ha_ulb/06-JOS.usfm

1354 lines
94 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id JOS
\ide UTF-8
\h Littafin Yoshuwa
\toc1 Littafin Yoshuwa
\toc2 Littafin Yoshuwa
\toc3 jos
\mt Littafin Yoshuwa
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Ya zamana fa bayan mutuwar Musa bawan Yahweh, sai Yahweh ya yi magana da Yoshuwa ɗan Nun, babban mataimakin Musa, ya ce,
\v 2 "Bawana Musa, ya rasu. Yanzu fa, ka tashi, ka haye wannan kogin Yodan, da kai da dukkan mutanen nan, zuwa cikin wannan ƙasa da zan ba su - ga mutanen Isra'ila.
\v 3 Na rigaya na ba ku dukkan inda sawun ƙafafunku za su taka. Na baku ita, kamar yadda na yi wa Musa alƙawari.
\s5
\v 4 Daga jejin Lebanon, har zuwa babban kogin Yufaratas, dukkan ƙasar Hatiyawa, da Babban Teku, inda rana take faɗuwa, za ta zama ƙasarku.
\v 5 Ba wanda zai iya tsayayya da kai dukkan kwanakin ranka. Zan kasance tare da kai kamar yadda na kasance da Musa. Bazan yasheka ba ko in bar ka.
\s5
\v 6 Ka dage ka yi ƙarfin hali. Za ka sa mutanen nan su gaji ƙasar da na alƙawarta wa kakanninsu zan ba su.
\v 7 Ka dage ka yi ƙarfin hali sosai. Ka yi hankali ka yi biyayya da dukkan dokokin da bawana Musa ya umarce ka. Kada ka kauce masu zuwa dama ko hagu, domin ka yi nasara duk inda ka tafi.
\s5
\v 8 Kullum za ka riƙa yin magana a kan wannan littafin shari'a. Za ka riƙa binbini a kansa dare da rana domin ka yi biyayya da dukkan abin da aka rubuta a ciki. Sa'annan za ka zama da albarka da nasara.
\v 9 Ba ni ne na urmace ka ba? Ka ƙarfafa ka yi ƙarfin hali! Kada ka ji tsoro. Kada ka karaya. Yahweh Allahnka ya na nan tare da kai duk inda ka tafi."
\s5
\v 10 Sai Yoshuwa ya umarci shugabannin jama'a,
\v 11 "Ku tafi cikin sansanin ku dokaci mutanen, 'Ku shirya wa kanku guzuri. Cikin kwana uku za ku haye wannan Yodan ku mallaki wannan ƙasa da Yahweh Allahnku ya ke ba ku gãdo."'
\s5
\v 12 Ga Rubainawa, da Gadawa da rabin kabilar Manasse, Yoshuwa ya ce,
\v 13 "Ku tuna da maganar da Musa bawan Yahweh, ya umarce ku sa'ad da ya ce, 'Yahweh Allahnku ya na ba ku hutawa, ya na kuma ba ku wannan ƙasa.'
\s5
\v 14 Matanku, da 'yan ƙanananku, da dabbobin ku za ku barsu a ƙasar da Musa ya ba ku, can ƙetaren Yodan. Amma jarumawanku za su tafi da 'yan 'uwanku su taimaka masu
\v 15 har sai Yahweh ya ba 'yan 'uwanku hutawa kamar yadda ya baku. Haka su ma za su mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ke ba su. Sa'annan za ku dawo zuwa taku ƙasar ku gaje ta, ƙasar da Musa bawan Yahweh ya baku can ketaren Yodan inda rana take fitowa."
\s5
\v 16 Sa'annan su ka amsa wa Yoshuwa, su ka ce, "Za mu yi dukkan abin da ka umarce mu, kuma duk in da ka aike mu za mu je.
\v 17 Za mu yi maka biyayya kamar yadda muka yi wa Musa biyayya. Allahnka Yahweh dai ya kasance tare da kai, kamar yadda ya kasance da Musa.
\v 18 Duk wanda ya yi tawaye gãba da umarninka ya kuma yi rashin biyayya da maganarka za a kashe shi. Ka dage ka yi ƙarfin hali."
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Sai Yoshuwa ɗan Nun a asirce ya aiki mutum biyu daga Shittim magewaya. Ya ce; "Ku je, ku dubo ƙasar, musamman Yeriko." Su ka yi tafiyarsu su ka isa gidan wata karuwa mai suna Rahab, a nan ne su ka sauka.
\v 2 Aka cewa sarkin Yeriko, "Duba, mutanen Isra'ila sun zo nan domin su leƙi ƙasar."
\v 3 Sai sarkin Yeriko ya aika wa Rahab cewa, "Ki fito da mutanen da su ka zo wurinki waɗanda su ka shiga gidanki, gama sun zo ne domin leƙen dukkan ƙasar."
\s5
\v 4 Amma matar ta rigaya ta ɗauki mutanen nan biyu ta ɓoye su. Sai ta amsa masu, "I, mutanen sun zo wurina amma ban san daga inda su ka fito ba.
\v 5 Sun bar nan da sauran duhu, lokacin da ake kulle ƙofar birni. Ban san inda su ka tafi ba. Mai yiwuwa ku cim masu idan kun bi su da sauri."
\s5
\v 6 Gama ta rigaya ta kai su bisa rufin ɗakinta ta rufe su da ƙeƙasheshen rama waɗanda ta shinfiɗa a bisa rufin.
\v 7 Sai mutanen su ka bi su a kan hanya da ta kai su kwarin Yodan. Nan da nan aka rufe ƙofar bayan da masu bin su su ka fita.
\s5
\v 8 Kafin mutanen su kwanta da dare, sai ta zo wurinsu a rufin kan ɗaki.
\v 9 Ta ce, "Na sani Yahweh ya rigaya ya ba ku ƙasar kuma tsoronku ya faɗo kanmu. Dukkan waɗanda ke zaune a ƙasar za su narke a gabanku.
\s5
\v 10 Mun ji yadda Yahweh ya sa ruwan Jan teku ya ƙafe dominku sa'ad da kuka fito daga Masar. Mun ji kuma abin da ku ka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa a hayin Yodan - Su Sihon da - Og waɗanda ku ka hallaka dukka.
\v 11 Da dai mu ka ji haka, zukatanmu su ka narke har babu karfin hali da ya rage a cikin ko ɗayanmu. Domin Yahweh Allahnku, shi ne Allah na sama da na duniya a ƙasa.
\s5
\v 12 Yanzu dai, ku rantse mani da Yahweh cewa, kamar yadda na yi maku alheri, kuma ku yi wa gidan ubana alheri. Ku bani tabbatacciyar alama
\v 13 cewa za ku tsirar da ran mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan 'uwana maza, da mata da dukkan iyalansu, za ku kuma cece mu daga mutuwa."
\s5
\v 14 Mutanen su ka ce ma ta, "Ran mu a bakin na ki, har ma ga mutuwa! Idan baki tona al'amarin nan ba, idan Yahweh ya ba mu ƙasar za mu nuna maki jinkai da aminci."
\s5
\v 15 Sai ta zura su ƙasa ta taga da igiya. Gidan da take zaune an gina shi cikin ganuwar birnin.
\v 16 Ta ce masu, "Ku hau cikin duwatsu ku ɓoye, ka da masu bin ku su same ku. ku ɓoye a can har kwana uku bayan masu bin ku sun dawo. Sa'annan ku yi tafiyarku."
\v 17 Mutanen su ka ce ma ta, "Za mu zama kuɓutattu da ga rantsuwar da mu ka rantse ma ki, idan ba ki riƙe amanar ba.
\s5
\v 18 Lokacin da za mu zo ƙasar, dole ki ɗaura wannan jar igiya a tagar da ki ka zura mu, za ki kawo cikin gidan ki mahaifinki da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki da dukkan gidan mahaifinki.
\v 19 Duk wanda ya fita daga ƙofar gidanki zuwa titi, jininsu na bisa kansu, mu kuwa mun kuɓuta. Amma idan muka sa hannu a kan wanda ke cikin gida tare da ke, alhakin jininsa na kan mu.
\s5
\v 20 Amma idan ki ka furta al'amarin nan, za mu kuɓuta daga rantsuwar da ki ka sa mu ka rantse maki,"
\v 21 Rahab ta amsa, "Bisa ga maganar da ku ka faɗa bari ya zama haka." Sai ta sallame su, su ka tafi. Sai ta ɗaura jar igiyar a tagar.
\s5
\v 22 Su ka tafi su ka haye cikin tsaunuka su ka kuma zauna can kwana uku har sai da masu bin sawun su su ka koma. masu bin sawunsu su ka yi ta neman su a kan hanya ba su sami komai ba.
\s5
\v 23 Mutanen biyu su ka ƙetare su ka komo wurin Yoshuwa, ɗan Nun, su ka labarta masa dukkan abubuwan da su ka faru da su.
\v 24 Su ka ce ma Yoshuwa, "Gaskiya Yahweh ya ba mu wannan ƙasar. Dukkan mazaunan ƙasar su na ta narkewa sabili da mu."
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Yoshuwa ya tashi da sassafe, sai su ka yi ƙaura daga Shittim. Su ka iso Yodan, shi da dukkan mutanen Isra'ila, su ka sauka a nan kafin su haye.
\s5
\v 2 Bayan kwana uku, sai shugabanni su ka ratsa ta tsakiyar zangon;
\v 3 su ka umarci mutane, "Lokacin da ku ka ga akwatin alƙawari na Yahweh Allahnku, da firistoci daga kabilar Lebiyawa ɗauke da shi, sai dole ku bar nan wajen ku bi shi.
\v 4 Dole ku sa ratar ƙafa dubu biyu tsakanin ku da akwatin. Kada ku je kusa da shi, domin ku iya hango inda za ku bi, da shike ba ku taɓa bin wannan hanyar ba,"
\s5
\v 5 Yoshuwa ya cewa jama'a; "Ku tsarkake kanku gobe, domin Yahweh zai yi abin al'ajibi a tsakanin ku."
\v 6 Sa'annan Yoshuwa ya cewa Firistoci, "Ku ɗauki akwatin alƙawari ku wuce gaban jama'a." Sai su ka ɗauki akwatin alƙawarin su ka wuce gaban jama'a da shi.
\s5
\v 7 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "A ranar yau zan maishe ka babban mutum a idanun Isra'ilawa dukka. Za su sani, kamar yadda na kasance da Musa, zan kasance da kai.
\v 8 Za ka umarci Firistoci su ɗauki akwatin alƙawari, 'Lokacin da ku ka isa bakin ruwayen Yodan, dole ku tsaya cik a cikin Kogin Yodan."'
\s5
\v 9 Yoshuwa ya cewa mutanen Isra'ila, "Ku zo nan ku saurari maganar Yahweh Allahnku.
\v 10 Ta wurin wannan za ku sani Allah mai rai na tare da ku zai kori Kan'aniyawa, Hatiyawa da Hibiyawa da Farizziyawa da Girgashiyawa da Amoriyawa da Yebusawa daga gaban ku.
\v 11 Duba! Akwatin alƙawari na Ubangijin dukkan duniya ya shiga gaban ku zuwa cikin Yodan.
\s5
\v 12 Yanzu ku zaɓi mutum goma sha biyu daga ƙabilar Isra'ila, mutum guda daga kowannen su.
\v 13 Sa'ad da tafin sawun firistoci masu ɗauke da akawatin Yahweh, Ubangijin dukkan duniya, ya taɓa ruwayen Yodan, ruwayen za su datse, har ma ruwayen da suke kwararowa daga bisan kogin za su daina kwararowa su tsaya a tari guda."
\s5
\v 14 A lokacin da jama'a su ka tashi domin su ƙetare Yodan, firistoci ɗauke da akwatin alƙawari su ka wuce gaban jama'a.
\v 15 Da zarar mutane masu ɗauke da akwatin su ka iso Yodan, da ƙafafunsu su ka taɓa gacin ruwan (Yodan dai yakan yi ambaliya dukkan lokacin girbi),
\v 16 sai ruwayen da suke gangarowa daga tudun rafin su ka taru wuri guda. Ruwan ya dena gangarowa daga nesa. Ya kuma dena gagarowa daga Adam, birnin da ke kusa da Zaretan, har ya zuwa tekun Negeb, Tekun Gishiri. Jama'a su ka ƙetare kurkusa da Yeriko.
\s5
\v 17 Firistocin da ke ɗauke da akwatin alƙawari na Yahweh su ka tsaya a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Yodan har sai da jama'ar Isra'ila su ka ƙetare a kan busasshiyar ƙasa.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Sa'ad da dukkan mutane su ka ƙetare Yodan, Yahweh ya cewa Yoshuwa,
\v 2 "Ku zaɓa wa kan ku mutum goma sha biyu, daga kowanne kabila mutum ɗaya.
\v 3 Ka ba su wannan umarni: 'Ku ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Yodan inda firitoci ke tsaye a kan busasshiyar ƙasa, ku kawo su ku ajiye su inda za ku kwana daren yau."'
\s5
\v 4 Sai Yoshuwa ya kira mutanen nan goma sha biyu waɗanda ya zaɓo daga kabilar Isra'ila, guda ɗaya daga kowacce kabila.
\v 5 Yoshuwa ya ce masu, "Ku wuce gaban akwatin Yahweh Allahnku zuwa cikin tsakiyar Yodan. Kowannen ku zai ɗauki dutse a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilun mutanen Israila.
\s5
\v 6 Wannan zai zamar ma ku alama a tsakanin ku sa'ad da 'ya'yanku za su tambaya a kwanaki masu zuwa, 'Menene ake nufi da waɗannan duwatsu?'
\v 7 Sa'annan za ku ce, 'An yanke ruwayen Yodan a gaban akwatin alƙawari na Yahweh. Lokacin da ya ƙetare Yodan, ruwan Yodan ya yanke. Saboda haka waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga jama'ar Isra'ila har abada."'
\s5
\v 8 Jama'ar Isra'ila su ka yi dai-dai abin da Yoshuwa ya umarce su, su ka ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Yodan, kamar yadda Yahweh ya cewa Yoshuwa. Suka shirya duwatsun yadda lambar kabilar Isra'ila ta ke. Su ka ɗebo duwatsu, su ka kawo masaukinsu su ka shirya su a nan.
\v 9 Sa'annan Yoshuwa ya jera wasu duwatsu a tsakiyar Kogin Yodan, a inda sawun firistoci da su ka ɗauki akwatin alƙawari su ka tsaya. Wannan alamar tana nan har yau.
\s5
\v 10 Firitoci da ke ɗauke da akwatin alƙawari su ka tsaya a tsakiyar Yodan cik har sai duk abubuwan da Yahweh ya umarci Yoshuwa ya faɗa wa mutane sun cika sarai, bisa ga duk abin da Musa ya umarci Yoshuwa.
\v 11 Sa'ad da dukkan jama'a su ka gama ƙetarewa, akwatin Yahweh da firistoci su ka ƙetare a gaban jama'a.
\s5
\v 12 Kabilar Ruben, da kabilar Gad, da rabin kabilar Manasse su ka wuce a gaban Isra'ilawa shirye 'yan yaƙi, kamar yadda Musa ya ce masu.
\v 13 Kimanin maza dubu arba'in shiryayyu mayaƙa su ka wuce a gaban Yahweh, domin yaƙi wajen filayen Yeriko.
\v 14 A ranan nan Yahweh ya ɗaukaka Yoshuwa a idanun dukkan Isra'ilawa. Su ka girmama shi - dai dai da yadda su ka ga ƙwarjinin Musa - dukkan kwanakinsa.
\s5
\v 15 Sai Yahweh ya yi magana da Yoshuwa,
\v 16 "Ka umarci firistoci masu ɗauke da akwatin alƙawari su hauro daga cikin Yodan."
\s5
\v 17 Sai, Yoshuwa ya umarci firistoci, "Ku fito daga cikin Yodan."
\v 18 Da firistoci da ke ɗauke da akwatin alƙawari na Yahweh su ka fito daga tsakiyar Yodan, su ka sa tafin ƙafarsu a busasshiyar ƙasa, sai ruwayen Yodan su ka koma magudanarsu su ka cike ta da ambaliya, kamar yadda ta ke kwanaki hudu da su ka wuce.
\s5
\v 19 Jama'a su ka fito daga Yodan a rana ta goma ga watan ɗaya. Su ka zauna a Gilgal, gabashin Yeriko.
\v 20 Duwatsu sha biyu da su ka ɗauko daga Yodan, Yoshuwa ya shiryasu a Gilgal.
