ha_ulb/04-NUM.usfm

2488 lines
168 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id NUM
\ide UTF-8
\h Littafin Lissafi
\toc1 Littafin Lissafi
\toc2 Littafin Lissafi
\toc3 num
\mt Littafin Lissafi
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa a runfar taruwa a cikin jejin Sinai. Wannan ya fãru ne a rana ta farko a wata na biyu a shekara ta biyu bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar. Yahweh yace,
\v 2 "Ka yi ƙidayar dukkan mutanen Isra'ila daga kowanne dangi, a cikin iyalan ubanninsu. Ka ƙidaya su bisa ga sunaye. Ka ƙidaya kowanne namiji, kowanne mutum
\v 3 wanda ke shekaru ashirin ko fiye. Ka ƙidaya dukkan waɗanda ke iya faɗa a matsayin sojoji domin Isra'ila. Kai da Haruna tilas ku rubuta lissafin dukkan mazaje a rukunonin mayaƙansu.
\s5
\v 4 Mutum daga kowacce kabila, kan dangi, tilas ya yi hidima tare da ku a matsayin shugaban kabilarsa. Kowanne shugaba tilas ya shugabanci mazajen da zasu yi faɗa kabilarsa.
\v 5 Waɗannan ne sunayen shugabannin waɗanda tilas su yi faɗa tare da ku: Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;
\v 6 daga kabilar Simiyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;
\s5
\v 7 daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;
\v 8 daga kabilar Issaka, Netanel ɗan Zuwar;
\v 9 daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;
\s5
\v 10 daga kabilar Ifraim ɗan Yosef, Elishama ɗan Ammihud; daga kabilar Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;
\v 11 daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gidiyoni;
\s5
\v 12 daga kabilar Dan, Ahiyeza ɗan Ammishaddai;
\v 13 daga kabilar Asha, Fagiyel ɗan Okran;
\v 14 daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Duwel;
\v 15 kuma daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan."
\s5
\v 16 Waɗannan ne mazajen da aka zaɓa daga mutanen. Suka bida kabilun kakanninsu. Sune shugabannin kabilun a Isra'ila.
\s5
\v 17 Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane, waɗanda aka lissafa da sunayensu,
\v 18 tare da waɗannan mutanen tattaro dukkan mutanen Isra'ila a rana ta farko na wata na biyu. Daga nan kowanne mutum ɗan shekaru ashirin da sama ya tantance asalinsa. Dole ya bada suna ga dangi da iyalan zuriyar daga kakanninsa.
\v 19 Daga nan Musa ya rubuta lissafinsu a cikin jejin Sinai, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.
\s5
\v 20 Daga zuriyar Ruben, haihuwar fãrin Isra'ila, an yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 21 Suka ƙidaya mutane 46,500 daga kabilar Ruben.
\s5
\v 22 Daga zuriyar Simiyon kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu.
\v 23 Suka ƙidaya mutane 59,300 daga kabilar Simiyon.
\s5
\v 24 Daga zuriyar Gad kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 25 Suka ƙidaya mutane 45,650 daga kabilar Gad.
\s5
\v 26 Daga zuriyar Yahuda kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum kuma ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 27 Suka ƙidaya mutane 74,600 daga kabilar Yahuda.
\s5
\v 28 Daga zuriyar Issaka kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 29 Suka ƙidaya mutane 54,400 daga kabilar Issaka.
\s5
\v 30 Daga zuriyar Zebulun kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 31 Suka ƙidaya mutane 57,400 daga kabilar Zebulun.
\s5
\v 32 Daga zuriyar Ifraim kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 33 Suka ƙidaya mutane 40,500 daga kabilar Ifraim.
\s5
\v 34 Daga zuriyar Manasse kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen dangin kakanninsu da iyalansu.
\v 35 Suka ƙidaya mutane 32,200 daga kabilar Manasse.
\s5
\v 36 Daga zuriyar Benyamin kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu.
\v 37 Suka ƙidaya mutane 35,400 daga kabilar Benyamin.
\s5
\v 38 Daga zuriyar Dan kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu.
\v 39 Suka ƙidaya mutane 62,700 daga kabilar Dan.
\s5
\v 40 Daga zuriyar Asha kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu.
\v 41 Suka ƙidaya mutane 41,500 daga kabilar Asha.
\s5
\v 42 Daga zuriyar Naftali kuma aka yi ƙidayar dukkan sunayen kowanne mutum ɗan shekaru ashirin ko sama wanda ke iya zuwa yaƙi, daga rubuce-rubucen kabilun kakanninsu da iyalansu.
\v 43 Suka ƙidaya mutane 53,400 daga kabilar Naftali.
\s5
\v 44 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan waɗannan mutane, tare da mutanen sha biyu waɗanda ke shugabancin kabilun sha biyu na Isra'ila.
\v 45 Haka dukkan mazajen Isra'ila daga 'yan shekaru ashirin zuwa sama, dukkan waɗanda ke iya faɗa a yaƙi, aka ƙidaya su a kowanne iyalansu.
\v 46 Suka ƙidaya mutane 603,550.
\s5
\v 47 Amma mazajen da suka fito daga zuriyar Lebi ba a ƙidaya su ba,
\v 48 saboda Yahweh ya cewa Musa,
\v 49 "Tilas baza ka ƙidaya kabilar Lebi ba ko ka haɗa da su cikin jimillar mutanen Isra'ila.
\s5
\v 50 A maimakon haka, ka sa Lebiyawa lura da runfar alƙawarin dokoki, su kuma lura da dukkan kayayyakin adon runfar da kowanne abu dake cikinta. Tilas Lebiyawa su ɗauki runfar, kuma tilas su ɗauki kayayyakin adon runfar. Tilas su lura da runfar, su kuma yi wa kansu sansani kewaye da ita.
\s5
\v 51 Sa'ad da za a matsa da runfar zuwa wani wuri, tilas Lebiyawa su sauke ta. Sa'ad da za a kafa runfar, tilas Lebiyawa su kafa ta. Duk wani baƙo da ya zo kusa da runfar tilas a kashe shi.
\v 52 Sa'ad da mutanen Isra'ila zasu kafa runfunansu, kowanne mutum tillas ya yi haka kusa da tutar da take ta ƙungiyar mayaƙansa.
\s5
\v 53 Duk da haka, Lebiyawa tilas su kafa runfunansu kewaye da runfar alƙawarin dokoki kada fushina ya sauko bisa mutanen Isra'ila. Tilas Lebiyawa su lura da runfar alƙawarin dokoki."
\v 54 Mutanen Isra'ila suka yi dukkan waɗannan abubuwa. Suka yi kowanne abin da Yahweh ya umarta ta wurin Musa.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Yahweh ya sake magana da Musa da Haruna. Ya ce,
\v 2 "Kowanne Ba'isra'ile dole ya yi sansani wajen matsayinsa, tare da tutocin gidan ubanninsa. Za su yi sansani kewaye da rumfar taruwa ta kowanne gefe.
\s5
\v 3 Waɗanda za su yi sansani gabas da rumfar taruwa, inda rana ke fitowa, su ne sansanin Yahuda kuma suna sansani a ƙarƙashin matsayinsu. Nashon ɗan Amminadab shi ne shugaban mutanen Yahuda.
\v 4 Lissafin mutanen Yahuda 74,600 ne.
\s5
\v 5 Kabilar Issaka tilas su yi sansani a gaba da Yahuda. Netanel ɗan Zuyar tilas ya shugabanci mayaƙan Issaka.
\v 6 Lissafin bataliyar mutane 54,400 ne.
\s5
\v 7 Kabilar Zebulun tilas su yi sansani a gaba da Issaka. Eliyab ɗan Helon tilas ya shugabanci mayaƙan Zebulun.
\v 8 Lissafin bataliyarsa 57,400 ne.
\s5
\v 9 Dukkan lissafin sansanin Yahuda 186,400 ne. Sune za su fãra tafiya.
\s5
\v 10 Gefen kudu zai zama sansanin Ruben a wajen matsayinsu. Shugaban sansanin Ruben shi ne Elizur ɗan Shedewur.
\v 11 Lissafin dake bataliyarsa 46,500 ne.
\s5
\v 12 Simiyon zai yi sansani a gaba da Ruben. Shugaban mutanen Simiyon shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
\v 13 Lissafin bataliyarsa shi ne 59.300.
\s5
\v 14 Kabilar Gad su ne gaba. Shugaban mutanen Gad shi ne Eliyasaf ɗan Deuyel.
\v 15 Lissafin bataliyarsa shi ne 45,650.
\s5
\v 16 Lissafin dukkan mutanen da aka bayar ga sansanin Ruben, bisa ga bataliyarsu, shi ne 151,450.
\s5
\v 17 Na gaba, rumfar sansanin tilas ta fita daga sansanin tare da Lebiyawa a tsakiyar dukkan sansanan. Tilas su fita daga sansanin bisa ga tsarin yadda suka shiga sansanin. Kowanne mutum tilas ya tsaya a wurinsa, gefen tutarsa.
\s5
\v 18 Rabe-raben zangon sansanin Ifraim a ƙarƙashin matsayinsu. Shugaban mutanen Ifraim shi ne Elishama ɗan Ammihud.
\v 19 Lissafin bataliyarsa shi ne 40,500.
\s5
\v 20 Gaba dasu su ne Kabilar Manasse. Shugaban Manasse shi ne Gamaliyel ɗan Fedazur.
\v 21 Lissafin bataliyarsa shi ne 32,200.
\s5
\v 22 Gaba da su zai kasance kabilar Benyamin. Shugaban Benyamin shi ne Abidan ɗan Gidiyoni.
\v 23 Lissafin dake bataliyarsa 35,400 ne.
\s5
\v 24 Dukkan waɗanda aka lissafa a sansanin Ifraim 108,100 ne. Su ne na ukun fita.
\s5
\v 25 Daga arewa zai kasance bataliyoyin sansanin Dan. Shugaban mutanen Dan shi ne Ahiyeza ɗan Ammishaddai.
\v 26 Lissafin dake bataliyarsa 62,700 ne.
\s5
\v 27 Mutanen kabilar Asha suka yi sansani gaba da Dan. Shugaban Asha shi ne Fagiyel ɗan Okran.
\v 28 Lissafin bataliyarsa 41,500 ne.
\s5
\v 29 Kabilar Naftali su ne gaba. Shugaban Naftali shi ne Ahira ɗan Enan.
\v 30 Lissafin dake bataliyarsa 53,400 ne.
\s5
\v 31 Dukkan waɗanda aka lissafa a sansanin tare da Dan 157,600 ne. Sune na ƙarshen fita daga sansanin, a ƙarƙashin tutarsu."
\s5
\v 32 Waɗannan ne Isra'ilawa, an lissafa su bisa ga iyalansu. Dukkan waɗanda aka ƙidaya a sansanansu, bisa ga bataliyoyinsu, 603,550 ne.
\v 33 Amma Musa da Haruna ba su ƙidaya Lebiyawa ba a cikin mutanen Isra'ila. Wannan bisa ga yadda Yahweh ya umarci Musa ne.
\s5
\v 34 Mutanen Isra'ila suka yi kowanne abu da Yahweh ya umarci Musa. Suka yi sansani bisa ga tutocinsu. Suka fita daga sansanin bisa ga dangoginsu, bisa ga tsarin iyalan kakanninsu.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Yanzu wannan ne tarihin zuriyar Haruna da Musa sa'ad da Yahweh ya yi magana da Musa a Tsaunin Sinai.
\v 2 Sunayen 'ya'yan Haruna maza su ne Nadab haihuwar farko, da Abihu, Eliyeza, da Itama.
\s5
\v 3 Waɗannan ne sunayen 'ya'yan Haruna maza, firistoci waɗanda aka shafe aka kuma naɗa su yi hidima a matsayin firistoci.
\v 4 Amma Nadab da Abihu sun fãɗi sun mutu a gaban Yahweh sa'ad da suka miƙa masa wuta marar karɓuwa a cikin jejin Sinai. Nadab da Abihu ba su da 'ya'ya, sai Eliyeza da Itama ne kawai suka yi hidima a matsayin firistoci tare da Haruna mahaifinsu.
\s5
\v 5 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 6 "Ka kawo kabilar Lebiyawa ka gabatar da su ga Haruna firist domin su taimake shi.
\s5
\v 7 Tilas su aiwatar da ayyuka a madadin Haruna da dukkan jama'a a gaban rumfar taruwa. Tilas su yi hidima a rumfar sujada.
\v 8 Tilas su lura da dukkan kayan ado na cikin rumfar taruwa, kuma tilas su taimaki kabilun Isra'ila su aiwatar da hidimar rumfar sujada.
\s5
\v 9 Tilas ka bayar da Lebiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza. An bayar da su ɗungun su taimaka masa ya yi hidima ga mutanen Isra'ila.
\v 10 Tilas ka naɗa Haruna da 'ya'yansa maza a matsayin firistoci, amma duk wani bãre da yazo kusa tilas a kashe shi."
\s5
\v 11 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 12 "Duba, na ɗauki Lebiyawa daga tsakanin mutanen Isra'ila. Na yi haka ne a maimakon ɗaukar kowanne haihuwar fãri namiji wanda aka haifa a cikin mutanen Isra'ila. Lebiyawa nawa ne.
\v 13 Dukkan haihuwar fãri nawa ne. A ranar dana kai hari ga dukkan haihuwar fãri na ƙasar Masar, na keɓewa kaina dukkan haihuwar fãri cikin Isra'ila, mutane duk da dabbobi. Nawa ne su. Ni ne Yahweh."
\s5
\v 14 Yahweh ya yi magana da Musa a jejin Sinai. Ya ce,
\v 15 "Ka ƙidaya zuriyar Lebi a kowanne iyali, cikin dangoginsu. Ka ƙidaya kowanne namiji daga wata ɗaya zuwa sama.
\v 16 "Musa ya ƙidaya su, yana bin maganar Yahweh, kamar yadda dai aka umarce shi ya yi.
\s5
\v 17 Sunayen 'ya'yan Lebi maza su ne Gashon, Kohat, da Merari.
\v 18 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Gashon maza su ne Libni da Shimai.
\v 19 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Kohat maza su ne Amram, Izhar, Hebron, da Uzziyel.
\v 20 Dangin da suka fito daga 'ya'yan Merari maza su ne Mahli da Mushi. Waɗannan ne dangogin Lebiyawa, aka rubuta dangi zuwa dangi.
\s5
\v 21 Dangin Libniyawa da Shimaiyawa sun fito daga Gashon. Waɗannan ne dangogin Gashonawa.
\v 22 Dukkan mazaje daga wata ɗaya zuwa sama an ƙidaya su, jimilla 7,500.
\v 23 Kabiluin Gashonawa tilas su yi sansani gefen yamma da rumfar sujada.
\s5
\v 24 Eliyasaf ɗan Layel tilas ya shugabanci kabilun zuriyar Gashonawa.
\v 25 Iyalin Gashon tilas su lura da rumfar taruwa duk da rumfar sujada. Tilas su lura da rumfar, da abin rufewar ta, da labulen da ake amfani da shi a shiga rumfar taruwar.
\v 26 Tilas su lura da masagalen labulen harabar, labulen dake ƙofar harabar - harabar dake kewaye da tsattsarkan wuri da bagadi. Tilas su lura da igiyoyin rumfar taruwa kuma domin kowanne abu dake cikinta.
\s5
\v 27 Waɗannan kabilun sun zo daga Kohat: kabilar Amramiyawa, dangin Izrahiyawa, kabilar Hebroniyawa, da kabilar Uzziyeliyawa. Waɗannan kabilar Kohatawa ne.
\v 28 Mazaje 8,600 an ƙidaya su shekaru daga wata ɗaya zuwa sama su lura da abubuwan dake na Yahweh.
\v 29 Dangogin Kohat tilas su yi sansani a gefen kudu da rumfar sujada.
\s5
\v 30 Elizafan ɗan Uzziyel tilas ya shugabanci dangogin Kohatawa.
\v 31 Tilas su lura da akwatin, da teburin, da abin ajiyar fitila, da bagadai, da abubuwa masu tsarki da ake amfani da su wajen hidimarsu, labule, da dukkan aiki dake kewaye da shi.
\v 32 Eliyeza ɗan Haruna firist tilas ya shugabanci mutanen dake shugabantar Lebiyawa. Tilas ya kula da mutanen dake lura da wuri mai tsarki.
\s5
\v 33 Dangogi biyu suka zo daga Merari: Dangin Mahliyawa da dangin Mushiyawa. Waɗannan dangogi sun zo daga Merari.
\v 34 Mazaje 6,200 aka ƙidaya shekara daga wata ɗaya zuwa sama.
\v 35 Zuriyel ɗan Abihayil tilas ya shugabanci dangogin Merari. Tilas su yi sansani a gefen arewa da rumfar sujada.
\s5
\v 36 Zuriyar Merari tilas su lura da katakan rumfar sujada, da sandunan gittawa, dana dirkoki, dana kafa harsashe, dukkan kaya masu ƙarfi, da duk wani abu da yake tattare dasu, duk da
\v 37 ginshiƙai da dirkokin harabar dake kewaye da rumfar sujada, tare da kwasfofinsu, turkuna, da igiyoyin.
\s5
\v 38 Musa da Haruna da 'ya'yansu maza tilas su yi sansani a gefen gabas na rumfar sujada, a gaban rumfar taruwa, zuwa tasowar rana. Sune ke da nauyi domin cika ayyukan tsattsarkan wuri da ayyukan mutanen Isra'ila. Duk wani bãre da ya gabato tsattsarkan wuri tilas a kashe shi.
\v 39 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan mazajen dake cikin dangogin Lebi masu shekaru daga wata ɗaya zuwa sama, kamar dai yadda Yahweh ya umarta. Suka ƙidaya maza dubu ashirin da biyu.
\s5
\v 40 Yahweh ya cewa Musa, "Ka ƙidaya dukkan mazaje haihuwar fãri na mutanen Isra'ila masu shekaru daga wata ɗaya zuwa sama. Ka lissafa sunayensu.
\v 41 Tilas ka ɗauki Lebiyawa domina - Ni ne Yahweh - maimakon dukkan haihuwar fãri na mutanen Isra'ila, da dabbobin Lebiyawa maimakon haihuwar fãri na dabbobin zuriyar Isra'ila."
\s5
\v 42 Musa ya ƙidaya dukkan haihuwar fãri na mutanen Isra'ila yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.
\v 43 Ya ƙidaya sunan dukkan mazaje haihuwar fãri, shekara daga wata ɗaya zuwa sama. Ya ƙidaya maza 22,273.
\s5
\v 44 Yahweh, ya sake magana da Musa. Ya ce,
\v 45 "Ka ɗauki Lebiyawa a maimakon dukkan haihuwar fãri daga cikin mutanen Isra'ila, ka kuma ɗauki dabbobin Lebiyawa a maimakon dabbobin mutanen. Lebiyawa nawa ne - Ni ne Yahweh.
\s5
\v 46 Tilas ne ka karɓi shekel biyar domin fansar kowanne ɗaya daga cikin 273 haihuwar fãri na mutanen Isra'ila da suka zarce lissafin Lebiyawa.
\v 47 Tilas ka yi amfani da shekel na tsattsarkan wuri a matsayin adadin awo. Shekel na dai-dai da awo ashirin na gera.
\v 48 Tilas ku bayar da kuɗin fansa da kuka biya ga Haruna da 'ya'yansa maza."
\s5
\v 49 Sai Musa ya karɓi biyan fansar daga wurin waɗanda suka zarce lissafin waɗanda Lebiyawa suka fansa.
\v 50 Musa ya karɓi kuɗin daga haihuwar fari na mutanen Isra'ila ya karɓi shekel 1,365 an auna da shekel na tsattsarkan wuri. Musa ya bayar da kuɗin fansa ga Haruna da 'ya'yansa maza.
\v 51 Musa ya yi kowanne abu da aka ce masa yayi ta maganar Yahweh kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce,
\v 2 "Ka yi ƙidayar mazaje zuriyar Kohat daga cikin Lebiyawa, bisa ga dangoginsu da iyalansu.
\v 3 Ka ƙidaya dukkan mazan dake shekaru talatin zuwa hamsin. Waɗannan mutane tilas su shiga ayarin hidima a cikin rumfar taruwa.
\v 4 Zuriyar Kohat tilas su lura da abubuwa mafi tsarki da aka keɓe domina a cikin rumfar taruwa.
\s5
\v 5 Sa'ad da sansanin ya shirya matsawa gaba, Haruna da 'ya'yansa maza tilas su shiga cikin rumfar, su sauke labulen da ya raba tsakanin wuri mafi tsarki da wuri mai tsarki su kuma rufe akwatin alƙawari da shi.
\v 6 Tilas su rufe akwatin da fãtun saniyar teku. Tilas su baza shuɗiyar sutura a kai. Tilas su sãƙa dirkokin don su ɗauke shi.
\s5
\v 7 Za su baza shuɗiyar sutura bisa teburin gurasa da ke gabansa. A bisan sa tilas su sa kwanonin, da cokulan, da langunan, da kwalaben zubawa. Tilas koyaushe gurasa ta kasance a teburin.
\v 8 Tilas su rufe ta da jar sutura kuma tare da fãtar saniyar teku. Tilas su sãƙa dirkoki na ɗaukar teburin.
\s5
\v 9 Tilas su ɗauki shuɗiyar sutura su rufe mazaunin fitilar, tare da fitilun, da mamurɗan, da tururrukan, da dukkan kwalaben mai domin fitilun.
\v 10 Tilas su sanya mazaunin fitilar tare da kayayyakinsa a cikin abin rufewar da aka yi da fãtar saniyar teku, tilas su sanya shi cikin katakon ɗauka.
\v 11 Tilas su baza sutura shuɗiya bisa bagadin zinariya. Tilas su rufe shi da abin rufewar da aka yi da fãtun saniyar teku, daga nan kuma a sãƙa dirkokin ɗauka.
\s5
\v 12 Tilas su ɗauki dukkan kayayyakin aikin wuri mai tsarki a kuma rufe su da shuɗiyar sutura. Tilas su rufe shi da fãtun saniyar teku a sanya kuma kayayyakin cikin katakon ɗauka.
\v 13 Tilas su ɗebe toka daga bagadi su kuma shimfiɗa sutura shunayya bisa bagadin.
\v 14 Tilas su sanya dukkan kayayyaki da suka yi amfani da su wurin aikin bagadi bisa katakon ɗauka. Waɗannan kayayyaki su ne kaskunan wuta, cokula masu yatsu, cebura, kwanuka, da dukkan sauran kayayyaki domin bagadi. Tilas su rufe bagadin da fãtun saniyar teku Daga nan kuma su sãƙa dirkokin ɗauka.
\s5
\v 15 Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka kammala rufe wuri mai tsarki da dukkan kayayyakinsa, sa'ad da kuma sansani ya matsa gaba, Daga nan zuriyar Kohat tilas su zo su ɗauki wuri mai tsarki. Idan suka taɓa kayayyakin aikin masu tsarki, tilas su mutu. Wannan ne aikin zuriyar Kohat, su ɗauki kayayyakin ado na cikin rumfar taruwa.
\v 16 Eliyeza ɗan Haruna firist zai shugabanci lura da mai domin haskakawa, turare mai daɗi, baikon hatsi da aka saba yi, da mai na shafewa. Zai shugabanci lura da rumfar sujadar gaba ɗaya da dukkan abin dake cikin ta, wuri mai tsarki da kayayyakinsa."
\s5
\v 17 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce,
\v 18 "Kada ku bari a cire kabilar dangogin Kohatawa daga cikin Lebiyawa.
\v 19 Ku kãre su, domin su rayu kada kuma su mutu, ta wurin yin haka. Sa'ad da suka kusanci abubuwa mafi tsarki
\v 20 tilas ba za su je su duba wuri mai tsarki ba ko dana ɗan taƙi, ko kuwa tilas su mutu. Haruna da 'ya'yansa maza tilas su shiga ciki, Daga nan kuma Haruna da 'ya'yansa maza tilas su sanya kowanne daga cikin Kohatawa ga aikinsa, ga aikinsa na musamman."
\s5
\v 21 Yahweh ya sake magana da Musa, ya ce,
\v 22 "Ka yi ƙidayar zuriyar Gashon kuma, bisa ga iyalan kakanninsu bisa ga dangoginsu.
\v 23 Ka ƙidaya waɗanda suke shekaru talatin zuwa shekaru hamsin. Ka ƙidaya dukkan waɗanda za su shiga ayarin su yi bauta a rumfar taruwa.
\s5
\v 24 Wannan ne aikin kabilun Gashonawa sa'ad da suka yi bauta da abin da suka ɗauka.
\v 25 Tilas su ɗauki labulan rumfar sujada, da rumfar taruwa da abin rufe ta, abin rufe ta na fãtar saniyar teku, da labulan hanyar shiga rumfar taruwa.
\v 26 Tilas su ɗauki labulan harabar, labule domin hanyar ƙofa ta ƙofar harabar, wadda ke kusa da rumfar sujada kusa kuma da bagadi, igiyoyinsu, da dukkan kayayyakin aiki domin hidimarsu. Duk abin da ya kamata a yi da waɗanan abubuwa, tilas su yi shi.
\s5
\v 27 Haruna da 'ya'yansa maza tilas su bida dukkan hidimar zuriyar Gashonawa, a cikin dukkan abin da suka ɗauko, a cikin kuma dukkan hidimarsu.
\v 28 Tilas ka sanya su ga dukkan ayyukansu. Wannan ne hidimar dangogin zuriyar Gashonawa domin rumfar taruwa. Itama ɗan Haruna firist tilas ne ya bida su cikin hidimarsu.
\s5
\v 29 Tilas ka ƙidaya zuriya Merari bisa ga dangoginsu, ka kuma shirya su bisa ga iyalan kakanninsu,
\v 30 daga shekaru talatin zuwa sama har shekaru hamsin. Ka ƙidaya dukkan waɗanda za su shiga ayari su kuma yi bauta a rumfar taruwa.
\s5
\v 31 Wannan ne hakkinsu da aikinsu a cikin dukkan hidima domin rumfar taruwa. Tilas su lura da katakan rumfar sujada, da sandunan gittawa, dirkoki, da mahaɗai,
\v 32 tare da dirkokin filin harabar dake kewaye da rumfar sujada, mahaɗansu, turkuna, da igiyoyinsu, tare da dukkan kayayyakinsu. Ka lissafa bisa sunan kayayyakin da tilas su ɗauka.
\s5
\v 33 Wannan ne aikin kabilun zuriyar Merari, abin da za su yi domin rumfar taruwa, ƙarƙashin bishewar Itama ɗan Haruna firist."
\s5
\v 34 Musa da Haruna da shugabannin jama'a suka ƙidaya zuriyar Kohatawa bisa ga dangogin iyalan kakanninsu.
\v 35 Suka ƙidaya su daga shekaru talatin zuwa sama har shekaru hamsin. Suka ƙidaya kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a rumfar taruwa.
\v 36 Suka ƙidaya mazaje 2,750 bisa ga dangoginsu.
\s5
\v 37 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan mazaje a cikin dangogi da iyalan Kohatawa waɗanda suke bauta a rumfar taruwa. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa.
\s5
\v 38 Aka ƙidaya zuriyar Gashon a cikin dangoginsu, ta wurin iyalan kakanninsu,
\v 39 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin, kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a rumfar taruwa.
