawa kuma suka zo da ƙaramar rundunar soja, amma Yahweh ya ba su nasara kan babbar rundunar soja, domin Yahuda ta yi watsi da Yahweh na kakanninsu. Allah na kakanninsu. Da haka Armeniyawa suka kawo hukunci a kan Yowash.
\s5
\v 25 A lokacin da Armeniyawa suka fice, an yi wa Yowash mummunan rauni. Bayinsa suka yi masa maƙarƙashiya saboda ya kashe Zakariya ɗan Yehoyida, firist. Suka kashe shi a kan gadonsa; suka binne shi a birnin Dauda, amma ba a maƙabartar sarakuna ba.
\v 26 Waɗannan su ne mutanen da suka yi masa maƙarƙashiya: Zabad ɗan Shimeyat mace Ba'ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit, mace Bamowabiya.
\s5
\v 27 To lissafin 'ya'yansa, da kuma annabci mai muhimmanci da aka yi a kansa, da kuma sake gina haikalin Allah, duba an rubuta su a cikin Littafin shashi akan sarakuna. Sai Amaziya ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Amaziya yana da shekaru ashirin da biyar a lokacin da ya fara sarauta; ya yi sarauta ta shekaru ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddan ta Yerusalem.
\v 2 ya yi abin da kemai kyau a gaban Yahweh, amma ba da cikakkiyar miƙa zuciya ba.
\s5
\v 3 Sai ya zamana nan da nan bayan mulkinsa ya kafu sai ya kashe bayin da suka kashe mahaifinsa, sarki.
\v 4 Amma bai kashe 'ya'yan waɗanda suka yi kisan kan ba. Amma ya yi kamar yadda aka rubuta cikin shari'ar Musa, kamar yadda Yahweh ya umarta, "Dole ne iyaye ba zasu taɓa mutuwa ba saboda 'ya'ya, ko 'ya'ya su mutu saboda iyayensu ba, a maimakon haka, kowa zai ɗauki alhakin zunubinsa."
\s5
\v 5 Bugu da ƙari, Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya yi masu ƙidaya bisa ga kabilar kakanninsu, a ƙarƙashin jagorancin shugabannin dubu-dubu da na ɗari-ɗari da dukkan Yahuda da Benyamin. Ya ƙirga su daga 'yan shekaru ashirin zuwa sama, ya sami mutane kusan 300,000 zaɓaɓɓu domin yaƙi waɗanda zasu iya riƙe mashi da garkuwa.
\v 6 Hakannan ya yi hayar mayaƙa 100,000 daga Isra'ila akan kuɗi azurfa ɗari ɗaya.
\s5
\v 7 Amma sai mutumin Allah ya zo gunsa ya ce masa "Sarki kada ka bari mutanen Israi'la domin Yahweh ba ya tare da Isra'ila - ba ko ɗaya daga cikin mutanen Ifiraimu,
\v 8 Amma ko dama a ce kana da ƙarfi na yi yin yaƙin Ubangiji zai rikirtar da kai a gaban maƙiya, domin Yahweh ya na da ikon taimako yana kuma da ikon rushewa."
\s5
\v 9 Amaziya ya ce da mutumin Allah, "Amma me za muyi da talanti ɗari dana ba sojojin Isra'ila?" Mutumin Allah ya amsa da cewa "Yahweh zai iya baka fiye da wannan."
\v 10 To sai Amaziya ya rarraba sojojin da suka zo daga Ifiraimu; ya sake aika su gida. Fushinsu ya yi zafi sosai a kan Yahuda, suka koma gida da matsanancin fushi.
\s5
\v 11 Amaziya ya yi ƙarfin hali har ya tafi da mutanensa zuwa Kwarin Gishiri; a can ya karkashe sojojin Seyir guda dubu goma.
\v 12 Sojojin Yahuda kuma suka kama sojoji duba goma da ransu. Suka kai su can ƙonƙolin tsauni suka tutturo su ƙasa duk suka kakkarye.
\s5
\v 13 Amma sojojin da Amaziya ya komar da su domin kada su je yaƙi tare da shi, suka je suka kai hari a Yahuda daga Samariya har zuwa Betahoron. Suka kashe mutane dubu uku suka kuma kwashi ganima mai yawa.
\s5
\v 14 Sai ya zamana, bayan Amaziya ya dawo daga kisan Idomawa, sai ya kwaso allolin Seyir ya maida su allolinsa. Ya russuna masu ya kuma ƙona masu turare.
\v 15 Domin haka fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan Amaziya. Ya aika masa da saƙo ta hannun annabi cewa, "Meyasa ka je ka tuntuɓi allololin da basu iya ceton mutanensu daga hannunka ba?"
\s5
\v 16 To lokacin da annabin keyi masa magana, sarki ya ce da shi, "Ko mun maida kai mashawarcin sarki ne? Ka bari! donme za a kashe ka?" Daga nan sai annabin ya bari ya ce na sani Allah ya yi ƙudiri na hallakar da kai saboda ka yi waɗannan abubuwa ba ka kuma ji shawarata ba."
\s5
\v 17 To sai Amaziya sarkin Yahuda ya tuntuɓi mashawartansa ya aika da 'yan saƙo zuwa ga Yehowash ɗan Yehoyahaz ɗan Yehu, sarkin Isra'ila, cewa, "Ka zo mu sadu da juna fuska da fuska a cikin yaƙi."
\s5
\v 18 Amma Yehowash sarkin Isra'ila ya aika da 'yan saƙo ga Amaziya sarkin Yahuda, cewa, "Ɗan ƙaramin sassabe da kea Lebanon ya aika da saƙo ga itacen sida a Lebanon, cewa, "Ka bada 'yarka ga ɗana a matsayin mata; amma sai dabbar daji a Lebanon ta zo ta tattake ɗan sassaben.
\v 19 Ka kuma ce, duba na rugurguje Idom; amma zuciyarka ta kumburaka. Ka yi taƙama da ɗaukakarka, amma ka tsaya a gida, gama donme zaka jawo wa kanka masifa da faɗuwa, kai da Yahuda tare da kai?"
\s5
\v 20 Amma Amaziya ba zai saurara ba, domin wannan al'amarin daga Allah ne, domin ya miƙa Yahuda ga hannun maƙiyanta, domin sun nemi shawara daga allolin Idom.
\v 21 To sai Yowash sarkin Isra'ila ya kai hari; shi da Amaziya, sarkin Yahuda, suka gamu fuska da fuska a Betshemesh, wadda take mallakar Yahuda.
\v 22 A ka ragargaza Yahuda a idon Isra'ila kowa kuma ya tsere gida.
\s5
\v 23 Yehowash, sarkin Isra'ila, ya kame Amaziya ɗan Yehowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, a Betshemesh. Ya kawo shi Yerusalem daga Ifiraimu ya kuma rushe ganuwar Yerusalem daga ƙofar Ifiraimu zuwa kusurwar ƙofar, tsawon kamu ɗari huɗu ne.
\v 24 Ya kwashe dukkan zinariya da duk abubuwan da ya iske a gidan Allah da Obida da Idom, da kuma abubuwa masu daraja na gidan sarki, tare da kamammun yaƙi, sai ya koma Samariya.
\s5
\v 25 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuda ya yi mulki na tsawon shekaru sha biyar yana mulkin Yahuda bayan mutuwar Yehoyash, ɗan Yehoyahaz, sarkin Isra'ila.
\v 26 Game da sauran ayyukan Amaziya na farko da na ƙarshe duba an rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda da Isra'ila.
\s5
\v 27 Yanzu tun daga lokacin da Amaziya ya juya wa Yahweh baya, sai suka fara shirya masa maƙarƙashiya a Yeruslem. Sai ya gudu zuwa Lakish suka kashe shi a can.
\v 28 Suka komo da shi a kan dawakai suka binne shi a maƙabartar kakanninsa a birnin Yahuda.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Dukkan mutanen Yahuda suka ɗauki Uziya lokacin ya na ɗan shekara sha shida suka naɗă shi sarki a madadin babansa Amaziya.
\v 2 Shi ne wanda ya sake gina Ilat ya sake komo da ita Yahuda. Bayan wannan sai ya mutu tare da kakanninsa.
\v 3 Uziya yana da shekara sha shida lokacin da ya fara sarauta. ya yi mulki na tsawon shekaru hamsin da biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya; ita daga Yerusalem ce.
\s5
\v 4 ya yi abin da kemai kyau a gaban Yahweh, ya bi misalin mahaifinsa, Amaziya, ta kowanne abu.
\v 5 Yasa kansa ga tafarkin neman Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya bashi dokoki na yin biyayya ga Allah. Da yake ya nemi Yahweh sai Yahweh ya wadata shi.
\s5
\v 6 Sai Uziya ya fita ya je ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe ganuwar birnin Gat da Yamna da ta Ashdod; ya gina birane a ƙasar Ashdod da` kuma cikin Filistiyawa.
\v 7 Allah ya taimake shi gãba da Filistiyawa da Larabawan da suka zauna a Gurba'al da kuma Maunayawa.
