ha_ulb/11-1KI.usfm

1607 lines
120 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 1KI
\ide UTF-8
\h Littafin Sarakuna Na Ɗaya
\toc1 Littafin Sarakuna Na Ɗaya
\toc2 Littafin Sarakuna Na Ɗaya
\toc3 1ki
\mt Littafin Sarakuna Na Ɗaya
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Sa'ad da Sarki Dauda ya tsufa sosai, suka lulluɓe shi da barguna amma bai ji ɗumi ba.
\v 2 Sai bayinsa suka ce, "Bari mu samo wa shugabanmu sarki wata budurwa domin ta yi wa sarki hidima ta kula da shi. Ta kwanta a damatsen shugabanmu sarki domin ya ji ɗumi."
\s5
\v 3 Suka bincika cikin dukkan lungunan Isra'ila, sai suka samo Abisha Bashunamiye su ka kawo ta wurin sarki. Budurwar kyakkyawa ce ƙwarai.
\v 4 Ta yi wa sarki hidima ta lura da shi, amma sarkin bai kwana da ita ba.
\s5
\v 5 A wannan lokacin Adonija ɗan Haggit ya ɗaukaka kansa, cewa, "Ni zan zama sarki." Ya shirya wa kansa karusai da mahaya, mazaje hamsin su wuce gabansa.
\v 6 Babansa bai dame shi ba da cewa, "Meyasa ka yi wannan ko wancan?" Adonija ma kyakkyawan mutum ne ƙwarai, shi aka haifa bayan Absalom.
\s5
\v 7 Ya haɗa kai da Yowab ɗan Zeruyiya da Abiyata firist. Suka bi Adonija suka taimaka masa.
\v 8 Amma Zadok firist da Benayiya ɗan Yehoiada da Natan annabi da Shimai da Reyi da jarumawan da ke tare da Dauda ba su bi Adonija ba.
\s5
\v 9 Adonija ya yi hadayar tumaki da bijjimai da kiwatattun shanu kusa da dutsen Zohelet, wanda ke daura da En Rogel. Ya gayyaci dukkan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki da dukkan mazajen Yahuda da bayin sarki.
\v 10 Amma Natan annabi da Benayiya da mazajen Suleman ɗan'uwansa bai gaiyace su ba.
\s5
\v 11 Sai Natan ya yi wa Batsheba uwar Suleman magana, cewa, "Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba, kuma ba da sannin Dauda shugabanmu ba?
\v 12 Bari in ba ki shawara yanzu domin ki ceci ranki da na ɗanki Suleman.
\s5
\v 13 Ki je wurin sarki Dauda, ki ce, shugabana, ba ka yi rantsuwa ga baiwarka ba, cewa, "Babu shakka Suleman ɗanki shi ne zai yi sarauta bayana, ya zauna kan kursiyina ba?" Me ya sa Adonija ke mulki?'
\v 14 Sa'ad da ki ke magana da sarki, zan zo in tabbatar masa da maganganunki."
\s5
\v 15 Sai Batsheba ta tafi ɗakin sarki. Sarki ya tsufa ƙwarai, Abisha Bashunamiya tana yi wa sarki hidima.
\v 16 Batsheba ta sunkuya ta kwanta a gaban sarki. Sarki ya ce da ita, "Me ki ke so?"
\v 17 Ta ce da shi, "Shugabana, ka rantsewa baiwarka da Yahweh Allahnka, cewa, 'Babu shakka Suleman ɗanki, shi zai yi mulki baya na, shi zai zauna a kursiyina?'
\s5
\v 18 To yanzu ka ga, Adonija ne sarki, kai kuma shugabana sarki ba ka sani ba.
\v 19 Ya yi hadaya da bijjimai da kiwatattun shanu da tumaki da yawa, kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki da Abiyata firist da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Suleman bawanka ba.
\s5
\v 20 Game da kai shugabana sarki, dukkan idanun Isra'ila kai suke kallo, suna jira ka ce da su ga wanda zai yi mulki a bayana, shugabana.
\v 21 Idan kuwa ba haka ba, zai zama bayan da shugana sarki ya yi barci tare da ubanninsa, ni da ɗana Suleman za a mai da mu kamar 'yan ta'adda."
\s5
\v 22 Tana cikin magana da sarki, sai Natan annabi ya shigo.
\v 23 Barori suka ce da sarki, "ga Natan annabi ya zo." Sa'ad da ya shigo gaban sarki, ya kwanta da fukarsa a ƙasa a gaban sarki.
\s5
\v 24 Natan yace, "Shugabana sarki, ka ce Adonija zai yi mulki bayana, shi zai zauna kan kursiyina ne?'
\v 25 Gama ya tafi yau ya yi hadaya da bijjimai da kiwattatun shanu da tumaki da yawa, kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki da shugaban sojoji da Abiyata firist. Suna ci suna sha a gabansa, suna cewa, 'ranka ya daɗe sarki Adonija!'
\s5
\v 26 Amma ni, bawanka da Zadok firist da Benaiya ɗan Yehoiada da bawanka Suleman bai gayyace mu ba.
\v 27 Shugabana ya yi haka ba tare da ya gaya mana bayinka ba, wanda zai zauna a kan kursiyinsa?"
\s5
\v 28 Sai sarki ya amsa ya ce, "kira mani Batsheba ta dawo." Ta zo gaban sarki ta tsaya.
\v 29 Sarki ya yi alƙawari ya ce, "Da ran Yahweh wanda ya cece ni daga dukkan wahalhalu,
\v 30 kamar yadda na rantse maku da Yahweh, Allah na Isra'ila, cewa, 'Suleman ɗanki, shi zai yi mulki bayana, zai zauna kan kursiyna, zan yi haka yau."
\v 31 Sa'an nan sai Batsheba ta sunkuya da fuskarta a ƙasa ta kwanta gaban sarki ta ce, "Ranka ya daɗe shugabana, sarki Dauda!"
\s5
\v 32 Sarki Dauda yace, "A kira mani Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yahoiada." Sai su ka zo gaban sarki.
\v 33 Sarki ya ce, "ku tafi da barorin shugabanku, ku sa Suleman ya hau alfadarina ku kai shi Gihon.
\v 34 Bari Zadok firist da Natan annabi su shafe shi ya zama sarki akan Isra'ila su busa ƙaho su ce, 'Ranka ya daɗe sarki Suleman!'
\s5
\v 35 Sai ku biyo shi, ya zo ya zauna kan kursiyina; domin shi ne zai gaje ni. Na naɗa shi ya zama sarki bisa Isra'ila da Yahuda."
\v 36 Benayiya ɗan Yehoiada ya amsawa sarki ya ce, "Bari ya zama haka! Yahweh Allah na shugabana sarki, ya tabbatar da shi.
\v 37 Kamar yadda Yahweh ya kasance da shugabana sarki, bari ya kasance da Suleman, kursiyinsa ya ɗaukaka fiye da kursiyin shugabana sarki Dauda."
\s5
\v 38 Sai Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yehoiada da Keretawa da Feletiyawa suka je suka ɗora Suleman akan alfadarin Sarki Dauda; suka kawo shi Gihon.
\v 39 Zadok firist ya ɗauko ƙahon mai daga cikin rumfa ya shafe Suleman. Sa'an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka ce, "Ranka ya daɗe sarki Suleman."
\v 40 Sa'an nan dukkan mutane suka biyo shi suna busa sarewa suna farinciki da murna sosai, har ƙasa ta girgiza saboda ƙararsu.
\s5
\v 41 Adonija da bãƙinsa da ke tare da shi suka ji sa'ad da suka gama ciye-ciye. Sa'ad da Yowab ya ji ƙarar ƙahon ya ce, "Me ya sa a ke hargowa a cikin birni?"
\v 42 Yana cikin magana Yonatan ɗan Abiyata firist ya zo. Adonija yace, "Shiga, kai mai aminci ne ka kuma kawo labari mai daɗi."
\s5
\v 43 Yonatan yace da Adonija, "Shugabanmu sarki Dauda ya sa Suleman ya zama sarki,
\v 44 kuma sarki ya aiko shi tare da Zadok firist da Natan annabi da Benayiya ɗan Yehoiada da Keretawa da Feletiyawa. Sun sa Suleman ya hau alfadarin sarki.
\v 45 Zadok firist da Natan annabi sun shafe shi ya zama sarki a Gihon, sun taho daga can su na murna, saboda haka birni ya cika da hargowa. Wannan ita ce hayaniyar da ka ke ji.
\s5
\v 46 Kuma, Suleman yana zaune akan kursiyin mulki.
\v 47 Bayan haka, barorin sarki sun zo suna sawa sarki Dauda albarka suna cewa, 'Bari Allahnka ya sa sunan Suleman ya fi naka.' Sai sarki ya sunkuya akan gado.
\v 48 Sai sarki ya ce, 'Albarka ga Yahweh Allah na Isra'ila, da ya bada wanda zai zauna akan kursiyina yau, kuma idona yana gani.'"
\s5
\v 49 Sai dukkan bãƙin Adonija suka firgita. Suka tashi tsaye kowa ya bi hanyarsa.
\v 50 Adonija yana jin tsoron Suleman, ya je ya riƙe ƙahonin bagadi.
\v 51 Sai aka gaya wa Suleman cewa, Duba, Adonija yana jin tsoron sarki Suleman, gama gashi can ya na riƙe da ƙahonin bagadi, yana cewa, 'Bari sarki Suleman ya rantse mani cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba."'
\s5
\v 52 Suleman yace, "Idan zai nuna kansa mutumin kirki, ko gashin kansa ba zai faɗi a ƙasa ba, amma idan aka sami mugunta a wurinsa to zai mutu."
\v 53 Sarki Suleman ya aika mutane suka saukar da Adonija daga bagadi. Ya zo ya russana a gaban Suleman, Suleman ya ce da shi, "Tafi gidanka."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Sa'ad da ranar mutuwar Dauda ta gabato, ya umurci ɗansa, Suleman cewa,
\v 2 "ina bin hanyar dukkan duniya, ka ƙarfafa, ka nuna kanka namiji.
\v 3 Ka kiyaye dokokin Ubangiji Allahnka, ka yi tafiya cikin hanyoyinsa, ka kiyaye farillansa da dokokinsa da shawarwarinsa da alƙawaransa, kana kiyaye abin da da aka rubuta cikin dokokin Musa domin ka wadata cikin dukkan abin da ka ke yi, a dukkan inda ka nufa,
\v 4 domin Yahweh ya cika maganarsa wadda ya faɗi game da ni, cewa, 'Idan 'ya'yanka suka lura da tafarkinsu, suka yi tafiya a gabana da aminci da dukkan zuciyarsu da dukkan ransu, ba za ka rasa mutum akan kursiyin Isra'ila ba.'
\s5
\v 5 Ka san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi ma ni da abin da ya yi wa jami'an sojojin Isra'ila su biyu, Abna ɗan Ner da Amasa ɗan Yatar waɗanda ya kashe. Ya zubar da jinin yaƙi cikin salama, ya sa jinin yaƙi akan ɗamarar da ke ƙugunsa da takalman da ke ƙafafunsa.
\v 6 Ka yi da Yowab bisa ga hikimar da ka koya, amma kada ka bari furfurarsa ta tafi kabari cikin salama.
\s5
\v 7 Duk da haka, ku yi mutunci ga 'ya'yan Barzilai Bagilide, ku bar su su zauna a cikinku su ci a teburinka, gama sun je wurina sa'ad da na gudu daga wurin ɗan'wanka Absolom.
\s5
\v 8 Duba, Shimai ɗan Gera mutumin Benyamin ta Bahurim yana tare da ku, wanda ya zage ni, ya wulaƙanta ni, ya zazzage ni ranar da na je Mahanayim. Ya zo ya tarbe ni a Yodan, na rantse masa da sunan Yahweh cewa, 'Ba zan kashe ka da takobi ba.'
\v 9 Kada ka bar shi ya tafi ba tare da ka hore shi ba. Kana da hikima ka san yadda za ka yi da shi. Ka sa furfurarsa ta faɗi cikin jini."
\s5
\v 10 Sa'an nan Dauda ya yi barci tare da ubanninsa aka bizne shi a birnin Dauda.
\v 11 Dauda ya yi mulki a Isra'ila shekaru arba'in, shekaru bakwai ya yi mulki a Hebron, a Yerusalem kuma ya yi mulki shekaru talatin da uku.
\v 12 Suleman ya zauna akan kursiyin Dauda ubansa, mulkinsa kuwa ya kahu da ƙarfi ƙwarai.
\s5
\v 13 Sai Adonija ɗan Haggit ya zo wurin Batsheba uwar Suleman. "Ta ce da shi cikin salama ka zo?" Ya ce, cikin salama ƙwarai."
\v 14 Ya ce, ina da wani abu da zan faɗa maki." Sai ta ce, "To ka faɗi."
\v 15 Adonija yace, "Kin san mulkin nawane, dukkan Isra'ila sun yi zaton ni zan zama sarki. Amma abubuwa sun canza, an ba ɗan'uwana sarauta, kuma wannan daga Yahweh ne.
\s5
\v 16 Zan roƙi abu ɗaya a wurin ki, kada ki juya mani baya, Batsheba ta ce, "Ka faɗi."
\v 17 Ya ce, "Ki yi magana da Suleman sarki, na san ba zai ƙi jin maganar ki ba, ki ce da shi ya ba ni Abishag Bashunamiye ta zama matata.
\v 18 Batsheba ta ce, "Ya yi kyau, zan yi magana da sarki."
\s5
\v 19 Sai Batsheba ta je wurin sarki ta faɗa masa maganar da Adonija ya yi. Sarki ya je ya tarbe ta, ya russana a gabanta. Sa'an nan ya zauna a kan kursiyinsa kuma ya sa aka kawo wa mamar sarki kujera. Ta zauna a hannun damarsa.
\v 20 Ta ce da shi, "Zan roƙi wani ɗan abu daga wurinka, na sani ba za ka ƙi ba." Sai sarki ya ce, "Ki roƙa mama, ba zan ƙi ba."
\v 21 Ta ce, "Ka bari a ba Adonija ɗan'uwanka Abishag Bashunamiye ta zama matarsa."
\s5
\v 22 Sarki Suleman ya amsa ya ce da mamarsa, "Meyasa ki ka ce a ba Adonija Abishag Bashunamiye ta zama matarsa? Meyasa ba ki ce a ba shi mulkin ba kuma gama shi yayana ne - ne dai, domin Abiyata firist, ko domin Yowab ɗan Zeruya?"
\v 23 Sarki Suleman ya rantse da sunan Yahweh, ya ce, "Bari Allah ya yi mani fiye da haka, idan Adonija ba a bakin ransa ya faɗi wannan magana ba.
\s5
\v 24 Yanzu da ran Yahweh, wanda ya sa ni a kan kursiyin Dauda mahaifina, ya yi gida domina, babu shakka yau za a kashe Adonija."
\v 25 Sarki Suleman ya aiki Benayiya ɗan Yehoiada, ya nemi Adonija ya kashe shi.
\s5
\v 26 Sa'an nan sarki ya ce da Abiyata firist, ka tafi Anatot, ga gonakinka, kaima ka isa mutuwa, amma ba zan kashe ka a wannan lokaci ba, domin ka ɗauki akwatin Ubangiji Yahweh a gaban Dauda mahaifina, ka sha wahala kamar yadda mahaifina ya sha."
\v 27 Ta haka Suleman ya kori Abiyatar daga zama firist na Yahweh, domin maganar da Yahweh ya faɗi a Shilo game da gidan Eli ta cika.
\s5
\v 28 Sai maganar ta zo ga Yowab saboda ya goyi bayan Adonija, ko da ya ke bai goyi bayan Absolom ba. Sai Yowab ya gudu ya shiga rumfar Yahweh ya kama ƙahonin bagadi ya riƙe.
\v 29 Sai aka gaya wa Suleman sarki, cewa ga Yowab can cikin rumfar Yahweh, sai ya ce da Benayiya ɗan Yehoiada, "Je ka same shi ka kashe shi."
\s5
\v 30 To sai Benayiya ya zo rumfar Yahweh, ya ce masa, "Sarki ya ce, 'ka fito"' Yowab ya amsa ya ce, "A'a ni zan mutu a nan." Sai Benaiya ya koma ya gaya wa sarki, cewa, Yowab yace, Yana so ya mutu a kan bagadi."
\v 31 Sai sarki ya ce da shi, yi yadda ya faɗi. Kashe shi ka ɗauke shi, ka bizne domin a kawar da jinin da Yowab ya zubar ba dalili daga gidan mahaifina.
\s5
\v 32 Yahweh ya sa jininsa ya koma kansa, gama ya sami mutane biyu waɗanda sun fi shi, kuma sun fi shi sarki, ya kashe su da kaifin takobi. Wato Abna ɗan Na shugaban sojojin Isra'ila da Amasa ɗan Yeter shugaban sojojin Yahuda, ba tare da sanin mahaifina sarki Dauda ba.
\v 33 Bari jininsu ya dawo kan Yowab da zuriyarsa har abada. Amma ga Dauda da zuriyarsa da gidansa da kursiyinsa, bari salama daga Yahweh ta kasance har abada."
\s5
\v 34 Sai Benayiya ya je ya sami Yowab, ya far masa ya kashe shi. A ka bizne shi a gidansa cikin daji.
\v 35 Sarki ya sa Binayiya ɗan Yehoiada ya zama shugaban sojoji maimakon sa, ya kuma sa Zadok firist a gurbin Abiyata.
\s5
\v 36 Sai kuma sarki ya aika a ka kira Shimai, yace masa, "Ka gina gida domin kanka a cikin Yerusalem ka zauna nan, kada ka bar wurin ka je ko'ina.
\v 37 Duk randa ka fita ka wuce kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu. Kuma jininka zai koma kanka."
\v 38 Sai Shimai ya cewa sarki abin da ka faɗi ya yi kyau. Kamar yadda shugabana sarki ya faɗi, haka bawanka za ya yi." Daga nan Shimai ya zauna a Yerusalem kwanaki da yawa.
\s5
\v 39 Amma bayan shekaru uku, bayin Shemai guda biyu suka guda suka je wurin Akish ɗan Ma'aka, sarkin Gat. A ka gaya wa Shimai, cewa, duba, bayinka "biyu fa sun koma Gat."
\v 40 Sai Shimai ya tashi, ya sa sirdi a kan jakinsa, ya je wurin Akish a Gat neman bayinsa. Ya dawo da bayinsa daga Gat.
\s5
\v 41 Sa'ad da a ka gaya wa Suleman, cewa Shimai ya fita daga Yerusalem ya je Gat ya dawo,
\v 42 sarki ya aika a ka kira Shimai ya ce da shi, "Ba na sa ka yi rantsuwa da Yahweh ba na shaida maka, cewa, 'Ka sani duk randa ka bar nan ka je wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba.'? Ka ce mani, 'abin da ka faɗi ya yi kyau.'
\s5
\v 43 To meyasa ba ka cika alƙawarinka ga Yahweh ba, da abin da na umurce ka?"
\v 44 Sa'an nan sarki ya cewa Shimai, "Ka sani cikin zuciyarka dukkan muguntar da ka yi wa mahaifina Dauda. To Yahweh zai sa muguntarka ta koma kanka.
\s5
\v 45 Amma sarki Suleman zai zama mai albarka, kursiyin Dauda kuma zai tabbata a gaban Yahweh har abada."
\v 46 Sa'an nan sarki ya ummurci Benayiya ɗan Yehoiada. Ya fita waje ya kashe Shimai. Haka mulkin ya tabbata a hannun Suleman.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Suleman ya yi yarjejeniya da Fir'auna sarkin Masar ta dalilin aure. Ya ɗauko ɗiyar Fir'auna ya kawo ta cikin birnin Dauda har sai lokacin da ya gama ginin gidansa da gidan Yahweh da ganuwar da ta kewaye Yerusalem.
\v 2 Mutane suna ta miƙa hadayu a wurare masu bisa, saboda ba a gina gida saboda sunan Yahweh ba tukuna.
\v 3 Suleman ya nuna ƙauna ga Yahweh ta wurin tafiya cikin tafarkun mahaifinsa Dauda, sai dai shi ma ya miƙa hadaya kuma ya ƙona turare a wurare masu bisa.
