ha_ulb/10-2SA.usfm

1389 lines
105 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 2SA
\ide UTF-8
\h Littafin Sama'ila Na Biyu
\toc1 Littafin Sama'ila Na Biyu
\toc2 Littafin Sama'ila Na Biyu
\toc3 2sa
\mt Littafin Sama'ila Na Biyu
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Bayan mutuwar Saul, Dauda ya dawo daga harin Amelikawa ya kuma zauna a Ziglak kwana biyu.
\v 2 A rana ta uku, wani mutum ya zo daga sansanin Saul da tufafinsa a yage da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dauda sai ya kwanta rub da ciki a ƙasa ya miƙe jikinsa ya yi ruku'u a gabansa.
\s5
\v 3 Dauda ya ce masa, "Daga ina ka fito?" Ya amsa, "Na kubce daga sansanin Isra'ila ne."
\v 4 Dauda ya ce masa, Idan ka yarda ka gaya mani yadda abubuwa suka kasance." Ya amsa, "Mutane sun gudu daga yaƙi. Da yawa sun faɗi kuma da yawa sun mutu. Saul da Yonatan ɗansa su ma sun mutu."
\v 5 Dauda ya ce ma saurayin, "Yaya ka sani cewa Saul da Yonatan ɗansa sun mutu?"
\s5
\v 6 Saurayin ya amsa, "Sa'a ce na ci. ya zamana ne ina kan Dutsen Gilbowa, sai ga Saul yana jingine akan mashinsa, karusai da mahaya suka kusa rutsasu.
\v 7 Saul ya juya ya gan ni ya kuma kira ni da murya. Na amsa, 'Ga ni.'
\s5
\v 8 Ya ce mani, "Waye kai?" Na amsa masa, 'Ni Ba-amelike ne.'
\v 9 Ya ce mani, ' Idan ka yarda ka tsaya a kaina ka kasheni, gama zafin azaba ya sha kaina, amma duk da haka rai yana ciki na'
\v 10 Saboda haka na tsaya a kansa na kasheshi, domin na sani ba zai rayu ba bayan ya faɗi. Sa'an nan na ɗauki kambin da ke kansa da ɗamarar da ke damtsensa kuma, na kawo su nan gunka, ubangidana."
\s5
\v 11 Sai Dauda ya ƙeƙƙece tufafinsa dukkan mutanen da ke tare da shi suka yi haka su ma.
\v 12 Suka yi makoki, da kuka, kuma suka yi azumi har yamma saboda Saul, domin ɗansa Yonatan, domin mutanen Yahweh, domin kuma gidan Isra'ila sabili da sun faɗi ta hannun takobi.
\v 13 Dauda ya cewa saurayin, 'Daga ina ka ke?' Ya amsa, 'Ni yaron wani baƙo ne a ƙasar, Ba-amaleke."
\s5
\v 14 Dauda ya ce masa, "Me ya sa ba ka ji tsoron kashe shafaffen sarki na Yahweh da hannunka ba?"
\v 15 Dauda ya kira ɗaya daga cikin samarin ya ce, "Tafi ka kashe shi." Sai wannan mutumin ya tafi ya buga shi ƙasa. Sai Ba-ameliken ya mutu.
\v 16 Sai Dauda ya cewa mataccen Ba'ameliken, '" Alhakin jininka na kanka domin bakinka da kansa yana shaida gãba da kai ya ce, 'Na kashe shafaffen sarki na Yahweh.'"
\s5
\v 17 Sa'an nan Dauda ya yi wannan waƙar makoki game da Saul da Yonatan ɗansa.
\v 18 Ya bada doka ga mutane su koyar da Waƙar Bãka ga 'ya'yan Yahuda, wanda aka rubuta a Littafin Yashar.
\v 19 "Ɗaukakarki, Isra'ila, ya mutu, an yi kisa a tuddanki! Aiya jarumawa sun faɗi!
\v 20 Kada ku faɗa a Gat, kada ku yi shelarsa a titunan Askelon, domin kada 'yan'matan Filistiyawa su yi farinciki, domin kada 'yan'matan marasa kaciya su yi biki.
\s5
\v 21 Duwatsun Gilbowa, kada raɓa ko ruwan sama su kasance a kanku, ko gonaki masu bada hatsi domin baiko, gama a nan aka lalata garkuwar ƙarfafa. Garkuwar Saul ba a ƙara shafe ta da mai ba.
\v 22 Daga jinin waɗanda aka kashe, daga jikin ƙaƙƙarfa, bãkan Yonatan bai juya ba, kuma takobin Saul bata dawo wofi ba.
\s5
\v 23 Saul da Yonathan ƙaunatattu ne masu alheri a rayuwa, a mutuwarsu ba a raba su ba. Sun fi gaggafai zafin gudu, sun fi zakoki ƙarfi.
\v 24 Ku 'yan'matan Isra'ila, ku yi kuka domin Saul, wanda ya suturtar daku cikin shunayya da duwatsu masu daraja da kayan zinariya masu ƙayatarwa a tufafinku.
\s5
\v 25 Aiya jarumawa sun faɗi tsakiyar yaƙi! An kashe Yonatan a tuddanki,
\v 26 Ina da damuwa domin ka, ɗan'uwana Yonatan. Amintacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abin al'ajibi ne, ya zarce ƙaunar mata.
\v 27 Aiya jarumawa sun faɗi, makaman yaƙi kuma sun lalace!"
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Bayan wannan Dauda ya tambayi Yahweh ya ce, 'Ko in haura zuwa ɗaya daga cikin biranen Yahuda?" Yahweh ya amsa masa, "Ka haura." Dauda ya ce, "Wanne birnin zan je?" Yahweh ya amsa, "Zuwa Hebron."
\v 2 Sai Dauda ya tafi Hebron da matayensa guda biyu, Ahinowam daga Yezril, da Abigel daga Karmel, gwauruwar Nabal.
\v 3 Dauda ya kawo mutanen da ke tare da shi, waɗanda kowannen su ya kawo nasa iyalin, zuwa biranen Hebron inda suka fara zaunawa.
\s5
\v 4 Sa'an nan mutane daga Yahuda suka zo suka naɗa Dauda sarki bisa gidan Yahuda. Aka cewa Dauda, '"Mutanen Yabes Giliyad ne suka bizne Saul."
\v 5 Sai Dauda ya aiki manzanni ga mutanen Yabes Giliyad suka kuma ce masu, "Yahweh ya albarkace ku, tunda ku ka nuna wannan riƙon amana ga ubangidanku Saul har ku ka bizne shi.
\s5
\v 6 Bari yanzu Yahweh ya nuna maku alƙawarin riƙon amana da aminci. Ni kuma zan yi maku wannan alheri domin kun yi wannan abu.
\v 7 Yanzu dai, bari hannuwanku su ƙarfafa; ku yi ƙarfin hali domin Saul ubangidanku ya mutu kuma gidan Yahuda sun naɗa ni shafaffen sarki bisan su."
\s5
\v 8 Amma Abna ɗan Nã, sarkin yaƙin rundunar Saul, ya ɗauki Ishboshet ɗan Saul ya kuma kawo shi Mahanam,
\v 9 Ya naɗa Ishboshet sarki bisa Giliyad, Ashar, Yazril, Ifraim, Benyamin, da kuma bisa dukkan Isra'ila.
\s5
\v 10 Ishboshet ɗan Saul, yana da shekaru arba'in da ya soma mulki bisa Isra'ila, ya kuma yi mulki shekara biyu. Amma gidan Yahuda suka bi Dauda.
\v 11 Lokacin da Dauda ke sarki cikin Hebron bisa gidan Yahuda shekara bakwai ne da wata shida.
\s5
\v 12 Abna ɗan Nã, da barorin Ishboshet ɗan Saul, su ka tafi daga Mahanayim zuwa Gibiyan.
\v 13 Yowab ɗan Zeruya da barorin Dauda suka fita suka gamu da su a tafkin Gibiyan. A nan suka zauna, ɗaya ƙungiyar a ɗaya gefen tafkin ɗayan kuma a ɗaya wancan gefen.
\s5
\v 14 Abna ya cewa Yowab, "Bari samarin su tashi su yi gãsa a gabanmu." Sai Yowab ya ce, "Bari su tashi."
\v 15 Sai samarin suka tashi suka tattaru tare, sha biyu domin Benyami da Ishboshet ɗan Saul, kuma sha biyu daga barorin Dauda.
\s5
\v 16 Kowanne ya danƙe abokin gasarsa a kai ya soke gefen cikin ɗan'uwansa da takobi, sai su ka faɗi ƙasa tare. Shi ya sa aka kira wurin nan da Ibraniyanci, "Helkat Hazzurim." ko "Filin Takkuba" wanda ya ke cikin Gibiyan.
\v 17 Yaƙin ya yi zafi ainun a ranar nan kuma aka buga Abna da mutanen Isra'ila a gaban barorin Dauda.
\s5
\v 18 'Ya'ya maza uku na Zeruya suna wurin: Yowab, Abishai, da Asahel. Asahel mai zafin gudu da ƙafa ne kamar barewar jeji.
\v 19 Asahel ya sheƙa da gudu bayan Abna ya bishi kurkusa ba ratsewa wani gefen.
\s5
\v 20 Abna ya waiga bayansa ya ce, "Kai ne kuwa Asahel?" Ya amsa, "I, ni ne."
\v 21 Abna ya ce masa, "Ka juya zuwa gefenka na dama ko hagunka, ka cafke ɗaya daga cikin samarin ka karɓe makaminsa." Amma Asahel ya ƙi ratsewa wani gefen.
\s5
\v 22 Sai Abna ya sãke cewa Asahel, "Ka dena bi na donme zan buga ka ƙasa? Ƙaƙa kuma zan fuskanci, ɗan'uwanka Yowab?"
\v 23 Amma Asahel ya ƙi ratsewa, saboda haka Abna ya soki jikinsa da kan mashinsa marar kaifi har ma mashin ya fito ta wancan gefen. Asahel ya faɗi ya mutu. Ya zamana fa duk wanda ya iso inda Asahel ya faɗi ya mutu, sai ya dakata ya tsaya shuru.
\s5
\v 24 Amma Yowab da Abishai suka bi Abna. Sa'ad da rana take faɗuwa, suka iso tudun Amana, da ke kusa da Giya a hanyar da ta bi ta jejin Gibiyon.
\v 25 Mutanen Benyaminu suka haɗa kansu gaba ɗaya suka goyi bayan Abna suka tsaya a kan tudu.
\s5
\v 26 Sai Abna ya kira Yowab ya ce, "Dole ne takobi ya hallakar har abada? Ba ka sani zai zama da ɗaci a ƙarshe ba? Har yaushe zai zamana kafin ka gaya wa mutanenka su janye daga fafarar 'yan uwansu?"
\v 27 Yowab ya amsa, "Na rantse da Yahweh, hakika da baka faɗi haka ba, da sojojina sun fafari 'yan 'uwansu har zuwa safiya!"
\s5
\v 28 Sai Yowab ya busa ƙaho, mutanensa duk suka tsaya suka dena fafarar Isra'ila, kuma ba su sake yin faɗa ba.
\v 29 Abna da mutanensa suka yi ta tafiya dare farai cikin Araba. Suka haye Yodan, suka yi ta tafiya dukkan safiyan nan, sa'annan ne suka kai Mahanayim.
\s5
\v 30 Yowab ya juyo daga fafarar Abna. Ya tara dukkan mutanensa, cikinsu aka rasa Asahel da sojojin Dauda guda goma sha tara.
\v 31 Amma mutanen Dauda sun riga sun kashe mutane 360 na Benyamin da ke tare da Abna.
\v 32 Sai suka ɗauki Asahel suka binne shi cikin kabarin mahaifinsa, da ke a Baitalami. Yowab da mutanensa suka yi tafiya dare farai, gari kuma ya waye masu a Hebron.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Akwanakin nan dai aka yi dogon yaƙi tsakani gidan Saul da gidan Dauda. Gidan Dauda ya yi ta ƙara ƙarfi, amma gidan Saul ya yi ta raguwa.
\s5
\v 2 Aka haifa wa Dauda 'ya'ya maza a Hebron. Ɗan farinsa Amon, da Ahinowam daga Yazril ta haifa masa.
\v 3 Ɗansa na biyu, Kilyab, Abigel gwauruwar marigayi Nabal daga Karmel ta haifeshi, Ɗansa na ukun Absalom ne, ɗan Ma'aka, ɗiyar Talmai, sarki Geshu.
\s5
\v 4 Ɗan Dauda na huɗu, Adonija, ɗan Hagit ne. Ɗansa na biyar Sefatiya ne ɗan Abtiyal,
\v 5 na shidan, Itram ne, ɗan Egla matar Dauda. Waɗannan 'ya'ya maza aka haifa wa Dauda a Hebron.
\s5
\v 6 Ya zamana fa a lokacin yaƙi tsakanin gidan Saul da gidan Dauda sai Abna ya ƙarfafa kansa a gidan Saul.
\v 7 Saul na da kwarkwara wadda sunanta Risfa, ɗiyar Aya ce. Sai Ishboshet ya cewa Abna, "Me yasa ka kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?"
\s5
\v 8 Sai Abna ya husata da maganganun Ishboshet ya ce, "Ni kan kare ne na Yahuda? Yau ina nuna aminci ga gidan Saul, mahaifinka, da 'yan'uwansa, da kuma abokanansa, ta wurin yadda ban basheku ba cikin hannun Dauda. Amma yanzu kana zargi na da laifi game da wannan matar.
\s5
\v 9 Bari Allah ya yi mani, Abna, harma fiye da haka, idan ban yi wa Dauda yadda Yahweh ya rantse masa ba,
\v 10 a tada masarautar daga gidan Saul, a kafa kursiyin Dauda bisa Isra'ila da bisa Yahuda daga Dan zuwa Bayasheba."
\v 11 Ishboshet bai iya amsa wa Abna ba koda magana ɗaya, domin yana jin tsoronsa.
\s5
\v 12 Sa'an nan Abna ya aika manzanni ga Dauda su yi masa magana dominsa cewa, "Ƙasar wane ne wannan? Ka yi yarjejeniya da ni, gama hannuna na tare da kai, in kawo maka dukkan Isra'ila."
\v 13 Dauda ya amsa, "Da kyau zan yi yarjejeniya da kai. Abu ɗaya na ke biɗa a gare ka shi ne cewa ba za ka ga fuskata ba sai dai da farko ka kawo Mikal, ɗiyar Saul, sa'ad da za ka zo ka gan ni."
\s5
\v 14 Sai Dauda ya aika manzanni zuwa wurin Ishboshet, ɗan Saul, cewa, "Ka ba ni matata Ishboshet Mikal, wadda na biya sadakin loɓar kaciya ɗari na Filistiyawa domin ta.
\v 15 Sai Ishboshet ya aika a kawo Mikal, ya kuma karɓe ta daga mijinta, Faltiyel ɗan Layis.
\v 16 Mijinta ya tafi tare da ita, yana tafiya yana kuka, ya bi ta zuwa Bahurim. Sai Abna ya ce masa, "Ka koma gida yanzu." Sai ya koma.
\s5
\v 17 Abna ya yi magana da dattawan Isra'ila cewa, "Da daɗewa kun yi ta ƙoƙarin ku naɗa Dauda ya zama sarki bisan ku.
\v 18 Yanzu ku yi haka. Gama Yahweh ya yi magana game da Dauda cewa, 'Ta hannun bawana Dauda zan ceci mutanena Isra'ila daga hannun Filistiyawa daga kuma dukkan hannun maƙiyansu.'"
\s5
\v 19 Abna kuma da kansa ya yi magana da mutanen Benyamin. Sai Abna kuma ya tafi ya yi magana da Dauda a Hebron domin ya bayyana masa dukkan abin da Isra'ila da dukkan gidan Benyamin gaba ɗaya suka yi niyar aikatawa.
\v 20 Da Abna da mutanensa guda ashirin suka iso cikin Hebran domin su ga Dauda, Dauda ya shirya masu liyafa.
\s5
\v 21 Abna ya bayyana wa Dauda, "Zan tashi in tattaro maka dukkan Isra'ila, ubangidana sarkina, domin su yi alƙawari da kai, domin ka yi mulki bisa dukkan abin da kake marmari." Sai Dauda ya sallami Abna, Abna kuma ya koma da salama.
\s5
\v 22 Sai sojojin Dauda da Yowab suka dawo daga hari, tare da ganima mai tarin yawa. Amma Abna ba ya tare da Dauda a Hebran. Dauda ya rigaya ya sallame shi, Abna kuma ya tafi cikin salama.
\v 23 Lokacin da Yowab da dukkan sojojin da ke tare da shi suka iso, aka gaya wa Yowab, "Abna ɗan Nã ya zo gun sarki, kuma sarki ya sallame shi, Abna kuma ya tafi cikin salama."
\s5
\v 24 Sai Yowab ya zo wurin Sarki ya ce, "Mene ne ke nan ka yi? Duba, Abna ya zo wurin ka! Me yasa ka sallame shi, kuma ga shi ya tafi?
\v 25 Baka sani ba Abna ɗan Nã ya zo domin ya yaudare ka ya kuma san shirye-shiryenka ya gane duk abubuwan da kake yi?"
\v 26 Da Yowab ya bar Dauda, sai ya aika manzanni su bi Abna, suka kuma dawo da shi daga rijiyar Sira, amma Dauda bai san wannan ba.
\s5
\v 27 Da Abna ya dawo Hebron, Yowab ya kai shi gefe a tsakiyar ƙofa domin ya yi magana da shi a kaɗaice. Nan Yowab ya soke shi a ciki ya kashe shi. Da haka Yowab ya ɗau fansar jinin ɗan'uwansa. Asahel.
\s5
\v 28 Da Dauda ya ji wannan ya ce, "Da ni da mulkina baratattu ne a gaban Yahweh har abada game da jinin Abna ɗan Nã.
\v 29 Bari alhakin mutuwar Abna ya faɗi kan Yowab da kuma dukkan gidan mahaifinsa. Bari kada a taɓa rasa a cikin iyalin Yowab wani wanda ke ɗigar miƙi ko ciwon fata ko kuma wanda ya ke gurgu kuma dole ya yi tafiya tokare da sanda ko kuma wanda takobi ya kashe shi ko wanda ya ke da rashin abinci."
\v 30 Haka Yowab da ɗan uwansa Abishai suka kashe Abna, domin ya kashe ɗan uwansu Asahel a Gibiyan cikin yaƙi.
\s5
\v 31 Dauda ya cewa Yowab da dukkan mutanen da ke tare da shi, "Ku kekketa tufafinku, ku sa tsumoki, ku yi makoki a gaban gawar Abna."
