ha_ulb/05-DEU.usfm

2029 lines
143 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id DEU
\ide UTF-8
\h Littafin Maimaitawar Shari'a
\toc1 Littafin Maimaitawar Shari'a
\toc2 Littafin Maimaitawar Shari'a
\toc3 deu
\mt Littafin Maimaitawar Shari'a
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Waɗannan ne maganganun da Musa ya gaya wa dukkan Isra'ila a ƙetaren Yodan a cikin jeji, a sararin kwarin Kogin Yodan daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da kuma Di Zahab.
\v 2 Tafiyar kwana sha ɗaya ce daga Horeb ta hanyar Dutsen Seyir zuwa Kadesh Barniya.
\s5
\v 3 Ya kasance a shekara ta arba'in, a wata na sha ɗaya, a kan ranar farko na watan, Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila, yana gaya masu dukkan abin da Yahweh ya umarce shi game da su.
\v 4 Wannan kuwa bayan da Yahweh ya kai hari ga Sihon sarkin Amoriyawa ne, wanda ke zama a Heshbon, da Og sarkin Bashan, wanda ke zama a Ashtarot a Edrayi.
\s5
\v 5 A ƙetaren Yodan, ƙasar Mowab, Musa ya fara sanar da waɗannan umarnai, cewa,
\v 6 "Yahweh Allahnmu ya yi magana da mu a Horeb, cewa, 'Dogon zaman da kuka yi a wannan ƙasar tudu ya isa.
\s5
\v 7 Ku juya ku kama tafiyarku, ku kuma tafi ƙasar tudu ta Amoriyawa da dukkan wurare kusa da sararin kwarin Kogin Yodan, a cikin ƙasar tudu, a cikin ƙasar kwari, a cikin Negeb, da bakin teku - ƙasar Kan'aniyawa, da cikin Lebanon har ya zuwa babban kogi, wato Yufiretis.
\v 8 Duba, na sanya ƙasar a gaban ku; ku tafi ciki ku kuma mallaki ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku - ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu - ya basu da kuma zuriyarsu a bayansu.'
\s5
\v 9 Na yi magana da ku a wancan lokacin, cewa, 'Bazan iya ɗaukarku da kaina ni kaɗai ba.
\v 10 Yahweh Allahnku ya riɓanɓanya ku, kuma, duba, a yau kun riɓanɓanyu kamar taurarin sama.
\v 11 Bari Yahweh, Allahn ubanninku, ya maida ku fiye da yadda kuke sau dubu, ya kuma albarkace ku, kamar yadda ya yi maku alƙawari!
\s5
\v 12 Amma ta yaya ni da kaina ni kaɗai zan ɗauki nawayoyinku, karkiyoyinku, da saɓananku?
\v 13 Ku ɗauki mutane masu hikima, mutane masu fahimta, da mutane masu kyakkyawar shaida daga kowacce kabila, zan kuma sanya su shugabanni a bisan ku.'
\v 14 Kuka amsa mani kuka ce, ' Abin da ka faɗa ya yi mana kyau mu yi.'
\s5
\v 15 Sai na ɗauki shugabanni daga cikin kabilunku, mutane masu hikima, mutane kuma masu kyakkyawar shaida, na kuma mai da su shugabanni a bisan ku, hafsoshin dubbai, hafsoshin ɗaruruwa, hafsoshin hamsin-hamsin, hafsoshin goma-goma, da ofisoshi, kabila bayan kabila.
\v 16 Na umarci alƙalanku a wancan lokaci, cewa, 'Ku saurari saɓanai tsakanin 'yan'uwanku, ku kuma yi hukuncin adalci tsakanin mutum da ɗan'uwansa, da bãre wanda ya ke tare da shi.
\s5
\v 17 Ba zaku nuna sonkai ga kowa ba a cikin saɓani; zaku saurari ƙarami da babba bai ɗaya. Ba zaku ji tsoron fuskar mutum ba, domin hukuncin na Allah ne. Saɓanin da yafi ƙarfinku, zaku kawo a gare ni, zan kuma saurare shi.'
\v 18 Na umarce ku a wancan lokaci dukkan abubuwan da zaku yi.
\s5
\v 19 Muka yi tafiyarmu daga Horeb muka kuma tafi ta cikin dukkan babban jeji da ban razana da kuka gani, a kan hanyarmu ta zuwa ƙasar tudu ta Amoriyawa, kamar yadda Yahweh Allahnmu ya umarce mu; kuma muka zo Kadesh Barniya.
\s5
\v 20 Na ce maku, 'Kun zo ƙasar tudu ta Amoriyawa, wadda Yahweh Allahnmu ya ke bamu.
\v 21 Duba, Yahweh Allahnku ya sanya ƙasar a gaban ku; ku tafi, ku mallaketa, kamar yadda Yahweh, Allah na ubanninku, ya faɗi maku; kada ku ji tsoro, ko ku karaya.'
\s5
\v 22 Kowannenku ya zo gare ni ya kuma ce, 'Bari mu aika da mutane gaba da mu, saboda suyi binciken ƙasar domin mu, su kuma kawo mana magana game da hanyar da zamu bi mu kai hari, game kuma da biranen da zamu je.'
\v 23 Shawarar ta gamshe ni sosai; na ɗauki mutanenku sha biyu, mutum ɗaya domin kowacce kabila.
\v 24 Suka juya suka tafi zuwa cikin ƙasar tudu, suka isa kwarin Eshkol, suka kuma yawace shi.
\s5
\v 25 Suka ɗauko daga cikin amfanin ƙasar a cikin hannuwansu, suka kuma kawo mana. Suka kuma kawo mana magana suka kuma ce, 'Ƙasa ce mai kyau da Yahweh Allahnmu ya ke bamu.'
\s5
\v 26 Duk da haka kuka ƙi kai hari, amma kuka yi tawaye gãba da dokar Yahweh Allahnku.
\v 27 Kuka yi gunaguni a rumfunanku kuka kuma ce, "Saboda Yahweh ya ƙi mu ne ya fito da mu daga ƙasar Masar, ya bayar da mu cikin hannun Amoriyawa su hallaka mu.
\v 28 Ina zamu iya zuwa yanzu? 'Yan'uwanmu sun sa zuciyarmu ta narke, cewa, 'Waɗannan mutane masu girma ne da tsayi fiye da mu; biranensu kuma manya ne kuma da garu har cikin sammai; bugu da ƙari, munga 'ya'ya maza na Anakim a wurin."'
\s5
\v 29 Daganan nace maku, 'Kada ku firgita, ko ku ji tsoronsu.
\v 30 Yahweh Allahnku, wanda ya ke tafiya a gaban ku, zai yi yaƙi domin ku, kamar dukkan abin da ya yi domin ku a Masar, a gaban idanunku,
\v 31 da kuma a cikin jeji, inda kuka ga yadda Yahweh Allahnku ya ɗauke ku, kamar yadda mutum ke ɗaukar ɗansa, dukkan inda kuka tafi har sai da kuka zo wannan wuri.'
\s5
\v 32 Amma duk da wannan magana baku gaskata da Yahweh Allahnku ba,
\v 33 wanda ya tafi a gaban ku a bisa hanya don ya sami wuri domin kuyi sansani, cikin wuta da dare cikin kuma girgije da rana.
\s5
\v 34 Yahweh ya ji ƙarar maganganunku ya kuma yi fushi; ya yi rantsuwa ya ce,
\v 35 'Tabbas babu ko ɗaya daga cikin waɗannan mutane na wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba kakanninku,
\v 36 sai Kaleb ɗan Yefunne; zai gan ta. A gare shi zan bayar da ƙasar da ya taka akai, ga 'ya'yansa kuma, saboda ya bi Yahweh ɗungum.'
\s5
\v 37 Sa'an nan Yahweh ya fusata da ni saboda ku, cewa, 'Kai ma baza ka je cikin wurin ba;
\v 38 Yoshuwa ɗan Nun, wanda ke tsayawa a gaban ka, shi zai je cikin wurin; ka ƙarfafa shi, domin zai bida Isra'ila su gãje ta.
\s5
\v 39 Haka kuma, ƙananan yaranku, waɗanda kuka ce zasu hallaka, waɗanda a yau basu da sanin nagarta ko mugunta - zasu je cikin wurin. A gare su zan bayar da ita, kuma zasu mallake ta.
\v 40 Amma game da ku, ku juya ku kama tafiyarku zuwa cikin jeji ta gefen hanyar zuwa Tekun Iwa.'
\s5
\v 41 Daganan kuka amsa kuka ce mani, 'Mun yi zunubi gãba da Yahweh; zamu tafi mu yi yaƙi, kuma zamu bi dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya umarce mu mu yi.' kowanne mutum a cikin ku ya sanya makaman yaƙinsa, kuma kuka shirya ku kai hari ga ƙasar tudu.
\v 42 Yahweh ya ce mani, 'Ka ce masu, "Kada ku kai hari kuma kada ku yi yaƙi, gama bazan kasance tare da ku ba, kuma zaku sha kaye daga maƙiyanku.'
\s5
\v 43 Na yi magana da ku ta wannan hanya, amma baku saurara ba. Kuka yi tawaye gãba da dokar Yahweh; kuka kangare kuma kuka kai hari ga ƙasar tudu.
\v 44 Amma Amoriyawa, waɗanda ke zaune a ƙasar tudu, suka fito gãba da ku kuma suka kore ku kamar zuma, suka kuma mãke ku ƙasa a Seyir, har nesa zuwa Horma.
\s5
\v 45 Kuka dawo kuma kuka yi kuka a gaban Yahweh; amma Yahweh bai saurari muryarku ba, ko kuma ya kula da ku ba.
\v 46 Sai kuka dakata a Kadesh na kwanaki da yawa, dukkan kwanakin da kuka dakata a can.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Daga nan muka juya muka ɗauki tafiyarmu ta hanyar cikin jeji ta wajen Tekun Iwa, kamar yadda Yahweh ya yi magana da ni; muka tafi kewaye da Dutsen Seyir na kwanaki da yawa.
\v 2 Yahweh ya yi magana da ni, cewa,
\v 3 'Tafiyarku kewaye da wannan dutse ya isa; ku juya arewa.
\s5
\v 4 Ka umarci mutanen, cewa, "Zaku bi ta cikin kan iyakar 'yan'uwanku, zuriyar Isuwa, waɗanda ke zaune a Seyir; zasu ji tsoronku. Saboda haka ku kiyaye
\v 5 kada ku yi yaƙi da su, domin ba zan baku ko ɗaya daga cikin ƙasarsu ba, a'a, bama wadda ta isa tafin ƙafarku ya taka ba; gama na bayar da Dutsen Seyir ga Isuwa a matsayin mallaka.
\s5
\v 6 Za ku sayi abinci daga gare su da kuɗi, domin ku ci; zaku kuma sayi ruwa daga gare su da kuɗi, domin ku sha.
\v 7 Gama Yahweh ya albarkace ku a cikin dukkan aikin hannunku; ya san tafiyarku cikin wannan babban jeji. Cikin waɗannan shekaru arba'in Yahweh Allahnku yana tare daku, kuma baku rasa komai ba."'
\s5
\v 8 Sai muka ratsa ta wurin 'yan'uwanmu, zuriyar Isuwa da ke zaune a Seyir, nesa da hanyar Araba, daga Elat daga kuma Eziyon Gebar. Daganan muka juya muka kuma ratsa ta jejin Mowab.
\s5
\v 9 Yahweh ya ce mani, 'Kada ku matsawa Mowab, kada kuma ku yi faɗa da su a yaƙi. Domin ba zan bayar da ƙasarsa ba a gare ku domin mallakar ku, saboda na bayar da Ar ga zuriyar Lutu, domin mallakar su,'
\s5
\v 10 (Emiyawa suka yi zama a wurin a dã, mutane manya, masu yawa, masu tsayi kuma kamar Anakimawa;
\v 11 su kuma waɗannan ana ɗaukar su 'yan Refayim, kamar Anakimawa; amma Mowabawa suna kiransu Emiyawa.
\s5
\v 12 Horitawa su kuma sun yi zama a Seyir a dã, amma zuriyar Isuwa suka gaje su. Suka hallakar da su a gabansu suka kuma zauna a wurin su, kamar yadda Isra'ila ya yi da ƙasar mallakarsa wadda Yahweh ya basu.)
\s5
\v 13 Yanzu ku tashi ku tafi tsallaken kwarin Zered.' Sai muka tafi tsallaken rafin Zered.
\v 14 Yanzu daga kwanakin da muka zo daga Kadesh Barniya har muka ketare rafin Zered, shekaru talatin da takwas ne. A wannan lokacin ne dukkan tsarar mazajen da suka isa yaƙi aka kawar da su daga mutanen, kamar yadda Yahweh ya rantse masu.
\v 15 Haka nan kuma, hannun Yahweh ya yi gãba da wannan tsara domin a lalatar da su daga mutanen har sai da suka ƙare.
\s5
\v 16 Sai ya kasance, sa'ad da dukkan mazajen da suka isa yaƙi suka mutu suka kuma ƙare daga cikin mutanen,
\v 17 sai Yahweh ya yi magana da ni, cewa,
\v 18 'A yau ne zaku ƙetare Ar, kan iyakar Mowab.
\v 19 Sa'ad da kuka zo kusa daura da mutanen Ammon, kada ku matsa masu ko ku yi yaƙi da su; gama ba zan baku ko ɗaya daga cikin ƙasar mutanen Ammon ba a matsayin mallaka; saboda na bayar da ita ga zuriyar Lutu a matsayin mallaka."'
\s5
\v 20 (Wannan ita ma an ɗauke ta ƙasar Refayim. Refayim ne suka yi zama a wurin a dã - amma Ammoniyawa suna kiransu Zamzumiyawa -
\v 21 mutane manya, masu yawa, masu tsayi kuma kamar Anakimawa. Amma Yahweh ya hallakar da su a gaban Ammoniyawa, suka kuma gaje su suka zauna a wurin su.
\v 22 Wannan kuma Yahweh ya yi domin mutanen Isuwa, waɗanda ke zaune a Seyir, da ya hallakar da Horinawa a gabansu, zuriyar Isuwa kuma suka gaje su suka zauna a wurin su har ya zuwa yau.
\s5
\v 23 Amma game da Abibiyawa waɗanda ke zaune a ƙauyuka har nesa zuwa Gaza, Kaftorimawa, waɗanda suka zo daga Kafto, suka hallakar da su suka zauna a wurin su.)
\s5
\v 24 Yanzu ku tashi, ku kama tafiyarku, ku kuma ratsa ta kwarin Arnon; duba, Na bayar cikin hannunku Sihon Ba'amoriye, sarkin Heshbon, da ƙasarsa. Ku fara mallakarta, ku kuma yi faɗa da shi a yaƙi.
\v 25 A yau zan fara sanya tsoronku da fargabanku a bisa mutanen da ke dukkan ƙarƙashin sama; zasu ji labari game da ku zasu kuma yi rawar jiki su kuma kasance cikin ƙunci sabili da ku.'
\s5
\v 26 Na aika da manzanni daga jejin Kedemot ga Sihon, sarkin Heshbon, da maganar salama, cewa,
\v 27 Bari in ratsa ta cikin ƙasarka; zan bi ta kan titi; bazan juya ko zuwa hannun dama ba ko zuwa na hagu.
\s5
\v 28 Za ka sayar mani da abinci domin kuɗi, saboda in ci; ka bani ruwa domin kuɗi, saboda in sha; ka dai bar ni kawai in ratsa ta ciki bisa sawaye na;
\v 29 kamar zuriyar Isuwa da ke zaune a Seyir, da Mowabawa da ke zaune a Ar; har sai na ketare Yodan zuwa cikin ƙasar da Yahweh Allahnmu ya ke bamu.'
\s5
\v 30 Amma Sihon, sarkin Heshbon, ba zai barmu mu ratsa ta wurinsa ba; domin Yahweh Allahnku ya taurare tunaninsa ya kuma sa zuciyarsa ta kafe, domin ya kayar da shi ta wurin ƙarfinku, wanda yanzu ya yi shi a yau.
\v 31 Yahweh ya ce mani, 'Duba, Na fara miƙa Sihon da ƙasarsa a gaban ku; ku fara mallakar ta, domin ya zama kun gaji ƙasarsa.'
\s5
\v 32 Daganan Sihon ya fito gãba da mu, shi da dukkan mutanensa, su yi faɗa a Yahaz.
\v 33 Yahweh Allahnmu ya bayar da shi a gare mu muka kuma kayar da shi da 'ya'yansa maza da dukkan mutanensa.
\s5
\v 34 Muka ɗauki dukkan biranensa a wancan lokaci muka kuma hallakar da kowanne birni ɗungum - maza da mata da ƙanana; bamu bar mai tsira ba.
\v 35 Garken dabbobi ne kawai muka ɗauka a matsayin ganima domin mu, tare da ganimar biranen da muka ɗauka.
\s5
\v 36 Daga Arowa, wadda ke gefen kwarin Arnon, daga kuma birnin da ke cikin kwarin, dukkan hanya har Giliyad, babu birnin da ya fi ƙarfin mu. Yahweh Allahnmu ya bayar da su cikin hannuwanmu.
\v 37 Ƙasar zuriyar Ammon ce kawai baku je ba, har ma dukkan gefen kogin Yabbok, da biranen ƙasar tudu - kowanne wurin da Yahweh Allahnmu ya hana mu zuwa.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Daga nan muka juya muka tafi hanyar Bashan. Og, sarkin Bashan, yazo kuma ya kawo mana hari, shi da dukkan mutanensa, ya yi faɗa a Edrai.
\v 2 Yahweh ya ce mani, "Kada ka ji tsoronsa; gama na baka nasara a kansa kuma na sanya dukkan mutanensa da ƙasarsa a ƙarƙashin mulkinka. Zaka yi masa yadda kayi wa Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda ya zauna a Heshbon.'
\s5
\v 3 Sai Yahweh Allahnmu ya bamu nasara a bisa Og sarkin Bashan, dukkan mutanensa kuma aka sanya su ƙarƙashin mulkinmu. Muka fyaɗe su har ba ko ɗaya daga cikin mutanensa da ya rage.
\v 4 Muka ɗauki dukkan biranensa a wancan lokaci. Babu ko ɗaya daga cikin biranen nan sittin da bamu karɓe ba daga gare su - dukkan lardin Argob, masarautar Og a Bashan.
\s5
\v 5 Dukkan waɗannan birane tsararru ne da dogayen ganuwoyi, ƙofofi, da ƙarafuna; waɗannan kuwa baya ga ƙauyuka marasa ganuwa masu yawan gaske.
\v 6 Muka hallakar da su ɗungum, kamar yadda muka yi da Sihon sarkin Heshbon, muka hallakar da kowanne birni ɗungum - maza da mata da ƙanana.
\v 7 Amma dukkan garken dabbobin da ganimar biranen, muka ɗauka a matsayin ganima domin mu.
\s5
\v 8 A wannan lokacin muka ɗauke ƙasar daga hannun sarakunan Amoriyawa biyu, waɗanda ke ƙetaren Yodan, daga kwarin Arnon zuwa dutsen Hamon
\v 9 (Sidoniyawa na kiran dutsen Hamon Siriyon, Amoriyawa kuma na kiran sa Senir)
\v 10 da dukkan biranen sarari, dukkan Giliyad, da dukkan Bashan, har ya zuwa Saleka da Edrai, biranen masarautar Og a Bashan."
\s5
\v 11 (Game da ragowar Refayim, Og sarkin Bashan ne kaɗai ya rage. Duba! gadonsa gadon ƙarfe ne. Ba yana a Rabba ba, inda zuriyar Ammon suka zauna? tsawonsa kamu tara ne fãɗinsa kuma kamu huɗu, bisa ga yadda mutane ke gwaji.)
\s5
\v 12 Wannan ƙasa muka ɗauka mallaka a wannan lokaci - daga Arowa, wato ta gefen kwarin Arnon, da rabin ƙasar tudu ta Giliyad, da biranenta - Na bayar ga Rubenawa ga kuma Gadanawa.
\v 13 Sauran Giliyad da dukkan Bashan, masarautar Og, Na bayar ga rabin kabilar Manasse. (Dukkan lardin Argob, da dukkan Bashan. Wannan gundumar ce ake kira ƙasar Refayim.
\s5
\v 14 Yayir, wata zuriyar Manasse, suka ɗauki dukkan lardin Argob zuwa kan iyakar Geshurawa da Ma'akatawa. Ya kira lardin, wato Bashan, da sunansa, Habbot Yayir, har ya zuwa yau.)
\s5
\v 15 Na bayar da Giliyad ga Makir.
\v 16 Ga Rubenawa ga kuma Gadawa na bayar da gunduma daga Giliyad zuwa kwarin Arnon - tsakiyar kwarin shi ne kan iyakar gundumar - zuwa kuma kogin Yabbok, wanda ke kan iyaka tare da zuriyar Ammon.
\s5
\v 17 Wasu kan iyakokinta kuma su ne sararin kwarin Kogin Yodan, daga Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri) zuwa gangarowar Dutsen Fisga maso gabas.
\s5
\v 18 Na dokace ku a wancan lokaci, cewa, 'Yahweh Allahnku ya baku wannan ƙasa ku mallake ta; ku, dukkan ku mazajen yaƙi, zaku ƙetare shirye da makamai a gaban 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila.
\s5
\v 19 Amma matayenku, da ƙanananku, da garken dabbobinku (nasan kuna da garken dabbobi masu yawa), zasu tsaya a biranen da na baku,
\v 20 har sai Yahweh ya bayar da hutawa ga 'yan'uwanku, kamar yadda ya yi a gare ku, har su ma sai sun mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ke bayarwa a gare su a ƙetaren Yodan; daganan za ku dawo, kowanne mutum a cikinku, ga kaddararku da na bayar a gare ku.'
\s5
\v 21 Na dokaci Yoshuwa a wancan lokacin, cewa, 'Idanunka sun ga dukkan abin da Yahweh Allahnka ya yi ga waɗannan sarakuna biyu; Yahweh zai yi irin haka ga dukkan masarautun da za ku je a ƙetare.
\v 22 Ba za ku ji tsoronsu ba, gama Yahweh Allahnku shi ne zai yi yaƙi dominku.'
\s5
\v 23 Na yi roƙo da naciya ga Yahweh a wancan lokaci, cewa,
\v 24 'Ya Ubangiji Yahweh, ka fãra nuna wa bawanka girmanka da ƙarfin hannunka; gama wanne allah ne a sama ko a duniya da zai yi irin ayyukan da ka aiwatar, kuma dai-dai irin manyan ayyukan?
\v 25 Ka barni in ƙetare, na roƙe ka, in kuma kalli ƙasar mai kyau da ke ƙetaren Yodan, wannan ƙasar tudu mai kyau, da kuma Lebanon.'
\s5
\v 26 Amma Yahweh ya yi fushi da ni saboda ku; bai saurare ni ba. Yahweh ya ce mani, 'Bari wannan ya ishe ka - kada ka ƙara yi mani magana game da wannan al'amari:
\v 27 ka hau zuwa ƙwalƙolin Fisga ka kuma ɗaga idanunka zuwa yamma, zuwa arewa, zuwa kudu, da zuwa gabas; ka duba da idanunka, domin ba zaka je ƙetaren Yodan ba.
\s5
\v 28 A maimakon haka, ka umarci Yoshuwa ya ƙarfafa ka kuma ƙarfafashi, gama zai shiga gaban waɗannan mutane ya ƙetare, zai kuma sa su gãji ƙasar da za ka gani.'
\v 29 Sai muka tsaya a kwari daura da Bet Feyo.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Yanzu, Isra'ila, ku saurari shari'o'i da dokoki da nake gab da koya maku, ku aikata su; saboda ku rayu ku kuma shiga ku kuma mallaki ƙasar da Yahweh, Allah na ubanninku, ya ke baku.
\v 2 Ba zaku ƙara bisa ga maganganun dana umarce ku ba, ko kuma ku rage su, saboda ku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku wanda na ke gab da umartar ku.
\s5
\v 3 Idanunku sun ga abin da Yahweh ya yi saboda Ba'al Feyo; domin dukkan mutanen da suka bi Ba'al na Feyo; Yahweh Allahnku ya lalatar da su a tsakaninku.
\v 4 Amma ku da kuka manne wa Yahweh Allahnku kuna raye a yau, kowannen ku.
