ha_ulb/12-2KI.usfm

1425 lines
117 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 2KI
\ide UTF-8
\h Littafin Sarakuna Na Biyu
\toc1 Littafin Sarakuna Na Biyu
\toc2 Littafin Sarakuna Na Biyu
\toc3 2ki
\mt Littafin Sarakuna Na Biyu
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Mowab ta tayar wa Isra'ila a bayan mutuwa Ahab.
\v 2 To sai Ahaziya ya faɗo daga sakatar gidan samansa a Samariya, har ya yi rauni. Sai ya aika 'yan saƙo ya ce da su, "Ku je ku tambayi Ba'al Zebub, allahn Ekron, ko zan warke daga wannan raunin."
\s5
\v 3 Amma mala'ikan Yahweh yace da Iliya Batishbe, "ka tashi ka je ka sadu da 'yan saƙon sarkin Samariya, ka tambaye su, ko domin ba Allah ne a Isra'ila shi ya sa kuka je kuka tuntuɓi Ba'al Zebub, allahn Ekron?
\v 4 Domin haka Yahweh ya ce, ba za ka sauko daga wannan gadon da ka hau ba; a maimakon haka za ka mutu.'"' Daga nan sai Iliya ya tafi.
\s5
\v 5 Bayan 'yan saƙon sun dawo wurin Ahaziya, sai ya ce da su, "Meyasa ku ka dawo?"
\v 6 suka ce da shi wani mutum ne ya zo ya gamu da mu ya ce mana, ku koma wurin wanda ya aiko ku ku ce da shi, "Yahweh ya faɗi wannan; Ashe babu Allah ne a Isra'ila da ka aika 'yan saƙo Ekron su tambayi Ba'al Zebub? saboda haka ba za ka tashi daga gadon jinyarka ba, a maimakon haka hakika zaka mutu."""
\s5
\v 7 Ahaziya yace da 'yansaƙonsa "wanne irin mutum ne shi, mutumin da ya zo wurinku ya faɗa muku wannan magana"?
\v 8 Suka ce da shi yana saye da rigar da a ka yi da gasusuwa da kuma ɗammara ta fata a kwankwasonsa," sai sarkin ya amsa ya ce Iliya ne Batishbe."
\s5
\v 9 Sai sarki ya aika jami'ai da sojoji hamsin wurin Iliya. Jami'an suka je wurin Iliya a inda ya ke zaune a saman dutse. Jami'an suka yi magana da shi cewa, "Kai mutumin Allah, sarki ya ce ka sauko ƙasa."
\v 10 Iliya ya amsa ya ce da jami'an, "In ni mutumin Allah ne, bari wuta tasauko daga sama ta ƙone mutanenku guda hamsin." Wuta ta sauko daga sama ta ƙone mutanensa hamsin tare da shi.
\s5
\v 11 Sai sarki Ahaziya ya sake yin aike wurin Iliya da wata runduna ta mutum hamsin tare da hafsa. shi ma wannan hafsan ya sake cewa da Iliya, "Kai mutumin Allah, sarki ya ce ka sauko da sauri."
\v 12 Iliya ya amsa ya ce da su, in ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta ƙone ku tare da mutanenka guda hamsin." Sai wuta ta sake saukowa daga sama ta ƙone shi tare da mutanensa guda hamsin.
\s5
\v 13 Sarki kuma ya sake aikawa da ƙungiya ta uku tare da mazaje hamsin mayaƙa. wannan hafsan sai ya je ya durƙusa a gwiwarsa a gaban Iliya, ya roƙe shi ya ce da shi, "kai mutumin Allah ina roƙonka bari raina da na waɗannan sojoji hamsin ya sami daraja a gabanka.
\v 14 Hakika wuta ta sauko daga sama ta ƙone rundunoni guda biyu na farko tare da hafsoshinsu, amma yanzu ina roƙo bari raina ya zama da daraja a gabanka."
\s5
\v 15 Sai mala'ikan Yahweh yace da Iliya, "Ka sauka ƙasa tare da shi. kada ka ji tsoronsa." Sai Iliya ya tashi ya sauka ya tafi tare da shi zuwa wurin sarki.
\v 16 Can sai Iliya ya ce da Ahaziya, "Wannan shi ne abin da Yahweh ya ce, 'Ka aika manzanni su tambayi Ba'al Zebub allan Ekron. Shin domin ba bu Allah ne a Isra'ila wanda zaka tambaya domin samun sadarwa? to yanzu hakika ba zaka sauko daga gadon da ka hau ba hakika za ka mutu."
\s5
\v 17 Don haka sarki Ahaziya ya mutu bisa maganar Yahweh wadda Iliya ya furta. Sai Yorom ya gaji sarautarsa, a shekara ta biyu ta Yehoram ɗan Yehoshafat sarkin Yahuda, saboda Ahaziya ba shi da ɗa.
\v 18 Game kuma da sauran abubuwa game da Ahaziya, ashe ba a rubuta su a littafin ayyukan sarakunan Isra'ila ba?
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 To sai ya zama a lokacin da Yahweh zai ɗauki Iliya zuwa sama ta guguwa, da Iliya ya rabu da Elisha zuwa Gilgal.
\v 2 Iliya ya ce da Elisha "ka jira nan ina roƙonka domin Yahweh ya aike ni zuwa Betel, Elisha ya ce da shi "Muddin Yahweh na raye, kana kuma raye, ba zan bar ka ba." To sai suka tafi Betel tare.
\s5
\v 3 "Ya'yan annabawa da ke a Betel suka zo wurin Elisha suka ce da shi, Ko ka san Yahweh zai ɗauke shugabanka daga gare ka yau?" Elisha ya amsa masu, i na sani, amma kada ku yi magana tukuna."
\v 4 Iliya ya ce da shi, Elisha ka jira a nan, Domin Yahweh ya aike ni Yeriko." Sai Elisha ya amsa, "Muddin Yahweh na raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba." Domin haka suka tafi Yeriko.
\s5
\v 5 Sai 'ya'yan annabawa da ke a Yariko suka zo wurin Elisha suka ce da shi, "Ko ka san cewa yau Yahweh zai ɗauke shugabanka da ga gare ka? "Elisha ya amsa, "I na sani, amma ka da ku yi maganar tukuna."
\v 6 Sai Iliya ya ce da shi, "Ka tsaya nan, domin Yahweh ya aike ni Yodan.'" Elisha ya amsa, Muddin Yahweh na raye, kai kuma kana raye, Ba zan rabu da kai ba." domin haka su biyun suka tafi.
\s5
\v 7 Can an jima sai 'ya'yan annabawa hamsin suka tsaya a gefensu da ɗan nisa su kuma biyun suka tsaya a gefen Yodan.
\v 8 Iliya ya cire tufafinsa, ya naɗe shi sai ya bugi ruwa da shi. sai rafin ya rabu biyu ta kowanne gefe su biyu suka taka sandararriyar ƙasa suka ƙetare.
\s5
\v 9 Bayan sun ƙetare, sai Iliya ya ce da Elisha, "ka roƙi abin da zan yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka." Elisha ya amsa, ina roƙo a ba ni riɓi biyu na ruhunka ya sauko a kaina."
\v 10 Iliya ya amsa, "Ka roƙi abu mai wuya. amma duk haka, in ka gan ni a lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, wannan zai faru sabo domin ka, amma in ba haka ba, ba zai faru ba."
\s5
\v 11 Da suka ƙara tafiya suna magana, sai ga karusai na wuta da dawakai na wuta suka baiyana, waɗanda suka raba tsakanin su, Iliya ya tafi sama ta guguwa.
\v 12 Da Elisha ya gani ya yi kuka, ya ce "Babana, Babana, karusai na Isra'ila da mahaya dawakansu!" Bai ƙara ganin Iliya ba, sai ya ɗauki tufafinsa ya keta su biyu.
\s5
\v 13 Sai ya ɗauki alkyabar Iliya da ta faɗo masa, ya koma ya tsaya a bakin Yodan. Ya bugi ruwan da tufafin Iliya wanda ya faɗo ya ce, "Ina Yahweh, Allah na Iliya?"
\v 14 Bayan ya bugi ruwan sai ruwan ya rabu biyu ta kowanne gefe sai Elisha ya ƙetare.
\s5
\v 15 Lokacin da 'ya'yan annabawa da ke Yeriko suka ga ya ƙetaro daga wurinsu, suka ce "Ruhun Iliya ya sauko akan Elisha!" Sai suka zo domin su tare shi, suka sunkuyar da kawunansu a ƙasa a gabansa.
\v 16 Suka ce da shi, Duba yanzu a cikin barorinka akwai mazaje hamsin majiya ƙarfi. Ka bar su su je su nemo shugabanka, ƙila ko Ruhun Yahweh ya ɗauke shi ya kai shi bisa wasu duwatsu, ko kuma waɗansu kwarurruka." Elisha ya amsa ya ce kada ku aike su."
\s5
\v 17 Amma bayan sun matsa masa sai ya ji nauyi, ya ce "ku aike su." Suka aiki mazaje hamsin suka yi ta nema har kwana uku amma basu same shi ba.
\v 18 Suka dawo wurin Elisha, a lokacin da yake a Yeriko, sai ya ce da su, "Ashe ban ce da ku kada ku je ba'?"
\s5
\v 19 Mutanen birnin suka ce da Elisha, "Duba muna roƙon ka, halin da muke ciki a garin nan yana da faranta rai sosai kamar yadda shugabana ya gani, amma ruwan ba shi da kyau ƙasar kuma ba ta bada hatsi."
\v 20 Elisha ya amsa, "Ku samo mini sabon daro ku sa gishiri a cikinsa," domin haka suka kawo masa daro.
\s5
\v 21 Sai Elisha ya fita ya tafi mafitar ruwan rafin ya sa gishirin a cikinsa; sai ya ce ga abin da Yahweh ya ce, na warkar da waɗannan ruwaye. daga yanzu ba za a sami mutuwa ko rashin 'ya'ya ba a cikin ƙasar.'"
\v 22 Domin haka ruwan ya gyaru har ya zuwa yau, ta wurin maganar Elisha.
\s5
\v 23 Sai ya tafi can zuwa Betel. Lokacin da yake tafiya akan hanya, sai samari suka fito daga birni suka yi masa ba'a; suka ce da shi, "Kai mai saiƙo ka tafi, kai mai saiƙo ka tafi!"
\v 24 Sai Elisha ya duba gefensa ya gan su; Sai ya yi kira ga Yahweh ya la'antasu. Sai matan damisa guda biyu suka fito daga kogo suka raunata samari guda arba'in da biyu.
\v 25 Daga nan sai Elisha ya bar wurin ya tafi Tsaunin Karmel, daga can kuma sai ya koma Samariya.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 A shekara ta sha takwas ta Yohoshafat sarkin Yahuda, Yoram ɗan Ahab ya fara mulkin Isra'ila a Samariya; ya yi mulki na shekaru sha biyu.
\v 2 Ya yi abin da ke mugu a gaban Yahweh, amma ba kamar mahaifinsa da mahaifiyarsa ba; domin ya kawar da masujadar Ba'al da mahaifinsa ya gina.
\v 3 Duk da haka ya riƙe zunubin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi, bai kauce daga gare su ba.
\s5
\v 4 Sai Mesha sarkin Mowab ya yi sausayar tumaki. Ya ba sarkin Isra'ila raguna 100,000 da kuma fatun raguna 100,000.
\v 5 Amma bayan Ahab ya mutu, sai sarkin Mowab ya tayar wa sarkin Isra'ila.
\v 6 Domin haka sarki Yoram ya gudu daga Samariya a wancan lokacin domin ya shirya sojojin Isra'ila domin yaƙi.
\s5
\v 7 Sai ya aika da saƙo ga Yohoshafat sarkin Yahuda, cewa, Sarkin Mowab ya tayar mani. Ko za ka tafi tare da ni yaƙi gãba da Mowab?" Yehoshafat ya amsa, "Zan je. Ni ma kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina kamar dawakanka ne."
\v 8 Sai ya ce, "Ta wacce hanya zamu kai masu hari?" Yehoshafat ya amsa, "Ta hanyar jejin Idom."
\s5
\v 9 To sai sarakunan Isra'ila da Yahuda dana Idom suka yi ta kai da kawowa har tsawon kwanaki bakwai. Babu ruwan sha domin sojojinsu, babu kuma domin dawakansu ko kuma sauran dabbobi.
\v 10 To sai sarkin Isra'ila ya ce, Me kenan? ko Yahweh ya tattaro sarakuna guda uku ya bashe su a hannun Mowab ne?"
\s5
\v 11 Amma Yehoshafat ya ce, Ko babu wani annabin Yahweh ne, da zamu tambayi Yahweh ta wurinsa?" Sai ɗaya daga cikin barorin sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Eleisha ɗan Shafat yana nan, shi ne ya zuba ruwa a hannun Iliya."
\v 12 Yehoshafat ya ce Maganar Yahweh na tare da shi." Domin haka Yehoshafat sarkin Isra'ila da sarkin Idom suka tafi wurinsa.
\s5
\v 13 Elisha yace da sarkin Isra'ila, Me zan yi da kai? Ka tafi wurin annabawan mahaifinka da mahaifiyarka." Sai sarkin Isra'ila ya ce da shi, A'a domin Yahweh ya kira waɗannan sarakuna guda uku tare domin ya bashe su a hannun Mowab."
\v 14 Elisha ya amsa, Muddin Yahweh na raye a gaban wanda nake tsaye, tabbas in da ba domin ina ganin darajar kasancewar Yehoshafat sarkin Yahuda ba, da ba zan ji ku ko in dube ku ba.
\s5
\v 15 Amma yanzu ka kawo mani makaɗi."Sai mai kiɗa ya yi kiɗa, sai hannun Yahweh ya zo kan Elisha.
\v 16 Ya ce Yahweh ya faɗi wannan, 'Ka sa tsirai su fito daga wannan kwarin.'
\v 17 Domin Yahweh ya faɗi wannan, Ba zaka ga iska ba, ko kuma ka ga ruwan sama ba, amma wannan rafin zai cika da ruwa, zaku kuma sha, kai da bisashenka da dukkan dabbobinka.'
\s5
\v 18 Wannan abu ne mai sauƙi a gaban Yahweh, Zai kuma ba ka nasara akan Mowabawa.
\v 19 Za ka kai hari akan ƙayatatcen birni da kowanne birni ku sare kowacce bishiya mai kyau, ku kuma busar da kowanne wuri mai fid da ruwa, ku kuma mayar da kowanne wuri kufai da duwatsu."
\s5
\v 20 Da safe a kusan lokacin miƙa hadaya, sai ga ruwa daga wajejen Idom; sai ƙasar ta cika da ruwa.
\s5
\v 21 To bayan duk Mowabawa sun ji cewa sarakuna sun zo su yaƙe su, sai suka tattara kansu, duk waɗanda kan iya ɗaukar makami, sai suka tsaya akan iyaka.
\v 22 Suka tashi da sassafe rana kuma ta haskaka. Da Mowabawa suka ga ruwa kusa da su, ya zama ja kamar jini.
\v 23 Sai suka ce "Wannan jini ne! Hakika an hallaka sarakuna, sun kuma karkashe juna! To yanzu Mowab, ku mu je mu kwashe su ganima!"
\s5
\v 24 Bayan sun zo sansanin Isra'ilawa, Isra'ilawa suka ba su mamaki suka hari Mowabawa, waɗanda suka tsere daga gabansu. Sojojin Isra'ila suka kori Mowabawa daga ƙasar, suka karkashe su.
\v 25 Suka rushe biranen, da kuma duk wani yankin ƙasa kowannen su ya dinga tura dutse har sai da suka rufe birnin suka cike kowanne kwari na ruwa, suka cinye kowanne ɗan itaciya. Amma sojojin saye da kayan yaƙi suka sake kai hari a kansa.
\s5
\v 26 Bayan sarki Mesha na Mowab ya ga ya yi rashin nasara, sai ya ɗauki mayaƙa masu sara domin su hari sarkin Idom, amma suka kasa.
\v 27 Sai ya ɗauki babban ɗansa, wanda zai yi sarauta bayansa, ya miƙa shi a matsayin baiko na ƙonawa akan ganuwa. Domin haka aka sami babbar hasala gãba da Isra'ila, sojojin Isra'ila kuma suka rabu da sarki Mesha suka koma ƙasarsu.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Sai matar ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa ta zo tana kuka da Elisah, tana cewa, "Baranka mai gidana ya mutu, kuma ka sani baranka ya ji tsoron Yahweh. To wanda ke binsa bashi ya zo ya kwashe 'ya'yana maza guda biyu su zama bayinsa.'
\v 2 'Sai Elesha ya ce da ita "Me ki ke so in yi maki? Ki faɗa mani abin da ki ke da shi a cikin gida? "Ta ce, baiwarka ba ta da komai a cikin gida, sai 'yar tukunya ɗaya ta mai."
\s5
\v 3 Sai Elisha yace, "Ki je ki aro tuluna daga maƙwabtanki, tulunan da ba komai a ciki. Ki aro gwargwadon yadda za ki iya arowa.
\v 4 Dole ne ki shiga ɗaki ki kulle ƙofa da ke da iyalanki sai ki zuzzuba mai a cikin dukkan tulunan; sai ki kawar da waɗanda suka cika."
\s5
\v 5 Sai ta bar wurin Elesha ta kulle ƙofa ita da 'ya'yanta suka kawo mata tulunan, ta kuma cika su da mai.
\v 6 Da tulunan suka cika, ta ce da ɗanta "Ka ƙaro mani wani tulun." Amma ya ce da ita, "Babu sauran tuluna." Sai man ya dena tsiyayowa.
\s5
\v 7 Sai ta zo ta faɗawa damutumin Allah. Ya ce "Je ki sayar da man; ki biya bashinki, sauran sai ki gudanar da rayuwarki tare da 'ya'yanki da shi."
\s5
\v 8 Wata rana Elisha ya je Shunem inda wata mata mai muhimmanci ke zama; Ta roƙe shi ya ci abinci tare da ita. Sau da dama Elisha yakan wuce ta wurin, ya kan bi ta wurin ya ci abinci.
\v 9 Sai matar ta ce da mijinta, "Duba, yanzu na gane wannan mutum mai tsarki ne na Allah wanda yake wucewa kullun.
\s5
\v 10 Sai mu yi masa ɗan ɗaki a saman rufi domin Elisha, sai mu sa gado a cikin ɗakin da teburi da kujeru da fitila. Domin in ya zo wurin mu, sai ya zauna a can."
\v 11 To da ranar ta zo da Elisha ya tsaya a can, sai ya shiga can ya huta.
\s5
\v 12 Elesha yace da Gehazi baransa, "Ka kira wannan Bashumaniye." Bayan ya kira ta, ta tsaya a gabansu.
\v 13 Elisha yace da shi, "Ka ce da ita, kin sha duk wannan fama domin ki kula da mu. Me zamu yi maki? Ko ma yi magana da sarki ko kuma da Kwamandan soja?'" Ta amsa "Ina zama a cikin mutanena."
\s5
\v 14 14 Domin haka Elisha yace,"To me za mu yi mata?" Gehazi ya amsa, "Hakika ba ta da ɗa Mai gidanta kuma ya tsufa."
\v 15 Domin haka Elisha ya amsa, "Kira ta." Bayan ya kira ta, sai ta tsaya a ƙofa.
\v 16 Elisha ya ce shekara mai zuwa war haka za ki riƙe ɗa." Ta ce, "A'a ya shugabana da kuma mutumin Allah, kada ka yi wa baiwarka ƙarya."
\s5
\v 17 Amma matar ta yi ciki sai ta haifi ɗa a dai-dai lokacin da Elisha ya faɗa mata.