\v 21 Ya cewa jama'ar Isra'ila, "Sa'ad da zuriyarku za su tambayi ubanninku a zamanai masu zuwa, 'Waɗannan duwatsun fa?'
\s5
\v 22 Ku gayawa 'ya'yanku, 'Nan ne Isra'ila ya ƙetare Yodan kan busasshiyar ƙasa.'
\v 23 Yahweh Allahnku ya janye ruwan Yodan domin ku, har sai da su ka ƙetare, kamar yadda Yahweh Allahnku ya yi wa Jan Teku, wadda ya busar da ita domin mu sai da muka haye,
\v 24 domin mutanen duniya dukka su sa ni hannun Yahweh mai karfi ne, ku kuma ku girmama Yahweh Allahnku har abada."
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Nan da nan da dukkan sarakunan Amoriyawa na yamma da Yodan, da dukkan sarakunan Kan'aniyawa, waɗanda su ke gefen Babbar Teku, su ka ji yadda Yahweh ya sa ruwayen Yodan su ka ƙafe har sai da jama'ar Isra'ila suka haye zuwa ɗaya gacin, sai zukatansu suka narke, ba su da sauran wani ƙarfin hali kuma saboda mutanen Isra'ila.
\s5
\v 2 A lokacin sai Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka yi wuƙar dutse ka sake yi wa dukkan mazajen isra'ila kaciya."
\v 3 Sai Yoshuwa ya yi wuƙar dutse ya yi wa dukkan mazajen Isra'ila kaciya a Gibiyat Hãralot.
\s5
\v 4 Wannan shi ne dalilin da Yoshuwa ya yi masu kaciya: dukkan mazajen da su ka fito daga Masar, tare da dukkan mayaƙa, sun mutu a cikin jeji a kan hanya, bayan sun baro Masar,
\v 5 Ko da shike dukkan mazajen da su ka baro Masar suna da kaciya, amma, duk yara maza da aka haifa cikin jeji a kan hanyar fitowar su daga Masar ba su da kaciya.
\s5
\v 6 Gama mutanen Isra'ila su ka yi tafiya shekara arba'in a jeji, har sai da dukkan mazajen da su ka fito Masar mayaƙa su ka mutu, domin ba su yi biyayya da muryar Yahweh ba. Yahweh ya rantse masu ba za su shiga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba mu, ƙasa wadda take zubo da madara da zuma.
\v 7 'Ya'yansu ne waɗanda Yahweh ya tăda a madadinsu, su ne Yoshuwa ya yi wa kaciya, domin ba a yi masu kaciya a hanya ba.
\s5
\v 8 Sa'ad da aka yi wa dukkan su kaciya, su ka zauna cikin sansani har sai da su ka warke.
\v 9 Sai Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Wannan rana ta yau na cire ƙunyar Masar daga gare ku." Saboda haka, ake kiran sunan wurin Gilgal har wa yau.
\s5
\v 10 Jama'ar Isra'ila su ka yi sansani a Gilgal. Su ka kiyaye Idin Ketarewa a rana ta goma sha hudu ga wata, da yammaci, a filayen Yeriko.
\v 11 Su ka ci daga waɗansu amfanin ƙasar a rana ta fari bayan Idin Ketarewa: waina marar yisti da gasasshen hatsi.
\s5
\v 12 Manna ta dena saukowa bayan ranar da su ka ci daga amfanin ƙasar. Babu manna kuma domin jama'ar Isra'ila, amma su ka ci daga cikin amfanin ƙasar Kan'ana a shekaran nan.
\s5
\v 13 Sa'ad da Yoshuwa ya kusa da Yariko, sai ya tada idanunsa ya duba, sai, ga wani mutum tsaye a gabansa; da takobi a zare a hannunsa. Yoshuwa ya tafi wurin sa ya ce, "Kana wajenmu ne ko kana wajen abokan găbarmu?"
\s5
\v 14 Sai ya ce, "Ko ɗaya. Ni ne sarkin yaƙin rundunar Yahweh. Yanzu na zo." Sai Yoshuwa ya russuna da fuskarsa ƙasa ya yi masa sujada ya ce, "Menene ubangijina zai faɗa wa bawansa?"
\v 15 Sai sarkin yaƙin rundunar Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka cire takalmanka daga ƙafafunka, domin inda ka ke tsaye wuri mai tsarki ne." Haka kuwa Yoshuwa ya yi.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Aka rufe dukkan ƙofofin shiga Yeriko saboda mayaƙan Isra'ila. Ba wanda ya fita ko ya shigo.
\v 2 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Duba, na bada Yeriko da sarkinta, da horarrun sojojinta a hannunka.
\s5
\v 3 Dole ku zagaya birnin, dukkan mazaje mayaƙa za su zaga birnin sau ɗaya. Dole za ku yi haka har kwana shida.
\v 4 Dole firistoci bakwai su ɗauki ƙahonni bakwai na raguna a gaban akwati. A rana ta bakwai, dole ku zagaya brinin sau bakwai, firistoci kuma dole su busa ƙahonni da babbar busa.
\s5
\v 5 Daga nan dole su yi doguwar busa da ƙahon rago, kuma sa'ad da ku ka ji busar ƙahon dukkan mutane dole su yi ihu da babbar murya, garun birnin zai faɗi ya rushe. Dole sojojin su kai hari, kowannensu ya miƙe ya tafi gaba."
\s5
\v 6 Sa'annan Yoshuwa ɗan Nun ya kira firistoci ya ce masu, "Ku ɗauki akwatin alƙawari, kuma firistoci bakwai su ɗauki ƙahonnin raguna bakwai a gaban akwatin Yahweh."
\v 7 Ya cewa jama'a, "Ku tafi ku zagaya birnin, masu makamai kuma za su je gaban akwatin Yahweh."
\s5
\v 8 Kamar yadda Yoshuwa ya cewa mutane, firistoci bakwai su ka ɗauki ƙahonni bakwai na raguna a gaban Yahweh. Da su ka cigaba da tafiya sai su ka busa ƙaho da babbar murya. Akwatin alƙawari na Yahweh na biye da su.
\v 9 Masu makamai su ka tafi gaban firistoci, su ka yi babbar busa, wasu masu makamai kuma su ka bi bayan akwatin, firistoci kuma su ka yi ta busa ƙahonni.
\s5
\v 10 Amma Yoshuwa ya dokaci mutane, cewa, "Kada ku yi ihu. Kada wata ƙara ta fito daga bakinku sai randa na ce ku yi ihu. Lokacin ne za ku yi ihu."
\v 11 Sai ya sa aka zagaya birnin da akwatin Yahweh sau ɗaya a ranar. Sa'annan suka komo sansaninsu, su ka kwanta daren nan.
\s5
\v 12 Sai Yoshuwa ya tashi da sassafe, firistoci kuma su ka ɗauki akwatin Yahweh.
\v 13 Firistoci bakwai, masu ɗauke da ƙahonnin raguna bakwai a gaban akwatin Yahweh su ka yi ta busa ƙahonni su na tafiya gaba gaɗi. Sojoji masu makamai suna tafiya a gabansu. Amma sa'ad da 'yan tsaron baya su ka biyo akwatin Yahweh, sai aka dinga busa ƙahonni.
\v 14 Su ka zaga birnin sau daya a rana ta biyu su ka komo sansaninsu. Haka suka dinga yi har kwana shida.
\s5
\v 15 A rana ta bakwai su ka tashi da sassafe kafin gari ya waye, su ka zãga birnin kamar yadda su ka saba yi, wannan karon sau bakwai.
\v 16 A wannan ranar ce su ka zagaya birnin sau bakwai, firistoci su ka busa ƙahonni, sai Yoshuwa ya umarci mutane, "Ku yi ihu! Gama Yahweh ya ba ku birnin.
\s5
\v 17 Za a keɓe wa Yahweh birnin da dukkan abin da ke cikinta domin hallakarwa. Rahab karuwan nan ce kaɗai za ta rayu - ita da dukkan waɗanda ke tare da ita a gidanta - domin ta ɓoye waɗanda mu ka aika.
\v 18 Amma ku kam, ku yi lura game da abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa, domin kada bayan kun waresu saboda hallakarwa, ku koma ku ɗauka. Idan ku ka yi haka, za ku maida sansanin Isra'ila abin da za a hallakar kuma za ku jawo ma ta masifa.
\v 19 Dukkan azurfa, zinariya da abubuwan tagulla da ƙarfe a keɓe su ga Yahweh. Dole a kai su cikin ma'ajin Yahweh."
\s5
\v 20 Da su ka yi babbar busa ƙahonni, sai mutane su ka yi gawurtaccen ihu ganuwar ta faɗi ƙasa, sa'annan kowanne mutum ya shiga ciki kai tsaye su ka ci birnin.
\v 21 Su ka lalatar da dukkan abin da ke birnin da kaifin takobi - maza da mata, yaro da tsoho, shanu, tumaki, da jakai.
\s5
\v 22 Sa'annan Yoshuwa ya cewa mutanen biyu da su ka leƙo asirin ƙasar, "Ku shiga gidan karuwar nan. Ku fitar da ita waje da dukkan waɗanda suke tare da ita, kamar yadda ku ka rantse ma ta."
\s5
\v 23 Sai samarin nan biyu magewaya su ka shiga ciki su ka fitar da Rahab. Su ka fitar da mahaifinta, mahaifiyarta, 'yan'uwanta maza da dukkan 'yan'uwanta da su ke tare da ita. Su ka kai su wani wuri dabam da sansanin Isra'ila.
\v 24 Su ka ƙona garin da dukkan abin da ke cikinsa. Sai dai azurfa, zinariya da kwanonin tagulla da na ƙarfe ne su ka ajiye a ma'ajin gidan Yahweh.
\s5
\v 25 Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwa, gidan ubanta, da dukkan waɗanda ke tare da ita da rai. Tana zaune a Isra'ila har wayau domin ta ɓoye masu leƙen asirin ƙasa waɗanda Yoshuwa ya aika su leƙo Yeriko.
\s5
\v 26 Sai Yoshuwa ya umarce su a lokacin da rantsuwa, ya kuma ce, "La'anannen mutum ne a idon Yahweh wanda ya sake gina wannan birni, Yeriko. A bakin ran ɗan farinsa, zai sa harsashen, a kuma bakin ran ɗan autansa, zai kafa ƙofofinta."
\v 27 Haka Yahweh ya kasance tare da Yoshuwa, sunansa ya shahara ko'ina a faɗin ƙasar.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Amma jama'ar Isra'ila su ka yi rashin aminci game da abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa. Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi ɗan Zera, daga kabilar Yahuda ya ɗauka daga cikin abubuwan da aka ƙeɓe domin hallakarwa, sai fushin Yahweh ya yi ƙuna a kan 'ya'yan Isra'ila.
\s5
\v 2 Yoshuwa ya aiki mutane daga Yeriko zuwa Ai da take kusa da Bet Aben gabas da Betel. Ya ce masu, "Ku tafi ku leƙo ƙasar." Sai mutanen su ka tafi su ka leƙo Ai.
\v 3 Da su ka dawo wurin Yoshuwa, su ka ce masa, "Kada ka aika mutane dukka zuwa Ai. Ka aika misalin dubu biyu ko uku kawai, su je su kai ma ta hari. Kada ka bari dukkan mutane su wahala a yaƙi, domin ba su da yawa."
\s5
\v 4 Saboda haka mutum dubu uku ne kaɗai cikin mayaƙa su ka tafi.
\v 5 Mutanen Ai su ka kashe misalin mutane talatin da shida su ka fafare su daga ƙofar birnin har zuwa mafasar duwatsu, su ka karkashe su sa'ad da su ke gangarowa daga kan tudu. Zukatan mutanen su ka tsorata ƙarfin halinsu kuma ya rabu da su.
\s5
\v 6 Sai Yoshuwa ya yayyage tufafinsa. Da shi da shugabanin Isra'ila su ka zuba ƙura a kansu su ka faɗi rub da ciki a ƙasa a gaban akwatin Yahweh har yamma.
\v 7 Sa'annan Yoshuwa ya ce, "Ya Ubangiji Yahweh, me ya sa ma ka haye da mutanennan daga Yodan? Don ka bashe mu a cikin hannun Amoriyawa su hallakar da mu? Ai da mun gwammace mu yi zamanmu a wancan hayin Yodan!
\s5
\v 8 Ubangiji, me zan ce, bayan Isra'ila ta juya ta guje ma abokan gabanta?
\v 9 Gama Kan'aniyawa da dukkan mazaunan ƙasar za su ji. Za su kewaye mu su sa mutanen duniya su manta da sunanmu. To me za ka yi domin sunanka mai girma?"
\s5
\v 10 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Tashi! Me ya sa ka kwanta fuskarka ƙasa?
\v 11 Isra'ila ta yi zunubi. Sun karya dokata da na umurce su. Sun sãci waɗansu abubuwan da aka keɓe. Sun sata sun kuma ɓoye zunubinsu ta wurin aje abubuwan da su ka ɗauka cikin kayansu.
\v 12 Saboda haka ne, mutanen Isra'ila ba za su iya tsayawa a gaban maƙiyansu ba. Sun juya wa maƙiyansu baya domin su kan su an ƙebe su domin hallakarwa. Ba zan kasance tare da ku kuma ba sai ko kun hallaka waɗannan abubuwa da ya kamata an hallakar da su, amma suna nan tare da ku.
\s5
\v 13 Tashi! Ka tsarkake jama'ar a gareni ka ce masu, 'Ku tsarkake kanku domin gobe. Domin Yahweh, Allah na Isra'ila ya ce, "Akwai abubuwan da aka keɓe saboda hallakarwa waɗanda su ke a tsakaninku, Isra'ila. Ba za ku iya tsayawa gaban maƙiyanku ba, sai kun fitar da dukkan abubuwan da aka keɓe domin hallakarwa daga tsakaninku."
\s5
\v 14 Da safe, dole ku taru bisa ga kabilarku. Kabilar da Yahweh ya zaɓa za ta matso iyali - iyali. Iyalin da Yahweh ya zaɓa dole su matso gida - gida. Gidan da Yahweh ya ware dole a gabatar da su mutum - mutum.
\v 15 Zai zamana duk wanda aka zaɓa, da yake da waɗannan keɓaɓɓun abubuwan hallakarwa, za a ƙone shi, da duk abin da yake da shi, domin ya karya dokar Yahweh, kuma ya yi abin ban kunya a Isra'ila."'
\s5
\v 16 Saboda haka, Yoshuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa, kabila - kabila, sai aka zaɓi kabilar Yahuda.
\v 17 Yoshuwa ya gabatar da kabilar Yahuda, sai aka zaɓi iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera mutum - mutum, sai aka zaɓi gidan Zabdi.
\v 18 Ya gabatar da gidan Zabdi, mutum - mutum, sai aka zaɓi Akan, ɗan Karmi, ɗan Zera daga kabilar Yahuda, shi ne aka zaɓa.
\s5
\v 19 Sai Yoshuwa ya cewa Akan, "Ɗana, ka faɗi gaskiya a gaban Yahweh Allah na Isra'ila, ka ba da shaidarka gareshi. Idan ka yarda, ka gaya ma ni abin da ka yi. Ka da ka ɓoye ma ni."
\v 20 Akan ya amsa wa Yoshuwa, "Gaskiya na yi wa Yahweh zunubi, Allah na Isra'ila. Ga abin da na yi:
\v 21 Sa'ad da na ga wata kyakkyawar alkyabba daga Babila, a cikin ganima, da shekel dari biyu na azurfa, da curin zinariya mai nawin shekel hamsin, sai na yi sha'awarsu na ɗauka. Sunanan a binne a ƙasa a tsakiyar rumfata, azurfar kuwa ta na ƙarƙashinsu.
\s5
\v 22 Yoshuwa ya aiki manzanni, da su ka sheƙa da gudu zuwa rumfar, sai kuwa gasu. Da suka duba, su ka tarar da abubuwan bizne cikin rumfarsa, da azurfar a ƙarƙashi.
\v 23 Sai su ka kwaso su daga tsakiyar rumfar su ka kawo wa Yoshuwa da dukkan mutanen Isra'ila. Su ka zuba su gaban Yahweh.
\s5
\v 24 Sai Yoshuwa, tare da dukkan Isra'ila, su ka ɗauki Akan ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da curin zinariyar, da 'ya'yansa maza da mata, da shanunsa, da jakunansa da tumakinsa, da rumfarsa da dukkan mallakarsa, su ka kawo su Kwarin Akor.
