ha_ulb/08-RUT.usfm

181 lines
12 KiB
Plaintext

\id RUT
\ide UTF-8
\h Littafin Rut
\toc1 Littafin Rut
\toc2 Littafin Rut
\toc3 rut
\mt Littafin Rut
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Ya kasance a kwanakin da alƙalai ke mulki, sai a ka yi yunwa a cikin ƙasar, sai kuma wani mutumin Betlehem ta Yahuda ya tafi ƙasar Mowab tare da matarsa da 'ya'yansa maza guda biyu.
\v 2 Sunan mutumin Elimelek, sunan matarsa kuma Na'omi. Sunayen 'ya'yansa biyu kuwa su ne Mahlon da Kiliyon, su Ifratawa ta Betlehem ta Yahuda ne, sai suka je ƙasar Mowab suka zauna a can.
\s5
\v 3 Ana nan sai Elimelek mijin Na'omi ya mutu a ka bar ta da 'ya'yanta maza biyu.
\v 4 Waɗannan 'ya'ya maza suka yi aure da 'yan matan Mowabawa guda biyu, sunayensu kuwa shi ne Orfa da Rut sun zauna a can har kusan shekaru goma.
\v 5 A na nan sai Mahlon da Kiliyon suka mutu, aka bar Na'omi ba miji ba 'ya'yanta guda biyu.
\s5
\v 6 Daga nan sai Na'omi ta yanke shawara ta bar Mowab tare da matan 'ya'yanta zuwa Yahuda saboda ta ji cewa Yahweh ya taimaki mutanensa da ke cikin buƙata ya kuma basu abinci.
\v 7 Saboda haka sai ta bar wurin da take tare da surukanta biyu, suka kama hanya don su koma ƙasar Yahuda.
\s5
\v 8 Sai Na'omi ta ce da surukanta biyu "Kowaccenku ta koma gidan iyayenta. Dama Yahweh ya yi mu ku jinkai, kamar yadda ku ka nuna jinkai gare ni da kuma mamatan.
\v 9 Dama Ubangiji ya ba ku hutu a gidan mazanku da za ku aura. "Sai ta sunbace su sai suka tada murya suka yi kuka.
\v 10 Sai suka ce da ita "A'a za mu koma wurin mutanenki tare da ke".
\s5
\v 11 Amma Na'omi ta ce, "ku koma, 'ya'yana! Don me za ku tafi tare da ni? Har yanzu ina da sauran 'ya'ya maza a cikina dominku, da za su aure ku?
\v 12 Haba 'ya'yana ku koma, don na tsufa sosai har da zan yi aure, Ko da ma ace ina begen yin aure yanzu, in haifi 'ya'ya maza,
\v 13 Za ku jira har su yi girma? Za ku yi ta jira ba za ku yi aure yanzu ba? A'a 'ya'yana! Hakika ina cike da baƙin ciki sosai, fiye da na ku bakin cikin, Don Yahweh ya juya mani baya."
\s5
\v 14 Sai surukanta su ka sake ɗaga murya su ka ɓarke da kuka. Sai Orfa ta sumbaci surukarta suka yi ban kwana, amma Rut ta manne mata.
\v 15 Na'omi ta ce, kin ga 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da 'yar'uwarki."
\s5
\v 16 Amma Rut ta ce, "Kar ki sa in rabu da ke, don inda za ki can za ni; inda kika zauna nan zan zauna, mutanenki za su zama mutanena, kuma Allahnki zai zama Allahna.
\v 17 Inda ki ka mutu can zan mutu, a binne ni a can. Yahweh ya hukunta ni fiye da haka, idan har wani abu in ba mutuwa ba ya raba mu."
\v 18 Sa'adda Na'omi ta ga Rut ta ƙudurta ta bi ta, sai ta dena gardama da ita.
\s5
\v 19 Sai su biyun su ka yi tafiya har garin Betlehem. Bayan sun zo sai duk garin ya cika da murna saboda su, Sai mataye suka ce "Na'omi ce wannan?"
\v 20 Amma ta ce da su "Kada ku kira ni Na'omi. Ku kira ni mai baƙinciki, don Mai Iko Dukka ya azabtar da ni.
\v 21 Na fita a wadace, amma Yahweh ya sake dawo da ni gida hannu wofi. To don me ku ke kira na Na'omi, da ya ke Yahweh ya yashe ni, Mai iko dukka ya wahalshe ni?"