\v 8 Ammoniyawa kuma su ka biya haraji ga Uziya ƙarfinsa kuma ya kai har Masar, domin yana ƙara samun iko sosai.
\s5
\v 9 Bugu da ƙari kuma Uziya ya gina hasumiya a Yerusalem akan Ƙofar Kwana, a Ƙofar Kwari, ya kuma ƙayata su.
\v 10 Ya kuma gina hasumiyar tsaro a jeji ya kuma haƙa rijiyoyi da yawa domin yana da dabbobi masu yawa a kwarurruka da kuma a saura. Yana da manoma da masu kula da itatuwan inabi a ƙasa mai duwatsu da kuma a filaye masu 'ya'yan itatuwa, domin ya ƙaunaci aikin gona sosai.
\s5
\v 11 Kuma Uziya yana da mayaƙan sojoji da kezuwa yaƙi a ƙungiyance bisa yadda aka rarraba su bisa ga yawansu yadda Yeyil marubuci da Ma'asiya, hafsa, ƙarƙashin ikon Hananiya ɗaya daga ciki kwamandojin sarki.
\v 12 Dukkan yawan shugabannin mayaƙa na kabilu shi ne 2600.
\v 13 A karƙashin ikonsu kuma akwai soja guda 307,500 da keyin yaƙi da iko mai ƙarfi domin su taimaki sarki yaƙi da maƙiya.
\s5
\v 14 Uziya ya shirya su - domin su zama da dukkan garkuwoyi suturun yaƙi da kwari da kibaw da duwatsun majajjawa.
\v 15 A Yerusalem ya yi masu aikin ƙira da mutane masu fasaha suka samar su kasance a kan hasumiyoyin da kuma filayen dãga, domin su dinga harba kibiyoyi da kuma manyan duwatsu. Ikonsa ya kai har ƙasashe masu nisa, domin ya sami taimako sosai har sai da ya zama da iko sosai.
\s5
\v 16 Amma bayan Uziya ya sami iko sosai sai zuciyarsa ta kumbura domin haka ya yi abin da ba shi da kyau; ya yi wa Yahweh Allahnsa zunubi, domin ya tafi gidan Yahweh domin ya ƙona turare akan bagadin ƙona turare.
\v 17 Sai Azariya firist ya bi shi tare da shi kuma akwai firistocin Yahweh guda tamanin, waɗanda mutane ne masu ƙarfin hali.
\v 18 Suka yi tsayayya da sarki Uziya, suka ce da shi, "Uziya ba aikinka bane ka ƙona turare, amma aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna waɗanda aka keɓe su ƙona turare. Ka fita daga wuri mai tsarki, domin kana da rashin aminci kuma Yahweh Allah ba zai girmamaka ba"
\s5
\v 19 Sai Uziya ya yi fushi. yana riƙe da sandan tasar ƙona turare a hannunsa. Lokacin da yake fushi da firistoci, sai kuturta ta kama shi a goshi a gaban firistocin a gidan Yahweh, a gefen bagadin ƙona turare.
\v 20 Sai Azariya da dukkan firistoci suka duba, sai, suka ga ya zama kuturu a goshinsa. Sai suka yi sauri suka fitar da shi daga can. Hakika, shima ya gaugauta fita, domin Yahweh ya buge shi.
\s5
\v 21 Sarki Uziya ya zama kuturu har ya zuwa randa ya mutu, ya kuma zauna a keɓaɓɓen gida saboda ya zama kuturu, domin an fitar da shi daga gidan Yahweh. Ɗansa, Yotam, ya zama mai kula da gidan sarki, ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.
\s5
\v 22 Game kuma da sauran abubuwa akan Uziya farko da ƙarshe, an rubuta su a cikin abin da annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta.
\v 23 Sai Uziya ya yi barci tare da kakanninsa aka binne shi a maƙabartar sarakuna, domin sun ce, "Shi kuturu ne." Yotam, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Yotam yana da shekaru ashirin da biyar lokacin da ya fara mulki; ya yi mulki na shekaru sha shida a Yerusalem, sunan mahaifiyarsa Yerusha; ita ɗiyar Zadok ce.
\v 2 Ya yi abin da kemai kyau a idon Yahweh, ya bi gurbin mahaifinsa Uziya ta kowanne abu. Ya kuma ƙi shiga wuri mai tsarki na Yahweh, amma duk da haka mutane basu daina aikin mugunta ba.
\s5
\v 3 Ya gina ƙofar sama ta gidan Yahweh, akan tsaunin Ofel kuma ya yi gine-gine masu yawa.
\v 4 Ya kuma yi gine-gine a ƙasa mai duwatsu ta Yahuda, a cikin daji kuma ya gina tsararrun wurare da hasumiyoyi.
\s5
\v 5 Ya kuma yi yaƙi da mutanen Amon ya kuma cinye su. A wannan shekarar, dai mutanen Amon suka bashi talanti ɗari na zinariya, da awo goma na alkama, da awo goma na riɗi, haka mutanen Amon suka riƙa ba shi a shekara ta biyu da ta uku.
\s5
\v 6 Sai Yotam ya zama da iko sosai saboda ya yi tafiya da ƙarfi tare da Yahweh Allahnsa.
\v 7 Game kuma da sauran abubuwa game da Yotam, da dukkan yaƙe-yaƙensa, duba, an rubuta su a cikin littafin sarakunan Isra'ila da Yahuda.
\s5
\v 8 Yana da shekaru ashirin da biyar a lokacin da ya fara mulki, ya yi mulki a Yerusalem na tsawon shekaru sha shida.
\v 9 Yotam ya yi barci tare da kakanninsa, aka binne shi a birnin Dauda. Ahaz, ɗansa, ya gaje shi a sarauta.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Ahaz na da shekaru ashirin ne sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki na shekara goma sha shida a Yerusalem. Bai yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh ba, kamar yadda Dauda kakansa ya yi,
\v 2 Maimakon haka, ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra'ila; ya kuma ƙera zubin ƙarfe domin Ba'al.
\s5
\v 3 Bugu da ƙari, ya ƙona turare a ƙwarin Ben Hinnom kuma yasa 'ya'yansa cikin wuta, bisa ga ayyukan ɓautar gumaka na mutanen da Yahweh ya kora daga ƙasarsu kafin mutanen Isra'ila.
\v 4 ya yi hadaya da ƙona turare a wuraren bisa da kan tuddai da ƙarƙashin kowanne koren itace.
\s5
\v 5 Saboda haka Yahweh Allahn Ahaz, ya bada shi ga hannun sarkin Aram. Aramiyawan suka buge shi kuma suka ɗauke daga gare shi gagarumin taron ɗaurarru, aka tafi da su Damaskus. Ahaz ma aka bada shi ga hannun sarkin Isra'ila wanda ya buge shi da mummunar kisa.
\v 6 Gama Pekah ɗan Remaliya a rana ɗaya, ya kashe sojoji Yahuda 120,000, dukkansu maza masu ƙarfin hali ne, saboda sun yashe da Yahweh, Allahn kakanninsu.
\s5
\v 7 Zikiri, mutum mai ƙarfi daga Ifraimu, ya kashe Ma'asiyya ɗan sarki, Azirikam, shugaban făda da Elkana, wanda ke bin sarki a muƙami.
\v 8 Mayaƙan Isra'ila sun ɗauki kãmammu daga danginsu mata 200,000 da 'ya'ya maza da mata. Suka kuma kwaso ganima da yawa, wadda suka komo da su Samariya.
\s5
\v 9 Amma akwai wani annabin Yahweh a wurin, sunansa Oded. Ya je ya sadu da mayaƙan da kezuwa Samariya. Ya ce masu, "Saboda Yahweh, Allahn kakanninku, na fushi daYahuda, ya bada su ga hannun ku. Amma kuka yanka su cikin harzuƙan da ta kai samma.
\v 10 Yanzu kun yi niyar ku ajiye maza da matan Yahuda da Yerusalem kamar bayinku. Amma ba ku da laifin zunubanku ga Yahweh Allahnku?
\v 11 To yanzu, ku saurare ni: Ku mayar da kamammun, waɗanda kuka ɗauko cikin naku 'yan'uwan, gama zafin fushin Yahweh na kanku."
\s5
\v 12 Sa'annan waɗansu shugabannin mutanen Ifraimu- Azariya ɗan Yohanan da Berakiya ɗan Meshilemot da Yehizkiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka taso gãba da waɗanda suka dawo daga yaƙin.
\v 13 Suka ce da su, "Kada ku kawo kamammun nan, gama kunyi niyar wani abu da zai kawo wa kanmu zunubi ga Yahweh, ya kuma ƙara a kan zunubanmu da laifofinmu, gama laifofinmu na da yawa, kuma akwai fushi mai zafi a kan Isra'ila."
\s5
\v 14 Sai mayaƙan suka bar kamammun da ganimar a gaban shugabannin da dukkan taron.
\v 15 Mutanen da aka kira sunansu suka tashi suka ɗauki kãmammun, suka suturad da dukkan waɗanda ke a tsirance cikinsu tare da ganimar. Suka suturad da su suka basu takalma. Suka basu abinci su ci su sha. Suka yi jinyar masu raunuka kuma suka sa masu rauni a kan jakuna. Suka komo da su ga iyalansu a Yeriko, (wadda ake kira Birnin Dabino). Sa'annan suka koma Samariya.