\s5
\v 4 Sarki ya je Gibiyon domin ya miƙa hadaya a can, domin can akwai wurare masu bisa sosai. Suleman ya miƙa hadayu dubu a kan bagadi.
\v 5 Yahweh ya bayyana ga Suleman a cikin mafarki a Gibiyon, ya ce, "Ka roƙa! Mene ne zan ba ka?"
\s5
\v 6 Sai Suleman yace, "Ka nuna girman alƙawarinka da jinƙai da aminci ga bawanka, mahaifina Dauda, saboda ya yi tafiya a gabanka cikin aminci da tsarki da gaskiya cikin zuciyarsa. Ka riƙe wannan alƙawarin da aminci da ka ba shi ɗa wanda zai zauna a kan kursiyinsa yau.
\s5
\v 7 Yanzu fa, ya Yahweh Allahna, ka sa bawanka ya zama sarki a maimakon mahaifina Dauda, ko da ya ke ni ɗan yaro ne. Ban san yadda zan fita ko in shiga ba.
\v 8 Bawanka yana cikin tsakiyar mutane waɗanda ka zaɓa, mutane masu yawa da sun fi gaban a lisafta ko a ƙidaya su.
\v 9 Ka ba bawanka zuciya mai fahimta domin ya hukunta mutanenka, domin in gane bambanci tsakanin abu mai kyau da mummuna. Gama wane ne zai iya hukunta wannan jama'a taka mai yawa haka?"
\s5
\v 10 Wannan roƙo na Suleman ya gamshi Ubangiji.
\v 11 Sai Allah ya ce da shi, "Saboda ka roƙi wannan, ba ka roƙi tsawon rai ba, ko dukiya ko ran maƙiyanka ba, Amma ka roƙi fahimta domin ka gane gaskiya,
\v 12 duba zan yi maka dukkan abin da ka roƙa a gare ni. Na ba ka zuciya mai hikima da ganewa, ba a yi wani mai hikima kamar ka a dã ba, ba kuma za a sami wani mai hikima kamar ka ba a nan gaba bayanka.
\s5
\v 13 Kuma na ba ka har ma abin da ba ka roƙa ba, dukiya da martaba, yadda ba za a sami wani kamar ka ba a cikin sarakuna dukkan kwanakin ranka.
\v 14 Idan ka yi tafiya cikin hanyoyina da farillaina da dokokina kamar yadda Dauda mahaifinka ya yi tafiya, zan haskaka kwanakinka."
\s5
\v 15 Sai Suleman ya farka, ashe mafarki ya yi. Ya zo Yerusalem ya tsaya a gaban akwatin alƙawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa da na salama kuma ya yi liyafa domin dukkan bayinsa.
\s5
\v 16 Sai ga waɗansu mata biyu karuwai suka zo gabansa suka tsaya.
\v 17 Sai ɗaya matar ta ce, "Ya shugabana, ni da wannan matar muna zama a gida ɗaya, ni da ita muka haihu a gidan.
\s5
\v 18 Bayan na haihu da kwana uku, wannan matar kuma sai ta haihu. muna tare. Ba kowa tare da mu sai mu biyu a gidan.
\v 19 Sai ɗan wannan matar ya mutu cikin dare saboda ta kwanta a kansa.
\v 20 Sai ta tashi cikin tsakiyar dare ta ɗauke ɗana daga kusa da ni, domin baiwarka ta yi barci, ta kwantar da shi a ƙirjinta, sai ta kwantar da nata mataccen ɗan a ƙirjina.
\s5
\v 21 Sa'ad da na tashi da safe domin in shayar da ɗana sai na ga ya mutu. Amma da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ba ɗana ba ne wanda na haifa."
\v 22 Sa'an nan sai ɗaya matar ta ce, "Ba haka ba ne, ɗan mai rai nawa ne ke kuma mataccen ne naki." Sai ɗaya matar ta ce, "A'a mataccen ne naki mai ran kuma shi ne ɗana." Haka suka yi ta magana a gaban sarki.
\s5
\v 23 Daga nan sarki yace, "Ke kin ce, "Wannan ɗana ne mai ran, kuma naki ne mataccen,' ɗayar kuma ta ce, 'A'a, ɗanki shi ne mataccen, ɗana kuma shi ne mai ran."'
\v 24 Sai sarki yace, "Ku kawo mani takobi." Sai aka kawo wa sarki takobi.
\v 25 Daga nan sarki ya ce, "Ku raba ɗan mai rai kashi biyu, ku ba wannan mata rabi, rabi kuma ga ɗayar."
\s5
\v 26 Sai ɗaya matar wadda ɗanta ne ya ke da rai, ta yi magana ta ce da sarki, gama zuciyarta ta cika da tausayi saboda ɗanta, ta ce, "Aiya, shugabana, a ba ta ɗan mai rai kada a kashe shi." Amma ɗaya matar ta ce, "Ba zai zama naki ko nawa ba. A raba shi."
\v 27 Sai sarki ya yi magana ya ce, "Ku ba da ɗan mai rai ga matar ta farko, kada ku kashe shi, ita ce mahaifiyarsa."
\v 28 Sa'ad da dukkan Isra'ila suka ji wannan hukunci, suka ji tsoron sarki, saboda sun ga hikimar Yahweh na tare da shi domin yanke hukunci.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Suleman shi ne sarki a bisa dukkan Isra'ila.
\v 2 Waɗannan su ne jami'ansa: Azariya ɗan Zadok shi ne firist.
\v 3 Elihoref da Ahija 'ya'yan Shisha su ne magatakarda, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci.
\v 4 Benayiya ɗan Yehoiada shi ne shugaban sojoji. Zadok da Abiyata su ne firistoci.
\s5
\v 5 Azariya ɗan Natan shi ne shugaban ma'aikata. Zabud ɗan Natan shi ma firist ne kuma abokin sarki.
\v 6 Ahisha shi ne sarkin gida. Adoniram ɗan Abda shi ne shugaban masu aikin ƙarfi.
\s5
\v 7 Suleman ya na da jami'ai goma sha biyu a dukkan Isra'ila waɗanda su ke tanada abinci domin sarki da mutanen gidansa. Kowanne mutum zai kawo abincin wata ɗaya a shekara.
\v 8 Ga sunayensu: Ben Hur shi ne mai kula da tudun Ifraim;
\v 9 Ben Deker shi ne a Makaz da Sha'albim da Bet Shemesh da Elon Bet Hanan;
\v 10 Ben-Hesed a Arubbot (shi a ka damƙawa Sokoh da dukkan ƙasar Hefa);
\s5
\v 11 Ben Abinadab shi ne cikin dukkan Nafot Dor (Tafat ɗiyar Suleman ita ce matarsa);
\v 12 Ba'ana ɗan Ahilud ya na cikin Ta'anak da Megiddo da dukkan Bet Shan, wato kusa da Zaretan gangaren Yeziriyel, daga Bet Shan zuwa Abel Meholah har zuwa ɗaya gefen na Yokmiyam;
\v 13 Ben Geber cikin Ramot Giliyad (shi aka danƙawa garuruwan Ja'ir ɗan Manasse waɗanda ke cikin Giliyad yankin Argob na wanda ke cikin Bashan ma nasa ne, manyan birane sittin masu ƙofofin jan ƙarfe);
\v 14 Abinadab ɗan Iddo cikin Mahaniyam;
\s5
\v 15 Ahima'az cikin Naftali (kuma ya auri Basemat ɗiyar Suleman ta zama matarsa);
\v 16 Ba'ana ɗan Hushai cikin Asha da Bi'alot;
\v 17 Yehoshafat ɗan Faruya cikin Issaka;
\s5
\v 18 Shimei ɗan Ela, cikin Benyamin;
\v 19 da Geber ɗan Uri cikin ƙasar Giliyad, da ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da Og sarki Bashan, kuma shi ne kaɗai jami'in da ke cikin ƙasar.
\s5
\v 20 Yawan Yahuda da Isra'ila yana kama da yashin teku. Su na ci suna sha suna jin daɗi.
\v 21 Suleman ya yi mulki kan dukkan mulkoki tun daga Kogi har zuwa ƙasar Filistiyawa da iyakar Masar. Suna bautawa Suleman suna kawo masa gaisuwa dukkan kwanakinsa.
\v 22 Abincin gidan Suleman na rana ɗaya shi ne bahu talatin na niƙaƙƙen gari da kuma tsaba bahu sittin,
\v 23 da bijimai masu ƙiba guda goma da shanu guda ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari, banda barewa da gadã da namijin barewai, da kaji masu mai.
\s5
\v 24 Gama shi ne ya ke mulkin dukkan yankin da ke hayin Kogi, tun daga Tifsa har zuwa Gaza, a bisa dukkan sarakunan da ke hayin Kogi, kuma yana da salama a kowanne gefe.
\v 25 Yahuda da Isra'ila sun sami tsaro har kowanne mutum yana zuwa gonarsa ta inabi da ta ɓaure, tun daga Dan zuwa Biyasheba a dukkan kwanakin Suleman.
\s5
\v 26 Suleman yana da ɗakunan dawakai dubu arba'in domin karusansa, da masu hawan dawakai mutum dubu goma sha biyu.
\v 27 Waɗannan jami'ai suna tanado abinci domin sarki Suleman da dukkan wanda ya zo ya ci a teburin sarki, kowanne mutum da watansa, ba su bari an rasa komai ba.
\v 28 Kuma suna kawo hatsi da ciyawa saboda dawakan da suke jan karusai, kowanne mutum bisa ga iyawarsa.
\s5
\v 29 Allah ya ba Suleman ƙasaitacciyar hikima da fahimta, faɗin ganewarsa yana kama da yashin da ke bakin teku.
\v 30 Hikimar Suleman ta fi ta dukkan mutanen gabas da dukkan hikimar Masar.
\v 31 Hikimarsa ta fi ta dukkan mutane - ya fi Etan Ba-ezrahi hikima harma da Heman da Kalkol da Darda 'ya'yan Mahol - ya zama sananne a dukkan al'umman da ke kewaye.
\s5
\v 32 Ya faɗi misalai dubu uku, ya yi waƙoƙi dubu da biyar.
\v 33 Ya yi bayani a kan tsire-tsire da itacen sidar da ke Lebanon har zuwa waɗanda suke fitowa a jikin bangon ɗaki. Ya yi bayani a kan namun daji da tsuntsaye da kifaye.
\v 34 Mutane sukan zo daga wurare daban-daban domin su ji hikimar Suleman. Sukan zo daga wurin dukkan sarakunan da suka ji hikimar Suleman.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Hiram sarkin Taya ya aiki barorinsa wurin Suleman saboda ya ji an naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa; gama Hiram mai ƙaunar Dauda ne.
\v 2 Suleman ya aika da magana zuwa ga Hiram, cewa,
\v 3 "Ka sani mahaifina Dauda bai iya gina gida domin Yahweh Allansa ba, saboda yaƙe-yaƙen da suka kewaye shi, gama a lokacinsa Yahweh na ta sa abokan gabarsa a ƙarƙashin tafin sawunsa.
\s5
\v 4 Amma yanzu, Yahweh ya ba ni hutawa a kowanne gefe. Ba abokin gãba kuma babu annoba.
\v 5 To yanzu na yi niyya in gina haikali domin sunan Yahweh Allahna, kamar yadda Yahweh ya yi magana da mahaifina Dauda cewa, 'Ɗanka wanda zan sa a kan kursiyin mulki ya gaje ka, shi ne zai gina haikali domin sunana.'
\s5
\v 6 To yanzu sai ka ba da umurni a saro mani itacen sida daga Lebanon. Bayina za su haɗu da bayinka, kuma zan biya bayinka dai-dai bisa ga abin da ka yarda da shi. Domin ka san a cikin mu ba wanda ya iya yankan katako kamar Sidoniyawa."
\s5
\v 7 Lokacin da Hiram ya ji maganar Suleman, ya yi murna ƙwarai da gaske, ya ce, "Bari albarka ta kasance ga Yahweh yau, saboda ya ba Dauda ɗa mai hikima a kan jama'arsa mai girma."
\v 8 Hiram ya aika da magana zuwa ga Suleman, cewa, "Na ji saƙon da ka aiko wurina. Zan ba ka dukkan katakon sida da na fir yadda ka ke bukata.
\s5
\v 9 Bayina za su kawo itatuwan daga Lebanon zuwa teku, zan sa a ɗaɗɗaure su yadda za a iya sawo su a teku yadda ka ke so in yi, zan sa a yayyanka su domin ka ɗauko. Zan so ka bada abinci domin iyalin gidana.
\s5
\v 10 Haka Hiram ya ba Suleman dukkan katakon sida da fir yadda ya bukata.
\v 11 Suleman ya ba Hiram bahu dubu ashirin na alkama da mai wanda a ka tace garwa ashirin domin abincin gidansa, haka Suleman ya ba Hiram shekara biye da shekara.
\v 12 Yahweh ya ba Suleman hikima, kamar yadda ya yi alƙawari. Salama ta kasance tsakanin Suleman da Hiram, suka ƙulla amana.
\s5
\v 13 Sarki Suleman ya sa wa Isra'ilawa aikin dole. Mutanen da a ka sa aikin dolen sun kai dubu talatin.
\v 14 Ya aika su Lebanon, mutum dubu goma an sa kowanne wata, wata ɗaya suna Lebanon, wata biyu kuma su na gida. Adoniram ya shugabanci waɗanda a ka sa su yi aikin dole ɗin.
\s5
\v 15 Suleman yana da mutum dubu saba'in masu ɗaukar kaya, dubu takwas da kuma masu saro dutse cikin tsaunuka,
\v 16 ban da haka Suleman yana da mutum 3,300 jami'ai ne na ma'aikata kuma masu duba ma'aikata.
\s5
\v 17 Bisa ga ummurnin sarki, suka sassaƙo manyan duwatsu masu ƙwari domin a kafa tushen haikali.
\v 18 Haka masu gini na wajan Suleman da na wajan Hiram da Gebalawa suka saro katakan suka shirya su tare da duwatsun domin ginin haikali.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Suleman ya fara gina haikalin Yahweh. Hakan ya faru a shekara ta 480 bayan dawowar 'ya'yan Isra'la daga Masar, a cikin shekara ta huɗu ta mulkin Suleman a bisa Isra'ila cikin watan Zif wato wata na biyu.
\v 2 Haikalin da Sarki Suleman ya gina wa Yahweh, ratarsa kamu sittin ne, faɗinsa kamu ashirin ne, tsawonsa kuma kamu talatin ne.
\s5
\v 3 Ratar shirayin da ke ƙofar haikalin kamu ashirin ne, dai-dai suke da faɗin haikalin, a gaban haikalin kuma ta kai kamu goma.
\v 4 Ya yi wa gidan tagogi waɗanda faɗinsu daga ciki ya fi daga waje.
\s5
\v 5 Ya gina ɗakuna kewaye da ɗakin taro, ɗakuna sun kewaye ɗakuna na ciki da na waje. Ya gina ɗakuna a kowanne gefe.
\v 6 Bene na can ƙasa kamu biyar ne faɗinsa, na tsakiya kuma kamu shida ne a faɗi, na uku kuma kamu bakwai ne faɗinsa. Domin a kewaye da bangon gidan ya yi matokarai a bangon gidan a kowanne gefe domin kada a kafa wani abu a bangon gidan.
\s5
\v 7 An gina gidan da sassaƙaƙƙun duwatsun da a ka shiryo a mahaƙar duwatsu. Sa'adda a ke ginin gidan ba a ji ƙarar gatari ko guduma ba.
\v 8 A fuskar kudu ta haikalin an yi wurin shigowa daga ƙasa, a ka yi matakalu suka yi sama zuwa tsakiya, suka tafi har zuwa hawa na uku.
\s5
\v 9 Haka Suleman ya gina haikalin ya gama shi; ya rufe gidan da matokarai da katakai na sida.
\v 10 Ya yi ɗakuna a jikin ɗakunan taro na haikali, kowanne tsawonsa kamu biyar ne; a ka jingina su jikin gidan da katakai na sida.
\s5
\v 11 Sai maganar Yahweh ta zo ga Suleman, cewa,
\v 12 "Game da gidan da ka ke ginawa, idan ka kiyaye farillaina ka yi adalci, ka kiyaye dokokina ka yi tafiya a cikin su, sa'an nan zan tabbatar maka da alƙawarin da na yi wa Dauda mahaifinka.
\v 13 Zan zauna cikin mutanen Isra'ila, ba zan yashe su ba."
\s5
\v 14 Haka Suleman ya gina gidan ya gama shi.
\v 15 Sa'an nan ya gina bangaye na ciki da falankai na sida. Ya rufe gidan da katakai tun daga ƙasa har sama, daɓen kuma ya rufe shi da falankai na fir.
\s5
\v 16 Daga bayan gidan ya gina waɗansu ɗakuna masu kamu ashirin da katakai na sida tun daga ƙasa har sama. Ya gina wani ɗaki can ciki, shi ne wuri mafi tsarki.
\v 17 Babban ɗakin, wato wuri mai tsarki wanda ke gaban wuri ma fi tsarki, tsawonsa kamu arba'in ne.
\v 18 Akwai itacen sida a gidan, wanda a ka sassaƙa shi kamar ƙwarya a buɗe da furanni. Dukka sida ne a ciki. Ba bu aikin duwatsu da ake gani a ciki.
\s5
\v 19 Suleman ya yi wani ɗaki can ciki domin a ajiye akwatin Yahweh a ciki.
\v 20 Ratar ɗakin na can ciki kamu ashirin ne, faɗinsa kamu ashirin tsawonsa ma kamu ashirin ne. Suleman ya shafe bangayen da zinariya tsantsa bagadin kuma ya rufe shi da itacen sida.
\s5
\v 21 Suleman ya shafe haikalin da zinariya tsantsa, ɗaki na can ciki kuma ya yi masa dajiya da zinariya, ya shafe gabansa da zinariya.
\v 22 Ciki dukka ya shafe shi da zinariya har sai da a ka gama haikalin dukka. Bagadi na ɗaki na can ciki kuma ya shafe shi da zinariya.
\s5
\v 23 Suleman ya yi sifofi biyu na kerubim da itacen zaitun, domin ɗaki na can ciki masu tsawon kamu goma.
\v 24 Kowanne fiffike na kerub ɗin tsawonsa kamu biyar ne. Ya zama daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan ya zama kamu goma kenan.
\v 25 Ɗayan kerub ɗin ma faɗin fiffikensa kamu goma ne. Dukkan kerubim ɗin dai-dai suke da juna ba wanda ya fi wani.
\v 26 Tsayin kerub ɗaya kamu goma ne haka kuma na ɗayan kerub ɗin.
\s5
\v 27 Suleman ya ajiye kerubim ɗin a ɗaki na can ciki. Suka buɗe fukafukansu na wannan ya taɓa wancan bango, na wancan kuma ya taɓa wancan bango. Fukafukansu suna taɓa juna a cikin wuri mafi tsarki.
\v 28 Suleman ya shafe kerubin ɗin da zinariya.
\s5
\v 29 Bangayen ɗakin an zane su da yatsun kerubim da ganyen dabino da buɗaɗɗun furanni tun daga ciki har waje.
\v 30 Ƙasan gidan Suleman ya shafe shi da zinariya tun daga ɗakuna na ciki har zuwa na waje.
\s5
\v 31 Ɗaki na ciki Suleman ya yi masa ƙofofin shiga da itacen zaitun. Dogaran ƙofar da ginshiƙansu suna da aiyanannun sassa guda biyar.
\v 32 Haka ya yi ƙofofi biyu na itacen zaitun, ya sa a ka zana kerubim da ganyen dabino da furanni buɗaɗɗu. Ya shafe su da zinariya, kuma ya yayyafa zinariya a kan kerubim ɗin da kuma ganyen dabinan.
\s5
\v 33 Ta haka Suleman ya yi wa haikalin ƙofofin shiga da itacen zaitun da aiyanannun sassa guda huɗu
\v 34 da ƙofofi biyu na itacen fir. Ɓangare biyu na wannan ƙofa a kan naɗe su haka ma ɓangare biyu na waccan ƙofa a kan naɗe su.
