ha_ulb/07-JDG.usfm

1293 lines
94 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id JDG
\ide UTF-8
\h Littafin Alƙalai
\toc1 Littafin Alƙalai
\toc2 Littafin Alƙalai
\toc3 jdg
\mt Littafin Alƙalai
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Bayan mutuwar Yoshuwa, mutanen Isra'ila suka tambayi Yahweh cewa, "Wane ne zai fara kai wa kan'aniyawa hari domin mu, don yin faɗa da su?"
\v 2 Sai Yahweh yace "Yahuda zai kai hari, Duba, na ba su iko a kan ƙasar."
\v 3 Mutanen Yahuda suka ce da mutanen Simiyon, 'yan'uwansu, "Ku zo tare da mu a yankin da aka ɗebo mana don mu je tare mu yi yaƙi da Ka'aniyawa. Mu ma za mu je tare da ku a yankin da aka ɗiba maku". Sai kabilar Simiyon ta tafi tare da su.
\s5
\v 4 Mutanen Yahuda suka kai hari kuma Yahweh ya ba su nasara a kan Ka'aniyawa, da Feriziyawa. Suka kashe masu mutum dubu goma a Bezek.
\v 5 Suka sami Adoni-Bezek a Bazek, sai suka yi yaƙi da shi suka kuma cinye Kan'aniyawa da Feriziyawa a yaƙi.
\s5
\v 6 Amma Adoni-Bezek ya gudu, sai suka fafare shi suka kamo shi suka yanke yatsunsa da tafin ƙafafunsa.
\v 7 Adoni-Bezek yace "Sarakuna saba'in da aka yanke masu yatsunsu da tafin ƙafafunsu suna neman abincinsu a ƙarƙashin teburina. "Kamar yadda na yi haka nima Allah ya yi mani." Sai suka kawo shi Yerusalem, ya kuma mutu a can.
\s5
\v 8 Mutanen Yahuda sun yaƙi birnin Yerusalem suka kuma ɗauke ta. Sun kai hari da kaifin takobi kuma suka banka wa garin wuta.
\v 9 Bayan haka mutanen Yahuda suka je suyi faɗa da Ka'aniyawa da ke zaune a bisan tsibirin ƙasar, a cikin Negeb, da cikin tsibirin duwatsun yammacin.
\v 10 Yahuda ya haura gãba da Ka'aniyawa da ke zaune a Hebiron (sunan Hebiron a dã shi ne Kiriyat Arba), suka kuma buge Sheshai, da Ahiman, da Talmaye.
\s5
\v 11 Daga can sai mutanen Yahuda suka nausa gãba da mazaunan Debir (sunan Debir a dã shi ne Kiriyat Sefa).
\v 12 Kalibu ya ce, "Duk wanda ya kai wa Kiriyat Sefa hari ya kuma ɗauke ta, Zan ba shi Aksa, ɗiyata, ta zama matarsa."
\v 13 Otniyel ɗan Kenaz (ƙanin Kaleb) ya yi nasara a kan Debir, sai Kaleb ya ba shi Aksa, ɗiyarsa, ta zama matarsa.
\s5
\v 14 Da sauri Aksa ta zo wurin Otniyel, sai ta iza shi ya sa mahaifinta ya bata fili. Da ta ke saukowa a kan jaki, Kaleb ya tambaye ta, "Mene ne zan yi maki?"
\v 15 Ta ce da shi, "Ba ni albarka. Tun da ka ba ni ƙasar Negeb, ka kuma ba ni maɓulɓullan ruwa." Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓullan tudu da na fadama.
\s5
\v 16 Zuriyar surukin Musa Bakenine sun hauro daga Birnin Dabino tare da mutanen Yahuda, zuwa ga tsibirin Yahuda, wanda ke cikin Negeb, su zauna tare da mutanen Yahuda kusa da Arad.
\v 17 Mutanen Yahuda suka tafi tare da mutanen Simiyon 'yan'uwansu sai suka tunkari Kan'aniyawan da ke zaune a Zefat suka hallakar da su kakaf. Sunan birnin Hormah.
\s5
\v 18 Mutanen Yahuda suka kuma kame Gaza da ƙasashen da ke kewaye da ita, Ashkelon da ƙasar da ke maƙwabtaka da ita, da kuma Ekron tare da ƙasar da ke kewaye da ita.
\v 19 Yahweh na tare da mutanen Yahuda suka kuma ɗauki mallakar ƙasar kan tudu, amma ba su iya korar mazaunan ƙasar kan tudun ba don su masu karusan ƙarfe ne.
\s5
\v 20 Hebron kuwa Kaleb aka baiwa (kamar yarda Musa yace), ya kuma kori 'ya'yan Anak uku daga wurin.
\v 21 Amma mutanen Benyamin ba su kori Yebusiyawan da ke zaune a Yerusalem ba. Sai Yebusiyawan suka zauna tare da mutanen Benyamin a Yerusalem har ranar nan.
\s5
\v 22 Gidan Yosef suka yi shirin kai wa Betel hari, kuma Yahweh na tare da su.
\v 23 Suka aiki maza su leƙo asirin Betel (Birnin da dã ake kira Luz).
\v 24 Masu leken asirin suka ga wani mutum na fitowa daga birnin, sai suka ce da shi, "In ka yarda, nuna mana yadda za a shiga cikin birnin nan, kuma za mu yi maka alheri."
\s5
\v 25 Ya nuna masu hanyar zuwa cikin birnin, sai suka kai wa birnin hari da kaifin takobi, amma suka bar mutumin da dukkan iyalinsa suka kuɓuta.
\v 26 Sai mutumin ya je ƙasar Hitiyawa ya gina wani birnin da ya kira shi Luz, shi ne kuwa sunansa har wa yau.
\s5
\v 27 Mutanen Manasse ba su kori mutanen da ke zama a biranen Bet Shan da ƙauyukansu ba, ko Ta'anak da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Dor da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Ibilim da ƙauyukansu, ko waɗanda suka zauna a Megiddo da ƙauyukansu ba, domin Ka'aniyawan sun bugi ƙirjinsu don zama a cikin ƙasar.
\v 28 Da Isra'ila ta yi ƙarfi, suka tilasta wa Ka'aniyawa su yi masu bauta ta aiki mai tsanani, amma ba su taɓa korar su kakaf ba.
\s5
\v 29 Ifraim bai kori Ka'aniyawan da suka zauna a Gezer ba, don haka Ka'aniyawa suka ci gaba da zama a Gezer a cikin su.
\s5
\v 30 Zebulun bai tumɓuke mutanen da ke zama a Kitiron, ko mutanen da ke zama a Nahalol ba, saboda haka Ka'aniyawan suka ci gaba da zama a cikinsu, amma Zebulun ya tilasta wa Ka'aniyawan su bauta masu tare da aiki mai tsanani.
\s5
\v 31 Asha bai tumɓuke mutanen da ke zama a Akko, ko mutanen da ke zama a Sidon, ko waɗanda ke zama a Alab, Akzib, Helba, Afek, ko Rehob ba.
\v 32 Don haka kabilar Asha ta zauna cikin Ka'aniyawan (waɗanda ke zaune a ƙasar), saboda ba su kore su ba.
\s5
\v 33 Kabilar Naftali ba su kori waɗanda ke zaune a Bet Shemesha, ko waɗanda ke zaune a Bet Anat ba. Don haka kabilar Naftali ta zauna cikin Ka'aniyawa (mutanen da tun asali ke zaune a ƙasar). Duk da haka, aka nawaita wa mazaunan Bet Shemesha da Bet Anata aikin bauta ga Naftali
\s5
\v 34 Amoriyawa suka tilasta wa kabilar Dan su zauna a ƙasar kan tudu, ba su kuma ba su damar saukowa kwari ba.
\v 35 Don haka Amoriyawa suka zauna a Tsaunin Heres, a Aijalon, da Sha'albim, amma ƙarfin mayaƙan gidan Yosef ya mamaye su, ya kuma sa aka tilasta masu su bauta masu da aiki mai tsanani.
\v 36 Iyakar Amoriyawa ta kama daga tudun Akrabbim a Sela zuwa cikin ƙasar kan tudu.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Mala'ikan Yahweh ya taso daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, "Na fitar da ku daga Masar, na kuma kawo ku ƙasar da na yi rantsuwa zan ba kakaninku. Na ce 'ba zan taɓa karya alƙawarina da ku ba.
\v 2 Ba za ku yi yarjejeniya da mazaunan garin nan ba. Wajibi ne ku rurrushe bagadansu.' Amma ba ku saurari muryata ba. Me kenan ku ka yi?
\s5
\v 3 Yanzu sai na ce, 'ba zan kori Kan'aniyawa daga gare ku ba, amma za su zama ƙaya a gare ku, kuma allolinsu za su zama tarko a gare ku."'
\v 4 A lokacin da mala'ikan Yahweh ya furta waɗannan kalmomin ga mutanen Isra'ila, sai suka yi kuka mai ƙarfi.
\v 5 Suka kira wurin Bokim. A wurin suka miƙa hadayu ga Yahweh.
\s5
\v 6 Sa'ad da Yoshuwa ya aike mutanen a hanyarsu, kowanne ɗaya daga mutanen Isra'ila kuwa kowa ya nufi wurin da aka sa shi don mallakar ƙasar.
\v 7 Mutanen kuwa sun bauta wa Yahweh a zamanin Yoshuwa da kuma ta dattawan da suka bi bayansa, waɗanda suka ga dukkan abubuwa masu girma da Yahweh ya yi wa Isra'ila.
\v 8 Yoshuwa ɗan Nun, bawan Yahweh, ya rasu yana da shekaru 110.
\s5
\v 9 Aka kuwa binne shi a tsibirin ƙasar da aka ba shi ya mallaka a Timnat Heres, a tudun ƙasar Ifiraim, arewa da Tsaunin Ga'ash.
\v 10 Dukkan wannan tsarar kuwa sun kasance tare da kakaninsu. bayansu sai wata tsara da ba ta san Yahweh ko abin da ya yi wa Isra'ila ba ta taso biye da su.
\s5
\v 11 Mutanen Isra'ila kuwa sun yi mugun abu a fuskar Yahweh suka kuma bautawa Ba'aloli.
\v 12 Sun kauce daga Yahweh, Allahn kakaninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar. Sun bi waɗansu alloli, wato allolin mutanen da ke kewaye da su, kuma sun rusuna ƙasa gare su. Suka sa Yahweh ya fusata domin
\v 13 sun kauce daga Yahweh sun kuma yi wa Ba'al da Ashtoret sujada.
\s5
\v 14 Fushin Yahweh ya taso wa Isra'ila, sai ya sa 'yan fashi suka ƙwace mallakarsu daga gare su. Ya maishe su barorin da ke ƙarƙashin ƙarfin maƙiyansu da ke kewaye da su, saboda haka ba su iya kare kansu daga maƙiyansu ba.
\v 15 Duk inda Isra'ila su ka je faɗa, hanuwan Yahweh na gãba da su don a yi nasara da su, kamar dai yadda ya rantse masu kuma sun shiga ƙunci mai tsanani.
\s5
\v 16 Sa'an nan Yahweh ya taso da Alƙalai, waɗanda su ka ceto su daga hanuwan masu satar mallakarsu.
\v 17 Duk da haka ba su saurari alƙalansu ba. Suka zama marasa aminci ga Yahweh, suka kuma maida kansu kamar karuwai ga waɗansu alloli suka kuma yi masu sujada. Suka juya baya daga hanyar da kakaninsu suka yi rayuwarsu - waɗanda suka yi biyayya da umurnin Yahweh - amma su da kansu ba su yi haka ba.
\s5
\v 18 A lokacin da Yahweh ya naɗa masu alƙalai, Yahweh ya taimaki alƙalan ya kuma ƙuɓutar da su daga hanuwan maƙiyansu a dukkan kwanakin alƙalan. Yahweh ya yi masu tagomashi yayin da suke nishi saboda waɗanda ke zalunta da kuma ƙuntata masu.
\v 19 Amma sa'ad da alƙalan su ka mutu, sai suka juya baya suna yin miyagun abubuwan da suka fi waɗanda ma ubaninsu suka yi. Suka biɗi waɗansu alloli don su bauta masu su kuma yi masu sujada. Suka ƙi barin miyagun ayukansu ko taurin kansu.
\s5
\v 20 Fushin Yahweh kuwa ya taso ma Isra'ila; ya ce "Saboda wannan al'umma ta karya sharuɗan alkawarina wanda na kafa domin ubaninsu-saboda ba su saurari muryata ba -
\v 21 Daga yanzu ba zan korar masu ko ɗaya daga cikin al'umman da Yoshuwa ya rage kafin mutuwarsa ba.
\v 22 Zan yi haka domin in gwada Isra'ila, ko za su yi biyayya da hanyar Yahweh da tafiya cikinta ko ba za su yi ba. Kamar yadda ubaninsu suka yi biyayya."
\v 23 Shi ya sa Yahweh ya bar al'ummomin nan bai kuma kore su da sauri ya ba da su ga hannun Yoshuwa ba.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Yanzu kuwa Yahweh ya bar waɗannan ƙasashen domin ya gwada Isra'ila ne, wato duk wanda bai taɓa sanin yaƙe-yaƙen da Isra'ila ta yi da Kan'ana ba
\v 2 (Ya yi wannan ne domin ya koyar da al'amarin yaƙi ga sabon zamanin Isra'ilawan da ba su san shi ba.)
\v 3 Waɗannan su ne alu'mman: sarakuna biyar wato Filistiyawa da dukkan Kan'aniyawa da Sidoniyawa, da Hibitiyawa da ke zaune a duwatsun Lebanon, daga Tsaunin Ba'al Hermon zuwa Hamat Fass.
\s5
\v 4 Waɗannan al'umman aka rage da manufar kasancewar hanyar da Yaahweh zai gwada Isra'ila, ko tabbas za su yi biyayya da dokokin da ya ba kakaninsu ta wurin Musa.
\v 5 Mutanen Isra'ila kuwa sun yi zama a cikin Kan'aniyawa da Hitiyawa da Amoriyawa da Feriziyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa.
\v 6 Suka ɗauki 'yammatansu su zama matayensu, haka kuma nasu 'yammatan suka bayar ga samarinsu, suka kuma bauta wa allolinsu.
\s5
\v 7 Mutanen Isra'ila sun yi mugun abu a fuskar Yahweh kuma sun mance da Yahweh Allahnsu. Suka bauta wa gumakan Ba'al da Ashira.
\v 8 Ta haka, fushin Yahweh mai zafi ya sauko wa Isra'ila, sai ya sayar da su ga hannun Kushan Rishata'imi sarkin Aram Naharayim. Mutanen Isra'ila kuwa sun bautawa Kushan Rishatayim shekaru takwas.
\s5
\v 9 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya tayar da wani wanda zai taimaka wa mutanen Isra'ila, wanda kuma zai kuɓutar da su: Otniyel ɗan Kenaz (ƙanin Kaleb).
\v 10 Ruhun Yahweh ya ƙarfafa shi, ya yi alƙalancin Isra'ila, ya kuma je yaƙi. Yahweh ya ba shi nasara a kan Kushan Rishatayim sarkin Aram. Hanuwan Otniyel ya ragargaza Kushan Rishatayim.
\v 11 Ƙasar ta kasance da salama shekaru arba'in. Sai Otniyel ɗan Kenaz ya mutu.
\s5
\v 12 Bayan haka, Isra'ilawa kuma sun yi mugun abu a fuskar Yahweh, sai Yahweh ya ba Eglon sarkin Mowab ƙarfin da zai mallaki Isra'ilawa.
\v 13 Eglon ya haɗu da Amoniyawa da Amelikawa sai suka yi nasara da Isra'ila, suka kuma ɗauki mallakar Birnin Dabino.
\v 14 Mutanen Isra'ila sun bauta wa Eglon sarkin Mowab shekaru goma sha takwas.
\s5
\v 15 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, sai Yahweh ya tayar da wani mai taimako wanda zai taimake su, Ehud ɗan Gera, na kabilar Benyamin, bahago ne shi. Mutanen Isra'ila sun aike shi, da kyautukkansu, zuwa ga Eglon sarkin Mowab.
\s5
\v 16 Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai ƙaifi biyu, kamu guda a tsawo; ya yi ɗammara da ta a ƙarƙashin tufafinsa ta wajen cinyarsa ta dama.
\v 17 Ya ba da kyautar ga sarki Eglon na Mowab. (Eglon kuwa mai ƙiba ne.)
\v 18 Bayan Ehud ya gama miƙa kyautar, sai ya bar wurin tare da waɗanda suka ɗauke ta suka kai ciki.
\s5
\v 19 Ehud da kansa kuwa, ko da yake, lokacin da ya iso wurin da ake yin siffofi kusa da Gilgal, sai ya juyo ya koma baya, sai ya ce, "Ina da saƙo a asirce domin ka, sarkina." Eglon yace, "Shiru" Sai dukkan waɗanda ke yi masa hidima suka bar ɗakin.