\s5
\v 16 A wancan lokacin sarki Ahaz ya aiki manzanni zuwa sarakunan Assiriya domin neman su taimake shi.
\v 17 Gama Idomawa sun sake kawo wa Yahuda hari, suna ɗaukar kamammu suna tafiya da su.
\v 18 Filistiyawa kuma sun mamaye biranen da keƙwararru da na Negev ta Yahuda. Suka ɗauki Beth Shemesh, da Aijalon, da Gederot, da Soko tare da ƙauyukanta, da Timna tare da ƙauyukanta, da kuma Gimzo tare da ƙauyukanta. Suka tafi su zauna a wuraren.
\s5
\v 19 Gama Yahweh ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz, sarkin Isra'ila; domin ya yi mugunta a Yahuda kuma ya yi wa Yahweh zunubi mai nauyi.
\v 20 Tiglat Filesar, sarkin Assiriya, ya zo wurinsa ya dame shi maimakon ya ƙarfafa shi.
\v 21 Domin Ahaz ya ɗebo kaya daga gidan Yahweh da gidajen sarki da shugabanni, ya bada abubuwa masu daraja ga sarakunan Assiriya. Amma yin hakan bai sa yaci riba ba.
\s5
\v 22 Wannan sarki Ahaz kuma ya yi zunubi ƙwarai ga Yahweh a lokacin wahalarsa.
\v 23 Gama ya yi wa allolin Damaskus hadaya, allolin da suka kada shi. Ya ce, "Saboda allolin sarakunan Aram sun taimaka masu, zan yi masu hadaya, don su taimake ni." Amma su suka zama masa dalilin lalacewa da dukkan Isra'ila.
\s5
\v 24 Ahaz ya tattara kayan ɗaki na gidan Allah ya datse su gunduwa-gunduwa. Ya ƙulle kofofin gidan Yahweh sai ya yi wa kansa bagadai a dukkan lungunan Yerusalem.
\v 25 A kowanne birni a Yahuda ya yi wuraren tuddai na ƙone hadaya ga waɗansu alloli. Ya harzuƙa Yahweh, Allahn kakaninsa, ga fushi.
\s5
\v 26 Yanzu sauran aikinsa, da dukkan hanyoyinsa, na farko dana karshe, Duba, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila.
\v 27 Ahaz ya kwanta da kakanninsa, kuma suka binne shi a birnin, a Yerusalem, amma ba su kawo shi cikin hurumin sarakunan Isra'ila ba. Hezekiya, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Hezekiya ya fara mulki a sa'ad da yake da shekaru ashirin da biyar da haifuwa; ya yi mulki shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Abijah; ita ɗiyar Zakariya ce.
\v 2 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh kamar yadda mahaifinsa Dauda ya yi.
\s5
\v 3 A shekara ta farko na mulkinsa, A wata na farko, Hezekiya ya ɓuɗe ƙofofin Gidan Yahweh ya gyaggyara su.
\v 4 Ya kawo firistoci da Lebiyawa, ya tattaro su a farfajiyar gefen gabas.
\v 5 ya ce da su, "Ku saurare ni, ku Lebiyawa! Ku keɓe kanku, ku kuma keɓe gidan Yahweh, Allahn kakanninku, ku cire ƙazamci daga wuri mai tsarki.
\s5
\v 6 Gama kakanninmu sun kauce daga hanya suka yi mugun abu a fuskar Yahweh Allahnmu; suka yashe shi, suka juye fuskarsu daga wurin da Yahweh ke zamne, kuma suka juya ma wurin baya.
\v 7 Haka kuma suka kukkulle ƙofofin rumfuna suka kakkashe wutan fitilun; basu ƙona turare ko miƙa baye-baye na ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra'ila ba.
\s5
\v 8 Saboda haka fushinYahweh ya faɗo wa Yahuda da Yerusalem, kuma yasa suka zama abin razana da tsoro da ba'a, kamar yadda ku ke gani da idanunku.
\v 9 Wannan shi yasa ubaninmu suka faɗi ta kaifin takobi, kuma 'ya'ya mazanmu da 'ya'ya matanmu da matayenmu suke cikin bautar talala.
\s5
\v 10 Yanzu kuwa yana zuciyata in yi alƙawari da Yahweh, Allah na Isra'ila, saboda zafin fushinsa ya juya daga auko mana.
\v 11 'Ya'yana maza kada ku zama da ragwanci yanzu, gama Yahweh ya zaɓe ku ku tsaya a gabansa, kuyi masa sujada, ku kuma zama barorinsa ku ƙona turare."
\s5
\v 12 Sa'annan Lebiyawa suka tashi: Mahat ɗan Amasai da Yowel ɗan Azariya, na mutanen Kohatawa; da mutanen Merari, wato Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yahalelel; da Gershonawa, wato Yowa ɗan Zimma, da Iden ɗan Yowa;
\v 13 na 'ya'yan Elizafan, Shimri da Yewuyel; dana 'ya'yan Asaf wato Zekariya da Mataniya;
\v 14 na 'ya'yan Heman, Yehuwel da Shimei; da na 'ya'yan Yedutun wato Shemayya da Uziyel.
\s5
\v 15 Suka tattara 'yan'uwansu maza suka tsarkake kawunansu, sai suka shiga ciki, kamar yadda sarki ya umarta, biye da maganar Yahweh, a tsabtace gidan Yahweh.
\v 16 Firistocin suka je cikin gidan Yahweh domin su tsabtace shi suka fitar da dukkan kazamtar da suka samo a haikalin Yahweh, suka zuba a harabar gidan. Sai Lebiyawa suka kwashe ta suka kai waje zuwa rafin Kidron.
\v 17 Sai suka fara aikin tsarkakewa a rana ta fari a watan ɗaya. A rana ta takwas ga wata suka kai shirayin Yahweh da aikin, Sa'annan bayan kwana takwas kuma suka tsarkake gidan Yahweh. A ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.
\s5
\v 18 Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya, a cikin fada, suka ce, "Mun tsabtace haikalin Yahweh dukka da bagadin baye-bayen ƙonawa tare da dukkan tasoshi, da kayayyaki, da teburan gurasar kasancewa, da dukkan kayayyakin da suke ciki.
\v 19 Saboda haka muka shirya muka kuma tsarkake dukkan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar sa'ad da ya yi aikin rashin aminci a lokacin da yake mulki. Duba, su na nan a gaban bagadin Yahweh."
\s5
\v 20 Sa'annan sarki Hezekiya ya tashi da sassafe ya tattara shugabanin birnin; ya haura can zuwa gidan Yahweh.
\v 21 Suka kawo bijimai bakwai da raguna bakwai da 'yan raguna bakwai da bunsura bakwai a matsayin baikon zunubi masarauta da wuri mai tsarki, domin kuma Yahuda. Sai ya umarci firistioci, wato 'ya'yan Haruna maza, su miƙa su a kan bagadin Yahweh.
\s5
\v 22 Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a bagadin. Suka yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagadin; hakanan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagadin.
\v 23 Suka kawo bunsuran yin hadaya domin zunubi a gaban sarki da taron jama'a; suka ɗora hannuwansu a kansu.
\v 24 Sai firistoci suka yankasu suka yi hadaya domin zunubi da jinin a bagadin domin ayi kafara saboda dukkan Isra'ila, gama sarki ya umarta ayi baiko na ƙonawa da baiko domin zunubi saboda dukkan Isra'ila.
\s5
\v 25 Sai Hezekiya ya sanya Lebiyawa a gidan Yahweh tare da kuge da molaye da garayu. Suka jerasu bisa ga umarnin Dauda, da na Gad, mai gani na sarki, da annabi Nathan, gama umarnin daga wurin Yahweh ya zo ta wurin annabawansa.
\v 26 Lebiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dauda, firistoci kuwa suna rike da ƙahonni.
\s5
\v 27 Sai Hezekiya ya bada umarni a miƙa baiko na ƙonawa a bisa bagadin. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa sai waƙa ga Yahweh ma ta fara tasowa tare da busa ƙaho da sauran kayan kiɗe-kiɗe dana bushe- bushe na Dauda sarkin Isra'ila.
\v 28 Dukkan taron suka yi sujada. mawaƙa suka raira waƙa, masu ƙahonni su ka yi ta busawa; Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa.
\s5
\v 29 Bayan da aka gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukkan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada.
\v 30 Bugu da ƙari, sarki Hezekiya, tare da shugabanin suka umarci Lebiyawa su raira waƙar yabo ga Yahweh da kalmomin Dauda da na Asaf mai gani. Suka raira wakokin yabo tare da murna, suka sunkuya suka yi sujada.
\s5
\v 31 Sai Hezekiya ya ce, "yanzu dai kun tsarkake kanku ga Yahweh. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a cikin gidan Yahweh. Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, kuma dukkan waɗanda suka yi niya sun kawo hadayan ƙonawa.
\s5
\v 32 Jimilar hadayu na waɗanda taron suka kawo su ne bijimai saba'in da raguna ɗari da 'yan raguna ɗari biyu. waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Yahweh.