\s5
\v 25 Sa'annan Yoshuwa ya ce, "Don me ka wahalshe mu? Yahweh zai wahalsheka yau." Dukkan Isra'ila su ka jejjefe shi da duwatsu. Su ka jejjefi sauran da duwatsu su ka ƙone su da wuta.
\v 26 Su ka tula duwatsu a kansa mai tudu da su ke nan har yau. Yahweh ya juya daga fushinsa mai zafi. Saboda haka aka kira sunan wurin Kwarin Akor har zuwa yau.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka da ka ji tsoro; ka da ka karaya. Ka ɗauki dukkan mayaƙa. Ku haura zuwa Ai. Duba, na rigaya na ba ka sarkin Ai, da mutanensa, birninsa da kuma ƙasarsa a hunnunka.
\v 2 Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yeriko da sarkinta, amma za ku washe ganima da dabbobi domin kan ku. Ku yi kwanto a bayan birnin."
\s5
\v 3 Saboda haka Yoshuwa ya tashi ya ɗauki dukkan mazaje mayaƙa zuwa Ai. Sa'annan Yoshuwa ya zaɓi mazaje dubu talatin - ƙarfafa, jarumawa -- ya aike su da dare.
\v 4 Ya umarce su, "Ku duba, za ku yi wa birnin kwanto, a bayansa. ka da ku yi nisa da birnin sosai, amma dukkan ku ku kasance a shirye.
\s5
\v 5 Ni da dukkan mutanen da ke tare da ni za mu kusanci birnin, sa'ad da da za su fito su yi karo da mu, za mu guje da ga garesu kamar dă.
\v 6 Za su fito su fafare mu har sai mun rinjayesu daga birnin. Za su ce, 'Suna guje ma na karmar dă.' Haka za mu gudu da ga garesu.'
\v 7 Sa'annan za ku fito da ga maɓuyarku, ku ci birnin. Yahweh Allahnku zai ba da shi a hannunku.
\s5
\v 8 Sa'ad da ku ka ci birnin, za ku cinna masa wuta. Za ku yi wannan lokacin da ku ka yi biyayya da umarnin da aka bayar cikin maganar Yahweh. Duba, na umarce ku."
\v 9 Yoshuwa ya aike su, su ka tafi wurin kwanto, su ka yi faƙo tsakanin Betal da Ai, wato yamma da Ai ke nan. Yoshuwa kuwa ya kwana cikin jama'a a daren nan.
\s5
\v 10 Yoshuwa ya tashi da sassafe ya shirya sojojinsa, shi da shugabannin Isra'ila su ka kai wa mutanen Ai hari.
\v 11 Dukkan mayaƙa maza da ke tare da shi su ka tafi tare da shi su ka kusanci birnin. Su ka matsa kusa arewa da Ai. Akwai kwari tsakaninsu da Ai.
\v 12 Ya ɗauki mayaƙa kusan dubu biyar ya sa su ka yi kwanto yamma da birnin tsakanin Betel da Ai.
\s5
\v 13 Ya sanya dukkan sojojin ko'ina, muhimman rundunar ya sa su arewa da birnin, 'yan tsaron baya kuwa a yammancin birnin. Yoshuwa ya kwana a kwari a darennan.
\v 14 Ananan da sarkin Ai ya ga haka, sai shi da mayaƙansa suka tashi da sassafe su ka gaggauta su ka kai wa Isra'ila hari ta gefen da ya fuskanci kwarin kogin Yodan. Bai sani ba cewa 'yan kwanto suna jiran su auka wa birnin ta baya.
\s5
\v 15 Yoshuwa da dukkan Isra'ila suka yi kamar an rinjayesu su ka gudu cikin jeji.
\v 16 Aka kira dukkan mutane da ke cikin birnin su ka fafare su, su ka sheƙa da gudu su na bin Yoshuwa, aka kuwa rinjaye su nesa da birnin.
\v 17 Ba a bar ko mutum ɗaya a cikin Ai da kuma Betel da bai fito ya fafari mutanen Isra'ila ba. Su ka bar birnin da ƙofofin sa a buɗe sa'ad da suke fafarar Israi'ila.
\s5
\v 18 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Ka miƙa mashin da ke hannun ka wajen Ai, domin zan ba da Ai cikin hannunka."Yoshuwa ya miƙa mashin da ke hannunsa wajen birnin.
\v 19 Sai sojojin da su ka yi kwanto a saura su ka fito da ga inda suke sa'ad da ya mika hannunsa. Su ka yi gudu su ka shiga birinin su ka cinye shi. Nan da nan su ka cinna wa birnin wuta.
\s5
\v 20 Mutanen Ai su ka waiga baya. Su ka ga hayaƙi da ga birnin ya turmuƙe ya tashi sama, ba su iya kuɓucewa nan ko can ba. Gama sojojin Isra'ila da su ka gudu jeji su ka juyo su ka fuskanci masu fafarar su.
\v 21 Sa'ad da Yoshuwa da dukkan Isra'ila su ka ga mutanen da su ka ɓoye sun kone birnin, da kuma hayaƙin da ke tashi, su ka juyo su ka karkashe mutanen Ai.
\s5
\v 22 Sauran sojojin Isra'ila, waɗanda su ka shiga birnin, su ka fito su kai masu hari. Ta haka aka cafke mutanen Ai gaba da baya a tsakiyar rundunar Isra'ila, wasu a wannan gefe wasu a can. Isra'ila su ka buga mayaƙan Ai; ba wanda ya tsira ko ya kuɓuce.
\v 23 Su ka tsare sarkin Ai, wanda suka kama da rai, su ka kawo shi wurin Yoshuwa.
\s5
\v 24 Ana nan da Isra'ila ta gama karkashe mazaunan Ai a fili kusa da jejin da su ka fafare su, sa'ad da dukkansu, har ga na ƙarshe su ka mutu da kaifin takobi, dukkan Isra'ila su ka koma Ai. Su ka faɗa masu da kaifin takobi.
\v 25 Dukkan waɗanda aka kashe maza da mata, dubu goma sha biyu ne, dukkan mutanen Ai.
\v 26 Yoshuwa bai janye hannunsa ba da ya mika ta sa'ad da ya ke rike da mashi, har sai da ya gama hallakar da dukkan mutanen Ai.
\s5
\v 27 Isra'ila su ka ɗauki dabbobi kawai da ganimar da ke cikin birnin don kan su, kamar yadda Yahweh ya umarci Yoshuwa.
\v 28 Yoshuwa ya ƙone Ai ya maishe ta kango har abada. Yasasshen wurin ne har yau.
\s5
\v 29 Ya rataye sarkin Ai akan bishiya har sai maraice. Da rana ta kusan faɗuwa, Yoshuwa ya umarta a saukar da gangar jikin sarki da ga itace a jeffa shi a kofar birnin. A nan ne su ka tula tarin duwatsu akansa. Tsibin ya na nan har yau.
\s5
\v 30 Sai Yoshuwa ya ginawa Yahweh bagadi, Allah na Isra'ila, a kan Dutsen Ebal,
\v 31 dai - dai yadda Musa bawan Yahweh ya umarci mutanen Isra'ila, kamar yadda aka rubuta a littafin shari'a ta Musa: "Bagadi da ga duwatsun da ba a sassaƙa ba, wanda ba mutumin da ya ɗibiya guduma a kai." Ya mika hadayun ƙonawa ga Yahweh akan bagadin, su ka kuma miƙa hadayun salama.
\v 32 A nan a gaban mutanen Isra'ila ya rubuta shari'ar Musa bisa duwatsun.
\s5
\v 33 Dukkan Isra'ila, da shugabanninsu, da hakimai, da mahukuntansu, su ka tsaya a gefe biyu na akwatin alƙawari a gaban firistoci da Lebiyawa da ke ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh - baƙi da haifaffun wurin - rabinsu su ka tsaya a gaban Dutsen Gerizin, rabin kuma su ka tsaya a gaban Dutsen Ebal. Su ka albarkaci mutanen Isra'ila, kamar yadda Musa bawan Yahweh ya umarce su tun da farko.
\s5
\v 34 Bayan haka, Yoshuwa ya karanta dukkan zantattukan shari'a, da albarkun da la'anun, kamar yadda aka rubuta a littafin shari'a.
\v 35 Babu kalma ko ɗaya da ga dukkan abin da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta a gaban taron Isra'ila ba, har ma da mata, da ƙananan yara. da baƙin da su ke zaune tare da su.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Sai dukkan sarakunan dake zaune a ƙetaren Yodan a ƙasar duwatsu, da kuma kwarin gaɓar Babbar Teku wajen Lebanon - Hitiyawa, Amoriyawa Kan'aniyawa, Feriziyawa Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa -
\v 2 waɗannan su ka tattaru ƙarƙashin tuta guda, domin su yaƙi Yoshuwa da Isra'ila.
\s5
\v 3 Da mazaunan Gibiyon su ka ji abin da Yoshuwa ya yi wa Yeriko da Ai,
\v 4 su ka yi masu hila. Suka tafi kamar jakadu. Su ka ɗauki koɗaɗɗun buhuna su ka ɗibiya su kan jakunansu. Su ka kuma ɗauki tsofaffin salkunan ruwan inabi da su ka ƙoɗe, yagaggu, sun kuma sha ɗinki.
\v 5 Su ka sa tsoffofin takalman da suka sha gyara a ƙafafunsu, su ka sa ka tsofoffin riguna da su ka koɗe. Guzurin wainarsu kuma duk sun bushe sun yi fumfuna.
\s5
\v 6 Su ka tafi wurin Yoshuwa a sansanin Gilgal, su ka ce masa da shi da mutanen Isra'ila, "Mun taho da ga ƙasa mai nisa, saboda haka sai ku yi alƙawari da mu."
\v 7 mutanen Isra'ila su ka cewa Hiviyawa, "Watakila ku na zaune kusa da mu. Ƙaƙa za mu yi alƙawari da ku?"
\v 8 Su ka cewa Yoshuwa, "Mu bayinka ne," Yoshuwa ya ce masu, "Ku su wanene? Daga ina ku ka fito?"
\s5
\v 9 Su ka ce masa, "Barorinka sun zo daga ƙasa mai nisa, sabili da sunan Yahweh Allahnka. Mun ji rahoto a kan sa da kuma dukkan abubuwan da ya yi a Masar -
\v 10 da dukkan abubuwan nan da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa da ke hayin Yodan - Sihon sarkin Hesbon da kuma Og sarkin Bashan da ke Astarot.
\s5
\v 11 Dattawanmu da dukkan mazaunan ƙasarmu su ka ce mana, 'Ku ɗauki guzuri a hannuwanku saboda tafiyarku. Ku je ku same su ku ce masu, "Mu bayinku ne. Ku yi yarjejeniya da mu."
\v 12 Waɗannan gurasunmu ne, da ɗumi mu ka ɗauko su daga gida ranar da mu ka fito tafiya gunku. Amma yanzu, ku duba, sun bushe sun kuma yi funfuna.
\v 13 Wannan salkunan ruwan inabi sabbi ne da muka cika su, amma ku duba, yanzu suna ɗiga. Rigunanmu da takalmanmu sun koɗe saboda nisan tafiya."'
\s5
\v 14 Sai Isra'ilawa su ka karɓi waɗansu guzurinsu, amma ba su biɗi shawara ba da ga Yahweh domin ya bishe su.
\v 15 Yoshuwa ya dai - daita da su ya kuma yi alƙawari da su, a barsu su rayu. Shugabannin mutanen kuma su ka yi masu alƙawari.
\s5
\v 16 Bayan kwana uku da Isra'ilawa su ka yi alƙawari da su, sai su ka ji ai makwabtansu ne kuma su na zaune kurkusa.
\v 17 Sai mutanen Israa'ila su ka tashi su ka isa biranensu a kan rana ta uku. Biranensu kenan Gibiya, Kefira, Birot, da Kiriyet - Yarim.
\s5
\v 18 Mutanen Isra'ila ba su kai masu hari ba saboda shugabanninsu sun rantse masu a gaban Yahweh, Allah na Isra'ila. Isra'ilawa dukka su ka yi ta gunaguni găba da shugabanninsu.
\v 19 Amma dukkan shugabanni su ka cewa mutane dukka, "Mun rigaya mun rantse masu da Yahweh Allah na Isra'ila, yanzu fa ba za mu cuce su ba.
\s5
\v 20 Ga abin da za mu yi masu: Domin mu guji duk wani fushi da zai afko mana sabili da rantsuwa da mu ka yi masu, za mu bar su su rayu.
\v 21 Shugabanni su ka cewa mutanensu, "Mu bar su su rayu." Sabili da haka, Gibiyaniyawa su ka zama masu sarar itace da masu jan ruwa domin dukkan Israa'ilawa, kamar yadda shugabanni su ka umarta game da su.
\s5
\v 22 Yoshuwa ya kira su ya ce, "Me ya sa ku ka ruɗemu ku ka ce, 'Muna nesa da ku', alhali kuwa ku na nan cikinmu?
\v 23 Yanzu fa, sabili da wannan, la'anannu ne ku waɗansunku za su zama bayi ko yaushe, masu saro itace da masu jan ruwa domin gidan Allahnmu."
\s5
\v 24 Su ka amsa wa Yoshuwa su ka ce, "Sabili da an faɗa wa bayinka cewa, Yahweh Allahnku ya umarci bawansa Musa ya ba ku dukkan ƙasar, ya kuma karkashe dukkan mazaunan ƙasar a gabanku - shi ne mu ka ji tsoronku saboda ranmu. Shi ya sa mu ka yi wannan abu.
\v 25 Yanzu dai, ku duba, muna ƙalƙashin ikonku. Duk iyakar abin da ku ka ga ya dace kuma dai -dai ne ku yi da mu, sai ku aiwatar."
\s5
\v 26 Sai Yoshuwa ya yi masu haka: ya fitar da su da ga ƙarƙashin mallakar mutanen Isra'ila. Isra'ilawa kuwa ba su kashe su ba.
\v 27 A ranar Yoshuwa ya maida Gibiyanawa masu sarar itace da masu jawo ruwa domin mutanen Isra'ila, da na bagadin Yahweh, har wa yau, duk inda Yahweh ya zaɓa.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Yanzu da Adonizedek, sarkin Yerusalem, ya ji yadda Yoshuwa ya kama Ai kuma har ya hallakar da ita baki ɗaya (kamar yadda ya yi da Yeriko da kuma sarkinta) ya kuma ji yadda mutanen Gibeyon suka ƙulla alkawarin zaman lafiya da Isra'ila har ma suna acikinsu.
\v 2 Mutanen Yerusalem sun tsorata ƙwarai gama Gibeyon babban birnin ainin, kamar ɗaya daga cikin manyan sarakunan biranen. Har ma ta fi Ai ga shi kuma dukkan mayaƙan mazaje ne ƙarfafa.
\s5
\v 3 Saboda haka Adonizedek, sarkin Yerusalem, ya aika da saƙo ga Hoham, sarkin Hebron, ga Piram, sarkinYarmut, da Yafiya sarkin Lakish, da kuma Debir sarkin Eglon:
\v 4 "Ku zo nan wurina ku taimake ni. Bari mu je mu yaƙi Gibeyon gama sun ƙulla alkawarin salama tare da Joshuwa da kuma mutanen Isra'ila."
\s5
\v 5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarkin Yerusalem da sarkin Hebron da sarkin Yarmut da sarkin Lakish, da sarkin Eglon sun zo, dukkansu kuma da abokan gãbarsu. Sun kafawa Gibeyon sansani domin su yaƙe ta.
\s5
\v 6 Mutanen Gibeyon sun aika da saƙo ga Yoshuwa da kuma sojojin Gilgal. Sun ce, "Zo da sauri! Kada ka janye hanuwanka daga bayinka. Zo wurinmu da sauri ka ce-ce mu. Taimaka mana, domin dukkan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu."
\v 7 Joshuwa ya tafi daga Gilgal, shi da dukkan mutanen yaƙinsa, tare da dukkan jarumawa.
\s5
\v 8 Yahweh kuma ya ce da Yoshuwa, "Kada ka ji tsoronsu. Na riga na ba da su a hannunka. Babu wani daga cikinsu da zai hana ka yaƙe su."
\s5
\v 9 Yoshuwa ya tafi nan da nan ya auka masu, bayan ya yi tattaki dukkan dare daga Gilgal.
\v 10 Yahweh kuwa ya rikita abokan gãbar Isra'ila, Isra'ilawa kuwa su ka kashe su da yawa a Gibeyon su ka bi su ta hanyar haurawa zuwa Ber-horon, a nan masu ka yi ta karkashe su a hanyar Azeka da Makkeda.