\v 32 Sarki Dauda ya bi bayan gawar cikin tawagar makokin. Suka binne Abna a Hebron. Sarki ya yi kuka da kururuwa mai ƙara a kabarin Abna, dukkan mutane kuma su ka yi kuka.
\s5
\v 33 Sarki ya yi makoki domin Abna ya yi waƙa, "Ya ƙyautu Abna ya mutu kamar yadda wawa ke mutuwa?
\v 34 Ba wai an ɗaure hannuwanka ba. Ƙafafunka ba a ɗaure su da sarƙa ba. Kamar yadda mutum yakan faɗi a gaban 'ya'yan rashin gaskiya, haka ka faɗi." Sai kuma dukkan mutane suka ƙara kuka a bisansa.
\s5
\v 35 Dukkan mutane suka zo su sa Dauda ya ci abinci tun da sauran rana. Amma Dauda ya rantse, "Bari Allah ya hukunta ni, ya kuma ƙara yi, idan na ci abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi."
\v 36 Dukkan mutane suka lura da ɓacin ran Dauda, suka ji daɗi, duk abin da sarki ya yi suka ji daɗin sa.
\s5
\v 37 Sai dukkan mutane da kuma dukkan Isra'ila suka gane a ranar nan ba niyyar sarki ba ce a kashe Abna ɗan Nã.
\v 38 Sarki ya cewa barorinsa, "Ba ku sani basarake da kuma babban mutum ne ya faɗi yau a cikin Isra'ila ba?
\v 39 Yanzu na rarrauna yau, koda shi ke ni sarki ne zaɓaɓɓe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi kowa mugunta a gare ni. Bari Yahweh ya sãka wa mugu da hukuncin da ya cancanci muguntarsa."
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Lokacin da Ishboshet, ɗan Saul, ya ji Abna ya mutu a Hebron, sai hannuwasa suka yi rauni, dukkan Isra'ila suka tsorata.
\v 2 Ɗan Saul yana da mutane biyu waɗanda shugabanni ne na ƙungiyoyin sojoji. Sunan ɗayan Bãna ɗayan kuma Rekab, 'ya'yan Rimon Babirote na mutanen Benyamin (gama ana ɗaukar Birot a yankin Benyamin ta ke),
\v 3 Birotiyawa sun gudu ne zuwa Gittam kuma har yau suna zama a can.
\s5
\v 4 Yanzu dai, Yonatan ɗan Saul, yana da ɗa wanda gurgu ne a ƙafa. Yana da shekara biyar sa'ad da labari ya zo akan Saul da Yonatan daga Yeziril. Sai mai renonsa ta ɗauke shi don ta gudu da shi. Amma da ta ke gudu, sai ɗan Yonatan ya faɗi ya gurgunce. Sunansa Mafiboshet.
\s5
\v 5 Sai 'ya'yan Rimon Babirote, Rekab da Ba'ana, suka yi tafiya cikin zafin rana zuwa gidan
\v 6 Mafiboshet lokacin da ya ke hutawa da tsakar rana. Matar da ke tsaron ƙofar barci ya kwashe ta sa'ad da ta ke tankaɗen alkama, sai Rekab da Bãna suka yi sanɗo shuru suka wuce ta.
\v 7 To bayan da suka shiga ɗakin, sai suka faɗa masa suka kashe shi sa'ad da ya ke ƙwance kan gadonsa. Suka yanke kansa suka tafi da shi, suka yi tafiya dukkan dare zuwa Araba.
\s5
\v 8 Suka kawo kan Mafiboshet gun Dauda a Hebron, suka kuma ce da sarki, "Duba, wannan kan Mafiboshet ɗan Saul ne, maƙiyinka, wanda ya nemi ranka. Yau Yahweh ya sãka wa maigidanmu sarki gãba da Saul da zuriyarsa."
\v 9 Dauda ya amsa wa Rekab da Bãna ɗan'uwansa, 'ya'yan Riman Babirote; ya ce masu, "Na rantse da ran Yahweh, wanda ya ceci raina daga kowacce wahala,
\v 10 dã wani ya gaya mani; 'Duba, Saul ya mutu,' yana tsammanin ya kawo labari mai daɗi, sai na danƙe shi na kashe shi a Ziglag. Wannan shi ne ladan dana bashi don labarinsa mai daɗi.
\s5
\v 11 To ba zan yi fiye da haka ba, sa'ad da mugayen mutane suka kashe mutum marar laifi a cikin gidansa a kan gadonsa, yanzu ba zan nemi jininsa daga hannunku in kuma tumbuƙe ku daga duniya ba?"
\v 12 Sa'an nan Dauda ya umarci samari, suka kashe su suka yanke hannuwansu da ƙafafunsu kuma suka rataye su a gaɓar tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Mefiboshet suka binne shi a kabarin Abna a Hebron.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Sa'an nan dukkan kabilun Isra'ila suka zo gun Dauda a Hebron suka ce, "Duba mu jikinka ne da ƙashinka.
\v 2 A kwanakin baya, da Saul ya ke mulki bisanmu, kai ne ka bi da rundunar yaƙi ta Isra'ila. Yahweh ya ce maka, "Za ka yi kiwon jama'ata Isra'ila, za ka kuma zama sarki bisa Isra'ila.'"
\s5
\v 3 Sai dukkan dattawan Isra'ila suka zo wurin sarki a Hebron, Sarki Dauda ya yi alƙawari da su a gaban Yahweh. Suka naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila.
\v 4 Dauda yana da shekaru talatin sa'ad da ya fara sarauta, ya kuma yi mulki shekara arba'in.
\v 5 A Hebron ya yi mulkin bisa Yahuda shekaru bakwai da wata shida, kuma a Yerusalem ya yi mulki shekaru talatin da uku bisa dukkan Isra'ila da Yahuda.
\s5
\v 6 Sarki da mutanensa suka zo Yerusalem gãba da Yebusiyawa, mazamnan ƙasar. Suka cewa Dauda, "Ba za ka iya zuwa nan sai dai idan makafi da guragu ne za su kore ka. Dauda ba zai iya zuwa nan ba."
\v 7 Duk da haka Dauda ya ci kagarar Sihiyona, wadda yanzu shi ne birnin Dauda.
\s5
\v 8 A lokacin nan Dauda ya ce, "Waɗanda suka hari Yebusiyawa dole su bi ta wuriyar ruwa domin su kai ga "guragu da makafi' waɗanda su ne maƙiyan Dauda." Shi yasa mutane ke cewa, "Da 'makafi da kuma guragu' ba za su shiga fãda ba."
\v 9 Sai Dauda ya zauna cikin kagara ya kira shi birnin Dauda. Ya tsare shi da gine- gine kewaye da shi tun daga waje zuwa ciki.
\v 10 Dauda ya ƙasaita domin Yahweh, Allah mai runduna, yana tare da shi.
\s5
\v 11 Sa'an nan Hiram sarkin Taya ya aika da manzanni gun Dauda, da itacen sida, da masassaƙa da masu fãsa duwatsu. Suka gina wa Dauda gida.
\v 12 Dauda ya sani Yahweh ya naɗa shi sarki bisa Isra'ila kuma ya ɗaukaka masarautarsa sabili da mutanensa Isar'ila.
\s5
\v 13 Bayan da Dauda ya bar Hebron ya zo Yerusalem, ya ƙara ɗaukar ƙwaraƙwarai da mataye a Yerusalem, aka ƙara haifa masa 'ya'ya maza da 'ya'ya mata.
\v 14 Waɗannan su ne sunayen yaran da aka haifa masa a Yerusalem: Shammuwa, Sobab, Natan, Suleman,
\v 15 Ibha, Elisuwa, Nefeg, Yafiya,
\v 16 Elishama, Eliyada, da Elifelet
\s5
\v 17 Da dai Filistiyawa suka ji cewa an naɗa Dauda sarki bisa Isra'ila, sai suka fita dukka suna nemansa. Amma Dauda ya ji abin, sai ya gangara zuwa mafaƙa.
\v 18 Yanzu Filistiyawa sun rigaya sun fito sun bazu a Kwarin Refayim.
\s5
\v 19 Sai Dauda ya roƙi taimako daga Yahweh. Ya ce, "Ko in hari Filistiyawa? Za ka bani nasara akan su?" Yahweh ya cewa Dauda, "Ka hare su, domin hakika zan ba ka nasara bisa Filistiyawa."
\v 20 Sai Dauda ya kai hari a Ba'al Ferazim, a nan ya kayar da su. Ya ce haka, "Yahweh ya fantsamo cikin maƙiyana a gabana kamar fantsamowar ruwan ambaliya." Saboda haka sunan wurin ya zama Ba'al Ferazim.
\v 21 Filistiyawa suka bar gumakunsu a nan, Dauda kuma da mutanensa suka ɗauke su suka tafi da su.
\s5
\v 22 Sai Filistiyawa suka sake tasowa kuma suka ƙara bazuwa cikin Kwarin Refayim.
\v 23 Sai Dauda ya sake roƙon taimako daga Yahweh. Yahweh kuma ya ce masa, "Kada ka kai hari ta gabansu, maimakon haka ka zagaya ta bayansu ku afka masu ta cikin itatuwan tsamiya.
\s5
\v 24 Sa'ad da kuka ji ƙarar takawar yaƙi cikin iska da ke bugawa a ƙwanƙolin itatuwan tsamiya, sai ku kai hari da karfi. Kuyi wannan domin Yahweh ya rigaya ya sha gabanku ya hari rundunar Filistiyawa."
\v 25 Sai Dauda ya yi yadda Yahweh ya umarce shi. Ya kashe Filistiyawa daga Geba har zuwa Geza.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Dauda ya sake tattaro dukkan zaɓabbun mutanen Isra'ila, dubu talatin.
\v 2 Dauda ya tashi ya tafi da dukkan mutanensa da ke tare da shi daga Bãla cikin Yahuda domin a ɗauko akwatin Yahweh daga can wanda ake kira da sunan Yahweh mai runduna, wanda ya ke zaune a kursiyi bisa kerubim.
\s5
\v 3 Suka ɗora akwatin Yahweh bisa sabuwar karusa. Suka fito da shi daga gidan Abinadab, da ke kan wani tudu. Uza, da Ahiyo, 'ya'yansa, suke bi da sabuwar karusar.
\v 4 Suka fito da karusar daga gidan Abinadab daga kan tudu tare da akwatin Yahweh a bisan sa. Ahiyo na tafiya a gaban akwatin.
\v 5 Sai Dauda da dukkan gidan Isra'ila suka fara wasa a gaban Yahweh, suna biki tare da sassaƙaƙƙun kayayyakin waƙa, molaye, garayu, kacau-kacau, da kuge.
\s5
\v 6 Da suka iso masussukar Nakon, sai sãn ya yi tuntuɓe, sai Uza ya miƙa hannunsa ya tallafi akwatin Allah, ya kuma kama shi.
\v 7 Sai fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan Uza. Allahj ya kai masa hari nan take sabili da zunubinsa. Uza ya mutu nan take da akwatin Allah.
\s5
\v 8 Dauda ya yi fushi domin Yahweh ya kai wa Uza hari, ya kira sunan wurin nan Ferez Uza. Wurin nan har yau ana kiransa Ferez Uza.
\v 9 Dauda ya ji tsoron Yahweh a ranan nan. Ya ce, "Ƙaƙa akwatin Yahweh zai zo gare ni."
\s5
\v 10 Saboda haka Dauda bai so ya ɗauki akwatin Yahweh tare da shi zuwa cikin birnin Dauda ba. Maimakon haka, sai ya ajiye shi a gefe cikin gidan Obed Idom Bagitte.
\v 11 Akwatin Yahweh ya kasance a gidan Obed Idom Bagitte wata uku. Sai Yahweh yasa masa albarka da dukkan gidansa.
\s5
\v 12 Sai aka gaya wa sarki Dauda, "Yahweh ya albarkaci gidan Obed Idom da dukkan abubuwan da ke nasa saboda akwatin Yahweh" Sai Dauda ta tafi ya ɗauko akwatin Yahweh daga gida Obed Idom zuwa birnin Dauda da murna.
\v 13 Lokacin da waɗanda suke ɗauke da akwatin Yahweh suka yi tafiya taki shida, sai ya yi hadayarsa da kiwataccen ɗan maraƙi.
\s5
\v 14 Dauda ya yi rawa a gaban Yahweh da dukkan ƙarfinsa; yana sanye da ɗan feton lilin kaɗai.
\v 15 Sai Dauda da dukka gidan Isra'ila suka ɗauko akwatin Yahweh tare da sowa da kuma ƙarar ƙahonni.
\s5
\v 16 Sa'ad da akwatin Yahweh ya shigo birnin Dauda, Mikal, ɗiyar Saul, ta leƙa waje ta taga. Ta ga Sarki Dauda yana tsalle yana rawa a gaban Yahweh. Sai ta rena shi a zuciyarta.
\v 17 Suka kawo akwatin Yahweh ciki suka ajeye shi a mazauninsa, a tsakiyar rumfar da Dauda ya shirya dominsa. Sai Dauda ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a gaban Yahweh.
\s5
\v 18 Lokacin da Dauda ya gama miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ya albarkaci mutane a cikin sunan Yahweh mai runduna.
\v 19 Sai ya rarraba wa dukkan mutane, dukkan cin-cirindon Isra'ila gaba ɗaya, maza da mata, dunƙulen gurasa, ɗan gutsuren nama, da wainar kauɗar inabi. Sa'annan dukkan mutane suka tafi, kowanne ɗayan su ya koma zuwa nasa gida.
\s5
\v 20 Sai Dauda ya koma ya albarkaci iyalinsa. Mikal, ɗiyar Saul, ta fito ta taryi Dauda ta ce, "Ina misalin girmamawar da sarkin Isra'ila ya samu yau, wanda ya tsirance kansa yau a idanun bayi 'yan mata cikin barorinsa, kamar ɗaya daga cikin ashararrun mutane wanda ba ko kunya yana tsiraratar da kansa!"
\s5
\v 21 Dauda ya amsa wa Mikal, "Na yi wannan a gaban Yahweh, wanda ya zaɓe ni fiye da mahaifinki fiye kuma da dukkan iyalin gidansa, wanda ya aza ni shugaba bisa mutanen Yahweh, bisa Isra'ila, A gaban Yahweh zan yi murna!
\v 22 Zan zama ma da tawali'u fiye da haka, in kuma kunyata a idanuna ma. Amma game da 'yan mata bayi da kika ambata, za a girmamani."
\v 23 Saboda haka Mikal ɗiyar Saul, ba ta da 'ya'ya har ranar mutuwarta.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Ya zamana sa'ad da sarki yana zaune cikin gidansa, kuma Yahweh ya bashi hutu daga dukkan maƙiyansa kewaye,
\v 2 sarki ya cewa annabi Natan, "Duba, ina zaune cikin gidan sida, amma akwatin Yahweh yana zaune a cikin tsakiyar rumfa."
\s5
\v 3 Sai Natan ya cewa sarki, "Je ka, ka yi abin da ke zuciyarka, gama Yahweh yana tare da kai."
\v 4 Amma a daren nan maganar Yahweh ta zo gun Natan cewa,
\v 5 "Ka tafi ka gaya wa bawana Dauda, "Wannan shi ne abin da Yahweh ya faɗi: Zaka gina mani gida inda zan zauna a ciki?
\s5
\v 6 Gama ban taɓa zama a cikin gida ba daga ranar da na fitar da mutanen Isra'ila daga Masar har zuwa rana ta yau; maimakon haka ina ta yawo a cikin rumfa, a rumfar sujada.
\v 7 A dukkan wuraren dana yi yawo a cikin mutanen Isra'ila, na taɓa gaya wa wani ɗaya daga cikin shugabannin Isra'ila wanda na naɗa ya yi makiyayancin mutanena Isra'ila, cewa, "Donme ba ka gina mani gidan itatuwan sida ba?'"'
\s5
\v 8 Yanzu dai, ka gaya wa bawana Dauda, "Wannan shi ne abin da Yahweh mai runduna ya ce: "Na ɗauko ka daga makiyaya, daga bin tumaki, domin ka zama mai mulki bisa mutanena Isra'ila.
\v 9 Na kasance tare da kai duk inda ka tafi. Na datse dukkan maƙiyan ka daga gaban ka. Yanzu zan sa sunanka ya shahara kamar sunayen shahararrun nan na duniya.
\s5
\v 10 Zan sanya wa mutanena Isra'ila wuri, zan kuma kafa su a can, domin su zauna a mazaunin kansu kuma ba za a ƙara wahalshe su ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zambatar su ba, kamar yadda suka yi a dã,
\v 11 kamar yadda suke ta yi daga ranar dana umarci alƙalai su kasance bisa mutane na Isra'ila. Yanzu zan ba su hutawa daga dukkan magabtansu. Bugu da ƙari, "Ni, Yahweh, na furta maka cewa zan yi maka gida.
\s5
\v 12 Sa'ad da kwanakinka suka cika kuma ka kwanta tare da ubanninka, zan tada wani daga zuriyar ka a bayan ka, wanda zai fito daga cikin jikinka, kuma zan kafa mulkinsa.
\v 13 Shi zai gina gida domin sunana, kuma ni zan kafa kursiyin mulkinsa har abada.
\v 14 Zan zama uba a gare shi, shi kuma zai zama ɗana. Idan ya yi zunubi, zan hore shi da sandar mutane da kuma bulalar 'ya'yan mutane.
\s5
\v 15 Amma alƙawarin amincina ba zai barshi ba, kamar yadda da na ɗauke shi daga Saul, wanda na kawar daga gabana.
\v 16 Gidanka da mulkinka za a tabbatar har abada a gabanka. Kursiyinka zai tabbata har abada.'"
\v 17 Natan ya yi magana da Dauda ya kuma gaya masa dukkan maganganun nan, ya kuma gaya masa game da wahayin dukka.
\s5
\v 18 Sai sarki Dauda ya shiga ciki ya zauna a gaban Yahweh ya ce, "Wane ne ni, Yahweh Allah, kuma mene ne iyalina har daka kawo ni ga haka?
\v 19 Yanzu dai wannan ƙaramin abu ne a idonka, Ubangiji Yahweh. Har ma ka yi magana game da iyalin bawanka a kan lokatai masu zuwa, ka kuma nuna mani tsararraki masu zuwa, Ubangiji Yahweh!
\v 20 Me kuma ni, Dauda, zan ce maka? Ka girmama bawanka, Ubangiji Yahweh.
\s5
\v 21 Sabili da maganarka, domin kuma ka cika nufinka, ka yi wannan babban abu kuma ka bayyana shi ga bawanka.
\v 22 Saboda haka kai mai girma ne, Ubangiji Yahweh, domin babu wani kamar ka, kuma babu wani Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.