\v 33 Tsarkakakkun baye-bayen kuwa bijimai ɗari shida da tumaki dubu uku ne.
\s5
\v 34 Amma firistocin kima ne don haka suka kasa feɗe dukkan dabbobin da za a miƙa su baye-baye na ƙonawa, sai 'yan'uwansu, Lebiyawa, suka taimake su har aka gama aikin kamin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. gama Lebiyawan su na la'akari da tsarkake kansu fiye da firistocin.
\s5
\v 35 Bugu da ƙari, akwai hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi; suka aikatu da kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowacce hadaya ta ƙonawa. Da haka aka maido da hidimar gidan Yahweh.
\v 36 Hezekiya ya ji daɗi, haka ma dukkan jama'a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama'a, gama farat ɗaya aka yi aikin.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Hezikiya ya aiko da saƙo ga dukkan Isra'ila da Yahuda, ya kuma rubutawa Manasa da Ifraimu wasiƙu, da cewa su zo gidan Yahweh a Yerusalem, su yi Idin Ƙetarewa ga Yahweh, Allah na Isra'ila,
\v 2 Gama sarkin, da shugabaninsa da dukkan taron jama'a sun gana tare, cewa sun shirya su yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu.
\v 3 Ba su iya yinsa a lokacin da aka saba yi ba, saboda babu firistocin da suka tsarkake kansu, kuma mutane ba su tattaro kansu gaba ɗaya zuwa Yerusalem ba.
\s5
\v 4 Wannan shirin kuwa ya yi dai-dai a idanuwan sarki da dukkan taron jama'a.
\v 5 Saboda haka suka yarda su yi shelar umarnin a ko'ina a Isra'ila daga Biyarsheba zuwa Dan, cewa mutanen su zo su yi bikin Idin Ƙetarewa ga Yahweh, Allahn Isra'ila, a Yerusalem. Domin sun lura ba su taɓa yin sa da mutane da yawa ba, bisa ga abin da kea rubuce.
\s5
\v 6 Sai masu kai saƙo suka tafi da wasiƙu daga sarki da shugabaninsa zuwa ga dukkan Isra'ila da Yahuda, da umarnin sarkin, Suka ce ku mutanen Isra'ila, ku juyo ga Yahweh, Allahn Ibrahim da Ishaku da Iara'ila. Saboda shi ma ya sake juyowa ga ragowarku da kuka kuɓuta daga hannun sarkin Assiriya.
\s5
\v 7 Kada ku zama kamar kakaninku ko 'yan'uwanku maza, waɗanda suka kauce daga Yahweh, Allahn kakaninsu, har yasa ya bar su ga hallaka, kamar yadda kuka gani.
\v 8 Yanzu kuwa kada kuyi taurin kai, kamar yadda kakaninku suka yi, ku miƙa kanku ga Yahweh, ku kuma zo wurinsa mai tsarki, wadda ya tsarkake har abada, kuyi sujada ga Yahweh Allahnku, saboda zafin fushinsa zai kauce daga aukowa maku.
\v 9 Gama idan kuka juya baya ga Yahweh, 'yanuwanku maza da yaranku zasu sami tagomashi a gaban waɗanda suka tafi da su a matsayin kamammu, kuma zasu dawo wannan ƙasar. Gama Yahweh Allahnku mai alheri da jinkai ne kuma ba zai juya fuskarsa daga gare ku ba idan kun juyo zuwa gare shi."
\s5
\v 10 Sai manzanin suka wuce daga birni zuwa birni a dukkan lardin Ifraimu da Manasa, har zuwa Zabulun, amma mutanen suka yi masu dariya da ba'a.
\v 11 Ko da yake, waɗansu mutanen Asha da Manasa da Zabulun suka yi tawali'u suka zo Yerusalem.
\v 12 Hannun Allah kuma ya zo ga Yahuda, ya basu zuciya daya, su yi abin da sarki da shugabanin suka umarta ta wurin maganar Yahweh.
\s5
\v 13 Mutane da yawa, taron jama'a mai girma, suka taru a Yerusalem domin su yi Bikin Idin Abinci Marar Gami a wata na biyu.
\v 14 Suka tashi suka cire bagadan da kecikin Yerusalem, da dukkan bagadan ƙona turare; suka zubar da su a kwarin Kidron.
\v 15 Sa'an nan suka kashe ragunan Idin Ƙetarewa a rana ta huɗu ga watan biyu, Firistoci da Lebiyawa kuwa suka ji kunya, saboda haka suka tsarkake kansu suka kawo hadayu na ƙonawa a gidan Ubangiji.
\s5
\v 16 Suka ɗauki gwalgwadon matsayinsu, bisa ga yadda dokar Musa, mutumin tsauni ta faɗa, Firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lebiyawa.
\v 17 Gama akwai waɗansu da yawa a taron da ba su tsarkake kansu ba. Saboda haka Lebiyawan suka yanka ragunan Idin Ƙetarewa domin duk wanda ba shi da tsarki kuma ba zai iya tsarkake hadayunsa ga Yahweh ba
\s5
\v 18 Gama babban taron mutane, yawancinsu daga Ifraimu da Manasa da Issaka da Zabulun, ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci abincin Idin, găba da rubutaccen umarnan. Gama Hezekiya ya yi masu addu'a cewa,
\v 19 "Ubangiji Yahweh ya gafarci duk wanda ya sa zuciyarsa ga neman tsauni, Yahweh, tsaunin kakaninsa, ko bai da tsarki ta ka'idar tsarkakewa na wuri mai tsarki."
\v 20 Saboda haka Yahweh ya saurari Hezekiya ya kuma warkar da mutanen.
\s5
\v 21 Mutanen Isra'ila waɗanda suke a Yerusalem sun yi Idin Abinci Mara Gami da murna mai yawa har kwana bakwai. Lebiyawa da firistoci suka yabi Yahweh rana bayan rana, suna waƙa da kayayyakin kiɗe-kiɗe masu ƙara ga Yahweh.
\v 22 Hezekiya ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukkan Lebiyawan da suka gane hidimar Yahweh. Sai suka ci abinci a duk lokacin idin na kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta furta zunubai ga Yahweh, tsauni na kakaninsu.
\s5
\v 23 Dukkan taron jama'an kuwa suka shirya su ƙara yi bikin na kwana bakwai kuma, suka kuma yi haka da murna.
\v 24 Gama Hezekiya sarkin Yahuda ya ba jama'an bijimai dubu ɗaya da tumaki dubu bakwai a matsayin baiko; shugabanin kuma suka baiwa jama'ar bijimai dubu ɗaya da tumakai da awakai dubu ɗaya. Firistoci da yawa kuma suka tsarkake kansu.
\s5
\v 25 Dukkan jama'ar Yahuda, tare da firistoci da Lebiyawa, da dukkan mutanen da suka zo tare daga Isra'ila, da kuma baƙin da suka zo daga ƙasar Isra'ila da waɗanda ke zaune a Yahuda - Dukkansu sun yi farin ciki.
\v 26 Saboda haka aka yi babban murna a Yerusalem, gama tun daga lokacin Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila, babu wani abu kamar haka a Yerusalem.
\v 27 Sa'an nan firistoci da Lebiyawa suka tashi suka sa wa mutane albarka. Aka kuwa ji muryarsu, addu'arsu kuma ta kai sama, wuri mai tsarki da tsauni yake.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Yanzu sa'ad da aka gama dukkan waɗannan, sai mutanen Isra'ila da kewurin suka fiita daga biranen Yahuda suka rurrushe ginshiƙan duwatsu suka kakkarye sandunan Ashera, suka kuma karya masujadar bisa da bagadun a dukkan Yahuda da Benyamin da Ifraim da Manasse, har sai da suka rurrusa su dukka. Sai dukkan mutanen Isra'ila suka dawo, kowanne ga nasa mallaka da nasa birnin.
\s5
\v 2 Hezekiya ya rarraba ɓangarorin firistoci Lebiyawa kumaya shirya su bisa ga ɓangarorinsu, kowanne mutum da aikinsa, da firistoci da Lebiyawa. Yasa su su yi hadayun ƙonawa dana zumunci, su yi hidima, su yi godiya, su yi yabo a ƙofar haikalin Yahweh.
\v 3 Ya kuma shirya sashin hadayar ƙonawa ta sarki daga mallakarsa, wato domin hadayun ƙonawa na safe dana yamma da hadayun ƙonawa domin ranakun Asabar, saɓobbin watanni, da sanyayyun bukukuwa, kamar yadda yake a rubuce a shari'ar Yahweh.
\s5
\v 4 Bugu da ƙari, ya umarci mutanen da kezama a Yerusalem su bada ɓangaren da ya shafi firistoci da Lebiyawa, saboda su ci gaba da sa ƙarfi ga biyayya da doka na Yahweh.
\v 5 Ba tare da ɓata lokaci ba bayan an aiko da umarnin, mutanen Isra'ila suka bayar hannu sake wato nunan fari na hatsi da sabon ruwan inabi da maida zuma da dukkan girbin gona. Suka kawo zakka na dukkan kome; waɗannan abu kuwa masu tarin yawa ne.