\v 18 Bayan yaron ya yi girma, sai ya tafi wurin mahaifinsa wata rana, wanda ya ke tare da masu girbi. Sai ya ce da babansa, "Kaina, kaina."
\v 19 Mahaifinsa ya ce da bayinsa, "Ku kai shi wurin mahaifiyarsa."
\v 20 Lokacin da bayin suka ɗauki yaron suka kawo shi wurin mahaifiyarsa, yaron ya zauna a gwiwarta har tsakar rana daga nan sai ya mutu.
\s5
\v 21 Sai matar ta tashi ta kwantar da yaron a gadon mutumin Allah, ta kulle ƙofa, ta fita.
\v 22 Ta kira maigidanta, ta ce, "Ina roƙo ka aiko mani da ɗaya daga cikin bayi da kuma ɗaya daga cikin jakunan domin in yi sauri zuwa wurin mutumin Allah sa'an nan in dawo."
\s5
\v 23 Maigidanta ya ce donme ki ke so ki je wurinsa yau? Ba sabon wata ba ne ko kuma Asabar ba. "Sai ta amsa, "Komai zai yi dai-dai.
\v 24 " Sai ta ɗaura wa jaki sirdi ta ce da bayinta, "Ku kora shi da sauri; kada ku sausauta har sai na ce ku yi haka."
\s5
\v 25 To sai ta tafi ta je wurin mutumin Allah a Tsaunin Karmel. Lokacin da mutumin Allah ya hange ta daga nesa, sai ya ce da Gehazi baransa, "Duba ga matar nan Bashunamiya tana tafe.
\v 26 Ka ruga a guje ka tambaye ta, ko komai lafiya yake game da ita da maigidanta da kuma ɗanta?"' Ta amsa, "Ba damuwa."
\s5
\v 27 Lokacin da ta zo wurin mutumin Allah akan dutsen sai ta kama ƙafafunsa, sai Gehazi ya zo zai ture ta amma mutumin Allah ya ce "Ka ƙyale ta, domin hankalinta a tashe yake Yahweh kuma ya ɓoye mani al'amarin, bai kuma faɗa mani komai ba."
\s5
\v 28 Daga nan sai ta ce, "Na roƙe ka ɗa ne, ya shugaba na, Ashe ban ce kada ka yaudare ni ba?"
\v 29 Sai Elisha ya ce da Gehazi, "Maza shirya ka riƙe sandana a hanunka. Ka je gidanta. "In ka gamu da wani in ya gaishe ka kada ka amsa, kada ka amsa masa. Ka ɗora sandana a fuskar yaron."
\s5
\v 30 Amma mahaifiyar yaron ta ce, "Muddin Yahweh na raye, kana kuma raye, ba zan bar ka ba."Saboda haka Elisha ya tashi ya bi ta.
\v 31 Gehazi ya ruga kafin su kai ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma yaron bai iya ji ko kuma ya yi magana ba. Saboda haka Gehazi ya dawo ya gamu da su, ya ce da Elisha "Yaron bai farfaɗo ba."
\s5
\v 32 Lokacin da Elisha ya shiga gidan yaron a mace yake, yana kuma kwance akan gado.
\v 33 Sai Elisha ya shiga ya kulle ƙofa da yaron ya yi addu'a ga Yahweh.
\v 34 Sai ya hau ya kwanta akan yaron; ya sa bakinsa a bakinsa, idonnsa a idonsa, hannunsa a hannunsa. Sai ya miƙe akan yaron sai jikinsa ya yi ɗumi.
\s5
\v 35 Sai Elisha ya tashi ya zagaya ɗakin ya sake kwantawa akan yaron ya miƙe, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, sai ya buɗe idonsa!
\v 36 Sai Elisha ya kira Gehazi ya ce da shi "Ka kira Bashunamiye!" Sai ya kira ta, da ya kira ta, da ta shiga ɗakin sai Elisha ya ce da ita "Ɗauki ɗanki."
\v 37 Sai ta kwanta a ƙafafunsa fuskarta a ƙasa, daga nan sai ta ɗauki ɗanta ta fita.
\s5
\v 38 Sai Elisha ya sake zuwa Gilgal. Akwai yunwa kuma a ƙasar, 'ya'yan annabawa kuma na zaune a gabansa. Ya ce da baransa. "Ka ɗora babbar tukunya ka dafa miya domin 'ya'yan annabawa."
\v 39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura domin ya samo ganyayen abinci sai ya samon ganyen inabi mai guba ya tara shi da yawa ya cika haɓar rigarsa, Suka yayyanka suka zuba a cikin abincin, amma ba su san irin su ba.
\s5
\v 40 Sai suka zuba masu abinci su ci, can suna cikin cin abincin sai suka yi kuka suka ce "Da guba a cikin tukunyar!" Domin haka basu ƙara cin abincin ba.
\v 41 Amma Elisha ya ce "Ku kawo mani gãri." Sai ya zuba a tukunyar ya ce, ku zuba wa mutane su ci, daga nan ba a sami wata guba a cikin tukunyar ba.
\s5
\v 42 Sai wani mutum ya zo daga Ba'al Shalisha wurin mutumin Allah ya kawo masa curin gurasar sha'ir guda ashirin a cikin jakarsa daga cikin girbinsa, da kuma sababbin zargankun hatsi. Ya ce, "Ka ba mutane wannan domin su ci."
\v 43 Bayinsa suka ce "Ƙaƙa zamu ba da wannan ga mutane ɗari?" Amma Elisha yace "Ku ba su wannan domin su ci, domin Yahweh ya ce, 'Za su ci su kuma bar saura.'"
\v 44 Sai bayinsa suka ajiye shi a gabansu; suka ci suka bar saura, kamar yadda maganar Yahweh ta alkawarta.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Na'aman kwamadan sojan sarkin Aram, yana da girma da ƙima a gun shugabansa, saboda shi Yahweh yakan ba Aram nasara. Hakannan shi mutum ne mai ƙarfi da kuma ƙarfin halin, amma shi kuturu ne.
\v 2 Aremiyawa suka kai hari runduna runduna suka ɗauki wata yarinya daga ƙasar Isra'ila, ta yiwa matar Na'aman hidima.
\s5
\v 3 Sai yarinyar ta ce shugabarta, "Na so a ce shugabana tare yake da annabin da ke a Samariya! To zai warkar da shugabana daga kututtarsa."
\v 4 Sai Na'aman ya je ya faɗa wa sarki abin da yarinyar da ta zo daga ƙasar Isra'ila ta faɗa.
\s5
\v 5 Saboda haka sarkin Aram ya ce, "Yanzu ka tafi, zan kuma aika da wasiƙa zuwa ga sarkin Isra'ila." Sai Na'amam ya tafi ya ɗauki talanti goma na azurfa, da tsabar zinariya dubu shida, da kuma sauyin sutura guda goma.
\v 6 Hakannan ya kai wa sarkin Isra'ila wasiƙar da ta ce, Lokacin da wannan wasiƙa ta zo wurinka, za ka ga cewa na aiko da barana Na'aman zuwa wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa."
\s5
\v 7 Bayan sarkin Isra'ila ya karɓi wasiƙar ya karanta ta sai ya keta tufafinsa ya ce, "Ni Allah ne da zan iya rayarwa ko in kashe, da wannan mutum zai so in warkar da mutum daga kuturtarsa? Da alama yana neman jayayya da ni."
\s5
\v 8 To bayan Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya ce "Me yasa ka keta tufafinka? Ka bar shi ya zo wurina yanzu zai kuma sani akwai annabi a Isra'iula."
\v 9 Sai Na'aman ya je da karusarsa ya tsaya a ƙofar gidan Elisha.
\v 10 Elisha ya aika masa da 'yan saƙo gare shi cewa. "Ka je ka yi nutso sau bakwai a kogin Yodan, jikinka zai dawo, zaka kuma tsaftata.
\s5
\v 11 Amma Na'aman ya fusata ya tafi ya ce, "Duba na yi zaton tabbas zai zo wurina ya tsaya ya kira sunanYahweh Allahnsa, ya kuma ɗaga hannunsa a wurin ya warkar da kuturtar tawa,
\v 12 Ashe kogunan Abana da na Farfar wato kogunan Damaskus, basu fi duk waɗannan ruwayen na Isra'ila tsafta ba?" Sai ya juya cikin matuƙar hasala.
\s5
\v 13 Sai bayin Na'aman suka zo kusa suka yi magana da shi, "Babana, in da annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya ashe ba za ka yi ba? Amma me ya fi wannan da ya ce maka, "Ka yi nutso ka tsarkaka?'"
\v 14 Daga nan sai ya gangara ya je ya yi nutson sau bakwai a kogin Yodan ya yi biyayya ga ummarnin mutumin Allah. Sai jikinsa ya dawo kamar na jariri sabuwar haihuwa, ya kuma warke.
\s5
\v 15 Sai Na'aman ya koma wurin mutumin Allah shi da rundunarsa, ya ce "Duba yanzu na sani babu wani Allah a duk duniya sai a Isra'ila. To yanzu sai ka karɓi kyautai daga wurin baranka",
\v 16 Amma Elisha ya ce "Muddin Yahweh wanda nake tsaye a gabansa na raye ba zan karɓi komai ba," Na'aman ya matsa wa Elisha ya karɓa amma Elisha ya ƙi karɓa.
\s5
\v 17 To sai Na'aman yace, "In ba za ka karɓa ba sai a ba baranka kayan takarkari na kayan alatu, domin daga yanzu baranka ba zai miƙa hadaya ta ƙonawa ga wani allah ba sai ga Yahweh.
\v 18 Ka gafarci baranka, wato a lokacin da sarkina ya je gidan Rimmon domin ya yi sujada a can, ya kuma lashe hannuna na kuma sunkuya a gidan Rimmon, ina roƙon Yahweh ya gafarci baranka akan wannan."
\v 19 Elisha yace da shi, "Ka tafi da salama." Sai Na'aman ya tafi.
\s5
\v 20 Ya ɗan yi nisa kenan, lokacin da Gehazi baran Elisha mutumin Allah ya ce a ransa, Duba, shugabana ya kyale Na'aman ɗin nan mutumin Aremiya bai karɓi kyautai da ya ya kawo daga hannunsa ba. Muddin Yahweh na raye zan bi shi in karɓi wani abu daga wurinsa."
\v 21 Sai Gehazi ya bi Na'aman. Da Na'aman ya ga wani na biye da shi, sai ya dirgo daga karusa domin ya tare shi ya ce, "In ce ko lafiya?"
\v 22 Gehazi yace, "Lafiya ƙalau. Ubangidana ne ya aiko ni, cewa, 'Duba, yanzunan ya yi baƙi daga ƙasa mai duwatsu ta Ifiraim samari biyu na 'ya'yan annabawa. Ina roƙo ka ba su jaka biyu na zinariya, da kayan alfarma guda biyu."
\s5
\v 23 Na'aman ya amsa, "Ina murna sosai in ba ka talanti biyu." Na'aman ya bukaci Gehazi kuma ya ɗaure talanti biyu na azurfa a cikin jaka biyu, da riguna biyu, sai ya ɗora su akan bayinsa biyu, waɗanda ke ɗauke da jaka na azurfa a gaban Gehazi.
\v 24 Bayan Gehazi ya zo wurin duwatsu, sai ya karɓe jaka na azurfa daga hannunsu ya ɓoye su a cikin gida; ya sallami mutanen, suka tafi.
\v 25 Bayan Gehazi ya shiga ciki ya tsaya a gaban shugabansa, Elisha yace da shi, "Daga ina ka dawo, Gehazi?" Ya amsa, "Baranka bai je ko'ina ba."
\s5
\v 26 Elisha yace da Gehazi, "Ashe ruhuna baya tare da kai ne a lokacin da mutumin ya juyo da karusarsa domin ya gamu da kai? Ko wannan ne lokacin karɓar kuɗi da sutura da man zaitun da garkar inabi, da tumaki da bijimai, da bayi maza da mata?
\v 27 To kuturtar Na'aman za ta koma kanka da kuma zuriyarka har abada." Sai Gehazi ya fita daga gabansa a kuturce fari fat kamar auduga.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 'Ya'yan annabawa suka ce da Elisha, "Wurin da muke zama tare da kai ya gaza mana dukkanmu.
\v 2 Muna roƙo ka bar mu mu je Yodan, sai kowannen mu ya saro itace a can, sai mu gina wurin da zamu zauna." Elisha ya amsa, "To ku je"
\v 3 Ɗaya daga cikinsu ya ce, "Ina roƙo ka tafi tare da barorinka." Elisha ya amsa "za ni."
\s5
\v 4 To sai ya tafi tare da su, a lokacin da suka fara saran itatuwan.
\v 5 Amma a lokacin da ɗayansu ke sara sai kan gatarin ya faɗa a cikin ruwa; sai ya yi waiyo ya ce "Ya shugabana, aro shi aka yi!"
\s5
\v 6 Sai mutumin Allah yace, "A ina ya faɗa?" Mutumin ya nuna wa Elisha wurin. Sai ya saro 'yar tsafga, ya jefa ta cikin ruwa, sai ta sa ƙarfen ya ɗago sama.
\v 7 Elisha yace, "Ka ɗauko shi." Sai mutumin ya ɗauko shi.
\s5
\v 8 Sai sarkin Aram ya shirya kai hari kan Isra'ila. ya tuntuɓi barorinsa, cewa, "Sansanina ga yadda zai kasance da kuma inda zai kasance."
\v 9 Sai mutumin Allah ya aika wurin sarkin Isra'ila, cewa, "Ka yi hankali kada ka wuce ta wurin nan, domin Aremiyawa suna gangarawa can."
\s5
\v 10 Sai sarkin Isra'ila ya aika da saƙo can game da abin da mutumin Allah ya faɗa masa ya kuma gargaɗe shi. Ba sau ɗaya ko sau biyu ba duk lokacin da sarki zai wuce wurin yana cikin tsaro.
\v 11 Sarkin Aram ya da mugame da wannan gargaɗi, sai ya kira bayinsa ya ce da su, "Ba za ku faɗa mani wane ne daga cikinmu ya ke goyon bayan sarkin Isra'ila ba"
\s5
\v 12 Sai ɗaya daga cikin bayin ya ce, "Ba haka ba ne shugabana, sarki, domin Elisha annabi na Isra'ila ne ya faɗawa sarkin Isra'ila maganar da ka faɗa a ɗakin kwananka!"
\v 13 Sarki ya amsa, "ku je ku duba inda Elisha yake domin in aika da mutane su kamo shi." An faɗa masa, "Duba yana a Dotan."
\s5
\v 14 Domin haka sarki ya aika mahaya dawakai da karusai da sojoji masu yawa zuwa Dotan. Suka zo da dare suka kewaye birnin.
\v 15 Da baran mutumin Allah ya tashi da asuba ya fita waje, sai ga rundunonin sojoji da karusai da mahaya dawakai sun kewaye birnin. Baransa ya ce da shi, "Ya shugabana! Me za mu yi?"
\v 16 Elisha ya amsa, "Kada ka ji tsoro, domin waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su."
\s5
\v 17 Elisha ya addu'a ya ce, "Yahweh, ina roƙonka ka buɗe idanunsa domin ya gani." Sai Yahweh ya buɗe idanun baran, Sai ya ga tsaunin na cike da dawakai da karusai na wuta kewaye da Elisha!
\v 18 Lokacin da Aremiyawa suka zo gare shi, Elisha ya yi addu'a ga Yahweh ya ce, "Ka bugi mutanen nan da makanta, ina roƙonka." Sai Yahweh ya makantar da su, kamar yadda Elisha ya roƙa.
\v 19 Sai Elisha ya ce da Aremiyawa, "Ba wannan ba ce hanyar, ba kuma wannan ba ne birnin. Ku biyo ni zan kai ku wurin mutumin da ku ke nema." Sai ya kai su Samariya.
\s5
\v 20 Bayan sun zo Samariya, Elisha yace, "Yahweh, ka buɗe idanun mutanen nan domin su gani." Yahweh ya buɗe idanunsu, sai suka gan su a tsakiyar birnin Samariya.
\v 21 Da sarkin Isra'ila ya gan su ya ce da Elisha "'Babana, in kashe su ne? In kashe sun ne?"
\s5
\v 22 Elisha ya amsa, "Kada ka kashe su. Ko ka kashe bayin da ka kama da bãkanka da kuma takobinka? Ka ba su gurasa da ruwa domin su ci su sha, sai su tafi wurin shugabansu."
\v 23 Sai sarki ya shirya abinci sosai domin su, bayan su ci sun sha, sai ya sallame su, suka je wurin shugabansu. Waɗannan ƙungiyoyin sojojin Aremiyawan ba su daɗe ba sosai a Isra'ila.
\s5
\v 24 Bayan wannan Ben Hadad sarkin Aram ya tara dukkan sojojinsa ya kaiwa Samariya hari ya kwashe ta.
\v 25 Domin haka aka yi babbar yunwa a Samariya. Duba sun washe ta har ana sayar da kan jaki tsaba tamanin na shekel, ana kuma sayar da kofin kashin kurciya a shekel biyar.
\v 26 Da sarkin Isra'ila ya zo wucewa ta gefen katanga sai wata mata ta yi masa kuka, cewa, "Ka yi temako shugabana, sarki."
\s5
\v 27 Ya ce, "Idan Yahweh bai taimake ki ba, ta yaya zan taimake ki? Ana samun wani abu ne daga masussuka ko kuma daga wurin matsar ruwan inabi?"
\v 28 Sarki ya ci gaba, "Me ke damun ki?" Ta amsa, "Wanan matar ta ce da ni, 'Ki ba ni ɗanki domin mu dafa mu ci yau, gobe kuma sai mu ci ɗana."'
\v 29 Domin haka muka dafa ɗana mu ka cinye shi, da gari ya waye na ce da ita, "Ki bada ɗanki domin mu cinye shi, amma ta ɓoye ɗanta."
\s5
\v 30 To bayan sarki ya ji maganar wannan mata, sai ya keta tufafinsa (yana wucewa gefen katanga) sai mutane suka gan shi saye da tufafin makoki a jikinsa.
\v 31 Sai ya ce "Dama Allah ya yi mini haka, in har kan Elisha ɗan Shafat ya tsaya a kansa yau."
\s5
\v 32 Amma Elisha na zaune a gidansa, dattawa kuma na zaune tare da shi. Sai sarki ya aika manzo ya zo wurinsa, amma da manzon ya zo wurin Elisha, sai ya ce da dattawan, "Dubi yadda wannan ɗan mai kisan kai ya aika a sare mani kai? Duba lokacin da manzon ya zo, kulle ƙofa kulle ƙofar a hana masa shiga. Ashe ba ƙarar sawun mai gidansa na biye da shi ba?"
\v 33 Yana cikin yi masu magana sai ɗan saƙo ya zo wurinsa. "Sarki ya ce, "Duba wannan matsala daga wurin Yahweh ta zo. Donme kuma zan ƙara jiran Yahweh?"
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Elisha yace, ka ji maganar Yahweh, wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗa: gobe kamar i yanzu a ƙofar shiga Samariya za a sayar da kofin garin alkama a shekel ɗaya, awo biyu na sha'ir a shekel,'"
\v 2 Sai hafsan da aka aiko wurin Elisha ya ce da mutumin Allah, "Ko da ma ace Yahweh zai buɗe sakatun sama, wannan abin zai faru? "Elisha ya amsa, "Duba za ka ga abin na faruwa da idonka amma ba za ka ɗanɗana ko kaɗan daga cikinsa ba."
\s5
\v 3 To akwai mutun huɗu da ke da ciwon kuturta a wajen ƙofar birni. Sai suka cewa juna, "Domin me za mu yi ta zama a nan har mu mutu?