\v 20 Ehud ya je wurin sa. Sarkin yana zaune da kansa, shi kaɗai a inuwar bene. Ehud yace, "Ina da saƙo daga Allah domin ka." Sarkin ya miƙe tsaye daga kujerarsa.
\s5
\v 21 Ehud ya shigar da hannun hagunsa ya ɗauki takobin daga cinyarsa ta dama, sai ya cake jikin sarkin.
\v 22 Ƙotar takobin kuma ta shige cikin jikinsa biye da wuƙar. Tsinin takobin ya fita ta bayansa kuma rufe da ƙitse, domin Ehud bai zaro takobin daga tumbinsa ba.
\v 23 Sai Ehud ya fita daga shirayin ya kukkulle ƙofofin babban benen a bayansa.
\s5
\v 24 Bayan Ehud ya tafi, barorin sarki suka zo; suka ga ƙofofin ɓenen a kulle, sai suka yi zaton, "Tabbas ya na hutawa a inuwar benen ne."
\v 25 Suka yi ta ƙaruwa da kulawa har sai da suka ji lallai suna sakaci da aikinsu ne yayin da sarki fa bai buɗe ƙofofin babban benen ba. Sai suka ɗauki makullin suka buɗe, sai ga ubangijinsu a kwance, a ƙasa, matacce.
\s5
\v 26 Yayin da barorin ke jira, suka rasa mema za su yi, Ehud kuwa ya tsere har ya wuce wurin da ake sassaƙa sifofin gumaka, sai ya tsere zuwa Se'ira.
\v 27 Sa'ad da ya iso, sai ya busa kakaki a ƙasar tudu ta Ifraim. Sa'an nan mutanen Isra'ila suka je ƙasa tare da shi daga tuddai, kuma yana yi masu jagora.
\s5
\v 28 Ya ce masu, "Ku biyo ni, gama Yahweh na gab da yin nasara da maƙiyanku, Mowabawa. "Suka bi shi suka kuma kama mashigin Yodan ƙetare zuwa Mowabawa, ba su kuma bar wani ya ƙetare kogin ba.
\v 29 A lokacin nan ne suka kashe kusan dubu goma na mazajen Mowab, kuma dukkan su masu ƙarfi ne gwarzaye. Babu ko ɗayan da ya tsere.
\v 30 Wato, a ranar nan ne Isra'ila ta mamaye Mowab da ƙarfinta, kuma ƙasar ta sami hutawa shekaru tamanin
\s5
\v 31 Bayan Ehud, alƙali na biye shi ne Shamgar ɗan Anat wanda ya kashe maza 600 na Filistiyawa da tsabgar dabbobi. Ya kuma kuɓutar da Isra'ila daga hatsari.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Bayan da Ehud ya mutu, mutanen Isra'ila suka sake yin mugun abu a fuskar Yahweh.
\v 2 Yahweh ya sayar da su ga hanun Yabin sarkin Kan'ana wanda ya yi mulki a Hazor. Babban shugaban rundunar sojojinsa shi ne Sisera, yana zaune a Haroshet Haggoyim.
\v 3 Mutanen Isra'ila sun yi kira ga Yahweh domin taimako, saboda Sisera na da karusan ƙarfe guda ɗari tara ya kuma ƙuntata wa mutanen Isra'ila shekaru ashirin.
\s5
\v 4 Debora kuwa, annabiya (matar Laffidot), tana jagoranci a matsayin mai sharia a Isra'ila a lokacin.
\v 5 Ta kan zauna a ƙarƙashin itacen dabino na Debora tsaƙanin Ramah da Betel a tuddun ƙasar Ifraim, kuma mutanen Isra'ila na zuwa wurinta domin sassanta jayayya a tsakaninsu
\s5
\v 6 Ta aika saƙo ga Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali. Ta ce masa, "Yahweh, Allahn Isra'ila, ya umarce ka, 'Jeka Tsaunin Tabor, tare da kai ka ɗauki maza dubu goma daga Naftali da Zabulun.
\v 7 Zan ciro Sisera, shugaban rundunar sojojin Yabin, ya haɗu da kai a Kogin Kishon, tare da karusansa da sojojinsa, kuma Zan ba ka nasara a kansa."
\s5
\v 8 Barak yace ma ta, "Idan za ki tafi tare da ni zan je, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ba za ni ba."
\v 9 Ta ce, "Zan tafi tare da kai tabbas. Ko da yake, hanyar da ka ke tafiya ba za ta kai ka ga martaba ba, domin Yahweh zai sayar da Sisera ga hannun mace." Sai Debora ta tashi tsaye ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh.
\s5
\v 10 Barak ya yi kira ga mazan Zebulun da Naftali su zo tare a Kedesh. Maza dubu goma suka bi shi, kuma Debora ta tafi tare da shi.
\s5
\v 11 Haber kuwa (Bakeniye) ya raba kansa daga Keniyawa - su zuriyar Hobab ne (surukin Musa) - ya kuma kafa rumfarsa a gefen itacen al'ul a Za'ananim kusa da Kedesh
\s5
\v 12 Sa'ad da suka faɗa wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya hauro Tsaunin Tabor,
\v 13 Sisera ya kira dukkan karussansa, karussan ƙarfe ɗari tara, da dukkan sojojin da ke tare da shi, daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.
\s5
\v 14 Debora ta ce da Barak, "Jeka! Domin wannan ranar ce Yahweh ya ba ka nasara a kan Sisera. Ashe ba Yahweh ne ke jagorantakar ka ba?" Sai Barak ya je gangare daga Tsaunin Tabor tare da maza dubu goma biye da shi.
\s5
\v 15 Yahweh ya sa sojojin Sisera su ruɗe, dukkan karusansa, da dukkan sojojinsa. Mazajen Barak suka faɗa masu har Sisera ya sauko daga karusa ya gudu da ƙafa.
\v 16 Amma Barak ya runtumi karusan da sojojin zuwa Haroshet Haggoyim, sai aka kashe dukkan sojojin Sisera da kaifin takobi, kuma babu mutumin da ya tsira.
\s5
\v 17 Amma Sisera ya ruga a guje da kafa zuwa rumfar Ya'el, matar Heber Bakenine, gama akwai salama tsakanin Yabin sarkin Hazor, da gidan Heber Bakenine.
\v 18 Ya'el ta fito ta sadu da Sisera sai ta ce masa, juyo, ubangijina; juyo gare ni kar ka ji tsoro." Sai ya juyo gare ta ya zo wurinta cikin rumfarta, sai ta rufe shi da bargo.
\s5
\v 19 Ya ce mata, "In kin yarda ki ba ni ruwa kaɗan in sha, don ina jin ƙishi." Ta buɗe jakar fata ta madara ta ba shi ya sha, sai ta sake rufe shi.
\v 20 Ya ce mata, "Tsaya a ƙofar rumfar. Idan wani ya zo ya tambaye ki, 'akwai wani a nan ne?', ki ce 'A a'."
\s5
\v 21 Sai Ya'el (matar Heber) ta ɗauki turken rumfar da guduma a hannunta ta je gunsa a asirce, gama ya na cikin zurfin barci, sai ta kafa turken rumfar ta ɗora guduma har ta soke gefen kansa zuwa ƙasa, har ya mutu.
\v 22 Yayin da Barak ke fakon Sisera, Ya'el ta je ta tarye shi ta ce masa, "Zo, Zan nuna maka mutumin da ka ke nema." Sai ya je tare da ita, sai ga Sisera kwance matacce, tare da turken rumfar a gefen kansa.
\s5
\v 23 Don haka a ranar nan Allah ya yi nasara da Yabin, sarkin Kan'ana, a idon mutanen Isra'ila.
\v 24 Ƙarfin mutanen Isra'ila ya ƙaru sosai gãba da Yabin sarkin Kan'ana, har suka hallakar da shi.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 A ranar nan ne Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa:
\v 2 "Sa'ad da shugabanin suka ɗauki jagorancin Isra'ila, sa'ad da mutane cikin murna suka miƙa kai domin yaƙi - mu yabi Yahweh!
\s5
\v 3 Ku saurara, ku sarakuna! Mai da hankali, ku shugabanni! Ni, Zan raira waƙa ga Yahweh, Allahn Isra'ila.
\v 4 Yahweh, sa'ad da ka fito daga Se'ir, a sa'ad da ka tako daga Idom, ƙasa ta girgiza, kuma sammai sun yi makyarkyata; har giza-gizai sun zubo ruwa ƙasa.
\s5
\v 5 Duwatsu na rawa a gaban Yahweh; har Tsaunin Sinai na rawa a gaban Yahweh, Allahn Isra'ila.
\v 6 A kwanakin Shamgar (ɗan Anat), a kwanakin Ya'el, an ƙyale manyan hanyoyi, kuma waɗanda ke tafiya na yin amfani da ƙananan hanyoyin ne kurum.
\s5
\v 7 Akwai jarumawa ƙaɗan ne a Isra'ila, har sai lokacin da ni Debora, na ɗauki matsayin shugabanci a Isra'ila - uwa ta ɗauki shugabancin a Isra'ila!
\v 8 Sa'ad da suka zaɓi sababbin alloli, an yi faɗa a ƙofofin biranen amma duk da haka babu garkuwoyin yaƙi ko mãsu da aka gani a cikin mutum dubu arba'in a Isra'ila.
\s5
\v 9 Zuciyata ta tafi ga shugabanin rundunar sojojin Isra'ila, tare da mutanen da a cikin murna suka miƙa kansu - mu yabi Yahweh domin su!
\v 10 Yi tunani a kan wannan - ku masu hawan fararen jakuna kuna zaune a shinfiɗun ɗaurawa, da ku masu tafiya a hanyar.
\s5
\v 11 Ji muryoyin waɗanda ke waƙa a cikin lambu. A wurin suke sake faɗin adalcin ayyukan Yahweh, da aikin adalcin jarumansa a Isra'ila. Sai mutanen suka sauko ƙasa zuwa ƙofofin birnin
\s5
\v 12 Tashi, tashi, Debora! Tashi, tashi, ki raira waƙa! Tashi tsaye, Barak, ka kama 'yan kurkukunka, kai ɗan Abinowam.
\v 13 Sai waɗanda suka tsira suka zo gun masu martaba; mutanen Yahweh suka zo gare ni tare da jarumawa.
\s5
\v 14 Suka iso daga Ifraim, waɗanda asalinsu na Amalek ne; mutanen Benyamin sun bi ka. Daga Makir shugabanin yaƙi suka iso, daga Zebulun kuma waɗanda ke ɗauke da sandar hafsan.
\s5
\v 15 Sarakunan da ke Issaka na tare da Debora; kuma Issaka na tare da Barak yana biye da shi da sauri har cikin kwari a bisa ga umurninsa. Cikin zuriyar Ruben ana ta nazari a zuci.
\s5
\v 16 Me ya sa kuka zauna a tsaƙanin wuraren jin ɗumi, kuna sauraron makiyaya na wasa da sandunansu domin garkensu? Zuriyar Ruben dai suna ta nazari a zuci.
\s5
\v 17 Giliyad ya tsaya a ƙeteren Yodan; kuma Dan, me ya sa yake ta zirgazirga a jiragen ruwa? Asha ya kasance a bakin teku ya kuma zauna kusa da babbar matsayar jiragen teku,
\v 18 Zebulun kabila ce waɗanda suka sadaukar da rayukansu har ga mutuwa, har da Naftali ma, a filin yaƙi.
\s5
\v 19 Sarakunan suka iso, suka yi faɗa; sarakunan Kan'ana suka yi faɗa a Ta'anak cikin ruwayen Megiddo, Amma ba su ɗauki azurfa a matsayin ganima ba.
\v 20 Daga sammai, taurari suka yi faɗa, daga hanyoyinsu a ƙeteren sammai suka yi faɗa gãba da Sisera.
\s5
\v 21 Kogin Kishon ya share su daga nan, wannan tsohon kogin, Kogin Kishon. Taka ya raina, ka yi ƙarfin hali!
\v 22 Sai ƙarar kofaton dawakan - sukuwa, sukuwar jarumawansa.
\s5
\v 23 'La'anta Meroz!' inji mala'ikan Yahweh. 'Tabbas la'anta mazaunanta! - saboda ba su zo sun taimake Yahweh ba - su taimaki Yahweh a yaƙi gãba da manyan jarumawa.'
\s5
\v 24 An albarkaci Ya'el fiye da dukkan mata, Ya'el (matar Heber Bakenine), ita mai albarka ce fiye da dukkan matan da ke zama a rumfuna.
\v 25 Mutumin ya biɗi ruwa, sai ta ba shi madara; ta kawo masa nono a akushin da ya cancanci a ba 'ya'yan sarki.
\s5
\v 26 Ta sa hannunta a turken rumfa, da guduma a hannun damarta; da gudumar ta buge Sisera, ta ragargaza kansa. ta farfasa masa ƙwaƙwalwa sa'ad da ta soke shi ta gefen kansa.
\v 27 Ya kasa tashi tsakanin tafinta, ya kwanta warwas a wurin. Tsakanin tafin kafafunta ya faɖi laƙwas. A wurin da ya ɓungire ne aka kashe shi ƙarfi da yaji.
\s5
\v 28 Ta taga ta duba - mahaifiyar Sisera ta duba ta taga ta yi kira cikin baƙinciki, 'Me ya sa aka ɗauki tsawon lokaci karusansa basu iso ba? Me ya sa karar kofaton dawakan da ke jan karusansa suka yi jinkiri?'
\s5
\v 29 Gimbiyoyinta masu hikima suka ba ta amsa, ita kuma ta ba kanta amsa irin tasu.
\v 30 Ko basu samo ganima sun raba ba ne? - Mace, mata biyu domin kowanne mutum; ganimar kyawawan tufafi domin Sisera, tufafi masu tsada, kashi biyu na tufafi masu tsada domin wuyan waɗanda suka kwaso ganima?
\s5
\v 31 Don haka bari dukkan maƙiyanka su lalace, Yahweh! Amma abokanka su zama kamar rana sa'ad da ta tashi a cikin ƙarfinta." Sai ƙasar ta sami salama shekaru arba'in.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Mutanen Isra'ila sun kuma yin abin da ke mugu a fuskar Yahweh, sai ya bada su ga hannun Midiyan na tsawon shekaru bakwai.
\v 2 Ikon Midiyan ya ƙuntata wa Isra'ila. Saboda Midiyan, mutanen Isra'ila sun yi wa kansu mafaka a ramummuka a tuddai da kogonni da wuraren ɓoyewa.
\s5
\v 3 Sai ya zamana a duk lokacin da Isra'ila suka shuka amfanin gona, sai Midiyanawa da Amelikawa da mutanen gabas su kai wa Isra'ila hari
\v 4 Sukan sa mayaƙansu a ƙasar su lalatar da hatsi, har zuwa Gaza. Ba za su bar ko abinci a Isra'ila ba, ko tumaki, ko shanu, ko jakuna ba.
\s5
\v 5 Sa'ad da suka iso da dabbobbinsu da rumfuna, sukan shigo kamar cincirundon fãri, kuma ya kan zama da wuya a ƙidaya mutanen ko raƙumansu, Sun farmaƙe ƙasar ne don su hallaka ta.
\v 6 Midiyan sun rage ƙarfin Isra'ilawa ƙwarai har ya kai ga mutanen Isra'ila yin kira ga Yahweh.
\s5
\v 7 Sa'ad da mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh saboda Midiyan,
\v 8 Yahweh ya aiko annabi ga mutanen Isra'ila. Anabin ya ce masu, "Wannan ne abin da Yahweh, Allahn Isra'ila ya faɗi: 'Na kawo ku daga Masar; Na fitar da ku daga gidan bauta.
\s5
\v 9 Na kuɓutar da ku daga hannun Masarawa, daga kuma hannun dukkan waɗanda ke muzguna maku. Na kore su daga gare ku, na kuma ba ku ƙasarsu.
\v 10 Na ce da ku, "Ni ne Yahweh Ahllahnku; Na Umurce ku kada ku bauta wa allolin Amoriyawa, waɗanda a cikin ƙasarsu ku ke." Amma ba ku yi biyayya da muryata ba,"'
\s5
\v 11 Yanzu kuwa Malai'kan Yahweh ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen rimi a Ofra, wanda yake na Yowash (Ba'abiyezare), sa'ad da Gidiyon, ɗan Yowash, ke bugun alkama a masussuka, a wurin matsar ruwan inabi - don ya ɓoye shi daga Midiyanawa.
\v 12 Mala'ikan Yahweh ya bayyana gare shi ya ce masa, "Yahweh na tare da kai, kai jarumi mai ƙarfi!"