\v 23 Wacce al'umma ce kamar mutanenka Isra'ila, al'umman nan guda ɗaya a duniya wadda, kai Allah, ka je ka fanshe mu domin kanka? Ka yi wannan domin su zama mutanenka, domin ka yiwa kanka suna, ka kuma yi manyan al'amura dana ban tsoro domin ƙasarka. Ka kori al'ummai da gumakunsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar da su daga Masar.
\s5
\v 24 Ka kafa Isra'ila a matsayin mutanenka har abada, kuma kai, Yahweh, ka zama Allahnsu.
\v 25 Saboda haka yanzu, Yahweh Allah, bari alƙawarin da ka yi game da bawanka da iyalinsa ya tabbata har abada. Ka yi yadda ka faɗa.
\v 26 Bari sunanka ya zama da girma har abada, domin mutane su ce, Yahweh mai runduna shi ne Allah na Isra'ila,' sa'an nan gidana ni, Dauda, bawanka ya tabbata a gaban ka.
\s5
\v 27 Domin kai, Yahweh mai runduna, Allah na Isra'ila, ka bayyana wa bawanka cewa za ka gina masa gida. Shi yasa, ni, bawanka, na sami ƙarfin hali in yi addu'a gare ka.
\v 28 Yanzu dai, Ubangiji Yahweh, kai ne Allah, maganganunka abin dogara ne a gare su, kuma ka yi wannan alƙawari mai ƙyau ga bawanka.
\v 29 Yanzu dai, bari ya gamsheka ka albarkaci gidan bawanka, domin ya dawwama a gabanka har abada. Domin kai, Ubangiji Yahweh, ka faɗi waɗannan abubuwa, da kuma albarkarka gidan bawanka zai zama da albarka har abada."
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Bayan wannan ya zamana Dauda ya hari Filistiyawa ya kuma ci su, Sai Dauda ya karɓe Gat da ƙauyukanta daga karkashin linzamin Filistiyawa.
\s5
\v 2 Sa'an nan ya buga Mowabawa, ya gwada mutanensu da igiya ta wurin sasu su kwanta a ƙasa. Ya gwada layi biyu da zai kashe, layi ɗaya mai tsawo sosai da zai bari da rai. Haka Mowabawa suka zama bayi ga Dauda suka biya shi haraji.
\s5
\v 3 Dauda ya buga Hadadeza ɗan Rehob, sarkin Zoba, sa'ad da Hadadeza ya ke tafiya garin ya mai da mulkinsa na dã wajen Kogin Efratis.
\v 4 Dauda ya ƙwace karusai daga gunsa guda 1,700 da matafiya a ƙasa dubu ashirin. Dauda ya yanke jijiyar ƙafafun dawakai masu jan karusai, amma ya bar wasu domin karusai ɗari.
\s5
\v 5 Lokacin da Armeniyawa na Damaskus suka zo su taimaki Hadadeza sarkin Zoba, Dauda ya kashe Armeniyawa mutum dubu ashirin da biyu.
\v 6 Sai Dauda ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Aram ta Damaskus, kuma Armeniyawa suka zama bayinsa suna biyan haraji. Yahweh ya ba Dauda nasara duk inda ya tafi.
\s5
\v 7 Dauda ya ɗauko garkuwoyin zinariya da suke kan bayin Hadadeza ya kawo su Yerusalem.
\v 8 Daga Beta da Berotai, biranen Hadadeza, Sarki Dauda ya kwaso tagulla masu ɗumbun yawa.
\s5
\v 9 Da Tou, sarkin Hamat, ya ji Dauda ya kayar da dukkan rundunar Hadadeza,
\v 10 Tou ya aika Hadoram ɗansa gun Sarki Dauda ya gaishe shi ya kuma sa masa albarka, domin Dauda ya yi yaƙi gãba da Hadadeza ya kuma ci shi, domin kuma a dã Hadadeza ya yi yaƙi gãba da Tou. Hadoram kansa ya zo tare da kayayyakin azurfa, zinariya, da tagulla.
\s5
\v 11 Sarki Dauda ya ƙeɓe waɗannan kayayyaki domin Yahweh, su azurfa da zinariya daga dukkan al'umman da ya ci da yaƙi -
\v 12 Aram, Mowab, da mutanen Ammon, da Filistiyawa, da Amelik, tare kuma da dukkan kayayyakin ganima na Hadadeza ɗan Rehob sarkin Zoba.
\s5
\v 13 Sunan Dauda ya shahara sa'ad da ya komo daga bugun Armeniyawa cikin Kwarin Gishiri, da su da mutanensu dubu goma sha takwas.
\v 14 Ya ajiye ƙungiyoyin sojoji cikin dukkan yankin Idom, dukkan Idomiyawa suka zama bayi gare shi. Yahweh ya ba Dauda nasara duk inda ya tafi.
\s5
\v 15 Dauda ya yi mulki bisa dukkan Isra'ila, ya kuma aikata adalci da gaskiya ga dukkan mutanensa.
\v 16 Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban rundunar yaƙi, Yehoshafat ɗan Alihud kuwa shi ne magatakarda.
\v 17 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Seraya ne marubuci.
\v 18 Binaya ɗan Yehoyaida shi ne mai lura da Keretiyawa da Feletiyawa, 'ya'yan Dauda su ne manyan hakimai masu ba sarki shawara.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Dauda yace, "Akwai ko ɗaya wanda ya rage cikin iyalin Saul wanda zan nuna masa alheri sabili da Yonatan?"
\v 2 Akwai wani bawa cikin iyalin Saul mai suna Ziba, aka kuma kira shi ga Dauda. Sarki ya ce masa, "Kai ne Ziba," Ya amsa, "I. Ni ne bawanka."
\s5
\v 3 Sai sarki yace, "Babu ko ɗaya da ya rage daga iyalin Saul wanda zan nuna masa alherin Allah." Ziba ya amsa wa sarki, "Yonatan har yanzu yana da ɗa, wanda yana da gurguntaka."
\v 4 Sarki ya ce masa, "Ina ya ke." Ziba ya amsa wa sarki ya ce, "Duba, yana cikin gidan Maki ɗan Ammiyel a Lo Deba."
\s5
\v 5 Sa'an nan Sarki Dauda ya aika a ka fito da shi daga gidan Maki ɗan Ammiyel a Lo Deba.
\v 6 Sai Mefiboshet ɗan Yonatan ɗan Saul, ya zo gun Dauda ya russuna fuskarsa ƙasa ya girmama Dauda. Dauda ya ce, '"Mefiboshet," Ya amsa, "Duba, ni baranka ne!"
\s5
\v 7 Dauda ya ce masa, "Kada ka ji tsoro, gama hakika zan nuna maka alheri sabili da Yonatan mahaifinka, kuma zan mayar maka dukkan ƙasar kakanka, za ka kuma ci kullum a teburina."
\v 8 Mefiboshet ya russuna ya ce, "Wane ne ni baranka, da za ka dube ni da tagomashi mataccen kare kamar ni?"
\s5
\v 9 Sai sarki ya kira Ziba, baran Saul, ya ce masa, "Duk mallakar Saul da iyalinsa na ba jikan ubangidanka.
\v 10 Da kai, da 'ya'yanka maza, da kuma barorinka dole ku noma masa gonakansa dole kuma ku yi masa girbi domin jikan ubangidanka ya sami abinci. Gama dole Mefiboshet, jikan ubangidanka, ya riƙa ci kullum a teburina." Ziba yana da 'ya'ya maza goma sha biyar da barori ashirin.
\s5
\v 11 Sai Ziba ya cewa sarki, bawanka zaiyi dukkan abin da ubangijinsa sarki ya dokaci bawansa." Sarki ya ƙara da cewa, "Game da Mefiboshet zai riƙa ci a teburina, kamar ɗaya daga cikin 'ya'yan sarki."
\v 12 Mefiboshet yana da wani ɗa ƙarami mai suna Mika, Duk waɗanda suke zauna a gidan Ziba barori ne na Mefiboshet.
\v 13 Sai Mefiboshet ya zauna a Yerusalem, kullum kuwa ya na ci a teburin sarki, koda shi ke gurgu ne a dukkan ƙafafunsa biyu.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Ananan da jimawa sai sarkin mutanen Ammon ya mutu, kuma ɗansa Hanun ya zama sarki a madadinsa.
\v 2 Dauda ya ce, "Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahas, kamar yadda mahaifinsa ya nuna mani alheri." Sai Dauda ya aiki barorinsa su kai ta'aziya ga Hanun domin mahaifinsa. Barorinsa suka shiga ƙasar mutanen Ammon.
\v 3 Amma shugabannin mutanen Ammon suka cewa Hanun ubangijinsu, Kana tsammani da gaske Dauda ya ke girmama mahaifinka saboda ya aiko mutane su yi maka ta'aziya? Ba Dauda ya aiko barorinsa domin su dubi birnin ba, su san shi, domin su hallaka shi?"
\s5
\v 4 Sai Hanun ya ɗauki barorin Dauda, ya aske rabin gemunsu, ya yanke rigunansu har zuwa ɗuwawunsu, a sa'annan ya sallame su suka tafi.
\v 5 Da suka labarta wa Dauda wannan, ya aika domin ya sadu da su, domin mutanen sun kunyata ainun. Sarki ya ce, "Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya toho, sa'annan ku dawo.
\s5
\v 6 Lokaci da mutanen Ammon suka ga sun zama abin ƙyama ga Dauda, sai suka aika manzanni suka kuma yi hayar Aremiyawan Bet Rehob da Zoba, da sojoji 'yan tafiya a ƙasa dubu ashirin, da sarkin Mãka mai dubun mutane, da mutanen Tob masu mutane dubu goma sha biyu.
\v 7 Da Dauda ya ji haka, sai ya aiki Yowab da dukkan rundunar sojoji.
\v 8 Ammonawa suka fito suka ja dagar yaƙi a mashigar ƙofar garinsu, Aremiyawan Zoba kuwa da na Rehob, da kuma mutanen Tob da Mãka, suka tsaya su kaɗai a filaye.
\s5
\v 9 Da Yowab ya ga dagar yaƙi biyu sun fuskance shi gaba da baya, sai ya zaɓi ƙwararrun mayaƙa na Isra'ila ya jera su gãba da Aremiyawa.
\v 10 Sauran rundunar kuwa, ya bashe su ƙarƙashin jagorancin Abishai ɗan'uwansa ya sa kuma suka ja dagar yaƙi gaba da rundunar Ammon.
\s5
\v 11 Yowab ya ce, Idan Aremiyawa suka sha ƙarfi na, sai kai Abishai ka ƙwace ni, amma idan rundunar Ammon suka sha ƙarfinka zan zo in ƙwace ka.
\v 12 Ku ƙarfafa, mu kuma nuna kanmu masu ƙarfi ne domin mutanenmu da kuma biranen Allahnmu, gama Yahweh zai yi abin da ke da kyau domin nufinsa.
\s5
\v 13 Sai Yowab da sojojin rundunarsa suka tashi zuwa yaƙi gãba da Aremiyawa waɗanda dole suka gudu daga gaban rundunar Isra'ila.
\v 14 Da rundunar Ammoniyawa suka ga Aremiyawa sun gudu, sai suma suka gudu daga Abishai suka koma cikin birni. Sai Yowab ya dawo daga fafarar mutanen Ammon ya koma Yerusalem.
\s5
\v 15 Da Aremiyawa suka ga Isra'ila na cinsu, suka sake tattara kansu.
\v 16 Sai Hadareza ya aika sojojin Aremiya su zo daga ƙasar ƙetaren Kogin Yuferetis. Suka zo Helam da Shobak, sarkin yaƙi na rundunar Hadareza ya shugabance su.
\s5
\v 17 Da aka gaya wa Dauda wannan, sai ya tara dukkan Isra'ila gaba ɗaya, suka haye Yodan, suka iso Helam. Aremiyawa suka ja dagar yaƙi gãba da Dauda suka yaƙe shi.
\v 18 Aremiyawa suka gudu a gaban Isra'ila. Dauda ya kashe mahayan karusai ɗari bakwai na Aremiyawa, da dubu arba'in na mahaya dawakai. Shobak sarkin yaƙin rundunarsu aka ji masa rauni, ya mutu a nan.
\v 19 Sa'ad da dukkan sarakunan da ke barorin Hadareza suka ga Isr'ila ta ci su, sai suka biɗi sulhu da Isra'ila suka zama bayinsu. Sai Aremiyawa suka ji tsoron su ƙara taimakon mutanen Ammon.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Ya zamana da bazara, lokacin da sarakuna ke tafiya yaƙi, sai sarki Dauda ya aiki Yowab, da barorinsa, da dukkan rundunar Isra'ila. Suka ragargaza rundunar Ammon, suka kafa wa Rabba sansani. Amma Dauda ya zauna a Yerusalem.
\s5
\v 2 A na nan wata rana da yammaci, Dauda ya tashi daga gadonsa yana tafiya a kan soron fadarsa, Daga nan ya hango wata mata wadda take wanka, matar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai abar sha'awa.
\v 3 Sai Dauda ya aika ya kuma tambayi mutane waɗanda suka san wani abu game da matar. Sai wani ya ce, "Ashe wannan ba Batsheba ce ba, ɗiyar Eliyam, kuma ashe ba matar Yuriya ba ce Bahitte?"
\s5
\v 4 Dauda ya aika manzanni, aka ɗaukota, ta shiga ciki wurinsa sai ya kwana da ita (gama ba ta daɗe da tsarkake kanta daga hailarta ba). Sa'an nan ta koma gidanta.
\v 5 Matar ta yi ciki sai ta aika aka gaya wa Dauda; ta ce, "Ina da ciki."
\s5
\v 6 Sai Dauda ya aika wurin Yowab, "Ka aiko mani Yuriya Bahitte. Sai Yowab ya aika wa Dauda Yuriya.
\v 7 Da Yuriya ya iso, Dauda ya tambaye shi yadda Yowab ya ke, yadda rundunar take, da kuma yadda yaƙin ke tafiya.
\v 8 Dauda ya cewa Yuriya, "Ka gangara zuwa gidanka, ka wanke ƙafafuwanka." Sai Yuriya ya bar fadar sarki, sai sarki ya aika wa Yuriya kyauta bayan tafiyarsa.
\s5
\v 9 Amma Yuriya ya yi barci a ƙofar fadar sarki tare da dukkan barorin maigidansa, bai kuwa gangara zuwa gidansa ba.
\v 10 Da aka gaya wa Dauda, "Yuriya bai gangara zuwa gidansa ba." Dauda ya cewa Yuriya, "Ashe ba yanzu ka dawo daga tafiya ba, me yasa ba ka tafi gida ba?"
\v 11 Yuriya ya amsa wa Dauda, "Akwatin alƙawari, da Isra'ila da Yahuda suna zaune cikin rumfa, maigidana kuma Yowab da barorin maigidana sun kafa sansani a fili. Ƙaƙa fa zan tafi cikin gidana in ci in sha in kuma kwana da mata ta? Na rantse da ranka, ba zan yi wannan abu ba."
\s5
\v 12 Sai Dauda ya cewa Yuriya, "Ka zauna a nan gobe zan barka ka tafi." Sai Yuriya ya zauna a Yerusalem ranar nan da kashegari kuma. Lokacin da Dauda ya kira shi, ya ci ya sha a gabansa,
\v 13 Dauda ya bugar da shi. Da yamma Yuriya ya fita ya je ya kwanta a gadonsa tare da barorin maigidansa bai gangara zuwa gidansa ba.
\s5
\v 14 Saboda haka da safe Dauda ya rubuta wa Yowab takarda, ya ba da ita ta hannun Yuriya.
\v 15 Dauda ya rubuta cikin wasiƙar cewa, "A sa Yuriya a gaba in da yaƙi yafi zafi sosai, sa'an nan ku janye daga gare shi, domin a buge shi ya mutu."
\s5
\v 16 Sa'ad da Yowab ya kafa wa birnin daga, ya sa Yuriya a inda ya sani ƙarfafan sojojin abokan gaba za su yi yaƙi.
\v 17 Da mutanen garin suka fito suka gwabza yaƙi da rundunar Yowab, waɗansu sojojin Dauda suka faɗi, kuma Yuriya Bahitte shi ma aka kashe shi a wurin.
\s5
\v 18 Da Yowab ya aika saƙo ga Dauda yadda dukkan abu ya gudana a yaƙin,
\v 19 ya umarci manzon cewa, '"Sa'ad da ka gama faɗin komai game da yaƙin ga sarki,
\v 20 mai yiwuwa sarki ya husata, ya kuma ce maka, "Me ya sa kuka matsa kusa da birnin kuka yi yaƙi? Ba ku sani za su yiwo harbi daga garun ba?
\s5
\v 21 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubeset? Ba wata mace ce ta jeho dutsen niƙa daga kan garu a kansa ba, sai ya zo ya mutu a Tebez? Me ya sa kuka matsa kurkusa da garun?' Sa'an nan dole za ka amsa, "Bawanka Yuriya Bahitte shi ma ya mutu.'"
\s5
\v 22 Sai manzon ya tashi ya tafi wurin Dauda ya faɗa masa dukkan abin da Yowab ya aike shi ya faɗa.
\v 23 Sai manzon ya cewa Dauda, "Abokan gãba suka fi mu ƙarfi da fari; suka fafaremu har zuwa jeji, amma muka kora su baya har zuwa ƙofar gari.
\s5
\v 24 Sai maharbansu suka harbi sojojinka daga kan garu, aka kashe waɗansu barorin sarki, shi ma baranka Yuriya Bahitte an kashe shi."
\v 25 Sai Dauda ya cewa manzon, "Ka faɗa wa Yowab wannan, 'Kada ka da mu, 'Kada ka bar wannan ya ɓata maka rai, gama takobi ya kan hallakar da wannan da kuma wancan. Ka matsa wa birnin lamba da yaƙi, ku kãda shi,' ka kuma ƙarfafa shi."
\s5
\v 26 Sa'ad da matar Yuriya ta ji cewa Yuriya mijinta ya mutu, ta yi makoki sosai domin mijnta.
\v 27 Sa'ad da makokinta ya wuce, Dauda ya aika aka ɗaukota aka kawota gida a fãdarsa, ta zama matarsa ta kuma haifa masa yaro. Amma abin da Dauda ya yi ya baƙanta wa Yahweh rai.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sa'an nan Yahweh ya aiki Natan wurin Dauda. Ya tafi wurinsa ya ce, "A kwai waɗansu mutum biyu cikin wani birni. Ɗaya mutumin mai arziƙi ne ɗayan kuwa matalauci.