\s5
\v 22 To Na'omi da surukarta Rut 'Yar Mowabawa su ka komo daga ƙasar Mowab. Suka zo Betlehem a farkon kakar bali.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Mijin Na'omi Elimelek ya na da ɗan'uwa mai suna Bo'aza, shi mawadaci ne, sananne.
\v 2 Sai Rut 'yar Mowabawa ta ce da Na'omi, "Yanzu ki bar ni in je in yi kalar abin da ya ragu a gonakin hatsi. Zan bi duk wanda na sami tagomashi a wurinsa". Sai Na'omi ta ce da ita, '"Yata, ki je."
\s5
\v 3 Sai Rut ta tafi ta yi kalar abin da ya ragu a gonaki bayan sun yi girbi, Sai ta je yankin gonar Bo'aza, wanda ɗan'uwa ne ga Elimelek.
\v 4 Sai Bo'aza ya zo daga Betlehem ya ce da masu girbin, "Yahweh ya kasance tare da ku" Suka amsa masa, "Yahweh ya albarkace ka."
\s5
\v 5 Sai Bo'aza ya ce wa barorinsa da ke kula da masu girbin, "Wannan yarinyar ɗiyar wanene?"
\v 6 Baran da ke kula da masu girbin ya amsa, "Yar Mowabawa ce da ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab.
\v 7 Ta ce da ni, "Ina roƙon ka bar ni in yi kalar abin da ya rage a gonar bayan masu girbin sun girbe hatsin. Sai ta zo nan tun da safe har yanzu, sai dai ɗan shaƙatawa da ta yi a gida"
\s5
\v 8 Daga nan sai Bo'aza ya ce da Rut, 'Yata ki na ji na? Kada ki bar gonata ki je wata gona don ki yi kala, amma ki tsaya nan ki yi aiki tare da barorina mata da ke aiki.
\v 9 Ki zuba idonki kawai a inda masu girbin ke girbi ki na bin bayan sauran matan. Ashe ban umarci mazan da kada su taɓa ki ba? Duk lokacin da ki ka ji ƙishi sai ki je wurin tulunan ruwa ki sha ruwan da mazan su ka ɗebo."
\s5
\v 10 Daga nan sai ta sunkuyar da kanta har ƙasa a gaban Bo'aza. Ta ce, 'Ta yaya na sami tagomashi a gabanka, har da zaka kula da ni, ni da nake baƙuwa?"
\v 11 Bo'aza ya amsa ya ce da ita, an labarta mini duk abin da ki ka yi tun lokacin da mijinki ya mutu, kin bar babanki, da kuma ƙasarki, ki ka biyo surukarki, ki ka zo wirin mutanen da ba ki sani ba.
\v 12 Yahweh ya ba ki lada kan abin da ki ka yi, dama ki sami cikkaken lada daga Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda ki ka sami mafaka a gare shi."
\s5
\v 13 Sai ta ce, "Bari in sami tagomashi a gareka, shugabana, don ka ta'azzantar da ni, ka yi mani maganar kirki, ko da ya ke ni ba ɗaya daga cikin barorinka mata ba ce."
\s5
\v 14 A lokacin cin abinci sai Bo'aza ya ce da Rut "Zo nan ki ci wani abinci, ki kuma sa gutsuranki a cikin kunu." Sai ta zauna a gefen masu girbin, sai ya ba ta wani gasasshen hatsi. Ta ci har sai da ta ƙoshi ta bar sauransa.
\s5
\v 15 Da ta tashi za ta yi kala sai Bo'aza ya ce da ma'aikatansa, "Ku barta ta yi kala har ma daga cikin dammunan, kada ku hana ta.
\v 16 kuma ku dinga zarar ma ta zangarkun hatsin daga dammuna, ku bar ma ta ta tara ka da ku tsauta ma ta."
\s5
\v 17 To sai ta yi ta kala a gonar har yamma. Daganan ta sussuke zangarkun hatsin ta sami kusan garwa biyu na bali.
\v 18 Sai ta ɗauka ta tafi gari. Sai surukarta ta ga abin da ta samo. Rut kuma ta zo mata da soyayyen hatsin da ta ci ta rage sai ta bata.
\s5
\v 19 Surukarta ta ce da ita, "Ina ki ka je kala yau? Ina ki ka je aiki yau? Dama mutumin da ya taimake ki ya sami albarka". Sai Rut ta faɗawa surukarta labarin mutumin da ya ke da gonar da kuma inda ta yi aiki. Ta ce "Sunan mutumin da na yi aiki a gonarsa Bo'aza"
\v 20 Na'omi ta ce da surukarta Yahweh ya albarkace shi, wanda bai dena nuna amincinsa ga rayayyu da matattu ba." Na'omi ta ce wannan mutumin danginmune na kusa mai kuma fansarmu."