\s5
\v 11 A sa'ad da suke gudu daga Isra'ilawa, a gangarar hawan Bet-horon, Yahweh ya jefe su da manyan duwatsu daga sama a kansu dukka hanyar zuwa Azeka, sun kuma mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi yawan mutanen Isra'ila su ka kashe da takobi.
\s5
\v 12 Sai Yoshuwa ya yi magana da Yahweh a ranar da Yahweh ya ba mutanen Israila nasara a kan Amoriyawa. Wannan shi ne abin da Yoshuwa ya ce da Yahweh a gaban Isra'ila, "Rana, ki tsaya a Gibeyon, wata kuma, a kwarin Ayalon."
\s5
\v 13 Rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya ba ya motsi har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gãbarsu. Wannan ba shi ne ke rubuce a Littafin Yashar ba? Rana ta tsaya a tsakar sararin sama; ba ta faɗi ba dukkan yini.
\v 14 Ba a taba yin yini kamar wannan ba ko kuma makamancinsa ba, da Yahweh ya saurari muryar mutum. Domin Yahweh ya yi yaƙi a madadin Isra'ila.
\s5
\v 15 Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila sun koma zango a Gilgal.
\v 16 Yanzu waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu suka ɓuya a cikin kogon Makkeda.
\v 17 Sai aka faɗawa Yoshuwa, "An same su-sarakuna biyar suna ɓoye a kogon Makkeda."
\s5
\v 18 Yoshuwa ya ce, "Murgina manyan duwatsu a kan bakin kógon a kuma sa sojoji a wurin don su tsaresu.
\v 19 Amma kada ku tsaya. Sai ku runtumi abokan ǧabanku ku kuma faɗa masu daga baya. Kada ku bar su su shiga biranensu, gama Yahweh Allahnku ya rigaya ya ba da su a hannunku."
\s5
\v 20 Yoshuwa da 'ya'yan Isra'ila sun gama karkashe su kisa mai yawa ƙwarai, har sai da aka kusan halaka su dukka; sai sauran kaɗan ne ba a kashe ba; sauran da su ka ragu suka shige birane masu garu.
\v 21 Sa'annan dukkan sojojin sun koma da salama wurin Joshuwa a sansani a Makkeda. Ba kuma mutumin da ya faɗi wata kalmar ǧaba da ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 22 Sai Yoshuwa ya ce, "Ku buɗe bakin kógon kuma daga cikin kogon ku ba ni waɗannan sarakuna biyar."
\v 23 Sun aikata kamar yadda ya ce. Sun kawo masa waɗannan sarakuna biyar daga kógon--sarkin Yerusalem, sarkin Hebron, sarkin Yarmut, sarkin Lakish, da kuma sarkin Eglon.
\s5
\v 24 Da su ka kawo sarakunan a wurin Yoshuwa, ya ƙirawo kowanne mutum da ke Isra'ila. Ya cewa shugabanin mayaƙa waɗanda su ka tafi tare da shi, "Ku sa ƙafafunwanku a wuyansu."Su kuwa sun zo sun taka wuyansu da ƙafafuwansu.
\v 25 Sai ya ce da su, "Kada ku ji tsoro ko kuwa ku razana. Ku yi ƙarfin hali. Wannan shi ne abin da Yahweh zai yi da dukkan abokan gãbarku waɗanda za ku yi yaƙi da su.
\s5
\v 26 Sai Yoshuwa ya kai masu hari har ya kashe sarakunan. Ya kuma rataye su a kan itatuwa biyar. An rataye su a kan itatuwa har yamma.
\v 27 Amma sa'ad da rana take faɗuwa, Yoshuwa ya ba da umarni, sai aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan sai aka jefa su cikin kõgon da su ka ɓoye kansu. Sai su ka sa manyan duwatsu aka rufe baƙin kõgon. Waɗannan duwatsun suna nan har wannan rana.
\s5
\v 28 Ta wannan hanya, Yoshuwa ya kama Makkeda a ranar, ya kuma kashe kome a wurin da takobi, har ma da sarkin. Ya hallakar da su da dukkan wani abu mai rai a wurin. Bai ƙyale kowa da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
\s5
\v 29 Yoshuwa tare da dukkan Isra'ilawa sun zarce daga Makkeda zuwa Libna.
\v 30 Yahweh kuma ya ba su ita ta hannun Isra'ila -- tare da sarkinsu. Yoshuwa kuwa ya kashe kowanne abu da ke rayuwa a cikinta da takobi. Bai bar wani abu da zai rayu ba a cikinta. Ya yi wa sarkin kamar yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
\s5
\v 31 Sai Joshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka zarce daga Libna zuwa Lakish. Ya kewaye ta kuma ya auka mata da yaƙi.
\v 32 Yahweh ya ba da Lakish a hannun Isra'ila. Yoshuwa ya cinye ta a rana ta biyu. Ya kashe kowanne abu mai rayuwa da takobi wanda ke cikinta, kamar yadda ya yi da Libna.
\s5
\v 33 Sai Horam, sarkin Gezer, ya zo ya kawo wa Lakish taimako. Yoshuwa kuwa ya fãɗa masa shi da sojojinsa har babu wani abu mai rai da ya rage.
\s5
\v 34 Sai Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka zarce zuwa Lakish ta Eglon.
\v 35 Sun kewaye ta sun auka mata da yaƙi, a wannan rana su ka cinyeta da yaƙi. Sun buge ta da takobi sun kuma hallaka kowanne mutum da ke cikinta, kamar yadda Yoshuwa ya yi a Lakish.
\s5
\v 36 Sai Yoshuwa tare da dukkan Isra'ila su ka haura daga Eglon zuwa Hebron.
\v 37 Sun auka mata da yaƙi. Sun cinyeta suka kuma bugi kowanne mutum da ke cikinta da takobi, har ma da sarkin da kuma dukkan ƙauyukan da ke kewaye da ita, sun karkashe komai da ke rayuwa a cikinta, ba su ƙyale wani abu da zai rayu ba, kamar yadda Yoshuwa ya yi wa Eglon. Ya hallaka komai da kowanne abu mai raI a cikinta.
\s5
\v 38 Sai Yoshuwa ya juya, tare da dukkan sojojin Isra'ila da ke tare da shi, sun kuma wuce zuwa Debir sun kuma auka mata da yaƙi.
\v 39 Ya kame ta tare da sarkinta, da dukkan ƙauyukan da ke kewaye da ita. Sun buge su da takobi har sun kashe dukkan abun da ke rayuwa a cikinta. Yoshuwa bai bar masu rayuwa ba, kamar yadda ya yi a Hebron da sarkinta, da kuma kamar yadda ya yi a Libna da sarkinta.
\s5
\v 40 Yoshuwa ya ci nasara da dukkan ƙasar, da tuddan ƙasar, da Negeb, da filayen kwarurruka, da kuma gangare. Da dukkan sarakunansu babu wanda ya tsira. Ya karkashe su babu wani abu mai rai, kamar yadda Yahweh, Allah na Isra'ila, ya ummarta.
\v 41 Yoshuwa kuwa ya kai masu hari da takobi tun daga Kadesh Barneya har zuwa Gaza, da dukkan ƙasar Goshen zuwa Gibeyon.
\s5
\v 42 Yoshuwa kuma ya cinye dukkan waɗannan sarakuna da kuma ƙasashensu a lokaci ɗaya domin Yahweh Allah na Isra'ila, ya yi yaƙin don Isra'ila.
\v 43 Sa'annan Yoshuwa, da dukkan Isra'ila tare da shi, sun koma zuwa zango a Gilgal.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Sa'ad da Yabin, sarkin Hazor, yaji wannan, ya aika da saƙo ga Yobab, sarkin Madon, zuwa ga sarkin Shimron, da sarkin Akshaf.
\v 2 Ya kuma aika da saƙon ga sarakuna waɗanda suke arewacin ƙasar tuddai, da ke cikin kudancin Kinneret, da ke cikin filayen kwari da kuma tuddai da ke cikin Dor a yamma.
\v 3 Ya kuma aika da saƙon zuwa ga Kanaaniya gabas da yamma da Amoriyawa da Hatiyawa da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa da suke cikin ƙasar tuddai, da kuma Hiwiyawa da ke Tsaunin Harmon a ƙasar Mizfa.
\s5
\v 4 Dukkan mayaƙansu su ka fito wurinsu, babbar rundunar sojoji mai yawa kamar yashin teku. Su na da yawan dawakai da karusai ƙwarai da gaske.
\v 5 Dukkan waɗannan sarakuna kuwa su ka shirya lokacin da za su haɗu, sun yi sansani a bakin ruwayen Merom don su yi yaƙi da Isra'ila.
\s5
\v 6 Yahweh ya cewa Yoshuwa, "Kada ka ji tsoron kasancewarsu, domin gobe war haka zan ba da su ga dukkan Isra'ila kamar matattun mutane. Za ku daddatse agaran dawakansu, za ku kuma ƙone karusansu"
\v 7 Yoshuwa da dukkan mayaƙansa za su ma-mayesu. Nan da nan suka zo ruwayen Meron, suka karkashe abokan ǧabarsu.
\s5
\v 8 Yahweh kuma ya ba da abokan gãbar a hannun Isra'ila, sun kuma hallaka su da takobi su ka runtume su har zuwa Sidon, Misrefot Ma'im, har zuwa gabashin ƙwarin Mizfa. Sun karkashe su har babu wani mai tsira da ya rage a cikinsu.
\v 9 Yoshuwa kuwa ya yi masu kamar yadda Yahweh ya faɗa masa. Ya daddatse agaran dawakansu ya kuma ƙone ƙarusansu.
\s5
\v 10 A wannan lokaci Yoshuwa ya juya da baya ya ci Hazor. Ya kashe sarkinta da takobi. (Hazor ita ce cibiyar dukkan waɗannan mulkokin.)
\v 11 Sun kashe dukkan abin da ke raye a wannan wurin da takobi, ya kuma hallakar da su kakaf, saboda haka babu wanda aka rage da rai a wurin. Ya kuma ƙone Hazor.
\s5
\v 12 Yoshuwa kuwa ya ci dukkan biranen sarakunan. Ya kuma ci dukkan sarakunansu da takobi. Ya hallakar da su kakaf kamar yadda Musa bawan Yahweh ya ummarta.
\v 13 Isra'ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da aka gina bisa tuddai ba, sai dai Hazor, ita kaɗai Yoshuwa ya ƙone.
\s5
\v 14 Sojojin Isra'ila kuwa su ka kwashe dukkan ganima daga waɗannan birane tare da shanu domin kansu. Sun kashe kowanne mutum da takobi har sai da dukkansu su ka mutu. Ba su bar wata hallita da ke da rai ba.
\v 15 Kamar yadda Yahweh ya ummarci bawansa Musa, ta hanyar da Musa ya ummarci Yoshuwa, haka nan Yoshuwa ya yi da ita. Bai bar kome ba da bai aikata ba cikin dukkan abin da Yahweh ya ummarci Musa ya yi.
\s5
\v 16 Yoshuwa ya ɗauke dukkan ƙasar, da ƙasar tuddai, da dukkan Negeb, da dukkan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Yodan Kogin kwari, da ƙasar tuddai ta Isra'ila, da filayen gangare.
\v 17 Daga Tsaunin Halak kusa da Idom, da wanda ya tafi zuwa arewa har zuwa wajen Ba'al Gad a kwari kusa da Lebanon a ƙarƙashin Tsaunin Hermon, ya kama dukkan sarakunansu ya kuma kashe su.
\s5
\v 18 Yoshuwa ya ɗauki dogon lokaci yana yaƙi da dukkan sarakunan.
\v 19 Ba bu wani birni da ya yi zaman salama da sojojin Isra'ila sai dai Hiwiyawa da su ke zaune a Gibiyon. Isra'ila kuwa ta ci dukkan sauran biranen da yaƙi.
\v 20 Domin Yahweh ne ya taurare zukatansu har da za su tasar ma Isra'ila da yaƙi, don a hallaka su a kuma shafe su ba tare da tausayi ba, kamar yadda aka ummarci Musa.
\s5
\v 21 A wannan lokaci kuwa Yoshuwa ya tafi ya kuma hallaka Anakawa. Ya kuma yi wannan a ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da kuma dukkan ƙasar tuddai ta Yahuda, da dukkan ƙasar tuddai ta Isra'ila. Yoshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu.
\v 22 Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar Isra'ila sai ko Gaza, da Gat, da kuma Ashdod.
\s5
\v 23 Ta haka Yoshuwa ya ci dukkan ƙasar, kamar yadda Yahweh ya faɗawa Musa. Yoshuwa kuwa ya ba da ita gãdo ga Israila bisa ga kabilar kowa, Sai ƙasar ta shaƙata daga yaƙe -yaƙe.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Yanzu waɗannan su ne sarakunan ƙasar, wadda mutanen Isra'ila su ka cinye da yaƙi. Isra'ilawa sun mallaki ƙasar a gabashin Yodan inda rana ta ke fitowa daga Kwarin Kogin Arnon zuwa Tsaunin Harmon, da dukkan Arabah wajen gabas.
\v 2 Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower, wadda ta ke iyakar kwarin Arnon Gorge daga tsakiyar kwarin, har rabin Giliyad zuwa ga Kogin Yabbok iyakar Amoniyawa.
\s5
\v 3 Sihon kuma ya yi mulki a kan Arabah zuwa Tekun Kinneret, da zuwa gabashin Tekun Arabah (Tekun Gishiri) a wajen gabas, da dukkan hanyar Ber Yeshimot da wajen kudu, zuwa gangaren gindin Tsaunin Fisga.
\v 4 Og, sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayim, wanda ya zauna a Ashtarot da Edirai.
\v 5 Ya yi mulki a Tsaunin Hermon, Salika, da dukkan Bashan, har zuwa iyakar mutanen Geshur da kuma Ma'akatiyawa, da rabin Giliyad, zuwa kan iyakar Sihon, sarkin Heshbon.
\s5
\v 6 Musa bawan Yahweh, da mutanen Isra'ila sun yi nasara da su, kuma Musa bawan Yahweh ya ba su ƙasar gãdo ga Rubenawa, da Gadawa, da kuma rabin kabilar Manassa.
\s5
\v 7 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar waɗanda Yoshuwa da mutanen Isra'ila suka ci a yammacin Yodan, daga Ba'al Gad a ƙwari kusa da Lebanon zuwa Tsaunin Halak kusa da Idom. Yoshuwa ya ba da ƙasar ga kabilun Isra'ila don su ǧada.
\v 8 Ya ba da tuddan ƙasar, da kwaruruka, da Arabah, da gefan tuddai, da jejin da kuma Negeb - ƙasar Hitiyawa, Amoriyawa, Kan'aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa.
\s5
\v 9 Sarakunan sun haɗa da sarkin Yeriko da sarkin Ai da ke kusa da Betel,
\v 10 da sarkin Yerusalem da sarkin Enayim,
\v 11 da sarkin Yarmut da sarkin Lakish,
\v 12 da sarkin Eglon da sarkin Gezer,
\s5
\v 13 da sarkin Debir da sarkin Geder,
\v 14 da sarkin Horma da sarkin Arad,
\v 15 da sarkin Libna da sarkin Adullam,
\v 16 da sarkin Makkeda da sarkin Betel,
\s5
\v 17 da sarkin Taffuwa da sarkin Hefer,
\v 18 da sarkin Afek da sarkin Lasharon,
\v 19 da sarkin Madon da sarkin Hazor,
\v 20 da sarkin Shimron Meron da sarkin Akshaf,
\s5
\v 21 da sarkin Ta'anak da sarkin Megiddo,
\v 22 da sarkin Kedesh da sarkin Yokniyam a Karmel,
\v 23 da sarkin Dor a Nafat Dor da sarkin Goyim a Gilgal,
\v 24 da kuma sarkin Tirza. Yawan sarakunan kuwa talatin da ɗaya ne dukkansu.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Yanzu Yoshuwa ya tsufa ƙwarai sai Yahweh ya ce da shi, "Ka tsufa ƙwarai, amma har yanzu akwai sauran ƙasar da yawa da ba a mallaka ba.
\s5
\v 2 Wannan ita ce ƙasar da ta rage: a dukkan sashin Filistiyawa, da dukkan waɗanda ke Geshuriyawa,
\v 3 (daga Shihor, wanda ke gabas da Masar da wajen arewanci iyakar Ekron, wanda ake ɗauka ta Kan'aniyawa ce, da sarakuna biyar na Filistiyawa, da su ke Gaza, Ashdod, Ashkelon, Gat da Ekron - da ƙasar Aviyawa).