\s5
\v 5 Duba, na koya maku shari'u da dokoki, kamar yadda Yahweh Allahna ya umarce ni, cewa kuyi haka a tsakiyar ƙasa inda kuke tafiya ciki domin ku mallake ta.
\v 6 Saboda haka ku kiyaye su ku kuma aikata su; domin wannan shi ne hikimarku da fahimtarku a idanun mutanen da zasu ji dukkan waɗannan farillai su kuma ce, 'Tabbas wannan babbar al'umma mutane ne masu hikima da fahimta.'
\s5
\v 7 Gama wacce al'umma ce da suke da allah da ke kusa da su sosai, kamar yadda Yahweh Allahnmu ya ke a duk sa'ad da muka yi kira a gare shi?
\v 8 Wacce babbar al'umma ce da ke nan da take da shari'u da dokoki masu adalci sosai kamar dukkan shari'a da nake shiryawa a gaban ku a yau?
\s5
\v 9 Kawai dai ku lura ku kuma jagoranci kanku a hankali, domin kada ku manta da abin da idanunku suka gani, saboda kada su bar zukatanku domin dukkan kwanakin rayuwarku. A maimakon haka, ku sanar da su ga 'ya'yanku da 'ya'yan 'ya'yanku.
\v 10 A ranar da kuka tsaya a gaban Yahweh Allahnku a Horeb, sa'ad da Yahweh ya ce mani, 'Ka tattara mani mutanen, zan kuma sa su su ji maganganuna, domin su koyi jin tsorona dukkan kwanakin da suke raye a duniya, domin kuma su koyawa 'ya'yansu.'
\s5
\v 11 Kuka zo kusa kuka tsaya a gindin dutsen. Dutsen na ƙonewa da wuta har tsakiyar sama, tare da duhu, girgije, da duhu mai kauri.
\v 12 Yahweh ya yi magana daku daga cikin tsakiyar wuta; kuka ji muryar tare da maganganunta, amma baku ga wata siffa ba; murya kaɗai kuka ji.
\s5
\v 13 Ya furta maku alƙawarinsa da ya umarceku ku aikata, Dokoki goma. Ya rubuta su a allunan duwatsu biyu.
\v 14 Yahweh ya dokace ni a wannan lokaci da in koya maku farillai da shari'u, saboda ku aikata su a cikin ƙasar da kuke ƙetarawa ku ɗauki mallaka.
\s5
\v 15 Saboda haka ku yi hankali da kanku - domin baku ga wata siffa ba a ranar da Yahweh ya yi magana daku a Horeb daga tsakiyar wuta -
\v 16 domin kada ku lalata kanku ta wurin yin sassaƙaƙƙen siffa bisa ga siffar wani abu, a cikin kamannin namiji ko mace,
\v 17 a cikin kamannin kowacce irin dabba a duniya, kamannin kowanne irin tsuntsu mai fukafukai da ke shawagi a sammai,
\v 18 kamannin kowanne irin abu da ke rarrafe a bisa ƙasa, ko kamannin kowanne irin kifi da ke cikin ruwa a ƙarƙashin duniya.
\s5
\v 19 Ba zaku ɗaga idanunku zuwa sammai ba ku dubi rana, wata, ko taurari ba - dukkan rundunar sammai - kuma ku janye zuwa yi masu sujada ku kuma girmama su - waɗannan abubuwa waɗanda Yahweh Allahnku ya bada kaso ga dukkan mutanen ƙarƙashin sararin sama baki ɗaya.
\v 20 Amma Yahweh ya ɗauko ku ya kawo ku kuma daga tanderun ƙarfe, daga Masar, ku zama a gare shi mutanen gãdonsa, kamar yadda kuke a yau.
\s5
\v 21 Yahweh yaji haushina saboda ku; ya yi rantsuwa cewa bazan ƙetare Yodan ba, da cewa kada in tafi cikin wannan ƙasa mai kyau, ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke bayarwa a gare ku a matsayin gãdo.
\v 22 A maimako, tilas in mutu a wannan ƙasa; tilas ba zan tafi ƙetaren Yodan ba; amma ku zaku ƙetare ku kuma mallaki ƙasar mai kyau.
\s5
\v 23 Ku lura da kanku, domin kada ku manta da alƙawarin Yahweh Allahnku, wanda ya yi tare daku, ku kuma yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa a cikin siffar wani abu wanda Yahweh Allahnku ya hanaku ku yi.
\v 24 Gama Yahweh Allahnku wuta ne mai lanƙwamewa, Allah ne mai kishi.
\s5
\v 25 Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya da 'ya'yan 'ya'ya, sa'ad da kuma kuka kasance a ƙasar na dogon lokaci, idan kuma kuka lalata kanku kuka kuma yi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa bisa ga siffar kowanne abu, kuka kuma aikata abin da ke na mugunta a idanun Yahweh Allahnku, domin ku tunzura shi zuwa fushi -
\v 26 na kira sama da duniya suyi shaida gãba da ku a yau cewa ba da daɗewa ba zaku lalace daga ƙasar da kuke ƙetare Yodan domin ku mallaka; ba zaku tsawonta kwanakinku ba a cikin ta, amma ɗungum zaku rushe.
\s5
\v 27 Yahweh zai warwatsa ku cikin mutane, kuma zaku zama 'yan kaɗan a cikin al'ummai, inda Yahweh zai aika da ku.
\v 28 A can zaku yi bautar wasu alloli, ayyukan hannuwan mutane, katako da dutse, waɗanda basu gani, ji, ci, ko sunsunawa.
\s5
\v 29 Amma daga can zaku biɗi Yahweh Allahnku, kuma zaku same shi, sa'ad da kuka neme shi da dukkan zuciyarku da dukkan ranku.
\s5
\v 30 Sa'ad da kuke cikin ƙunci, sa'ad da kuma dukkan waɗannan abubuwa suka zo kanku, cikin waɗannan kwanakin ƙarshe zaku dawo ga Yahweh Allahnku kuma ku saurari muryarsa.
\v 31 Gama Yahweh Allahnku Allah ne cike da jinƙai; ba zai gaza maku ba ko ya rusa ku, ko kuwa ya manta da alƙawarin ubanninku wanda ya rantse masu.
\s5
\v 32 Ku yi tambaya yanzu game da kwanakin da suka wuce, waɗanda suke kafin lokacinku, tun ranar da Allah ya halitta mutum a duniya, ku yi tambaya daga ƙarshen sama zuwa ɗaya ƙarshen sama, ko an taɓa yin wani abu babba kamar wannan, ko an taɓa jin wani abu kamar wannan?
\v 33 Ko an taɓa yin wasu mutane da suka ji muryar Allah na magana daga cikin wuta, kamar yadda kuka ji, kuka kuma rayu?
\s5
\v 34 Ko kuwa Allah ya taɓa ɗaukar wani mataki yaje ya ɗaukarwa kansa al'umma daga cikin wata al'ummar, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu, da ta wurin al'ajibai, da ta wurin yaƙi, da ta wurin hannu mai ƙarfi, da ta wurin miƙaƙƙen damtse, da ta wurin babbar razana, kamar dukkan abin da Yahweh Allahnku ya yi domin ku a Masar a gaban idanunku?
\s5
\v 35 A gare ku aka nuna waɗannan abubuwa, saboda ku sani cewa Yahweh shi ne Allah, kuma da cewa babu wani baya gare shi.
\v 36 Daga sama ya sa kuka ji muryarsa, saboda ya umarce ku; a duniya ya sa kuka ga babbar wutarsa; kuka ji maganganunsa daga cikin tsakiyar wutar.
\s5
\v 37 Saboda yana ƙaunar ubanninku, ya zaɓi zuriyarsu bayansu, ya kuma fito daku daga Masar tare da bayyanuwarsa, tare da babban ikonsa;
\v 38 domin ya kore daga gabanku al'ummai da suka fi ku girma da ƙarfi, saboda ya kawo ku ciki, saboda ya baku ƙasarsu a matsayin gãdo, kamar a yau.
\s5
\v 39 Saboda haka ku sani a yau, ku kuma ajiye shi a zukatanku, cewa Yahweh shi ne Allah a sama can da duniya a ƙarƙashi; babu wani kuma.
\v 40 Zaku kiyaye farillansa da dokokinsa waɗanda ya dokace ku a yau, domin lafiya ta tafi tare da ku da 'ya'yanku a bayanku, saboda kuma ku tsawonta kwanakinku a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku har abada."
\s5
\v 41 Daganan Musa ya zaɓi birane uku daga sashen gabas da Yodan,
\v 42 saboda wani yana iya gudu zuwa ɗaya daga cikinsu idan ya kashe wani taliki cikin kuskure, wanda ba maƙiyinsa bane a dã. Ta wurin tserewa zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane, zai iya tsira.
\v 43 Su ne: Bezar a jeji, ƙasar sarari, domin Rubenawa; Ramot a Giliyad, domin Gadawa; da Golan a Bashan, domin Manasawa.
\s5
\v 44 Wannan ita ce shari'ar da Musa yasa a gaban mutanen Isra'ila;
\v 45 waɗannan ne dokokin alƙawari, shari'u, da sauran dokoki daya faɗi ga mutanen Isra'ila sa'ad da suka fito daga Masar,
\v 46 sa'ad da suke a gabas da Yodan, a kwari daura da Bet Feyo, a ƙasar Sihon, sarkin Amoriyawa, wanda ya zauna a Heshbon, wanda Musa da mutanen Isra'ila suka kayar sa'ad da suka fito daga Masar.
\s5
\v 47 Suka ɗauki ƙasarsa a matsayin mallaka, da ƙasar Og sarkin Bashan - waɗannan, sarakuna biyu na Amoriyawa, waɗanda ke ƙetaren Yodan zuwa gabas.
\v 48 Wannan gunduma ta tafi daga Arowa, a gaɓas Kwarin Arnon, zuwa Dutsen Sihiyona (ko Dutsen Hamon),
\v 49 ya kuma haɗa da dukkan sararin kwarin Kogin Yodan, maso gabas a ƙetaren Yodan, zuwa Tekun Araba, zuwa gangaren Dutsen Fisga.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Musa ya yi kira ga dukkan Isra'ila ya ce masu, "Ku saurara, Isra'ila, ga farillai da dokoki da zan faɗa cikin kunnuwanku a yau, domin ku koye su ku kuma kiyaye su.
\v 2 Yahweh Allahnmu ya yi alƙawari tare da mu a Horeb.
\v 3 Yahweh bai yi wannan alƙawari tare da kakanninmu ba, amma tare da mu, dukkan mu da muke a raye a nan a yau.
\s5
\v 4 Yahweh ya yi magana daku fuska da fuska a dutse daga tsakiyar wuta
\v 5 (na tsaya tsakanin Yahweh daku a wancan lokaci, in bayyana maku maganarsa; domin kuna jin tsoro saboda wutar, kuma baku hau zuwa tsaunin ba). Yahweh ya ce,
\v 6 'Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
\s5
\v 7 Ba za ku yi wasu alloli ba a gabana.
\v 8 Ba za kuyi wa kanku sassaƙaƙƙen siffa ba ko kamannin wani irin abu da ke sama can, ko da ke a duniya a ƙasa, ko da ke a cikin ruwa a ƙarƙashi.
\s5
\v 9 Ba zaku russuna masu ba ko ku bauta masu, domin Ni, Yahweh Allahnku, ni Allah ne mai kishi. Ina hukunta muguntar kakanni ta wurin sauko da hukunci bisa 'ya'yan, har zuwa tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni,
\v 10 da nuna alƙawarin aminci ga dubbai, ga waɗanda ke ƙaunata da kiyaye dokokina.
\s5
\v 11 Ba zaku ɗauki sunan Yahweh Allahnku ba a banza, gama Yahweh ba zai riƙe shi marar laifi ba shi wanda ya ɗauki sunansa a banza.
\s5
\v 12 Ka lura da ranar Asabaci ka kiyaye ta da tsarki, kamar yadda Yahweh Allahnka ya dokace ka.
\v 13 Gama cikin kwana shida zaka yi aikin ƙarfi kayi kuma dukkan ayyuka;
\v 14 amma rana ta bakwai Asabaci ce ga Yahweh Allahnka. A cikin ta ba za ka yi wani aiki ba - ban da kai, ko ɗanka, ko ɗiyarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko san ka, ko jakinka, ko wani daga cikin garken dabbobinka, ko wani baƙo daga cikin ƙofofinka. Wannan kuwa haka ne domin bawanka da baiwarka su huta kamar yadda za ka huta.
\s5
\v 15 Za ka tuna da cewa kaima bawa ne a ƙasar Masar, kuma Yahweh Allahnka ya fito da kai daga can da hannu mai ƙarfi da miƙaƙƙen damtse. Saboda haka Yahweh Allahnka ya dokace ka da ka kiyaye ranar Asabaci.
\s5
\v 16 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kamar yadda Yahweh Allahnka ya dokace ka kayi, domin ka zauna na dogon lokaci a cikin ƙasar da Yahweh Allahnka ya ke baka, domin kuma ya kasance lafiya tare da kai.
\s5
\v 17 Ba za kayi kisa ba.
\v 18 Ba zaka aikata zina ba.
\v 19 Ba zaka yi sata ba.
\v 20 Ba zaka bada shaidar zur ba gãba da maƙwabcinka.
\s5
\v 21 Ba zaka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ba zaka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba, ko gonarsa, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko wani abu da ke na maƙwabcinka.'
\s5
\v 22 Waɗannan maganganu Yahweh ya faɗi da babbar murya ga dukkan taronku a bisa dutse daga tsakiyar wuta, daga gizagizai, daga kuma duhu mai kauri; baiyi ƙarin wasu maganganu ba. Ya rubuta su bisa allunan dutse ya kuma bani su.
\s5
\v 23 Sai ya kasance, da kuka ji muryar daga tsakiyar duhu, yayin da dutsen ke ƙonewa, sai kuka zo kusa da ni - dukkan dattawanku da shugabannin kabilunku.
\v 24 Kuka ce, 'Duba, Yahweh Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da girmansa, kuma mun ji muryarsa daga tsakiyar wuta; mun gani a yau cewa sa'ad da Yahweh ya yi magana da mutane, za su iya rayuwa.
\s5
\v 25 Amma me yasa zamu mutu? gama wannan babbar wuta zata cinye mu; idan muka ƙara jin muryar Yahweh Allahnmu, zamu mutu.
\v 26 Gama banda mu wane ne a cikin nama da jini, ya taɓa jin muryar Allah mai rai daga tsakiyar wuta ya kuma rayu, kamar yadda muka yi?
\v 27 Game da kai, ka tafi ka saurari dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya ce; ka maimaita mana dukkan abin da Yahweh Allahnmu ya ce maka; zamu saurara kuma mu yi biyayya.'
\s5
\v 28 Yahweh yaji maganganunku sa'ad da kuka yi zance da ni. Ya ce mani, 'Na ji maganganun waɗannan mutane, abin da suka ce maka. Abin da suka ce mai kyau ne.
\v 29 Oh, ace ma akwai irin wannan zuciyar a cikinsu, cewa zasu girmama ni kuma koyaushe zasu kiyaye dokokina, domin ya tafi lafiya tare da su tare kuma da 'ya'yansu har abada!
\v 30 Ka je kace masu, "Ku koma rumfunanku."
\s5
\v 31 Amma game da kai, ka tsaya nan gefe na, zan kuma gaya maka dukkan dokokin, farillai, da shari'u da zaka koya masu, saboda su kiyaye su a cikin ƙasar da zan ba su su mallaka.'
\s5
\v 32 Saboda haka, zaku kiyaye, abin da Yahweh Allahnku ya dokace ku; ba zaku kauce ba zuwa hannun dama ko hagu.
\v 33 Zaku yi tafiya cikin dukkan hanyoyi da Yahweh Allahnku ya dokace ku, domin ku rayu, domin kuma ya tafi lafiya tare da ku, ku kuma tsawonta kwanakinku a cikin ƙasar da zaku mallaka.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Yanzu waɗannan ne dokoki, da farillai, da kuma shari'un da Yahweh Allahnku ya dokace ni in koya maku, domin ku kiyaye su a cikin ƙasar da kuke tafiya ƙetaren Yodan ku mallaka;
\v 2 saboda ku iya girmama Yahweh Allahnku, saboda ku kiyaye dukkan farillansa da dokokinsa waɗanda nake dokatarku a yau - ku, da 'ya'yanku, da 'ya'yan 'ya'yanku, dukkan kwanakin rayuwarku, saboda kwanakinku su yi tsawo.
\s5
\v 3 Saboda haka ku saurare su, Isra'ila, ku kuma kiyaye su, saboda ya tafi lafiya tare daku, saboda ku yi babbar ruɓanɓanya, a cikin ƙasar da ke malalowa da madara da zuma, kamar yadda Yahweh, Allah na ubanninku, ya yi maku alƙawari zai yi.
\s5
\v 4 Ku saurara, Isra'ila:
\v 5 Yahweh Allahnmu ɗaya ne. Zaku ƙaunaci Yahweh Allahnku tare da dukkan zuciyarku, tare da dukkan ranku, tare kuma da dukkan ƙarfinku.
\s5
\v 6 Maganganun da nake umartarku a yau za su kasance a zukatanku;
\v 7 da ƙwazo kuma zaku koyar da su ga 'ya'yanku; zaku yi magana game da su sa'ad da kuke zaune cikin gida, sa'ad da kuke tafiya akan hanya, sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.
\s5
\v 8 Za ku ɗaura su a matsayin alama a bisa hannunku, zasu kuma zama kamar 'yan goshi a tsakanin idanunku.
\v 9 Zaku rubuta su a ginshiƙan gidajenku da ƙofofinku.
\s5
\v 10 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya yi rantsuwa ga ubanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu, cewa zai baku, da birane manya-manya kyawawa da baku gina ba,
\v 11 da gidaje cike da dukkan abubuwa iri-iri masu kyau da baku yi ba, tankunan ruwa da baku gina ba, garkunan inabi da itatuwan zaitun da baku dasa ba, zaku ci ku ƙoshi -
\v 12 daganan ku lura saboda kada ku manta da Yahweh, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan ƙunci.
\s5
\v 13 Zaku girmama Yahweh Allahnku; shi ne zaku yi wa sujada, kuma zaku yi rantsuwa da sunansa.
\v 14 Ba zaku bi waɗansu alloli ba, allolin mutanen da suke kewaye daku kakaf -
\v 15 domin Yahweh Allahnku da ke tsakiyarku Allah ne mai kishi - idan kuka yi, fushin Yahweh Allahnku zai kunnu gãba daku kuma zai hallakar daku daga fuskar duniya.
\s5
\v 16 Ba zaku gwada Yahweh Allahnku ba kamar yadda kuka gwada shi a Massa.
\v 17 Zaku yi ƙwazo ku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku, dokokinsa natsastsu, da farillansa, waɗanda ya dokace ku.
\s5
\v 18 Zaku yi abin da ke dai-dai mai kyau kuma a idanun Yahweh, saboda ya kasance lafiya a gare ku, ku kuma iya zuwa ku mallaki ƙasa mai kyau da Yahweh ya rantse wa ubanninku,
\v 19 ya kori dukkan maƙiyanku daga gare ku, kamar yadda Yahweh ya faɗa.
\s5
\v 20 Sa'ad da ɗanku ya tambaye ku a lokaci mai zuwa, cewa, 'Waɗanne ne dokokin alƙawari da farillai da sauran dokoki da Yahweh Allahnmu ya umarce ku?
\v 21 daganan zaku cewa ɗanku, 'Mu bayin Fir'auna ne a Masar; Yahweh ya fito da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi,
\v 22 ya kuma aiwatar da alamu, da al'ajibai, manya masu tsanani, a bisa Masar, a bisa Fir'auna, a kuma bisa dukkan gidansa, a gaban idanunmu;
\v 23 ya kuma fito da mu daga wurin, saboda ya kawo mu ciki, ya ba mu ƙasar da ya rantse wa ubanninmu.
\s5
\v 24 Yahweh ya dokace mu da a koyaushe mu kiyaye waɗannan farillai, mu ji tsoron Yahweh Allahnmu domin kyaunmu, domin ya iya kiyaye mu a raye, kamar yadda muke a yau.
\v 25 Idan muka kiyaye dukkan waɗannan dokoki a gaban Yahweh Allahnmu, kamar yadda ya dokace mu, wannan ne zai zama adalcinmu.'
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Lokacin da Yahweh Allahnku ya kawo ku zuwa ƙasar da kuke shiga domin ku mallake ta, za ya kori al'ummai masu yawa - su Hittiyawa, da Girgashawa da Amoriyawa da Kan'aniyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa da kuma Yebusawa - al'ummai guda bakwai masu girma da ƙarfi fiye da ku.
\s5
\v 2 Yahweh Allahnku ne ya miƙa su cikin hannunku lokacin da kuka ci su da yaƙi, haka nan kuma dole ne ku hallaka su dukka. Ba zaku ɗauki alƙawari da su ba, kada kuma ku nuna masu jinƙai.
\v 3 Kada kuma ku shirya aurayya da su. Ba zaku miƙa 'ya'yanku mata aure ga 'ya'yansu maza ba, kuma ba zaku ɗauko 'ya'yansu mata domin 'ya'yanku maza ba.
\s5
\v 4 Gama zasu juyar da hankalin 'ya'yanku maza daga bina, domin su yi sujada ga wasu alloli. Da haka fushin Yahweh za shi yi ƙuna gãba daku, kuma za ya hallaka ku da sauri.
\v 5 Ga yadda zaku yi da su: Zaku rushe har ƙasa bagadansu, ku farfashe umudansu, ku datse Asherim da mazamninta, ku kuma ƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.
\s5
\v 6 Gama ku al'umma ce da aka keɓe ga Yahweh Allahnku. Ya zaɓe ku ku zama mutane domin ya mallaka, gaba da dukkan sauran mutanen da ke fuskar duniya.
\s5
\v 7 Yahweh bai ɗora ƙaunarsa bisanku ko ya zaɓe ku domin kun fi sauran mutane yawa bane - gama kun zama ƙalilan cikin dukkan mutane -
\v 8 amma domin ya ƙaunace ku, kuma yana kiyaye alƙawarinsa da ya yi wa ubanninku. Wannan shi ne dalilin da yasa Yahweh ya fito daku da hannu mai girma ya kuma fanshe ku daga gidan bauta, daga hannun Fir'auna, sarkin Masar.
\s5
\v 9 Saboda haka ku san cewa Yahweh Allahnku - shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alƙawari da kuma aminci ga dubban tsararraki da waɗanda suke ƙaunarsa suna kuma kiyaye dokokinsa,
\v 10 amma yana saka wa waɗanda suka ƙi shi a fuskarsu, domin ya hallaka su; ba za ya tausaya wa duk wanda ya ƙi shi ba; zai yi masa sakamako yana ji yana gani.
\v 11 Don haka zaku kiyaye dokoki, da farillai, da kuma umarnai dana dokace ku yau, domin ku aikata su.
\s5
\v 12 Idan kuka saurari waɗannan umarnai, kuka kiyaye ku kuma aikata su, za shi zama kuma Yahweh Allahnku za ya kiyaye ku da alƙawari da kuma amincin da ya rantse wa ubanninku.
\v 13 Za ya ƙaunace ku, ya albarkace ku, ya kuma riɓanɓanya ku; za ya kuma albarkaci 'ya'yan jikinku da kuma na ƙasarku, hatsinku, da sabuwar inabinku, da kuma mai da ke naku, da ƙaruwar garkunanku da 'ya'yan garkunanku, a cikin ƙasan da ya rantse wa ubanninku zai baku.
\s5
\v 14 Zaku yi albarka fiye da dukkan sauran mutane; ba za a samu bakararre ko bakararriya cikinku ba ko a cikin garkunanku.
\v 15 Yahweh zai ɗauke dukkan ciwo daga gare ku; babu ko ɗaya daga cikin mugayen cututtuka na Masarawa da kuka sani da zai sa a bisanku, amma zai sa su bisa dukkan waɗanda suka ƙi ku.
\s5
\v 16 Zaku hallaka dukkan mutanen da Yahweh Allahnku za ya bada su cikin hannunku, kuma idanunku ba zasu tausaya masu ba. Kada ku yi sujada ga allolinsu, gama wannan tarko ne a gare ku.