\s5
\v 13 Gidiyon yace masa, "Kash, ubangijina, idan Yahweh na tare da mu, me yasa dukkan waɗannan abubuwan suke faruwa da mu? Ina dukkan ayyukan al'ajibansa da ubaninmu suka labarta mana, sa'ad da suka ce, 'Ba Yahweh ba ne ya kawo mu daga can Masar ba? Amma yanzu Yahweh ya yashe mu ya bayar da mu ga hannun Midiyanawa."
\s5
\v 14 Yahweh ya dube shi ya ce, "Jeka cikin ƙarfin da ka ke da shi. Ka kuɓutar da Isra'ila daga hannun Midiyan. Ko ban aike ka ba ne?"
\v 15 Gidiyon yace masa, "In ka yarda Ubangiji, ta yaya zan kuɓutar da Isra'ila? Duba, iyalina su ne mafi rashin ƙarfi a Manasse, kuma ni ne mafi ƙarancin muhimmanci a gidan mahaifina."
\s5
\v 16 Yahweh yace masa, "Zan kasance tare da kai, kuma za ka yi nasara da dukkan sojojin Midiyanawa kai kaɗai kuwa."
\v 17 Gidiyon yace masa, "Idan kana farinciki da ni, ka ba ni allamar cewa kai ne ka ke magana da ni.
\v 18 In ka yarda, kar ka bar nan, sai na zo gare ka na kawo kyautata na ajiye a gabanka." Yahweh ya ce, "Zan jira sai ka dawo."
\s5
\v 19 Gidiyon kuwa ya je ya shirya ɗan'akuya ya kuma auna gari misalin mudu guda, ya yi gurasa mara yisti. Ya sa nama a kwando, ya kuma sa romon a tukunya ya kawo su gare shi a ƙarƙashin itacen rimi, sai ya miƙa su.
\v 20 Mala'ikan Allah ya ce masa, "Ɗauki naman da gurasa mara yisti ka sa su a wannan dutsen, ka kuma zuba romon a bisan su." Haka kuwa Gidiyon ya yi.
\s5
\v 21 Sai mala'ikan Yahweh ya miƙo kan sandar da ke hannunsa. Da ita ya taɓa naman da gurasa mara yisti; Wuta kuwa ta fito daga dutsen ta cinye naman da gurasar mara yisti. Sai mala'ikan Yahweh ya tafi Gidiyon kuma bai kara ganin shi ba.
\s5
\v 22 Gidiyon ya fahimci cewa wannan mala'ikan Yahweh ne. Gidiyon yace, Ah! Ubangiji Yahweh! Gama na ga mala'ikan Yahweh fuska da fuska!"
\v 23 Yahweh yace ma sa, Salama a gareka! Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba."
\v 24 Sai Gidiyon ya gina bagadi a wurin domin Yahweh. Ya kira shi, "Yahweh salama ne." Har yau yana nan a Ofra ta iyalin Abiyeza.
\s5
\v 25 A daren nan Yahweh yace masa, "Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da bijimi na biyu mai shekara bakwai, kuma ka rurushe bagadin mahaifinka, ka sare Ashera da ke kusa da shi.
\v 26 Ka gina wa Yahweh Allahnka bagadi a kan wannan wurin fakewa, ka gina shi da kyau. Ka miƙa bijimi na biyu a matsayin hadaya ta ƙonawa, kana amfani da itacen Ashera da ka sare."
\s5
\v 27 Sai Gidiyon ya ɗauki goma daga cikin barorinsa ya yi dai dai yadda Yahweh ya faɗa masa. Amma saboda tsananin tsoron iyalin gidan mahaifinsa da mutanen gari bai yi shi da rana ba sai da dare.
\s5
\v 28 Da sassafe lokacin da mutanen gari suka tashi, an kakkarya bagadin Ba'al, Ashera da ke kusa da shi kuma an datse shi, bajimi na biyu kuma an miƙa shi hadaya a kan bagadin da aka gina.
\v 29 Mutanen gari suka ce da junansu, "wa ya yi wannan abu?" Da suka yi magana da waɗansu suka nemi amsoshi, suka ce, "Gidiyon ɗan Yowash ne ya yi wannan abu."
\s5
\v 30 Daga nan sai mutanen gari suka ce da Yowash, Ka fiito da ɗanka domin a kashe shi, saboda ya rushe bagadin Ba'al, ya kuma datse Ashera da ke gefensa."
\s5
\v 31 Yowash yace da dukkan mutanen da ke jayayya da shi, "Za ku yi hamayya domin Ba'al ne? Za ku cece shi ne? Duk wanda ya yi hamayya dominsa, bari a kashe shi da safe, Idan Ba'al allah ne, bari ya kare kansa sa'ad da wani ya rushe bagadinsa."
\v 32 Saboda haka a ranan nan suka kira Gidiyon "Yerub Ba'al," domin ya ce, "Bari Ba'al ya kare kansa," domin Gidiyon ya rushe bagadin Ba'al.
\s5
\v 33 Yanzu dukkan Midiyanawa da Amelikawa da mutanen gabas suka taru wuri ɗaya. Suka ƙetare kogin Yodan suka kuma kafa sansaninsu a kwarin Yezriyel
\s5
\v 34 Amma Ruhun Yahweh ya sauko wa Gidiyon. Gidiyon ya busa ƙaho, yana kiran zuriyar Abiyeza, ko za su bi shi.
\v 35 Ya aiki 'yan saƙo ga dukkan Manasse, kuma suma an kirawo su su bi shi. Ya kuma aiko da 'yan saƙo ga Asha da Zebulun da Naftali, suka kuma fito su tarbe shi.
\s5
\v 36 Gidiyon yace da Allah, "Idan ka yi niyar ka more ni don ka ceci Isra'ila, kamar yadda ka faɗa -
\v 37 Duba, Zan shimfiɗa ƙyallen ulu a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan kyallen ulu kaɗai, amma ƙasa ta kasance a bushe, to zan sani cewa zaka more ni ka ceci Isra'ila kamar yadda ka ce."
\s5
\v 38 Ga abin da ya faru - washegari Gidiyon ya tashi da sassafe, ya matse kyallen ulun wuri ɗaya, har ruwan raɓar daga kyallen ulun ya cika ƙwarya.
\s5
\v 39 Sai Gidiyon yace da Allah, "Kada ka yi fushi da ni, Zan yi magana sau ɗaya kuma. In ka yarda ka bari in ƙara gwaji ɗaya kuma da ƙyallen ulun. Wannan karon, ka sa ƙyallen ulun ya bushe amma bari dukkan ƙasa ta kasance da raɓa.
\v 40 Allah ya yi abin da ya roƙa a cikin daren nan. ƙyallen ulun ya bushe amma ƙasa ta kasance da raɓa kewaye da shi.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Sai Yerub Ba'al (wato Gidiyon) ya tashi da sassafe, da dukkan mutanen da ke tare da shi, sai suka yi sansani a gefen rafin Harod. Zangon Midiyan kuwa na ɓangaren arewa da su a kwari kusa da tuddun Moreh.
\s5
\v 2 Yahweh yace da Gidiyon, "Ana da sojoji fiye da yadda nake so domin in ba ka nasara kan Midiyanawa, don kar Isra'ila ta yi taƙama a kaina, cewa, 'Ikonmu ne ya cece mu.' Yanzu kuwa, ka shaida a cikin kunuwan mutanen ka ce,
\v 3 'Duk wanda ya ke jin tsoro, duk wanda ke rawar jiki, bari ya koma ya tashi daga Tsaunin Giliyad."' Sai mutane dubu ashirin da biyu suka tafi, dubu goma kuma suka rage.
\s5
\v 4 Sai Yahweh yace da Gidiyon, "Mutanen sun yi yawa har yanzu, Kai su wurin ruwa, Ni kuma zan rage yawansu domin ka a wurin. Idan nace maka, 'Wannan zai tafi da kai,' zai tafi da kai; amma idan na ce, 'Wannan ba zai tafi da kai ba,' ba zai tafi ba."
\s5
\v 5 Sai Gidiyon ya kawo mutanen wurin ruwan, Yahweh kuma ya ce masa, "Ware duk wanda ya lashi ruwan, kamar yadda kare ke lasa, daga waɗanda suka durƙusa ƙasa suka sha."
\v 6 Mutum ɗari uku suka lasa.
\s5
\v 7 Yahweh yace da Gidiyon, "Da mutum ɗari ukun da suka lashi ruwa, zan 'yantar da kai in ba ka nasara a kan Midiyanawa. Sai kowanne mutum ya koma wurinsa."
\v 8 Saboda haka waɗanda aka zaɓa suka ɗauki kayayyakin aiki da kakakinsu. Gidiyon ya komar da mazan Isra'ila, kowanne zuwa rumfarsa, amma ya keɓe mutum ɗari uku. Midiyanawan kuwa sun yi zango a ƙasa da shi a cikin kwari.
\s5
\v 9 A wannan daren Yahweh ya ce masa, "Tashi! ka kai wa sansanin hari, domin zan ba ka nasara a kansa.
\v 10 Amma idan kana tsoron gangarawa kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka,
\v 11 sai ka ji abin da suke faɗi, ƙarfin halinka kuma ya ƙarfafa har ka kai hari a sansanin." Sai Gidiyon ya tafi da Fura baransa, zuwa ƙofar sansanin.
\s5
\v 12 Midiyanawa, da Amelikawa da dukkan mutanen gabas suka yi shiri a kwarin, yawansu kamar cincirindon fãra. Raƙumansu sun fi ƙarfin a ƙirga; sun fi yashin teku yawa.
\s5
\v 13 Sa'ad da Gidiyon ya iso wurin, wani mutum ya na gaya wa abokinsa mafarkin da ya yi. Mutumin yace, "Duba! Na yi mafarki, sai na ga dunƙulen gurasar bali mai fuskar waina ta na gangarawa zuwa sansanin Midiyanawa. Ta iso rumfar, ta kuma buge ta da ƙarfi har sai da ta faɗi ta juyad da rumfar, ta kuma kwantar da ita ƙasa.
\v 14 Sai ɗaya mutumin ya ce, "Wannan ba komai ba ne ban da takobin Gidiyon (ɗan Yowash), Ba'isra'ile. Allah ya ba shi nasara a kan Midiyan da dukkan sojojinsu."
\s5
\v 15 Sa'ad da Gidiyon ya ji yadda aka sake faɗin mafarkin da fasararsa, ya russuna ƙasa ya yi sujada. Ya koma sansanin Isra'ila ya ce, "Ku tashi tsaye! Yahweh ya ba ku nasara a kan sojojin Midiyan."
\v 16 Ya raba mutun ɗari uku kashi uku, sai ya ba dukkansu kakaki da gorunan da ba kome a ciki, sai cocila.
\s5
\v 17 Ya ce masu, "Dube ni ku yi abin da na yi. Duba! Sa'ad da na iso gab da iyakar sansanin, dole ku yi abin da na yi.
\v 18 Sa'ad da na busa kakaki, Ni da duk waɗanda ke tare da ni, sai ku busa naku kakakin har a dukkan gefen sansanin gaba ɗaya kuma ku yi ihu, 'Domin Yahweh da kuma domin Gidiyon!'"
\s5
\v 19 Sai Gidiyon da mazaje ɗari uku waɗanda ke tare da shi suka iso gabashin sansanin, misalin ƙarfe goma na dare. Dai-dai lokacin da Midiyanawan na canjin masu gadi, suka busa kakaki suka kuma farfasa gorunan da ke hanuwansu
\s5
\v 20 Rundunoni ukun suka busa kakaki suka kuma farfasa gorunan. Suka riƙe tociloli a hannayen hagunsu da kuma kakaki a hannayen damarsu don su busa su. suka yi ihu, "Takobin Yahweh da na Gidiyon."
\v 21 Kowanne mutum ya tsaya a wurinsa a kewaye da sansanin sai dukkan sojojin Midiyanawa suka tsere suka yi ihu suka ruga a guje.
\s5
\v 22 Sa'ad da suka busa kakaki ɗari ukun, Yahweh ya sa kowanne sojan Midiyanawa ya ɗauki takobi gãba da ɗan'uwansa da kuma gãba da dukkan sojojin. Sojojin suka tsere ta Bet Shitta har zuwa Zerera, harma ga iyakar Abel Mehola, kusa da Tabbat.
\v 23 Aka kira mazajen Isra'ila daga Naftali da Asha, da dukkan Manasa, suka kuma fafari Midiyan.
\s5
\v 24 Gidiyon ya aiki masu ba da saƙo a ko'ina a duk tuddun ƙasar Ifraim, cewa, "A gangara gãba da Midiyan a mamaye Kogin Yodan, har faɗin Bet Bara, a tsayar da su." Saboda haka dukkan mutanen Ifraim suka taru suka kuma mamaye ruwayen, har zuwa Bet Bara da Kogin Yodan.
\v 25 Suka cafko 'ya'yan sarakuna biyu na Midiyan wato Oreb da Ze'eb. Suka kashe Oreb a dutsen Oreb, suka kuma kashe Ze'eb a wurin matsar ruwan Inabi ta Ze'eb. Suka bi bayan Midiyanawa, suka kuma taho da kawunan Oreb da Ze'eb ga Gidiyon, wanda ke a keteren Yodan.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Mutanen Ifraim suka ce da Gidiyon, "Mene ne wannan da ka yi mana? Ba ka kira mu ba sa'ad da ka tafi wurin faɗa da Midiyan." Daga nan sai suka yi gardama mai zafi da shi.
\s5
\v 2 Sai ya ce da su, "Me na yi idan a ka kwatanta da ku?" Kalar inabin Ifraim, ba ta fi cikakken girbin inabin Abiyeza ba?
\v 3 Allah ya ba ku nasara a kan 'ya'yan sarakunan Midiyan -- Oreb da Ze'eb! Wacce riba na ci idan an kwatanta da ku?" Sai fushinsu ya huce sa'ad da ya faɗi masu haka.
\s5
\v 4 Gidiyon ya zo ya haye Yodan, shi da mutane ɗari uku da ke tare da shi. Sun gaji, amma duk da haka ba su fasa bi ba.
\v 5 Ya ce da mutanen Sukkot, "Idan kun yarda ku ba mutanen da suka biyo ni dunƙulen gurasa, gama sun gaji, domin ina bin sawunsu Zeba da Zalmunna sarakunan Midiyan."
\s5
\v 6 Sai shugabannin suka ce, "Hannuwan Ziba da Zalmunna suna hannunka ne a yanzu? Me zai sa mu ba sojojin ka gurasa?"
\v 7 Gidiyon yace, "Idan Yahweh ya ba mu nasara a kan Zeba da Zalmunna, zan yayyaga maku fata da ƙayayuwan sahara da tsabgogi."
\s5
\v 8 Ya wuce zuwa Feniyel ya yi magana ga mutanen can ma, mutanen Feniyel masu ka ba shi amsa dai-dai da ta mutanen Sukkot.
\v 9 Shi kuma ya yi magana da mutanen Feniyel ya ce, "Idan na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiyar."
\s5
\v 10 Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da sojansu, wajan mutum dubu goma sha biyar, dukkan waɗanda suka rage a sojojin mutanen Gabas, gama mutane 120,000 waɗanda a ka koyar a yaƙi da takobi sun faɗi.
\s5
\v 11 Gidiyon ya yi gaba kan hanyar da mazauna rumfa, ya wuce Nabo da Yogbeha. Ya ci nasara a kan sojojin abokan gãba, da yake ba su yi zaton za a kawo masu hari ba.
\v 12 Zeba da Zalmunna suka gudu, Gidiyon kuma ya bi su, ya kamo sarakunan Midiyan su biyu - Zeba da Zalmunna - ya sa sojojinsu cikin ruɗami.
\s5
\v 13 Gidiyon ɗan Yowash ya dawo daga yaƙi, ya bi ta Heres.
\v 14 Ya gamu da wani saurayi daga mutanen Sukkot, ya nemi shawara daga wurinsa. Shi kuma ya baiyana masa game da shugabannin Sukkot da dattawansu mutum saba'in da bakwai.
\s5
\v 15 Gidiyon ya zo ya sami mutanen Sukkot, ya ce "Da su ga Zeba da Zalmunna, da ku ka yi mani ba'a a kansu cewa, ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ne?" Ba mu sani wai sai mun ba sojojinka gurasa ba.
\v 16 Gidiyon ya ɗauki dattawan ya hori mutanen Sukkot da ƙayayuwa.
\v 17 Ya rushe hasumiyar Feniyel ya kashe mutanen wannan birnin.
\s5
\v 18 Sa'an nan Gidiyon yace da Zeba da Zalmuna, "Wadanne irin mazaje ku ka kashe a Tabor"? Suka amsa, "Kamar yadda ka ke haka su ke, kowannensu kamar ɗan sarki ya ke."