\v 2 Mai arziƙin na da tumaki masu tarin yawa a garkunansa,
\v 3 amma talakan nan ba shi da komai sai dai wata 'yar ƙaramar tunkiya, wacce ya saya ya yi kiwonta. Ta yi girma tare da shi da kuma yaransa. Har ma 'yar tunkiyar takan ci tare da shi ta kuma sha daga moɗarsa, takan yi barci cikin hannuwansa har ma kamar ɗiya take a gunsa. '
\s5
\v 4 Wata rana wani baƙo ya zo gun mutumin nan mai arziƙi, amma mai arziƙin nan bai so ya ɗauki dabba daga cikin nasa garken domin ya ciyar da shi ba. Mai makon haka ya ɗauki 'yar tunkiyar matalaucin nan ya yi wa baƙon abinci da ita.
\v 5 Dauda ya husata ƙwarai gãba da mutumin nan mai arziƙi, sai ya tasar wa Natan da ihu,
\v 6 "Na rantse da ran Yahweh, mutumin da ya yi wannan ya cancanci mutuwa. Dole ya biya ninki huɗu tamanin 'yar tunkiyan nan domin ya yi wannan domin kuma bai ji tausayin matalaucin nan ba.
\s5
\v 7 Sai Natan ya cewa Dauda, "Kai ne mutumin! Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ce, 'Na naɗa ka sarki bisa Isra'ila, na kuma kuɓutar da kai daga hannun Saul.
\v 8 Na baka gidan ubangidanka, da matan ubangidanka a hannnuwanka. Na kuma ba ka gidan Isra'ila da Yahuda. Idan dã waɗannan sun yi ƙanƙanta dana ba ka waɗansu abubuwa ƙari bisansu.
\s5
\v 9 To me yasa ka raina dokokin Yahweh, har ka aikata abin da ke na mugunta a idonsa? Ka kashe Yuriya Bahitte da takobi ka ɗauki matarsa ta zama matarka. Ka kashe shi da takobin rundunar Ammon.
\v 10 Saboda haka yanzu takobi ba zata taɓa rabuwa da gidanka ba, domin ka rena ni ka ɗauki matar Yuriya Bahitte ta zama matarka.'
\s5
\v 11 Yahweh ya ce, "Duba, zan tayar maka da masifa gãba da kai daga cikin gidanka. A idanunka, zan ɗauki matanka in ba da su ga maƙwabcinka, zai kwana da matanka rana katã.
\v 12 Gama ka yi naka zunubin a asirce, amma ni zan yi wannan a gaban duk Isra'ila, rana katã.'"
\v 13 Sai Dauda ya cewa Natan, "Na yiwa Yahweh zunubi." Natan ya amsa wa Dauda, "Yahweh ma ya shafe zunubinka. Ba za a kashe ka ba.
\s5
\v 14 Duk da haka, domin ta wurin yin wannan ka rena Yahweh, yaron da za a haifa maka hakika zai mutu."
\v 15 Sa'an nan Natan ya bar shi ya tafi gida. Yahweh ya kai wa yaron da matar Yuriya ta haifa Dauda hari, da matsanancin ciwo.
\s5
\v 16 Dauda ya roƙi Yahweh domin yaron. Dauda ya yi azumi ya shiga cikin ɗaki ya kwanta a ƙasa dukkan dare.
\v 17 Dattawan gidansa suka tashi suka tsaya a gefensa, domin su tashe shi daga ƙasa, amma yaƙi ya tashi kuma ya ƙi ya ci tare da su.
\v 18 Sai ya zamana a rana ta bakwai yaron ya mutu. Barorin Dauda suka ji tsoron su gaya masa cewa yaron ya rasu, domin sun ce, "Duba, sa'ad da yaron ke raye mun yi masa magana bai saurari muryar mu ba. Me zai yiwa kansa idan muka ce masa yaron ya mutu?!"
\s5
\v 19 Amma da Dauda ya ga barorinsa suna raɗa da junansu, Dauda ya gane yaron ya mutu. Ya cewa barorinsa, "Yaron ya mutu?" Suka amsa, "Ya mutu."
\v 20 Sai Dauda ya tashi daga ƙasa ya wanke kansa, ya shafa mai, ya canza rigunansa. Ya tafi zuwa rumfar sujada ta Yahweh, ya yi sujada a can, sa'an nan ya dawo fadarsa. Da ya buƙata, sai suka sa abinci a gabansa, ya kuma ci.
\s5
\v 21 Sai barorinsa suka ce masa, "Me yasa ka yi haka? Ka yi azumi da kuka saboda yaron, sa'ad da ya ke da rai, amma da yaron ya mutu, ka tashi ka ci abinci."
\v 22 Dauda ya amsa, "Sa'ad da yaron ke da rai na yi azumi da kuka. Na ce, 'Wa ya sani watakila Yahweh zai yi mani alheri, ya bar yaron da rai?'
\v 23 Amma yanzu ya mutu, to donme zan yi azumi? Zan iya komo da shi da rai ne? Ni zan je gunsa, amma shi ba zai komo wuri na ba."
\s5
\v 24 Dauda ya ta'azantar da Batsheba matarsa, ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Daga baya ta haifi yaro, aka sa wa yaron suna Suleman. Yahweh ya ƙaunace shi
\v 25 ya kuma aika da saƙo ta hannun annabi Natan cewa a sa masa suna Yedidiya, domin Yahweh ya ƙauna ce shi.
\s5
\v 26 Yanzu dai Yowab ya yi yaƙi gãba da Rabba, birnin masarautar mutanen Ammon, ya kama kagararta.
\v 27 Sai Yowab ya aiki manzanni ga Dauda ya ce, "Na yaƙi Rabba, na kuma kama mashigar ruwan birnin.
\v 28 Yanzu fa ka tattaro sauran rudunar ka kafa wa birnin sansani ka ci shi, domin in na ci birnin, za a kira shi da sunana."
\s5
\v 29 Sai Dauda ya tattaro dukkan rundunar ga baki ɗaya suka tafi Rabba; suka yaƙi birnin, suka ci shi.
\v 30 Dauda ya cire kambin zinariya da ke kan sarkin - nauyinsa talanti guda ne na zinariya, akwai wani dutse mai daraja a cikinsa. Aka ɗora wannan kambi a kan Dauda. Sa'an nan ya fito da ganimar birnin masu ɗumbun yawa.
\s5
\v 31 Ya fitar da mutanen da ke cikin birnin, ya tislasta masu su yi aiki da zartuna, faretani, da gatura; ya kuma sa su su yi aiki a maginar tubali. Dauda ya tilasta wa dukkan biranen mutanen Ammon su yi wannan aiki tuƙuru. Sai Dauda da dukkan rundunarsa suka koma Yerusalem.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Ya zama fa bayan wannan sai Amnon ɗan Dauda, ya yi sha'awar 'yar'uwarsa Tama kyakkyawa wanda ubansu ɗaya ne, amma 'yar'uwar Absalom ce uwa ɗaya uba ɗaya, shi ma ɗaya ne daga cikin 'ya'yan Dauda maza.
\v 2 Amnon ya jarabtu har ya kama ciwo saboda 'yar 'uwarsa Tama. Ita kuwa budurwa ce, a ganin Amnon ba zai taɓa yiwuwa ya yi ma ta wani abu ba.
\s5
\v 3 Amma Amnon ya na da wani aboki mai suna Yonadab ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda. Yehonadab wani mutum ne mai hila.
\v 4 Yehonadab ya cewa Amnon, "Me yasa ga ka ɗan sarki, kake damuwa kowacce safiya? Ba za ka gaya mani ba?" Amnon ya amsa masa, "Ina ƙaunar Tamar, 'yar 'uwar ɗan'uwana Absalom."
\s5
\v 5 Sai Yonadab ya ce masa, "Ka kwanta a gadonka ka yi kamar baka da lafiya. Sa'ad da mahaifinka zai zo ganin ka, ka tambaye shi, "Idan ka yarda ka aiko Tama 'yar'uwata ta ba ni wani abu in ci, bari ta girka shi a gaba na, domin in gan shi in kuma ci shi daga hannunta?'"
\v 6 Sai Amnon ya kwanta kamar ba shi da lafiya. Da sarki ya zo domin ya dube shi, Amnon ya cewa sarki, "Idan ka yarda ka aiko 'yar'uwata Tama ta yi mani ɗan abinci saboda rashin lafiyata domin in ci daga hannunta.'"
\s5
\v 7 Sai Dauda ya aika saƙo ga Tama a fãdarsa, cewa, "Ki tafi yanzu gidan ɗan'uwanki Amnon ki shirya masa abinci."
\v 8 Sai Tama ta tafi gidan ɗan'uwanta Amnon in da ya ke kwance. Sai ta ɗauki ƙullu ta cuɗa ta yi waina a idonsa, sa'an nan ta toya.
\v 9 Ta ɗauki kaskon kuma ta ba shi wainar, amma ya ƙi ci. Sa'an nan Amnon ya cewa waɗanda ke wurinsa, '"Kowa ya fita waje, ku ba ni wuri." Sai kowanne ɗayan su ya fita daga gare shi.
\s5
\v 10 Sai Amnon ya cewa Tama, "Kawo abincin nan ɗakina domin in ci daga hannunki." Sai Tama ta ɗauki wainar da ta yi, ta kawo ta cikin ɗakin Amnon ɗan'uwanta.
\v 11 Da ta kawo masa abincin, sai ya cafke hannunta ya ce mata, "Ki zo, ki kwana da ni, 'yar uwata."
\v 12 Ta amsa masa, "A'a, ɗan'uwana, kada ka matsa mani, domin ba makamancin abu haka da ya kamata ya faru a Isra'ila. Kada ka yi wannan abin kunya!
\s5
\v 13 Ƙaƙa zan rabu da kunyata? Kai kuma fa? Za ka zama kamar ɗaya daga cikin sakarkaru na Isra'ila! Yanzu fa in ka yarda ka yiwa sarki magana, ba zai hana ka ni ba."
\v 14 Duk da haka Amnon ya ƙi ya saurare ta. Tun da ya fi Tama ƙarfi, sai ya kama ta ya kwana da ita.
\s5
\v 15 Sa'an nan Amnon ya ƙi Tama da mummunar ƙiyayya. Ya ƙi ta fiye da yadda dã ya yi sha'awarta. Amnon ya ce mata,
\v 16 "Tashi ki tafi." Amma ta amsa masa, "A, a! Wannan babbar muguntar sallamata in tafi ta fi muni da abin da ka yi mani!" Amma Amnon bai saurare ta ba.
\v 17 Maimakon haka, sai ya kira baransa ya ce, "Ka fitar da wannan mata daga gabana, ka kulle ƙofar a bayanta."
\s5
\v 18 Sai baransa ya fitar da ita ya kulle ƙofar a bayanta. Tama ta na saye da wata taguwa mai ado sosai domin 'ya'yan sarki mata waɗanda budurwai ne suna yin shiga irin haka.
\v 19 Tama ta baɗa toka a kanta ta keta taguwarta. Ta ɗibiya hannayenta a kanta ta tafi, tana rusa kuka sa'ad da take tafiya.
\s5
\v 20 Absalom ɗan'uwanta ya ce mata, "Ko ɗan'uwanki Amnon ya sadu da ke ne? Amma yanzu ki yi shuru, 'yar uwata. Shi ɗan'uwanki ne. Ka da ki riƙe wannan a zuciya." Haka Tama ta zauna ita kaɗai a gidan wanta Absalom.
\v 21 Sa'ad da Sarki Dauda ya ji dukkan waɗannan abubuwa, sai ya husata ƙwarai.
\v 22 Absalom bai cewa Amnon komai ba, gama Absalom ya ƙi shi sabili da abin da ya yi mata da yadda ya kunyatar da 'yar'uwarsa Tama.
\s5
\v 23 Ya zama fa bayan shekara biyu cur, Absalom na da masu sausayar tumaki da ke aiki a Bãl Hazor, wadda ke kusa da Ifraim, Absalom kuma ya gayyaci dukkan 'ya'yan sarki maza su ziyarci wurin.
\v 24 Absalom ya tafi wurin sarki ya ce, "Duba yanzu, bawanka yana da masu sausayar tumaki. Idan ka yarda bari sarki da barorinsa su zo tare da ni, bawanka."
\s5
\v 25 Sarki ya amsa wa Absalom, "A'a, ɗana kada dukkanmu mu tafi domin za mu wahalshe ka." Absalom ya ƙarfafa sarki, amma bai yarda ya tafi ba, sai dai ya albarkaci Absalom.
\v 26 Sai Absalom ya ce, "In ba haka ba, idan ka yarda bari ɗan'uwana Amnon ya je tare da mu." Sai sarki ya ce masa, "Donme Amnon zai je tare da ku?"
\s5
\v 27 Absalom ya matsa wa Dauda, sai ya bari Amnon da dukkan 'ya'yan sarki maza su tafi tare da shi.
\v 28 Absalom ya dokaci barorinsa cewa, "Ku saurara sosai. Sa'ad da Amnon ya soma buguwa sosai da ruwan inabi, kuma sa'ad da zan ce maku, 'Ku hari Amnon,' sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ba nine na dokace ku ba? Ku yi ƙarfin hali ku yi mazakutta."
\v 29 Sai barorin Absalom suka yiwa Amnon yadda aka dokace su. Sai dukkan 'ya'yan sarki maza suka tashi, kowanne mutum ya haye bisa alfadarinsa ya tsere.
\s5
\v 30 Ya zamana fa, lokacin da suke kan hanya, sai labari ya kai wurin Dauda cewa, "Absalom ya kashe dukkan 'ya'yan sarki maza kuma babu ko ɗaya da ya rage a cikinsu."
\v 31 Sai sarki ya miƙe ya kekketa tufafinsa, ya kwanta a ƙasa; dukkan barorinsa suka tsaya nan da tufafinsu a yayyage.
\s5
\v 32 Yehonadab ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda, ya amsa ya ce, "Kada ubangidana ya gaskata cewa sun kashe dukkan samari waɗanda 'ya'yan sarki maza ne, gama Amnon ka ɗai ya mutu. Absalom ya ƙudura wanna abu tun daga randa Amnon ya ɓata 'yar'uwarsa Tama.
\v 33 Saboda haka fa, kada maigidana sarki ya riƙe wannan rahoto a zuciyarsa har da zai gaskata cewa dukkan 'ya'yan sarki maza suka mutu, gama Amnon ne kaɗai ya mutu."
\s5
\v 34 Absalom ya gudu. Wani bawa da ke tsaro ya tada idanunsa ya ga mutane da yawa suna zuwa a kan hanya a gefen dutse yamma da shi.
\v 35 Sai Yonadab ya cewa sarki, "Duba, 'ya'yan sarki maza suna zuwa. Ya yi dai-dai da yadda bawanka ya faɗa."
\v 36 Ya zama fa sa'ad da ya gama magana sai 'ya'yan sarki maza suka iso suka tada muryoyinsu suka yi kuka. Sarki da dukkan barorinsa ma suka yi kuka mai zafi.
\s5
\v 37 Amma Absalom ya gudu ya tafi gunTalmai ɗan Ammihud, sarkin Geshu. Dauda ya yi ta makokin ɗansa da daɗewa.
\v 38 Sai Absalom ya gudu ya tafi Geshu, inda ya kasance har shekara uku.
\v 39 Ran Sarki Dauda ya yi marmarin ya tafi ya ga Absalom, gama ya ta'azantu game da Amnon da mutuwarsa.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Yanzu fa Yowab ɗan Zeruya ya fahimci cewar ran sarki na marmarin ganin Absalom.
\v 2 Yowab ya aika da kalmar saƙo a Tekowa yasa a kawo masa mace mai hikima. Ya ce mata, "Ina roƙonki kiyi kamar kina makoki kisa tufafin makoki. Ina roƙon ki kada ki shafa mai a jikinki, amma kiyi kamar mace wadda ta daɗe tana makoki domin matacce.
\v 3 Daga nan sai ki je wurin sarki kiyi magana da shi game da abin da zan kwatanta." Sai Yowab ya faɗa mata maganganun da za ta faɗi a wurin sarki.
\s5
\v 4 Sa'ad da matar nan daga Tekowa ta yi magana da sarki, sai ta kwanta da fuskarta a ƙasa ta ce, "Ka taimake ni, ya sarki."
\v 5 Sarki ya ce mata, "Me ya faru?" Sai ta amsa, "Gaskiyar ita ce ni gwauruwa ce, maigidana kuma ya mutu.
\v 6 Ni baiwarka, ina da 'ya'ya biyu, sun yi faɗa tare a cikin saura, ba kuwa wani wanda zai raba su. Ɗaya ya bugi ɗayan har ya kashe shi.
\s5
\v 7 Yanzu duk zuriyar sun tashi gãba da baiwarka, su ka ce, 'Ki ba mu mutumin da ya kashe ɗan'uwansa cikin hannunmu, domin mu kashe shi, domin biyan ran ɗan'uwansa wanda ya kashe.' Da haka kuma za su hallaka magajin. Ta yin haka za su ɓice wutata da ta rage, kuma ba za su bar wa maigidana suna ko zuriya a doron ƙasa ba."
\s5
\v 8 Sai sarki ya cewa matar, "Ki tafi gidanki, kuma zan umarta ayi wani abu domin ki."
\v 9 Sai matar nan ta Tekowa ta amsa wa sarki, "Ya shugabana, sarki, bari alhakin laifin ya komo kaina da gidan iyalin mahaifina. Sarki da kursiyinsa basu da laifi."
\s5
\v 10 Sai sarki ya amsa, duk wanda ya ce maki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara taɓa ki ba."
\v 11 Daga nan sai ta ce, "Ina roƙon ka, bari sarki ya tuna da Yahweh Allahnka, domin kada mai ɗaukar fansar jini ya ƙara hallakar da wani, domin kada su hallaka ɗana." Sai sarki ya amsa, "Bisa ran Yahweh, babu gashin ɗanki ko ɗaya da zai faɗi ƙasa."
\s5
\v 12 Daganan sai matar ta ce, "In ka yarda bari baiwarka ta sake yin magana ga shugabana sarki." Ya ce, "Ci gaba da magana"
\v 13 Sai matar ta ce, "Donme ka kutta wannan maƙida gãba da mutanen Allah? Gama ta wurin faɗin wannan, sarki ya zama kamar wani mai laifi, saboda sarki bai sake dawo da korarren ɗansa gida ba.
\v 14 Gama dukkan mu dole mu mutu, kuma muna kama da ruwan da aka zubar a ƙasa, wanda ba za a sake tattara shi ba. Amma Allah ba zai ɗauki rai ba; maimakon haka, ya kan nemi hanya domin waɗanda aka kora su dawo.
\s5
\v 15 Yanzu fa, ganin yadda na zo in faɗi wannan abu ga shugabana sarki, saboda mutane sun sa na ji tsoro. Sai baiwarka ta ce a ranta, 'yanzu zan yi magana da sarki. Maiyiwuwa ne sarki ya aikata bisa ga roƙon baiwarsa.