\s5
\v 21 Rut mutumiyar Mowab ta ce, "Hakika, ya ce mani, "Ki dinga bin bayan ma'aikatana har sai sun gama girbin dukkan amfanin".
\v 22 Sai Na'omi ta ce da Rut surukarta, '"Yata ya fi kyau da kike tafiya tare da ma'aikatansa 'yanmata, don ka da ki je wata gonar ki cutu."
\s5
\v 23 To sai ta tsaya kusa da ma'aikatan Bo'aza 'yanmata don ta dinga kala har ya zuwa karshen kakar bali, don haka sai ta zauna tare da surukarta.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Surukarta, Naomi ta ce ma ta, '"Yata "Ba sai in samar miki wurin da za ki huta ba, don komai ya zamar miki dai-dai?
\v 2 To yanzu shi Bo'aza da ki ke aiki tare da ma'aikantansa mata ba danginmu ba ne? Kin ga zai je shikar bali yau a masussuka.
\s5
\v 3 Don haka, sai ki yi wanka ki yi kwalliya, ki sa tufafinki mafi kyau, ki tafi masussukar. Amma kada ki yarda ya gan ki har sai ya gama ci da sha.
\v 4 Amma bayan ya kwanta, sai ki kula da inda ya kwanta don in an jima ki je wurinsa, ki yaye mayafinsa, ki kwanta a ƙafafunsa. Daga nan zai faɗa miki abin da za ki yi"
\v 5 Rut ta ce wa Na'omi, "Zan yi duk abin da ki ka ce."
\s5
\v 6 To sai ta tashi ta tafi masussukar, ta kuma bi umarnin surukarta.
\v 7 Bayan Bo'aza ya ci ya sha zuciyarsa na annashuwa, sai ya je don ya kwanta a ƙarshen tarin hatsinsa. Daga nan sai ta lallaɓa ta yaye ƙafafunsa, ta kwanta.
\s5
\v 8 Can wajen tsakar dare bayan mutumin ya farka, sai ya juya kawai sai ya ji mace kwance a ƙafafunsa!
\v 9 Ya ce, "Ke wacece?". Ta ce, "Ni ce Rut baiwarka. Gama kai danginmune na kusa, sai ka bude mayafinka ka rufe ni."
\s5
\v 10 Bo'aza ya ce '"Yata, Yahweh ya sa miki albarka. Yanzu a ƙarshe kin nuna kirki fiye da na farko, saboda ba ki je wurin matasa, ko matalauta, ko mawadata ba.
\v 11 Yanzu, 'yata, ka da ki ji tsoro! Zan yi miki duk abin da ki ka ce, don duk mutanen garin nan sun san ke mace ce da ta can-canta.
\s5
\v 12 Gaskiya ne ni dangi ne, amma akwai ɗan'uwan da ya fi kusa da ku fiye da ni.
\v 13 Yanzu sai ki tsaya nan, da safe kuma in zai cika hakin ɗan'uwa a kanki to ya yi dai-dai, sai ya cika, Amma idan ba zai cika hakin ɗan'uwa ba to ni zan cika hakin ɗan'uwa a kanki, na rantse da Yahweh. Ki kwanta har sai da safe."
\s5
\v 14 To sai ta kwanta a ƙafafunsa har sai da gari ya waye. Amma ta tashi tun kamin a fara gane mutane da sassafe. Don Bo'aza ya ce, "Don ka da a san cewa mace ta zo massusukar"
\v 15 Bo'aza ya ce, "Kawo gyalenki ki shimfiɗa." Bayan ta yi haka, sai ya auna ma ta bali tiya shida a ciki ya dora ma ta. Daga nan sai ya tafi gari.
\s5
\v 16 Bayan Rut ta dawo wurin surukarta sai ta ce, "Yaya ki ka yi ɗiyata?." Rut ta faɗa ma ta duk abin da mutumin ya yi ma ta.
\v 17 Ta ce, "Wannan tiya shida ta bali shi ne ya ba ni, don ya ce, "Kada ki koma wurin surukarki ba tare da komai ba".
\v 18 Sai Na'omi ta ce, "Yata ki zauna a nan, har sai kin san yadda al'amarin zai zama, don mutumin ba zai huta ba har sai ya gama wannan al'amarin yau."