\v 19 Gidiyon yace, 'Yan'uwana ne, 'ya'yan mamata ne. Muddin Yahweh na raye, da ba ku kashe su ba, ni ma da ba zan kashe ku ba."
\s5
\v 20 Ya ce da Yeter (ɗansa na fari), "Tashi ka karkashe su!" Amma matashin bai zaro takobinsa ba, yana jin tsoro, saboda shi yaro ne.
\v 21 Sai Zeba da Zalmunna suka ce, "Tashi ka kashe mu kai da kan ka! gama yadda mutum yake, haka ƙarfinsa yake." Gidiyon ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna, kuma ya ɗauke kayan adon da ke a wuyan raƙumansu.
\s5
\v 22 Mutanen Isra'ila suka ce da Gidiyon, "Ka yi mulkin mu da kai - da 'ya'yanka da jikokinka,- saboda ka cece mu daga hannun Midiyan."
\v 23 Gidiyon yace da su, "Ni ba zan mulke ku ba, ɗana kuma ba zai mulke ku ba. Yahweh ne zai yi mulkinku.
\s5
\v 24 Gidiyon yace da su, "Zan roƙe ku: abu ɗaya, kowannenku ya ba ni ɗankunne daga abin da ya samu ganima." (Midiyanawa su na da 'yankunne na zinariya saboda su "ya'yan Isma'ila ne.)
\v 25 Suka amsa suka ce, "Da farinciki za mu baka su". Suka yi shimfiɗa, kowannen su ya buɗe ganimarsa suka yi ta jefa 'yan kunnen a kan ta daga cikin ganima.
\s5
\v 26 'Yankunnen da ya buƙata, nauyinsu shekel 1,700 na zinariya ne. Wannan ganimar ƙari ee a kan kayan adon sarakunan Midiyan wato tufafinsu na shunaiya. Da kuma sarƙoƙin da ake sawa a wuyan raƙumansu.
\s5
\v 27 Gidiyon ya yi falmara da 'yankunnen da yakarɓa yasa a cikin birnisa, a Ofra, dukkan Isra'ila suka yi karuwanci ta wurin yi masa sujada a can. Wannan ya zama tarko ga Gidiyon da waɗanda ke cikin gidansa.
\v 28 Mutanen Isra'ila suka mallake Midiyanawa, kuma basu ƙara tada kansu ba. Ƙasar ta zauna cikin salama shakara arba'in a cikin kwanakin Gidiyon.
\s5
\v 29 Yerub Ba'al ɗan Yowash ye je ya zauna a cikin gidansa.
\v 30 Gidiyon yana da 'ya'ya saba'in a zuriyarsa, da yake yana da mata da yawa.
\v 31 Ƙwarƙwararsa wadda ke a Shekem ma ta haifa masa ɗa, Gidiyon kuma ya ba shi suna Abimelek.
\s5
\v 32 Gidiyon ɗan Yowash ya mutu cikin shekarun tsufa masu kyau, aka bizne shi cikin kabarin Yowash ubansa, na kabilar Abiyeza.
\v 33 Bayan mutuwar Gidiyon mutanen Isra'ila suka koma karuwanci ta wurin bautawa Ba'aloli, sun maida Ba'al Berit allahnsu.
\s5
\v 34 Mutanen Isra'ila ba su tuna su girmama Yahweh Allahnsu ba, wanda ya kuɓutar da su daga hannun abokan gãbarsu ta kowanne gefe.
\v 35 Ba su kiyaye alƙawuransu ga gidan Yerub Ba'al ba (wato Gidiyon), sakamakon dukkan abin kirki da ya yi a Isra'ila.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Abimelek ɗan Yarub Ba'al, ya tafi wajan 'yan'uwan mamarsa a Shekem, ya ce da su da dukkan dangin mamarsa,
\v 2 "Idan ka yarda ka fadi wannan domin dukkan shugabannin Shekem su ji, 'Wanne ya fi a gare ku, dukkan 'ya'ya saba'in na Yerub Ba'al su yi mulki a kanku ko kuwa guda ɗaya ya mulke ku?' Ku tuna ni ƙashinku ne da jikinku."
\s5
\v 3 Dangin mamarsa suka yiwa shugabannin Shekem magana a kansa, suka amince, gama suka ce, "Shi ɗan'uwanmu ne"
\v 4 Suka ba shi azurfa guda saba'in daga gidan Ba'al Berit, Abimelek kuma ya yi anfani da ita ya gaiyato mutane marasa ɗa'a da rashin hankali suka yi tafiya tare da shi.
\s5
\v 5 Abimelek ya tafi gidan ubansa a Ofra ya yi makokin 'yan'uwansa su saba'in, 'ya'yan Yerub Ba'al a bisa wani dutse. Yotam ƙaraminsu kaɗai ya rage cikin 'ya'yan Yerub Ba'al, gama ya ɓoye kansa.
\v 6 Dukkan shugabannin Shekem da Bet Millo suka zo suka taru suka maida Abimelek ya zama sarki daura da rimi, kusa da ginshiƙi wanda ke cikin Shekem.
\s5
\v 7 Sa'ad da Yotam ya ji haka, ya tafi ya tsaya a kan Tsaunin Gerizim. Ya tada murya ya ce da su, "Ku saurare ni, ku shugabannin Shekem, ko Allah ya ji ku.
\v 8 Itatuwa suka je domin su naɗa sarki. Gama sun ce da itacen zaitun ka zama sarkinmu,'
\s5
\v 9 Amma itacen zaitun yace da su, 'In dena ba da maina da ake anfani da shi ana girmama alloli da mutane, in kuma dawo wurin sauran itatuwa?'
\v 10 Itatuwan suka ce da itacen ɓaure, 'Kazo ka yi mulkin mu,'
\v 11 Amma itacen ɓaure yace da su, 'Zan bar zaƙina da 'ya'yana masu kyau, domin in dawo in dogara ga sauran itatuwa?'
\s5
\v 12 Itatuwa suka ce da inabi, 'Kazo ka yi mulkin mu,'
\v 13 Inabi ya cewa, 'Zan bar ba da sabon ruwan anab ɗina mai ƙarfafa alloli da mutane, in dawo in dogara ga sauran itatuwa?'
\v 14 Sai dukkan itatuwa suka ce da ƙaya, 'Ki zo ki yi mulkin mu.'
\s5
\v 15 Sai ƙaya ta ce da itatuwa, 'Idan gaskiya ne kuna so ku naɗa ni sarauniya a bisanku, sai kowannenku ya zo ya sami wuri a ƙarƙashin inuwata. Idan ba haka ba, bari wuta ta fito daga cikin ƙaya ta ƙone rimi na Lebanon.
\v 16 To yanzu, idan dai gaskiya ne kun yi aminci, da kuka sa Abimelek ya zama sarkinku, idan kun yi abin da ya wajaba ga Yerub Ba'al da gidansa, kuma kun yi masa horon da ya kamata -
\s5
\v 17 - da tunanin ubana ya yi faɗa dominba, ya sa ransa cikin hatsari ya kuɓutar da ku daga hannun Midiyan -
\v 18 amma yau kun tashi gãba da gidan ubana, kun kashe 'ya'yansa saba'in a bisa dutse ɗaya. Sa'an nan kun maida Abimelek ɗan baiwarsa ya zama sarkin shugabanin Shekem, da yake shi ɗan'uwanku ne.
\s5
\v 19 Idan dai kun yi gaskiya da girmamawa ga gidan Yerub Ba'al, to ku yi farinciki da Abimelek shi ma ya yi farinciki da ku.
\v 20 Amma idan ba haka ba ne, bari wuta ta fito daga cikin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet Millo. Bari wuta ta fito daga mutanen Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek.
\v 21 Yotam ya gudu ya tafi ya gudu ya tafi Biya. Ya zauna a can da ya ke nesa ta ke da Abimelek, ɗan'uwansa.
\s5
\v 22 Abimelek ya yi mulkin Isra'ila shekaru uku.
\v 23 Sai Yahweh ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da shugabannin Shekem. Shugabannin Shekem suka juyawa Abimelek baya.
\v 24 Yahweh ya yi haka ne domin a rama muguntar da aka yi a kan 'ya'yan Yerub Ba'al su saba'in, aka kuma lissafta muguntar a kan Abimelek ɗan'uwansu. Haka kuma aka lissafta muguntar kisan a kan shugabannin Shekem saboda sun taya Abimelek ya kashe 'yan'uwansa maza.
\s5
\v 25 Shugabannin Shekem suka sa mazaje su yi masa kwanton ɓauna, suka yiwa dukkan masu wucewa fashi a kan hanyar. Aka kaiwa Abimelek rahoton wannan abu.
\s5
\v 26 Ga'al ɗan Ebed yazo shi da 'yan'uwansa suka je Shekem. Shugabannin Shekem kuwa sun amince da shi.
\v 27 Suka je cikin gona suka kakkaryo kuringar anab domin su bi ta kai. Suka yi buki a gidan allahnsu, suka ci suka sha, suka la'anci Abimelek.
\s5
\v 28 Ga'al ɗan Ebed ya ce, "Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub Ba'al ba ne? Zebul ba jami'in sa ba ne? Ya bautawa mutanen Hamor, uban Shekem! Me zai sa mu bautawa Abimelek?
\v 29 Dama mutanen nan ƙarƙashi na suke! In fitar da Abimelek. In ce da Abimelek, 'Ka kira dukkan sojanka dukka.'"
\s5
\v 30 Sa'ad da Zebul, jami'in birni, ya ji maganar Ga'al da Ebed, ya ji haushi sosai.
\v 31 Ya aika da 'yan saƙo zuwa ga Abimelek domin ya ruɗe shi, cewa, "Duba, ga Ga'al ɗan Ebed da 'yan'uwansa suna zuwa Shekem, suna kuma zuga birnin gãba da kai.
\s5
\v 32 Ka tashi idan dare ya yi, kai da sojojin da ke tare da kai ku yi masu kwanton ɓauna a cikin daji.
\v 33 Da safiya ta yi, sa'ad da rana ta fito, ka shiga ka kaiwa birnin hari. Idan shi da mutanensa suka taso maka, ka yi masu abin da ka ga dama."
\s5
\v 34 Abimelek ya tashi daddare, suka kasu huɗu suka yiwa Shekem kwanton ɓauna.
\v 35 Ga'al ɗan Ebed ya tashi ya tsaya a ƙofar birni. Abimelek da mazajen da ke tare da shi suka fito daga inda suke a ɓoye.
\s5
\v 36 Da Ga'al ya ga mazajen, ya ce da Zebul, "Duba ga mutane na gangarowa daga kan duwatsu!" Zebul ya ce da shi, "Kana ganin inuwoyi a kan duwatsu ne kamar mutane."
\v 37 Ga'al ya ƙara cewa, "Duba mutane suna gangarowa daga tsakiyar ƙasa, wani kashi kuma na zuwa ta hanyar rimi na masu duba."
\s5
\v 38 Sai Zebul ya ce da shi, "Ina maganarka ta fankama yanzu, 'Kai da ka ce wane ne Abimelek da zamu bauta masa?' Waɗannan ba su ne mazajen da ka rena ba? Ka fita yanzu ka yi faɗa da su."
\v 39 Ga'al ya jagoranci mazajen Shekem, suka yi faɗa da Abimelek.
\v 40 Abimelek ya kore shi, Ga'al ya gudu daga gabansa. Da yawa suka faɗi da raunuka kafin mashgin ƙofar birni.
\s5
\v 41 Abimelek ya tsaya a Aruma, Zebul ya kori Ga'al da 'yan'uwansa daga cikin Shekem.
\v 42 Washegari mutanen Shekem suka fita cikin jeji, a ka kaiwa Abimelek rahoton haka.
\v 43 Ya ɗauki mazajensa ya raba su uku, su ka yi kwanton ɓauna a jeji. Ya ga mazajen suna fitowa daga cikin birni, ya kai masu hari ya kashe su.
\s5
\v 44 Abimelek da ƙungiyoyin da ke tare da shi suka kai hari suka toshe ƙofar birni. Sauran kungiyoyi biyu suka kaiwa waɗanda ke cikin jeji suka kashe su.
\v 45 Abimelek ya yi faɗa da birnin dukkan yini, ya ci birnin ya kashe mutanen da ke cikinsa. Ya rushe ganuwar birnin ya barbaɗa mata gishiri.
\s5
\v 46 Sa'ad da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji, suka shiga babbar maɓoya ta gidan El-Berit.
\v 47 Aka kaiwa Abimelek labari cewa dukan shugabannin sun taru a hasumiyar Shekem.
\s5
\v 48 Abimelek tare da mazajen da ke tare shi suka hau Tsaunin Zalmon. Abimelek ya ɗauki gatari ya datso rassa. Ya ɗora a kafaɗarsa ya ummurci mazajen da ke tare da shi. "Abin da ku ka ga na yi, ku yi sauri kowa ya yi."
\v 49 Haka kowannen su ya saro rassa suka bi Abimelek. Suka tara su jikin hasumiyar birni, suka sa wuta, dukkan mutanen da ke hasumiyar Shekem suka mutu, kusan su dubu maza da mata.
\s5
\v 50 Sai Abimelek ya tafi Tebez, ya ya kafa sansani a Tebez ya mallake ta.
\v 51 Amma akwai wata hasumiya mai karfi a birnin, dukan mazaje da mata suka shiga cikin ta suka kulle kansu. Sa'an nan sai suka hau can kan hasumiyar.
\s5
\v 52 Abimelek yazo wurin hasumiyar da faɗa, ya zo kusa kofar domin ya ƙone ta.
\v 53 Amma wata mace ta sako nuƙunyar dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa masa kwanya.
\v 54 Nan da nan ya kira saurayin da ke ɗaukar masa kayan yaƙi ya ce masa, "Ka zaro takobinka ka kashe ni, domin kada a ce, 'mace ce ta kashe shi.'" Sai saurayin ya soke shi, ya mutu.
\s5
\v 55 Sa'ad da mazajen Isra'ila suka ga Abimelek ya mutu, sai suka koma gida.
\v 56 Yahweh ya ɗauki fansa a kan Abimelek saboda muguntar da ya yi ta kashe 'yan'uwansa su saba'in.
\v 57 Yahweh ya mai da muguntar mutanen Shekem ta koma kan su, da la'anar Yotam ɗan Yerub Ba'al.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Bayan Abimelek, Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo, mutumin Issaka wanda ya zauna a Shamir, a ƙasar duwatsu ta Ifraim, ya taso domin ya ceci Isra'ila.
\v 2 Ya alƙalanci Isra'ila shekara ashirin da uku. Ya mutu aka binne shi a Shamir.
\s5
\v 3 Ya'ir Bagiliyade ya bi bayansa, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara ashirin da biyu.
\v 4 Yana da 'ya'ya talatin, masu hawan jakuna talatin, suna da birane talatin, waɗanda a ke kira Habbot Ya'ir har zuwa yau, suna cikin ƙasar Giliyad.
\v 5 Ya'ir ya mutu a ka binne shi a cikin Kamon.
\s5
\v 6 Mutanen Isra'ila suka ƙara a kan muguntar da suka yi a idanun Yahweh, suka bautawa Ba'al, da Ashtoret allolin Aram, da allolin Sidon, da allolin Mowab da allolin mutanen Amon da allolin Filistiyawa. Suka watsar da Yahweh suka dena bauta masa.
\v 7 Yahweh ya yi fushi da mutanen Isra'ila, ya sayar da su a hannun Filistiyawa da Amoniyawa.
\s5
\v 8 Suka ragargaza Isra'ila suka gallaza masu azaba a wannan shekara, shekara goma sha takwas suna gallazawa mutanen Isra'ila waɗanda suke a ƙetaren Yodan a ƙasar Amoriyawa wadda ke cikin ƙasar Giliyad.
\v 9 Sai Amoniyawa suka ƙetare Yodan garin su yi faɗa da Yahuda, da Benyamin da gidan Ifraim, domin a wulaƙanta Isra'ila.
\s5
\v 10 Sa'an nan mutanen Isra'ila suka yi kira ga Yahweh, suka ce, "Mun yi maka zunubi da yake mun watsar da kai mun bautawa Ba'al."
\v 11 Yahweh yace da mutanen Isra'ila, "Ban ceto ku daga Masarawa da Amoriyawa da Amoniyawa da Filistiyawa
\v 12 da kuma Sidoniyawa ba?" Amelikawa da Ma'oniyawa waɗanda suke gallaza maku; kuka kira ni na, ceto ku daga ikonsu.
\s5
\v 13 Duk da haka kuka watsar da ni kuka bautawa waɗansu alloli. Saboda haka ba zan ƙara wani lokaci na ceton ku ba.
\v 14 Ku tafi wurin allolin da ku ke bautawa. Sai su kuɓutar da ku idan kuna da damuwa."