\s5
\v 17 Idan kun ce cikin zuciyarku, 'Waɗannan al'ummai sun sha ƙarfinmu da yawa; yaya zan ci ƙarfinsu in kore su?' -
\v 18 kada ka ji tsoronsu; ka tuna da abin da Yahweh ya yi ma Fir'auna da dukkan Masarawa;
\v 19 anobai masu girma da idanuwanka suka gani, alamu, da al'ajibai, hannu mai ƙarfi, da kuma miƙaƙƙiyar hannu wadda Yahweh Allahnku ya fito daku. Yahweh zai yi haka kuma ga dukkan mutanen da kuke tsoron su.
\s5
\v 20 Bayan wannan kuma, Yahweh Allahnku zai aika zirnaƙo a cikinsu, har sai duk waɗanda suka rage da waɗanda suka ɓoye kansu daga gare ku sun hallaka daga fuskarku.
\v 21 Ba zaku razana ta dalilinsu ba, gama Yahweh Allahnku na cikinku, Allah mai girma mai ban razana.
\v 22 Yahweh Allahnku zaya kori waɗannan al'ummai daga gabanku kaɗan-kaɗan. Ba zaku iya hallaka su dukka a lokaci ɗaya ba, don kada namomin jeji su yi yawa kewaye daku.
\s5
\v 23 Amma Yahweh Allahnku zaya baku nasara bisansu sa'ad da kuka gamu da su a dagar yaƙi; za ya rikitar da su matuƙa har sai sun lalace sarai.
\v 24 Za ya sanya sarakunansu a ƙalƙashin ikonku, kuma zaku sa sunansu ya hallaka daga doron ƙasa. Babu wanda zaya iya tsayayya daku, har sai kun hallaka su sarai.
\s5
\v 25 Zaku ƙona sassaƙaƙƙun siffofin allolinsu - kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da ta dalaye su ku kuma ɗauke ta domin amfaninku, don in kun yi haka, zai zama tarko gare ku - gama abin kyama ne ga Yahweh Allahnku.
\v 26 Ba zaku kawo kowanne ƙazamtaccen abu cikin gidanku ba har da zaku yi masa sujada. Amma zaku yi matuƙar ƙyama ku kuma tsane su, gama keɓaɓɓe ne domin hallakarwa.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Dole ku kiyaye dukkan dokokin da nake baku yau, domin ku rayu ku kuma riɓaɓɓanya, ku kuma fita ku mallaki ƙasar da Yahweh ya rantse ga ubanninku.
\v 2 Zaku tuna da dukkan hanyoyin da Yahweh Allahnku ya bi daku waɗannan shekaru arba'in cikin jeji, domin ya ɗauke girman kai daga gare ku, domin ya gwada ku ya kuma san mene ne ke cikin zuciyarku, ko zaku kiyaye dokokinsa ko a'a.
\s5
\v 3 Ya ɗauke girman kanku, ya sa kun ji yunwa, ya kuma ciyar daku da manna, wadda ba ku taɓa sani ba wadda kuma ubanninku ba u sani ba. Ya yi haka ne domin ya koya maku da cewa bada gurasa kaɗai mutane ke rayuwa ba; sai dai, ta kowacce abin da ke fitowa daga bakin Yahweh mutane ke rayuwa.
\s5
\v 4 Tufafinku basu koɗe su kuma faɗi daga jikinku ba, kuma sawayenku basu kumbura cikin shekarun nan arba'in ba.
\v 5 Zaku yi tunani cikin zuciyarku, ta yaya, kamar yadda mutum ke horon ɗansa, haka Yahweh Allahnku ya ke horonku.
\v 6 Zaku kiyaye dokokin Yahweh Allahnku, domin ku yi tafiya cikin tafarkunsa ku kuma girmama shi.
\s5
\v 7 Gama Yahweh Allahnku yana kawo ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka, da ɓulɓulai da zurfafa da masu gangarowa daga tuddai, suna gudu zuwa cikin kwarurrukai da tuddai;
\v 8 ƙasa mai alkama da bali, na inabi, itacen ɓaure, dana rumana; ƙasar da akwai man zaitun da kuma zuma.
\s5
\v 9 ́Ƙasa ce inda zaku ci gurasa babu rashi, kuma inda zaku tafi ba da rashin komai ba; ƙasa wadda duwatsunta tama ce, kuma daga cikin tsaunukanta kana iya haƙa jan ƙarfe.
\v 10 Zaku ci ku kuma ƙoshi, ku kuma albarkaci Yahweh Allahnku domin ƙasa mai kyau da ya baku.
\s5
\v 11 Ku kula kada ku manta da Yahweh Allahnku, kuma kada kuyi banza da dokokinsa, farillansa, da umurnansa da nake dokace ku yau,
\v 12 in ba haka ba, lokacin da kuka ci kuka kuma ƙoshi, kuka kuma gina gidaje kuka kuma zauna cikinsu, zuciyarku za ta yi kumburi.
\s5
\v 13 Ku kula sa'ad da garkunanku na shanu dana tumaki suka ƙaru kuma lokacin da azurfanku da zinariyarku suka ƙaru, da dukkan mallakarku suka yawaita,
\v 14 sai zuciyarku ta kumbura har ku manta da Yahweh Allahnku, wanda ya fito daku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
\s5
\v 15 Kada ku manta da shi wanda ya bishe ku ta cikin jeji babba da mai ban-razana, tare da macizai masu masifa da kunamai da ƙasa mai ƙishi inda babu ruwa, wanda ya fito maku da ruwa daga dutse fa.
\v 16 Ya ciyas da ku cikin jeji da manna abin da ubanninku basu taɓa sanin ta ba, domin ya ɗauke fahariya daga gare ku ya kuma gwada ku, domin ya yi maku alheri a ƙarshe,
\v 17 amma zaku ce a zuciyarku, 'Ai ƙarfina ne da ikon hannuna ne suka bani wannan dukkan dukiyar.'
\s5
\v 18 Amma zaku tuna da Yahweh Allahnku, domin shi ne ke baku iko don ku wadata; domin ya kafa alƙawarinsa da ya yi wa ubanninku, kamar yadda ya ke a yau.
\v 19 Haka za shi zama, idan zaku manta da Yahweh Allahnku ku kuma bi wasu alloli, kuyi masu sujada, ku kuma girmamasu, nayi shaida gãba daku yau da cewa zaku hallaka.
\v 20 Kamar al'ummai da Yahweh ke sasu hallaka a gaban ku, haka kuma zaku hallaka, domin kun ƙi ku saurari muryar Yahweh Allahnku.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Ku saurara, Isra'ila; kuna gab da ƙetare Yodan yau, ku shiga ciki ku kaɓantar da al'ummai waɗanda suka fi ku girma da kuma ƙarfi, da kuma birane ƙarfafa da ganuwa na tsaro da ke kaiwa har sama,
\v 2 mutane masu girma da tsawo, 'ya'yan Anakim, waɗanda kuka sani, kuma waɗanda kuka ji mutane ke cewa game da su, 'Waye zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?'
\s5
\v 3 Saboda haka yau ku sani cewa Yahweh Allahnku shi ne wanda ya ke tafiya a gabanku kamar wuta mai cinyewa; zaya hallakar da su, kuma zaya ci ƙarfinsu a gabanku; da haka zaku kore su ku kuma sasu hallaka da sauri, kamar yadda Yahweh ya gaya maku.
\s5
\v 4 Kada ku faɗi a zuciyarku, bayan da Yahweh Allahnku ya ture su waje a gabanku, 'Saboda adalcina ne Yahweh ya kawo ni ciki domin in mallaki wannan ƙasa; gama sabili da muguntar waɗannan al'ummai ne yasa Yahweh ya ke korarsu a gabanku.
\s5
\v 5 Ba saboda adalcinku ko dai-daituwa ta zuciyarku ne yasa zaku shiga ku mallaki ƙasarsu ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne yasa Allahnku ke koran su waje daga gabanku, kuma domin ya cika maganarsa da ya rantse wa ubanninku, ga Ibarahim, da Ishaku, da kuma Yakubu.
\s5
\v 6 Don haka ku san cewa, Yahweh Allahnku ba yana baku wannan ƙasa mai kyau domin ku mallake ta don adalcin ku bane, gama ku mutane ne masu taurin zuciya.
\s5
\v 7 Ku tuna kada kuma ku manta yadda kuka tozarta Yahweh Allahnku ga fushi a cikin jeji; daga ranar da kuka baro ƙasar Masar har kuka iso wannan ƙasa, kun yi ta tayarwa gãba da Yahweh.
\v 8 Haka ma a Horeb kuka tozarta Yahweh ga fushi, har Yahweh ya yi fushin da har zai iya hallaka ku.
\s5
\v 9 Da na tafi kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, alluna na alƙawarin da Yahweh ya yi da ku, na zauna a dutsen har kwanaki arba'in da dare arba'in; ban ci gurasa ba ban kuma sha ruwa ba.
\v 10 Yahweh ya ba ni allunan dutse guda biyu da ya yi rubutu da yatsansa; a cikinsu kuma aka rubuta dukkan maganganun da Yahweh ya shaida maku a kan dutse daga cikin tsakiyar wuta a ranan taro.
\s5
\v 11 Haka ya zama a ƙarshen waɗannan yini arba'in da dare arba'in da Yahweh ya bani allunan duwatsu guda biyu, alluna na alƙawari.
\v 12 Yahweh ya ce da ni, 'Tashi, sauka ƙasa da sauri daga nan, gama mutanen ka, waɗanda ka fito da su daga Masar, sun ƙazamtar da kansu. Sun yi hamzari daga juyawa daga tafarkin dana dokace su. Sun yi ma kansu sassaƙaƙƙen siffa.'
\s5
\v 13 Gaba da wannan, Yahweh ya yi mani magana ya ce, 'Na ga waɗannan mutanen; mutane ne masu taurin zuciya.
\v 14 Ka bar ni, don in hallaka su in shafe sunansu daga ƙarƙashin sama, sai kuma in maishe ka al'umma mafi ƙarfi da girma fiye da su.'
\s5
\v 15 Sai na juya na kuma sauko daga dutsen, dutsen kuma na ci da wuta. Allunan alƙawari guda biyu a cikin hannuwana.
\v 16 Sai na duba, ai kuwa, kun rigaya kun saɓa wa Yahweh Allahnku. Kun yi wa kanku siffar gumaka. Kun juya da sauri daga tafarkin da Yahweh ya dokace ku.
\s5
\v 17 Sai na ɗauko alluna biyun na jefar da su daga hannuwana. Na karya su a idanunku.
\v 18 Sai na sake kwantawa da fuska a ƙasa a gaban Yahweh yini arba'in da dare arba'in; ban ci ko burodi ko in sha ruwa ba, saboda zunubinku da kuka yi, na aikata abin da ke na mugunta a gaban Yahweh, domin ku tozarta shi ga fushi.
\s5
\v 19 Gama na ji tsoron fushi da rashin jin daɗi mai zafi irin wadda Yahweh ya yi gãba daku da ya isa har ya hallaka ku. Amma Yahweh ya saurare ni a wannan lokaci kuma.
\v 20 Yahweh ya yi matuƙar fushi da Haruna har da zai hallaka shi; Na yi ma Haruna addu'a shi ma a wannan sa'a.
\s5
\v 21 Na ɗauki zunubinku, siffar ɗan maraƙin da kuka yi, na ƙone shi, na tattake shi, na kuma niƙa su gaba ɗaya, har ya zama kamar ƙura. Na zubas da ƙurar cikin rafin da ke gangarowa daga dutsen.
\s5
\v 22 A Tabera, a Massa, da kuma Kibrot Hatta'aba, kuka cakuni Yahweh ya fusata.
\v 23 Lokacin da Yahweh ya aike ku daga Kadesh Barniya ya kuma ce, 'Ku haura ku mallaki ƙasar dana rigaya na baku,' sai kuka yi tawaye da dokokin Yahweh Allahnku, baku kuma gaskanta da shi ba koku saurari muryarsa ba.
\v 24 Kun daɗe kuna tayaswa gãba da Yahweh tun daga ranar dana sanku.
\s5
\v 25 Sai na faɗi da fuskata ƙasa a gaban Yahweh a waɗannan yini arba'in da dare arba'in, domin ya ce zai hallaka ku.
\v 26 Na yi addu'a ga Yahweh na kuma ce, 'Ya Ubangiji Yahweh, kada ka hallakar da mutanenka ko abin gãdon ka daka fanshe su ta wurin girmanka, waɗanda ka fitar daga Masar da hannu mai iko.
\s5
\v 27 Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu; kada ka kula da taurin kan waɗannan mutane, ba kuma ga muguntarsu ba, ko ga zunubinsu ba,
\v 28 domin kada ƙasar daka fito da mu su ce, "Domin Yahweh bai iya ya kai su zuwa cikin ƙasar da ya yi alƙawari garesu ba, kuma domin ya ƙisu, sai ya fito da su zuwa jeji domin ya kashe su a nan."
\v 29 Duk da haka su mutanenka ne da kuma abin gãdonka, wanda ka fito da su da girman ƙarfinka da kuma ta wurin bayyana aikakkiyar ikonka.'
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 A wannan lokaci Yahweh ya ce da ni, 'Kayi sassakan alluna guda biyu kamar na farko, sai ka hauro wurina kan dutsen, kayi akwatin alƙawari na itace.
\v 2 Zan yi rubutu a cikin allunan maganganun da suke cikin alluna na farkon daka farfasa, zaka kuma sanya su cikin akwatin.'
\s5
\v 3 Sai na yi akwatin alƙawari daga itacen maje, sai na sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, sai kuma na haura zuwa saman dutse, riƙe da allunan biyu a hannuna.
\v 4 ya yi rubutu a bisa allunan, kamar rubutu na farko, Dokoki Goma wanda Yahweh ya yi maku magana a kan dutse daga cikin tsakiyar wuta a ranar taruwa; sai Yahweh ya miƙa mani su.
\s5
\v 5 Sai na juyo na sauko daga dutsen, na kuma sanya allunan cikin akwatin alƙawarin dana yi; a nan suke, kamar yadda Yahweh ya umarce ni."
\s5
\v 6 (Jama'ar Isra'la suka yi tafiya daga Birot Bene Ya'akan zuwa Mosera. A nan ne Haruna ya rasu, a nan kuma aka binne shi; Eleyaza, ɗansa, ya yi hidima na firist a matsayinsa.
\v 7 Daga can suka yi tafiya zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma zuwa Yotbata, ƙasa mai rafuffuka na ruwa.
\s5
\v 8 A wannan lokaci sai Yahweh ya zaɓi ƙabilar Lebi don su ɗauki akwatin alƙawari na Yahweh, domin su tsaya a gaban Yahweh su yi masa hidima, su kuma albarkaci mutane a cikin sunansa, kamar yau.
\v 9 Don haka Lebi ba shi da rabo ko gãdon ƙasa tare da 'yan'uwansa; Yahweh ne gãdonsa, kamar yadda Yahweh Allahnka ya yi masa magana.)
\s5
\v 10 "Na zauna a kan dutsen kamar yadda nayi da farko, yini arba'in dare arba'in. Yahweh ya saurare ni wannan lokaci kuma; Yahweh ba shi da niyyar hallaka ku.
\v 11 Yahweh ya ce mani, 'Ka tashi, ka sha gaban mutanen domin ka shugabance su a kan hanyarsu; za su shiga ciki su kuma mallaki ƙasar dana rantse wa ubanninsu in ba su.'
\s5
\v 12 Yanzu, Isra'ila, mene ne Yahweh Allahnka ke buƙata daga gare ka, sai dai ka ji tsoron Yahweh Allahnka, kayi tafiya cikin dukkan tafarkunsa, ka ƙaunace shi, ka kuma yi sujada ga Yahweh Allahnka da dukkan zuciyarka da kuma dukkan ranka,
\v 13 don ka kiyaye dokokin Yahweh, da farillansa, waɗanda nake umartan ka yau domin lafiyarka?
\s5
\v 14 Duba, sama da kuma sama ta sammai na Yahweh Allahnka ne, duniyan, da dukkan abin da ke cikinta.
\v 15 Yahweh ne kawai ya ji daɗin ubanninku da har ya ƙaunace su, ya kuma zaɓe ku, zuriyarsu, a bayansu, fiye da kowanne sauran mutane, kamar yadda ya ke yi yau.
\s5
\v 16 Don haka kuyi wa loɓan zuciyarku kachiya, kuma kada ku ƙara taurin kai kuma.
\v 17 Gama Yahweh Allahnku, shi ne Allahn alloli da kuma Ubangijin iyayengiji, Allah Alƙadiru, mai girma mai bantsoro, wanda baya nuna sonkai baya kuma karɓan toshi.
\s5
\v 18 Yana aikata adalci domin marayu da gwamraye, kuma yana nuna ƙauna ga wanda ke baƙo ta yadda ya ke ba shi abinci da tufafi.
\v 19 Saboda haka ka ƙaunaci wanda ya ke baƙo; gama ku da kanku dã baƙi ne a ƙasar Masar.
\s5
\v 20 Zaka ji tsoron Yahweh Allahnku; shi ne zaka yi masa sujada. Gare shi dole zaka manne, kuma da sunansa zaka yi rantsuwa.
\v 21 Shi ne yabonka, kuma shi ne Allahnka, wanda ya aikata domin ka waɗannan al'amura masu girma da kuma ban-tsoro, waɗanda idanunku suka gani.
\s5
\v 22 Ubanninku suka tafi cikin Masar su mutum saba'in ne; yanzu Yahweh Allahnka ya maishe ka dayawa kamar taurarin sammai.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Saboda haka zaka kaunaci Yahweh Allahnka ka kuma kiyaye umarnansa, da farillansa, da shari'unsa, da dokokinsa koyaushe.
\s5
\v 2 Ku yi la'akari da cewa ba da 'ya'yan ku nake magana ba, waɗanda basu sani ko suka ga hukuncin Yahweh Allahnku, da girmansa, hannunsa mai iko, ko miƙaƙƙiyar zira'assa,
\v 3 da alamomi da kuma ayyukan da ya yi cikin Masar ga Fir'auna, sarkin Masar, ga kuma dukkan ƙasarsa.
\s5
\v 4 Ba su kuma ga abin da ya yi wa rundunar Masarawa ba, ko ya yi wa karusansu, yadda ya sa ruwayen Jan Teku suka haɗiye su yayin da suke bin bayansu, da kuma yadda Yahweh ya hallakar da su har wa yau,
\v 5 ko abin da ya yi maku cikin jeji har kuka zo wannan wuri.
\s5
\v 6 Ba su ga abin da Yahweh ya yi wa Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab ɗan Ruben ba, yadda ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su dukka, da danginsu, da rumfarsu, da kowanne abu mai rai da ya biyo su, a tsakiyar dukkan Isra'ila.
\v 7 Amma idanunku sun ga dukkan manyan ayyukan Yahweh da ya aiwatar.
\s5
\v 8 Don haka ku kiyaye dukkan dokokin da nake baku yau, domin ku yi ƙarfi, ku kuma shiga ku mallaki ƙasa inda kuke shigowa don ku mallake ta,
\v 9 don kuma kwanakinku ya daɗe cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku domin ya basu da kuma zuriyarsu, ƙasa mai zubowa da madara da zuma.
\s5
\v 10 Gama ƙasar, inda kuke shiga don ku mallake ta, ba kamar ƙasar Masar ba ne, inda kuka fito, wurin da kuka yi shukin irinku kuka kuma yi ban-ruwa da kafafunku, kamar lambun baƙulai;
\v 11 amma ƙasar, da zaku shiga don ku mallake ta, ƙasa ce mai tuddai da kwaruruka, suna kuma shanye ruwan sama na sammai,
\v 12 ƙasa wacce Yahweh Allahnku ke kula da ita; idanun Yahweh Allahnku na bisan ta koyaushe, daga farkon shekara har zuwa ƙarshen shekara.
\s5
\v 13 Zai faru haka, idan kuka saurara da aniya ga dokokina da nake dokace ku yau, cewa ku ƙaunaci Yahweh Allahnku ku kuma bauta masa da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku,
\v 14 sa'an nan zan bada ruwan sama na ƙasarku a kan lokaci, ruwa na farko dana ƙarshe, domin ku tara hatsinku, da sabuwar inabinku, da kuma manku.
\v 15 Zan bada ciyawa cikin filayenku domin garkunanku, kuma zaku ci ku kuma ƙoshi.
\s5
\v 16 Ku lura da kanku don kada a ruɗar da zuciyarku, har da zaku kauce ku yi sujada ga wasu alloli ku kuma russuna masu;
\v 17 har fushin Yahweh shi yi ƙuna gãba daku; kuma har kada ya kulle sammai da baza a yi ruwan sama ba, kuma ƙasa ta ƙi bada amfaninta, da kuma har ku hallaka da gaggawa daga cikin ƙasa mai kyau da Yahweh ya ke baku.
\s5
\v 18 Saboda haka ku ajiye waɗannan maganganuna a cikin zuciyarku da ranku, ku ɗaura su kamar alama a hannunku, kuma bari su zama kamar layu a tsakiyar idanunku.
\v 19 Zaku koyar da su ga 'ya'yanku ku kuma yi zancensu lokacin da kuka zauna a gidanku, sa'ad da kuke tafiya kan hanya, da lokacin da kuke kwance, da kuma sa'ad da kuka tashi.
\s5
\v 20 Zaku rubuta su kan kofofin gidanku da kuma bisa kofofin biranenku,
\v 21 don kwanakinku dana 'ya'yanku shi riɓaɓɓanya cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa ubanninku ya ba su har iyakar tsawon yadda sammai ke bisa duniya.
\s5
\v 22 Domin idan kuka yi himma ga kiyaye dukkan waɗannan dokokin da nake dokatan ku, don ku aikata su, kuna ƙaunar Yahweh Allahnku, kuna tafiya cikin dukkan tafarkunsa, ku kuma manne masa,
\v 23 sa'annan Yahweh zai kori dukkan waɗannan al'ummai a gabanku, kuma zaku washe al'umman da suka fi ku yawa da kuma ƙarfi.
\s5
\v 24 Duk inda tafin sawunku zasu taka zasu zama naku; daga jeji zuwa Lebanon, daga kogin, Kogin Yufiretis, zuwa gabashin teku zasu zama iyakarku.
\v 25 Babu mutumin da za ya iya tsayayya da ku. Yahweh Allahnku zai sa tsoronku da kuma razanarku bisa dukkan ƙasan da kuka taka, kamar yadda ya gaya maku.
\s5
\v 26 Duba, na sa a gabanku yau albarka da kuma la'ana:
\v 27 albarkan, idan kuka yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku dana dokace ku yau,
\v 28 la'anar kuma, idan baku yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku ba, amma kuka juya daga hanyar dana dokace ku yau, don ku bi wasu allolin da baku sani ba.
\s5
\v 29 Zai zama kuma, sa'ad da Yahweh Allahnku ya kawo ku zuwa ƙasar da kuke shiga domin ku mallake ta, zaku aza albarka bisa Dutsen Gerizim, la'ana kuma a bisa Dutsen Ebal.
\v 30 Ba a ƙetaren Yodan suke ba, ta faɗuwar rana kan hanya, cikin ƙasar Kan'aniyawa waɗanda suke zama cikin Araba, gaba da Gilgal, daura da itatuwa na More?
\s5
\v 31 Gama zaku ƙetare Yodan domin ku shiga ciki ku mallaki ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kuma za ku mallaketa ku kuma zauna cikinta.
\v 32 Za ku kiyaye dukkan farillai da umarnan dana shirya a gabanku yau.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Waɗannan su ne farillai da dokoki da zaku kiyaye cikin ƙasar da Yahweh, Allahn ubanninku, ke baku domin ku mallaka, dukkan kwanakin da zaku rayu a duniya.
\v 2 Tabbas zaku lallata dukkan wuraren da al'umman da zaku kora suka bauta wa allolinsu, a bisa duwatsu masu tsawo, a bisa tsaunuka, da kuma ƙarƙashin kowanne koren itace.
\s5
\v 3 Dole ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje ginshiƙansu na dutse, ku ƙone dogayen sandunansu na Ashera. Dole ku sassare sassaƙaƙƙun siffofin allolinsu ku hallaka sunayensu daga wurin nan.
\v 4 Ba zaku yi sujada ga Yahweh Allahnku haka ba.