\s5
\v 4 A kudu (da ƙasar Aviyawa); akwai sauran ƙasashen Kan'aniyawa, da Ara wanda ta ke ta Sidoniyawa, zuwa Afek har kuma iyakar Amoriyawa;
\v 5 da ƙasar Gebaliyawa, dukkan Lebanon wajen fitowar rana, zuwa Ba'al Gad ƙasar Tsaunin Hermon zuwa Lebo Hamat.
\s5
\v 6 Kuma da dukkan mazaunan ƙasar tuddai daga Lebanon har zuwa can Misrefot Mayim, da dukkan mutanen Sidon. Zan kore su a gaban sojojin Isra'ila. Ka tabbatar ka raba ƙasar ga Isra'ila a matsayin gãdonsu, kamar yadda na ummarce ka.
\v 7 Raba wannan ƙasar a matsayin gãdo ga kabilu tara, da kuma ga rabin kabilar Manasse.
\s5
\v 8 Tare da sauran rabin kabilar Manasse, da Rubenawa da kuma mutanen Gad sun karɓi nasu gãdon wanda Musa ya ba su a wajen gabas da Yodan,
\v 9 daga Arowa wadda take a gefen kwarin Kogin Arnon (ya hada da birnin da ke tsakiyar kwarin), da dukkan ƙasar tudu ta Medeba har zuwa Dibon;
\s5
\v 10 dukkan biranen Sihon da sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, zuwa ga iyakar Amoniyawa;
\v 11 Giliyad, da kuma yankin Geshuriyawa da Makatiyawa da dukkan na Tsaunin Harmon da dukkan Bashan zuwa Saleka;
\v 12 da dukkan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarauta a Ashtarot da Edirai - waɗannan su ne ragowar mutanen Refayim - Musa ya buge su ya kuma kore su.
\s5
\v 13 Amma duk da haka mutanen Israila ba su kori Geshuriyawa ko Makatiyawa ba. Maimakon haka, Geshuriyawa da Makatiyawa sun zauna a cikin Isra'ila har wa yau.
\s5
\v 14 Ga kabilar Lebi ne kaɗai Musa bai ba da ta gado ba. Hadayu na Yahweh, Allah na Isra'ila, wanda aka yi da wuta, ǧadonsu, kamar yadda Allah ya faɗawa Musa.
\s5
\v 15 Musa ya riga ya ba kabilar Ruben nasu ǧadon bisa ga iyali-iyali.
\v 16 Nasu yankin ƙasar daga Arowa, a gefen ƙwarin Kogin Arnon, da kuma birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukkan tuddai kusa da Medeba.
\s5
\v 17 Ruben kuma ya sami Heshbon da dukkan biranenta da suke kan tudu, Dibon, da Bamot Ba-al, da Bet Ba'al Miyon,
\v 18 da Yahaz, da Kedemot, da Mefa'at,
\v 19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret Shahar da ta ke bisa tudun da yake cikin kwarin.
\s5
\v 20 Ruben kuma ya karɓi Bet Feyor, da gangaren Fisga, da Bet Yeshimot,
\v 21 da dukkan biranen kan tudu, da dukkan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya sarauci Heshbon, wanda Musa ya ci shi da yaƙi tare da shugabanin Midiyawa, Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba, sarakunan Sihon, wanda ya zauna a ƙasar.
\s5
\v 22 Mutanen Isra'ila kuma su ka kashe shi da takobi, Balaam ɗan Beyor, matsubbaci, daga cikin sauran waɗanda da su kashe.
\v 23 A iyakar kabilar Ruben akwai Kogin Yodan, wannan shi ne iyakarsu. Wannan shi ne ǧadon kabilar Ruben, da aka ba kowanensu na iyalinsu, tare da biranensu da ƙauyukansu.
\s5
\v 24 Wannan shi ne abin da Musa ya ba kabilar Gad, bisa ga iyalinsu:
\v 25 Yankin ƙasarsu shi ne Yaza, da dukkan biranen Giliyad da rabin ƙasar Ammoniyawa, zuwa Arowa, wadda ke gabas da Rabbah,
\v 26 daga Heshbon zuwa Ramat Mizfa da Betonim, daga Mahanayim zuwa iyakar Debir.
\s5
\v 27 A kwarin, Musa ya ba su Bet Haram, Bet Nimrah, Sukkot da Zafon da sauran ragowar mulkin Sihon sarkin Heshbon, tare da Yodan ne iyaka, zuwa iyakar Tekun Kinneret a gabashin hayin Yodan.
\v 28 Wannan shi ne gãdon kabilar Gad bisa ga iyalinsu, tare da biranensu da ƙauyukansu.
\s5
\v 29 Musa ya ba da gãdo ga rabin kabilar Manasse. An ba da ita ga rabin kabilar mutanen Manasse, bisa ga iyalinsu.
\v 30 Yankin ƙasarsu daga Mahanayim, da dukkan Bashan da dukkan sarautar Og sarkin Bashan da dukkan garuruwan Yayir da waɗanda su ke a Bashan, birane sittin ne;
\v 31 rabin Giliyad, da Ashtarot da Edirai (biranen masarautar Og a Bashan). Waɗannan ne aka ba da su ga iyalin Makir ɗan Manasse - rabin mutanen Makir, an ba kowanne iyali.
\s5
\v 32 Wannan shi ne gãdon da Musa ya ba su a kan filayen Mowab, a hayin gabashin Yodan na Yeriko.
\v 33 Musa bai ba kabilar Lebi gãdo ba. Yahweh, Allah na Isra'ila, shi ne gãdonsu, kamar yadda ya faɗa masu.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Waɗannan su ne yankunan ƙasar da mutanen Isra'ila suka karɓa matsayin gãdo a ƙasar Kan'ana, wanda Eliyeza firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma iyalin shugabainin kabilun kakaninsu na mutanen Isra'ila.
\s5
\v 2 Gãdonsu ya sa mu ne ta hanyar jefa kuri'a don kabilun nan tara da rabi, kamar yadda Yahweh ya ummarta ta hannun Musa.
\v 3 Domin Musa ya riga ya ba da gãdon ga kabilu biyu da rabi can hayin Yodan, amma ga Lebiyawa bai ba su gãdo ba.
\v 4 Kabila Yosef kuma kabilu biyu ne, Manasse da Ifaim. Lebiyawa kuwa ba a ba su wani yanki na ƙasar gãdo ba, sai dai an ba su birane da za su zauna, tare da filayen da za su yi kiwon garkensu da kuma kayan da su ke bukata.
\v 5 Mutanen Isra'ila kuwa su ka yi kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa, sun rarraba ƙasar.
\s5
\v 6 Sai kabilar Yahuda suka je wurin Yoshuwa a Gilgal. Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, "Ka san abin da Yahweh ya ce da Musa mutumin Allah a kanka da ni a Kadesh Barneya.
\v 7 Ina da shekaru arba'in sa'ad da Musa bawan Yahweh ya aike ni daga Kadesh Barneya in leƙo asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda ya ke a zuciyata.
\s5
\v 8 Amma 'yan'uwana da mu ka tafi tare sun karyar da zukatan mutanen da tsoro. Amma ni da na bi Yahweh Allahna.
\v 9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana, cewa, 'Hakika a ƙasar nan wanda ƙafafunka su ka ta ka za ta zama gãdonka da kai da 'ya'yanka har abada, domin ka bi Yahweh Allahnka sosai.'
\s5
\v 10 Yanzu, duba! Yahweh ya kiyaye ni da rai waɗannan shekaru arba'in da biyar, kamar yadda ya faɗa-daga lokacin da Yahweh ya faɗi wannan magana ga Musa, sa'ad da Isra'ila suke tafiya a jeji. Yanzu, duba! ina mai shekaru tamanin da biyar da haihuwa.
\v 11 Har wannan rana ina nan kamar ranar da Musa ya aike ni waje. ƙarfina yanzu yana nan kamar ƙarfin dă domin yaƙi da kuma zuwa da kowowa.
\s5
\v 12 Saboda haka yanzu ka ba ni ƙasar tuddai, wadda Yahweh ya yi mani alkawari a waccan rana. Gama ka ji a wannan rana yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu. Watakila Yahweh zai kasance tare da ni, ni kuma in kore su, kamar yadda Yahweh ya faɗa."
\s5
\v 13 Sai Yoshuwa ya sa masa albarka ya kuma ba da Hebron a matsayin gãdo ga Kalibu ɗan Yefunne.
\v 14 Saboda haka Hebron ta zama gãdon Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze har zuwa wannan rana, domin ya bi Yahweh, Allah na Israila sosai.
\v 15 Yanzu sunan Hebron kamar da Kiriyat Arba ne. (Arba kuwa ya zama babbban mutum ne cikin gwarzayen.) Ƙasar kuwa ta huta daga yaƙi.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Rabon ƙasar da aka yi wa kabilar mutanen Yahuda, an ba su ne bisa ga iyalansu, ya kai kudu iyaka da Idom, zuwa jejin Zin wanda ta ke can kudu nesa.
\v 2 Iyakarsu wajen kudu ta mike tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga sashen gaɓar da ta fuskanci kudu.
\s5
\v 3 Iyakarsu ta tafi har kudancin tuddan Akrabbim ta kuma zarce zuwa Zin, ta kuma tafi har zuwa kudancin Kadesh Barneya, ta wajen Hezron, har kuma zuwa Addar, ta kuwa karkata zuwa Karka.
\v 4 Ta wuce zuwa Azmon, ta bi ta rafin Masar, kuma ta zo ƙarshe a teku. Wannan ita ce iyakarsu a kudu.
\s5
\v 5 Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri, har zuwa bakin Yodan. Iyakar arewa kuma ta miƙe daga teku zuwa bakin Yodan.
\v 6 Ta tafi zuwa Bet Hogla ta kuma wuce zuwa arewa da Bet Arabah. Sai ta haura zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.
\s5
\v 7 Iyakar da ta tafi Debir zuwa Kwarin Achor, da kuma arewacin, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal, wadda ta ke daura da tuddun Adummim, wanda ke kudu da gefen kwari. Sai ta zarce zuwa ruwan En Shemesh ta kuma tafi En Rogel.
\v 8 Sai iyakar ta bi ta Kwarin Ben Hinnom a wajen kudancin birnin Yebusawa (wato Yerusalem). Sa'an nan ta bi ta sashen tuddun da ke shimfiɗe daura da kwarin Hinnom, wajen yamma, a arewacin ƙarshen Kwarin Refayim.
\s5
\v 9 Sa'an nan iyakar ta faɗaɗa daga bisan tuddai zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, har zuwa can biranen Tsaunin Efron. Sai iyakar ta karkata zuwa Ba'ala (wato Kiriyat Yeyarim).
\v 10 Sa'an nan iyakar ta kewaye yammacin Ba'ala zuwa Tsaunin Seyir, daga nan kuma ta zarce gefen Tsaunin Yeyarim a arewa (wato Kesalon), sai ta gangara zuwa Bet Shemesh, ta kuma ƙetare har can zuwa Timna.
\s5
\v 11 Iyakar kuwa ta bi ta gefen arewacin tuddun Ekron, sa'an nan ta karkata kewayin Shikkeron ta kuma wuce zuwa Tsaunin Ba'ala, daga wurin ta tafi zuwa Yabneyel. Iyakar ta ƙare a teku.
\v 12 Yammacin iyakar Babbar Tekun da kuma gaɓarta. Wannan iyakar na kewaye da kabilar Yahuda, bisa ga iyalin kowa.
\s5
\v 13 Don kiyaye ummarnin Yahweh ga Yoshuwa, Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne rabonsa na ƙasar a tsakiyar kabilar Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron (Arba shi ne uban Anak).
\v 14 Kaleb kuwa ya kori mazan 'ya'yansa uku daga wurin Anak: Sheshai, Ahiman da Talmai, zuriyar Anak.
\v 15 Ya tafi daga wurin ta wurin rashin amincewar mazaunan Debir (Debir da dã ake Kiriyat Sefer).
\s5
\v 16 Kaleb yace, "Duk mutumin da ya kai hari ga Kiriyat Sefer har kuma ya kama ta, zan ba shi 'yata Aksa a matsayin mata."
\v 17 Da Otniyel ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kaleb, ya ci ta, Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa matsayin matarsa.
\s5
\v 18 Bayan wannan, Aksa ta zo ga Otniyel ta kuma iza shi ya roƙi babanta fili. Da ta sauka daga kan jakinta, Kaleb ya ce mata, "Me kike bukata?"
\s5
\v 19 Aksa ta amsa, "Ka yi mani alheri na musamman, da yake ka ba ni ƙasa a Negeb: ka kuma ba ni maɓuɓɓugar ruwa."Kaleb kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddu da kuma maɓuɓɓugar kwari.
\s5
\v 20 Wannan shi ne gãdon kabilar Yahuda, da aka ba iyalinsu
\s5
\v 21 Biranen na kabilar Yahuda da ke can kudu sosai, suna wajen iyakar Idom, su ne Kabzeyel, Eder, Yagur,
\v 22 Kina, Dimona, Adada,
\v 23 Kedesh, Hazor, Yitnan,
\v 24 Zif, Telem, Beyalot.
\s5
\v 25 Hazor Hadatta, Kiriyot Hezron (wato an san shi da Hazor),
\v 26 Amam, Shema, Molada,
\v 27 Hazar Gadda, Heshmon, Bet Felet,
\v 28 Hazar Shuwal, Biyasheba, Biziyotiya.
\s5
\v 29 Ba'ala, Iyim, Ezem,
\v 30 Eltolad, Kesil, Horma,
\v 31 Ziklag, Madmanna, Sansanna,
\v 32 Labayot, Shilhim, Ayin, Rimmon. Wadannan su ne birane ashirin da tara dukkansu, har da ƙauyukansu.
\s5
\v 33 A kwarin ƙasar tuddu ta yamma, akwai su Eshtawol, Zora, Ashna,
\v 34 Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam,
\v 35 Yamut, Adullam, Soko, Azeka
\v 36 Shayarim, Aditayim, Gedera, (wato Gederotayim). Waɗannan su ne birane goma sha huɗu yawansu duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 37 Zenan, Hadasha, Migdalgad,
\v 38 Diliyan, Mizfa, Yokteyel,
\v 39 Lakish, Bozkat, Eglon.
\s5
\v 40 Kabbon, Lahmas; Kitlish,
\v 41 Gederot, Bet Dagon, Na'ama, Makkeda. Waɗannan su ne birane goma sha shida yawansu duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 42 Libna, Eter, Ashan,
\v 43 Yifta, Ashna, Nezib,
\v 44 Kaila, Akzib, Maresha. Waɗannan su ne birane tara, duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 45 Ekron, tare da kewayan garuruwa da ƙauyuka;
\v 46 daga Ekron zuwa Babbar Teku, dukkan mazaune waɗanda su ke kusa da Ashdod, da dukkan ƙauyukanta.
\v 47 Ashdod, da kewayan garuruwa da ƙauyukanta; Gaza, da kewayan garuruwa da ƙauyukanta; zuwa rafin Masar, da kuma zuwa Babbar Teku tare da gaɓarta.
\s5
\v 48 A tuddun ƙasar, Shamir, Yattir, Soko,
\v 49 Danna, Kiriyat Sanna (wato Debir),
\v 50 Anab, Eshtimo, Anim,
\v 51 Goshen, Holon, da Gilo. Waɗannan su ne birane goma sha daya, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 52 Arab, Duma, Eshan,
\v 53 Yanim, Bet Taffuwa, Afeka,
\v 54 Humta, Kiriyat Arba (wato Hebron), da Ziyor. Waɗannan su ne birane tara, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 55 Mawon, Karmel, Zif, Yutta,
\v 56 Yezriyel, Yokdiyam, Zanowa,
\v 57 Kayin, Gibiya, da kuma Timna, Waɗannan su ne birane goma, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 58 Halhul, Bet Zur, Gedor,
\v 59 Ma'arat, Bet Anot, da kuma Eltekon. Waɗannan su ne birane shida, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 60 Kiriyat Ba'al (wato Kiriyat Yeyarim), da kuma Rabba. Waɗannan su ne birane biyu, tare da ƙauyukansu.
\v 61 A cikin jeji kuwa, akwai su Bet Arabah, Middin, Sekaka,
\v 62 Nibshan, da Birnin Gishiri, da En Gedi. Waɗannan su ne birane shida, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 63 Amma domin Yebusiyawa, mazaunan Yerusalem, kabilar Yahuda ba su iya korar su ba, don haka Yebusiyawa su ka yi zamansu tare da kabilar Yahuda har zuwa wannan ranar.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Ƙasar da aka ba kabilar Yosef ta kama tun daga Yodan har zuwa Yeriko, gabas da ruwan Yeriko, zuwa daji, ta haura daga Yeriko zuwa ƙasar tuddun Betel.