\v 35 Ya zana kerubim da ganyen dabino da furanni buɗaɗɗu a kansu, ya shafe zanen da zinariya dai-dai wa daida.
\s5
\v 36 Ya gina farfajiya ta ciki da layika guda uku da sassaƙaƙƙen dutse da ginshiƙai na sida.
\s5
\v 37 An kafa tushen gidan Yahweh a cikin shekara ta huɗu, a watan zif.
\v 38 Cikin shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul wato wata na takwas a ka gama gidan, yadda a ke so tsarinsa ya kasance duka. Suleman ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Suleman ya ɗauki shekaru goma sha uku yana ginin fadarsa.
\v 2 Ya gina fada ta jejin Lebanon. Tsawonta kamu ɗari ne, faɗinta hamsin ratarta kuma kamu talatin ne. Fadar an gina ta layi huɗu da ginshiƙai na sida da kalankuwa a kan ginshiƙan.
\s5
\v 3 An rufe gidan da sida wanda ya kwanta a kan kalankuwoyin. Kalankuwoyin kuma ginshiƙai sun tallabe su.
\v 4 Akwai kalankuwoyi arba'in da biyar, kowanne layi yana da goma sha biyar. Akwai kalankuwoyi a layuka uku.
\v 5 Tagogin kuma suna duban junansu a layuka uku, dukkan ƙofofin tsawo da fãɗi bai ɗaya ne an yi masu kalankuwoyi kuma suna duban junansu layi uku.
\s5
\v 6 Akwai baranda mai tsawon kamu hamsin faɗinta kuma kamu talatin, a gaba an yi kwararo mai ginshiƙai da rufi.
\s5
\v 7 Suleman ya yi ɗakin kursiyinsa inda zai riƙa yin hukunci, wato ɗakin shari'ar adalci. An rufe dukkan daɓen shi da sida.
\s5
\v 8 Gidan da Suleman zai zauna kuma yana wani ɓangare na fãdar, an gina shi kamar yadda a ka gina ɗakin shari'ar. Ya yi wani gida kamar haka saboda ɗiyar Fir'auna wadda ya ɗauko ta zama matarsa.
\s5
\v 9 Gine-ginen an yi masu ado da duwatsu masu tsada waɗanda a ka sassaƙa su dai-dai a ka goge su a kowanne gefe. An yi amfani da duwatsun tun daga tushen ginin har zuwa sama, a waje kuma har zuwa babban ɗakin shari'a.
\v 10 An kafa tushen gidan da manyan duwatsu masu tsada ratar su kamu takwas ne zuwa goma.
\s5
\v 11 A sama an yi ado da duwatsu masu tsada waɗanda a ka sassaƙo su dai-dai wa daida, kuma da kalankuwa ta sida.
\v 12 Katafaren ɗakin taron da ya kewaye fadar ya na da layuka uku na sassaƙaƙƙen dutse da kalankuwa ta sida kamar wanda ya ke cikin haikalin Yahweh da wurin shan iskarsa.
\s5
\v 13 Sarki Suleman ya aika a ka kawo Huram daga Taya.
\v 14 Huram ɗan wata gwauruwa ne ta kabilar Naftali, babansa kuma mutumin Taya ne, shi gwani ne a aikin tagulla. Huram yana cike da hikima da fasaha da basirar yin babban aiki da tagulla. Ya zo wurin sarki Suleman domin ya yi wa sarki aikin tagulla.
\s5
\v 15 Huram ya tsara ginshiƙai biyu na tagulla kowanne tsawonsa kamu goma sha takwas ne kaurinsu kuma kamu goma sha biyu.
\v 16 Ya kuma yi zankaye biyu da za a sa a kan kowanne ginshiƙi. Tsawon kowanne zanko kamu biyar ne.
\v 17 Ya yi aikin raga da sarƙa ya yi wa zankayen ado don a sa su can saman ginshiƙan, guda bakwai ya yi domin kowanne zanko.
\s5
\v 18 Haka Huram ya yi layika biyu na tagulla kewaye da ginshiƙan ya yi wa zankayensu ado.
\v 19 Zankayen da ke kan ginshiƙan wurin shan iskar ya yi masu ado da furanni, kowanne fure, tsawonsa kamu huɗu.
\s5
\v 20 Zankayen da ke kan ginshiƙan nan biyu, an yi masu 'yan kwararo-kwararo guda ɗari biyu kewaye da su a can ƙoli.
\v 21 Ya ɗaga ginshiƙan wurin shan iska na haikali. Ginshiƙi na hannun dama ya ba shi suna Yakin, ginshiƙi na hannun hagu kuma ya ba shi suna Bo'aza.
\v 22 A bisa ginshiƙan akwai ado mai kama da furanni. Haka aka tsara ginshiƙan.
\s5
\v 23 Huram ya yi wani teku na zubi, kamu goma daga wannan gefe zuwa wancan. Tsawonsa kamu biyar ne, kewayensa kuma talatin.
\v 24 A ƙarƙashin tekun na zubi ya yi butoci kamu goma, ya yi su lokacin da ya ke yin tekun na zubi ya yi su tare.
\s5
\v 25 Ya ɗora tekun a bisa bijimai goma sha biyu, uku suna duban arewa, uku suna duban yamma, uku suna duban kudu, uku kuma suna duban gabas. aka ɗora "Tekun" a kansu, dukkan su cibiyoyinsu suna daga ciki.
\v 26 Kaurin tekun kamar tafin hannu ya ke, an yi masa baki kamar na ƙoƙo, kamar fure ya na sheƙi. Tekun ya na ɗaukar ruwa garwa dubu biyu.
\s5
\v 27 Huram ya yi diraku goma na tagulla. Ratar kowacce dirka kamu huɗu ne, faɗinta ma kamu huɗu, tsawonta kuma kamu uku.
\v 28 Aikin dirakun shi ne, suna da mahaɗai a tsakaninsu,
\v 29 kan dirakun da mahaɗarsu akwai zakuna da bijimai da kerubim. A saman zakunan da bijiman akwai zãnen furanni.
\s5
\v 30 Kowacce dirka ta na da ƙafafu huɗu na tagulla, kusurwoyinta huɗu suna da matokarai saboda bangajin. Matokaran an yi su da zanen furanni a gefen kowacce ɗaya.
\v 31 Bakinsu buɗe ya ke kamar kwano, faɗinsa kamu ɗaya da rabi ne, yana da kambi kamu ɗaya. A bakin su akwai zane-zane, kuma gefensu yana da tsawo da fãɗa bai ɗaya ba zagayayye ya ke ba.
\s5
\v 32 Ƙafafunsu huɗu suna daga ƙarƙashinsu, abin da ya riƙe su kuma yana cikin dirkar. Tsayin gargaren kamu ɗaya da rabi ne.
\v 33 Ƙafafunsu gargare kama da gargaren karusa. Abubuwan da suke riƙe da su da wayoyinsu ƙarfe ne na zubi.
\s5
\v 34 An yi wurin kamawa huɗu ga kowacce dirka waɗanda suke liƙe a jikinsu.
\v 35 a kan kowacce dirka an yi kambi rabin zurfinsa rabin kamu. Saman inda ta tsaya da gefenta haɗe su ke.
\s5
\v 36 Jikin matokaran da gefensu, Huram ya zana zakuna da kerubim da ganyen dabino ya rufe inda ƙofofi suke ya zagaye su da furanni.
\v 37 Yadda ya yi matokaran dukkan su zubinsu iri ɗaya ne girman su da tsarin su dukka ɗaya ne.
\s5
\v 38 Huram ya yi bangazai goma, kowannen su zai ɗauki ruwa garwa goma. Kowanne bangaji kamu huɗu ne kuma ya sa bangaji ɗaya a bisa matokaran su goma.
\v 39 Ya yi matokarai biyar daga kudu suna fuskantar haikalin, biyar kuma daga arewa su masu na fuskantar haikalin. Ya sa "Tekun" a kusurwar gabas, yana fuskantar kudu da haikalin.
\s5
\v 40 Huram ya yi bangazai da moɗa da tasoshin yayyafawa. Daga nan ya gama dukkan aikin da zai yi wa Sarki Suleman cikin haikalin Yahweh.
\v 41 Ginshiƙan biyu suna kama da zankayen da suke kan waɗancan ginshiƙan guda biyu. Ya yi zane guda biyu kamar tasoshi ya sa su domin su yi wa zankayen ado.
\s5
\v 42 Ya yi zãne-zãne ɗari huɗu saboda sahu biyu na kayan adon da ya yi (layi biyu na zãne-zãne domin su rufe zankayen da suke a kan ginshiƙan guda biyu da);
\v 43 matokaran su goma da bangajin nan guda goma na bisa matokaran.
\s5
\v 44 Ya yi tekun da bajiman nan goma sha biyu da ke ƙarƙashinsa;
\v 45 da tukwanen da moɗayen da bangazayen da dukkan sauran kayan aikin. Huram ya yi wa Sarki Suleman, su saboda haikalin Yahweh.
\s5
\v 46 Sarki ya sa a zuba su filin Yodan a ƙasar yumɓu da ke tsakanin Sokot da Zaretan.
\v 47 Suleman bai auna kayan aikin ba domin yawansu ya fi gaban aunawa, nauyin tagullar kuma ba za a iya auna su ba.
\s5
\v 48 Dukkan kayan da ke cikin haikalin Yahweh Suleman ya yi su da zinariya: bagadi na zinariya da teburi wanda za a ajiye keɓaɓɓiyar gurasa.
\v 49 Sandunan ajiye fitilu, biyar a hannun dama biyar kuma a hannun hagu, a gaba cikin ɗaki na can ciki an yi su da zinariya tsantsa da furannin da fitilun da yatsun dukka na zinariya ne.
\s5
\v 50 Kofinan da abubuwan kashe fitila da cokula da bangazaye da abubuwan ƙona turare dukka an yi su da zinariya tsantsa. Sakatu na ɗaki na can ciki wato wuri mafi tsarki da ƙofofin babban ɗakin taro na haikali dukka da zinariya aka yi su.
\s5
\v 51 Da haka aka gama dukkan aikin da Sarki Suleman ya yi domin gidan Yahweh. Sai Suleman ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dauda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayan ɗaki ya sa su a cikin ɗakin ajiya a gidan Yahweh.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Sa'an nan Suleman ya tattara dukkan dattawan Isra'ila da shugabannin kabilu da shugabannin iyalai na mutanen Isra'ila a gabansa a Yerusalem, domin ya kawo akwatin alƙawarin Yahweh daga birnin Dauda wato Sihiyona.
\v 2 Dukkan jama'ar Isra'ila suka taru a gaban Suleman a wurin liyafar, a cikin watan Itanim, wato wata na bakwai.
\s5
\v 3 Dukkan dattawan Isra'ila da firistoci suka ɗauki akwatin.
\v 4 Suka kawo akwatin Yahweh da rumfar taruwa da dukkan kaya masu tsarki da suke cikin rumfar. Firistoci da Lebiyawa ne suka kawo waɗannan kaya.
\v 5 Sarki Suleman tare da dukkan taron Isra'ila suka zo gaban akwatin, suna miƙa hadayar tumaki da bijimai waɗanda ba su ƙidayuwa.
\s5
\v 6 Firistoci suka kawo akwati na alƙawarin Yahweh suka sa shi a wurinsa, cikin ɗaki na can cikin gidan, wato wuri mafi tsarki a ƙarƙashin fukafukan kerubim.
\v 7 Gama fukafukan kerubim ɗin sun kai wurin da akwatin ya ke, kuma sun rufe akwatin tare da sandunan da a ke ɗaukar sa.
\v 8 Sandunan suna da tsawo sosai har ana iya ganin su daga wuri mafi tsarki a gaban ɗaki na can ciki, amma ba za a iya ganin su daga waje ba. Suna nan har zuwa yau.
\s5
\v 9 Babu kome a cikin akwatin sai dai allunan nan na dutse da Musa ya sa ciki a Horeb, sa'ad da Yahweh ya yi alƙawari da mutanen Isra'ila lokacin da suka fito daga ƙasar Masar.
\v 10 Ya zama lokacin da firistocin suka fito daga wuri mai tsarki sai girgije ya cika haikalin Yahweh.
\v 11 Firistoci ba su iya tsayawa su yi hidima ba saboda girgijen. Gama darajar Yahweh ta cika gidansa.
\s5
\v 12 Sa'an nan Suleman yace, "Yahweh ya ce zai zauna a cikin baƙin duhu,
\v 13 Amma na gina maka wuri mai ƙawa, wurin da za ka zauna har abada."
\s5
\v 14 Sa'an nan sarki ya juya ya sa wa taron jama'ar Isra'ila albarka sa'ad da jama'ar Isra'ila suke a tsaye.
\v 15 Ya ce, "Bari a yi yabo ga Yahweh Allah na Isra'ila wanda ya yi magana da mahaifina Dauda, kuma ya cika da hannunsa, cewa,
\v 16 'Tun ranar da na kawo Isra'ila jama'ata daga Masar, ban zaɓi birni da zan gina gida domin in sa sunana a ciki ba. Na dai zaɓi Dauda ya yi mulkin jama'ata Isra'ila.
\s5
\v 17 Yana dai cikin zuciyar Dauda mahaifina ya gina gida domin Yahweh Allah na Isra'ila.
\v 18 Amma Yahweh ya ce da Dauda mahaifina, 'Ya yi kyau da ka ke da tunani a zucyarka domin ka gina ma ni gida.
\v 19 Duk da haka ba za ka gina gidan ba, sai dai ɗanka wanda za a haifa ma ka shi ne zai gina gida domin sunana.'
\s5
\v 20 Yahweh ya cika maganar da ya faɗi gama na taso a matsayin mahaifina Dauda, kuma ina zaune a kan kursiyi na mulkin Isra'ila kamar yadda Yahweh ya yi alƙawari. Na gina gida domin sunan Yahweh Allah na Isra'ila.
\v 21 Na yi wa akwati wuri wanda a cikin sa alƙawarin Yahweh ya ke, wanda ya yi wa ubanninmu lokacin da ya fito da su daga ƙasar Masar."
\s5
\v 22 Suleman ya tsaya a gaban akwatin Yahweh, gaban taron jama'ar Isra'ila ya buɗe hannuwansa zuwa sama.
\v 23 Ya ce, "Yahweh, Allah na Isra'ila, babu wani Allah kamar ka a bisa cikin sama ko a nan ƙasa wanda ke riƙe alƙawarinsa da aminci zuwa ga bayinka waɗanda suke tafiya a gabanka da dukkan zuciyarsu;
\v 24 kai wanda ya riƙe alƙawarin da ka yi wa bawanka Dauda mahaifina. I, ka faɗi da bakinka kuma ka cika da hannunka, kamar yadda ya ke a yau.
\s5
\v 25 To yanzu dai, Yahweh, Allah na Isra'ila, ka cika alƙawarin da ka yi wa bawanka mahaifina Dauda, sa'ad da ka ce, 'Ba za ka rasa mutum wanda zai zauna a bisa kursiyin Isra'ila ba, idan dai zuriyarka za su yi hankali su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi tafiya a gabana.'
\v 26 To yanzu dai Allah na Isra'ila, ina roƙon alƙawarin da ka yi wa bawanka Dauda mahaifina, ya zama gaske.
\s5
\v 27 Amma gaskiya ne Allah zai zauna a ƙasa? Da ya ke dukkan duniya da sama ba za su iya riƙe ka ba, balle fa wannan haikalin da na gina!
\v 28 Duk da haka, Yahweh, Allahna, ka yarda da wannan addu'a da roƙo na bawanka; ka saurari kuka da addu'ar da bawanka ya yi a gabanka yau.
\s5
\v 29 Bari idanunka su zama a buɗe zuwa wannan haikali dare da rana, wanda ka yi magana a kansa cewa, 'Sunana da kasancewata za su zauna a can'- domin ka ji addu'o'in da bawanka zai yi a wurin nan.
\v 30 Ka ji roƙon bawanka da na jama'ar Isra'ila sa'ad da muke yin addu'a a wannan wuri. I, ka ji daga wurin da ka ke, daga sama, kuma sa'ad da ka ji, ka yi gafara.
\s5
\v 31 Idan wani mutum ya yi wa maƙwabcinsa zunubi, aka nemi da ya rantse da alƙawari, idan ya zo ya yi rantsuwa da alƙawari a gaban bagadinka a wannan gida,
\v 32 ka ji daga sama ka yi wa bayinka hukunci, ka hukunta mai laifi ka sa abin da ya yi ya koma kansa, ka baratar da mai adalci ka yi masa sakamako saboda adalcinsa.
\s5
\v 33 Idan abokin gãba ya yi nasara a kan bayinka jama'ar Isra'ila saboda suka yi maka zunubi, idan sun juyo sun kira sunanka a wnnan haikali, suka yi addu'a suka roƙi gafara -
\v 34 idan ka yarda, ka ji daga sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila; ka dawo da su ƙasar da ka bayar ga kakanninsu.
\s5
\v 35 Idan sama ta rufe babu ruwa, saboda mutanenka sun yi ma ka zunubi - idan su ka yi addu'a su na fuskantar wannan wuri, su ka kira sunanka kuma su ka juwo daga zunubinsu, bayan ka wahalshe su -
\v 36 sai ka ji daga sama ka gafarta zunubin bayinka da na mutanen Isra'ila, sa'ad da ka koya masu hanyoyi masu kyau da ya kamata su bi. Ka aiko da ruwa a ƙasar da ka ba mutanenka gãdo.
\s5
\v 37 A misali yunwa ta zo ƙasar ko cuta ko annobar gonaki ko cutar fatar jiki, ko fãri ko tsutsotsi, a misali kuma a ce abokin găba zai kawo hari a ƙasarsu, ko annoba ko wani ciwo -
\v 38 A misali kuma wani ya yi addu'a ko roƙo ko dukkan jama'arka Isra'ila - kowanne ɗayansu yana sane da annobar a cikin zuciyarsa, idan suka tada hannuwansu zuwa wannan haikali.
\s5
\v 39 Sai ka ji daga sama inda ka ke zaune, ka yi gafara kuma ka sãka wa kowanne mutum bisa ga dukkan abin da ya yi; ka san zucyarsa saboda kai kaɗai ne ka san dukkan zukatan mutane.
\v 40 Yi haka domin su ji tsoron ka muddin suna zaune a ƙasar da ka bayar ga kakanninmu.
\s5
\v 41 Har yanzu, game da baƙo wanda ba na cikin jama'arka Isra'ila ba ne: idan ya zo daga wuri mai nisa saboda sunanka -
\v 42 gama za su ji labarin sunanka mai girma da hannunka mai iko da hannunka wanda ka tayar, idan ya yi addu'a yana fuskantar wannan haikali,
\v 43 idan ka yarda, ka ji daga sama inda ka ke zaune, ka yi bisa ga abin da baƙon ya roƙe ka. Ka yi haka domin dukkan mutanen duniya su san ka su ji tsoron sunanka, kamar yadda jama'arka Isra'ila suke yi. Ka yi haka domin su san da sunanka a ke kiran wannan gida da na gina.
\s5
\v 44 Idan jama'arka suka je yaƙi da abokan gaba, ta kowacce hanya ka aike su, Yahweh, idan suka yi addu'a suna fuskantar wannan birni wanda ka zaɓa da wannan gida da na gina domin sunanka.
\v 45 Sai ka ji addu'arsu da roƙonsu daga sama ka yi taimako.
\s5
\v 46 A misali idan suka yi maka zunubi, tun da ya ke ba wanda ba ya yin zunubi, a misali idan ka yi fushi da su, ka bashe su ga abokin găba, abokin găba ya kwashe su zuwa ƙasarsu, ko da nesa ko kusa.
\v 47 A misali idan suka gane suna cikin ƙasar bauta, a misali idan suka tuba suka roƙi tagomashi a wurin ka daga ƙasar waɗanda suka bautar da su. A misali idan suka ce, 'Mun yi wauta mun yi zunubi. Mun yi aikin mugunta.'
\s5
\v 48 Amisali idan suka juwo gare ka da dukkan zuciyarsu da dukkan ransu a cikin ƙasar abokan gãbarsu waɗanda suka kwashe su, idan suka yi addu'a suna fuskantar ƙasarsu, suna fuskantar birnin da ka zaɓa da wannan gida da na gina domin sunanka.
