ha_ulb/09-1SA.usfm

1703 lines
127 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

This file contains Unicode characters that might be confused with other characters. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id 1SA
\ide UTF-8
\h Littafin Sama'ila Na Farko
\toc1 Littafin Sama'ila Na Farko
\toc2 Littafin Sama'ila Na Farko
\toc3 1sa
\mt Littafin Sama'ila Na Farko
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Akwai wani mutumin Ramatayim ta Zufiyawa, ta ƙasar tudu na Ifraim; Sunansa Elkana ɗan Yeroham ɗan Elihu ɗan Tohu ɗan Zuf, Ifraimiye.
\v 2 Yana da mata biyu; Sunan ta farkon Hannatu, sunan ta biyun kuma Fenina. Fenina na da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta da ko ɗaya.
\s5
\v 3 Wannan mutum yakan fita daga birninsa shekara bayan shekara domin ya yi sujada ya kuma yi hadaya ga Yahweh mai runduna a Shilo. 'Ya'yan Eli maza guda biyu, Hofni da Finehas, firistocin Yahweh, suna wurin.
\v 4 Idan ranar ta zo wadda Elkana ke yin hadaya ko wace shekara, koyaushe yakan ba Fenina matarsa kason nama mai yawa, da dukkan 'ya'yan ta maza da mata.
\s5
\v 5 Amma ga Hannatu a koyaushe yakan ba ta kaso ruɓi biyu, gama yana ƙaunarta, koda ya ke Yahweh ya rufe mahaifarta.
\v 6 Kishiyarta kuma na tsokanar ta ƙwarai da gaske domin ta tunzura ta, saboda Yahweh ya rufe mahaifarta.
\s5
\v 7 Domin haka shekara bayan shekara, idan ta tafi gidan Yahweh tare da iyalinta, kishiyarta a koyaushe tana tsokanar ta. Saboda haka takan yi kuka ta ƙi cin komai.
\v 8 Elkana mijinta a koyaushe sai ya ce mata, "Hannatu, me yasa ki ke kuka? Me yasa ba za ki ci komai ba? Me yasa zuciyarki ta ɓaci? Ban fi 'ya'ya maza goma ba a gareki?"
\s5
\v 9 A ɗaya daga cikin irin wannan tattaruwar, sai Hannatu ta tashi bayan da suka gama ci da sha a Shilo. Yanzu dai Eli firist yana zaune a bisa mazauninsa a ƙofar hanyar zuwa shiga Haikalin Yahweh.
\v 10 Tana cikin ɓacin rai mai zurfi; ta yi addu'a ga Yahweh ta kuma yi kuka mai ɗaci.
\s5
\v 11 Sai ta yi wa'adi ta ce, "Yahweh mai runduna, idan za ka dubi azabar baiwarka ka kuma tuna da ni, ba za ka kuma manta da baiwarka ba, amma za ka ba baiwarka ɗa namiji, daga nan zan ba da shi ga Yahweh dukkan kwanakin ransa, ba bu kuma wata aska da za ta taɓa kansa ko kaɗan."
\s5
\v 12 Yayin da ta ci gaba da addu'a a gaban Yahweh, Sai Eli ya lura da bakinta.
\v 13 Hannatu ta yi magana a zuciyarta. Leɓunanta na motsawa, amma ba a jin muryarta. Sai Eli ya yi tunanin ta bugu ne.
\v 14 Eli ya ce mata, "Har yaushe za ki zama cikin buguwa? ki kawar da ruwan inabinki."
\s5
\v 15 Hannatu ta amsa, "A a, shugabana, ni mace ce mai ruhu cike da baƙinciki. Ban sha ruwan inabi ba ko abin sha mai ƙarfi, amma ina kwarara rai na ne a gaban Yahweh.
\v 16 Kada ka ɗauki baiwar ka a matsayin mace marar kunya; Ina magana ne daga cikin yalwar damuwata da tsokanata."
\s5
\v 17 Daga nan Eli ya amsa ya ce, "Tafi cikin salama; bari Allah na Isra'ila ya ba ki abin nan da ki ka roƙe shi."
\v 18 Ta ce, "Bari baiwarka ta sami tagomashi a gaban ka." Daga nan matar ta yi tafiyarta ta kuma ci abinci; fuskarta kuma ba ta sake nuna baƙinciki ba.
\s5
\v 19 Suka tashi da sassafe suka kuma yi sujada a gaban Yahweh, daga nan kuma suka sake komawa gidansu a Rama. Elkana ya kwana da Hannatu matarsa, Yahweh kuma ya tuna da ita.
\v 20 Da lokacin ya zo, Hannatu ta ɗauki ciki ta haifi ɗa namiji. Ta kira sunansa Sama'ila, tana cewa, "Saboda na roƙo shi daga Yahweh."
\s5
\v 21 Sa'an nan kuma, Elkana da dukkan gidansa suka tafi domin su miƙa wa Yahweh hadaya ta shekara - shekara ya kuma biya wa'adinsa.
\v 22 Amma Hannatu ba ta tafi ba; ta riga ta faɗa wa mijinta, "Ba zan tafi ba sai an yaye yaron; daga nan zan kawo shi, domin ya kasance gaban Yahweh ya kuma zauna wurin har abada."
\v 23 Elkana mijinta ya ce da ita, "Ki yi abin da ya yi dai-dai a gare ki. Ki jira sai kin yaye shi; Yahweh ya tabbatar da maganarsa, kaɗai." Sai matar ta jira ta kuma yi renon ɗanta har sai da ta yaye shi.
\s5
\v 24 Da ta yaye shi, sai ta ɗauke shi tare da ita, tare da sã ɗan shekara uku, da gari mudu ɗaya, da kwalbar ruwan inabi ɗaya, ta kawo shi kuma gidan Yahweh a Shilo. To har yanzu dai yaron ƙarami ne.
\v 25 Suka yanka sãn, suka kuma kawo yaron wurin Eli.
\s5
\v 26 Ta ce, "Ya, shugabana! muddin ka na raye, shugabana, ni ce matar nan da ta tsaya kusa da kai tana addu'a ga Yahweh.
\v 27 Domin wannan yaron na yi addu'a kuma Yahweh ya ba ni abin da na roƙa daga gare shi.
\v 28 Na bayar da shi ga Yahweh, dukkan tsawon ransa an ba da shi rance ga Yahweh." Daga nan ya yi sujada ga Yahweh a wurin.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Hannatu ta yi addu'a ta ce, "Zuciyata ta ɗaukaka Yahweh. Ƙahona ya ɗaukaka cikin Yahweh. Bakina ya yi kuri mai yawa akan maƙiyana, saboda na yi farinciki cikin cetonka.
\s5
\v 2 Babu wani mai tsarki kamar Yahweh, Gama babu wani baya gare ka; babu wani dutse kamar Allahnmu.
\s5
\v 3 Kada a ƙara kuri cikin matuƙar girman kai; kada wata gadara ta fito daga bakinku. Gama Yahweh Allah ne masani; shi ne ke gwada ayyuka.
\v 4 Bakan mutane masu ƙarfi ya karye, amma waɗanda suka yi tuntuɓe suka sanya ƙarfi kamar ɗamara.
\s5
\v 5 Waɗanda suke a cike sun bayar da kansu haya domin gurasa; waɗanda suke jin yunwa sun daina jin yunwa. Bakarariya mata haifi bakwai, amma mace mai 'ya'ya da yawa ta yi yaushi.
\s5
\v 6 Yahweh na kashewa kuma ya rayar. Yana korawa ƙasa zuwa lahira yana kuma ɗagawa sama.
\v 7 Yahweh yana maida wasu mutane talakawa wasu kuma masu arziki. Yana ƙasƙantarwa yana kuma ɗaukakawa sama.
\s5
\v 8 Yana ɗaga talaka daga turɓaya. Yana ɗaukaka mabuƙaci daga tarin toka ya sa ya zauna tare da sarakuna ya kuma sa ya gaji wurin zama mai daraja. Gama ginshiƙan duniya na Yahweh ne ya kuma ɗora duniyar a bisan su.
\s5
\v 9 Yana bida sawayen amintattun mutanensa, amma za a rufe bakin mai mugunta cikin duhu, gama babu mai yin nasara ta ƙarfi.
\s5
\v 10 Waɗanda ke tsayayya da Yahweh zasu karye gutsu-gutsu; zaya yi cida daga sama a kansu. Yahweh za ya hukunta ƙarshen duniya; zaya bada ƙarfi ga sarkinsa ya kuma ɗaukaka ƙahon shafaffensa."
\s5
\v 11 Daga nan Elkana ya tafi Rama, zuwa gidansa. Yaron ya bauta wa Yahweh a gaban Eli firist.
\s5
\v 12 Yanzu dai 'ya'yan Eli mutane ne marasa cancanta. Ba su san Yahweh ba.
\v 13 Al'adar firistoci da mutanen shi ne idan kowanne mutum ya miƙa hadaya, bawan firist za ya zo da cokali mai yatsu uku a hannunsa, yayin da naman ke tafasa.
\v 14 Za ya caka cokalin a cikin kaskon, ko garwar, ko tanderun, ko tukunyar. Duk abin da cokalin ya tsamo sama firist za ya ɗaukar wa kansa. Haka suka riƙa yi a Shilo ga dukkan Isra'ilawa da suka zo wurin.
\s5
\v 15 Mafi ɓaci, kafin su ƙona kitsen, bawan firist za ya zo, ya kuma cewa mutumin da ke yin hadayar, "Bayar da naman gashi domin firist; domin ba za ya karɓi dafaffen nama ba daga gare ka, sai ɗanye kaɗai."
\v 16 Idan mutumin ya ce masa, "Dole ne su ƙona kitsen da farko, daga nan sai ka ɗauki iya yadda kake so." Daga nan sai ya ce, "A a, yanzu zaka ba ni; idan ba haka ba, zan ɗauka da ƙarfi da yaji."
\v 17 Zunubin waɗannan yara maza ya yi girma sosai a gaban Yahweh, gama sun wulaƙanta baikon Yahweh.
\s5
\v 18 Amma Sama'ila ya bauta wa Yahweh a matsayin yaro yana sanye da falmarar linin.
\v 19 Mahaifiyarsa takan yi masa ƙaramar riga ta kuma kai masa daga shekara zuwa shekara, idan ta zo tare da mijinta domin miƙa hadaya ta shekara-shekara.
\s5
\v 20 Eli za ya albarkaci Elkana da matarsa ya ce, "Bari Yahweh ya ba ka ƙarin 'ya'ya ta wurin wannan matar saboda roƙon da ta yi ga Yahweh." Daga nan sai su koma nasu gidan.
\v 21 Yahweh ya sake taimakon Hannatu, ta kuma sake ɗaukar ciki. Ta haifi 'ya'ya maza uku mata biyu. Yayin da ake haka, yaron kuwa Sama'ila ya yi girma gaban Yahweh.
\s5
\v 22 Yanzu dai Eli ya tsufa; ya ji kuma dukkan abin da 'ya'yansa maza ke yi ga dukkan Isra'ila, da yadda suke kwana da dukkan matayen da ke bauta a ƙofar shiga rumfar taruwa.
\v 23 ya ce masu, "Me yasa kuke yin irin abubuwan nan? gama na ji ayyukan muguntarku daga dukkan mutanen nan."
\v 24 A'a, 'ya'ya na; Ba rahoto bane mai kyau da na ji. Ku na sa mutanen Yahweh rashin biyayya.
\s5
\v 25 Idan mutum ɗaya ya yi zunubai gãba da wani, Allah za ya hukunta shi; amma idan mutum ya yi zunubai gãba da Yahweh, wane ne za ya yi magana a madadinsa?" Amma ba zasu saurari muryar mahaifinsu ba, saboda Yahweh ya shirya kashe su.
\v 26 Yaron kuwa Sama'ila ya girma, ya ƙaru a tagomashi tare da Yahweh tare kuma da mutane.
\s5
\v 27 Yanzu dai wani mutumin Allah ya zo wurin Eli ya ce ma shi, "Yahweh ya ce, 'Ban bayyana kai na ba ga gidan kakanka, sa'ad da suke a Masar cikin ƙangin gidan Fir'auna?
\v 28 Na zaɓe shi daga cikin dukkan kabilun Isra'ila ya zama firist ɗi na, ya hau zuwa bagadi na, ya kuma ƙona turare, ya sanya falmara a gabana. Na bayar ga gidan kakanka dukkan baye-bayen mutanen Isra'ila da aka yi tare da wuta.
\s5
\v 29 Me yasa, daga nan, ka yi ba'a ga hadayu na da baye-bayen da na buƙata a wurin da nake zama? Me yasa ka girmama 'ya'yanka fiye da ni ta wurin mai da kanka mai ƙiba tare da kowanne baikon mutane na Isra'ila?'
\v 30 Gama Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ce, 'Na yi alƙawarin cewa gidanka, da gidan kakanka, zasu yi tafiya a gabana har abada.' Amma yanzu Yahweh ya ce, 'Ya yi nesa da ni in yi haka, gama zan girmama waɗanda ke girmama ni, amma waɗanda suka rena ni zasu sha ƙasƙanci.
\s5
\v 31 Duba, kwanaki na zuwa da zan datse ƙarfinka da ƙarfin gidan mahaifinka, yadda ba za a sake samun tsohon mutum ba a cikin gidanka.
\v 32 Za ka ga ƙunci a cikin wurin da nake zama. Koda ya ke abu mai kyau za a ba Isra'ila, ba za a sake samun tsohon mutum ba a gidanka.
\v 33 Kowanne daga cikinku da ban datse ba daga bagadina, Zan kawo faɗawa ga idanunku, Zan kawo baƙinciki ga rayukanku. Dukkan mazajen da aka haifa a iyalinku zasu mutu.
\s5
\v 34 Wannan zai zamar maka alama da zata zo bisa 'ya'yanka maza biyu, bisa Hofni da Finehas: Dukkan su zasu mutu a rana ɗaya.
\v 35 Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai yi abin da ke cikin zuciyata da cikin raina. Zan gina masa tabbataccen gida; kuma za ya yi tafiya a gaban shafaffen sarkina har abada.
\s5
\v 36 Duk wanda aka bari daga cikin gidanka zaya zo ya rusuna masa, yana roƙon ɓallin azurfa da gutsuren gurasa, kuma za ya ce, "Ina roƙon ka ka naɗa ni ɗaya daga cikin guraben firistoci domin in samu in ci gutsuren gurasa.""'
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Yaron nan Sama'ila ya bauta wa Yahweh a gaban Eli. Maganar Yahweh ta yi ƙaranci a waɗannan kwanaki; babu yawan wahayin anabci.
\v 2 A wannan lokaci, sa'ad da Eli, wanda idanunsa sun fara yin dishi-dishi yadda ba ya iya gani sosai, yana kwance a bisa nasa gadon.
\v 3 Fitilar Allah bata riga ta mutu ba, kuma Sama'ila yana kwance domin ya yi barci a haikalin Yahweh, inda akwatin Yahweh ya ke.
\v 4 Yahweh ya yi kira ga Sama'ila, wanda ya ce, "Ga ni nan."
\s5
\v 5 Sama'ila ya ruga wurin Eli ya kuma ce, "Ga ni nan, gama ka kira ni." Eli ya ce, "Ban kira ka ba, ka sake kwantawa." Sai Sama'ila ya koma ya sake kwantawa.
\v 6 Yahweh ya sake kira, "Samai'la." Sama'ila ya sake tashi ya tafi wurin Eli ya kuma ce, "Gani nan, gama ka kira ni." Eli ya amsa, "Ban kira ka ba, ɗana, ka sake kwantawa."
\s5
\v 7 Yanzu dai Sama'ila bai taɓa samun wata gamuwa da Yahweh ba, ko wani saƙo daga Yahweh ya taɓa bayyana a gare shi ba.
\v 8 Yahweh ya sake kiran Sama'ila karo na uku. Sama'ila ya sake ta shi ya tafi wurin Eli ya ce, "Ga ni nan, gama ka kira ni." Daga nan Eli ya fahimci cewa Yahweh ya kira yaron.
\s5
\v 9 Daga nan Eli ya cewa Sama'ila, "Ka je ka sake kwantawa kuma, idan ya sake kiran ka, dole ka ce, 'Yi magana, Yahweh, gama bawanka yana saurare."' Daga nan Sama'ila ya tafi kuma ya sake kwantawa a na sa wurin kuma.
\s5
\v 10 Yahweh ya zo ya tsaya; ya yi kira kamar sauran lokuttan, "Sama'ila, Sama'ila." Daga nan Sama'ila ya ce, "Yi magana, gama bawanka yana sauraro."
\v 11 Yahweh ya cewa Sama'ila, duba, Ina gaf da yin wani abu a Isra'ila wanda kunnuwan dukkan wanda za ya ji za su karkaɗa.
\s5
\v 12 A wannan rana zan aiwatar ga Eli dukkan abin da na ce game da gidansa, daga farko har ƙarshe.
\v 13 Na gaya masa ina gaf da hukunta gidansa karo ɗaya tak domin zunubin da ya riga ya sani, saboda 'ya'yansa sun kawo la'ana a kansu bai kuma hana su ba.
\v 14 Saboda wannan na yi rantsuwa game da gidan Eli cewa zunuban gidansa ba za a iya yi masu kaffara ba da hadaya ko baiko."
\s5
\v 15 Sama'ila ya kwanta har gari ya waye; daga nan ya buɗe ƙofofin gidan Yahweh. Amma Sama'ila ya ji tsoron gaya wa Eli game da wahayin.
\v 16 Daga nan Eli ya kira Sama'ila ya ce, "Sama'ila, ɗana." Sama'ila ya ce, "Ga ni nan."
\s5
\v 17 ya ce, "Wacce magana ce ya faɗi maka? Ina roƙon ka kada ka ɓoye mani. Bari Allah ya yi maka haka, fiye da haka ma, idan ka ɓoye wani abu daga gare ni a dukkan maganganun da ya faɗi maka."
\v 18 Sama'ila ya faɗi masa dukkan abu; bai ɓoye masa komai ba. Eli ya ce, "Yahweh ne. Bari ya yi abin da ya yi kyau a gare shi."
\s5
\v 19 Sama'ila ya yi girma, kuma Yahweh na tare dashi kuma bai bar ko ɗaya daga cikin maganganun anabcinsa ba su kãsa zama gaskiya.
\v 20 Dukkan Isra'ila daga Dan zuwa Biyasheba suka sani cewa an naɗa Sama'ila annabin Yahweh.
\v 21 Yahweh ya sake bayyana a Shilo, gama ya bayyana kansa ga Sama'ila a Shilo ta wurin maganarsa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Maganar Sama'ila ta zo ga dukkan Isra'ila. Yanzu dai Isra'ila sun fita yaƙi gãba da Filistiyawa. Suka kafa sansani a Ebeneza, Filistiyawa kuma sukakafa sansani a Afek.
\v 2 Filistiyawa suka jera domin yaƙi gãba da Isra'ila. Da aka baza yaƙin, Filistiyawa sukakayar da Isra'ila, wanda sukakashe wajen mutum dubu huɗu a filin yaƙin.
\s5
\v 3 Da mutanen suka zo cikin sansanin, dattawan Isra'ila suka ce, "Me yasa Yahweh yakayar damu yau a gaban Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alƙawarin Yahweh a nan daga Shilo, domin yakasance a nan tare da mu, domin ya ajiye mu a tsare daga hannun maƙiyanmu."
\v 4 Sai mutanen suka aiki mazaje zuwa Shilo; daga nan suka ɗauko akwatin alƙawarin Yahweh mai runduna, wanda ke zaune a bisa kerubim. 'Ya'yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas, suna nan tare da akwatin alƙawarin Allah.
\s5
\v 5 Da akwatin alƙawarin Yahweh ya iso cikin sansani, dukkan mutanen Isra'ila suka yi babbar kururuwa, har ƙasa ta amsa.
\v 6 Da Filistiyawa suka ji ƙarar kururuwar, suka ce, "Me wannan ƙarar kururuwar a cikin sansani Ibraniyawa ke nufi?" Sai suka tantance cewa akwatin Yahweh ya zo cikin sansanin.
\s5
\v 7 Filistiyawa suka tsorata; suka ce, "Wani allah ya shigo cikin sansanin." Suka ce, "Kaitonmu! Babu wani abu kamar haka da ya faru a dã!
\v 8 Kaitonmu! Wane ne zai cece mu daga ƙarfin waɗannan alloli masu iko? Waɗannan allolin ne sukakaiwa Masarawa hari da allobai iri-iri a cikin jeji.
\v 9 Ku yi ƙarfin hali, ku kuma zama mazaje, ku Filistiyawa, ko kuwa ku zama bayi ga Ibraniyawa, kamar yadda suke bayi a gare ku. Ku zama mazaje, ku kuma yi faɗa."
\s5
\v 10 Filistiyawa suka yi faɗa, aka kumakayar da Isra'ila. Kowanne mutum ya tsere zuwa gidansa, kisan da aka yi babba ne ƙwarai; gama sojojin ƙasa dubu talatin ne daga Isra'ila suka faɗi.
\v 11 Aka ɗauke akwatin Allah, 'ya'yan Eli maza biyu kuma, Hofni da Finehas, suka mutu.
\s5
\v 12 Wani mutumin Benyamin ya gudu daga fagen yaƙin ya kuma zo Shilo a ranar nan, ya iso da tufafinsa a yage da kuma ƙasa bisakansa.
\v 13 Da ya iso, Eli na zaune bisa mazauninsa a bakin hanya yanakallo saboda zuciyarsa na fargaba tare da damuwa domin akwatin Allah. Da mutumin ya shiga cikin birnin ya faɗi labarin, dukkan birnin aka yi kuka.
\s5
\v 14 Da Eli ya ji ƙarar kukan, ya ce, "Mene ne ma'anar wannan yamitsin?" Mutumin ya zo da sauri ya kuma faɗa wa Eli.
\v 15 Yanzu dai Eli shekarunsa tasa'in da takwas; idanunsa ba su fuskanta dai-dai, kuma baya gani.
\s5
\v 16 Mutumin ya cewa Eli, "Ni ne na zo daga fagen yaƙin. Na gudo daga yaƙin yau." Eli ya ce, "Ya abin ya tafi, ɗa na?"
\v 17 Mutumin da yakawo labarin ya amsa kuma ya ce, "Isra'ila sun gudu daga Filistiyawa. Haka kuma, babbar kayarwa takasance a tsakanin mutanen. Haka kuma, 'ya'yan ka maza biyu, Hofni da Finehas, sun mutu, akwatin Allah kuma an ɗauke."