\s5
\v 5 Amma wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa daga cikin dukkan kabilunku ya sa sunansa, wannan zai zama wurin da zai zauna kuma wurin ne zaku tafi.
\v 6 A can ne zaku kawo baye-bayenku na ƙonawa, hadayunku, zakkarku, da baye-bayenku da kuka bayar da hannunku, baye-bayenku na wa'adodi, da baye-bayenku na yaddar rai, da 'ya'yan fari na garkunanku na shanu dana tumaki.
\s5
\v 7 A can ne zaku ci a gaban Yahweh Allahnku ku yi murna akan kowanne abin da kuka sa hannunku a gare shi, ku da iyalanku, wurin da Yahweh Allahnku ya albarkace ku.
\s5
\v 8 Ba zaku yi dukkan abubuwan da muke yi anan ba yau; yanzu kowanne yana yin abin da yaga ya dace a gare shi;
\v 9 gama baku zo wurin hutawa ba tukuna, ga abin gãdo da Yahweh Allahnku ya ke baku.
\s5
\v 10 Amma idan kuka haye Yodan kuka kuma zauna cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku ita gãdo, kuma zai baku hutu daga dukkan maƙiyanku da ke kewaye da ku, domin ku zauna lafiya.
\v 11 Daga nan zuwa wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa yasa sunansa ya zauna a wurin -- a can ne zaku kawo kowanne abin da na umarce ku: baye-bayenku na ƙonawa, da hadayunku, da zakkarku, da baye-bayen da kuka bayar da hannunku, da dukkan baye-bayen da kuka zaɓa domin wa'adodi da zaku yi wa'adi ga Yahweh.
\s5
\v 12 Zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da bayinku maza, da bayinku mata, da Lebiyawan da ke zama tare da ku, saboda ba shi da rabo ko gãdo a cikin ku.
\s5
\v 13 Ku kula da kanku kada ku miƙa baye-bayenku na ƙonawa a kowanne wurin da kuka gani;
\v 14 amma a wurin da Yahweh zai zaɓa a cikin ɗaya daga cikin kabilunku zaku miƙa baye-bayenku na ƙonawa, kuma a can ne zaku yi kowanne abin da na dokace ku.
\s5
\v 15 Duk da haka, zaku iya yanka dabbobi ku kuma ci a ko'ina cikin biranenku, kamar yadda kuke so, kuna karɓan albarkar Yahweh Allahnku domin dukkan abin da ya baku; mutane marasa tsarki da masu tsarki dukkansu za su iya ci, dabbobi kamar gada da barewa.
\v 16 Amma ba zaku ci jinin ba; zaku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
\s5
\v 17 Ba zaku ci waɗannan a garuruwanku ba daga zakkar hatsinku, sabon inabinku, man ku, ko 'ya'yan farin shanunku, ko tumakinku; ba zaku ci kowanne nama da kuka yi hadaya tare da kowanne wa'adodinku da kuka yi, ko kuma baye-bayenku na yaddar rai, ko baikon da kuka bayar da hannunku.
\s5
\v 18 Maimakon haka, sai ku ci su a gaban Yahweh Allahnku a wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku maza, da barorinku mata, da Balebi wanda ke zaune a garuruwanku; zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku game da kowanne abin da ya sa a hannunku.
\v 19 Ku lura da kanku domin kada ku manta da Lebiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.
\s5
\v 20 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya fãɗaɗa iyakokinku, kamar yadda ya alƙawarta maku, sa'annan kuka ce, 'Zan ci nama,' saboda ƙãwar cin nama, zaku iya cin nama, yadda ranku ya ke so.
\s5
\v 21 Idan wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa ya sa sunansa ya yi maku nisa sosai, daganan sai ku yanka wasu daga garken shanunku da tumaki da Yahweh ya baku, kamar yadda na umarce ku; zaku iya ci a garuruwanku, kamar yadda ranku ya ke so.
\v 22 Kamar gada da barewa zaku ci, sai ku ci su, mutane marasa tsarki da masu tsarki za su iya ci su ma.
\s5
\v 23 Sai dai ku tabbata baku ci jinin ba, gama jinin shi ne ran; ba zaku ci rai da nama ba.
\v 24 Kada ku ci shi, zaku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
\v 25 Ba zaku ci shi ba, domin kome ya tafi lafiya tare da ku, tare da 'ya'yanku a bayan ku, idan kuka yi abin da ke dai dai a gaban Yahweh.
\s5
\v 26 Amma abubuwan da ke na Yahweh da kuke da su da baye-bayen wa'adodinku -- zaku ɗauki waɗannan zuwa wurin da Yahweh ya zaɓa.
\v 27 A can ne zaku miƙa baye-bayenku na ƙonawa, naman da jinin, akan bagadin Yahweh Allahnku; za a zubar da jinin hadayunku akan bagadin Yahweh Allahnku, kuma zaku ci naman.
\s5
\v 28 Ku lura kuma ku saurara ga dukkan kalmomin da na dokace ku da su, don ku sami zaman lafiya tare da 'ya'yanku a bayanku har abada, yayin da kuke yin abin da ke mai kyau da yin dai-dai a gaban idanun Yahweh Allahnku.
\s5
\v 29 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya datse al'umman daga gabanku, sa'ad da kuka je kuka kore su, kuka mallake su, kuka zauna cikin ƙasarsu,
\v 30 ku yi hankali da kanku kada ku faɗa cikin tarkon bin su, bayan da an hallaka su a gabanku -- kada ku faɗa cikin tarkon binciko allolinsu, cikin tambayar, 'Ta yaya waɗannan al'ummai suka yi wa allolinsu sujada? Zan yi kamar yadda suka yi.'
\s5
\v 31 Kada ku yi wa Yahweh Allahnku sujada ta irin wannan hanya, gama kowanne abin ƙyama ga Yahweh, abubuwan da ya ƙi -- sun yi waɗannan abubuwa tare da allolinsu; har sun ƙona 'ya'yansu maza da mata cikin wuta domin allolinsu.
\v 32 Iyakar abin dana dokace ku, ku aikata shi, kada ku ƙara masa ko ku rage daga gare shi.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Idan wani annabi ya tashi daga cikinku ko mai mafarkin mafarkai, kuma idan ya baku wata alama ko mu'ujiza,
\v 2 kuma idan alamar ko mu'ujizar ta faru, wanda ya yi maku magana ya ce, 'Bari mu bi waɗansu allolin, da baku sani ba, kuma bari muyi masu sujada,'
\v 3 kada ku saurari maganganun annabin nan, ko mai mafarkin mafarkan; gama Yahweh Allahnku yana gwada kune ya sani ko kuna ƙaunar Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku tare da dukkan ranku.
\s5
\v 4 Zaku bi Yahweh Allahnku, ku girmama shi, ku kiyaye dokokinsa, kuyi biyayya da muryarsa za kuyi masa sujada kuma ku manne masa.
\v 5 Wannan annabin ko wannan mai mafarkin mafarkai za a kashe shi, saboda ya yi maganar tayarwa gãba da Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, da wanda ya fãnshe ku daga gidan bauta. Wannan annabi yana so ya karkatarda ku daga hanyar da Yahweh Allahnku ya dokace ku ku yi tafiya a kanta. Don haka sai ku kawar da mugunta daga cikinku.
\s5
\v 6 Idan ɗan'uwanka, ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko ɗiyarka, ko matar da ke ƙirjinka, ko abokinka wanda ke ƙaunar ranka, a asirce ya lallasheka ya ce, 'Bari muje mu bauta wa wasu allolin da baku sani ba, ko ku ko kakanninku --
\v 7 kowanne allolin mutanen da ke kewaye daku, ko kusa daku, ko nesa can daku, daga wannan iyakar duniya zuwa ƙarshen waccan iyakar duniya,'
\s5
\v 8 Kada ku yarda da shi ko ku saurare shi, kada ku bari idonku ya ji tausayinsa, kada ku barshi koku ɓoye shi.
\v 9 Maimakon haka, ku tabbata kun kashe shi; hannunku ne zai zama na farko wajen kisan sa, daga nan sai hannun dukkan jama'a.
\s5
\v 10 Zaku jejjefe shi da duwatsu har ya mutu, saboda ya yi ƙoƙarin janye ku daga Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
\v 11 Dukkan Isra'ila zasu ji kuma suji tsoro, kuma ba zasu ci gaba da yin irin wannan mugun abu a cikin ku ba.
\s5
\v 12 Idan kuka ji wani ya ce wani abu game da ɗaya daga cikin biranenku, da Yahweh Allahnku ya baku ku zauna ciki:
\v 13 Waɗansu mugaye sun fita daga cikinku har sun janye mazaunan birnin suka ce, 'Bari muje muyi sujada ga allolin da baku sani ba.'
\v 14 Daganan sai ku yi nazarin shaidar, ku bincika, ku tabbatar da kyau. Idan kun gãne cewa gaskiya ne kun haƙiƙance cewa abin ƙyama irin wannan ya faru a cikinku, daganan sai ku ɗauki mataki.
\s5
\v 15 Ku tabbatar kun kai wa mazaunan birnin hari da kaifin takobi, ku hallaka shi da dukkan mutanen da ke zaune ciki, tare da dabbobinsa, da kaifin takobi gaba ɗaya.
\v 16 Zaku tattara dukkan ganimar daga gare shi zuwa cikin tsakiyar tituna zaku ƙone birnin, da dukkan ganimar -- domin Yahweh Allahnku. Birnin zai zama tsibin kufai har abada; ba za a ƙara gina shi ba.
\s5
\v 17 Ba ɗaya daga cikin abubuwan da aka keɓe domin hallakarwa da zai liƙe cikin hannunku. Dole haka ya faru, domin Yahweh ya juya daga zafin fushinsa, ya nuna maku jinkai, ya ji tausayinku, yasa ku riɓanɓanya, kamar yadda ya rantse wa kakanninku.
\v 18 Zai yi wannan saboda kuna sauraron muryar Yahweh Allahnku, kuna kiyaye dukkan dokokin dana dokace ku da su yau, kuna yin abin da ke dai-dai a gaban Yahweh Allahnku.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Ku mutanen Yahweh Allahnku ne. Kada ku tsãge kanku, ko ku aske kowanne sashi na fuskarku domin matacce.
\v 2 Gama ku al'umma ce keɓaɓɓiya ga Yahweh Allahnku, Yahweh kuma ya zaɓe ku ku zama mutane abin mallaka, fiye da dukkan al'umman da ke a fuskar duniya.
\s5
\v 3 Ba zaku ci kowanne abin da ke haram ba.
\v 4 Waɗannan su ne dabbobin da zaku iya ci: saniya, da tunkiya, da akuya,
\v 5 da mariri, da barewa, da mazo, da bunsurun daji, da makwarwa, da gada, da ragon dutse.
\s5
\v 6 Zaku iya cin kowacce dabbar da ke da rababben kofato, wato, wadda kofatonta sun rabu kashi biyu, kuma tana tuƙa.
\v 7 Duk da haka, ba zaku ci waɗansu dabbobin da suke tuƙa kuma suke da rababben kofato ba misali: raƙumi, da zomo, da reman dutse; saboda suna tuƙa amma ba su da rababben kofato, marasa tsarki ne a gare ku.
\s5
\v 8 Alade ma ba shi da tsarki a gare ku saboda yana da rababben kofato amma ba ya yin tuƙa; haram ne a gare ku. Kada kuci naman alade, kada kuma ku taɓa mushensu.
\s5
\v 9 Daga irin waɗannan da suke cikin ruwa zaku iya ci: duk abin da ke da ƙege da ɓanɓaroki;
\v 10 amma duk abin da ba shi da ƙege da ɓanɓaroki kada ku ci su; marasa tsarki ne a gare ku.
\s5
\v 11 Zaku iya cin dukkan tsarkakakkun tsuntsaye.
\v 12 Amma waɗannan tsuntsayen da ba zaku ci ba: Mikiya, da Ungulu, da ƙwaƙwa,
\v 13 da jar shirwa da baƙar shirwa, da kowanne irin shaho.
\s5
\v 14 Kada ku ci kowanne irin hankaka,
\v 15 da jimina, da ƙururu, da harbiyar ruwa, kowanne irin shaho,
\v 16 ƙaramar mujiya da babbar mujiya, da farar mujiya,
\v 17 da zalben ruwa, da ungulu, da agwagwar daji.
\s5
\v 18 Ba zaku ci zalɓe ba, da kowanne irin jinjimi, bunburwa da jemage.
\v 19 Dukkan abin da ke da fiffike da masu rarrafe marasa tsarki ne a gare ku; ba zaku ci su ba.
\v 20 Zaku iya cin dukkan tsarkakakkun abubuwan da suke shawagi.
\s5
\v 21 Kada ku ci kowanne abin da ya mutu da kansa; za ku iya ba baƙon da ke cikin garuruwanku, domin ya ci; ko ku sayar da shi ga baƙo. Gama ku al'umma ce keɓaɓɓiya ga Yahweh Allahnku. Ba zaku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa ba.
\s5
\v 22 Dole ku tabbata kun fitar da zakkar dukkan amfanin irin da kuka shuka, wanda ke tsirowa a gona kowacce shekara.
\v 23 Dole ku ci a gaban Yahweh Allahnku, a wurin da zai zaɓa a matsayin wuri mai tsarki, zakkar hatsin ku, da sabon inabi, dana manku, da 'ya'yan farin shanunku dana dabbobinku; domin kullum ku koyi girmama Yahweh Allahnku.
\s5
\v 24 Idan tafiyar ta yi maku nisa kwarai da baza ku iya kai ta ba, saboda wurin da Yahweh Allahnku ya zaɓa a matsayin wurin sa mai tsarki ya yi maku nisa, daganan, idan Yahweh ya albarkace ku,
\v 25 sai ku sayar da zakkar ku mai da ita kuɗi, sai ku ƙulle kuɗin cikin hannunku, ku tafi wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa.
\s5
\v 26 A can ne zaku kashe kuɗin akan duk abin da kuke marmari: domin sã, ko domin tunkiya, ko domin ruwan inabi, ko domin abin sha mai ƙarfi, ko domin duk abin da kuke so; zaku ci a can a gaban Yahweh Allahnku, kuma ku yi murna, kuda iyalin gidanku.
\v 27 Balebi wanda ya ke cikin garuruwanku -- kada ku yashe shi, gama ba shi da rabo ko gãdo tare da ku.
\s5
\v 28 A ƙarshen kowacce shekara uku za ku kawo dukkan zakkar amfaninku cikin wannan shekarar, zaku ajiye ta cikin ƙofofinku;
\v 29 Balebi kuma, saboda ba shi da rabo ba shi da gãdo tare daku, da baƙo, da maraya, da gwamruwa waɗanda ke cikin ƙofofinku, za su zo su ci su ƙoshi. Ku yi haka domin Yahweh Allahnku ya albarkace ku cikin dukkan aikin da hannuwanku ke yi.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 A ƙarshen kowacce shekara bakwai, dole ku yafe basussuwa.
\v 2 Ga yadda za a yi yafiyar: Kowanne mai bin bashi zai yafe abin da ya rantawa maƙwabcinsa; ba zai neme shi daga wurin maƙwabcinsa ba ko ɗan'uwansa saboda an yi shelar yafe basussuwa ta Yahweh.
\v 3 Zaka iya nema daga wurin baƙo; amma duk abin da ke naka ya ke tare da ɗan'uwanka ba za ka nemi a biya ka ba.
\s5
\v 4 Har yanzu, ba za a sami matalauci a cikinku ba (gama lallai Yahweh zai albarkace ku a cikin ƙasar da ya ke baku ita a matsayin gãdo ku mallaka),
\v 5 muddin kuka saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye dukkan waɗannan dokoki da nake umartarku da su yau.
\v 6 Gama Yahweh Allahnku zai albarkace ku, kamar yadda ya alƙawarta maku; zaku ba al'ummai da yawa rance, amma ba zaku ranta ba; zaku yi mulkin al'ummai da yawa, amma ba zasu yi mulkin ku ba.
\s5
\v 7 Idan akwai wani mutum matalauci a cikinku, ɗaya daga cikin 'yan'uwanku, a tsakanin kowacce ƙofofinku cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kada ku taurare zuciyarku koku rufe hannunku daga ɗan'uwanku matalauci;
\v 8 amma lallai sai ku buɗe hannunku gare shi kuma ku ranta masa issashe domin biyan bukatarsa.
\s5
\v 9 Ku lura kada ku kasance da mugun tunani a cikin zuciyarku, kuna cewa, 'Ai shekara ta bakwai, shekarar yafewa, ta kusa,' domin kada ku zama da maƙo game da ɗan'uwanku ku kuma ƙi bashi kome; zai iya yin kuka ga Yahweh game daku, kuma ya zama zunubi a gare ku.
\v 10 Lallai dole ku bashi, zuciyarku kuma ba zata da mu ba idan kuka bashi, saboda wannan Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin dukkan aikinku da kuma dukkan abin da kuka sanya cikin hannunku ku yi.
\s5
\v 11 Gama ba za a rasa matalauta a cikin ƙasar ba; saboda haka na dokace ku cewa, 'Dole ku zama da hannu sake ga ɗan'uwanku, ga mabuƙatanku, da kuma matalauci a cikin ƙasarku.'
\s5
\v 12 Idan aka sayar maku da ɗan'uwanku, Ba'ibrane ko mace ko namiji sai ya bauta maku shekara shida, daga nan a cikin shekara ta bakwai dole ku 'yantar da shi daga gare ku.
\v 13 Idan kuka 'yantar da shi daga gare ku, ba zaku barshi ya tafi hannun wofi ba.
\v 14 Dole ku bashi kyauta a yalwace daga cikin tumakinku, da masussukar hatsinku, da wurin matsewar inabinku. Kamar yadda Yahweh Allahnku ya albarkace ku, dole ku ba shi.
\s5
\v 15 Dole ku tuna cewa dã ku bayi ne a cikin ƙasar Masar, kuma Yahweh Allahnku ya fãnshe ku; don haka nake umartarku yau ku yi haka.
\v 16 Idan kuma ya ce maku, 'Ba zan tafi daga gare ku ba,' saboda yana ƙaunarku da gidanku, kuma yana jin daɗin zama tare da ku,
\v 17 daganan sai ku ɗauki bisilla ku huda kunnensa har dogaran ƙofa, zai zama bawanku har iyakar rayuwa. Haka kuma zaku yi da mace baiwa.
\s5
\v 18 Kada ya zama da damuwa a gare ku idan kuka 'yantar shi daga gare ku, saboda ya yi maku bauta shekaru shida darajar bautarsa ta ninka biyu da ta mutumin da aka yi hayarsa. Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin dukkan abin da kuke yi.
\s5
\v 19 Dukkan 'ya'yan farin a cikin garkunan shanunku dana tumaki dole ku keɓe su ga Yahweh Allahnku. Kada ku yi aiki da 'ya'yan farin shanunku, koku yi sausayar ɗan farin tumakinku.
\v 20 Dole ku ci ɗan farin a gaban Yahweh Allahnku kowacce shekara a wurin da Yahweh ya zaɓa, ku da iyalinku.
\v 21 Idan tana da wani cikas -- misali, gurguntaka, ko makanta ko tana da wani cikas ta kowanne iri -- kada ku miƙa ta hadaya ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 22 Zaku ci ta a garuruwanku; mutane marasa tsarki da masu tsarki su ma dole su ci, kamar mariri ko barewa.
\v 23 Sai dai kada ku ci jinin; dole ku zubar da jinin a ƙasa kamar ruwa.
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Ku kiyaye watan Abib, kuma ku kiyaye Bukin Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku, gama a watan Abib ne Yahweh Allahnku ya fito daku daga Masar da daddare.
\v 2 Zaku miƙa hadayar Ƙetarewa ga Yahweh Allahnku tare da wasu garkunan tumakinku dana shanu a wurin da Yahweh zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki.
\s5
\v 3 Ba zaku ci abinci mai gami tare da ita ba; kwana bakwai zaku ci abinci mara gami tare da hadayar, abincin wahala ne; gama kun fito daga ƙasar Masar da gaggawa. Kuyi haka dukkan kwanakinku domin ku tuna da ranar da kuka fito daga ƙasar Masar.
\v 4 Kada a ga gami a cikinku a dukkan iyakokinku a lokacin kwanaki bakwai; kada kowanne naman da kuka miƙa hadaya da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.
\s5
\v 5 Kada ku miƙa hadayar Ƙetarewa a kowanne garin da Yahweh ya ke baku.
\v 6 Maimakon haka, ku miƙa ta a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. A can zaku miƙa hadayar Ƙetarewa da yamma da faɗuwar rana, a dai-dai lokacin da shekarar da kuka fito daga Masar.
\s5
\v 7 Dole ku gasa shi kuma ku ci shi a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa; da safe zaku juya ku koma zuwa rumfunanku.
\v 8 Kwana shida zaku yi kuna cin abinci mara gami; a rana ta bakwai sai kuyi muhimmin taro domin Yahweh Allahnku; a wannan ranar kada kuyi aiki.
\s5
\v 9 Zaku ƙirga mako bakwai domin kanku; daga lokacin da kuka fara sa lauje ga hatsinku da ke tsaye dole ku fara ƙirga makonni bakwai.
\v 10 Dole ku kiyaye Bikin Makonni domin Yahweh Allahnku tare da bada gudunmuwa ta yaddar rai daga hannunku da zaku bayar, gwargwadon yadda Yahweh Allahnku ya albarkace ku.
\s5
\v 11 Zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku - ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku maza, da barorinku mata, da Balebiyen da ke zaune a ƙofofin garinku, da baƙo, da marayu, da gwamruwa waɗanda ke tare da ku, a wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa domin wurinsa mai tsarki.
\v 12 Ku tuna dã ku bayi ne a Masar; dole ku kiyaye kuma ku aikata waɗannan farillai.
\s5
\v 13 Dole ku kiyaye Bikin Bukkoki kwanaki bakwai bayan da kun gama tattara amfaninku daga masussukanku da wurin matsewar ruwan inabinku.
\v 14 Zaku yi murna a lokaci bikin -- ku, da 'ya'yanku maza, da 'ya'yanku mata, da barorinku mata, da Balebiye, da baƙo, da maraya da gwamruwa waɗanda ke a garuruwanku.
\s5
\v 15 Kwana bakwai zaku kiyaye biki ga Yahweh Allahnku a wurin da Yahweh zai zaɓa, saboda Yahweh Allahnku zai albarkace ku a cikin dukkan aikin hannuwanku, kuma dole ku zama da cikakkiyar murna.
\s5
\v 16 Sau uku a shekara dole dukkan mazajenku su hallara a gaban Yahweh Allahnku a wurin da zai zaɓa: a lokacin Bikin Abinci Marar Gami, da lokacin Bikin Makonni, da kuma lokacin Bikin Bukkoki. Kada wani ya hallara gaban Yahweh hannu- wofi;
\v 17 maimakon haka, kowanne mutum zai bayar gwargawdon abin da zai iya, domin ku san albarkar da Yahweh Allahnku ya bayar gare ku.
\s5
\v 18 Dole ku naɗa alƙalai da shugabannai a dukkan ƙofofin garuruwanku da Yahweh Allahnku ya ke baku; za a ɗauko su daga kowacce kabilarku, dole su shari'anta jama'a da shari'a ta adalci.
\v 19 Kada ku ɗauke adalci da ƙarfi; kada ku nuna son kai koku karɓi cin hanci, gama cin hanci yana makantar da idanun mai hikima ya karkatar da maganganun adali.
\v 20 Dole kubi adalci, bayan adalci kaɗai, domin ku rayu ku iya gãdon ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku.
\s5
\v 21 Kada ku sanya wa kanku Asherah, kowanne irin itace, kusa da bagadin Yahweh Allahnku da zaku yi domin kanku.