\v 16 Watakila sarki zai saurare ni kuma ya ceci baiwarsa daga hannun mutumin da zai hallaka ni da ɗana tare, daga cikin gãdon da Allah ya ba mu.'
\v 17 Daga nan baiwarka ta yi addua, ta ce, Yahweh, in ka yarda bari maganar shugabana sarki ta ba ni sauƙi, gama kamar yadda mala'ikan Allah ya ke, haka shugabana sarki ya ke wajen faɗin abu mai kyau daga mugunta.' Bari Yahweh Allahnka ya kasance tare da kai."
\s5
\v 18 Daga nan sarki ya amsa wa matar ya ce, 'Ina roƙon ki kada ki ɓoye mani komai da zan tambaye ki." Sai matar ta amsa ta ce, 'Yanzu bari shugabana sarki ya yi magana."
\v 19 Sai sarki ya ce "Ko hannun Yowab bai tare da ke cikin dukkan al'amarin nan?" Sai matar ta amsa ta ce, "Bisa ga ranka, ya shugaba sarki, ba wani ko ɗaya da zai kuɓuta daga hannun dama ko hagu daga duk wani abin da shugabana sarki ya faɗi. Gama bawanka Yowab ne ya umarce ni ya kuma gaya mani dukkan abubuwan da baiwarka ta faɗi.
\v 20 Bawanka Yowab ya yi wannan domin ya canza yanayin abin da ya ke faruwa. Shugabana kuma yana da hikima, hikima irinta mala'ikan Allah, kuma ya san dukkan abin da ya ke faruwa a cikin ƙasa."
\s5
\v 21 Sai sarki ya cewa Yowab, Yanzu fa ka duba, zan yi wannan, jeka fa, ka komo da saurayin nan Absalom."
\v 22 Sai Yowab ya kwanta da fuskarsa ƙasa cikin darajantawa da godiya ga sarki. Yowab ya ce, "Yau bawanka ya sani cewa Na sami tagomashi a idonka, ya shugabana, sarki, da shi ke sarki ya aikata bisa ga roƙon bawansa."
\s5
\v 23 Sai Yowab ya ta shi, ya tafi Geshu, kuma ya zo da AbsalomYerusalem.
\v 24 Sarki ya ce, "Zai iya komawa gidansa, amma ba lallai ya ga fuskata ba." Absalom ya dawo gidansa, amma bai ga fuskar sarki ba.
\s5
\v 25 Yanzu kuwa a cikin dukkan Isra'ila babu wanda ake yabo domin kyansa fiye da Absalom. Daga tafin sawunsa zuwa bisa kansa babu wani aibi a cikinsa.
\v 26 Sa'ad da ya aske gashin kansa a ƙarshen kowacce shekara, saboda ya kan yi masa nauyi, yakan auna gashin kansa, ya kan kai kimanin awo ɗari biyu, bisa ga mizanin ma'aunin sarki.
\v 27 An haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace ɗaya, sunanta Tama. Ita kyakkyawar mace ce.
\s5
\v 28 Absalom ya zauna cikakkun shekaru biyu a Yerusalem, ba tare da ganin fuskar sarki ba.
\v 29 Daga nan Absalom ya aika a kira Yowab domin ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa wurinsa. Har yanzu Absalom ya sake aikawa karo na biyu, duk da haka Yowab ya ƙi zuwa.
\s5
\v 30 Domin wannan Absalom ya ce da barorinsa, "Duba, gonar Yowab tana kusa da tawa, ga shi yana da bali a wurin. Ku je ku sa mata wuta."
\v 31 Sai barorin Absalom suka sawa gonar wuta. Daga nan sai Yowab ya tashi ya zo wurin Absalom a gidansa, ya ce masa, "Donme barorinka suka sawa gonata wuta?"
\s5
\v 32 Absalom ya amsa wa Yowab, "Duba na aika maka cewa, ka zo nan domin in aike ka wurin sarki ka ce, "Donme na dawo daga Geshu? ya fi mani sauƙi a ce har yanzu ina can. Yanzu bari in ga fuskar sarki, idan bani da gaskiya, bari ya kashe ni.'"'
\v 33 Sai Yowab ya je wurin sarki ya faɗa masa. Sa'ad da sarki ya kira Absalom, sai ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki, sarki kuwa ya sumbaci Absalom.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Ana nan bayan wannan kuma Absalom ya shirya karusa da dawakai domin kansa, tare da mutane hamsin masu gudu a gabansa.
\v 2 Absalom zai tashi da wuri ya tsaya a bakin hanya mai zuwa ƙofar birni, sa'ad da kowanne mutum ya ke da matsalar da za a kawo wa sarki domin shari'a, daga nan sai Absalom ya kira shi ya ce, "Daga wanne birni ka zo?" sai mutumin ya amsa, "Bawanka daga ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila ya ke."
\s5
\v 3 Sai Absalom ya ce masa, Duba, maganarka tana da kyau da kuma gaskiya, amma sarki bai sanya kowa da zai ji maganarka ba."
\v 4 Absalom ya ƙara da cewa, "Ina ma da ni aka sanya in zama alƙali cikin ƙasar, domin kowanne mutum da ke da kowacce irin matsala ko dalili ya zo wurina, kuma zan yi masa adalci!"
\s5
\v 5 Ya zama kuwa idan kowanne mutum ya zo wurin Absalom domin ya girmama shi, Absalom ya kan miƙa hannunsa ya kama shi ya yi masa sumba.
\v 6 Absalom ya aikata wannan ga dukkan Isra'ila musamman wanda ya zo wurin sarki domin shari'a. Da haka Absalom ya sace zukatan mutanen Isra'ila.
\s5
\v 7 Ana nan bayan shekaru huɗu sai Absalom ya cewa sarki, "Ina roƙonka ka yardar mani in tafi in cika wa'adin da na yiwa Yahweh cikin Hebron.
\v 8 Gama bawanka ya yi wa'adi lokacin da nake zama a Geshu cikin Aram, cewa, 'Idan ya tabbata Yahweh ya sake dawo da ni Yerusalem, daga nan zan yi wa Yahweh sujada.'"
\s5
\v 9 Sai sarki ya ce masa, "Tafi lafiya" Sai Absalom ya tashi ya tafi Hebron.
\v 10 Amma Absalom ya aika da masu leƙen asirin ƙasa cikin dukkan kabilun Isra'ila, ya na cewa, da zarar kun ji busar ƙaho, daga nan dole ku ce, 'Absalom ne sarki cikin Hebron.'"
\s5
\v 11 Mazaje ɗari biyu suka ta fi tare da Absalom daga Yerusalem, waɗanda aka gayyata. Sun tafi cikin rashin sanin su, ba su da masaniyar abin da Absalom ya rigaya ya shirya.
\v 12 Lokacin da Absalom ke cikin miƙa hadayu, ya aika a kirawo Ahitofel daga garinsa a Gilo. Shi ne mai ba Dauda shawara. Makircin Absalom kuwa ya yi ƙarfi, gama mutanen da ke bin Absalom kullum sai ƙaruwa suke yi.
\s5
\v 13 Wani ɗan saƙo ya zo wurin Dauda ya ce, "Zukatan mutanen Isra'ila sun koma wajen Absalom."
\v 14 Sai Dauda ya cewa dukkan bayinsa da e tare da shi a Yerusalem, "Tashi bari mu gudu, in ba haka ba a cikinmu babu wanda zai kuɓuta daga hannun Absalom. Mu hanzarta tashi, kada ya same mu da sauri, kuma ya kawo bala'i a kanmu ya bugi birnin da kaifin takobi.
\v 15 Bayin sarki suka cewa sarki, "Duba, bayin sarki a shirye suke su yi duk iyakar abin da shugabanmu sarki ya ayyana."
\s5
\v 16 Sarki ya fita dukkan iyalinsa kuma suka bi shi, amma sarki ya bar mata goma, waɗanda ƙwaraƙwarai ne domin su kula da fãda.
\v 17 Bayan da sarki ya fita tare da dukkan mutanen da ke bayansa, suka tsaya a gida na ƙarshe.
\v 18 Dukkan rundunarsa suka tafi tare da shi, a gaban sa kuma dukkan Keretawa, da dukkan Feletawa, da dukkan Gittiyawa - mutum ɗari shida waɗanda suka bi shi tun daga Gat.
\s5
\v 19 Sa'an nan sarki ya cewa Ittai Bagitti, "Donme za ka zo, tare da mu? Ka koma ka zauna tare da sarki Absalom, gama kai baƙo ne ɗan bauta kuma, ka koma wurinka.
\v 20 Da ya ke jiya kaɗai ka tafi, donme zan sa ka kai da komowa tare da mu? Gashi kuwa ban ma san inda zan tafi ba. Don haka sai ka juya ka koma ka ɗauki 'yan ƙasarka. Bari bangirmanka da aminci su tafi tare da kai."
\s5
\v 21 Amma Ittai ya amsa wa sarki ya ce, "Na rantse da ran Yahweh, da ran shugabana sarki kuma, hakika duk wurinda shugabana sarki ya tafi, can ne kuma bawanka za shi, ko ya kai ga rayuwa ko ga mutuwa."
\v 22 Sai Dauda ya cewa Ittai, "Jeka ka ci gaba tare da mu" Sai Ittai Bagitti ya haye tare da sarki, da dukkan mutane da dukkan iyalin da ke tare da shi.
\v 23 Dukkan ƙasar kuwa ta yi kuka da babbar murya yayin da dukkan mutane suka ratsa ta hayin kwarin Kidron, sarki ma da kansa ya haye. Dukkan mutane suka yi tafiya a ƙasa zuwa wajen hanyar jeji.
\s5
\v 24 Har su Zadok da dukkan Lebiyawa, masu ɗauke da akwatin alƙawarin Allah, suna wurin. Suka ajiye akwatin Allah a ƙasa, Abiyata ya bi su. Suka jira har saida dukkan mutane suka gama fitowa daga cikin birni.
\v 25 Sai sarki ya cewa Zadok, "Ka ɗauki akwatin Allah ka mai da shi cikin birni. Idan na sami tagomashi a idon Yahweh, zai komo da ni nan, ya kuma sake nuna mani akwatin da wurin zamansa.
\v 26 Amma idan ya ce, "Ba na jin daɗinka,' Duba Ina nan, bari ya yi mani abin da ya ga ya yi masa kyau."
\s5
\v 27 Sai sarki ya cewa Zadok firist, kai ba mai gani ba ne? Ka koma cikin birni lafiya, da 'ya'yanka biyu tare da kai, Ahimãz ɗanka, da Yonatan ɗan Abiyata.
\v 28 Duba, a wurin mashigai na jeji zan jira har sai magana ta zo daga gare ku ka sanar da ni."
\v 29 Sai Zadok da Abiyata suka ɗauki akwatin alƙawari na Allah suka mai da shi cikin Yerusalem, suka kuma zauna can.
\s5
\v 30 Amma Dauda ya haura ba takalmi yana kuka har zuwa Dutsen Zaituna, kuma ya rufe kansa. Kowanne mutum cikin mutanen da ke tare da shi ya rufe kansa, suka hau suna kuka yayin da suke tafiya.
\v 31 Sai wani ya faɗawa Dauda ya ce, Ahitofel na cikin masu maƙida da Absalom." Dauda ya yi addu'a ya ce, "Ya Yahweh, ina roƙonka ka juyar da shawarar Ahitofel ta zama wawanci."
\s5
\v 32 Ana nan sa'ad da Dauda ya kai kan hanya, inda a ke yiwa Allah sujada, Hushai Ba'arkite ya zo ya sadu da shi da yagaggar tufa da ƙura a kansa.
\v 33 Dauda ya ce masa, "I dan za ka yi tafiya tare da ni, za ka zama nawaya a gare ni.
\v 34 Amma idan ka juya cikin birni ka ce da Absalom, 'Zan zama bawanka, ya sarki, kamar yadda na zama bawan mahaifinka a kwanakin baya, haka kuma yanzu zan zama bawanka,' ta haka za ka ruɗar da shawarar Ahitofel domina.
\s5
\v 35 Ba za ka tafi tare da Zadok da Abiyata firist tare da kai ba? Zai zama kuwa duk abin da ka ji a fadar sarki, dole ka faɗawa Zadok da Abiyata firist.
\v 36 Duba can suna tare da 'yayansu biyu, Ahimãz ɗan Zadok da Yonatan ɗan Abiyata. Dole ta hannunsu za ku aiko mani da dukkan abin da kuka ji."
\v 37 Sai Hushai, abokin Dauda, ya zo cikin birni yayin da Absalom ya kai kuma ya shiga cikin Yerusalem.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Sa'ad da Dauda ya hau har ya wuce kan tudu kaɗan, Ziba bawan Mefiboshet ya gamu da shi da jãkai guda biyu labtattu; a kansu kuwa dunƙulen gurasa guda ɗari biyu na curin kauɗar inabi ɗari, da curin 'ya'yan itacen ɓaure ɗari, da salkar ruwan inabi.
\v 2 Sarki ya cewa Ziba, "Donme ka kawo waɗannan abubuwa?" Ziba ya amsa ya ce, "Jakai domin iyalin sarki ne su hau, gurasa da wainar itacen ɓaure domin mutanenka su ci, ruwan inabi kuma domin duk wanda ya sũma a cikin jeji ya sha."
\s5
\v 3 Sarki ya ce, Ina jikan shugabanka?" Ziba ya amsa wa sarki ya ce, "Duba, ya tsaya baya cikin Yerusalem, gama ya ce, 'Yau gidan Isra'ila za su mayar mani da sarautar mahaifina.'"
\v 4 Daga nan sai sarki ya cewa Ziba, "Duba, dukkan abin da ke mallakar Mefiboshet yanzu naka ne,'" Sai Ziba ya amsa, na sunkuya cikin bangirma gare ka, ya shugabana, sarki. Bari in sami tagomashi a idanunka."
\s5
\v 5 Sa'ad da sarki Dauda ya gabato Bahurim, wani mutum daga gidan iyalin Saul ya zo, sunansa Shimei ɗan Gera. Ya fito yana tafiya yana la'antarwa.
\v 6 Ya jefi Dauda da duwatsu har da shugabannin sarki, duk da sojoji da masu tsaro da ke hannun damansa da hannun hagu.
\s5
\v 7 Shimei ya yi kira cikin la'antarwa, "Tafi daga nan, mutumin banza, mutumin jini!
\v 8 Yahweh ya sãka wa dukkanku domin jinin iyalin gidan Saul, wanda kake mulki a matsayinsa. Yahweh ya bada mulkin a cikin hannun Absalom ɗanka. Gashi yanzu kuma ka hallaka saboda ka zama mutum mai zubda jini."
\s5
\v 9 Daga nan sai Abishai ɗan Zeruya ya cewa sarki, "Donme wannan mataccen karen zai la'anta shugabana sarki? Ina roƙonka ka yardar mani in haye in fille masa kai."
\v 10 Amma sarki ya ce, "Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Mai yiwuwa yana la'antani saboda Yahweh ne ya ce masa, "La'anta Dauda.' Wane ne zai ce masa, 'Donme kake la'antar sarki?'"
\s5
\v 11 Sai Dauda ya cewa Abishai da dukkan bayinsa, "Duba, ɗana, wanda aka haifa daga cikin jikina, yana so ya ɗauki raina. Balle wannan mutumin Benyamin da ke marmarin ganin hallaka ta, Ku ƙyale shi kawai ku bar shi ya yi ta la'antarwa, gama Yahweh ne ya umarce shi.
\v 12 Maiyiwuwa Yahweh ya duba irin gagarumin baƙincikin da ke kaina, ya sãka mani da alheri saboda la'antarwar da ya yi mani yau."
\s5
\v 13 Hakanan Dauda da mazajensa suka yi tafiya kan hanya, Shimei kuma ya zaga gefen gangaren tudu, yana tafiya yana la'antarwa yana jifansa da duwatsu yana zuba masa turɓaya yayin da ya ke tafiya,
\v 14 Daga nan sarki da dukkan mutanen da ke tare da shi suka zo da gajiya, can ya huta lokacin da suka tsaya da dare.
\s5
\v 15 Absalom kuwa da dukkan matanen Isra'ila waɗanda ke tare da shi, suka zo Yerusalem, Ahitofel kuma na tare da shi.
\v 16 Ya zama kuwa sa'ad da Hushai - Ba'arkite, abokin Dauda, ya zo wurin Absalom Hushai ya cewa Absalom, "Ran sarki ya daɗe! Ran sarki ya daɗe!"
\s5
\v 17 Absalom ya cewa Hushai, "Wannan ita ce biyayyarka ga abokinka? Donme ba ka tafi tare da shi ba?"
\v 18 Hushai ya cewa Absalom, "A'a! maimakon haka, shi wanda Yahweh da wannan jama'a da dukkan mutanen Isra'ila suka zaɓa, shi ne mutumin da ni zan zama nasa, kuma zan zauna tare da shi.
\s5
\v 19 Kuma, wanne mutum zan bautawa? Ba gaban ɗansa ya kamata in yi bautar ba? kamar yadda na yi bautar gaban mahaifinka, hakanan zan yi bautar a gabanka."
\s5
\v 20 Sa'an nan Absalom ya cewa Ahitofel sai ka ba mu shawara game da abin da za mu yi."
\v 21 Ahitofel ya amsa wa Absalom, "Ka je ka kwana da bayin matan mahaifinka waɗanda ya bari domin su kula da fãda, daga nan dukkan Isra'ila za su ji ka zama abin ƙyama ga mahaifinka. Daga nan hannuwan dukkan waɗanda ke tare da kai za su yi ƙarfi."
\s5
\v 22 Sai suka baza wa Absalom rumfa a bisa fãda, Absalom kuwa ya kwana da mata bayin mahaifinsa a idanun dukkan Isra'ila.
\v 23 Ya zama kuwa shawarar da Ahitofel ya bayar a waɗannan kwanaki ta zama kamar wadda mutum ya ji daga bakin Allah da kansa. Haka dukkan shawarar Ahitofel ta zama a wurin Dauda da Absalom.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Daga nan sai Ahitofel ya cewa Absalom, "Yanzu bari in zaɓi maza dubu goma sha biyu, kuma zan tashi in fafari Dauda yau a daren nan.
\v 2 Zan auka masa lokacin da ya yi raụni ya gaji in kuma ba shi mamaki da tsoro. Mutanen da ke tare da shi za su gudu, sarki kaɗai zan buge.
\v 3 Zan dawo da dukkan mutane a gare ka. kamar amaryar da ke zuwa wurin mijinta, daga nan dukkan mutane za su zauna lafiya ƙarƙashinka."
\v 4 Abin da Ahitofel ya faɗi ya faranta wa Absalom rai da dukkan dattawan Isra'ila.