\s5
\v 18 Da ya faɗi akwatin Allah, Eli ya fãɗi ta baya daga bisa kujerarsa ta gefen ƙofa. Wuyansa yakarye, ya kuma mutu, saboda ya tsufa kuma yana da nauyi. ya yi alƙalancin Isra'ila shekaru arba'in.
\s5
\v 19 Yanzu dai surukarsa, matar Finehas, tana da ciki kuma ta yi gaf da haihuwa. Da ta ji labarin an cafke akwatin Allah da surukinta da mijinta kuma sun mutu, ta durƙusa kuma ta haihu, amma zafin naƙudarta ya mamaye ta.
\v 20 Wajen lokacin mutuwarta matan da ke yi mata unguwar zoma suka ce mata, "Kada ki ji tsoro, gama kin haifi ɗa namiji." Amma ba ta amsa ba ko ta ɗauki abin da suka ce a zuciya.
\s5
\v 21 Ta raɗa masa suna Ikabod, cewa, "Ɗaukaka ta tafi da ga Isra'ila!" domin an cafke akwatin Allah, saboda kuma surukinta da mijinta.
\v 22 Ta ce, "Ɗaukaka ta tafi daga Isra'ila, saboda an cafke akwatin Allah."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Yanzu dai Filistiyawa sun cafke akwatin Allah, su ka kumakawo shi daga Ebeneza zuwa Asdod.
\v 2 Filistiyawa suka ɗauki akwatin Allah, sukakawo shi cikin gidan Dagon, suka jera shi a gefen Dagon.
\v 3 Da mutanen Asdod suka tashi da sassafe washegari, duba, Dagon ya faɗi ƙasa da fuskarsa ƙasa gaban Yahweh. Sai suka ɗauki Dagon suka kuma sake jera shi a wurinsa.
\s5
\v 4 Amma da suka tashi da sassafe washegari, duba, Dagon ya faɗi ƙasa da fuskarsa ƙasa a gaban akwatin Yahweh. Kan Dagon da hannuwansa suna kwance datsastsu a hanyar ƙofa. Gangar jikin Dagon kawai ya rage.
\v 5 Wannan ne yasa, har yau ma, firistocin Dagon da ko wane ne ya zo cikin gidan Dagon ba ya taka hanyar ƙofar Dagon a Asdod.
\s5
\v 6 Hannun Yahweh kuwa ya yi nauyi a bisa mutanen Asdod. Ya lalatar da su ya azabce su da marurai. Asdod duk da kewayenta.
\v 7 Da mutanen Asdod suka lura da abin da ke faruwa, suka ce, "Akwatin Allahn Isra'ila dole ba za ya zauna ta re da mu ba, saboda hannunsa ya yi tsanani gãba da mu da gãba da allahnmu Dagon."
\s5
\v 8 Sai suka aika suka kuma tattaro tare dukkan shugabannin Filistiyawa; suka ce masu, "Me za mu yi da akwatin Allah na Isra'ila?" Suka amsa, "Bari akawo akwatin Allah na Isra'ila zuwa Gat." Sai suka ɗauki akwatin Allah na Isra'ila zuwa can.
\v 9 Amma bayan da sukakawo shi wurin, hannun Yahweh ya yi gãba da birnin, ya sanya babbar ruɗewa. Ya azabtar da mutanen birnin, ƙarami da babba dukka; marurai kuma suka faso akansu.
\s5
\v 10 Sai suka aika da akwatin Allah zuwa Ekron. Amma nan da nan da akwatin Allah ya zo cikin Ekron, Ekroniyawa suka koka, cewa, "Sun kawo mana akwatin Allah na Isra"ila domin yakashe mu da mutanenmu."
\s5
\v 11 Sai suka aika aka tattaro tare dukkan shugabannin Filistiyawa; suka ce masu, "Ku aika da akwatin Allah na Isra'ila, bari kuma ya koma na sa wurin, domin kada yakashe mu da mutanenmu." Domin akwai razana mai mutuwa cikin dukkan birnin; hannun Allah yana da nauyi sosai a wurin.
\v 12 Mutanen da ba su mutu ba an azabce su da marurai, kukan birnin kuma ya hau zuwa sammai.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Yanzu dai akwatin Yahweh na cikin ƙasar Filistiyawa har watanni bakwai.
\v 2 Daga nan Mutanen Filistiyawa suka kira firistoci da masu sihiri; suka ce masu, "Me zamu yi da akwatin Yahweh? ku gaya mana yadda zamu aika da shi zuwa ƙasarsa."
\s5
\v 3 Firistoci da masu sihiri suka ce, "Idan kuka aika da akwatin Allah na Isra'ila, kada ku aika da shi ba tare da kyauta ba; ta ko ƙaƙa ku aika masa da baiko na laifi. Daga nan zaku warke, daga nan kuma zaku ga ne dalilin da yasa hannunsa bai ɗauke ba daga bisanku har yanzu.
\v 4 Daga nan suka ce, "Mene ne za ya zama baiko na laifin da zamu maida masa?" Suka maida amsa, "Marurai na zinariya biyar da ɓerayen zinariya biyar, biyar lissafin yawa ne wanda ya yi dai-dai da lissafin yawan shugabannin Filistiyawa. Domin annoba iri ɗaya ce ta azabce ku da shugabanninku.
\s5
\v 5 Dole ku yi marurai na kwaikwayo, da ɓerayen kwaikwayo da suka addabi ƙasar, ku kuma bada ɗaukaka ga Allah na Isra'ila. Wataƙila zai ɗauke hannun sa daga gare ku, daga allolinku, daga kuma ƙasarku.
\v 6 Me yasa zaku taurare zukatanku, kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Ta haka Allah na Isra'ila ya tsananta masu da zafi; Ashe Masarawan basu fitar da mutanen ba, suka kuma tafi?
\s5
\v 7 To yanzu, ku shirya amalanke da shanu biyu masu shayarwa waɗanda ba a taɓa ɗaurawakarkiya ba. Ku ɗaura shanun ga amalanken, amma ku ɗauki 'yan maruƙansu daga gare su, ku kai gida.
\v 8 Daga nan ku ɗauki akwatin Yahweh ku sa cikin amalanken. Ku sanya siffofin zinariyar da zaku maida masa a matsayin baiko na laifi cikin wani akwatin a gefensa. Daga nan ku aika da shi kuma bari ya tafi hanyarsa.
\v 9 Daga nan ku kalla; Idan ya yi tafiyarsa bisa hanya zuwa cikin ƙasarsa zuwa Bet Shemesh, to Yahweh ne ya zartar da wannan babban bala'i. Amma idan ba haka ba, daga nan za mu sani cewa ba hannunsa ba ne ya azabtar damu ba; maimakon haka, zamu sani cewa ya faru da mu ne hakakawai."
\s5
\v 10 Mutanen suka yi yadda aka gaya masu; suka ɗauki shanu biyu masu shayarwa; suka ɗaura su ga amalanken, suka tsare 'yan maruƙansu a gida.
\v 11 Suka sanya akwatin Yahweh a cikin amalanken, tare da akwatin da ke ɗauke da ɓerayen zinariyar da sarrafaffun maruransu.
\v 12 Shanun suka tafi a miƙe a hanyar Bet Shemesh. Suka tafi bisa babbar hanya, suna tafiya suna kuka, ba su kumakauce daga hanya ba ko zuwa dama ko zuwa hagu. Shugabannin Filistiyawa suka bi bayansu har zuwakan iyakar Bet Shemesh.
\s5
\v 13 Yanzu dai mutanen Bet Shemesh suna girbin alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga idanunsu suka ga akwatin, suka yi farinciki.
\s5
\v 14 Amalanken ya iso cikin gonar Yoshuwa daga Bet Shemesh ya kuma tsaya a wurin. Wani babban dutse na wurin, suka tsinke itacen amalanken, suka miƙa shanun a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh.
\v 15 Lebiyawa suka sauke akwatin Yahweh da akwatin da ke tare da shi, inda siffofin zinariyar suke, suka ɗora su bisa babban dutsen. Mutanen Bet Shemesh suka miƙa baye-baye na ƙonawa suka kuma yi hadayu a wannan rana ga Yahweh.
\s5
\v 16 Da shugabannin Filistiyawa biyar suka ga haka, suka koma Ekron a ranar.
\s5
\v 17 Waɗannan ne maruran zinariya da Filistiyawa suka maido domin baiko na laifi ga Yahweh: ɗaya domin Asdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Askelon, ɗaya domin Gat, ɗaya domin Ekron.
\v 18 Ɓerayen zinariyar ma lissafinsu ya yi dai-dai da lissafin dukkan biranen Filistiyawa da sukakasance na shugabannin biyar, dukkansu tsararrun birane ne da ƙauyukansu. Babban dutsen, gefen da aka ajiye akwatin Yahweh, ya zama shaida har yau a cikin filin Yoshuwa Betshemiye.
\s5
\v 19 Yahweh yakai hari ga wasu daga cikin mutanen Bet Shemesh saboda sun duba cikin akwatin Yahweh. Yakashe mutum 50,070. Mutanen suka yi makoki, saboda Yahweh ya ba mutanen babban naushi.
\v 20 Mutanen Bet Shemesh suka ce, "Wane ne zaya iya tsayawa gaban Yahweh, wannan Allah mai tsarki? daga gare mu wurin wa akwatin zaya tafi?"
\s5
\v 21 Suka aika manzanni zuwa ga mutanen Kiriyat Yerim, cewa, "Filistiyawa sun maido da akwatin Yahweh; ku zo ku ɗauka ku kuma koma da shi tare da ku."
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Mutanen Kiriyat Yerim suka zo, suka ɗauki akwatin Yahweh, suka kumakawo shi cikin gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa Eliyeza ya ajiye akwatin Yahweh.
\v 2 Daga ranar da akwatin ya zauna a Kiriyat Yerim, lokaci mai tsawo ya wuce, shekaru ashirin. Dukkan mutanen Isra'ila suka yi makoki kuma suka yi marmarin komawa ga Yahweh.
\s5
\v 3 Sama'ila ya cewa gidan Isra'ila gaba ɗaya, "Idan kun dawo ga Yahweh da dukkan zuciyarku, ku cire bãƙin alloli da kuma Ashtoret daga cikinku, ku juyo da zukatanku ga Yahweh, ku kuma yi masa sujada shi kaɗai, daga nan zai kuɓutar daku daga hannun Filistiyawa."
\v 4 Daga nan mutanen Isra'ila suka fitar da Ba'aloli da Ashtoret, suka kuma yi sujada ga Yahweh kaɗai.
\s5
\v 5 Daga nan Sama'ila ya ce, "Ku kawo a tattare dukkan Isra'ila zuwa Mizfa, zan kuma yi addu'a ga Yahweh domin ku."
\v 6 Suka tattaru a Mizfa, suka jawo ruwa suka zuba kuma a gaban Yahweh. Suka yi azumi a ranar suka ce, "Mun yi zunubi ga Yahweh." A can ne Sama'ila ya sasanta saɓanai domin mutanen Isra'ila ya kuma shugabanci mutanen.
\s5
\v 7 Yanzu da Filistiyawa suka ji mutanen Isra'ila sun taru a Mizfa, sai shugabannin Filistiyawa sukakai hari ga Isra'ila. Da mutanen Isra'ila suka ji haka, suka ji tsoron Filistiyawa.
\v 8 Daga nan mutanen Isra'ila suka cewa Sama'ila, "Kadaka daina kira ga Yahweh Allahnmu domin mu, domin ya cece mu daga hannun Filistiyawa."
\s5
\v 9 Sama'ila ya ɗauki ɗan rago mai shan nono ya miƙa shi gaba ɗaya a matsayin baikon ƙonawa ga Yahweh. Daga nan Sama'ila ya yi kuka ga Yahweh domin Isra'ila, Yahweh kuma ya amsa masa.
\s5
\v 10 Yayin da Sama'ila ke miƙa baikon ƙonawar, Filistiyawa suka matso domin su kawo hari ga Isra'ila. Amma Yahweh ya yi kwarankwatsi da babbar ƙara a wannan rana ga Filistiyawa ya kuma watsa su cikin ruɗewa, kuma suka shakaye a gaban Isra'ila.
\v 11 Mutanen Isra'ila suka tafi daga Mizfa, suka kuma runtumi Filistiyawa suka kumakarkashe su har ya zuwa ƙarƙashin Bet Ka.
\s5
\v 12 Daga nan Sama'ila ya ɗauki dutse yakafa tsakanin Mizfa da Shen. Ya raɗa masa suna Ebeneza, cewa, "Har ya zuwa haka Yahweh ya taimake mu."
\s5
\v 13 Saboda haka Filistiyawa suka shakaye ba su kuma iya shigakan iyakar Isra'ila ba. Hannun Yahweh ya yi gãba da Filistiyawa dukkan kwanakin Sama'ila.
\v 14 Garuruwan da Filistiyawa sukakarɓe daga Isra'ila aka maidawa Isra'ila, daga Ekron zuwa Gat; Isra'ila suka maido da lardinsu daga Filistiyawa. Daga nan aka sami salama tsakanin Isra'ila da Amoriyawa.
\s5
\v 15 Sama'ila ya yi alƙalancin Isra'ila dukkan kwanakin ransa.
\v 16 Kowacce shekara yakan tafi ya zagaye zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa. Yana ɗaukar mataki akan saɓanai domin Isra'ila a dukkan waɗannan wurare.
\v 17 Daga nan sai ya koma Rama, saboda gidansa na wurin; haka kuma a anan yana ɗaukar mataki akan saɓanai domin Isra'ila. Ya kuma gina bagadi a wurin ga Yahweh.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa alƙalai bisa Isra'ila.
\v 2 Sunan ɗan farinsa Yowel, sunan kuma ɗansa na biyu Abiya.
\v 3 Su alƙalai ne a Biyasheba. 'Ya'yansa ba su yi tafiya bisa hanyoyinsa ba, amma suka bi bayan ƙazamar riba. Sukakarɓi cin hanci suka danne adalci.
\s5
\v 4 Daga nan dukkan dattawan Isra'ila suka tattaru tare suka kuma zo wurin Sama'ila a Rama.
\v 5 Suka ce masa, "Duba, ka tsufa, kuma 'ya'yanka ba su yi tafiya cikin hanyoyinka ba. Ka naɗa mana sarki ya yi hukunci akan mu kamar sauran al'ummai."
\s5
\v 6 Amma Sama'ila bai ji daɗi ba da suka ce, "Ka bamu sarki ya yi hukuncinmu." Sai Sama'ila ya yi addu'a ga Yahweh.
\v 7 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Ka yi biyayya da muryar mutanen a cikin dukkan abin da suka ce maka; gama bakai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarki a bisansu.
\s5
\v 8 Suna aikatawa yanzu dai-dai yadda suka yi tun daga ranar dana fito da su daga Masar, suka yashe ni, da bautar wasu alloli, haka kumakaima suke yi maka.
\v 9 Yanzu ka saurare su; ammaka gargaɗe su da aniya bari kuma su san yadda sarkin zai yi mulki akansu."
\s5
\v 10 Sai Sama'ila ya faɗi dukkan maganganun Yahweh ga mutanen da ke tambaya domin sarki.
\v 11 Ya ce, "Wannan zai zama al'adar sarkin da zai yi mulki a bisanku. Zai ɗauki 'ya'yanku maza ya naɗa su gakarusansa ya kuma sa su zama mutanen dawakansa, su kuma yi gudu a gaban karusansa.
\v 12 Zai naɗa wakansa ofisoshin bataliyar sojoji dubbai, da ofisoshin bataliyar sojoji hamsin. Zai sa wasu su yi noman gonarsa, wasu suyi girbin amfaninsa, wasu kuma suyi masa makaman yaƙi dakayan karusansa.
\s5
\v 13 Zai kuma ɗauki 'ya'yanku mata su zama masu yi masa turare, da girke-girke, da gashe-gashe.
\v 14 Zai ɗauki gonakinku mafi kyau, da garkunan inabinku, da kuma fadamunku na itatuwan zaitun, ya bayar dasu ga bayinsa.
\v 15 Zai ɗauki kashi goma daga cikin hatsinku da garkarku ya kuma ba ofisoshinsa da bayinsa.
\s5
\v 16 Zai ɗauki bayinku maza da bayinku mata da mafi nagarta na matasanku maza da jakanku; zai sanya su duka su yi masa aiki.
\v 17 Zai ɗauki kashi goma daga cikin garken dabbobinku, kuma za ku zama bayinsa.
\v 18 Daga nan a wannan rana za ku koka game da sarkinku wanda kuka zaɓarwakanku; amma Yahweh ba zai amsa maku ba a ranar."
\s5
\v 19 Amma mutanen suka ƙi sauraron Sama'ila; suka ce, "A a! dole sarki yakasance a bisanmu
\v 20 saboda mu zamakamar dukkan sauran al'ummai, saboda kuma sarkinmu ya hukunta mu ya kuma fita a gabanmu ya kuma yi faɗan yaƙe-yaƙenmu."
\s5
\v 21 Da Sama'ila ya ji dukkan maganganun mutanen sai ya maimaita su a kunnuwan Yahweh.
\v 22 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Ka yi biyayya da muryarsu ka kuma sa wani ya zama sarki domin su." Sai Sama'ila ya cewa mutanen Isra'ila, "Kowanne mutum dole ya tafi nasa birnin."
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Akwai wani mutum a Benyamin, sanannen mutum. Sunansa Kish ɗan Abiyel ɗan Zeror ɗan Bekorat ɗan Afiya, ɗan wani Benyamine.
\v 2 Yana da wani ɗa mai suna Saul, kyakkyawan saurayi. Babu wani taliki a cikin mutanen Isra'ila wanda ya ke mai asali ne fiye da shi. Dagakafaɗarsa zuwa sama yafi kowanne mutanen tsayi.
\s5
\v 3 Yanzu dai jakan Kish, mahaifin Saul, sun ɓace. Sai Kish ya cewa ɗansa Saul, "Ka ɗauki ɗaya daga cikin bayin tare dakai; ka ta shi ka tafi neman jakan."
\v 4 Sai Saul ya ratsa ta cikin ƙasar tudu ta Ifraim ya kuma tafi ta cikin ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Daga nan suka ratsa ta cikin ƙasar Sha'alim, amma ba su a wurin. Sai ya ratsa ta cikin ƙasar Benyaminawa, amma ba su same su ba.
\s5
\v 5 Da suka zo ƙasar Zuf, sai Saul ya cewa bawansa da ke tare da shi, "Zo, bari mu koma, ko mahaifina na iya daina damuwa domin jakan ya fara damuwa game da mu."
\v 6 Amma bawan ya ce masa, "Saurara, akwai mutumin Allah a cikin wannan birnin. Mutum ne da aka riƙe da daraja; duk abin da ya ce yana zama gaskiya. Mu tafi can; watakila zai iya gaya mana wacce hanya zamu bi a tafiyarmu."
\s5
\v 7 Daga nan Saul ya cewa bawansa, "Amma idan muka je, me za mu kawo wa mutumin? Domin gurasar da ke jakarmu ta ƙare, ba bu kuma wata kyauta da za mu kawo wa mutumin Allahn. Me muke da shi?"
\v 8 Bawan ya amsa wa Saul ya kuma ce, "Nan, akwai tare da ni kwatar shekel na azurfa da zan ba mutumin Allahn, ya gaya mana hanyar da za mu je."
\s5
\v 9 (A dã a Isra'ila, idan mutum ya tafi neman sanin nufin Allah, zai ce, "Zo, bari mu tafi wurin mai gani." Gama annabi a yau mai gani ake kiran sa a dã.)
\v 10 Daga nan Saul ya cewa bawansa, "Faɗar ta yi dai-dai. Zo, bari mu tafi." Sai suka tafi birnin inda mutumin Allah ya ke.
\v 11 Yayin da suka tafi zuwa tudun birnin, sai suka sami 'yan mata na fitowa jan ruwa; Saul da bawansa suka ce masu, "Mai ganin na nan?"
\s5
\v 12 Suka amsa, suka kuma ce, "Yana nan; kalli, yana ɗan gaba da ku. Yi sauri, gama yana zuwa birnin yau, saboda mutanen suna hadaya a yau a wuri mai bisa.
\v 13 Da zarar kun shiga birnin zaku same shi, kafin ya hau zuwa wuri mai bisa domin cin abinci. Mutanen ba zasu ci ba sai ya zo, saboda zai albarkaci hadayar; bayan haka waɗanda aka gayyata zasu ci. yanzu ku haura, gama zaku same shi nan da nan."
\s5
\v 14 Sai suka tafi zuwa birnin. Yayin da suke shiga birnin, suka ga Sama'ila na zuwa ta wurinsu, domin ya tafi zuwa wuri mai bisa.
\s5
\v 15 Yanzu dai ana gobe Saul zai zo, Yahweh ya bayyanawa Sama'ila:
\v 16 "Gobe war haka zan aiko maka wani mutum daga ƙasar Benyamin, zaka kuma naɗa shi ya zama shugaba bisa mutane na Isra'ila. za ya ceci mutanena daga hannun Filistiyawa. Domin na dubi mutanena tare da tausayi saboda kiran su domin taimako ya zo gare ni."
\s5
\v 17 Da Sama'ila ya ga Saul, Yahweh ya ce masa, "Shi ne mutumin da na gaya maka game da shi! shi ne wanda zai yi mulki bisa mutanena."
\v 18 Daga nan Saul ya zo kusa da Sama'ila a ƙofa kuma ya ce, "Ka gaya mani ina ne gidan mai gani?"
\v 19 Sama'ila ya amsa wa Saul ya ce, "Ni ne mai gani. Ka hau a gabana zuwa wuri mai bisa, domin yau zaka ci tare da ni. Da safe zan bar kaka tafi, kuma zan gaya maka kowanne abu da ke cikin ranka.
\s5
\v 20 Game da jakanka da suka ɓace kwana uku da suka wuce, kadaka damu game da su, domin an same su. Daga nan akan wane ne dukkan marmarin Isra'ila yakasance? Ba akanka ba ne da kuma dukkan gidan mahaifinka?"
\v 21 Saul ya amsa ya ce, "Ni ba Benyamine ba ne, daga mafi ƙanƙanta nakabilun Isra'ila? Ba zuriyarmu ce mafi ƙanƙanta ba a cikin dukkan zuriyar Benyamin? To me yasakake magana da ni irin haka.
\s5
\v 22 Sai Sama'ila ya ɗauki Saul da baransa, yakawo su cikin harabar, ya zaunar da su a wuri mafi girma na waɗanda aka gayyata, waɗanda kimanin mutum talatin ne.