\v 40 Dukkan mazaje, da aka ƙidaya ta wurin dangogi da iyalan kakanninsu, lissafi 2,630 ne.
\s5
\v 41 Musa da Haruna suka ƙidaya dangogin zuriyar Gashon waɗanda za su yi bauta a cikin rumfar taruwa. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa.
\s5
\v 42 Aka ƙidaya zuriyar Merari a cikin dangoginsu ta wurin iyalan kakanninsu,
\v 43 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin, kowanne da zai shiga ayari ya yi bauta a cikin rumfar taruwa.
\v 44 Dukkan mazaje, da aka ƙidaya ta wurin dangoginsu da iyalan kakanninsu, lissafi 3,200 ne.
\s5
\v 45 Musa da Haruna suka ƙidaya dukkan waɗannan mazaje, zuriyar Merari. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su suyi ta wurin Musa.
\s5
\v 46 Sai Musa, Haruna, da shugabannin Isra'ila suka ƙidaya dukkan Lebiyawa ta wurin dangoginsu cikin iyalan kakanninsu
\v 47 daga shekaru talatin zuwa shekaru hamsin. Suka ƙidaya kowanne da zai yi aiki a cikin rumfar sujada.
\v 48 Suka ƙidaya mazaje 8,580.
\s5
\v 49 Ta umarnin Yahweh, Musa ya ƙidaya kowanne mutum, yana ajiyar ƙidayar kowanne bisa ga irin aikin da aka ba shi ya yi. Ya ƙidaya kowanne mutum bisa ga irin hakkin da aka ɗora masa ya ɗauka. A cikin yin haka, sun yi biyayya da abin da Yahweh ya umarce su su yi ta wurin Musa.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila su kori kowanne mutum daga sansani wanda ke da cutar fãta da ake ɗauka, da kowanne dake da ƙurjin dake fitar da ruwa, da duk wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa.
\v 3 Ko namiji ko mace, tilas ka kore su daga sansanin. Tilas ne ba za su gurɓata sansanin ba, saboda ina zaune a cikin sa."
\v 4 Mutanen Isra'ila suka yi haka. Suka kore su daga sansanin, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa. Mutanen Isra'ila suka yi biyayya da Yahweh.
\s5
\v 5 Yahweh ya sa ke magana da Musa. Ya ce,
\v 6 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Sa'ad da wani mutum ko wata mata suka aikata zunubi irin wanda mutane ke aikatawa ga junansu, kuma ya yi rashin aminci a gare ni, wannan mutum ya yi laifi.
\v 7 Daga nan tilas ya furta zunubin da ya yi. Tilas ya biya farashin laifinsa gaba ɗaya ya kuma ƙara akan farashin kashi ɗaya cikin biyar. Tilas ya bayar da wannan ga wanda ya yiwa laifin.
\s5
\v 8 Amma idan wanda aka yiwa laifin bai da ɗan'uwa na kusa da zai karɓi biyan, tilas ya biya farashin laifinsa gare ni ta wurin firist, tare da rago na yin kaffara domin sa.
\v 9 Kowanne baiko na mutanen Isra'ila, abubuwan da aka keɓe aka kuma kawo ga firist ta wurin mutanen Isra'ila, zai zama nasa.
\v 10 Baye-bayen kowanne taliki zai zama domin firist; idan wani ya bayar da wani abu ga firist, zai zama nasa."
\s5
\v 11 Bugu da ƙari, Yahweh yayi magana da Musa. Ya ce,
\v 12 "Kayi magana da mutanen Isra'ila. Ka ce da su, 'Ga misali idan matar wani ta kauce hanya ta kuma yi zunubi gãba da mijinta.
\s5
\v 13 Misali a ce wani mutum ya kwana da ita. A wannan al'amari, ta ƙazantu. Ko da mijinta bai gani ba ko kuma ya san da hakan, kuma ko da ba wanda ya kama ta cikin aikata hakan kuma ba bu wanda zai bada shaida gãba da ita,
\v 14 duk da haka. ruhun kishi zai sanarwa mijin cewa matarsa ta ƙazamtu. Ko da yake, ruhun kishi na ƙarya na iya sauko wa mutum alhali matarsa ba ta ƙazantu ba.
\s5
\v 15 A cikin irin waɗannan al'amura, tilas mutumin ya kawo matarsa ga firist. Tilas mutumin ya zo da baikon da ake buƙata a madadin ta, kashi goma na awon garin bali. Tilas ne kuma ba zai zuba mai a kai ba ko kuma ya zuba turaren ƙonawa a kai ba, saboda baikon hatsi ne na kishi, baikon hatsi domin tunawa, a matsayin abin tunawa da laifin.
\s5
\v 16 Tilas firist ya kawo ta kusa ya miƙa ta gaban Yahweh.
\v 17 Tilas firist ya ɗauki gorar ruwa mai tsarki ya kuma ɗibi ƙurar ƙasan rumfar sujada. Tilas ya zuba ƙurar cikin ruwan.
\s5
\v 18 Firist zai sa matar gaban Yahweh kuma zai kwance gashin dake kan matar. Zai sanya cikin hannuwanta baikon hatsi na tunawa, wanda shi ne baikon hatsi na zato. Firist zai riƙe a hannunsa ruwa mai ɗaci da zai iya kawo la'ana.
\v 19 Firist zai sanya matar ƙarƙashin rantsuwa ya kuma ce mata, 'Idan babu mutumin da yayi saduwar jima'i dake, idan kuma baki fita iskanci ba kika kuma aikata rashin tsarki, to zaki 'yantu daga wannan ruwa na ɗaci da zai iya kawo la'ana.
\s5
\v 20 Amma idan ke, mace ƙarƙashin mijinta, kin fita iskanci, idan kin ƙazantu, idan kuma wani mutum daban ya kwana da ke,
\v 21 daga nan, (tilas firist ya sa matar ta ɗauki rantsuwar da za ta sauko mata da la'ana, daga nan kuma tilas ya ci gaba da magana da matar) 'Yahweh zai maida ke la'ana da za a nuna wa mutanenki ya kasance haka. Wannan zai kasance idan Yahweh ya sa cinyarki ta ruɓe kuma mararki ta kumbura.
\v 22 Wannan ruwan da zai kawo la'ana zai shiga cikin cikinki ya sa mararki ta kumbura cinyoyinki kuma su ruɓe.' Matar kuma za ta maida amsa, 'I, bari haka ya kasance idan ina da laifi.'
\s5
\v 23 Firist tilas ne ya rubuta waɗannan la'anoni cikin naɗaɗɗen littafi, Daga nan kuma tilas ya wanke rubutattun la'anonin cikin ruwa mai ɗaci.
\s5
\v 24 Tilas firist ya sa matar ta sha ruwa mai ɗaci da zai kawo la'ana. Ruwan dake kawo la'ana zai shiga cikinta ya zama ɗaci.
\v 25 Firist tilas ya ɗauke baikon hatsi na kishi daga hannun matar. Dole ya riƙe baikon hatsin a gaban Yahweh ya kuma kawo shi zuwa bagadi.
\v 26 Firist tilas ya ɗibi tafin hannu na baikon hatsin a matsayin baikon madadi, ya kuma ƙonashi bisa bagadi. Daga nan tilas ya ba matar ruwa mai ɗaci ta sha.
\s5
\v 27 Sa'ad da ya ba ta ruwan ta sha, idan ta ƙazantu saboda ta aikata zunubi gãba da mijinta, to ruwan dake kawo la'ana zai shiga cikinta, ya kuma zama ɗaci. Mararta za ta kumbura kuma cinyarta ta ruɓe. Matar za ta zama la'ananna a cikin mutanenta.
\v 28 Amma idan matar ba ta ƙazantu ba kuma da tsabtarta, to tilas ta 'yantu. Za ta iya haihuwar 'ya'ya.
\s5
\v 29 Wannan ce shari'ar kishi. Shari'a ce domin matar da ta fita iskanci daga wurin mijinta ta kuma ƙazantu.
\v 30 Shari'a ce domin mutumin da ka tare da ruhun kishi sa'ad da yake kishin matarsa. Tilas ya kawo matar a gaban Yahweh, kuma firist tilas ya yi mata dukkan abin da shari'ar kishi ta tsara.
\s5
\v 31 Mutumin zai 'yantu daga laifi domin kawo matarsa da ya yi a gaban firist. Tilas ne matar ta ɗauki nauyin kowanne laifi da take da shi."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Ka ce masu, 'Idan namiji ko mace ya keɓe kansa ga Yahweh tare da alƙawari na musamman na zama Nazari,
\v 3 ba zai taɓa shan ruwan inabi da abin sha mai ƙarfi ba. Ba zai taɓa shan abin sha mai tsami da aka yi daga ruwan inabi ba ko daga abin sha mai ƙarfi. Ba zai taɓa shan abin da aka matso daga inabi ba ko ya ci sabobbin 'ya'yan inabi ko busassun 'ya'yan inabi ba.
\v 4 A cikin dukkan kwanakin keɓewarsa gare ni, ba zai ci wani abin da aka yi da inabi ba, tare da dukkan abin da aka yi daga tsabar inabin zuwa fãtunsa.
\s5
\v 5 A cikin dukkan lokacin alƙawarinsa na keɓewa, ba za a yi amfani da aska ba a bisa kansa har sai kwanakin keɓewarsa ga Yahweh sun cika. Tilas a ware shi ga Yahweh. Tilas ya bar gashinsa ya yi tsawo a bisa kansa.
\s5
\v 6 A cikin dukkan lokacin da ya keɓe kansa ga Yahweh, tilas ne ba zai zo kusa da gawa ba.
\v 7 Tilas ne ba zai mai da kansa marar tsarki ba ko da domin mahaifinsa, mahaifiyarsa, ɗan'uwansa, da 'yar uwarsa ba, idan suka mutu. Wannan kuwa saboda an keɓe shi ga Allah, kamar yadda kowa zai gani ta wurin dogon gashinsa.
\v 8 A cikin dukkan lokacin keɓewarsa mai tsarki ne shi, ajiyayye domin Yahweh.
\s5
\v 9 Idan wani da gaske farat ɗaya ya mutu a gefensa, ya kuma ɓãta keɓaɓɓen kansa, Daga nan tilas ya aske kansa a ranar tsarkakewarsa - a rana ta bakwai tilas ya aske shi.
\s5
\v 10 A rana ta takwas tilas ya kawo kurciyoyi biyu ko tantabaru 'yan shila biyu ga firist a ƙofar shiga rumfar taruwa.
\v 11 Firist kuma tilas ya miƙa tsuntsuwa ɗaya a matsayin baikon zunubi, ɗaya kuma a matsayin baikon ƙonawa. Waɗannan za su yi masa kafara saboda ya yi zunubi ta wurin kasancewa kusa da gawa. Tilas ya sake keɓe kansa kuma a wannan rana.
\s5
\v 12 Tilas ya kiyaye kansa ga Yahweh domin kwanakin keɓewarsa. Tilas ya kawo ɗan rago ɗan shekara ɗaya a matsayin baikon laifi. Kwanakin da ya yi kafin ya ƙazantar da kansa tilas ba za a lissafa su ba, domin keɓewarsa ta ƙazantu.
\s5
\v 13 Wannan ce shari'a game da Nazari domin sa'ad da lokacin keɓewarsa ya cika. Tilas a kawo shi ƙofar shiga rumfar taruwa.
\v 14 Tilas ya gabatar da baikonsa ga Yahweh. Tilas ya miƙa a matsayin baikon ƙonawa ɗan rago ɗan shekara ɗaya kuma marar aibi. Tilas ya miƙa a matsayin baikon zunubi 'yar tunkiya 'yar shekara ɗaya kuma marar aibi. Tilas ya kawo rago a matsayin baikon zumunta wanda yake marar aibi.
\v 15 Tilas ya kawo kwandon gurasa da aka yi ba tare da gami ba, dunƙule-dunƙule na gari mai laushi da aka gauraya da mai, waina marar gami da aka shafe da mai, tare da baikon hatsinsu da baye-baye na sha.
\s5
\v 16 Tilas ne firist ya gabatar da su a gaban Yahweh. Tilas ya miƙa baikon zunubinsa da baikon ƙonawa.
\v 17 Tare da kwandon gurasa marar gami, tilas ya miƙa ragon a matsayin hadaya, baikon zumunta ga Yahweh. Firist kuma tilas ya gabatar da baikon hatsi da baikon abin sha.
\s5
\v 18 Nazirin tilas ya aske kansa don a nuna cewa an keɓe shi ga Allah a ƙofar shiga rumfar taruwa. Tilas ya ɗauki gashin dake daga kansa ya kuma sanya a cikin wutar dake ƙarƙashin hadayar baye-bayen zumunta.
\s5
\v 19 Tilas firist ya ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, curin gurasa ɗaya marar gami daga cikin kwandon, da waina ɗaya marar gami. Tilas ya ɗora su cikin hannuwan Banazaren bayan ya aske kansa nuna keɓewa.
\v 20 Tilas firist ya wurga su a matsayin baiko a gaban Yahweh, kaso mai tsarki domin firist, tare da ƙirgin da aka wurga da kuma cinyar da aka gabatar domin firist. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.
\s5
\v 21 Wannan ce shari'a domin Nazari wanda ya yi alƙawarin baikonsa ga Yahweh domin keɓewarsa. Kowanne abu kuma da zai iya bayarwa, tilas ya kiyaye ka'idodin alƙawarin da ya ɗauka, ya kiyaye alƙawarin da aka nuna ta wurin shari'a domin Banazare."'
\s5
\v 22 Yahweh ya sake magana da Musa. Ya ce,
\v 23 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza. Cewa, 'Tilas ku albarkaci mutanen Isra'ila ta wannan hanya. Tilas ku ce masu,
\v 24 "Bari Yahweh ya albarkace ku ya kuma kiyaye ku.
\s5
\v 25 Bari Yahweh ya sa fuskarsa ta haskaka a bisanku ya kuma yi maku alheri.
\v 26 Bari Yahweh ya kalle ku da tagomashi ya kuma ba ku salama."'
\v 27 Ta wannan hanya ce tilas za su bayar da sunana ga mutanen Isra'ila. Daga nan zan albarkace su.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 A ranar da Musa ya kammala rumfar sujadar, sai ya shafe ta ya kuma keɓe ta ga Yahweh, tare da dukkan kayan adonta. Ya yi haka kuma domin bagadin da dukkan kayayyakinsa. Ya shafesu ya kuma keɓe su ga Yahweh.
\v 2 A wannan rana, shugabannin Isra'ila, shugabannin iyalan kakanninsu, suka miƙa hadayu. Waɗannan mutane ne ke shugabancin kabilun. Sun shugabanci lissafin mazajen a ƙidaya.
\v 3 Suka kawo baye-bayensu gaban Yahweh. Suka kawo kekunan noma rufaffu guda shida da shanu sha biyu. Suka kawo kowanne keken noma ɗaya domin shugabanni biyu, kuma kowanne shugaba ya kawo sã ɗaya. Suka gabatar da waɗannan abubuwa a gaban rumfar sujada.
\s5
\v 4 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 5 "Ka karɓi baye-bayen daga garesu ka kuma yi amfani da baye-bayen domin aikin rumfar taruwa. Ka bayar da baye-bayen ga Lebiyawa, ga kowannen su bisa ga yadda aikinsa ke buƙatarsu."
\s5
\v 6 Musa ya ɗauki kekunan noman da shanun, ya kuma bayar da su ga Lebiyawa.
\v 7 Ya bayar da kekunan noma biyu da shanu huɗu ga zuriyar Gashon, saboda abin da aikinsu ke buƙata.
\v 8 Ya bayar da kekunan noma huɗu da shanu takwas ga zuriyar Merari, cikin kulawar Itama ɗan Haruna firist. Ya yi wannan ne saboda abin da aikinsu ya ke buƙata.
\s5
\v 9 Amma bai ba da ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ba ga zuriyar Kohat, saboda nasu zai kasance aikin dake da dangantaka da abubuwan dake na Yahweh wanda za su ɗauka bisa kafaɗunsu.
\s5
\v 10 Shugabannin suka miƙa kayayyakinsu domin keɓewar bagadi a ranar da Musa ya shafe bagadi. Shugabannin suka miƙa hadayunsu a gaban bagadin.
\v 11 Yahweh ya cewa Musa, "Kowanne shugaba a ranarsa zai miƙa hadayarsa domin keɓewar bagadi."
\s5
\v 12 A rana ta farko, Nashon ɗan Amminadab, na kabilar Yahuda, ya miƙa tasa hadayar.
\v 13 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awo na rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 14 Ya bayar da kwanon zinariya guda ɗaya mai nauyin awo goma cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 15 Ya bayar da bijimi ɗaya domin baiko na ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 16 Ya bayar da bunsuru ɗaya domin baikon zunubi.
\v 17 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.
\s5
\v 18 A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuyar, shugaban Issaka, ya miƙa hadayarsa.
\v 19 Ya miƙa a matsayin hadaya tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa ɗaya mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\s5
\v 20 Ya kuma bayar da kwanon zinariya guda ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\v 21 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 22 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 23 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuyar.
\s5
\v 24 A rana ta ukku, Eliyab ɗan Helon, shugaban zuriyar Zebulun, ya miƙa hadayarsa.
\v 25 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130, da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 26 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 27 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 28 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon sujada.
\v 29 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.
\s5
\v 30 A rana ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban zuriyar Ruben, ya miƙa hadayarsa.
\v 31 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 32 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 33 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya.
\v 34 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 35 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.
\s5
\v 36 A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban zuriyar Simiyon, ya miƙa hadayarsa.
\v 37 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 38 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 39 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya.
\v 40 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 41 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar, a matsayi hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
\s5
\v 42 A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deuyel, shugaban zuriyar Gad, ya miƙa hadayarsa.
\v 43 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi.
\v 44 Ya kuma bayar da kwanon azurfa ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 45 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya.
\v 46 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 47 Ya bayar da shanu biyu, roga biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deuyel.
\s5
\v 48 A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban zuriyar Ifraim, ya miƙa hadayarsa.
\v 49 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi.
\v 50 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 51 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 52 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 53 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.
\s5
\v 54 A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban zuriyar Manasse, ya miƙa hadayarsa.
\v 55 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 56 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 57 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 58 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 59 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, da 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.
\s5
\v 60 A rana ta tara, Abidan ɗan Gidiyoni, shugaban zuriyar Benyamin, ya miƙa hadayarsa.
\v 61 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 62 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 63 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 64 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 65 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gidiyoni.
\s5
\v 66 A rana ta goma, Ahiyeza ɗan Ammishaddai, shugaban zuriyar Dan, ya miƙa hadayarsa.
\v 67 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi.
\v 68 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 69 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, ɗan rago shekara ɗaya.
\v 70 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 71 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Ahiyeza ɗan Ammishaddai.
\s5
\v 72 A rana ta sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban zuriyar Asha, ya miƙa hadayarsa.
\v 73 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai a matsayin baikon hatsi.
\v 74 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 75 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 76 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 77 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.
\s5
\v 78 A rana ta sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban zuriyar Naftali, ya miƙa hadayarsa.
\v 79 Hadayarsa ita ce tire ɗaya na azurfa mai nauyin awo 130 da bangajin azurfa mai nauyin awo saba'in, bisa ga matakin awon rumfar sujada. Dukkan waɗannan kaya na cike da gari mai laushi gauraye da mai domin baikon hatsi.
\v 80 Ya kuma bayar da kwanon zinariya ɗaya mai nauyin awo goma, cike da turaren ƙonawa.
\s5
\v 81 Ya bayar da bijimi ɗaya a matsayin baikon ƙonawa, rago ɗaya, da ɗan rago shekara ɗaya.
\v 82 Ya bayar da bunsuru ɗaya a matsayin baikon zunubi.
\v 83 Ya bayar da shanu biyu, rago biyar, bunsuru biyar, 'yan raguna biyar dake shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.
\s5
\v 84 Shugabannin Isra'ila suka keɓe dukkan waɗannan a ranar da Musa ya shafe bagadi. Suka keɓe tirirrikan azurfa sha biyu, bangajin azurfa sha biyu, da kwanukan zinariya sha biyu.
\v 85 Kowanne tire nauyin awo 130 kowanne bangaji kuma nauyin awo saba'in. Dukkan kayan azurfar nauyin su awo 2,400 ne, bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada.
\v 86 Kowanne kwanukan zinariya sha biyu, cike da turaren ƙonawa, nauyin awo goma bisa ga matakin nauyin awon rumfar sujada. Dukkan kwanukan zinariyar nauyin awo 120 ne.
\s5
\v 87 Suka keɓe dukkan dabbobi domin baye-baye na ƙonawa, bijimai sha biyu, rago sha biyu, 'yan raguna sha biyu 'yan shekara ɗaya. Suka bayar da baikon hatsinsu. Suka bayar da bunsuru sha biyu a matsayin baikon zunubi.
\v 88 Daga dukkan garken dabbobinsu, suka bayar da bijimai ashirin da huɗu, rago sittin, bunsuru sittin, da 'yan raguna sittin 'yan shekara ɗaya, a matsayin hadaya domin baikon zumunta. Wannan domin keɓewar bagadi ne bayan an shafe shi.
\s5
\v 89 Sa'ad da Musa ya shiga cikin rumfar taruwa domin ya yi magana tare da Yahweh, ya ji muryarsa ya na magana da shi. Yahweh ya yi magana da shi daga bisan marfin kafara dake a kan akwatin alƙawari., daga tsakanin kerubim biyu. Ya yi masa magana.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Ka yi magana da Haruna. Ka ce da shi, 'Fitilun nan guda bakwai su bada haske a gaban wurin ɗora fitilar idan ka kunna su."'
\s5
\v 3 Haruna kuwa ya yi haka. Ya kunna fitilun yadda za su ba da haske wajan gaban inda a ke ɗora fitilun, kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa.
\v 4 Haka a ka yi wurin ɗora fitilun yadda Yahweh ya nuna wa Musa. Ya zama bugaggiyar zinariya tun daga ƙasa har sama, da bugaggun koffuna kamar furanni.
\s5
\v 5 Yahweh, ya sake yin magana da Musa. Ya ce,
\v 6 "Ka ɗebi Lebiyawa daga cikin mutanen Isra'ila ka tsarkake su.
\s5
\v 7 Ga yadda za ka tsarkake su: Ka yayyafa ruwan kafara a kansu. Ka sa su aske jikinsu dukka, su wanke tufafinsu ta haka za su tsarkake kansu.
\v 8 Ka sa su sami ɗan bijimi da baikonsa na gari wanda a ka gauraya da mai. Su kuma sami wani ɗan bijimin domin baiko na zunubi.
\s5
\v 9 Ka kawo Lebiyawan gaban rumfa ta taruwa ka kuma tattara dukkan mutanen Isra'ila.
\v 10 Sa'ad da ka kawo Lebiyawan gaban Yahweh, sai dukkan mutanen Isra'ila su ɗora hannuwansu a kan Lebiyawan.
\v 11 Sai Haruna ya miƙa Lebiyawan a gaban Yahweh, kamar bayarwa ta ɗagawa daga mutanen Isra'ila domin su yi wa Yahweh hidima.
\s5
\v 12 Sai Lebiyawan su ɗora hannuwansu a bisa kawunan bajiman. Sai ka miƙa bijimi ɗaya baiko na zunubi, ɗaya bijimin kuma baiko na ƙonawa gare ni, sai a yi wa Lebiyawan kafara.
\v 13 Sai ka gabatar da Lebiyawan ga Haruna da 'ya'yansa, ka ɗaga su kamar baiko na ɗagawa a gare ni.
\s5
\v 14 Ta haka za ka keɓe Lebiyawan daga cikin mutanen Isra'ila. Lebiyawan za su zama nawa.
\v 15 Bayan wannan sai Lebiyawan su shiga su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa. Dole ne ka tsarkake su. Dole kuma ka miƙa su kamar baikon na ɗagawa.
\s5
\v 16 Ka yi haka, saboda sun zama nawa ɗungum daga cikin mutanen Isra'ila. Su za su zama kamar kowanne ɗă namiji da aka fara haifuwa, ɗa na fari daga kowacce zuriya ta Isra'ila. Na ɗauki Lebiyawa domin kaina.
\v 17 Kowanne ɗă na fari na mutanen Isra'ila nawa ne, na mutum dana dabba. A ranar dana ɗauke dukkan rayukan 'ya'yan fari cikin ƙasar Masar, na keɓe su gare ni.
\s5
\v 18 Na ɗauki Lebiyawa daga cikin mutanen Isra'ila a madadin dukkan 'ya'yan fari.
\v 19 Na bayar da Lebiyawa kyauta ga Haruna da 'ya'yansa. Na ɗauke su daga cikin mutanen Isra'ila domin su yi aikin mutanen Isra'ila a cikin rumfa ta taruwa. Na bayar da su domin su yi kafara saboda mutanen Isra'ila domin kada annoba ta same su sa'ad da suka zo kusa da wuri mai tsarki."
\s5
\v 20 Musa da Haruna da dukkan taron mutanen Isra'ila suka yi haka da Lebiyawa. Suka yi dukkan abin da Yahweh ya ummurci Musa game da Lebiyawa. Mutanen Isra'ila suka yi haka da su.
\v 21 Lebiyawan su ka tsarkake kansu suka wanke tufafinsu, Haruna ya gabatar da su kamar baiko na ɗagawa ga Yahweh kuma ya yi kafara domin su ya tsaftace su
\s5
\v 22 Bayan haka, sai Lebiyawan suka shiga domin su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa a gaban Haruna da 'ya'yansa. Wannan ya zama kamar yadda Yahweh ya ummarci Musa game da Lebiyawa. Haka suka yi da dukkan Lebiyawa.
\s5
\v 23 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce,
\v 24 "Dukkan wannan saboda Lebiyawan da suka kai shekara ashirin da biyar ne zuwa gaba. Za su haɗu da sauran su yi hidima a cikin rumfa ta taruwa.
\s5
\v 25 Za su dena yin hidima sa'ad da suka kai shekara hamsin. A waɗannan shekarun ba za su ƙara yin hidima ba.
\v 26 Za su iya taimakon 'yan'uwansu waɗanda suke ci gaba da yin hidima a rumfa ta taruwa, amma su ba za su ƙara yin hidima ba. Sai ka jagoranci Lebiyawa cikin dukkan waɗannan al'amura.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa a cikin jejin Sinai, a cikin wata na biyu bayan sun fito daga ƙasar Masar. Ya ce,
\v 2 "Sai mutanen Isra'ila su kiyaye idin Ƙetarewa a lokacin da aka ayyana cikin shekara.
\v 3 A kan rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da yamma, dole ne ku kiyaye idin Ƙetarewa a lokacin da aka ayyana shi a shekara. Ku kiyaye shi ku bi dukkan ka'idodi, ku yi biyayya da dukkan farillan da aka ayyana domin sa."
\s5
\v 4 Haka, Musa ya gaya wa mutanen Isra'ila ya wajaba su riƙa kiyaye Idin Ƙetarewa.
\v 5 Haka suka kiyaye Idin Ƙetarewa a cikin wata na fari a kan rana ta goma sha huɗu ga watan, da yamma, a cikin jejin Sinai. Mutanen Isra'ila suka kiyaye dukkan abin da Yahweh ya ummarci Musa ya yi.