\v 4 In mun ce za mu cikin birni yunwar na can, za mu kuma mutu a can. Bari mu je sansanin Aremiyawa. In sun bar mu da rai mu rayu, in kuma zamu mutu mu mutu a can, amma ko da ma mun tsaya a nan zamu mutu. To yanzu sai mu je sansanin Aremiyawa. In sun bar mu da rai to, za mu rayau, in kuma sun kashe mu mutuwa kawai zamu yi."
\s5
\v 5 To sai suka tashi da almuru suka nufi sansanin Aremiyawa; da suka isa tsakiyar wurin ba kowa a sansanin ba ko mutun ɗaya a wurin.
\v 6 Domin Ubangiji yasa sojojin Aremiyawa su ji ƙarar karusai da ƙarar mahayan dawakai da kuma babbar ƙarar rundunar soja, suka ce da junansu. "Sarkin Isra'ila ya yi hayar sarakunan Hitiyawa da na Masar domin su kawo mana hari."
\s5
\v 7 Domin haka sojoji suka ruga da almuru; suka bar rumfunansu, da dawakansu, da jakunansu da sansanin kamar yadda yake suka gudu domin su tsirar da ransu.
\v 8 Lokacin da mutanen da ke da kuturta suka shiga tsakiyar sansanin suka shiga wata rumfa suka ci suka sha, suka kwashi shekel da zinariya da azurfa da da suturu suka tafi da su suka ɓoye su suka sake dawowa suka shiga wani sansanin suka kwashi ganima daga can suka tafi suka ɓoye ta.
\s5
\v 9 Daga nan suka ce da juna, "Ba mu yin abin da ke dai dai ba yau. wannan ranar ta kai soƙo mai daɗi ce, amma munyi shiru game da batun. In mun jira har gari ya waye za mu fuskaci horo. To yanzu, ku zo mu je mu faɗa wa dukkan gidan sarki."
\v 10 Sai suka tafi suka kira masu tsaron ƙofar birnin. Suka faɗa masu cewa, Mun je sansanin Aremiyawa, amma ba kowa a can, ba kuma motsin kowa, amma akwai dawakai a ɗaure, da jakai a ɗaure da kuma rumfunan kamar yadda suke."
\v 11 Daga nan sai masu tsaron ƙofofin suka baza labarin, daga nan sai aka faɗa a cikin dukkan gidan sarki.
\s5
\v 12 Sai sarki ya tashi da dare ya ce da bayinsa, "Yanzu zan faɗa maku abin da Aremiyawa suka yi mana. Sun sani muna jin yunwa, to sai suka bar sansanin suka je suka ɓuya a cikin sauruka. Suna cewa, "in sun fito wajen birnin, zamu kama su da rai, mu shiga cikin birnin."'
\v 13 Ɗaya daga cikin bayin sarki ya ce, "'Ina roƙonka ka bar waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka rage a birnin. Su kamar sauran yawan Isra'ila ne da suka ragu - domin da yawansu sun mutu; sai mu aike su mu gani."
\s5
\v 14 Sai suka kwashi karusan dawakai guda biyu, sai sarki ya aike su su bi Aremiyawa cewa, "Ku je ku gani."
\v 15 Sai suka tafi har zuwa Yodan, hanyar kuma ta cika da suturu birjik da kuma kayayyakin da Aremiyawa suka warwatsar cikin saurinsu. Sai manzannin suka dawo suka faɗawa sarki.
\s5
\v 16 Sai mutane suka fita suka kwashi ganimar sansanin Aremiyawa. Domin haka aka sayar da awon alkama a shekel ɗaya da kuma awon sha'ir biyu a shekel, kamar dai yadda maganar Yahweh ta faɗa.
\v 17 Sai sarki ya sa wannan hafsan da ya aika ya zama mai kula da ƙofar, sai mutane suka tattake shi a ƙofar. Ya mutu kamar yadda mutumin Allah ya faɗa, a lokacin da sarki ya zo wurinsa.
\s5
\v 18 Haka ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya faɗa wa sarki, cewa, war haka a ƙofar shiga Samariya, za, a sayar da awo biyu na sha'ir a shekel, awo ɗaya na alkama kuma a shekel."
\v 19 Wannan hafsan ya ce da mutumin Allah, "Duba ko da Yahweh zai sa sakatun sama su buɗe, ko wannan zai faru?" Elisha ya ce, "Duba za ka gani yana faruwa a idanunka, amma ba za ka ci daga cikinsa ba."
\v 20 Wannan shi ne hakikanin abin da ya faru da shi, domin mutane sun tattake shi a bakin ƙofa, ya kuma mutu.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 To sai Elisha ya yi magana da matar da ya komar da ɗanta da rai. Ya ce da ita, "Ki tashi, da dukkan gidanki, zauna a duk inda za ki zauna a wata ƙasa, domin Yahweh ya saukar da yunwa a wannan ƙasa har tsawo shekaru bakwai."
\v 2 Sai matar ta tashi ta yi biyayya da maganar mutumin Allah. Ta tafi da ita da mutanen gidanta zuwa ƙasar Filistiyawa har tsawon shekaru bakwai.
\s5
\v 3 To a ƙarshen shekaru bakwai da wannan mata ta komo daga ƙasar filistiyawa, ta je wurin sarki ta roƙe shi domin gidanta da kuma ƙasarta.
\v 4 To sarki na magana da Gehazi baran mutumin Allah, cewa "Ina roƙo ka faɗa mini dukkan manyan abubuwan da Elisha ya yi."
\s5
\v 5 A lokacin da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya komar da ran yaron da ya mutu, sai wannan dai matar ta zo ta roƙi sarki saboda gidanta da kuma ƙasarta. Gehazi yace, "Shugabana, sarki, ga matar da kuma ɗan nata, da Elisha ya mayar wa da rai."
\v 6 Lokacin da sarki ya tambayi matar game da ɗanta, ta yi masa bayani. Sai sarki ya sa wani hafsa dominta ya ce, "Ka ba ta duk abin da ke nata da kuma dukkan girbin gonarta tun daga ranar da ta bar ƙasar har ya zuwa yanzu."
\s5
\v 7 Sai Elisha ya zo Damaskus. Inda Ben Hadad sarkin Aram ke ciwo. Sai aka faɗa wa sarki cewa, "Mutumin Allah ya zo nan."
\v 8 Sai sarki yace da Hazayel, "Ɗauki kyauta a hannunka ka je wurin mutumin Allah, ka tuntuɓi Yahweh ta wurinsa, cewa 'Ko zan wartsake daga wannan rashin lafiyar?"'
\v 9 To sai Hazayel ya tafi wurinsa da kyauta ta kowanne abu mai kyau na Damaskus, ya ɗora wa raƙuma arba'in. Sai Hazayel ya zo ya tsaya a gaban Elisha ya ce "Ɗanka Ben Hadad sarkin Aram ne ya aiko ni gare ka, cewa 'ko zan warke daga wannan rashin lafiyar?"'
\s5
\v 10 Elisha ya ce da shi, "Ka je ka ce da Ben Hadad, 'Hakika za ka warke; amma Yahweh ya nuna mani cewa hakika zai mutu."
\v 11 Sai Elisha ya ƙarfafa Hazayel har sai da ya ji kunya, mutumin Allah kuma ya yi kuka.
\v 12 Hazayel ya tambaya, "Meyasa ka yi kuka, ya shugabana?" Ya amsa, "Saboda na san irin muguntar da zaka yi wa mutanen Isra'ila. Za ka ƙone hasumayoyinsu da wuta, za ka kuma kashe samarinsu da takobi, zaka kuma daddatsa 'yan ƙananansu, za ka kuma feɗe matayensu masu juna biyu."
\s5
\v 13 Hazayel ya masa, "Wane ne baranka, da zai yi wannan babban abu? Ai shi kare ne kawai. Elisha ya amsa, Yahweh ya nuna mani cewa za ka yi sarautar Aram.
\v 14 Daga nan Hazayel ya rabu da Elisha ya komo wurin mai gidansa, wanda ya ce da shi "Me Elisha ya faɗa maka?" ya amsa, ya faɗa mani hakika za ka warke."
\v 15 To washegari Hazayel ya ɗauki bargo ya tsoma shi a ruwa, ya shimfiɗa shi a kan fuskar Ben Hadad da haka ya mutu. Sai Hazayel ya zama sarki a maimakon sa.
\s5
\v 16 A shekara ta biyar ta sarautar Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, Yahoram ya fara sarauta. Shi ɗan Yehoshafat ne sarkin Yahuda. Ya fara sarauta a lokacin da Yehoshafat ke sarautar Yahuda.
\v 17 Yahoram yana da shekaru talatin da biyu a lokacin da ya fara sarauta, ya yi sarauta ta shekaru takwas a Yerusalem.
\s5
\v 18 Yahoram ya bi tafarkin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi; domin ya auri 'yar Ahab a matsayin matarsa, ya kuma yi abin da ke mugu a gaban Yahweh.
\v 19 Duk da haka, saboda baransa Dauda bai so ya hallaka Yahuda ba, tun da ya yi masa alƙawari cewa har kullum ba za a rasa wanda zai yi sarauta daga zuriyarsa ba.
\s5
\v 20 A kwanakin Yahoram, sai Idom ta tayar wa mulkin Yahuda, suka kuma naɗa wa kansu sarki. Sai
\v 21 Yahoram ya tsallake shi da hafsoshinsa da dukkan karusansa. Sai ya tashi da duhu ya kai hari ya washe Idomawa, waɗanda suka kewaye shi da kuma hafsoshin karusai. Sai sojojin Yaharom suka tsere gidajensu.
\s5
\v 22 To da haka Idom ta tayar wa mulkin Yahuda har ya zuwa yau. Libna ita ma ta tayar alokaci guda.
\v 23 To game da sauran abubuwa game da Yahoram, da duk abin da ya yi, ashe ba a rubuce suke a littafin ayyukan sarakunan Yahuda ba?
\v 24 Yahoram ya mutu ya huta tare da ubanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dauda. Daga nan ɗansa Ahaziya ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 25 A shekara ta sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, da Ahaziya ɗăn Yehoram, sarkin Yahuda, suka fara mulki.
\v 26 Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu lokacin da ya fara sarauta; ya yi sarautar shekara ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Ataliya; Ita 'yar Omri ce, sarkin Isra'ila.
\v 27 Ahaziya ya bi tafarkin gidan Ahab; ya yi abin da ke mugu a gaban Yahweh, kamar dai sauran abin da Ahab ya yi, domin Ahaziya suruki ne ga gidan Ahab.
\s5
\v 28 Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab, domin su yi yaƙi gãba da Hazayel, sarkin Aram, a Ramot Giliyad. Aremiyawa suka yi wa Yoram rauni.
\v 29 Sarki Yoram ya koma gida domin ya warke a Yazriyel daga raunin da aka yi masa a Rama, a lokacin da ya yi yaƙi da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yahoram sarkin Yahuda, ya tafi Yezriyel domin ya ga Yoram ɗan Ahab, saboda an yi wa Yoram rauni.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Sai annabi Elisha ya kira ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa ya ce da shi, "Ka shirya domin tafiya, ka riƙe wannan 'yar kwalbar man ka tafi Ramot Giliyad
\v 2 lokacin da ka je sai ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat ɗan Nimshi, sai ka shiga ciki ka sa shi ya tashi daga abokan taraiyarsa ka bi da shi can cikin lalloki rumfa
\v 3 Sai ka ɗauki kwalbar ka tsiyaya masa mai aka ce Yahweh ya faɗi wannan: "Na keɓe ka ka zama sarkin Isra'ila" daga nan sai ka buɗe ƙofa ka yi sauri ka gudu, kada ka yi jinkiri.
\s5
\v 4 Sai saurayin, wato matashin annabin, ya tafi Ramot Giliyad.
\v 5 Da ya isa sai ga hafsoshin sojoji na zaune. Sai matashin annabin ya ce, "Na zo wurin ɗaya daga cikinku, ne hafsoshi." Yehu ya amsa, Ga wa daga cikinmu?" Matashin annabin ya amsa "Gareka, hafsa"
\v 6 Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida, sai annabin ya zuba masa mai a kã yace da Yehu, "Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi wannan: 'Na keɓe ka ka zama sarki akan mutanen Yahweh, Isra'ila.
\s5
\v 7 Dole ne ka kashe iyalin Ahab shugabannka, domin in yi ramako akan bayina annabawa, da kuma jinin dukkan bayin Yahweh waɗanda Yezebel ta kashe.
\v 8 Domin dukkan iyalan Ahab za su lalace zan kuma datse dukkan 'ya'ya maza na zuriyar Ahab ko shi bawa ne ko kuma mai 'yanci.
\s5
\v 9 Zan mayar da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, kamar kuma gidan Ba'asha ɗan Ahija.
\v 10 Karnuka kuma za su ci naman Yezebel a Yezriyel kuma ba za 'a sami wanda zai bizne ta ba.'" Daga nan sai annabin ya buɗe ƙofar, ya gudu.
\s5
\v 11 Sai Yehu ya fito waje zuwa wurin bayin shugabansa, sai ɗaya daga cikinsu ya ce da shi, "Ko dai lafiya? Meyasa wannan mahaukacin ya zo wurinka?" Yehu ya amsa musu, "Kun san irin mutumin da irin abin da ya ke faɗi."
\v 12 Suka ce, "Wannan ƙarya ne. Ka faɗa." Yehu ya amsa, "Ya faɗa mani abu kaza da kaza, hakan nan ya ce 'Ga abin da Yahweh yace: Na kebe ka ka zama sarkin Isra'ila."'
\v 13 Sai dukkan su suka yi sauri suka tuɓe rigarsa ta waje suka sa ta ƙarƙashin Yehu akan matakan. Suka hura kakaki suka ce, "Yehu sarki ne."
\s5
\v 14 Ta haka Yehu ɗan Yehoshafat ɗan Nimshi suka ƙulla maƙarƙashiya kan Yoram. A lokacin, Yoram yana kare Ramot Giliyad, shi da dukkan Isra'ila, saboda Hazayel sarkin Aram,
\v 15 amma sarki Yoram ya koma Yezriyel domin ya warke daga raunin da Aremiyawa suka yi masa, lokacin da suka yi faɗa da Hazayel sarkin Aram. Yehu yace da bawan Yoram, "In wannan shi ne ra'ayinka, to kada kowa ya tsira ya fita daga birnin, saboda aje a faɗi labarin a Yezriyel."
\v 16 Sai Yehu ya tuƙa karusa zuwa Yezriyel; Yoram yana shaƙatawa a can. Sai Ahaziya sarkin Yahuda ya zo domin ya ga Yoram.
\s5
\v 17 Ɗan tsaro na tsaye akan hasumaya a Yezriyel, sai ya ga rundunar Yehu da ya matso kusa; sai yace, "Na ga kungiyar mazaje na zuwa." Yoram yace, "Ka kwashi mahayin dawakai, ka aike shi wurinsu; ka ce da shi ya tambaye su 'Kuna zuwa da salama ne?"'
\v 18 Sai ya aika mutumin akan doki ya koma ya tare shi; sai ya ce, sarki ne ya faɗi wannan: 'Kuna zuwa da salama ne?"' Sai Yehu yace, "Me zaku yi da salama? Ka juya ka biyo ni."Sai ɗan tsaron ya faɗa wa sarki, "Ɗan saƙon ya same shi, amma ba zai dawo ba."
\s5
\v 19 Sai ya sake aikar mutum na biyu ya sake komawa akan doki, wanda ya zo wurinsu ya ce, "Sarki ya faɗi wannan: 'Kuna zuwa da salama ne?'" Yehu ya amsa "Me za ku yi da salama? ka juyo ka biyo ni."
\v 20 Sai wannan manzon ya sake mayar da amsa, "Ya same su, amma ba zai dawo ba. Domin hanyar da ya ke tuƙa dawakan ita ce Yehu ɗan Nimshi ya bi; kuma yana tuki a sukwane."
\s5
\v 21 Sai Yoram yace, "Ka shirya karusata." Suka shiya karusarsa, sai Yoram sarkin Isra'ila da Ahaziya sarkin Yahuda suka fita akan dawakai, kowa da karusarsa domin su gamu da Yehu. Suka same shi a mallakar Nabot Bayezriyile.
\v 22 Da Yoram ya ga Yehu, sai ya ce, "Yehu kana zuwa da salama ne?" Ya amsa, "Wacce salama kuma ke a can bayan akin zina da maitanci na mahaifiyarka Yezebel sun yi yawa?"
\s5
\v 23 Sai Yoram ya juya karusarsa ya tsere ya ce da Ahaziya, "Akwai tashin hankali Ahaziya."
\v 24 Daga nan Yehu ya ɗauko bakãnsa da cikkakken ƙarfinsa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa; kibiyar ta bi ta zuciyarsa, sai ya faɗi a cikin karusarsa.
\s5
\v 25 Sai Yehu yace da Bidkar hafsansa, "Ciro shi ka jefar da shi a filin Nabot Bayezriyile. Tuna da yadda muka bi babansa Ahab, Yahweh ya ajeye hukuncinsa a kansa:
\v 26 'Jiya na ga jinin Nabot da kuma jinin 'ya'yansa - inji Yahweh - kuma hakika zan sa ka biya shi a wannan fili - inji Yahweh. Yanzu, sai ka ciro shi ka jefar da shi a filin, bisa ga maganar Yahweh."
\s5
\v 27 Da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga wannan, sai ya gudu daga hanya zuwa Bet Haggan. Amma Yehu ya bi shi, ya ce "Shi maku kashe shi a cikin karusarsa," sai suka harbe shi kusa da Gur, wadda ke wajen Ibliyam. Ahaziya ya gudu zuwa Megiddo ya mutu a can.
\v 28 Bayin suka ɗauke gawarsa a cikin karusa zuwa Yerusalem suka bizne shi a maƙabarta tare da ubanninsa a birnin Dauda.
\s5
\v 29 A shekara ta sha ɗaya ne ta Yoram ɗan Ahab Ahaziya ya fara mulkin Yahuda,
\s5
\v 30 Da Yehu ya zo Yezriyel, Yezebel ta ji labari, sai ta yi kwalliya ta yi wa idonta zane ta gyara gashinta, ta duba ta taga.
\v 31 A lokacin da Yehu ke shiga ƙofar ta ce da shi, "Kana zuwa da salama ne, kai Zimri, an kashe shugabanka ne?"
\v 32 Yehu ya dubi tagar ya cewa, "Ke tare da ni? Ke?" Sai bãbãni biyu ko uku suka duba waje.
\s5
\v 33 Sai Yehu yace, "Ku wurgo ta ƙasa." Sai su ka wurgo Yezebel ƙasa, har jininta ya fallatsa a bango da kuma jikin dawakai, Yehu kuma ya tattake ta da ƙafafu.
\v 34 Da Yehu ya shiga fãdar sai ya ci ya sha. Ya ce, "Duba yanzu ku ɗauki wannan la'anarniyar matar ku bizne ta, domin ita 'yar sarki ce."
\s5
\v 35 Sai suka tafi domin su bizne ta, amma ba su tarar da komai nata ba sai ƙoƙon kanta da ƙafa da tafin hannuwa.
\v 36 Sai suka dawo suka faɗa wa Yehu. Ya ce, "Wannan maganar Yahweh ce wadda annabi Iliya Batishbe, ya faɗa, cewa 'A filin Yezriyel karnuka za su cinye gangar jikin Yezebel,
\v 37 gangar jikin Yezebel kuma za ta zama kamar ɗan kututture a cikin filaye a ƙasar Yezriyel, domin kada wani ya iya cewa, "Wannan ce Yezebel.'"'
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Ahab yana da zuriya saba'in a Samariya. Yehu ya rubuta wasiƙu ya aika da su Samariya, ga shugabannin Yezriyel, haɗe da dattawa da 'yan tsaro na zuriyar Ahab, cewa,
\v 2 "Zuriyar shugabanku na tare da ku, kuma kuna da karusai da dawakai da ƙayatattun birane da makamai.