\s5
\v 23 Sama'ila ya cewa mai girkin, "Kakawo kason da na baka, wanda na ce maka, 'Ka ajiye shi a gefe."'
\v 24 Sai mai girkin ya ɗauko cinyar da abin da ke bisanta ya kuma sanya a gaban Saul. Daga nan Sama'ila ya ce, "Kalli abin da aka ajiye an sanya a gabanka. Ka ci, saboda an ajiye maka har zuwa zaɓaɓɓen lokaci, daga lokacin da na ce, 'Na gayyaci mutanen."' Sai Saul ya ci tare da Sama'ila a ranar.
\s5
\v 25 Da suka sauko daga wuri mai bisa zuwa cikin birnin, Sama'ila ya yi magana da Saul a bisa saman rufi.
\v 26 Daga nan da gari ya waye, Sama'ila ya yi kira ga Saul a bisa saman rufi ya kuma ce, "Ta shi, domin in aika dakai kan hanyarka." Sai Saul ya tashi, da shi da Sama'ila kuma dukka suka fita bisa titi.
\s5
\v 27 Suna cikin tafiya zuwa waje da birnin, Sama'ila ya cewa Saul, "Ka cewa baran ya tafi gaba da mu" - sai ya tafi gaba - "amma dole ka tsaya a nan na ɗan lokaci, domin in shelar da saƙon Allah a gare ka."
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Sai Sama'ila ya ɗauki kwalbar mai, ya zuba akan Saul, ya kuma sumbace shi. Ya ce, "Ba Yahweh ya shafe ka baka zama shugaba bisa gãdonsa?
\v 2 Idan ka bar ni yau, zaka sami mutum biyu kusa dakabarin Rahila, cikin lardin Benyamin a Zelza. Zasu ce maka, 'Jakan dakake nema an same su. Yanzu mahaifinka ya daina kula wa da jakan yana damuwa game dakai, cewa, "Me zanyi game da ɗa na?"'
\s5
\v 3 Daga nan zaka tafi daga wurin, zaka kuma zo rimin Tabor. Mutane uku masu tafiya wurin Allah a Betel zasu gamu dakai a wurin, ɗaya na ɗauke da 'yan awaki uku, wani kuma na ɗauke da dunƙulen gurasa uku, wani kuma na ɗauke da salkar inabi.
\v 4 Zasu gaishe ka su baka dunƙulen gurasa biyu, wanda zakakarɓa daga hannuwansu.
\s5
\v 5 Bayan wannan, zaka zo tudun Allah, inda sansanin Filistiyawa ya ke. Idan ka isa birnin, zaka iske ƙungiyar annabawa na saukowa daga wuri mai bisa tare da algaita, da tambari, dakakaki, da sarewa, a gabansu; za su riƙayin anabci.
\v 6 Ruhun Yahweh zai abko maka, zaka kuma yi anabci tare da su, zaka kuma sauya zuwa wani mutum daban.
\s5
\v 7 Yanzu, idan waɗannan alamu suka zo maka, ka aiwatar da duk abin da hannunka ya sami damar yi, gama Allah na tare dakai.
\v 8 Ka gangara gaba da ni zuwa Gilgal. Daga nan zan gangaro zuwa gare ka in miƙa baye-baye na ƙonawa in kuma yi hadayar baye-baye na salama. Ka jira kwana bakwai har sai na zo gare ka in kuma nuna maka abin da dole ka yi."
\s5
\v 9 Da Saul ya juya bayansa domin ya bar Sama'ila, Allah ya ba shi wata zuciyar. Daga nan dukkan waɗannan alamu suka faru a ranar.
\v 10 Da suka iso tudun, wata ƙungiyar annabawa ta gamu da shi, Ruhun Allah kuma ya abko bisansa har ya yi anabci tare da su.
\s5
\v 11 Da dukkan waɗanda suka san shi a dã suka ga yana anabci tare da annabawan, mutanen suka ce da junansu, "Mene ne ya faru da ɗan Kish? Saul shi ma ɗaya daga cikin annabawan ne yanzu?"
\v 12 Wani mutum da ya fito daga wuri ɗaya da shi ya amsa, "To wane ne mahaifinsa?" Saboda wannan, ya zama abin faɗi, "Saul shi ma ɗaya ne daga cikin annabawan?"
\v 13 Da ya gama anabcin, ya zo wuri mai bisan.
\s5
\v 14 Daga nan kawun Saul ya ce masa da kuma bawansa, "Ina kuka je?" Ya mai da amsa, "Neman jakan. Da muka ga ba mu iya samo su ba, muka je wurin Sama'ila."
\v 15 Kawun Saul ya ce, "Ina roƙon kaka gaya mani abin da Sama'ila ya ce maka."
\v 16 Saul ya amsa wakawunsa, "Ya gaya mana a sarari cewa an samo jakan." Amma bai gaya masa game da al'amarin masarautar ba, wanda Sama'ila ya yi magana akai.
\s5
\v 17 Yanzu Sama'ila ya kira mutanen tare a gaban Yahweh a Mizfa.
\v 18 Ya cewa mutanen Isra'ila, "Wannan ne abin da Yahweh, Allah na Isra'ila ya faɗa: 'Nakawo Isra'ila daga ƙasar Masar kuma na ƙwato ku daga hannun Masarawa, daga kuma hannun dukkan masarautun da suka tsananta maku.'
\v 19 Amma yau kun watsar da Allahnku, wanda ya cece ku daga dukkan bala'o'inku da ƙuncinku; kuma kun ce da shi, 'Naɗa sarki a bisanmu.' Yanzu ku gabatar dakanku a gaban Yahweh takabilunku da zuriyarku."
\s5
\v 20 Sai Sama'ila yakawo dukkan kabilun Isra'ila kusa, kumakabilar Benyamin aka zaɓa.
\v 21 Daga nan yakawo kabilar Benyamin kusa ta zuriyarsu; kuma zuriyar Matirawa aka zaɓa; kuma Saul ɗan Kish aka zaɓa. Amma da suka tafi neman sa, ba a iya samun sa ba.
\s5
\v 22 Daga nan mutanen suka so su roƙi Allah ƙarin tambayoyi, "Akwai kuma wani mutumin da zai zo?" Yahweh ya amsa, "Ya ɓoye kansa cikin kayayyaki."
\v 23 Daga nan suka ruga suka tsamo Saul daga wurin. Da ya tsaya cikin mutanen, yafi kowanne daga cikin mutanen tsayi, dagakafaɗarsa zuwa sama.
\s5
\v 24 Daga nan Sama'ila ya cewa mutanen, "Kun ga mutumin da Yahweh ya zaɓa?" Babu wani kamar sa daga cikin dukkan mutanen!" Dukkan mutanen suka yi sowa, "Ran sarki ya daɗe!"
\s5
\v 25 Daga nan Sama'ila ya gaya wa mutanen al'adu da dokokin sarautar, ya rubuta su cikin littafi, ya kuma ajiye su gaban Yahweh. Daga nan Sama'ila ya sallami dukkan mutanen, kowanne mutum zuwa nasa gidan.
\s5
\v 26 Saul shi ma ya tafi gidansa a Gibiya, tare da shi kuma wasu ƙarfafan mutane, waɗanda Allah ya taɓa zukatansu.
\v 27 Amma wasu mutane marasa amfani suka ce, "Ta yaya wannan mutum zai cece mu?" Waɗannan mutane suka rena Saul, ba su kumaka wo masa wata kyauta ba. Amma Saul ya yi shiru.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Daga nan Nahash Ba'ammoniye ya tafi yakafa sansani ga Yabesh Giliyad. Dukkan mutanen Yabesh suka cewa Nahash, "Ka yi alƙawari da mu, kuma za mu bauta maka."
\v 2 Nahash Ba'ammoniye ya maida amsa, "Bisa wannan matsayin zan yi alƙawari da ku, cewa zan ƙwaƙule dukkan idanunku na dama, ta wannan hanya kuma in kawo kunya bisa dukkan Isra'ila."
\s5
\v 3 Daga nan dattawan Yabesh Giliyad suka mai da masa amsa, "Ka rabu da mu na kwana bakwai, saboda mu aika da saƙonni ga dukkan lardin Isra'ila. Daga nan, idan ba bu wani da zai cece mu, za mu sadauƙar a gare ka."
\s5
\v 4 Manzannin suka zo Gibiya, inda Saul ke zama, suka kuma gayawa mutanen abin da ya faru. Dukkan mutanen suka yi kuka da ƙarfi.
\v 5 Yanzu dai Saul na biye da shanu daga saura. Saul ya ce, "Me ke damun mutanen da suke kuka?" Suka gaya wa Saul abin da mutanen Yabesh suka ce.
\s5
\v 6 Da Saul ya ji haka, Ruhun Allah ya afko masa, ya kuma fusata sosai.
\v 7 Ya ɗauki shanun huɗa biyu, ya datse su gunduwa-gunduwa, ya kuma aika da su cikin dukkan lardin Isra'ila tare da manzanni. ya ce, "Duk wanda bai fito bayan Saul da bayan Sama'ila ba, haka za a yi wa shanun huɗarsa." Daga nan razanar Yahweh ta faɗo bisa mutanen, suka kuma fito tare a matsayin mutum ɗaya.
\v 8 Da ya tattara su a Berek, mutanen Isra'ila dubu ɗari uku ne, mutanen Yahuda kuma dubu talatin.
\s5
\v 9 Suka ce wa manzannin da suka zo, "Za ku cewa mutanen Yabesh Giliyad, "Gobe, lokacin da rana takai tsaka, za a ceto ku." Sai manzannin suka tafi suka gaya wa mutanen Yabesh, suka kuma yi farinciki.
\v 10 Daga nan mutanen Yabesh suka cewa Nahash, "Gobe za mu sadaukar a gare ka, sai kumaka yi da mu duk abin da ya yi kyau a gare ka."
\s5
\v 11 washegari Saul yasa mutanen ƙungiya uku. Suka zo tsakiyar sansanin a lokacin wayewar gari, suka kumakai hari suka kumakayar da Ammoniyawa har zafin rana. Waɗanda suka tsira su ka watse, har babu mutum biyun su da aka bari tare.
\s5
\v 12 Daga nan mutanen suka ce wa Sama'ila, "Wane ne wanda ya ce, 'Saul zai yi mulki a bisanmu?' akawo mutanen, domin mu kashe su."
\v 13 Amma Saul ya ce, "Babu wanda za akashe dole a wannan ranar, saboda a wannan ranar Yahweh ya ceto Isra'ila."
\s5
\v 14 Daga nan Sama'ila ya cewa mutanen, "Ku zo, bari mu tafi Gilgal mu sabunta sarautar a can."
\v 15 Saboda haka dukkan mutanen suka tafi Gilgal suka kuma maida Saul sarki a gaban Yahweh a Gilgal. A can suka yi hadayar baye-baye don salama a gaban Yahweh, da Saul da dukkan mutanen Isra'ila suka yi farinciki babba.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sama'ila ya cewa dukkan Isra'ila, "Na saurari dukkan abin da kuka faɗi mani, na kuma naɗa sarki a bisanku.
\v 2 Yanzu, ga sarkin nan na tafiya a gabanku; kuma na tsufa da furfura; kuma, 'ya'yana maza na tare da ku. Nayi tafiya a gabanku daga ƙuruciyata har wa yau.
\s5
\v 3 Ga ni nan; ku yi shaida gãba da ni a gaban Yahweh da gaban shafaffensa. Saniyar wa na ɗauka? Jakin wa na ɗauka? Wane ne na yi wa damfara? Wane ne na tsanantawa? Daga hannun wa nakarɓi cin hanci don ya makantar da idanuna da shi? Ku shaida gãba da ni, kuma zan maido maku da shi."
\s5
\v 4 Suka ce, "Baka cuce mu ba, baka tsananta mana, ko ka saci wani abu daga hannun wani mutum ba."
\v 5 ya ce masu, "Yahweh ne shaida gãba da ku, kuma shafaffensa shaida ne a yau, cewa ba ku sami komai ba a cikin hannuna." Suka mai da amsa, "Yahweh ne shaida."
\s5
\v 6 Sama'ila ya ce da mutanen, "Yahweh ne ya naɗa Musa da Haruna, wanda kuma ya fito da ubanninku daga ƙasar Masar.
\v 7 Yanzu daga nan, ku miƙakanku, domin in yi roƙo tare da ku a gaban Yahweh game da dukkan ayyukan adalci na Yahweh, wanda ya yi domin ku da ubanninku.
\s5
\v 8 Da Yakubu ya zo Masar, kumakakanninku suka yi kuka ga Yahweh, daga nan Yahweh ya aika da Musa da Haruna, waɗanda suka bi dakakanninku fita daga Masar suka kuma zauna a wannan wuri.
\v 9 Amma suka manta da Yahweh Allahnsu; ya sayar da su cikin hannun Sisera, shugaban sojojin Hãzo, cikin hannun Filistiyawa, kuma cikin hannun sarkin mutanen Mowab; dukkan waɗannan suka yi faɗa gãba dakakanninku.
\s5
\v 10 Suka yi kuka ga Yahweh suka kuma ce, 'Mun yi zunubi, saboda mun yashe da Yahweh kuma mun bauta wa Ba'aloli da Ashtatori. Amma yanzu ka cece mu daga hannun maƙiyanmu, kuma za mu bauta maka.'
\v 11 Sai Yahweh ya aika da Yerub Ba'al, Bedan, Yefta, da Sama'ila, ya kuma ba ku nasara akan maƙiyanku dukka a kewaye da ku, yadda kuka zauna cikin tsaro.
\s5
\v 12 Da kuka ga Nahash sarkin mutanen Ammon yakawo maku hari, kuka ce mani, "A a! maimako, dole wani sarki ya yi mulki akanmu' - ko da ya ke Yahweh Allahnku, shi ne sarkinku.
\v 13 Yanzu ga sarkin daku ka zaɓa, wanda kuka yi roƙo domin sa wanda kuma Yahweh ya naɗa sarki a bisanku.
\s5
\v 14 Idan ku na tsoron Yahweh, ku bauta masa, ku yi biyayya da muryarsa, kuma ba wai ku kangare ga dokokin Yahweh ba, daga nan ku dukka da sarkin da ke mulki a bisanku za ku zama masu bin Yahweh Allahnku.
\v 15 Idan ba ku yi biyayya da muryar Yahweh ba, amma kukakangare ga dokokin Yahweh, daga nan hannun Yahweh zai yi gãba da ku, kamar yadda ya yi gãba dakakanninku.
\s5
\v 16 Ko yanzu ma ku miƙakanku kuma ku ga wannan babban abu wanda Yahweh zai yi a gaban idanunku.
\v 17 Ba kamar alkama ba ce yau? Zan yi kira ga Yahweh, domin ya aiko da aradu da ruwan sama. Daga nan za ku sani ku kuma gani cewa muguntarku babba ce, wadda kuka aikata a idanun Yahweh, cikin roƙar wakanku sarki."
\v 18 Sai Sama'ila ya yi kira ga Yahweh; a wannan rana kuma Yahweh ya aiko da aradu da ruwan sama. Daga nan dukkan mutanen suka ji tsoron Yahweh da Sama'ila ƙwarai.
\s5
\v 19 Daga nan dukkan mutanen suka ce da Sama'ila, "Ka yi addu'a domin bayinka ga Yahweh Allahnka, domin kada mu mutu. Gama mun ƙara wakanmu dukkan zunubanmu wannan muguntar cikin roƙo domin sarki domin kanmu."
\v 20 Sama'ila ya maida amsa, "Kada ku ji tsoro. Kun yi dukkan wannan mugunta, ammakada ku juya ga Yahweh, amma ku bauta wa Yahweh da dukkan zuciyarku.
\v 21 Kada ku juya zuwa holoƙan abubuwa waɗanda ba za su iya bada riba ko cetonku ba, saboda ba su da amfani.
\s5
\v 22 Domin albarkacin sunansa mai girma, Yahweh ba zai watsar da mutanensa ba, saboda ya gamshi Yahweh ya maida ku mutane domin kansa.
\v 23 Game da ni, ya yi ne sa da ni in yi zunubi gãba da Yahweh ta wurin tsaida yin addu'a domin ku. Maimako, zan koyar da ku hanya da ke mai kyau kuma dai-dai.
\s5
\v 24 Kawai dai ku ji tsoron Yahweh kuma ku bauta masa cikin gaskiya da dukkan zuciyarku. Kuyi la'akari da manyan abubuwan da ya yi domin ku.
\v 25 Amma idan kuka nace ga aikata mugunta, ku dukka da sarkinku zaku lalace."
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Saul na da shekaru talatin sa'ad da ya fara mulki; sa'ad da ya yi mulki shekaru arba'in a bisa Isra'ila,
\v 2 ya zaɓi mutane dubu uku na Isra'ila. Dubu biyu suna tare da shi a Mikmash da kuma ƙasar tudu ta Betel, dubu ɗaya kuma suna tare da Yonatan a Gibiya ta Benyamin. Sauran sojojin ya aika da su gida, kowanne mutum zuwa rumfarsa.
\s5
\v 3 Yonatan yakayar da sansanin Filistiyawa da ke Geba Filistiyawa kuma suka ji haka. Daga nan Saul ya busa ƙaho cikin dukkan ƙasar, cewa, "Bari Ibraniyawa su ji."
\v 4 Dukkan Isra'ila kuwa suka ji cewa Saul yakayar da sansanin Filistiyawa, da cewa kuma Isra'ila ta zama ɗoyi mai ruɓa ga Filistiyawa. Daga nan aka yi wa sojojin sammace tare su haɗu da Saul a Gilgal.
\s5
\v 5 Filistiyawa suka tattaru tare suyi faɗa gãba da Isra'ila: karusai dubu uku, mutane dubu shida suyi tuƙin karusan, rundunai kuma yawan su kamar rairayin da ke bakin teku. Suka zo sukakafa sansani a Mikmash, gabas da Bet Aben.
\s5
\v 6 Da mutanen Isra'ila suka ga cewa suna cikin matsala - domin mutanen sun ƙuntata, mutanen suka ɓoɓɓoye a kogonni, da ƙarƙashin zangarniyoyi, da duwatsu, da rijiyoyi, da ramuka.
\v 7 Wasu Ibraniyawan suka tafi ƙetaren Yodan zuwa ƙasar Gad da Giliyad. Amma Saul yana Gilgal tukuna, dukkan mutanen kuma suka bi shi suna rawar jiki.
\s5
\v 8 Ya jira kwana bakwai, lokacin da Sama'ila ya tsaida. Amma Sama'ila bai zo Gilgal ba, mutanen kuma suna warwatsewa daga Saul.
\v 9 Saul ya ce, "Kawo mani baikon ƙonawar da baye-bayen salamar." Daga nan ya miƙa baikon ƙonawar.
\v 10 Nan da nan yana gama miƙa baikon ƙonawar Sama'ila ya iso. Saul ya fita domin ya same shi ya kuma gaishe shi.
\s5
\v 11 Daga nan Sama'ila ya ce, "Mene ne ka yi?" Saul ya maida amsa, "Da naga cewa mutanen na bari na, kuma cewa baka zo ba cikin lokacin da aka tsaida, kuma cewa Filistiyawa sun riga sun taru a Mikmash,
\v 12 Na ce, 'Yanzu Filistiyawa zasu gangaro gãba da ni a Gilgal, kuma ban biɗi tagomashin Yahweh ba.' Sai na tilasta wakaina in miƙa baikon ƙonawar."
\s5
\v 13 Daga nan Sama'ila ya cewa Saul, "Ka yi wawanci. Baka kiyaye dokar Yahweh Allahnka ba wadda ya baka. Domin daga nan da Yahweh ya tabbatar da mulkin ka bisa Isra'ila har abada.
\v 14 Amma yanzu mulkin ka ba zai ci gaba ba. Yahweh ya samo wani mutum bisa ga zuciyarsa, kuma Yahweh ya naɗa shi ya zama shugaba bisa mutanensa, saboda baka yi biyayya da abin da ya dokace ka ba."
\s5
\v 15 Daga nan Sama'ila ya tashi ya tafi ya haye daga Gilgal zuwa Gibiya ta Benyamin. Daga nan Saul ya lissafa mutanen da ke tare da shi, kimanin mutane ɗari shida.
\v 16 Saul, da ɗansa Yonatan, da mutanen da ke tare da su, suka tsaya a Geba ta Benyamin. Amma Filistiyawan suka yi sansani a Mikmash.
\s5
\v 17 Mahaya suka zo daga sansanin Filistiyawa cikin ƙungiyoyi uku. Ƙungiya ɗaya ta juya wajen Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.
\v 18 Wata ƙungiyar ta juya wajen Bet Horon, wata ƙungiyar kuma ta juya wajen kan iyakar da ke fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji.
\s5
\v 19 Babu wani maƙeri da aka iya samu cikin dukkan ƙasar Isra'ila, saboda Filistiyawan sun ce, "Idan ba haka ba Ibraniyawa zasu yi takubba da mãsu domin kansu."
\v 20 Amma dukkan mutanen Isra'ila sukan je wurin Filistiyawa, kowanne domin ya wãsakayan aikin gonarsa, da addarsa, da gatarinsa, da laujensa.
\v 21 Farashin kuwakashi biyu cikin uku ne na shekel akan kowanne washin bakin kayan aiki, da adduna, dakashi ɗaya cikin uku na shekel domin washin gatura, domin kuma miƙar da silkuna.
\s5
\v 22 Saboda haka a ranar yaƙi, babu takubba ko mãsu da aka samu a hannuwan ko ɗaya daga cikin sojojin da ke tare da Saul da Yonatan; Saul ne kaɗai da ɗansa Yonatan suke da su.
\v 23 Sai sansanin Filistiyawa suka fita zuwa hanyar Mikmash.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Wata rana, Yonatan ɗan Saul ya cewa saurayin da ke ɗauke da makamansa, "Zo, mu tafi zuwa sansanin Filistiyawa da ke ɗaya ɓarayin." Amma bai gaya wa mahaifinsa ba.
\s5
\v 2 Saul na zama a waje da Gibiya a ƙarƙashin itacen manta'uwa da ke cikin Migron. Wajen mutane ɗari shida na tare da shi,
\v 3 har da Ahija ɗan Ahitub (ɗan'uwan Ikabod) ɗan Fenihas ɗan Eli, firist ɗin Yahweh a Shilo, wanda ya sanya falmara. Mutane ba su san cewa Yonatan ya tafi ba.