\s5
\v 6 Akwai waɗansu mutanen da suka zama ƙazamtattu ta wurin taɓa gawa. Ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a wannan ranar ba.
\v 7 Waɗannan mutane suka ce da Musa, "Mun ƙazamtu ta wurin taɓa gawar wani mutum. Meyasa hana aka mu miƙa hadaya ga Yahweh tare da sauran mutanen Isra'ila a lokacin da a ka ayyana na shekara?"
\v 8 Musa yace da su, "Ku jira in ji umarnin da Yahweh zai bani saboda ku."
\s5
\v 9 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 10 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila. Cewa, 'Idan wani a cikin ku, ko zuriyarku ya ƙazamtu ta wurin taɓa gawa, yana cikin tafiya mai nisa, zai iya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Yahweh.'
\s5
\v 11 A cikin wata na biyu a kan rana ta goma sha huɗu da yamma, za su iya cin abincin Idin Ƙetarewa. Za su ci ragon Idin Ƙetarewa da gurasa marar gami da ganyaye masu ɗăci.
\v 12 Kada su rage shi har zuwa safiya, ko su karya ƙasusuwan. Dole ne su kiyaye dukkan ka'idodin da aka ayyan na Idin Ƙetarewar.
\s5
\v 13 Amma dukkan mutum mai tsarki kuma ba tafiya ya ke yi ba, amma bai yi Idin Ƙetarewar ba, wannan mutum za a datse shi daga cikin mutanensa saboda bai miƙa hadaya ga Yahweh yadda ake bukata a lokacin da aka ayyana a shekara ba. Wannan mutum zai ɗauki zunubinsa.
\v 14 Idan akwai baƙo a cikin ku yana kiyaye Idin Ƙetarewa domin ya ba Yahweh girma, sai ya kiyaye dukkan abin da aka umarta, da ka'idodinsa, da dukkan dokokinsa. Dokoki ɗaya ne za su shafi wanda aka haifa a ƙasar da kuma baƙo."
\s5
\v 15 A ranar da aka kafa alfarwar, sai girgije ya sauka ya rufe ta, wato rumfar ta alƙawari. Da yamma girgijen yana bisan alfarwar. Ya zama kamar wuta har zuwa safiya.
\v 16 Haka ya ci gaba. Da dare girgijen ya rufe alfarwar kamar wuta.
\v 17 Duk lokacin da aka ɗauke girgijen daga bisa rumfar, sai mutanen Isra'ila su ci gaba da tafiyarsu. Dukkan sa'adda girgijen ya tsaya wuri ɗaya, sai mutanen su yi zango.
\s5
\v 18 Idan Yahweh ya bada ummurni, sai mutanen Isra'ila su tafi, idan ya bada ummurni sai su yi zango. Sa'ad da girgijen ya tsaya a bisan alfarwar, sai su tsaya a zangonsu.
\v 19 Idan girgijen ya tsaya a bisan alfarwar kwanaki da yawa, sai mutanen Isra'ila su yi biyayya da ka'idodin Yahweh ba za su tafi ba.
\s5
\v 20 Wani lokaci girgijen yakan tsaya a bisa alfarwar har 'yan kwanaki. A wannan lokaci, sai su yi biyayya da umarnin Yahweh--sai su yi zango sai in ya bada umarni sai su tafi.
\v 21 Wani lokacin sai girgijen ya kasance a bisa zangon tun daga yamma har safiya. Idan girgijen ya tashi da safe sai su tafi. Idan kuma ya ci gaba da tsayawa dare da rana, sai sa'ad da girgijen ya tashi za su tafi.
\s5
\v 22 Duk sa'ad da girgijen ya tsaya a bisa alfarwar kwana biyu ko wata ɗaya ko shekara, idan dai girgijen yana tsaye a nan, mutanen za su tsaya a zangonsu ba za su tafi ba. Amma duk lokacin da aka ɗauke girgijen sai su kama tafiyarsu.
\v 23 Za su yi zango sa'adda Yahweh ya bada umarni, kuma su tafi bisa ga umarninsa. Sun yi biyayya da umarnin da Yahweh ya ba Musa.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Ka yi kakaki biyu na azurfa. Ka yi su da bugaggiyar azurfa. Ka yi amfani da ƙahonin domin ka kira ƙungiyoyin jama'a su zo su taru kuma domin ka kira ƙungiyoyin jama'a su zakuɗa da zangunansu.
\s5
\v 3 Fristoci su busa kakakin domin su kira dukkan ƙungiyoyin jama'a su taru a gaban rumfa ta taruwa.
\v 4 Idan firistoci suka busa kakaki ɗaya, sai shugabanni da shugabannin iyalai na Isra; ila, su zo su taru.
\v 5 Idan ka busa alama mai ƙara, sai zangon gabas su fara tafiyarsu.
\s5
\v 6 Idan ka busa alama mai ƙara ta biyu, sai zanguna na zangon kudu su fara tafiyarsu. Suma sai su busa alama mai ƙara domin su tafi.
\v 7 Sa'anda jama'a suka taru wuri ɗaya sai ka busa ƙahonin, amma ba da ƙarfi ba.
\v 8 'Ya'yan Haruna da firistoci ne za su busa kakakin. Wannan za ta zama ka'ida a gare ka dukkan zamanun mutanenka.
\s5
\v 9 Idan kuka tafi yaƙi cikin ƙasarku da maƙiyi wanda yake găba da ku, sai ku busa alama da kakakin. Ni, Yahweh Allahnku, zan tuna daku in cece ku daga maƙiyanku.
\s5
\v 10 Kuma, lokacin bukukuwa, da bukukuwanku na yau da kullum ko na farkon wata, sai ku busa kakaki saboda baye--bayenku na ƙonawa da hadayinku da baye--bayenku na zumunci. Waɗannan abubuwa za su sa in tuna da ku, Ni Allahnku. Ni ne Yahweh Allahnku."
\s5
\v 11 A cikin shekara ta biyu, a cikin wata na biyu, a rana ta ashirin ga watan, sai aka ɗauke girgijen daga bisa rumfar taruwa ta umarnin alƙawari.
\v 12 Sai mutanen Isra'ila suka ci gaba da tafiyarsu daga jejin Sinai. Sai girgijen ya tsaya a jejin Faran.
\v 13 Suka yi tafiyarsu ta fari, suna bin umarnin da Yahweh ya ba Musa.
\s5
\v 14 Sai zangon dake ƙarƙashin tutar zuriyar Yahuda suka fara tafiya, suka fara gusawa da sojojinsu. Nashon ɗan Amminadab ya jagoranci sojojin Yahuda.
\v 15 Netanel ɗan Zuyar ya jagoranci sojojin zuriyar Issaka.
\v 16 Eliyab ɗan Helon ya jagoranci sojojin zuriyar Zebulun.
\s5
\v 17 Zuriyar Geshon da Merari, waɗanda ke lura da alfarwa, suka ɗauki alfarwar suka tafi.
\v 18 Na biye su ne sojojin dake ƙarƙashin tutar zangon Ruben suka shirya suka tafi. Elizur ɗan Shedur ya jagoranci sojojin Ruben.
\v 19 Shenumiyel ɗan Zurishaddai ya jagoranci sojojin zuriyar Simeyon.
\v 20 Eliyasaf ɗan Dewuyel ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Gad.
\s5
\v 21 Sai Kohatiyawa suka shirya fita. Suka ɗauki kayayyaki masu tsarki na wurin sujada. Waɗansu za su shirya alfarwa kafin Kohatiyawa su zo zango na gaba.
\v 22 Sojoji na ƙarƙashin tutar zuriyar Ifraim su ne na gaba. Elishama ɗan Amihud ya jagoranci sojojin Ifraim.
\v 23 Gamaliyel ɗan Fedazur ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Manasse.
\v 24 Abidan ɗan Gidiyoni ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Banyami.
\s5
\v 25 Sojojin da suka yi zango a ƙarƙashin tutar zuriyar Dan su ne suka tashi daga ƙarshe. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ya jagoranci sojojin Dan.
\v 26 Fagiyel ɗan Okran ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Asha.
\v 27 Ahira ɗan Inan ya jagoranci sojojin kabilar zuriyar Naftali.
\v 28 Wannan shi ne yadda sojojin mutanen Isra'ila suka shirya suka fita tafiyarsu.
\s5
\v 29 Musa ya yi magana da Hobab ɗan Rewuyel mutumin Midiya. Rewuyel ne mahaifin matar Musa. Musa ya yi magana da Hobab ya ce, "Za mu tafi wurin da Yahweh ya bayyana. Yahweh yace, 'Zan baku shi.' Ka biyo mu zamu kyautata maka. Yahweh ya yi alƙawari zai kyautatawa Isra'ila."
\v 30 Amma Hobab yace da Musa, "Ba zan bi ku ba. Zan tafi ƙasata wurin mutanena."
\s5
\v 31 Sai Musa ya amsa, "Idan ka yarda kada ka rabu da mu. Ka san yadda a ke yin zango a cikin jeji. Sai ka kula da mu.
\v 32 Idan ka biyo mu, zamu kyautata ma ka kamar yadda Yahweh zai kyautata mana."
\s5
\v 33 Suka yi tafiya ta kwana uku daga tsaunin Yahweh. Akwatin alƙawari na Yahweh ya tafi a gabansu kwana uku domin ya samar masu wurin da za su huta.
\v 34 Girgijen Yahweh yana bisansu da rana inda suke tafiya.
\s5
\v 35 Dukkan lokacin da akwatin alƙawari ya tashi, Sai Musa yace, "Yahweh, tashi ka watsar da maƙiyanka. Ka sa masu ƙin ka su gudu daga wurinka."
\v 36 Duk sa'ad da akwatin alƙawari ya tsaya, sai Musa yace,"Yahweh ka dawo wurin Isra'ila masu yawa dubbai."
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Sai mutanen suka yi kuka game da matsalolinsu Yahweh kuwa yana ji. Yahweh ya ji ya yi fushi. Sai wuta ta fito daga wurin Yahweh ta kama a cikinsu har ta ƙone gefunan wasu bayan wani zangon.
\v 2 Sai mutanen suka yi kira ga Musa, sai Musa ya yi addu'a ga Yahweh, sai wutar ta mutu.
\v 3 Aka kira wannan wurin da suna Tabera, saboda wutar Yahweh ta yi ƙuna a wurin.
\s5
\v 4 Sai waɗansu baƙi suka fara sauka a zangon zuriyar Isra'ila. Suka so su ci abinci mai kyau. Daga nan mutanen Isra'ila suka fara kuka suka ce, "Wane ne zai ba mu nama mu ci?
\v 5 Mun tuna da kifin da muka ci a Masar kyauta, da kukumba da kabewa da albasa da kankana da tafarnuwa.
\v 6 Yanzu har ma bamu da marmari, saboda wannan mannar kaɗai muke iya gani."
\s5
\v 7 Manna dai tana kama da ƙwayar riɗi. Launinta kuma kamar ƙaro.
\v 8 Mutanen suka zagaya suka ɗebo ta. Suka niƙa ta a dutse, suka daka ta a turmi, su ka dafa ta a tukwane, suka yi waina da ita. Sai ɗanɗanonta ya zama kamar na sabon man zaitun.
\s5
\v 9 Sa'ad da raɓa ta sauko a kan zangon da dare, manna kuma ta faɗo.
\v 10 Musa ya ji mutanen suna ta kuka cikin iyalansu, kowanne mutum ya fito ƙofar rumfarsa. Sai Yahweh ya yi fushi ƙwarai, Musa kuwa yana ganin koken-koken nasu bai yi dai-dai ba.
\s5
\v 11 Musa yace da Yahweh, "Me yasa ka yiwa mutanenka mummunan abu haka? Me yasa baka yarda da ni ba? Ka sa na ɗauki nawaiyar mutanen nan dukka.
\v 12 Ni na ɗauki cikin dukkan mutanen nan? Ni na haife su da zaka ce dani, 'Ka ɗauke su a ƙirjinka kamar yadda uba yake ɗaukar jariri?' Ni zan ɗauke su in kai su ƙasar da ka rantse wa kakaninsu cewa za ka ba su?
\s5
\v 13 A ina zan sami naman da zan ba dukkan mutanen nan? Suna ta kuka a gabana suna cewa, 'Ka bamu nama mu ci.'
\v 14 Ba zan iya da mutanen nan ba ni kaɗai. Sun yi mani yawa.
\v 15 Tun da haka kake yi da ni, gara ka kashe ni yanzu--Idan na sami tagomashi a idanunka -- kada ka bari in ga takaicina."
\s5
\v 16 Sai Yahweh yace da Musa, "Ka kawo dattawan Isra'ila guda saba'in a wurina. Ka tabbatar su dattawa ne kuma shugabannin jama'a. Ka kawo su rumfa ta taruwa su tsaya nan tare da kai.
\v 17 Zan sauko in yi magana da su a can. Zan ɗauka daga Ruhun da yake a kanka in sashi a kansu. Za su ɗauki nawayar mutanen tare da kai. Ba za kayi ta fama da su kai kaɗai ba.
\s5
\v 18 Ka ce da mutanen, 'Ku tsarkake kanku, gama gobe za ku ci nama sosai, gama kun yi kuka kuma Yahweh ya ji. Kun ce, "Wane ne zai ba mu nama mu ci? Gama dã abincinmu ne a Masar." Yahweh zai ba ku nama, kuma za ku ci shi.
\v 19 Ba wai zaku ci nama yini ɗaya ko biyu ko biyar ko goma ko ma ashirin ba,
\v 20 amma zaku yi wata guda kuna cin nama har sai ya fito maku a ƙofar hancinku. Sai ya ginshe ku, gama kun ƙi Yahweh, wanda ke cikin ku. Kun yi kuka a gabansa. Kun ce, "Meyasa muka baro Masar""'
\s5
\v 21 Sa'an nan Musa yace, "Mutane 600,000 ne ke tare dani, kuma ka ce, 'Zan ba su nama su yi ta ci har wata guda ɗungum.'
\v 22 Garkunan shanu dana tumaki za a yanka har ya ƙosar da su?"
\v 23 Sai Yahweh yace da Musa, "Hannuna ya kasa ne? Yanzu zaka gani ko maganata gaskiya ce ko a'a."
\s5
\v 24 Musa ya fita ya faɗawa mutanen maganar Yahweh. Ya tattara dattawan su saba'in ya sa suka kewaye rumfar.
\v 25 Yahweh ya zo cikin girgije ya yi magana da Musa. Yahweh ya ɗauka daga cikin Ruhun da yake kan Musa ya sa a kan dattawan su saba'in. Sa'ad da Ruhun ya sauko a kansu, sai suka yi anabci, amma a wannan lokacin ne kaɗai ba su ƙara yi ba kuma.
\s5
\v 26 Sai mutane biyu suka rage a zangon, su ne Eldad da Medad. Su ma Ruhun ya sauko a kansu. An rubuta sunayensu, amma basu fita sun je rumfa ta taruwa ba. Duk da haka, sun yi anabci a cikin zangon.
\v 27 Wani saurayi ya ruga daga cikin zangon ya gaya wa Musa cewa, Ga Eldad da Medad suna yin anabci a cikin zango."
\s5
\v 28 Sai ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun mutanensa Yoshuwa mataimakin Musa, ya ce da Musa, "Shugabana Musa, ka hana su."
\v 29 Musa yace da shi, "Kana jin kishi saboda ni ne? So na ne dukkan mutanen Yahweh su zama annabawa ya kuma sawa dukkan su Ruhunsa!"
\v 30 Daga nan sai Musa da dattawan Isra'ila suka koma cikin zango.
\s5
\v 31 Daga nan sai iska ta taso daga wurin Yahweh ta kawo makware daga teku. Suka faɗo kusa da zangon, misalin kusan tafiyar yini ɗaya a wannan sashi, haka kuma a ɗaya sashin. Makwaren suka kewaye zangon wajen kamu ɗaya daga bisa suka kere ƙasa.
\v 32 Mutanen suka yi ta tara makware a wannan yini dukka da wannan daren dukka da kuma washe gari dukka. Kowanne mutum ya kama makware da yawan gaske. Suka raba makwaren cikin zangon dukka.
\s5
\v 33 Sa'anda naman ke tsakankanin haƙoransu, suna tauna shi, Sai Yahweh ya yi fushi da su. Ya sa wani ciwo mai zafi ya auko masu.
\v 34 Aka kira sunan wannan wurin Kibrot Hattãba, saboda sun rufe mutanen da suka yi zarin cin nama.
\v 35 Daga Kibrot Hattãba mutanen suka yi tafiya zuwa Hazerot, suka tsaya a can.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sai ya zama Miriyam da Haruna suka yi gunaguni a kan Musa saboda wata mace Bakushiya da ya aura.
\v 2 Suka ce, "Kai kaɗai ne Yahweh ya yi magana da kai? Mu ma bai yi magana da mu ba ne?" Sai Yahweh ya ji abin da suka ce.
\v 3 Musa kuwa mutum ne mai tawali'u, fiye da kowa a duniya.
\s5
\v 4 Nan take Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna da Miriyam: "Ku uku ɗin, ku fito, ku zo rumfa ta taruwa." Sai su uku ɗin suka fito suka je.
\v 5 Sa'an nan Yahweh ya sauko ta cikin umudin girgije. Ya tsaya a ƙofar rumfa ta taruwa ya kira Haruna da Miriyam. Sai suka matso.
\s5
\v 6 Sai Yahweh yace, "Sa'ad da annabina ke tare da ku, zan bayyana kaina a wurinsa ta wurin ruya in yi magana da shi cikin mafarkai.
\v 7 Bawana Musa ba haka yake ba. Shi mai aminci ne a cikin dukkan gidana.
\v 8 Na kan yi magana da shi kai tsaye, ba a zaurance ko da ruya ba. Ya kan ga zatina. Me yasa ba ku ji tsoron yin gunaguni a kan bawana Musa ba?"
\s5
\v 9 Fushin Yahweh ya yi ƙuna a kansu, kana ya bar su.
\v 10 Girgijen ya tashi daga bisa rumfar, nan da nan Miriyam ta zama kuturwa--ta yi fari kamar auduga. Da Haruna ya juya sai ya ga Miriyam ta zama kuturwa.
\s5
\v 11 Sai Haruna yace da Musa, "Ya shugabana, idan ka yarda kada ka riƙe mu a kan wannan abu. Mun yi magana cikin wawanci, kuma mun yi zunubi.
\v 12 Idan ka yarda kada ka barta ta zama kamar jaririn da naman jikinsa ya lalace sa'ad da yake fitowa daga cikin mahaifar uwarsa."
\s5
\v 13 Sai Musa ya yi kira zuwa ga Yahweh. Ya ce, "Idan ka yarda ka warkar da ita, Ya Allah, idan ka yarda."
\v 14 Sai Yahweh yace da Musa, "Idan ubanta ya tofa mata yau a fuska, za a ƙasƙantar da ita har kwana bakwai. Ka rufe ta a bayan zango har kwana bakwai. Bayan haka sai ka dawo da ita."
\v 15 Haka aka rufe Miriyam har kwana bakwai a bayan zango. Mutanen ba su tafi ba sai da ta dawo zangon.
\s5
\v 16 Bayan haka, mutanen suka tafi daga Hazerot suka yi zango a cikin jejin Faran.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Ka aiki waɗansu mutane su dubo ƙasar Kan'ana, wadda na ba mutanen Isra'ila. Ka aiki mutum ɗaya daga kowacce kabila ta ubanninsu. Kowanne ya zama shugaba ne a cikinsu."
\s5
\v 3 Musa ya aike su daga jejin Faran, domin su yi biyayya da ummarnin Yahweh. Dukkan su shugabanni ne a cikin mutanen Isra'ila.
\v 4 Ga sunayensu: daga kabilar Ruben, Shammuya ɗan Zakkur;
\s5
\v 5 daga kabilar Simiyon kuma, Shafat ɗan Hori;
\v 6 daga kabilar Yahuda, kuma Kaleb ɗan Yefunne;
\v 7 daga kabilar Issakar kuma, Igal ɗan Yosef;
\v 8 daga kabilar Ifraim kuma, Hosheya ɗan Nun;
\s5
\v 9 daga kabilar Benyamin kuma, Falti ɗan Rafu;
\v 10 daga kabilar Zebulun kuma, Gaddiyel ɗan Sodi;
\v 11 daga kabilar Yosef kuma, (wato daga kabilar Manasse), Gaddi ɗan Susi;
\v 12 daga kabilar Dan kuma, Ammiyel ɗan Gemalli;
\s5
\v 13 daga kabilar Asha kuma, Shetur ɗan Mikayel;
\v 14 daga kabilar Naftali kuma, Nãbi ɗan Bofsi;
\v 15 daga kabilar Gad kuma, Gewuyel ɗan Maki.
\v 16 Waɗannan su ne sunyen mazajen da Musa ya aika su dubo ƙasar. Musa ya kira Hosheya ɗan Nun da suna Yoshuwa.
\s5
\v 17 Musa ya aike su domin su dubo ƙasar Kan'ana. Ya ce da su, "Ku bi ta Negeb ku hau ta ƙasar kan tudu.
\v 18 Ku dubo ƙasar ku ga yadda ta ke. Ku yi la'akari da irin mutanen da suke zauna a can, ko suna da ƙarfi ko kuwa raunana ne, kuma ko suna da yawa ko 'yan kaɗan ne.
\v 19 Ku ga yadda ƙasar ta ke inda suke zaune. Ta na da kyau ko ba ta da kyau? Yaya biranen suke? Kamar zango--zango suke, ko kuwa ƙayatattun birane ne?
\v 20 Ku gano yadda ƙasar ta ke, ko shuka za ta iya yin girma da kyau ko babu, ko akwai itatuwa ko babu. Ku yi ƙarfin hali ku kawo abin misali daga irin amfanin ƙasar." Lokacin kuwa na nunar fari na inabi ne.
\s5
\v 21 Sai mazajen suka je suka duba ƙasar tun daga jejin Zin zuwa Rehob, kusa da Lebo Hamat.
\v 22 Suka hau ta Negeb suka ɓullo Hebron. Ahiman da Sheshayi da Talmai, waɗanda jinsinsu ya fito daga Anak, suna nan. Ya zama an gina Hebron shekaru bakwai kafin Zowan ta cikin Masar.
\s5
\v 23 Sa'ad da suka kawo kwarin Eshkol, suka yanki reshe da kurshen zaitun. Suka sagalo shi a jikin sanda tsakanin ƙungiyoyinsu biyu. Suka kawo rumman da ɓaure kuma.
\v 24 Wannan wurin a ka kira da suna kwarin Eshkol, saboda kurshen zaitun da mutanen Isra'ila suka yanko daga can.
\s5
\v 25 Bayan kwana arba'in, suka dawo daga dubo ƙasar.
\v 26 Suka dawo wurin Musa da Haruna da dukkan taron jama'ar Isra'ila a cikin jejin Faran a Kadesh. Suka kawo masu labari tare da dukkan jama'a, suka nuna masu irin amfanin ƙasar.
\s5
\v 27 Suka ce da Musa, "Mun kai ƙasar daka aike mu. Gaskiya ne tana zubo da madara da zuma. Ga irin amfanin wurin.
\v 28 Duk da haka, mutanen da suka yi gidajensu a can ƙarfafa ne. Biranen ƙayatattu ne manya ne kuma. Mun kuma ga kabilar Anak a can.
\v 29 Amelekawa na zaune a Negeb. Hitiyawa da Yebusawa da Amoriyawa na da gidajensu a ƙasar kan tudu. Kan'aniyawa na zama a bakin teku kusa da Kogin Yodan."
\s5
\v 30 Kaleb ya sa mutanen suka yi shiru a gaban Musa yace, '"Bari mu je mu karɓe ƙasar, gama ba shakka za mu iya cin nasara da ita."
\v 31 Amma mazajen da suka je tare da shi suka ce, "Ba za mu iya kai wa mutanen nan hari ba domin sun fi mu ƙarfi."
\s5
\v 32 Sai suka kai rahoton karya gwiwa ga mutanen Israila game da ƙasar da suka je suka dubo. Suka ce, "Ƙasar da muka je muka dubo cinye mazauna ƙasar su ke yi. Dukkan mazajen da muka gano a can dogaye ne ƙwarai.
\v 33 Mun gano jarumawa a can, zuriyar Anak, waɗanda dama jarumawa ne. Idan a ka kwatanta mu da su, mu kamar fara mu ke, haka kuma suka gan mu."
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 A wannan daren al'ummar dukka ta yi kuka da ƙarfi.
\v 2 Dukkan mutanen suka ba Musa da Haruna laifi. Dukkan al'ummar suka ce da su, "Da ma mun mutu a ƙasar Masar, ko nan cikin jeji!
\v 3 Meyasa Yahweh ya kawo mu wannan ƙasar mu mutu ta wurin takobi? Matayenmu da ƙanananmu za su cutu. Ba zai fi kyau a gare mu mu koma Masar ba?"
\s5
\v 4 Suka cewa junansu, "Bari mu zaɓi wani shugaba, mu koma Masar."
\v 5 Sai Musa da Haruna suka kwanta a gaban taron mutanen Isra'ila da fuskokinsu a ƙasa.
\s5
\v 6 Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne, waɗanda ke cikin waɗanda aka aika dubo ƙasar, suka tsage tufafinsu.
\v 7 Suka yi magana da al'ummar mutanen Isra'ila. Suka ce, "Ƙasar da muka ratsa muka dubo muka wuce, ƙasa ce mai kyau ƙwarai.
\v 8 Idan Yahweh ya ji daɗin mu, zai kai mu cikin wannan ƙasa ya ba mu ita. Ƙasar tana zubowa da madara da zuma.
\s5
\v 9 Amma kada ku bijire wa Yahweh, kuma kada ku ji tsoron mutanen ƙasar, gama su gurasa ne a gare mu. Tsaronsu zai rabu da su, saboda Yahweh na tare da mu. Kada ku ji tsoron su."
\v 10 Sai dukkan taron suka ce a jejjefe su da duwatsu. Amma sai ga darajar Yahweh ta bayyana ga dukkan mutanen Isra'ila a rumfar taruwa.
\s5
\v 11 Yahweh yace da Musa, "Har yaushe waɗannan mutane za su rena ni? Har yaushe za su kasa gaskatawa dani, su rena dukkan alamu da ikon dana yi a cikin su?
\v 12 Zan sa annoba ta auko masu, ba za su zama gãdona ba kuma, in sa kabilarka ta zama babbar al'ummar da za ta fi su girma."
\s5
\v 13 Musa yace da Yahweh, "Idan ka yi haka Masarawa za su ji labari, saboda ka kuɓutar da waɗannan mutane da ikonka daga wurinsu.
\v 14 Za su gaya wa mazaunan wannan ƙasar. Sun ji labarinka, Yahweh, kana tare da waɗannan mutane ne saboda ana ganin ka fuska da fuska. Girgijenka yana tsayawa a bisa mutanenka. Kana tafiya a gabansu da umudin girgije da rana da dare kuwa da umudi na wuta.
\s5
\v 15 Yanzu idan ka kashe mutanen nan kamar mutum ɗaya, sa'an nan al'umman da suka ji labarin jaruntakarka zasu ce,
\v 16 'Saboda Yahweh ya kăsă kai mutanen nan ƙasar da ya rantse zai ba su, sai ya kashe su a cikin jeji.'