\s5
\v 6 Mutanen Isra'ila da Yahuda waɗanda ke zama a biranen Yahuda suka kawo zakkar shanu da tumaki, da kuma zakkar abubuwa masu tsarkin da aka keɓe ga Yahweh tsauninsu, kuma suka tattaro su dami-dami.
\v 7 A watan uku ne sa'ad da suka fara harhaɗa gudunmawarsu dami-dami, suka kuma gama a wata na bakwai.
\v 8 Sa'an da Hezekiya da shugabanin suka zo suka ga dammunan, suka albarkaci sunan Yahweh da mutanensa Isra'ila.
\s5
\v 9 Sa'annan Hezekiya ya tambayi firistocin da Lebiyawa game da dammunan.
\v 10 Azariya, babban firist, na gidan Zadok, ya amsa masa ya ce, "Tun da mutanen suka fara kawo baye-baye cikin gidan Yahweh, Mun ci kuma mun sami isasshe, kuma muna da ragowa da yawa, gama Yahweh ya albarkaci mutanensa. Abin da ya rage shi ne wannan da yawa a nan."
\s5
\v 11 Sa'an nan Hezekiya ya umarta ayi wuraren ajiya a gidan Yahweh, sai suka kuwa shirya wuraren.
\v 12 Sa'an nan suka yi aminci suka kawo baye-bayen, zakka da abubuwan da kena Yahweh. Kononiya, Balebiye, shi ne shugaba mai lura da su, kuma Shimei, dan'uwansa ne na biye da shi.
\v 13 Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaya na karkashin Konaniya da Shime'i dan'uwamsa, bisa ga zaɓen Hezekiya, sarki, da Azariya, mai lura da gidan Yahweh.
\s5
\v 14 Kore ɗan Imna Balebiye da shugaba na ƙofar gabas, su ne masu lura da bayarwar yardar rai ga tsauni da shugabanci a kan rarrabawar baye-baye ga Yahweh da abubuwa mafi tsarki cikin baye-bayen.
\v 15 A ƙarƙashinsa akwai Iden da Mini'amin da Yeshuwa da Shemaya da Amariya da Shekaniya a biranen firistocin. Suka cika ayyukan amanar shugabanci, Domin a bayar da waɗannan baye-baye ga 'yan'uwansu maza ɓangare ɓangare ga kowa da kowa.
\s5
\v 16 Suka kuma ba wa mazajen da keshekara uku zuwa sama, waɗanda aka lisafta a rohotonin kakaninsu da suka shiga gidan Yahweh, kamar yadda ake bukata a kowacce rana, ayi aiki bisa ga muƙamansu da ɓangarorinsu.
\s5
\v 17 Suka rarraba wa firistocin bisa ga rahotonin kakaninsu, haka kuma ga Lebiyawan da kesama da shekara ashirin ko fiye, bisa ga muƙamansu da ɓangarorinsu.
\v 18 Suka haɗa da 'yan ƙananansu da matayensu da 'ya'ya mazansu da 'ya'ya matansu, a dukkan unguwan, gama su masu aminci ne ga kiyaye zaman tsarkinsu.
\v 19 Gama firistocin wato zuriyar Haruna waɗanda ke filayen ƙauyukan da keta biranensu ne, ko kuwa a kowacce birni dai, akwai mazajen da aka sa da sunayesu, su bada rabo ga duk mazaje cikin firistoci, da kuma ga waɗanda aka lisafta a rahotonin kakaninsu cewa suna cikin Lebiyawa.
\s5
\v 20 Hezekiya ya yi wannan a dukan Yahuda. Ya aiwatar da abin da kenagari, dai-dai, da kuma aminci a gaban Yahweh, tsauninsa,
\v 21 A duk aikin da ya fara cikin hidimar gidan tsauni da dokoki da farilai, don kusantuwa da tsauninsa, ya aikata su da dukkan zuciyarsa, kuma ya yi nasara.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Bayan waɗannan abubuwan da amintattun ayyuka, Senakirib sarkin Asuriya, ya zo ya shiga Yahuda. Ya kafa sansani ya kai ma birane masu garu hari, da niyar ya yi kamu domin kansa.
\s5
\v 2 Sa'ad da Hezekiya ya ga Senakirib ya iso kuma ya yi niyar yaƙi da Yerusalem,
\v 3 sai ya yi shawara da shugabanninsa da mazajensa masu iko su tsayar da ruwayen da kefitowa daga maɓuɓɓugar da suke bayan birnin; suka taimake shi ya yi hakan.
\v 4 Saboda haka mutane da yawa suka taru suka tsayar da dukkan maɓuɓɓugai da rafuffuka da kegudu ta cikin ƙasar. Su na cewa, "Me zai sa sarakunan Asuriya su zo su sami ruwa mai yawa?"
\s5
\v 5 Hezekiya ya yi karfin hali ya sake gina dukkan ganuwar da aka rushe, ya gina hasumiyar da inganci, haka kuma ɗaya garun da kewaje. Ya kuwa ƙara ƙarfin Milo a birnin Dauda, ya kuma yi makamai na yaƙi da yawa da garkuwoyi.
\s5
\v 6 Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci mutane. Ya tattaro su gareshi a dandalin ƙofar birnin ya yi magana ta ƙarfafawa da su. Ya ce,
\v 7 "Ku ƙarfafa da nagartaccen ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Asuriya da dukkan sojojin da ketare da shi, gama wani yana tare da mu wanda ya fi waɗanda ke tare da shi.
\v 8 Hannun mutum ne kawai ke tare da shi, amma mu Yahweh tsauninmu yake tare da mu domin ya taimake mu ya yi mana yaƙi." Mutane kuwa suka ta'azantu da maganar Hezekiya, sarkin Yahuda.
\s5
\v 9 Bayan wannan, sai Senakirib sarkin Asuriya ya aika da barorinsa zuwa Yerusalem (Yanzu dai yana a gaban Lakish, kuma dukkan mayaƙansa na tare da shi), ga Hezekiya, sarkin Yahuda da dukkan Yahuda waɗanda ke a Yerusalem. Ya ce,
\v 10 Ga abin da Senakirib, sarkin Asuriya, ya ce: "Ga me kake dogara a kai don ka dage wa yaƙi kewaye da kai a cikin Yerusalem?
\s5
\v 11 Ba ruɗin ku Hezekiya yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi, sa'ad da yake gayă maku, 'Yahweh tsauninmu zai cece mu daga hannun sarkin Asuriya'?
\v 12 Ba wannan Hezekiyan ba ne yake ɗauke wuraren bisansa da bagadensa ya kuma umarci Yahuda da Yerusalem, 'A kan bagadi guda ne ya wajaba ku yi sujada, a kansa ne kuma zaku ƙona hadayunku?
\s5
\v 13 Ba kun san abin da ni da kakannina muka yi wa dukkan manyan mutane na waɗansu ƙasashen ba? Allolin manyan mutane na ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna?
\v 14 Daga cikin dukkan manyan waɗancan al'ummai waɗanda kakannina suka hallakar kakaf, da wanda ya iya ceton mutanensa daga hannuna? Donme tsauninku zai iya cetonku daga hannuna?
\v 15 Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku ko ya ɓadda ku haka. Kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani tsauni na wata al'umma ko mulki wanda ya taɓa ceton mutanensa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane ne tsaunin ku har da zai iya cetonku daga hannuna?"
\s5
\v 16 Barorin Senakirib sun yi maganganu fiye da haka găba da Yahweh tsauni da bawansa Hezekiya.
\v 17 Senakirib ya kuma rubuta wasiƙu don ya yi ba'a ga Yahweh, tsauni na Isra'ila, ya kuma yi maganar găba da shi. Ya ce, "Kamar yadda allolin al'ummai na sauran ƙasashe basu ceci mutanensu daga hannuna ba, hakanan kuma tsaunin Hezekiya ba zai iya ceton mutanensa daga hannuna ba."
\s5
\v 18 Suka yi kuka da babban murya, da harshen Yahudanci, suka yi ta magana da mutanen Yerusalem waɗanda suke kan garu, don su tsoratar da su, su kuma firgita su, domin su danƙe birnin.
\v 19 Suka yi magana a kan tsauni na Yerusalem kamar yadda suka yi ta magana a kan allolin waɗansu mutanen duniya, waɗanda aikin hannuwan mutane ne kurum.
\s5
\v 20 Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu'a saboda wannan al'amari kuma suka yi kuka zuwa sama
\v 21 Yahweh kuwa ya aiki mala'ika, wanda ya karkashe mazajen yaƙi da manyan jarumawa da shugabanni na sarkin a sansanin. Saboda haka Senakirib ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan tsauninsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
\s5
\v 22 Ta haka Yahweh ya ceci Hezikiya da mazaunan Yerusalem daga hannun Senakirib, sarkin Asuriya, daga kuma hannun dukkan sauran, ya kuma hutar da su ta kowace ɓangare.