\s5
\v 49 Sai ka ji addu'arsu da roƙonsu na neman taimako daga sama inda ka ke, ka dai-daita al'muransu.
\v 50 Ka gafartawa mutanenka zunubin da suka yi maka da dukkan zunubansu da suka ƙetare dokokinka. Ka ji tausayin mutanenka a gaban abokan gãbarsu, domin abokan găbarsu su ji tausayin mutanenka.
\s5
\v 51 Su mutanenka ne da ka zaɓa, waɗanda ka kuɓutar daga Masar kamar daga cikin tanderu inda a ke narkar da ƙarfe.
\v 52 Ina roƙon idanunka su buɗe ga roƙon bawanka da roƙe-roƙen mutanenka Isra'ila, ka ji su daga ko'ina suka yi kuka gare ka.
\v 53 Gama ka keɓe su daga dukkan mutanen duniya su zama na ka, su kuma karɓi alƙawuranka, Yahweh Ubangiji, kamar yadda ka bayyana ta wurin bawanka Musa sa'ad da ka kawo ubanninmu daga Masar, Ubangiji Yahweh."
\s5
\v 54 Haka ya zama sa'ad da Suleman ya gama yin addu'a da dukkan roƙon da zai yi zuwa ga Yahweh, ya tashi daga gaban bagadin Yahweh, daga yin durƙusonsa a kan guiwoyinsa da ta da hannuwansa zuwa sama.
\v 55 Ya miƙe ya sa wa dukkan taron jama'ar Isra'ila albarka da babbar murya, cewa,
\v 56 yabo ga Yahweh wanda ya ba mutanensa Isra'ila hutawa, ya cika alƙawuransa. Ko kalma ɗaya ba a rasa ba cikin dukkan alƙawura masu kyau da Yahweh ya yi da bawansa Musa.
\s5
\v 57 Yahweh ya kasance tare da mu, kamar yadda ya kasance tare da kakanninmu, kada ya bar mu ko ya yashe mu,
\v 58 ya sa zuciyarmu ta manne masa, mu rayu cikin dokokinsa da ka'idodinsa da farillansa, waɗanda ya umurci ubanninmu.
\s5
\v 59 Bari waɗannan maganganu da na faɗi, na yi roƙo ga Yahweh, su zauna a kusa da Yahweh Allahna, dare da rana, domin ya yi taimako cikin al'amuran bawansa da al'amuran jama'arsa Isra'ila a kowacce rana;
\v 60 domin dukkan mutanen duniya su sani Yahweh shi ne Allah kuma ba bu wani Allah!
\v 61 Saboda haka zuciyarku ta yi aminci ga Yahweh Allanmu, ku kiyaye farillansa da dokokinsa, kamar a yau."
\s5
\v 62 Sai sarki tare da dukkan Isra'ila suka miƙa hadayu ga Yahweh.
\v 63 Suleman ya miƙa baye-baye na zumunci waɗanda ya yi wa Yahweh: bijimai dubu ashirin da biyu da tumaki 120,000. Haka sarki da dukkan Isra'ila su ka keɓe gidan Yahweh.
\s5
\v 64 A wannan ranar ne kuma sarki ya keɓe filin da ke tsakiya a gaban haikalin Yahweh. Gama a nan ne sarki ya miƙa baye-baye na ƙonawa, baye-baye na hatsi da kitsen baye-baye na zumunta, saboda bagadin da ya ke gaban Yahweh bai kai girman da zai ɗauki baikon ba, wato baye-baye na hatsi da kitsen baye-baye na zumunta.
\s5
\v 65 Haka sarki ya yi liyafa a wannan lokaci da dukkan Isra'ila tare da shi, babban taro. Tun daga Lebo Hamat har zuwa iyakar Masar, suna gaban Ubangiji Allah kwana bakwai da waɗansu kwana bakwai kuma, wato kwana goma sha huɗu kenan dukka.
\v 66 A kan rana ta takwas ya sallami mutanen, suka sa wa sarki albarka kowanne ya tafi gidansa da murna da farinciki saboda abubuwa masu kyau waɗanda Yahweh ya yi wa Dauda bawansa, da Isra'ila, mutanensa.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Bayan da Suleman ya gama ginin gidan Yahweh da fădar sarki, kuma bayan da ya gama dukkan abubuwan da ya ke so ya yi,
\v 2 Sai Yahweh ya bayyana ga Suleman sau na biyu, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibiyon.
\s5
\v 3 Daga nan Yahweh ya ce da shi, "Na ji addu'arka da roƙon da ka yi zuwa gare ni. Na keɓe wannan gida, wanda ka gina, domin kaina, in sa sunana a wurin. Idanuna da zuciyata za su kasance a wurin kowanne lokaci.
\s5
\v 4 A gare ka kuma, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dauda mahaifinka ya yi cikin aminci da sahihancin zuciya, ka na yin biyayya ga dukkan abin da na ummurce ka ka na kiyaye farillaina da shari'una,
\v 5 zan tabbatar da mulkinka a kan Isra'ila har abada, kamar yadda na yi wa Dauda mahaifinka alƙawari, cewa, 'Ba za a taɓa rasa zuriyarka a kan kursiyin Isra'ila ba.'
\s5
\v 6 Amma idan ka fanɗare, ko kai, ko 'ya'yanka, ba ku kiyaye dokokina da farillaina waɗanda na shimfiɗa a gabanka ba, idan ku ka je ku ka bauta wa waɗansu alloli ku ka russana masu,
\v 7 zan kawar da Isra'ila daga ƙasar da na ba su, wannan gida kuma wanda na keɓe domin sunana, zan kawar da fuskata daga gare shi, Isra'ila kuma za su zama misali da abin ba'a da abin raini ga dukkan mutane.
\s5
\v 8 Wannan haikali kuma zai zama tarin juji, dukkan wanda ya wuce ta kusa da shi zai kaɗu ya yi ajiyar zuciya. Zai yi tambaya haka, 'Me ya sa Yahweh ya yi haka ga wannan ƙasa da wannan gida?'
\v 9 Waɗansu za su amsa da cewa, 'Saboda sun watsar da Yahweh Allahnsu, wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, sun koma ga waɗansu alloli sun russana masu sun yi masu sujada. Shi ya sa Yahweh ya auko masu da wannan masifar.'"
\s5
\v 10 Ya zama shekaru ashirin bayan da Suleman ya gama gine-ginen nan biyu, wato haikalin Yahweh da fãdar sarki.
\v 11 Hiram sarkin Taya ya tanadawa Suleman sida da itatuwan fir da zinariya da dukkan abin da Suleman ya bukata-sai sarki Suleman ya ba shi birane ashirin cikin ƙasar Galili.
\s5
\v 12 Sai Hiram ya zo daga Taya domin ya ga biranen da Suleman ya ba shi, amma ba su gamshe shi ba.
\v 13 Hiram yace, "Waɗanne irin birane ne waɗannan da ka ba ni, ɗan'uwana?" Hiram ya ce da su ƙasar Kabul, haka a ke kiran su har yau.
\v 14 Dã ma Hiram ya aika wa sarki zinariya awo 120.
\s5
\v 15 Wannan shi ne dalilin aikin dole wanda sarki Suleman ya sa a yi: wato a gina haikalin Yahweh da fãdarsa, kuma a gina Millo da garun Yerusalem da kuma kariya ta Hazor da Maggido da Gezer.
\v 16 Fir'auna sarkin Masar ya je ya kama Gezer. Ya ƙone ta ya karkashe Kan'aniyawan cikin birnin. Sai Fir'auna ya ba ɗiyarsa matar Suleman, biranen a matsayin kyautar aure.
\s5
\v 17 Haka Suleman ya sake gina Gezer da Bet Horon ta gangare,
\v 18 da Ba'alat da Tamar a ƙasar Yahuda cikin jeji,
\v 19 da biranen da ya ke da su na ajiya da na karusansa da na mahaya dawakinsa da dukkan abin da ya yi sha'awar ginawa a Yerusalem domin jin daɗinsa a Lebanon da dukkan ƙasashen da su ke ƙarƙashin mulkinsa.
\s5
\v 20 Game da mutanen da su ka rage na wajen Amoriyawa da Hittiyawa da Ferizziyawa da Hiwiyawa da Yebusiyawa waɗanda ba sa cikin mutanen Isra'ila ba,
\v 21 da zuriyarsu waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakawa duka ba, Suleman ya sa su ka zama masu aikin tilas haka kuwa su ke har yau.
\s5
\v 22 Amma Suleman bai sa mutanen Isra'ila aikin tilas ba. Maimakon haka sai ya sa suka zama sojojinsa da bayinsa da jami'ansa da jami'an karusansa da mahaya dawakinsa.
\s5
\v 23 Suleman ya na da jami'ai masu hidimar lura da masu duba aiki, yawan su shi ne 550, su ne suke lura da mutanen da suke yin aiki.
\s5
\v 24 Ɗiyar Fir'auna ta tashi daga birnin Dauda ta koma gidan da Suleman da ya gina mata, sa'an nan Suleman ya gina Millo.
\s5
\v 25 A shekara sau uku Suleman ya ke miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a kan bagadin da ya gina wa Yahweh, a gaban Yahweh ya ke ƙona su da turare. Ya gama haikalin yanzu yana amfani da shi.
\s5
\v 26 Sarki Suleman kuma ya yi tashar jiragen ruwa a Eziyon Geber wadda ta ke kusa da Elat a bakin Jan Teku a ƙasar Idom.
\v 27 Hiram ya aiko bayinsa zuwa tashar Suleman, masu tuƙin jirgi waɗanda suka saba da teku tare da bayin Suleman.
\v 28 Suka je Ofir da bayin Suleman. Suka kawowa Suleman zinariya awo 420 daga can.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Sa'ad da sarauniyar Sheba ta ji labarin Suleman ya zama sananne game da sunan Yahweh, sai ta zo ta gwada shi da tambayoyi masu wuya.
\v 2 Ta zo Yerusalem da raƙuma da yawa, da raƙuman da aka ɗorowa kayan yaji da zinariya mai yawa da duwatsu masu daraja da yawa. Sa'ad da ta zo sai ta gayawa Suleman dukkan abin da ke cikin zuciyarta.
\s5
\v 3 Suleman ya amsa dukkan tambayoyinta. Ba wani abu da ta tambaya wanda Suleman bai ba da amsarsa ba.
\v 4 Sa'ad da sarauniyar Sheba ta ga dukkan hikimar Suleman da fãdar da ya gina,
\v 5 da abincin da ke kan teburinsa da wurin da bayinsa suke zama da ayyukan da bayinsa suke yi da tufafinsu, da masu yi ma sa hidima da yadda ya ke miƙa baye-baye na ƙonawa, sai ta zama ba ta da sauran ƙarfi.
\s5
\v 6 Ta ce da sarki, "Rahoton da na ji a ƙasata game da maganarka da hikimarka gaskiya ne.
\v 7 Ban gaskata da abin da na ji ba sai da na zo nan, yanzu idanuna sun gani. Ko rabin hikimarka da wadatarka ma ba a gaya mani ba! Sunanka ya wuce abin da na ji.
\s5
\v 8 Matanka masu albarka ne, bayinka waɗanda suke tsayawa a gabanka kullum, masu albarka ne saboda suna jin hikimarka.
\v 9 Yabo ga Yahweh Allahnka wanda ya yi farinciki da kai ya sa ka a bisa kursiyin Isra'ila. Saboda Yahweh ya ƙaunaci Isra'ila har abada ya sa ka zama sarki domin ka yi masu hukunci da adalci!"
\s5
\v 10 Ta ba sarki awo 120 na zinariya da kayan yaji da yawa da duwatsu masu daraja. Ba a ƙara ba sarki Suleman kayan yaji masu yawa fiye da wanda sarauniyar Sheba ta ba shi ba.
\s5
\v 11 Jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, daga Ofir ɗin kuma sun kawo itacen almug mai yawa da duwatsu masu daraja.
\v 12 Sarkin ya yi ginshiƙai na itacen almug a haikalin Yahweh da fãdar sarki, kuma ya yi wa mawaƙa molaye da girayu. Ba a ƙara ganin itacen almug da yawa haka ba har zuwa yau.
\s5
\v 13 Sarki Suleman ya ba sarauniyar Sheba dukkan abin da ta nuna sha'awa a kai da dukkan abin da ta roƙa, ƙari a kan kyautar da ya riga ya ba ta saboda karamci. Sai ta koma ƙasarta tare da bayinta.
\s5
\v 14 Nauyin zinariyar da ta zo wa Suleman a cikin shekara ɗaya awo 666 ne,
\v 15 ban da zinariyar da "yan kasuwa da fatake suka kawo. Dukkan sarakunan Arebiya da hakiman ƙasar masu ka kawo wa Suleman zinariya da azurfa.
\s5
\v 16 Sarki Suleman ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na gogaggiyar zinariya. Kowaccen su an yi ta da awo ɗari shida na zinariya.
\v 17 Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi ɗari uku na gogaggiyar zinariya, awon zinariya uku suka shiga kowacce garkuwa; sarki ya sa su can cikin fadar da ta ke a jejin Lebanon.
\s5
\v 18 Kuma sarki ya yi wani babban dakalin mulki na hauren giwa ya shafe shi da zinariya mafi kyau.
\v 19 Dakalin yana da matakalai shida, bayan shi kuma shan ƙwai ne a can sama. Kowannen su yana da wurin ajiye hannu a gefe, akwai zakuna biyu a tsaye gefen wurin ajiye hannun.
\v 20 Zakuna goma sha biyu suna tsaye a kan matakalun, ɗaya a kan kowacce matakala. Babu wata masarautar da take da dakali kamar sa.
\s5
\v 21 Dukkan kofinan sha na sarki Suleman na zinariya ne, dukkan kofinan sha da suke fãdar da ke cikin jejin Lebanon na zinariya ne tsantsa. Ba na azurfa ko ɗaya domin a zamanin Suleman azurfa ba ta da daraja.
\v 22 Sarki ya na da jiragen ruwa masu yawo a kan teku, tare da jiragen Hiram. Sau ɗaya a cikin shekara uku jiragen ruwan sukan kawo zinariya da azurfa da hauren giwa da buka da ɗawisu masu daraja.
\s5
\v 23 Sarki Suleman ya fi dukkan sarakunan duniya arziki da hikima.
\v 24 Kowa da kowa a duniya suna so su zo wurin Suleman domin su ji hikimar da Yahweh ya sa cikin zuciyarsa.
\v 25 Waɗanda ke zuwa su na kawo haraji, na santulan azurfa da zinariya, da kayan sawa da sulke da kayan yaji da dawakai da alfadarai, shekara biye da shekara.
\s5
\v 26 Suleman ya tara karusai da mahaya dawaki. Ya na da karusai 1400 da mahaya dawaki dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye su a biranen da a ka ajiye karusai shi kansa kuwa ya na cikin Yerusalem.
\v 27 Sarki ya na da azurfa a Yerusalem kamar yawan duwatsun da suke a doron ƙasa. Yana da itatuwan sida da yawa kamar yadda itatuwan ɓaure suke a cikin fadama.
\s5
\v 28 Suleman ya na da dawakai da aka kawo daga Masar da Kilikiya. Abokan cinikin sarki sukan saye su garke-garke kowanne garke bisa ga farashinsa.
\v 29 Akan sayo karusai daga Masar kowacce akan awo ɗari shida na azurfa, dawaki kuma akan 150 kowanne. Akan sayar da wasu da yawa daga cikin su ga sarakunan Hittiyawa da Siriya.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Yanzu sarki Suleman ya kaunaci baƙin mata: ɗiyar Fir'auna, da matan Mowabawa, da Ammonawa da Idomawa da Sidoniyawa da Hittiyawa.
\v 2 Su na daga al'ummai waɗanda Yahweh ya ce da mutanen Isra'ila, "Ba za ku shiga cikinsu ba da aure, ko su zo cikinku, domin lallai za su juyar da zukatanku ga allolinsu." Amma duk da wannan Suleman kuwa ya ƙaunaci waɗannan mata.
\s5
\v 3 Suleman ya na da gimbiyoyin mata ɗari bakwai da kuma ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matayensa su ka juyar da zuciyarsa.
\v 4 Gama sa'ad da Suleman ya tsufa, sai matansa su ka juyar da zuciyarsa zuwa bin wasu alloli; bai miƙa dukkan zuciyarsa ga Yahweh Allahnsa ba, kamar zuciyar Dauda mahaifinsa.
\s5
\v 5 Gama Suleman ya bi Ashtoret, gunkin Sidoniyawa, ya kuma bi Molek, wato gunkin Ammonawa.
\v 6 Suleman ya yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh; bai bi Yahweh da zuciya ɗaya ba, ba kamar yadda mahaifinsa Dauda ya yi ba.
\s5
\v 7 Sai Suleman ya gina masujadai domin Kemosh, kyamattacen gunkin Mowab, akan dutsen gabashin Yerusalem, da kuma domin Molek, da kyamataccen gunkin mutanen Amonawa.
\v 8 Ya kuma gina masujadai domin dukkan baƙin mata, waɗanda su ke ƙona turare da hadayu ga allolinsu.
\s5
\v 9 Yahweh kuwa ya yi fushi da Suleman, domin zuciyarsa ta rabu daga gare shi, Allah na Isra'ila, ko da ya ke ya bayyana a gare shi sau biyu,
\v 10 ya kuma umarce shi akan wannan abu, da kada ya bi wasu allolin. Amma bai yi biyayya da wannan umarni na Yahweh ba.
\s5
\v 11 Saboda haka Yahweh ya ce da Suleman, "Domin ka yi wannan ka kuma ƙi kiyaye alƙawari da ka'idodina waɗanda na umarceka, hakika zan tsaga mulkin daga gare ka in ba baranka.
\v 12 Amma, saboda mahaifinka Dauda, ba zan yi ba a lokacin rayuwarka, amma zan tsaga ta daga hannun ɗanka.
\v 13 Duk da haka ba zan ƙwace dukkan mulkin ba, zan ba kabila ɗaya ga ɗanka, saboda bawana Dauda, don kuma Yerusalem, wanda na zaɓa."
\s5
\v 14 Sai Yahweh ya ta da abokin gãba ga Suleman, Hadad Ba'idome. Shi kuma daga iyalin sarautar Idom ne.
\v 15 Gama sa'ad da Dauda yana cikin Idom, Yowab shugaban sojoji ya tafi don ya bizne matattu, kowanne mutum wanda aka kashe a Idom.
\v 16 Yowab da dukkan Isra'ila su ka tsaya a Idom wata shida har sai da ya kashe mazajen Idom.
\v 17 Amma an ɗauki Hadad tare da wasu Idomawa ta wurin bayin mahaifinsa zuwa Masar, tun lokacin da Hadad yana karamin yaro.
\s5
\v 18 Su ka bar Madayana su ka zo Faran, daga nan su ka ɗauki mutane tare da su zuwa Masar, wurin Fir'auna sarkin Masar, wanda ya ba shi gida da kuma ƙasa da abinci.
\v 19 Hadad kuwa ya sami tagomashi ƙwarai a fuskar Fir'auna, saboda haka Fir'auna ya bashi mata, ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes sarauniya.
\s5
\v 20 'Yar'uwar Tafenes ta haifa wa Hadad ɗa. Suka sa masa suna Genubat. Tafenes ta yi renon sa a fadar. Genubat ya zauna a fadar Fir'auna a cikin yaran Fir'auna.
\v 21 A lokacin da ya ke a Masar, Hadad ya ji labari Dauda ya rasu aka kuma rufe shi tare da kakanninsa, Yowab shugaban sojoji kuma ya mutu, sai Hadad ya cewa Fir'auna, "Ka yardar mani in tashi, in koma ƙasata."
\v 22 Sai Fir'auna ya ce masa, "Amma me ka rasa a nan har da ka ke neman komawa ƙasarka?" Hadad ya amsa, "Ba bu kome, idan ka yarda bar ni in koma.
\s5
\v 23 Allah kuma ya ta da wani abokin gãba ga Suleman, Rezon ɗan Eliyada, wanda ya zo daga wurin maigidansa Hadadezar sarkin Zobah.