\s5
\v 17 Ina roƙon ka, ka yi amfani da ikonka mai girma. Gama ka ce,
\v 18 'Yahweh mai jinkirin fushi ne kuma mai yalwar jinƙai. Yakan gafarta mugunta da laifofi. Ba zai yafe mugunta ba sa'ad da ya kawo horon zunubin kakanni a kan zuriyarsu, har zuwa zuriya ta uku da ta huɗu.'
\v 19 Ka yafe, zunubin mutanen nan, ina roƙon ka, saboda alƙawarin jinƙanka mai girma, kamar yadda kake ta gafarta wa mutanen nan tun daga cikin Masar har zuwa yanzu."
\s5
\v 20 Sai Yahweh yace, "Na yafe masu saboda roƙonka,
\v 21 amma gaskiya, kamar yadda nake a raye, dukkan duniya zata cika da ɗaukakata,
\v 22 dukkan mutanen nan da suka ga ɗaukakata da alamu na ikon da na yi a cikin Masar da cikin jeji--har yanzu suna jarabta ta sau goma kenan ba su saurari muryata ba.
\s5
\v 23 Babu shakka ba za su ga wannan ƙasar da nayi wa ubanninsu alƙawari ba. Waɗannan da suka rena ni ba ko ɗaya a cikin su da zai gan ta,
\v 24 sai bawana Kaleb kaɗai, saboda da ruhunsa daban yake. Ya bini da gaske; zan kai shi ƙasar da ya je ya dubo. Zuriyarsa zasu gaje ta.
\v 25 (To Amelikawa da Kan'aniyawa suna zaune a cikin kwari.) Gobe ka juya ka tafi jejin ka bi ta Teku na Iwa."
\s5
\v 26 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna. Ya ce,
\v 27 "Har yaushe zan jure da muguntar mutanen nan da suke ta ganin laifina? Na ji gunagunin mutanen Isra'ila game da ni.
\s5
\v 28 Ka ce da su, 'Yahweh yace, 'kamar yadda nike a raye, 'kamar yadda kuka yi magana ina ji, ga abin da zan yi ma ku:
\v 29 Dukkan ku da kuka yi gunaguni a kaina zaku mutu a cikin jeji, ku da aka ƙirga cikin lissafi, dukkan ma su shekara ashirin zuwa gaba.
\v 30 Babu shakka ba zaku shiga ƙasar dana yi alƙawari zan yi maku gida ba. Sai dai Kaleb ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.
\s5
\v 31 Amma ƙanananku da kuka ce abin zai shafe su, su zan kai cikin ƙasar. Za su ji yadda ƙasar da kuka ƙi ta ke!
\v 32 Ku kuwa jikkunanku za su faɗi su mutu a cikin jeji.
\v 33 'Ya'yanku za su zama makiyaya a cikin jeji har shekara arba'in. Dole ne za su sha sakamakon aikinku na bijirewa a cikin jeji har sai gawarwakinku sun ƙare.
\s5
\v 34 Kamar yadda kuka yi kwana arba'in kuna dubo ƙasar, Haka zaku yi shekara arba'in kuna ɗaukar alhakin zunubanku-- kowanne kwana ɗaya a matsayin shekara ɗaya, zaku gane abin da zai faru da ku idan na yi găba da ku.
\v 35 Ni, Yahweh ne na faɗa. Babu shakka haka zan yi wa wannan al'umma mai mugunta da suka haɗa kai gãba dani. Za a datse su gaba ɗaya, a nan za su mutu."
\s5
\v 36 Haka mazajen da Musa ya aika su gewayo ƙasar, waɗanda suka dawo suka kawo rahoton da ya sa dukkan taron jama'a suka yi gunaguni a kan Musa game da ƙasar--
\v 37 Waɗan nan mazaje da suka kawo rahoto marar daɗi aka hallaka su da annoba daga wurin Yahweh suka mutu.
\v 38 A cikin mazajen da suka gewaya ƙasar, Yoshuwa ɗan Nun da Kaleb ɗan Yefunne ne kaɗai suka rage da rai.
\s5
\v 39 Sa'ad da Musa ya bada wannan rahota ga mutanen Isra'ila dukka, sai suka yi baƙinciki ƙwarai.
\v 40 Suka fita tun da sassafe suka hau bisa kan tsauni suka ce, "Dubã, ga mu nan, kuma za mu tafi wurin da Yahweh ya yi alƙawari, gama mun yi zunubi."
\s5
\v 41 Amma Musa yace, "Meyasa kuke wulakanta ummarnin Yahweh? Ba za ku yi nasara ba.
\v 42 Kada ku tafi, saboda Yahweh ba ya tare da ku, domin ya kare ku, don kada abokan gãbarku su yi nasara a kanku ba.
\v 43 Su Amelekawa da Kan'aniyawa suna can, kun zo ku mutu da kaifin takobi saboda kun dena bin Yahweh. Saboda haka ba zai kasance tare da ku ba."
\s5
\v 44 Amma sai suka yi taurin kai suka tafi ƙasar kan tudu; amma kuma, ko Musa ko akwatin alƙawarin Yahweh ba wanda ya bar zangon.
\v 45 Sai Amelekawa suka sauko, Kan'aniyawa ma suka sauko daga tuddai. Suka kai hari a kan Isra'ilawa suka kuma ci nasara a kansu har zuwa Horma.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Sai Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Kayi magana da mutanen Isra'ila ka ce dasu, 'Sa'ad da kuka shiga ƙasar da zaku zauna, wadda Yahweh zai ba ku,
\v 3 sai ku shirya baiko da wuta domin Yahweh, ko baiko na ƙonawa ko hadaya domin a cika alƙawarin baiko na yardar rai, ko baiko na idodinku, domin ku kawowa Yahweh baiko na ƙamshi mai daɗi daga garkenku ko daga dangwalinku.
\s5
\v 4 Dole ku kawo wa Yahweh baiko na ƙonawa da baiko na gari da hadaya ta sha ta gari mai kyau wanda aka gauraya da mai kwalba bakwai.
\v 5 Kuma za ku haɗa baiko na ƙonawar ko hadayar da ruwan inabi saboda sha domin kowanne ɗan rago.
\s5
\v 6 Idan rago ne ake miƙawa, sai kuma a shirya baiko na gari awo uku wanda aka gauraya da mai kwalba biyar.
\v 7 Domin baiko na sha kuwa sai a bada ruwan inabi kwalba biyar. Zai bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh.
\s5
\v 8 Idan kuka shiya bijimi domin baiko na ƙonawa ko hadaya domin ku cika alƙawari, ko baiko na zumunci ga Yahweh,
\v 9 sai ku miƙa bijimin tare da baiko na hatsi, gari mai kyau awo uku wanda aka gauraya da mai kwalba biyu.
\v 10 Dole kuma ku ba da baiko na ruwan inabi kwalba biyu, baikon da aka yi da wuta, da zai bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh.
\s5
\v 11 Haka za ayi wa kowanne bijimi da kowanne rago da kowanne ɗan rago da 'yan awaki.
\v 12 Kowacce hadaya za ku shirya ku miƙa haka za ku yi ta kamar yadda aka bayyana a nan.
\v 13 Dukkan 'yan ƙasa da aka haifa a Isra'ila haka za su yi waɗannan abubuwa, sa'adda wani ya kawo baikon da za ayi da wuta, domin ya kawo ƙanshin da zai gamshi Yahweh.
\s5
\v 14 Idan baƙo na zaune wurinku, ko duk wanda zai zauna a cikin ku a dukkan zamanin mutanenku, dole ne ya yi baikon da za ayi da wuta domin ya bada ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. Dole ne shi ma ya yi kamar yadda kuke yi.
\v 15 Dokar da ta shafi taron jama'arku ita ce za ta shafi baƙon da yake zaune a wurinku, wannan zaunanniyar doka ce gare ku dukkan zamanin jama'arku. Kamar yadda kuke haka ma wanda ya zo wurin ku zai zama. Dole ne ya yi kamar yadda kuke yi a gaban Yahweh.
\v 16 Doka da ka'idar da ta shafe ku ita ce kuma za ta shafi baƙon da yake tare da ku.'"
\s5
\v 17 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce,
\v 18 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce da su, 'Idan kuka zo ƙasar da zan kai ku,
\v 19 idan kuka ci abincin da aka yi a ƙasar, sai ku yi baiko ku miƙa shi gare ni.
\s5
\v 20 Cikin abin da za ku fara ɓarzawa sai ku yi dunƙule da shi ku ɗaga shi kamar baiko na ɗagawa a masussuka. Ga yadda za ku ɗaga shi.
\v 21 Daga abin da kuka ɓarza da fari sai ku yi bayarwa ta ɗagawa a dukkan zamanin mutanenku.
\s5
\v 22 Wani lokaci za ku yi zunubi ba tare da saninku ba, idan ba ku yi biyayya da dukkan umarnin dana gaya wa Musa ba--
\v 23 dukkan abin dana umarce ku ta wurin Musa tun daga ranar dana fara baku umarni har zuwa zamanin mutanenku dukka.
\v 24 A lamarin zunubin da aka yi ba tare da niyya ba kuma jama'a ba su sani ba, sai dukkan jama'a kowa ya yi baiko na ƙonawa da bijimi domin ya bada shessheƙi na ƙanshi mai daɗi ga Yahweh. Tare da wannan sai a yi baiko na hatsi dana sha, kamar yadda aka umarta a ka'idodi, da baiko na ɗan akuya ɗaya domin baiko na zunubi.
\s5
\v 25 Sai firist ya yi kafara domin dukkan taron jama'ar Isra'ila. Za a gafarta masu saboda zunubin kuskure ne. Sun kawo hadayarsu, baikon da aka yi da wuta zuwa gare ni. Sun kawo baiko na zunubi gare ni gama kuskure ne.
\v 26 Sa'an nan za a gafartawa dukkan taron jama'ar Isra'ila, da dukkan baƙin da suke zaune tare da su, saboda dukkan taron jama'ar sun yi zunubin ba tare da sanin su ba,
\s5
\v 27 Idan wani mutum ya yi zunubi cikin rashin sani, sai ya miƙa baiko na ɗan akuya bana ɗaya saboda zunubinsa.
\v 28 Sai firist ya yi kafara a gaban Yahweh saboda mutumin da ya yi zunubi ba tare da saninsa ba. Idan aka yi kafara za a gafarta wa wannan mutum.
\v 29 Sai ku kasance da doka iri ɗaya ga duk wanda ya yi wani abu ba tare da saninsa ba. Doka ɗaya da ta shafi ɗan ƙasa da aka haifa a Isar'ila ita ce kuma za ta shafi baƙin dake zaune a cikin su.
\s5
\v 30 Amma idan mutum ya yi ba dai--dai ba cikin sanin sa, ko ɗan ƙasa ne ko baƙo, ya yi mani zunubi. Wannan mutum za a datse shi daga cikin mutanensa.
\v 31 Saboda ya rena maganata ya karya dokokina, wannan mutum za a datse shi sarai. Zunubinsa zai zauna a kansa.
\s5
\v 32 Sa'ad da mutanen Isra'ila ke a cikin jeji, sai suka tarar da wani mutum na tattara itace ranar Asabaci.
\v 33 Waɗanda suka tarar da shi suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukkan taron jama'ar Isra'ila.
\v 34 Sai suka sa shi a cikin kurkuku saboda ba a yanke abin da za a yi masa ba.
\s5
\v 35 Sa'an nan Yahweh yace da Musa, "Sai a kashe wannan mutum. A kai shi bayan zango, dukkan jama'a su jejjefe shi da duwatsu.
\v 36 Haka dukkan jama'ar suka kawo shi bayan zango suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\v 37 Yahweh ya sake yin magana da Musa. Ya ce,
\v 38 "Kayi magana da 'ya'yan Isra'ila ka umarce su da su yi tutoci su maƙala a kafaɗun rigunansu, su maƙala su a kowacce kafaɗa da shuɗin zare. Za su yi haka a dukkan zamanin mutanensu.
\v 39 Idan kuka dube su za su zama abin tunawa da dukkan dokokina na musamman a gare ku. Ku ɗauke su a wurinku domin kada ku dubi zuciyarku da idanunku ku yi karuwanci da su.
\s5
\v 40 Ku yi wannan domin ku tuna ku yi biyayya da dukkan dokokina, kuma domin ku zama da tsarki, keɓaɓɓu domina Allahnku.
\v 41 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, ya zama Allahnku. Ni ne Yahweh Allahnku."
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Ana nan sai Korah ɗan Izhar ɗan Kohat ɗan Lawi, tare da Datan da Abiram 'ya'yan Eliyab da On ɗan Felet, zuriyar Ruben, suka taru da waɗansu mutane.
\v 2 Suka tayar wa Musa, tare da waɗansu daga cikin mutanen Isra'ila, su ɗari biyu da hamsin shugabannin jama'a sanannu sosai a cikin jama'a.
\v 3 Suka tattaro kansu domin su fuskanci Musa da Haruna. Suka ce da su, "Fankamarku ta yi yawa! Dukkan mutanen keɓaɓɓu ne, kowanne ɗayan su, kuma Yahweh na tare da su. Meyasa kuke ɗaukaka kanku fiye da sauran mutanen Yahweh?"
\s5
\v 4 Sa'ad da Musa ya ji haka, sai ya kwanta da fuskarsa ƙasa.
\v 5 Ya yi magana da Korah da dukkan waɗanda ke tare da shi, "Gobe da safe Yahweh zai nuna wanda ke nasa, da wanda ya keɓe domin kansa. Zai kawo wannan mutum kusa da shi. Zai kawo wanda ya zaɓa kusa da shi.
\s5
\v 6 Korah, kai da ƙungiyarka ga abin da za ku yi.
\v 7 Gobe ku ɗauki turare ku sa wuta a gaban Yahweh. Wanda Yahweh ya zaɓa, zai zama keɓaɓɓe na Yahweh. Fankamarku ta yi yawa, ku 'ya'yan Lebi."
\s5
\v 8 Musa ya ƙara cewa da Korah, "Ka saurara, kai zuriyar Lebi:
\v 9 ƙaramin abu ne a wurin ka da Allah na Isra'ila ya keɓe ka daga cikin mutanen Isra'ila, ya kawo ka kusa da shi, domin ka yi aiki cikin alfarwar Yahweh, kuma ka tsaya a gaban jama'a ka yi masu hidima?
\v 10 Ya kawo ku kusa da dukkan 'ya'uwanka, zuriyar Lebi, tare da kai, kuma kana nema ka zama firist!
\v 11 Wannan ne yasa kai da ƙungiyarka kuka taru ku yiwa Yahweh tayarwa. Meyasa kake gunaguni a kan Haruna, wanda ya yi biyayya da Yahweh?"
\s5
\v 12 Sai Musa ya kira Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, amma suka ce, "Ba za mu hawo ba.
\v 13 Ƙaramin abu kayi daka fito da mu daga ƙasa mai zubo da madara da zuma, ka kashe mu a cikin jeji? Yanzu kana so ka maida kanka mai mulki a kan mu!
\v 14 Bugu da ƙari, baka kai mu ƙasar dake zubowa da madara da zuma ba, ko ka bamu gonaki da lambuna su zama gadonmu. Yanzu kana so ka makantar da mu da alƙawuran wofi? Ba zamu zo wurin ka ba."
\s5
\v 15 Musa ya yi fushi ƙwarai ya ce da Yahweh, "Kada ka karɓi baikonsu. Ban ɗauki ko jaki ɗaya daga wurin su ba, kuma ban ji wa ko ɗaya a cikin su ba.
\v 16 Sa'an nan Musa yace da Korah, "Gobe kai da mutanenka za ku je gaban Yahweh--kai da su, da Haruna.
\v 17 Kowannen ku ya ɗauki tasa ya sa turare a ciki. Kuma dole kowanne mutum ya kawo tasarsa gaban Yahweh, tasoshi ɗari biyu da hamsin. Kai da Haruna kuma kowa ya kawo tasarsa,"
\s5
\v 18 Sai kowanne mutum ya ɗauki tasarsa, yasa wuta a ciki, yasa turare a cikin ta, suka tsaitsaya a ƙofar rumfa ta taruwa tare da Musa da Haruna.
\v 19 Sai Korah kuma ya tattara dukkan mutanen da suke tayarwa Musa da Haruna a ƙofar rumfa ta taruwa, sai ɗaukakar Yahweh ta bayyana ga dukkan jama'a.
\s5
\v 20 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna:
\v 21 "Ku ware kanku daga cikin wannan taron domin in hallaka su yanzun nan."
\v 22 Musa da Haruna suka kwanta da fuskokinsu a ƙasa suka ce, "Ya Allah, Allah na ruhohin dukkan mutane, idan mutum ɗaya ya yi zunubi, ka yi fushi da dukkan mutane?"
\s5
\v 23 Yahweh ya amsa wa Musa. Ya ce,
\v 24 "Ka faɗawa taron jama'ar. Ka ce, 'Ku gudu daga rumfar Kora da Datan da Abiram."'
\s5
\v 25 Sai Musa ya tashi ya je wurin Datan da Abiram; dattawan Isra'ila suka bi shi.
\v 26 Ya yi magana da taron ya ce, "Sai ku gudu daga rumfunan waɗannan mugayen mutane kada ku taɓa kome nasu."Idan ba haka ba zunubinsu zai cinye ku dukka."
\v 27 Haka jama'ar dake cikin rumfunan su Korah da Datan da Abiram suka rabu da su. Datan da Abiram suka fito suka tsaya a ƙofar rumfunansu, tare da matansu da 'ya'yansu da ƙananansu.
\s5
\v 28 Sa'an nan Musa yace, "Ta wurin wannan za ku sani Yahweh ne ya aiko ni in yi dukkan waɗannan ayyuka, gama ba domin kaina nake yin su ba.
\v 29 Idan mutanen nan suka yi mutuwa irin ta kowanne mutum, kamar yadda abu yakan sami kowanne mutum, ba Yahweh ne ya aiko ni ba.
\v 30 Amma idan Yahweh ya halitto wani sabon abu, idan ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su, tare da dukkan abin da suke da shi, suka tafi cikin lahira da rai, sa'an nan za ku gane waɗannan mutane sun rena Yahweh."
\s5
\v 31 Da dai Musa ya gama faɗin wannan magana, ƙasa ta buɗe a ƙarƙashin waɗannan mutane.
\v 32 Ƙasa ta buɗe bakinta ta haɗiye su, da iyalinsu da dukkan jama'ar dake na Korah, tare da dukkan abin da suka mallaka.
\s5
\v 33 Haka su da dukkan abin da suka mallaka suka tafi lahira da ransu. Ƙasa ta rufe a kan su, suka lalace daga wurin taron jama'a.
\v 34 Dukkan mutanen Isra'ila dake kewaye da su suka gudu daga biranensu. Suka yi kururuwa, watakila mu ma ƙasa za ta haɗiye mu!"
\v 35 Sa'an nan wuta ta walƙato daga wurin Yahweh ta haɗiye mutane 250 da suka miƙa turare.
\s5
\v 36 Yahweh ya ƙara yin magana da Musa ya ce,
\v 37 Ka yi magana da Eliyeza ɗan Haruna firist bari ya ɗauke tasoshin daga cikin wuta, gama tasoshin keɓaɓɓu ne a gare ni. Sa'an nan ya barbaza garwashin daga nesa.
\v 38 Ɗauke tasoshin waɗanda suka rasa rayukansu saboda zunubinsu. A bubbuge su su zama marfin bagadinsu. Waɗancan mutanen sun miƙa su a gabana, don haka sun zama keɓaɓɓu a gare ni. Za su zama alamar kasancewata ga mutanen Isra'ila."
\s5
\v 39 Sai Eliyeza firist ya ɗauki tasoshi na tagulla da mutanen da suka ƙone suka yi amfani da su, aka bubbuga su, suka zama marfin bagadin,
\v 40 domin su zama abin tunawa ga mutanen Isra'ila, domin ya zama ba wani baƙo wanda ba a cikin kabilar Haruna yake ba da zai zo ya ƙona turure a gaban Yahweh, domin kada su zama kamar Korah da ƙungiyarsa--kamar yadda Yahweh ya bada umarni ta wurin Musa.
\s5
\v 41 Amma da safiya ta yi sai dukkan taron jama'ar suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna. Suka ce, "Kun kashe mutanen Yahweh."
\v 42 Sai ya zama, sa'ad da mutanen suka taru gãba da Musa da Haruna, da suka duba wajen rumfa ta taruwa, duba sai gashi girgije ya rufe ta. Darajar Yahweh ta bayyana,
\v 43 sai Musa da Haruna suka zo gaban rumfar ta taruwa.
\s5
\v 44 Sa'an nan Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 45 "Ka gudu daga gaban wannan taron domin in hallaka su yanzu--yanzu." Sai Musa da Haruna suka kwanta da fuskokinsu a ƙasa.
\v 46 Musa yace da Haruna, "Ka ɗauki tasa, ka sa wuta a ciki ba a kan bagadin ba, ka sa turare a cikin ta, ka kai ta wurin taron jama'ar, da sauri ka yi kafara saboda su, saboda fushi na zuwa daga wurin Yahweh. Annobar ta fara."
\s5
\v 47 Sai Haruna ya yi kamar yadda Musa ya ummurce shi. Ya ruga cikin tsakiyar taron jama'ar. Annobar ta fara bazuwa a cikin mutanen, sai ya sa turaren a ciki ya yi kafara saboda mutanen.
\v 48 Haruna ya tsaya a tsakanin matattu da masu rai; ta haka annobar ta tsaya.
\s5
\v 49 Waɗanda annobar ta kashe sun kai 14,700, ban da waɗanda suka mutu cikin lamarin Korah.
\v 50 Haruna ya dawo wurin Musa a ƙofar rumfa ta taruwa, sai annobar ta ƙare.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa. Ya ce,
\v 2 "Faɗa wa mutanen Isra'ila, su ɗauki sanduna daga gare su, kowanne ɗaya domin kabilar kakanni, sanduna goma sha biyu. Rubuta sunan kowanne mutum a kan sandarsa.
\s5
\v 3 Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lebi. A kan kowacce sanda domin shugaban kabilar kowanne kakanninsa.
\v 4 Ka ajiye sandunan a cikin alfarwar taro a gaban ka'idodi alƙawari, wurin da nakan sadu da kai.
\v 5 Zai zamana sandan mutumin dana zaɓa za ta yi toho. Zan sa ƙorafe-ƙorafe daga mutanen Isra'ila ya tsaya, waɗanda suke magana a kanka."
\s5
\v 6 Sai Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila. Dukkan shugabannin kabilu suka ba shi sandunan, sanda ɗaya daga kowanne shugaba, da aka zaɓa daga dukkan kabilun kakanin, sanduna goma sha biyu dukka. Sandan Haruna na cikinsu.
\v 7 Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Yahweh cikin alfarwar ka'idodin alƙawari.
\s5
\v 8 Kashegari Musa ya tafi cikin alfarwar ka'dodin alƙawari, sai ga shi, sandar Haruna ta kabilar Lebiyawa ta yi toho. Ta tuko tayi toho ta bada 'ya'yan almon nunannu!
\v 9 Musa kuwa ya fito da dukkan sandunan a gaban Yahweh zuwa ga dukkan mutanen Isra'ila, sai kowanne mutum ya ɗauki sandansa.
\s5
\v 10 Yahweh yace da Musa, "Sa sandan Haruna a gaban ka'idodin alƙawari. Ka ajiye ta alama ce a kan mutane waɗanda ke tawaye saboda ka kawo ƙarshen gunaguni a kaina, ko kuwa za su mutu.
\v 11 Musa kuwa ya yi kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 12 Mutanen Isra'ila suka yi magana da Musa suka ce, "Za mu mutu a nan. Dukkan mu zamu lalace! Duk wanda ya zo nan, kowa ya kusanci alfarwar Yahweh, zai mutu.
\v 13 Mu dukka za mu lalace?"
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Yahweh yace da Haruna, "Kai, da 'ya'yanka, da kabilar kakanninka za ku ɗauki hakkin dukkan zunubai da za ayi game da alfarwar sujada. Amma kai da 'ya'yanka ne kaɗai za ku ɗauki hakkin dukkan zunuban da ya shafi kowanne firist.
\v 2 Kuma sauran 'yan'uwan kabilar Lebi, kakanninka, ka kawo su tare da kai saboda su kasance tare da kai don su taimake ka da 'ya'yanka aiki a gaban alfarwa ta ka'idodin alƙawari.
\s5
\v 3 Su yi maka dukkan ayyukan alfarwa. Amma ba za su zo su kusanci kowanne abu dake a wuri mai tsarki, ko wani abu da ya shafi bagaɗi ba, ko su da kai dukka ku mutu.
\v 4 Su haɗu da kai, don su lura da alfarwar taruwa, domin dukkan aikace-aikace na alfarwar. Kada wani baƙo ya zo kusa da ku.
\v 5 Ku ɗauki nauyin ayyukan wuri mai tsarki da kuma bagaɗi saboda kada fushina ya zo a kan mutanen Isra'ila kuma.
\s5
\v 6 Duba, ni da kaina na zaɓi 'yan 'uwan Lebiyawa daga cikin zuriyar Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, an bani su don su yi aikin lura da alfarwar taro.
\v 7 Amma da kai da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagaɗi da dukkan aiki na bayan labule. Kune da kanku za ku yi waɗannan aikace-aikace. Ina baku aikin firist a matsayin kyauta. Duk wani baƙo wanda ya matso zai mutu."
\s5
\v 8 Sai Yahweh ya cewa Haruna, "Duba, na baka aikin, kula da baikon ɗagawa a gare ni, da dukkan baye -baye masu tsarki da mutanen Isra'ila suka bani. Na bada dukkan baye-bayen a gare ka da 'ya'yanka maza har abada.
\v 9 Wannan zai zama rabonka daga abubuwa masu tsarkin gaske da za a ajiye daga wuta. Daga kowanne baiko nasu--kowacce bayarwar hatsi, da kowacce bayarwa don zunubi da bayarwar laifi--za su ajiye su gare ka da 'ya'yanka.
\s5
\v 10 Waɗannan baye-baye suna da tsarki sosai, kowanne namiji ya ci shi, domin suna da tsarki a gare ka.
\v 11 Waɗannan su ne baye-bayen da za su zama naka: sun zama da tsarki daga dukkan bayarwar ɗagawa daga mutanen Isra'ila. Na bada su a gare ka da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata, a matsayin naka har abada. Duk wanda yake da tsarki a iyalinka zai iya cin kowanne daga waɗannan baye-bayen.
\s5
\v 12 Dukkan mai mai kyau, dukkan sabon ruwan inabi da hatsi da nunar fari masu kyau da mutane suka bada gare ni--dukkan waɗannan abubuwa na bada su a gare ka.
\v 13 Nunan fari na dukkan amfanin gonarsu, wanda suke kawo wa gare ni, za su zama naka. Duk wanda yake da tsarki a iyalinka zai iya cin waɗannan abubuwa.
\s5
\v 14 Iyakar abin da aka keɓe a Isra'ila zai zama naka.
\v 15 Dukkan abin da aka haifa, dukkan nunar fari wadda jama'a suka bayar ga Yahweh, mutum ko dabba, zai zama naka. Duk da haka, mutane dole su fanshi kowanne haihuwar fari na mutum, su kuma fanshi ɗan fari na dabba namiji da ba shi da tsarki.