\s5
\v 15 Mutanen Isra'ila suka ce da Yahweh, "Mun yi zunubi. Ka yi mana abin da ya yi maka kyau. Sai dai idan ka yarda ka cece mu yau."
\v 16 Suka rabu da baƙin allolin da ke tare da su, suka yi sujada ga Yahweh. Daga nan ne Yahweh bai ƙara riƙe damuwarsu ba.
\s5
\v 17 Sa'an nan Amoniyawa suka taru suka kafa sansani a Giliyad. Isra'ilawa kuma suka taru suka kafa sansaninsu a Mizfa.
\v 18 Shugabannin Giliyad suka ce da junansu, "Wane ne zai fara yin faɗa da Amoniyawa? Shi ne zai zama shugaba a kan dukkan mazauna Giliyad."
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Sai ga Yafta mutumi Giliyad babban mayaƙi ne, amma ɗan karuwane. Giliyad ne ubansa.
\v 2 Matar Giliyad ta haifa masa waɗansu 'ya'ya, sa'ad da suka yi girma sai suka kori Yafta daga gidan, suka ce masa, "Ba zaka gaji kome a iyalinmu ba. Kai ɗan wata mata ne."
\v 3 Sai Yafta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya tafi ya zauna a ƙasar Tob. Mutane marar sa ɗa'a suka haɗu da Yafta, suka tafi tare da shi.
\s5
\v 4 Bayan waɗansu kwanaki, mutanen Amon suka yi yaƙi da Isra'ila.
\v 5 Sa'ad da mutanen Amon suka yi yaƙi da Isra'ila, sai shugabannin Giliyad suka je suka dawo da Yafta daga ƙasar Tob.
\v 6 Suka ce da Yafta, "Zo ka zama shugabanmu domin mu yi faɗa da mutanen Amon."
\s5
\v 7 Yafta yace da shugabannin Giliyad, "Kun ƙi ni kun kore ni daga gidan ubana. Me ya sa kuka zo wurina yanzu da kuka sami damuwa?"
\v 8 Shugabannin Giliyad, suka ce da Yafta, "Shi yasa muka zo wurin ka yanzu, ka zo muje ka yi faɗa da mutanen Amon, za ka zama shugaba a kan dukan mazauna a Giliyad."
\s5
\v 9 Yafta yace da Shugannin Giliyad, "Idan ku ka kawo ni gida domin in yi faɗa da mutanen Amon, idan Yahweh ya ba mu nasara a kan su, zan zama shugabanku."
\v 10 Shugabannin Giliyad suka ce da Yafta, "Yahweh ya zama shaida tsakanin mu da kai idan ba mu yi yadda muka ce ba."
\v 11 Sai Yafta ya tafi tare da shugabannin Giliyad, mutanen suka sa ya zama jagora da shugaban sojojinsu. Sa'ad da yake a gaban Yahweh a Mizfa, Yafta ya maimaita dukkan alƙawuran da ya yi.
\s5
\v 12 Daga nan Yafta ya aika jakadu wurin sarkin mutanen Amom, cewa, "Wacce matsala ce tsakaninmu da ku? Me ya sa kuka zo ku ƙwace kasarmu?
\v 13 Sarkin mutanen Amon ya amsa wa jakadun Yafta, "Saboda lokacin da Isra'ila suka fito daga Masar, sun ƙwace ƙasarmu daga Arnon zuwa Yabbok har zuwa Yodan. Yanzu ku maido mana da ƙasarmu cikin salama."
\s5
\v 14 Yafta ya sake aikawa da jakadu wurin sarkin mutanen Amon,
\v 15 ya ce, "Ga abin da Yafta ke cewa: Isra'ila ba su ɗauki ƙasar Mowab da ƙasar mutanen Amon ba,
\v 16 amma Isra'ila sun fito daga Masar suka bi ta jeji zuwa Tekun Iwa zuwa Kadesh."
\s5
\v 17 Sa'ad da Isra'ila suka aika jakadu zuwa sarkin Idom, cewa, 'Idan ka yarda ka bari mu wuce ta ƙasarka', amma sarkin Idom bai saurare su ba. Suka kuma aika da jakadu wurin sarkin Mowab, amma ya ƙi, sai Isra'ila suka tsaya a Kadesh.
\v 18 Sai suka bi ta jeji su kewaye ƙasar Idom da ƙasar Mowab, sai suka bi ta gabas da ƙasar Mowab, suka raɓi ƙasar Arnon suka sauka. Amma ba su je yankin Mowab ba, da ya ke Arnon iyakar Mowab ce.
\s5
\v 19 Isra'ila suka aika da jakadu wurin Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon; Isra'ila suka ce masa, 'Idan ka yarda ka bari mu bi ta ƙasarka mu je wurin da ke namu.'
\v 20 Amma Sihon bai amince da Isra'ila su bi ta yankinsa ba. Sai Sihon ya tattara sojojinsa ya zakuɗa zuwa Jahaz, can ya yi faɗa da Isra'ila.
\s5
\v 21 Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ba da Sihon da mutanensa a hannun Isra'ila suka yi nasara a kan su. Isra'ila suka mallaki ƙasar Amoriyawa waɗanda ke zaune a wannan, ƙasar.
\v 22 Suka mallake komi da komi na ƙasar Amoriyawa tun daga Arnon har zuwa Yabbok, daga jeji kuma har zuwa Yodan.
\s5
\v 23 Haka kuma Yahweh, Allah na Isra'ila ya kori Amoriyawa a gaban mutanen Isra'ila, ko yanzu kuma za ku mallake ƙasarsu?
\v 24 Ba zaku mallaki ƙasar da Kemosh, allahnku yake ba ku ba? Domin haka duk ƙasar da Yahweh Allahnmu ya ba mu za mu mamaye ta.
\v 25 Yanzu ka fi Balak ɗan Ziffo, sarkin Mowab ne? Ya taɓa yin jayayya da Isra'ila ne? Ya taɓa yin yaƙi da su ne?
\s5
\v 26 Sa'ad da Isra'ila suka zauna a Hesbon da ƙauyukanta shekara dari uku, da Arowa da ƙauyukanta, da kan iyakokin Arnon - meyasa ba ka mallake su a wancan lokaci ba?
\v 27 Ni ban yi maka laifi ba, kai ne ka yi mani laifi da ka kawo mani hari. Yahweh mai shari'a, yau zaya hukunta tsakanin mutanen Isra'ila da mutanen Amon."
\v 28 Amma sarkin mutanen Amon ya yi ƙi gargaɗin da Yafta ya aika masa.
\s5
\v 29 Sai Ruhun Yahweh ya sauko kan Yafta, ya ratsa ta Giliyad da Manasse, ya kuma ratsa ta Giliyad ɗin Mizfa, daga Giliyad ɗin Mizfa ya bi ta mutanen Amon.
\v 30 Yafta ya yi alƙawari da Yahweh ya ce, "Idan ka ba ni nasara a kan mutanen Amon, idan na dawo cikin salama,
\v 31 duk abin da ya fito daga ƙofofin gidana ya tarbe ni zai zama na Yahweh, zan miƙa shi hadaya."
\s5
\v 32 To sai Yafta ya bi ta wurin mutanen Amon ya yi faɗa da su, Yahweh kuma ya ba shi nasara.
\v 33 Yakai masu hari ya yi babban kisa tun daga Arowa har zuwa Minnit - birane ashirin - da zuwa Abel Keramim. Ta haka mutanen Amon suka zauna a ƙarƙashin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 34 Yafta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga ɗiyarsa ta fito tarbarsa da kayan kiɗi da rawa. Ita kaɗai ce ɗiyarsa, banda ita ba shi da wani ɗa ko ɗiya.
\v 35 Da dai ya gan ta ya yage tufafinsa ya ce, "Haba ɗiyata! Kin sa ni nukura, kin sa mani jin zafi a raina! Gama nayi alƙawari ga Yahweh, ba zan iya janye alƙawarina ba.
\s5
\v 36 Ta ce masa "Babana, Ka yi wa Yahweh alƙawari, ka yi mani ko mene ne ka yi wa Yahweh alƙawari gama Yahweh ya ɗaukar maka fansa a kan abokan gabarka, Amoniyawa.
\v 37 "Ta cewa babanta, "Bari wannan alƙawari ya zauna a kaina, ka bani wata biyu da zan je kan duwatsu in yi kukan budurcina ni da ƙawayena."
\s5
\v 38 Ya ce da ita. "Jeki." Ya bata wata biyu. Ta tafi, ta bar shi ta tafi ita da Ƙawayenta suka yi kukan budurci a cikin tuddai.
\v 39 Bayan watanni biyun ta dawo wurin babanta, wanda da ita bisa ga alƙawari na wa'adi. Ita kuwa ba ta san namiji ba, wannan ya zama al'ada a cikin Isra'ila
\v 40 'yan'matan Isra'ila kowacce shekara sukan ɗauki kwanaki huɗu, suna maimaita labarin ɗiyar Yafta Bagiliyade.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Kira ya zo ga mazajen Ifraim, suka bi ta Zafon suka ce da Yafta, "Meyasa ka wuce ka yi faɗa da mutanen Amon baka ce mu zo mu tafi tare da kai ba? Za mu ƙone gidanka a kan ka."
\v 2 Yafta ya ce da su, "Ni da mutanena muna da babbar matsala da mutanen Amon. Sa'ad da na kira ku baku cece ni daga wurinsu ba."
\s5
\v 3 Sa'ad da naga ba ku cece ni ba, sai na sa raina da ƙarfina na wuce gãba da su, kuma Yahweh ya ba ni nasara. Meyasa kuka zo ku yi faɗa da ni yau?
\v 4 Yafta ya tattaro dukan mazajen Giliyad ya yi faɗa da Ifraim. Mazajen Giliyad suka kai hari ga mazajen Ifraim saboda sun ce, "Ku Giliyadawa masu gudu ne na cikin Ifraim - da Ifraim da cikin Manasse."
\s5
\v 5 Giliyadawa suka kama magangarun Yodan masu kaiwa Ifraim. Idan wani wanda ya tsira na Ifraim ya zo yace, "Bari in haye kogin", sai mazajen Giliyad su ce da shi, "Kai Ba'ifrane ne?" Idan ya ce, "A'a,"
\v 6 sai su ce da shi ka ce, "Shibbolet," idan ya ce, "Sibbolet" (gama ba zai iya fadin kalmar dai-dai ba), Giliyadawa sai su kama shi su kashe shi a magangarun Yodan. Mutanen Ifraim dubu arba'in da biyu aka kashe a wannan lokacin.
\s5
\v 7 Yafta ya yi alƙalanci a Isra'ila shekara shida. Sa'an nan Yafta ya mutu aka bizne shi a cikin ɗaya daga biranen Giliyad.
\s5
\v 8 Bayan shi Ibzan na Betlehem ya yi alƙalancin Isra'ila.
\v 9 Yana da 'ya'ya talatin. Ya aurar da 'ya'ya mata talatin, kuma ya kawo wa 'ya'yansa 'yan'mata talatin, daga waje. Ya yi alƙalancin Isra'ila shekara bakwai.
\s5
\v 10 Ibzan ya mutu aka bizne shi a Betlehem.
\v 11 Bayan shi Ilon mutumin Zebulun ya yi alƙalanci a Isra'ila, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara goma.
\v 12 Ilon mutumin Zebulun ya mutu aka bizne shi a Aijalon cikin ƙasar Zebulun.
\s5
\v 13 Bayan shi, Abdon ɗan Hillel Ba-firatone ya yi alƙalancin Isra'ila.
\v 14 Yana da 'ya'ya arba'in da jikoki talatin. Suna hawan jakai saba'in, ya yi alƙalancin Isra'ila shekara takwas.
\v 15 Abdon dan Hillel Ba-firatone ya mutu aka bizne shi a Firaton cikin ƙasar Ifraim a ƙasar duwatsu ta Amelikawa.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Mutanen Isra'ila suka sake yin aikin mugunta a fuskar Yahweh, kuma ya bayar da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in.
\v 2 Akwai wani mutumin Zorah, na iyalin Danawa, sunansa Manowa. Matarsa ba ta iya ɗaukar juna biyu saboda haka bata haihu ba.
\s5
\v 3 Mala'ikan Yahweh ya baiyana ga matar ya ce da ita, "Duba, baki iya kin ɗauki juna biyu ba, kuma baki haihu ba, amma za ki sami juna biyu, za ki haifi ɗa.
\v 4 Duba, kada ki sha ruwan inabi, kada ki ci abu marar tsarki.
\v 5 Duba za ki sami juna biyu, za ki haifi ɗa. Ba za a yi anfani da reza a kansa ba, gama yaron zai zama Naziri ga Yahweh tun daga cikin ciki. Shi zaya fara kuɓutar da Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa."
\s5
\v 6 Matar ta je ta gaya wa mijinta, "Wani mutumin Yahweh, ya zo wurina, kamanninsa kamar na mala'ikan Yahweh, da ban razana ƙwarai. Ban tambaye shi daga inda ya fito ba, kuma bai faɗa mani sunansa ba.
\v 7 Ya ce da ni, "Duba! Za ki yi juna biyu za ki haifi ɗa. Kada ki sha ruwan inabi ko wani abin sha mai ƙarfi, kada ki ci abin da shari'a ta ce ba shi da tsarki, gama yaron zai zama Naziri ga Yahweh tun daga cikin ciki har ranar mutuwarsa."
\s5
\v 8 Sai Manowa ya yi addu'a ga Yahweh, ya ce, "Ya Yahweh, idan ka yarda ka sake aiko da wannan mutum domin ya koya mana yadda za mu yi da yaron da za a haifa ba da daɗewa ba."
\v 9 Yahweh ya saurari muryar Manowa, kuma sai mala'ikan Yahweh ya zo wurin matar lokacin da ta ke zaune a fili. Amma mijinta Manowa ba ya tare da ita.
\s5
\v 10 Sai matar ta yi gudu da sauri ta gaya wa mijinta, "Duba! Mutumin ya baiyana gare ni, wanda ya zo wuri na waccan ranar!"
\v 11 Manowa ya tashi ya bi matarsa. Sa'ad da ya zo wurin mutumin, ya ce, "Kai ne mutumin da ya yi magana da matata?" Mutumin yace, "Ni ne."
\s5
\v 12 Sai Manowa yace, bari maganganunka su zama gaskiya. Mene ne zai zama ka'idodi game da yaron, kuma mene ne zai zama aikinsa?"
\v 13 Mala'ikan Yahweh ya ce da Manowa, "Dole ta yi hankali ta yi dukan abin da na faɗa mata.
\v 14 Kada ta ci kowanne abu da ya fito daga kuringa, kada ta sha ruwan inabi ko abin sha mai ƙarfi; kada ka bari ta ci kowanne abinci da shari'a ta ce ba shi da tsarki. Ta yi biyaiya da dukan abin da na ummurce ta ta yi."
\s5
\v 15 Manowa yace da mala'ikan Yahweh, "Idan ka yarda ka ɗan jira, ka ba mu lokaci mu shirya maka 'yar burguma."
\v 16 Sai mala'ikan Yahweh yace da Manowa, "Ko na tsaya ba zan ci abincinku ba. Idan kun shirya hadaya ta ƙonawa, ku miƙa ta ga Yahweh." (Manowa bai san cewa shi mala'ikan Yahweh ne ba.)
\s5
\v 17 Manowa yace da mala'ikan Yahweh, "Mene ne sunanka, domin mu darajanta ka, idan kalmominka suka zama gaskiya?"
\v 18 Mala'ikan Yahweh ya ce masa, "Meyasa ka ke tambayar sunana? Shi ne abin mamaki!"
\s5
\v 19 Sai Manowa ya ɗauki 'yar akuya da baiko na hatsi ya miƙa su a dutsen Yahweh. Ya yi wani abin mamaki Manowa da matasa suna kallo.
\v 20 Sa'ad da harshen wuta ya tashi sama daga bagadin, mala'ikan Yahweh ya tafi sama cikin harshen wuta na bagadin. Da ganin haka Manowa da matarsa suka faɗi da fuskokinsu a ƙasa.
\s5
\v 21 Mala'ikan Yahweh bai ƙara baiyana ga Manowa ba ko matarsa. Sa'an nan ne Manowa ya sani mala'ikan Yahweh ne.
\v 22 Manowa yace da matarsa, "Ba shakka za mu mutu da ya ke mun ga Yahweh!"
\s5
\v 23 Matarsa ta ce da shi, "Da Yahweh ya so ya kashe mu, da bai karɓi baiko na ƙonawa da hatsin da muka ba shi ba. "Da bai nuna mana dukkan waɗannan abubuwan ba, ko ya bari mu ji waɗannan abubuwa a wannan lokaci."
\s5
\v 24 Daga baya, matar ta haifi ɗa, aka kira sunansa Samsin. Yaron ya yi girma, Yahweh ya albarkace shi.