\v 3 Domin haka da zarar wannan wasiƙa ta same ku, sai ku zaɓi wanda yafi cancanta daga cikin zuriyar shugabanku ku ɗora shi akan gadon sarautar mahaifinsa, ku kuma yi yaƙi domin gidan sarautar shugabanku."
\s5
\v 4 Amma suka tsorata suka ce da junansu, "Duba sarukuna biyu ma ba su iya ja da Yehu ba. To yaya zamu iya ja da shi?"
\v 5 Daga nan sai wanda ke shugabantar fãdar, da mai kula da birnin da kuma dattawan da kuma masu renon yara, suka sake mayar da magana ga Yehu, cewa, "Mu bayinka ne. Za mu yi duk abin da ka umarce mu. Baza mu naɗa kowa a matsayin sarki ba. Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau a idanunka."
\s5
\v 6 Sai Yehu ya rubuta wasiƙa ta biyu zuwa gare su, cewa, "In kuna tare da ni, in kuma za ku ji muryata, dole ne ku ɗauko wanda yake shi ne shugaban zuriyarku ku zo da shi Yezriyel gobe war haka." To sai zuriyar sarkin, su saba'in, suka zama manyan mutane masu daraja a birnin waɗanda suke kula da su
\v 7 To da wasiƙa ta zo gare su, sai suka kama 'ya'yan sarki suka karkashe su, mutane saba'in, suka ɗauki kawunansu suka aikawa da Yehu a Yezriyel.
\s5
\v 8 Sai manzo ya zo wurin Yehu, ya ce, "Sun kawo kawunan 'ya'yan sarki maza." Sai ya ce ku ajiye su a mazubin a ƙofar shiga har sai gari ya waye."
\v 9 Da safe sai Yehu ya fito ya tsaya ya ce da dukkan mutane, "Ba ku da laifi. Na shirya makirci kan shugabana na kuma kashe shi, amma wane ne ya kashe dukkan waɗannan?
\s5
\v 10 To yanzu sai ku san cewa ba wani sashe na maganar Yahweh, da aka faɗa game da gidan Ahab, da zai faɗi ƙasa, domin Yahweh ya yi abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya."
\v 11 Sai Yehu ya karkashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezriyel, ya kuma kashe mutanensa masu muhimmanci, da abokansa na ƙut da ƙut, da firistocinsa, har ta kai ga ba wanda ya ragu.
\s5
\v 12 Sai Yehu ya tashi ya tafi; ya tafi zuwa Samariya. Da ya je Bet Eked ta makiyaya,
\v 13 sai ya tarar da 'yan'uwan Ahaziya sarkin Yahuda. Yehu yace da su "Ku su wane ne?" Suka ce, "Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, kuma zamu mu gai da 'ya'yan sarki ne da kuma 'ya'yan Sarauniya Yezebel."
\v 14 Yehu ya ce da mutanensa, "Ku kama su da ransu." Sai suka kama su da ransu suka karkashe su a ramin Bet Eked, dukkan mutanen arba'in da biyu ne. Bai bar ko ɗaya daga cikinsu da rai ba.
\s5
\v 15 Da Yehu ya bar wurin, sai ya tarar da Yonadab ɗan Rekab yana zuwa domin ya same shi. Yehu ya gaishe shi ya ce da shi, "Ko zuciyarka na tare da ni, kamar yadda zuciyata ke tare da taka?" Yonadab ya amsa, "Tana nan." Yehu ya amsa, "In tana nan, ka ba ni hannunka." Sai Yonadab ya ba shi hannunsa, sai Yehu ya ɗauke shi a cikin karusarsa.
\v 16 Yehu ya ce, "Ka zo tare da ni ka ga himmata domin Yahweh." Sai ya tafi da Yonadab yana tuƙi tare da shi a karusarsa.
\v 17 Da ya zo Samariya, sai Yehu ya karkashe duk waɗanda suka ragu daga zuriyar Ahab a Samariya, har sai da ya kashe duk wani mai jinin sarauta na iyalin Ahab, kamar dai yadda maganar Yahweh ta faɗa ta wurin Iliya.
\s5
\v 18 Sai Yehu ya tattara dukkan mutane wuri ɗaya ya ce da su, "Ahab ya bauta wa Ba'al ɗan kaɗan, amma Yehu ya fi bauta masa ya yawa.
\v 19 To yanzu sai ku kirawo mani dukkan annabawan Ba'al, da duk masu bautarsa, da duk firistocinsa. Kar ku rage ko da guda ɗaya, domin ina da babbar hadaya da zan miƙa ga Ba'al. Duk wanda bai zo ba za, a kashe shi." Amma Yehu ya yi wannan yaudarar ne domin ya kashe duk masu bauta wa Ba'al.
\v 20 Yehu yace, "Ku shirya lokaci da za mu yi taruwa domin Ba'al." Domin haka suka yi sanarwar ta.
\s5
\v 21 Sai Yehu ya aika a ko'ina cikin dukkan Isra'ila sai duk masu bautar Ba'al suka zo, har ba waninsu da bai zo ba. Suka zo masujadar Ba'al, ta kuma cika maƙil.
\v 22 Yehu yace da mutane masu, kula da ma'ajiyar kayan firistoci, "Ku fito da tufafi domin duk masu bautar Ba'al." Sai mutumin ya fito da tufafi dominsu.
\s5
\v 23 Sai Yehu ya tafi tare da Yonadab ɗan Rekab zuwa gidan Ba'al, ya ce da masu bautar Ba'al, "Ku bincika ku tabbatar cewa ba wani daga cikin masu bautar Yahweh a cikinku, amma sai dai masu bautar Ba'al kaɗăi."
\v 24 Sai suka shiga domin su miƙa hadayu da baiko na ƙonawa. Sa'an nan Yehu ya zaɓi mutane tamanin da ke tsaye a waje, ya ce da su, "In wani ya bar mutanen nan da na kawo ya kuɓuta to a bakin ransa, zan kashe wanda ya yi sakaci har wani ya gudu a madadin wancan da ya gudu."
\s5
\v 25 To nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya da baiko na ƙona wa, ya ce da 'yan tsaro da hafsoshi, "Ku shiga ku kashe su. Kar ku bar wani ya fito waje." Domin haka suka karkashe su da kaifin takobi, da 'yan tsaro da hafsoshin suka jejjefar da su waje suka shiga can ƙuryar ɗakin gidan Ba'al.
\v 26 Suka mummurgina duwatsun ginshiƙan gidan Ba'al suka ƙone su.
\v 27 Suka kuma kakkarya ginshiƙan Ba'al, suka hallakar da gidan Ba'al suka mayar da shi makewayi wanda har yanzu haka wurin ya ke.
\v 28 Da haka Yehu ya hallakar da bautar Ba'al daga Isra'ila.
\s5
\v 29 Amma Yehu bai ƙyale zunubin Yerobowom ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi - wato bautar ɗan maraƙin zinariya a Betal da Dan.
\v 30 Domin haka Yahweh yace da Yehu, "Saboda ka yi abin da ke dai dai a idona, ka kuma iy wa gidan Ahab gwargwadon abin da ke a zuciyata, zuriyarka zasu yi mulkin Isra'ila har ya zuwa tsara ta huɗju."
\v 31 Amma Yehu bai da muya yi tafiya bisa tafarkin Yahweh, Allah na Isra'ila, da dukkan zuciyarsa ba. Bai kuma bar zunubinYarobowam ba, ta haka ya sa Isra'ila yin zunubi.
\s5
\v 32 A waɗancan kwanakin Yahweh ya fara yanke sassa daga Isra'ila, sai Hazayel ya ci Isra'ila akan iyakokin Isra'ila,
\v 33 daga gabashin Yodan, dukkan ƙasar Giliyad da ta Gadiyawa da ta Rubenawa da ta Manassawa, daga Arowa wadda ke a Kwarin Arno har ya zuwa Giliyad da kuma zuwa Bashan.
\s5
\v 34 Game kuma da sauran abubuwa game da Yehu, da kuma duk abin da ya yi da dukkan ikonsa, ashe ba a rubuta su a cikin ayukan sarakunan Isra'ila ba?
\v 35 Yehu ya yi barci tare da ubanninsa, suka kuma bizne shi a Samariya. Sai Yehoahaz ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\v 36 Tsawon lokacin da Yehu ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shi ne shekaru ashirin da takwas.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 To da Ataliya, mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta kashe duk 'ya'yan gidan sarauta.
\v 2 Amma Yehosheba, 'yar sarki Yahoram da 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yo'ash ɗan Ahaziya ta ɓoye shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, tare da mai renonsa; ta sa su a ɗakin kwana. Suka ɓoye shi domin kada Ataliya ta gan shi ta kashe shi.
\v 3 Yana tare da Yahosheba a ɓoye a gidan Yahweh har tsawon shekaru shida, a lokacin da Ataliya ke sarautar ƙasar.
\s5
\v 4 A shekara ta bakwai, Yeho'iada ya aika da saƙonnin ya kuma fito da kwamandojin na ɗari-ɗari na Karitawa wato wata ƙungiyar mayaƙa ta gidan sarauta da 'yan tsaro ya kawo su wurinsa, cikin haikalin Yahweh. Ya yi yarjejeniya da su, ya kuma sa su su rantse a gidan Yahweh. Daga nan sai ya nuna musu ɗan sarki.
\v 5 Ya umarce su, da cewa, "Wannan shi ne abin da tilas za ku yi. Kashi uku daga cikinku waɗanda ke zuwa da ranar Asabaci za su yi tsaron gidan sarki,
\v 6 kashi uku su tsaya a Ƙofaf Sur, kuma kashe uku su tsaya a ƙofar bayan gidan 'yan tsaro."
\s5
\v 7 Sauran ƙungiyoyin guda biyu da ba ku yin hidima da ranar asabar, dole ne ku yi tsaron gidan Yahweh domin sarki.
\v 8 Dole ne ku kewaye sarki kowanne mutum da makaminsa a hannunsa, duk wanda ya shigo wurinku sai ku kashe shi. za ku kasance tare da sarki a lokacin da ya fita da lokacin da ya dawo ciki.
\s5
\v 9 Sai kwamandojin ɗari-ɗari suka yi biyayya da duk abin da Yeho'iada ya firist ya ba da umarni. Kowannen su ya ya kwashi mutanensa, waɗanda ke zuwa hidima da Asabaci, da waɗanda ke zuwa daina hidima da Asabaci; suka zo wurin Yeho'iada firist.
\v 10 Sai Yeho'iada firist ya ya ba kwamandojin ɗari-ɗari mãsu da garkuwoyi na sarki Dauda da kuma waɗanda ke gidan Yahweh.
\s5
\v 11 Saboda haka 'yan tsaron suka tsaya, kowanne da makaminsa a hannunsa, daga gefen dama na haikalin zuwa gefen hagun na haikalin, kusa da bagadi da kuma haikalin, suna kewaye da sarki.
\v 12 Sai Yeho'iada ya kawo ɗan sarki Yo'ash, ya sa masa kambi a kansa, ya kuma ba shi sharruɗan yarjejeniya. Sai suka naɗa shi sarki suka kuma shafe shi da mai. Suka tafa hannuwansu suka ce, "Ran sarki ya daɗe!"
\s5
\v 13 Da Ataliya ta ji hayaniya ta 'yan tsaro da ta mutane, sai ta zo wurin mutane a gidan Yahweh.
\v 14 Tana dubawa sai ga sarki a tsaye a jikin ginshiƙin, kamar yadda al'adar ta ke, da hafsoshi da masu hura ƙahonni na tare da sarki. Dukkan mutanen ƙasar na murna suna hura ƙahonni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta yi ihu tana cewa, "Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!"
\s5
\v 15 Sai Yeho'iada firist ya bada umarni ga kwamandoji na ɗari ɗari masu shugabantar sojojin cewa, "Ku kawo ta a tsakanin rundunarku. Kuma duk wanda ya biyo ta, ku kashe shi da takobi. Domin firist ya ce, "Kada ku kashe ta a gidan Yahweh."
\v 16 Domin haka suka ja ta da ta kai dai dai inda dawakai ke shiga wurin 'yan tsaron fãda a can aka kashe ta.
\s5
\v 17 Sai Yeho'iada firist ya yi yarjejeniya da tsakanin Yahweh da sarki da kuma mutane, cewa za su zama mutanen Yahweh, hakannan kuma tsakanin mutane da sarki.
\v 18 Domin haka dukkan mutanen ƙasar suka tafi gidan Ba'al suka rurrushe shi. Suka bubbuge bagadin Ba'al da gumakansa rugu rugu, suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagadojin. Sai Yeho'iada firist ya naɗa 'yan tsaro a haikalin Yahweh.
\s5
\v 19 Sai Yeho'iada ya kwashi kwamandojin ɗari ɗari da Karitiyawa, mayaƙan fãda, da 'yan tsaro, da dukkan mutanen ƙasar tare suka ka kawo sarki daga gidan Yahweh suka tafi gidan sarki ta hanyar ƙofar 'yan tsaro. Sai Yo'ash ya hau gadon sarauta.
\v 20 Domin haka duk mutanen ƙasar suka yi murna, sai birnin ya sami kwanciyar hankali bayan an kashe Ataliya da takobi a gidan sarki.
\s5
\v 21 Yo'ash yana da shekaru bakwai a lokacin da ya fara sarauta.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 A shekara ta bakwai ta Yehu, sarautar Yo'ash ta fara; ya yi sarauta tsawon shekaru arba'in a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ta Biyasheba.
\v 2 Yoash ya yi abin da ke nagari a gaban Yahweh a dukkan lokaci, saboda Yeho'iada firist yana yi masa gargaɗi.
\v 3 Amma ba a kawar da manya manya wurare ba. Har yanzu mutane na yin hadaya da ƙona turare a manyan wurare.
\s5
\v 4 Sai Yo'ash yace da firistoci, "Dukkan ƙuɗaɗen da aka kawo a keɓaɓɓen wuri a cikin gidan Yahweh, wannan kuɗin da kuɗaɗen da aka tsara wa mutane - ko kuɗin da aka karɓa a wurin ƙidaya ne, ko kuma kuɗin da aka karɓa saboda wa'adi ne, ko kuma kuɗin da aka tara ta wurin yadda Yahweh ya zuga mutanensa -
\v 5 sai firistoci su karbi kuɗin daga ɗaya daga cikin ma'ajiyarsu su gyara duk wata ɓarna da suka gani a cikin haikali."
\s5
\v 6 Amma a shekara ta ashirin ta sarautar sarkin Yo'ash, firistoci ba su gyara komai ba a cikin haikalin.
\v 7 Sai sarki Yo'ash ya kira Yeho'iada firist da kuma sauran firistoci, ya ce da su, "Meyasa baku gyara komai a cikin haikalin ba? To yanzu kada ku ƙara ɗaukan kuɗi daga masu biyan harajinku, amma ku ɗauki wanda aka karɓa ku ba waɗanda za su yi gyaran haikalin."
\v 8 Sai firistoci suka yarda cewa ba za su ƙara karɓar kuɗi daga wurin mutane domin gyaran haikali da kansu ba.
\s5
\v 9 A maimakon, Yeho'iada firist ya ɗauki mazubi ya yi masa huduwa a ƙasa, ya ajiye shi kusa da bagadin, daga gefen dama dai-dai inda mutane ke shiga gidan Yahweh. Sai firistoci da ke kula da ƙofar shiga haikalin suka zuba dukkan kuɗin da aka kawo gidan Yahweh.
\v 10 Da zarar sun ga akwai kuɗi da yawa a cikin mazubin, sai marubuta na sarki da manyan firistoci su zo su zuba kuɗin a jakkuna sai su ƙirga kuɗin da aka samu a haikalin Yahweh.
\s5
\v 11 Suka ba da kuɗin da aka tattaro daga hannun mutane masu kula da haikalin Yahweh. Suka biya masu aikin katako da magina waɗanda suka yi aiki a haikalin Yahweh,
\v 12 haka kuma masu sayo katakai da yankawa, da masu sassaƙa duwatsu, domin gyaran haikalin Yahweh, da kuma duk abin da ake bukatar a biya shi.
\s5
\v 13 Amma kuɗin da aka kawo cikin haikalin Yahweh ba a biya domin aikin yin kofin zinariya da fitilu da kwangiri da kakaki, ko kuma duk wani aiki na azurfa ba.
\v 14 Sun bada kuɗin ga waɗanda suka yi aikin gyaran gidan Yahweh.
\s5
\v 15 Haka kuma, basu bukaci kuɗi domin su biya masu biyan ma'aikata ba, domin waɗannan mutanen suna da aminci.
\v 16 Amma kuɗin baiko na hadayar laifi da kuma na hadayar zunubi ba a kawo su zuwa cikin haikalin Yahweh ba, domin na firistoci ne.
\s5
\v 17 Sai Hazayel sarkin Aram ya kai hari kan Gat ya kuma kame ta. Sai ya Hazayel ya juyo domin ya kawo hari Yerusalem.
\v 18 Sai Yo'ash sarkin Yahuda ya ɗauke duk abubuwan da Yehoshafat da Yehoram da Ahaziya mahaifinsa da sarkunan Yahuda suka keɓe, da dukkan zinariya da aka samu a ɗakin ajiya na gidajen Yahweh da na gidan sarki ya aika da su wurin Hazayel sarkin Aram Sai Hazayel ya fita daga Yerusalem.
\s5
\v 19 Game kuma da sauran abubuwa game da sarki Yo'ash da duk abin da ya yi, ashe ba a rubuta su a cikin littafin ayukan sarakunan Yahuda ba?
\v 20 Sai barorinsa suka tashi suka haɗa kai suka shirya maƙarƙashiya; suka kai hari ga Yo'ash a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla.
\v 21 Jozabad ɗan Shimeyet da Yehozabad ɗan Shomar, bayinsa suka kai masa hari, ya kuma mutu. Suka bizne Yo'ash tare da kakanninsa a birnin Dauda, Amaziya, ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 A shekara ta ashirin da uku na Yo'ash ɗan Ahaziya sarkin Yahuda, Yehoahaz ɗan Yehu ya fara mulki akan Isra'ila da Samariya; ya yi mulkin har tsawon shekaru goma. sha bakwai.
\v 2 Ya kuwa yi abin mugunta a fuskar Yahweh da bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi; kuma Yehoahaz bai juya baya daga hakan ba.
\s5
\v 3 Fushin Yahweh ya yi ƙuna gãba da Isra'ila, sai ya ci gaba da bada su ga hannun Hazayel sarkin Aram da kuma ga hannun Ben Hadad ɗan Hazayel.
\v 4 Saboda haka Yehoahaz ya yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya saurare shi domin ya ga danniyar da ake yi wa Isra'ila, yadda sarkin Aram ya ke zaluntarsu.
\v 5 Don haka sai Yahweh ya ba Isra'ila maceci, sai suka kuɓuta daga ƙasar Aramiyawan, sai mutanen Isra'ila suka fara zama a gidajensu kamar yadda suke a dã.
\s5
\v 6 Duk da haka, ba su kauce daga zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila suka yi zunubi, kuma suka ci gaba a cikin su; kuma gunkiyar Asherah tana nan a Samariya.
\v 7 Aramiyawan suka bar Yehoahaz da mahayan dawakai hamsin ne kawai da karusai goma da dakarai dubu goma, gama sarkin Aram ya halakar da su kamar ƙaiƙai a lokacin casa.
\s5
\v 8 Akan sauran zantuttukan game da Yehoahaz kuwa, da dukkan abin da ya yi da ikonsa, ba an rubuta su littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 9 Sai Yehoahaz ya kwanta tare da kakaninsa, aka kuwa bizine shi a Samariya. Yohoash ɗansa ya zama sarkin da ya gaje shi.