\v 23 Mutane da yawa suka kawo wa Yahweh sadakoki a Yerusalem, da kuma abubuwa masu daraja ga Hezekiya sarkin Yahuda, saboda haka ya sami ɗaukaka a idanun dukkan sauran al'ummai tun daga lokaci nan har zuwa gaba.
\s5
\v 24 A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa. Sai ya yi addu'a ga Yahweh, wanda kuwa ya yi magana da shi ya ba shi alamar cewa zai warke.
\v 25 Amma Hezekiya bai mayar da godiya a kan taimakon da ya ba shi ba, domin a zuciyarsa akwai girman kai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuda da Yerusalem.
\v 26 Duk da haka dai, daga baya Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda fahariyar zuciya da ya yi, da shi da mazaunan Yerusalem, don haka hasalar Yahweh ba ta faɗo masu ba a kwanakin Hezekiya.
\s5
\v 27 Hezekiya yana da dukiya ƙwarai yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiye azurfa da zinariya da duwatsu masu daraja da kayan yaji da garkuwoyi da dukkan tasoshi, da kwanoni masu daraja.
\v 28 Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi dana mai, da wuraren turke dabbobi na kowanne iri, yana kuma da garkuna a cikin rufar dabbobinsa.
\v 29 Bugu da ƙari, ya kuma tanada wa kansa birane da mallakar garkunnan tumaki da na shanu a yalwace. Gama tsauni yaba shi wadata mai yawa.
\s5
\v 30 Hezekiyan nan ne kuwa ya datse ruwan da yake gangarowa daga kogin Gihon, ya kuma kawo su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dauda. Hezekiya ya yi nasara da dukkan ayyukansa.
\v 31 Ko da shi ke, game da jakadun hakiman Babila, waɗanda aka aika su tambaye shi game da waɗanda suka san irin abin al'ajibin da aka yi a ƙasar, sai tsauni ya ƙyale shi kurum, don ya jaraba shi ya san dukkan abin da kea zuciyarsa.
\s5
\v 32 Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, gashi an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz a littafin Sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
\v 33 Sai Hezekiya ya rasu, suka bizne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dauda, maza da dukkan Yahuda da mazaunan Yerusalem suka girmama shi sa'ad da ya rasu, sai Manasa ɗansa ya gaji gădon sarautarsa.
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Manasse yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru hamsin da biyar a Yerusalem.
\v 2 Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh, kamar ƙazantattun abubuwan da al'umman da Yahweh ya kore su a gaban mutanen Isra'ila.
\v 3 Gama ya gina wuraren kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe, kuma ya gina bagadai domin Ba'aloli. Ya ƙera sandunan Ashera, kuma ya russuna wa dukkan taurarin sammai ya yi masu sujada.
\s5
\v 4 Manasse ya gina bagadin a gidan Yahweh, koda shi ke dai Yahweh bai umarta ba, "A Yerusalem ne sunana zai kafu har abada."
\v 5 Ya gina bagadai ga dukkan taurarin sama a cikin shirayu biyun da kegidan Yahweh.
\v 6 A Kwarin Ben Hinnom ya sa 'ya'yansa maza a wuta. Ya aikata tsafe-tsafen tsubbu; ya yi karatun baƙaƙen zabura; kuma ya tuntuɓi masu magana da matattu da ruhohi. Manasse aikata miyagun ayyuka da dama a fuskar Yahweh, ya kuma tsokani Yahweh ga fushi.
\s5
\v 7 Sarafaffen siffar da ya yi, ya sa shi a gidan tsauni. A kan wannan gidan ne tsauni ya yi magana da Dauda da Suleman ɗansa. Ya ce, "A wannan gidan da Yerusalem ne, waɗanda na zaɓa daga dukan ƙabilun Isra'ila, cewa zan kafa sunana har abada.
\v 8 Ba zan ƙara fitar da mutanen Isra'ila daga ƙasar dana ba wa kakaninsu ba, idan za su yi biyayya su kiyaye dukkan abin dana umarce su, su bi dukkan dokoki da farillai dana umarta ta hannun Musa."
\v 9 Manasse ya jagoranci Yahuda da mazaunan Yerusalem ga yin mugunta fiye da al'umman da tsauni ya hallakar a gaban mutanen Isra'ila.
\s5
\v 10 Yahweh ya yi magana da Manasse da jama'arsa amma babu wanda ya kula.
\v 11 Saboda haka Yahweh yasa sarakunan yaƙi na sarkin Asiriya su kama Manasase su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla su kai shi Babila.
\s5
\v 12 Sa'ad da Manasse ke shan wahala, sai ya roƙi Yahweh, tsauninsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban tsauni na kakaninsa.
\v 13 ya yi addu'a zuwa gare shi; sai ya roƙi tsauni, sai tsauni ya ji rokonsa ya komo da shi Yerusalem, ga mulkinsa. Sa'an nan ne Manasse ya sani Yahweh shi ne tsauni.
\s5
\v 14 Bayan haka sai Manasse ya gina garu a bayan birnin Dauda a gefen yammacin Gihon, a kwari, zuwa Ƙofar Kifi. Ya kewaye tudun Ofel, bayan wannan kuma ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan yasa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuda.
\v 15 Ya kwashe baƙin alloli, wato gumaku daga cikin gidan Yahweh, da dukkan bagadin da ya giggina a bisa dutse na gidan Yahweh da Yerusalem. Ya zubar da su a bayan birnin.
\s5
\v 16 Ya kuma komar da bagadin Ubangiji ya miƙa hadayu na salama dana godiya a kansu; ya kuma umarci Yahuda da ta bauta wa Yahweh, tsauni na Isra'ila.
\v 17 Duk da haka, jama'a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadar bisa, amma ga Yahweh, tsauninsu kaɗai.
\s5
\v 18 Game da sauran ayyukan Manasse da addu'o'insa ga tsauninsa, da abubuwan da masu gani suka faɗa masa cikin sunan Yahweh, tsauni na Isra'ila, gasu, suna a rubuce cikin ayyukan sarakunan Isra'ila.
\v 19 A cikin rahoton akwai tarihin addu'arsa, da yadda tsauni ya ƙarɓi rokonsa, akwai kuma rahoton dukkan zunubinsa da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujada a bisa, ya kafa sandar Ashera da sarafaffun siffofi, kamin ya ƙasƙantar da kansa - suna nan a rubuce a Tarihin Masu Duba.
\v 20 Haka dai Manasse ya kwanta tare da kakaninsa, suka binne shi a gidansa. Sai Amon, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya fara sarauta, ya yi shekara biyu yana mulki a Yerusalem.
\v 22 Ya aikata mugunta a gaban Yahweh, kamar yadda Manasse, mahaifisa ya yi. Amon ya miƙa hadayu ga dukkan siffofin da mahaifinsa Manasse ya yi, ya bauta masu.
\v 23 Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Yahweh, kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi ba. Maimakon haka, shi wannan Amon fa ya ƙara yin zunubi gaba-gaba.
\s5
\v 24 Sai fadawansa suka yi masa maƙarkashiya suka kashe shi a gidansa.
\v 25 Amma jama'ar ƙasar suka ƙarkashe dukkan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiya, sai suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gaji gadon sarautarsa.
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya fara sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Yerusalem.
\v 2 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh, ya kuma yi tafiya a hanyoyin Dauda mahaifinsa, kuma bai juya dama ko hagu ba.
\v 3 Gama a shekara ta takwas na mulkinsa, tun yana yaro ya fara biɗan tsauni na Dauda, kakansa, a shekara ta goma sha biyu ne ya fara tsarkake Yahuda da Yerusalem daga tsafin wuraren bisa da sandar Ashera da sarafaffun siffofi da zuben siffofin ƙarfe.
\s5
\v 4 Mutanen suka rurrusa bagadan Ba'alolin a gabansa; ya rurrusa bagadan turaren da kebisansu. Ya karya sandar Ashera da saraffaffun sifoffi da siffofin ƙarafuna har suka ragargaje zuwa ƙura. Ya yayyafa ƙurar a kan kaburburan waɗanda suka yi masu hadaya.
\v 5 Ya ƙona kasusuwan firistocinsu a bagadansu. Ta haka ya tsarkake Yahuda da Yerusalem.
\s5
\v 6 Ya yi haka kuma a biranen Manasa da Ifraimu da Saminu har zuwa Naftali da lalatattun wurare da kekewaye da su.
\v 7 Ya rusar da bagadan; ya ragargaza sandar Ashira da sarafaffun siffofi zuwa gǎri, ya kuma rurrusa bagadan turare a dukkan ƙasar Isra'ila; sa'an nan ya koma Yerusalem.
\s5
\v 8 Yanzu a shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan Yosiya ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Ma'aseya da gwamnan birnin da Yowa ɗan Yowahaz magatakarda, da su gyaggyara gidan Yahweh tsauninsa.
\v 9 Suka je wurin Hilkaya, babban firist, suka danƙa masa kuɗin da aka kawo gidan Yahweh wanda Lebiyawa da masu gadin ƙofofi suka tara daga Manasse da Ifraimu, daga dukkan ragowar Isra'ila, daga dukkan Yahuda da Benyamin da kuma daga mazaunan Yerusalem.