\v 25 Ruhun Yahweh ya fara ƙarfafa shi a cikin Mahane Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Samsin ya je Timna, a can ya ga wata mata, ɗiyar Filistiyawa.
\v 2 Sa'ad da ya dawo ya ce da babansa da mamarsa, "Na ga wata mata a Timna, ɗaya daga cikin 'ya'yan Filistiyawa. Sai ku ɗauko mani ita ta zama mata ta."
\s5
\v 3 Babansa da mamarsa suka ce da shi, "Ba wata mata a cikin 'ya'yan danginka, ko cikin dukkan mutanen mu?" Za ka ɗauko mata daga Filistiyawa marasa kaciya?" Samsin yace da babansa, "A ɗauko ta domi na, idan na dube ta, ta gamshe ni."
\v 4 Amma babansa da mamarsa ba su sani ba wannan daga wurin Yahweh ne, domin ya yi shirin ƙulla husuma da Filistiyawa (gama a wannan lokaci Filistiyawa ne ke mulki a Isra'ila).
\s5
\v 5 Samsin ya gangara zuwa Timna tare da babansa da mamarsa, suka zo gonakin Timnah. Sai ga wani ɗan zaki ya taso masa ya na ruri.
\v 6 Ruhun Yahweh ya zo kansa ya yayyaga ɗan zakin kamar ɗan akuya, kuma ba komi a hannunsa. Amma bai gaya wa babansa ko mamarsa abin da ya yi ba.
\s5
\v 7 Ya je ya yi magana da matar, sa'ad da ya dube ta ta gamshi Samson.
\v 8 Bayan 'yan kwanaki da ya dawo ya aure ta, ya juya ya dubi gawar zakin. Sai ga kututun zuma a cikin abin da ya rage na gawar zakin.
\v 9 Ya yagi zuman ya tafi, yana tafiya ya na ci. Ya zo wurin babansa da mamarsa ya ba su su ma suka ci. Amma bai gaya masu ya samo zuman daga abin da ya rage na jikin gawar zakin ba ne.
\s5
\v 10 Baban Samsin ya je wurin da matar ta ke, Samson ya yi buki a wurin gama wannan ita ce al'adar samarin.
\v 11 Da dai danginta suka gan shi suka kawo masa abokai talatin su zauna tare da shi.
\s5
\v 12 Samsin ya ce masu, "Bari in gaya maku wani karin magana. Idan wani a cikin ku ya gaya ma ni ma'anarsa cikin kwanakin nan bakwai na biki, zan ba da rigunan lilin guda talatin da suturu guda talatin.
\v 13 Amma idan ba ku iya ba ni amsa ba, za ku ba ni rigunan lilin talatin da suturu guda talatin. Suka ce da shi, "Ka faɗa mana karin maganarka mu ji."
\s5
\v 14 Ya ce da su, "A cikin maciyi, akwai abin da za a ci; a cikin mai ƙarfi akwai abu mai zaƙi." Amma baƙinsa ba su iya gano amsar cikin kwana uku ba.
\s5
\v 15 A kan rana ta huɗu suka ce da matar Samsin, "Ki zolayi mijinki domin ya gaya mana amsar karin maganar, ko kuma mu ƙone gidan mahaifinki. Kin gaiyato mu nan ne domin ki mai da mu marasa anfani?"
\s5
\v 16 Matar Samsin ta fara yin kuka a gabansa ta ce, "Dukkan abin da ka ke yi ƙi na! Ka ke yi ba ka ƙauna ta. Ka gaya wa waɗansu mutanena karin magana, amma ba ka gaya mani amsar ba." Samsin yace da ita, "Duba nan, abin da ban gaya wa babana ko mamata ba, sai in gaya maki?"
\v 17 Dukkan kwanakin nan bakwai na buki ita tana ta kuka. Ta matsa masa ƙwarai, a rana ta bakwai ya gaya mata amsar. Ita kuma ta gayawa dangin mutanenta amsar.
\s5
\v 18 A rana ta bakwai kafin rana ta faɗi, mazajen garin suka ce da shi, "Me ya fi zuma zaƙi? Me ya fi zaki ƙarfi? Samsin yace da su, "Da ba domin kun yi huɗa da karsanata ba, da ba ku gano amsar karin maganata ba."
\s5
\v 19 Sai Ruhun Yahweh ya zo kan Samsin da iko. Samsin ya je Ashkelon ya kashe mazajen su guda talatin. Ya kwashe ganimarsu, ya bada tufafinsu ga waɗanda suka baiyana masa karin zaurancensa. Ya tafi gidan ubansa cikin fushi mai zafi.
\v 20 Aka bada matar Samsin ga babban abokinsa.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Bayan waɗansu kwanaki, a lokacin girbin alkama, sai Samsin ya ɗauki 'yar akuya ya tafi domin ya ziyarci matarsa. Ya ce a ransa, "Zan shiga ɗakin matata." Amma mahaifinta bai bar shi ya shiga ba.
\v 2 Sai mahaifinta yace, "Tabbas na zaci ka ƙi jininta, sai na bayar da ita ga abokinka. Ai ƙanwarta ta fi ta kyau, ko kuwa? Sai ka ɗauke ta a maimakonta."
\s5
\v 3 Samsin yace masu, "Wannan karon ba ni da hakkin Filistiyawa duk zafin da zan sa masu game da wannan al'amari."
\v 4 Samsin ya tafi ya kamo diloli ɗari uku ya ɗaura su biyu-biyu, bindi da bindi. Sai ya ɗauko gaushen wuta ya ɗaɗɗaura a tsakiyar kowanne ɗaurin bindi biyu.
\s5
\v 5 Da ya kunnawa gaushen wuta, sai ya tura dilolin cikin hatsin Filistiyawa, suka cinnawa hatsin wuta duk da zangarniyar da ke cikin gonakin, duk da Inabinsu garka-garka da lambunan zaitun.
\v 6 Filistiyawa kuwa suka yi tambaya, "Wane ne ya yi wannan?" Aka gaya masu, "Samsin ne, surukin Batimne ya yi haka, domin Batimnen ya ɗauki matar Samsin ya ba abokinsa." Sai Filistiyawan suka tafi suka ƙone ta tare da mahaifinta.
\s5
\v 7 Samsin yace masu, "Idan haka ku ka yi, zan ɗauki ramuwata a kanku, bayan haka ya faru, zan dakata."
\v 8 Sai ya datsa su gunduwa-gunduwa, kwankwaso da cinya, da babbar gunduwa. Sai ya gangara ya tafi ya zauna cikin kogon dutsen Itam.
\s5
\v 9 Sai Filistiyawa suka fito da shirin yaƙi cikin Yahuda suka kuma jera sojojinsu a Lehi.
\v 10 Mutanen Yahuda suka ce, "Mene ne ya sa ku ka fito ku kawo mana hari?" Suka ce, "Mun kawo hari ne domin mu kama Samsin, kuma mu yi masa yadda ya yi mana."
\s5
\v 11 Sai mutanen Yahuda su dubu uku suka tafi suka gangara kogon dutsen Itam, suka kuma cewa Samsin, "Ba ka san cewa Filistiyawa ne ke mulkinmu ba? Mene ne ka yi mana haka?" Samsin yace masu, "Sun yi mani, saboda haka nima na yi masu."
\s5
\v 12 Suka cewa Samsin, "Mun gangaro ne domin mu ɗaure ka kuma mu miƙa ka cikin hannun Filistiyawa." Samsin yace masu, "Ku rantse mani cewa ku da kanku ba za ku kashe ni ba."
\v 13 Suka ce masa, "A a, zamu ɗaure ka ne kawai da igiyoyi kuma mu miƙa ka gare su. Mun yi alƙawari ba za mu kashe ka ba." Daga nan suka ɗaure shi da sabbin igiyoyi biyu suka fito da shi daga dutsen.
\s5
\v 14 Da ya zo Lehi, Filistiyawa suka fito da Ihu yayin da suke zuwa su gamu da shi. Sai Ruhun Yahweh ya sauko kansa da iko. Sai igiyoyin da ke bisa hannuwansa suka zama kamar ƙonannar ciyawa, suka kuma zube daga hannuwansa.
\s5
\v 15 Sai Samsin ya samo sabon ƙashin muƙamuƙin jaki, ya ɗauko ya kuma kashe mutane dubu da shi.
\v 16 Samsin yace, "Da ƙashin muƙamuƙin jaki, tari bisa tari, da ƙashin muƙamuƙin jaki na kashe mutane dubu."
\s5
\v 17 Da Samsin ya gama magana, sai ya jefar da ƙashin muƙamuƙin jakin, sai ya kira wurin da suna Ramat Lehi.
\v 18 Samsin ya ji ƙishi sosai sai ya yi kira ga Yahweh ya ce, "Ka bayar da nasara mai girma ga bawanka. Amma yanzu zan mutu da ƙishi ne kuma in faɗa cikin hannuwan waɗancan marasa kaciyar?"
\s5
\v 19 Sai Allah ya tsaga cikin sararin da ke Lehi sai ruwa ya ɓulɓulo. Da ya sha, sai karfinsa ya dawo kuma ya farfaɗo. Saboda haka ya kira sunan wannan wuri En Hakkori, kuma yana nan a Lehi har yau.
\v 20 Samsin ya yi alƙalancin Isra'ilawa a zamanin Filistiyawa har shekaru ashirin.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Samsin ya tafi Gaza sai ya ga karuwa a can, sai kuwa ya kwana da ita.
\v 2 Aka faɗa wa Gazawa, "Samsin ya shigo nan fa." Gazawa suka kewaye wurin a asirce, suka yi masa kwanto tsawon dare a ƙofar birnin. Suka yi tsit dukkan tsawon daren. Sun riga sun ce, "Mu jira har sai wayewar gari, sa'an nan kuma mu kashe shi."
\s5
\v 3 Samsin ya yi kwance bisa gado har tsakiyar dare. Da dare ya yi tsaka sai Samsin ya tashi ya tafi ya kama ƙofar birnin da ginshiƙanta biyu. Ya tumɓuko su daga ƙasa, duk da ƙarafunan da komai, ya ɗorasu bisa kafaɗunsa, ya tafi da su bisa tudu, a gaban Hebron.
\s5
\v 4 Bayan wannan, Samsin ya zo ya ƙaunaci wata mata da ke zaune a Kwarin Sorek. Sunanta Delila.
\v 5 Masu mulkin Filistiyawa suka zo wurinta, suka ce da ita, "Ki yaudari Samsin domin ki gane inda babban ƙarfinsa yake, da kuma ta yaya zamu sha ƙarfinsa, domin mu ɗaure shi mu kuma yi masa wulaƙanci. Ki yi mana wannan, mu kuma kowanne zai ba ki azurfa 1,100 ."
\s5
\v 6 Daga nan Delila ta ce da Samsin, "Ina roƙonka, ka gaya mani yadda aka yi ka ke da ƙarfi haka, kuma ta yaya za a iya ɗaure ka, domin a mulke ka?"
\v 7 Samsin yace mata, "Idan aka ɗaure ni da ɗanyen ƙiri guda bakwai, daga nan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum."
\s5
\v 8 Sai masu mulkin Filistiyawa suka kawo wa Delila igiyoyin ƙiri guda bakwai ɗanyu, ita kuwa ta ɗaure Samsin da su.
\v 9 Ta riga ta ɓoye mutane a asirce, suna jira cikin ƙuryar ɗakinta. Sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Amma ya tsisttsinke igiyoyin kamar zare a mazari idan ya taɓa wuta. Ta haka ba a gane asirin ƙarfinsa ba.
\s5
\v 10 Daga nan Delila ta ce da Samsin, "Yadda ka ruɗe ni kenan kuma ka yi mani ƙarya. Ina roƙon ka, ka faɗa mani yadda za a sha ƙarfinka."
\v 11 Sai ya ce mata, "Idan aka ɗaure ni da sabbin igiyoyin da ba a taɓa aiki da su ba, daganan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum."
\v 12 Sai Delila ta ɗauki sabbin igiyoyi ta ɗaure shi da su, sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Mutanen kuwa 'yankwanto suna cikin ƙuryar ɗakin. Samsin kuwa ya tsisttsinke igiyoyin kamar zare.
\s5
\v 13 Delila ta ce da Samsin, "Har yanzu ruɗi na ka ke yi kuma kana faɗa mani ƙarairayi. Ka gaya mani yadda za a sha ƙarfinka." Samsin yace mata, "Idan ki ka saƙa tukkun kaina guda bakwai bisa masaƙa kamar yadda ake saƙa sutura, sa'an nan ki sa allura ki kafe gashin bisa gungumen masaƙar, zan zama kamar kowanne mutum."
\v 14 Yayin da ya yi barci, sai Delila ta yi wa tukkun kansa bakwai saƙa kamar an saƙa sutura bisa masaƙa ta kuma sa allura ta kafe shi bisa masaƙa, sai ta ce da shi, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" Ya farka daga barci kuma ya yage gashin duk da allurar daga jikin masaƙar.
\s5
\v 15 Sai ta ce masa, "Ta yaya za ka ce, 'Ina son ki,' amma baka iya faɗa mani asirinka ba? sau uku kenan kana yi mani ba a kuma ba ka gaya mani yadda aka yi ka ke da babban ƙarfi haka ba."
\v 16 Kowacce rana ta dinga gasa masa tsanani ta wurin maganganu, ta tsananta masa ƙwarai da gaske har ya gwammace ya mutu.
\s5
\v 17 Sai Samsin ya faɗa mata dukkan komai ya ce mata, "Ba a taɓa sa reza aka yanke gashin kaina ba, Gama ni Naziri ne domin Allah tun daga mahaifar uwata. Idan aka aske kaina, to ƙarfina zai rabu da ni, daganan zan zama marar ƙarfi kuma in zama kamar kowanne mutum."
\s5
\v 18 Da Delila ta ga cewa ya faɗa mata gaskiya game da komai, sai ta aika aka kira masu mulkin Filistiyawa, ta na cewa, "Ku sake dawowa, gama ya faɗa mani komai." Sai masu mulkin Filistiyawa suka tafi wurinta, suna ɗauke da azurfa a hannuwansu.
\v 19 Sai ta sa barci ya kwashe shi a bisa cinyarta. Ta kira wani mutum yazo ya aske tukkaye bakwai da ke a kansa, daga nan ta dinga jujjuya shi, domin ƙarfinsa ya riga ya rabu da shi.
\s5
\v 20 Ta ce, "Filistiyawa suna kanka, Samsin!" ya farka daga barcinsa ya ce, "Zan tashi kamar lokutan baya in kuma girgije kaina kuɓutacce." Amma ba ya sani cewa Yahweh ya riga ya rabu da shi ba.
\v 21 Filistiyawa suka kama shi suka ƙwaƙule masa idanu. Suka kawo shi har Gaza suka kuma ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Shi ne ke aikin juya dutsen niƙa a kurkuku.
\v 22 Amma gashin kansa ya soma sake tuƙowa bayan askin da aka yi masa.
\s5
\v 23 Masu mulkin Filistiyawa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga Dagon allahnsu, su kuma yi farinciki. Suka ce, "Allahnmu ya yi nasara da Samsin, maƙiyinmu, ya kuma sa shi cikin hannuwanmu."
\v 24 Da mutanen suka gan shi, sai suka yi yabo ga allahnsu, domin suka ce, "Allahnmu ya yi nasara da maƙiyinmu kuma ya miƙa shi gare mu - mai lalatar da ƙasarmu, wanda ya kashe masu yawa daga cikinmu."
\s5
\v 25 Yayin da suke cikin shagali, sai suka ce, "A kira mana Samsin, domin ya zo ya sa mu dariya." Aka kira Samsin daga cikin kurkuku ya zo ya yi ta ba su dariya. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙan ginin.
\v 26 Samsin yace da saurayin da ya riƙe hannunsa, "Ka bar ni in taɓa ginshiƙan da ke riƙe da ginin, domin in jingina da su."
\s5
\v 27 Yanzu fa gidan na cike da mutane maza da mata. Dukkan masu mulkin Filistiyawa suna wurin. A bisa rufin ginin akwai mutum dubu uku maza da mata, waɗanda ke kallo yayin da Samsin ke yi masu wasa.
\s5
\v 28 Samsin ya yi kira ga Yahweh ya ce, "Ubangiji Yahweh, ka tuna da ni! Ina roƙon ka ka ƙarfafa ni sau ɗaya kacal, ya Allah, domin in ɗauki fansa bugu ɗaya tak akan Filistiyawa saboda idanuna biyu da suka ƙwaƙule."
\v 29 Samsin ya riƙe ginshiƙan nan biyu da ke ɗauke da ginin, sai ya jingina kansa da su, hannunsa na dama na riƙe da ɗaya, kuma hannunsa na hagu na riƙe da ɗayan.