\v 2 Sai ta tafi zuwa Betel ta Luz ta kuma zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.
\s5
\v 3 Sai ta gangara yammacin karkarar Yafletiyawa, har can ƙarƙashin karkarar Bet Horon, ta kuma tafi har Gezer; ta ƙare a teku.
\v 4 Ta wannan hanyar ce kabilun Yosef, da Manasse da kuma Ifraim su ka sami na su gãdon.
\s5
\v 5 Karkarar kabilar Ifraim wadda aka ba iyalinsu ta kama kamar haka: iyakar gãdonsu a wajen gabas ta tafi zuwa Atarot Addar har can kwarin Bet Horon,
\v 6 daga can ta cigaba har teku. Daga Mikmetat a arewa ta juya zuwa gabashin Ta'anat Shilo, ta kuma wuce gaba wajen gabas da Yanowa.
\v 7 Sai ta tafi can har Yanowa zuwa Atarot ta kuma tafi Na'ara, ta kuma kai Yeriko, ƙarshen Yodan.
\s5
\v 8 Daga Taffuwa iyakarta ta tafi yammacin rafin Kana ta kuma ƙare a teku. Wannan shi ne gãdon kabilar Ifraim, wadda aka ba iyalinsu,
\v 9 tare da biranen da aka zaɓa don kabilar Ifraim a cikin gãdon kabilar Manasse - dukkan biranen, tare da ƙauyukansu.
\s5
\v 10 Su ba su ƙore Kan'aniyawa waɗanda su ke zama a Gezer ba, saboda haka Kan'aniyawan da ke zama cikin Ifraim su na nan har wannan rana, amma waɗannan mutanen an sa su yin aikin dole.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Wannan it ce ƙasar da aka ba kabilar Manasse (wanda ya ke shi ne ɗan farin Yosef) - wato, Makir wanda ya ke ɗan farin Manasse shi ma kuma uban Giliyad. Zuriyar Makir an ba su ƙasar Giliyad da Bashan, domin Makir mutum ne jarumi a gun yaƙi.
\v 2 Ƙasar an ba da ita ga sauran kabilar Manassa, an ba da ita ga iyalinsu -- Abiyeza, Helek, Asriyel, Shekem, Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne zuriyar maza na Manasse ɗan Yosef, bisa ga iyalinsu.
\s5
\v 3 Yanzu Zelofehad ɗan Hefer ɗan Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse ba shi da 'ya'ya maza, amma sai 'ya'ya mata kaɗai. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, Noah, Hogla, Milka, da Tirza.
\v 4 Sun zo wurin Eliyeza firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabanin, sun kuma ce, "Yahweh ya umarci Musa da ya ba mu gãdo tare da 'yanuwanmu maza." Saboda, bin umarnin Yahweh, ya ba waɗannan matan gãdo a cikin 'yan'uwansu maza na mahaifinsu.
\s5
\v 5 Yanki goma na ƙasar da aka ba Manasse a Giliyad da Bashan, wanda ya na ɗaya gefen Yodan,
\v 6 domin 'ya'ya mata na Manasse sun karɓi gãdonsu tare da 'ya'yansa maza. Ƙasar Giliyed an ba sauran kabilar Manasse.
\s5
\v 7 Yankin ƙasar Manasse ya kai daga Ashar zuwa Mikmetat, wadda ta ke gabas da Shekem. Sai kuma iyakarta ta tafi kudu zuwa waɗanda su ke zama kusa da ruwan Taffuwa.
\v 8 (Ƙasar Taffuwa ta ƙarƙashin Manasse, amma garin Taffuwa ya na kan iyakar Manassa ƙarƙashin kabilar Ifraim.)
\s5
\v 9 Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan biranen kudu da rafin da ke cikin garuruwan Manasse su na ƙarƙashin Ifraim. Iyakar Manasse kuwa tana arewacin rafin, ta kuma ƙarashe a teku.
\v 10 Ƙasar da ke kudu ta na ƙarƙashin Ifraim, kuma ƙasar da ke arewa ta Manasse ce; kuma teku ce ƙarshen iyakarta. A arewacin gefenta kuwa Ashar za a tarar, a kuma gabashinta, Issaka.
\s5
\v 11 A cikin Issaka kuma da Ashar, Manasse ya sa mi Bet Shan da ƙauyukanta, Ibleyam da ƙauyukanta, mazaunan Dor da ƙauyukanta, mazaunan Endor da ƙauyukanta, mazaunanTa'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta, (da kuma sulusin birin Nafet).
\v 12 Duk da haka kabilar Manasse ba su iya mallakar waɗannan biranen ba, domin Kan'aniyawa sun ci gaba da zama a wannan ƙasar.
\s5
\v 13 Lokacin da mutanen Isra'ila su ka yi ƙarfi, sai su ka tilasta wa Kan'aniyawa su yi aikin dole, amma ba su kore su gaba ki ɗaya ba.
\s5
\v 14 Sai zuriyar Yosef su ka ce da Yoshuwa, "Me ya sa ka ba mu ƙasa ɗaya kaɗai da kuma kashin gãdo ɗaya, da ya ke mu mutane masu yawa ne, duk da albarkar da Yahweh ya yi mana?"
\v 15 Yoshuwa yace da su, "Idan ku babbar jama'a masu yawa ce, ku tafi can da kanku a jeji ku gyarawa kanku ƙasa acikin ƙasar Ferizziyawa da kuma Refayawa. Ku yi haka, a tuddan ƙasar Ifraim da ya ke ta yi ma ku kaɗan ainun.
\s5
\v 16 Sai zuriyar Yosef su ka ce, "Ƙasar tuddai ba za ta ishe mu ba. Amma dukkan Kan'aniyawa da su ke zaune a kwarin su na da karusai na ƙarafa, dukkan waɗanda zaune a Bet Shan da ƙauyukanta, da kuma waɗanda ke zaune a kwarin Yezriyel."
\v 17 Yoshuwa kuwa ya cewa gidan Yosef - wato Ifraim da Manasse, "Ku mutane ne masu girma da yawa, kuma ku na da iko da ƙarfi. Kada ku tsaya a kashin ƙasa ɗaya kaɗai da aka ba ku.
\v 18 Ƙasar tuddai ma za ta zama taku. Ko da yake daji ne, ku gyara ta ku kuma mallake ta har iyakokinta masu nisa. Sai ku kore Kan'aniyawa daga cikinta, ko da ya ke su na da karusai na ƙarfe, kuma su na da ƙarfi ainun."
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Sai dukkan taron jama'ar Isra'ila su ka taru a Shilo. A wurin su ka kafa rumfar taruwa sun ci nasara akan ƙasar dake gabansu.
\v 2 Har yanzu akwai kabilu bakwai cikin mutanen Isra'ila waɗanda ba a ba su na su gãdon ba tukuna.
\s5
\v 3 Yoshuwa ya ce da mutanen Isra'ila, "Har yaushe za ku ƙi tafiya cikin ƙasa wadda Yahweh, Allah na kakanninku ya ba ku?
\v 4 Ku sanya wa kanku mutum uku daga kowacce kabila, kuma zan aike su waje. Za su fita su duba ƙasar tudu da gangare. Za su rubuta bayanin ta bisa ga gădon kowannensu, sa'an nan za su komo wuri na.
\s5
\v 5 Za su raba ta kashi bakwai. Yahuda za su kasance cikin na su yanki wajen kudu, sai gidan Yosef kuma za su ci gaba da zama a yankin arewa.
\v 6 Za ku kasa ƙasar kashi bakwai sa'annan ku kawo taswirar ƙasar wurina. Zan jefa ma ku ƙuri'u a nan gaban Yahweh Allahn mu.
\s5
\v 7 Gama Lebiyawa ba su da gădo a cikin ku, gama aikin Lebiyanci na Yahweh shi ne rabon su. Gad, da Ruben da rabin ƙabilar Manasse sun karɓi gadon su a ƙetaren Yodan. Wannan shi ne gãdon da Musa bawan Yahweh ya ba su."
\s5
\v 8 Sai mutanen su ka tashi su ka tafi. Yoshuwa ya umarci waɗan da su ka tafi domin su rubuta tsarin taswirar ƙasar, ya ce, "Ku tafi ku kai ku komo cikin ƙasar ku rubuta adadinta sa'annan ku komo wurina. Zan jefa ƙuri'u a nan domin ku a gaban Yahweh a Shilo."
\v 9 Mutanen kuwa su ka tashi suka tafi cikin ƙasar tudu da gangare su ka rubuta bayanin yadda ƙasar take kashi bakwai bisa ga biranenta, sun tsara biranen da sashin sa. Daga nan suka dawo wurin Yoshuwa cikin sansani a Shilo.
\s5
\v 10 Sai Yoshuwa ya jefa masu ƙuri'u a Shilo gaban Yahweh. A can ne Yoshuwa ya rabawa mutanen Isra'ila ƙasar, kowannesu aka bashi nasa rabon ƙasar.
\s5
\v 11 Ƙasar da aka ba kabilar Benyamin kowanne an ba su bisa ga iyalinsu. Yankin ƙasarsu tana tsakanin zuriyar Yahuda da zuriyar Yosef.
\v 12 Ta ɓangaren arewa, iyakarsu ta fara daga Yodan. Iyakar ta hau wajen sashin arewacin Yeriko, daga nan ta hau zuwa wajen tudun ƙasar yamma. Can ta kai jejin Bet Aben.
\s5
\v 13 Daga can iyakar ta wuce zuwa kudu sashen Luz (wato Betel ke nan). Iyakar kuwa ta gangara zuwa Atarot Addar, tabi ta tsaunin da ke kwance a kudancin Bet Horon.
\v 14 Sai iyakar tabi ta wani sashi dabam: ta ɓangaren yamma ya juya wajen kudu, ta nufi wajen hayin dutse daga Bet Horon. Wannan iyakar ta ƙarasa a Kiriyet Baal (wato Kiriyet Yeyarim), birni wanda mallakar kabilar Yahuda ne. Wannan ta haɗa iyakar yammaci.
\s5
\v 15 Iyaka ta wajen kudu ta fara daga wajen Kiriyat Yeyarim. Iyakar ta tafi daga nan zuwa Efron, zuwa maɓulɓular ruwayen Neftowa.
\v 16 Sai iyakar ta gangaro ƙasa zuwa iyakar dutsen dake akasi da Kwarin Ben Hinom, wanda ke arewacin ƙarshen Kwarin Refayim. Daga nan ya gangara zuwa Kwarin Hinnom, kudancin gangaren Yebusiyawa ya nausa ƙasa zuwa En Rogel.
\s5
\v 17 Ta juya wajen arewa, ta nufi wajen En Shemesh, daga nan kuma ta fita zuwa Gelilot, wanda ke akasi da mahayin Adumim. Daga nan sai ya gangara zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.
\v 18 Ya wuce zuwa arewa inda suke kafaɗa da Bet Arabah ta gangara zuwa Arabah.
\s5
\v 19 Iyakar ta wuce arewa kafaɗa da Bet Hogla. Iyakar ta ƙarasa arewa wajen gaɓar Tekun Gishiri, ta ɓangaren kudu ta ƙare a Yodan. Iyaka ta kudu kenan.
\v 20 Yodan kuwa ta kafa iyakarta ta ɓangaren gabas. Wannan shi ne gadon Kabilar Benyamin, an kuma ba kowannensu bi sa ga zuriyar su, iyaka bayan iyaka, a ko'ina.
\s5
\v 21 Biranen kabilar Benyamin bisa ga iyalansu su ne; Yeriko, Bet Hogla, da Emek Keziz,
\v 22 Bet Arabah, Zemarayim, Betel,
\v 23 Abbim, Fara, Ofra,
\v 24 Kefar Ammoni, Ofni da Geba. Birane goma sha biyu ne haɗe da ƙauyukansu.
\s5
\v 25 Akwai kuma biranen Gibiyon, Ramah,
\v 26 Birot, Mizfa, Kefira, Mozah,
\v 27 Rekem, Irfil, Tarala,
\v 28 Zela, Hayelef, Yebus, (wato Yerusalem ke nan) Gibiya da Kiriyat. Akwai birane goma sha hudu, duk da ƙauyukan su. Wannan shi ne gãdon Benyamin domin zuriyarsu.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Kaɗa ƙuri'u na biyu ta faɗa kan Simiyon aka ba su bisa ga zuriyarsu. Gãdonsu ya na tsakiyar gãdon kabilar Yahuda.
\s5
\v 2 Su ka samu domin gãdonsu Biyasheba, Sheba, Modala,
\v 3 Hazar Shuwal, Balal, Ezem,
\v 4 Eltolad, Betul, da Hormah.
\s5
\v 5 Simiyon kuma ya na da Ziklag, Bet Markabot, Hazar Susa,
\v 6 Bet Lebayot, da Sharuhen, Waɗannan birane goma sha uku sun haɗa da ƙauyukansu.
\v 7 Har yanzu Simiyon ya na da Ayin, Rimmon, Etar da Ashan. Birane huɗu kenan duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 8 Waɗannan tare da ƙauyaukan dake tare da biranen har zuwa Ba'alat Biya (ɗaya suke da Ramah cikin Negeb). Wannan shi ne gãdon ƙabilar Simiyon, wanda aka ba iyalinsu.
\v 9 Daga cikin gãdon ƙabilar Simiyon aka sami wani sashin rabon kabilar Yahuda. Saboda rabon ƙasar da aka ba Yahuda ya yi masu yawa, ƙabilar Simiyon sun karɓi gădonsu daga cikin tsakiyar nasu rabo.
\s5
\v 10 Kaɗa ƙuri'u na uku ya faɗa akan kabilar Zebulun, aka kuma ba da ita ga zuriyarsu. Iyakar gãdonsu ta fara daga Sarid.
\v 11 Iyakar su ta hau wajen yammaci ta nufi Marala, ta kai Dabbeshet; ta malala zuwa rafin dake akasi da Yokneyam.
\s5
\v 12 Daga Sarid iyakar ta karkato zuwa gabashi ta tafi zuwa iyakar Kislot Tabor. Daga nan ta fita zuwa Daberat ta hau zuwa Yafiya.
\v 13 Daga can ta ratsa zuwa gabas har Gat Hefa, zuwa Et Kazin; ta sake fita zuwa Rimmon ta juya zuwa wajen Neya.
\s5
\v 14 Iyakar ta karkato zuwa wajen arewa zuwa Hannaton ta ƙarasa a Kwarin Ifta El.
\v 15 Wannan yankin ya hada da biranen Kattat, Nahalal, Shimron, Idala da Betlehem. Akwai birane goma sha biyu duk da ƙauyukansu.
\v 16 Wannan shi ne gãdon ƙabilar Zebulun, wanda aka ba zuriyarsu - da birane duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 17 Kaɗa kuri'u na hudu ya faɗa kan Issaka, an ba su bisa ga zuriyarsu.
\v 18 Iyakarsu ta haɗa da Yezriyel, Kesulot, Shunem,
\v 19 Hafarayim, Shiyon da Anaharat.
\s5
\v 20 Ya haɗa da Rabbit, Kishon, Ebez,
\v 21 Remet, En Gannim, En Hadda da Bet Fazzez.
\v 22 Iyakarsu takai Tabor, Shahazuma, da Bet Shemesh, ta ƙarasa a Yodan. Birane goma sha shida, duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 23 Wannan shi ne gãdon kabilar Issaka, wanda aka ba su bisa ga zuriyarsu - birane da ƙauyukansu.
\s5
\v 24 Kaɗa Kuri'u na biyar ya faɗa kan kabilar Asha, aka kuma ba zuriyarsu.
\v 25 Iyakarsu ta hada da Helkat, Hali, Beten, Akshaf,
\v 26 Allammelek, Amad da Mishall. Daga yamma iyakar ta kai zuwa Karmel da Shiho Libnat.
\s5
\v 27 Daga nan ta karkata zuwa gabas zuwa Bet Dagon sa'an nan ta tafi har Zebulun, zuwa Kwarin Ifta El, arewaci zuwa Bet Emek da Neyiyel. Taci gaba zuwa Kabul wajen arewa.
\v 28 Daga nan tayi wajen Abdon, Rehob, Hammon da Kana har zuwa Babban Sidon.