\s5
\v 4 A kowanne gefen hanyar inda Yonatan ya so ya bi domin yakai ga sansanin Filistiyawan, akwai dutse mai tsini a gefe ɗaya da kuma wani dutsen mai tsini a ɗayan gefen. Ɗaya dutse mai tsinin a na kiran sa Bozez ɗaya kuma dutsen mai tsini a na kiran sa Sene.
\v 5 Ɗaya dutsen mai tsini yana tsaye a arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma a kudu a gaban Geba.
\s5
\v 6 Yonatan ya ce da saurayin da ke ɗauke da makamansa, "Zo, mu ƙetara sansanin waɗannan marasakaciyar. Zai yiwu cewa, Yahweh ya yi aiki a madadin mu, domin babu abin da zai tsaida Yahweh daga yin ceto ta wurin masu yawa ko mutane kaɗan."
\v 7 Mai ɗaukar makamansa ya maida amsa, "Ka yi duk abin da ke cikin zuciyarka. Ka yi gaba, duba, ina tare dakai, in yi biyayya ga dukkan dokokinka."
\s5
\v 8 Daga nan Yonatan ya ce, "Za mu ƙetara zuwa ga mutanen, za mu kuma nunakanmu gare su.
\v 9 Idan suka ce mana, 'Ku dakata nan har sai mun hauro gare ku'- daga nan za mu tsaya a wurinmu ba kuma za mu ƙetara zuwa gare su ba.
\v 10 Amma idan suka maida amsa, 'Ku ƙetaro zuwa gare mu,' daga nan za mu ƙetara; saboda Yahweh ya bayar da su cikin hannunmu. Wannan ne zai zama alama a gare mu."
\s5
\v 11 Sai dukkan su suka bayyanakansu ga sansanin Filistiyawa. Filistiyawan suka ce, "Duba, Ibraniyawa na fitowa daga ramukan da suka ɓoye kansu."
\v 12 Daga nan mutanen sansanin suka yi kira ga Yonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce kuma, "Ku zo gare mu, za mu kuma nuna maku wani abu." Yonatan ya ce da mai ɗaukar makamansa, "Bi yo bayana, saboda Yahweh ya bayar da su cikin hannun Isra'ila."
\s5
\v 13 Yonatan ya hau bisa hannuwansa da ƙafafunsa, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa. Filistiyawa suka sha kisa a gaban Yonatan, kuma mai ɗaukar makamansa yakarkashe wasu bayansa.
\v 14 Wannan hari na farko da Yonatan da mai ɗaukar makamansa sukakai, yakashe mutane ashirin a cikin yankin fili kimanin rabin Eka.
\s5
\v 15 akayi fargaba a sansanin, da cikin filayen, da kuma cikin mutane. Har sansanin da mahayansu suka yi fargaba. Ƙasa ta girgiza, aka kuma yi babbar fargaba.
\s5
\v 16 Daga nan matsaran Saul a Gibiya ta Benyamin suka duba; taron sojojin Filistiyawa na bajewa, kuma suna tafiya nan da can.
\v 17 Daga nan Saul ya ce da mutanen da ke tare da shi, "Ku lissafa ku gani wane ne ya ɓace a cikinmu." Da suka yi lissafi, Yonatan da mai ɗaukar makamansa sun ɓace.
\s5
\v 18 Saul ya cewa Ahija, "Kawo akwatin Allah a nan," domin a lokacin yana tare da mutanen Isra'ila.
\v 19 Yayin da Saul ke magana da firist, yamutsin a cikin sansanin Filistiyawa yana ci gaba kuma yana ƙaruwa. Daga nan Saul ya cewa firist, "Janye hannunka."
\s5
\v 20 Saul da dukkan mutanen da ke tare da shi suka jera kuma suka shiga cikin yaƙin. Kowacce takobin Bafaliste tayi gãba da mutumin garinta, aka kuma yi babbar rikicewa.
\v 21 Yanzu waɗannan Ibraniyawa waɗanda dã suke tare da Filistiyawa, waɗanda kuma suka tafi tare da su cikin sansani, su ma kuma suka haɗe tare da Isra'ilawan da ke tare da Saul da Yonatan.
\s5
\v 22 Da mutanen Isra'ila waɗanda suka ɓoye kansu cikin tuddai kusa da Ifraim suka ji cewa Filistiyawa na tserewa, su ma suka bi bayansu cikin yaƙi.
\v 23 Haka Yahweh ya ceto Isra'ila a wannan rana, Yaƙi kuma ya wuce har gaban Bet Aben.
\s5
\v 24 A wannan rana mutanen Isra'ila sukakasance cikin ƙunci saboda Saul ya sanya mutanen ƙarƙashin rantsuwa ya kuma ce, "La'ananne ne mutumin da yaci wani abin ci har sai da yamma kuma nayi ramuwa akan maƙiyana." Don haka babu wani cikin mayaƙan da ya ɗanɗana abinci.
\v 25 Daga nan dukkan mutanen suka shi ga cikin jeji kuma akwai zuma a bisa ƙasar.
\v 26 Da mutanen suka shiga cikin jejin, zuman ya malalo, amma babu wanda ya sanya hannunsa ga bakinsa domin mutanen sun ji tsoron rantsuwar.
\s5
\v 27 Amma Yonatan bai ji cewa mahaifinsa ya ɗaure mutanen tare da rantsuwa ba. Ya miƙa tsinin sandar da ke hannunsa ya luma cikin saƙar zuman. Ya ɗaga hannunsa zuwa bakinsa, idanunsa kuma suka wartsake.
\v 28 Daga nan ɗaya daga cikin mutanen, ya amsa, "Mahaifinka ya yi wa mutane umarni mai tsanani tare da rantsuwa, ta wurin cewa, 'La'ananne ne mutumin da yaci abinci a wannan ranar,' ko da ya ke mutanen sun yi yaushi saboda yunwa.
\s5
\v 29 Daga nan Yonatan ya ce, "Mahaifina ya aiwatar da matsala a ƙasar. Kalli yadda idanuna suka wartsake saboda na ɗanɗanakaɗan daga cikin zuman nan.
\v 30 Yaya kuma in da mutanen yau sun ci a sake daga cikin ganima daga maƙiyansu da suka samo? Saboda yanzu kisan bai yi yawa ba a cikin Filistiyawa."
\s5
\v 31 Sukakaiwa Filistiyawa hari a wannan rana daga Mikmash zuwa Aiyalon. Mutanen suka gaji sosai.
\v 32 Mutanen suka afka da haɗama bisa ganimar suka kuma ɗauki tumaki, da shanu da maruƙa, suka kuma yanka su a ƙasa. Mutanen suka cinye su tare da jinin.
\s5
\v 33 Daga nan suka gayawa Saul, "Duba, mutanen suna zunubi gãba da Yahweh ta wurin ci tare da jinin." Saul ya ce, "Kun aikata rashin aminci. Yanzu, a gangaro da wani babban dutse nan a gare ni."
\v 34 Saul ya ce, "Fita cikin mutanen, ku kuma gaya masu, 'Bari kowanne mutum yakawo sansa da tunkiyarsa, ya yanka su a nan, ya kuma ci. Kada kuyi zunubi gãba da Yahweh ta wurin ci tare da jinin."' Sai kowanne mutum yakawo sansa tare da shi a wannan dare ya kuma yanka a wurin.
\s5
\v 35 Saul ya gina bagadi ga Yahweh, shi ne kuma bagadi na farko da ya gina ga Yahweh.
\s5
\v 36 Daga nan Saul ya ce, "Bari mu runtumi Filistiyawa da dare mu kuma warwatsa su har wayewar gari; kada mu bar ko ɗayan su da rai." Suka amsa, "Kayi duk abin da ya yi kyau a gare ka." Amma firist ɗin ya ce, "Bari mu kusanci Allah a nan."
\v 37 Saul ya tambayi Allah, "In runtumi Filistiyawa? Zaka bayar da su cikin hannun Isra'ila?" Amma Allah bai amsa masa ba a wannan ranar.
\s5
\v 38 Daga nan Saul ya ce, "Ku zo nan, dukkan ku shugabannin mutane; ku koya ku kuma duba yadda wannan zunubin ya faru a yau.
\v 39 Domin, da wanzuwar Yahweh, wanda ke ceton Isra'ila, ko ma idan yana cikin Yonatan ne ɗana, tabbas zai mutu." Amma ba ko ɗaya daga cikin jama'ar daga cikin dukkan mutanen ya amsa masa.
\s5
\v 40 Daga nan ya ce da dukkan Isra'ila, "Dole ku tsaya gefe ɗaya ni da Yonatan ɗana kuma mu tsaya gefe ɗaya." Mutanen suka ce da Saul, "Ka yi abin da ya yi kyau a gare ka."
\v 41 Saul ya ce, Yahweh, Allah na Isra'ila! Idan ni ne na yi wannan zunubin ko kuma ɗana ne Yonatan ya yi shi, daga nan, Yahweh, Allah na Isra'ila, ka bada Urim. Amma idan wannan zunubi mutanenka Isra'ila ne suka aikata shi"Ka bada Tummim." Sai Yonatan da Saul aka ɗauka ta ƙuri'a, amma mayaƙan sukakaucewa Zaɓen.
\v 42 Daga nan Saul ya ce, "akaɗa ƙuri'u tsakani na da Yonatan ɗa na." Daga nan aka ɗauki Yonatan ta ƙuri'a.
\s5
\v 43 Daga nan Saul ya ce wa Yonatan, "Gaya mani abin daka yi." Yonatan ya gaya masa, "Na ɗanɗana zumakaɗan dakarshen sandar da ke hannuna. Ga ni nan; zan mutu."
\v 44 Saul ya ce, "Allah ya yi haka kuma fiye ma a gare ni, idan baka mutu ba, Yonatan."
\s5
\v 45 Daga nan mutanen suka cewa Saul, "Yonatan ya mutu kuwa, wanda ya aiwatar da wannan babbar nasara ga Isra'ila? Ya yi nesa da shi! da wanzuwar Yahweh, ba bu ko gashi ɗaya bisakansa da zai faɗi ƙasa, gama ya yi aiki tare da Allah a yau." Haka mutanen suka kuɓutar da Yonatan yadda bai mutu ba.
\v 46 Daga nan Saul ya tsaida runtumar Filistiyawa, kuma Filistiyawan suka tafi na su wurin.
\s5
\v 47 Da Saul ya fara mulki bisa Isra'ila, ya yi yaƙi gãba da maƙiyansa ta kowanne gefe. Ya yi yaƙi gãba da Mowab, Ammoniyawa, Idom, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya juya, yana azabta horo akansu.
\v 48 Ya yi aiki da ƙarfin hali mai girma yakayar da Amalekawa. Ya kuɓutar da Isra'ila daga hannuwan waɗanda suka washe su.
\s5
\v 49 'Ya'yan Saul maza su ne Yonatan, Ishbi, da Malkishuwa. Sunayen 'ya'yansa mata biyu kuwa su ne Merab, ta fari, da Mikal, ƙaramar.
\v 50 Sunan matar Saul shi ne Ahinowam; ita ce ɗiyar Ahimãz. Sunan shugaban sojojinsa kuwa Abna ɗan Nã, kawun Saul.
\v 51 Kish ne mahaifin Saul; Nã kuma, mahaifin Abna, shi ne ɗan Abiyel.
\s5
\v 52 An yi yaƙi mai tsanani gãba da Filistiyawa dukkan kwanakin Saul. Idan Saul ya ga wani ƙaƙƙarfan mutum, ko mutum mai ƙwazo, sai ya jawo shi a gare shi.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Sama'ila ya cewa Saul, "Yahweh ya aiko ni in shafe ka sarki bisa mutanensa Isra'ila. Yanzu ka saurari maganganun Yahweh.
\v 2 Wannan ne abin da Yahweh mai runduna ya ce, 'Na lura da abin da Amalek ya yiwa Isra'ila cikin tsayayya da su a bisa hanya, sa'ad da suka fito daga cikin Masar.
\v 3 Yanzu ka je kakai hari ga Amalek ka kuma lalata duk abin da suke da shi ɗungum. Kadaka raga masu, ammaka kashe su maza da mata, yaro da jariri, saniya da tunkiya, raƙumi da jaki."'
\s5
\v 4 Saul ya tattaro mutanen ya ƙidaya su a birnin Telem: mutane dubu ɗari bisa ƙafa, da mutanen Yahuda dubu goma.
\v 5 Daga nan Saul ya zo cikin birnin Amalek ya kuma jira a cikin kwari.
\s5
\v 6 Daga nan Saul ya cewa Keniyawa, "Ku je, ku tafi, ku fito daga cikin Amalekawa, domin kada in lalatar da ku tare da su. Domin kun nuna halin kirki ga dukkan mutanen Isra'ila, sa'ad da suka zo daga Masar." Sai Keniyawa suka wãre daga Amalekawa.
\v 7 Sai Saul yakai hari ga Amalekawa, daga Habila har ya zuwa Shur, wadda ke gabas da Masar.
\s5
\v 8 Daga nan ya ɗauki Agag sarkin Amalekawa da rai; gaba ɗaya ya lalatar da dukkan mutanen dakaifin takobi.
\v 9 Amma Saul da mutanen suka bar Agag, duk da mafi kyau daga cikin tumaki, da shanu, da maraƙai masu ƙiba, da raguna. Kowanne abu da ke da kyau, ba su lalatar ba. Amma gaba ɗaya suka lalatar da duk wani abu wulaƙantacce marar amfani kuma.
\s5
\v 10 Daga nan maganar Yahweh ta zo ga Sama'ila, cewa,
\v 11 "Ya ba ni ɓacin rai cewa na naɗa Saul sarki, domin ya juya baya daga bi na bai kuma aiwatar da dokokina ba." Sama'ila ya fusata; ya yi kuka ga Yahweh dukkan dare.
\s5
\v 12 Sama'ila ya farka da wurwuri domin ya sami Saul da safe. Aka cewa Sama'ila, "Saul ya tafi Kamel kuma yakafa wakansa wurin tunawa, daga nan ya juya kuma ya ci gaba zuwa Gilgal."
\v 13 Daga nan Sama'ila ya zo wurin Saul, Saul kuma ya ce masa, "Mai albarka ne kai daga Yahweh! Na cika dokar Yahweh."
\s5
\v 14 Sama'ila ya ce, "Daga nan mene ne wannan kukan tumakin a kunnuwa na, da kukan shanun da na ke ji?"
\v 15 Saul ya maida amsa, "An kawo su ne daga Amalekawa. Domin mutanen sun keɓe mafi kyau daga cikin tumakin da shanun, domin hadaya ga Yahweh Allahnka. Sauran gaba ɗaya mun hallakar da su."
\v 16 Daga nan Sama'ila ya cewa Saul, "Jira, kuma zan faɗi maka abin da Yahweh ya ce mani da daren nan." Saul ya ce masa, "Yi magana!"
\s5
\v 17 Sama'ila ya ce, "Koda ya ke kai ƙarami ne a idanunka, ba an mai she ka shugaban kabilun Isra'ila ba? Daga nan Yahweh ya shafe ka sarki bisa Isra'ila,
\v 18 Yahweh kuma ya aike ka bisa hanyarka ya kuma ce, 'Je kuma gaba ɗayaka hallakar da masu zunubi, Amalekawa, ka kuma yi faɗa gãba da su har sai sun hallaka.'
\v 19 Me yasa baka yi biyayya da muryar Yahweh ba, amma a maimako ka ƙwato ganimaka kuma yi abin da ke mugunta a gaban Yahweh?"
\s5
\v 20 Daga nan Saul ya cewa Sama'ila, "Lallai na yi biyayya da muryar Yahweh, kuma na tafi bisa hanyar da Yahweh ya aike ni. Nakamo Agag, sarkin Amalek, kuma gaba ɗaya na hallakar da Amalekawa.
\v 21 Amma mutanen suka ɗauko wasu daga cikin ganimar - tumaki da shanu, abubuwa mafi kyau da aka keɓe ga hallakarwa, domin hadaya ga Yahweh Allahnka a Gilgal."
\s5
\v 22 Sama'ila ya maida amsa, "Yahweh yana gamsuwa da baye-baye na ƙonawa da hadayu, fiye da biyayya da muryar Yahweh? Biyayya tafi hadaya, kuma saurare ya fi kitsen raguna.
\v 23 Domin tawaye kamar zunubin tsafi ya ke, taurin kai kumakamar mugunta da ƙazanta. Sabodaka yi watsi da maganar Yahweh, shi ma ya ƙika da ga zama sarki."
\s5
\v 24 Daga nan Saul ya cewa Sama'ila, "Na yi zunubi; domin nakarya dokar Yahweh da maganganunka, saboda ina jin tsoron mutanen na kuma yi biyayya da muryarsu.
\v 25 Yanzu, ina roƙon kaka yafe zunubina, ka kuma juyo tare da ni domin in yi sujada ga Yahweh."
\s5
\v 26 Sama'ila ya cewa Saul, "Ba zan koma tare dakai ba; domin ka yi watsi da maganar Yahweh, Yahweh kuma ya ƙika da zama sarki bisa Isra'ila."
\v 27 Yayin da Sama'ila ya juya domin ya tafi, Saul ya riƙe haɓar rigarsa, ta kuma yage.
\s5
\v 28 Sama'ila ya ce masa, "Yahweh ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka a yau ya kuma bayar da ita ga makwabcinka, wani wanda ya fi ka.
\v 29 Haka kuma, Ƙarfin Isra'ila ba zai yi ƙarya ba ko ya canza ra'ayinsa; domin shi ba mutum ba ne, da zai canza ra'ayinsa."
\s5
\v 30 Daga nan Saul ya ce, "Na yi zunubi. Amma ina roƙon kaka darajanta ni yanzu a gaban dattawan mutanena da gaban Isra'ila. Ka sake juyowa tare da ni, domin in yi sujada ga Yahweh Allahnka."
\v 31 Sai Sama'ila ya sake juyowa bayan Saul, Saul kuma ya yi sujada ga Yahweh.
\s5
\v 32 Daga nan Sama'ila ya ce, "Kawo Agag sarkin Amalekawa nan wurina." Agag ya zo gare shi ɗaure cikin sarƙoƙi ya kuma ce, "Tabbas ɗacin mutuwa ya wuce."
\v 33 Sama'ila ya maida amsa, "Kamar yadda takobin ka ta maida mata marasa 'ya'ya, haka mahaifiyarka za ta zama marar ɗa a cikin mata." Daga nan Sama'ila ya datse Agag gunduwa-gunduwa a gaban Yahweh a Gilgal.
\s5
\v 34 Sama'ila ya tafi Rama, Saul kuma ya tafi gidansa a Gibiya ta Saul.
\v 35 Sama'ila bai sake ganin Saul ba har sai ranar mutuwarsa, gama ya yi makoki domin Saul. Yahweh ya yi baƙinciki da cewa ya naɗa Saul sarki bisa Isra'ila.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Yahweh ya cewa Sama'ila, "Har yaushe zaka yi makoki domin Saul, tunda nayi watsi da shi daga zama sarki bisa Isra'ila? Ka cika ƙahonka da mai ka kuma tafi. Zan aike ka ga Yesse na Betlehem, domin na zaɓar wakaina sarki cikin 'ya'yansa maza."
\s5
\v 2 Sama'ila ya ce, "Yaya zan tafi? Idan Saul ya ji haka, zai kashe ni." Yahweh ya ce, "Ka ɗauki maraƙi tare dakai ka kuma ce, 'Na zo in yi hadaya ga Yahweh.'
\v 3 Ka kira Yesse zuwa hadayar, zan kuma nuna maka abin da zaka yi. Zaka shafe mani wanda zan gaya maka."
\s5
\v 4 Sama'ila ya yi yadda Yahweh ya faɗi ya kuma tafi Betlehem. Dattawan birnin suna rawar jiki yayin da su ka zo suka same shi suka kuma ce, "Kana zuwa cikin salama?"
\v 5 Ya ce, "Cikin salama; Na zo in yi hadaya ga Yahweh. Ku shirya ku keɓe kanku ku kuma zo tare da ni wurin hadayar." Daga nan ya ware Yesse da kuma 'ya'yansa maza ya kuma gayyace su zuwa hadayar.
\s5
\v 6 Da suka zo, yakalli Iliyab ya kuma faɗi wakansa cewa shafaffe na Yahweh ba bu shakka yana tsaye a gaba na.
\v 7 Amma Yahweh ya cewa Sama'ila, "Kadaka dubi siffarsa ta zahiri, ko tsawon ƙirarsa; saboda na ƙi shi. Domin Yahweh ba ya duba yadda mutum ke duba wa; mutum yanakallon siffa a zahiri, amma Yahweh yanakallon zuciya."
\s5
\v 8 Daga nan Yesse ya kira Abinadab ya kuma sa ya gitta a gaban Sama'ila. Daga nan Sama'ila ya ce, "Wannan ma Yahweh bai zaɓe shi ba."
\v 9 Yesse daga nan yasa Shamma ya gitta, amma Sama'ila ya ce, "Wannan ma Yahweh bai zaɓe shi ba."
\v 10 Yesse yasa 'ya'yansa maza bakwai suka gitta a gaban Sama'ila. Daga nan Sama'ila ya cewa Yesse, "Yahweh bai zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan ba."
\s5
\v 11 Daga nan Sama'ila ya cewa Yesse, "Dukkan 'ya'yanka maza suna nan?" Ya maida amsa, "Akwai ƙaramin su da ya rage, amma yana lura da tumaki." Sama'ila ya cewa Yesse, "Ka aika akawo shi; domin ba za mu zauna ba har sai ya zo nan."
\v 12 Yesse ya aika aka zo da shi ciki. Yanzu dai wannan ɗa jã ne da kyawawan idanu da kyakkyawar siffa. Yahweh ya ce, "Tãshi, shafe shi; domin shi ne."
\s5
\v 13 Daga nan Sama'ila ya ɗauki ƙahon mai ya kuma shafe shi a tsakiyar 'yan uwansa. Ruhun Yahweh ya afko bisa Dauda daga wannan rana har zuwa gaba. Daga nan Sama'ila ya tashi ya kuma tafi Rama.
\s5
\v 14 Yanzu Ruhun Yahweh ya bar Saul, ruhu mai illa kuma daga Yahweh yana azabtar da shi a maimako.
\v 15 Bãyin Saul suka ce masa, "Duba, ruhu mai illa daga Allah na azabtar dakai.