\s5
\v 5 Daga nan sai Absalom ya ce, yanzu ku kira Hushai Ba'akite shima, bari mu ji abin da ya ce."
\v 6 Sa'ad da Hushai ya zo wurin Absalom, Absalom ya bayyana masa abin da Ahitofel ya faɗi sai ya tambayi Hushai, "Ko za mu iya yin abin da Ahitofel ya ce? In ba haka ba sai ka faɗi shawararka."
\v 7 Sai Hushai ya cewa Absalom, "Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokacin ba ta da kyau."
\s5
\v 8 Hushai ya ƙara da cewa, "Ka san mahaifinka da mazajensa jarumawa ne masu ƙarfi, kuma suna da zafin rai, kamar damisar da a ka ƙwace wa 'ya'yanta a cikin saura. Mahaifinka mayaƙine, ba zai kwana tare da mutane a daren nan ba.
\v 9 Duba, yanzu haka mai yiwuwa yana wurin ɓuya cikin wasu ramummuka ko a wani wuri. Za ya zama kuwa idan aka kashe waɗansu mutanenka a farkon harin, iyakar wanda yaji zai ce, 'An yi yanka tsakanin sojojin da ke bin Absalom.'
\v 10 Daga nan har su sojoji masu ƙarfin zuciya, waɗanda zukatansu suna kama da zuciyar zaki, za su ji tsoro domin dukkan Isra'ila sun sani cewa mahaifinka jarumi ne, kuma mutanen da ke tare da shi suna da ƙarfi ƙwarai.
\s5
\v 11 Shawarata a gare ka ita ce a tattara dukkan Isra'ila a gare ka, daga Dan zuwa Biyasheba, kamar yashin da ke bakin teku yawa, kai kuwa da kanka ka tafi yaƙi.
\v 12 Daga nan zamu abka masa a wurin da za a same shi, za mu rufe shi kamar yadda raɓa take faɗowa ƙasa. Ba za mu bar ko ɗaya daga cikin mazajensa, ko shi kansa, da rai ba.
\s5
\v 13 Idan ya toge cikin birni, daga nan dukkan Isra'ila za su kawo igiyoyi zuwa ga birnin nan kuma za mu jãshi zuwa cikin rafi, har da ba za a tarar da ko ƙanƙanen dutse ɗaya a wurin ba."
\v 14 Daga nan sai Absalom da dukkan mazajen Isra'ila suka ce, shawarar Hushai Ba-arkite tafi shawarar Ahitofel." Yahweh ya wajabta ƙin amincewa da shawara mai kyau ta Ahitofel domin a kawo hallakarwa a kan Absalom.
\s5
\v 15 Daga nan sai Hushai ya cewa Zadok da Abiyata firistoci, "Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Israi'ila irin wannan shawarar, amma ni na bada wata shawarar dabam.
\v 16 Yanzu kuwa, sai ku tafi da sauri ku sanar da Dauda; ku ce masa, 'Kada ku yi sansani a daren yau a mashigan Araba, amma ta ko ƙaƙa ka haye, in ba haka ba za a haɗiye sarki da dukkan mutanen da ke tare da shi."
\s5
\v 17 Yanzu Yonatan da Ahimãz suna zama a maɓuɓɓugar En-Rogel. Wata mace baiwa takan je ta sanar da su abin da ya kamata su sani, domin bashi yiwuwa su ɗauki kasadar a yi ta ganinsu suna tafiya cikin birni. Idan saƙo ya zo sukan je su faɗa wa sarki Dauda.
\v 18 Amma wani saurayi ya gan su a wannan lokacin sai ya faɗa wa Absalom. Sai Yonatan da Ahimãz suka fita a gaggauce suka zo gidan wani mutum a cikin Bahurim, wanda ya ke da rijiya a harabar gidansa, inda suka sauka ciki.
\s5
\v 19 Matar mutumin kuma ta ɗauki murfin rijiyar ta rufe bakin rijiyar da shi, ta zuba hatsi a kai, ba wanda ya san cewa Yonatan da Ahimãz suna cikin rijiyar.
\v 20 Mutanen Absalom suka zo wurin matar gidan suka ce, "Ina Ahimãz da Yonatan?" Sai matar tace masu, "Sun haye rafi." Bayan da suka dudduba ko'ina ba su same su ba, sai suka koma Yerusalem.
\s5
\v 21 Ya zama kuwa bayan da suka tafi sai Yonatan da Ahimãz suka fito daga cikin rijiyar. Suka tafi su kai wa sarki Dauda rahoto; suka ce masa, "Ku tashi ku haye ruwa da sauri saboda Ahitofel ya bada irin wannan shawarar game da ku."
\v 22 Daga nan sai Dauda ya tashi da dukkan mutanen da ke tare da shi, suka haye Yodan. Kafin wayewar hasken safiya babu ko ɗaya daga cikin su da ya kasa hayewa Yodan.
\s5
\v 23 Sa'ad da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yiwa jãkinsa sirdi ya tafi. Ya koma gida cikin nasa birni, ya kimtsa al'amuransa, kuma ya rataye kansa. Ta haka ya mutu aka kuma bizne shi cikin kabarin mahaifinsa.
\s5
\v 24 Daga nan sai Dauda ya zo Mahanayim. Absalom kuma, ya hayeYodan, shi da dukkan mazajen Isra'ila tare da shi.
\v 25 Absalom kuma yasa Amasa shugaban rundunar yaƙi maimakon Yowab. Amasa ɗan Yeta Isma'ile, wanda ya kwana da Abigel wadda take ɗiyar Nahash 'yar'uwar Zeruya uwar Yowab.
\v 26 Daga nan Isra'ila da Absalom suka kafa sansani cikin ƙasar Giliyad.
\s5
\v 27 Ya zama kuwa sa'ad da Dauda ya zo Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabbah na Ammonawa, da Maki ɗan Amiyel daga Lo Deba, da Barzillai Bagiliye daga Rogelim,
\v 28 suka kawo tabarmin kwanciya da barguna, da masakai da tukwane, da alkama, garin bali, gasasshen hatsi, wake, da ganye,
\v 29 zuma, da mai, tumaki da manshanu, domin Dauda da mutanen da ke tare da shi su ci. Mutanen nan suka ce, "Mutanen nan suna jin yunwa, da gajiya, da ƙishi a cikin jeji."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Dauda ya ƙidaya sojojin da ke tare da shi ya naɗa shugabanni na dubbai da na ɗarurruka a bisansu.
\v 2 Daga nan Dauda ya aika da rundunar soja, ɗaya bisa uku ƙarƙashin, umarnin Yowab, waɗansu kashi uku kuma ƙarƙashin umarnin Abishai ɗan Zeruya, ɗan uwan Yowab, har yanzu wani kashi na uku kuma ƙarƙashin umarnin Ittai Ba-gitte. Sarki kuma ya cewa rundunar yaƙi, "Lallai zan fita tare daku da kaina, nima."
\s5
\v 3 Amma mazajen suka ce, "Ba dole sai ka je yaƙi ba, gama idan mun gudu ba za su kula da mu ba, ko idan rabin mu sun mutu ba za su kula ba. Amma darajarka a bakin zambar goma tamu ce! Domin wannan ya fi kyau kai ka kasance da shirin yi mana taimako daga cikin birni."
\v 4 Sai sarki ya amsa masu, "Zan yi duk abin da ku ka ga yafi maku kyau." Sarki ya tsaya a bakin ƙofar birni yayin da dukkan rundunar yaƙi suka fita ɗari-ɗari da dubu-dubu.
\s5
\v 5 Sai sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai cewa, "kuyi a hankali da saurayin nan, da Absalom, sabili da ni." Dukkan mutane sun ji cewa sarki ya ba shugabanni wannan umarni game da Absalom.
\s5
\v 6 Rundunar yaƙi suka fita zuwa cikin filin karkara garin suyi yaƙi da Isra'ila; yaƙin ya bazu zuwa cikin kurmin Ifraim.
\v 7 Rundunar yaƙin Isra'ila sun sha kãshi a wurin a hannun sojojin Dauda; a rannar kuwa aka yi kisa mai yawa a wurin an kashe mazaje dubu ashirin.
\v 8 Faɗan ya bazu ko'ina cikin ɓangaren ƙasar, mazajen da kurmi ya cinye suka fi waɗanda suka mutu ta kaifin takobi.
\s5
\v 9 Ya kasance kuwa Absalom ya gamu da waɗansu sojojin Dauda. Absalom yana tafiya kan alfadarinsa, alfadarin kuwa ya shiga ƙarƙashin cikin rassa masu kauri na itacen rimi, itacen kuwa ya kama kansa cikin rassan. Yana reto tsakanin sama da ƙasa alfadarin da ya ke haye akai kuwa ya ci gaba da tafiya.
\v 10 Wani mutum daya gani sai ya fada wa Yowab, "Duba, na ga Absalom rataye a itacen rimi!"
\v 11 Yowab ya ce da mutumin daya faɗa masa game da Absalom, "Duba! ka ganshi! donme ba ka buge shi a ƙasa ba? Ai da na baka azurfa goma da ɗammara."
\s5
\v 12 Sai mutumin ya amsa wa Yowab, "Koda na karɓi shekel ɗin azurfa dubu, duk da haka bazan miƙa hannuna gãba da ɗan sarki ba, domin mun ji umarnin da sarki ya ba ku, Abishai da Ittai cewa, 'kada kowa ya taɓa saurayin nan Abasalom.'
\v 13 Da na yi kasada da raina ta wurin ƙarya (kuma babu abin da ke ɓoye a wurin sarki), da ka yashe ni,"
\s5
\v 14 Daga nan sai Yowab ya ce, "Ba zan jira ka ba." Sai Yowab ya ɗauki mãshi uku cikin hannunsa ya caka su cikin zuciyar Absalom, yayin da ya ke da rai ya ke kuma rataye a itacen rimi.
\v 15 Daga nan majiya ƙarfi guda goma masu ɗauke da sulken Yowab suka kewaye Absalom, suka buge shi, suka kashe shi.
\s5
\v 16 Yowab ya busa ƙaho, rundunar yaƙi suka dawo daga runtumar Isra'ilawa, gama Yowab ya rinjayi mutane.
\v 17 Suka ɗauki Absalom suka jefa shi cikin babban rami a cikin kurmin; suka bizne jikinsa cikin ƙarƙashin babban tarin duwatsu, sa'an nan dukkan Isra'ila suka gudu, kowanne mutum zuwa nasa gida.
\s5
\v 18 Yanzu kuwa, lokacin da Absalom ya ke da rai, ya gina wa kansa babban ginshiƙin dutse cikin kwarin sarki, gama ya ce, "Bani da ɗan da zai ɗauki suna na wanda za a tuna da ni." Ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kiran sunansa Surar Absalom har wa yau.
\s5
\v 19 Sa'an nan Ahimãz, ɗan Zadok ya ce, "Bari in gudu yanzu in kai wa sarki labari mai daɗi, yadda Yahweh ya kuɓutar da shi daga hannun abokan gabarsa."
\v 20 Yowab ya amsa masa, "Ba kai ne za ka zama mai ɗaukar labari yau ba; amma wata rana za ka kai. Yau ba za ka kai kowanne labari ba gama ɗan sarki ya mutu."
\s5
\v 21 Sai Yowab ya cewa Ba-kushi, "Jeka ka faɗa wa sarki abin da ka gani. Sai Ba-kushi ya sunkuyar da kansa gaban Yowab, sai ya ruga.
\v 22 Daga nan sai Ahimãz ɗan Zadok ya sake cewa Yowab, ba tare da la'akari da komai zai faru ba, ina roƙon ka ka bar ni in ruga in bi Ba-kushen."Yowab ya amsa, donme kake so ka ruga, ɗana? Ganin ba za ka sami wa ta ladar kai labarin ba?"
\v 23 Kome ya faru, in ji Ahimãz, "Zan ruga" Yowab ya amsa ya ce masa, "Ruga." Sa'an nan Ahimãz ya ruga ta hanyar fili, ya tsere wa Ba-kushen.
\s5
\v 24 Dauda kuwa yana zaune tsakanin ƙofofi biyu na ciki da na waje. Mai tsaro kuma ya hau benen ƙofa har zuwa cikin rufin garu ya tãda idanunsa. Da ya duba, sai ga wani ya sheƙo a guje shi kaɗai.
\v 25 Sai mai tsaron ya tada murya ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, "Idan shi kaɗai ne, akwai labari a bakinsa." Mai gudun ya zo kurkusa kuma dab da birnin.
\s5
\v 26 Sai mai tsaron ya lura da wani mutum kuma yana gudu, sai mai tsaron ya kira mai kula da ƙofa; ya ce, "Duba, ga wani mutum kuma yana gudu shi kaɗai," Sai sarki ya ce, "Shi ma yana kawo labari."
\v 27 Sai mai tsaron ya ce, "A ganina irin gudun na gaban nan ya yi kama da gudun Ahimãz ɗan Zadok." Sarki ya ce, "Shi nagarin mutum ne, yana zuwa da labari mai daɗi."
\s5
\v 28 Daga nan sai Ahimãz ya yi kira ya cewa sarki, "Komai lafiya lau ne" kuma ya sunkuyar da kansa da fuskarsa gaban sarki har ƙasa ya ce, "Mai albarka ne Yahweh Allahnka! Ya ba da mutanen da su miƙar da hannayensu gãba da shugabana sarki."
\v 29 Sai Sarki ya amsa, "Ko saurayin nan Absalom yana lafiya?" Ahimãz ya amsa ya ce, lokacin da Yowab ya aike ni, bawan sarki, wurinka, ya sarki, na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba."
\v 30 Sai sarki ya ce, "Juya gefe ka tsaya nan." Sai Ahimãz ya juya ya tsaya cik.
\s5
\v 31 Nan da nan Ba-kushen ya zo ya ce, "Akwai albishir mai daɗi domin shugabana sarki, gama Yahweh ya ɗaukar maka fansa yau daga dukkan waɗanda suka tayar maka."
\v 32 Daga nan sai sarki ya cewa Ba-kushen, ko lafiya dai da saurayin nan Absalom?" Ba-kushen ya amsa, maƙiyan shugabana sarki, da dukkan waɗanda suka tayar maka domin su cutar da kai, "Su zama kamar yadda saurayin nan ya ke."
\v 33 Daga nan sarki ya yi juyayi mai zurfi, ya tafi ya hau kan ƙofar bene ya yi kuka. Yayin da ya ke baƙinciki yana tafe yana cewa "ɗana Absalom, ya ɗana, Absalom! Da ma ni ne na mutu a madadinka, Absalom, ɗana, ɗana!"
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Aka faɗa wa Yowab cewa, "Duba, sarki yana kuka yana makoki domin Absalom."
\v 2 Wato nasara ta ranar nan ta koma makoki ga dukkan jama'a, gama jama'a sun ji cewa a ran nan sarki yana makoki saboda ɗansa."
\s5
\v 3 Ya zama lallai ga sojoji su saɗaɗa shiru cikin birni a wannan ranar, kamar mutane masu jin kunya su kan sace jiki sa'ad da suka gudu daga yaƙi.
\v 4 Sarki ya rufe fuskarsa ya yi kuka da babbar murya, "Ya ɗana Absalom, Absalom, ya ɗana, ya ɗana!"
\s5
\v 5 Yowab ya shigo cikin gida wurin sarki ya ce masa, "Yau ka kunyatar da fuskokin dukkan sojoji, waɗanda suka ceci ranka yau, da rayukan 'ya'yanka maza da mata, da rayukan matanka, da rayukan matanka bayi,
\v 6 saboda kafi ƙaunar waɗanda suke ƙinka, kuma kana ƙin masoyanka. Gama yau ka nuna cewa Hafsoshi da sojoji ba komai bane a gare ka. Yau na gaskanta da Absalom ya rayu, dukkan mu kuma da mun mutu, wannan da ya faranta maka rai.
\s5
\v 7 Yanzu fa sai ka tashi ka fita kayi magana mai daɗi ga sojojinka, gama na rantse da Yahweh, idan baka tafi ba, babu wanda zai zauna tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni cikin dukkan bala'o'in da suka faru da kai daga ƙuruciyarka zuwa yau."
\v 8 Sa'an nan sarki ya tashi ya zauna a ƙofar birni, aka faɗa wa dukkan jama'a, cewa, "Duba fa, ga sarki can yana zaune a cikin ƙofa." Daga nan sai dukkan mutane suka zo gaban sarki. Isra'ila kuma suka gudu, kowanne mutum ya tafi gidansa.
\s5
\v 9 Dukkan mutane kuma suna ta muhawara da juna cikin dukkan kabilun Isra'ila suna cewa, "Sarki ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya kuma cece mu daga hannun Filistiyawa yanzu kuma ya gudu daga ƙasar saboda Absalom.
\v 10 Absalom kuma wanda muka sarautar da shi bisa kanmu, ya mutu cikin yaƙi, Yanzu fa donme bama cewa komai game da dawo da sarki?"
\s5
\v 11 Sarki Dauda ya aika wurin Zadok da Abiyata firist cewa, 'Kuyi magana da dattawan Yahuda cewa, donme kune na ƙarshe wajen dawo da sarki fãdarsa, da shi ke sarki ya sami tagomashi daga dukkan Isra'ila, a dawo dashi fãdarsa?
\v 12 Ku 'yan'uwana ne, ƙashina ne da namana. Donme ku ne na ƙarshen dawo da sarki?'
\s5
\v 13 Ku cewa Amasa, 'Kai ba ƙashina bane da kuma namana? Allah ya yi mani haka, ya kuma ƙara mani, idan ba ka zama shugaban runduna ta ba daga yanzu zuwa nan gaba a madadin Yowab.'"
\v 14 Kuma ya rinjayo da zukatan dukkan mutanen Yahuda kamar zuciyar mutum guda, sai suka aika wa sarki cewa, "Ka dawo, kai da dukkan mutanenka."
\v 15 Sai sarki ya dawo, ya zo Yodan. Mutanen Yahuda kuma suka zo Gilgal don su tarbi sarki, daga nan suka kawo sarki ƙetaren Yodan.
\s5
\v 16 Shimei ɗan Gera, Benyamine, wanda ya zo daga Bahurim, ya hanzarta ya sauko tare da mutanen Yahuda domin taryar sarki Dauda.
\v 17 Akwai mutanen Benyamin dubu goma tare da shi, da Ziba bawan Saul, da kuma 'ya'yansa goma sha biyar da barorinsa ashirin tare da shi.
\v 18 Suka haye taYodan a gaban sarki. Suka haye domin su kawo iyalin sarki domin ya yi abin da ya yi masa kyau. Shimei kuma ɗan Gera ya sunkuya a gaban sarki tun kafin ya fara haye Yodan.