\s5
\v 29 Iyakar tayi kwana zuwa Ramah, zuwa birnin Taya mai ganuwa. Sai iyakar ta karkata zuwa Hosa ta ƙarasa a teku a yankin Akzib,
\v 30 Umma, Afek, da Rehob. Akwai birane ashirin da biyu duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 31 Wannan shi ne gãdon kabilar Asha, an basu bisa ga zuriyarsu - birane da ƙauyukansu.
\s5
\v 32 Kaɗa Kuri'u na shida ya faɗa kan Naftali, aka kuma ba zuriyarsu.
\v 33 Iyakar ta fara daga oak a Za'ananim, zuwa Adami Nekeb da Yabneyel, zuwa Lakkum; ta ƙarasa a Yodan.
\v 34 Iyakar ta karkata zuwa yammaci har Aznot Tabor ta nausa zuwa Hukkok; ta taɓa Zebulun daga kudanci ta kai Asha daga yamma da Yahuda daga gabas har Kogin Yodan.
\s5
\v 35 Birane masu ganuwa sune Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,
\v 36 Adama, Ramah, Hazor,
\v 37 Kedesh, Edirai da En Hazor.
\s5
\v 38 Har yanzu akwai Yiron, Migdal El, Horem, Bet Anat da Bet Shemesh. Akwai birane goma sha tara, duk da ƙauyukansu.
\v 39 Wannan shi ne gãdon kabilar Naftali wanda aka ba zuriyarsu biranensu duk da ƙauyukansu.
\s5
\v 40 Kãɗa kuri'u na bakwai suka faɗa kan kabilar Dan an basu bisa ga zuriyarsu.
\v 41 Iyakar rabon su ya haɗa da Zora, Estawol, Ir Shemesh,
\v 42 Sha'alabbin, Aijalon da Itla.
\s5
\v 43 Ta haɗa da Elon, Timna, Ekron,
\v 44 Elteke, Gibbeton, Ba'alat,
\v 45 Yehud, Bene Berak, Gat Rimmon.
\v 46 Me Yarkon da Rakkon tare da iyaka a ƙetare daga Yoppa.
\s5
\v 47 Lokacin da iyakar kabilar Dan ta ɓace masu, sai su ka kaiwa Leshem hari su ka yi yaƙi da su, suka ci su, su ka kashe kowanensu da kaifin takobi, suka kwashe mallakar su, suka zauna cikin ta. Suka sake ma Leshem suna zuwa Dan sunan kakansu.
\v 48 Wannan shi ne gãdon kabilar Dan, an ba zuriyarsu - biranensu, da ƙauyukansu.
\s5
\v 49 Bayan da suka gama rarraba ƙasar a matsayin gãdonsu, mutanen Isra'ila suka ɗauka daga cikin gãdonsu suka ba Yoshuwa ɗan Nun.
\v 50 Bisa ga umarnin Yahweh suka bashi birnin daya roƙa, an bashi Timnat Sera cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim. Ya gina birni ya zauna ciki.
\s5
\v 51 Waɗannan sune gãdon da Eliyeza firist, Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin kabilu na mutanen Isra'ila suka raba bisa ga ƙuri'a a Shiloh, a gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa. Da haka suka gama rarraba ƙasar.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sai Yahweh yace da Yoshuwa.
\v 2 "Kayi magana da mutanen Isra'ila, kace, 'Ka keɓe biranen mafaka wanda nayi magana da kai ta hannun Musa.
\v 3 Kayi haka domin duk wanda ya kashe wani bada gangan ba zai iya zuwa can. Waɗannan birane za su zama wurin mafaka domin duk wanda ya nemi ɗaukar fansar jinin mutumin da aka kashe.
\s5
\v 4 Zai ruga zuwa ɗaya daga cikin waɗannan biranen zai tsaya a ƙofar shiga birnin, zai bayyyana damuwarsa ga dattawan garin. Daga nan za su ɗauke shi zuwa cikin birni su bashi wuri domin ya zauna a cikinsu.
\s5
\v 5 Idan wani daga cikin su ya zo domin ya yi ƙoƙarin ɗaukar fansar jinin wanda aka kashe, mutanen garin ba za su bada wanda ya yi kisan ga hukuma ba. Ba za su yi haka ba domin ba da gan - gan ne ya kashe maƙwabcinsa ba, kuma bashi da wata ƙiyayya game dashi a baya.
\v 6 Dole ya zauna cikin birnin har lokacin da zai tsaya gaban jama'a domin hukunci, har lokacin mutuwar babban Firist mai aiki a kwanakin nan, daga nan sai shi wanda ya yi kisan bisa ga kuskure ya koma garinsu gidansa kuma, daga in da ya gudu."'
\s5
\v 7 Sai Isra'ilawa suka zaɓi Kedesh cikin Galili, cikin ƙasar duwatsu ta Naftali, Shekem cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim da Kiriyet Arba (wato Hebron ke nan) cikin ƙasar duwatsu ta Yahuda.
\v 8 Ƙetaren Yodan gabashin Yeriko, suka zaɓi Beza, cikin jeji bisa tudu daga kabilar Ruben; Ramot Giliyad, daga kabilar Gad; da Golan cikin Bashan, daga kabilar Manasse.
\s5
\v 9 Waɗannan sune biranen da aka zaɓa domin dukkan mutanen Isra'ila da kuma baƙin dake zaune cikinsu, domin duk wanda ya kashe wani bada gan - gan ba zai iya rugawa don tsirar da ransa. Wannan mutum ba zai mutu ta hanun wanda yake son ɗaukar fansar jinin da aka zubar ba, har sai shi wanda ake zargin ya tsaya gaban taron jama'a.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Daga nan sai shugabanni na zuriyar Lebiyawa suka zo wurin Eliyeza firist, da Yoshuwa ɗan Nun da shugabanni na iyalan kakanninsu a tsakanin mutanen Isra'ila.
\v 2 Sai suka yi magana da su a Shilo cikin ƙasar Kan'ana suka ce, "Yahweh ya umarta ta hannun Musa a ba mu birane mu zauna ciki, tare da makiyayarsu domin dabbobinmu."
\s5
\v 3 Bisa ga umarnin Yahweh, mutanen Isra'ila suka ɗiba daga cikin gãdonsu na birane da makiyayarsu suka ba Lebiyawa.
\s5
\v 4 Kaɗa kuri'u domin zuriyar Kohatawa ya bada wannan sakamako: Firistoci - zuriyar Haruna waɗanda su ke daga Lebiyawa - sun karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuda, daga kabilar Simiyon da kuma daga kabilar Benyamin.
\v 5 Sauran zuriyar Kohatawa bisa ga kuri'u sun karɓi birane goma daga zuriyar kabilar Ifraim, Dan da rabin kabilar Manasse.
\s5
\v 6 Mutanen zuriyar Gashon an basu, ta wurin kaɗa kuri'u birane goma sha uku daga zuriyar Issaka, Asha, Naftali da rabin kabilar Manasse cikin Bashan.
\v 7 Mutanen da su ke daga zuriyar Merari sun karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ruben, Gad da Zebulun.
\s5
\v 8 Don haka mutanen Isra'ila sun bada waɗannan birane, ga Lebiyawa ta wurin jefa kuri'u (duk da makiyayarsu) kamar yadda Yahweh ya umarta ta hannun Musa.
\v 9 Daga kabilun Yahuda da Simiyon aka bada waɗannan birane da aka lisafta sunayensu a nan.
\v 10 Waɗannan birane an bayar da su ga zuriyar Haruna, waɗanda su ke daga zuriyar Kohatawa waɗanda daga kabilar Lebi su ke. Waɗanda kaɗa ƙuri'un farko kansu ya faɗa.
\s5
\v 11 Isra'ilawa sun basu Kiriyat Arba (Arba shi ne uban Anak), wato Hebron ke nan, cikin ƙasar duwatsu ta Yahuda, tare da makiyayar da ke kewaye da ita.
\v 12 Amma gonakin da ke birane da ƙauyukansu an riga an ba Kaleb ɗan Yefunne, a matsayin mallakarsa.
\s5
\v 13 Ga zuriyar Haruna firist sun bashi Hebron da makiyayarta, wanda shi ne birnin mafaka ga wanda ya kashe wani cikin kuskure da Libna duk da makiyayarta.
\v 14 Yattir da makiyayarta da Eshtemowa da makiyayarta.
\v 15 Suka kuma ba da Holon da makiyayarta, Debir da makiyayaarta,
\v 16 Ayin da makiyayarta, Jutta da makiyayarta da Bet Shemesh da makiyayarta. Akwai birane tara da aka bayar daga cikin kabilun nan biyu.
\s5
\v 17 Daga kabilar Benyamin an bada Gibiyon duk da makiyayarta, Geba da makiyayarta,
\v 18 Anatot duk da makiyayarta, da Almon da kewayenta birane huɗu ke nan.
\v 19 Biranen da aka ba firistoci zuriyar Haruna, dukkan su birane goma sha uku ne, haɗe da makiyayarsu.
\s5
\v 20 Sauran Kohatawa - su Lebiyawan nan waɗanda su ke daga iyalin Kohat - sun sami nasu biranen daga kabilar Ifraim, ta wurin jefa kuri'u.
\v 21 An basu Shekem duk da makiyayarsu cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure - Geza da makiyayarsu.
\v 22 Kibzayim da makiyayarsu, da Bet Horon da makiyayarsu - birane huɗu ne dukka.
\s5
\v 23 Daga kabilar Dan, zuriyar Kohat an ba su Eltike da makiyayarsu, Gibbeton da makiyayarsu.
\v 24 Aijalon da makiyayarsu da Gat Rimmon da makiyayarsu - duka birane huɗu ne.
\s5
\v 25 Daga rabin kabilar Manasse, zuriyar Kohat an basu Ta'anak tare da makiyayarsu da Gar Rimmon tare da makiyayarsu - birane biyu.
\v 26 Akwai birane goma dukka domin sauran zuriyar Kohatawa, duk da makiyayarsu.
\s5
\v 27 Daga rabin kabilar Manasse, zuwa zuriyar Gashon waɗannan sauran zuriyar Lebi ne, an bada Golan cikin Bashan tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai bisa ga kuskure, tare da Be Eshtera da makiyayarsu - birane biyu ne duka.
\s5
\v 28 Ga zuriyar Gashon an basu Kishon daga kabilar Issaka, tare da makiyayarsu, Daberat tare da makiyayarsu,
\v 29 Yarmut tare da makiyayarsu, da En Gannim tare da makiyayarsu.- birane hudu.
\v 30 Daga kabilar Asha, sun bada Mishal tare da makiyayarsu, Abdon tare da makiyayarsu,
\v 31 Helkat tare da makiyayarsu da Rehob tare da makiyayarsu - birane huɗu ne dukka.
\s5
\v 32 Daga kabilar Naftali, sun ba zuriyar Gashon Kedesh cikin Galili tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure; Hammot Dor tare da makiyayarsu, da Kartan tare da makiyayarsu - birane uku ne duka.
\v 33 Akwai birane goma sha uku duka, daga zuriyar Gashon, tare da makiyayarsu.
\s5
\v 34 Ga sauran Lebiyawa - na zuriyar Merari - an ba su daga cikin kabilar Zebulun: Yokniyam tare da makiyayarsu, Karta tare da makyyayarsu,
\v 35 Dimna tare da makiyayarsu, da Nahalal tare da makiyayarsu - dukka birane huɗu ke nan.
\s5
\v 36 Ga zuriyar Merari an ba su daga kabilar Ruben: Bezer tare da makiyayarsu, Yahaz tare da makiyayayarsu,
\v 37 Kedemot tare da makiyayarsu, da Mefa'at tare da makiyayarsu - birane huɗu.
\v 38 Daga cikin kabilar Gad an ba su Ramot cikin Giliyad tare da makiyayarsu - birnin mafaka domin wanda ya yi kisan kai cikin kuskure - da Mahanayim tare da makiyayarsu.
\s5
\v 39 Zuriyar Merari an ba su Heshbon tare da makiyayarsu, da Yazer tare da makiyayarsu. Waɗannan birane huɗu ne dukka.
\v 40 Dukkan waɗannan birane ne na zuriyar Merari, waɗanda su ke daga kabilar Lebi - dukka birane goma sha biyun an ba su ne bisa ga kaɗa ƙuri'u.
\s5
\v 41 Biranen Lebiyawa da aka ɗauka daga cikin tsakiyar mallakar Isra'ila sun kai birane arba'in da takwas, ya haɗa da wuraren kiwonsu.
\v 42 Waɗannan birane kowanne ya haɗa da makiyayarsu da ke kewaye da su. Haka ya ke ga dukkan waɗannan birane.
\s5
\v 43 Haka nan Yahweh ya ba da wannan dukkan ƙasa da ya rantse wa kakanninsu, Isra'ilawa su ka mallaketa, su ka zauna cikinta.
\v 44 Yahweh ya ba su hutawa ta kowanne gefe, kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin maƙiyansu da zai yi nasara da su. Yahweh ya ba da dukkan abokan gabarsu cikin hannunsu.
\v 45 Babu wani cikin dukkan alƙawura masu kyau da Yahweh ya furta a kan gidan Isra'ila da ya kasa cika. Dukkan su sun tabbata.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 A wan can lokaci Yoshuwa ya kira Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse.
\v 2 ya ce masu, "Kun yi dukkan abin da Musa bawan Yahweh ya umarce ku. Kunyi biyayya da muryata a kan dukkan abinda na umarce ku.
\v 3 Baku yãshe da 'yan uwanku a yawan kwanakin nan ba, har ya zuwa wannan rana, kun kuma kiyaye umarnan Yahweh Allahn ku.
\s5
\v 4 Yanzu Yahweh Allahnku ya ba da hutu ga "yan'uwanku, kamar yadda ya alƙawarta masu. Don haka ku juya ku tafi rumfunanku cikin ƙasar mallakarku, wadda Musa bawan Yahweh ya baku a ƙetaren Yodan.
\v 5 Don haka sai ku kula sosai ku kiyaye dokoki da umarnai waɗanda Musa bawan Yahweh ya umarce ku, ku ƙaunaci Yahweh Allahnku. Kuyi tafiya cikin hanyoyinsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa kuyi masa sujada da dukkan zuciyarku da ranku."
\v 6 Sai Yoshuwa ya albarkace su ya sallame su sai su ka koma rumfunansu.
\s5
\v 7 Yanzu ga rabin kabilar Manasse Musa ya rigaya ya ba su gãdonsu cikin Bashan, amma ga ɗaya rabin Yoshuwa ya bada gãdo daga cikin na 'yan'uwansu a yammacin Yodan. Yoshuwa ya sallamesu zuwa rumfunansu; ya sa masu albarka, ya ce da su,
\v 8 "Ku koma rumfunanku da kuɗi masu yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa da zinariya, da tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawan gaske. Ku raba ganimar abokan gabanku tare da 'yan'uwanku."
\s5
\v 9 Sai zuriyar Ruben da zuriyar Gad, da rabin kabilar Manasse su ka koma gida, suka bar mutanen Isra'ila a Shilo, wadda ke cikin ƙasar Kan'ana. Sun tafi zuwa yankin ƙasar Giliyad, zuwa ƙasar su, wadda su da kansu su ka mallaka, cikin biyayya ga umarnin Yahweh, ta hannun Musa.
\s5
\v 10 Sa'ad da suka zo Yodan wadda ke cikin ƙasar Kan'ana, sai Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse su ka gina bagadi kusa da Yodan, babban bagadi shahararre kuma.
\v 11 Da mutanen Isra'ila suka ji labarin nan cewa, "Duba! mutanen Ruben da Gad da rabin kabilar Manasse sun gina bagadi a gaban ƙasar Kan'ana a Gelilot, a yankin da ke kusa da Yodan, a yankin da ke mallakar mutanen Isra'ila."
\s5
\v 12 Da mutanen suka ji haka, sai dukkan mutanen Isra'ila suka taru a Shilo domin su je su yi yaƙi gãba da su.
\s5
\v 13 Sai mutanen Isra'ila suka aiki 'yan saƙo ga su Rubenawa da Gadawa da rabin kabilar Manasse, cikin ƙasar Giliyad. Sun kuma aiki Finehas ɗan Eliyeza, Firist.
\v 14 Tare da shi kuma akwai shugabanni goma, ɗaya daga cikin kowacce kabilar Isra'ila, kuma kowannensu shugabane daga cikin zuriyar mutanen Isra'ila.