\v 16 Bari ubangijinmu yanzu ya umarci bãyinsa waɗanda ke tsaye a gabanka su nemo mutum wanda ya kware a kiɗin garaya. Daga nan idan ruhu mai illa daga Allah yana bisanka, zai kaɗa ta kuma zaka sami lafiya."
\s5
\v 17 Saul ya cewa bãyinsa, "Ku samo mani mutum da ya iyakaɗa wa sosai ku kumakawo mani shi."
\v 18 Daga nan ɗaya daga cikin samarin ya amsa, ya kuma ce, "Na ga wani ɗan Yesse Betlehemiye, wanda ya kware akaɗa wa, ƙaƙƙarfa, mutum mai ƙarfin hali, mutumin yãƙi, mai tattali a zance, mutum mai asali; kuma Yahweh yana tare da shi."
\v 19 Sai Saul ya aika da manzanni wurin Yesse, ya kuma ce, "Ka aiko mani da ɗanka Dauda, wanda ke tare da tumaki."
\s5
\v 20 Yesse ya ɗauki jaki danƙare da gurasa, da salkar inabi, da 'yar akuya, ya kuma aika da su tare da ɗansa Dauda wurin Saul.
\v 21 Daga nan Dauda ya zo wurin Saul ya kuma shiga hidimarsa. Saul ya ƙaunace shi sosai, ya kuma zama mai ɗaukar makamansa.
\s5
\v 22 Saul ya aika wa Yesse, cewa, "Bari Dauda ya tsaya a gabana, domin ya sami tagomashi a idanu na."
\v 23 Duk sa'ad da ruhu mai illa daga Allah yana bisan Saul, Dauda zai ɗauki garaya ya kumakaɗa ta. Sai Saul ya wartsake ya kuma yi lafiya, kuma ruhu mai illar sai ya tafi daga gare shi.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Yanzu Filistiyawa suka tara rundunarsu domin yaƙi. Suka taru a Soko, wacce take ta Yahuda. Suka yi sansani tsakanin Soko da Azeka, cikin Ifes Dammim.
\s5
\v 2 Saul tare da mutanen Isra'ila suka taru sukakafa sansani a kwarin Ila, suka jã layin dãga dominsu fuskanci Filistiyawa.
\v 3 Filistiyawa suka tsaya a bisa dutse a sashen gefe, Isra'ila kuma na bisa dutse a wancan gefen a kwari da ke tsakaninsu.
\s5
\v 4 Wani mutum mai ƙarfi ya fito daga cikin sansanin Filistiyawa, mutum mai suna Goliyat daga Gat, wanda tsayinsa kãmu shida ne da rabi.
\v 5 Yana da hular tagulla a bisakansa, yana kuma sanye da tufafin yaƙi. Rigar nada nauyin Shekel dubu biyar na tagulla.
\s5
\v 6 Yana sanye da makarin ƙafa na tagulla da kuma mãshi na tagulla a tsakiyar kafaɗunsa.
\v 7 Sandar mashinsa na da girma, da tausasshen igiya domin harba takamar dirkar masaka. Kan mashinsa na da nauyin shekel na ƙarfe ɗari shida. Mai ɗaukar masa garkuwa na a gaba da shi.
\s5
\v 8 Ya tsaya ya yi ihu ga sojojin Isra'ilawa, "Donme kuka fito waje kukakafa sansanin yaƙi? Ni ba Bafiliste ba ne, ku kuma ba bayi ne na Saul ba? Ku zaɓa wakanku mutum kuma bari ya sauko gare ni.
\v 9 Idan ya iya faɗa da ni ya kumakashe ni, sa'an nan zamu zama bayinku. Amma idan na kãda shi na kumakashe shi, sai ku zama bayinmu ku kuma bauta mana."
\s5
\v 10 Sai kuma Bafilisten ya ce, "Na ƙalubalanci rundunar Isra'ila yau. Ku ba ni wanda zamu yi faɗa tare."
\v 11 Lokacin da Saul da dukkan Isra'ila suka ji abin da Bafilisten ya faɗi, sai sukakaraya da babban tsoro.
\s5
\v 12 Yanzu dai Dauda ɗan Ifraimiye ne na Betlehem cikin Yahuda, mai suna Yesse. Yana da 'ya'ya maza takwas. Yesse tsohon mutum ne a cikin kwanakin Saul, tsoho ne tukub a tsakanin mutane.
\v 13 Manyan 'ya'ya maza na Yesse suna tare da Saul a filin dãga. Sunayen 'ya'yansa maza uku da suka tafi bakin dãga su ne Iliyab wanda shi ne ɗan fari, na biyun Abinadab, sai na ukun Shammah.
\s5
\v 14 Dauda shi ne ɗan ƙaraminsu. Yayyensa uku suka bi Saul.
\v 15 Yanzu dai Dauda yana fita yana shigowa gaba da baya tsakanin rundunar Saul da kuma tumakin babansa a Betlehem, domin ya ciyar da su.
\v 16 Kwana arba'in mai ƙarfin nan Bafilisten yana zuwa gaba safiya da yamma domin ya miƙakansa ga yaƙi.
\s5
\v 17 Sai Yesse ya cewa ɗansa Dauda, "Ka ɗauko wa 'yan uwanka mudu 22 na wannan gasasshen hatsin da kuma wannan gurasar goma, ka kuma ɗauko su da sauri kakai su sansani zuwa ga 'yan'uwanka.
\v 18 Ka kuma ɗauki curin man shanu goma ga shugabansu na dubu. Ka duba lafiyar 'yan'uwankaka kuma dawo da tabbacin suna lafiya.
\s5
\v 19 'Yan'uwanka suna tare da Saul da dukkan mazajen Isra'ila a cikin kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa."
\v 20 Dauda ya tashi da sassafe ya bar garken cikin hannun wani makiyayi domin ya kula da su. Ya ɗauki abincin ya tafi, kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya iso sansani lokacin da rundunar ke fitowa zuwa filin dãga suna sowa ta yaƙi.
\v 21 Sa'an nan Isra'ila da Filistiyawa sukakafa layi domin dãga, runduna gãba da juna.
\s5
\v 22 Dauda ya bar kayayyakinsa ajiya wurin maitsaron kayayyaki, ya ruga da gudu zuwa wurin rundunar, ya gaida 'yan'uwansa.
\v 23 Yayin da ya ke cikin magana da su, mutumin mai ƙarfin, Bafilisten na Gat, mai suna Goliyat, ya kuma fito daga cikin rundunar Filistiyawa, ya kuma furta maganganun da ya ke furtawakamar da farko, Dauda kuwa ya ji su.
\v 24 A lokacin da dukkan Isra'ila suka ga mutumin, suka yi gudu daga wurinsa kuma suka ji tsoro matuƙa.
\s5
\v 25 Mazajen Isra'ila suka ce, "Ko kun ga wannan mutumin wanda ya fito? Ya fito domin ya cakuni Isra'ila. Sarki zai bai wa duk wadda yakashe shi dukiya mai yawa. kuma zai ba da ɗiyarsa gare shi ya aura, Kuma za ya raba gidan ubansa daga biyan haraji a Isra'ila."
\s5
\v 26 Dauda ya cewa mutanen da ke tsaye kusa da shi, "Mene ne za a yiwa mutumin da yakashe wannan Bafilisten domin yakawar da kunya ga Isra'ila? Wane ne wannan Bafilite marar kaciya da har ya ke rena rundunar Allah mai rai?"
\v 27 Sai mutanen suka furta abin da suka faɗa tun farko kuma suka ce masa, "Haka za a yiwa mutumin da yakashe shi."
\s5
\v 28 Iliyab babban ɗan'uwansa ya ji sa'ad da ya yi magana da mutanen. Sai fushin Iliyab ya yi ƙuna a bisa Dauda, sai ya ce, "Mene ne dalilin da yasaka gangaro nan wurin? A hannun wane ne ka baro 'yan tumakan nan cikin jeji? Na san girman kanka, da kuma fahariyar zuciyarka; domin ka gangaro nan domin kayi kallon yaƙi ne."
\v 29 Dauda ya ce, "Mene ne na yi yanzu? Ba tambayakawai na yi ba?"
\v 30 Ya juya ya bar shi zuwa wurin wani, ya sake irin magana a yadda ya yi dã. Mutanen suka amsa masakamar dã.
\s5
\v 31 Da aka ji maganganun da Dauda ya faɗa, sojoji suka maimaita su ga Saul, shi kuwa ya aika akakawo Dauda.
\v 32 Sai Dauda ya cewa Saul. "Kada zuciyar kowanne mutum takaraya sabili da wancan Bafilisten; bawanka zai tafi ya yi faɗa da wannan Bafilisten."
\v 33 Saul ya cewa Dauda, "Ba zaka iya fãɗawa Bafilisten nan ba domin ka yi faɗa da shi; gamakai matashi ne, amma shi mutum ne mayaƙi tun yana saurayi."
\s5
\v 34 Amma Dauda ya cewa Saul, "Bawanka yana kula da tumakin mahaifinsa. Lokacin da zaki ko damisa ya taso ya ɗauki 'yar akuya daga cikin garken,
\v 35 nakan bisu in kumakai masu farmaki, in kuma ƙubutar da shi daga bakinsa. Lokacin da zai tayar mani, nakama shi a gemunsa, na buga shi, na kumakashe shi.
\s5
\v 36 Bawanka yakashe zaki da damisa. Wannan Bafilisten marar kaciya zai zamakamar ɗayansu, tunda ya ƙalubalanci rundunar Allah mai rai."
\s5
\v 37 Dauda ya ce, "Yahweh ya ƙubutar da ni daga hannun zaki da kuma hannun damisa. Za ya ƙubutar da ni daga hannun wannan bafilisten." Sa'an nan Saul ya cewa Dauda, "Je ka, bari kuma Yahweh yakasance tare dakai."
\v 38 Saul ya sanya wa Daudakayan yaƙinsa. Yasa masa hular tagulla akansa, ya kuma sanya masa mayafin wayoyi.
\s5
\v 39 Dauda ya ɗaura takobinsa a rigar yaƙi. Amma yakasa tafiya ciki, domin baya yi koyi da su ba. Sai Dauda ya cewa Saul, "Ba zan iya fita in yi faɗa da wannan kaya ba, gama ban yi koyo da su ba." Saboda haka Dauda ya kwaɓe kayan.
\v 40 Ya ɗauki sandar kiwonsa cikin hannunsa ya kuma zaɓi duwatsu biyar daga cikin rafi; ya zuba su cikin jakarsa ta kiwo. Majajjawarsa na cikin hannunsa sa'ad da ya fuskanci Bafilisten.
\s5
\v 41 Bafilisten ya rugo zuwa wurin Dauda, da mai ɗaukar masa makamai a gabansa.
\v 42 A lokacin da Bafilisten ya juya ya kuma ga Dauda, sai ya rena shi, gama ɗan yaro ne kawai, kuma jã, mai asalin siffa.
\v 43 Sai Bafilisten ya cewa Dauda, "Ni kare ne, da zaka zo gare ni da sanduna?," sai kuma Bafilisten ya la'anci Dauda da allolinsa.
\s5
\v 44 Bafilisten ya cewa Dauda, "Zo gare ni, zan kuma bada namanka ga tsunytsayen sammai ga kuma namomin jeji."
\v 45 Dauda kuwa ya amsa wa Bafilisten, "Kai kana zuwa gare ni da takobi, da mashi, da kibiya. Amma na zo gare ka a cikin sunan Yahweh mai runduna, Allah na rundunar Isra'ila, wandaka rena.
\s5
\v 46 Yau Yahweh zai ba ni nasara bisanka, zan kumakashe ka in kuma cire kanka daga jikinka. Yau zan miƙɑ gawawakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sammai ga kuma namomin jeji na ƙasa, saboda dukkan duniya ta san cewa akwai Allah a Isra'ila,
\v 47 kuma dukkan wannan taro su san cewa Yahweh ba ya ba da nasara ta dalilin takobi ko mãshi. Gama yaƙin na Yahweh ne, kuma za ya miƙaka cikin hannunmu."
\s5
\v 48 A lokacin da Bafilisten ya tashi ya kuma taso ga Dauda, sai Dauda ya rugo da sauri zuwa ga rundunar magabcin domin ya gamu da shi.
\v 49 Dauda yasa hannunsa cikin jaka, ya ɗauko dutse daga ciki, sai ya jefi Bafilisten a tsakiyar goshi, sai ya faɗi a fuskarsa ƙasa.
\s5
\v 50 Dauda ya ci nasara ga Bafilisten da majajjawa da dutse. Ya jefe Bafilisten ya kumakashe shi. Babu takobi cikin hannun Dauda.
\v 51 Sai Dauda ya sheƙa a guje ya kuma tsaya a bisa Bafilisten ya kuma dauƙe takobinsa, ya zaro ta daga gidanta, yakashe shi, ya datse kansa da ita. A lokacin da Filistiyawa suka ga cewa mutuminsu mai ƙarfi ya mutu, suka gudu.
\s5
\v 52 Sai mazajen Isra'ila da na Yahuda suka tashi da sowa, suka kuma runtumi Filistiyawa har zuwa kwari da ƙofofin Ekron. Matattun Filistiyawa suka kwanta akan hanya zuwa Sharem, hanyar zuwa Gat da Ekron.
\v 53 Mutanen Isra'ila suka dawo daga runtumar Filistiyawa, suka kuma washe sansaninsu.
\v 54 Dauda ya ɗauki kan Bafilisten yakawo shi Yerusalem, amma ya ajiye rigar yaƙinsa a tasa rumfar.
\s5
\v 55 Da Saul ya ga Dauda ya fita gãba da Filistiyawa, ya cewa Abna, shugaban runduna, "Abna, yaron wane ne wannan matashin?" Abna ya ce, "Ranka ya daɗe, sarki, ban sani ba."
\v 56 Sarkin ya ce, "Ka tambayi waɗanda suna iya sani, ɗan wane ne."
\s5
\v 57 Da Dauda ya dawo daga kisan Filistiyawan, Abna ya ɗauke shi, yakawo shi wurin Saul tare dakan Bafilisten a cikin hannunsa.
\v 58 Saul ya ce masa, "Kai ɗan wane ne, ɗan saurayi?" Dauda ya amsa, "Ni yaron bawanka ne Yesse mutumin Betlehem."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Bayan da ya gama magana da Saul, sai ran Yonatan ya manne wa ran Dauda, Yonatan kuwa ya ƙaunace shi kamar ransa.
\v 2 Saul ya ɗauki Dauda zuwa cikin hidimarsa a wannan rana; baya barshi ya koma gidan mahaifinsa ba.
\s5
\v 3 Sai Yonatan da Dauda suka yi alƙawari da juna na abokantaka domin Yonatan ya ƙaunace shi kamar ransa.
\v 4 Yonatan ya tuɓe rigarsa wadda ya ke yãfe da ita ya kuma ba Dauda tare da rigar yaƙinsa, har da takobinsa, bakansa, da kuma maɗaurinsa.
\s5
\v 5 Dauda ya tafi duk inda Saul ya aike shi, kuma ya ci nasara. Saul ya maida shi kai bisa mazajen yaƙi. Wannan ya ƙayatar a idanun dukkan mutanen da kuma idanun bayin Saul.
\s5
\v 6 Da suka dawo daga hallaka Filistiyawan, matayen suka fito daga dukkan biranen Isra'ila, suna raira waƙa da rawa, su taryi Saul, dakacakaura, da farinciki, da kumakayan kiɗe-kiɗe.
\v 7 Matayen suka riƙa yin waƙa da juna sa'ad da suke kaɗawa. Suka raira: "Saul yakashe dubbansa, Dauda kuma dubbansa goma."
\s5
\v 8 Saul ya ji haushi ƙwarai, kuma wannan waƙa ta baƙanta masa rai. Ya ce, "Sun ba Dauda dubbai goma, amma ni sun ba ni dubbai kawai. To mene ne ya rage masa idan ba mulkin ba?"
\v 9 Saul kuwa daga wannan rana ya fara yi wa Daudakallon rashin yarda.
\s5
\v 10 washegari wani mugun ruhu daga wurin Allah ya saukar wa Saul ya kuma yi hauka cikin gidan. Sai Dauda yakaɗa garayarsa, kamar yadda ya saba kowacce rana. Saul yana ɗauke da mashi cikin hannunsa.
\v 11 Saul ya jefa mashin, gama ya yi tunani, "Zan tsire Dauda ga bango." Amma Dauda ya tsira daga gaban Saul sau biyu kamar haka.
\v 12 Saul ya ji tsoron Dauda, gama Yahweh na tare da shi, amma baya kuma tare da Saul.
\s5
\v 13 Sai Saul ya fitar da shi daga gabansa ya kuma maishe shi shugaban dubu. Da haka Dauda ya dinga fita yana shigowa a fuskar mutanen.
\v 14 Dauda ya yi nasara a dukkan hanyoyinsa, gama Yahweh na tare da shi.
\s5
\v 15 Da Saul ya ga yana ci gaba, sai ya ji tsoronsa.
\v 16 Amma dukkan Isra'ila da Yahuda suka ƙaunaci Dauda, gama yana fita yana shigowa a idanunsu.
\s5
\v 17 Sai Saul ya cewa Dauda, "Ga babbar ɗiyata Merab. Zan baka ita ta zama matarka. Sai dai ka yi mazakutta dominaka kuma yi yaƙin Yahweh." Gama Saul ya yi tunani, "Kada hannuna ya tayar masa, amma bari hannun Filistiyawa ya sauka bisansa."
\v 18 Dauda ya cewa Saul, "Ni wane ne, kuma su wane ne 'yan uwana, ko gidan mahaifina cikin Isra'ila, da zan zama suruki ga sarki?"
\s5
\v 19 Amma a lokacin da Merab, ɗiyar Saul, yakamata a bada ita ga Dauda, sai aka bada ita ga Adriyel mutumin Meholat ta zama matarsa.
\s5
\v 20 Amma Mikal, ɗiyar Saul, ta ƙaunaci Dauda. Suka gaya wa Saul, wannan kuma ya yiwa Saul daɗi.
\v 21 Sai Saul ya ce a zuciyarsa, "Zan ba da ita gare shi, domin ta zama tarko a gare shi, kuma hannun Filistiyawa ya yi gãba da shi." Saboda haka Saul ya cewa Daudakaro na biyu, "Zaka zama surukina."
\s5
\v 22 Saul ya umarce bayinsa, "Ku yi magana da Dauda a asirce, ku ce, 'Duba, sarki yana jin daɗinka, kuma dukkan bayinsa suna ƙaunar ka. To yanzu, ka zama surukin sarki."'
\s5
\v 23 Saboda haka bayin Saul suka furta waɗannan maganganu ga Dauda. Sai Dauda ya ce, "Ko ƙaramin abu ne gare ku zaman surukin sarki, ganin cewar ni talaka ne, kuma ba sananne ba?"
\v 24 Bayin Dauda suka mayar wa Saul da maganganun da Dauda ya faɗa.
\s5
\v 25 Sai Saul ya ce, "Ku faɗi wannan ga Dauda, 'Sarki ba ya buƙatar wani sadãki, sai dai fatar loɓar Filistiyawa ɗari daya, da za a rama daga maƙiyan sarki."' Yanzu Saul ya yi tunani dai yasa Dauda ya mutu ta hannun Filistiyawa.
\v 26 Da bayinsa suka gaya wa Dauda waɗannan maganganu, sai ya yiwa Dauda dai-dai ya zama surukin sarki.
\s5
\v 27 Kafin waɗanan kwanaki su wuce, Dauda ya tafi tare da mazajensa ya kumakashe Filistiyawa ɗari biyu. Dauda ya dawo da fatar loɓarsu, sai aka miƙa su cikakku ga sarki, domin ya zama surukin sarki. Sai Saul ya ba Dauda Mikal ɗiyarsa ta zama matarsa.
\v 28 Da Saul ya gani, ya kuma sasance da cewa Yahweh na tare da Dauda, kuma Mikal, ɗiyar Saul, ta ƙaunace shi,
\v 29 Saul ya ƙara jin tsoron Dauda. Saul ya ci gaba da zama magabcin Dauda.
\s5
\v 30 Sai sarakunan Filistiyawa suka fito domin yaƙi, kamar dai yadda suke fitowa, hakannan Dauda ya ke nasara fiye da dukkan bayin Saul, har sunansa ya zama abin girmamawa.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Saul ya cewa Yonatan ɗansa da kuma dukkan bayinsa cewa su kashe Dauda. Amma Yonatan, ɗan Saul, ya yi fahariya da Dauda.
\v 2 Saboda haka Yonatan ya gaya wa Dauda, "Saul mahaifina na neman yakashe ka. Saboda hakaka yi zaman tsaro da safe ka kuma ɓoye kanka a boyayyen wuri.
\v 3 Zan fita in tsaya kusa da mahaifina cikin fili a indakake, zan kuma yi magana da mahaifina game dakai. Idan na ji wani abu akanka, zan gaya maka."
\s5
\v 4 Yonatan ya yi maganar alheri game da Dauda ga Saul mahaifinsa ya kuma ce masa, "Bari kada sarki ya yi laifi ga bawansa Dauda. Gama ba ya yi maka laifi ba, kuma ayyukansa masu kyau sun kawo maka alheri.
\v 5 Gama ya ɗauki ransa cikin hannunsa ya kumakashe Bafilisten. Yahweh yakawo babbar nasara ga dukkan Isra'ila. Ka gani ka kuma yi murna. Donme zaka yi zunubi ga jinin marar laifi da zakakashe Dauda babu dalili?"
\s5
\v 6 Saul ya saurari Yonatan. Saul ya rantse, "Har ga Allah, ba zai kashe shi ba."
\v 7 Sai Yonatan ya kira Dauda, sai kuma Yonatan ya gaya masa dukkan waɗannan abubuwan. Yonatan kuma yakawo Dauda wurin Saul, yana kuma tsayawa a gabansakamar dã.
\s5
\v 8 Sai aka sake yin yaƙi, Dauda kuma ya fita ya yi faɗa da Filistiyawa ya kuma ci nasara da su da babbar hallaka. Suka gudu daga fuskarsa.
\v 9 Wani mugun ruhu daga wurin Yahweh ya saukar wa Saul da ya ke zaune a gidansa da mashinsa cikin hannunsa, kuma yayin da Dauda ke kaɗakayan kiɗinsa.
\s5
\v 10 Saul ya yi koƙarin tsire Dauda har ga bango da mashinsa, amma ya tsere daga gaban Saul, har Saul yakafe mashin cikin bangon. Dauda ya gudu ya tsere a wannan dare.