\s5
\v 19 Sai Shimei ya cewa sarki, "Kada, shugabana, ya same ni da laifi ko ya tuna da taurin kan da bawanka ya yi a ranar da shugabana sarki ya bar Yerusalem. In ka yarda, kada sarki ya ajiye wannan a zuciyarsa.
\v 20 Gama bawanka ya sani na yi zunubi. Duba, shi yasa na zo yau a matsayin na fari daga cikin dukkan iyalin Yosef na zo domin in taryi shugabana sarki."
\s5
\v 21 Amma Abishai ɗan Zeruya ya amsa ya ce, "Ba za a kashe Shimei ba saboda wannan, saboda ya la'anta shafaffe na Yahweh?"
\v 22 Daga nan sai Dauda ya ce, "Me zanyi da ku, ku 'ya'yan Zeruya, da yau za ku zama maƙiyana? Za a kashe wani mutum yau a cikin Isra'ila? Gama bana sani cewa yau ni ne sarki bisa Isra'ila ba?"
\v 23 Sarki kuwa ya cewa Shimei, "Ba za ka mutu ba" Sai sarki ya yi masa alƙawari tare da rantsuwa.
\s5
\v 24 Daga nan sai Mefiboshet ɗan Saul ya zo domin ya tarbi sarki. Bai kuwa gyara ƙafafunsa ba, ko ya aske gemunsa, ko ya wanke tufafinsa tun daga lokacin da sarki ya tashi har ranar daya dawo cikin salama.
\v 25 Ya zama kuwa sa'ad da ya zoYerusalem domin ya tarbi sarki, sarki ya ce masa, "Donme ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?
\s5
\v 26 Sai ya amsa, "Ya shugabana sarki, bawana ya ruɗe ni, gama Na ce, bari in yi ma jakina sirdi, domin in hau in tafi tare da sarki, gama bawanka gurgu ne.'
\v 27 Bawana Ziba yaci zarafina, bawanka, a wurin shugabana sarki. Amma shugabana sarki kamar mala'ikan Allah ya ke. Don haka, sai ka yi duk abin da kaga ya gamshe ka.
\v 28 Gama duk iyalin gidan mahaifina sun zama matattun mutane gaban shugabana sarki, amma ka sanya bawanka a cikin masu ci a teburinka. Wanne 'yanci nake dashi kuma da zan ƙara yiwa sarki kuka?"
\s5
\v 29 Daga nan sarki ya ce masa, "Donme ka ƙara wani abu kuma? Na yanke shawarar cewa kai da Ziba za ku raba gonakin."
\v 30 Sai Mefiboshet ya amsa wa sarki, "I, bari ya ɗauka duka, da shi ke shugabana sarki ya dawo gidansa lafiya."
\s5
\v 31 Daga nan sai Barzillai Bagiliye ya zo daga Rogelim ya haye Yodan tare da sarki, domin ya raka shi hayin Yodan.
\v 32 Yanzu dai Barzillai ya tsufa ƙwarai, shekarunsa tamanin. Ya tanadarwa sarki abin zaman gari lokacin da ya ke zaune a Mahanayim, gama shi mai arzaki ne.
\v 33 Sarki ya ce da Barzillai, "Sai ka haye tare da ni, ni kuwa zan tanada maka ka zauna tare da ni a Yerusalem."
\s5
\v 34 Barzillai ya amsa wa sarki, "Sauran kwanaki nawa suka rage cikin shekarun rayuwata, da zan haura tare da sarki zuwa Yerusalem?
\v 35 Shekaruna tamanin. Zan iya banbance tsakanin abu mai kyau da mugu? Ko bawanka zai iya ɗanɗana abin da nake ci ko abin da nake sha? Yanzu zan iya jin kowacce muryar mawaƙa maza da waƙar mata? Donme bawanka za ya zama nawaya ga shugabana sarki?
\v 36 Bawanka yana so ya haye Yodan kaɗai tare da sarki. Donme sarki zai saka mani da irin wannan ladar?
\s5
\v 37 Ina roƙonka ka bar bawanka ya koma gida, domin in mutu cikin birnina a kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ka duba, ga bawanka Kimham. Bari ya haye tare da shugabana sarki, kayi masa abin da ya yi maka kyau."
\s5
\v 38 Sarki ya amsa ya ce, "Kimham zai haye tare da ni, kuma zan yi masa abin da kake so, iyakar abin da kake nema kuma a gare ni, zan yi maka."
\v 39 Daga nan sai dukkan mutane suka haye Yodan, sarki ma ya haye, sai sarki ya sumbaci Barzillai ya kuma albarkace shi. Daga nan sai Barzillai ya koma gidansa.
\s5
\v 40 Sai sarki ya haye zuwa Gilgal, Kimham kuma ya haye tare da shi. Dukkan jama'ar Yahuda kuma suka ƙetarar da sarki, da rabin jama'ar Isra'ila kuma.
\v 41 Nan da nan sai dukkan mutanen Isra'ila suka fara zuwa wurin sarki suka ce da sarki, "Donme 'yan'uwanmu, mutanen Yahuda, suka sace ka suka kawo sarki da iyalinsa hayin Yodan, da dukkan mazajen Dauda tare da shi?"
\s5
\v 42 Sai mutanen Yahuda suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, domin sarki danginmu ne na kusa. donme kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abin da ya zama lallai sarki dole ya biya? Ko ya ba mu wasu kyaututtuka?"
\v 43 Sai mutanen Isra'ila suka amsa wa mutanen Yahuda, "Mu na da kabilai goma da suke dangantaka da sarki, 'yancin da muke dashi wurin Dauda yafi naku. Donme ku ka rena mu? Ba shawarar mu aka fara ji ba ta dawo da sarkinmu?" Amma kalmomin mutanen Yahuda sun fi kalmomin mutanen Isra'ila zafi.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Ya kasance kuma a wannan wurin akwai wani mai tada hankali sunansa Sheba ɗan Bikri, Benyamine. Sai ya busa ƙaho ya ce, "Ba mu da rabo cikin Dauda ba mu kuwa da gãdo cikin ɗan Yesse, bari kowanne mutum ya koma gidansa, Isra'ila,"
\v 2 Sai dukkan mutanen Isra'ila suka yashe da Dauda suka bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka bi sarkinsu kurkusa, daga Yodan har zuwa Yerusalem.
\s5
\v 3 Lokacin da Dauda yazo fãdarsa a Yerusalem, sai ya ɗauki matan nan goma bayi waɗanda ya bari su kula da fãda, ya sa su cikin gida yasa a kula da su, ya biya buƙatunsu, amma bai ƙara kwana da su ba. An kulle su har ranar mutuwarsu, suna zama kamar gwamraye.
\s5
\v 4 Daga nan sai sarki ya ce da Amasa, ka kira mazajen Yahuda tare cikin kwana uku; dole kai ma ka kasance, a nan,
\v 5 Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuda tare, amma ya jinkirta ya wuce lokacin da sarki ya sanya dominsa.
\s5
\v 6 Sai Dauda ya ce da Abishai, "Yanzu Sheba ɗan Bikri za ya yi mana ɓarnar da ta fi wadda Absalom ya yi. Ka ɗauki bayin shugabanka, sojojina, ka bi bayansu, in ba haka ba zai iya samun birane masu ganuwa ya ɓace mana da gani."
\v 7 Sai mutanen Yowab suka bi bayansa, da su da Keretawa da su da Feletawa, da dukkan jarumawa. Suka fita Yerusalem suka bi Sheba ɗan Bikri.
\s5
\v 8 Yayin da suke a babban dutsen da ke a Gibeyon, Amasa ya zo ya tarbe su, Yowab kuwa yana saye da tufafinsa na yaƙi, wanda ya haɗa da ɗammara kewaye da ƙugunsa da takobin yaƙi ɗaure da shi. Ya yin da ya ci gaba da tafiya sai takobin ya faɗi.
\s5
\v 9 Sai Yowab ya ce da Amasa, "Lafiya kake, ɗan'uwana?" Yowab ya kama Amasa wajen gemunsa da hannunsa na dama don ya yi masa sumba.
\v 10 Amasa bai kula da takobin da ke cikin hannun Yowab na hagu ba. Yowab ya daɓa wa Amasa a ciki 'yan hanjinsa suka faɗi a ƙasa. Yowab bai sake bugunsa ba, Amasa kuwa ya mutu. Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi Sheba ɗan Bikri.
\s5
\v 11 Sai ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya wajen Amasa, mutumin ya ce, "Wanda ya ke wajen Yowab da wanda ke wajen Dauda, bari ya bi Yowab."
\v 12 Amasa ya kwanta yana ta birgima cikin jini a cikin tsakiyar hanya. Yayin da mutumin yaga dukkan jama'a sun tsaya cik, sai ya ɗauki Amasa ya kawar dashi daga kan hanya zuwa cikin saura. Ya jefa mayafi a kansa saboda ya ga duk wanda ya zo sai ya tsaya a kansa.
\v 13 Bayan da aka kawar da Amasa a kan hanya, dukkan mutane suka bi bayan Yowab, wajen bin Sheba ɗan Bikri.
\s5
\v 14 Sheba ya ratsa dukkan kabilun Isra'ila zuwa Abel ta Bet Maka, da zuwa dukkan kasar Beriyawa, waɗanda suka tattaru domin bin Sheba.
\v 15 Suka kama shi suka kafa masa sansani cikin Abel ta Bet Maka. Suka tãra tulin tudun ƙasa gãba da birnin da ganuwar. Dukkan jama'ar da ke tare da Yowab suka bubbuge ganuwar suka rushe ta.
\v 16 Sa'an nan wata mace mai hikima tayi kuka daga cikin birni ta ce, "Ku ji, ina roƙon ku kuji, Yowab, ka matso kusa da ni domin in yi magana da kai."
\s5
\v 17 Sai Yowab ya je kusa da ita, sai matar ta ce, kai ne Yowab?" Sai ya amsa ya ce, "Ni ne," Sa'an nan ta ce masa, ka saurari kalmomin baiwarka," Ya amsa ya ce, Ina ji."
\v 18 Sai ta ce, kwanakin dã an saba cewa, 'Lallai sai ka nemi shawara a Abel.' Wannan shawarar kuwa takan kawo ƙarshen al'amarin.
\v 19 Mu ne ɗaya daga cikin birni da ke da salama da aminci a cikin Isra'ila. Ka na ƙoƙarin ka hallaka birni wanda ya ke uwa a cikin Isra'ila. Donme za ka haɗiye gãdon Yahweh?"
\s5
\v 20 Sai Yowab ya amsa ya ce, "Hakika ba zai faru ba, bari ya zama nesa daga gare ni, da zan haɗiye ko in hallakar.
\v 21 Wannan ba gaskiya ba ne. Amma wani mutum daga duwatsun ƙasar Ifraim sunan sa Sheba ɗan Bikri, ya ɗaga hannunsa sama gãba da sarki, gãba da Dauda. Shi kaɗai za a bayar ni kuwa zan janye daga birnin." Sai matar ta cewa Yowab, "Za a jefa maka kansa ta bisa ganuwa."
\v 22 Daga nan sai matar taje wurin dukkan jama'a cikin hikimarta. Suka yanke kan Sheba ɗan Bikri, suka jefa shi waje wurin Yowab. Daga nan sai ya busa ƙaho mutanen Yowab suka bar birnin, kowa ya koma gidansa. Sai Yowab ya komaYerusalem wurin sarki.
\s5
\v 23 Yanzu fa Yowab yana kan rundunar yaƙi ta Isra'ila, Benaiya kuma ɗan Yehoyida yana bisa kan Keretawa da Feletawa.
\v 24 Adoram yana bisa mutane masu yin aikin dole, Yehoshafat kuma ɗan Ahilud shi ne magatakarda.
\v 25 Sheba kuma marubuci da Zadok da Abiyata su ne Firistoci.
\v 26 Ira Bajairi kuma babban mai yin hidima ga Dauda
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 A cikin zamanin Dauda aka yi yunwa shekara uku akai akai, Dauda kuwa ya nemi fuskar Yahweh. Sai Yahweh ya ce, "Wannan yunwar tana kan ka ne saboda Saul da iyalinsa masu kisa, saboda ya kashe Gibiyonawa."
\s5
\v 2 Yanzu fa Gibiyonawa ba daga jama'ar Isra'ila bane, amma daga wajen sauran Amoriyawa ne. Mutanen Isra'ila sun rantse masu ba za su kashe su ba, amma saul ya yi ƙoƙari ya kashe su dukka a cikin himmarsa domin mutanen Isra'ila da Yahuda.
\v 3 Sai Dauda ya kira mutanen Gibiyonawa ya ce masu, "Me zan yi domin ku? Ta yaya zan yi kaffara, domin ku albarkaci mutanen Yahweh, waɗanda suka gãji alherinsa da alƙawarai?"
\s5
\v 4 Gibiyonawa suka ce masa, ba zancen azurfa ko zinariya tsakanin mu da Saul ko iyalinsa. Kuma ba domin mu za a kashe kowanne mutum a cikin Isra'ila ba." Dauda ya amsa, "Duk abin da za ku roƙa, shi ne abin da zan yi maku."
\s5
\v 5 Sai suka amsa wa sarki suka ce, mutumin da ya yi ƙoƙarin ya kashe mu dukka, wanda ya ƙulla mana makirci, wanda da yanzu an hallaka mu, mu rasa wuri a tsakanin iyakar Isra'ila.
\v 6 Bari a bamu mutum bakwai daga cikin zuriyarsa, mu kuwa za mu rataye su ga Yahweh cikin Gibiya ta Saul, zaɓaɓɓe na Yahweh." Sai sarki ya ce, "Zan ba ku su."
\s5
\v 7 Amma sarki ya keɓe Mefiboshet ɗan Yonatan ɗan Saul, saboda rantsuwar Yahweh da ke tsakanin su, tsakanin Dauda da Yonatan ɗan Saul.
\v 8 Amma sarki ya ɗauki 'ya'ya biyu na Rizfa ɗiyar Ayiya, 'ya'yan da ta haifawa Saul, sunayen 'ya'ya biyun data haifa su ne, Armoni da Mefiboshet; Dauda kuma ya ɗauki 'ya'ya biyar na Mirab ɗiyar Saul, waɗanda ta haifawa Adriyel ɗan Barzillai Meholatiye.
\v 9 Ya miƙa su cikin hannun Gibiyonawa. Suka rataye su a kan dutse, gaban Yahweh. Dukkan su bakwai ɗin suka mutu tare. Sun mutu a lokacin girbi, kwanakin farko ne a farkon kakar bali.
\s5
\v 10 Daga nan sai Rizfa ɗiyar Ayiya ta ɗauki tsummoki ta shimfiɗa wa kanta su a bisa dutsen, gefen gawarwakin, daga farkon kãka har lokacin da ruwan sama ya sauko a kansu. Bata bari tsuntsayen sararin sama su dame su da rana ba, ko namomin jeji da dare.
\v 11 Aka faɗa wa Dauda abin da Rizfa ɗiyar Ayiya, baiwar matar Saul, ta yi.
\s5
\v 12 Sai Dauda ya tafi ya ɗauki ƙasusuwan Saul da ƙasusuwan Yonatan ɗansa daga hannun mutanen Yabesh Giliyad, waɗanda suka sace a wurin filin Bet - Shan, inda Filistiyawa suka rataye su, bayan da Filistiyawa suka kashe Saul a Gilbowa.
\v 13 Dauda ya kawar da ƙasusuwan Saul da ƙasusuwan Yonatan ɗansa, suka kuma tattara ƙasusuwan mutane bakwai waɗanda aka rataye su kuma.
\s5
\v 14 Suka bizne ƙasusuwan Saul da Yonatan ɗansa cikin ƙasar Benyamin cikin Zela cikin kabarin Kish mahaifinsa. Suka aikata dukkan abin da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya amsa addu'o'insu domin ƙasar.
\s5
\v 15 Daga nan sai Filistiyawa suka je su sake yin yaƙi da Isra'ilawa. Sai Dauda ya sauka da shi da mutanensa su yi yaƙi da Filistiyawa. Amma gajiyar yaƙi ta sa Dauda ya yi suwu.
\v 16 Ishbi-Benob na zuriyar ƙattin nan wanda nauyin mashinsa ya yi nauyin shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma ɗauke da sabuwar takobi, ya yi nufin ya kashe Dauda.
\v 17 Amma Abishai ɗan Zeruya ya ceci Dauda, ya bugi Bafilisten nan, ya kashe shi. Daga nan mazajen Dauda suka rantse masa, cewa, "Ba zaka ƙara tafiya yaƙi tare da mu ba, domin kada ka ɓice fitilar Isra'ila."
\s5
\v 18 Bayan wannan kuwa aka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gob, lokacin da Sibbekai Bahushati ya kashe Saf, wanda ke ɗaya daga cikin zuriyar Refayim.
\v 19 Ya zama kuma aka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Yayir mutumin Betlehem ya kashe Goliyat Bagittiye, wanda mãshin sa yana kama da dirkar masaƙa.
\s5
\v 20 Ya zama kuma aka sake yin yaƙi a Gat inda akwai wani mutum mai tsayin gaske a kowanne hannunsa yana da yatsu shida a kowacce ƙafa kuma yana da yatsu shida, dukka ashirin da huɗu kenan. Shi ma har yanzu daga zuriyar Refayim ne.
\v 21 Sa'ad da ya zazzagi Isra'ila, Yonatan ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dauda, ya kashe shi.
\v 22 Waɗannan su ne zuriyar Refahayim na Gat an kashe su ta hannun Dauda da kuma ta hannun sojojinsa.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Dauda ya yi amfani da waɗannan kalmomi ya raira waƙa ga Yahweh a ranar da ya cece shi daga hannun dukkan abokan gabarsa, da kuma hannun Saul.
\v 2 "Ya yi addu'a ya ce, Yahweh shi ne dutsena, da kagarata, shi wanda ya cece ni.
\s5
\v 3 Allah shi ne dutse na. A cikinsa na sami mafaka, garkuwata da ƙahon cetona, hasumiyata mai tsawo, mafakata kuma, shi ne wanda ya cece ni daga tashin hankali.
\v 4 Zan kira bisa Yahweh, wanda ya isa a yabe shi, kuma zan tsira daga hannun maƙiyana.
\s5
\v 5 Gama ambaliyun mutuwa sun kewaye ni, haukan ruwayen hallakarwa sun tsoratadda ni.
\v 6 Igiyoyin lahira sun kewaye ni; tarkunan mutuwa sun kama ni.
\s5
\v 7 A cikin ƙuncina na kira Yahweh; Na kira Allahna; daga cikin haikalinsa ya ji muryata, kira na na neman taimako ya kai cikin kunnuwansa.
\s5
\v 8 Sa'an nan ƙasa ta girgiza ta yi makyarkyata. Tussan sammai suka girgiza aka motsa su, saboda Allah ya yi fushi.