\v 16 Waɗanda mutane za su fansa dole sai sun kai wata ɗaya da haihuwa. Sa'an nan mutane zasu iya fansar su, gama kuɗinsu shekel biyar ne bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi na shekel, wanda ya ke dai dai da awo ashirin na gerah.
\s5
\v 17 Amma haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya ko ta akuya--ba za ka fanshi waɗannan dabbobi ba; keɓaɓɓu ne a gare ni. Sai ka yayyafa jininsu a kan bagaɗi, ka ƙona kitsensu a matsayin baiko na ƙonawa, abin ƙanshi mai gamsarwa ga Yahweh.
\v 18 Namansu zai zama naka. Kamar ƙirjin da aka ɗaga da cinyar dama, namansu zai zama naka.
\s5
\v 19 Dukkan baye--baye masu tsarki da mutanen Isra'ila suka bayar ga Yahweh, na bada su gare ka da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata tare da kai, yadda za ku ci gaba da samun rabo ke nan. Wannan alƙawarin gishiri mara ƙarewa ne, alƙawarin yana nan har abada, a gaban Yahweh domin ka da zuriyarka.
\v 20 Yahweh yace da Haruna, "Ba za ka sami gãdo a cikin ƙasar mutane ba, ko ka sami rabon kaya a cikin mutane. Ni ne rabonka da gãdonka a cikin mutanen Isra'ila.
\s5
\v 21 Duba, ga zuriyar Lebi, na ba su dukkan zakar Isra'ila a matsayin gãdonsu saboda hidimar da suke yi a cikin rumfa ta taruwa.
\v 22 Daga yanzu mutanen Isra'ila za su zo kusa da rumfa ta taruwa, ko su ɗauki alhakin wannan zunubi, su mutu.
\s5
\v 23 Lebiyawa ne za su yi aikin da ya shafi rumfa ta taruwa. Za su ɗauki alhakin kowane zunubi dangane da shi. Wannan zai zama doka ta din-din-din a dukkan zamanan mutanenka. A cikin mutanen Isra'ila ba za su sami gãdo ba.
\v 24 Gama zakkar mutanen Isra'ila, wadda za su miƙa a matsayin gudummuwarsu gare ni-- waɗannan ne na bayar ga Lebiyawa a matsayin gãdonsu. Wannan shi yasa na ce da su, 'Baza su sami gãdo ba a cikin mutanen Isra'ila.'"
\s5
\v 25 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 26 "Dole ka yi magana da Lebiyawa ka ce da su, 'Sa'ad da suka karɓi kashi goma daga mutanen Isra'ila wanda na basu gãdo, sai ku bada gudummuwa daga cikin ta ga Yahweh, kashi goma na zakkar.
\v 27 dole ku ɗauke ta kamar kashi goma na hatsinsu ne daga masussuka ko kuma kamar amfani daga wurin matsewar inabinku.
\s5
\v 28 Haka kuma dole ku miƙa gudummuwa ga Yahweh daga dukkan zakkar da kuke karɓa daga wurin mutanen Isra'ila. Daga ciki dole za ku bayar da gudummuwa ga Haruna firist.
\v 29 Daga dukkan kyaututtukan da kuke karɓa, dole ku bada kowacce gudummuwa ga Yahweh. Dole ku yi wannan daga dukkan abu mafi kyau mafi tsarki da aka ba ku.'
\s5
\v 30 Saboda haka dole ka ce da su, 'Sa'ad da kuka bada mafi kyau daga ciki, sai ya zama na Lebiyawa kamar amfanin da ya fito daga masussuka da wurin matsewar inabi.
\v 31 Za ku iya cin sauran kyaututtukanku a kowanne wuri, ku da iyalinku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a rumfa ta taruwa.
\v 32 Ba kuwa za ta zama maku sanadin laifi ba ta wurin cinta da shanta, in dai har kuka bada ga Yahweh mafi kyau daga cikin abin da ku ka karɓa. Amma ba za ku ɓata tsarkakakken baye-bayen na mutanen Isra'ila ba, ko ku mutu.'"
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna.
\v 2 Ya ce, "Wannan ita ce ka'ida, da doka wadda nake umartar ku: Ka faɗawa mutanen Isra'ila dole su kawo maka jar karsana marar lahani ko wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba.
\s5
\v 3 Sai ka ba Eliyeza firist karsanar. Dole ya kawo ta a wajen zango, kuma dole wani zai yanka ta a gabansa.
\v 4 Dole Eliyeza, firist, ya ɗibi jininta da yatsansa ya yayyafa sau bakwai a gaban rumfa ta taruwa.
\v 5 Dole sai wani firist ya ƙone karsanar a idonsa. Dole zai ƙone fatarta da namanta da jinin tare da ƙashinta.
\v 6 Dole firist ya ɗauki itacen al'ul da abin tsaftacewa da mulufi ya jefa su dukka a cikin tsakiyar wutar da take ƙone karsanar.
\s5
\v 7 Sa'an nan dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka a cikin ruwa. Sa'an nan zai zo ya shiga zangon, a wurin zai zama da ƙazamta har zuwa maraice.
\v 8 Shi kuwa wanda ya ƙone karsanar zai wanke tufafinsa a cikin ruwa, ya yi wanka a cikin ruwa. Zai zama da ƙazamta har zuwa maraice.
\s5
\v 9 Mutumin dake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya sa ta wajen sansani a wuri mai tsabta. Za a adana tokar saboda jama'a mutanen Isra'ila. Za su riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi, tun da yake tokar daga bayarwar zunubi ce.
\v 10 Shi kuwa wanda ya tara tokar karsanar sai ya wanke tufafinsa. Zai zama ƙazantacce har maraice. Wannan doka ce ta har abada domin mutanen Isra'ila da baƙin dake zama tare da su."
\s5
\v 11 Duk wanda ya taɓa jikin gawar mutum zai ƙazantu har kwana bakwai.
\v 12 Wannan mutum zai tsarkake kansa a rana ta uku da rana ta bakwai. Sa'an nan zai tsarkaka. Amma in a rana ta uku bai tsarkake kansa ba, ba zai zama da tsarki ba a rana ta bakwai.
\v 13 Duk wanda ya taɓa jikin gawar mutum wanda ya mutu, bai tsarkake kansa ba--wannan mutum zai kazantar da alfarwar Yahweh. Wannan mutum za a yanke shi daga cikin Isra'ila domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba. Zai kasance ƙazantacce; ƙazancewarsa za ta kasance a kansa.
\s5
\v 14 Wannan ita ce doka a kan wanda ya rasu a cikin alfarwa. Duk wanda ya shiga alfarwar da wanda ke cikin alfarwar za su ƙazantu har kwana bakwai.
\v 15 Kowanne buɗaɗɗen akwati da ba a rufe ba, zai ƙazantu.
\v 16 Hakanan ma duk wanda ke wajen alfarwar ya taɓa jikin mamacin wanda aka kashe da takobi, ko kowacce gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari--wannan mutumin zai ƙazantu har kwana bakwai.
\s5
\v 17 A yi wannan domin mutumin da ya ƙazantu: A ɗibi toka daga cikin bayarwar ƙonawa a haɗa su a cikin tulu tare da sabon ruwa.
\v 18 Duk wanda ke da tsarki zai ɗauki abin tsaftacewar ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar da dukkan kayayyakin dake cikin alfarwar, da mutanen dake a wurin, da wanda ya taɓa ƙashin ko wanda aka kashe ko wanda ya mutu, ko kabari.
\v 19 A kan rana ta uku da ta bakwai kuma wanda yake da tsarki zai yayyafa wa mutum marar tsarkin ruwa. A rana ta bakwai mutum mara tsarki zai tsarkake kansa. Zai wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa. Da maraice kuwa zai tsarkaka.
\s5
\v 20 Amma duk wanda ya kasance da rashin tsarki, wanda ya ƙi ya tsarkake kansa--wannan mutum za a datse shi daga jama'a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Yahweh. Kuma ba a yayyafa masa ruwan da ake yayyafa wa marasa tsarki ba.
\v 21 Wannan zai zama doka a gare su a kan abubuwa kamar haka. Wanda ya yayyafa ruwan don tsarkakewa, zai wanke tufafinsa, wanda kuma ya taɓa ruwan don tsarkakewa zai zama marar tasrki har maraice.
\v 22 Duk abin da mutumin da ba shi da tsarki ya taɓa, zai ƙazantu. Duk wanda kuma ya taɓa abu marar tsarki, zai ƙazantu har maraice."
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Sai mutanen Isra'ila da dukkan taron jama'a suka zo jejin Zin a wata na fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta rasu, a nan kuma aka bizne ta.
\s5
\v 2 Babu ruwa domin jama'a, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna.
\v 3 Mutane kuwa suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, "Zai fi kyau idan da mun mutu yadda 'yan'uwanmu Israilawa suka mutu a gaban Yahweh!
\s5
\v 4 Donme ka fito da taron jama'ar Yahweh a cikin wannan jeji mu mutu a nan, mu da dabobbinmu?
\v 5 Donme kuma ka sa muka fito daga Masar ka kawo mu a wannan mugun wuri? A nan babu hatsi, ko ɓaure ko inabi ko rumman ko ruwan da za a sha."
\s5
\v 6 Sai Musa da Haruna suka tafi daga gaban taron. Suka shiga alfarwar taro, suka faɗi rub da ciki. A wurin ɗaukakar Yahweh ta bayyana a gare su.
\s5
\v 7 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 8 "ɗauki sandarka ka tara jama'a, kai da Haruna ɗan'uwanka. Yi magana da dutse a gaban idanunsu, ya bada ruwan dake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo daga dutsen domin su, ka bada ruwan ga jama'ar da garkunansu su sha."
\v 9 Musa ya ɗauki sandar daga gaban Yahweh, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.
\s5
\v 10 Sai Musa da Haruna suka tara dukkan jama'ar, a gaban dutsen. Musa yace da su, "Ku saurara yanzu, ku 'yan tawaye. Za mu fito da ruwa daga cikin dutsen nan domin ku?
\v 11 Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandarsa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Jama'a kuwa suka sha, dabobbi ma suka sha.
\s5
\v 12 Sai Yahweh yace da Musa da Haruna, "Tun da yake baku gaskata ni ba, baku kuwa ɗaukaka ni akan ni mai tsarki bane a idon mutanen Isra'ila, to, baza ku kai wannan taron a cikin ƙasar dana ba su ba."
\v 13 Wannan wuri ne aka kira shi ruwan Meriba domin mutanen Isra'ila suka yi wa Yahweh gunaguni a wurin, inda shi kuma ya nuna masu shi kansa mai tsarki ne.
\s5
\v 14 Musa ya aika da manzanni daga Kadesh zuwa ga sarkin Idom: Yan'uwanka Israila sun faɗi wannan: "Ka san dukkan wahalun da suka same mu.
\v 15 Ka san yadda kakanninmu suka tafi can Masar, suka zauna a Masar da daɗewa. Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.
\v 16 Sa'ad da muka yi kira ga Yahweh, ya ji muryarmu, ya aiko da mala'ikansa, ya fishe mu daga Masar. Duba, muna nan a Kadesh, birni dake kan iyakar ƙasarka.
\s5
\v 17 Ina roƙonka ka yardar mana mu ratsa ƙasarka. Za mu bi ta cikinta mu wuce gona, ko gonar inabi, ba za mu sha ruwa daga cikin rijiyarka ba. Za mu bi ta gwadaben sarki. Ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka."
\s5
\v 18 Amma sarkin Idom ya amsa masa, "Ba za ku ratsa ta nan ba. Idan kuwa kuka yi, zan fita tare da takobi, za mu ci ku da yaƙi."
\v 19 Sai mutanen Isra'ila suka ce da shi, "Za mu bi gwadabe ne kawai. Idan kuwa mu da dabobbinmu mun sha ruwanku, za mu biya. Mu dai, a yardar mana mu wuce a ƙafafunmu, ba tare da yin wani abu ba kuma."
\s5
\v 20 Amma sarkin Idom ya sake amsa masu da cewa, "Ba mu yarda ba. "Sai sarkin Idom ya fito gãba da Isra'ila da runduna mai yawa.
\v 21 Sarkin Idom ya ƙi ya bar Isra'ila su ratsa a kan iyakarsu. Domin wannan, Isra'ila suka juya daga ƙasar Idom.
\s5
\v 22 Sai mutane suka kama tafiya daga Kadesh. Mutanen Isra'ila da dukkan jama'a suka zo Tsaunin Hor.
\v 23 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna a Tsaunin Hor, a iyakar Idom. Ya ce,
\v 24 "Dole ne Haruna ya tarar da mutanensa, don ba zai shiga ƙasar dana ba mutanen Isra'ila ba. Wannan domin ku biyun kun yi mani tawaye a kan maganata a kan ruwan Meriba.
\s5
\v 25 Ka ɗauki Haruna da Eliyeza ɗansa, ka zo da su bisa Tsaunin Hor.
\v 26 Ka ɗauki rigar firistanci ta Haruna, ka sawa ɗansa Eliyeza. Haruna zai mutu, za a tara shi ga mutanensa a can.
\s5
\v 27 Musa kuwa ya yi yadda Yahweh ya umarta. Suka hau bisa Tsaunin Hor a idon dukkan jama'a.
\v 28 Musa ya ɗauki rigar Haruna ta firist ya sawa Eliyeza ɗansa. Haruna kuwa ya rasu a bisa tsaunin. Sa'an nan Musa da Eliyeza suka sauko ƙasa.
\v 29 Sa'ad da dukkan jama'a suka ga Haruna ya rasu, sai dukkan jama'a suka yi kuka da makoki domin Haruna har kwana talatin.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Sa'ad da sarkin Kan'ana na Arad wanda ke zaune a Negeb, ya ji Isra'ila na zuwa ta hanyar Atarim, sai ya yi faɗa da Isra'ila ya ɗauki waɗansu a matsayin kamammun yaƙi.
\v 2 Isra'ila suka yi wa'adi ga Yahweh cewa, "Idan zaka ba mu nasara a kan waɗannan mutane, sai mun hallakar da su da biranensu."
\v 3 Yahweh ya saurari muryar Isra'ila, ya kuma ba su nasara a kan Kan'aniyawa. Suka hallaka su da biranensu. Shiyasa ake kiran wurin Horma.
\s5
\v 4 Suka yi tafiya daga Tsaunin Hor ta hanya zuwa Tekun Iwa a kewayen ƙasar Idom. Sai mutane suka kusan fitar da zuciya a hanya.
\v 5 Mutane suka yi gunaguni da Allah da Musa: "Meyasa kuka fitar da mu daga Masar don mu mutu a cikin jeji? Babu abinci, babu ruwa kuma bamu son irin wannan abinci mai gundura."
\s5
\v 6 Sai Yahweh ya aika da macizai masu zafin dafi a cikin mutane. Suka kuwa sassari mutane, har mutane da yawa suka mutu.
\v 7 Mutane suka zo wurin Musa suka ce, "Mun yi zunubi gama mun yi wa Yahweh gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Yahweh domin ya ɗauke macizan daga gare mu." Musa kuwa ya yi addu'a saboda mutanen.
\s5
\v 8 Yahweh ya cewa Musa, "Ka yi maciji ka sa shi a sanda, zai zamana duk wanda macijin ya sare shi idan ya dubi macijin tagulla zai tsira."
\v 9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla ya sarƙafa shi a bisa dirka. Idan kuwa maciji ya sari mutum, in dai ya dubi macijin tagulla sai ya tsira.
\s5
\v 10 Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya suka yi zango a Obot.
\v 11 Sun yi tafiya daga Obot, suka yi zango a Iye Abarim a cikin jeji suna fuskantar Mowab wajen gabas.
\s5
\v 12 Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered.
\v 13 Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda ke cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Kogin Arnon shi ne kan iyakar Mowab, tsakanin Mowab da Amoriyawa.
\s5
\v 14 Saboda haka aka faɗa a littafin Yaƙoƙi na Yahweh,"--"Waheb ta cikin yankin Sufa da kwaruruka na kogin Arnon,
\v 15 da gangaren kwaruruka wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab."
\s5
\v 16 Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, rijiya wadda Yahweh yace da Musa, "Ka tattara mutane wuri ɗaya domi na, zan kuwa ba su ruwa."
\s5
\v 17 Sai Isra'ila suka raira waka: "Ƙorama ki, ɓuɓɓugo yadda ya kamata! Rera waƙa a game da ita,
\v 18 a game da rijiyar da shugabanninmu suka gina, rijiyar da mutanenmu masu daraja suka gina, da sandan sarauta da kuma sandunansu." Daga cikin jeji suka tafi har zuwa Mattana.
\s5
\v 19 Daga Mattana suka tafi Nahaliyel, daga can kuma suka tafi Bamot,
\v 20 daga Bamot kuma suka tafi kwarin dake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda ke duban hamada.
\s5
\v 21 Sai Israila suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon sarkin Amoriyawa suna cewa,
\v 22 "Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu ratsa ta cikin gonaki ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai har mu fita daga iyakarka."
\v 23 Amma sarkin Sihon bai yarda wa Isra'ila su ratsa ta kan iyakarsa ba. Maimakon haka, sai ya tattara dukkan sojojinsa don su kaiwa Isra'ila hari a cikin jeji. Ya zo Yahaz, wurin da ya yi yaƙi da Isra'ila.
\s5
\v 24 Sojojin Isra'ila suka faɗa su da karkashewa da kaifin takobi suka karɓe ƙasar daga Arnon zuwa kogin Yabbok, har ma zuwa ƙasar mutanen Ammonawa. To sai aka ƙayata iyakar mutanen Amonawa.
\v 25 Isra'ila kuwa su ka ci dukkan biranen Amoriyawa da dukkan waɗanda su ke zama da su, ya haɗa da Heshbon da dukkan kauyukanta.
\v 26 Heshbon ita ce birnin Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi yaƙi da sarkin Mowab a dã. Sihon ya ƙwace dukkan ƙasarsa daga yakinsa zuwa Kogin Arnon.
\s5
\v 27 Don haka shi ya sa waɗanda suka yi magana suke misali cewa, "Ku zo Heshbon. Bari birnin Sihon a sake gina shi, ya kuma tabbata.
\v 28 Wuta daga Heshbon, hasken wuta daga birnin Sihon ya lanƙwame Ar ta Mowab, da mazaunan tuddan wuraren Arnon.
\s5
\v 29 Kaitonki, Mowab! Kin lalace, mutanen Kemosh. Ya sa 'ya'yansa maza na gudu, an kama 'ya'yansa mata sun zama 'yan kurkukun Sihon sarkin Amoriyawa.
\v 30 Amma yanzu an ci nasarar Sihon. Heshbon ta lalata dukkan hanya zuwa Dibon. Mun ci nasararsu a dukkan hanya zuwa Nofa, wadda ta kai kusa da Medeba."
\s5
\v 31 Sai Isra'ila suka fara zama a ƙasar Amoriyawa.
\v 32 Musa ya aika mutane su leko asirin Yazar. Suka tafi suka ci ƙauyukanta, suka kori Amoriyawa daga cikinta waɗanda ke a can.
\s5
\v 33 Sa'an nan suka juya suka tafi su haura ta hanyar Bashan. Og sarkin Bashan ya fita gãba da su, shi da dukkan sojojinsa su yi yaƙi da su a Edirai.
\v 34 Sai Yahweh yace da Musa, "Kada ka ji tsoronsa, gama na baka nasara a kansa, da dukkan sojojinsa da ƙasarsa. Ka yi masa yadda ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, waɗanda suka zauna a Heshbon."
\v 35 Haka fa suka kashe shi da 'ya'yansa maza da dukkan sojojinsa, har babu wani a mutanensa da ya rage a raye. Sai suka mallaki ƙasarsa.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Mutanen Isra'ila suka kama tafiya har suka yi zango a filayen Mowab kusa da Yeriko, a ɗaya gefen a Kogin Yodan daga birnin.
\s5
\v 2 Balak ɗan Ziffor ya ga dukkan abin da Isra'ila suka yi wa Amoriyawa.
\v 3 Mowab sun firgita kwarai saboda mutanen, domin suna da yawa. Mowab sun ji tsoron mutanen Isra'ila kwarai.
\v 4 Sarkin Mowab ya cewa dattawan Midiyanawa, "Wannan taro zai cinye dukkan abin da ke kewaye da mu, kamar yadda sã ya kan cinye ciyawar saura" Yanzu Balak ɗan Zippor wanda ke sarkin Mowab a wancan lokacin.
\s5
\v 5 Ya aika da manzanni zuwa wurin Balaam dan Beyor, a Fetor wadda ke kusa da Kogin Yuferatis, a cikin ƙasar al'ummar mutanensa. Ya kira shi ya ce, "Duba, mutane sun zo nan daga Masar. Sun rufe fuskar duniya, ga shi suna zaune kusa da ni.
\v 6 Ina roƙonka ka zo, ka la'anta mutanen nan domi na, gama suna da ƙarfi sosai fiye da ni. Ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar. Na sani duk wanda ka sawa albarka zai albarkatu, wanda kuwa ka la'anta zai zama la'ananne."
\s5
\v 7 Sai dattawan Mowab da dattawan Midiyanawa suka tafi, suka ɗauki ladar duba tsibbu. Suka tafi wurin Balaam suka faɗa masa saƙon Balak.
\v 8 Balaam yace da su, "Ku kwana a nan. Ni kuwa zan baku abin da Yahweh ya faɗa mani." Shugabannin Mowab suka tsaya suka kwana tare da Balaam.
\s5
\v 9 Allah kuwa ya zo wurin Balaam yace,
\v 10 "Su wane ne mutanen dake tare da kai? Balaam ya amsa wa Allah, Balak ɗan Zippor, sarkin Mowab, ya aiko su gare ni. Ya ce,
\v 11 'Duba, mutanen da suka zo daga Masar suka cika fuskar ƙasata. Yanzu zo ka la'anta su domi na. Watakila zan iya faɗa da su, har in kore su.'"
\s5
\v 12 Allah ya amsa wa Balaam, "Ba za ka tafi tare da mutanen ba, ba kuwa za ka la'anta mutanen Isra'ila ba domin masu albarka ne."
\v 13 Balaam ya tashi da safe ya yi magana da shugabannin Balak, "Ku koma ƙasarku gama Yahweh ya hana ni in tafi tare da ku."
\v 14 Shugabannin Mowab suka koma wurin Balak. Suka ce, "Balaam ya ƙi ya taho tare da mu."
\s5
\v 15 Sai Balak ya sake aiken shugabannin, kuma masu yawa masu daraja fiye dana fari.
\v 16 Suka zo wurin Balaam suka ce da shi, "Balak ɗan Zippor ya faɗi wannan, 'Idan ka yarda kada ka bar wani ya hana ka zuwa gare ni,
\v 17 gama zan biya ka sosai, za a ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mani in yi, zan yi. Ka zo ka la'anta wannan jama'a domi na.'"
\s5
\v 18 Balaam ya amsa, yacewa mutanen Balak, "Ko da a ce Balak zai bani fadarsa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Yahweh, Allahna ba, ba zan ƙara wani abu ko in rage ba sai dai abin da ya faɗa mani.
\v 19 Amma yanzu, ina rokonku ku kwana a nan, har in san abin da Yahweh zai sake faɗa mani."
\v 20 Allah ya zo wurin Balaam da dare, ya ce masa, "Tun da mutanen nan sun zo kiran ka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin dana umarce ka kaɗai za ka yi."
\s5
\v 21 Balaam ya tashi da safe, ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da shugabannin Mowab.
\v 22 Amma saboda ya tafi, fushin Allah ya yi zafi. Mala'ikan Yahweh ya tsaya a hanya kamar wani ya tarye Balaam, wanda ya ke bisa jakarsa. Barorin Balaam biyu na tare da shi.
\v 23 Jakar kuwa ta ga mala'ikan Yahweh na tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa. Sai jakar ta kauce daga hanya ta shiga saura. Balaam ya bugi jakar don ta juyo a kan hanyar.
\s5
\v 24 Sai mala'ikan Yahweh ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi, bango a gefen damarsa da bango gefen hagunsa.
\v 25 Jakar ta ga mala'ikan Yahweh kuma. Sai ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Balaam ga bangon. Balaam ya sake bugunta.
\s5
\v 26 Mala'ikan Yahweh kuma ya sha kanta ya tsaya a ƙuntataccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.
\v 27 Jakar ta ga mala'ikan Yahweh, sai ta kwanta a ƙafafun Balaam. Sai Balaam ya husata ya bugi jakar da sandarsa.
\s5
\v 28 Sa'an nan Yahweh ya buɗe bakin jakar har ta yi magana. Ta ce da Balaam, "Me nayi maka da ka buge ni har sau uku?"
\v 29 Balaam ya amsa wa jakar, "Domin kin shashantar da ni. Dama a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki."
\v 30 Jakar ta ce wa Balaam, "Ba ni ce jakarka ba wadda kake ta hawa dukkan lokacin rayuwarka har zuwa wannan ranar ba? Na taɓa yi maka haka? Balaam ya ce, "A'a."
\s5
\v 31 Sa'an nan Yahweh ya buɗe idanun Balaam, ya ga mala'ikan Yahweh na tsaye a hanya da takobi zare a hanunsa. Balaam ya sunkuyar da kansa, ya faɗi rubda ciki.
\v 32 Mala'ikan Yahweh yace da shi, "Meyasa ka bugi jakarka har sau uku? Duba, na fito ne kamar wani abokin gãba don ayyukanka a wuri na mugunta ne.
\v 33 Jakar ta gan ni, ta kauce mani har sau uku. Da a ce bata kauce mani ba, lallai da na kashe ka, in bar ta da rai."
\s5
\v 34 Balaam ya cewa mala'ikan Yahweh, "Na yi zunubi. Ban san ka tsaya gãba da ni a hanya ba. To yanzu, idan ka ga mugun abu ne, sai in koma."
\v 35 Amma mala'ikan Yahweh ya cewa Balaam, "Tafi tare da mutanen. Amma abin da na faɗa maka shi kaɗai zaka faɗa." Sai Balaam ya tafi tare da shugabannin Balak.
\s5
\v 36 Sa'ad da Balak ya ji Balaam ya zo, ya fita ya tarye shi a birnin Mowab a Arnon, wadda ke kan iyaka.
\v 37 Balak yace wa Balaam, "Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Meyasa baka zo wurina ba? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?"
\s5
\v 38 Sai Balaam ya amsa wa Balak yace, "Ga shi, na zo gare ka. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Zan iya faɗin maganar da Allah ya sa a bakina ne kawai."
\v 39 Balaam ya tafi tare da Balak, suka je Kiriyat Huzot.
\v 40 Sai Balak ya yi hadaya da sã da tunkiya ya aika wa Balaam da shugabannin da ke tare da shi.
\s5
\v 41 Washegari, Balak ya ɗauki Balaam ya kai shi kan tudu wurin Ba'al. Daga wurin Balaam ya ga wasu daga mutanen Isra'ilawa a zangonsu.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Balaam ya cewa Balak, "Ka gina mani bagadai guda bakwai a nan, ka shirya bijimai bakwai da raguna bakwai."
\v 2 Balak ya yi yadda Balaam ya bukace shi ya yi. Sai Balak da Balaam suka miƙa bijimi da rago a kan dukkan bagadan.