\v 11 Saul ya aika da manzanni zuwa gidan Dauda su kula da shi domin yakashe shi da safe. Mikal, matar Dauda, ta ce masa, "Idan baka ceci ranka a wannan daren ba, gobe za akashe ka."
\s5
\v 12 Saboda haka Mikal ta zura Dauda ta tãga. Ya tafi ya gudu, ya tsere.
\v 13 Mikal ta ɗauki gunkin gida ta ajiye bisa gado. Sai ta sanya matashin kai na gashin akuya akansa, ta kuma rufe shi dakayayyaki.
\s5
\v 14 Da Saul ya aika 'yan saƙo su ɗauko Dauda, ta ce, "Yana barci."
\v 15 Sai Saul ya aika 'yan saƙo su ga Dauda; ya ce, "Ku kawo mani shi akan gadon, domin in kashe shi."
\s5
\v 16 A lokacin da 'yan saƙon suka shigo ciki, gashi, gunkin gida na bisakan gado bisa matashin kai mai gashi na ɗan rago a bisakansa.
\v 17 Saul ya cewa Mikal, "Donme ki ka ruɗe ni har ki ka bar makiyina ya tafi, har ya tsira?" Mikal ta amsa wa Saul, "Ya ce mani, 'Bar ni in tafi. Donme zan kashe ka?"
\s5
\v 18 Yanzu Dauda ya gudu ya kuma tsira, ya tafi wurin Sama'ila a Rama ya kuma gaya masa dukkan abin da Saul ya yi masa. Sa'annan shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot.
\v 19 Aka gaya wa Saul, cewa, "Duba, Dauda na Nayot cikin Rama."
\v 20 Sai Saul ya aika da 'yan saƙo su kamo Dauda. Da suka ga taron annabawa na annabci, Sama'ila kuma na tsaye a matsayin shugabansu, sai Ruhun Allah ya sauko bisa 'yan saƙon Saul, sai su ma suka yi annabci.
\s5
\v 21 Da aka gaya wa Saul wannan, sai ya aika da wasu 'yan saƙon, sai suma suka yi anabci. Sai Saul ya sake aikawa da wasu 'yan saƙo kãro na uku, sai suma suka yi anabci.
\v 22 Sai shi ma ya tafi Rama ya zo wurin rijiya mai zurfi da ke a Seku. Ya yi tambaya, "Ina Sama'ila da Dauda?" Wani ya ce, "Duba, suna a Natot cikin Rama."
\s5
\v 23 Saul ya tafi Nayot a Rama. Sai Ruhun Allah ya sauko bisansa, yayin da ya ke tafiya ya yi ta anabci har ya iso Nayot a Rama.
\v 24 Ya tuɓe rigunansa ya kuma yi anabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta tsirara dukkan rana da dukkan dare. Shi yasa suke tambaya, "Wai Saul na ɗaya daga cikin annabawa ne?"
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sai Dauda ya gudu daga Nayot a Rama ya kuma zo ya cewa Yonatan, "Me na yi? Mene ne laifina? Mene ne zunubina ga mahaifinka, da ya ke neman ɗaukan raina?"
\v 2 Yonatan ya cewa Dauda, "Sam ba haka ba ne; ba zaka mutu ba. mahaifina ba ya yin wani abu mai girma ko ƙanƙani ba tare da ya gaya mani ba. Donme mahaifina zai ɓoye mani wannan abu daga gare ni? Ba haka ba ne."
\s5
\v 3 Duk da haka Dauda ya sake rantsuwa kuma ce, "Mahaifinka ya san da cewar na sami tagomashi a idanunka. Dama ya ce, 'Kada a bari Yonatan ya san wannan, don kada ya damu.' Amma tabbas tun da Yahweh na raye, kumakamar yaddakaimaka ke rayuwa, rãtakaɗan ne tsakani na da mutuwa."
\s5
\v 4 Sai Yonatan ya cewa Dauda, "Duk abin daka ce, zan yi maka."
\v 5 Dauda ya cewa Yonatan, "Gobe ne sabon wata, kuma yakamata in zauna wurin cin abinci da sarki. Ammaka bar ni in tafi, domin in ɓoye kaina cikin saura har kwana na uku da yamma.
\s5
\v 6 Idan mahaifinka ya damu game da ni sarai, sai kace, 'Dauda ya nemi izini daga wajena domin ya tafi Betlehem birninsa. Domin lokacin hadaya ta shekara ce ga dukkan dangin.'
\v 7 Idan ya ce, 'lafiya lau,' bawanka zai sami salama. Amma idan ya husata ƙwarai, to ka sani ya ƙudurci aikata mugunta.
\s5
\v 8 Saboda hakaka kyauta wa bawanka. Gamaka jawo bawanka cikin alƙawari na Yahweh tare dakai. Amma idan akwai zunubi cikina, kakashe ni dakanka; gama mene ne dalilin da zai saka kawo ni ga mahaifinka?"
\v 9 Yonatan ya ce, "Sam haka ba zai yiwu ba! Idan na gane mahaifina yana da niyyar cutar dakai, ba zan gaya maka ba?"
\s5
\v 10 Sai Dauda ya cewa Yonatan, "wane ne zai gaya mani idan ya zama cewa mahaifinka ya amsa maka da faɗa?"
\v 11 Yonatan ya cewa Dauda, "Zo, mu tafi cikin saura." Sai suka tafi cikin saura tare su biyu.
\s5
\v 12 Yonatan ya cewa Dauda, "Bari Yahweh, Allah na Isra'ila, ya zama shaida. A lokacin da zan tambayi mahaifina gobe war haka, ko rana ta uku, duba, idan akwai shirin alheri game da Dauda, ba zan aika gare ka in kuma sanar dakai ba?
\v 13 Idan ya gamshi mahaifina da ya cutar dakai, bari Yahweh ya yi wa Yonatan har fiye kuma idan ban sanar dakai in kuma sallame kaka tafi ba, domin ka tafi cikin salama. Bari Yahweh yakasance tare dakai, kamar yadda ya ke tare da mahaifina.
\s5
\v 14 Idan ina nan da rai, ba zaka nuna mani amintaccen alƙawarin Yahweh ba, domin kada in mutu?
\v 15 Kadaka datse amintaccen alƙawarinka daga gidana har abada- koda Yahweh ya datse kowanne magabcin Dauda daga fuskar ƙasa.
\v 16 Saboda haka Yonatan ya yi alƙawari da gidan Dauda ya kuma ce, "Bari Yahweh ya nemi lissafi daga hannun magabtan Dauda."
\s5
\v 17 Yonatan yasa Dauda ya yi rantsuwa kuma domin ƙaunar da ya ke kaunarsa, gama yanakaunarsakamar yadda ya ke kaunar ransa.
\v 18 Sai Yonatan ya ce masa, "Gobe ne sabon wata. Za a yi kewarka domin mazauninka zai zama babu kowa.
\v 19 Bayan ka zauna can har kwana uku, sai ka sake komawa can indaka ɓoye kanka a lokacin da al'amuran ke ci gaba, ka tsaya kusa da dutsen Ezel.
\s5
\v 20 Zan harba kibiyoyi uku gefensa, kamar ina auna inda nakeso in harba.
\v 21 Daga nan zan aika ɗan matashina in kuma ce masa, 'Tafi ka nemo kibiyoyin.' Idan na cewa ɗan yaron, 'Duba, kibiyoyin suna wannan gefenka; nemo su."; sai ka zo; gama akwai kariya dominka kuma ba cutarwa, na rantse da ran Yahweh.
\s5
\v 22 Amma idan na ce wa matashin, 'Duba, kibiyoyin suna can gaba dakai,' sai ka yi tafiyarka, gama Yahweh ya sallame ka.
\v 23 Amma batun alƙawarin da ni dakai mu ka furta, gama, Yahweh na tsakani na dakai har abada."
\s5
\v 24 Sai Dauda ya ɓoye kansa cikin saura. Lokacin da sabon wata ya fito, sarkin ya zauna domin cin abinci.
\v 25 Sarkin ya zauna a bisa kujerarsa, yadda ya saba, a bisa kujera ta jikin bango. Yonatan ya tashi, Abna kuma ya zauna ta gefen Saul. Amma kujerar Dauda babu kowa.
\s5
\v 26 Duk da haka Saul baya ce komai ba wannan rana, domin ya yi tunani, "Wani abin ne ya faru da shi. Ba shi da tsarki; tabbas ba shi dai da tsarki."
\v 27 Amma a rana ta biyu, ranar bayan sabon wata, wurin zaman Dauda babu kowa. Saul ya cewa Yonatan ɗansa, "Me yasa ɗan Yesse bai zo ya ci abinci jiya da yau ba?"
\s5
\v 28 Yonatan ya amsa wa Saul, "Dauda ya nemi izini sosai daga wurina domin ya tafi Betlehem.
\v 29 Ya ce, 'Na roƙe ka. Gama iyalina na da hadaya a birni, kuma ɗan'uwana ya umarce ni da in kasance. Yanzu, idan na sami tagomashi a idanunka, Na roƙe ka bari in je in ga 'yan'uwana. Saboda wannan dalili yasa bai zo kujerar sarki ba."
\s5
\v 30 Sai haushin Saul ya yi ƙuna bisa Yonatan, ya kuma ce masa, "Kai ɗan lalatacciya, mace mai tayarwa! Ashe ban sani baka zaɓi ɗan gidan Yesse ga kunyarka, ga kuma kunyar tsiraicin mahaifiyarka?
\v 31 Idan har ɗan Yesse na a raye a ƙasar, ko kai ko mulkinka ba zai kafu ba. To yanzu, ka aika akawo shi gare ni, gama dole ne ya mutu."
\s5
\v 32 Yonatan ya amsa wa mahaifinsa, "Da wane dalili za akashe shi? Me ya yi?"
\v 33 Sai Saul ya jefa mashinsa don yakashe shi. Sai Yonatan ya gane cewa mahaifinsa ya ƙudurta yakashe Dauda.
\v 34 Yonatan ya tashi ya bar teburin cikin hasalar fushi baya kuma ci abinci ba a rana ta biyu ga watan, gama yana baƙinciki saboda Dauda, domin mahaifinsa ya wulaƙanta shi.
\s5
\v 35 Da safe, Yonatan ya fita zuwa saura inda suka shirya su haɗu da Dauda, kuma ɗan saurayin na tare da shi.
\v 36 Ya cewa ɗan saurayin, "Ka yi gudu ka nemi kibiyoyin da na harba." Yayin da ɗan saurayin ya ruga, ya harba wata kibiyar gaba da shi.
\v 37 Lokacin da ɗan saurayin ya iso inda kibiyar da Yonatan ya harba ta sauka, Yonatan ya kira ɗan saurayin, ya ce, "Ba kibiyar na gabanka ba?"
\s5
\v 38 Sai Yonatan ya kirawo ɗan saurayin, "Yi sauri, hanzarta, kadaka tsaya!" Sai ɗan saurayin Yonatan ya tattara kibiyoyin ya dawo wurin ubangidansa.
\v 39 Amma ɗan saurayin bai san komai ba. Yonatan da Dauda ne kaɗai suka san zancen.
\v 40 Yonatan ya ba ɗan saurayin makamansa ya ce masa, "Tafi, kakai su cikin birnin."
\s5
\v 41 Ba da jimawa ba bayan tafiyar ɗan saurayin, Dauda ya fito daga bayan dutsen, ya kwanta fuskarsa ƙasa, ya durƙusa ƙasa har sau uku. Suka yi wa juna sumba da kuka tare, Dauda ya yi kuka sosai.
\v 42 Yonatan ya cewa Dauda, "Ka tafi cikin salama, gama mu biyu mun rigaya mun rantse da sunan Yahweh muka kuma ce, 'Bari Yahweh yakasance tsakanin kai da ni, kuma tsakanin zuriyata da zuriyarka, har abada."' Sa'an nan Dauda ya tashi tsaye ya tafi, Yonatan kuma ya koma cikin birnin.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Sa'an nan Dauda ya zo Nob domin ya ga Ahimelek babban firist. Ahimelek yazo domin ya taryi Dauda jikinsa na rawa ya kuma ce masa, "Donme kake kai kaɗai kuma babu wani tare dakai?"
\v 2 Dauda ya cewa Ahimelek babban firist, "Sarki ya aike ni wata hidima ya kuma ce da ni, 'Kada kowa yasan komai game da abin nan da na aike ka, da kuma abin da na umarce ka.' Na aike 'yan matasan wani wurin.
\s5
\v 3 Yanzu dai me kake da shi a hannu? Ba ni 'yar gurasa guda biyar, ko duk abin da ke samuwa."
\v 4 Firist ya amsa wa Dauda ya kuma ce, "Babu gurasa da ba a tsarkake ba, amma akwai gurasa mai tsarki- Idan 'yan samarin sun keɓe kansu daga mata."
\s5
\v 5 Dauda ya amsa wa firist, "Tabbas mata sun yi nisa da mu tun kwana uku da suka wuce, kamar yadda ya ke idan na fita. Abin da ke na mazajen an keɓe su har ma game da ɗan ƙanƙanin hidimomi. Balle irin wannan na yau lalle duk abin da suke da shi za a keɓe!"
\v 6 Saboda haka sai firist ya ba shi gurasa da aka keɓe. Gama babu wata gurasa a wurin sai dai gurasar bagadi, wadda aka cire daga wurin Yahweh, domin ya sanya gurasa mai zafi a wurinta a ranar da aka ɗauke ta.
\s5
\v 7 Yanzu dai ɗaya daga cikin bayin Saul yana nan a wannan rana, tsararre a gaban Yahweh. Sunansa Doweg mutumin Idom, shugaban makiyayan Saul.
\s5
\v 8 Dauda ya cewa Ahimelek, "Yanzu babu wani mashi ko takobi? Domin ban kawo takobi ko makamaina tare da ni ba, domin hidimar sarki na buƙatar hanzari."
\v 9 Firist ya ce, "takobin Goliyat Bafiliste, wandaka kashe a cikin kwarin Ila, tana nan nannaɗe cikin kaya a bayan falmara. Idan kana so ka ɗauki wannan, ka ɗauke ta, gama babu wani makami a nan." Dauda ya ce, "Babu wata takobi irin wannan; ba ni ita."
\s5
\v 10 Dauda ya tashi ya gudu daga wurin Saul a wannan rana ya kuma tafi wurin Akish, sarkin Gat.
\v 11 Bayin Akish suka ce masa, "Ba wannan ba ne Dauda, sarkin ƙasar? Ba sun yi waƙa da rawa ga juna dominsa ba, 'Saul yakashe nasa dubbai, Dauda kuma yakashe nasa dubbai goma?"
\s5
\v 12 Dauda ya ajiye waɗannan maganganu cikin zuciyarsa yana kuma jin tsoran Akish, sarkin Gat.
\v 13 Sai ya canza yanayinsa ya yi kamar marar hankali cikin hannuwansu; sai ya yi alamomi a bisa ƙofofin kyamaren ya kuma bar yawu na zubowa ƙasa zuwa gemunsa.
\s5
\v 14 Sai Akish ya cewa bayinsa, "Duba, ku ga mutumin na hauka. Donme kukakawo shi wurina?
\v 15 Ko na rasa mahaukatan mutane ne, har da zaku kawo mani wannan talikin yana yin wannan hali a gabana? Anya wannan taliki zai shigo cikin gidana?"
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Sai Dauda ya bar can ya kuma tsere zuwa ƙogon Adullam. A lokacin da 'yan'uwansa da dukkan gidan mahaifinsa suka ji haka, sai suka gangara zuwa wurinsa.
\v 2 Duk wanda ke cikin ƙunci, da duk wanda ke cikin bãshi, da kuma marar jin daɗi-dukkansu suka taru wurinsa. Dauda ya zama shugabansu. An sami mazaje kamar ɗari huɗu tare da shi.
\s5
\v 3 Sai Dauda ya bar wurin zuwa Mizfa cikin Mowab. Ya cewa sarkin Mowab, "Na roƙe kaka bar mahaifina da mahaifiyata su zauna dakai har sai na san abin da Allah zai yi mani."
\v 4 Sai ya bar su tare da sarkin Mowab. Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka zauna tare da shi dukkan kwanakin da Dauda ke cikin sansaninsa.
\v 5 Sai annabi Gad ya cewa Dauda, "Kadaka tsaya a sansaninka. Tashi ka kuma shiga cikin ƙasar Yahuda." Sai Dauda ya bar wurin ya kuma tafi cikin jejin Heret.
\s5
\v 6 Saul ya ji cewa an ga Dauda, tare da mutanen da ke tare da shi. A yanzu dai Saul yana a Gibiya ƙarƙashin itaciyar tamarisk a Rama, da mashinsa a hannu, kuma dukkan bayinsa na tsaye zagaye da shi.
\s5
\v 7 Saul ya cewa bayinsa da ke tsaye zagaye da shi, "Ku saurara yanzu, mutanen Benyamin! Ko ɗan Yesse zai ba kowannenku filayen zaitun ne? Zai maida ku dukka shugabannin dubbai da shugabannin ɗari,
\v 8 domin misanyar dukkan ku don tayar mani? Babu wani daga cikin ku da ya gaya mani lokacin da ɗa na ya yi alƙawari da ɗan Yesse. Babu waninku da ya ji tausayi na. Babu waninku da ya gaya mani cewar ɗana ya zuga bawana Dauda gãba da ni. Yau ya ɓoye yana jirana domin su kai mani farmaki."
\s5
\v 9 Sai Doweg mutumin Idom, wanda ya tsaya kusa da bayin Saul, ya amsa, "Na ga ɗan Yesse ya iso Nob, wurin Ahimelek ɗan Ahitub.
\v 10 Ya yi addu'a ga Yahweh don ya taimake shi, kuma ya bashi guziri da kuma takobin Goliyat Bafiliste."
\s5
\v 11 Sai sarki ya aiki wani domin yakawo Ahimelek Firist ɗan Ahitub da dukkan gidan mahaifinsa, su firistocin da ke a Nob. Dukkansu suka zo wurin sarkin.
\v 12 Saul ya ce, "Saurara yanzu, ɗan Ahitub." Ya amsa, "Ga ni nan, ubangidana."
\v 13 Saul ya ce masa, "Donme ka yi mani makirci, kai da ɗan gidan Yesse, har ka ba shi gurasa, da takobi, ka kuma yi addu'a ga Allah domin ya taimake shi, domin ya tayar mani, ya ɓoye a asirce, kamar yadda ya ke yi a yau?"
\s5
\v 14 Sai Ahimelek ya amsa wa sarki ya kuma ce, "Wane ne cikin dukkan bayinka da ke amintacce kamar Dauda, wanda ya ke surukin sarki kuma shugaba bisa 'yan tsaro, kuma ana girmama shi cikin gidanka?
\v 15 Yau ne na fara yi masa addu'a Allah ya taimake shi? Nesa da ni! Kada sarki ya sanya wa bawansa wani laifi ko ga dukkan gidan mahaifina. Gama bawanka bai san komai ba game da wannan batu."
\s5
\v 16 Sarki ya amsa, "Dole ka mutu, Ahimelek, kai da gidan mahaifinka."
\v 17 Sarki ya cewa mai tsaron da ke tsaye kusa da shi, "Ka juyaka kashe firistocin Yahweh. Domin hannunsu na tare da Dauda, kuma domin sun san ya gudu, amma ba su gaya mani ba." Amma bayin sarkin ba su iya ɗibiya hannunsu su kashe firistocin Yahweh ba.
\s5
\v 18 Sa'an nan ya cewa Doweg, "Juyaka kashe firistocin." Sai Doweg Ba-Idome ya juya ya fãɗawa firistocin; yakashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke yafe da falmarar linin a wannan rana.
\v 19 Dakaifin takobi, ya abkawa Nob, birnin firistocin, mazaje da mataye, yara da jarirai, kuma bijimai da jakai da tumakai yakashe su dukka dakaifin takobi.
\s5
\v 20 Amma ɗaya daga cikin 'ya'yan Ahimelek ɗan Ahitub, mai suna Abiyata, ya tsere ya gudu zuwa wurin Dauda.
\v 21 Abiyata ya gaya wa Dauda cewar Saul yakashe firistocin Yahweh.
\s5
\v 22 Dauda ya cewa Abiyata, "Na sani a wannan ranar, da Doweg Ba-Idome ke wajen, zai faɗa wa Saul. Ni ke da laifi domin mutuwar kowanne a cikin iyalin mahaifinka!
\v 23 Ka zauna tare da ni kumakadaka ji tsoro. Gama wanda ya ke neman ranka shi ke neman nawa kuma. Zaka zauna lafiya tare da ni."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Aka gaya wa Dauda, "Ga shi, Filistiyawa na yaƙar Keila kuma suna washe wurin shiƙar hatsi."
\v 2 Sai Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako ya kuma tambaye shi, "Ko na tafi in kai wa waɗannan Filistiyawan farmaƙi? Yahweh ya cewa Dauda, "Tafi kakai wa Filistiyawa farmaƙi ka ƙubutar da Keila."
\s5
\v 3 Mazajen Dauda suka ce masa, "Duba, muna jin fargaba a nan Yahuda. Balle wai har mu tafi Keila Gãba da rundunar Filistiyawa?"
\v 4 Sai Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako kuma. Yahweh ya amsa, "Ka tashi, gangara zuwa Keila. Gama zan baka nasara a bisa Filistiyawan."
\s5
\v 5 Dauda da mutanensa suka tafi Keila suka kuma yi yaƙi da Filistiyawa. Ya kora garkunansu ya kuma buga su da babban yanka. Da haka Dauda ya kuɓutar da mazaunan Keila.
\v 6 Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek ya gudu zuwa wurin Dauda a Keila, ya zo da falmara a hannunsa.
\s5
\v 7 Aka gaya wa Saul cewa Dauda ya tafi Keila. Saul ya ce, "Allah ya ba da shi cikin hannuna. Gama yana tsare domin ya shiga cikin birnin da ke da ƙofofi da ƙyamare."
\v 8 Saul ya tattara dukkan rundunarsa domin yaƙi, don ya gangara zuwa Keila, don ya kewaye Dauda da mutanensa.
\v 9 Dauda na sane da cewar Saul na ƙulla cuta gãba da shi. Ya cewa Abiyata firist, "Kawo falmara nan."
\s5
\v 10 Sai Dauda ya ce, "Yahweh, Allah na Isra'ila, bawanka tabbas ya ji cewa Saul na shirin zuwa Keila, ya lallatar da birnin sabili da ni.