\s5
\v 10 A shekara ta talatin da bakwai na Yo'ash sarkin Yahuda, mulkin Yohoash ɗan Yahoahaz ya fara kan Isra'ila a Samariya; ya yi mulki shekara goma sha shida.
\v 11 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai bar ko wani abu daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, ta yadda ya sa Isra'ila ta yi zunubi, amma ya yi tafiya cikinsu.
\s5
\v 12 A batun sauran zantuttukan da suka shafi Yohoash, da dukkan abin da ya yi, da ikonsa ta yadda ya yaƙi Amaziya sarkin Yahuda, ba an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 13 Yohoash ya kwanta tare da kakaninsa, sai Yerobowam ya zauna a kursiyinsa. An bizne Yohoash a Samariya tare da sarakunan Isra'ila.
\s5
\v 14 Sai Elisha ya yi rashin lafiya da ciwon da yasa ya mutu daga baya, don haka sai Yohoash sarkin Isra'ila ya zo gare shi ya yi kuka a kansa. Ya ce, "Babana, babana, karusan Isra'ila da mahayan dawakanta suna ɗaukan ka!"
\v 15 Elisha yace masa, "Ɗauki baka da kibbau," sai Yo'ash ya ɗauki baka da wassu kibbau.
\v 16 Elisha ya cewa sarkin Isra'ila, "Ka sa hannuwanka a bakan," sai ya sa hannuwansa a nan. Sai Elisha ya dafa hannuwansa a hannuwan sarkin.
\s5
\v 17 Elisha yace, "Buɗe tagar da ke wajen gabas," sai ya buɗe ta. Sa'annan Elisha yace, "Harba!", sai ya harba. Elisha yace, "Wannan kibiyar nasarar Yahweh ce, kibiyar nasara akan Aram, gama za ka kai wa Aramiyawan hari a Afek har sai ka yi kaca kaca da su."
\v 18 Sai Elisha yace, "Ɗauki kibau," sai Yo'ash ya ɗauke su. Ya cewa sarkin Isra'ila, "Ka caki ƙasa da su," sai ya caki ƙasa sau uku, sa'annan ya tsaya.
\v 19 Amma mutumin Allah ya yi fushi da shi ya ce, "Da ka bugi ƙasa sau biyar ko shida. Sa'annan da ka kai wa Aram hari har sai ka hallakar da ita, amma yanzu za ka kai wa Aram hari sau uku ne kawai."
\s5
\v 20 Sai Elisha ya mutu, kuma aka bizne shi. Sai gungun Mowabawa suka mamaye ƙasar a farkon shekara.
\v 21 Sa'ad da suke bizne wani mutun, suka ga gungũn Mowabawa, sai suka jefar da gangar jikin cikin kabarin Elisha. Da zarar mutumin ya taɓi ƙasussuwan Elisha, sai ya farfaɗo ya miƙe tsaye da kafafunsa.
\s5
\v 22 Hazayel sarkin Aram ya muzguna wa Isra'ila dukkan kwanakin Yehoahaz.
\v 23 Amma Yahweh ya yi alheri ga Isra'ila, ya kuma ji tausayin su ya kuma kula da su, saboda alƙawarinsa ga Ibrahim, Ishaku da Yakubu. Don haka Yahweh bai hallakar da su ba, haka kuma bai kore su daga gare shi ba.
\s5
\v 24 Hazayel sarkin Aram ya mutu, sai Ben Hadad ɗansa ya gaji sarautarsa.
\v 25 Yehoash ɗan Yehoahaz ya karɓi biranen daga Ben Hadah ɗan Hazayel wanɗanda Yehoahaz mahaifinsa ya ƙwato ta yaki. Yehoash ya kai masa hari sau uku, kuma ya karɓe biranen Isra'ila.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 A shekara ta biyu ta Yehoash ɗan Yehoahaz, sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yo'ash, sarkin Yahuda, ya fara mulki.
\v 2 Yana shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara sarauta; ya yi mulki na tsawon shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yehoaddan, ta Yerusalem.
\v 3 Ya yi abin da ke da kyau a fuskar Yahweh, duk da haka ba kamar Dauda mahaifinsa ba. Ya yi dukkan abin da Yo'ash, mahaifinsa, ya yi.
\s5
\v 4 Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane dai suka yi ta miƙa hadaya da ƙona turare a tuddan tsafi.
\v 5 Sai ya zamana sa'ad da mulkinsa ya kafu sosai, sai ya kashe barorin da suka kashe mahaifinsa sarki.
\s5
\v 6 Duk da haka bai kashe 'ya'yan masu kisan ba; maimakon haka, ya yi aiki bisa ga abin da ke rubuce a shari'a, a cikin Littafin Musa, kamar yadda Yahweh ya umurta, cewa, "Ubanni bai wajaba a kashe su saboda "ya'yansu ba, ko kuma a kashe 'ya'yan saboda iyayensu ba. Maimakon haka, duk mutumin da ya yi laifi lallai ne a kashe shi domin nasa zunuban."
\v 7 Ya kashe sojoji dubu goma na Idom a Kwarin Gishiri; ya kuma cafko Sela a yaƙi ya kira ta Yoktil, kuma haka ake kiranta har wa yau.
\s5
\v 8 Sa'an nan Amaziya ya aiko da manzanni ga Yehoash ɗan Yehoahaz ɗan Yehu sarkin Isra'ila, cewa, "Ka zo, mu sadu da juna ido da ido a yaƙi."
\v 9 Amma Yehoash sarkin Isra'ila ya aike manzani su mayar da Amaziya sarkin Yahuda, cewa, "'Yar ƙaya da ke Lebanan ta aiko da saƙo ga itacen al'ul a Lebanan, cewa, 'Ki ba da ɗiyarki ga ɗa na don aure,' amma naman jeji a Lebanan ya wuce ta wurin ya tattaka ƙayar.
\v 10 Hakika ka kai wa Idom hari, kuma zuciyarka ta ɗaga ka sama. Ka yi fahariya da nasararka, amma ka zauna a gida, gama donme zaka sawa kanka matsala ka faɗi, da kai da Yahuda tare da kai?"
\s5
\v 11 Amma Amaziya bai saurara ba. Saboda haka Yehoash sarkin Isra'ila ya kai hari kuma shi da Amaziya sarkin Yahuda sun sadu da juna ido da ido a Beth Shemesh, wadda ke ta Yahuda.
\v 12 Isra'ila ta kãda Yahuda, kuma kowanne mutun ya gudu gida
\s5
\v 13 Yehoash sarkin Isra'ila, ya kamo Amaziya, sarkin Yahuda ɗan Yehoash ɗan Ahaziya, a Beth Shemesh. Ya zo Yerusalem ya rushe bangon Yerusalem daga Ƙofar Ifraim zuwa Ƙofar Kwana, mai nisan mita ɗari da tamanin.
\v 14 Ya ɗauke dukkan zinariya da azurfa da dukkan abubuwan da aka samu a gidan Yahweh, da abubuwa masu daraja na fãdar sarki, tare da mutanen da aka ba da su jingina, sai ya koma Samariya.
\s5
\v 15 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yehoash kuwa, dukkan abin da ya yi da ikonsa da yadda ya yi yaƙi da Amaziya sarkin Yahuda, ba an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 16 Sa'an nan Yehoash ya yi barci tare da kakaninsa kuma aka bizne shi a Samariya tare da sarakunan Isra'ila, kuma Yerobowam, ɗansa, ya zama sarki a madadin sa.
\s5
\v 17 Amaziya ɗan Yo'ash, sarkin Yahuda, ya yi shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehoash ɗan Yehoahaz, sarkin Isra'ila.
\v 18 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Amaziya, ba an rubota su a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 19 Suka yi maƙarƙashiya gãba da Amaziya a Yerusalem, sai ya gudu zuwa Lakish. Ya gudu zuwa ga Lakishna, amma an aiko da maza su bishi har Lakish su kashe shi a wurin.
\s5
\v 20 Suka dawo da shi akan dawakai, sai aka bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda.
\v 21 Dukkan mutanen Yahuda suka ɗauki Azariya, wanda ke shekara goma sha shida, suka maida shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya.
\v 22 Azariya ne wanda ya gina Elat ya maida ita ta Yahuda, bayan Sarki Amaziya ya kwanta da kakaninsa.
\s5
\v 23 A shekara ta goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yo'ash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehoash sarkin Isra'ila ya fara sarauta a Samariya; ya yi mulki shekara arba'in da ɗaya.
\v 24 Ya aikata mugunta a fuskar Yahweh. Bai kauce wa dukkan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi.
\v 25 Ya maida iyakar Isra'ila daga Lebo Hamath zuwa Tekun Arabah, bisa ga bin umurnai na kalmar Yahweh, Allahn Isra'ila, wanda ya faɗa ta wurin bawansa Yona ɗan Amittai, annabin nan da ke daga Gat Hefa.
\s5
\v 26 Gama Yahweh ya ga azabar da Isra'ila ke ciki, kowa yana cikin tsananin wahala, da bawa da sakakke, kuma babu maceci don Isra'ila.
\v 27 Saboda haka Yahweh ya ce ba zai shafe sunan Isra'ila daga ƙarƙashin sammai ba; maimakon haka, Ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yehoash.
\s5
\v 28 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yerobowam, da dukkan abin da ya yi da ikonsa, da yadda ya yi yaƙi ya ƙwato Damaskus da Hamath, waɗanda ke na Yahuda a dã, domin Isra'ila, Ba an rubuta su a littafin abubuwan da suka faru da sarakunan Isra'ila ba?
\v 29 Yerobowam ya kwanta da kakaninsa, tare da sarakunan Isra'ila, sai Zekariya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam, sarkin Isra'ila, Azariya ɗan Amaziya sarkin Yahuda ya fara mulki.
\v 2 Azariya yana shekara goma sha shida sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi sarauta ta shekara hamsin da biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya, kuma ita daga Yerusalem take.
\v 3 Ya yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh, kamar yarda mahaifinsa Amaziya ya yi.
\s5
\v 4 Sai dai, wuraren tsafin kan tuddai ba a rusa su ba. Mutanen dai na miƙa hadaya da ƙona turare a saman tuddai.
\v 5 Yahweh ya addabi sarkin da kuturta har zuwa ranar mutuwarsa kuma ya yi ta zama a gidan da aka ware ne. Yotam, ɗan sarki, ya shugabanci gidan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.
\s5
\v 6 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Azariya da dukkan abin da ya yi, ba an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 7 Saboda haka Azariya ya yi barci tare da kakaninsa; su ka bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda. Yotam, ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 8 A shekara ta talatin da takwas ta Azariya sarkin Isra'ila, Zekariya ɗan Yerobowam ya yi mulki a Isra'ila ta Samariya na wata shida.
\v 9 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh, kamar yadda mahaifansa suka yi. Bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi.
\s5
\v 10 Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla wa Zekariya maƙarƙashiya, ya kai masa hari a Ibleam, ya kashe shi. Sai ya zama sarki a madadinsa.
\v 11 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Zekariya, An rubuta su a littafin abubuwan da suka faru da sarakunan Isra'ila.
\v 12 Wannan ne batun da Yahweh ya faɗa wa Yehu, cewa, "Zuriyarka za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har zuwa tsara ta huɗu." Abin da ya faru kenan
\s5
\v 13 Shullum ɗan Yabesh ya fara mulki a shekara ta talatin da tara na Azariya sarkin Yahuda, kuma ya yi mulki na wata ɗaya a Samariya.
\v 14 Menahem ɗan Gadi ya tafi can daga Tirza zuwa Samariya. a wurin ya kai wa Shullum ɗan Yabesh hari, a Samariya. Ya kashe shi ya kuma zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 15 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Shallum da maƙarƙashiya da ya shirya, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila. Sa'an nan
\v 16 Menahem ya kai hari a Tifsa da dukkan waɗanda ke wurin da iyakar wuraren Tirzah, saboda ba su ba shi zarafin shiga birnin ba. Sai ya kai mata hari ya kuma feɗe dukkan mata masu junabiyu a ƙauyen nan.
\s5
\v 17 A shekara ta talatin da tara ta Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya fara mulki a kan Isra'ila, Ya yi mulkin shekara goma a Samariya.
\v 18 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Gama a dukkan rayuwarsa, bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi.
\s5
\v 19 Sa'an nan Ful sarkin Asiriya ya zo gãba da ƙasar, sai Menaham ya bai wa Ful talanti dubu na azurfa, saboda Ful ya taimaka da gudumawa domin masarautar Isra'ila ta ƙarfafa a hannunsa.
\v 20 Manehen ya ƙarbi wannan kuɗin daga Isra'ila ta wurin neman awo hamsin na azurfa daga dukkan atajiri domin ya bai wa sarkin Asiriya. Don haka Sarkin Asiriya ya juya baya kuma bai zauna cikin ƙasar ba.
\s5
\v 21 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Manahem, da dukkan abin da ya yi, ba a rubuce suke a litaffin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 22 Sai Manahem ya yi barci tare da kakaninsa, kuma Fekahiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 23 A shekara ta hamsin ta Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya fara mulki a Isra'ila cikin Samariya; ya yi mulki shekara biyu.
\v 24 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai juya daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ta wurin hakan ya sa Isra'ila ta yi zunubi.
\s5
\v 25 Fekahiya yana da hafsa mai suna Feka ɗan Remaliya, wanda ya ƙulla masa maƙarkashiya. Tare da mutane hamsin na Giliyad, Feka ya kashe Fekahiya da kuma Argob da Ariye a Samariya, a cikin sansanin hasumayar fadar sarki. Feka ya kashe Fekahiya ya kuma zama sarki a madadinsa.
\v 26 Game da sauran zantuttuka da suka shafi Fekahiya da dukkan abin da ya yi, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
\s5
\v 27 A shekara ta hamsin da biyu na Azariya sarkin Yahuda, Fekah ɗan Remaliya ya fara mulki akan Isra'ila cikin Samariya; ya yi mulki shekara ashirin.
\v 28 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh. Bai kauce daga zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi.
\s5
\v 29 A kwanakin Feka sarkin Isra'ila, Tiglat Filesa sarkin Asiriya ya zo ya ɗauki Ijon da Abel Bet Ma'aka da Janoya da Kedesh da Hazor da Giliyad da Galili da dukkan ƙasar Naftali. Ya ɗauki mutanen zuwa Asiriya.
\v 30 Don haka Hosheya ɗan Elah ya shirya maaƙarƙashiya găba da Feka ɗan Remaliya. Ya kai masa hari ya kuma kashe shi. Sa'an nan ya zama sarki a madadinsa, a shekara ta ashirn ta yotam ɗan Uzziya.
\v 31 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Feka da dukkan abin da ya yi, a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
\s5
\v 32 A shekara ta biyu ta Peka ɗan Remaliya, sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya, sarkin Yahuda ya fara mulki.
\v 33 Yana da shekara ashirin da biyar a sa'ad da ya fara mulki; Ya yi mulki shekara goma sha shida a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yerushah; Ita ɗiyar Zadok ce.
\s5
\v 34 Yotam ya yi abin da ke da kyau a fuskar Yahweh. Ya bi misalin dukkan abubuwan da mahaifisa Azariya ya yi.
\v 35 Duk da haka, ba a ƙwato wuraren tsafin kan tuddai ba. Mutanen na yin hadaya da ƙona turare a samman tuddai, Yotam ya gina ƙofarta bisa ta gidan Yaweh.
\v 36 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yotam, da dukkan abin da ya yi, ba a rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\s5
\v 37 A kwanakin nan ne Yahweh ya fara aiko da Rezin sarkin Aram da Peka ɗan Remaliya gaba da Yahuda.
\v 38 Yotam ya kwanta da kakaninsa a birnin Dauda, kakansa. Sa'an nan Ahaz ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 A shekara ta goma sha bakwai ta Feka ɗan Remaliya,
\v 2 Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda, ya fara mulki, kuma ya yi mulki shekara goma sha shida a Yerusalem. Bai yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh Allahnsa ba, kamar yadda Dauda kakansa ya yi ba.
\s5
\v 3 Maimakon haka, ya yi tafiya a hanyar sarakunan Isra'ila; hakika, ya sa ɗansa a wuta domin hadaya ta ƙonawa, yana bin ayyukan ban ƙyama na al'ummai, waɗanda Yahwe ya fitar daga gaban mutanen Isra'ila.
\v 4 Ya miƙa hadayu da kuma ƙona turare awurare bisa tuddai da ƙarƙashin kowanne koren Itace.
\s5
\v 5 Sa'an nan Rezin, sarkin Aram da Feka ɗan Remaliya, sarkin Isra'ila, ya zo Yerusalem ya kawo hari. Suka tunkari Ahaz, amma ba su iya mamayar sa ba.
\v 6 A lokacin nan, Rezin sarkin Aram ya maido Elath domin Aram ya kori mazajen Yahuda daga Elat. Sa'an nan Aramiyawa suka zo gun Elat inda suka zauna har yau.
\s5
\v 7 Sai Ahaz ya aiki manzanni ga Tiglat Filesa sarkin Asiriya, cewa, "Ni baranka ne da ɗanka. Ka zo ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra'ila, waɗanda suka kawo mani hari."
\v 8 Sai Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyan da aka tarar a gidan Yahweh da na cikin kayayyaki masu daraja na fãdar sarki ya aikar da su kyauta ga sarkin Asiriya.
\v 9 Sa'an nan sarkin Asiriya ya saurare shi, kuma sarkin Asiriya ya farmaƙi Damaskus, ya mamaye ta, ya kuma ɗauke mutanenta ya kai su zaman bauta a Kir. Ya kuma kashe Rezin sarkin Aram.
\s5
\v 10 Sarki Ahaz ya tafi Damaskus ya sadu da Tiglat Filesa sarkin Asiriya. A Damaskus ya ga wani bagadi. Ya aika wa Yuriya firist irin fasalin bagaden da yanayinsa da zane domin dukkan aikin da ake bukata.
\v 11 Don haka Yuriya firist ya gina bagaden da zai zama kamar tsarin da sarki Ahaz ya aiko daga Damaskus. Ya gama shi kafin sarki Ahaz ya dawo daga Damaskus.
\v 12 Sa'ad da sarki ya zo daga Damaskus ya ga bagaden; sarkin ya kusanci bagaden ya kuma yi bayarwa akan sa
\s5
\v 13 Ya yi hadayarsa ta ƙonawar da hadayarsa ta hatsi, ya zubo hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta zumunci a bagaden.
\v 14 Bagaden tagulla wanda ke gaban Yahweh - ya kawo shi daga gaban haikalin, daga tsakanin bagaden da haikalin Yahweh ya sa shi a gefen arewacin bagadensa
\s5
\v 15 Sai sarki Ahaz ya umurci Yuriya firist, cewa, "A babban bagaden ka ƙona baikon ƙonawa na safe da baikon hatsi na yamma, da kuma baikon na ƙonawa na sarki da baikon hatsinsa, da baikon na ƙonawa na dukkan mutanen ƙasar, da baikon hatsinsu da baikon shansu. Ka yayyafa jinin akan dukkan baiko na ƙonawa, da dukka jinin hadayar. Amma bagadin tagulla zai zama nawa domin neman shawara don jagoranci."
\v 16 Yuriya firist kuwa ya yi abin da sarki Ahaz ya umurta.
\s5
\v 17 Sa'an nan sarki Ahaz ya ciro dakalan da darunan da suke bisansu; ya kuma ɗauke babban daron daga bijimin tagullar da ke ƙarƙashinsa ya sa shi a daɓen dutse.
\v 18 Ya cire hanyar da aka killace ta Asabaci wanda aka gina a haikalin, tare da ƙofar dake waje ta shigar sarki zuwa haikalin Yahweh, saboda sarkin Asiriya.