\v 3 Balaam yace da Balak, "Tsaya kusa da bayarwar ƙonawa, ni kuwa zan tafi can. Watakila Yahweh zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mani zan faɗa maka." Ya kuwa tafi wani fako a kan tudu wurin da ba itatuwa.
\s5
\v 4 A lokacin da yake a kan tudu, Allah ya sadu da shi, Balaam yace da shi, "Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimai guda da rago guda a kan kowanne bagadi."
\v 5 Yahweh ya sa magana a bakin Balaam yace, "Koma wurin Balak, ka yi magana da shi."
\v 6 Sai ya koma wurin Balak, wanda ke tsaye kusa da hadayar ƙonawarsa, da dukkan shugabannin Mowab tare da shi.
\s5
\v 7 Balaam kuwa ya fara maganarsa ta annabci ya ce, "Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab daga duwatsun gabas. 'Zo, la'anta Yakubu domi na,' ya ce, 'Zo, ka tsine wa Isra'ila.'
\v 8 Ƙaƙa zan iya la'anta waɗanda Allah bai la'antar ba? Ƙaƙa zan iya tsine wa waɗanda Yahweh bai tsine wa ba?
\s5
\v 9 Gama daga kan duwatsu na gan shi, daga bisa kan tuddai na hange shi. Duba, akwai mutane waɗanda ke zama su kaɗai, ba su ɗauki kansu a bakin kome ba a cikin jama'a.
\s5
\v 10 Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yakubu ko ya iya yin lissafin ɗaya bisa hudu na Isra'ila? Ka sa in mutu mutuwar adalin mutum, ka sa in mutu cikin salama kamar irin mutuwarsa."
\s5
\v 11 Balak ya cewa Balaam, "Me kenan ka yi mani? Na kawo ka ka la'anta abokan gãbana amma ga shi sai albarka kake sa masu."
\v 12 Balaam ya amsa ya ce, "Ba zan yi hankali da abin da zan ce abin da Yahweh ya sa a bakina ba?
\s5
\v 13 Balak yace da shi, "Idan ka yarda zo tare da ni zuwa wani wuri inda za ka gan su. Za ka gansu a kurkusa, ba dukkansu ba. A can sai ka la'anta su domi na."
\v 14 Ya kuwa ɗauki Balaam a cikin filin Zofim, a bisa Dutsen Fisga, ya gina bagadai bakwai. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowanne bagadi.
\v 15 Sai Balaam yace da Balak, "Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Yahweh a can.
\s5
\v 16 Yahweh kuwa ya sadu da Balaam, ya sa masa magana a bakinsa. Ya ce, "Koma wurin Balak ka faɗa masa maganata."
\v 17 Balaam ya koma wurinsa, ga shi a tsaye kusa da bayarwarsa ta ƙonawa, shugabannin Mowab na tare da shi. Balak yace da shi, "Me Yahweh ya ce?"
\v 18 Balaam ya fara annabcinsa. Ya ce, "Tashi, Balak, ka ji. Ka saurare ni, ya ɗan Ziffor.
\s5
\v 19 Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, ko kuwa mutum ne, da zai canza tunaninsa. Ya yi wani alƙawarin da bai cika shi ba? Ko ya ce zai yi wani abu kuma bai yi shi ba?
\v 20 Duba, an umarce ni in sa albarka. Allah ya bada albarka, ba zan iya janye ta ba.
\s5
\v 21 Ya ga babu mugunta a Yakubu ko wahala a Isra'ila. Yahweh Allahnsu na tare da su, suna sowa domin sarkinsu na cikinsu.
\v 22 Allah ne ya fishe su daga Masar da ƙarfi kamar kutunkun ɓauna.
\s5
\v 23 Babu wata maitar da zata cuci Yakubu, ba sihirin da zai cuci Isra'ila. Maimakon haka dole ace da, Yakubu da Isra'ila, 'Duba abin da Allah ya yi!'
\s5
\v 24 Duba, mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfan zaki, yadda zai fito ya hallakar. Ba ya kwantawa har sai ya cinye ganimarsa, ya lashe jinin abin da ya kashe."
\s5
\v 25 Sai Balak ya cewa Balaam, "Kada ka la'anta su ko ka albarka ce su dukka."
\v 26 Amma Balaam ya amsa ya ce da Balak, "Ban faɗa maka ba, zan faɗi dukkan abin da Yahweh ya ce da ni shi zan ce?"
\v 27 Balak ya amsa wa Balaam, "Ka zo yanzu, zan ɗauke ka zuwa wani wuri. Watakila Allah zai yarda ka la'anta su a can domi na."
\s5
\v 28 Balak kuwa ya kai Balaam a ƙwanƙolin Dutsen Feyor, wanda ke fuskantar hamada.
\v 29 Balaam yace da Balak, "Gina mani bagadai bakwai a nan ka shirya bijimai bakwai da raguna bakwai."
\v 30 Balak ya yi yadda Balaam ya ce ya yi; ya miƙa hadayar bijimi da rago a kan kowanne bagadi.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Da Balaam ya ga Yahweh ya ji daɗin da aka sawa Isra'ila albarka, bai tafi ba, kamar waɗancan lokutan, don ya yi aiki da tsafi. Maimakon haka, sai ya duba wajen jeji.
\s5
\v 2 Ya tada idanunsa, ya ga Isra'ila sun yi zango, kowa a cikin kabilarsu, Ruhun Allah ya sauko masa.
\v 3 Ya karɓi wannan annabci, ya ce, "Balaam ɗan Beyor ne ke magana, mutumin da idanuwansa a buɗe suke.
\s5
\v 4 Ya faɗa, an ji maganar Allah. Ya ga wahayi daga wurin Maɗaukaki. A gaban wanda ke durƙushe tare da idanuwansa a buɗe.
\v 5 Yaya kyan alfarwarka, Yakubu, a wurin da ka zauna, Isra'ila!
\s5
\v 6 Kamar kwarurruka suka bazo, kamar gonaki a gefen kogi, kamar itatuwan aloyes da Yahweh ya dasa, kamar itatuwan al'ul a gefen ruwaye.
\s5
\v 7 Ruwa na malalowa daga bokatansu, iri ya jiƙu sosai. Sarkinsu zai fi Agag girma, za a ɗaukaka mulkinsu.
\s5
\v 8 Allah ne ya fisshe su daga Masar da iko kamar kutunkun ɓauna. Zai cinye al'ummai waɗanda suka yi faɗa gãba da shi. Zai kakkarya ƙasusuwansu gutsu gutsu. Zai harbe su da kibiyoyinsa.
\s5
\v 9 Zai laɓe a ƙasa kamar zaki, kamar zakanya. Ba bu wanda zai dame shi? Bari duk wanda ya albarka ce shi ya yi albarka; duk wanda ya la'anta shi ya zama la'ananne."
\s5
\v 10 Balak ya husata da Balaam, ya tafa hannunsa a cikin fushi. Balak yace da Balaam, "Na kirawo ka ka la'anta maƙiyana, amma ga shi har sau uku kana sa masu albarka.
\v 11 Yanzu sai ka tafi gidanka. Na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi Yahweh ya hana ka samun wani lada."
\s5
\v 12 Sai Balaam ya amsa wa Balak, "Na faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni.
\v 13 Idan Balak ya ba ni fadarsa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Yahweh ba, da wani mugun abu ko mai kyau ne, kai kowanne irin abu ne zan so in yi. Zan faɗi abin da Yahweh ya faɗa mani shi zan ce.' Ban faɗa masu haka ba?
\v 14 Saboda haka yanzu, ga shi, zan koma ga mutanena. Amma da farko bari in gargaɗe ka abin da waɗannan mutane za su yiwa mutanenka a ranaku masu zuwa."
\s5
\v 15 Balaam ya fara wannan annabci. Ya ce, "Balaam ɗan Beyor ya faɗa, mutumin da idanunsa ke buɗe.
\v 16 Wannan shi ne annabcin wanda yake jin magana daga Allah, wanda ke da ilimi daga wurin Maɗaukaki, wanda ke da wahayi daga Mai Iko Dukka, A gaban wanda yake durƙurshe tare da idannunsa a buɗe.
\s5
\v 17 Na gan shi, amma baya nan yanzu. Ina hangensa, amma baya kusa. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, kendir zai fito daga cikin Isra'ila. Za ya ragargaje shugabannin Mowab ya hallaka dukkan zuriyar Shitu.
\s5
\v 18 Sai Idom ta zama mallakar Isra'ila, Seyir kuma za ta zama mallakarsu, abokan gãbar Isra'ila, waɗanda Isra'ila zasu ci da ƙarfi.
\v 19 Daga cikin Yakubu sarki zai zo wanda zai yi mulki, zai hallaka waɗanda suka ragu a birninsu."
\s5
\v 20 Sai Balaam ya dubi Amalek ya fara annabcinsa. Ya ce, "Amalek mafi girma ne cikin al'ummai, amma ƙarshensa zai kasance hallaka."
\s5
\v 21 Sai Balaam ya duba zuwa wajen Kan'aniyawa, ya fara annabcinsa. Ya ce, "Wurin da kuke zama mai ƙarko ne, gidajenku kuma na cikin duwatsu.
\v 22 Duk da haka ku Kan'aniyawa za a lalatar da ku da wuta idan Asiriyawa suka ɗauke ku bayi."
\s5
\v 23 Sai Balaam ya fara annabcinsa na ƙarshe. Ya ce, "Kaito! Wa zai rayu sa'ad da Allah ya yi wannan
\v 24 Jiragen ruwa kuwa za su zo daga gaɓar tekun Kittim; za su faɗawa Asiriya, zasu ci Eber, amma kuma, ƙarshensu hallaka ce."
\s5
\v 25 Sai Balaam ya tashi ya tafi. Ya koma gidansa, Balak ma yayi tafiyarsa.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Isra'ila ta zauna a Shittim, maza suka fara yin karuwancinsu da matan Mowab,
\v 2 domin Mowabawa sun gayyaci mutane zuwa wajen hadayar allolinsu. Saboda haka mutane suka ci suka durƙusa wa allolin Mowabawa.
\v 3 Mutanen Isra'ila suka shiga bautawa gumakun Ba'al na Feyor, Yahweh ya yi fushi da Isra'ila.
\s5
\v 4 Yahweh yace da Musa, "Kashe dukkan shugabannin mutanen, ka rataye su a gabana a nuna su a fili, don in huce daga fushi da nake yi da Isra'ila."
\v 5 Musa kuwa ya cewa shugabanin Isra'ila, "Kowannen ku dole ya kashe mutanensa waɗanda suka shiga bautar gumakun Ba'al Feyor."
\s5
\v 6 Sai ɗaya daga cikin mutanen Isra'ila ya zo, ya kawo mace Bamidiyaniya cikin iyalinsa. Wannan ya faru ne a idannun Musa da dukkan jama'ar mutanen Isra'ila, a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwar taro.
\v 7 Finehas ɗan Eliyeza ɗan Haruna firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin jama'a, ya ɗauki mãshi a hannunsa.
\s5
\v 8 Ya bi Ba'isra'ilen cikin alfarwa, ya soke dukkansu biyu, Ba'isra'ilen da macen. Da haka aka tsaida annobar da Allah ya aiko wa mutanen Isra'ila.
\v 9 Waɗanda suka mutu saboda annobar sun kai jimilar mutane dubu ashirin da hudu.
\s5
\v 10 Yahweh ya faɗa wa Musa ya ce,
\v 11 "Finehas ɗan Eliyeza ɗan Haruna firist, ya kawar da fushina daga mutanen Isra'ila gama yayi kishi irin nawa a cikinsu. Saboda haka ba zan hallakar da mutanen Isra'ila da fushina ba.
\s5
\v 12 Saboda haka ne, 'Yahweh ya faɗa, "Duba, ina ba Finehas alƙawarin salamata.
\v 13 Dominsa da zuriyarsa zasu bi shi, alƙawarin da ba zai taɓa ƙarewa ba daga firistoci gama yana da kishi domin, Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin mutanen Isra'ila.'"'
\s5
\v 14 Yanzu sunan Ba'isra'ilen da aka kashe tare da Bamidiyar, Zimri ɗan Salu, shugaban zuriyar iyalin Simiyonawa.
\v 15 Sunan Bamidiyar wanda aka kashe, ita ce Kozbi 'ɗiyar Zur, wanda yake shi ne shugaban wata kabila na iyalin Midiyan.
\s5
\v 16 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 17 "Ku fãɗa wa Midiyanawa abokan gãbarku, ku hallaka su,
\v 18 gama sun yi maku kamar abokan gãbanku da makircinsu. Sun kai ku cikin mugun abu a kan Feyor da na Kozbi 'yar'uwarsu, ɗiyar shugaban Midiyan, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor."
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Ya zamana bayan annobar sai Yahweh ya yi magana da Musa da Eliyeza ɗan Haruna firist. Ya ce,
\v 2 "Ku ƙidaya dukkan taron mutanen Isra'ila, daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, bisa ga zuriyar kakanninsu, da dukkan waɗanda za su iya zuwa yaƙi domin Isra'ila."
\s5
\v 3 Musa da Eliyeza firist suka yi masu magana a filayen Mowab daura da Yodan a Yeriko, suka ce,
\v 4 "A ƙidaya mutane daga mai shekaru ashirin zuwa gaba kamar yadda Yahweh ya umarci Musa da mutanen Isra'ila, waɗanda suka fito daga ƙasar Masar."
\s5
\v 5 Ruben shi ne ɗan fari na Isra'ila. Daga ɗansa Hanok kabilar Hanokiyawa ta zo. Daga Fallu kabilar Falluniyawa ta zo.
\v 6 Daga Hesruna har zuwa kabilar Hezaroniyawa. Daga Karmi har zuwa kabilar Karmiyawa.
\v 7 Waɗannan su ne kabilun Ruben, waɗannan yawansu ya kai jimilar mutane 43,730.
\s5
\v 8 Eliyab shi ne ɗan Fallu.
\v 9 'Ya'yan Eliyab su ne Nemuwel da Datan da Abiram. Waɗannan su ne Datan da Abiram waɗanda suka bi Korah a lokacin da suka yi wa Musa da Haruna ƙalubale, suka kuma yi tawaye ga Yahweh.
\s5
\v 10 Ƙasa kuwa ta buɗe bakinta ta haɗiye su tare da Kora da dukkan mabiyansa suka mutu. A wancan lokaci, wuta kuma ta cinye mutane 250, waɗanda suka zama abin faɗakarwa.
\v 11 Amma iyalin Kora ba su mutu ba.
\s5
\v 12 Kabilar zuriyar Simiyon su ne waɗannan: Ta wurin Nemuwel, aka sami kabilar Nemuwelawa, ta wurin Yamin, kabilar Yaminawa, ta wurin Yakin, kabilar Yakinawa,
\v 13 ta wurin Zera, kabilar Zerawa, ta wurin Shawul, kabilar Shawulawa.
\v 14 Waɗannan su ne kabilun zuriyar Simiyon, waɗanda aka ƙidaya jimilar mutane 22,200.
\s5
\v 15 Kabilar zuriyar Gad su ne waɗannan: Ta wurin Zifon, aka sami kabilar Zifonawa, ta wurin Haggi, kabilar Haggiyawa, ta wurin Shuni, kabilar Shuniyawa
\v 16 ta wurin Ozni, kabilar Oziniyawa, ta wurin Eri, kabilar Eritiyawa,
\v 17 ta wurin Arod kabilar Arodiyawa, ta wurin Areli, aka sami kabilar Areliyawa.
\v 18 Waɗannan su ne kabilar zuriyar Gad sun kai jimilar mutane 40,500.
\s5
\v 19 'Ya'yan Yahuda su ne Er da Onan, amma waɗannan mutane sun rasu a ƙasar Kan'ana.
\v 20 Sauran kabilar zuriyar Yahuda su ne: ta wurin Shela, kabilar Shelatawa, ta wurin Feresa, kabilar Feresawa, da ta wurin Zera, kabilar Zerawa.
\v 21 Zuriyar Ferez su ne: Ta wurin Hezron, kabilar Hezronawa, ta wurin Hamul, kabilar Hamulawa.
\v 22 Waɗannan su ne zuriyar kabilar Yahuda sun kai jimilar mutane 76,500.
\s5
\v 23 Kabilar zuriyar Issaka su ne: Ta wurin Tola, kabilar Tolawa, ta wurin Fuwa, kabilar Fuwayawa,
\v 24 ta wurin Yashub, kabilar Yashubawa, ta wurin Shimron, kabilar Shimronawa.
\v 25 Waɗannan su ne kabilun Issaka, waɗanda sun kai jimilar mutane 64,300.
\s5
\v 26 Zuriyar kabilar Zebulun su ne waɗannan: Ta wurin Sered, kabilar Seredawa, ta wurin Elon, kabilar Elonawa, ta wurin Yaleyel, kabilar Yaleyawa.
\v 27 Waɗannan su ne kabilun Zebulun, sun kai jimilar mutane 60,500.
\s5
\v 28 Zuriyar kabilar Yosef su ne Manasse da Ifraim.
\v 29 Zuriyar Manasse su ne waɗannan: ta wurin Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Giliyad), ta wurin Giliyad, kabilar Gilidiyawa.
\s5
\v 30 Zuriyar Giliyad su ne waɗannan: Ta wurin Leza, kabilar Lezawa, ta wurin Helek, kabilar Helekawa,
\v 31 ta wurin Asriyel, kabilar Asrilawa,
\v 32 ta wurin Shekem, kabilar Shekemawa, ta wurin Shemida, kabilar Shemidawa, ta wurin Hefer, kabilar Heferawa.
\s5
\v 33 Zelofehad ɗan Hefer ba shi da 'ya'ya maza, amma sai 'ya'ya mata kaɗai. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka daTirza.
\v 34 Waɗannan su ne kabilar Manasse, sun kai jimilar mutane 52,700.
\s5
\v 35 Zuriyar kabilar Ifraim su ne waɗannan: Ta wurin Shutela, kabilar Shutelawa, ta wurin Beker, kabilar Bekerawa, ta wurin Tahat, kabilar Tahatawa.
\v 36 Zuriyar Shutela su ne, ta wurin Eran, kabilar Eraniyawa.
\v 37 Waɗannan su ne zuriyar kabilar Ifraim, sun kai jimilar mutane 32,500. Waɗannan su ne zuriyar Yosef an lissafta kowanne bisa ga kabilunsu.
\s5
\v 38 Zuriyar kabilar Benyamin su ne waɗannan: Ta wurin Bela, kabilar Belayawa, ta wurin Ashbel, kabilar Ashbelawa, ta wurin Ahiram, kabilar Ahiramawa,
\v 39 ta wurin Shefufam, kabilar Shefufamawa, ta wurin Hufam, kabilar Hufamawa.
\v 40 'Ya'yan Bela maza su ne Ard da Na'aman. Daga Ard aka sami kabilar Ardawa, daga Na'aman aka sami kabilar Na'amawa.
\v 41 Waɗannan su ne zuriyar Benyamin. Yawan mutane 45,600 ne.
\s5
\v 42 Zuriyar kabilar Dan su ne, ta wurin Shuham, aka sami kabilar Shuhamawa. Waɗannan su ne zuriyar kabilun Dan.
\v 43 Dukkan kabilun Shuhamawa sun kai yawan mutane 64,400.
\s5
\v 44 Zuriyar kabilar Asha su ne waɗannan: Ta wurin Imna, kabilar Imnawa, ta wurin Ishbi, kabilar Ishabawa, ta wurin Beriya, kabilar Beriyawa.
\v 45 Zuriyar Beriya su ne waɗannan: Ta wurin Hebar, kabilar Hebarawa, ta wurin Malkiyel, kabilar Malkiyawa.
\v 46 Sunan 'yar Asha Sera.
\v 47 Waɗannan su ne zuriyar kabilun Asha, sun kai jimilar mutane 53,400.
\s5
\v 48 Zuriyar kabilar Naftali su ne waɗannan: Ta wurin Yazeyel, kabilar Yazelawa, ta wurin Guni, kabilar Guniyawa,
\v 49 ta wurin Yezer, kabilar Yezerawa, ta wurin Shilem, kabilar Shilemawa.
\v 50 Waɗannan su ne zuriyar kabilun Naftali sun kai jimilar mutane 45,400.
\s5
\v 51 Wannan shi ne cikakken lissafin maza a cikin mutanen Isra'ila: 601,730.
\s5
\v 52 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 53 "Dole a raba ƙasar ga waɗannan mutane gãdo bisa ga yawan sunayensu.
\s5
\v 54 Za ka ba babbar kabila babban rabon gãdo, ka ba karamar kabila karamin rabon gãdo. Kowacce kabila za a ba ta gãdo bisa ga yawan mutanenta da aka lissafta.
\v 55 Amma za a rarraba ƙasar ta wurin kuri'a. Za su gaji ƙasar yadda aka raba a tsakanin kabilun kakanninsu.
\v 56 Za a rarraba gãdo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a."
\s5
\v 57 Kabilar Lebiyawa da aka ƙidaya bisa kabila kabila, su ne waɗannan: Ta wurin Gershon, kabilar Gershawa, ta wurin Kohat, kabilar Kohatiyawa, ta wurin Merari, kabilar Merariyawa.
\v 58 Kabilar Lebi su ne waɗannan: kabilar Lebiyawa da kabilar Hebroniyawa da kabilar Maliyawa da kabilar Mushiyawa da kabilar Koriyawa. Kohat shi ne kakan Amram.
\v 59 Sunan matar Amram ita ce Yokabed, zuriyar Lebi, wanda ya haifi Lebiyawa a Masar. Ta haifa wa Amram 'ya'yansu, su ne Haruna da Musa da Miriyam 'yar uwarsu.
\s5
\v 60 Haruna ya haifi Nadab da Abihu, Eliyeza da Itamar.
\v 61 Nadab da Abihu sun rasu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Yahweh.
\v 62 Mazan da aka ƙidaya daga cikinsu sun kai dubu ashirin da uku, dukkansu maza daga wata ɗaya zuwa sama. Amma ba a ƙidaya su ba cikin zuriyar Isra'ila domin ba a ba su gãdo a cikin mutanen Isra'ila ba.
\s5
\v 63 Waɗannan su ne waɗanda Musa da Eliyeza firist suka ƙidaya. Suka ƙidaya mutanen Isra'ila a kwarin Mowab Yodan a Yeriko.
\v 64 Gama a cikin waɗannan babu mutum wanda Musa da Haruna firist ba su ƙidaya ba a zuriyar Isra'ila da aka ƙidaya a jeji Sinai.
\s5
\v 65 Gama Yahweh ya ce da dukkan waɗannan mutane lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne da Yoshuwa ɗan Nun.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Sai Musa ya zo wurin 'ya'ya mata na Zelofehad ɗan Hefer ɗan Giliyad ɗan Makir ɗan Manasse, kabilar Manasse ɗan Yosef. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yansa mata: Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.
\s5
\v 2 Suka tsaya a gaban Musa da Eliyeza firist, da shugabanni, da dukkan jama'a a ƙofar shiga rumfar taro. Suka ce,
\v 3 "Mahaifinmu ya rasu a cikin jeji. Ba ya cikin waɗanda suka tayar wa Yahweh a ƙungiyar Kora. Ya mutu saboda alhakin zunubinsa, ga shi ba shi da 'ya'ya maza.
\s5
\v 4 Donme za a cire sunan mahaifinmu daga cikin kabilar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? Ka ba mu gãdo tare da 'yan'uwan mahaifinmu"
\v 5 Musa ya kai maganarsu a gaban Yahweh.
\s5
\v 6 Yahweh ya yi magana da Musa, ya ce,
\v 7 "Ya'ya mata na Zelofehad suna magana dai dai. Ka ba su ƙasa a matsayin gãdo a cikin 'yan'uwansu, za ka tabbatar sun sami gãdon mahaifinsu.
\v 8 Ka yi magana da mutanen Isra'ila, ka ce, 'Idan mutum ya rasu, ba shi da ɗa, sai ka sa gãdon mahaifinsa ya koma kan 'yarsa.
\s5
\v 9 Idan ba shi da 'ya, sai ka bada gãdon ga 'yan'uwansa.
\v 10 Idan kuma ba shi da 'yan'uwa maza, sai ka bada gãdonsa ga 'yan'uwan mahaifinsa maza.
\v 11 Idan kuwa ba shi da 'yan'uwa maza, sai ka bada gãdonsa ga 'yan'uwansa na kusa a kabilarsa, zai ɗauke ta don kansa. Wannan ita ce doka da aka tabbatar da ka'ida saboda mutanen Isra'ila, kamar yadda Yahweh ya umarce ni.'"
\s5
\v 12 Yahweh yace da Musa, "Tafi bisa duwatsun Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba mutanen Isra'ila.
\v 13 Bayan daka ganta, kai ma, za a tara ka ga mutanenka, kamar Haruna ɗan'uwanka.
\v 14 Wannan zai kasance domin ku biyun kun yi tawaye akan umarnina cikin jejin Zin. A can, lokacin da ruwa ke kwararowa daga dutse, a cikin fushi baku girmama ni kamar mai tsarki a gaban idannun dukkan jama'a ba." Waɗannan su ne ruwayen Meriba dana Kadesh a jejin Zin.
\s5
\v 15 Sai Musa ya yi magana da Yahweh, ya ce,
\v 16 "Bari kai, Yahweh, Allah na ruhohin dukkan 'yan adam, ya naɗa mutum bisa kan jama'a,
\v 17 mutum wanda zai tafi, ya dawo a gabansu, ya shugabance su ya fita, ya dawo, saboda jama'arka ba kamar tumakin da ba makiyayi suke ba."
\s5
\v 18 Yahweh yace da Musa, "Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutum wanda Ruhuna yake raye a cikinsa, ka sa hannunka a kansa.
\v 19 Sa shi a gaban Eliyeza firist da gaban dukkan jama'a, ka umarce shi a gaban idanunsu ya shugabance su.
\s5
\v 20 Ka danka masa ikonka a kansa, don dukkan jama'ar mutanen Isa'ila su yi masa biyayya.
\v 21 Zai wuce gaban Eliyeza firist ya nemi nufina domin sa, ta wurin yanke shawarar Urim. Zai zama bisa ga umarninsa da mutane za su tafi waje su kuma komo ciki, shi da dukkan mutanen Isra'ila tare da shi, da kuma dukkan jama'a."
\s5
\v 22 Sai Musa ya yi kamar yadda Yahweh ya umarce shi. Ya ɗauki Yoshuwa ya sa shi a gaban Ele'yazar firist da dukkan jama'a.
\v 23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya umarce shi ya yi shugabanci, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila, ka ce da su, 'Za ku miƙa hadaya gare ni a ayyanannun lokatai, ta abincin baye-baye na ta wurin wuta mai daɗin ƙanshi domi na.'
\s5
\v 3 Ka kuma ce da su, 'Wannan bayarwa da za a yi da wuta, za ku bayar ga Yahweh--ɗan tunkiya shekara ɗaya wanda babu lahani a gare shi, guda biyu kowacce rana, matsayin bayarwar ƙonawa.
\v 4 Dan tunkiya ɗaya za ku bayar da safe, ɗaya kuma da maraice.
\v 5 Za ku bayar da mudun lallausan garin filawa matsayin bayarwar hatsi, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa.
\s5
\v 6 Wannan zata zama ta bayarwar ƙonawa da za ku riƙa yi yadda an umarta a Tsaunin Sinai baiko mai daɗin ƙanshi, da aka yi da wuta ga Yahweh.