\v 11 Mutanen Keila zasu bashe ni cikin hannunsa? Saul zai gangaro, kamar yadda bawanka ya ji? Yahweh, Allah na Isra'ila, na roƙe ka, ka gaya wa bawanka." Yahweh ya ce, "Zai gangaro ya zo."
\s5
\v 12 Sai Dauda ya ce, "Mutanen Keila zasu miƙa ni da mazaje na cikin hannun Saul?" Yahweh ya ce, "Zasu miƙaka."
\s5
\v 13 Sai Dauda tare da mazajensa, da suke kamar ɗari shida, suka tashi suka fita daga Keila, suka kuma tafi daga wancan wuri zuwa wancan wurin. Aka gaya wa Saul da cewar Dauda ya kubce daga cikin Keila, daga nan kuma ya fãsa bin sa.
\v 14 Dauda ya zauna cikin ƙarfafan wuraren tsaro cikin jeji, a cikin ƙasar duwatsu cikin hamada ta Zif. Saul ya nace da nemansa kowacce rana, amma Allah bai miƙa shi cikin hannunsa ba.
\s5
\v 15 Dauda yaga cewar Saul ya fito neman ransa; a yanzu dai Dauda na cikin Hamadar Zif a Horesh.
\v 16 Sa'an nan Yonatan, ɗan Saul, ya tashi ya tafi wurin Dauda a Horesh, ya kuma ƙarfafa hannunsa cikin Allah.
\s5
\v 17 Ya ce masa, "Ka daka ji tsoro. Gama hannun Saul mahaifina ba zai same ka ba. Zaka zama sarki bisa Isra'ila, ni kuma zan zama na kusa dakai. Saul mahaifina shi ma ya san da haka."
\v 18 Suka yi alƙawari a gaban Yahweh. Dauda ya zauna a Horesh, Yonatan kuma ya tafi gida.
\s5
\v 19 Sai Zifiyawa suka zo wurin Saul a Gibiya suka ce, "Ba a wurinmu Dauda ya ke ɓuya ba cikin ƙarfafan wuraren tsaro na Horesh, a bisa tudun Hakila, wanda ya ke kudu da Yeshimon?
\v 20 Yanzu ka zo, sarki! Bisa ga buƙatarka, ka zo! Namu fannin shi ne mu miƙa shi a hannun sarki."
\s5
\v 21 Saul ya ce, "Bari Yahweh ya albarkace ku. Gama kun ji tausayina.
\v 22 Ku tafi, ku tabbatar da hakan. Ku lura ku gane inda ya ke ɓuya da kuma wane ne ya gan shi a wurin. An gaya mani cewa yana da wayau ƙwarai.
\v 23 Sai ku lura, ku kuma fahimci dukkan wuraren da ya ke ɓoye kansa. Ku dawo gare ni da tabbataccen zance, sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana cikin ƙasar, zan binciko shi waje daga dukkan dubban Yahuda."
\s5
\v 24 Sai suka tashi suka riga Saul zuwa Zif. Yanzu Dauda da mazajensa suna a cikin hamadar Mawon, a cikin Araba zuwa Kudu da Yeshimon.
\v 25 Saul da mutanensa suka tafi neman shi. Amma aka gaya wa Dauda wannan, sai ya tafi zuwa tudun duwatsu ya kuma zauna a hamadar Mawon. Lokacin da Saul ya ji, ya runtumi Dauda zuwa hamadar Mawon.
\s5
\v 26 Saul ya bi ta wancan sashen tudun, Dauda kuma da mazajensa na tafiya a wancan sashen tudun. Dauda ya hanzarta ya guje wa Saul. Da Saul da mutanensa na kewaye da Dauda da mazajensa don su kama su,
\v 27 sai ɗan saƙo ya iso wurin Saul ya kuma ce, "Hanzartaka kuma zo, gama Filistiyawa sun kawo hari a ƙasar."
\s5
\v 28 Saboda haka Saul ya komo daga bin Dauda ya kuma tafi gãba da Filistiyawa. Saboda haka ake kiran wurin Dutsen Tsira.
\v 29 Dauda ya tafi daga nan ya kuma zauna cikin ƙarfafan wuraren tsaro na Engedi.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Lokacin da Saul ya komo daga bin Filistiyawa, aka gaya masa, "Dauda na cikin Hamadar Engedi."
\v 2 Sai Saul ya ɗauki mazaje zaɓaɓɓu dubu uku daga dukkan Isra'ila ya tafi neman Dauda da mazajensa a bisa Duwatsu na Awakin jeji.
\s5
\v 3 Ya zo wurin mazamnin awakai nakan hanya, a inda akwai kogo. Saul ya shiga ciki don ya rufe ƙafarsa. Yanzu Dauda da mazajensa na zama a can ƙarshen ƙurewar kogon.
\v 4 Mazajen Dauda suka ce masa, "Wannan ita ce ranar da Yahweh ya yi magana da ya ce maka, 'Zan bã da maƙiyanka cikin hannunka, don ka yi masa duk abin daka ga dama."' Sai Dauda ya tashi a hankali yana tafiya gaba a rarrafe ya kuma yanko sashen rigar Saul.
\s5
\v 5 Daga baya sai zuciyar Dauda ta dame shi domin ya yagi sashen rigar Saul.
\v 6 Ya cewa mazajensa, "Yahweh ya sauwaƙe da yiwa ubangidana haka, shafaffen Yahweh, har da zan miƙa hannu gãba da shi, ganin cewar shafaffe ne na Yahweh."
\v 7 Don haka sai Dauda ya tsauta wa mazajensa da waɗannan maganganu, kuma bai bar su su kai wa Saul farmaƙi ba. Saul ya tashi, ya fita daga cikin kogon, yakama hanyarsa.
\s5
\v 8 Bayan haka, Dauda shi ma ya tashi, ya fita daga cikin kogon, ya yi kira ga Saul: "Ubangidana sarki." Lokacin da Saul ya waiga bayansa, sai Dauda ya rusuna da fuskarsa ƙasa ya nuna masa bangirma.
\v 9 Dauda ya ce wa Saul, "Me yasakake sauraron mutanen da ke cewa, 'Duba, Dauda yana neman ya cutar dakai?'
\s5
\v 10 Yau ka ga yadda Yahweh ya miƙaka cikin hannuna sa'ad da muke a cikin kogon. Wasu suka ce mani in kashe ka, amma na bar ka. Na ce, 'Ba zan miƙa hannuna gãba da ubangidana ba; gama shafaffe ne na Yahweh.'
\v 11 Duba, mahaifina, dubi sashen rigarka a hannuna. Ai ko yadda na yanki sashen rigarka amma ban kashe ka ba, kana iya fahimta da ganin cewa babu wata mugunta ko makirci cikin hannuna, kuma ban yi maka zunubi ba, ko da ya ke kana neman rainaka ɗauke.
\s5
\v 12 Bari Yahweh ya shar'anta tsakanina dakai, kuma bari Yahweh ya sãka mani gãba dakai, amma hannuna ba zai tayar maka ba.
\v 13 Kamar yaddakarin maganar mutanen dã ke cewa, 'Daga cikin mugu mugunta ke fitowa.' Amma hannuna ba za ya tayar maka ba.
\s5
\v 14 Wane ne sarki ke fita neman sa? Wane ne kake kora? Mataccen kare! Wofi!
\v 15 Bari Yahweh ya zama mai shari'a ya kuma shar'anta tsakani na dakai, ya kuma tabbatar, ya kuma tsaya mani ya kuma sa in tsira daga hannunka."
\s5
\v 16 Bayan da Dauda ya gama furta waɗannan maganganun ga Saul, Saul ya ce, "Muryarka ce wannan, ɗana Dauda?" Saul ya tãda muryarsa ya yi kuka.
\s5
\v 17 Ya ce wa Dauda, "Kai mai adalci ne fiye da ni. Gamaka sake biya na da alheri, inda na maido maka mugunta.
\v 18 Ka furta yau yaddaka yi mani alheri, gama baka kashe ni ba lokacin da Yahweh ya miƙa ni ga jinƙanka.
\s5
\v 19 Domin idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Bari Yahweh ya sãka maka da alheri yaddaka yi mani a yau.
\v 20 Yanzu, na sani tabbas zaka zama sarki kuma sarautar Isra'ila zatakafu a hannunka.
\s5
\v 21 Ka rantse mani har ga Yahweh cewar ba zaka datse zuriyata bayana ba, kuma ba zaka lallatar da sunana daga gidan mahaifina ba.
\v 22 Sai Dauda ya yi alƙawari ga Saul. Sa'an nan Saul ya tafi gida, amma Dauda da mazajensa suka haura zuwakagara mai ƙarfi.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Yanzu dai Sama'ila ya mutu. Dukkan Isra'ila suka taru tare suka kuma yi masa makoki, suka kuma binne shi a cikin gidansa a Rama. Sa'an nan Dauda ya tashi ya kuma tafi cikin hamadar Faran.
\s5
\v 2 Akwai wani mutum a Mawon, wanda dukiyarsa na cikin Karmel. Mutumin mai arziki ne ainun. Yana da tumakai dubu uku da awakai dubu ɗaya. Yana sausayar gashin tumakinsa akamel.
\v 3 Sunan mutumin Nabal, kuma sunan matarsa Abigel. Mata ce mai hikima da kyan gani. Amma mutumin mai zafin hali da mugun tafarki ne a al'amuransa. Shi daga zuriyar gidan Kaleb ne.
\s5
\v 4 Dauda ya ji daga cikin hamada cewa Nabal yana sausayar gashin tumakinsa.
\v 5 Don haka Dauda ya aika samari mutum goma. "Ku tafi zuwakamel, ku tafi wurin Nabal, ku gaishe shi da sunana.
\v 6 Za ku ce masa, 'Ka zauna cikin wadata. Salama gare ka salama ga gidanka, kuma salama ga dukkan mallakarka.
\s5
\v 7 Na ji cewakana da 'yan sausaya. Makiyayanka na tare da mu, kuma bamu cutar da su ba, basu kuma rasa komai ba cikin dukkan lokacin da suke akarmel.
\v 8 Ka tambayi samarinka, zasu kuma gaya maka. Yanzu bari 'yan samarina su sami tagomashi a idanunka, gama mun kawo ga ranar buki. Na roƙe kaka bã da duk abin dakake da shi a hannunka ga bayinka ga kuma ɗan ka Dauda."
\s5
\v 9 Lokacin da samarin Dauda suka iso, suka faɗi dukkan wannan ga Nabal a madadin Dauda suka kuma jira.
\v 10 Nabal ya amsa wa bayin Dauda, "Wane ne Dauda, kuma wane ne ɗan Yesse? Akwai bayi da yawa da ke ƙaurace wa iyayen gidansu a wannan kwanaki.
\v 11 To na ɗauki gurasata da ruwa na da namana da na yanka domin 'yan sausayata, in kuma bada su ga mutanen da ban san ko daga ina suke ba?"
\s5
\v 12 Saboda haka 'yan samarin Dauda suka juya suka tafi suka kuma dawo, suka kuma gaya masa duk abin da aka ce.
\v 13 Dauda ya cewa mazajensa, "Kowanne mutum ya ɗaura takobinsa." Sai kowanne mutum ya ɗaura takobinsa. Dauda shi ma ya ɗaura takobinsa. Mazajen wajen ɗari huɗu suka bi Dauda, ɗari biyu kuma suka tsaya wurin kayayyaki.
\s5
\v 14 Amma ɗaya daga cikin 'yan samarin ya gaya wa Abigel, matar Nabal; ya ce, "Dauda ya aiko da manzanni daga cikin hamada domin su gaishe da ubangidanmu, amma ya zage su.
\v 15 Kuma mazajen sun nuna mana alheri. Ba mu cutu ba kuma ba mu ɓatar da komai ba cikin dukkan tafiyar da muka yi da su lokacin da muke cikin filaye.
\s5
\v 16 Sun zama ganuwa a garemu da rana da dare, dukkan lokutan da muke tare da su muna kula da garken.
\v 17 Saboda haka ki san wannan ki kuma san abin da zaki yi, gama akwai shirin mugunta game da ubangidanmu, kuma gãba da dukkan gidansa. Shi mutum ne marar cancanta da ba mai iya shawartar sa."
\s5
\v 18 Sai Abigel ta tashi da sauri ta ɗauki gurasa curi ɗari biyu, inabi kwalba biyu, tumakai guda biyar gyararru, awo biyar na busasshen hatsi, da curin kauɗar inabi guda ɗari, da wainar 'ya'yan ɓaure guda ɗari biyu, ta ɗora su bisa jakai.
\v 19 Ta cewa matasanta, "Ku sha gabana, zan kuma bi ku a baya." Amma bata gaya wa mijinta Nabal ba.
\s5
\v 20 Yayin da take zuwa bisa jakinta ta kuma sauka daga bakin ƙofar dutsen, Dauda da shi da mazajensa suna saukowa zuwa gare ta, ta kuma tarbe su.
\s5
\v 21 Yanzu Dauda ya riga ya faɗa cewa, "Tabbas a banza na tsare dukkan mallakar wannan mutum cikin hamada, har babu abin da ya ɓace cikin dukkan abin da ke nasa, kuma sai ya sãka mani da mugunta.
\v 22 Bari Allah ya yi mani haka, Dauda, fiye da haka kuma, idan war haka da safe na bar ko da namiji ɗaya wanda ke nasa."
\s5
\v 23 Lokacin da Abigel ta ga Dauda, ta hanzarta ta sauko daga jakarta ta kuma kwanta a gaban Dauda da fuskarta ƙasa ta kuma rusunar dakanta zuwa ƙasa.
\v 24 Ta kwanta dab da ƙafafunsa ta kuma ce, "akainakaɗai, ubangidana, laifin yakasance. Na roƙe ka bari baiwarka ta yi magana dakai, ka kuma saurari maganganun baiwarka.
\s5
\v 25 Kada ubangidana ya kula da wannan talikin marar amfani, Nabal, gama yadda sunansa ya ke, haka ya ke. Nabal ne sunansa, kuma sakarci na tare da shi. Amma ni baiwarka ban ga 'yan samarin ubangidana ba, waɗandaka aiko.
\v 26 Yanzu dai, ubangidana, a bisa ran Yahweh, da kuma ranka, har tun da Yahweh ya tsare ka daga zubda jini, kuma daga ramuwa domin kanka da hannunka, yanzu bari maƙiyanka, da waɗanda ke neman yin mugunta ga ubangidana, su zamakamar Nabal.
\s5
\v 27 Yanzu bari wannan kyautar da baiwarka takawo ga ubangidana a ba 'yan samarin da ke biye da ubangidana.
\v 28 Na roƙe ka daka gafarta wa bawanka, gama Yahweh za ya gina wa ubangidana tabbataccen gida, domin ubangidana yana yaƙin Yahweh ne; kuma ba za a sami mugunta a cikinka ba dukkan kwanakin ranka."
\s5
\v 29 Koda shi ke mutane sun tashi neman ranka, duk da haka ran ubangidana za a kãre shi cikin taro na masu rai daga wurin Yahweh Allahnka; kuma za ya ɗauke rayukan maƙiyanka, kamar daga aljihu na majajjawa.
\s5
\v 30 Yahweh zai aiwatar wa ubangidana komai da ya alƙawarta maka, ya kuma zaɓe ka shugaba bisa Isra'ila.
\v 31 Wannan ba zai zama abin nauyi gare ka ba - cewaka zubar da jinin marar laifi, ko domin ubangidana na ƙoƙarin kuɓutar dakansa. Gama a lokacin da Yahweh zai yi wa ubangidana alheri, ka tuna da baiwarka."
\s5
\v 32 Dauda ya cewa Abigel, "Mai albarka ne Yahweh, Allah na Isra'ila, shi wanda ya aiko ki da kika same ni yau.
\v 33 Hikimarki mai albarka ce kuma ke mai albarka ce, domin kin tsare ni daga zubar da jini kuma daga rama wakaina da hannuna!
\s5
\v 34 A gaskiya, yadda Yahweh, Allah na Isra'ila, ke raye, shi wanda ya kiyaye ni daga cutar da ke, da ba domin kin yi sauri kin zo gare ni ba, da ba za a sami wani ragowa domin Nabal ko da ɗan jariri ne zuwa wayewar gari ba."
\v 35 Sai Dauda yakarɓi abin da takawo masa daga hannunta; ya ce ma ta, "Tafi cikin salama zuwa gidanki; duba, na saurari muryarki kuma na gamsu."
\s5
\v 36 Sai Abigel ta koma ga Nabal; gashi kuwa, ya shirya shagali a gidansa, kamar shagali na sarki; kuma zuciyar Nabal ta shagalta cikinsa, gama ya bugu ainun. Sai ta ƙi gaya masa komai har hasken safiya.
\s5
\v 37 Sai ya zamana da safe, lokacin da ƙarfin giya ya fita daga Nabal, sai matarsa ta gaya masa waɗannan abubuwan; zuciyarsa ta mutu cikinsa, sai ya zamakamar dutse.
\v 38 Sai ya zama bayan kwana goma sai Yahweh yakai wa Nabal farmaƙi har yakashe shi.
\s5
\v 39 Da Dauda ya ji cewa Nabal ya mutu, ya ce, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda ya ɗauki zargin zãgin da na sha daga hannun Nabal ya kuma kãre bawansa daga mugunta. Ya juyar da aikin muguntar Nabal bisakansa." Sai Dauda ya aika ya kuma yi magana da Abigel, domin ya ɗauke ta a matsayin matarsa.
\v 40 Lokacin da bayin Dauda suka iso wurin Abigel akarmel, suka yi mata magana suka ce, "Dauda ya aike mu gare ki mu ɗauke ki zuwa wurinsa ki zama matarsa."
\s5
\v 41 Ta tashi, ta sunkuyar dakanta zuwa ƙasa, ta kuma ce, "Duba, baiwarka baiwa ce da za ta wanke ƙafafun bayin ubangidana."
\v 42 Sai Abigel ta yi sauri ta tashi, ta hawo bisa jaka tare da bayi 'yanmata biyar da ke nata waɗanda suka biyo ta; sai kuma ta biyo bayin Dauda ta kuma zama matarsa.
\s5
\v 43 Yanzu dai Dauda ya ɗauko wakansa Ahinowam ta Jezril a matsayin matarsa; su biyu suka zama matansa.
\v 44 Haka kuma, Saul ya rigaya ya bayar da 'yarsa, matar Dauda, ga Falti ɗan Layish, wanda mutumin Galim ne.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Sai Zifiyawa suka zo wurin Saul a Gibiya suka kuma ce, "Ba Dauda yana ɓoyewa a cikin tudun Hakila ba, wanda ya ke kamin Yeshimon?"
\v 2 Sai Saul ya tashi ya kuma tafi zuwa hamada ta Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra'ila, domin neman Dauda a cikin hamadar Zif.
\s5
\v 3 Saul yakafa sansani a bisa tudun Hakila, wanda ke kafin Yeshimon, a gefen hanya. Amma Dauda na zama cikin hamadar, kuma ya ga cewa Saul na zuwa gare shi a cikin hamadar.
\v 4 Sai Dauda ya aiki 'yan leken asiri kuma ya fahimci cewa tabbas Saul ya zo.
\s5
\v 5 Dauda ya tashi ya kuma tafi wurin da Saul yakafa sansani; ya ga inda Saul ya kwanta, tare da Abna ɗan Nã, shugaban rundunarsa; Saul ya kwanta cikin sansanin, kuma mutanen suka zagaye shi, dukkansu suna barci.
\s5
\v 6 Sa'an nan Dauda ya cewa Ahimelek Bahittiye, kuma ga Abishai ɗan Zeruwa, ɗan'uwan Yowab, "Wane ne zai tafi da ni wurin Saul a cikin sansani?" Abishai ya ce, "Ni! Zan tafi tare dakai."
\v 7 Sai Dauda tare da Abishai suka tafi wurin rundunar cikin dare. Saul na barci cikin tsakiyar sansani tare da mãshinsakafe da ƙasa kusa dakansa. Abna da kuma sojojinsa suka kwanta zagaye da shi.
\v 8 Sai Abishai ya cewa Dauda, "Yau Allah ya miƙa maƙiyinka cikin hannunka. Yanzu na roƙe kaka bar ni in cake shi har ƙasa da mashi da bugu ɗaya tak. Ba zan cake shi sau biyu ba."
\s5
\v 9 Dauda ya cewa Abishai, "Kadaka hallaka shi; gama wane ne za ya miƙa hannunsa gãba da shafaffen Yahweh ya kuma zama marar laifi?"
\v 10 Dauda ya ce, "Na rantse da ran Yahweh, Yahweh zai kashe shi, ko kuma ranar mutuwarsa ta zo, ko kuma ya tafi yaƙi ya mutu.
\s5
\v 11 Bari Yahweh ya sauwaƙe mani da in miƙa hannuna gãba da shafaffe; amma yanzu, na roƙe ka, ka ɗauki mashin da ke kusa dakansa da kuma gorar ruwa, sai mu tafi."
\v 12 Sai Dauda ya ɗauke mashin da gorar ruwan da ke kusa dakan Saul, suka kuma tafi. Babu wanda ya gansu ko ya san komai game da haka, ko wani ya farka, gama duk sun yi barci, gama barci mai nauyi daga wurin Yahweh ya faɗo bisansu.
\s5
\v 13 Sa'an nan Dauda ya tashi ya tafi wancan ɓangaren ya kuma tsaya akan tsauni can nesa; akwai babbar rãta tsakaninsu.
\v 14 Dauda ya yi kira da ihu ga mutanen ga kuma Abna ɗan Nã; ya ce, "Baka amsa ba, Abna?" Sai Abna ya amsa ya ce, "Kai wane ne da ke yi wa sarki ihu?"
\s5
\v 15 Dauda ya cewa Abna, "Kai ba mutum ba ne mai ƙarfin hali? Wane ne kamarka a Isra'ila? To donme baka yi tsaron ubangidanka sarki ba? Gama wani ya shigo domin yakashe sarki ubangidanka.
\v 16 Wannan abin daka yi ba shi da kyau. Na rantse da ran Yahweh, ka cancanci ka mutu domin baka yi tsaron ran sarki ubangidanka ba, shafaffe na Yahweh. Yanzu ka duba inda mashi da gorar ruwa da ke kusa dakansa suke!"
\s5
\v 17 Saul ya sasance muryar Dauda ya kuma ce, "Wannan muryarka ce, ɗana Dauda?" Dauda ya ce, "Muryata ce, ubangidana, sarki."
\v 18 Ya ce, "Me yasa ubangidana ke neman bawansa? Me na yi? Wacce mugunta ce ke cikin hannuna?