\v 22 Kada kuma ku gina wa kanku al'amudin dutse, wanda Yahweh Allahnku ya ke ƙi.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Kada ku miƙa wa Yahweh Allahnku hadaya ta sã ko tunkiya da ke da kowanne lahani ko duk abin da bashi da kyau, gama wannan zai zama abin ƙyama ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 2 Idan aka sami wani, a tsakanin kowaɗanne ƙofofin garinku da Yahweh Allahnku ya ke baku, kowanne mutum ko mace, wanda ya aikata abin da ke mugu a gaban Yahweh Allahnku yana karya alƙawarinsa,
\v 3 duk wanda yaje ya yi sujada ga waɗansu alloli ya kuma russuna masu, ko rana, ko wata, ko kowacce rundunar sama - ba abin dana umarce ku ba -
\v 4 idan aka faɗa maku game da wannan, ko kuka ji labarinsa, daganan dole kuyi bincike a hankali. Idan gaskiya ne kuma an tabbatar da anyi irin wannan abin ƙyamar a Isra'ila, wannan shi ne abin da zaku yi.
\s5
\v 5 Dole ku kawo wannan mutum ko macen, wanda ya aikata wannan mugun abu, ga ƙofofin garuruwanku, wannan mutumin ko macen, dole ku jejjefe shi da duwatsu har ya mutu.
\v 6 Bisa ga shaidu biyu ko shaidu uku, za a kashe shi; amma ba za a kashe mutum bisa ga shaidar mutum ɗaya ba.
\v 7 Hannun shaidun zasu fara jifansa ga mutuwa, daganan sauran dukkan jama'a; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku.
\s5
\v 8 Idan wani abu ya taso da ya zama da wahala a gare ku ku shari'anta - watakila zancen kisankai ko haɗarin mutuwa, ta zancen 'yancin wani da ta wani, ko tambaya akan wani irin lahani da aka yi, ko dai wani al'amari, al'amura masu wahalarwa a cikin ƙofofin garinku -- daga nan dole ku tafi wurin da Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki.
\v 9 Dole ku je wurin firist, zuriyar Lebi, da kuma wurin alƙali da zai yi hidima a lokacin; zaku nemi shawararsu, zasu baku mafita.
\s5
\v 10 Dole ku bi shari'ar da aka baku a wurin da Yahweh zai zaɓa a matsayin wurinsa mai tsarki. Dole ku lura ku yi dukkan abin da suka jagorance ku ga yi.
\v 11 Kubi shari'ar da suka koya maku, ku kuma yi bisa ga shawarwarin da suka baku. Kada ku kauce daga abin da suka faɗa maku, zuwa hananun dama ko zuwa hannun hagu.
\s5
\v 12 Duk wanda ya yi isgilanci, ta wurin ƙin sauraron firist wanda ke tsaye ya bauta wa Yahweh Allahnku, ko ta ƙin sauraron alƙali - wannan mutum zai mutu; dole ku kawar da mugunta daga Isra'ila.
\v 13 Dukkan mutane dole suji kuma suji tsoro, ba zasu ƙara yi isgilanci ba.
\s5
\v 14 Sa'ad da kuka zo ƙasar da Yahweh Allahnku ya ba ku, kuma idan kuka mallake ta kuka fara zama cikinta, sa'an nan kuka ce, 'Zan sanya sarki a bisa kaina, kamar dukkan al'umman da suke kewaye da ni,'
\v 15 daga nan dole ku tabbatar kun naɗa wa kanku sarki wanda Yahweh Allahnku zai zaɓa. Dole ku naɗa wa kanku sarki wanda ke daga cikin 'yan'uwanku. kada ku sanya baƙo, wanda ba ɗan'uwanku ba, a bisa kanku.
\s5
\v 16 Amma kada ya ƙara wa kansa dawakai, kada ya sa mutane su koma Masar don su ƙaro masa dawakai, gama Yahweh ya ce maku, 'Kada ku ƙara komawa can.'
\v 17 Kada ya ɗauki mata da yawa domin kansa, domin kada zuciyarsa ta karkace. Kada ya tattara wa kansa tulin kuɗin azurfa da zinariya.
\s5
\v 18 Sa'ada da ya zauna kan gadon sarautar mulkinsa, dole ya rubutawa kansa a cikin naɗaɗɗen kwafin littafi shari' an nan, daga shari'a da ke gaban firist, waɗanda suke Lebiyawa.
\v 19 Naɗaɗɗen littafin zai kasance tare da shi, kuma dole ya karanta shi cikin dukkan kwanakin ransa, domin ya koyi girmama Yahweh Allahnsa, domin ya kiyaye dukkan kalmomin shari'ar da waɗannan farillai, ya kiyaye su.
\s5
\v 20 Dole ya yi haka domin kada zuciyarsa ta kumbura bisa kan 'yan'uwansa, domin kada ya kauce daga bin dokokin, zuwa dama ko hagu; domin ya sami dalilin daɗewa cikin mulkinsa, shi da 'ya'yansa, a cikin Isra'ila.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Firistoci, da suke Lebiyawa, da dukkan kabilar Lebi, ba za su sami rabo ko gãdo tare da Isra'ila ba; dole su ci baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta a matsayin gãdonsu.
\v 2 Ba zasu sami gãdo tare da 'yan'uwansu ba; Yahweh shi ne gãdon su, kamar yadda ya faɗa masu.
\s5
\v 3 Wannan shi ne rabon da aka ba firistoci, aka basu daga mutanen da suka miƙa hadaya, ko ta sã ne ko tunkiya ce: kafaɗar, kumatu biyu, da kuma kayan ciki.
\v 4 Sai nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabi, da manku, da gashin tumakinku da kuka fara sausaya, dole ku ba shi.
\v 5 Gama Yahweh Allahnku ya zaɓe shi da ga cikin kabilunku su tsaya su yi hidima a cikin sunan Yahweh, shi da 'ya'yansa har abada.
\s5
\v 6 Idan Balebiye ya fito daga kowanne garinku na dukkan Isra'ila daga inda ya ke zama, kuma ya yi marmari da dukkan ransa ya zo wurin da Yahweh ya zaɓa,
\v 7 daganan dole ya yi hidima a cikin sunan Yahweh Allahnsa kamar yadda dukkan 'yan'uwansa Lebiyawa suke yi, waɗanda ke tsayawa a can a gaban Yahweh.
\v 8 Dole su sami rabo iri ɗaya su ci, banda abin da ke zuwa daga abin da iyalinsa suka sayar na gãdo.
\s5
\v 9 Sa'ad da kuka zo cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku, kada kuyi kwaikwayon ayyukan banƙyama na waɗannan al'ummai.
\v 10 Kada a sami wani a cikinku da zai miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya cikin wuta, duk wanda ke amfani da maita ko mai faɗin gaibu, ko mai sihiri, ko ya shiga maita,
\v 11 duk mabiya, ko mai sha'ani da ruhohi ko mai surkulle, mai magana da ruhohin matattu.
\s5
\v 12 Gama duk mai yin waɗannan abubuwa abin ƙyama ne ga Yahweh; saboda waɗannan abubuwan ban ƙyama ne Yahweh Allahnku ya ke korarsu daga gaban ku.
\v 13 Sai ku zama marasa aibu a gaban Yahweh Allahnku.
\v 14 Gama waɗannan al'ummai da zaku kora suna sauraran masu aikata maita da masu duba; amma ku, Yahweh Allahnku bai yaddar maku ku yi haka ba.
\s5
\v 15 Yahweh Allahnku zai tayar maku da wani annabi daga cikinku, ɗaya daga cikin 'yan'uwanku, kama ta. Dole ku saurare shi.
\v 16 Wannan shi ne abin da kuka roƙa a wurin Yahweh Allahnku a Horeb a ranar taron, cewa, 'Kada ka barmu mu ƙara jin muryar Yahweh Allahnmu, ko mu ƙara ganin wannan babbar wuta, don zamu mutu.'
\s5
\v 17 Yahweh ya ce mani, 'Abin da suka ce yana da kyau.
\v 18 Zan tayar masu da wani annabi daga cikin 'yan'uwansu, kamar ka. Zan sa maganganuna cikin bakinsa, zai faɗa masu dukkan abin da na dokace shi.
\v 19 Zai kasance kuwa duk wanda bai saurari maganganuna da zai faɗa a cikin sunana ba, Zan nemi haƙƙinta a gareshi.
\s5
\v 20 Amma annabin da ya faɗi maganar isgilanci cikin sunana, maganar da ban umarce shi ba ya faɗa, ko wanda ya yi magana cikin sunan waɗansu alloli, wannan annabin dole ya mutu.'
\v 21 Wannan shi ne abin da zaku ce a cikin zuciyarku: 'Ta yaya zamu san saƙon da Yahweh bai faɗi ba?'
\s5
\v 22 Zaku gane saƙon da Yahweh ya faɗa idan annabi ya yi magana a cikin sunan Yahweh. Idan wannan abin bai zo ba, ko bai faru ba, daganan wannan shi ne abin da Yahweh bai faɗa ba kuma annabin ya faɗe shi ne cikin isgilanci, kada ku ji tsoronsa.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Sa'ad da Yahweh Allahnku ya datse al'ummai, waɗannan waɗanda Yahweh Allahnku zai baku ƙasarsu, sa'ad da kuka zo bayansu kuka zauna a cikin garuruwansu da gidajensu,
\v 2 sai ku zaɓi birane uku domin kanku a tsakiyar ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke ba ku ku mallaka.
\v 3 Sai ku gina hanyoyi ku kuma raba iyakokin ƙasarku kashi uku, ƙasar da Yahweh Allahnku ke saku gãda, domin duk wanda ya kashe wani mutum sai ya gudu zuwa can.
\s5
\v 4 Wannan itace doka domin wanda ya kashe wani da wanda ya gudu can don ya tsira - duk wanda ya kashe maƙwabcinsa ba don ya yi niyya ba, kuma bai ƙi shi ba a dã.
\v 5 Misali, idan mutum ya tafi cikin jeji tare da maƙwabcinsa domin su saro itace, sai ruwan gatarin ya kwaɓe daga ƙotar ya sari maƙwabcinsa ya kashe shi - daganan wannan mutumin dole ya gudu zuwa ɗaya daga biranen domin ya tsirar da ransa.
\s5
\v 6 Idan ba haka ba mai bin haƙƙin jini zai iya bin shi wanda ya ɗauki ran, cikin zafin fushinsa ya cim masa, idan nisan ya yi yawa sosai, ya cim masa ya kashe shi, koda shike mutumin nan bai cancanci mutuwa ba, tunda shike bai ƙi shi ba a dã.
\v 7 Don haka na dokace ku ku keɓe wa kanku birane uku.
\s5
\v 8 Idan Yahweh Allahnku ya fãɗaɗa iyakokinku, kamar yadda ya alƙawarta wa kakanninku zai yi, ya baku dukkan ƙasar da ya alƙawarta ya ba kakanninku;
\v 9 idan kuka kiyaye dukkan waɗannan dokoki kuka aikata su, waɗanda nake dokatarku da su yau - dokokin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku kullum kuyi tafiya cikin hanyoyinsa, daganan sai ku ƙara birane uku domin kanku, akan waɗannan ukun kuma.
\v 10 Kuyi haka domin kada a zubar da jinin mara laifi a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku domin gãdo, domin kada alhakin jini ya kasance a kanku.
\s5
\v 11 Amma idan wani yana ƙin maƙwabcinsa, ya yi kwanto yana jiransa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, idan ya gudu zuwa cikin ɗaya daga cikin biranen nan -
\v 12 daganan dattawan garinsu dole su aika a kawo shi daga can, daganan su miƙa shi a hannun ɗan'uwan mai bin hakƙin jini domin a kashe shi.
\v 13 Kada idannunku su tausaya masa; maimakon haka dole ku kawar da alhakin zubar da jini daga Isra'ila, domin ku sami zaman lafiya.
\s5
\v 14 Kada ku kawar da iyakar maƙwabcinka da kakanninku suka kafa tuntuni, a cikin gãdon da zaku gãda, a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka.
\s5
\v 15 Shaidar mutum ɗaya ba zata isa a tabbatar da cewa mutum ya yi kowanne irin laifi ba, ko kowanne zunubi, a kan kowanne zunubin da ya yi; sai an ji a bakin shaidu biyu ko uku, kafin a tabbatar da kowanne abu.
\v 16 Alal misali idan mashaidi marar adalci ya tashi gãba da kowanne mutum ya shaida sharri game da laifinsa.
\s5
\v 17 Daganan sai dukkansu mutanen, waɗanda rashin jituwar ta faru tsakaninsu, dole su tsaya gaban Yahweh, a gaban firistoci da alƙalai masu yin hidima akwanakin nan.
\v 18 Dole alƙalan suyi bincike sosai; su duba, idan mai shaidar mai shaidar zur ne, ya yi shaidar ƙarya game da ɗan'uwansa,
\v 19 daganan sai ku yi masa, kamar yadda ya so ayi wa ɗan'uwansa; kuma zaku kawar da mugunta daga cikinku tawurin yin haka.
\s5
\v 20 Daganan sauran da suka ragu zasu ji su ji tsoro, kuma daganan ba zasu ƙara aikata irin wannan mugunta a cikinku ba.
\v 21 Kada idannunku su tausaya; rai maimakon rai, ido mai makon ido, haƙori mai makon haƙori, hannu mai makon hannu, ƙafa mai makon ƙafa.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sa'ad da kuka tafi yaƙi gãba da maƙiyanku, idan kunga dawakai, karusai, da mutanen da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu; Gama Yahweh Allahnku yana tare daku, shi wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.
\s5
\v 2 Sa'ad da kuke gab da shiga cikin yaƙi, sai firist ya kusato ya yi magana da mutane.
\v 3 Dole ya ce masu, 'Ku saurara, Isra'ila, zaku tafi yaƙi gãba da maƙiyanku. Kada ku bari zukatanku su karaya. Kada kuji tsoro ko ku firgita. Kada kuji tsoronsu.
\v 4 Gama Yahweh Allahnku shi ne mai tafiya tare daku ya yi yaƙi domin ku gãba da maƙiyanku ya cece ku kuma.'
\s5
\v 5 Dole shugabanni suyi magana da mutane su ce, 'Ko akwai wani mutum wanda ya gina sabon gida da bai buɗe shi ba? Bari ya koma gidansa, domin kada ya mutu cikin yaƙi sa'an nan wani mutum dabam ya yi bikin buɗewarsa.
\s5
\v 6 Ko akwai wani daya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Bari ya koma gida, domin kada ya mutu a cikin yaƙi wani mutum dabam yaci amfaninta.
\v 7 Wanne mutum ne ya ke tashin mace amma bai aure ta ba tukuna? Bari ya koma gida domin kada ya mutu a cikin yaƙi sa'an nan wani mutum dabam ya aure ta.'
\s5
\v 8 Shugabannin zasu ci gaba da yiwa mutane magana su ce, 'Ko a kwai wani mutum a nan da ya ke jin tsoro ko mai karyayyar zuciya? Bari ya koma gidansa, domin kada zuciyar 'yan'uwansa su narke kamar yadda zuciyarsa ta narke.'
\v 9 Sa'ad da shugabanni suka gama yin magana da mutane, dole su naɗa hafsoshi a kansu.
\s5
\v 10 Sa'ad da kuka kusanci wani birni don ku kai masa hari, ku ba mutanen birnin kyautar salama.
\v 11 Idan suka karɓi kyautar ku har suka buɗe maku ƙofofinsu, dukkan mutanen da kuka sãmu a cikinsa dole suyi maku aikin gandu kuma su bauta maku.
\s5
\v 12 Amma idan ya ƙi yin salama daku, maimakon haka sai ya yi yaƙi daku, daganan sai ku kewaye shi da yaƙi,
\v 13 idan kuma Yahweh Allahnku ya baku nasara ya sa su ƙarƙashin sarrafawar ku, dole ku kashe kowanne mutum a cikin garin.
\s5
\v 14 Amma mata da ƙanana, da dabbobi, da kowanne abin da ke cikin birnin, da dukkan ganimarsu, zaku ɗauka a matsayin ganima domin kanku. Zaku ci ganimar maƙiyanku, wadda Yahweh Allahnku ya baku.
\v 15 Haka zaku aikata ga dukkan biranen da ke nesa daku sosai, biranen da ba biranen waɗannan al'ummai ba.
\s5
\v 16 A cikin biranen al'umman nan da Yahweh Allahnku ya ke baku a matsayin gãdo, kada ku bar kowanne abin da ke numfashi da rai.
\v 17 Maimakon haka zaku hallakar da su ƙarƙaf: Su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan'aniyawa, da Feriziyawa, da Hibiyawa, da Yebusiyawa, kamar yadda Yahweh Allahnku ya dokace ku.
\v 18 Ku yi haka domin kada su koya maku ku aikata kowanne abin banƙyamarsu kamar yadda suka yi tare da allolinsu. Idan kuka yi, zaku yi zunubi ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 19 Sa'ad da kuka daɗe da kewaye birni, yayin da kuke yaƙi da shi domin ku ci shi, kada ku hallaka itatuwansa da gatari ta wurin saransu. Gama zaku iya ci daga gare su, don haka kada ku sare su ƙasa. Gama itacen gona mutum ne da zaku kewaye shi da yaƙi?
\v 20 Itatuwan kaɗai da kuka sani ba itatuwan da ake ci ba, zaku iya hallakarwa ku sare su ƙasa; zaku gina kagara da su gãba da birnin da ke yaƙi daku, har sai ya faɗi.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Idan aka iske an kashe wani a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka, a kwance cikin gona, kuma ba a san wanda ya kai masa hari ba;
\v 2 daganan sai dattawanku da alƙalanku su fita, dole su auna zuwa garuruwan da ke kewaye da shi wanda aka kashe.
\s5
\v 3 Daganan dattawan garin da ke kusa da gawar mataccen dole su ɗauki karsana daga garke, wadda ba a taɓa aiki da ita ba, kuma ba a taɓa sa mata karkiya ba.
\v 4 Daganan dole su jagoranci karsanar zuwa kwari inda ruwa ke gudu, kwarin da ba a noma ko shuka ba, kuma a can cikin kwarin zasu karya wuyar karsanar.
\s5
\v 5 Sai firistoci, zuriyar Lebi, dole su zo gaba, domin Yahweh Allahnku ya zaɓe su su hidimta masa su kuma sa albarka a cikin sunan Yahweh su kuma dai-dai ta kowacce matsalar jayayya da cin mutunci ta wurin maganarsu.
\s5
\v 6 Dukkan dattawan birni da ya fi kusa da mutumin da aka kashe dole su wanke hannuwansu a kan karsanar wadda aka karya wuyanta a cikin kwari;
\v 7 kuma dole su amsa ga matsalar su ce, 'Hannayenmu ba su zubar da wannan jinin ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba.
\s5
\v 8 Yahweh, ka gafarta, wa mutanenka Isra'ila, waɗanda ka fansa, kuma kada ka ɗora alhakin jinin mara laifin nan a tsakiyar mutanenka Isra'ila.' Daganan za a yafe masu zubar da jinin.
\v 9 Ta haka zaku kawar da alhakin jinin mara laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da ke dai-dai a idanun Yahweh.
\s5
\v 10 Sa'ad da kuka fita yaƙi gãba da maƙiyanku Yahweh Allahnku kuwa ya baku nasara yasa su ƙarƙashin sarrafawarku, kuka kuwa ɗauke su a matsayin bayi,
\v 11 idan a cikin bayinka akwai kyakkyawar mace, wadda ka yi sha'awarta kuma kana so ka ɗauke ta domin ta zama matarka,
\v 12 daganan sai ka kawo ta gidanka; za ta aske kanta ta kuma yanke farshenta.
\s5
\v 13 Daganan zata tuɓe tufafinta da take sawa sa'ad da aka ɗauko ta bauta zata kasance cikin gidanka tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta wata guda cif. Bayan haka zaka iya kwana tare da ita ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka.
\v 14 Idan ka ji baka jin daɗinta, daganan sai ka barta ta tafi wurin da ta ga dama. Amma kada ka yarda ka sayar da ita domin kuɗi, kada kuma ka wahalsheta kamar baiwa, saboda ka ƙasƙantar da ita.
\s5
\v 15 Idan mutum yana da mata biyu sai ya nuna yana son ɗayar kuma ya ƙi ɗayar, kuma dukkansu sun haifa masa 'ya'ya - dukka da wadda ya ke ƙauna da wadda ya ke ƙi - idan ɗan farin na wadda ya ke ƙi ce,
\v 16 daganan a ranar da zai sa 'ya'yansa su gãji abin da ya mallaka, kada yasa ɗan matar da ya ke ƙauna ya zama ɗan fari gaban ɗan matar da ya ke ƙi, wanda shi ne ainihin ɗan farin.
\v 17 Maimakon haka, dole ya amince da wanda ya ke ɗan farin, wato ɗan matar da ya ke ƙi, ta wurin bashi kaso biyu na dukkan abin da ya mallaka; gama wannan ɗan shi ne farkon ƙarfinsa; haƙin ɗan fari nasa ne.
\s5
\v 18 Idan mutum yana da gagararren ɗa kuma mai tayaswa wanda ba ya biyayya da maganar mahaifinsa ko maganar mahaifiyarsa, kuma wanda, koda shike sun kwaɓe shi, ba ya sauraron su;
\v 19 daganan sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su cafke shi su kawo shi waje wurin dattawansu na birni kuma zuwa ƙofar birninsa.
\s5
\v 20 Dole su ce da dattawan birnisa, 'Wannan ɗanmu ne gagararre ne kuma ɗan tayarwa; baya biyayya da maganar mu; shi mai zarin ci ne kuma mashayi.'
\v 21 Daganan dukkan mutanen birni dole su jejjefeshi da duwatsu har ya mutu; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku. Dukkan Isra'ila zasu ji suji tsoro.
\s5
\v 22 Idan mutum ya aikata zunubin da ya isa mutuwa kuma aka kashe shi, kuma aka rataye shi a bisa itace,
\v 23 daganan kada abar jikinsa ya kwana dukkan dare a kan itace, amma, dole ku tabbatar kun bizne shi a ranar; gama duk wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Allah. Ku yi biyayya da dokar nan domin kada ku ƙazantar da ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku a matsayin gãdo.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Kada ku kalli sã ko tunkiyar ɗan'uwanku Ba-isra'ile yana ɓacewa ku ƙyale su; dole ku tabbatar kun dawo da su ga maishi.
\v 2 Idan ɗan'uwanku mutumin Isra'ila ba ya kusa daku, ko idan baku sanshi ba, daganan dole ku kawo dabbar wurinku a gidanku, za ta kasance tare daku har lokacin da ya zo neman ta, daganan dole ku mayar masa da ita.
\s5
\v 3 Dole kuyi irin haka da jakinsa, dole kuyi haka ga rigarsa; dole kuyi haka da kowanne abin da ya ɓace na ɗan'uwanku Ba-isra'ile, duk abin da ya ɓata kuka tsinta; lallai ba zaku ɓoye kanku ba.
\v 4 Ba zaku ga jaki ko san ɗan'uwanku Ba-isra'ile ya faɗi a hanya ku ƙyale su ba; dole ku tabbatar kun taimake shi tawurin sake ɗaga shi sama.
\s5
\v 5 Kada mace ta sanya abin da ya shafi suturar maza, kuma kada namiji ya sanya suturar mata; gama duk wanda ya yi waɗannan abubuwa abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 6 Idan kuna tafiya a kan hanya sai kuka ga sheƙar tsuntsu, a kan kowanne itace, ko a ƙasa, da 'ya'yansa ko ƙwayaye a ciki, uwar kuma na kwance a kan 'ya'yan ko a kan ƙwayayen, kada ku kama uwar duk da 'ya'yan.
\v 7 Ku tabbatar uwar ta tafi, amma zaku iya kwashe 'ya'yan domin kanku. Ku yi biyayya da dokar nan domin ku sami zaman lafiya ta haka kuma zaku tsawaita kwanakinku.
\s5
\v 8 Sa'ad da kuka gina sabon gida, daganan dole ku ja rawani a rufin domin kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya faɗi daga can.
\s5
\v 9 Kada ku shuka iri biyu a gonar inabinku, domin kada wuri mai tsarki ya karɓe dukkan amfaninku, irin da kuka shuka da kuma amfanin gonar inabinku.
\v 10 Kada ku haɗa sa da jaki suyi huɗa tare.
\v 11 Kada ku sanya rigar da aka saƙa da ulu garwaye da lilin.
\s5
\v 12 Dole kuyi wa kanku geza a kusurwoyi huɗu na suturar da kuke suturta kanku.