\v 24 Rezon ya tattaro wa kansa mutane har ya zama shugaba akan kananan mayaƙa, bayan da Dauda ya ci nasara akan mutanen Zobah. Rezo ya mulki Damaskus.
\v 25 Ya zama abokin gãbar Isra'ila dukkan kwanakin Suleman, tare da wahalar da Hadad ya kawo. Rezon ya ƙi mutanen Isra'ila ƙwarai, ya yi mulkin Aram.
\s5
\v 26 Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zeredan, ma'aikacin Suleman ne, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.
\v 27 Dalilin da ya sa ya tayar wa sarki shi ne domin Suleman ya gina masujada a Millo ya kuma gyara garun birnin Dauda mahaifinsa.
\s5
\v 28 Yerobowam ƙaƙƙarfan mutum mai fasaha. Suleman ya ga saurayi ne mai himma, sai ya sa shi shugabanci akan dukkan aikin gidan Yosef.
\v 29 A wanan lokacin, sai Yerobowam ya fita daga Yerusalem, annabi Ahijah mutumin Shilo ya same shi a hanya.
\v 30 Yanzu kuwa Ahijah ya na saye da sabuwar riga tare da mutune biyu kaɗai a filin. Sai Ahijah ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa kashi goma sha biyu.
\s5
\v 31 Ya cewa Yerobowam, "Ɗauki kyalle goma, gama haka Yahweh, Allahn Isra'ila, ya faɗa, 'Duba, zan yaga mulkin daga hannun Suleman zan kuma ba da kabilu goma a gare ka
\v 32 (amma Suleman zai sami kabila ɗaya, saboda bawana Dauda, ɗaya kuma saboda Yerusalem - birnin da na zaɓa daga cikin dukkan kabilan Isra'ila),
\v 33 domin sun rabu da ni su na bauta wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, Kemosh allahn Mowab, da Milkon allahn mutanen Ammonawa. Ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ko su yi abin da ke dai-dai a idanuna da kiyaye dokokina da ka'idodina, kamar yadda Dauda mahaifinsa ya yi.
\s5
\v 34 Duk da haka ba zan ɗauke dukkan mulkin daga hannun Suleman ba. A maimakon haka zan sa shi ya yi mulki dukkan kwanakin rayuwarsa, saboda bawana Dauda wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnina da dokokina.
\v 35 Amma zan ɗauke mulkin daga hannun ɗansa, zan ba da shi gare ka, kabilu goma.
\v 36 Zan ba da kabila ɗaya ga ɗan Suleman, saboda bawana Dauda wanda kullum yana riƙe fitila a gabana a Yerusalem, birnin da na zaɓa in sa sunana.
\s5
\v 37 Zan ɗauke ka, za ka yi mulki ka cika dukkan buƙatarka, kuma za ka zama sarki akan Isra'ila,
\v 38 Idan za ka saurari dukkan abin da zan umarce ka, idan kuma ka bi hanyata ka yi abin da ke dai-dai a idanuna, ka kiyaye dokokina da umarnina, kamar yadda Dauda bawana ya yi, sai in kasance tare da kai zan sa gidanka ya kahu, kamar yadda na sa gidan Dauda, zan ba da Isra'ila a gare ka.
\v 39 Zan hori zuriyar Dauda, amma ba har abada ba."
\s5
\v 40 Suleman kuwa ya yi ƙoƙarin kashe Yerobowam. Amma Yerobowam ya tashi ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak sarkin Masar, ya zauna a can har mutuwar Suleman.
\s5
\v 41 Kamar sauran abubuwa game da Suleman, dukkan abin da ya yi da hikimarsa ba a rubuta su a littafin ayyukan Suleman ba?
\v 42 Suleman ya yi mulki a Yerusalem akan dukkan Isra'ila har shekaru arba'in.
\v 43 Ya mutu tare da kakaninsa kuma aka bizne shi a birnin Dauda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Rehobowam ya tafi Shekem, domin dukkan Isra'ila sun tafi Shekem su maida shi sarki.
\v 2 Ya zamana sa'ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (domin shi yana Masar, inda, ya gudu daga gaban sarki Suleman), don Yerobowam ya na zaune a Masar.
\s5
\p
\v 3 Sai su ka aika a kirawo shi, Yerobowam tare da dukkan taron mutanen Isra'ila suka zo suka ce da Rehobowam,
\v 4 '"Mahaifinka ya nawaita mana. Yanzu sai ka rage mana wahalar aikin da tsohonka ya nawaita a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka."
\v 5 Yerobowam ya ce da su, "Ku tafi har nan da kwana uku, sai bayan kwana uku ku dawo wuri na." Sai mutanen su ka tafi.
\s5
\v 6 Sarki Rehobowam kuwa ya yi shawara tare da dattawa waɗanda suka tsaya tare da Suleman mahaifinsa a lokacin da ya ke da rai, sai ya ce masu, "Wacce shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?"
\v 7 Su ka yi magana da shi, suka ce, "Idan za ka zama bara yau ga waɗannan mutane sai ka bauta masu, ka kuma amsa masu da magana mai kyau, su kuwa kullum za su zama barorinka."
\s5
\v 8 Amma Rehobowam ya yi watsi da shawarar da dattawan mutanen su ka ba shi, sai ya yi shawara tare da matasan mutane waɗanda su ka yi girma tare da shi.
\v 9 Ya ce masu, "Wacce shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka yi magana da ni cewa, 'Ka rage wahalar da tsohonka ya aza mana?'"
\s5
\v 10 Matasan waɗanda su ka yi girma tare da Rehobowam su ka yi magana da shi, cewa, "Yi magana da mutanen nan waɗanda suka faɗa maka mahaifinka Suleman ya nawaita masu amma sai kai ka sauwaƙa masu. Sai ka ce da su, 'Karamin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri.
\v 11 To yanzu, ko da mahaifina ya wahalar da ku da bauta, zan ƙara maku nawayar. Mahaifina ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.'"
\s5
\v 12 Sai Yerobowom da dukkan mutane suka zo wurin Rehobowom a rana ta uku, kamar yadda sarki ya umarta a lokacin da ya ce, "Ku dawo wurina a rana ta uku."
\v 13 Sarki ya amsa wa mutanen da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi.
\v 14 Ya yi masu magana bisa ga shawarar matasa; ya ce, "Mahaifina ya nawaita maku, amma ni zan ƙara nawaita maku. mahaifina ya yi maku horo da bulala, amma ni zan yi maku da kunamai."
\s5
\v 15 Haka nan kuwa sarki bai saurari mutanen ba, gama wannan al'amarin ya zama haka bisa ga shirin Yahweh, akan yadda zai cika maganar da ya faɗa ta wurin Ahijah Bashiloniye zuwa ga Yerobowom ɗan Nebat.
\s5
\v 16 Sa'ad da dukkan mutane Isra'ila suka ga sarki bai saurare su ba, sai mutanen suka amsa masa suka ce, "Mene ne rabonmu da Dauda? Ba mu da gãdo a cikin ɗan Yesse! Ku tafi rumfunanku, Isra'ila. Yanzu ka duba gidanka, Dauda." Isra'ila suka koma rumfunansu.
\v 17 Amma mutanen Isra'ila waɗanda suka zauna a biranen Yahuda, Rehobowom ya zama sarkinsu.
\s5
\v 18 Sai sarki Rehobowom ya aiki Adoniram, wanda ya ke shi ne shugaban aikin tilas, amma dukkan Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowom da gaggawa ya hau karusarsa ya tsere zuwa Yerusalem.
\v 19 Mutanen Isra'ila kuwa suka tayar wa gidan Dauda har zuwa wannan rana.
\s5
\v 20 Ya zama haka dukkan Isra'ila suka ji Yerobowom ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron, suka naɗa shi sarki akan dukkan Isra'ila. Babu wanda ya bi iyalin Dauda, sai dai kabilar Yahuda.
\s5
\v 21 Da Rehobowom ya komo Yerusalem, ya tara dukkan mutanen gidan Yahuda da kabilar Benyamin; suka kai mayaƙa 180,000 mutanen da aka zaɓa sojoji, da za su yi faɗa gãba da gidan Isra'ila, domin su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowom ɗan Suleman.
\s5
\v 22 Amma maganar Allah ta zo ga Shemayya, mutumin Allah; ta ce,
\v 23 "Faɗa wa Rehobowom ɗan Suleman, sarkin Yahuda, da Benyamin da sauran jama'a, ka ce,
\v 24 "Yahweh ya ce wannan: Ba za ka yi yaƙi ko faɗa da 'yan'uwanku mutanen Isra'ila ba. Kowannenku ya koma gidansa, gama wannan al'amari ya faru ne daga gare ni.'" Sai suka saurari maganar Yahweh, suka juya suka koma hanyarsu, suka yi biyayya da maganarsa.
\s5
\v 25 Sai Yerobowom ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraim, ya zauna a can. Ya fita daga can ya gina Feniyel.
\v 26 Yerobowam kuwa ya yi tunani a cikin zuciyarsa, '"Yanzu mulki fa zai koma gidan Dauda.
\v 27 Idan waɗannan mutanen suka ci gaba da miƙa hadiyu a haikalin Yahweh a Yerusalem, sai zuciyar waɗannan mutane su juya su yi gãba da maigidansu, Reroboam sarkin Yahuda. Za su kashe ni su koma wurin Rehobowom sarkin Yahuda."
\s5
\v 28 Sai sarki Yerobowom ya nemi shawara ya siffanta 'yan maruka biyu da zinariya; ya cewa mutane, "Zai yi maku wuya don ku yi ta tafiya zuwa Yerusalem. Duba, ga waɗannan allolinku, ya Isra'ila, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar."
\v 29 Ya sa siffar ɗaya a Betel ɗaya kuma a Dan. Wannan abu ya zama zunubi.
\v 30 Mutane suka tafi wurin ɗaya ko ɗayan, dukka suka kama hanya zuwa Dan.
\s5
\v 31 Yerobowom ya gina masujadai a tuddai, ya kuma sa firistoci a cikin dukkan mutanen, waɗanda ba 'ya'yan Lebi ba.
\v 32 Yerobowom kuma ya sa a yi idi a watan takwas, ran goma sha biyar ga wata, kamar yadda ake yin idi a Yahuda, ya tafi bagadi. Ya yi kuma a Betel, hadayun siffofin maruƙan da ya yi a Betel ya sa firistoci a masujadan da ya gina.
\s5
\v 33 Yerobowom ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, a watan ya shirya a tunaninsa; ya yi biki don mutanen Isra'ila ya kuma tafi bagade ya ƙona turare.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Mutumin Allah ya fito daga Yahuda ta wurin maganar Yahweh zuwa Betel. Yerobowom yana tsaye kusa da bagadin ƙona turare.
\v 2 Ya yi kuka akan wannan mugunta ta bagadi ta wurin maganar Yahweh: "Bagadi, bagadi! Wannan shi ne abin da Yahweh ya fada, 'Duba, mai suna Yosiya za a haife shi a iyalin Dauda, da kai zan yi hadayun firistoci na masujadan tuddai waɗanda za su ƙona turare a kanka. A kanka kuma za su ƙona ƙasusuwan mutane.'"
\v 3 Sai mutumin Allah ya ba da alamar ranar, cewa, "Wannan shi ne alamar da Yahweh ya yi magana: 'Duba, za a rushe bagadin, za a kuma watsar da tokar waje.'"
\s5
\v 4 Da sarki ya ji abin da mutumin Allah ya ce, sai ya yi kuka akan bagadin da ya ke Betel, Yerobowam ya miƙa hannunsa daga bagadin, cewa, "Ku kama shi. "Sai hannun da ya miƙa akan mutumin ya bushe, domin bai iya komo da shi ba.
\v 5 (Aka rushe bagadin aka kuma zubar da tokar bagadin, alamar da mutumin Allah ya ba da bisa ga maganar Yahweh.)
\s5
\v 6 Sarki Yerobowom ya amsa ya ce da mutumin Allah, "Ka yi roƙo domin in sami tagomashi a wurin Yahweh Allahnka kuma ka yi addu'a domina, saboda ya warkar da hannuna." Mutumin Allah ya yi addu'a ga Yahweh, hannun sarki kuwa ya dawo gare shi kuma, dai-dai kamar yadda ya ke a dã.
\v 7 Sarki ya ce da mutumin Allah, "Ka zo gida tare da ni ka shakata, zan ba ka lada."
\s5
\v 8 Mutumin Allah kuwa ya ce da sarki, "Ko da za ka ba ni rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ko in ci abinci ko in sha ruwa a wannan wurin ba,
\v 9 gama Yahweh ya umarce ni ta wurin maganarsa, 'Ba za ka ci gurasa ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo ba.'"
\v 10 Haka kuwa mutumin Allah ya koma ta wata hanya dabam zuwa gidansa ba ta hanyar da ya zo Betel ba.
\s5
\v 11 To akwai wani tsohon annabi wanda ke zaune a Betel, ɗaya daga cikin 'ya 'yansa maza ya tafi ya faɗa masa dukkan abubuwan da mutumin Allah ya yi a wannan rana a Betel. 'Ya'yansa kuwa suka faɗa wa mahaifinsu maganar da mutumin Allah ya faɗa wa sarki.
\v 12 Mahaifinsu ya ce da su, "Wacce hanyar ya bi ya tafi?" 'Ya'yansa sun ga hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi ya tafi.
\v 13 Ya ce da 'ya'yansa ku ɗaura wa jaki shimfiɗa domina." Sai suka ɗaura wa jaki shimfiɗa, shi kuwa ya hau ya tafi.
\s5
\v 14 Tsohon annabin ya bi bayan mutumin Allah har ya same shi yana zama a ƙarƙashin itacen rimi; ya ce masa, "Kai ne mutumin Allahn nan da ya zo daga Yahuda?" Ya amsa, "I, ni ne."
\v 15 Sai tsohon annabi ya ce da shi, "Zo gida tare da ni ka ci abinci."
\v 16 Mutumin Allah ya amsa, ba zan koma tare da kai ba ko kuwa in shiga tare da kai, ko kuwa in ci abinci ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri,
\v 17 gama umarni gare ni ta wurin maganar Yahweh, 'ba za ka ci wani abinci ko ka sha ruwa a wurin ba, ko ka koma ta hanyar da ka zo.'"
\s5
\v 18 Sai tsohon annabin ya ce da shi, "Ai ni ma annabi ne kamar ka, mala'ika ya yi magana da ni ta wurin maganar Yahweh, cewa, 'Ka zo da shi tare da kai cikin gidanka, don ya ci abinci ya sha ruwa.'" Amma ƙarya ce tsohon annabin ya ke faɗa wa mutumin Allah.
\v 19 Saboda haka sai mutumin Allah ya koma tare da tsohon annabi ya ci abinci ya kuma sha ruwa a gidansa.
\s5
\v 20 Ya yin da suka zauna a tebur, sai maganar Yahweh ta zo ga annabi wanda ya komo da shi,
\v 21 sai ya kira mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, cewa, "Yahweh ya ce, 'Domin ka yi rashin biyayya da maganar Yahweh, ba ka kuma kiyaye umarnin Yahweh Allahnka da ya ba ka ba,
\v 22 amma ka komo ka ci abinci ka sha ruwa a wannan wurin wanda Yahweh ya faɗa ma ka kada ka ci abinci ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a bizne jikinka a kabarin ubanninka ba.'"
\s5
\v 23 Bayan da ya ci abinci, ya kuma sha, sai annabin ya ɗaura wa jakin mutumin Allah sirdi, da kuma mutumin da ya komo tare da shi.
\v 24 Sa'ad da mutumin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya ya kashe shi, ya bar gawar akan hanya. Sai jakin ya tsaya a gefenta, haka nan ma zaki ya tsaya kusa da gawar.
\v 25 Sa'ad da mutane da ke wucewa ta wurin suka ga an yar da gawar akan hanya, zaki kuma ya tsaya a gefenta, suka zo suka faɗa a cikin birnin da tsohon annabi ya ke.
\s5
\v 26 Sa'ad da annabi wanda ya komo da shi daga hanyar ya ji, sai ya ce, "Wannan mutumin Allah ne wanda bai yi biyayya da maganar Yahweh ba. Saboda haka Yahweh ya ba da shi ga zaki, wanda ya yayyage shi, ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Yahweh ta gargaɗe shi."
\v 27 Sai tsohon annabi ya yi magana da 'ya 'yansa maza, cewa, "Ku ɗaura wa jakina sirdi," su kuma suka ɗaura wa jakin sirdi.
\v 28 Ya tafi ya sami gawar an bar ta a hanya, jakin da zaki su na tsaye a gefen gawar. Zaki bai ci gawar ba, ko ma ya farma jakin.
\s5
\v 29 Annabin ya ɗauki gawar mutumin Allah, ya ɗora ta akan jaki, ya komo da ita. Ya zo da ita birninsa ya yi makoki ya bizne shi.
\v 30 Ya bizne gawar a cikin kabarinsa, suka yi makoki domin sa, cewa. "Kaito, ɗan'uwana!"
\s5
\v 31 To bayan da ya bizne shi, tsohon annabin ya faɗa wa 'ya'yansa maza, cewa, "Sa'ad da na mutu, ku bizne ni a cikin kabari inda aka bizne mutumin Allah. Ku sa ƙasusuwana a kusa da nasa.
\v 32 Gama an furta saƙon maganar Yahweh, a bagadin da ke Betel da kuma dukkan gidajen da ke kan tuddai a biranen Samariya, abin da lallai zai faru."
\s5
\v 33 Bayan wannan Yerobowom bai juyo daga muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci don masujadai da ke kan tuddai a cikin dukkan mutane. Duk wanda ya ke so sai ya karɓe shi a matsayin firist.
\v 34 Wannan abu ya zama zunubi ga iyalin Yerobowam ya yi dalilin da aka hallaka iyalinsa aka kuma shafe su kakaf daga fuskar duniya.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 A lokacin nan Abija ɗan Yerobowom ba shi da lafiya sosai.
\v 2 Yerobowom ya cewa matarsa, "Idan kin yarda ki tashi ki bad da kamarki, don ka da a gane ke matata ce, ki tafi Shilo, domin Ahija annabi yana can, shi ne wanda ya ce mani zan zama sarki akan waɗannan mutane.
\v 3 Tare da ke ki ɗauki malmalar abinci goma, da waina da kurtun zuma, ki tafi wurin Ahija. Zai faɗa ma ki abin da zai faru da yaron."
\s5
\v 4 Matar Yerobowom kuwa ta yi haka; ta tashi ta tafi Shilo har ta iso gidan Ahija. Yanzu Ahija ba ya gani; saboda ya rasa gani don tsufa.
\v 5 Yahweh ya cewa Ahija, "Duba, ga matar Yerobowom ta na zuwa ta nemi shawara daga gare ka akan ɗanta, domin ba shi da lafiya. Ka ce haka, da haka da ita, gama sa'ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam."
\s5
\v 6 Sa'ad da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin kofa, ya ce, "Ki shigo ciki, matar Yerobowam. Meyasa ki ke yi kamar ba ke ce ba? An aiko ni gare ki da labari mara daɗi.
\v 7 Tafi, ki faɗa wa Yerobowam cewa Yahweh, Allah na Isra'ila ya ce, 'Na ɗaukaka daga cikin mutane na sa ka zama shugaba akan mutanena Isra'ila.
\v 8 Na yage mulki daga iyalin Dauda na baka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dauda ba, wanda ya kiyaye umarnina ya bi ni da dukkan zuciyarsa, ya yi abin da ke dai-dai a idanuna.
\s5
\v 9 Maimako haka, ka aikata mugunta, fiye da dukkan waɗanda suka riga ka. Ka yi waɗansu alloli, ka yi siffofi na zubi ka tsokane ni in yi fushi, ka jefar da ni a bayanka.
\v 10 Saboda haka, duba, zan kawo masifa a iyalinka; zan datse daga gare ka kowanne ɗa namiji a Isra'ila, ko bawa ko 'yantacce, zan ƙori iyalinka gaba ɗaya, kamar mutum wanda ya ƙone juji kurmus.