\s5
\v 19 Yanzu saboda haka, na roƙe ka, bari ubangidana sarki ya saurari maganganun bawansa. Idan Yahweh ne ya zugaka gãba da ni, bari yakarɓi baiko; amma idan mutum ne, bari ya la'anta a fuskar Yahweh, gama yau sun kore ni waje, domin kada in manne wa gãdon Yahweh; sun ce mani, "Je ka yi sujada ga wasu alloli.'
\v 20 Saboda haka yanzu, kadaka bar jinina ya zuba nesa da fuskar Yahweh; gama sarkin Isra'ila ya fito neman ƙwaro ɗayakamar yadda wani ke fita farautar makwarwa a bisa duwatsu."
\s5
\v 21 Sai Saul ya ce, "Na yi zunubi. Dawo, Dauda, ɗana; domin ba zan ƙara cutar dakai ba, domin yau raina ya zama abin daraja a idonka. Duba, na yi kamar wawa kuma na yi mugun kuskure."
\s5
\v 22 Dauda ya amsa ya kuma ce, "Duba, mashin ka yana nan, sarki! Bari ɗaya daga cikin samarin ka ya zo yakarɓa yakai maka.
\v 23 Bari Yahweh ya sãka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa; domin Yahweh ya miƙaka cikin hannuna yau, amma ba zan bugi shafaffensa ba.
\s5
\v 24 Duba, kamar yadda ranka ke da daraja a idanuna yau, bari raina ya zama da daraja a fuskar Yahweh, kuma bari ya kuɓutar da ni daga dukkan wahala."
\v 25 Sai Saul ya cewa Dauda, "Bari ka yi albarka, Dauda ɗana! Lallai zaka yi manyan abubuwa kuma zaka yi nasara cikin dukkansu." Sai Dauda yakama hanyarsa, Saul kuma ya koma fadarsa.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Dauda ya faɗi a cikin zuciyarsa, "Wata rana zan hallaka ta hannun Saul; ba abin da ya fiye mani sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa; da haka Saul zai dena nema na cikin dukkan iyakar Isra'ila; ta haka zan kubce daga hannunsa."
\s5
\v 2 Dauda ya tashi ya tsallaka can, shi da mazajensa ɗari shida da ke tare da shi, wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat.
\v 3 Dauda ya zauna tare da Akish a Gat, shi da mazajensa, kowanne mutum da iyalansa, Dauda tare da matayensa biyu, Ahinowam Yeziriya, da kuma Abigel Bakameliya, matar Nabal.
\v 4 Da aka gaya wa Saul cewa Dauda ya tsere zuwa Gat, sai bai sãke neman sa ba.
\s5
\v 5 Dauda ya cewa Akish, "Idan na sami tagomashi a idanunka, bari su bani wuri cikin ɗaya daga cikin biranen ƙasar, domin in zauna nan: donme bawanka za shi zauna cikin masarauta tare dakai?"
\v 6 Sai Akish ya ba shi Ziklag a wannan rana; shi yasa Ziklag ta zama ta sarakunan Yahuda har wa yau.
\v 7 Shekarun da Dauda ya zauna cikin ƙasar Filistiyawa shekara ɗaya ce cikakkiya da wata huɗu.
\s5
\v 8 Dauda da mazajensa sukakaiwa wurare dabam dabam farmaƙi, suka hari Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa; gama waɗannan al'ummai su ne asalin mazaunan ƙasar, idan kana tafiya zuwa Shur, har zuwa ƙasar Masar. Suna zama a nan wurin tun zamanun dã.
\v 9 Dauda yakai wa ƙasar farmaƙi kuma bai bar namiji ko mace da rai ba; ya kwashi tumaki, da awakai, da jakuna, da raƙuma, da kumakayayyaki; sai ya dawo kuma zuwa Akish.
\s5
\v 10 Akish zai ce, "Gãba da su waye yau kakai hari?" Dauda zai amsa, "Gãba da kudancin Yahuda," ko "Gãba da kudancin Yeramiyawa," ko "Gãba da kudancin Keniyawa."
\s5
\v 11 Dauda bai bar namiji ko mace da rai domin yakawo su zuwa Gat ba, ya ce, "Sabodakada su yi magana game da mu, su ce 'Dauda ya yi kaza dakaza.'" Haka ya yi dukkan lokutan da ya ke zama a ƙasar Filistiyawa.
\v 12 Akish ya amince da Dauda, yana cewa, "Ya sa mutanensa Isra'ilawa suna ƙyamarsa; zai zama bawana har abada."
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Sai ya zama a wannan kwanaki Filistiyawa suka tara rundunar yaƙinsu domin yaƙi da Isra'ila. Akish ya cewa Dauda, "Ka san da cewar zaka fita tare da ni cikin runduna, kai da mazajenka."
\v 2 Dauda ya cewa Akish, "Da haka zaka san abin da bawanka zai iya aikatawa." Akish ya cewa Dauda, "Da haka zan maishe ka mai tsarona na din-din din."
\s5
\v 3 Yanzu dai Sama'ila ya mutu, kuma dukkan Isra'ila sun yi masa makoki suka kuma binne shi a Rama, a cikin birninsa. Haka kuma, Saul ya fanfari masu hurɗa da matattu ko da ruhohi.
\v 4 Sai Filistiyawa suka tarakansu wuri ɗaya suka zo sukakafa sansani a Shunem; Saul kuma ya tara dukkan Isra'ila tare, suka kumakafa sansani a Gilbowa.
\s5
\v 5 Lokacin da Saul ya ga rundunar Filistiyawa, sai ya ji tsoro, zuciyarsa kuma ta yi rawa sosai.
\v 6 Saul ya yi addu'a ga Yahweh domin taimako, amma Yahweh bai amsa masa ba - ko ta mafarki, ko da Urim, kuma wurin annabawa ba.
\v 7 Sai Saul ya cewa bayinsa, "Ku nemo mani mace wadda ta ke magana da matattu, domin in tafi wurinta in nemi shawararta." Bayinsa suka ce masa, "Duba, akwai wata mace a Endo wadda ta ke faɗin cewa tana magana da matattu."
\s5
\v 8 Saul ya ɓaddakama, ya sanya wasu kaya, ya tafi, shi da mutum biyu tare da shi; suka tafi wurin matar da dare. Ya ce, "Ki duba mani, na roƙe ki, da ruhu, ki kuma kirawo mani duk wanda na faɗi maki."
\v 9 Matar ta ce masa, "Duba, kasan dai abin da Saul ya yi, yadda ya kori waɗanda ke magana da matattu ko ga ruhohi. To me yasakake shirya wa raina tarko, ka sa ni in mutu?"
\v 10 Saul ya rantse mata har ga Yahweh ya kuma ce, "Na rantse da ran Yahweh, babu hukuncin da zai same ki domin wannan."
\s5
\v 11 Matar ta ce, "Wane ne kake so in kirawo maka?" Saul ya ce, "Kirawo mani Sama'ila."
\v 12 Da matar ta ga Sama'ila, sai tayi ihu da babbar murya ta kuma yi magana da Saul, cewa, "Donme ka ruɗe ni? Gamakai Saul ne."
\s5
\v 13 Sarkin ya ce ma ta, "Kada ki ji tsoro. Me kika gani?" Matar ta cewa Saul, "Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa."
\v 14 Ya ce mata, "Yayakamaninsa ya ke?" Ta ce, "Tsohon mutum yana haurowa sama; yana sanye dakaya." Saul ya gane cewa Sama'ila ne, sai ya faɗi ƙasa fuskarsa ƙasa ya kuma nuna bangirmansa.
\s5
\v 15 Sama'ila ya cewa Saul, "Donme ka dame ni har daka hauro da ni sama?" Saul ya amsa, "Na gaji sosai, Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni kuma ya ƙi ya amsa mani, ko ta wurin annabawa, ko ta mafarkai. Saboda haka na kirawo ka, domin ka sanar da ni abin da zan yi."
\s5
\v 16 Sama'ila ya ce, "Mene ne kake tambaya ta, tun da Yahweh ya bar ka, kuma ya zama abokin gãbarka?
\v 17 Yahweh ya aiwatar maka da abin da ya faɗa zai yi. Yahweh ya raba mulkin daga hannunka ya kuma bayar ga wani - ga Dauda.
\s5
\v 18 Domin bakayi biyayya da muryar Yahweh ba kuma baka aiwatar da fushinsa mai ƙuna bisa Amalekawa ba, shi kuma ya yi maka haka a wannan rana.
\v 19 Duk da haka, Yahweh zai miƙa Isra'ila dakai cikin hannuwan Filistiyawa. Gobe kai da 'ya'yanka maza zaku kasance tare da ni. Yahweh kuma za ya miƙa rundunar Isra'ila cikin hannuwan Filistiyawa."
\s5
\v 20 Sa'an nan Saul nan da nan ya faɗi da ƙarfinsa zuwa ƙasa da kuma fargaba saboda maganganun Sama'ila. Babu wani sauran ƙarfi a cikinsa, gama bai ci abinci ba dukkan yini, ko a wannan dare.
\v 21 Macen ta zo wurin Saul ta ga cewa yana cikin babbar damuwa, Ta ce masa, "Duba, baiwarka ta saurari muryarka; Na ɗibiya raina a cikin hannuwana na kuma saurari maganganun daka faɗi mani.
\s5
\v 22 Don haka yanzu, na roƙe ka, kai maka saurari muryar baiwarka macen, na kuma shirya maka abinci ɗan kaɗan a gabanka. Ka ci sabodaka maido da ƙarfi domin sa'ad da zakakama hanyarka."
\v 23 Amma Saul bai yarda ba ya kuma ce, "Ba zan ci ba." Amma bayinsa, tare da macen, suka nace masa, ya kuma saurari muryarsu. Saboda haka ya tashi daga ƙasa ya zaunakan gado.
\s5
\v 24 Matar tana da ɗan maraƙi mai ƙiba a cikin gidan; ta yi sauri ta yanka shi; ta ɗauki gari, ta cuɗa shi, ta kuma shirya gurasa da shi.
\v 25 Takawo ga Saul da bayinsa, suka kuma ci. Sa'an nan suka tashi suka kuma yi tafiyarsu a wannan daren.
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Yanzu Filistiyawa sun taru tare dukkan rundunarsu a Afek; Isra'ilawa suka yi sansani kusa da magudanar ruwa da ke cikin Yezril.
\v 2 Sarakunan Filistiyawa suka wuce a ɗari-ɗarinsu da kuma dubbai; Dauda da mazajensa suka wuce suna daga baya tare da Akish.
\s5
\v 3 Sai sarakunan Filistiyawa suka ce, "Mene ne wannan Ibraniyawan ke yi a nan?" AKish ya cewa sauran sarakunan Filistiyawan, "Ba wannan ba ne Dauda, bawan Saul, sarkin Isra'ila, wanda ke tare da ni kwanakin nan, ko ace waɗannan shekaru, kuma ban same shi da wani laifi ba tun ranar da ya zo wurina har wa yau?"
\s5
\v 4 Amma sarakunan Filistiyawa suka yi fushi da shi; suka ce masa, "Ka sa wannan mutum ya tafi, domin ya tafi wurin daka bashi, kadaka bar shi ya biyo mu zuwa filin dãga, domin kada ya juya ya zama maƙiyinmu cikin yaƙi. Don ta yaya wannan talikin zai yi sulhu da ubangidansa? Ba ta ɗaukar kawunan mutanen mu ba ne?
\s5
\v 5 Ba wannan ba ne Dauda wanda aka yi wa waƙa a junansu cikin rawa, cewa, 'Saul yakashe dubbansa, Dauda kuma yakashe nasa dubbai goma'?"
\s5
\v 6 Sai Akish ya kirawo Dauda ya kuma ce masa, "Na rantse da ran Yahweh, ka zama nagari, kuma fitarka da shigowarka tare da ni cikin runduna mai kyau ne a gani na; gama ban iske wani laifi gare ka ba tun randa ka zo wurina zuwa wannan rana.
\v 7 Sai ka juya yanzu ka kuma tafi cikin salama, domin kada ka yi wa sarakunan Filistiyawa laifi."
\s5
\v 8 Dauda ya cewa Akish, "Amma me na yi? Mene ne ka samu a cikin bawanka duk sa'ad da nake tare da kai zuwa wannan rana, da har ba zan je inyi yaƙi da maƙiyan ubangidana sarki ba?"
\v 9 Akish ya amsa ya kuma cewa Dauda, "Na san da cewa kai marar laifi ne a idanuna kamar mala'ikan Allah; duk da haka sarakunan Filistiyawa suka ce, 'Ba zai haura tare da mu ba zuwa yaƙin.'
\s5
\v 10 Saboda haka sai ka tashi da sassafe tare da bayin ubangidanka waɗanda suka zo tare da kai; da zarar ka tashi da asussuba ka kuma sami haske, ka tafi."
\v 11 Sai Dauda ya tashi da sauri, shi da mazajensa, don su tafi da safe, su dawo ƙasar Filistiyawa. Amma Filistiyawan suka haura zuwa Yezril.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Ya zama kuma, da Dauda da mazajensa suka iso Ziklag a rana ta uku, da Amalekawa suka kawo farmaki bisa Negeb da kuma kan Ziklag. Suka kai wa Ziklag hari, suka ƙona ta,
\v 2 suka kwashe matayen da kowa da ya ke ciki, da manya da ƙanana. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe suka yi tafiyarsu.
\s5
\v 3 Lokacin da Dauda da mazajensa suka iso birnin, an ƙone, kuma matayensu, da 'ya'yansu maza, da 'ya'yansu mata an ɗauke su zuwa bauta.
\v 4 Sa'an nan Dauda da mutanen da ke tare da shi suka tãda murya suka yi kuka har sai da babu wani sauran ƙarfi kuma da za su yi kuka.
\s5
\v 5 Aka kwashe matan Dauda guda biyu, Ahinowam Yeziriya, da Abigel matar Nabal mutumiyar Karmel.
\v 6 Dauda ya dãmu ƙwarai, gama mutanen suna magana game da su jefe shi da duwatsu, gama dukkan mutanen suna ɓacin rai, kowanne mutum domin 'ya'yansa maza da mata; amma Dauda ya ƙarfafa kansa cikin Yahweh, Allahnsa.
\s5
\v 7 Dauda ya cewa Abiyata ɗan Ahimelek, firist, "Na roƙe ka, ka kawo mani falmara a nan wurina." Sai Abiyata ya kawo falmarar wurin Dauda.
\v 8 Dauda ya yi addu'a ga Yahweh domin bishewa, cewa, "Idan na bi wannan mayaƙan, zan sha kansu?" Yahweh ya amsa, "Bi su, domin lallai za ka sha kansu, kuma tabbas za ka sake ƙwato dukkan abubuwan."
\s5
\v 9 Sai Dauda ya tafi, shi da mazajensa ɗari shida waɗanda ke tare da shi; suka iso magudanar Beso, inda waɗanda aka bari suka zauna.
\v 10 Amma Dauda ya ci gaba da runtumar su, shi da mazaje ɗari huɗu; gama ɗari biyu sun tsaya a baya, wato waɗanda ƙarfinsu ya gãza da baza su iya haurawa zuwa magudanar Beso ba.
\s5
\v 11 Suka gamu da wani Bamasare cikin saura suka kawo shi ga Dauda; suka ba shi gurasa, ya kuma ci; suka ba shi ruwa ya sha;
\v 12 sai kuma suka ba shi gutsuren wainar 'ya'yan ɓaure da curin kauɗar inabi guda biyu. Bayan da ya ci, ƙarfinsa ya dawo kuma, gama bai ci gurasa ba ko ya sha wani ruwa har kwana uku da yini uku.
\s5
\v 13 Dauda ya ce masa, "Kai na wane ne? Daga ina ka fito?" Ya ce, "Ni ɗan matashin ƙasar Masar ne, bawan Ba-amaleke; ubangidana ya baro ni domin kwana uku da suka shige rashin lafiya ta same ni.
\v 14 Mu ka kai farmaƙi a yankin Negeb na Keretiyawa, da abin da ya ke na Yahuda, da kuma Nageb na Kaleb, kuma muka ƙona Ziklag."
\s5
\v 15 Dauda ya ce masa, "Za ka kawo ni zuwa wurin waɗannan maharan?" Bamasaren ya ce, "Ka rantse mani ga Allah da cewar ba zaka kashe ni ko ka bashe ni a cikin hannuwan ubangidana ba, ni kuma zan kawo ka wurin waɗannan maharan."
\s5
\v 16 Da Bamasaren ya kawo Dauda wurin, maharan na nan barbaje a dukkan ƙasar, suna ci suna sha suna rawa saboda dukkan ganimar da suka kwaso daga cikin ƙasar Filistiyawa da kuma ƙasar Yahuda.
\v 17 Sai Dauda ya kai masu hari tun daga wayewar gari har yammancin da gari ya waye. babu mutum wanda ya tsira sai dai 'yan matasa guda ɗari, waɗanda suka haura bisa raƙuma suka kuma gudu.
\s5
\v 18 Sai Dauda ya maido da dukkan abin da Amalekawa suka ɗauke; kuma Dauda ya ƙubutar da matansa biyu.
\v 19 Babu abin da ya ɓace, ko ƙarami ko babba, ko 'ya'ya maza ko 'ya'ya mata, ko kayan ganima, ko wani abu da maharan suka ɗauko wa kansu.
\v 20 Dauda ya dawo da komai. Dauda ya ɗauko dukkan garken da kuma dabbobin, waɗanda mazajen suka koro gaba da sauran garkunan. Suka ce, "Wannan ganimar Dauda ce."
\s5
\v 21 Sai Dauda ya komo wurin sauran ɗari biyun da ƙarfinsu ya gãza ba su bi shi ba, waɗanda sauran suka sa su jira a magudanar Beso. Waɗannan mazajen suka zo domin su tarbi Dauda da kuma mutanen da ke tare da shi. Da Dauda ya iso wurin mutanensu, ya gaishe su.
\v 22 Sai dukkan mugayen mutanen da marasa amfani da ke cikin waɗanda suka tafi tare da Dauda suka ce, "Domin waɗannan mazajen ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su komai daga cikin ganimar da muka samu ba. Sai dai kowanne ɗaya daga cikinsu ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa, ya bishe su, su tafi."
\s5
\v 23 Sa'an nan Dauda ya ce, "Ba za ku yi haka ba, 'yan'uwana, da abin da Yahweh ya ba mu. Ya kiyaye mu ya kuma bayar da maharan da suka tayar mana a hannuwanmu.
\v 24 Waye zai saurari ku a kan wannan zance? Gama kamar yadda rabon kowanne da ya tafi yaƙin, haka zaya zama rabon duk wadda ya jira wurin kaya; za su sami rabo dai-dai da kowa."
\v 25 Haka ya ci gaba da zama daga wannan rana har wa yau, gama Dauda ya maida haka doka da kuma ka'ida a Isra'ila.
\s5
\v 26 Da Dauda ya kai Ziklag, ya aika daga cikin ganimar zuwa ga shugabannin Yahuda, zuwa ga abokansa, cewa, "Duba, ga kyauta domin ku daga ganimar maƙiyan Yahweh."
\v 27 Ya kuma aika da waɗansu zuwa ga shugabannin da ke a Betel, da kuma waɗanda ke a Ramot na Kudu, kuma ga waɗanda suke daga Jattir,
\v 28 kuma ga waɗanda ke cikin Arowa, kuma zuwa ga waɗanda ke a Sifmot, kuma ga waɗanda suke a Ishtemowa.
\s5
\v 29 Ya kuma aika zuwa ga shugabannin da ke cikin Rakal, kuma zuwa ga waɗanda ke cikin biranen Yeramilawa, kuma ga waɗanda ke cikin biranen Kenawa,
\v 30 kuma ga waɗanda ke cikin Homa, da kuma waɗanda ke zama a Borashan, ga kuma waɗanda ke cikin Atak,
\v 31 ga kuma waɗanda ke cikin Hebron, ga kuma dukkan wuraren da Dauda da kansa da mazajensa ke zuwa kodayaushe.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Yanzu Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ila. Mazajen Isra'ila suka gudu daga fuskar Filistiyawa suka kuma faɗi matattu a Tsaunin Gilbowa.
\v 2 Filistiyawa suka runtumi Saul da 'ya'yansa. Filistiyawa suka kashe Yonatan, Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yansa maza.
\v 3 Yaƙin ya yi zafi gãba da Saul, kuma masu harbin bãka suka sha kansa. Yana cikin ƙunci da zafi sabili da su.
\s5
\v 4 Sai Saul ya cewa mai ɗaukar masa makamai, "Zaro takobinka ka soke ni da ita. In ba haka ba, waɗannan marasa kaciyar zasu zo su wulaƙanta ni." Amma mai ɗaukar masa makamai ya ƙi, gama yana jin tsoro. Sai Saul ya ɗauki takobinsa ya faɗi bisanta.
\v 5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya ɗauki ta sa takobin ya faɗa kanta ya mutu da shi.
\v 6 Haka Saul ya mutu, 'ya'yansa uku, da kuma mai ɗaukar masa makamai - waɗannan mutanen dukka suka mutu tare rana ɗaya.
\s5
\v 7 Lokacin da mutanen Isra'ila da ke a wancan ɓangaren kwarin, da kuma waɗanda ke gaba da Yodan, suka ga cewa mazajen Isra'ila sun gudu, kuma Saul da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka ƙaurace wa ƙauyukansu suka gudu, sai kuma Filistiyawa suka zo suka zauna cikinsu.
\v 8 Sai ya zama kuma washegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka ga Saul tare da 'ya'yansa maza uku sun faɗi a Dutsen Gilbowa.
\s5
\v 9 Suka yanke kansa suka kuma cire kayan yaƙinsa, suka kuma aika 'yan saƙo cikin ƙasar Filistiyawa ko'ina domin su kai labarai ga haikalin gumakansu kuma ga mutanensu.
\v 10 Suka ajiye rigar yaƙinsa cikin haikalin Ashtoret, kuma suka rataye jikinsa ga ganuwar birnin Bet Shan.
\s5
\v 11 Lokacin da mazaunan Yabesh Giliyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,
\v 12 dukkan mazaje 'yan yaƙi suka tashi suka yi tafiya dukkan dare suka ɗauki jikin Saul da kuma jikkunan 'ya'yansa daga ganuwar Bet Shan. Suka tafi Yabesh suka ƙona su a can.
\v 13 Sai Suka ɗauki ƙasusuwansu suka binne su a ƙarƙashin itaciyar tamarisk a Yabesh, suka yi azumi na kwana bakwai.