\s5
\v 30 Samsin yace, "Bari in mutu tare da Filistiyawa!" Ya miƙe iya ƙarfinsa ginin kuwa ya rugurguje bisa masu mulkin da dukkan mutanen da ke ciki. Saboda haka matattun da ya kashe a mutuwarsa sun fi waɗanda ya kashe a lokacin rayuwarsa.
\v 31 Daga nan 'yan'uwansa da dukkan gidan mahaifinsa suka gangaro. Suka ɗauko shi, suka dawo da shi suka kuma binne shi tsakanin Zora da Eshtawol a maƙabartar Manowa, mahaifinsa. Samsin ya yi alƙalacin Isra'ila shekaru ashirin.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Akwai wani mutum a ƙasar tudu ta Ifraim, sunansa Mika.
\v 2 Sai ya ce da mahaifiyarsa, "Azurfarki 1,100 da aka ɗauke maki, wanda kuma ki ka furta la'ana akai, wanda kuma na ji - duba nan! azurfar na wurina. Ni ne na sace." Mahaifiyarsa ta ce, "Yahweh ya albarkace ka, ɗana!"
\s5
\v 3 Sai ya maido wa mahaifiyarsa azurfa 1,100 sai mahaifiyarsa ta ce, "Na keɓe wannan azurfa ga Yahweh, domin ɗana ya sassaƙa kuma ya sarrafa siffofi na ƙarfe. Saboda haka yanzu, na maido maka azurfar."
\v 4 Da ya maido wa mahaifiyarsa kuɗin, sai mahaifiyarsa ta ɗauki azurfa ɗari biyu ta ba maƙeri wanda shi kuma ya sassaƙa ya kuma sarrafa siffofi na karfe da su, sai aka ajiye su a gidan Mika.
\s5
\v 5 Mutumin nan Mika ya na da gidan gumaka sai ya yi falmarar haikali da kuma allolin gida, sai ya ɗauki hayar ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama firist.
\v 6 A waɗannan kwanaki ba sarki a Isra'ila, kowa na yin abin da ya yi dai-dai a idanunsa.
\s5
\v 7 Akwai wani saurayi daga Betlehem ta cikin Yahuda, daga iyalin Yahuda, shi kuwa Balebi ne. Ya na zaune anan domin ya aiwatar da ayyukansa.
\v 8 Mutumin ya bar Betlehem ta Yahuda ne domin ya fita ya je ya sami wani wurin zama. Yayin da ya ke tafiya, sai ya zo gidan Mika da ke ƙasar tuddun Ifraim.
\v 9 Sai Mika yace masa, "Daga ina ka fito?" Mutumin yace masa, "Ni Balebi ne na Betlehem ta cikin Yahuda, kuma na fito tafiya ne domin neman wurin zama."
\s5
\v 10 Mika yace da shi, "Ka zauna da ni, sai ka zama uba da firist a gare ni. Zan ba ka azurfa goma a shekara, da kayan sawa, da abinci." Sai Balebin ya shiga cikin gidansa.
\v 11 Balebin ya dangana da zama da mutumin, kuma saurayin ya zame wa Mika kamar ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza.
\s5
\v 12 Mika ya keɓe Balebin saboda ayyukan ibada, sai saurayin ya zama firist ɗinsa, kuma yana cikin gidan Mika.
\v 13 Sai Mika yace, "Yanzu na sani cewa Yahweh zai yi mani abin alheri, domin Balebin nan ya zama firist ɗina."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 A waɗannan kwanaki babu sarki a Isra'ila. Kabilar zuriyar Dan suna neman wajen da za su yi wa kansu wurin zama, domin har zuwa wannan lokaci ba su karɓi wani gãdo daga cikin kabilun Isra'ila ba.
\v 2 Mutanen Dan suka aika da mutum biyar daga dukkan cikin kabilarsu, mutanen da suka ƙware wajen yaƙi daga Zora zuwa Eshtawol, domin su kewaye ƙasar da ƙafa, kuma su duba ta. Suka ce masu, "Ku je ku duba ƙasar." Suka zo ƙasar tudu ta Ifraim, suka zo gidan Mika, suka kwana anan.
\s5
\v 3 Da su na kusa da gidan Mika, sai suka gane karin harshen saurayin nan Balebiye. Sai suka tsaya suka tambaye shi, "Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan wurin? Meyasa ka ke nan?"
\v 4 Ya ce masu, "Ga abin da Mika ya yi mani: Ya ɗauki hayata in zama firist ɗin sa."
\s5
\v 5 Suka ce da shi, "Muna roƙon ka ka nemi shawara daga Allah, domin mu sani ko tafiyar nan da muke yi za ta yi nasara."
\v 6 Sai firist ɗin ya ce masu, "Ku tafi cikin salama. Yahweh za ya bi da ku hanyar da zaku bi."
\s5
\v 7 Sai mutanen nan biyar suka tafi har suka isa Layish, sai suka iske mutanen na zaune lafiya, hakanan kuma Sidoniyawa suke zaune, babu abin da ya dame su a tsare suke. Babu wanda ya taɓa yin nasara da su ko kuma ya taɓa tsananta masu a ƙasar ko kaɗan. Suna zaune nesa da Sidoniyawa kuma ba su da wata hurɗa da kowa.
\v 8 Suka dawo wurin kabilarsu a Zora da Eshtawol. 'Yan'uwansu suka tambaye su, "Mene ne rahotonku?"
\s5
\v 9 Suka ce, "Ku zo! Mu kai masu hari! Mun ga ƙasar kuma mai nagarta ce. Ba za kuyi wani abu ba? Kada ku yi jinkirin kai hari kuma ku ci ƙasar.
\v 10 Idan ku ka je, za ku iske mutane waɗanda ke tunanin a tsare suke, kuma ƙasar na da fãɗi! Allah ya bayar da ita a gare ku - wurin da babu rashin komai a ƙasar."
\s5
\v 11 Mutane ɗari shida daga kabilar Dan, shirye da kayan yaƙi, suka fito daga Zora da Eshtawol.
\v 12 Suka tafi su ka yi sansani a Kiriyat Yerayim, cikin Yahuda. Wannan ya sa mutane ke kiran wurin Mahane Dan har wa yau; yana yamma da Kiriyat Yerayim.
\s5
\v 13 Suka tafi daga wurin zuwa ƙasar tudu ta Ifraim sai suka zo gidan Mika.
\v 14 Sai mutanen nan biyar da suka je gewayar ƙasar Layish suka ce da 'yan'uwansu, "Kun kuwa san cewa a cikin gidajen nan akwai falmarar haikali, da allolin gida, sassaƙaƙƙiyar siffa, da siffar ƙarfe da aka sarrafa? Yanzu ku yi shawarar abin da za ku yi."
\s5
\v 15 Sai suka juya daga nan suka shiga gidan saurayin nan Balebi, a gidan Mika, sai suka gaishe shi.
\v 16 Daga nan Danawan nan ɗari shida, shirye da kayan yaƙi, suka tsaitsaya a ƙofar gidan.
\s5
\v 17 Mutanen nan biyar da suka je gewayar ƙasar suka shiga suka ɗauko sassaƙaƙƙiyar siffar, da falmarar haikalin, da allolin gida, da sarrafaffiyar siffar ƙarfen, lokacin da firist ɗin ke tsaye bakin ƙofar gidan tare da mutanen nan ɗari shidda da ke shirye da kayan yaƙi.
\v 18 Da waɗannan suka shiga cikin gidan Mika suka ɗauko sassaƙaƙƙiyar siffar nan, da falmarar haikali, da allolin gida, da sarrafaffiyar siffar ƙarfen nan, sai firist ɗin ya ce masu, "Me ku ke yi?"
\s5
\v 19 Suka ce da shi, "Yi shiru! Ka sa hannunka a bakinka ka taho tare da mu, sai ka zama Uba da firist a gare mu. Wanne ne ya fi maka ka zama firist na gidan mutum ɗaya, ko kuwa ka zama firist na kabila da kuma ɗaya daga cikin zuriyar Isra'ila?"
\v 20 Firist ɗin ya yi murna a zuciyarsa. Ya ɗauki falmarar haikalin, da allolin gidan, da sassaƙaƙƙiyar siffar, sai ya tafi tare da mutanen.
\s5
\v 21 Sai suka juya suka yi tafiyarsu. Suka sa ƙananan yaran a gabansu, da kuma shanun da dukkan mallakarsu.
\v 22 Da suka yi 'yar tazara daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da ke maƙwaftaka da gidan Mika suka tattaru, suka tafi suka tarar da Danawan.
\v 23 Suka yi kururuwa ga Danawan, suka juya suka ce wa Mika, "Me ya sa ku ka tattaro kanku?"
\s5
\v 24 Ya ce, "Kun sãce allolin da na yi, kun ɗauke mani firist, kuma kun tafi. Me kuma ya rage mani? ya ya za ku yi mani tambaya, "Me ke damun ka?"
\v 25 Mutanen Dan suka ce da shi, "Kada ka bari mu ji ka ce wani abu, ko kuwa wasu mutane masu fushi da ke nan wurin ransu ya ɓaci sosai su kai maka hari, kai da iyalinka kuma a kashe ku."
\v 26 Sai mutanen Dan suka yi tafiyarsu. Da Mika ya ga cewa sun sha ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gidansa.
\s5
\v 27 Mutanen Dan suka ɗauke abin da Mika ya sassaƙa, duk da firist ɗinsa, sai suka zo Layish, wurin mutanen da babu abin da ya dame su kuma cikin tsaro suka kashe su da takobi suka ƙone birnin.
\v 28 Babu wanda yazo ya cece su domin sun yi nisa da Sidon, kuma ba su da wata hurɗa da wani. A kwari ne da ke kusa da Bet Rehob. Danawan suka sake gina birnin suka zauna a ciki.
\v 29 Suka sa wa birnin suna Dan, bisa ga sunan Dan kakansu, wanda ya ke ɗaya daga cikin 'ya'yan Isra'ila. Amma dã sunan birnin Layish ne.
\s5
\v 30 Mutanen Dan suka kafa wa kansu sassaƙaƙƙiyar siffar nan. Yonatan ɗan Gashom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza suka zama firistocin kabilar Danawa har zuwa ranar tafiya ƙasar bauta.
\v 31 Haka nan suka yi sujada ga sassaƙaƙƙiyar siffar Mika wanda ya sarrafa dukkan tsawon kwanakin da gidan Allah ya ke a Shilo.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 A waɗannan kwanaki, sa'ad da babu sarki a Isra'ila, akwai wani mutum, Balebi, ya yi zama na ɗan wani lokaci a wani ƙauye a ƙasar tudu ta Ifraim. Sai ya ɗauko wa kansa mace, kuyanga daga Betlehem cikin Yahuda.
\v 2 Amma kuyangar tasa ta yi masa rashin aminci; sai ta bar shi ta koma gidan mahaifinta a Betlehem cikin Yahuda. Ta zauna a can watanni huɗu.
\s5
\v 3 Sai mijinta ya tashi ya tafi wurinta domin ya lallashe ta ta dawo. Baransa kuwa na tare da shi, da jakai guda biyu. Sai ta kawo shi cikin gidan mahaifinta. Da mahaifin yarinyar ya gan shi, sai ya yi murna.
\v 4 Sai surukinsa, mahaifin yarinyar, ya lallashe shi ya zauna kwana uku. Suka ci su ka sha suka kwana a can.
\s5
\v 5 A rana ta huɗu suka tashi suka yi asubanci suka shirya domin su tafi, amma mahaifin yarinyar ya ce da surukinsa, "Ka ci ɗan abinci domin ka sami ƙarfi, daga nan sai ka tafi."
\v 6 Sai su biyun suka zauna domin su ci su kuma sha tare. Daga nan mahaifin yariyar ya ce, "Ina roƙon ka ka yarda ka sãke kwana domin ka wartsake."
\s5
\v 7 Da Balebin ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya roƙe shi da ya tsaya, sai ya canza shirinsa ya sake kwana.
\v 8 A rana ta biyar ya tashi ya yi asubanci domin ya tafi, amma mahaifin yarinyar ya ce, "Ka ƙarfafa kanka, ka jira sai rana tayi." Sai suka zauna su ka ci abinci su biyu.
\s5
\v 9 Da Balebin da kuyangarsa da baransa suka tashi za su tafi, sai surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce da shi, "Duba, yanzu yamma ta ƙarato. Ina roƙonka ka tsaya ka sãke kwana, ka kuma wartsake. Kana iya yin asubanci gobe ka tashi ka koma gida."
\s5
\v 10 Amma Balebin ba ya so ya sake kwana. Sai ya tashi ya tafi. Ya yi tafiya ya fuskanci Yebus (wato Yerusalem). Yana da jakai biyu shiryayyu domin hawa - kuma kuyangarsa na tare da shi.
\v 11 Da suka iso gaf da Yebus, rana ta kusa faɗuwa, sai baran ya ce wa maigidansa, "Ka zo, mu juya mu shiga birnin Yebusawa mu kwana a ciki."
\s5
\v 12 Sai ubangidansa yace masa, "Ba za mu juya mu shiga birnin bãre waɗanda ba na mutanen Isra'ila ba ne. Mu ci gaba da tafiya mu kai Gibiya."
\v 13 Balebin ya ce wa bãransa, "Zo, mu tafi ɗaya daga cikin wuraren nan, mu kwana a can ko dai Gibiya ko kuma Ramah."
\s5
\v 14 Sai suka ci gaba da tafiya, rana kuwa ta faɗi da suka yi gaf da Gibiya, cikin yankin Benyamin.
\v 15 Sai suka juya suka shiga domin su kwana a Gibiya. Sai suka je suka zauna a dandalin birnin, amma babu wanda ya kira su domin su kwana a gidansa.
\s5
\v 16 Amma sai ga wani mutum tsoho yana dawowa daga aikin gonarsa a yammacin nan. Shi kuwa mutumin ƙasar tudu ta Ifraim ne, amma ya na zama a Gibiya na ɗan wani lokaci. Amma mutanen da ke zama a wannan wuri Benyaminawa ne.
\v 17 Ya ɗaga idanunsa sai ya ga matafiyin a dandalin birni. Tsohon ya ce, "Ina za ku? Daga ina ku ka fito?"
\s5
\v 18 Balebinn yace masa, "Mun fito ne daga Betlehem cikin Yahuda za mu wani ƙauyen ƙasar tudu ta Ifraim, wato inda na fito. Na je Betlehem cikin Yahuda, kuma za ni gidan Yahweh, amma babu wanda zai karɓe ni cikin gidansa.
\v 19 Muna da harawa da abinci domin jakkanmu, akwai gurasa da ruwan inabi domina da wannan mace baiwarka a nan, da kuma wannan saurayin tare da barorinka. Ba mu rasa komai ba."
\s5
\v 20 Sai tsohon nan ya gaishe su, "Salama a gare ku! Zan biya dukkan buƙatunku. Kada dai ku kwana a dandali kawai."
\v 21 Sai mutumin ya kawo Balebinn cikin gidansa ya kuma ba da abinci ga jakunansa. Suka wanke sawayensu suka ci suka sha.
\s5
\v 22 Lokacin da suke cikin annashuwa, sai waɗansu mutanen birnin, 'yan'iskan gari, suka zo suka kewaye gidan, suna bubbuga ƙofar. Suka yi wa tsohon nan magana, wato mai gidan, suna cewa, "Ka fito da mutumin nan da ya shigo cikin gidanka, domin mu yi luɗu da shi."
\v 23 Mutumin nan, mai gidan, ya fita ya same su ya ce masu, "A 'a, 'yan'uwana, ina roƙon ku kada ku yi wannan irin mugun abu! Tun da wannan mutum baƙon gidana ne, kada ku yi wannan irin mugun abu!
\s5
\v 24 Duba, ɗiyata budurwa da kuma kuyangarsa ga su nan. Bari in fito da su yanzu. Ku yi masu fyaɗe ku kuma yi yadda kuka ga dama da su. Amma kada ku yi wannan irin mugun abu ga mutumin nan!"
\v 25 Amma mutanen nan ba su saurare shi ba, sai mutumin nan ya fizgi kuyangarsa ya kuma fitar masu da ita. Suka fizge ta, suka yi mata fyaɗe, suka wulaƙanta ta dukkan tsawon dare, da asuba ta yi suka bar ta ta tafi.
\v 26 Da asuba matar ta dawo sai ta faɗi a bakin ƙofar gidan mutumin inda maigidanta ya ke, sai ta yi kwance a nan har gari ya waye sarai.
\s5
\v 27 Maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofofin gidan ya fita domin ya kama hanyar tafiyarsa. Sai ya lura da kuyangarsa a kwance a bakin ƙofa, da hannuwanta bisa dankarin ƙofar.
\v 28 Balebin ya ce mata, "Tashi. Mu tafi." Amma ba ta amsa ba. Sai ya ɗora ta bisa jaki, mutumin kuwa ya kama hanya zuwa gidansa.