\s5
\v 10 Suka danƙa kuɗin ga mazan da kelura da gidan Yahweh. Waɗannan mazan ne ke biyan ma'aikatan da ke gyaggyarawa da adana haikalin.
\v 11 Suka biya kafintoci da magina kuɗin da zasu sayi sassaƙaƙƙen duwatsu da katakai domin yin tsaiko kuma da tankaru don gine- ginen da waɗansu sarakuna na Yahuda suka bar su suka lalace.
\s5
\v 12 Mazajen sun yi aikin da aminci. Masu shugabancinsu su ne Yahat da Obadiya wato Lebiyawa, 'ya'yan Merari; da Zekariya da Meshullam, daga 'ya'ya mazan Kohatawa. Sauran Lebiyawan waɗanda dukkansu ƙwararrun mawaƙa ne, sun yi shugabancin ma'aikatan.
\v 13 Waɗannan Lebiyawan ne ke shugabancin masu ɗaukan kayan gini da duk sauran ma'aikata daban-daban. Akwai kuma Lebiyawan da kemasu rubuce=rubuce da masu gudanar da shugabanci da masu gadin ƙofofi.
\s5
\v 14 Sa'ad da suka kawo kuɗin da aka kawo gidan Yahweh, Hikaya firist ya samo littafin shari'a ta Yahweh wanda aka bayar ta wurin Musa.
\v 15 Hikaya ya cewa Shafan magatakarda, "Na sami littafin shari'a a gidan Yahweh." Hikaya ya kawo littafin ga Shafan.
\v 16 Shafan ya kai ma sarki littafin, ya kuwa ba shi rahoto, cewa, "Barorinka na yin dukkan abubuwan da aka basu amanan yi.
\s5
\v 17 Suka tattaro kuɗin da aka samu agidan Yahweh, sai suka bayar da shi ga hannun shugabannin lura da mazan aikin."
\v 18 Shafan magatakarda ya faɗa wa sarki, "Hilkaya firist ya ba ni littafi." Sa'an nan Shafan ya karanta wa sarkin.
\v 19 Ya zamana kuwa a sa'an da sarki ya ji kalmomin shari'a, sai ya yayyage tufafinsa.
\s5
\v 20 Sarkin ya umarce Hilkaya da Ahikam ɗan Shafan da Abdon ɗan Micah da Shafan magatakarada da Ashaya, baransa, cewa,
\v 21 "Ku je ku bincika nufin Yahweh domina, da kuma domin waɗanda aka bar su a Isra'ila da Yahuda, saboda kalmomin littafi da aka samo. Gama yana da girma, hasalar Yahweh da aka zubo mana. yana da yawa, saboda kakaninmu basu saurari kalmomin wannan littafi ba don su yi biyayya da dukkan abin da aka rubuto cikinta."
\s5
\v 22 Saboda haka Hilkaya, da waɗanda sarki ya umarta, suka je wurin annabiya Huldah, matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai lura da tufafin firistoci (tayi zama a Yerusalem a Gunduma ta Biyu), sai suka yi magana da ita haka.
\s5
\v 23 Sai ta ce masu, "Ga abin da Yahweh, tsaunin Isra'ila, ya ce: "Gaya wa mutumin da ya aiko ku wuri na,
\v 24 Ga abin da Yahweh ya faɗi: Duba. 'Ina gab da kawo bala'i a nan wurin da kan mazaunanta, dukkan la'anonin da aka rubuta a littafi da suka karanta a gaban sarkin Yahuda.
\v 25 Saboda sun ƙi ni kuma sun ƙona turare ga waɗansu alloli, saboda su zuga ni ga fushi da dukkan ayyukan da suka aikata- Don haka fushi na zai zubo a wannan wurin, kuma ba za a datse shi ba.'
\s5
\v 26 Amma ga sarkin Yahuda, wanda ya aiko ku ku tambayi Yahweh abin da zai yi, ga abin da zaku gaya ma sa, 'Yahweh, tsauni na Isra'ila ya faɗi haka: Game da maganganun da ka ji,
\v 27 saboda baka taurare zuciyarka ba, kuma ka ƙasƙantar da kanka a gaban tsauni sa'ad da ka saurari maganganu game da wannan wurin da mazaunanta, kuma domin ka ƙasƙantar da kanka a gaba na, ka yayyaga taufafinka ka yi kuka a gabana, Ni kuma na saurare ka - wannan furcin Yahweh ne -
\v 28 duba, Zan tattara ka da kakaninka. Za a tattara ka zuwa kabarinka cikin salama, kuma idanuwanka ba za su ga bala'in da zan kawo a wurin nan da mazaunanta ba." Mazajen nan suka kai wa sarki wannan saƙon.
\s5
\v 29 Sa'an nan sarkin ya aiko manzanni su tattaro dukkan dattawan Yahuda da Yerusalem tare.
\v 30 Sa'an nan sarkin ya haura zuwa gidan Yahweh, da dukkan mazajen Yahuda da mazaunan Yerusalem, da firistoci da Lebiyawa da dukkan mutane, daga manya zuwa ƙanana. Sa'an nan ya karanto ga saurarawarsu dukkan kalamomin littafin Alƙawari da aka samo a gidan Yahweh.
\s5
\v 31 Sarkin ya tsaya a wurinsa ya yi alƙawari a gaban Yahweh, ya yi tafiya bisa ga jagorancin Yahweh, ya kuma kiyaye dokokinsa da farillansa da umarnansa, da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa, ya yi biyayya da maganganun alƙawari da kea rubuce a wannan littafi.
\v 32 Ya sa dukkan waɗanda aka same su a Yerusalem da Benyamin su tsaya a kan alƙawarin. Mazaunan Yerusalem sun yi aiki cikin biyayya ga alƙawarin tsauni, tsauni na kakanninsu.
\s5
\v 33 Yosiya ya ɗauke dukkan ƙazamtattun abubuwa daga ƙasashen da suke na mutanen Isra'ila. Ya sa kowa a Isra'ila ya bauta wa Yahweh, tsauninsa. Gama a dukkan kwanakinsa, ba su juya daga bin Yahweh, tsaunin kakaninsu ba.
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Yosiya ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Yahweh a Yerusalem, kuma suka kashe 'yan ragunan Idin a rana ta goma sha huɗu ga wata na fari.
\v 2 Ya sa firistocin a matsayinsu ya ƙarfafa su a cikin hidimar gidan Yahweh.
\s5
\v 3 Ya cewa Lebiyawan da suka koyar da dukkan Isra'ila waɗanda aka keɓe ga Yahweh, "Ku sa akwati mai tsarki a gidan da Suleman ɗan Dauda, sarkin Isra'ila ya gina. Kada ku dinga ɗaukar sa a bisa kafaɗunku kuma. Yanzu ku bauta wa Yahweh tsauninku, ku yi wa mutanensa Isra'ila hidima.
\v 4 Ku shirya kanku ta sunayen gidajen kakaninku da ɓangarorinku, bisa ga rubutaccen umarnin Dauda, sarkin Isra'ila, da ta Suleman, ɗansa.
\s5
\v 5 Ku tsaya a wuri mai tsarki, kuna ɗaukan matsayinku tare da ɓangarorin 'yan'uwanninku maza ta cikin gidajen kakaninku da zuriyoyin mutane, kuna kuma ɗaukan matsayinku tare da ɓangarorinku ta cikin gidajen kakaninku na Lebiyawa.
\v 6 Ku kashe 'yan ragunan Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya ragunan domin 'yan'uwanku maza, kuyi bisa ga maganar Yahweh da aka bayar ta hannun Musa."
\s5
\v 7 Yosiya ya baiwa dukkan mutane 'yan raguna dubu talatin da 'yan awakai daga turkuna domin baikon Idin Ƙetarewa ga dukkan waɗanda suka kasance. Ya kuma bada bijimai dubu talatin; waɗannan daga mallakar sarki ne.
\v 8 Shugabaninsa sun bayar da baikon yardar rai ga mutane da firistoci da Lebiyawa. Hilkaya da Zekariya da Yehiyel da manyan ma'aikatan da kelura da gidan tsauni, sun ba firistoci baikon ƙananan shanu 2,600 da bijimai ɗari uku domin Idin Ƙetarewa.
\v 9 Konaniya kuwa da Shemaya da Netanel, 'yan'uwansa maza, da Hashabiya da Ye'iyel, da Yozabad, waɗanda ke shugabancin Lebiyawa, sun ba Lebiyawan baiko domin Idin Ƙetarewa ƙananan shanu dubu da bijimai ɗari biyar.
\s5
\v 10 Don haka aka shirya hidimar, sai firistocin suka tsaya bisa ga matsayinsu, da Lebiyawan ta ɓangarorinsu, cikin yin biyayya da umarnin sarki.
\v 11 Suka kashe 'yan ragunan Idin Ƙetarewa, sai firistoci suka zuba jinin da suka karɓo daga hannun Lebiyawan, sai Lebiyawan suka feɗe 'yan ragunan.
\v 12 Suka cire hadayun ƙonawa, don su rarraba su ga ɓangarorin gidajen kakanin mutanen, suƙa miƙa su ga Yahweh, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Musa. Suka yi haka kuma da bijiman.