\s5
\v 11 Duk wanda ya ke na iyalinka wanda ya mutu a birni karnuka su cinye shi, wanda kuma ya mutu a fili tsuntsayen sammai su cinye shi, gama ni, Yahweh na faɗa.
\v 12 Ki tashi, matar Yerobowom ki koma gidanki; ya yin da ƙafarki ta shiga birni, yaron Abija zai mutu.
\v 13 Dukkan mutanen Isra'ila za su yi makoki dominsa za a bizne shi. Shi kaɗai ne daga iyalin Yerobowom wanda zai je kabari, gama shi kaɗai ne, daga cikin gidan Yerobowom, aka sa me shi da aikata abu mai kyau a fuskar Yahweh, Allah na Isra'ila.
\s5
\v 14 Haka nan Yahweh zai ta da wani sarki a Isra'ila wanda zai yanke iyalin Yerobowom a wannan rana. Yau ita ce wannan rana, yanzun nan.
\v 15 Gama Yahweh zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a ruwa, zai tuge Isra'ila daga wannan ƙasa mai kyau wadda ya ba kakanninsu. Zai watsar da su bayan Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu turaku na Ashera domin su tsokani Yahweh ya yi fushi.
\v 16 Zai bayar da Isra'ila domin zunuban Yerobowom, zunuban da ya aikata, ta wurin sa Isra'ila su yi zunubi.
\s5
\v 17 Sai matar Yerobowom ta tashi ta tafi, ta zo Tirza. Tana zuwa bakin ƙofar gidanta kenan, yaron ya mutu.
\v 18 Dukkan Isra'ila su ka bizne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda aka faɗa masu ta wurin maganar Yahweh wanda ya yi magana ta wurin bawansa Ahija annabi.
\s5
\v 19 Game da sauran abubuwa akan Yerobowom, yadda ya yi yaƙe-yaƙensa da sarautarsa, duba, an rubuta su a cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
\v 20 Yerobowom ya yi mulki shekaru ashirin da biyu sa'an nan ya rasu tare da kakaninsa, ɗansa Nadab ya gaji sarauta a matsayin mahaifinsa.
\s5
\v 21 Yanzu Rehobowom ɗan Suleman ya yi mulki a Yahuda. Rehobowom yana da shekare arba'in da ɗaya sa'ad da ya zama sarki, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai a Yerusalem, birnin da Yahweh ya zaɓa daga dukkan kabilun Isra'ila in da ya sa sunansa. Sunan mahaifiyarsa kuwa Na'ama Ammoniya.
\v 22 Yahuda ta yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh; suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata, fiye da abin da kakanninsu suka yi.
\s5
\v 23 Gama suma sun gina wa kansu wuraren tsafi, ginshiƙan dutse da turken Ashera a kan kowanne tudu mai tsawo da ƙarƙashin kowanne koren itace.
\v 24 Akwai kuma karuwan tsafi a ƙasar. Suka yi abubuwan bankyama kamar al'ummai da Yahweh ya kawar daga wurin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 25 Wannan ya faru a shekara ta goma sha biyar ta mulkin Rehobowom da Shishak sarkin Masar ya gãba da Yerusalem.
\v 26 Ya kwashe dukiyar gidan Yahweh, da dukiyar gidan sarki. Ya ɗauke kome da kome ya tafi da shi; ya kuma ɗauki garkuwoyin zinariya waɗanda Suleman ya yi.
\s5
\v 27 Sarki Rehobowom ya yi garkuwoyin tagulla ya sa a hannun shugabannin masu tsaro, waɗanda ke tsaron ƙofar gidan sarki.
\v 28 Ya zamana duk lokacin da sarki zai shiga gidan Yahweh, matsara za su ɗauke su; sai su kawo su a gidan tsaro.
\s5
\v 29 Game da sauran abubuwa akan Rehobowom, dukkan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuda.
\v 30 Kullum ana ta yin yaƙi tsakanin Rehobowom da Yerobowom.
\v 31 Rehobowom kuwa ya yi barci tare da kakaninsa aka kuma bizne shi tare da su a birnin Dauda. Sunan mahaifiyarsa kuwa Na'ama daga Ammoniyawa. Abija ya gaji sarauta a matsayin mahaifinsa.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 A shekara ta goma sha takwas ta sarki Yerobowom ɗan Nebat, Abija ya fara sarauta akan Yahuda.
\v 2 Ya yi mulki shekaru uku a Yerusalem. Sunan mahaifiyarsa Ma'aka. Ita ɗiyar Abishalom ce.
\v 3 Shi ma ya yi tafiya a cikin dukkan irin zunubai da tsohonsa ya yi a lokacinsa; bai ba Yahweh Allahnsa dukkan zuciyarsa ba kamar yadda Dauda kakansa ya yi ba.
\s5
\v 4 Duk da haka, saboda Dauda, Yahweh Allahnsa ya ba shi fitila a Yerusalem ta wurin ba ɗansa ya gaje shi saboda ya ƙarfafa Yerusalem.
\v 5 Allah ya yi wannan domin Dauda ya yi abin da ke dai-dai a idanuwansa; a cikin dukkan kwanakin ransa, bai juya daga kowanne umarnin da aka ba shi ba, sai dai akan Yuriya Bahitte.
\v 6 Yanzu akwai yaƙi a tsakanin Abija ɗan Yerobowom dukkan kwanakin rayuwar Abija.
\s5
\v 7 Kamar sauran ayyukan Abija, duk da abubuwan da ya yi, ba suna rubuce a cikin littafin tarihi na sarakunan Yahuda ba? Akwai yaƙi tsakanin Abija ɗan Yerobowom.
\v 8 Abija ya barci tare da kakaninsa, su ka bizne ne shi a birnin Dauda. Asa ɗansa ya zama sarki a maimakon mahaifinsa.
\s5
\v 9 A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowom sarkin Isra'ila, Asa ya fara sarauta a Yahuda.
\v 10 Ya yi shekaru arba'in da ɗaya yana sarauta a Yerusalem. Sunan kakarsa kuwa Ma'aka, yar Abishalom.
\v 11 Asa ya yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh, kamar yadda Dauda, kakansa ya yi.
\s5
\v 12 Ya kori karuwai matsafa daga ƙasar ya kuma cire dukkan gumakun da kakaninsa suka yi.
\v 13 Ya kuma fitar Ma'aka da kakarsa, daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazamar siffa daga turken Ashera. Asa ya sassare ƙazamar siffar ya ƙone ta a Kwarin Kidron.
\s5
\v 14 Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba. Duk da haka, Asa ya ba Yahweh dukkan zuciyarsa a dukkan kwanakinsa.
\v 15 Ya kawo abubuwan da mahaifinsa ya keɓe da kuma azurfa da zinariya da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi a cikin gidan Yahweh.
\s5
\v 16 Akwai yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha sarkin Isra'ila, dukkan kwanakinsu.
\v 17 Ba'asha sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuda yaƙi ya gina Rama, don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga ƙasar Asa sarkin Yahuda.
\s5
\v 18 Sai Asa ya kwashe dukkan azurfa da zinariya da suka rage a ɗakunan ajiya na gidan Yahweh, da na ɗakin ajiyar fãdar sarki. Ya sa su a cikin hannuwan barorinsa su kai su ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda ke zaune a Damaskus. Ya ce.
\v 19 "Bari mu ƙulla alƙawari tsakani na da kai, kamar yadda ya ke tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Ka karya alƙawarinka da Ba'asha sarkin Isra'ila, domin ya bar ni."
\s5
\v 20 Ben-Hadad kuwa ya saurari sarki Asa ya kuma aika shugabanin sojojinsa su ka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka yi faɗa da Iyon da Dan da Abe ta bet Ma'aka, da dukkan Kenneret tare da dukkan ƙasar Naftali.
\v 21 Da Ba'asha ya ji wannan, sai ya daina ginin Rama ya koma Tirzah.
\v 22 Sa'an nan sarki Asa ya yi jawabi ga dukkan mutanen Yahuda. Ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi su ka ɗauki duwatsu da katakai a Ramah waɗanda Ba'asha ke gina birnin. Sai sarki Asa ya yi amfani da kayan ginin ya gina Geba ta Benyamin da Mizfa.
\s5
\v 23 Sauran dukkan abubuwa a game da Asa, dukkan ƙarfinsa, dukkan abubuwan da ya yi, da biranen da ya gina, ba su na nan ba a rubuce a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda?
\v 24 Amma lokacin tsufansa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa. Asa ya rasu tare kakaninsa aka kuma bizne shi tare da su a cikin birnin Dauda mahaifinsa. Yehoshafat ɗansa ya zama sarki a matsayinsa.
\s5
\v 25 Nadab ɗan Yerobowom ya fara sarauta a Isra'ila a shekara ta biyu ta sarki Asa na yin mulkin a Yahuda; ya yi sarautar Isra'ila shekaru biyu.
\v 26 Ya yi mugunta a fuskar Yahweh ya yi tafiya a hanyar da mahaifinsa ya yi a cikin zunubinsa, ya jagoranci Isra'ila su yi zunubi.
\s5
\v 27 Ba'asha ɗan Ahiji, na iyalin Issaka, ya yi wa Nadab maƙarƙashiya; Ba'asha kashe shi a Gibbeton wadda ke ta Filistiyawa, gama Nadab da dukkan Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.
\v 28 A cikin shekara ta uku da sarki Asa ke mulkin Yahuda, Ba'sha ya kashe Nadab ya kuma zama sarki a gurbinsa.
\s5
\v 29 Nan da nan da ya zama sarki, Ba"asha ya kashe dukkan iyalin Yerobowom. Bai bar kowa ba a zuriyar Yerobowom wanda ke numfashi ba; a wannan hanya ya hallakar da gidan sarautarsa, kamar yadda Yahweh ya faɗa ta wurin bawansa Ahija mutumin Shilo,
\v 30 domin zunuban Yerobowom wanda ya yi da kuma zunubin da ya sa mutanen Isra'ila suka yi, don ya tsokani Yahweh, Allah na Isra'ila ya yi fushi.
\s5
\v 31 Kamar sauran abubuwa a kan Nadab, da dukkan abin da ya yi, ba suna a rubuci ba a cikin littafin tarihi na ayyukan sarakunan Isra'ila?
\v 32 Akwai yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha sarkin Isra'ila a dukkan kwanakinsu.
\s5
\v 33 A cikin shekara ta uku da Asa sarkin Yahuda, Ba'asha ɗan Ahija ya fara sarauta akan dukkan Isra'ila a Tirza ya kuma yi mulki sheraka ashirin da huɗu.
\v 34 Ya yi abin da ke na mugunta a fuskar Yahweh ya kuma bi hanyar Yerobowom da kuma zunubin da ya sa Isra'ila suka yi.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Maganar Yahweh ta zo ga Yehu ɗan Hanani akan Ba'asha, cewa,
\v 2 "Ko da ya ke na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaba akan mutanena Isra'ila, kai kuwa ka yi tafiya irin ta Yerobowom ka sa mutanena Isra'ila sun aikata zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu.
\s5
\v 3 Duba, zan shafe Ba'asha da iyalinsa gaba ɗaya, zan maida iyalinka kamar iyalin Yerobowom ɗan Nebat.
\v 4 Karnuka ne za su cinye kowanne mutum da ke na Ba'asha idan ya mutu a birni, tsuntsayen sama kuma ne za su cinye kowanne mutum da ya mutu a saura."
\s5
\v 5 Sauran ayyuka akan Ba'asha, da abubuwan da ya yi, da ƙarfinsa, ba suna a rubuce a littafin tarihi na sarakunan Isra'ila ba?
\v 6 Ba'asha ya yi barci aka kuma bizne shi tare da kakanninsa a Tirzah, Ela ɗansa kuma ya zama sarki a gurbinsa.
\s5
\v 7 Sai maganar Yahweh ta zo wurin annabi Yehu ɗan Hanani akan Ba'asha da iyalinsa, duka kuma saboda dukkan mugutar da ya aikata a fuskar Yahweh, har ya yi fushi da ayyukan hannuwansa, kamar iyalin Yerobowom, kuma saboda ya hallaka dukkan iyalin Yerobowom.
\s5
\v 8 A shekara ta ashirin da shida da Asa ke mulkin Yahuda, Ela ɗan Ba'asha ya fara sarauta akan Isra'ila a Tirzah; ya yi sarauta shekaru biyu.
\v 9 Bawansa Zimri, shugaban rabin karusansa ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ela ya ke Tirzah, ya sha ya bugu a gidan Arza, wanda ya ke lura da fada a Tirzah.
\v 10 Zimri ya tafi cikin gidan, ya buge shi har ya kashe shi, a shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Asa sarkin Yahuda, ya zama sarki a gurbinsa.
\s5
\v 11 Da Zimri ya fara sarauta ya zauna akan kujerar mulki, yakashe dukkan iyalin Ba'asha. Bai bar namiji ko ɗaya a raye ba dangi ko abokai.
\v 12 Haka Zimri ya hallaka dukkan iyalin Ba'asha, bisa ga maganar da Yahweh wanda ya faɗa akan Ba'asha ta bakin annabi Yehu,
\v 13 saboda dukkan zunuban Ba'asha da zunuban Ela ɗansa su ka yi, da wanda su ka sa Isra'ila su ka yi, don sun tsokani Yahweh, Allah na Isra'ila, ya yi fushi da gumakunsu.
\s5
\v 14 Game da sauran ayyukan Ela, da dukkan abin da ya yi, ba suna a rubuce a cikin littafin tarihi na sarakunan Isra'ila ba?
\s5
\v 15 A shekara ta ashirin da bakwai da sarki Asa ke mulkin Yahuda, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirzah. A lokacin nan sojoji sun yi sansani a Gibbeton, wanda ta ke ta Filistiyawa.
\v 16 Sojojin da suka yi sansani a wurin suka ji an ce, "Zimri ya shirya makirci ya kashe sarki." A wannan rana a sansanin, dukkan mutanen Isra'ila suka naɗa Omri, shugaban sojojin, sarkin Isra'ila.
\v 17 Omri kuwa ya tafi daga Gibbeton da dukkan mutanen Israila tare da shi, su ka kewayeTirzah da yaƙi.
\s5
\v 18 Da Zimri ya ga an ci birnin sai ya tafi ya shiga hasumiyar da ta ke a fãdar sarki, ya sawa fãdar ginin wuta ta cinye duk da shi, ta wannan hanyar ya mutu a zafin wuta.
\v 19 Wannan ya faru saboda da zunuban da ya aikata ta wurin aikata mugunta a fuskar Yahweh, ya bi hanyar Yerobowam da zunuban da ya sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.
\v 20 Game da sauran ayyuka akan Zimri da makircin da ya aiwatar, ba a rubuce su ke ba a cikin littafin tarihi na sarakunan Isra'ila?
\s5
\v 21 Sai mutanen Isra'ila suka rabu gida biyu. Rabin mutanen suka bi Tibni ɗan Ginat, don su naɗa shi sarki, rabi kuma suka bi Omri.
\v 22 Amma mutane waɗanda suka bi Omri suna da ƙarfi fiye da mutanen da suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki.
\s5
\v 23 Omri ya fara sarauta akan Isra'ila a shekara ta talatin da ɗaya ta Asa sarkin Yahuda, ya yi shekaru goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekaru shida yana mulki a Tirzah.
\v 24 Ya sayi tudun Samariya daga Shemer akan talanti biyu na azurfa. Ya gina birni a tudu aka kira sunansa birnin Samariya, bayan sunan Shemer, mai tudun.
\s5
\v 25 Omri kuwa ya aikata mugunta a fuskar Yahweh, ya yi mugunta fiye da dukkan waɗanda suka riga shi.
\v 26 Gama ya yi tafiya a dukkan hanyoyin da Yerobowom ɗan Nebat da irin zunubansa wanda ya sa Isra'ila suka yi zunubi, suka sa Yahweh, Allah na Isra'ila, fushi don gumakunsu na wofi.
\s5
\v 27 Game da sauran ayyuka wanda Omri ya yi, da ƙarfinsa da ya nuna, ba suna nan a cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 28 Omri kuwa ya yi barci, aka bizne shi tare da kakaninsa a Samariya, Ahab ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifnsa
\s5
\v 29 A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya fara sarauta a Isra'ila. Ahab ɗan Omri ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shekaru ashirin da biyu.
\v 30 Ahab ɗan Omri ya yi abubuwan da ke mugunta a fuskar Yahweh, fiye da dukkan waɗanda su ka riga shi.
\s5
\v 31 Da ya ke Ahab abu ne mai sauki a gare shi ya bi zunuban Yerobowom ɗan Nebat, sai ya auro matarsa Yezebel 'yar Etba'al, sarkin Sidon; ya je yana bauta wa Ba'al, yana kuma yi masa sujada.
\v 32 Ya gina bagadi domin Ba'al a gidan Ba'al, wanda ya gina a Samariya.
\v 33 Ahab kuma ya yi turken gunkiyar nan Ashera. Ahab dai ya yi abin da zai tsokani Yahweh Allah na Isra'ila, zuwa fushi fiye da dukkan sarakunan Isra'ila waɗanda suka riga shi.
\s5
\v 34 A lokacin sarautar Ahab, Hiyel na Betel ya gina Yariko. Hiyel ya sa tushen birni da farashin ran Abiram, ɗan farinsa; Segub, ɗan autansa, ya rasa ransa a lokacin da ya ke gina ƙofofin birnin, ta cikin ajiye maganar Yahweh wanda ya yi magana ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Iliya Batishbe, daga Tishbi a Giliyad, ya ce da Ahab, "Kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila ya ke raye wanda nake tsaye a gabansa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a waɗannan shekaru sai da faɗata."
\s5
\v 2 Maganar Yahweh ta zo ga Iliya, cewa,
\v 3 "Tashi daga nan ka tafi wajen gabas; ka ɓoye kanka a rafin Kerit, gabashin Yodan.
\v 4 A can zai zamana inda za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can."
\s5
\v 5 Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Yahweh ya umarta. Ya tafi ya zauna a rafin Kerit, gabas da Yodan.
\v 6 Hankaki kuwa suka riƙa kawo masa abinci da nama da safe abinci da nama da maraice, yana shan ruwa daga rafin.
\v 7 Amma bayan wani ɗan lokaci sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.
\s5
\v 8 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya, cewa.
\v 9 "Tashi ka tafi Zarefat, wadda da ta ke ta Sidon, ka zauna a can. Duba, na umarci wata mace gwauruwa ta ciyar da kai."
\v 10 Shi kuwa ya tashi ya tafi Zarefat, sa'ad da ya isa ƙofar birnin sai ga wata gwauruwa a wurin ta na tattara itace. Sai ya kira ta ya ce, "Idan kin yarda ki kawo mani ɗan ruwa in sha."
\s5
\v 11 Tana juyawa za ta tafi ta kawo masa ruwan sha kenan, sai ya kira ta ya ce, "Idan kin yarda ki ba ni ɗan abinci a hannunki."
\v 12 Sai ta amsa, "Kamar yadda Yahweh Allahnka ya ke da rai, ba ni da abinci, sai dai ɗan garin da ya ragu a tukunya da ɗan man da ke cikin kwalba. Ga ni, ina tattara yan itatuwa biyu don in je in girka shi domin ni da ɗana, mu ci, mu mutu."
\v 13 Iliya ya ce mata, "Kada ki ji tsoro. Tafi ki yi yadda na ce, amma ki fara yi mani gurasa kaɗan tukuna ki kawo mani. Sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki.
\s5
\v 14 Gama Yahweh Allah na Isra'ila, ya ce, 'Garin da ya ke a tukunyarki ba zai ƙare ba, ko da man ma ba zai dena zubuwa ba, sai dai ranar da Yahweh ya aiko da ruwan sama a duniya."
\v 15 Ta tafi ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Ita da Iliya da sauran yan gidan, sun ci har kwanaki da yawa.
\v 16 Garin bai ƙare ba, kwalbar man ma bata dena zubuwa ba, kamar yadda maganar Yahweh ta ce, kamar kuma yadda Iliya ya faɗa.
\s5
\v 17 Bayan waɗannan abubuwa sai ɗan macen, matar wadda take da gidan, ya yi ciwo. Ciwonsa kuwa ya tsananta har ba sauran numfashi a cikinsa.