\v 7 Bayarwar sha zata zama ɗaya bisa huɗu na moɗa don ɗaya ɗan rago. Za a kwarara a wuri mai tsarki baiko na sha mai ƙarfi ga Yahweh.
\v 8 Ɗaya ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice tare da baiko na gari kamar baiko na safe. Dole ne kuma a miƙa wani na sha tare da shi, baikon ƙonawa da wuta, mai daɗin ƙamshi ga Yahweh.
\s5
\v 9 A ranar Asabaci kuwa za a miƙa 'ya'yan raguna biyu kowanne bana ɗaya marasa lahani, da mudu biyu na lallausan gari a matsayin baiko, kwaɓaɓɓe da mai, da baiko na sha tare da shi.
\v 10 Wannan shi ne baikon ƙonawa domin kowacce Asabaci, a kan kowanne baiko na ƙonawa da baiko na sha tare da shi.
\s5
\v 11 A farkon kowanne wata, za a miƙa baikon ƙonawa ga Yahweh. Za a miƙa 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya da kuma 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya, marasa lahani.
\v 12 Za a kuma miƙa kwaɓaɓɓen gari kashi uku bisa ɗaya na garwa da man zaitun don kowanne bijimi, da gari kashi biyu bisa goma na garwa don rago ɗaya.
\v 13 Za a kuma miƙa humushin lallausan gari za a haɗa shi da mai kamar baikon hatsi don kowanne rago. Wannan zai zama baikon ƙonawa, domin ya bayar da ƙamshi mai daɗi, baiko da aka yi da wuta ga Yahweh.
\s5
\v 14 Baiko na sha na mutane dole ya zama rabin moɗa na ruwan inabi don bijimi, da ɗaya bisa uku na moɗa don rago da ɗaya bisa huɗu na moɗa don ɗan rago. Wannan shi ne baiko na ƙonawa a kowanne wata a dukkan watannin shekara.
\v 15 Dole kuma a miƙa bunsuru ɗaya a matsayin baiko na zunubi ga Yahweh. Wannan zai zama ƙarin baiko na ƙonawa da baiko na sha da za a riƙa yi da su.
\s5
\v 16 A cikin wata na farko, a rana ta goma sha huɗu ga watan, idin Ƙetarewa ga Yahweh.
\v 17 A kan rana ta goma sha biyar ga wannan watan kuwa za a yi idi. Gama kwanaki bakwai na cin abinci mara gami ne.
\v 18 A rana ta fari, za ku yi tsarkakakken taron girmama Yahweh. Ba za ku yi aikin da kuka saba yi a ranar ba.
\s5
\v 19 Duk da haka, dole ku miƙa baiko da aka yi da wuta, a baiko na ƙonawa ga Yahweh. Dole ku miƙa 'yan bijimai biyu da rago ɗaya, da 'yan tumaki bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani.
\v 20 Tare da bijimi, za ku miƙa lallausan gari kashi uku na garwa wanda aka kwaɓa da mai tare da rago, kashi biyu bisa uku.
\v 21 Tare da kowanne 'yan raguna bakwai, za ku miƙa lallausan gari haɗe da mai,
\v 22 da ɗan akuya ɗaya a matsayin baikon zunubin ƙafara domin kanku.
\s5
\v 23 Dole ku miƙa waɗannan a kan bayarwar ƙonawa da kuke miƙawa kowacce safiya.
\v 24 Kamar yadda aka nuna a nan, za ku miƙa waɗannan hadayu kullum, saboda ranaku bakwai na Idin Ƙetarewa, za ku yi baikon abincin da aka yi da wuta mai daɗin kamshi ga Yahweh. Za a miƙa a kan bayarwar ƙonawa da kuke yi da baiko na sha.
\v 25 A rana ta bakwai za ku yi tsattsarkan taro na girmama Yahweh, ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba a ranar.
\s5
\v 26 Haka nan a ranar nunar fari, da kuke miƙa baikon sabon hatsi ga Yahweh a Bikin Makonni, za ku yi tsattsarkan taro na girmama Yahweh, ba za ku yi aikin da kun saba yi ba a ranar.
\v 27 Dole ne ku miƙa baikon ƙonawa mai dadin ƙamshi ga Yahweh. Dole ne ku miƙa 'yan bijimai biyu da rago ɗaya da 'yan tumakai maza guda bakwai bana ɗaya ɗaya.
\v 28 Kuma ku miƙa baikon gari tare da su: gari haɗe da mai, gari kashi uku bisa uku da aka haɗa da mai domin kowanne bijimi da kashi biyu don rago ɗaya.
\s5
\v 29 Ku miƙa kashi goma na garwa da aka haɗa da mai don kowanne 'yan raguna bakwai,
\v 30 da ɗan akuya na ƙafara domin kanku.
\v 31 Idan kuka miƙa waɗannan dabobbin marasa lahani, tare da baye bayenku na sha, wannan zai zama a kan baye-bayen ƙonawa, da hatsi da kuke bayarwa tare su.'"
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 A cikin wata na bakwai, a rana ta farko ta watan, za ku yi taro mai tsarki na girmama Yahweh. Tilas ba za ku yi wani aikin da aka saba a koda yaushe ba a wannan rana. Dole ne ta zama ranar da za ku busa ƙahonni.
\s5
\v 2 Za ku miƙa ƙonannen baiko domin abin daɗi da ƙamshi ga Yahweh. Dole ku miƙa ɗan bijimi, rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai masu shekara ɗaya, mara aibi.
\s5
\v 3 Dole ne ku miƙa su tare da baikonsu na hatsi, gari mai laushi cuɗaɗɗe da mai, uku cikin goma na efa domin bijimi, biyu cikin goma domin ragon,
\v 4 ɗaya cikin goma kuma domin kowanne cikin raguna bakwai.
\v 5 Dole ne ku miƙa bunsuru ɗaya domin baiko na zunubi don a yi maku kafara.
\s5
\v 6 A miƙa waɗannan baye-baye a cikin wata na bakwai a bisa kan sauran dukkan baye-bayen da za ku bayar a ranar farko ta kowanne wata: ƙonannen baiko na musamman da kuma baiko na hatsi a haɗa da shi. Waɗannan dole za a miƙa su zama ƙãri bisa ga ƙonannen baikon da aka sãba, baiko hatsin, da kuma baye-bayensa na sha. Sa'ad da kuka miƙa waɗannan baye-bayen, za ku yi biyayya da abin da aka umurtar don ya bãda ƙamshi mai daɗi, baiko na wurin wuta ga Yahweh.
\s5
\v 7 A rana ta goma ga watan bakwai za ku yi taro mai tsarki don girmama Yahweh. Dole ku ƙasƙantar da kanku ba za ku yi wani aiki ba.
\v 8 Dole ku miƙa baiko na ƙonawa mai bãda ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Dole ku miƙa ɗan bijimi ɗaya, da ɗan rago ɗaya, da kuma 'yan raguna 'yan shekara ɗaya guda bakwai.
\s5
\v 9 Dole ku miƙa tare da su baiko na hatsi, gãri mai laushi gauraye da mai,
\v 10 uku cikin goma na efa domin bijimi, biyu cikin uku domin tunkiya guda ɗaya, da kuma kashi goma na efa domin dukkan raguna bakwai ɗin.
\v 11 Dole ku miƙa ɗan akuya ɗaya don baikon na zunubi. Wannan zai zama ƙãri bisa baikon zunubi na kaffara, da baye-bayensu na sha.
\s5
\v 12 A rana ta sha biyar ga watan bakwai za ku yi taro mai tsarki don girmama Yahweh. Ba za ku taɓa yin wani aiki yadda kuka sãba a kodayaushe a wannan rana ba, kuma za ku yi buki gare shi kwana bakwai.
\v 13 Dole ku miƙa baiko na ƙonawa, hadaya da aka miƙa ta wurin wuta domin abin ƙamshi da daɗi ga Yahweh. Dole ku miƙa 'yan bijimi guda sha uku, tumaki guda biyu, da kuma tumakai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya. Kowanen su ya zama mara aibi.
\s5
\v 14 Dole ne ku miƙa tare da su baiko na hatsi, niƙaƙƙen gari harɗe da mai, kashi uku na efa don kowanne rago na raguna sha ukun, kashi biyu domin kowanne rago na raguna biyun,
\v 15 da kashi ɗaya na efa domin dukkan tumaki guda sha huɗun.
\v 16 Dole ku miƙa baiko na zunubi namijin akuya ɗaya ƙãri bisa ƙonannun baiko na kodayaushe, baikon hatsin, tare da shi kuma da baikon abin sha.
\s5
\v 17 A rana ta biyu na taruwa, dole ne ku miƙa 'yan raguna guda sha biyu, tumaki biyu, da awakai maza goma sha huɗu 'yan shekara ɗaya, kowanne mara aibi.
\v 18 Dole ku miƙa su tare da baikon hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku.
\v 19 Dole ne ku miƙa baiko na zunubi ɗan rago ɗaya ƙãri bisa baiko na ƙonawa a kodayaushe yaushe, da kuma baye-bayensu na shã.
\s5
\v 20 A rana ta uku na taruwan, dole ne ku miƙa raguna shaɗaya, tumaki biyu, da bunsurai sha huɗu 'yan shekara ɗaya, kowanne mara aibi.
\v 21 Dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da baye-baye na abin shã domin ragunan, domin su tumakin, da kuma don su awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku.
\v 22 Dole ne ku miƙa namijin tunkiya ɗaya baiko na zunubi ƙãri bisa baiko na ƙonawa na kodayaushe, baikon hatsinta, da kuma baye-bayensu.
\s5
\v 23 A rana ta huɗu ta taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda goma, tumaki guda biyu, da mazajen awakai 'yan shekara ɗaya guda shahuɗu, kowannensu marasa aibi.
\v 24 Dole ne ku yi tare da su baiko na hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, da kuma domin awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umarce ku.
\v 25 Dole ne ku miƙa bunsuru ɗaya baiko na zunubi ƙãri bisa baiko na ƙonawa na kodayaushe, baiko na hatsinsa, da baye-bayensu na shã.
\s5
\v 26 A rana ta biyar ta taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda tãra, tumaki biyu, da bunsurai 'yan shekara ɗaya guda sha huɗu, marasa aibi.
\v 27 Dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da kuma baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakin, domin kuma awakan, ana miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurta.
\v 28 Dole ne ku miƙa namijin tunkiya ɗaya na baikon domin zunubi ƙari bisa ƙonannen baiko na kodayaushe, baikon hatsin, da baye-baye na shãnsu.
\s5
\v 29 A rana ta shida ta taruwar, dole ne ku miƙa raguna takwas, tumaki biyu, da mazajen awakai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya, marasa aibi.
\v 30 dole ne ku miƙa su tare da baiko na hatsi da kuma baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakan, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurce ku.
\v 31 dole ne ku miƙa bunsuru guda ɗaya baiko na zunubi, baikon hatsi, da baye-bayensu na shã.
\s5
\v 32 A rana ta bakwai na taruwa, dole ne ku miƙa raguna guda bakwai, tumakai biyu, da kuma bunsurai guda sha huɗu 'yan shekara ɗaya, marasa aibi.
\v 33 Dole ne ku miƙa tare da su baiko na hatsi da baye-baye na shã domin ragunan, domin tumakan, domin kuma awakan, kuna miƙa baye-baye masu yawa kamar yadda aka umurce ku.
\v 34 Dole ne ku miƙa namijin akuya domin baiko na zunubi don ƙari bisa ga baiko na ƙonawa kamar na kodayaushe, domin baiko na hatsin, da kuma baye-bayensu na shã.
\s5
\v 35 A rana ta takwas zaku sake yin wani taron mai tsarki. Kar ku kuskura ku yi wani aiki kamar yadda kuka saba a wannan rana.
\v 36 Dole ne ku miƙa hadaya na ƙonawa, baiko da aka yi da wuta domin a miƙa abin ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Za ku miƙa ɗan bijimi guda ɗaya, akuya ɗaya, da kuma 'yan raguna guda bakwai masu shekara ɗaya, kowanne mara aibi.
\s5
\v 37 Dole ne ku miƙa baikon hatsinsu da kuma baikon abin sha domin bijimi, domin ɗan akuya, kuma domin 'yan raguna, kuna miƙa baye-baye kamar yadda aka umurta.
\v 38 Dole ne ku miƙa bunsuru guda ɗaya baiko na zunubi ƙari bisa ƙonannen baikon da aka sãba kodayaushe, baikon hatsinsu, da kuma baye-bayensu na shã.
\s5
\v 39 Waɗannan su ne dole ku miƙa ga Yahweh a tsayayyun bukukuwanku. Waɗannan za su zama ƙãri ne bisa alƙawaranku da kuma baye-bayenku na yardan rai. Dole ne ku miƙa waɗannan a matsayin baye-bayenku na ƙonawa, baye-baye na hatsi, baye-baye na shã, da baye-baye na zumunci."
\v 40 Sai Musa ya gaya wa mutanen Isra'ila dukkan abin da Yahweh ya umurce shi ya faɗa.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Musa ya yi magana da shugabannin ƙabilun mutanen Isra'ila. Ya ce, "Ga abin da Yahweh ya umarta.
\v 2 Idan wani ya yi wa'adi ga Yahweh, ko ya yi rantsuwa don ya riƙe kansa ga alƙawari, kada ya karya maganarsa. Dole ya cika alƙawarinsa ya aikata duk abin da ya fito daga bakinsa.
\s5
\v 3 Idan 'yar matashiya mace mai zama cikin gidan mahaifinta ta yi wa'adi ga Yahweh ta ɗaure kanta ga alƙawari,
\v 4 idan mahaifinta ya ji wa'adin da kuma alƙawarin da ta daukar wa kanta, kuma idan bai ce komai ba domin ya hana ta ba, to dukka wa'adodinta za su tsaya. Kowanne alƙawarin da ta ɗaukar wa kanta zai tsaya.
\s5
\v 5 Amma idan mahaifinta ya ji game da wa'adinta da alƙawarinta, idan kuma bai ce da ita komai ba, to dukkan wa'adodinta da alƙawaranta da ta ɗaukar wa kanta za su tsaya.
\s5
\v 6 Amma, idan mahaifinta ya ji dukkan wa'adodin da ta yi da kuma alƙawura masu tsarki da ta ɗaukar wa kanta, idan kuma ya sọke abin da ta yi a wannan ranar, to ba za su tsaya ba. Yahweh zai gafarta mata domin mahaifinta ya sọke abin da ta yi.
\v 7 Idan ta auri mutum yayin da ta ke ƙarƙashin waɗannan wa'adodin, ko kuma idan ta furta alƙawarai cikin garaje da ta ɗaukar wa kanta nawaya, wannan nawayar tilas ta tsaya.
\s5
\v 8 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji game da zancen, sa'an nan ya hana alƙawarin da ta ɗauka, maganar gangancin da ta yi ta fita daga leɓunanta da ta ɗaure kanta. Yahweh zai sãke ta.
\s5
\v 9 Amma game da gwauruwa ko sakakkiyar mace, dukkan abin da ta ɗaure kanta da shi zai tsaya a kanta.
\v 10 Idan mace ta ɗauki alƙawari a cikin gidan mijinta ko ta yi wa kanta hani ta wurin yin rantsuwa,
\v 11 sai kuma maigidanta ya ji game da wannan, amma bai ce mata komai ba, to sai dukkan abin da ta alƙawarta su tsaya.
\s5
\v 12 Amma idan maigidanta ya hana su a wannan ranar da ya ji game da su, to duk abin da ya fito daga leɓunanta game da wa'adodinta ko alƙawaranta baza su tsaya ba. Mijinta ya hana su. Yahweh zai sãke ta.
\s5
\v 13 Kowanne wa'adi ko rantsuwar da mace ta yi da suka ɗaure ta har ta hana wa kanta wani abu maigidanta na iya tabbatarwa ko ya hana.
\v 14 Amma idan bai ce mata komai a ranar ba, to ya tabbatar da dukkan wa'adodi da zaunannun alƙawarai wadanda ta ɗauka. Ta haka ya tabbatas da su domin bai ce da ita komi ba a ranar da ya ji game da su.
\s5
\v 15 Idan mijinta yayi ƙoƙarin hana alƙawarin da matarsa ta ɗauka da daɗewa bayan ya ji shi, don haka zai ɗauki laifinta."
\v 16 Waɗannan su ne farillan da Yahweh ya umarci Musa da ya sanar - da farillai game da abin dake tsakanin mutum da matarsa da kuma tsakanin mahaifi da ɗiyarsa a matashiyarta sa'ad da take tare da iyalin mahaifinta.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce,
\v 2 "Ka ɗauki fansa a bisa Midiniyawa kan abin da suka yi wa Isra'ilawa. Bayan ka yi wannan, za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka."
\s5
\v 3 Sai Musa ya yi magana da mutanen. Ya ce, "Ku shirya wasu daga cikin mazajenku don yaƙi gãba da Midiyan, ku kuma yi ramako na Yahweh a bisanta.
\v 4 Kowacce kabila cikin dukkan Isra'ila dole ta aika da sojoji dubu zuwa yaƙi."
\v 5 Saboda haka cikin dubban mazajen Isra'ila, aka aika da dubu ɗaya daga kowacce kabila, mazaje dubu sha biyu shiryayyu don yaƙi.
\s5
\v 6 Sai Musa ya aika da su zuwa yaƙi, daga kowacce kabila dubu ɗaya, tare da Finehas ɗan Eliyeza firist, da kuma wasu kayayyaki daga cikin wuri mai tsarki da kuma su ƙahonni dake a hannunsa don busawa ta alamar yaƙi.
\v 7 Suka yi yaƙi da Midiya, kamar yadda Yahweh ya bada umarni ga Musa. Suka karkashe kowanne mutum.
\v 8 Suka kashe sarakunan Midiyan tare da sauran matattunsu: Ebi, da Rekem, da Zur, da Hur, da kuma Reba, sarakuna guda biyar na Midiyan. Suka kuma kashe Bala'am ɗan Beyor, da takobi.
\s5
\v 9 Rundunar Isra'ila suka kwashe bayi matayen Midiyan, da yaransu, da dukkan shanunsu, da garkunansu, da dukkan dukiyarsu. Suka kwashe su ganima.
\v 10 Suka ƙone dukkan biranensu inda suke zama da dukkan sansaninsu.
\s5
\v 11 Suka kwashe dukkan ganimar da kuma 'yan sarƙoƙi, da mutane da dabbobi.
\v 12 Suka dawo da 'yan sarƙoƙin, da ganimar, da abubuwan da aka ƙwace wurin Musa, ga Eliyeza firist, zuwa kuma ga jama'ar Isra'ila. Suka kawo su zuwa cikin sansani cikin kwarurukan Mowab, wanda ke bakin Yodan kurkusa da Yeriko.
\s5
\v 13 Musa, da Eliyeza firist, da dukkan shugabannin jama'a suka fito domin su tarye su a wajen sansani.
\v 14 Amma Musa ya yi haushi da shugabannin rundunar, kwamandojin na dubbai da kuma na ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga yaƙi.
\v 15 Musa yace masu, "Kun bar dukkan matayen su rayu ko?
\s5
\v 16 Duba, waɗannan mataye sun jawo wa mutanen Isra'ila, ta wurin shawarar Bala'am, su aikata zunubi ga Yahweh ga zancen Feyor, yayinda annoba ta bazu cikin mutanen Yahweh.
\v 17 Yanzu fa, sai ku kashe kowanne namiji cikin dukkan ƙananan, ku kuma kashe kowacce macen da ta taɓa kwana da namiji.
\s5
\v 18 Amma ku ɗaukar wa kanku dukkan 'yan matan da ba su taɓa kwana da namiji ba.
\v 19 Dole ku yi sansani can a wajen sansani na Isra'ila har na kwana bakwai. Dukkan ku da kuka kashe wani da kuma ko kuka taɓa duk wani matacce -dole ku tsarkake kanku a rana ta uku a rana ta bakwai kuma- ku da bayinku.
\v 20 Dole ku tsarkake kowacce tufa da kowanne abin da aka yi da fatar dabba da gashin akuya, da kuma kowanne abin da aka yi da itace."
\s5
\v 21 Sai Eliyeza yace da sojoji waɗanda suka tafi yaƙi, "Wannan shi ne umarnin shari'a da Yahweh ya bayar ga Musa:
\v 22 Zinariyar, da azurfa, da jangaci, da tama, da kuza, da dalma,
\v 23 da kuma kowanne abin da ya jimre ma wuta, sai ka saka shi ta wurin wuta, za shi kuma yi tsabta. Dole daga nan ka tsarkake waɗannan abubuwa da ruwan tsarkakewa. Duk abin da ba za shi shiga ta wuta ba sai ka tsarkake da ruwa.
\v 24 Dole ku wanke tufafinku a rana ta bakwai, daga nan zaku zama da tsabta. Daga nan kuna iya shigowa cikin sansanin Isra'ila."
\s5
\v 25 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya kuma ce,
\v 26 "Ka ƙirga dukkan abin ganimar da aka kawo, da mutane da dabbobi. Kai, da Eliyeza firist, da kuma shugabanni na gidajen ubanni na mutane
\v 27 za a raba ganimar gida biyu. Ka raba a tsakanin sojojin da suka tafi yaƙi da kuma dukkan sauran mutanen.
\s5
\v 28 Sa'an nan za ka sa a karɓi haraji domina daga wurin sojojin da suka tafi yaƙi. Wannan harajin dole ya zama ɗaya daga cikin kowanne ɗari biyar, ko na mutane, ko na dabbobi, ko na jakuna, ko na awakai, ko tumakai.
\v 29 Ka ɗauki wannan haraji daga rabinsu ka kuma bada su ga Eliyeza firist abin baikon da za a miƙa gare ni.
\s5
\v 30 Haka kuma daga rabin mutanen Isra'ila, sai ka karɓi ɗaya daga cikin kowanne hamsin - daga wurin mutane, ko shanu, ko jakai, ko awakai, da kuma tumaki. Ka miƙa su ga Lebiyawa ma su lura da mazamnina.
\v 31 Sai Musa da Eliyeza firist suka yi kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\v 32 To yanzu dai ganimar da ta rage daga cikin abin da sojojin suka ɗauka su ne tumaki 675,000,
\v 33 shanu dubu saba'in da biyu,
\v 34 jakuna dubu sittin da ɗaya,
\v 35 da kuma 'yan mata dubu talatin da biyu waɗanda ba su taɓa kwana da wani namiji ba.
\s5
\v 36 Rabin da aka ajiye domin sojoji tumaki 337,000 ne.
\v 37 Tumaki waɗanda suke na Yahweh kuma 675 ne.
\v 38 Shanu dubu talatin da shida ne waɗanda harajin Yahweh saba'in da biyu ne.
\s5
\v 39 Jakunan 30,500 ne, waɗanda daga ciki na Yahweh sittin da ɗaya ne.
\v 40 Mutum dubu sittin ne daga ciki kuwa na harajin Yahweh talatin da biyu ne.
\v 41 Sai Musa ya ɗauki harajin da za a miƙa ta baiko ga Yahweh. Ya bayar ga Eliyeza firist, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\v 42 Game da rabi na mutanen Isra'ila waɗanda Musa ya karɓa daga sojojin da suka tafi yaƙi -
\v 43 rabi na mutane kuwa, tumaki 337,500 ne,
\v 44 shanu dubu sittin ne,
\v 45 jakai 30,500 ne,
\v 46 mata kuma dubu sha shida.
\s5
\v 47 Daga cikin rabi na mutanen Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga kowanne hamsin, da na mutane da kuma dabbobi. Ya bayar da su ga Lebiyawa waɗanda ke lura da mazaunin Yahweh, kamar yadda Yahweh ya umarce shi ya yi.
\s5
\v 48 Sai shugabannin runduna, da na dubu dubu da kuma na bisa ɗari ɗari, suka zo wurin Musa.
\v 49 Suka ce masa, "Bayinka sun lisafta sojojin dake a ƙarƙashinsu, kuma babu mutum ɗaya da ya ɓace.
\s5
\v 50 Mun kawo baiko na Yahweh, abin da kowanne mutum ya samu, kayayyakin ado na zinariya, ƙarafu na ƙafa da na hannu, zoben hannu, da zoben kunne, da kayan ado na wuya, domin a yi kafara domin mu kanmu a gaban Yahweh."
\v 51 Sai Musa da Eliyeza firist suka karɓa daga garesu zinariyar da dukkan kayayyaki na aikin gwaninta.
\s5
\v 52 Dukkan baiko na zinariya da suka miƙa ga Yahweh - baye-baye daga shugabanni na dubbai daga kuma shugabanni na ɗari ɗari - an auna shekel 16,750.
\v 53 Kowanne soja ya ɗauki ganima, kowanne mutum domin kansa.
\v 54 Musa da Eliyeza firist suka karɓi zinariyar daga shugabanni na dubbai da na ɗari ɗari. Suka kai zuwa cikin alfarwa ta taruwa domin tunawa ta mutanen Isra'ila ga Yahweh.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 A wannan lokacin zuriyar Ruben da ta Gad suna da garkunan shanu masu yawan gaske. Da suka lura cewa ƙasar Yaza da Giliyad, ƙasa ce mai kyaun gaske domin kiwon shanu.
\v 2 Saboda haka zuriyar Gad da ta Ruben suka zo suka yiwa Musa magana, ga Eliyeza firist, ga kuma shugabannin jama'a. Suka ce,
\v 3 "Ga lissafin wuraren da muka yi bincike: Atarot, Dibon, Yaza, Nimra, da Heshbon, Eliyele, Sebam, Nebo, da kuma Beyon.
\s5
\v 4 Waɗannan su ne ƙasashen da Yahweh ya yaƙa a gaban shugabannin Isra'ila, kuma suna da kyau domin kiwon shanu. Mu, bayinka muna da shanu masu yawa."
\v 5 Suka ce, "Idan mun sami tagomashi a wurinka, bari a bamu wannan ƙasa, mu bayinka, abin mallaka. Kada a ƙetare Yodan da mu."
\s5
\v 6 Sai Musa ya amsa wa zuriyar Gad da ta Ruben, "To 'yan'uwanku sun tafi yaƙi, ku kuma kwa zauna a nan?
\v 7 Don me kuke karya zuciyar mutanen Isra'ila daga shiga cikin ƙasar alƙawarin da Yahweh ya ba su?
\s5
\v 8 Haka ubanninku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh Barniya su yi duban ƙasa.
\v 9 Suka tafi zuwa kwarin Eshkol. Suka ga ƙasar amma suka karya zukatan mutanen Isra'ila har da ba su yarda su shiga ƙasar da Yahweh ya basu ba.
\s5
\v 10 Fushin Yahweh ya yi ƙuna a wannan rana. Ya kuma yi rantsuwa ya ce,
\v 11 'Hakika babu wani daga cikin mazajen da suka fito daga cikin Masar, daga mai shekara ashirin da fiye da haka, da zai ga ƙasa wadda na yiwa Ibrahim, da Yakubu, da Ishaku alƙawari, domin basu bi ni da dukkan yadda ya kamata ba, sai dai
\v 12 Kaleb ɗan Yefunne Bakeniziye, da kuma Yoshuwa ɗan Nun. Kaleb da Yoshuwa kaɗai suka bi ni yadda ya kamata.'