\s5
\v 13 Suka gaggasa 'yan ragunan Idin Ƙetarewan da wuta bisa ga umarni. Game da tsarkakkun baye-bayen, suka dafa su cikin ruwa a tukwane daban-daban, suka kuma ɗauka da sauri suka kai wa dukkan mutane.
\v 14 Suka shirya baye-baye daga baya domin kansu da firistocin, saboda firistocin, wato zuriyar Haruna, suna fama da miƙa hadaya ta ƙonawa da kitsen har sai dare ya yi, saboda haka Lebiyawan sun shirya baye-bayen domin kansu da firistoci, zuriyar Haruna.
\s5
\v 15 Mawaƙan, zuriyar Asaf, suna wurin, bisa ga bishewar Dauda da Asaf da Heman da Yedutun mai duba na sarki, kuma masu tsaro suna a kowacce ƙofa. Ba za su taɓa barin wurin tsayawarsu ba, saboda 'yan'uwansu Lebiyawa sun shirya abu dominsu.
\s5
\v 16 Don haka, a lokacin nan dukkan hidimar Yahweh ana yi domin bikin Idin Ƙetarewa ne da miƙa baye-bayen ƙonawa a bagaden Yahweh, kamar yadda sarki Yosiya ya umarta.
\v 17 Mutanen Isra'ilan da suka kasance sun kiyaye Idin Ƙetarewa a lokacin, sa'an nan kuma da Shagulgulan Gurasa Marar Gami na kwana bakwai.
\s5
\v 18 Irin wannan bikin Idin Ƙetarewan ba a taɓa yin sa a Isra'ila ba tun daga kwanakin su annabi Sama'ila, ba kuwa wani daga cikin sauran sarakunan Isra'ila da ya yi hidimar bikin Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci da Lebiyawa da dukkan mutanen Isra'ilan da suka kasance, kuma da mazaunan Yerusalem.
\v 19 Wannan Idin Ƙetarewa an kiyaye shi ne a shekara ta goma sha takwas na mulkin Yosiya.
\s5
\v 20 Bayan dukkan wannan, bayan Yosiya ya shirya haikalin bisa ga tsari, Neko, sarkin Masar, ya hauro ya yi faɗa da Karkemish a Kogin Yuferetis, sai Yosiya ya je ya yi faɗa da shi.
\v 21 Amma Neko ya aiko wakilai gun sa, cewa, "Mene ne zan yi da kai, sarkin Yahuda? Ba na zuwa găba da kai yau, amma găba da gidan da nake yaƙi da su. tsauni ya umarce ni da in yi sauri, saboda haka ka janye daga shisshigi da Allah, wanda ke tare da ni, don zai iya hallaka ka."
\s5
\v 22 Koda shi ke, Yosiya ya ƙi ya juyo daga gare shi. Ya ɓoye kamaninsa don ya yi yaƙi da shi. Bai saurari maganar Neko da ta zo daga bakin Allah ba; sai ya je ya yi faɗa a Kwarin Megiddo.
\s5
\v 23 Jarumawa suka harbi Yosiya, sai sarki ya cewa barorinsa, "Ku tafi dani, gama na sami mumunar rauni,"
\v 24 Sai barorinsa suka ɗauke shi daga karusar, suka sa shi a karusa ta biyu. Suka kai shi Yerusalem, inda ya mutu. Aka binne shi a wurin binne kakaninsa. Dukkan Yahuda da Yerusalem suka yi makoki domin Yosiya.
\s5
\v 25 Irimiya ya yi makoki domin Yosiya; dukkan mazaje da mata mawaƙa suna maƙoƙi game da Yosiya har yau. Waɗannan waƙoƙin suka zama al'ada a Isra'ila; Suna a rubuce a waƙoƙin maƙoƙi.
\s5
\v 26 Game da sauran abubuwan da suka shafi Yosiya, da nagargarun ayyukansa da ya yi cikin biyayya da abin da kea rubuce a shari'ar Yahweh -
\v 27 kuma dukkan ayyukansa, daga farko zuwa karshe, na a rubuce cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila.
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Sa'an nan mutanen ƙasar suka ɗauki Yehowahas ɗan Yosiya, suka maida shi sarki a madadin mahaifinsa a Yerusalem.
\v 2 Yehowahas yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya fara mulki, ya kuma yi mulki watanni uku a Yerusalem.
\s5
\v 3 Sarkin Masar ya cire shi a Yerusalem, ya sa wa ƙasar tara na talenti ɗari na azurfa da talenti ɗaya na zinariya.
\v 4 Sarkin Masar ya maida Iliyakim, ɗan'uwansa, sarki a kan Yahuda da Yerusalem, (ya sauya wa Iliyakim suna zuwa Yehoyakim). Sa'an nan Neko ya ɗauki ɗan'uwan Iliyakim Yehowahas ya kawo shi Masar.
\s5
\v 5 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Yerusalem. Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh Allahnsa.
\v 6 Sa'an nan Nebukadnezar, sarkin Babila, ya kai masa hari ya ɗaure shi da sarƙoƙi ya kai shi Babila.
\v 7 Nebukadnezar kuma ya ɗauki waɗansu kayayyakin gidan Yahweh zuwa Babila, ya sa su a fadarsa a Babila.
\s5
\v 8 Game da sauran zantattukan da suka shafi Yehoyakim, abubuwan ƙazamtar da ya yi, da abin da aka samo găba da shi, gashi, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra'ila. Sa'an nan Yehoyakin, ɗansa, ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 9 Yehoyakin yana da shekara takwas sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki wata uku da kwana goma a Yerusalem. Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh.
\v 10 Da bazara, Sarki Nebudkanezar ya aiki mazaje aka kawo shi Babila, tare da abubuwa masu daraja daga gidan Yahweh, sai ya maida Zedekiya, danginsa, sarki a kan Yahuda da Yerusalem.
\s5
\v 11 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Yerusalem.
\v 12 Ya yi abin da kemugunta a fuskar Yahweh Allahnsa. Bai ƙasƙantar da kansa a gaban annabi Irimiya ba, wanda ya yi magana daga bakin Yahweh.
\s5
\v 13 Zedekiya kuwa ya yi tayarwa gãba da Sarki Nebudkanezar, wanda ya sa shi rantsuwar yin biyayya gare shi da sunan Allah. Amma Zedekiya ya taurare zuciyarsa da wuyansa gãba da juyowa ga Yahweh, Allahn Isra'ila.
\v 14 Bugu da ƙari, dukkan shugabannin firistocin da mutanen sun yi mummunan rashin aminci, kuma suka bi kazamtattun aikin al'ummai. Suka lalatar da gidan Yahweh wanda ya tsarkake a Yerusalem.
\s5
\v 15 Yahweh, Allahn kakaninsu, ya aiko da kalma garesu ta manzaninsa a kai a kai, saboda yana da tausayi a kan mutanensa da wurin da yake zamne.
\v 16 Amma sun yi ma manzanin Allah ba'a, suka yi banza da maganarsa, suka kuma wulaƙantar da annabawansa, har sai da fushin Allah ya taso gãba da mutanensa, har babu taimako game da haka.
\s5
\v 17 Don haka Allah ya kawo masu sarkin Kaldiyawa, wanda ya kashe 'yan mazansu da takobi a masujada, kuma ba su ji tausayin 'yan maza ko budurwai ko tsofoffin maza ko masu farin gashi ba. Allah ya bayar da su dukka ga hannunsa.
\s5
\v 18 Dukkan kayan ɗaki na gidan Allah, masu manya da ƙanana da dukiyoyin gidan Yahweh da dukiyoyin sarki da ma'aikatansa- dukkan waɗannan ya kwashe zuwa Babila.
\v 19 Suka ƙona gidan Allah, suka rurrushe garun Yerusalem, suka ƙona dukkan fadodinta, kuma suka hallakar da dukkan abubuwa masu kyau a ciki.
\s5
\v 20 Sarki ya ɗauke zuwa Babila waɗanda suka kuɓce wa takobi. Suka zama barori dominsa da 'ya'yansa maza har zuwa mulkin Fasha.
\v 21 Wannan ya faru ne domin a cika maganar Yahweh ta bakin Irimiya, har sai ƙasar ta ji daɗin hutun Asabatunta. Ta jira Asabbatu na tsawon lokacin da take zama a yashe, don a wuce shekaru saba'in ta haka.
\s5
\v 22 Yanzu kuwa a shekara ta farko ta Sairus, sarkin Fasha, domin maganar Yahweh ta bakin Irimiya ta cika, Yahweh ya zuga ruhun Sairus, sarkin Fasha, don haka ya sanar da umarni ga dukkan mulkinsa, ya kuma sa ta a rubuce. Ya ce,
\v 23 Ga abin da Sairus, sarkin Fasha, ya ce: "Yahweh, Allahn sammai, ya bani dukkan mulkokin duniya. Ya umarce ni in gina gida dominsa a Yerusalem, wanda yake a Yahuda. Duk wanda ke cikinku daga dukkan mutanesa, Yahweh Allahnku, ya kasance tare da ku. Bari ya haura can zuwa ƙasar."