\v 9 Hayaƙi ya fito daga hancinsa, wuta mai cinyewa ta fito daga bakinsa. Ta kunna gawayi ta wurinsa.
\s5
\v 10 Ya buɗe sammai ya sauko ƙasa, duhu baƙiƙƙirin yana ƙarƙashin sawayensa.
\v 11 Ya hau bisa Kerub, ya tashi. A bisa fukafukan iska aka ganshi.
\v 12 Ya kuma maida duhu rumfa kewaye da shi, manyan hadura na tattaruwa cikin sararin sammai.
\s5
\v 13 Daga sheƙin hasken gabansa gawayin wuta suka faɗo.
\v 14 Yahweh ya yi tsawa daga sammai. Maɗaukaki ya tada muryarsa.
\v 15 Ya harba kibawunsa, ya tarwatsa maƙiyansa - curirrikan walƙiya kuma sun tarwatsa su.
\s5
\v 16 Sa'an nan hanyoyin ruwa suka bayyana; harsasun duniya suka tonu a kukan tsautawar Yahweh, da jin hucin numfashi daga hancinsa.
\s5
\v 17 Daga bisa ya kai ƙasa; Ya riƙe ni! Daga cikin ruwaye masu yawa ya jawo ni.
\v 18 Ya cece ni daga wurin maƙiyina mai ƙarfi, daga hannun waɗanda suka ƙi ni, gama sun fi karfina.
\s5
\v 19 Suka afko mani a ranar masifata, amma Yahweh shi ne abin dogarata.
\v 20 Ya kuma kawo ni waje a buɗaɗɗen wuri. Ya cece ni saboda yana murna da ni.
\v 21 Yahweh ya sãka mani bisa ga ma'aunin adalcina; ya sãke gyara ni bisa ga tsabtar hannuwana.
\s5
\v 22 Gama na kiyaye hanyoyin Yahweh ban kuma juya wa Allah baya ba ta wurin aikata mugunta.
\v 23 Gama dukkan shari'unsa na adalci suna gabana; game da zancen farillansa kuma, ban rabu da su ba.
\s5
\v 24 Marar laifi nake a gabansa, na kuma kiyaye kaina daga zunubi.
\v 25 Domin wannan Yahweh ya sabunta ni ya sãka mani bisa ga adalcina, bisa ga matsayin tsabtata a idonsa.
\s5
\v 26 Ga mai aminci, ka nuna kanka mai aminci ne; ga mutumin da ya ke marar laifi, zaka nuna kanka marar laifi.
\v 27 Ga mai tsabta, ka zama da tsabta, amma ga fãsiki ka zama a murɗe.
\s5
\v 28 Ka ceci rauna nan mutane, amma idanun ka na gãba da masu girmankai, kuma ka kawo su ƙasa.
\v 29 Gama kai ne fitilata, Yahweh. Yahweh ya haskaka duhuna.
\s5
\v 30 Gama ta wurinka zan iya zarce taron yaƙi; ta wurin Allahna nake tsallake ganuwa.
\v 31 Domin Allah, hanyarsa cikakkiya ce. Shi garkuwa ne ga dukkan waɗanda suka nemi mafaka a cikin sa.
\s5
\v 32 Gama wane ne Allah sai Yahweh? Wane ne dutse kuma sai Allahnmu?
\v 33 Allah shi ne mafakata, yana kuma bida mutum marar laifi cikin hanyarsa.
\s5
\v 34 Yana maida ƙafafuna suyi sauri kamar na naman jeji, ya kuma sanya ni a bisa dogayen tuddai.
\v 35 Yana koyar da hannuwana domin yaƙi, damtsuna kuma su tausa baka na jan ƙarfe.
\s5
\v 36 Ka kuma bani garkuwar cetonka, tagomashinka ya maishe ni mai girma.
\v 37 Ka sanya wuri mai faɗi ƙarƙashin sawayena, santsi bai kwashe ƙafafuna ba.
\s5
\v 38 Na fafari maƙiyana na kuma hallaka su. Ban juya ba har sai da suka hallaka.
\v 39 Na cinye su na ragargaza su; ba za su tashi ba. Sun fãɗi ƙarƙashin sawayena.
\s5
\v 40 Ka sanya ƙarfi a jikina kamar ɗammara domin yaƙi; waɗanda suka tayar mani ka sanya su ƙarƙashina.
\v 41 Ka bani bayan maƙiyana' da wuyansu; Na datse wuyan waɗanda suka ƙi ni.
\s5
\v 42 Sun yi kuka domin neman taimako, amma ba wanda ya cece su; sun yi kuka ga Yahweh, amma bai amsa masu ba.
\v 43 Na buge su da kyau na niƙesu kamar turɓaya a ƙasa, na tattake su kamar laka na watsar da su cikin tituna.
\s5
\v 44 Ka kuma ƙwatoni daga husumar mutanena. Ka kiyayeni a matsayin shugaban al'ummai. Mutanen da ban sani ba sun yi mani hidima.
\v 45 Baƙi sun russuna mani dole. Da jin labarina, sun yi mani biyayya.
\v 46 Baƙi sun fito daga wurin ɓuyarsu suna rawar jiki.
\s5
\v 47 Yahweh mai rai ne! Bari a yabi dutsena. Bari Allah ya ɗaukaka, dutsen cetona.
\v 48 Wannan shi ne Allah wanda ke tabbatar da sakayya domina, shi wanda ke ƙasƙantar da al'ummai ƙarƙashina.
\v 49 Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiyana. Tabbas, ka ɗaukaka ni bisa kan waɗanda suka tayar mani. Ka kuɓutar da ni daga masu son cutar da ni.
\s5
\v 50 Domin wannan Zan yi godiya gare ka, Yahweh, a tsakanin al'ummai; Zan raira waƙoƙin yabbai ga sunanka.
\v 51 Allah ya bayar da babban ceto ga sarkinsa, yana nuna alƙawarin biyayya ga shafaffe na sa, ga Dauda da zuriyarsa har abada."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Yanzu fa waɗannan su ne ƙarshen zantattukan Dauda - Dauda ɗan Yesse, mutumin da aka girmama ƙwarai, shi wanda ya ke shafaffe daga Allahn Yakubu, mawaƙi mai daɗi na Isra'ila.
\v 2 "Ruhun Yahweh ya yi magana da ni, maganarsa kuma tana kan harshena.
\s5
\v 3 Allah na Isra'ila ya faɗi, Dutsen Isra'ila ya ce mani, 'Shi wanda ya ke mulkin mutane cikin adalci, mai yin mulki cikin tsoron Allah.
\v 4 Zai zama kamar hasken safiya sa'ad da rana take fitowa, safiyar da babu giza-gizai, sa'ad da ɗanyar ciyawa take tsirowa daga ƙasa ta wurin hasken rana bayan saukowar ruwan sama.
\s5
\v 5 Hakika ba haka iyalina suke a gaban Allah ba? Ko bai yi madawwamin alƙawari da ni, shimfiɗaɗɗe bisa ga ƙa'ida ya tabbatar ta kowacce hanya ba? Ko bai ƙara cetona ba kuma ya biya kowanne muradina ba?
\s5
\v 6 Amma marasa amfani za su zama kamar ƙayayuwa da za a zubar, gama ba za su tattaru da hannu ɗaya ba.
\v 7 Mutumin daya taɓa su dole ya yi amfani da makamin ƙarfe ko mashi mai tsini. Dole a ƙone su sarai a wurin da suka kwanta."
\s5
\v 8 Waɗannan su ne sunayen shahararrun sojojin Dauda: Yeshbal mutumin Hakmoniya shugabane na sojoji masu ƙarfi. Ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci ɗaya.
\s5
\v 9 Bayansa kuma sai Eliyazar ɗan Dodai Ba'ahotiye, ɗaya daga cikin jarumawa uku na Dauda. Yana nan lokacin da suka rena Filistiyawa da suka tattaru tare don suyi yaƙi, lokacin da mutanen Isra'ila sun rigaya sun bar wurin.
\v 10 Eliyaza ya tashi tsaye ya bugi Filistiyawa har hannunsa ya gaji hannunsa kuma ya liƙe wa takobinsa. Yahweh ya kawo babbar nasara a wannan ranar. Jama'a suka koma bayan Eliyaza, domin kawai su tuɓe jikuna.
\s5
\v 11 Bayansa kuma sai Shamma ɗan Agee, Harariye. Filistiyawa suka taru a filin dagar yaƙi, mutane kuwa suka gudu daga gabansu.
\v 12 Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar yankin ƙasar ya kuma kareta. Ya kashe Filistiyawa, Yahweh ya kawo babbar nasara.
\s5
\v 13 Uku daga cikin su talatin sojojin suka gangaro zuwa wurin Dauda a lokacin girbi, zuwa kogon Adullam. Rundunar Filistiyawa sunyi sansani cikin kwarin Refim.
\v 14 A lokacin nan Dauda yana cikin kagararsa, a kogo, yayin da Filistiyawa kuma suka kafu a Betlehem.
\s5
\v 15 Dauda ya ji ƙịṣḥi ya ce, "Ina ma wani zai bani ruwa daga rijiyar da ke a Betlehem, rijiyar da ke kusa da ƙofa!"
\v 16 Sai jarumawannan uku suka fasa rundunar Filistiyawa suka ɗebo ruwa daga rijiyar da ke Betlehem, wadda ke kusa da ƙofa. Suka ɗauki ruwan suka kawowa Dauda, amma yaƙi sha, Maimakon haka sai ya zuba wa Yahweh.
\v 17 Daga nan sai ya ce, "Bari wannan ya yi nesa da ni, Yahweh, har da zan sha wannan. Zan sha jinin mutanen da suka sadaukar da rayukansu?" Domin wannan bai yarda ya sha ba, Waɗannan su ne al'amuran da jarumawan nan uku suka yi.
\s5
\v 18 Abishai ɗan'uwan Yowab, ɗan Zeruya, shi ne babba cikin su uku. Ya taɓa yin yaƙi da mashinsa ya kuwa kashe mutum ɗari uku. An sha ambatonsa tare da sojojin nan guda uku.
\v 19 Ba shi ya fi ukun suna ba? An sanya shi shugabansu. Duk da haka, sunansa ba a kwatanta shi da darajar sauran sojoji ukun.
\s5
\v 20 Benaiya daga Kabzeyel shi ɗa ne wurin Yahoiyada; shi mutum ne mai ƙarfi wanda ya yi manyan abubuwa na kasada. Ya kashe 'ya'ya biyu na Ariyel na Mowab. Ya kuma shiga cikin rami ya kashe zaki a lokacin dusar ƙanƙara.
\v 21 Kuma ya kashe wani Bamasare mutum mai daraja. Bamasaren yana da mashi a hannunsa, amma Benaiya ya yi yaƙi dashi da sanda kawai, ya fizge mashin a hannun Bamasaren sa'an nan ya kashe shi da mashinsa.
\s5
\v 22 Benaiya ɗan Yehoiyada ya yi waɗannan ayyukan kasada, an lissafa sunansa cikin sunayen jarumawannan uku.
\v 23 An mutumta shi fiye da sauran sojojin nan talatin gaba ɗaya. Amma bai kai sauran sojojin nan uku masu ƙarfi ba. Duk da haka Dauda ya sa shi a bisa matsaransa.
\s5
\v 24 Mutum talatin ɗin sun haɗa da: Asahel ɗan'uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,
\v 25 Shamma Baharodiye, Elika Baharodiye,
\v 26 Helez Bafaltiye, Ira ɗan Ikkesh Batekoyi,
\v 27 Abiyeza Ba'anatote, Mebunnai Bahushatiye,
\v 28 Zalmon Ba'ahohite, Maharai Banetofatiye;
\s5
\v 29 Heleb ɗan Bãna, Banetofatiye, Ittai ɗan Ribai daga Gibiya ta Benyamin,
\v 30 Benaiya Bafiratoniye, Hiddai na wajen kwarin Gãsh.
\v 31 Abi albon Ba'arbatiye, Azmabet Babarhumi,
\v 32 Eliyaba Bashãlboniye 'ya'yan Yashen, Yonatan ɗan Shamma Baharariye;
\s5
\v 33 Ahiyam ɗan Sharar Ba'arariye,
\v 34 Elifelet ɗan Ahasbai Ma'akatiye, Eliyam ɗan Ahitofel Bagilone,
\v 35 Hezro Bakarmile, Fãrai Ba'abite,
\v 36 Igal ɗan Natan daga Zoba, Bani daga kabilar Gad.
\s5
\v 37 Zelek Ammoniye, Naharai Baberote masu ɗaukarwa Yowab kayan yaƙi ɗan Zeruya,
\v 38 Ira Ba'i tire, Gareb Ba'itire,
\v 39 Yuriya Bahittiye dukkan su talatin da bakwai
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Fushin Yahweh ya sake ƙuna akan Isra'ila, ya kuma iza Dauda akansu ya ce, "Jeka ka ƙidaya Isra'ila da Yahuda."
\v 2 Sarki ya ce da Yowab shugaban runduna, wanda ya ke tare dashi, "Ka tafi cikin dukkan kabilun Isra'ila, daga Dan zuwa Biyasheba, ka ƙirga dukkan mutane, domin in san jimillar dukkan mutane da suka cancanta domin yaƙi."
\s5
\v 3 Yowab ya cewa sarki, "Bari Yahweh Allahnka ya riɓanɓanya mutane sau ɗari, kuma bari idanun sarki shugabana ya ga faruwar haka. Amma donme shugabana sarki ya ke son wannan?"
\v 4 Duk da haka maganar sarki ta zama ita ce ta ƙarshe akan ta Yowab da sauran shugabannin rundunar yaƙi. Sai Yowab da sarakunan rundunar yaƙi suka fita daga gaban sarki domin su ƙirga yawan mutanen Isra'ila.
\s5
\v 5 Suka haye Yodan suka sauka kusa da Arowa, hannun dama ga birnin da ke cikin kwari. Daga nan suka yi tafiya zuwa Gad har zuwa Yazer.
\v 6 Suka zo Giliyad da kuma ƙasar Tahtim Hodshi, daga nan sai Dan yăn da kewayen wajen Sidon.
\v 7 Suka zo kagarar Taya da dukkan biranen Hibiyawa dana Kan'aniyawa. Daga nan suka fita zuwa Negeb cikin Yahuda a Biyasheba.
\s5
\v 8 Ya yin da suka je dukkan ƙasar, sai suka dawo Yerusalem a ƙarshen watan tara da kwana ashirin.
\v 9 Yowab ya bada rahoton jimillar yawan mayaƙa ga sarki. Akwai mutum 800,000 a cikin Isra'ila jarumawa masu zarar takobi, mazajen Yahuda kuma su 500,000 ne.
\s5
\v 10 Daga nan sai zuciyar Dauda ta soke shi bayan ya lissafta mutanen. Sai ya ce da Yahweh, "Na yi babban zunubi ta wurin yin wannan. Yanzu fa, Yahweh, ka ɗauke laifin bawanka, gama na aikata wauta ƙwarai."
\s5
\v 11 Sa'ad da Dauda ya tashi da safe, sai maganar Yahweh ta zo wurin annabi Gad, mai duba, na Dauda cewa,
\v 12 "ka je kace da Dauda: 'Wanan shi ne abin da Yahweh ya ce: "'Ina miƙa maka abu uku, sai ka zaɓi ɗaya cikinsu.""
\s5
\v 13 Sai Gad ya je wurin Dauda ya ce masa, "Ko shekaru uku na yunwa su zo maka cikin ƙasarka, ko kuwa zaka yi ta gudu wata uku daga abokan gabarka suna bin ka? ko kuwa za ayi annoba kwana uku a cikin ƙasarka? Yanzu sai kayi shawarar amsar da zan maida wa shi wanda ya aiko ni."
\v 14 Sai Dauda ya cewa Gad, "I na cikin babbar damuwa." Bari mu faɗa cikin hannun Yahweh da mu faɗa cikin hannun mutum, gama ayyukan jinƙansa da girma suke."
\s5
\v 15 Sai Yahweh ya aika da annoba kan Isra'ila daga safe zuwa lokacin da aka sanya, mutane dubu saba'in suka mutu daga Dan zuwa Biyasheba.
\v 16 Lokacin da mala'ika ya miƙa hannunsa wajen Yerusalem domin ya hallakata, Yahweh ya canza tunaninsa game da ɓarnar, ya ce da mala'ikan da ke hallakar da mutanen, "Ya isa! Sai ka janye hannunka yanzu." A wancan lokacin mala'ikan Yahweh yana tsaye a masussukar Arauna Bayebushe.
\s5
\v 17 Dauda ya yi magana da Yahweh da ya ga mala'ikan da ya bugi mutanen, ya ce, "Na yi zunubi, kuma na yi aikin shiririta. Amma tumakin nan me suka yi? Ina roƙon ka bari hannunka ya hukunta ni da iyalin mahaifina!"
\s5
\v 18 Ran nan sai Gad ya zo wurin Dauda ya ce masa, "Ka hau ka gina bagade ga Yahweh a masussukar Arauna Bayebushe."
\v 19 Dauda kuwa ya hau kamar yadda Gad ya faɗa masa ya yi, kamar yadda Yahweh ya umarta.
\v 20 Arauna ya duba ya ga sarki da bayinsa suna isowa. Sai Arauna ya fito ya sunkuyar da kansa ga sarki da fuskarsa a ƙasa.
\s5
\v 21 Daga nan sai Arauna ya ce, "Donme shugabana sarki ya zo wurina, bawansa?" Dauda ya amsa, "Domin in sa yi masussukarka, domin in gina bagadi ga Yahweh, domin a iya kawar da annoba cikin mutane."
\v 22 Arauna ya cewa Dauda, "Ka ɗauke ta kamar ta ka, ya shugabana sarki. Ka yi dukka abin da ka ga dama. Duba, ga shanu domin hadaya ta ƙonawa da kayan masussuka da karkiyoyin shanu domin itace.
\v 23 Dukkan waɗannan, sarkina, Ni, Arauna, zan ba ka." Sai ya ce da sarki, "Bari Yahweh Allahnka ya karɓe ka."
\s5
\v 24 Sai sarki ya cewa Arauna, "A'a, lallai sai dai mu yi ciniki in saye ta. Ba zan miƙa hadayar ƙonawa ga Yahweh ta kowanne abin da ban biya ba." Dauda ya sayi masussukar da shanun akan awo hamsin na azurfa.
\v 25 Dauda ya gina wa Yahweh bagadi a wurin ya miƙa ƙonannun hadayu, da hadayun zumunta. Da haka suka roƙi Yahweh a madadin ƙasar, ya kuma sa annobar ta tsaya a ko'ina cikin Isra'ila.