\s5
\v 13 Idan mutum ya ɗauki mace, ya kwana da ita, daga nan ya ƙi ta,
\v 14 kuma yana zarginta da yin abubuwan kunya ya sanya mummunar shaida akan ta, ya ce, 'Na ɗauki wannan mace, amma sa'ad da na yi kusa da ita, Na iske babu shaidar budurci a cikinta.'
\s5
\v 15 Daganan sai mahaifinta da mahaifiyar yarinyar su kawo shaidar budurcinta gaban dattawa a ƙofar birni.
\s5
\v 16 Mahaifin yarinyar zai cewa dattawan, 'Na bada 'yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta.
\v 17 Duba, ya zarge ta da abubuwan kunya har ya ce, 'Ban sami ɗiyarka da shaidar budurci ba.' Amma ga shaidar budurcin 'yata.' Daganan zasu shimfiɗa ƙyalle a gaban dattawan birni.
\s5
\v 18 Sai dattawan garin su kama wannan mutumin su hukunta shi;
\v 19 kuma zasu yi masa tarar awo ɗari na azurfa, su bada su ga mahaifin yarinyar, saboda mutumin ya bada mummunar shaida ga budurwa a Isra'ila. Dole ta zama matarsa; ba shi da iko ya sallame ta dukkan kwanakin ransa.
\s5
\v 20 Amma idan wannan gaskiya ne, cewa ba a ga shaidar budurci a cikin yarinyar ba,
\v 21 daganan dole su kawo yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, daganan mutanen garin dole su jejjefeta da duwatsu har ta mutu, saboda ta aikata abin kunya a cikin Isra'ila, ta aikata karuwanci a cikin gidan mahaifinta; ta haka za ku kawar da mugunta a cikinku.
\s5
\v 22 Idan aka iske mutum yana kwana da matar wani, dukkansu biyu dole su mutu, wato mutumin da ke kwana da matar da matar kanta; ta haka zaku kawar da mugunta daga cikinku.
\s5
\v 23 Idan akwai yarinyar da ke budurwa, da wani ke tashinta, sai wani mutum ya iske ta cikin gari ya kwana da ita,
\v 24 ku ɗauki dukkansu biyun zuwa ƙofar birni, a jejjefe su su mutu. Dole ku jejjefe yarinyar da duwatsu, saboda bata yi kururuwa ba, koda shike tana cikin gari. Dole ku jejjefe mutumin, saboda ya ɓata matar maƙwabcinsa; kuma dole ku kawar da mugunta daga cikinku.
\s5
\v 25 Amma idan mutumin ya iske yarinyar a cikin gona, idan ya ɗauke ta da ƙarfi ya kwana da ita, daga nan mutumin kaɗai daya kwana da ita za a kashe.
\v 26 Amma ga yarinyar ba za ayi mata kome ba; domin bata yi zunubin da ya cancanci mutuwa ba. Gama wannan matsalar na dai-dai da mutumin da ya fãɗa wa maƙwabcinsa ya kashe shi.
\v 27 Gama ya same ta a cikin gona; ita wadda ake tashinta ta yi kururuwa, amma ba wanda zai cece ta.
\s5
\v 28 Idan mutum ya iske yarinya wadda take budurwa amma ba a tashinta, idan ya kama ta da ƙarfi ya kwana da ita, idan aka gane su,
\v 29 shi mutumin da ya kwana da ita dole ya biya shekel hamsin na azurfa ga mahaifin yarinyar, kuma dole ta zama matarsa, saboda ya ƙasƙantar da ita. Ba zai sallame ta ba dukkan kwanakin ransa.
\s5
\v 30 Kada mutum ya ɗauki matar mahaifinsa a matsayin matarsa; kada kuma ya ɗauke 'yancin auren mahaifinsa.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Ba mutumin da aka yi wa rauni ta wurin dandaƙa ko yanke gabansa da zai shiga taron jama'ar Yahweh.
\v 2 Shegen ɗa ba zai shiga taron jama'ar Yahweh ba; har tsara ta goma ta zuriyarsa, ba mutum a cikinsu da zai kasance a taron jama'ar Yahweh.
\s5
\v 3 Ba'ammone ko Bamowabe ba zai zama cikakken mutum a taron jama'ar Yahweh ba; har tsara ta goma ta zuriyarsu, ba wani a cikinsu da zai shiga taron jama'ar Yahweh ba.
\v 4 Saboda basu zo sun tarye ku da abinci da ruwa ba sa'ad da kuke kan hanyarku lokacin da kuka fito daga Masar, kuma suka yi hayar Bala'am ɗan Beyor daga Fetor cikin Aram Naharayim, ya la'anta ku.
\s5
\v 5 Amma Yahweh Allahnku bai saurari Bala'am ba; sai Yahweh Allahnku ya juyar da la'anar ta zama albarka dominku, saboda Yahweh Allahnku yana ƙaunarku.
\v 6 Kada ku taɓa nemar musu zaman lafiya ko wadata, lokacin dukkan kwanakinku.
\s5
\v 7 Kada kuji ƙyamar Ba'idome, gama shi ɗan uwanku ne; kada ku ƙi Bamasare, domin kunyi baƙunci a cikin ƙasarsa.
\v 8 Zuriyarsu tsara ta uku da aka haifa masu zasu iya shiga taron jama'ar Yahweh.
\s5
\v 9 Sa'ad da kuka fita domin ku kafa sansani gãba da maƙiyanku, daganan dole ku kiyaye kanku daga kowanne mugun abu.
\v 10 Idan a cikinku akwai wani mutum daya ƙazantu saboda abin da ya faru da shi da dare, daganan dole ya fita daga cikin sansanin; kada ya komo cikin sansanin.
\v 11 Sa'ad da yamma ta yi, dole ya yi wanka cikin ruwa; sa'ad da rana ta faɗi, sai ya dawo cikin sansani.
\s5
\v 12 Dole ku kasance da wani wuri kuma a bayan sansani in da zaku je;
\v 13 kuma sai ku kasance da wani abu cikin kayanku da zaku yi gini da shi; sa'ad da kuka tsuguna domin kuyi bayan gari, dole kuyi gini da shi daganan sai ku mayar da ƙasar ku rufe bayan garin da kuka yi.
\v 14 Gama Yahweh Allahnku yakan yi yawo cikin sansaninku ya baku nasara ya kuma bada maƙiyanku cikin hannunku. Domin haka dole sansaninku ya kasance da tsarki, domin kada ya ga abu mara tsarki a cikinku ya juya daga gare ku.
\s5
\v 15 Kada ku bada bawan da ya tsere daga ubangijinsa.
\v 16 Ku bar shi ya zauna tare daku, a cikin kowanne garin da ya zaɓa. Kada ku tsananta masa.
\s5
\v 17 Kada a sami ko ɗaya daga cikin 'yan'matan Isra'ila, ko 'ya'yansu maza a cikin ƙungiyar karuwanci na addini.
\v 18 Kada ku kawo kuɗin da aka samu ta wurin karuwanci ko kuɗin da aka samu tawurin yin luɗu a cikin haikalin Yahweh Allahnku domin cika kowanne wa'adi; gama dukkan wannan abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 19 Kada ku bada bashi da ruwa ga danginku Ba-isra'ile - ribar kuɗi, ribar abinci, kona kowanne irin abu da akan bada shi da ruwa.
\v 20 Ga wanda ya ke baƙo zaku iya bashi rance da ruwa, domin Yahweh Allahnku yasa maku albarka a kan dukkan abin da kuka sa hannunku ga yi, a cikin ƙasar da zaku shiga ku mallake ta.
\s5
\v 21 Sa'ad da kuka yi wa'adi ga Yahweh Allahnku, kada kuyi jinkirin cikawa, gama Yahweh Allahnku lallai zai neme shi gare ku; zai zama zunubi a gare ku idan baku cika shi ba.
\v 22 Amma idan kuka nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.
\v 23 Duk abin da ya fita daga cikin leɓunanku dole ku kula ku aikata; bisa ga yadda kuka alƙawarta ga Yahweh Allahnku, duk abin da kuka alƙawarta da yaddar ranku da bakinku.
\s5
\v 24 Sa'ad da kuka shiga cikin gonar inabin maƙwabcinku, zaku iya cin inabin 'ya'yan inabin yadda kuke so har ku ƙoshi, amma kada ku sa ko ɗaya a cikin kwandonku.
\v 25 Sa'ad da kuka shiga cikin hatsin maƙwabcinku daya nuna, zaku iya tsinke kawunan hatsin da hannunku, amma kada ku sa lauje ku yanki hatsin maƙwabcinku da ya nuna.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Idan namiji ya ɗauki mata ya aure ta, idan bata sami tagomashi a idanunsa ba saboda ya sami wani abin aibatarwa da ita, sai dole ya rubuta mata takardar saki, yasa a hannunta, ya sallame ta daga gidansa.
\v 2 Sa'ad da ta fita daga gidansa, zata iya ta tafi ta zama matar wani.
\s5
\v 3 Idan mijinta na biyun ya ƙi ta ya kuma rubuta mata takardar saki, yasa mata a hannunta, ya kuma sallame ta daga gidansa; ko kuma mijinta na biyun ya rasu, wato mutumin daya ɗauke ta ta zama matarsa -
\v 4 sai mijinta na dã, wannan na farko wanda ya fara sallamar ta, ba zai koma ya ɗauke ta ta zama matarsa kuma ba, bayan ta rigaya ta ƙazamtu; domin wannan zai zama abin ƙyama ga Yahweh. Ba zaku sa ƙasar ta zama da laifi ba, ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku abin gado.
\s5
\v 5 Lokacin da namiji ya ɗauki sabuwar mata, ba zai tafi yaƙi da sauran mayaƙa ba, ba za a kuma umarce shi ya tafi ya yi aikin ƙarfi da yaji ba; yana da 'yanci ya zauna a gida har shekara guda ya faranta wa matarsa da ya aura rai.
\s5
\v 6 Kada wani ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, domin wannan zai zama karɓar ran mutum ne jingina.
\s5
\v 7 Idan an kama wani ya saci ɗan'uwansa daga cikin mutanen Isra'ila, ya mai da shi kamar bawa ya saida shi, wannan ɓarawon dole ya mutu; haka zaku kawar da mugunta daga tsakaninku.
\s5
\v 8 Ku kula game da annobar kuturta, domin ku aikata dai-dai a kowace ka'ida da aka baku, wanda firistoci, da lebiyawa, suka koya maku; kamar yadda na umarce su, haka zaku yi.
\v 9 Ku tuna da abin da Yahweh Allahnku ya yi wa Maryamu sa'ad da kuke fitowa daga Masar.
\s5
\v 10 Sa'ad da ka ranta wa makwabcinka wani irin abu, ba zaka shiga cikin gidansa ka ɗauko jinginar ba.
\v 11 Zaka tsaya a waje, sa'an nan mutumin nan daka ba shi rance zai fito waje ya baka jinginar.
\s5
\v 12 Idan mutumin matalauci ne, kada jinginarsa ta kwana a hannunka.
\v 13 Hakika dole zaka mayar masa da jinginarsa kafin faɗuwar rana, domin ya yi barci cikin mayafinsa yasa maka albarka; zai zama adalci dominka a gaban Yahweh Allahnka
\s5
\v 14 Ba zaka zalumci bawanka ɗan ƙwadago matalauci fakiri ba, ko shi ɗan'uwanka Ba'isra'ile, ko daga baƙi waɗanda ke cikin ƙasarku cikin ƙofofin biranenku;
\v 15 Dole kowacce rana ka bashi albashinsa; kada rana ta faɗi baka cika wa'adin nan ba, domin matalauci ne zuciyarsa tana kan hakinsa. Kayi wannan domin kada ya yi kuka gãba da kai ga Yahweh, kuma domin kada ya zama zunubin daka aikata.
\s5
\v 16 Ba za a kashe iyaye saboda 'ya'yansu ba, haka ma 'ya'ya ba za a kashe su saboda iyayensu ba. Maimakon haka, dole ne kowa ya mutu domin nasa zunubin.
\s5
\v 17 Ba zaka fizgi adalci daya cancanta karfi da yaji daga baƙo ba, ko maraya, ko ka ɗauki mayafin gwauruwa don jingina.
\v 18 Maimakon haka, zaku tuna ku bayi ne dã a Masar, kuma Yahweh Allahnku ya kuɓutar daku daga can. Saboda haka ina umartar ku kuyi biyayya da wannan doka.
\s5
\v 19 Sa'ad da kuka girbe amfaninku daga gonakinku, idan kuka manta da dami guda a gonar, kada ku koma domin ku ɗauko shi; dole zai zama domin baƙo, domin marayu, domin gwauruwa, saboda Yahweh Allahnku ya albarkace ku a cikin dukkan aikin hannuwanku.
\v 20 Sa'ad da kuka kakkaɓe itacen zaitunku, kada ku koma ku rore rassansu, zai zama domin baƙo, da marayu da, kuma gwauruwa.
\s5
\v 21 Sa'ad da kuka tattara 'ya'yan inabin garkarku, ba zaku yi kalarta kuma ba. Abin da aka bari baya zai zama na baƙo, na marayu, dana gwauruwa.
\v 22 Dole ne ku tuna dã ku bayi ne a cikin ƙasar Masar. Saboda haka ina umartarku kuyi biyayya da wannan doka.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Idan akwai jayayya tsakanin mutane sai suka tafi kotu, sai al'ƙalai suka shari'anta su, zasu kuɓutar da mai adalci su hukunta mugun.
\v 2 Idan mai laifi ya cancanci dukã, sai al'ƙali yasa shi ya kwanta ayi masa bulala a gabansa iya ƙididdigar bugun, daya dace da laifinsa.
\s5
\v 3 Al'ƙali zai iya yi masa bulala arba'in, amma ba zai zarce wannan lambar ba; gama idan ya zarce lambar nan ya bulale shi da abin da yafi haka yawa, to za a ƙasƙantar da ɗan'uwanku Ba'isra'ile a kan idanunku.
\s5
\v 4 Ba zaku sa wa san da ke casar hatsi takunkumi ba.
\s5
\v 5 Idan 'yan'uwa maza suna zaune tare sai ɗayan ya rasu, kuma bashi da ɗa, ba za a aurar da matar marigayin ba ga wani a waje wanda baya cikin iyalin. Maimakon haka, dole ɗan'uwan miji marigayi ya kwana da ita ya ɗauke ta ta zama matarsa, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi mata.
\v 6 Wannan ya zama haka domin ɗan farin da zata haifa zai ci gaba da sunan ɗan'uwa marigayi, domin kada sunansa ya ɓace a Isra'ila.
\s5
\v 7 Amma idan mutumin baya so ya ɗauki matar ɗan'uwansa, sai matar ɗan'uwan ta tafi ƙofa wurin dattawa ta ce, 'Ɗan'uwan mijina yaƙi ya wanzar da sunan ɗan'uwansa a Isra'ila; ba zai yi abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi mani ba.'
\v 8 Dole sai dattawan birnin su kira shi suyi masa magana. Amma idan yaƙi ya ce, 'bana so in ɗauke ta.'
\s5
\v 9 Dole matar ɗan'uwansa ta je wajensa a gaban dattawa, ta cire takalminsa daga ƙafarsa, ta tofa masa miyau a fuskarsa. Zata amsa masa ta ce, 'Wannan shi ne abin da ake yi wa wanda yaƙi gina gidan ɗan'uwansa.'
\v 10 Za a kira sunansa a Isra'ila, 'Gidan wandan aka saluɓe takalminsa.'
\s5
\v 11 Idan mutane suka yi faɗa da junansu, sai matar ɗaya daga cikinsu ta zo ta kuɓutar da mijinta daga hannun wanda ya mare shi, idan ta miƙa hannuta ta kama gabansa,
\v 12 sai dole a yanke hannunta; kada idonku ya ji tausayi.
\s5
\v 13 Ba zaku riƙe ma'aunan nauyi iri biyu a jakarku ba, da babba da ƙarami.
\v 14 Ba zaku ajiye a cikin gidanku ma'aunai iri biyu ba, da babba da ƙarami.
\s5
\v 15 Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da ya ke dai dai; mudu na adalci zaku kasance da shi, domin kwanakinku suyi tsawo a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku.
\v 16 Domin duk masu yin irin abubuwan nan, duk waɗanda ke aikata rashin gaskiya, abin ƙyama ne ga Yahweh Allahnku.
\s5
\v 17 Ku tuna da abin da Amalek suka yi maku a hanya sa'ad da kuka fito daga Masar,
\v 18 yadda suka gamu daku a hanya suka fãɗa wa na bayanku, dukkan marasa ƙarfi na bayanku, sa'ad da kuka some kuka gaji; bai girmama Allah ba.
\v 19 Saboda haka, sa'ad da Yahweh Allahnku zai baku hutawa daga dukkan maƙiyanku da kewaye, a cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ya ke baku ku mallaka abin gado, ba zaku manta cewa dole ku shafe tunawa da Amalek daga ƙarƙashin sama ba.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Sa'ad da kuka zo ƙasar da Yahweh Allahnku ke ba ku abin gãdo, kuma lokacin da kuka mallaƙeta kuka zauna cikinta,
\v 2 sai dole ku ɗauki nunan farinku na dukkan girbin ƙasar wanda kuka kawo cikin gida daga ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku. Dole kusa shi a kwando ku je inda Yahweh Allahnku zai zaɓa a matsayin haikalinsa.
\s5
\v 3 Dole za ku je wajen firist wanda shi ne mai hidima a kwanakin nan kuce masa, 'Ina shaida yau ga Yahweh Allahnka cewa nazo ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninmu zai bamu.'
\v 4 Dole firist zai karɓi kwandon daga hannunsa ya ajiye shi a gaban bagadin Yahweh Allahnku.
\s5
\v 5 Dole ku faɗi haka a gaban Yahweh Allahnku, 'Kakana mayawacin Ba'aramiye ne. Ya gangara zuwa cikin Masar ya zauna a can, kuma mutanensa kima ne. A can ya yi girma, ya ƙasaita, kuma ya zama al'umma mai jama'a.
\s5
\v 6 Masarawa suka wulaƙanta mu ainun suka tsananta mana. Suka bautar da mu.
\v 7 Muka yi kuka ga Yahweh, Allah na ubanninmu, ya kuma ji muryarmu, ya dubi azabarmu da wahalarmu, da zalumtarmu da aka yita yi.
\s5
\v 8 Yahweh ya fitar da mu daga Masar da hannu mai ƙarfi, da damtsensa miƙaƙƙe, da babbar razanarwa, da alamu da kuma al'ajibai;
\v 9 ya kuma kawo mu nan wajen ya kuma bamu wannan ƙasar, ƙasa wacce take zuba da madara da zuma.
\s5
\v 10 Duba yanzu, na kawo maka nunan fari na girbin ƙasar da kai, Yahweh, ka bani.' Dole ka ajiye shi a gaban Yahweh Allahnka kayi sujada a gabansa;
\v 11 kuma dole kayi farinciki cikin dukkan abubuwa nagari da Yahweh Allahnka ya yi dominka, da kuma gidanka - da kai. da kuma Lebiyawa, da baƙon da ke tsakiyarku.
\s5
\v 12 Bayan kun gama bada dukkan zakkarku ta girbi a shekara ta uku, wato, shekara ta zakka, dole ne kuba Lebiyawa, da baƙo, da maraya, da kuma gwauruwa, domin su ci a ƙofofin biranenku su kuma ƙoshi.
\v 13 Dole ku ce a gaban Yahweh Allahnku, 'Na kawo waɗannan daga cikin gidana abubuwan da suke na Yahweh, na kuma ba Lebiyawa, da baƙo da maraya, da kuma gwauruwa, bisa ga dukkan umarnai waɗanda ka bani. Ban kuskure ko kaɗan ba daga umarnanka, ban kuma manta da su ba.
\s5
\v 14 Ban ci ko kaɗan daga cikinsu a cikin baƙin cikina ba, ban kuma aje su a wani wuri marar tsarki ba, ko in miƙa su don girmama matacce. Na saurari muryar Yahweh Allahna; Nayi biyayya da dukkan abin da ka umarce ni in yi.
\v 15 Ka duba daga wuri mai tsarki inda kake zaune, daga sama, ka albarkaci mutanenka Isra'ila, da ƙasar daka bamu, kamar yadda ka rantse wa ubanninmu, ƙasa wadda take zuba da madara da zuma.'
\s5
\v 16 Yau, Yahweh Allahnku yana umartarku kuyi biyayya da ka'idodinsa da dokokinsa; saboda haka za ku kiyaye su zaku yi biyayya da su da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku.
\v 17 Kun furta yau cewa Yahweh shi ne Allahnku, zaku kuma yi tafiya a tafarkunsa ku kuma kiyaye ka'idodinsa, da umarnansa da dokokinsa, cewa kuma zaku kasa kunne da muryarsa.
\s5
\v 18 Yau Yahweh ya furta cewa ku mutane ne waɗanda mallakarsa ce, kamar yadda ya alƙawarta maku, cewa zaku yi biyayya da dukkan umarnansa,
\v 19 zai fifita ku sama da dukkan sauran al'umman da ya yi, zaku kuma sami yabo, da suna, da daraja. Zaku zama mutanen da aka keɓe su ga Yahweh Allahnku, kamar yadda ya faɗi."
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Musa da dattawan Isra'ila suka umarci mutanen suka ce, "Ku kiyaye dukkan umarnan dana umarce ku yau.
\v 2 A ranar da zaku tsallake Yodan zuwa ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku, sai dole ku kafa manyan duwatsu ku shafe su da farar ƙasa.
\v 3 Dole ne ku rubuta a kansu dukkan maganganun dokokin nan sa'ad da kuka rigaya kuka ƙetare; domin ku tafi cikin ƙasar da Yahweh Allahnku ke baku, ƙasa mai zubar da madara da zuma, kamar yadda Yahweh, Allahn kakanninku ya yi maku alƙawari.
\s5
\v 4 Sa'ad da kuka ƙetare Yodan, ku kafa waɗannan duwatsu da nake umartanku yau, a kan Dutsen Ibal, ku shafe su da farar ƙasa.
\v 5 A can zaku gina bagadi ga Yahweh Allahnku, bagadi na duwatsu; amma ba zaku yi amfani da alatu na ƙarfe ku sassaƙa duwatsun ba.
\s5
\v 6 Dole ku gina wa Yahweh Allahnku bagadin da ba a sassaƙa duwatsun ba. Dole ku miƙa baye-baye na ƙonawa a kansa ga Yahweh Allahnku,
\v 7 zaku miƙa hadayar baye-baye na zumunci ku kuma ci a can; zaku yi farinciki a gaban Yahweh Allahnku.
\v 8 Zaku rubuta dukkan waɗannan maganganu na wannan dokoki a kan duwatsu su fita a fili sosai."
\s5
\v 9 Musa da firistoci, da Lebiyawa, suka yi magana da dukkan Isra'ilawa suka ce,
\v 10 "Kuyi shuru ku saurara, ya Isra'ila: Yau kun zama mutanen Yahweh Allahnku. Saboda haka dole kuyi biyayya da muryar Yahweh Allahnku ku kuma yi biyayya da umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartan ku yau."
\s5
\v 11 Musa ya umarci mutanen a ranan nan ya ce,
\v 12 "Waɗannan kabilu dole su tsaya a kan Dutsen Gerizim su albarkaci mutane bayan kun ƙetare Yodan: Simiyon, da Lebi, da Yahuda, da Isakar, da Yosef, da kuma Benyamin.
\s5
\v 13 Waɗannan su ne kabilun da dole su tsaya a kan Dutsen Ibal su furta la'anu: Ruben, da Gad, da Ashar, da Zebulun, da Dan da kuma Naftali.
\v 14 Lebiyawa zasu amsa su cewa dukkan mutanen Isra'ila da murya mai ƙafi:
\s5
\v 15 Bari mutumin ya zama la'ananne wanda ya siffanta ko ya yi zubin ƙarfe, abin ƙyama ga Yahweh, aikin hannun gwanin masassaƙi, wanda ya kafa shi a asirce.' Dole ne dukkan mutane su amsa su ce, 'Amin.'
\s5
\v 16 'Bari mutumin ya zama la'ananne wanda bai girmama mahaifinsa da mahaifiyarsa ba.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\v 17 'Bari mutumin ya zama la'ananne wanda ya cire shaidar iyakar makwabcinsa.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\s5
\v 18 Bari mutumin ya zama la'ananne wanda yasa makaho ya saki hanya.' Sai dole mutanen su ce,; Amin.'