\s5
\v 19 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Ahaz da abin da ya yi, ba a rubuce suke cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 20 Ahaz ya kwanta da kakaninsa aka kuma bizne shi tare da kakaninsa a birnin Dauda. Hezekiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 A shekara ta goma sha biyu ta Ahaz sarkin Yahuda, mulkin Hosheya ɗan Elah ya fara, ya yi mulki a Samariya akan Isra'ila na shekara tara.
\v 2 Ya yi abin mugunta a fuskar Yahweh, duk da haka ba kamar sarakunan Isra'ila waɗanda suka gabace shi ba.
\v 3 Shalmaneser sarkin Asiriya ya kai masa hari, kuma Hosheya ya zama baransa ya kawo masa haraji.
\s5
\v 4 Sa'an nan sarkin Asiriya ya gano cewa Hosheya na ƙulla maƙarƙshiya gãba da shi, don Hoshiya ya aiko manzanni ga So sarkin Masar; haka kuma, babu kyautar da ya miƙo wa sarkin Asiriya, kamar yadda ya saba yi shekara da shekara. Saboda haka sarkin Assiriya ya kulle shi ya ɗaure shi a kurkuku.
\v 5 Sa'an nan sarkin Asiriya ya kai hari a ko'ina a ƙasar, ya kuma kai wa Samariya hari ya mamaye ta shekara uku.
\v 6 A shekara ta tara ta Hosheya, sarkin Asiriya ya ɗauki Samariya ya kuma ɗauki Isra'ila zuwa Asiriya. Ya sa su a Halah, a harabar Kogin Gozan, da kuma cikin biranen Medeyawa.
\s5
\v 7 Mãmewar ta faru ne saboda mutanen Isra'ila sun yi zunubi ga Yahweh Allahnsu, wanda ya kawo su daga ƙasar Masar, daga ƙarƙashin hannun Fir'auna sarkin Masar. Mutanen suna bautawa waɗansu alloli ne
\v 8 kuma suna tafiya cikin ayyukan al'umman da Yahweh ya kora daga mutanen Isra'ila, da kuma cikin ayyukan sarakunan Isra'ila da suka yi.
\s5
\v 9 Mutanen Isra'ila sun yi wa Yahweh Allahnsu abubuwan da ba dai-dai ba a asirce. Sun gina wa kansu manyan wurare a dukkan biranensu, daga hasumiya zuwa birni mai garu.
\v 10 Suka kuma kafa ginshiƙai da sandunan Ashera a ko'ina bisan tudu da ƙarƙashin dukkan koren itace.
\s5
\v 11 A wurin suka ƙona turare cikin dukkan wurare masu bisa, kamar yarda al'ummai suka yi, waɗanda Yahweh ya fitar da su kafin su. Isra'ilawa sun aikata mugayen abubuwan da suka zuga Yahweh ga fushi,
\v 12 sun bauta wa gumaka, irin waɗanda Yahweh ya ce masu, "Ba za ku yi wannan abin ba."
\s5
\v 13 Duk da haka Yahweh ya yi shaida ga Isra'ila da kuma ga Yahuda ta wurin kowanne annabi da kowanne mai gani, cewa, "Ku juyo daga hanyoyin mugunta ku tsare dokokina da farillaina, kuma ku yi hankali da tsare dukkan dokokin da na ummurce ubanninku, da waɗanda na aiko maku ta hanun barorina annabawa."
\s5
\v 14 Amma ba za su saurara ba; maiimakon haka suka taurare kamar ubanninsu waaɗnda ba su da aminci cikin Yahweh Allahnsu.
\v 15 Suka ƙi dokokinsa da alƙawarin da ya yi da kakaninsu, da ummurnan alƙawarin da ya ba su. Suka bi ayyuka marasa amfani kuma su kansu suka zama marasa amfani. Suka bi al'umman arnan da ke kewaye da su, waɗanda Yahweh ya ummurce su kada su kwaikwaye su.
\s5
\v 16 Suka ƙyale dukkan dokokin Yahweh Allahnsu. Suka ƙera sifofin zubi na ƙarfe na 'yan muruƙa biyu domin su bauta masu. Suka yi sandan Ashera, kuma suka bautawa dukkan taurari na sama da Ba'al.
\v 17 Suka sa 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata cikin wutan, suka yi duba da tsubbace tsubbace, suka sayar da kansu don su yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh, kuma suka sa shi shi ya yi fushi.
\v 18 Saboda haka Yahweh ya yi matuƙar fushi da Isra'ila ya cire su daga gabansa, Babu wanda aka bari ban da ƙabilar Yahuda ita ƙaɗai.
\s5
\v 19 Ko Yahuda ma ba su tsare dokokin Yahweh Allahnsu ba, amma maimakon haka suka bi abin da Isra'ila ta yi.
\v 20 Sai Yahweh ya ƙi dukkan zuriyar Isra'ila; ya wahalshe su ya bada su ga hannun waɗanda za su ɗauki mallakarsu a matakin ganima, har sai da ya watsar da su daga fuskarsa
\s5
\v 21 Y a yago Isra'ila daga sarautar ta layin Dauda, suka kuma maida Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam ya kawar da Isra'ila daga bin Yahweh ya sa suka aikata gagarumin zunubi.
\v 22 Mutanen Isra'ila kuwa suka bi dukkan zunuban Yerobowam kuma ba su kauce daga yin su ba,
\v 23 saboda haka Yahweh ya cire Isra'ila daga fuskarsa, kamar yadda ya faɗa ta wurin barorinsa annabawa cewa zai yi. Saboda haka aka ɗauke Isra'ila daga tasu ƙasar zuwa Asiriya, kuma haka yake har wannan rana
\s5
\v 24 Sarkin Asiriya ya kawo mutane daga Babila da Kutha da Avva da Hamat da Sefabayim, sai ya sa su a biranen Samariya a madadin mutanen Isra'ila. Suka mamaye Samariya suka zauna a biranenta.
\v 25 Ya kasance a farkon zamansu a wurin ba su girmama Yahweh ba. Sai Yahweh ya aiko da Zakunan da suka kashe waɗansu daga cikinsu.
\v 26 Sai suka yi magana da sarkin Asiriya, cewa, "Al'umman da ka ɗauke su ka sã a biranen Samariya ba su san ayyukan da allahn ƙasar ke buƙata ba. Saboda haka a aiko da zakuna a cikinsu, kuma, duba, zakunan na karkashe mutane a wurin saboda basu san ayyukan da allahn ƙasar ke buƙata ba
\s5
\v 27 Sa'an nan sarkin Asiriya ya ummurta, cewa, "Ɗauki ɗaya daga cikin firistocin wurin waɗanda ka kawo su daga wurin, kuma sai ya je ya zauna a wurin, ya kuma bari a koyar da su ayyukan da allan ƙasar ya sa a yi."
\v 28 Sai ɗaya daga cikin firistocin da aka ɗauko daga Samariya ya zo ya zauna a Betel; ya koya masu yadda za su girmama Yahweh.
\s5
\v 29 Kowacce kabila sun yi alloli na kansu, kuma suka sa su a wuraren da Samariyawa suka yi - kowacce kabila a biranen da suke zama.
\v 30 Mutanen Babila suka yi Succot Benot; mutanen Kuta suka yi Nergal; mutanen Hamat suka yi Ashima;
\v 31 Avvitawa suka yi Nibhaz da Tartak. Sefavitawa suka ƙone 'ya'yansu a wuta ga Adrammelek da Anammelek, allolin Sefavitawa.
\s5
\v 32 Suka girmama Yahweh, kuma suka naɗa firistocin manyan wuraren daga cikinsu, waɗanda ke yin masu hadaya a masujadai na tuddan wuraren.
\v 33 Suka girmama Yahweh suka kuma bauta wa alloli na kansu, bisa ga al'adar al'umman da aka kawar.
\s5
\v 34 Har wa yau suna ci gaba da al'adun dã. Basu girmama Yahweh, ko su bi farilla da umurni da doka, ko dokokin da Yahweh ya ba mutanen Yakubu - wanda ya kira Isra'ila ba -
\v 35 kuma wanda Yahweh ya yi alƙawari ya kuma ummurce su, "Kada ku ji tsoron waɗansu alloli, ko ku russunar da kanku gare su, ko ku bauta masu ko ku yi masu hadaya.
\s5
\v 36 Amma Yahweh, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar da iko mai girma da dantse a ɗage, shi ne wanda za ku girmama; gare shi ne za ku yi ruku'u, kuma gare shi za ku yi hadaya.
\v 37 Da Farillan da ummurnan da attaura da dokokin da ya rubuta domin ku, za ku tsare su har abada. Saboda kada ku ji tsoron waɗansu alloli,
\v 38 kuma alƙawarin da na yi da ku, ba zaku mance ba; kuma ba za ku girmama waɗansu alloli ba.
\s5
\v 39 Amma Yahweh Allahnku shi ne wanda za ku girmama. Zai ƙuɓutar da ku daga ikon maƙiyanku."
\v 40 Ba za su saurara ba, saboda sun ci gaba da yin abin da suke yi a baya.
\v 41 Don haka al'umman sun ji tsoron Yahweh suka kuma bauta wa ƙerarrun sifofinsu, kuma 'ya'yansu suka yi hakan kuma - kamar yadda 'ya'yan 'ya'yansu suka yi. Suka ci gaba da yin abin da kakaninsu suka yi har wa yau.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Yanzu a shekara ta uku na Hosheya ɗan Ela, sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz, sarkin Yahuda ya fara mulki.
\v 2 Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekara ashirin da tara a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Abija; ita ɗiyar Zekariya ce.
\v 3 Ya yi abin da ke dai-dai a fuskar Yahweh, ya na bin misalin dukkan abubuwan da Dauda, kakansa ya yi.
\s5
\v 4 Ya kawar da tuddan wurare, ya rusar da ginshiƙan dutse, ya farfashe sandan Ashera. Ya kakkarya tagullar macijin da Musa ya yi, saboda a kwanakin dã mutanen Isra'ila suna ƙona mata turare; a na kiran ta "Nehushtan."
\v 5 Hezekiya ya dogara ga Yahweh, Allahn Isra'ila, saboda bayansa babu wani kamarsa a cikin sarakunan Yahuda, koma a cikin waɗanda suka gabace shi.
\s5
\v 6 Gama ya manne wa Yahweh. Bai daina binsa ba gama ya kiyaye dokokinsa, waɗanda Yahweh ya ummurci Musa.
\v 7 Saboda haka Yahweh yana tare da Hezekiya, kuma duk inda ya je ya wadata. Ya yi wa sarkin Asiriya tawaye kuma bai bai bauta masa ba.
\v 8 Ya kai wa Filistiyawa hari har Gaza da iyakar da ke kewaya, daga hasumiyar zuwa birni mai garu.
\s5
\v 9 A shekara ta huɗu na Hezekiya, wadda ke dai-dai da shekara ta bakwai ta Hosheya ɗan Elah sarkin Isra'ila, Shalmanesar sarkin Asiriya ya kawo wa Samariya hari ya mamaye su.
\v 10 A ƙarshen shekaru uku suka ɗauke ta, a shekara ta shida na Hezekiya, wanda ke shekara ta tara ta Hosheya sarkin Isra'ila; a wannan hanyar kuwa aka kame Samariya.
\s5
\v 11 Sai sarkin Asiriya ya ɗauki Isra'la zuwa Asiriya ya sa su a Halah da kuma a kogin Habor a Gozan da biranen Medeyawa.
\v 12 Ya yi wannan ne saboda ba su yi biyayya da muryar Yahweh Allahnsu ba, amma sun wofintar da ƙudurorin alkawarinsa, dukkan abin da Musa bawan Yahweh ya ummurta. Suka ƙi su ji ko su aikata shi.
\s5
\v 13 Sa'an nan a shekara ta goma sha huɗu ta Sarki Hezekiya, Senakerib sarkin Asiriya ya kai wa dukkan birane masu garu na Yahuda hari ya kuma danƙe su.
\v 14 Saboda haka Hezekiya sarkin Yahuda ya aika wa sarkin Asiriya, wanda ke Lakish da kalma, cewa, "Na yi maka laifi. Ka janye daga gare ni. Duk abin da ka ɗora mani zan ɗauka." Sarkin Asiriya kuwa ya umarci Hezakiya sarkin Yahuda ya bada talanti ɗari uku na azurfa da talatin na zinariya masu yawa.
\v 15 Sai Hezekiya ya ba shi dukkan azurfan da ke gidan Yahweh da na cikin ma'aji na fãdar sarki.
\s5
\v 16 Sa'an nan Hezekiya ya ciro zinariyar da ke ƙofofin haikalin Yahweh da kuma daga madogaran da aka kafa; ya ba da zinarin ga sarkin Assiriya.
\v 17 Amma sarkin Asiriya ya shiryo gagarumin sojojinsa, Ya aiki Tartan da Rabsaris da babbar rundunar sojojin daga Lakish zuwa ga Sarki Hezekiya a Yerusalem. Suka yi tafiya ta hanyoyin su ka kai wajen Yerusalem. Suka nufi kududdufi na sama wurin kwanciyar ruwa, wanda ke a kan kwaruwa zuwa wurin wanki, suka tsaya ta wurin.
\v 18 Sa'ad da suka yi kira ga Sarki Hezekiya, Eliyakin ɗan Hilkiya, wanda ke wakilin gidan da Shebna magatakarda da Yowa ɗan Asaf, mai rubutun rohoto suka je su sadu da su.
\s5
\v 19 Sai shugaban rundunar sojojin ya ce masu su faɗa wa Hezekiya abin da sarki mai girma, sarkin Asiriya, ya faɗa: "Mene ne masomin karfin halinka?
\v 20 Kana faɗin kalmomi marasa amfani ne kawai, cewa akwai tarayya da ƙarfi domin yaƙi. Ga wa kake dogara? har da za ka tayar mani?
\v 21 Duba, ka dogara ga sandan tafiya na raunannan ciyayin Masar, amma idan mutum ya manne mata, za ta haɗu da hannunsa ta soke shi. Wannan ne abin da Fir'auna sarkin Masar ya ke ga duk wanda ya dogara gare shi.
\s5
\v 22 Amma idan ka ce mani, 'Muna dogara ga Yahweh Allahnmu ne,' ba shi ne wanda Hezekiya ya ɗauke masa wuraren sama da bagaden ba, ya kuma cewa Yahuda da Yerusalem, 'Lallai sai kun yi sujada a gaban bagaden nan a Yerusalem'?
\v 23 Yanzu dai, ina so in yi maka gudunmawa daga ubangijina sarkin Asiriya. Zan baka dawakai dubu biyu, idan za ka samar masu mahaya.
\s5
\v 24 Ta yaya zaka ma iya karawa da mafi ƙanƙantar shugaban sojojin ubangijina? Ka bada ƙarfinka ga Masar domin karusai da mahaya!
\v 25 Na taɓa zuwa nan in yi yaƙi in hallka ta ba tare da Yahweh ba? Yahweh ya ce mani, 'Ka kai wa ƙasar nan hari ka hallaka ta."'
\s5
\v 26 Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkaya da Shebna da Yowa suka cewa shugaban rundunar, "In ka yarda ka yi magana da harshen Aramayik, don shi muka gane. Kada ka yi magana da mu da harshen Yahuda a kunnen mutanen da ke a bangon."
\v 27 Amma shugaban rundunar ya ce masu, Ba maganar da ubangijina ya aike ni ga ubangijinku in faɗa kenan ba? Ba shi ya aiko ni wurin mazan da ke zaune a bangon, waɗanda za su ci kaãshinsu su kuma sha fitsarinsu tare da ku ba?"
\s5
\v 28 Sa'an nan shugaban rudunar sojojin ya tsaya ya yi kira da babbar murya a harshen Yahudawa, cewa, "Ku saurari maganar sarki mai girma, sarkin Asiriya.
\v 29 Sarkin ya ce, 'Kar ka bar Hezekiya ya ruɗe ka, gama ba zai iya ya ƙubutar da kai daga ikona ba.
\v 30 Kada ku yarda Hezekiya yasa ku dogara ga Allah, cewa, "Hakika Yahweh zai cece mu, kuma ba za a ba da wannan birnin ga hannun sarkin Asiriya ba.""
\s5
\v 31 Kada ku saurari Hezekiya, gama ga abin da sarkin Asiriya ya ce: 'Ku yi amana da ni ku kuma zo gare ni. Sa'an nan kowannen ku zai ci daga tasa kuringar inabi da itacen ɓaurensa ya kuma sha daga cikin randarsa.
\v 32 Zaku yi haka har lokacin da zan zo in ɗauke ku in kaiku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, ƙasar gurasa da lambuna, ƙasar itatuwan zaitun da zuma, saboda ku rayu kar ku mutu.' Kada ka saurari Hezekiya sa'ad da yake ƙoƙarin rinjayarku, cewa, 'Yahweh zai cece mu.'
\s5
\v 33 Ko akwai wani daga cikin allolin mutanen da ya ceto su daga hanun sarkin Asiriya?
\v 34 Ina allolin Hamat da Arfad? Ina allolin Sefabayim da Hena da Ivvah? Sun ceto Samariya daga hannuna ne?
\v 35 A cikin allolin ƙasashe, akwai wani allahn da ya ceci ƙasarsa daga ikona? Ta yaya Yahweh zai ceci Yerusalem daga ikona?"
\s5
\v 36 Amma mutane suka yi shiru basu ce uffan ba, domin sarki ya bada umarni, "Kada ku amsa masa."
\v 37 Sai Eliyakim ɗan Hikiya, wanda ke shugabantar gidan; Shebna magatakarda; da Yowa ɗan Asaf, mai ɗaukan rohoto, suka zo wurin Hezikiya da tufafinsu a yage, suka bada rahoto gare shi kan maganganun babban hafsan.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Sai ya zamana sa'ad da sarki Hezekiya ya ji rohotonsu, ya yayyaga tufafinsa, ya rufe kansa da tsumma, ya je gidan Yahweh.
\v 2 Ya aiki Eliyakim, wanda ke lura da gidan, da Shebna magatakarda, da dattawan firistoci, dukkan su saye da tufafin tsumma, ga annabi Ishaya ɗan Amoz.
\s5
\v 3 Suka ce masa, "Hezekiya ya ce, 'wannan ranar ta ƙunci da tsutawa da bankunya, gama 'ya'ya sun kai lokacin haifuwa amma babu ƙarfi domin haifar su.
\v 4 Yana yiwuwa Yahweh Allahnka zai ji dukkan kalmomin shugaban rundunar, wanda sarkin Asiriya ubangijinsa ya aiko don ya jã da Allah, ya kuma tsauta wa kalmomin da Yahweh Allahnka ya ji. To ka ɗaga murya cikin addu'arka domin ragowar da ke nan har yanzu.""
\s5
\v 5 Saboda haka barorin sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,
\v 6 sai Ishaya ya ce masu, "Ku faɗawa shugabanku: 'Yahweh ya ce, "Kada ku ji tsoron kalmomin da kuka ji, waɗanda barorin sarkin Asiriya suka yi mani rashin kunya.
\v 7 Duba, zan sa wani ruhu a cikinsa, sai ya ji wani rohoto ya koma zuwa ƙasarsa. Zan sa ya fãɗi ta takobi a nasa ƙasan.""'
\s5
\v 8 Sa'an nan shugaban rundunan ya komo ya tarar sarkin Asiriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji wai sarkin ya tashi daga Lakish.
\v 9 Sa'an nan Senakirib ya ji cewa Tirhaka sarkin Kush da Masar sun yi shiri su yaƙe shi, sai ya aiki manzanni kuma ga Hezekiya da saƙo:
\s5
\v 10 "Ku cewa Hezekiya sarkin Yahuda, 'Kada ka bar Allahnka wanda ka dogara gare shi ya ruɗe ka, cewa, "Ba zan ba da Yerusalem ga hannun sarkin Asiriya ba."