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 To sai Bo'aza ya tashi ya tafi ƙofar gari ya zauna a can. Ba da jimawa ba, sai ga wani daga cikin dangin Na'omi na kusa wanda Bo'aza ya yi maganarsa ya zo zai wuce. Bo'aza yace da shi. "Abokina, zo nan ka zauna." Sai mutumin ya zo ya zauna.
\v 2 Sai Bo'aza ya kira dattawan garin guda goma ya ce, "Ku zauna nan." Sai suka zauna.
\s5
\v 3 Bo'aza yace da ɗan'uwan na kusa, "Na'omi, da ta dawo daga ƙasar Mowab, za ta sayar da wata gonar ɗa'uwanmu Elimelek.
\v 4 Na yi tunanin in sanar da kai in kuma yi maka magana, 'ka saye ta a gaban waɗanda ke zaune tare da mu a nan, da a gaban dattawan mutanena, In har kana so ka fanshe ta. Amma in ba ka so ka fansa sai ka faɗa mani don in sani, don ba wanda ya dace ya fanshe ta daga kai sai ni a bayanka. "Sai mutumin ya ce zan fanshe ta."
\s5
\v 5 Sai Bo'aza yace "A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, dole ne kuma ka haɗa da Rut 'yar Mowabawa, matar marigayin, don a tada sunan marigayin akan gãdonsa."
\v 6 Sai wannan ɗan'uwan na kusa ya ce ba zan iya fansar ta don kaina ba, ba tare da ɓata nawa gãdon ba. Ka ɗauki tawa damar ta fansar don kanka, don ba zan iya fansar ta ba."
\s5
\v 7 To wannan ita ce al'adar Isra'ila a waɗancan kwanakin akan al'amuran fansa da kuma canjin kayayyaki. Don a tabbatar da komai, sai mutum ya cire takalminsa ƙafa ɗaya ya ba maƙwabcinsa, haka ake yin yarjejeniyar da ta dace a Isra'ila.
\v 8 To sai ɗan'uwan mafi kusa ya ce da Bo'aza, "Ka saye ta don kanka," sai ya tuɓe takalminsa.
\s5
\v 9 Daga nan sai Bo'aza yace da dattawan da dukkan jama'ar, "Ku ne shaidu cewa yau na saye dukkan mallakar Elimelek, da duk abin da ke na Kiliyon da Mahlon daga hannun Na'omi.
\v 10 Bugu da ƙari game da Rut ɗiyar Mowab, matar Mahlon; ita ma na mallake ta ta zama matata, don in tãda sunan marigayin a kan gãdonsa, don in kafa ma sa zuriya, don kada a yanke sunansa daga cikin 'yan'uwansa da kuma gidansa. Yau ku ne shaidu."
\s5
\v 11 Dukkan mutanen da ke ƙofar da dattawan su ka ce, "Mu shaidune. Dãma Yahweh ya sa matar da ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu, su biyu da su ka kafa gidan Isra'ila; kuma dãma ka azurta a Ifarata ka kuma yi suna a Betlehem
\v 12 Dãma gidanka ya zama kamar na Ferez wanda Tamar ta haifawa Yahuda, Ta wurin zuriyar da Yahweh zai ba ka tare da wannan matashiyar mata."
\s5
\v 13 Sai Bo'aza ya ɗauki Rut, daga nan ta zama matarsa. Sai ya kwana da ita, sai Yahweh ya sa ta yi ciki, sai ta haifi ɗa namiji.
\v 14 Sai mataye su ka ce da Na'omi, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, wanda bai bar ki yau ba ɗan'uwa na kusa ba, wannan yaron. Dãma ya zama sanannen mutum a Isra'ila.
\v 15 Dãma ya zama mai dawo maki da rayuwa ya kuma inganta kwanakinki na tsufa, saboda wannan surukar ta ki, wadda ta ƙaunace ki, wadda ta fi 'ya'ya bakwai maza a gare ki, ce ta haife shi."
\s5
\v 16 Na'omi ta ɗauki ɗan, ta rungume shi a kafaɗarta, ta kuma kula da shi.
\v 17 Mataye maƙwabta su ka ba shi suna cewa, "An haifawa Na'omi ɗa," Sai suka raɗa masa suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, wanda ya haifi Dauda.
\s5
\v 18 To waɗanan su ne zuriyar Ferez: Ferez ya haifi Hezron,
\v 19 Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab,
\v 20 Aminadab ya haifi Nahshon, Nahshon ya haifi Salmon,
\v 21 Salmon ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obed,
\v 22 Obed ya haifi Yesse, Yesse ya haifi Dauda.