\v 19 Bari mutumin ya zama la'ananne wandan karfi da yaji ya ƙwace adalci daga baƙo, maraya, ko gwauruwa.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce. 'Amin.'
\s5
\v 20 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, domin ya karɓe hakkin mahaifinsa.' Daganan sai dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\v 21 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da kowacce irin dabba.' Daganan dole ne dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\s5
\v 22 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, ɗiyar mahaifinsa, ko ɗiyar mahaifiyarsa.' Daganan dukkan mutane dole su ce, 'Amin.'
\v 23 'Bari mutumin nan da zai kwana da surukarsa ya zama la'ananne.' Daganan dukkan mutane dole su ce, 'Amin.'
\s5
\v 24 Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ya kashe makwabcinsa a ɓoye.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\v 25 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda zai karɓi toshiya domin ya kashe da mutum marar laifi.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\s5
\v 26 'Bari mutumin nan ya zama la'ananne wanda ba zai yi biyayya da shariɗun nan ba.' Sai dole dukkan mutane su ce, 'Amin.'
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Idan kuka saurari muryar Yahweh Allahnku da kirki domin ku kiyaye dukkan dokokin nan da nake umartan ku yau, Yahweh Allahnku zai fifita ku fiye da dukkan sauran al'umman duniya.
\v 2 Dukkan waɗannan albarku zasu zo bisanku har ma suyi amabaliya, idan kuka saurari muryar Yahweh Allahnku.
\s5
\v 3 Zaku zama da albarka cikin birni, kuma zaku zama da albarka a jeji.
\v 4 'Ya'yanku zasu zama da albarka, ƙasarku zata zama da albarka wajen bada amfani, da'ya'yan dabbobinku, shanunku zasu yi yabanya, haka ma 'ya'yan tumakinku.
\s5
\v 5 Kwandunanku zasu zama da albarka, haka ma wurin kwaɓar wainarku.
\v 6 Zaku shiga da albarka, ku fita da albarka.
\s5
\v 7 Yahweh zai sa maƙiyanku da suka tashi gãba daku a buge su a gaban ku; zasu tasar maku ta gefe guda amma zasu gudu daga gaban ku ta hanyoyi bakwai.
\v 8 Yahweh zai umarta albarka ta zo bisanku a cikin rumbunanku, kuma da cikin dukkan abin da kuka sa hannunku; zai albarkace ku a cikin ƙasar da ya ke ba ku.
\s5
\v 9 Yahweh zai kafa ku a matsayin mutanen daya keɓe domin kansa, kamar yadda ya rantse maku, idan kuka kiyaye umarnan Yahweh Allahnku, kuma kuka yi tafiya a hanyoyinsa.
\v 10 Dukkan al'umman duniya zasu ga ana kiranku da sunan Yahweh, zasu kuwa ji tsoronku.
\s5
\v 11 Yahweh zai azurta ku ainun, da 'ya'yan jikinku, da 'ya'yan shanunku, da amfanin ƙasa, a ƙasar da ya rantse wa ubanninku zai baku.
\v 12 Yahweh zai buɗe maku rumbunsa na sammai ya baku ruwa domin ƙasarku a dai-dai lokaci, ya kuma albarkaci dukkan aikin hannuwanku; zaku ranta wa al'ummai da yawa, amma ku ba zaku karɓi rance ba.
\s5
\v 13 Yahweh zai saku zama kai, ba wutsiya ba; zaku kasance kullum a bisa, ba a ƙasa ba, idan kun kasa kunne ga umarnan Yahweh Allahnku da nake umartanku yau., domin ku lura ku yi su,
\v 14 kuma idan baku juya daga waɗannan maganganu da nake umartanku a yau, ga hannun dama ko hagu ba, har da zaku bi waɗansu alloli ku bauta masu.
\s5
\v 15 Amma idan baku saurari muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye dukkan umarnansa da ka'idodinsa da nake umartan ku yau ba, to dukkan waɗannan la'anu zasu afka maku su mamayeku.
\s5
\v 16 La'anannu zaku zama cikin birni, la'anannu zaku zama a jeji.
\v 17 La'ana za ta bi kwandonku da kuma makwabar wainarku.
\s5
\v 18 'Ya'yanku zasu zama la'anannu, amfanin gonakinku zasu zama la'anannu, da 'yan maruƙanku da 'ya'yan garken tumakinku.
\v 19 La'anannu ne ku sa'ad da kuka shiga, la'anannu ne ku sa'ad da kuka fita.
\s5
\v 20 Yahweh zai aiko maku la'ana, ruɗewa, da kwaɓa a dukkan abin da kuka ɗibiya hannunku, har sai kun lalace har sai kun hallaka nan da nan sabili da miyagun ayyukanku ta yadda kuka yashe ni.
\v 21 Yahweh zai sa annoba ta manne maku har sai ya hallaka ku daga ƙasar da kuke tafiya zuwa cikin ta ku mallaka.
\s5
\v 22 Yahweh zai buge ku da annobai masu yaɗuwa, zazzaɓi, da marurai, da fãri, da zafin rana, da iska mai ƙuna, da kuturta. Waɗannan zasu runtume ku har sai kun hallaka.
\s5
\v 23 Samaniyar da ke kanku zata zama tagulla, ƙasar kuma da ke ƙarƙashinku zata zama ƙarfe.
\v 24 Yahweh zai maida ruwan saman ƙasarku gari da ƙura; daga sammai zasu sabko kanku, har sai kun hallaka.
\s5
\v 25 Yahweh zai sa a buge ku a gaban maƙiyanku; za ku fita ta hanya guda gãba da su zaku guje daga gabansu ta hanyoyi bakwai. Za a yi ta kora ku gaba da baya cikin dukkan mulkokin duniya.
\v 26 Gawawakinku za su zama abinci ga dukkan tsuntsayen sama da dabbobin duniya; ba wanda zai tsorata su su gudu.
\s5
\v 27 Yahweh zai far maku da maruran Masar da gyambuna, da ƙusumbi, da ƙaiƙayi wanda ba za a iya warkar daku daga su ba.
\v 28 Yahweh zai buge ku da ciwon hauka, da makamta, da rikicewar hankali.
\v 29 Zaku yita lalubawa da tsakar rana kamar yadda makaho ya ke yi a duhu, ba zaku azurta ba a ayyukanku; kullum za ayi ta zalumtarku ana maku ƙwace, ba kuma wanda zai cece ku.
\s5
\v 30 Zaku yi tashin matã, amma wani namiji zai ƙwace ta ya yi mata fyaɗe. Zaku gina gida amma ba zaku zauna a ciki ba; zaku noma garkar inabi amma ba zaku ji daɗin 'ya'yansa ba.
\v 31 Za a yanka san nomanku a kan idanunku; amma ba zaku ci namansa ba; za a karɓe jakinku ƙiri ƙiri ƙarfi da yaji ba za a kuma mayar maku ba. Za a bada tumakinku ga magabtanku, ba ko ɗaya da zaku samu ya taimaka maku.
\s5
\v 32 Za a bada 'ya'yanku maza da mata ga wasu mutane; idanunku zasu neme su dukkan rana, amma za su gaji da sa zuciya. Hannuwanku zasu yi rauni.
\s5
\v 33 Girbin ƙasarku da dukkan wahalarku - wata al'ummar da baku santa ba zata cinye su; kullum za a zalumce ku a murƙushe ku,
\v 34 haka zaku haukace tawurin abin da ya zama dole ku ga ya faru.
\v 35 Yahweh zai bugi gyiwowinku da ƙafafunku da marurai wanda ba za a iya warkar daku daga su ba, daga tafin kafafunku har ƙolƙolin kanku.
\s5
\v 36 Yahweh zai ɗauke ku da sarkin da zaku naɗa bisa kanku zuwa wata al'umma da baku santa ba, koku ko kakanninku; a can zaku yi sujada ga allolin itace da duwatsu.
\v 37 Zaku zama ban tsoro, da karin magana, da gatse, cikin dukkan mutane inda Yahweh zai kora ku.
\s5
\v 38 Zaku kai hatsi da yawa gona, amma zaku sami amfanin hatsin kaɗan, gama fãri zasu cinye su.
\v 39 Zaku dasa garkunan inabi ku kuma noma su, amma ko kaɗan ba zaku sha ruwansu ba, ba ma zaku girbi 'ya'yansu ba, gama tsutsotsi zasu cinye su.
\s5
\v 40 Zaku kasance da itatuwan zaitun a dukkan yankinku, amma ba zaku shafa ko ɗan man a jikinku ba, gama itatuwan zaitunku zasu zubar da 'ya'yansu.
\v 41 Zaku haifi 'ya'ya maza da mata, amma ba zasu zama naku ba, gama zasu tafi bautar talala.
\s5
\v 42 Dukkan itatuwanku da amfanin ƙasarku - fãri za su mamayesu.
\v 43 Baƙon da ke tsakiyarku zai yi ta ƙaruwa fiye daku gaba gaba; amma ku zaku yi ta komawa baya baya.
\v 44 Zai ranta maku, amma ku ba za ku ranta masa ba; shi zai zama kai, ku kuwa zaku zama wutsiya.
\s5
\v 45 Dukkan waɗannan la'anu zasu afko kanku su bi ku su chafke ku har sai sun hallaka ku. Wannan zai faru domin ba ku saurari muryar Yahweh Allahnku ba, da zaku kiyaye umarnansa da farillansa daya umarce ku.
\v 46 Waɗannan la'anu suna kanku a matsayin alamu da al'ajibai, da kuma kan zuriyarku har abada.
\s5
\v 47 Saboda baku yi sujada ga Yahweh Allahnku tare da murna da farin cikin zuciya lokacin yalwarku ba,
\v 48 domin wannan fa, zaku bauta wa maƙiyan da Yahweh zai aiko gãba da ku; zaku bauta masu da yunwa, cikin ƙishirwa, cikin tsiraici, da cikin talauci. Zai ɗibiya maku karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku.
\s5
\v 49 Yahweh zai aiko da wata al'umma gãba daku daga nesa, daga ƙarshen duniya, kamar yadda gaggafa takan fyauce abincinta, al'ummar da baku fahimci harshenta ba;
\v 50 al'umma da fuskarta abin ban razana ne waɗanda bata ganin kwarjinin tsoffi ko ta nuna alfarma ga matashi.
\v 51 Zasu cinye 'yan maruƙanku da amfanin ƙasarku har sai sun hallaka ku. Ba zasu bar maku hatsi ba, ko sabon ruwan inabi, ko mai, ko 'yan maruƙanku na shanu ko na tumaki, har sai sun saku ku lalace.
\s5
\v 52 Zasu yi maku kwanto a dukkan ƙofofin biranenku, har sai tsararrun ganuwowinku masu tsayi sun faɗi a koina a ƙasarku, garu waɗanda kuka dogara a gare su. Zasu kafa maku dãga a dukkan ƙofofin biranenku a dukkan iyakar ƙasar da Yahweh Allahnku ya baku.
\v 53 Zaku ci 'ya'yan da kuka haifa, naman 'ya'yanku maza da na 'ya'ya mata, waɗanda Yahweh Allahnku ya baku, a cikin kwanto da wahalai waɗanda maƙiyanku zasu ɗibiya maku.
\s5
\v 54 Mutum mai taushin zuciya kuma mai kula da ke tare daku-zai ji kyashin ɗan'uwansa da matarsa da ya ke ƙauna, da dukkan yaransa da suka rage.
\v 55 Ba zai ba ko ɗayansu naman 'ya'yan jikinsa da zai ci ba, domin ba abin da zai rage ya ci don kansa a cikin kwanto da wahalai da maƙiya suka ɗibiya maku a dukkan ƙofofin biranenku.
\s5
\v 56 Mace mai taushin zuciya mai kula da ke a cikinku, wanda ba za ta kuskura ta aje tafin sawunta a ƙasa saboda taushin zuciya da kyakkyawan hali - zata ji kyashin mijinta da take ƙauna, da ɗanta, da ɗiyarta,
\v 57 da sabon jaririnta da ya fito ta tsakanin ƙafafunta, da 'ya'ya waɗanda zata haifa. Zata cinye su a ɓoye domin babu abinci, a cikin kwanto da wahalai waɗanda maƙiyanku zasu ɗibiya maku a ƙofofin biranenku.
\s5
\v 58 Idan ba ku kiyaye dukkan maganganun dokokin da aka rubuta cikin wannan littafi ba, domin ku girmama wannan suna mai ɗaukaka da banrazana, Yahweh Allahnku,
\v 59 sai Yahweh ya tsananta annobarku, dana zuriyarku; za a yi maku manyan annobai, masu tsawon lokaci, cututuka masu azabtarwa, na dogon lokaci.
\s5
\v 60 Zai sake maido da dukkan cututukan Masar bisa kanku waɗanda kuka ji tsoronsu; zasu manne maku.
\v 61 Kuma kowacce cuta da annoba da ba a rubuta a wannan littafin shari'a ba, su kuma Yahweh zai kawo bisa kanku har sai kun hallaka.
\v 62 'Yan kaɗan zaku ragu, koda shike dã kuna kamar taurarin sammai a yawa, saboda baku saurari muryar Yahweh Allahnku ba.
\s5
\v 63 Kamar yadda dã Yahweh ya yi farinciki da yi maku kirki, ya riɓaɓɓanya ku, haka ma zai yi farinciki da saku ku lalace da kuma hallakar daku. Za a tumbuƙe ku daga ƙasar da kuke tafiya ku mallaka.
\v 64 Yahweh zai warwatsar daku cikin dukkan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan bangon duniya; a can za ku yi sujada ga allolin da baku taɓa sani ba, ko ku, ko kakanninku, allolin itace da dutse.
\s5
\v 65 Ba zaku sami sakewa wurin waɗannan al'umman ba, kuma babu hutawa ga tafin ƙafafunku; maimakon haka, Yahweh zai baku a can zuciya mai fargaba, idanu marasa gani, da rai mai makoki.
\v 66 Ranku zai kasance cikin shakka a gabanku; zaku zauna cikin tsoro kowanne dare da rana baku da tabbas ko kaɗan a dukkan rayyuwarku.
\s5
\v 67 Da safe zaku ce, 'Ina ma maraice ne!' da maraice zaku ce, 'Ina ma safiya ce!' saboda da tsoro a zukatanku da abubuwan da dole idanunku su gani.
\v 68 Yahweh zai dawo daku cikin Masar a jiragen ruwa, ta hanyar dana riga na faɗa maku, 'Ba zaku ƙara ganin Masar ba.' A can zaku miƙa kanku domin saye ga maƙiyanku bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku."
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Waɗannan su ne maganganun da Yahweh ya umarta wa Musa ya faɗi wa 'ya'yan Isra'ila a ƙasar Mowab, maganganu da aka ƙara a kan alƙawarin da ya yi da su a Horeb.
\s5
\v 2 Musa ya kira dukkan Isra'ila ya ce masu, "Kun dai ga dukkan abin da Yahweh ya yi a kan idanunku a ƙasar Masar ga Fir'auna, da dukkan barorinsa da dukkan ƙasarsa -
\v 3 manyan wahalai da idanunku suka gani, da alamu, da waɗannan dukkan al'ajibai.
\v 4 Har wa yau Yahweh bai baku zuciya ta sani ba, idanu domin a gani, ko kunnuwa domin ji.
\s5
\v 5 Na bisheku a jeji shekaru arba'in, rigunanku basu tsufa a jikinku ba, takalmanku ma basu tsufa a ƙafafunku ba.
\v 6 Baku ci waina ba, baku sha ruwan inabi ba, ko barasa mai sa maye, domin ku sani nine Yahweh Allahnku.
\s5
\v 7 Sa'ad da kuka zo wannan wurin, Sihon, sarkin Hesbon, da Og sarkin Bashan, suka fito suyi yaƙi gãba daku, muka buga su.
\v 8 Muka karɓe ƙasarsu muka ba Rubenawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manasa.
\v 9 Saboda haka, ku kiyaye waɗannan maganganun alƙawari ku aikata su, domin ku azurta cikin dukkan abubuwan da zaku yi.
\s5
\v 10 Kuna tsaye yau, dukkanku, a gaban Yahweh Allahnku, da sarkinku, da kabilunku, da dattawanku, da shugabanninku-da dukkan mazajen Isra'ila,
\v 11 da 'yan ƙanananku, da matanku, da baƙi waɗanda suke zaune a tsakiyarku cikin zangonku, da shi wanda ke saro maku itace da mai ɗibar maku ruwa.
\s5
\v 12 Kuna nan domin ku ƙulla alƙawari da Yahweh Allahnku da rantsuwa da Yahweh Allahnku ya ke yi da ku yau,
\v 13 domin ya maishe ku yau mutane na kansa, domin kuma ya zama Allahnku, kamar yadda ya yi maku magana, kamar kuma yadda ya rantse wa kakanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga kuma Yakubu.
\s5
\v 14 Domin bada ku kaɗai nake yin wannan alƙawari da rantsuwa ba -
\v 15 da kowannenku da ke tsaye tare da mu yau a gaban Yahweh Allahnmu - amma da kuma waɗanda basa nan tare da mu a yau.
\v 16 Kun sani mun zauna a ƙasar Masar, da yadda muka biyo ta tsakiyar al'ummai waɗanda kuka wuce.
\s5
\v 17 Kun ga allolinsu masu banƙyama da aka yi su da itace da dutse, azurfa da zinariya, da ke tsakiyar su.
\v 18 Ku tabbata ba wani a cikinku, wani mutum, mata, iyali, ko kabila da zuciyarsa take juyawa daga Yahweh Allahnmu, ya tafi ya yi sujada ga allolin waɗancan al'umman. Ku tabbata ba wani tushe a cikinku mai ba da ɗaci da dafi.
\v 19 Lokacin da mutumin nan yaji maganganun la'anan nan, zai albarkaci kansa ya ce a zuciyarsa, "Zan sami salama koda shike zan yi tafiya cikin taurin zuciyata.' Wannan zai haddasa hallaka mai adalci tare da mugu.
\s5
\v 20 Yahweh ba zai gafarta masa ba, fushin Yahweh da kishinsa zai auka wa mutumin nan, kuma dukkan la'anan da aka rubuta a littafin nan zasu bi ta kansa, Yahweh zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.
\v 21 Yahweh zai ware shi domin bala'i daga dukkan kabilun Isra'ila, domin kiyaye dukkan la'ana na alƙawari da aka rubuta cikin wannan littafin dokoki.
\s5
\v 22 Tsara mai zuwa, yaranku da zasu tashi a bayanku da baƙon da zai zo daga ƙasa mai nisa, zasu yi magana sa'ad da suka ga annobai a kan ƙasannan da cututukan da Yahweh yasa mata ciwo -
\v 23 sa'ad da suka ga dukkan ƙasar ta zama wuta da ƙibiritu, inda ba shuki ko ya bada 'ya'ya, inda ba tsiro, kamar sa'ad da aka kaɓar da Soduma da Gomarata, Adma da Zeboyim, waɗanda Yahweh ya hallakar cikin fushinsa da hasalarsa. -
\v 24 zasu ce tare da dukkan wasu al'ummai, 'Meyasa Yahweh ya yi wa ƙasar nan haka? Mene ne ma'anar zafin hasalar nan?'
\s5
\v 25 Sa'annan mutane zasu ce, 'Domin sun watsar da alƙawarin Yahweh, Allahn kakanninsu, da ya yi da su lokacin daya fitar da su daga ƙasar Masar,
\v 26 kuma domin sun tafi sun bauta wa wasu alloli suka russuna masu, allolin da basu sani ba ba kuma shi ya basu ba.
\s5
\v 27 Saboda haka fushin Yahweh ya yi ƙuna akan wannan ƙasa, har ya kawo a kanta dukkan la'anar da aka rubuta a littafin nan.
\v 28 Yahweh ya tumbuƙe su daga ƙasarsu cikin fushi, da hasala, da fushi mai ƙuna, ya kuma jefar da su cikin wata ƙasa, har wa yau.'
\s5
\v 29 Sanin abubuwan asiri na Yahweh Allahnmu ne kaɗai; amma abubuwan da aka bayyana su namu ne har abada mu da kuma zuriyarmu, domin mu aikata dukkan maganganun waɗannan dokoki.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Sa'ad da dukkan waɗannan abubuwa suka zo kanku, albarku da la'ana dana sa a gabanku, kuma sa'ad da kuka tuna da su yayin da kuna cikin dukkan al'ummai inda Yahweh Allahnku ya kora ku,
\v 2 sa'ad da kuma kuka koma ga Yahweh Allahnku kuka yi biyayya da muryarsa, kuna yin dukkan abin da na umarce ku yau - ku da 'ya'yanku, - da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku,
\v 3 sa'an nan Yahweh Allahnku zai komo daku daga bautar talala ya yi juyayinku; zai juya ya tattaroku daga cikin dukkan al'ummai da Yahweh Allahnku ya warwatsa ku.
\s5
\v 4 Idan korarrun mutanenku suna cikin manisantan wuraren ƙasa da sammai, daga can Yahweh Allahnku zai tattara ku, kuma daga can zai kawo ku.
\v 5 Yahweh Allahnku zai kawo ku cikin ƙasar da kakanninku suka mallaka, kuma zaku sake mallakarta; zai yi maku alheri ya riɓaɓɓanya ku fiye da yadda ya yi da kakanninku.
\s5
\v 6 Yahweh Allahnku zai yi wa zuciyarku kaciya da ta zuriyarku, domin ku ƙaunaci Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku da dukkan ranku, domin ku rayu.
\v 7 Yahweh Allahnku zai sa dukkan waɗannan la'ana a kan maƙiyanku da kan waɗanda suke ƙin ku, waɗanda suka tsananta maku.
\v 8 Zaku juyo kuyi biyayya da muryar Yahweh, kuma zaku aikata dukkan umarnansa da nake umartar ku yau.
\s5
\v 9 Yahweh Allahnku zai yalwata dukkan aikin hannunku, da 'ya'yan jikinku, da 'yan maruƙanku, da amfanin gonakinku, domin wadata; gama Yahweh zai sake yin farin ciki a kanku ya azurta ku, kamar yadda ya yi farinciki da ubanninku.
\v 10 Zai yi wannan idan kuka yi biyayya da muryar Yahweh Allahnku, kuka kiyaye umarnansa da sharuɗansa da ke rubuce cikin littafin dokokin nan, idan kuka juyo ga Yahweh Allahnku da dukkan zuciyarku da dukkan ranku.
\s5
\v 11 Domin wannan umarni da nake umartan ku yau baifi ƙarfin ku ba, kuma bai yi nisa har da ba zaku kama ba.
\v 12 Ba a sama ya ke ba, har da zaku ce, 'Wa zai je can sama domin mu ya sauko mana da ita yasa mu iya jinta, domin mu yi ta?'
\s5
\v 13 Kuma ba a ƙarshen ruwaye ya ke ba, da zaku ce, 'Wa zai haye ruwaye domin mu ya kawo mana ita yasa mu mu jita, domin mu aikata ta?'
\v 14 Amma maganar tana kurkusa da kai, a bakinka da kuma zuciyarka, domin ka aikata ta.
\s5
\v 15 Duba, yau nasa a gabanku rai da nagarta, mutuwa da mugunta.
\v 16 Idan kun yi biyayya da dokokin Yahweh Allahnku, waɗanda nake umartanku yau ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, ku yi tafiya a tafarkunsa, ku kuma kiyaye umarnansa, da ka'idodinsa da kuma farillansa, zaku rayu ku riɓaɓɓanya, kuma Yahweh Allahnku zai albarkace ku cikin ƙasar da kuke shigarta domin ku mallaka.
\s5
\v 17 Amma idan zuciyarku ta juya, baku saurara ba a maimako kuka janye kuka russuna wa waɗansu alloli kuka yi masu sujada,
\v 18 to yau ina maku shela cewa ba shakka zaku lalace; ba zaku yi tsawon kwanaki ba cikin ƙasar da kuke ƙetare Yodan domin ku shiga cikinta ku mallaka.
\s5
\v 19 Na kira sama da ƙasa suyi shaida gãba daku yau, cewa na ajiye a gabanku rai da mutuwa, albarku da la'ana; saboda haka ku zaɓi rai domin ku rayu, daku da zuriyarku.