\v 11 Duba, ka ji abin da sarkin Asiriya ya yi wa dukkan ƙasashe da ya hallakar da su sarai. To za ka kuɓuta?
\s5
\v 12 Allolin al'ummai sun kuɓutar da su ne, al'umman da ubannina suka hallakar wato Gozan da Haran da Rezef da mutanen Eden a Tel Assar?
\v 13 Ina sarakunan Hamat da na Arfad da na biranen Sefabayim da Ivvah?"'
\s5
\v 14 Hezekiya ya karɓa wasiƙar daga manzannin ya karanta ta. Sai ya haura zuwa gidan Yahweh ya shinfiɗa ta a gabansa.
\v 15 Sa'an nan Hezekiya ya yi addu'a a gaban Yahweh ya ce, '"Yahweh mai runduna, Allahn Isra'ila, Kai da ke zaune bisan kerubim, kai kaɗai ne Allah akan dukkan mulkokin duniya. Ka yi sammai da duniya.
\s5
\v 16 Ka kasa kunnenka, Yahweh, ka saurara. Ka buɗe idanuwanka Yahweh, ka gani, ka kuma ji kalaman Senakerib, waɗanda ya aiko don ya yi wa Allah mai rai ba'a.
\v 17 A gaskiya, Yahweh, sarakunan Asiriya sun hallakar da al'ummai da ƙasashensu.
\v 18 Suka sa allolinsu cikin wuta, gama su ba alloli ba ne amma aikin hannuwan mutane ne, katako da dutse kawai. Don haka Asiriyawan suka hallaka su.
\s5
\v 19 Yanzu, Yahweh Allahnmu, I na roƙe ka, ka cece mu, daga ikonsa, saboda dukkan mulkokin duniya su sani cewa kai, Yahweh, kai kaɗai ne Allah."
\s5
\v 20 Sa'an nan Ishaya ɗan Amoz ya aiko da saƙo ga Hezekiya, cewa, "Yahweh, Allahn Isra'ila ya faɗi, 'Saboda ka yi addu'a gare ni game da Senakerib sarkin Asiriya, Na ji ka.
\v 21 Wannan ita ce maganar da Yahweh ya faɗa game da shi: "Budurwan nan ɗiyar Sihiyona ta rena ka tana kuma yi maka dariyar reni. Ɗiyar Yerusalem na girgiza maka kanta.
\v 22 Wane ne ka saɓa wa ka kuma yi wa reni? Wanda kuma ka ɗaukaka muryarka ka ɗaga idanuwanka cikin taƙama gãba da shi? Gãba da Mai Tsarkin Isra'ila!
\s5
\v 23 Ta manzaninka ka saɓa wa Ubangiji, har ka ce, 'Tare da ɗumbin karusaina na kai duwatsu mafi tsawo, mafi tsawon tudddai ta Lebanan. Zan datse dogayen itatuwan sida da zaɓaɓɓun itatuwan Sifires a wurin. Zan shiga cikin manisancin kurminta, da dajinta da ya fi bada 'ya'ya.
\v 24 Na gina rijiyoyi na kuma sha ruwan baƙuwar ƙasa. Na busar da dukkan kogunan Masar a ƙarƙashin tafin ƙafafuna.'
\s5
\v 25 Ba ka taɓa jin yadda na ƙudura shi da daɗewa ba, na kuma yi shi tun zamanin zamanai ba? Yanzu zan aiwatar da shi. Kana nan domin rage birane masu wadata su zama kufai.
\v 26 Mazaunansu, masu ƙarancin ƙarfi, suna a warwatse, kuma an kunyata su. Su ganyaye ne a fili, koriyar ciyawa, ciyawa a rufi ko a fili, da aka ƙone kafin ta yi girma.
\s5
\v 27 Amma na san yadda kake zama a ƙasa da fitarka da shigarka, da tawayenka gãba da ni.
\v 28 Saboda tayarwarka gãba da ni, kuma saboda taƙamarka ta kai kunuwana, zan sa ƙugiya a hancinka, da linzami a bakinka; zan komo da kai baya ta inda ka iso."
\s5
\v 29 Wannan zai zama alama a gare ka: wannan shekarar za ku ci abin da ke girma a jeji, a shekara ta biyu kuma, abin da ya fita daga nan. amma a shekara ta uku kuma dole ka shuka ka girba, ka shuka gonakin inabi ka ci 'ya'yan itatuwansu
\v 30 Ragowar gidan Yahuda da suka rayu za su sake yin saiwa su yi "ya'ya.
\v 31 Gama daga Yerusalem za a fito da ragowa, daga Tsaunin Sihiyona waɗanda suka tsira za su zo. Himmar Yahweh mai runduna za ta yi haka.
\s5
\v 32 Saboda haka Yahweh ya faɗi haka game da sarkin Asiriya: "Ba zai zo cikin birnin ko ya harba kibiya a nan ba. Ko kuwa ya zo gabansa da garkuwa ko ya gina sansani gãba da shi ba.
\v 33 Ta hanyar da ya zo, ta nan kuma zai tafi; ba zai shiga wannan birnin ba - wannan furcin Yahweh ne."
\v 34 Gama zan kãre wannan birnin in kuɓutar da shi, domin kaina da kuma domin bawana Dauda."'
\s5
\v 35 Sai ya zamana a daren nan da mala'ikan Yahweh ya je ya kai hari ga sansanin Asiriyawa, ya sa sojoji 185,000 suka mutu. Sa'ad da mazaje suka tashi da sassafe, sai ga gawawwaki kwance ko'ina.
\v 36 Saboda haka Senakerib sarkin Asiriya ya bar Isra'ila ya tafi gida ya zauna a Nineba.
\v 37 Bayan 'yan lokuta ƙaɗan, yayin da yake yin sujada a gidan allansa Nisrok, sai 'ya'yansa Adrammalek da Shareza suka kashe shi da takobi. Sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai Esarhadon ɗansa ya zama sarki a madadinsa
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 A kwanakin nan Hezekiya ya yi rashin lafiya har ya kusa da mutuwa. Saboda haka annabi Ishaya ɗan Amoz, ya zo gare shi, ya ce masa, "Yahweh ya ce, 'Ka shirya gidanka; gama zaka mutu, ba zaka rayu ba."'
\v 2 Sa'an nan Hezekiya ya juya fuskarsa ga bango ya yi addu'a ga Yahweh yana cewa,
\v 3 "In ka yarda Yahweh, ka tuna da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukkan zuciyata, da kuma abubuwan masu kyau da na yi a fuskarka." Sai Hezekiya ya yi kuka.
\s5
\v 4 Kafin Ishaya ya fita cikin tsakiyar fãdar, maganar Yahweh ya zo gare shi, cewa,
\v 5 "Ka juya baya, ka cewa Hezekiya, shugaban mutanena, 'Wannan shi ne abin da Yahweh, Allahn Dauda kakanka na asali, ya ce: "Na ji addu'arka, na ga hawayenka. Ina gab da warkar da kai a rana ta uku, kuma za ka haura zuwa gidan Yahweh.
\s5
\v 6 Zan ƙara shekaru goma sha biyar ga rayuwarka, zan kuɓutar da wannan birnin daga hannun sarkin Asiriya, kuma zan kare birnin nan domin kaina domin kuma bawana Dauda"""
\v 7 Sai Ishaya yace, "Ka ɗauki curin ɓaure."Su ka yi haka suka sa a marurunsa, sai ya samI lafiya.
\s5
\v 8 Hezikiya ya cewa Ishaya, "Mene ne zai zama alamar cewa Yahweh zai warkar da ni, da kuma zai sa ni in je haikalin Yahweh a rana ta uku?"
\v 9 Ishaya ya amsa, "Wannan ne zai zama alama dominka daga Yahweh, cewa Yahweh zai yi abin da ya faɗa. Inuwa ta yi gaba da taki goma, ko ta yi baya da taki goma?"
\s5
\v 10 Hezekiya ya amsa, "Abu mai sauki ne ga inuwa ta yi gaba da taƙi goma. A'a, bari Inuwa ta yi baya da taƙi goma."
\v 11 Sai annabi Ishaya ya yi kira ga Yahweh, sai ya komo da inuwar taƙi goma baya, daga inda ta motsa a matakalin Ahaz.
\s5
\v 12 A lokacin nan Marduk-Baladan ɗan Baladan sarkin Babila ya aika da wasiƙu da kyautai ga Hezekiya, gama ya ji cewa Hezekiya ba shi da lafiya.
\v 13 Hezekiya ya saurari wasiƙun nan, sai ya nuna wa manzaNnin dukkan fǎda da abubuwa masu daraja da azurfa da zinariya da kayan ƙanshi da mai, mai daraja da gidan ajiyar kayan yaƙi da dukkan abin da ke samuwa a gidajen ajiyarsa. Babu wani abu a gidansa, ko a mulkinsa, da Hezekiya bai nuãna masu ba.
\s5
\v 14 Sa'annan annabi Ishaya ya zo wurin sarki Hezekiya ya tambaye shi, "Mene ne waɗannan mazajen suka ce maka? Daga ina suka fito?" Hezekiya ya ce, "Sun zo daga ƙasa mai nisa ta Babila."
\v 15 Ishaya ya tambaye shi, "Mene ne suka gani a gidanka?" Hezekiya ya amsa, "Sun ga kome a gidana. Babu wani abu cikin abubuwa masu daraja da ban nuna masu ba."
\s5
\v 16 Sai Ishaya ya cewa Hezekiya, "Ka saurari maganar Yahweh:
\v 17 'Duba, ranakun na kusatowa da kowanne abu a fǎdarka, da abubuwan da kakaninka suka ajiye har zuwa yau, za a ɗauke su zuwa Babila. Babu abin da zai rage, inji Yahweh.
\v 18 'Ya'yan da aka haifa maka waɗanda kai da kanka kake mahaifinsu - za a ɗauke su, zasu kuma zama bãbãni a fãdar sarkin Babila."'
\s5
\v 19 Sa'annan Hezekiya ya cewa Ishaya, "Maganar Yahweh da ka faɗa tana da kyau." Saboda yana tunanin, "Ba za a sami salama da zaman lafiya a kwanakina ba?"
\v 20 Game da waɗansu zantuttuka da suka shafi Hezekiya, da dukkan ikonsa da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa, da yadda ya kawo ruwa cikin birnin - ba a rubuce suke cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 21 Hezekiya ya yi barci tare da kakaninsa, sai Manasse ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Manasse na da shekaru goma sha biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru hamsin da biyar a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hefziba.
\v 2 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh, kamar abubuwan banƙyama na al'umman da Yahweh ya kora a gaban mutanen Isra'ila.
\v 3 Gama ya sake ginin wuraren bisa da Hezekiya mahaifinsa ya rurrushe, sai ya gina bagadi domin Ba'al, ya yi sandan Ashera, kamar yadda Ahab sarkin Isra'ila ya yi, ya kuma russuna wa dukkan tauraron sammai ya yi masu sujada.
\s5
\v 4 Manasse ya gina bagadai a cikin gidan Yahweh, ko da yake Yahweh ya ummurta, "A Yerusalem ne sunana zai kasance har abada."
\v 5 Ya gina bagadi domin dukkan taurarin sammai a filayen ciki biyu da ke gidan Yahweh.
\v 6 Ya sa ɗansa ya wuce ta wuta, ya yi sihiri da dubã da ma'amula da waɗanda ke magana da matattu da waɗanda ke magana da ruhohi. Ya yi mugunta da yawa a gaban Yahweh, yana sa shi yin fushi.
\s5
\v 7 Sarrafaffiyar siffa ta Ashera da ya yi, ya sata a gidan Yahweh. A game da wannan gidan ne Yahweh ya yi magana da Dauda da Suleimanu ɗansa; ya ce: "A wannan gidan da kuma Yerusalem ne, inda na zaɓa daga dukkan ƙabilun Isra'ila, da zan sa sunana har abada.
\v 8 Ba zan sa ƙafafun Isra'ila su ƙara fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, Idan har zasu kula su yi biyayya da dukkan abin da na ummurce su, su kuma bi dukkan dokokin da bawana Musa ya Ummurce su."
\v 9 Amma mutanen ba su ji ba, Manasse kuma ya jagorance su ga yin aikin mugunta fiye da al'umman da Yahweh ya hallakar a gaban mutanen Isra'ila.
\s5
\v 10 Sai Yahweh ya yi magana ta wurin bayinsa annabawa, cewa,
\v 11 "Saboda Manasse sarkin Yahuda ya yi waɗannan abubuwan banƙyama, ya kuma aikata mugunta fiye da dukkan abin da Amoriyawan da suke gabaninsa suka yi, ya kuma sa Yahuda ya yi zunubi da gumakansa,
\v 12 don haka Yahweh, Allah na Isra'ila, ya faɗi haka: Duba, Ina gab da kawo bala'i a Yerusalem da Yahuda wanda duk wanda ya ji abin, dukkan kunuwansa za su ƙaɗu.
\s5
\v 13 Zan miƙa a saman Yerusalem layin magwajin da zan gwada Samariya, da layin ma'aunin gwada gidan Ahab; Zan share Yerusalem fes-fes, kamar yadda mutum ke wanke kwano, yana share ta da kuma goge ta yana juya ta ko'ina.
\v 14 Zan jefar da ragowar gãdona in ba da su ga hannun maƙiyansu. Za su zama waɗanda aka yi wa laifi da ganima ga dukkan makiyansu,
\v 15 saboda sun yi abin mugunta a gabana, suka kuma zuga ni ga fushi, tun daga ranar da kakaninsu suka fito daga Masar, har yau."
\s5
\v 16 Haka kuma, Manasse ya zub da jinin adalai da yawa, har sai da ya cika Yerusalem daga gefe ɗaya zuwa wani gefen da mutuwa. Banda zunubin da ya sa Yahuda suka yi, sa'ad da suka yi mugunta a gaban Yahweh.
\v 17 A game da sauran zantuttukan da ya shafi Manasse da dukkan abin da ya yi, da zunuban da ya aikata, ba a rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 18 Manasse ya yi barci tare da kakaninsa aka bizne shi a lanbun gidansa, a lanbun Uzza. Amon ɗansa ya zama saki a madadinsa.
\s5
\v 19 Amon na da shekaru ashirin da biyu sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru biyu a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet; ita ɗiyar Haruz na Jotba ne.
\v 20 Ya yi akin mugunta a gaban Yahweh, kamar yanda Manasse mahaifinsa ya yi.
\s5
\p
\v 21 Amon ya bi dukkan hanyar da mahaifinsa ya yi tafiya ya kuma bauta wa gumakan da mahaifisa ya bauta wa, ya yi masu ruku'u.
\v 22 Ya ƙi Yahweh, Allah na ubanninsa, bai kuma yi tafiya a hanyar Yahweh ba.
\v 23 Barorin Amon suka shirya maƙarƙashiya gãba da shi suka kashe shi a cikin gidansa.
\s5
\v 24 Amma mutanen ƙasar suka kashe dukkan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiya, sai suka maida Yosiya, ɗansa sarki a madadinsa.
\v 25 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Amon da abin da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 26 Mutanen suka bizne shi a kabarinsa cikin lambun Uzza, sai Yosiya ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Yosiya yana da shekaru takwas sa'ad da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru talatin da uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Yedida (Ita ɗiyar Adayiya na Bozkat ce).
\v 2 Ya yi abin da ya dace a gaban Yahweh. Ya yi tafiya a hanyar Dauda kakansa, bai kuma kauce mata zuwa dama ko hagu ba.
\s5
\v 3 Sai ya zamana a shekara ta goma sha takwas ta sarki Yosiya, ya aike Shafan ɗan Azaliya ɗan Mashullam, magatakarda, zuwa gidan Yahweh, cewa,
\v 4 "Jeka wurin Hilkiya babban firist ka gaya masa ya ƙirga ƙuɗin da aka kawo cikin gidan Yahweh, wanda masu gadin haikali suka tara daga mutane.
\v 5 A ba da shi ga hannun ma'aikatan da ke lura da gidan Yahweh, su ba ma'aikatan da ke gidan Yahweh domin su yi gyare-gyare a haikali.
\s5
\v 6 Su bada ƙuɗi ga kafintoci da magina, a kuma sayi katakon timba a buga dutse domin gyaran haikali."
\v 7 Amma babu bukatar rohoton kashe kuɗin da aka ba su, saboda sun yi aiki da shi cikin aminci.
\s5
\v 8 Hilkiya babban firist ya cewa Shafan magatakarda, "Na sami littafin dokoki a gidan Yahweh." Sai Hilkiya ya ba da littafin ga Shafan, sai ya karanta shi.
\v 9 Shafan ya je ya kai littafin gun sarki, ya kuma sanar da shi, cewa, "Barorinka sun kashe kuɗin da aka samu a haikali kuma sun ba da shi ga hannun ma'aikatan da ke shugabancin lura da gidan Yahweh."
\v 10 Sa'annan Shafan magatakarda ya faɗa wa sarkin, "Hilkiya firist ya ba ni littafi." Sai Shafan ya karanta wa sarki.
\s5
\v 11 Sai ya zamana sa'ad da sarki ya ji kalmomin dokokin, sai ya yayyaga tufafinsa.
\v 12 Sarkin ya ummurci Hilkiya firist da Ahikam ɗan Shafan da Akbor ɗan Mikayiya da Shafan magatakarda da Asayiya bawansa cewa,
\v 13 "Ku je ku ji daga wurin Yahweh domina da mutanen da dukkan Yahuda, saboda kalmomin wannan littafin da aka samo. Gama fushin Yahweh a gare mu na da girma saboda kakanninmu ba su saurari kalmomin wannan littafin don yin biyayya game da dukkan abin da aka rubuta game da mu ba."
\s5
\v 14 Sa'an nan Hilkiya firist da Ahikam da Akbor da Shafan da Asayiya suka je wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikvah ɗan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiyan sutura (tana zaune a Yerusalem a yankin sabon birnin), sai suka yi magana tare da ita.
\v 15 Ta ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗI: 'Gaya wa mutumin da ya aike ki gare ni,
\v 16 Ga abin da Yahweh ya faɗi: 'Duba, zan auko da bala'i ga wannan wurin tare da mazaunansa, bisa ga dukkan abin da aka rubuta a littafin da sarkin Yahuda ya karanto.
\s5
\v 17 Saboda kun yashe ni kuka kuma ƙona turare ga waɗansu alloli, don su tsokane ni ga yin fushi da dukkan ayyukan da suka yi - don haka na fito da wutar hasalata gãba da wannan wurin, kuma ba za ta mutu ba."'
\v 18 Amma ga sarkin Yahuda, Wanda ya aike ku ku nemi nufin Yahweh, ga abin da zaku ce masa: "Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗi haka: 'game da kalmomin da ka ji,
\v 19 saboda zuciyarka ta yi taushi, ka kuma yi tawali'u a gaban Yahweh, sa'ad da ka ji abin da na faɗa gãba da wannan wurin da mazaunansa, akan yadda zasu zama kango da la'ana, saboda kuma ka yayyaga tufafinka ka yi kuka a gabana, Ni kuma na saurare ka - wannan furcin Yahweh ne.
\s5
\v 20 Duba, Zan tara ka ga kakanninka, kuma za a tara ka ga kabarinka cikin salama. Idanuwanka baza su ga dukkan masifun da zan auko da su akan wurin nan ba.""" Sai mazajen suka mayar da saƙon ga sarki.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Sa'an nan sarki ya aiko da manzanni waɗanda suka tara masa dukkan dattawan Yahuda da Yerusalem.
\v 2 Sai sarki ya haura zuwa gidan Yahweh da dukkan mazaunan Yahuda da Yerusalem da ke tare shi, da firistoci da annabawa da dukkan mutane, daga ƙanƙani zuwa babba. Sai ya karanta dukkan kalmomin littafin Alƙawarin da aka samu a gidan Yahweh a kunnuwansu.