\s5
\v 15 Suka zo wurin mutanen Ruben da Gad da rabin kabilar Manasse, cikin ƙasar Giliyad, suka yi magana da su:
\v 16 "Dukkan taron jama'ar Yahweh sun faɗi haka, "Wanne irin rashin aminci ne wannan ku ka aikata gãba da Allah na Isra'ila, a wannan rana kun juya daga bin Yahweh kun ginawa kanku bagadi don ku tayarwa Yahweh?
\s5
\v 17 Zunubinmu a Feyor bai ishe mu ba? Har yanzu bamu tsarkake kanmu daga gare shi ba. Saboda wannan zunubi annobai su ka abko wa jama'ar Yahweh.
\v 18 Ko ya zama dole ne ku juya ga bin Yahweh a wannnan rana? Idan kuma ku ka yi wa Yahweh tayarwa yau, gobe zai yi fushi da dukkan taron jama'ar Isra'ila.
\s5
\v 19 Idan ƙasar da ku ka mallaka ta ƙazantu, sai ku ƙetaro ƙasa inda mazaunin Yahweh ya ke zaune domin ku samar wa kanku mallaka daga cikin mu. Ku dai kada ku tayarwa Yahweh, ko ku tayar mana ta wurin gina wa kanku bagadi banda bagadin Yahweh Allahnmu.
\v 20 Ko Akan ɗan Zera, bai yi laifin karya imani akan zancen waɗannan abubuwa da su ke keɓaɓɓu domin Allah ba? ko hasala ba ta afko wa mutanen Isra'ila ba? Wannan mutum bai mutu shi kaɗai domin laifinsa ba."
\s5
\v 21 Daga nan sai kabilar Ruben Gad da rabin kabilar Mannasse suka amsa wa shugabannin zuriyar Isra'ila:
\v 22 "Maigirman nan, Allah, Yahweh! Maigirman nan, Allah, Yahweh! - Ya sani, bari Isra'ila kanta kuma ta sani! Idan cikin tayaswa ne ko cikin saɓawa imani gãba da Yahweh, kada ka yi mana ceto yau
\v 23 domin mun gina bagadi muka juya ga bin Yahweh. Idan mun gina wannan bagadi domin mu miƙa hadayun ƙonawa, hadayun gari, ko hadayun salama a kansa to bari Yahweh yasa mu biya.
\s5
\v 24 A'a! Munyi shi cikin tsoro da nufin cewa a lokaci mai zuwa 'ya'yanku za su iya cewa da 'ya'yanmu, 'Ina ruwanku da Yahweh, Allah na Isra'ila?
\s5
\v 25 Gama Yahweh ya sa Yodan ta zama iyaka tsakanin mu da ku. Ku mutanen Ruben da mutanen Gad, baku da abinda zaku yi da Yahweh.'Da haka 'ya'yan ku zasu iya sa 'ya'yan mu su dena yin sujada ga Yahweh.
\s5
\v 26 Don haka sai mu ka ce, 'Bari yanzu mu gina bagadi, ba don ƙonannun hadayu ba ba kuma domin wasu hadayu ba,
\v 27 amma domin zama shaida tsakanin mu da ku, da kuma don zuriya masu tasowa bayan mu, da kuma zamu bauta wa Yahweh a gaban sa, da ƙonannun hadayu da kuma hadayun mu tare da hadayun mu na salama, domin kada 'ya'yanku su ce da 'ya'yanmu a lokaci mai zuwa, "Baku da rabo cikin Yahweh."'
\s5
\v 28 Sai mu ka ce, 'Idan zasu faɗi mana haka ko su faɗi wa zuriyarmu a lokaci mai zuwa, za mu ce, "Duba! wannan shi ne kwatancin bagadin Yahweh, wanda kakanninmu suka yi, ba domin ƙonannun hadayu ba, ba kuma don hadayu ba, amma domin shaida tsakanin mu da ku".
\v 29 Bari tayaswa ga Yahweh ta yi nesa da mu, har yau mu juya daga bin sa ta wurin gina bagadi domin ƙonanniyar hadaya, domin hadaya ta gari, ko domin hadayar yanka, banda bagadin Yahweh Allahn mu wanda ke gaban mazamninsa."'
\s5
\v 30 Sa'ad da Fenihas firist da shugabannin jama'a, wato shugabannin zuriyar Isra'ila waɗanda suke tare dashi, su ka ji kalmomin mutanen Ruben, Gad, da Manasse suka ce, wannan ya zama abu mai kyau a garesu.
\v 31 Sai Fenihas ɗan Eliyeza firist ya ce da mutanen Ruben, Gad, da Manasse, "Yau mun sani cewa Yahweh yana tsakiyar mu, saboda baku aikata wannan saɓo gãba da shi ba. Yanzu kun ceci mutanen Isra'ila daga hannun Yahweh."
\s5
\v 32 Daga nan sai Fenihas ɗan Eliyeza firist da shugabannin su ka juya su ka bar Rubenawa da Gadawa, suka bar ƙasar Giliyad, su ka koma ƙasar Kan'ana, zuwa ga mutanen Isra'ila, su ka dawo masu da magana.
\v 33 Rahoton su ya gamshi mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka albarkaci Allah ba su ƙara maganar yaƙi da Rubenawa da Gadawa ba kan zancen hallaka ƙasar da su ke zaune a ciki.
\s5
\v 34 Sai mutanen Ruben da Gadawa suka ba bagadi suna, "Shaida" gama suka ce, "Shaida ce tsakanin mu cewa Yahweh shi ne Allah."
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Bayan kwanaki masu yawa, bayan da Yahweh ya bada hutu ga Isra'ila daga abokan gãbansu da ke kewaye da su, Yoshuwa kuma ya tsufa ƙwarai.
\v 2 Sai Yoshuwa ya kira dukkan Isra'ila, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da manyansu - ya ce masu, "Ni na tsufa sosai.
\v 3 Kunga dukkan abin da Yahweh Allahn ku ya yi da dukkan ƙasashen nan domin ku, domin Yahweh Allahn ku shi ne ya yi yaƙi domin ku.
\s5
\v 4 Duba! Na sanya sauran al'umman da su ka rage a cisu su zama abin gãdo ga kabilun ku tare da dukkan ƙasashen dana rigaya na hallakar daga Yodan zuwa Babban Teku daga yamma.
\v 5 Yahweh Allahnku zai kore su. Zai tuttura su daga gaban ku. Zai ƙwace ƙasar su, za ku mallaki ƙasar su, kamar yadda Yahweh ya alƙawarta ma ku.
\s5
\v 6 Sai ku yi ƙarfafa sosai, ku kuma kiyaye dukkan abin da aka rubuta cikin shari'ar Musa kada ku kauce daga gare ta dama ko hagu,
\v 7 domin kada ku yi cuɗanya da waɗannan al'ummai da su ka rage a cikin ku kada ma ku ambaci sunayen allolin su, ko ku rantse da su, ko ku yi masu sujada, ko ku russuna masu.
\v 8 Maimakon haka; dole ku manne wa Yahweh Allahn ku kamar yadda ku ka yi zuwa wannan rana.
\s5
\v 9 Gama Yahweh ya kori al'ummai da manya, masu ƙarfi daga gaban ku. Amma ku, ba mutumin da ya iya tsayawa a gaban ku har wa yau.
\v 10 Kowanne mutum ɗaya daga cikinku za ya runtumi dubu, domin Yahweh Allahnku, shi ne ya ke yaƙi domin ku, kamar yadda ya alƙawarta maku.
\v 11 Ku kula da kyau, domin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku.
\s5
\v 12 Amma idan ku ka juya ku ka manne wa waɗannan sauran al'ummai waɗanda su ka rage a tsakiyar ku, ko idan ku ka yi auratayya da su, ko in ku ka yi huɗɗa tare da su su kuma tare da ku,
\v 13 ku sani tabbas cewa Yahweh Allahnku ba zai ƙara korar waɗannan al'ummai daga gaban ku ba, maimakon haka, za su zama azargiya da tarko gareku, bulala a bayanku, ƙayayuwa cikin idanunku, har sai kun hallaka daga ƙasan nan mai kyau wadda Yahweh Allahnku ya baku.
\s5
\v 14 Gashi yanzu ina kan tafiya hanya ta dukkan duniya, kuma kun sani da dukkan zukatanku da rayukanku, babu wata kalma data kasa zama gaskiya cikin dukkan abubuwa masu kyau da Yahweh Allahnku ya alƙawarta game da ku, dukkan waɗannan abubuwa sun tabbata game da ku, babu wani abu daya ka sa cika.
\v 15 Ya zama kuwa kamar yadda kowacce maganar Yahweh Allahnku ya alƙawarta ma ku ta cika, Yahweh zai kawo ma ku dukkan miyagun abubuwa har sai ya hallakar da ku daga ƙasa mai kyau wadda Yahweh Allahnku ya baku.
\s5
\v 16 Zai yi haka idan har kuka karya alƙawarin Yahweh Allahnku, wadda ya umarce ku ku kiyaye. Idan ku ka je ku ka yi sujada ga waɗansu alloli ku ka russuna masu, sa'annan fushin Yahweh zai yi ƙuna a kan ku, da sauri zaku hallaka daga ƙasa mai kyau wadda ya baku."
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Sai Yoshuwa ya tara dukkan kabilun Isra'ila a shekem, ya kira dattawan Isra'ila, da shugabanninsu, da alƙalansu, da magabatansu, suka bayyana kan su gaban Allah.
\v 2 Sai Yoshuwa ya cewa dukkan jama'a, "Wannan shi ne abinda Yahweh Allah na Isra'ila, ya ce, 'Kakanninku da daɗewa su ka zauna a ƙetaren kogin Yuferatis - Tera, mahaifin Ibrahim da mahaifin Naho - sun kuma yi sujada ga waɗansu alloli.
\s5
\v 3 Amma na ɗauki mahaifinku zuwa ƙetaren Yuferitis na bishe shi cikin ƙasar Kan'ana na bashi zuriya masu yawa ta wurin ɗan sa Ishaku.
\v 4 Ga Ishaku na bashi Yakubu da Isuwa. Na ba Isuwa ƙasar tudu ta Seyir domin ya mallaketa, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar.
\s5
\v 5 Na aika masu Musa da Haruna, Na azabtar da Masarawa da annobai. Bayan haka, sai na fito da ku daga ciki,
\v 6 Na fito da kakanninku daga Masar. Ku ka zo teku. Masarawa su ka bi su da karusai da mahayan dawakai har zuwa jan teku.
\s5
\v 7 Sa'ad da kakannin ku su ka yi kira ga Yahweh, ya sa duhu tsakanin ku da Masarawa. Ya jawo teku a kan su ta rufe su. Kun ga abin da na yi cikin Masar. Da ga nan ku ka zauna kwanaki da yawa cikin jeji.
\s5
\v 8 Na kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, waɗanda su ke zaune a ƙetaren Yodan. Sun yi yaƙi da ku, na kuma bashe su cikin hannun ku. Ku ka mallaki ƙasar su, kuma na hallakar da su a gabanku.
\s5
\v 9 Sai Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya ta shi ya kai hari a Isra'ila. Ya aika a kira Balaam ɗan Beyor, ya la'antaku.
\v 10 Amma ban saurari Balaam ba. Babu shakka, sai ya albarkaceku. Da haka na cece ku daga hannunsa.
\s5
\v 11 Kuka haye Yodan ku ka zo Yeriko. Shugabannin Yeriko su ka yi yaƙi da ku, tare da Amoriyawa da Ferizziyawa da Kan'aniyawa, da Hittiyawa da Girgashiyawa da Hibiyawa da Yebusiyawa na ba ku nasara a kansu na sa su ƙarƙashin mulkinku.
\v 12 Na ku ma aike da zirnaƙo gabanku, ya kore su daga gabanku da sarakuna biyu na Amoriyawa daga gabanku, wannan bai faru ta wurin takobinku ko bakanku ba.
\s5
\v 13 Na ba ku ƙasa wadda ba ku yi aikin kome ba da biranen da ba ku gina ba, yanzu ku na zaune a cikinsu. Ku na cin 'ya'yan kuringar inabi da na zaitun wanda ba ku ne ku ka dasa su ba.'
\s5
\v 14 Yanzu fa sai ku ji tsoron Yahweh ku bauta masa da dukkan sahihanci da gaskiya; sai ku ƙi allolin da kakannin ku suka yi wa sujada a ƙetaren Yodan da cikin Masar, ku yi wa Yahweh sujada.
\v 15 Idan a gare ku ba daidai bane a yi wa Yahweh sujada, ku zaɓa da kan ku yau wanda zaku bautawa, ko dai alloli waɗanda kakanninku su ka yi wa sujada na ƙetaren Yufiretes ko kuwa allolin Amoriyawa, waɗanda ku ke zaune cikin ƙasarsu. Amma ni da gidana, Yahweh za mu yi wa sujada."
\s5
\v 16 Daga nan mutanen suka amsa suka ce, "Ba zamu taɓa yashe da Yahweh sa'annan mu bautawa wa su alloli ba,
\v 17 gama Yahweh Allahnmu wanda ya fitar da mu da kakanninmu da ga ƙasar Masar, da ga gidan bauta, wanda ya aikata manyan al'ajibai a idanun mu, ya ku ma tsare mu cikin dukkan hanyar da mu ka bi, da ku ma cikin dukkan al'umman da mu ka ratsa ta tsakiyarsu.
\v 18 Yahweh kuma ya kori dukkan mutane daga gabanmu, har da Amoriyawa da su ke zaune cikin ƙasar. Don haka mu ma zamu yi wa Yahweh sujada, gama shi ne Allahnmu."
\s5
\v 19 Amma Yoshuwa ya cewa mutane, "Ba zaku bautawa Yahweh ba, gama shi Allah ne mai kishi; ba zai gafarta laifofinku ko zunubanku ba.
\v 20 Idan ku ka yashe da Yahweh ku ka yi sujada ga baƙin alloli, daga nan zai juya ya azabtar da ku. Daga nan zai hallaka ku, bayan da ya riga ya kyautata ma ku."
\s5
\v 21 Amma mutanen suka cewa Yoshuwa, "Sam, za mu yi sujada ga Yahweh."
\v 22 Daga nan sai Yoshuwa ya ce ma mutanen, "Ku shaidu ne bisa kanku kun zaɓi Yahweh, ku yi masa sujada." Su ka ce, "Mu shaidune"
\v 23 Yanzu ku kawar da baƙin allolin da ke tare da ku, ku juyo da zuciyarku ga Yahweh, Allah na Isra'ila."
\s5
\v 24 Sai mutanen suka cewa Yoshuwa, "Za mu yi sujada ga Yahweh Allahnmu. Za mu saurari muryarsa."
\v 25 Yoshuwa ya yi wa'adi tare ta mutanen a wannan rana. Ya shimfiɗa masu dokoki da farillai a Shekem.
\v 26 Yoshuwa ya rubuta waɗannan maganganu cikin littafin shari'ar Allah. Ya ɗauki babban dutse ya kafa shi ƙarƙashin itacen oak da ke kusa da wuri mai tsarki na Yahweh.
\s5
\v 27 Yoshuwa ya cewa dukkan mutanen, "Duba, wannan dutse zai zama shaida a kanmu. Gama ya ji dukkan maganganun da Yahweh ya ce da mu. Don ha ka zai zama shaida a kanku, Idan har ku yi musun Allahnku."
\v 28 Sai Yoshuwa ya sallami mutanen, kowanne ya tafi wurin gãdonsa.
\s5
\v 29 Bayan waɗannan abubuwa Yoshuwa ɗan Nun, bawan Yahweh, ya rasu, yana da shekaru 110.
\v 30 Aka bizne shi cikin iyakar, gãdonsa a Timnat Sera, wadda ke cikin ƙasar tuddai ta Ifraim, arewacin Tsaunin Gaash.
\s5
\v 31 Isra'ila su ka yi sujada ga Yahweh dukkan kwanakin Yoshuwa, da dukkan kwanakin dattawan da su ka kasance bayan Yoshuwa, waɗanda su ka san dukkan abin da Yahweh ya yi domin Isra'ila.
\s5
\v 32 Ƙasusuwan Yosef, da mutanen Isra'ila suka ɗauko daga Masar - aka bizne su a Shekem, ciki yankin ƙasar da Yakubu ya sayo daga 'ya'yan Hamor, mahaifin Shekem. Ya saye ta a bakin azurfa ɗari, ta zama gãdon zuriyar Yosef.
\v 33 Eliyeza ɗan Haruna shi ma ya mutu. Su ka bizne shi a Gibiya, a birnin Fenihas ɗansa, wanda aka bashi. Tana cikin ƙasar duwatsu ta Ifraim.