\v 20 Kuyi wannan don ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, kuyi biyayya da muryarsa, ku kuma manne masa. Gama shi ne ranku da tsawon kwanakinku; kuyi haka domin ku zauna cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninku, ga Ibrahim, ga Ishaku, ga Yakubu kuma, zai ba su."
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Musa ya tafi ya faɗa wa Isra'ila waɗannan maganganu.
\v 2 Ya ce masu, "Yanzu ina da shekaru ɗari da ashirin bana iya shiga in fita; Yahweh ya ce mani, 'Ba zaka ƙetare wannan Yodan ba.'
\v 3 Yahweh Allahnku, zai sha gabanku; Zai hallaka waɗannan al'ummai a gaban ku, zaku ƙwace mallakarsu. Yoshuwa, zai jagorance ku, kamar yadda Yahweh ya faɗi.
\s5
\v 4 Yahweh zai yi masu kamar yadda ya yi wa Sihon da kuma Og, sarakunan Amoriyawa, da kuma ƙasarsu, waɗanda ya hallakar.
\v 5 Yahweh zai baku nasara a kansu sa'ad da zaku kara da su a yaƙi, zaku yi masu dukkan yadda na umarce ku.
\v 6 Ku ƙarfafa kuyi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, kada kuma ku firgita domin su; gama Yahweh Allahnku, shi ne wanda ya ke tafiya tare daku; ba zai kunyatar daku ba ko ya yashe ku."
\s5
\v 7 Musa ya kira Yoshuwa a gaban dukkan Isra'ila ya ce masa, "Ka ƙarfafa kayi karfin hali, gama zaka tafi da mutanen nan cikin ƙasar da Yahweh ya rantse wa kakanninsu zai basu; zaka sasu su gaje ta.
\v 8 Yahweh, shi ne wanda ya sha gabanku; zai kasance tare daku; ba zai kunyatar daku ba ba zai yashe ku ba; kada ku ji tsoro, kada ku karaya."
\s5
\v 9 Musa ya rubuta wannan doka yaba firistoci, 'ya'yan Lebi, waɗanda suke ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh; ya kuma ba dukkan dattawan Isra'ila.
\v 10 Musa ya umarce su ya ce, "A ƙarshen kowacce shekara bakwai, lokacin da aka ƙayyade domin kashe basussuka, lokacin Idin Rumfuna,
\v 11 lokacin da dukkan Isra'ila ke zuwa su bayyana a gaban Yahweh Allahnku a wurin da zai zaɓa domin haikalinsa, zaku karanta wannan doka a gaban dukkan Isra'ila a kunnuwansu.
\s5
\v 12 A tara mutane, da maza, da mata, da 'yan ƙanana, da baƙon da ya ke a cikin ƙofar birninku, domin su ji su koya, domin kuma su girmama Yahweh Allahnku su kiyaye dukkan maganganun wannan dokoki.
\v 13 Kuyi wannan domin 'ya'yansu da ba su sani ba, su ji su koya su girmama Yahweh Allahnku, dukkan kwanakin da zaku kasance a ƙasar nan da kuke ƙetare Yodan domin ku mallaketa."
\s5
\v 14 Yahweh ya cewa Musa, "Duba rana tana zuwa, da dole ka mutu; ka kira Yoshuwa ku nuna kanku a rumfar taruwa, domin in ba shi umarni." Sai Musa da Yoshuwa suka tafi suka nuna kansu a rumfar taruwa.
\v 15 Sai Yahweh ya bayyana a umudin girgije; umudin girgijen ya tsaya a bakin ƙofar rumfa.
\s5
\v 16 Yahweh ya cewa Musa, "Duba, zaka yi barci tare da ubanninka; waɗannan mutane zasu tashi suyi kamar karuwai su bi waɗansu baƙin alloli waɗanda ke a tsakaninsu a cikin ƙasar da zasu. Zasu yasheni su karya alƙawarin da nayi da su.
\s5
\v 17 Sa'annan, a ranar nan, fushina zai yi ƙuna a kansu zan kuwa yashe su. Zan ɓoye fuskata za a kuma hallaka su. Masifu da wahalai zasu auka masu zasu ce a ranan nan, 'Ba waɗannan masifu sun zo kanmu domin Allahnmu ba shi tare da mu ba?'
\v 18 Hakika zan ɓoye fuskata daga gare su a ranar nan, saboda dukkan muguntar da zasu aikata, domin sun juya ga waɗansu alloli.
\s5
\v 19 Saboda haka yanzu fa, ka rubuta wannan waƙa domin kanku ka koya wa mutanen Isra'ila. Ka sa a bakinsu, domin wannan waƙa ta zama shaida gãba da mutanen Isra'ila.
\v 20 Gama bayan na kawo su cikin wannan ƙasar dana rantse zan ba kakaninsu ƙasa mai zuba da madara da zuma, bayan sun ci sun ƙoshi sun yi ƙiba, zasu juya ga wasu alloli su kuma bauta masu su rena ni su karya alƙawarina.
\s5
\v 21 Sa'ad da mugayen abubuwa da wahalai suka zo kan mutanen nan wannan waƙa za ta faɗa a gabansu ita ce shaida (gama ba za a manta ta ba a bakunan tsararrakinsu). Gama na san shirye-shiryen da suke ƙuƙƙullawa yau, tun ma kafin in kawo su ƙasar dana alƙawarta masu."
\s5
\v 22 Sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranan nan ya kuma koya wa mutanen isra'ila.
\v 23 Yahweh ya ba Yoshuwa ɗan Nun umarni ya ce, "Ka ƙarfafa kayi ƙarfin hali; gama zaka kawo mutanen Isra'ila cikin ƙasar dana rantse masu, zan kuma kasance tare da kai."
\s5
\v 24 Da Musa ya gama rubuta waɗannan maganganun shari'a a cikin littafi,
\v 25 sai ya umarci Lebiyawa masu ɗaukar akwatin alƙawari na Yahweh, ya ce,
\v 26 "Ku ɗauki wannan littafin sharia ku aje shi a gefen akwatin alƙawari na Yahweh Allahnku, domin ya kasance a can ya zama maku shaida gãba da ku.
\s5
\v 27 Gama na san tayarwarku da taurin kanku; duba, da raina ma ina tare daku yau, kuna tawaye gãba da Yahweh; ballantana bayan na mutu?
\v 28 Ku tattaro mani dattawan kabilunku, da shugabanninku, domin in faɗi maganganun nan a kunnuwansu in kira sama da ƙasa suyi shaida gãba da su.
\v 29 Gama na sani bayan rasuwata zaku ƙazamtar da kanku zaku kauce ku bar tafarkin dana umarce ku; Masifa zata auka maku cikin kwanaki masu zuwa. Wannan zai faru domin zaku yi abin mugunta a idon Yahweh, har da zaku cakune shi ya yi fushi ta wurin aikin hannuwanku."
\s5
\v 30 Musa ya maimaita maganganun wannan waƙa a kunnuwan dukkan taron Isra'ila har sai da suka ƙare.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Ku saurara, ku sammai, bari in yi magana. Bari duniya ta saurari maganganun bakina.
\v 2 Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, bari maganata ta zubo kamar raɓa, kamar yayyafi a kan ɗanyar ciyawa, kamar ɗiɗɗigar ruwa akan shuke-shuke.
\s5
\v 3 Domin zan yi shelar sunan Yahweh, kuma in faɗi girman Allanmu.
\v 4 Dutse ne, aikinsa cikakke ne; gama duk hanyoyinsa na adalci ne. Shi Allah mai aminci ne, marar zunubi. Mai adalci ne nagari kuma.
\s5
\v 5 Sun aikata mugunta gãba da shi. Ba 'ya'yansa ba ne. Abin ƙasƙancinsu ne. Su kam kangararru ne karkatacciyar tsara.
\v 6 Haka zaku rama wa Yahweh, ku wawayen mutane marasa tunani? Shi ba mahaifinku bane, wanda ya hallice ku? Shi ya yi ku ya kuma kafa ku.
\s5
\v 7 Ku tuna da kwanakai da lokatan dã, ku tuna da shekaru na zamanai da yawa da suka wuce. Ku tambayi mahaifinku zai nuna maku, dattawanku zasu kuma gaya maku.
\v 8 Lokacin da Maɗaukaki yaba al'ummai gadonsu - sa'ad da ya raba 'yan adam, ya rabawa al'ummai wurin zamansu, kamar yadda ya san yawan allolinsu.
\s5
\v 9 Gama rabon Yahweh mutanensa ne; Yakubu shi ne rabon gadonsa.
\v 10 Ya same shi a cikin hamada, a cikin ƙasa marar amfani, wurin kuka a jeji; ya kare shi ya lura da shi, ya tsare shi kamar kwayar idonsa.
\s5
\v 11 Kamar yadda gaggafa take tsare sheƙarta tana shawagi bisa 'ya'yanta, haka Yahweh ya buɗe fuka- fukansa ya ɗauke su, ya tafi da su a kan kafaɗarsa.
\v 12 Yahweh kaɗai ya bishe su; babu baƙon allah tare da su.
\s5
\v 13 Ya sa shi ya hau manyan tuddai na ƙasar, ya ciyar da shi da 'ya'yan itatuwan saura; ya yi kiwonsu da zuma daga dutse, da mai daga dutsen daya tsage..
\s5
\v 14 Ya sha man shanu daga garke kuma ya sha madara daga garken tumaki, daga ƙibar 'yan tumaki, ragunan Bashan da awakai, da lallausar garin alkama - kuka sha ruwan inabi mai kumfa da aka yi da ruwan 'ya'yan itacen inabi.
\s5
\v 15 Amma Yeshurun ya yi ƙiba ya yi hauri - ka yi ƙiba, ka ma zarce da ƙiba, ka ci isasshe - sai ya yashe da Allahn da ya yi shi, yaƙi Dutsen cetonsa.
\v 16 Suka sa Yahweh ya ji kyashi ta wurin baƙin allolinsu; da abubuwan ƙyamarsu suka sa shi fushi.
\s5
\v 17 Suka yi wa al'jannu hadaya, waɗanda ba Allah ba - allolin da basu sani ba, sabobbin alloli, gumakun da ubanninku basu ji tsoro ba.
\v 18 Kuka yashe da Dutsen, daya zama maku mahaifi, kuka manta da Allahn daya haife ku.
\s5
\v 19 Yahweh ya ga haka ya kuma ƙi su, sabili da 'ya'yansa maza da 'ya'yansa mata sun tsokane shi.
\v 20 "Zan ɓoye fuskata daga gare su," ya ce, "zan ga yadda ƙarshensu zai zama; gama kangararrun tsara ne, 'ya'ya marasa aminci.
\s5
\v 21 Suka sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba suka sa ni fushi da abubuwan wofinsu. Zan sa suji kyashi da waɗanda ba mutane ba; tawurin wautar al'umma zan sasu yi fushi.
\s5
\v 22 Gama fushina ya kunna wuta yana kuma ci zuwa zurfafan Lahira; yana hallaka duniya da girbinta; yana kunna wuta a harsashin duwatsu.
\s5
\v 23 Zan tara masihu a kan su; zan harba dukkan kibiyoyina a kansu;
\v 24 Yunwa za ta ƙarasa su zasu hallaka da ƙuna mai zafi da hallakarwa mai ɗaci; zan aika a bisansu haƙoran namun jeji, da dafin abubuwan da ke rarrafe cikin ƙura.
\s5
\v 25 A waje takobi zai kawo rashi, a ɗakunan kwana razana zata yi haka. Zata hallaka matashi da budurwa, da jariri mai shan mama, da mutum mai furfura.
\v 26 Na ce zan warwatsa su da nisa, in sa tunawa da su ya shuɗe daga 'yan adam.
\s5
\v 27 Da ba domin ina tsoron tsokanar maƙiyi ba, cewa maƙiya zasu zaci kuskure, kuma zasu ce, 'Hannunmu ya sami ɗaukaka,' dana aikata dukkan waɗannan abubuwa.
\s5
\v 28 Gama Isra'ila al'umma ce marar hikima, babu fahimta a cikinsu.
\v 29 Ai ya, da suna da hikima, da sun fahimci wannan, da zasu yi la'akari da ƙaddararsu mai zuwa!
\s5
\v 30 Ta ya ya ɗaya zai kori dubu, biyu su sa dubu goma su tsere, sai ko Dutsensu ya sayar da su, Yahweh kuma ya sadakar da su?
\v 31 Gama dutsen maƙiyanmu ba kamar Dutsenmu ba, kamar dai yadda maƙiyanmu suke cewa.
\s5
\v 32 Gama kuringar inabinsu ta zo ne daga kuringar Saduma, daga kuma jejin Gomarata; inabinsu inabin dafi ne; nonan masu ɗaci ne.
\s5
\v 33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne, da mugun dafin kumurci.
\v 34 Wannan shiri ban aje shi a ɓoye ba, a kunle cikin kayayyakina masu daraja ba?
\s5
\v 35 Ni ke bada sakamako, da ramako, a lokacin da kafafunsu suka zarme; gama ranar masifa domin su tayi kusa, abubuwan da zasu zo ta kansu zasu hanzarta su faru."
\s5
\v 36 Gama Yahweh zai yi wa mutanensa adalci, kuma zai ji tausayin bayinsa. Zai ga cewa ƙarfinsu ya ƙare, kuma ba wanda ya rage, ko bawa ko baratattun mutane.
\s5
\v 37 Sa'annan zai ce, "Ina allolinsu suke, duwatsu waɗanda suka dogara a gare su? -
\v 38 allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka sha ruwan inabin baye-bayensu na sha. Bari su tashi su taimaka maku; bari su zamar maku kariya.
\s5
\v 39 Duba yanzu da Ni, har Ni, Allah nake, kuma babu wani allah banda ni; Nakan kashe, in kuma rayar; na kan sa rauni, in warkar, kuma ba wani da zai iya cetonku daga ƙarfina.
\v 40 Gama na kan tada hannuna zuwa sama in ce, "kamar yadda na dawwama har abada, zan aikata.
\s5
\v 41 Sa'ad da na wasa takobina mai walƙiya, kuma sa'ad da hannuna ya fara kawo adalci, zan yi sakayya akan maƙiyana, in kuma sãka wa duk waɗanda suka ƙi ni.
\s5
\v 42 Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, takobina zai ci tsoka tare da jinin kasassu da kamammu, tun daga kan shugabannin maƙiyan.'"
\s5
\v 43 Ku yi farinciki, ya ku al'ummai, da mutanen Allah, gama zai yi sakayyar jinin bayinsa; zai bada sakamako a kan maƙiyansa, kuma zai yi kafara domin ƙasarsa, kuma domin mutanensa.
\s5
\v 44 Musa ya zo ya maimaita dukkan maganganun waƙar nan a kunnuwan mutane, shi, da Yoshuwa ɗan Nun.
\v 45 Sai Musa ya gama maimaita dukkan waɗannan maganganun ga dukkan Isra'ila.
\s5
\v 46 Ya ce masu, "Ku sa zuciyarku akan maganganun da nayi maku kashedi yau, domin ku umarci 'ya'yanku su kiyaye su, dukkan maganganun shari'ar nan.
\v 47 Gama wannan ba wani abu ne kurum dominku ba, sabili da ranku ne, kuma tawurin wannan abu zaku tsawaita kwanakin ku a ƙasar da kuke tafiya ku haye Yodan ku mallaka."
\s5
\v 48 A ranar nan Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 49 "Ka hau cikin waɗannan duwatsen Abarim, ƙolƙolin Dutsen Nebo, wanda ke ƙasar Mowab, hannun riga da Yariko. Zaka duba ƙasar Kan'ana, wanda nake ba mutanen Isra'ila abin mallakarsu.
\s5
\v 50 Zaka mutu akan dutsen da zaka hau, za a tattara ka zuwa ga mutanenka, kamar yadda Haruna ɗan'uwanka Ba'isra'ile ya rasu akan Dutsen Hor aka tattara shi zuwa ga mutanensa.
\v 51 Wannan zai faru domin ka yi rashin aminci a gare ni a tsakiyar mutanen Isra'ila a bakin ruwayen Meriba a Kadesh, a jejin Zin; domin baka ɗaukakani ba kuma baka girmama ni cikin mutanen Isra'ila ba.
\v 52 Gama zaka hangi ƙasar a gabanka, amma ba zaka je can ba, cikin ƙasar da nake ba mutanen Isra'ila."
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya albarkaci mutanen Isra'ila da ita kafin rasuwarsa. Ya ce:
\v 2 Yahweh ya taho daga Sinai, kuma ya taso daga Seyir a bisansu. Ya haskaka daga Dutsen Faran, yazo da dubun dubbai goma na tsarkaka. A cikin hannun damarsa akwai tarwatsun walƙiya.
\s5
\v 3 Hakika, yana ƙaunar mutane; dukkan tsarkakansa suna cikin hannunka, suna kuma russunawa a ƙafafunka; suna karɓar maganganunka.
\v 4 Musa ya umarta mana ka'idodi, abin gãdo domin taro na Yakubu.
\s5
\v 5 A sa'annan akwai sarki a Yeshurun, lokacin da shugabannin mutane suka taru, dukkan kabilar Isra'ila suka taru.
\v 6 Bari Ruben ya rayu kada ya mutu, amma bari mutanensa su zama ƙalilan.
\s5
\v 7 Wannan ce albarkar Yahuda, Musa ya ce: Ku saurara, Yahweh, ga muryar Yahuda, a sake dawo da shi ga mutanensa. Kuyi yaƙi dominsa; ku zama taimako gãba da maƙiyansa.
\s5
\v 8 Game da Lebi, Musa ya ce: Da Tumim ka da Yurim ka na aminanka ne, waɗanda ka gwada su a Massa, waɗanda kayi jayayya da su a ruwayen Meriba.
\s5
\v 9 Mutumin da ya ce game da mahaifinsa da mahaifiyarsa, "Ni ban gansu ba." Bai kuma shaidi 'yan'uwansa maza ba, hallau bai yi la'akari da 'ya'yansa na cikinsa ba. Gama ya tsare maganganunka ya kuma kiyaye alƙawarinka.
\s5
\v 10 Yana koya wa Yakubu dokokinka da Isra'ila shari'arka. Zai sa turare a gabanka da dukkan baye- baye na ƙonawa akan bagadinka.
\s5
\v 11 Kasa albarka, Yahweh, bisa mallakarsa, ka karɓi aikin hannunsa. Ka rushe kwankwasan waɗanda suka tashi gãba da shi, da mutanen da suka ƙi shi, domin kada su sake tashi kuma.
\s5
\v 12 Game da Benyamin, Musa ya ce: Shi wanda Yahweh ya ke ƙauna yana zaune lafiya a gefensa; Yahweh ya kãre shi dukkan rana, yana zaune tsakiyar hannuwan Yahweh.
\s5
\v 13 Game da Yosef, Musa ya ce: Bari Yahweh ya albarkaci ƙasarsa da abubuwa masu daraja na sama, tare da raɓa, kuma tare da zurfafa da ke kwance a ƙasa.
\s5
\v 14 Bari ƙasarsa ta zama da albarkar abubuwa masu daraja na girbi dana rana, da abubuwa masu daraja na watanni,
\v 15 tare da kyawawan abubuwa daga duwatsun dã, da kuma abubuwa masu daraja daga dawwamammun tuddai.
\s5
\v 16 Bari a albarkaci ƙasarsa da abubuwa masu daraja na duniya duk da cikarta, tare kuma da fatan alheri ga wanda ya zauna cikin saura. Bari albarka ta sauka a kan Yosef, da a kan shi wanda ya zama sarki bisa 'yan'uwansa maza.
\s5
\v 17 Ɗan fari na bijimi, mai daraja ne shi, ƙahonninsa kamar ƙahonnin bijimin jeji ne. Da su zai tunkuɗe mutane, dukkansu, har ƙarshen duniya. Waɗannan su ne dubbai goma na Ifraimu; waɗannan su ne dubbai na Manasa.
\s5
\v 18 Game da Zebaluna, Musa ya ce: Kayi farinciki, Zebaluna, cikin fitarka, kai kuma, Isakar, a cikin rumfunarka.
\v 19 Zasu kira mutane zuwa duwatsu. A can zasu miƙa hadayu na adalci. Domin zasu sha wadatar tekuna, daga kuma yãshin da ke a bakin teku.
\s5
\v 20 Game da Gad, Musa ya ce: Mai albarka ne wanda ya faɗaɗa Gad. Zai zauna a can kamar zakanya, zai kuma farke hannu ko ƙoƙon kai.
\s5
\v 21 Ya samar wa kansa sashe mafi kyau, domin akwai rabon ƙasa da aka keɓe domin shugaba. Yazo da shugabannin mutane. Ya aiwata adalcin Yahweh da dokokinsa da Isra'ila.
\s5
\v 22 Game da Dan, Musa ya ce: Dan ɗan zaki ne da ya yi tsalle waje daga Bashan.
\s5
\v 23 Game da Naftali, Musa ya ce: Naftali, ya ƙoshi da tagomashi, cike ya ke da alheran Yahweh, ya mallaki ƙasar daga yamma da kudu.
\s5
\v 24 Game da Ashiru, Musa ya ce: Mai albarka ne Ashiru fiye da sauran 'ya'ya maza; bari ya zama karɓaɓɓe ga 'ya'uwansa maza, bari ya tsoma ƙafarsa cikin man zaitun.
\v 25 Bari ƙurfan birninka su zama na baƙin ƙarfe da tagulla; dukkan kwanakin ranka, haka ma tsaron lafiyarka.
\s5
\v 26 Babu ko ɗaya kamar Allah, Yeshurun - mai gaskiyan nan, mai hawa cikin sammai ya kawo maka taimako, kuma cikin darajarsa bisa gajimarai.
\s5
\v 27 Allah madawwami mafaka ne, a ƙarƙashi kuma dawwamammun hannuwa. Yakan kori maƙiya daga gaban ka, sai kuma ya ce, "Hallaka!"
\s5
\v 28 Isra'ila ta zauna lafiya. Maɓulɓular Yakubu tana tsare cikin ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi; labudda, bari sammansa su zubo raɓa a kansa.
\s5
\v 29 Albarkunka da yawa, Isra'ila! Wane ne kamarka, mutane da Yahweh ya ceta, garkuwar taimakonka, da takobin ɗaukakarka? Magabtanku zasu zo gare ku da rawar jiki, zaku tattake masujadarsu.
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Musa ya haura daga filin Mowab zuwa Dutsen Nebo, zuwa ƙwolƙwolin Fizga, wacce take hannun riga da Yariko. A nan Yahweh ya nuna masa dukkan ƙasar Giliyad har ya zuwa Dan,
\v 2 da dukkan Naftali, da ƙasar Ifraimu da ta Manasa, da dukkan ƙasar Yahuda, har ya zuwa tekun kudu,
\v 3 da Nageb, da filin Kwarin Yariko, Birnin Itatuwan Dabino, har ya zuwa Zowar.
\s5
\v 4 Yahweh ya ce masa, "Wannan ita ce ƙasar dana rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu, cewa, "Ni zan bada ita ga zuriyarku.' Na yardar maka ka ganta da idanunka, amma ba zaka je can ba."
\v 5 Sai Musa bawan Yahweh, ya rasu a nan ƙasar Mowab, kamar yadda maganar Yahweh ta alƙawarta.
\v 6 Yahweh ya bizne shi a cikin kwari cikin ƙasar Mowab mai hannun riga da Bet Feyor, amma ba wanda yasan inda kabarinsa ya ke har wa yau.
\s5
\v 7 Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu, idanunsa basu dushe ba ƙarfinsa kuma bai ragu ba.
\v 8 Mutanen Isra'ila suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana arba'in, sai kwanakin makoki domin Musa suka ƙare.
\s5
\v 9 Yoshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Mutanen Isra'ila suka saurare shi kuma suka yi abin da Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\v 10 Ba wani annabi da ya taɓa tashi a Isra'ila kamar Musa, wanda Yahweh ya san shi fuska da fuska.
\v 11 Ba a taɓa yin wani annabi kamarsa ba a cikin dukkan alamu da mu'ujizai waɗanda Yahweh ya aike shi ya yi a ƙasar Masar, wurin Fir'auna, da dukkan barorinsa, da dukkan ƙasarsa.
\v 12 Ba a taɓa yin wani annabi kamarsa ba a dukkan manyan, ayyukan ban tsoro da Musa ya yi a idanun dukkan Isra'ila.