\s5
\v 3 Sarkin ya tsaya a gefen ginshiƙi ya yi alƙawari ga Yahweh cewa zai bi Yahweh ya kiyaye dokokinsa, da ummurnansa da farillansa, da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa, ya kuma ka'idantar da kalmomin alƙawarin da aka rubuta a wannan littafin. Saboda haka mutanen suka yarda su tsaya akan alƙawarin.
\s5
\v 4 Sa'an nan sarki ya ummurce Hilkiya babban firist da firistoci da ke ƙarƙashinsa da masu tsaron ƙofa su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al da Ashera daga haikalin Yahweh, da dukkan taurarin sama. Ya ƙone su a bayan Yerusalem a filayen Kwarin Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.
\v 5 Ya kuma kawar da firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuda suka naɗa don a ƙona turare a wuraren tuddai a biranen Yahuda da kewayen Yerusalem - waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana da wata da duniyoyi da dukkan taurarin sama.
\s5
\v 6 Ya fitar da sandan Ashera daga haikalin Yahweh, wajen Yerusalem zuwa Kwarin Kidron ya ƙona shi a wurin. Ya buge ta har ga ƙura ya zubar da ƙurar cikin kaburburan talakawa.
\v 7 Ya rusa ɗakunan karuwai matsafa waɗanda ke a haikalin Yahweh, inda matan ke saƙa tufafin Ashera.
\s5
\v 8 Yosiya ya fitar da dukkan firistoci daga biranen Yahuda ya ƙazantar da tuddan wuraren da firistoci ke ƙona turare, daga Geba zuwa Biyasheba. Ya rurrushe tuddan wuraren a kofofin da ke mashigin ƙofofin Yoshuwa (gwamnan birnin), a gefen hagu na ƙofar birnin.
\v 9 Ko da shike ba a bar firistocin waɗannan tuddan wuraren su yi aiki a bagadin Yahweh a Yerusalem ba, sun ci gurasa mara yisti cikin 'yan'uwansu maza.
\s5
\v 10 Yosiya ya ƙazantar da Tofet, wanda ke cikin Kwarin Ben Hinom, saboda kar kowa ya sa ɗansa ko ɗiyarsa bi ta wuta a matsayin hadaya ga Molek.
\v 11 Ya ɗauki dawakan da sarakunan Yahuda suka miƙa wa rana, Suna nan a wurin a ƙofar haikalin Yahweh kusa da ɗakin Natan-Melek shugaban shirayin da ke cikin farfajiya. Yosiya ya ƙona karusan rana.
\s5
\v 12 Sarki Yosiya ya rurrusa bagadan da ke bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuda suka yi, da bagaden da Manasse ya yi a farfajiya biyu ta haikalin Yahweh. Yosiya ya rugurguza su ya jefar da su a Kwarin Kidron,
\v 13 Sarkin ya rurrushe tuddan wuraren tsafi da ke gabashin Yerusalem kudu da dutsen hallaka wanda Suleman sarkin Isra'ila ya gina wa Ashtoret da ƙazantacciyar gunkiyar Sidoniyawa; don Kemosh, ƙazantaccen gunkin Mowab; kuma na Molek, da ƙazantaccen gunkin Amonawa.
\v 14 Ya rurrushe ginshiƙai na dutse rugu-rugu ya kuma sassare sandunan Ashera sa'an nan ya rufe wuraren da ƙasussuwan mutane.
\s5
\v 15 Yosiya ya rurrushe bagadan da ke a Betel kakaf da wuri mai tudu da Yerobowam ɗan Nebat (wanda ya sa Isra'ila ta yi zunubi) ya gina. Ya kuma ƙona bagadin da wuri mai tudu, ya buge shi har ga ƙura, ya ƙona sandan Ashera.
\v 16 Yayin da Yosiya ya dubi dukkan kewayen, sai ya gano kaburburan da ke kan tuddu, ya aika maza su kwaso ƙasusuwan daga kaburburan; sai ya ƙona su a bagadin, wanda ya ƙazantar da shi. Wannan bisa ga maganar Yahweh ce wadda mutumin Allah ya faɗa, mutumin da ya faɗi waɗannan abubuwan tuntuni.
\s5
\v 17 Sa'an nan ya ce, "Wanne kabari ne waccan da na gani?" Mutanen birnin suka gaya masa, "Waccan ne kabarin mutumin Allah da ya zo daga Yahuda, ya yi magana akan abubuwan nan da kayi gãba da bagaden Betel."
\v 18 Sai Yosiya ya ce, ku bar shi kawai. Kada kowa ya motsa ƙasusuwansa, sai suka bar ƙasusuwansa tare da na annabin da yazo daga Samariya.
\s5
\v 19 Sa'an nan Yosiya ya cire dukkan gidajen wuraren kan tudu da ke a Samariya, wanda sarakunan Isra'ila su ka yi, da ya sa Allah ya yi fushi. Ya yi masu dai-dai da abin da aka yi a Betel.
\v 20 Ya yayyanka dukkan firistocin tuddan wuraren akan bagadan sai ya ƙona ƙasusuwan mutane akan su. Sa'an nan ya koma Yerusalem.
\s5
\v 21 Sa'an nan Sarkin ya ummurci dukkan mutane cewa, "Ku kiyaye bikin Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku, kamar yadda aka rubuta a Littafin Alƙawari."
\v 22 Irin hidimar bukin nan ba a taɓa yinsa ba tun daga kwanakin da alƙalai suka yi mulkin Isra'ila, ko dukkan kwanakin sarakunan Isra'ila ko Yahuda.
\v 23 Amma a shakara ta goma sha takwas ta sarki Yosiya an yi bikin wannan Ƙetarewa na Yahweh a Yerusalem.
\s5
\v 24 Yosiya kuwa ya kori dukkan mabiya waɗanda ke magana da matattu ko ruhohi. Ya kuma kori kawunan gidaje da gumaka da dukkan abubuwan banƙyama da ake gani a Yahuda da Yerusalem, saboda a ka'idantar da kalmomin dokokin da aka rubuta a littafin da Hilkiya firist ya samo a gidan Yahweh.
\v 25 Kafin Yosiya, ba a yi wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Yahweh da dukkan zuciyarsa da dukkan ransa da dukkan ƙarfinsa ba, wanda kuma ya bi dukkan dokokin Musa. Ba a kuwa yi wani sarki kamar Yosiya ba a bayansa.
\s5
\v 26 Duk da haka, Yahweh bai juya baya daga zafin fushinsa ba, wanda ya yi gãba da Yahuda saboda dukkan abubuwan da Manasse ya yi na sashi shi ya yi fushi.
\v 27 Saboda haka Yaweh ya ce, "Zan kuwa kawar da Yahuda daga fuskata, kamar yadda na tsige Isra'ila, zan kuma jefar da birnin da na zaɓa, Yerusalem, da kuma gidan da nace, 'Sunana zai kasance a wurin.'"
\s5
\v 28 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yosiya da dukkan abubuwan da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 29 A kwanakinsa, Fir'auna Neko, sarkin Masar, ya je yaƙi da sarkin Asiriya a kogin Yuferatis. Sarki Yosiya ya je ya sami Neko a yaƙi, sai Neko ya kashe shi a Megiddo.
\v 30 Sai baran Yosiya ya ɗauke shi a karusa daga Megiddo, ya taho da shi Yerusalem ya bizne shi a nasa kabarin. Sa'an nan Mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoahaz ɗan Yosiya, suka shafa masa mai, suka mai da shi sarki a madadin mahaifinsa.
\s5
\v 31 Yehoahaz yana da shekaru ashirin da uku lokacinin da ya fara mulki, ya yi mulkin shekaru uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hamutal; ita ɗiyar Irmiya na Libna ne,
\v 32 Yehoahaz ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh, kamar dukkan yadda kakaninsa suka yi.
\v 33 Fir'auna Neko ya ɗaure shi a Ribla, a ƙasar Hamat, saboda kar ya yi mulkin Yerusalem. Sa'an nan Neko ya yi wa Isra'ila tarar talanti ɗari na azurfa da talanti ɗaya na zinariya.
\s5
\v 34 Fir'auna Neko ya sa Eliyakim ɗan sarki Yosiya ya zama sarki a madadin mahaifinsa, sai ya canza masa suna zuwa Yehoiakim. Amma ya ɗauki Yehoahaz zuwa Masar har Yehoahaz ya mutu a can.
\v 35 Yehoiakim ya biya azurfa da zinariya ga Fir'auna. Don ya iya yin yadda Fir'auna yake so, Yehoiakim ya sa ƙasar biyan haraji kuma ya tilasta kowanne mutum daga cikin mutanen ƙasar ya biya da azurfa da zinariya bisa ga yanayin tsarinsu.
\s5
\v 36 Yehoiakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya fara mulki, kuma ya yi mulki na shekara goma sha ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Zebida ɗiyar Fediya na Ruma.
\v 37 Yehoiakim ya yi akin mugunta a fuskar Yahweh, kamar yadda kakaninsa suka yi.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 A kwanakin Yehoiakim, Nebukadnezza sarkin Babila ya kai wa Yahuda hari; Yehoiakim ya zama bawansa na shekaru uku. Sa'an nan Yehoiakim ya juya ya tayar wa Nebukadnezza.
\v 2 Yahweh ya aiko da Yehoiakim, maharan Kaldiyawa da Aramiyawa da Mowabawa da Amoniyawa, ya aike su gãba da Yahuda su hallakar da shi. Wannan ya zo dai-dai ne da maganar Yahweh da aka faɗa ta barorinsa annabawa.
\s5
\v 3 Hakika ta bakin Yahweh ne wannan ya zo ga Yahuda, ya cire su daga fuskarsa, saboda laifofin Manasse, dukkan abin da ya yi,
\v 4 kuma saboda zub da jinin bayin Allah da ya yi, gama ya cika Yerusalem da jinin adalai, Yahweh bai yi niyar gafarta hakan ba.
\s5
\v 5 Game da sauran zantuttukan da suka shafi Yehoiakim, da dukkan abubuwan da ya yi, ba a rubuce suke a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 6 Yehoiakim ya yi barci tare da kakaninsa, sai Yehoiacin ɗansa ya zama sarki a madadinsa.
\s5
\v 7 Sarkin Masar bai sake fita ƙasarsa ya kai wa wani hari ba, saboda sarkin Babila ya ƙwato dukkan ƙasashen da ke ƙarƙashin sarkin Masar, daga rafin Masar har zuwa kogin Yuferatis.
\s5
\v 8 Yehoiacin ya na da shekaru goma sha takwas yayin da ya fara mulki a Yerusalem; ya yi mulkin wata uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Nehushta; ɗiyar Elnatan na Yerusalem.
\v 9 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abubuwan da mahaifinsa ya yi.
\s5
\v 10 A lokacin nan ne sojojin Nebukadnezza sarkin Babila suka kai wa Yerusalem hari, suka kewaye birnin da yaƙi,
\v 11 Nebukadnezza ya zo birnin yayin da sojojinsa ke kewaye da shi,
\v 12 sai Yehoiacin sarkin Yahuda ya je ya tari sarkin Babila, shi da mahaifiyarsa da barorinsa da 'ya'yansa da hafsoshinsa. Sarkin Babila ya kama shi a shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa.
\s5
\v 13 Nebukadnezza ya ɗauki dukkan abubuwa masu daraja na gidan Yahweh, da waɗanda ke fãdar sarki. Ya farfashe dukkan tasoshin zinariyar da sarki Suleman ya yi a haikalin Yahweh, kamar yadda Yahweh ya ce zai faru.
\v 14 Ya ɗauki 'yan zuwa zaman talala daga dukkan Yerusalem, da dukkan shugabanin da dukkan mayaƙa da kamammu dubu goma da dukkan 'yan fasaha da maƙera. Babu wanda aka bari sai fakirai na ƙasar.
\s5
\v 15 Nebukadnezza ya ɗauki Yehoiacin zuwa zaman talala a Babila. da kuma mahaifiyar sarki da matansa da hafsoshi da manyan mazajen ƙasar. Ya ɗauke su zuwa zaman talala daga Yerusalem zuwa Babila.
\v 16 Dukkan mayaƙa dubu bakwai da masu sana'a da maƙera dubu ɗaya dukkansu ƙarfafa ne da suka isa zuwa yaƙi - sarkin Babila ya kawo waɗannan mutanen ga zaman talala a Babila.
\v 17 Sarkin Babila ya sa Mataniya, ɗan'uwan mahaifin Yehoiacin, ya zama sarki a madadinsa ya kuma canza masa suna zuwa Zedekiya.
\s5
\v 18 Zedekiya yana da shekaru ashirin da ɗaya yayin da ya fara mulki; ya yi mulki shekaru goma sha ɗaya a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Hamutal; ita ɗiyar Irmiya na Libna ne.
\v 19 Ya yi aikin mugunta a gaban Yahweh; ya yi dukkan abin da Yehoiakim ya yi.
\v 20 Ta dalilin fushin Yahweh ne, dukkan waɗannan abubuwan suka faru a Yerusalem da Yahuda, har sai ya kore su daga gare shi. Sa'an nan Zedekiya ya yi tayar da gãba da sarkin Babila.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Sai ya zamana a shekara na tara a mulkin Zedekiya, a wata na goma, a rana ta goma ga watan, Nebukadnezza sarkin Babila ya zo da dukkan sojojinsa gãba da Yerusalem. Ya yi sansani kusa da ita, ya gina kagarai kewaye da ita.
\v 2 Saboda haka aka kewaye birnin da yaƙi har shekara goma sha ɗaya na mulkin Zedekiya.
\v 3 A rana ta tara na watan huɗu na shekarar, yunwa ta yi tsanani a birnin har babu abinci domin mutanen ƙasar.
\s5
\v 4 Sa'an nan aka shigo birnin, sai dukkan masu yaƙin suka gudu ta ƙofar dake tsakanin katangu biyu, ta lambun sarki, ko da shike Kaldiyawa suna kewaye da birnin. Sarki ya yi ta wajen Araba.
\v 5 Amma sojojin Kaldiyawa suka yi fakon sarki Zedekiya har suka mamaye shi a filayen kwarin Kogin Yodan kusa da Yeriko. Dukkan sojinsa kuwa suka warwatsu daga gare shi.
\s5
\v 6 Suka kamo sarkin suka kai shi gun sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.
\v 7 Game da 'ya'yan Zedekiya maza kuwa, an yayyanka su a gabansa. Sa'annan ya ƙwaƙule masa idanunsa, ya ɗaure shi da sarƙa ta tagulla, ya kai shi Babila.
\s5
\v 8 Yanzu kuwa a wata na biyar, a rana ta bakwai ga watan, wanda ke a shekara ta goma sha tara ta mulkin Nebukadnezza sarkin Babila, Nebuzaradan, baran sarkin Babila da kuma shugaban masu gadin sarki, ya zo Yerusalem.
\v 9 Ya ƙona gidan Yahweh da fãdar sarki da dukkan gidajen Yerusalem; ya kuma ƙone dukkan manyan gine-ginen birnin.
\v 10 Game da garun kewaye da Yerusalem kuwa, dukkan sojojin Babilan da ke ƙarƙashin shugaban sun rurrushe su.
\s5
\v 11 Game da sauran mutanen da aka bari a birnin da waɗanda suka tafi wurin sarkin Babila, da sauran ragowar mutanen - Nebuzaradan, shugaban masu gadin sarki, ya ɗauke su zuwa zaman talala.
\v 12 Amma shugaban masu gadin sarki ya bar waɗansu matalautan ƙasar su ci gaba da aikin lambuna da filaye.
\s5
\v 13 Game da ginshiƙan tagulla da ke gidan Yahweh, da dakalansu da takwanniyar ruwa da ke cikin gidan Yahweh, Kaldiyawa sun ragargaza su su ka kuma ɗauke tagullan su ka kai su Babila.
\v 14 Kaldiyawan kuma su ka kwashe tukwane da manyan cokula da hantsuka da cokula da dukkan tasoshin tagulla waɗanda firistoci ke aiki da su a haikali - Kaldiyawa sun tafi da su dukka.
\v 15 Tukwanen da ake amfani da su domin cire tokar bagaden darurruka da aka yi da zinariya da azurfa - shugaban masu gadin sarkin ya kwashe su dukka ya tafi da su.
\s5
\v 16 Ginshiƙan biyu kuwa da takwanniyar ruwa da dakalan da Suleman ya yi domin gidan Yahweh suna ƙunshe da tagulla da yawa da ba a iya aunawa.
\v 17 Tsawon ginshiƙi na farkon kamu goma sha takwas ne. dajiyar tagulla akan ginshiƙin kamu uku ne, wadda aka kewaye da raga da rumman, kuma dukka da tagulla aka yi su. Ɗaya ginshiƙin da ragarsa na dai-dai da ta farkon.
\s5
\v 18 Shugaban masu gadin sarkin ya ɗauki Serayiya babban firist da Zefaniya da firist na biyun da mutun uku masu tsaron ƙofa.
\v 19 Daga birnin kuwa ya ɗauki waɗansu manyan sojoji da mashawartan sarki guda biyar waɗanda ba a tafi da su ba duk ya kamo ya tsare su don kada su gudu. Ya kuma kamo babban sojan da ke shugabancin ɗaukan sojoji aiki, tare da mutum sitin kuma da ke cikin birnin.
\s5
\v 20 Sa'an nan Nebuzaradan, shugaban masu gadin sarki, ya ɗauko su ya kai wa sarkin Babilan a Ribla.
\v 21 Sarkin Babila ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Ta haka Yahuda ya bar ƙasarsa zuwa zaman bauta.
\s5
\v 22 Game da mutanen da suka rage a ƙasar Yahuda, waɗanda Nebukadnezza sarkin Babilan ya bari, ya sa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, shugabancin su,
\v 23 Yanzu kuwa da dukkan shugabanin sojojin, su da mazajensu, suka ji sarkin Babila ya maida Gedaliya gwamna, sai suka je wurin Gedaliya a Mizpa. Waɗannan mazajen su ne Isma'il ɗan Netaniya da Yohanan ɗan Kariya da Serayiya ɗan Tanhumet Banetofate da Ya'azaniya ɗan Ma'akatite - su da mazajensu.
\v 24 Gedaliya ya yi amana da su da mazajensu, ya ce da su, "Kada ku ji tsoron shugabanin Kaldiyawa. Ku zauna a ƙasar ku yi wa sarkin Babilan hidima, kuma kome zai yi maku kyau."
\s5
\v 25 Amma ya zamana dai a watan bakwai Isma'il ɗan Netaniya ɗan Elishama, daga iyali mai martaba, ya zo ya da mutum goma ya kai wa Gedaliya hari. Gedaliya ya mutu, tare da mutum goma na Yahuda da Babilonawan da ke tare da shi a Mizfa.
\v 26 Sa'an nan dukkan mutanen, daga mafi ƙanƙanta zuwa masu muhiminci, da dukkan shugabani sojojin, suka tashi suka tafi Masar, saboda suna tsoron Babilonawan.
\s5
\v 27 Ya zamana daga baya a shekara ta talatin da bakwai na zaman talalar Yahoiacin sarkin Yahuda, a wata na goma sha biyu, sai Awel Marduk sarkin Babilan ya saki Yahoiacin sarkin Yahuda daga kurkuku. Wannan ya faru ne a shekarar da Awel- Marduk ya fara mulki.
\s5
\v 28 Ya yi maganar kirki da shi ya kuma ba shi wurin zaman da ya fi na waɗansu sarakunan da ke tare da shi a Babila.
\v 29 Awel-Marduk ya cire wa Yahoiacin tufafin kurkuku, har Yahoiacin ya ci gaba da liyafa a teburin sarki dukkan rayuwarsa.
\v 30 Ana kuwa biyansa albashin abinci dukkan kwanakin rayuwarsa.