\s5
\v 13 Fushin Yahweh kuma ya yi ƙuna a bisa Isra'ila. Ya sa suka yi watangaririya a cikin jeji na tsawon shekaru arba'in har sai da wannan tsãra ta waɗanda suka aikata wannan mugunta a fuskarsa suka hallaka.
\v 14 Duba, kun tashi a cikin mazaunin ubanninku, haka kuma kuke mazaje masu zunubi, domin ku daɗa fushin Allah mai ƙuna gãba da Isra'ila.
\v 15 Idan kuka juya daga binsa, shi kuma zai ƙara barinsu a cikin jeji, ku kuma da kun gama hallaka dukkan mutanen nan."
\s5
\v 16 Sai suka zo wurin Musa suka kuma ce, "Ka barmu mu gina ganuwa ta shimge a nan domin dabbobinmu da kuma birane domin iyalanmu.
\v 17 Duk da haka, mu da kanmu za mu shirya mu ɗauki makamai mu tafi tare da rundunar Isra'ila har sai mun tafi da su zuwa wurarensu. Amma iyalanmu za su zauna a birane masu ganuwa saboda sauran mutanen dake zama cikin ƙasar.
\s5
\v 18 Ba zamu dawo ba har sai dukkan mutanen Isra'ila kowa ya karɓi gãdonsa.
\v 19 Ba zamu ci gãdon ƙasan tare da su a ƙetaren Yodan ba, domin gãdonmu na a nan yamma da Yodan."
\s5
\v 20 Sai Musa ya amsa masu, "Idan kuka yi abin da kuka faɗa, idan kuka ɗauki makamai don ku wuce gaban Yahweh don yaƙi,
\v 21 don haka kowanne mutum daga cikin mayaƙanku za shi ƙetare Yodan a gaban Yahweh, har sai ya kori maƙiyansa daga gabansa,
\v 22 ƙasar kuma a ci mulkinta a gabansa. Sa'an nan daga baya ku komo. Za ku zama marasa laifi a gaban Yahweh da kuma wurin Isra'ila. Wannan ƙasa za ta zama abin mallaka a gaban Yahweh.
\s5
\v 23 Amma idan ba ku yi haka ba, duba, da ko za ku yi wa Yahweh zunubi. Ku kuma san da cewa lallai za a bayyana zunubinku a fili.
\v 24 Ku gina birane domin iyalanku, shimgayen kuwa domin dabbobinku; sai ku yi abin da kuka faɗi."
\v 25 Sai zuriyar Gad da na Ruben suka yi magana da Musa suka kuma ce, "Bayinka za su yi kamar yadda kai, shugabanmu, ka umarta.
\s5
\v 26 Da ƙanananmu, da matayenmu, da garkunan tumakinmu, da dukkan shanunmu za su zauna can cikin biranen Giliyad.
\v 27 Amma, mu, bayinka, za mu ƙetare a gaban Yahweh zuwa ga yaƙi, kowanne mutum a shirye domin yaƙi, yadda kai, ubangidanmu, ka faɗi."
\s5
\v 28 Don haka sai Musa ya yi umarni game da su zuwa ga Eliyeza firist, zuwa ga Yoshuwa ɗan Nun, da kuma zuwa ga shugabanni na ubannin kabilun mutanen Isra'ila.
\v 29 Musa yace masu, "Idan zuriyar Gad da na Ruben suka ƙetare Yodan tare da ku, kowanne mutum da ya yi shirin yaƙi a gaban Yahweh, idan kuwa aka sarayyar da ƙasar a gabanku, to, sai ku ba su ƙasar Giliyad abin mallaka.
\v 30 Amma idan har basu ƙetare da ku da shirin yaƙi ba, don haka za su sami ta su mallakar tare da ku a cikin ƙasar Kan'ana."
\s5
\v 31 Sai zuriyar Gad da ta Ruben suka amsa suka ce, "Kamar yadda Yahweh ya faɗa mana, mu bayinka, wannan ita za mu yi.
\v 32 Za mu ƙetare da shirin yaƙi a gaban Yahweh zuwa cikin ƙasar Kan'ana, amma namu gãdon mallakar za su zauna da mu a wannan sashe na Yodan."
\s5
\v 33 Don haka ga zuriyar Gad da na Ruben, da kuma ga rabin kabilar Manasse ɗan Yosef, Musa ya ba su masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da na Og, sarkin Bashan. Ya ba su ƙasar, ya kuma raba masu dukkan biranenta da iyakokinta, da biranen dake kewaye da su.
\s5
\v 34 Sai zuriyar Gad suka sãke gina Dibon, Atarot, Arowa,
\v 35 da Atrot Shofan, Yaza, Yogbeha,
\v 36 Bet Nimra, da Bet Haran birane masu ganuwa da shimgaye domin tumaki.
\s5
\v 37 Zuriyar Ruben kuma suka gina Heshbon, da Eleyale, da Kiriyatayim,
\v 38 da Nebo, da Ba'al Meyon - daga baya aka canza sunayensu, da kuma Sibma. Suka bada wasu sunaye ga biranen da suka sãke ginawa.
\v 39 Zuriyar Makir ɗan Manasse ya tashi ya tafi Giliyad, ya kuma ɗauke ta daga Amoriyawa waɗanda ke cikinta.
\s5
\v 40 Sai Musa ya bãda Gilyad ga Makir ɗan Manasse, mutanen sa kuma suka zauna nan.
\v 41 Yayir ɗan Manasse ya tashi ya tafi ya ci garuruwanta, ya kuma kira su da suna Habbot Yayir.
\v 42 Noba ya tafi ya kuma cinye Kenat da kauyukanta, ya kuma kirata da suna Noba, bisa ga sunansa.
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Waɗannan su ne zangon mutanen Isra'ila bayan da suka bar ƙasar Masar da runduna bayan runduna a ƙarƙashin shugabancin Musa da Haruna.
\v 2 Musa ya rubuta duk inda suka baro da inda suke kaiwa, yadda Yahweh ya umarta. Ga yadda zangon suka kasance, tashi bayan tashi.
\s5
\v 3 Suka yi tafiya daga Ramesis cikin wata na farko, da suka taso a rana ta sha biyar ga wata na farko. Da safe bayan Bikin Ƙetarewa, sai mutanen Isra'ila suka fito a fili, dukkan Masarawa na gani.
\v 4 Wannan ya faru ne sa'ad da Masarawa ke binne dukkan 'ya'yan farinsu matattu, waɗanda Yahweh ya kashe a cikinsu, gama ya kawo hukunci a bisa allolinsu.
\s5
\v 5 Sai mutanen Isra'ila suka tashi daga Ramesis suka kuma yi zango a Sukkot.
\v 6 Suka tashi daga Sukkot suka yi zango a Etam, a gacin jejin.
\v 7 Suka tashi daga Etam suka juya baya zuwa Fi Hahirot, wadda take kallon Ba'al Zefon, inda suka yi zango fuska da fuskar Migdol.
\s5
\v 8 Sai suka shirya tashi domi tafiya daga gaban Fi Hahirot suka kuma wuce ta tsakiyar teku zuwa cikin jeji. Sun yi tafiyar kwana uku zuwa cikin jejin Etam suka kuma yi zango a Mara.
\v 9 Suka shirya tafiya daga Mara suka kuma isa Elim. A Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa da kuma itatuwan dabino. A nan ne suka kafa zango.
\v 10 Sai suka tashi daga Elim suka kafa zango a bakin Tekun Iwa.
\s5
\v 11 Sai suka tashi daga bakin Tekun Iwa suka yi zango a cikin jejin Sin.
\v 12 Suka tashi daga jejin Sin suka yi zango a Dofka.
\v 13 Suka tashi daga Dofka suka kuma yi zango a Alush.
\v 14 Suka tashi daga Alush suka yi zango a Refidim, inda ba a sami ruwan da mutane zasu sha ba.
\s5
\v 15 Suka tashi daga Rafidim suka yi zango a cikin jejin Sinai.
\v 16 Suka tashi daga jejin Sinai suka kuma yi zango a Kibrot Hattaba.
\v 17 Suka tashi daga Kibrot Hattaba suka yi zango a Hazerot.
\v 18 Suka tashi daga Hazerot suka kuma yi zango a Ritma.
\s5
\v 19 Suka tashi daga Ritma suka kuma yi zango a Rimmon Ferez.
\v 20 Su ka tashi daga Rimmon Ferez suka kuma yi zango a Libna.
\v 21 Suka tashi daga Libna suka kuma yi zango a Rissa.
\v 22 Suka tashi daga Rissa suka kuma yi zango a Kehelata.
\s5
\v 23 Suka tashi daga Kehelata suka kuma yi zango a Tsaunin Shefa.
\v 24 Suka tashi daga Tsaunin Shafa suka yi zango a Harada.
\v 25 Suka tashi daga Harada suka kuma yi zango a Makhelot.
\v 26 Suka tashi daga Makhelot suka yi zango a Tahat.
\s5
\v 27 Suka tashi daga Tahat suka kuma yi zango a Tera.
\v 28 Suka tashi daga Tera suka kuma yi zango a Mitka.
\v 29 Suka tashi daga Mitka suka kuma yi zango a Hashmona.
\v 30 Suka tashi daga Hashmona suka kuma yi zango a Moserot.
\s5
\v 31 Suka tashi daga Moserot suka kuma yi zango a Bene Ya'akan.
\v 32 Suka tashi daga Bene Ya'akan suka kuma yi zango a Hor Haggidgad.
\v 33 Suka tashi daga Hor Haggidgad suka kuma yi zango a Yotbata.
\v 34 Suka tashi daga Yotbata suka kuma yi zango a Abrona.
\s5
\v 35 Suka tashi daga Abrona suka kuma yi zango a Ezion Geba.
\v 36 Suka tashi daga Ezion Geba suka kuma yi zango a cikin jejin Zin a Kadesh.
\v 37 Suka tashi daga Kadesh suka kuma yi zango a Tsaunin Hor, a bakin iyakar ƙasar Idom.
\s5
\v 38 Sai Haruna firist ya haura bisa Tsaunin Hor ga umarnin Yahweh ya kuma mutu can a cikin shekara ta arba'in bayan da mutanen Isra'ila suka fito daga ƙasar Masar, a cikin wata na biyar, a rana ta farko ga watan.
\v 39 Haruna na da shekaru 123 lokacin da ya mutu a Tsaunin Hor.
\s5
\v 40 Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda ke zama cikin kudancin jeji a ƙasar Kan'ana, ya ji game da isowar mutanen Isra'ila.
\s5
\v 41 Suka tashi daga Tsaunin Hor suka kuma yi zango a Zalmona.
\v 42 Suka tashi daga Zalmona suka kuma yi zango a Funon.
\v 43 Suka tashi daga Funon suka kuma yi zango a Obot.
\s5
\v 44 Suka tashi daga Obot suka kuma yi zango a Iye Abarim, a bakin iyakar Mowab.
\v 45 Suka tashi daga Iye Abarim suka kuma yi zango a Dibon Gad.
\v 46 Suka tashi daga Dibon Gad suka kuma yi zango a Almon Diblatayim.
\s5
\v 47 Suka tashi daga Almon Diblatayim suka kuma yi zango a cikin duwatsu na Abarim, fuska da Nebo.
\v 48 Suka tashi daga duwatsun na Abarim suka kuma yi zango a cikin kwarrurukan Mowab a bakin Yordnn a Yeriko.
\v 49 Suka yi zango a bakin Yodan, daga Bet Yeshimot zuwa Abel Shittim cikin filayen Mowab.
\s5
\v 50 Yahweh ya yi magana da Musa a cikin filayen Mowab a bakin Yodan a Yeriko ya kuma ce,
\v 51 "Ka yi magana da 'ya'yan Isra'ila ka kuma ce masu, 'Yayin da kuka ƙetare Yodan zuwa cikin ƙasar Kan'ana,
\v 52 dole ne ku kori dukkan mazauna ƙasar daga gareku. Dole ku hallakar da dukkan sassaƙaƙƙun siffofinsu. Dole ku hallakar da siffofinsu na zubi ku kuma farfasa dukkan tuddan wurarensu.
\s5
\v 53 Dole ku mallaki ƙasar ku kuma zauna cikinta, domi na baku ƙasar abin mallaka.
\v 54 Dole ne ku yi gãdon ƙasar yanki-yanki, bisa ga kowacce kabila. Dole ne ku bada yanki mai girma zuwa kabilar da tafi kowacce kabila, ga kabila mafi ƙanƙata kuwa ƙaramin yankin ƙasar. Duk sa'ad da yankin ya fãɗa ga kowacce kabila, wannan ƙasa zata zama tata. Za ku gãji ƙasar bisa ga kabilar ubanninku.
\s5
\v 55 Amma idan baku kori mazaunan ƙasar a gaban ku ba, sa'an nan mutanen da kuka bari su tsaya, za su zama maku kamar wani abu cikin idanunku da kuma ƙaya a kwiɓinku. Za su wahalshe da rayukanku cikin ƙasar da kuka zauna.
\v 56 Sa'an nan zai zama kuma duk abin da na yi niyyar yi wa waɗannan mutanen, zan yi maku shi."'
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 2 "Ka umarci mutanen Isra'ila ka kuma ce ma su, 'Sa'ad da kuka shiga cikin ƙasar Kan'ana, ƙasar da zata zama taku, ƙasar Kan'ana da iyakokinta,
\v 3 iyakarku daga yamma zata kai har cikin jejin Zin kusa da iyakar Idom. Gabashin ƙarshe na yamma za shi zama kan layin da ya kai ƙarshe a yammancin ƙarshe na Tekun Gishiri.
\s5
\v 4 Iyakarku zata juya zuwa yamma daga dutsen Akrabbim ta wuce ta jejin Zin. Daga nan, zata tashi zuwa gabas da Kadesh Baniya har ta kai Harza Adda zuwa ga Azmon.
\v 5 Daga nan, iyakar zata juya daga Azmon zuwa wajen rafin Masar ta kuma bi zuwa teku.
\s5
\v 6 Iyaka ta Kudu za ta zama kan iyakar Babban Teku. Wannan zai zama iyaka gareku ta yammanci.
\s5
\v 7 Iyakarku ta Arewa zata tashi daga kan layin da zaku sa alama daga Babban Teku zuwa Tsaunin Hor,
\v 8 daga Tsaunin Hor zuwa Lebo Hamat, daga nan zuwa Zedad.
\v 9 Daga nan iyakar zata ci gaba zuwa Zifuron ta tsaya a Hazar Enan. Wannan zata zama iyakarku ta arewa.
\s5
\v 10 Zaku saka alama mai nuna iyakarku ta gabas daga Hazar Enan kudu da Shefam.
\v 11 Daga nan iyaka ta gabas za ta kai daga Shefam zuwa Ribla, gabas da Ain. Iyakar za ta gangaro ta wajen gabas gefen Teku na Kinneret.
\v 12 Iyakar kuma za ta gangaro zuwa ga Kogin Yodan zuwa ga Tekun Gishiri ta kuma gangaro zuwa iyaka ta gabashin Tekun Gishiri. Wannan za ta zama ƙasarku, da dukkan iyakokinta dake zagaye da ita.
\s5
\v 13 Sai Musa ya umarci mutanen Isra'ila ya ce, "Wannan ce ƙasar da zaku yi gãdonta ta wurin rabo, wanda Yahweh ya umarta a bayar ga sauran kabilu tãre da kuma rabin kabilar.
\v 14 Kabila ta zuriyar Ruben, bisa ga rabon gãdo ga ubannin kabilunsu, da kuma kabila ta zuriyar Gad, bisa ga rabon gãdo ga ubannin kabilunsu, da kuma rabin kabilar Manasse dukkansu suka karɓi tasu ƙasar.
\v 15 Kabilun biyu da kuma rabin kabilar suka karɓi tasu gãdon na ƙasar a ƙetaren Yodan a sashen Gabashin Yeriko, wajen fitar rana."
\s5
\v 16 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 17 "Ga sunayen mazajen da zasu raba maku ƙasar domin gãdonku: Eliyeza firist da kuma Yoshuwa ɗan Nun.
\v 18 Za ku zaɓi shugaba daga kowanne kabila don ya raba ƙasar domin zuriyarsu.
\s5
\v 19 Ga sunayen mazajen: Daga kabilar Yahuda, Kaleb ɗan Yefunne.
\v 20 Daga kabilar zuriyar Simiyon, Shemuwel ɗan Ammihud.
\s5
\v 21 Daga kabilar Benyamin, Elidad ɗan Kislon.
\v 22 Daga kabila ta zuriyar Dan aka sami shugaba, Bukki ɗan Yogli.
\v 23 Daga cikin zuriyar Yosef, daga kabila ta zuriyar Manasse shugaba, Hanniyel ɗan Efod.
\s5
\v 24 Daga kabila ta zuriyar Ifraim aka sami shugaba, Kemuwel ɗan Shiftan.
\v 25 Daga kabila ta zuriyar Zebulun aka sami shugaba, Elizafan ɗan Farnak.
\v 26 Daga kabila ta zuriyar Issaka aka sami shugaba, Faltiyel ɗan Azzan.
\s5
\v 27 Daga kabila ta zuriyar Asha aka sami shugaba, Ahihu ɗan Shelomi.
\v 28 Daga kabila ta zuriyar Naftali aka sami shugaba, Fedahel ɗan Ammihud."
\v 29 Yahweh ya umarci waɗannan mutanen su raba ƙasar Kan'ana su kuma raba wa kowanne kabila na Isra'ila gãdonsu.
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa a kwarin Mowab kusa da Yodan a Yeriko ya kuma ce,
\v 2 "Ka umarci jama'ar Isra'ila su baiwa Lebiyawa kaɗan daga gãdonsu na ƙasar. Zasu basu birane su zauna ciki da kuma wuraren kiwo zagaye da waɗannan birane.
\s5
\v 3 Su Lebiyawan zasu sami waɗannan biranen su zauna a ciki. Wuraren kiwon za su zama domin garkunansu na shanu, da na tumaki, da na dukkan dabbobinsu.
\v 4 Wuraren kiwon zagaye da birnin da zaku baiwa Lebiyawan zai tashi daga bangon birnin kãmu dubu ɗaya a kowanne sashi.
\s5
\v 5 Dole ka auna kãmu dubu biyu daga wajen birnin a sashen gabas, kãmu dubu biyu zuwa sashen kudu, kãmu dubu biyu zuwa sashen yamma, kãmu dubu biyu kuma zuwa ga sashen arewa. Wannan za shi zama wuraren kiwo domin biranensu. Biranen zasu kasance a tsakiya.
\s5
\v 6 Birane shida da zaku ba Lebiyawa zasu zama biranen mafaka. Zaku ku yi tanadin waɗannan wurare domin duk wanda ya kashe wani na iya guduwa can. Haka kuma za ku yi tanadin wasu birane arba'in da takwas.
\v 7 Biranen da zaku bai wa Lebiyawa gaba ɗaya zai zama arba'in da takwas. Dole ku basu tare da wuraren kiwonsu.
\s5
\v 8 Manyan kabilu na jama'ar Isra'ila, kabilar da take da yawan ƙasa, zata tanada birane fiye da kowa. 'Yar ƙaramar kabila kuwa zata tanadi birane kaɗan. Kowacce kabila zata tanada wa Lebiyawa dai-dai bisa ga gãdon da ta karɓa.
\s5
\v 9 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 10 "Ka yi magana da 'ya'yan Isra'ila ka ce masu, 'Idan kuka ƙetare Yodan zuwa ƙasar Kan'ana,
\v 11 sa'an nan zaku zaɓi birane su zama biranen mafaka dominku, wurin da idan mutum ya kashe wani ba da gangan ba, yana iya guduwa can.
\s5
\v 12 Waɗannan biranen zasu zama mafakarku daga mai ramako, domin kada a kashe mai kisa ba tare da ya gurfana gaban shari'a a gaban jama'ar ba.
\v 13 Za ku zaɓi birane shida a matsayin birnin mafaka.
\s5
\v 14 Dole ku shirya birane uku a ƙetaren Yodan, uku kuma a cikin ƙasar Kan'ana. Za su zama birane na mafaka.
\v 15 Domin jama'ar Isra'ila, domin baƙi, domin kowanne mai zama tare da ku, waɗannan birane shida zasu zama maku mafaka ga duk wanda ya kashe wani ba da gangan ba yana iya gudu can.
\s5
\v 16 Amma idan mutumin mai kisan ya bugi wani da ƙarfe, idan kuma mutumin ya mutu, to mutumin tabbas mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi.
\v 17 Idan wani mutum ya bugi wani da dutse cikin hannunsa dake iya kashe wani, idan kuma mutumin ya mutu, to tabbas wannan mutumin mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi.
\v 18 Idan mutum mai kisa ya bugi wani mutum da makami na sanda dake iya kashe wani mutumin, idan kuma mutumin ya mutu, to tabbas wannan mutumin mai kisan kai ne. Lallai dole a kashe shi.
\s5
\v 19 Mai ramakon jini zai kashe mai kisan. Idan ya same shi, mai ramakon jini sai ya kashe shi.
\v 20 Idan ya bugi wani da ƙiyayya ko ya wurga masa wani abu, yayin da yake ɓuya domin ya yi masa kwanto, har mutumin ya mutu,
\v 21 ko idan ya buge shi ƙasa da ƙiyayya da hannunsa har mutumin ya mutu, to mai kisan da ya buge shi dole za a kashe shi. Shi mai kisan kai ne. Mai ramakon jini na iya kashe mai kisan kan idan ya gãmu da shi.
\s5
\v 22 Amma idan mutumin mai kisan ya bugi wani nan da nan ba tare da ya shirya ƙiyayya ko ya wurga wani abin da ya buge shi ba tare da ya yi niyar yin hakan ba
\v 23 ko ya wurga dutsen dake iya kashe shi ba tare da ya gan shi ba, don haka mai kisan bai zama maƙiyin sa ba; ba ƙoƙarin cutar da mutumin ya yi ba. Amma ga abin da za a yi idan mutumin ya mutu har wa yau.
\s5
\v 24 Idan haka ne, jama'ar zasu yi shari'a tsakanin mai kisan da mai ramakon jinin da waɗannan sharuɗa.
\v 25 Jama'ar zasu kuɓutar da mai kisan daga ikon mai ramakon jinin. Su jama'ar zasu komo da mai kisan kan zuwa birnin ramakon wanda asali ya guje daga gare shi. Za ya zauna a wurin har sai bayan mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai-tsarki.
\s5
\v 26 Amma idan mai kisan ya fita daga iyakar birnin mafakan da ya gudu zuwa gare ta,
\v 27 idan kuma mai ramakon jini ya gamu da shi a wajen iyakar birninsa na mafaka, idan kuma ya kashe mutumin mai kisan, mai ramakon jini ba zai zama mai laifi game da kisan kai ba.
\v 28 Dalili kuwa shi ne mutumin mai kisan kai da bai fito daga cikin birnin mafaka ba har sai babban firist ya mutu. Bayan mutuwar babban firist, mai kisan kan na iya komawa ƙasarsa inda gãdonsa yake.
\s5
\v 29 Waɗannan dokokin zasu zama maku farillai dominku cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan inda kuka zauna.
\v 30 Duk wanda ya kashe wani, za a kashe mai kisan, kamar yadda aka yi shaida daga shaidu. Amma shaidar mutum ɗaya baza ta iya sa a kashe mutum ba.
\s5
\v 31 Haka kuma, ba zaku karbi ɗiyya domin ran mai kisa wanda aka iske shi da laifin kisa ba. Dole a kashe shi.
\v 32 Ba zaku karbi ɗiyya domin wanda ya gudu zuwa birnin mafaka ba. Da haka ba zaku yardar ma sa ya zauna bisa gãdonsa ba har sai babban firist ya mutu.
\s5
\v 33 Kada ku ƙazantar da wannan ƙasar da kuke zama a cikinta ta yin haka, gama jinin da aka zubar ta hanyar kisa na ƙazantar da ƙasa. Babu kafarar da za a iya yi domin ƙasar yayin da aka zubar da jini bisanta, sai dai da jinin shi wanda ya zubas da jinin.
\v 34 Don haka baza ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama cikinta ba domni ina zama cikinta. Ni, Yahweh, ina zaune cikin mutanen Isra'ila."'
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Sa'an nan shugabanni na gidajen kakannin iyalai na zuriyar Giliyad ɗan Makir (wanda shi ne ɗan Manasse), waɗanda suke daga zuriyar Yusufu, suka iso suka yi magana da Musa da a gaban shugabanni waɗanda ke kan gaba daga gidajen kakanni na mutanen Isra'ila.
\v 2 Suka ce, "Yahweh ya umarce ka, ubangidanmu, ka bada rabon ƙasa bisa ga ƙuri'a ga mutanen Isra'ila. Yahweh ya umarce ka da ka bada rabon Zelofehad ɗan'uwanmu ga 'ya'yansa mata.
\s5
\v 3 Amma idan 'ya'yansa mata suka yi aure zuwa wata ƙabilar mutanen Isra'ila, sai gãdonsu na ƙasa a cire daga gãdon dake na ubanninmu. Za a ƙara bisa gãdon dake na ƙabilar da dã suka shiga. Don haka, za a cire daga namu gãdon.
\v 4 Don haka, idan shekarar Yubili na mutanen Isra'ila ta zo, sai a harɗa gãdonsu da gãdon kabilar da suka yi aure. Ta haka, za a cire gãdonsu daga gãdon kabilar kakanninmu."
\s5
\v 5 Sai Musa ya ba da umarni ga mutanen Isra'ila, bisa ga maganar Yahweh. Ya ce, "Abin da kabilar zuriyar Yosef suka ce dai-dai ne.
\v 6 Wannan ne abin da Yahweh ya faɗa game da 'ya'ya mata na Zelofehad. Ya ce, 'Bari su auri duk wanda ya yi masu dai-dai, amma dole ne su yi aure daga cikin zuriyar iyalin mahaifinsu.'
\s5
\v 7 Kada a canza gãdon wata kabilar mutanen Isra'ila zuwa ga wata kabilar. Duk mutumin Isra'ila dole ya ci gaba da zama da nasa gãdo na kabilar ubanninsa.
\s5
\v 8 Kowacce ɗiya ta mutanen Isra'ila wadda take da gãdo cikin kabilarta za ta auri wani daga zuriyar mahaifinta. Wannan zai zama haka domin dukkan mutanen Isra'ila su ajiye abin gãdonsu daga ubanninsu.
\v 9 Babu gãdon da za a ɗauka daga kabila ɗaya zuwa wata kabilar. Kowacce kabila ta mutanen Isra'ila za ta riƙe nata abin gãdon.
\s5
\v 10 Sai 'ya'ya ɗiyan Zelofehad suka aikata kamar yadda Yahweh ya umarce Musa.
\v 11 Mahal, Tirza, Hogla, Milka, da Nowa, 'ya'ya mata na Zelofehad, suka auri zuriyar Manasse.
\v 12 Suka yi aure cikin dangin iyalin Manasse ɗan Yosef. Ta haka, gãdonsu ta kasance tare da kabilar da mahaifinsu ya fito.
\s5
\v 13 Waɗannan su ne umarnai da shari'un da Yahweh ya bai wa mutanen Isra'ila ta bakin Musa a cikin kwarurukan Mowab a bakin Yodan a Yeriko.