\s5
\v 29 Sa'ad da Balebin nan ya iso gidansa, sai ya ɗauko wuƙa, ya kuma kama kunyangar tasa, ya daddatsa ta, ya yi mata gunduwa-gunduwa, ya kasa ta kashi goma sha biyu, sai ya aika da kashi-kashin nan ko'ina cikin dukkan ƙasar Isra'ila.
\v 30 Dukkan waɗanda suka ga wannan abu suka ce, "Wannan irin abu bai taɓa faruwa ba ko aka taɓa ganinsa ba tun daga ranar da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar har ya zuwa wannan rana. Ku yi tunani akai! Ku bamu shawara! Ku gaya mana abin da za'a yi!"
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Daga nan dukkan mutanen Isra'ila suka fito a matsayin mutum guda, daga Dan har zuwa Biyasheba, duk da ƙasar Giliyad ma, suka tattaru tare a gaban Yahweh a Mizfa.
\v 2 Shugabannin dukkan mutanen, da kuma dukkan kabilun Isra'ila, suka ɗauki wurarensu a cikin taron mutanen Allah - Mutane 400,000 a ƙasa, waɗanda ke a shirye domin su tafi su yi yaƙi da takobi.
\s5
\v 3 Mutanen Benyamin suka ji cewa mutanen Isra'ila sun haye zuwa Mizfa. Mutanen Isra'ila suka ce, "Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru."
\v 4 Balebin mai gidan matar wadda aka kashe, ya amsa, "Na zo Gibiya ne wadda ke yankin Benyamin, ni da kuyangata, domin mu kwana.
\s5
\v 5 A cikin dare, shugabannin Gibiya suka kawo mani hari, suka kewaye gidan suna nema su kashe ni. Suka fizge kuyangata su a yi mata fyaɗe, sai kuwa ta mutu.
\v 6 Na ɗauki kuyangata na datsa ta kashi-kashi, na kuma aika cikin kowanne lardin gãdon Isra'ila, saboda sun aikata wannan irin mugunta da hasala a cikin Isra'ila.
\v 7 Yanzu, dukkan ku Isra'ilawa, sai ku ba da shawara ku kuma ɗauki mataki a nan."
\s5
\v 8 Dukkan mutanen suka tashi tsaye a matsayin mutum guda, suka ce, "Babu wani cikinmu da za ya koma rumfarsa, babu kuma wani cikinmu da zaya koma gidansa!
\v 9 Amma dole yanzu ga abin da zamu yi wa Gibiya: Za mu kai mata hari bisa ga yadda ƙuri'a za ta bi da mu.
\s5
\v 10 Za mu ɗauki mutane goma cikin ɗari daga cikin dukkan kabilun Isra'ila, da kuma mutane ɗari cikin dubu, mutane dubu cikin dubu goma, su samo kayan masarufi domin waɗannan mutanen, domin idan suka zo Gibiya ta Benyamin, su ba su horo domin muguntar da suka aikata a Isra'ila."
\v 11 Sai dukkan sojojin Isra'ila suka taru a matsayin mutum guda, domin yin tsayayya da birnin.
\s5
\v 12 Sai kabilun Isra'ila suka aika da mutane cikin dukkan kabilar Benyamin, suna cewa, "Wacce irin mugunta ce haka aka aikata a cikinku?
\v 13 Saboda haka, ku ba mu waɗannan miyagun mutanen na Gibiya, domin mu kashe su, ta haka za mu cire wannan mugunta da ke cikin Isra'ila ɗungun." Amma Benyaminawa suka ƙi sauraron muryar 'yan'uwansu, mutanen Isra'ila.
\v 14 Sai mutanen Benyamin suka fito daga cikin biranensu suka tattaru a Gibiya domin su yi shirin yin yaƙi da mutanen Isra'ila.
\s5
\v 15 Mutanen Benyamin suka tattaro mutane daga cikin biranensu a wannan rana sojoji dubu ashirin da shida horarru wajen faɗa da takobi. Bugu da ƙari, akwai mutane ɗari bakwai zaɓaɓɓu daga cikin mazauna a Gibiya.
\v 16 Daga cikin waɗannan sojoji dukka akwai mutane ɗari bakwai zaɓaɓɓu waɗanda su bahagwai ne. Kowannen su za ya iya wurga dutse ga gashin kai ba tare da yin kuskure ba.
\s5
\v 17 Mutanen Isra'ila, ba tare da lissafin mutanen Benyamin ba, su mutum dubu ɗari huɗu ne, waɗanda kuma horarru ne wajen faɗa da takobi. Dukka waɗannan mutanen yaƙi ne.
\v 18 Mutanen Isra'ila suka tashi, suka hau zuwa Betel, suka tambayi shawara daga wurin Allah. Suka yi tambaya,"Wane ne za ya fara kai wa mutanen Benyamin hari domin mu?" Yahweh yace, "Yahuda ne za ya fara kai hari."
\s5
\v 19 Mutanen Isra'ila suka tashi da sassafe suka matsa da sansaninsu kusa da Gibiya.
\v 20 Mutanen Isra'ila suka tafi yin yaƙi da Benyamin. Suka tashi suka yi jeren yaƙi da Gibiya.
\v 21 Mutanen Benyamin suka fito daga cikin Gibiya, suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na sojojin Isra'ila a wannan rana.
\s5
\v 22 Amma mutanen Isra'ila suka ƙarfafa kansu suka sãke kafa layin yaƙi dai-dai wurin da suka jera a rana ta farko.
\v 23 Sai mutanen Isra'ila suka haye suka yi kuka a gaban Yahweh har zuwa yamma, suka kuma nemi bishewa daga wurin Yahweh. Suka ce, "Mu kuma sãke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Benyamin?" Yahweh yace, "Ku kai masu hari!"
\s5
\v 24 Sai mutanen Isra'ila suka kai hari ga sojojin Benyamin a rana ta biyu.
\v 25 A rana ta biyu, Benyamin ya fito daga Gibiya suka kuma kashe mutum dubu sha takwas daga cikin mutanen Isra'ila. Dukkan su horarru ne wajen faɗa da takobi.
\s5
\v 26 Daga nan dukkan sojojin Isra'ila da dukkan mutanen Isra'ila suka tashi su ka haye zuwa Betel suka yi kuka, a nan suka zauna a gaban Yahweh suka yi azumi a wannan rana har zuwa yamma suka miƙa baye-baye na ƙonawa da baye-baye na salama a gaban Yahweh.
\s5
\v 27 Mutanen Isra'ila su ka tambayi Yahweh - domin akwatin alƙawari na Allah na nan a waɗannan kwanaki,
\v 28 a sa'annan Fenihas, ɗan Eliyeza ɗan Haruna, yana hidima a gaban akwatin a waɗannan kwanaki - "Mu sake tafiya mu yaƙi mutanen Benyamin, 'yan'uwanmu, ko mu tsaya?" Yahweh yace, "Ku kai hari, gama gobe zan taimake ku ku yi nasara da su."
\s5
\v 29 Sai Isra'ila suka sa mutane suka kewaye Gibiya gaba ɗaya a asirce.
\v 30 Mutanen Isra'ila suka yi yaƙi da mutanen Benyamin a rana ta uku, suka kafa layin yaƙi da Gibiya kamar yadda suka yi a dã.
\s5
\v 31 Mutanen Benyamin suka fita suka yi yaƙi da mutanen, har suka fita suka yi nisa da birnin. Suka fara kashe wasu daga cikin mutanen. Wajen mutane talatin na Isra'ila suka mutu cikin gonaki da bisa hanyoyi. Ɗaya daga cikin hanyoyin ta hawa zuwa Betel ce, ɗayar kuma ta tafi zuwa Gibiya.
\s5
\v 32 Sai mutanen Benyamin suka ce, "An kãshe su gashi nan suna guduwa daga gare mu, kamar yadda ya faru da farko." Amma sojojin Isra'ila suka ce, "Mu gudu baya domin mu janye su daga cikin birnin zuwa bisa hanyoyi."
\v 33 Dukkan mutanen Isra'ila kuwa suka fito daga wurarensu suka jera kansu layi-layi domin yaƙi a Ba'al Tama. Sai sojojin Isra'ila waɗanda ke ɓoye a asirtattun wurare suka fito da gudu daga wurarensu daga Ma'are Gibiya.
\s5
\v 34 Sai ga shi an fito wa Gibiya da yaƙi mutane dubu goma daga cikin dukkan Isra'ila, yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Benyamin ba su san bala'i na gaf da su ba.
\v 35 Sai Yahweh ya kayar da Benyamin a gaban Isra'ila. A wannan rana, sojojin Isra'ila suka kashe mutum 25,100 na Benyamin. Dukkan waɗanda suka mutu horarru ne wajen faɗa da takobi.
\s5
\v 36 Sai sojojin Benyamin suka ga cewa an kayar da su. Mutanen Isra'ila kuwa sun ba Benyamin sarari, sabo da suna la'akari da mutanen da ke ɓoye a kewaye da Gibiya.
\v 37 Sai mutanen da ke a ɓoye suka tashi da sauri suka auka cikin Gibiya, da takubbansu kuwa suka kashe duk wanda ke zaune a cikin birnin.
\v 38 Alamar da aka shirya tsakanin sojojin Isra'ila da mutanen da ke ɓoye a asirtattun wurare shi ne za su ga girgijen hayaƙi ya turniƙe yana fitowa daga birnin.
\s5
\v 39 Idan aka aika da alamar sojojin Isra'ila za su juya daga yaƙin. To Benyamin ya fara kai hari har sun kashe mutane wajen talatin na Isra'ila, sai suka ce, "babu shakka an kayar da su a gabanmu, kamar a yaƙin farko."
\s5
\v 40 Amma da tuƙuƙin hayaƙi ya fara tashi sama daga cikin birnin, mutanen Benyamin kuwa suka juya suka ga hayaƙi na tashi daga cikin dukkan birnin har zuwa sararin sama.
\v 41 Sai kuwa mutanen Isra'ila suka juyo kansu. Mutanen Benyamin suka tsorata, domin sun ga bala'in da ya afko masu.
\s5
\v 42 Sai suka gudu daga wurin mutanen Isra'ila, suna tserewa hanyar zuwa jeji. Amma yaƙin ya ci ƙarfinsu. Sojojin Isra'ila suka fito daga birane suka kuwa karkashe su a inda suke tsaye.
\s5
\v 43 Suka kewaye mutanen Benyamin, su a kora su, suka tattake su a Noha, har ya zuwa gabashin Gibiya.
\v 44 Daga kabilar Benyamin, mutane dubu goma sha takwas suka mutu, dukkan su mutane ne ƙwararru a yaƙi.
\s5
\v 45 Suka juya suka sheƙa da gudu zuwa jeji zuwa dutsen Rimon. Isra'ilawa suka ƙara kashe mutane dubu biyar a kan hanyoyi. Suka ci gaba da bin su, suna binsu ƙut da ƙut har zuwa Gidom, suka kuma ƙara kashe dubu biyu a can.
\v 46 Dukkan sojojin Benyamin da suka fãɗi a wannan rana mutane dubu ashirin da biyar ne - horarrun mutane wajen faɗa da takobi, dukkan su ƙwararru ne a wajen yaƙi.
\s5
\v 47 Amma mutane ɗari shida suka juya suka gudu zuwa jeji, zuwa dutsen Rimon. Suka yi wata huɗu suna zama a dutsen Rimon.
\v 48 Sojojin Isra'ila suka juya su ka fãɗa wa mutanen Benyamin suka hare su suka kashe birnin gaba ɗaya, da shanu dukka, da dukkan abin da suka iske. Suka kuma ƙone duk wani gari da suka iske a hanyarsu.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Daga nan mutanen Isra'ila suka ɗauki alƙawari a Mizfa, "Babu wani cikin mu da zai bada ɗiyarsa aure ga Benyamine."
\v 2 Sai mutanen suka haye zuwa Betel suka zauna can a gaban Allah har yamma, da muryoyi masu ƙarfi suka yi kuka mai zafi.
\v 3 Suka yi kira, "Meyasa, Yahweh, Allah na Isra'ila, wannan irin abu ya faru da Isra'ila, cewa a yau ɗaya daga cikin kabilunmu ya ɓace?"
\s5
\v 4 Washegari mutanen suka tashi da sassafe suka gina bagadi suka miƙa baiko na ƙonawa da na salama.
\v 5 Mutanen Isra'ila suka ce, "Daga cikin kabilun Isra'ila dukka wane ne bai fito taron Yahweh ba?" Gama sun riga sun ɗauki alƙawari mai muhimmanci game da duk wanda bai zo wurin Yahweh ba a Mizfa. Suka ce, "Babu shakka za a kashe shi."
\s5
\v 6 Sai mutanen Isra'ila suka ji tausayin ɗan'uwansu Benyamin. Suka ce, "A yau an datse kabila ɗaya daga cikin Isra'ila.
\v 7 Wane ne za ya bada matayen aure ga waɗanda suka rage, tun da mun riga mun yi alƙawari ga Yahweh cewa babu wanda za ya bar wani daga cikin su ya auri 'ya'yanmu mata?"
\s5
\v 8 Suka ce, "Wace ce cikin kabilun Isra'ila ba ta zo wurin Yahweh ba a Mizfa?" Sai aka iske cewa babu wanda yazo taron daga Yabish Giliyad.
\v 9 Domin da aka sa mutane suka tsaya jeri-jeri, duba, babu ko ɗaya daga cikin mazaunan Yabish Giliyad da ya kasance.
\v 10 Sai taron suka aika da jarumawansu mutum dubu sha biyu da umarnin cewa su je Yabish Giliyad su kai masu hari, su kuma kashe su, har ma da mata da 'ya'ya.
\s5
\v 11 "Haka za ku yi: dole ne ku kashe kowanne namiji da kowace mace da ta san namiji."
\v 12 Mutanen suka samo daga cikin mazauna Yabish Giliyad 'yanmata ɗari huɗu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, suka kawo su sansani a Shilo, cikin Kan'ana.
\s5
\v 13 Taron ga baki ɗaya suka aika da saƙo ga mutanen Benyamin da ke a dutsen Rimon su na cewa muna neman ku da salama.
\v 14 Mutanen Benyamin suka dawo a wannan lokacin kuma suka basu matan Yabish Giliyad, amma kuma matan basu isa kowannen su ya samu ba.
\v 15 Mutanen suka yi juyayin abin da ya faru da Benyamin, saboda Yahweh ya sa rarrabuwa a tsakanin kabilun Isra'ila.
\s5
\v 16 Sai shugabannin taron suka ce, "Yaya za mu shirya wa mutanen Benyamin da suka rage matan aure, tun da an kashe matayen Benyamin?"
\v 17 Sai suka ce, "Dole ne a sami gãdo domin waɗanda suka tsira a Benyamin, domin ka da kabila ɗaya ta lalace a Isra'ila.
\s5
\v 18 Ba za mu iya ba su matan aure daga cikin 'ya'yanmu mata ba, gama mutanen Isra'ila sun yi alƙawari, 'La'ananne ne wanda ya ba da mace ga Benyamin.'"
\v 19 Sai suka ce, "Kun san akwai bikin idin Yahweh kowacce shekara a Shilo (wadda ke arewa da Betel, gabas da hanyar da ke tafiya daga Betel zuwa Shekem, a kudacin Lebona)."
\s5
\v 20 Sai suka yi wa mutanen Benyamin umarni, suka ce, "Ku je ku ɓoye a asirce ku yi kwanto cikin garkar inabi.
\v 21 Ku lura da lokacin da 'yanmata daga Shilo za su fito rawa, sai ku hanzarto daga garkar inabin kowanen ku ya kama wa kansa mata daga cikin 'yanmatan Shilo, daga nan ku koma ƙasar Benyamin.
\s5
\v 22 Idan ubanninsu ko 'yan'uwasu maza suka zo domin su yi mana tawaye, za mu ce masu, 'Ku yi mana tagomashi, ku bar su su zauna saboda ba mu samarwa dukkansu matan aure ba a lokacin yaƙin. Ba ku da laifi, tun da ba ku bayar da 'ya'yanku mata ba a gare su.'"
\s5
\v 23 Mutanen Benyamin suka yi yadda aka ce. Suka ɗauki iya matan auren da suke bukata daga cikin 'yan'matan da ke rawa sai su da ke raka kwashe su suka tafi da su su zama matansu. Suka koma wurin gãdonsu. Suka sake gina garuruwansu suka zauna a ciki.
\v 24 Daga nan mutanen Isra'ila suka bar wurin suka koma gida, kowanensu ya koma cikin kabilarsa da zuriyarsa, kowanensu kuma ga gãdonsa.
\s5
\v 25 A cikin waɗannan kwanaki babu sarki a Isra'ila. Kowa yana yin abin da ya ga ya yi dai-dai a idanunsa.