\v 18 Sai mahaifiyar yaron ta ce da Iliya, "Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo gare ni ne don ka tuna ma ni da zunubina ka kuma kashe ɗa na?"
\s5
\v 19 Sai Iliya ya amsa ma ta, "Ki ba ni ɗanki." Ya ɗauki yaron daga hannuwanta, ya kai shi a ɗaki inda ya ke zama, ya kwantar da yaron akan gadonsa.
\v 20 Ya yi kuka ga Yahweh ya ce, "Yahweh Allahna, ka kuma kawo masifa akan gwauruwar nan wadda na ke zaune wurinta, ta wurin kashe mata ɗa?
\v 21 Sa'an nan Iliya ya kwanta ya miƙe akan yaron sau uku, ya kuma yi kuka sosai ga Yahweh ya ce, "Yahweh Allahna, ina roƙonka, idan ka yarda bari ran yaron nan ya komo gare shi."
\s5
\v 22 Yahweh kuwa ya saurari muryar Iliya; ran yaron ya komo gare shi sai ya farfaɗo.
\v 23 Iliya ya ɗauki yaron daga ɗakinsa ya kawo shi ya kai shi cikin gida; ya bada yaron ga uwar ya ce, "Ki gani, ɗauki yaronki yana da rai." Matar kuwa ta cewa Iliya,
\v 24 "Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, kuma maganar Yahweh kuwa da ke cikin bakinka gaskiya ce."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Bayan kwanaki masu yawa sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya, a shekara ta uku ta farin, cewa,
\v 2 "Tafi, ka nuna kanka ga Ahab zan aiko da ruwan sama a ƙasar." Iliya kuwa ya tafi ya nuna kansa ga Ahab; yanzu kuwa yunwa ta tsananta a Samariya.
\s5
\v 3 Ahab ya kira Obadiya, wanda ya ke shugaban fada. Obadiya kuwa yana girmama Yahweh sosai,
\v 4 domin lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Yahweh, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin, hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su da gurasa ya kuma shayar da su.
\s5
\v 5 Ahab ya cewa Obadiya, "Tafi cikin ƙasar nan duk inda maɓuɓɓugar ruwa da fadamu suke. Watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa dukkan dabbobin nan."
\v 6 Saboda haka suka raba ƙasar a tsakaninsu suka shige ta su duba inda ruwa ya ke. Ahab ya bi ɗaya hanyar da kansa Obadiya kuma ya tafi wata hanyar.
\s5
\v 7 Sa'ad da Obadiya ya ke tafiya a hanya, Iliya ya yi kaciɓus da shi. Obadiya ya gane da shi sai ya russana a ƙasa. Ya ce, "Kai ne shugabana Iliya?"
\v 8 Iliya ya amsa masa. "Ni ne. Tafi ka faɗa wa shugabanka, 'Duba, Iliya na nan.'"
\s5
\v 9 Obadiya ya amsa, "Wanne zunubi na yi, har da za ka bada bawanka a cikin hannun Ahab, domin ya kashe ni?
\v 10 Kamar yadda Yahweh Allahnka ya ke raye, babu wata al'umma ko mulki da shugabana bai aika mutane a nemo ka ba. Duk wata al'umma ko mulki suka ce, 'Iliya ba ya nan,' Ahab ya sa su ɗauki rantsuwa ba su same ka ba.
\v 11 Amma yanzu ka ce, "Tafi, faɗa wa shugabana cewa ga Iliya a nan.'
\s5
\v 12 Ya yin da na tafi daga wurin ka, Ruhun Yahweh ya kai ka wurin da ban sani ba. Don haka idan na tafi na faɗa wa Ahab, idan kuma bai same ka ba, zai kashe ni. Ko da ya ke ni bawanka, ina bauta wa Yahweh tun daga kuruciyata.
\v 13 Ashe ba a faɗa maka ba, shugabana, abin da na yi a lokacin da Yezebel ta kashe annabawan Yahweh, abin da na yi na ɓoye annanbawan Yahweh ɗari na raba su hamsin hamsin a kogo na kuma ciyar da su da gurasa da ruwa?
\s5
\v 14 Yanzu kuwa ka ce da ni, "Tafi in faɗa wa shugabana ga Iliya a nan,' ai zai kashe ni."
\v 15 Sai Iliya ya amsa, "Kamar yadda Yahweh mai runduna ya ke da rai, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina ga Ahab yau."
\s5
\v 16 Saboda haka sai Obadiya ya tafi ya sadu da Ahab, ya faɗa masa abin da Iliya ya ce. Sai sarki ya tafi ya sadu da Iliya.
\v 17 Lokacin da Ahab ya ga Iliya, ya ce masa, "Kai ne? wanda ke kawo wahala ga Isra'ila!"
\s5
\v 18 Iliya ya amsa, "Ba ni ne na kawo wahala a Isra'ila ba, amma kai da iyalin mahaifinka su ne waɗanda suka jawo wahala ta wurin ƙin bin umarnan Yahweh kuna bin Ba'aloli.
\v 19 Yanzu sai, ka aika da magana a tattara mani dukkan Isra'ila a Tsaunin Karmel, tare da annabawan Ba'al 450 da ɗari huɗu na annabawan Ashera waɗanda ke ci a teburin Yezebel."
\s5
\v 20 Sai Ahab ya aika da magana ga dukkan mutanen Isra'ila da su tara annabawa gaba ɗaya a Dutsen Karmel.
\v 21 Iliya ya zo kusa da dukkan mutane ya ce, "Har yaushe ne za ku ci gaba da canza tunaninku? Idan Yahweh ne Allah, ku bi shi. Amma idan Ba'al shi ne Allah, sai ku bi shi." Duk da haka mutane ba su amsa masa da magana ba.
\s5
\v 22 Sai Iliya cewa mutane, "Ni, kaɗai ne na rage a matsayin annabin Yahweh, amma annabawan Ba'al su ɗari huɗu da hamsin.
\v 23 Ku ba mu bijimai biyu. Bari su zaɓi ɗaya bijimin don kansu su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa su akan itacen, kada a sa masa wuta a ƙarƙashinsa.
\v 24 Sai ku yi kira ga sunan allahnku, ni ma zan yi kira ga sunan Yahweh, duk Allahn da ya amsa da wuta bari ya kasance Allah. "Dukkan mutane suka amsa suka ce, "Wannan ya yi kyau."
\s5
\v 25 Sai Iliya yace da annabawan Ba'al, "Ku zaɓi bijimi ɗaya domin kanku ku kuma shirya shi da farko, gama kuna da mutane da yawa. Sa'an nan ku yi kira ga sunan allahnku, amma kada kuma fa ku sa wuta a ƙarƙashi bijimin."
\v 26 Suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi, suka yi kira da sunan Ba'al tun daga safe har rana ta yi tsaka, suna cewa, "Ba'al, ka ji mu mana." Amma babu wata murya, ko wani da ya amsa. Suka yi ta rawa a kewayan bagadin da suka gina.
\s5
\v 27 Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi masu ba'a ya ce, "Ku yi ihu da ƙarfi! Shi allah ne! Watakila ya yi tafiya da nisa, ko watakila yana barci ne, sai ku tashe shi."
\v 28 Suka yi ihu da ƙarfi sosai, suna kuma tsattsaga jikunansu, kamar yadda suke yi, tare da takubba da mãsu, har jini yana ta zuba daga jikunansu.
\v 29 Da tsakar rana ta wuce, sai su kai ta yin sambatu har lokacin baikon hadayar yamma, amma ba bu wata murya ko wani wanda ya amsa; babu wani wanda ya kula da roƙe -roƙensu.
\s5
\v 30 Sai Iliya yace da dukkan mutane, "Ku zo kusa da ni," dukkan mutane kuwa suka zo kusa da shi. Ya gyara bagadin Yahweh wanda aka lalatar.
\v 31 Iliya ya ɗauko duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan 'ya 'yan Yakubu, ga Yakubu wanda maganar Yahweh ta zo, cewa, "Isra'ila ne zai zama sunanka."
\v 32 Tare da duwatsun ya gina bagadi da sunan Yahweh, ya kuma haƙa rami babba sosai kewaye da bagadin isasshe da zai ci durom biyu na hatsi.
\s5
\v 33 Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Ya ce, "Ku cika tuluna da ruwa a kwarara akan hadaya ta ƙonawar da kuma kan itacen."
\v 34 Ya kuma ce, "Ku yi haka har sau lokaci na biyu," Suka yi haka a lokaci na biyu. Ya ce, "Su sake yi a lokaci na uku," suka yi haka a lokaci na uku.
\v 35 Ruwa kuwa ya malale bagadin, ya kuma cika ramin.
\s5
\v 36 Ya zama kuwa a lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai Iliya annabi ya matso kusa ya ce, "Yahweh, Allah na Ibrahim, na Ishaku da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa dukka bisa ga maganarka.
\v 37 Ka ji ni, Yahweh, ka ji ni, saboda waɗannan mutane su san ka, kai ne Yahweh, Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu gare ka kuma."
\s5
\v 38 Sai wutar Yahweh ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, duk da itacen, da duwatsun da kurar, ta kuma lashe ruwan da ya ke cikin ramin.
\v 39 Sa'ad da dukkan mutanen suka ga wannan, suka russana suka sunkuyar da kai suka ce, "Yahweh, shi ne Allah! Yahweh, shi ne Allah!"
\v 40 Iliya kuma ya ce masu, "Ku kama annabawan Ba'al. Ka da ku bar ko ɗaya daga cikinsu ya tsere." Sai suka kama su, Iliya ya kai annabawan Ba'al rafin Kishon, ya karkashe su a can.
\s5
\v 41 Iliya ya cewa Ahab, "Tashi, ka ci ka sha, gama akwai motsin saukowar ruwan sama."
\v 42 Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha. Iliya ya tafi can konkoli Karmel, ya zauna a ƙasa ya haɗa kai da gwiwa.
\s5
\v 43 Ya ce da baransa, "Ka tafi ka duba wajen teku." Baran ya tafi ya duba, ya ce, "Ba bu kome." Sai Iliya ce, "Tafi kuma, har sau bakwai."
\v 44 A zuwa na bakwai sai ya ce, "Na ga wani ɗan girgije yana zuwa daga teku, karami kamar tafin hannun mutum." Iliya ya amsa, "Tafi ka faɗa wa Ahab, 'Ya shirya karusarsa ya kuma gangara domin kada ruwan sama ya tsaida shi.'"
\s5
\v 45 Ya zamana fa jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da giza-gizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab ya hau ya tafi wurin Yezriyel,
\v 46 amma hannun Yahweh yana tare da Iliya. Ya sha ɗammara ya sheka a guje ya riga Ahab isa Yezriyel.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Ahab ya faɗa wa Yezebel dukkan abin da Iliya ya yi da yadda ya kashe dukkan annanbawa da takobi.
\v 2 Sai Yezebel ta aika wurin Iliya, cewa, "Bari alloli su yi mani, harma fiye kuma, idan ban mai da ran ka kamar ran ɗaya daga waɗannan annanbawa gobe a dai-dai wannan lokacin ba."
\v 3 Sa'ad da Iliya ya ji haka, ya ji tsoro, ya tsere domin ransa ya zo Biyasheba, wadda take ta Yahuda, ya bar baransa a can.
\s5
\v 4 Amma shi da kansa ya yi tafiyar yini guda cikin jeji, ya zo ya zauna a gindin itacen aduwa. Ya yi roƙo domin kansa yadda zai mutu, ya kuma ce, "Ya isa haka, yanzu, Yahweh; ɗauke raina, gama ban fi kakannina ba."
\v 5 Sai ya kwanta ya yi barci a gindin itace aduwa. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, "Tashi ka ci abinci."
\v 6 Da Iliya ya duba, kusa da kansa sai ga gurasa ana gasawa akan garwashi da butar ruwa. Ya ci, ya sha, ya koma ya kwanta kuma.
\s5
\v 7 Mala'ikan Yahweh kuma ya sake zuwa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, "Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za ta yi maka yawa.
\v 8 Sai ya tashi ya ci ya sha, ya sami ƙarfin tafiya da wannan abincin har kwana arba'in dare da rana zuwa Horeb, wato tsaunin Allah.
\s5
\v 9 Ya tafi wani kogo a can ya tsaya a cikinsa. Sai maganar Yahweh ta zo wurinsa ta ce da shi, "Me kake yi a nan, Iliya?
\v 10 Iliya ya amsa, "Ni mai kishi domin Yahweh, Allah mai runduna ne, gama mutanen Isra'ila suka manta da alƙawarin ka, suka lalata bagadanka, suka kuma karkashe annanbawanka da takobi. Yanzu ni kaɗai na rage da ba su kashe ba, suna ma ƙoƙarin su ɗauke raina."
\s5
\v 11 Yahweh ya amsa, "Tafi ka tsaya akan tsauni a gabana." Sai ga Yahweh yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsaga duwatsun, ta kuma farfasa shi rugu rugua gabanYahweh, amma Yahweh ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa ta zo, amma Yahweh ba ya cikin girgizar ƙasar.
\v 12 Bayan girgizar kuma sai wuta, amma Yahweh ba ya cikin wutar. Daga nan bayan wutar, sai natsastsar ƙaramar murya.
\s5
\v 13 Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai murya ta zo gare shi ta ce, "Me ka ke yi a nan, Iliya?
\v 14 Iliya ya amsa, "Ni na zama mai kishi domin Yahweh, Allah mai runduna ne, amma mutanen Israel sun karya alƙawarinka, suka lalata bagadannka suka kuma karkashe annabawanka da takobi. Yanzu ni, kaɗai na rage suna ma ƙoƙarin su ɗauki raina.
\s5
\v 15 Sai Yahweh yace da shi, "Tafi, ka juya akan hanyarka ta jeji kusa da Damaskus, idan ka isa can za ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya zama sarkin Aram,
\v 16 za ka kuma keɓe Yehu ɗan Nimshi ya zama sarkin Isra'ila, za ka kuma zuba wa Elisha ɗan Shafat na Abel Mehola mai ya zama annabi a gurbinka.
\s5
\v 17 Zai kasance Yehu zai kashe duk wanda ya tsere daga takobin Hazayel, Elisha zai kashe duk wanda ya tsere daga takobin Yehu.
\v 18 Amma zan barwa kaina mutum dubu bakwai na Isra'ila don kaina, waɗanda ba su russuna wa Ba'al da gwiwonsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakunansu ba."
\s5
\v 19 Iliya fa ya tashi daga wurin ya sami Elisha ɗan Shafat, wanda ke noma da shanun huɗa karkiya goma sha biyu, shi kansa kuma yana huɗa da karkiyar sha biyu. Iliya ya bi ta kusa da Elisha ya jefa masa alkyabbarsa.
\v 20 Sai Elisha ya bar shanun noman, ya sheka da gudu gun Iliya ya ce, "Idan ka yarda bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka." Sai Iliya ya ce da shi, "Koma, amma ka yi tunanin abin da na yi maka."
\s5
\v 21 Elisha ya komo daga wurin Iliya ya kama shanun noman, ya yanka dabbobin, ya dafa namansu da itace daga karkiyoyin. Sai ya ba mutane suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tara dukkan sojojinsa. Akwai sanannun sarakuna talatin da biyu da suke tare da shi, da dawakai da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya hari ya kuwa yi yaƙi da ita.
\v 2 Ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin Ahab sarkin Isra'ila, ya ce da shi, "Ben Hadad ya ce wannan:
\v 3 Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Matanka da 'ya'yanka, masu kyau, nawa ne.'"
\s5
\v 4 Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Ya kasance kamar yadda ka ce, shugabana, sarki. Ni da dukkan abin da na ke da shi naka ne."
\v 5 Jakadun suka dawo kuma suka ce, "Ben-Hadad ya ce wannan, 'Na aika maka da magana cewa dole ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka da 'ya'yanka.
\v 6 Amma zan aiko barorina wurinka gobe a dai-dai wannan lokacin, za su bincike gidanka da gidajen barorinka. Za su kwashe duk abin da ka ke da shi daga hannuwanka su ɗauke abubuwan da suka gamshi idanuwansu.'"
\s5
\v 7 Sai sarkin Isra'ila ya kirawo dukkan dattawan ƙasar ga baki ɗaya ya ce, "Idan kun yarda ku duba yadda wannan mutum ya ke neman rikici. Ya aiko wuri na domin in ba shi matana da 'ya'yana da azurfa da zinariyata, ni kuwa ban yardar masa ba."
\v 8 Dukkan dattawa da dukkan mutane suka cewa Ahab, "Kada ka saurare shi ko ka da mu da abin da ya ke so."
\s5
\v 9 Ahab ya ce da jakadun Ben-Hadad, "Ku faɗa wa shugabana sarki, 'Na yarda da dukkan abin da ka aiko barorinka su yi da farko, amma ba zan yarda da wannan buƙatar ta biyu ba.'" Jakadun kuwa suka koma da wannan amsa ga Ben-Hadad.
\v 10 Sai Ben-Hadad ya sake aikawa da saƙonsa ga Ahab, ya ce, "Bari alloli su yi mani haka harma fiye idan tokar Samariya ba za ta isa domin dukkan mutane waɗanda suka biyo ni kowannensu ya sami ɗan kaɗan ba.
\s5
\v 11 Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, "Ku faɗa wa Ben-Hadad, 'Ba wani wanda ya ke adali da zai sa sulke ya yi fahariya kamar ya ci yaƙin.'"
\v 12 Ben-Hadad ya ji wannan saƙo sa'ad da ya ke sha, shi da sarakuna da ke ƙarƙashinsa waɗanda suke cikin rumfunoni. Ben-Hadad ya umarce mutanensa, "Kowa ya tsaya a wurinsa domin yaƙi. "Suka shirya kansu suka tsaya domin yaƙin ya fada wa birnin.
\s5
\v 13 Sai ga wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra'ila ya ce, "Yahweh ya ce, "Ka ga wannan babban taron sojoji? Duba, zan ba da su a hannunka yau, za ka sani ni ne Yahweh.'"
\v 14 Ahab ya amsa, "Wane ne zai yi jagorar babbar rundunar?" Yahweh ya amsa ya ce, "Ta wurin matasan ofisoshi waɗanda su ke yi wa gwamnonin larduna hidima." Sai Ahab ya ce, "Wane ne zai fara yaƙin?" Yahweh ya amsa, "Kai ne."
\v 15 Sai Ahab ya tara matasan ofisoshi waɗanda suke yi wa gwamnonin larduna hidima. Su ɗari 232. Bayansu kuma ya tara dukkan sojoji da dukkan rundunar yaƙIn Isra'ila, jimilla dubu bakwai.
\s5
\v 16 Suka tafi da tsakar rana. Ben-Hadad yana a buge da abin sha a rumfa, shi da sarakunan da ke ƙarƙashinsa su talatin da biyu waɗanda suke goyan bayansa.
\v 17 Matasan ofisoshi waɗanda suke yi wa gwamnonin larduna hidima suka fara wucewa gaba. Sai Ben-Hadad ya ji labari ta wurin waɗanda ya aike su, "Mutane na zuwa daga Samariya."
\s5
\v 18 Ben-Hadad yace, "Ko da sun zo don salama ko da yaƙi, ku kama su da rai."
\v 19 Matasan ofisoshi waɗanda suke wa gwamnonin larduna hidima sun fita daga birnin sojoji kuma suna bin su.
\s5
\v 20 Kowa ya kashe abokin gãbarsa, Aremiyawa suka gudu. Isra'ila kuwa suka rutume su. Ben-Hadad sarkin Aram ya tsere akan doki tare da mahayan dawakai.
\v 21 Sarkin Isra'ila ya fita ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Aremiyawa masu yawa.
\s5
\v 22 Sa'an nan annabi ya je wurin sarkin Isra'ila ya ce da shi, "Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka fahimci shirin abin da zaka yi, gama da juyuwar shekara sarkin Aram zai zo maka da harin yaƙi."
\v 23 Barorin sarkin Aram suka ce da shi, "Na su allahn allah ne na tuddai. Don haka suka fi mu ƙarfi. Amma yanzu bari mu yi yaƙi da su a kwari, ba bu shakka za mu fi su ƙarfi.
\s5
\v 24 Dole ka yi wannan: ka fitar da sarakuna daga matsayinsu na shugabanci ka maida hafsoshin sojoji a mamadinsu.
\v 25 Ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa-dawakai domin dawakai da karusai domin karusai, mu kuma za mu yi yaƙi da su a kwari. Babu shakka za mu yi ƙarfi fiye da su." Ben-Hadad ya saurari shawararsu ya yi yadda suka ba da shawarar.
\s5
\v 26 Bayan farkon sabuwar shekara, Ben-Hadad ya tara Suriyawa su ka haura zuwa Afek su yi yaƙi da Isra'ila.
\v 27 Mutanen Isra'ila suka taru aka ba su guzuri da za su yi yaƙi da su. Mutanen Isra'ila suka kafa sasani a gabansu kamar kananan garkuna biyu na awaki, amma Aremiyawa suka cika ƙasar.
\s5
\v 28 Sai mutumin Allah ya zo kusa ya yi magana da sarkin Isra'ila ya ce, "Yahweh ya ce: 'Gama da ya ke Aremiyawa sun ce Yahweh shi allah na tuddai ne, amma ba shi ne allah na kwari ba, zan ba da dukkan wannan babban taron sojojin nan a hannunka, za ka sani Ni ne Yahweh.'"
\s5
\v 29 Sojojin suka kafa sansani daura da juna har kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin yaƙi ya fara. Mutanen Isra'ila suka kashe Aremiyawa nan ƙafa100,000 a rana ɗaya.
\v 30 Sauran suka gudu zuwa Afek, cikin birni, garun kuma ya faɗo akan mutune dubu ashirin da bakwai waɗanda suka rage. Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga cikin birni, cikin ƙuryar ɗaki.
\s5
\v 31 Barorin Ben-Hadad suka ce da shi, "Duba yanzu, mun ji cewa sarakunan gidan Isra'ila sarakuna ne masu jinƙai. Idan ka yarda bari mu sa tufafin makoki mu ɗaura igiyoyi a kawunanmu, mu tafi wurin sarkin Isra'ila. Watakila zai bar ka da rai."
\v 32 Sai suka sa tufafin makoki suka ɗaura igiyoyi a kawunansu suka tafi wurin sarkin Isra'ila suka ce, "Baranka Ben-Hadad ya ce, 'Idan ka yarda ka bar ni da rai.'" Ahab yace, "Har yanzu yana da rai? Shi ɗan'uwana ne."
\s5
\v 33 Yanzu mutanen suna sauraro kowace alama daga wurin Ahab, sai su yi saurin amsa masa, "I, ɗan'uwanka Ben-Hadad yana da rai." Sai Ahab ya ce, "Ku tafi ku kawo shi." Sai Ben-Hadad ya zo wurin sa, Ahab ya sa ya shiga da shi cikin karusarsa.
\v 34 Ben-Hadad ya ce da Ahab, "Zan dawo maka da biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, kai kuma za ka yi kasuwanci a Damaskus, kamar yadda tsohona ya yi a Samariya." Ahab ya ba shi amsa, "Zan bar ka, ka tafi a kan alƙawari." Ahab ya yi alƙawari da shi, sa'an nan ya bar shi ya tafi.
\s5
\v 35 Sai ga wani mutum, ɗaya daga cikin 'ya'yan annabawa, ya ce da ɗaya daga abokansa annabawa bisa ga maganar Yahweh, "Idan ka yarda ka buge ni." Amma mutumin ya ƙi ya buge shi.
\v 36 Sai annabin ya ce da abokinsa annabi, "Da ya ke ba ka yi biyayya da muryar Yahweh ba, da zarar ka tashi daga wurina, zaki zai kashe ka." Da ya tashi daga wurinsa kuwa zaki ya zo ya gamu da shi, ya kashe shi.
\s5
\v 37 Annabin kuma ya sami wani mutum ya ce, "Idan ka yarda ka buge ni." Mutumin kuwa ya buge shi har ya ji masa ciwo.
\v 38 Sai annabin ya tafi ya jira sarki a hanya; ya bad da kama, ya rufe idanunsa da ƙyalle.
\s5
\v 39 Sa'ad da sarki ya ke wucewa, sai annabi ya kira sarki ya ce, "Ni baranka na tafi wurin yaƙi mai zafi, sai soja ya tsaya ya kawo mani abokin gãba ya ce, 'Kula da wannan mutum. Idan wani abu ya sa ya tsere, za ka ba da ranka domin ransa, ko kuma ka biya talanti ɗaya na azurfa.'
\v 40 Gama da ya ke baranka yana fama da kai da kawowa, abokin gãbar soja ya tsere." Sai sarkin Isra'ila ya ce da shi, "Wannan shi ne irin hukuncin da zan yi - kai da kanka ka shawarta haka."
\s5
\v 41 Sai annabi ya yi sauri ya cire ƙyalle daga idanunsa, sarkin Isra'ila ya gane, ashe ɗaya daga cikin annabawa ne.
\v 42 Annabin ya cewa sarki, "Yahweh ya ce, 'Da ya ke ka bar shi ya tafi daga hannunka mutum wanda na ƙaddara ga mutuwa, ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka kuma maimakon mutanensa.'"
\v 43 Sarkin Isra'ila kuwa ya tafi gidansa da baƙinciki, a Samariya.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 A wani lokaci kuma, Nabot Bayezrile yana da gonar inabi a Yezriyel, kusa da fãdar Ahab, sarkin Samariya.
\v 2 Ahab ya yi magana da Nabot cewa, "Ka ba ni gonar inabinka, don in mai da ita lambu, domin gonar tana kusa da gidana. Ni kuwa zan ba ka wata gonar inabin mai kyau, ko kuma idan kana so, sai in biya ka tamanin kuɗinta."
\s5
\v 3 Amma Nabot ya amsa wa Ahab, "Yahweh ya sawwake in ba ka gãdon kakannina."
\v 4 Ahab ya koma fãdarsa da baƙinciki, saboda amsar da Nabot Bayezrile ya ba shi da ya ce, "Ni ba zan ba ka gãdon kakannina ba." Ya zauna akan gado, ya juya fuskarsa, ya ƙi cin kowanne abinci.
\s5
\v 5 Yezebel matarsa ta zo wuinsa, ta ce da shi, "Me ya sa zuciyarka ta da mu, har ka ƙi cin kowanne abinci?"
\v 6 Ya amsa mata, "Domin na yi magana da Nabot Bayezrile, na ce masa, 'Ya ba ni gonar inabinsa don in saya, idan ya yarda, zan ba ka wata gonar inabin ta zama ta ka.' Sai ya amsa mani, 'ba zan ba ka gonar inabina ba.'"
\v 7 Yezebel matarsa ta amsa masa, "Ba kai ne ka ke mulkin Isra'ila ba? Tashi ka ci abinci; bari zuciyarka ta yi farinciki, zan samar maka gonar inabin Nabot Bayezrile."
\s5
\v 8 Yezebel ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da su zuwa ga dattawa da mawadata masu kuɗi waɗanda suke zaune tare da shi a taruruka, da waɗanda suke zama kusa da Nabot.
\v 9 Ta rubuta a wasiƙun, cewa, "A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban mutane.
\v 10 A kuma sa 'yan iskan mutane biyu su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, 'Ka zagi Allah da sarki.'" Sa'an nan ku tafi da shi waje, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.
\s5
\v 11 Mutanen birnin da dattawa da masu arzaki da ke zaune a birnin Nabot, suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika masu.
\v 12 Su kuwa suka yi shelar azumi, suka zaunar da Nabot a gaban mutane.
\v 13 Sai mutune biyu suka zo, suka zauna a gaban Nabot suka yi ta shaidar zur akan Nabot a gaban mutane, cewa, "Nabot ya zagi Allah da sarki." Sai suka ɗauke shi wajen birni suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.
\v 14 Dattawa suka aika da magana ga Yezebel, cewa, "An jajjefe Nabot da duwatsu ya mutu."
\s5
\v 15 Yayin da Yezebel ta ji labari an jajjefe Nabot da duwatsu har ya mutu, sai ta ce da Ahab, "Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot Bayezrile wadda ya ƙi ya ba ka, ka ba shi kuɗi, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu."
\v 16 Da Ahab ya ji labarin Nabot Bayezrile ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezrile ya ɗauke ta ya mallake ta.
\s5
\v 17 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya Batishbe, cewa,
\v 18 "Tashi ka tafi ka sadu da Ahab sarkin Isra'ila, wanda ya ke zaune a Samariya. Yana cikin gonar inabin Nabot, inda ya tafi don ya mallake ta.
\s5
\v 19 Dole ka yi magana da shi ka ce Yahweh ya ce, 'Ka yi kisa, ka kuma ɗauki abin da ya mallaka? Sai ka faɗa masa Yahweh ya ce, 'A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka, i, jininka.'"
\v 20 Ahab ya ce da Iliya, "Ka same ni ko, maƙiyina?" Iliya ya amsa, na same ka, gama ka bada kanka ga aikata abin da ke mugunta a fuskar Yahweh.
\s5
\v 21 Yahweh yace wannan da kai: 'Duba, zan kawo maka masifa, in shafe ka, in datse daga gare ka kowanne ɗa namiji bawa ko 'yantarcen mutum a Isra'ila.
\v 22 Zan sa iyalinka kamar iyalin Yerobowam ɗan Nebat, su kuma zama kamar iyalin Ba'asha ɗan Ahija, saboda ka sani har na yi fushi, ka kuma sa mutanen Israila sun yi zunubi.'
\s5
\v 23 Yahweh kuma ya sake yin magana akan Yezebel, cewa, 'Karnuka za su cinye Yezebel a gefen katangar Yezriyel.'
\v 24 Duk wanda ya ke na Ahab da zai mutu a birni karnuka ne za su cinye shi, tsuntsayen sararin sama ne kuma za su cinye duk wanda ya mutu a saura."
\s5
\v 25 Babu wani kamar Ahab, da ya ba da kansa ga aikata mugunta a fuskar Yahweh, wanda matarsa Yezebel ta zuga shi yin zunubi.
\v 26 Ahab ya yi abin banƙyama ƙwarai saboda ya bi gumaka, kamar yadda Amoriyawa suka yi, waɗanda Yahweh ya kore su a gaban mutanen Isra'ila.
\s5
\v 27 Da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, ya yage tufafinsa ya sa na makoki a jikinsa, ya yi azumi, ya kuma kwanta a tsummokaran makoki, ya zama da damuwa.
\v 28 Sai maganar Yahweh ta zo ga Iliya Batishbe, cewa,
\v 29 "Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da ya ke ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba; sai dai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a cikin iyalinsa."
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Shekaru uku da suka wuce ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra'ila ba.
\v 2 Sai a cikin shekara ta uku ɗin, Yehoshafat sarkin Yahuda ya tafi wurin sarkin Isra'ila.
\s5
\v 3 Sarkin Isra'ila ya ce da barorinsa, "Ko kun san Ramot Giliyad tamu ce, amma ba ma yin komai domin mu ƙwace ta daga hannun sarkin Aram?"
\v 4 Ya ce da Yehoshafat, "Za ka tafi tare da ni zuwa yaƙi a Ramot Giliyad?" Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra'ila, "Ni kamar ka ne, mutanena kuma kamar mutanenka ne, dawakaina suna kamar naka ne."
\s5
\v 5 Yehoshafat ya cewa sarkin Isra'ila, "Idan ka yarda ka nemi shawara daga Yahweh duk abin da za ka yi tukuna."
\v 6 Sai sarkin Isra'ila ya tara annabawa wuri ɗaya, mutane ɗari huɗu ne, ya ce da su, "In tafi in yi yaƙi a Ramot Giliyad, ko kuwa kada in tafi?" Suka ce, "Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki."
\s5
\v 7 Amma Yehoshafat ya ce, "Ba wani annabin Yahweh ne a nan wanda za mu nemi shawara daga wurinsa?
\v 8 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu nemi shawara daga Yahweh da zai taimaka, Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, amma sai dai na masifa." Amma Yehoshafat ya ce, "Kada sarki ya ce haka."
\v 9 Sa'an nan sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafade, ya bada umarni, "Kawo Mikaiya ɗan Imla, yanzu a nan."
\s5
\v 10 Ahab sarkin Isra'ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune akan gãdon sarautarsu saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya, da dukkan annabawa suna ananbci a gabansu.
\v 11 Zedekiya ɗan Kena'ana ya yi wa kansa ƙahonin ƙarfe, ya ce, "Yahweh ya faɗi wannan: 'Tare da waɗannan za ka tunkuyi Aremiyawa har su hallaka.'"
\v 12 Dukkan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, cewa, "Ka haura zuwa Ramot Gileyad, zaka yi nasara, domin Yahweh zai ba da ita a hannun sarki."
\s5
\v 13 Ɗan saƙo wanda ya tafi ya kira Mikaiya ya yi magana da shi, cewa, duba yanzu, maganar annabawa abubuwa ne mai kyau ga sarki da baki ɗaya. Idan ka yarda bari maganarka ta zama kamar tasu ka faɗi abu mai kyau."
\v 14 Mikaiya ya amsa, "Kamar yadda Yahweh ke raye, ga abin da Yahweh ya ce da ni zan faɗa."
\v 15 Da ya zo gaban sarki, sarki ya ce da shi, "Mikaiya, mu tafi Ramot Giliyad don yaƙi, ko a'a?" Mikaiya ya amsa masa, "Ka haura za ka yi nasara, Yahweh zai ba da ita a hannun sarki."
\s5
\v 16 Sarki ya ce masa, "Sau nawa zan neme ka da ka rantse za ka faɗa mani kome idan ba gaskiya ba, da sunan Yahweh?"
\v 17 Mikaiya ya ce, "Na ga dukkan Isra'ila a warwatse akan tuddai, kamar tumaki waɗanda ba su da makiyayi, Yahweh ya ce, "Waɗannan ba su da makiyayi. Bari kowanne mutum ya koma gidansa da salama."
\s5
\v 18 Sarkin Isra'ila ya cewa Yehoshafat, "Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba, amma sai dai na masifa?"
\v 19 Mikaiya yace, "Saboda haka ka ji maganar Yahweh: na ga Yahweh yana zaune a kursiyansa tare da dukkan mala'ikun sama suna tsaye wajen damarsa da hagunsa.
\v 20 Yahweh yace, 'Wa zai yaudari Ahab, ya tafi ya faɗawa Ramot Giliyad?' Ɗaya daga cikin su ya faɗi wannan, wani kuma ya faɗi abu kaza.
\s5
\v 21 Sai wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Yahweh, ya ce, 'Ni zan yaudare shi.' Yahweh ya ce da shi, 'Ta ya ya?'
\v 22 Sai ruhun ya amsa, 'Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukkan annabawansa. 'Yahweh ya amsa, 'Kai za ka iya yaudarsa, za ka kuma yi nasara sosai. Tafi yanzu ka yi.'
\v 23 Duba yanzu, Yahweh ya sa ruhun ƙarya a bakin dukkan waɗannan annabawansa, Yahweh kuma ya zartar maka da masifa."
\s5
\v 24 Sai Zedekiya ɗan Kan'ana ya zo kusa ya mari Mikaiya a kumatu, ya ce, "Wacce hanya Ruhun Yahweh ya bar ni har ya zo wurinka ya yi magana da kai?"
\v 25 Mikaiya yace, "Duba, za ka sani a ranar nan, lokacin da ka gudu ka shiga har ƙuryar ɗaki don ka ɓuya."
\s5
\v 26 Sarkin Isra'ila ya ce da baransa, "Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, gwamnan birni, da Yowash, ɗana.
\v 27 Ku ce da shi, 'Sarki ya ce, a jefa wannan mutum a kurkuku a riƙa ciyar da shi da waina kaɗan da ruwan sha kaɗan, har sai na komo lafiya.'"
\v 28 Sai Mikaiya yace, "Idan har ka dawo lafiya, Yahweh bai yi magana da ni ba." Ya ƙara da cewa, "Ku saurari wannan, dukkan ku mutane."
\s5
\v 29 Ahab sarkin Isra'ila, da Yehoshafat sarkin Yahuda, sun tafi Ramot Giliyad.
\v 30 Sarkin Isra'ila ya ce da Yehoshafat, "Zan bad da kamata in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafin sarautarka." Sai sarkin Isra'ila ya bad da kamarsa ya tafi wurin yaƙi.
\s5
\v 31 Yanzu sarkin Aram ya rigaya ya umarci shugabannin karusan yaƙinsa su talatin da biyu, cewa, "Kada ku yi yaƙi da kowa komai matsayin sojojinsa. Sai dai sarkin Isra'ila kaɗai."
\v 32 Sa'ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat sai suka ce, "Babu shakka wannan shi ne sarkin Isra'ila." Sun juya don su yi yaƙi da shi, Yehoshafat kuwa ya yi ihu.
\v 33 Da shugabannin karusan yaƙi suka gane ba sarkin Isra'ila ba ne, sai su ka juya suka dena binsa.
\s5
\v 34 Sai wani mutum ya shilla kibiya kawai, sai ta sami sarkin Isra'ila a tsakanin ƙafar sulkensa. Ahab ya ce da mai kora karusarsa, "Ka juya ka ɗauke ni daga yaƙin nan gama an yi mani rauni sosai."
\s5
\v 35 A ran nan yaƙi ya yi tsanani ƙwarai, aka tallafi sarki a cikin karusarsa a gaban Aremiyawa. Ya mutu da yamma. Jinin yana fitowa daga raunin da aka yi masa yana zuba a cikin karusar.
\v 36 A lokacin faɗuwar rana aka yi wa sojoji shelar cewa, "Kowanne mutum ya koma birninsa kuma kowanne mutum ya koma jiharsa.
\s5
\v 37 Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, su ka bizne shi.
\v 38 Su ka wanke karusarsa a tafkin Samariya, karnuka su ka lashe jininsa (wannan shi ne wurin da karuwai su ke yin wanka a tafkin) kamar yadda Yahweh ya furta.
\s5
\v 39 Game da sauran al'amuran Ahab da dukkan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da biranen da ya gina, ba suna rubuce a littafin tarihin sarakunan Isra'ila ba?
\v 40 Ahab ya yi barci tare da kakaninsa, Ahaziya ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa.
\s5
\v 41 Yehoshafat ɗan Asa ya fara sarauta a Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra'ila.
\v 42 Yehoshafat yana da shekaru talatin da biyar sa'ad da ya fara sarauta, ya yi sarauta a Yerusalem yana da shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba 'yar Shilhi.
\s5
\v 43 Ya yi tafiya cikin hanyoyi irin na Asa, mahaifinsa; bai karkace daga gare su ba; ya yi abin da dai-dai a fuskar Yahweh. Duk da haka ba a ɗauke wuraren tsafi na tuddai ba. Mutanen sun ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a tuddan.
\v 44 Yehoshafat ya yi zaman salama da sarkin Isra'ila.
\s5
\v 45 Sauran ayyuka game da Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, ba suna rubuce a littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?
\v 46 Ya kori sauran karuwai daga ƙasar waɗanda suna nan tun zamanin mahaifinsa Asa.
\v 47 Babu sarki a Idom, amma wakili ne ya yi mulki a wurin.
\s5
\v 48 Yehoshafat ya yi jiragen ruwa, za su tafi Ofir domin zinariya, amma ba su iya tafiya ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon Geber.
\v 49 Sai Ahaziya ɗan Ahab ya ce da Yehoshafat, "Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage." Amma Yehoshafat bai yarda ba.
\v 50 Yehoshafat ya yi barci tare da kakaninsa aka bizne shi a wurin su a birnin Dauda, kakansa; Yahoram ɗansa ya zama sarki a gurbin mahaifinsa.
\s5
\v 51 Ahaziya ɗan Ahab ya fara sarauta a kan Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya yi sarauta shekara biyu a Isra'ila.
\v 52 Ya yi abin da ke mugu a fuskar Yahweh, ya yi tafiya ta hanyar mahaifinsa, a cikin hanyar mahaifiyarsa, da hanyar Yerobowom ɗan Nebot, wanda ya sa Isra'ila yin zunubi.
\v 53 Ya bauta wa Ba'al ya yi masa sujada, ya kuma tsokani Yahweh na Isra'ila ya yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi.