ha_ulb/03-LEV.usfm

1692 lines
126 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id LEV
\ide UTF-8
\h Littafin Lebitikus
\toc1 Littafin Lebitikus
\toc2 Littafin Lebitikus
\toc3 lev
\mt Littafin Lebitikus
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 Yahweh ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin rumfar taruwa, ya ce,
\v 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana ka gaya masu cewa, 'Sa'ad da waninku ya kawo baiko ga Yahweh, sai ya kawo baikon dabbar daga cikin dabbobinsa, daga garken shanu ko kuma na tumaki.
\s5
\v 3 Idan baikonsa baiko ne na ƙonawa daga garken shanu, dole ya miƙa namiji marar lahani. Zai miƙa shi a ƙofar rumfar taruwa, domin ya zama karɓaɓɓe a gaban Yahweh.
\v 4 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko na ƙonawar, sa'an nan za a karɓa daga gare shi a yi masa kaffara domin shi kansa.
\s5
\v 5 Dole ne ya yanka bijimin a gaban Yahweh. 'ya'yan Haruna maza, firistoci, zasu miƙa jinin su yayyafa shi a kan bagadi wanda ya ke a bakin ƙofar rumfar taruwa.
\v 6 Sa'an nan dole ya feɗe baikon ƙonawar ya kuma yanyanka shi gunduwa-gunduwa.
\s5
\v 7 Sa'an nan 'ya'ya maza na Haruna firist zasu kunna wuta a kan bagadin su sa itace domin iza wutar.
\v 8 'Ya'yan Haruna maza, firistoci zasu jera gunduwa-gunduwar nan, za su sa kan da fari sa'an nan kitsen a jere haka a kan itacen da ke bisa wutar da ke kan bagadi.
\v 9 Amma kayan cikinsa da ƙafafuwansa dole ya wanke su da ruwa. Sa'an nan firist zai ƙona dukka a kan bagadi a matsayin baiko na ƙonawa. Zai ba da ƙamshi mai daɗi a gare ni; zai zama baikon da aka yi mani da wuta.
\s5
\v 10 Idan baikonsa domin baiko na ƙonawa ne daga cikin garke, ɗaya daga cikin tumaki ko ɗaya daga cikin awaki, dole ya miƙa namiji marar lahani.
\v 11 Dole ya yanka shi a arewacin bagadin a gaban Yahweh. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, zasu yayyafa jinin a kowanne gefen bagadin.
\s5
\v 12 Sa'an nan dole zai yanka shi gunduwa-gunduwa, tare da kansa, da kuma kitsensa, firist zai jera su dai-dai akan itace da ke kan wuta, wadda take kan bagadi, amma kayan ciki da ƙafafun dole ya wanke su da ruwa.
\v 13 Sa'an nan firist zai miƙa dukka, ya ƙona shi a kan bagadin. baiko na ƙonawa ne, zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta.
\s5
\v 14 Idan baikonsa ga Yahweh zai zama baiko na ƙonawa na tsuntsaye, to dole ya kawo baikon kurciya ko 'yar tantabara.
\v 15 Dole firist ya kawo shi ga bagadi, ya murɗe kansa, ya ƙona shi a kan bagadin. Sa'an nan dole a tsiyaye jininsa a gefen bagadin.
\s5
\v 16 Dole ya cire ƙururunsa da abin da ke cikinsa, ya jefar da shi a gabashin bagadin a gefe, wurin da ake zuba toka.
\v 17 Dole ya tsaga shi biyu ya buɗe shi daga fukafukansa, amma ba zai raba shi biyu ba. Sa'an nan firist zai ƙona shi a kan bagadin, a kan itacen da ke kan wuta. Zai zama baiko na ƙonawa, kuma zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baiko da aka yi masa da wuta.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 Sa'ad da wani ya kawo baikon hatsi ga Yahweh, dole ne baikonsa ya zama na gari mai laushi, kuma ya zuba mai a kai ya sa turare a kai.
\v 2 Zai kai baikon ga 'ya'yan Haruna maza firistoci, a can firist zai ɗibi tafi guda na garin mai laushi tare da mai da turare da ke kansa. Sa'an nan firist zai ƙona baikon a kan bagadin baiko na tunawa kenan. Zai ba da ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta.
\v 3 Duk ragowar baiko na garin hatsi zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza. Mafi tsarki ne sosai ga Yahweh domin daga baye-baye ne da aka yi wa Yahweh da wuta.
\s5
\v 4 Sa'ad da kuka miƙa baiko na garin hatsi da babu gami da aka toya a tanda, dole ya zama waina mai laushi da aka yi da lallausar gari cuɗe da mai, ko waina mai tauri da bata da gami, da aka yayyafa mata mai.
\v 5 Idan baikonku na garin hatsi an toya shi a tandar ƙarfe ne, dole ya zama gari mai laushi marar gami cuɗaɗɗe da mai.
\s5
\v 6 Za ku yanyanka shi gunduwa-gunduwa a zuba mai a kai. Wannan shi ne baiko na hatsi.
\v 7 Idan baikonku na garin hatsi an dafa a tukunyar tuya ne, dole a yi shi da gari mai laushi da mai.
\s5
\v 8 Dole ku kawo baiko na garin hatsi da aka yi su daga waɗannan abubuwa ga Yahweh, za a kuma miƙa su ga firist, wanda zai kawo su wurin bagadi.
\v 9 Sa'an nan firist zai ɗauki wasu daga baiko na garin hatsin domin ya zama baikon madadi, zai kuma ƙona su a kan bagadin. Zai zama baikon da aka yi da wuta, zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh.
\v 10 Ragowar baikon garin hatsi zai zama na Haruna da 'ya'yansa maza. Abu ne mafi tsarki ga Yahweh daga cikin baye-baye da aka yi ga Yahweh da wuta.
\s5
\v 11 Kada baiko na garin hatsi da za ku miƙa wa Yahweh ya zama da gami, gama ba za ku ƙona gami ba, ko zuma, a baikon da aka yi da wuta ga Yahweh.
\v 12 Za ku miƙa su ga Yahweh a madadin baikon nunar fari, amma ba za a yi amfani da su don su bada ƙamshi mai daɗi a kan bagadi ba.
\v 13 Dole kowanne baye-bayenku na garin hatsi a sa masa ɗanɗanon gishiri. Kada ku fasa sa gishiri na alƙawari na Allahnku a cikin baikonku na garin hatsi. Cikin dukkan baye-bayenku dole ku miƙa gishiri.
\s5
\v 14 Idan kuka miƙa baikon hatsin nunar fari ga Yahweh, ku miƙa sabon hatsi wanda aka gasa da wuta sa'an nan aka ɓarza,
\v 15 Sai ku sa mai da turare a kai. Wannan shi ne baiko na garin hatsi.
\v 16 Sa'an nan firist zai ƙona wasu daga cikin ɓarzajjen hatsin da mai da turare sun zama baiko na madadi. Wannan baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 Idan wani ya miƙa hadayarsa wanda baiko ne na zumunta na dabba daga garken shanu, ko namiji ko mace, dole ya miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Yahweh.
\v 2 Zai ɗibiya hannusa a kan baikonsa ya yanka ta a ƙofar rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza firistoci zasu yayyafa jinin kewaye da bagadin.
\s5
\v 3 Mutumin zai miƙa hadayar baiko na zumunta da wuta ga Yahweh. Ƙitsen da ya rufe ko kuma da ke haɗe da kayan ciki,
\v 4 da ƙodoji biyu, da ƙitsen da ya ke kansu a wajen kwiɓi, da na taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai cire dukkan waɗannan.
\v 5 'Ya'yan Haruna maza zasu ƙona wannan a kan bagadi tare da baiko na ƙonawa, wanda ya ke a kan itacen da ya ke kan wuta. Wannan zai bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh; zai zama baikon da aka yi masa da wuta.
\s5
\v 6 Idan hadayar mutumin baikon zumunta ne ga Yahweh daga cikin garken tumaki; namiji ko mace, dole ya miƙa hadaya marar lahani.
\v 7 Idan ya miƙa ɗan rago domin hadaya, to dole ya miƙa shi a gaban Yahweh.
\v 8 Zai ɗibiya hannunsa a kan hadayar ya yanka shi a gaban rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza zasu yayyafa jinin kewaye da bagadin.
\s5
\v 9 Mutumin zai miƙa hadayar baye-bayen zumunta domin baiko da aka yi da wuta ga Yahweh. Kitsen, dukkan kitse na wajen wutsiya da aka yanke kusa da ƙashin baya, da kitsen da ya rufe kayan ciki da dukkan kitsen da ke kusa da kayan ciki,
\v 10 da kuma ƙodojin biyu da kitsen da ke tare da su, wanda ke kusa da kwiɓi, da na taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai cire duk waɗannan.
\v 11 Sa'an nan firist zai ƙona su dukka a kan bagadi ya zama baiko na ƙonawa na abinci ga Yahweh.
\s5
\v 12 Idan baikon mutumin akuya ce, to zai miƙa ta a gaban Yahweh.
\v 13 Dole ya ɗibiya hannunsa a kan akuyar ya yanka ta a gaban rumfar taruwa. Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza za su yayyafa jinin kewaye da bagadi.
\v 14 Mutumin zai miƙa hadayarsa da ya yi da wuta ga Yahweh. Zai cire kitsen da ya rufe kayan ciki, da kuma dukkan kitsen da ke kusa da kayan cikin.
\s5
\v 15 Zai kuma cire ƙodojin biyu da kitsen da ke tare da su, wanda ke wajen kwiɓi, da wajen taiɓar hanta tare da ƙodoji.
\v 16 Firist zai ƙona dukkan waɗannan a kan bagadi ya zama baiko na ƙonawa na abinci, da zai bada ƙamshi mai daɗi. Duk kitsen ya zama na Yahweh.
\v 17 Zai zama madawwamin farilla ga dukkan tsararrakin jama'arku a ko'ina da kowanne wuri da kuka maida shi mazauninku, cewa ba za ku ci kitse ba ko jini.'"
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Yahweh ya yi wa Musa magana, ya ce,
\v 2 "Ka gaya wa mutanen Isra'ila, 'Lokacin da wani ya yi zunubi ba da niyyar yin zunubi ba, ya yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya dokata kada a yi, idan ya yi abin da aka hana, ga abin da dole za a yi.
\v 3 Idan babban firist ne ya yi zunubin har ya kawo laifi a kan jama'a, domin zunubinsa da ya aikata sai ya miƙa ɗan maraƙi marar lahani ga Yahweh baiko don zunubi kenan.
\s5
\v 4 Dole ya kawo bijimin ƙofar rumfar taruwa a gaban Yahweh, ya ɗibiya hannunsa a kansa, ya yanka shi a gaban Yahweh.
\v 5 Keɓaɓɓen firist zai ɗiba daga jinin bijimin ya kai rumfar taruwa.
\s5
\v 6 Firist zai tsoma ɗan yatsansa cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Yahweh, a gaban labulen wuri mafi tsarki.
\v 7 Sa'an nan firist zai sa daga jinin a ƙahonnin bagadin na turare mai ƙamshi a gaban Yahweh, wanda ya ke cikin rumfar taruwa, zai kuma zuba dukkan sauran jinin bijimin a gindin bagadi domin baye-baye na ƙonawa, wanda ya ke a ƙofar rumfar taruwa.
\s5
\v 8 Zai yaɗe dukkan kitsen bijimin baiko don zunubi; kitsen da ya rufe kayan ciki, da dukkan kitsen da ke manne da kayan ciki,
\v 9 da ƙodojin biyu da kitsen da ke bisansu, wanda ke wajen kwiɓi, da taiɓar hanta, tare da ƙodoji - zai yanke duk wannan.
\v 10 Zai yanke shi dukka, kamar yadda ya yanke shi daga bijimi na hadayar baye-baye ta salama. Sa'an nan firist zai ƙona waɗannan ɓangare akan bagadin baye-bayen ƙonawa.
\s5
\v 11 Fatar bijimin da duk sauran naman, da kan da ƙafafunsa da kayan cikinsa da kashinsa,
\v 12 da dukkan sauran sashen bijimin - zai ɗauki dukkan waɗannan ya kai bayan sansani wurin da aka tsarkake domina, inda ake zuba toka; zasu ƙona waɗannan a bisa itace. Dole su ƙona waɗannan ragowar bijimin inda suke zubar da toka.
\s5
\v 13 Idan dukkan taron Isra'ila suka yi zunubin da ba na ganganci ba, kuma taron ba su san sun yi zunubi ba idan suka yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya umarta kada su yi, idan sunyi laifin,
\v 14 sa'annan, yayin da zunubin da suka aikata ya zama sananne, dole taron su miƙa ɗan bijimi baiko wato baiko don zunubi a kuma kawo shi gaban rumfar taruwa.
\v 15 Dattawan taro zasu ɗibiya hannuwansu a bisa kan bijimin a gaban Yahweh, za a yanka bijimin a gaban Yahweh.
\s5
\v 16 Keɓaɓɓen firist zai kawo daga jinin bijimin zuwa rumfar taruwa,
\v 17 firist kuma zai tsoma yatsansa cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Yahweh, a gaban labule.
\s5
\v 18 Zai sa daga jinin a ƙahonnin bagadin da ke gaban Yahweh, wanda ya ke cikin rumfar taruwa, zai kuma zuba jinin dukka a gindin bagadin baye-baye na ƙonawa, wanda ya ke a kofar rumfar taruwa.
\v 19 Zai ɗebe dukkan ƙitsen daga gare shi ya ƙona a kan bagadi.
\s5
\v 20 Wannan shi ne abin da zai yi dole da bijimin. Kamar yadda ya yi da bijimin baiko don zunubi, haka kuma zai yi da wannan bijimin, firist kuma zai yi kaffara domin mutane, za a kuma gafarta masu.
\v 21 Zai ɗauki bijimin ya kai shi bayan zango ya ƙona kamar yadda ya ƙona bijimi na farko. Wannan shi ne baiko don zunubi saboda taron.
\s5
\v 22 Sa'ad da shugaba ya yi zunubi ba dagangan ba, har ya yi ɗaya daga cikin dukkan abubuwan da Yahweh Allahnsa ya umarta ka da a yi, kuma ya yi laifin,
\v 23 sai aka sanar da shi a kan zunubin da ya aikata, dole ya kawo hadayarsa ta akuya, bunsuru marar lahani.
\s5
\v 24 Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun ya yanka shi inda aka yanka baiko na ƙonawa a gaban Yahweh. Wannan shi ne baiko domin zunubi.
\v 25 Firist zai tsoma ɗan yatsansa cikin jinin baiko domin zununbi ya sa shi a ƙahonnin bagadin domin baye-baye na ƙonawa, sai ya kuma zuba jinin a gindin bagadin baiko na ƙonawa.
\s5
\v 26 Zai ƙona dukkan kitsen a kan bagadi, dai-dai kamar na kitsen hadayar baye-baye na salama. Firist zai yi kafara domin shugaban game da zunubinsa, za a kuwa gafarta wa shugaban nan.
\s5
\v 27 Idan wani talaka ya yi zunubi ba dagangan ba, sai ya yi wani abu daga cikin abubuwan da Yahweh ya umarta kada a yi, idan ya gane laifinsa,
\v 28 sa'an nan za a bayyana masa zunubinsa, sai ya kawo akuya domin hadayarsa, ta mace marar lahani, domin zunubin da ya aikata.
\s5
\v 29 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko domin zunubi ya kashe baikon don zunubin a wurin yin baiko na ƙonawa.
\v 30 Firist zai lakuto daga jinin a yatsansa ya sa a ƙahonnin bagadi domin baye-baye na ƙonawa. Zai zuba dukkan sauran jinin a gindin bagadin.
\s5
\v 31 Zai yaɗe dukkan kitsen, dai-dai kamar yadda ya yaɗe kitsen da ke kan hadayar baye-baye na salama. Firist zai ƙona su a kan bagadi domin ya bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh. Firist zai yi kaffara domin mutumin, za a kuwa gafarta masa.
\s5
\v 32 Idan mutumin ya kawo ɗan rago domin hadayarsa ta baiko domin zunubi, zai kawo mace marar lahani.
\v 33 Zai ɗibiya hannunsa a kan baiko domin zunubi sai kuma a yanka ta saboda baiko domin zunubi a inda aka yanka baiko na ƙonawa.
\s5
\v 34 Firist zai ɗiba daga jinin baiko domin zunubi a ɗan yatsansa yasa su a kan ƙahonnin bagadi domin baye-baye na ƙonawa, zai zuba dukkan jinin a gindin bagadi.
\v 35 Zai yaɗe dukkan kitsen, kamar yadda aka yaɗe kitsen ɗan rago daga hadayar baye-bayen salama, firist zai ƙona shi a kan bagadi a bisa baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta. Firist zai yi kaffara saboda shi domin zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Idan wani ya yi zunubi domin bai bada shaida ba sa'ad da ya ga wani abu game da abin da yakamata ya yi shaida, ko ya gani, ko kuwa yaji akan abin, za a kama shi da laifi.
\v 2 Ko wani ya taɓa wani abin da Allah ya haramta shi marar tsarki, ko mushen haramtacciyar dabbar jeji ko ta gida da ta mutu, ko dabba mai rarrafe, ko da mutumin bai yi niyyar taɓa ta ba, ya ƙazamtu, ya kuma zama da laifi.
\s5
\v 3 Ko kuma idan ya taɓa ƙazamtar wani mutum, ko ma mene ne ƙazamtar, idan har bai sani ba, zai zama da laifi bayan an sanar da shi.
\v 4 Ko kuma wani ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa zai yi mugunta, ko ya yi nagari, ko mene ne mutum ya rantse da garaje, ko ma dai da rashin saninsa, idan an sanar da shi, zai zama da laifi a cikin abubuwan nan.
\s5
\v 5 Idan wani yana da laifi ko da guda ɗaya ne daga cikin waɗannan abubuwa, dole ya furta kowanne zunubi da ya aikata.
\v 6 Dole ya kawo wa Yahweh baiko na laifi domin zunubin da ya aikata, dabba mace daga cikin garke ko ɗan rago ko akuya, domin baiko na zunubi, firist kuma zai yi kaffara dominsa game da zunubinsa.
\s5
\v 7 Idan ba zai iya sayan ɗan rago ba, sai ya kawo baikonsa na laifi domin zunubinsa kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu ga Yahweh, ɗaya domin baiko na laifi ɗaya kuma domin baiko na ƙonawa.
\v 8 Dole ya kawo su ga firist, wanda zai miƙa ɗaya domin baiko domin zunubi da fari - zai murɗe kan daga wuya amma ba zai cire shi ɗungum daga jikinsa ba.
\v 9 Sa'an nan zai yayyafa kaɗan daga cikin jinin baikon domin zunubi a gefen bagadi, sauran jinin zai tsiyayar a gindin bagadi. Wannan shi ne baiko domin zunubi.
\s5
\v 10 Sa'an nan dole ya miƙa tsuntsu na biyu domin baiko na ƙonawa, kamar yadda aka bayyana a cikin farillai, sai firist kuma ya yi masa kaffara domin zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin.
\s5
\v 11 In kuwa ba zai iya sayan kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu ba, sai dole ya kawo hadaya domin zunubinsa tiya biyu na gari mai laushi saboda baiko domin zunubi. Ba zai sa mai ko turare a kai ba, saboda baiko ne domin zunubi.
\s5
\v 12 Dole ne ya kawo shi ga firist, firist kuma zai ɗiba dai-dai tafin hannu ya zama baiko domin tunawa Sa'an nan zai ƙona shi a kan bagadi, a bisa baye-baye da aka yi da wuta domin Yahweh. Wannan baiko domin zunubi kenan.
\v 13 Firist zai yi kaffara domin kowanne zunubin da mutumin ya aikata, za a kuwa gafarta wa mutumin nan. Duk ragowa daga baikon zai zama rabon firist, kamar dai baiko na hatsi.'"
\s5
\v 14 Sa'an nan Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa,
\v 15 "Idan wani ya yi zunubi ya aikata rashin aminci game da abubuwan da ke na Yahweh, amma ba dagangan ba, to dole ya kawo baiko domin laifi ga Yahweh. Wannan baiko dole ya zamana rago marar lahani daga garken tumaki; za a lisafta tamaninsa da ma'aunin azurfar - ma'auni na masujada - domin baiko na laifi.
\v 16 Dole ya gamshi Yahweh domin abin da ya yi marar kyau game da abu mai tsarki, dole kuma ya ƙara kashi ɗaya cikin biyar a kai domin ya ba firist. Sa'an nan firist zai yi masa kafara da ragon baiko na laifi, za a kuwa gafarta wa mutumin nan.
\s5
\v 17 Idan wani ya yi zunubi har ya yi wani abin da Yahweh ya bada doka kada a yi, idan ma bai ankara da yinsa ba, duk da haka ya yi laifi dole ne ya amsa laifinsa.
\v 18 Dole ya kawo rago marar lahani daga cikin garke, dai-dai tamanin kuɗinsa a yanzu, domin baiko domin laifi ga firist. Sa'an nan firist zai yi masa kaffara game da zunubin da ya aikata, wanda ya yi da rashin sani, za a kuwa gafarta masa.
\v 19 Baiko ne domin laifi, kuma hakika yana da laifi a gaban Yahweh."
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa,
\v 2 "Idan wani ya yi abin rashin aminci gãba da Yahweh ta wurin yaudarar makwabcinsa game da wani abin da aka bashi riƙon amana, ko game da wani abin da aka sace, ko dai ya yi ta zaluntar makwabcinsa,
\v 3 ko ya tsinci abin da makwabcinsa ya ɓatar ya yi musu a kansa, ya kuma rantse a kan ƙaryar, ko duk dai cikin abubuwa makamantan haka da mutane ke zunubi,
\v 4 idan ya zamana ya yi zunubi, har aka same shi mai laifi ne, dole ne ya mayar da abin da ya karɓe da ƙwace ko ta hanyar zalunci, ko ta ajiyar da aka bashi riƙon amana ko ta abin da ya ɓace ya kuma tsinta.
\s5
\v 5 Bugu da ƙari, a cikin kowanne al'amari da ya rantse a kan karya, dole ya mayar cif yadda ya ke ya kuma ƙara kashi ɗaya cikin biyar na tamanin abin da ya biya dukka ga mai ita a ranar da aka kama shi da laifi.
\v 6 Sa'an nan zai kawo wa Yahweh baiko na laifinsa, rãgo marar lahani daga cikin garke wanda tamaninsa haka ya ke a kasuwa, domin baiko na laifi ga firist.
\v 7 Firist zai yi masa kaffara a gaban Yahweh, za a kuma gafarta masa game da duk wani laifi da ya yi."
\s5
\v 8 Sa'an nan Yahweh ya yi wa Musa magana, cewa,
\v 9 "Ka dokaci Haruna da 'ya'yansa maza, cewa, 'Wannan ita ce dokar baiko na ƙonawa: Dole baiko na ƙonawa ya kasance a kan garwashin wutar bagadi dukkan dare har safiya, kuma wutar bagadin za a dinga izata tayi ta ci.
\s5
\v 10 Firist zai sanya rigunansa na lilin, zai kuma sa ƙananan kaya 'yan ciki na lilin. Zai kwashe tokar da ta rage bayan wuta ta cinye baiko na ƙonawa da ke kan bagadi, zai kuma sa tokar a gefen bagadin.
\v 11 Zai tuɓe rigunansa ya sa wasu rigunan domin ya kai tokar bayan zango a wuri mai tsabta.
\s5
\v 12 Wutar da ke kan bagadi za a dinga iza ta. Ba za a barta ta mutu ba, firist zai yi ta ƙona itace a kanta kowacce safiya. Zai shirya baiko na ƙonawa yadda ya kamata a bisansa, a kansa zai ƙona kitsen baye-baye na salama.
\v 13 Dole a sa wuta ta yi ta ci a kan bagadin ba fasawa. Kada a bari ta mutu.
\s5
\v 14 Wannan ita ce shari'a ta baiko na hatsi. 'Ya'yan Haruna maza zasu miƙa shi a gaban Yahweh a gaban bagadi.
\v 15 Firist zai ɗibi tafin hannu na lallausar gari daga cikin baiko na garin hatsi da na mai da kuma turare wanda ya ke a kan baiko na garin hatsi, zai ƙona shi a kan bagadin domin ya bada ƙamshi mai daɗi domin baiko na madadi.
\s5
\v 16 Haruna da 'ya'yansa maza zasu ci duk abin da ya rage daga baikon. Dole a ci shi ba gami a wuri mai tsarki. Za su ci shi a harabar rumfar taruwa.
\v 17 Ba za a toya shi da gami ba. Na ba su wannan kason ya zama nasu rabon daga nawa baye-baye da aka yi mani da wuta. Abu ne mafi tsarki, kamar baiko domin zunubi da baiko domin laifi.
\v 18 Domin dukkan lokatai masu zuwa dukkan tsararrakin mutanenku, kowanne ɗa namiji daga zuriyar Haruna zai iya cin rabonsa, daga baye-baye ga Yahweh da aka yi da wuta. Duk wanda ya taɓa su zai tsarkaka.'"
\s5
\v 19 Sai Yahweh ya sake yin magana da Musa, cewa,
\v 20 "Wannan shi ne baikon Haruna da 'ya'yansa maza, wanda zasu miƙa wa Yahweh a ranar da aka keɓe kowanne ɗa: kashi ɗaya cikin goma na garwar lallausar gari domin baiko na hatsi koyaushe, rabinsa da safe rabi kuma da maraice.
\s5
\v 21 Za a yi shi da mai a kaskon tuya. Sa'ad da aka jiƙa shi, za ku kawo shi ciki. A toye curi-curi za ku miƙa baiko na garin hatsi domin ya bada ƙamshi mai daɗi ga Yahweh.
\v 22 Ɗan babban firist wanda zai gaji babban firist daga cikin 'ya'yansa zai miƙa shi. Kamar yadda aka umarta har abada, za a ƙona shi dukka ga Yahweh.
\v 23 Kowanne baiko na garin hatsi na firist za a ƙona shi ƙurmus. Ba za a ci shi ba."
\s5
\v 24 Yahweh ya sake yin magana da Musa, cewa,
\v 25 "Ka yi wa Haruna da 'ya'yansa maza magana, cewa, "Wannan ita ce dokar baiko domin zunubi: Dole a kashe baiko domin zunubi inda aka kashe baiko na ƙonawa a gaban Yahweh. Abu ne mafi tsarki.
\v 26 Firist da ya miƙa shi don zunubi zai ci shi. Dole a ci shi a wuri mai tsarki a harabar rumfar taruwa.
\s5
\v 27 Duk abin da ya taɓa naman zai zama da tsarki, kuma idan aka yayyafa jinin akan wata riga, dole ku wanke ta, wannan shashen da ya ɗiga a kai, a wuri mai tsarki.
\v 28 Amma tukunyar yunɓun da aka dafata a ciki dole a fashe ta. Idan an dafa ne a tukunyar ƙarfe, dole ne a kankare ta a ɗauraye ta cikin ruwa mai tsabta.
\s5
\v 29 Kowanne ɗa namiji daga cikin firistoci zai iya ci daga ciki domin mafi tsarki ne.
\v 30 Amma kowanne baiko domin zunubi wanda aka kawo jininsa a rumfar taruwa domin a yi kaffara a wuri mai tsarki ba za a ci shi ba. Dole ne a ƙona shi.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Wannan ita ce dokar baiko domin laifi. Mafi tsarki ne.
\v 2 Dole a kashe baiko domin laifi a mayankarsa, dole kuma su yayyafa jininsa a kowanne gefen bagadi.
\v 3 Dukkan kitsen da ke cikinsa za a miƙa shi: kitsen wutsiya, da kitsen da ke a kan kayan ciki,
\v 4 da ƙodojin biyu da kitsen da ke bisan su, wanda ke kusa da kwiɓi, da wanda ya rufe hanta, tare da ƙodoji - duk wannan dole a cire su.
\s5
\v 5 Dole firist ya ƙona waɗannan sassa a kan bagadin shi ne baikon da aka yi da wuta ga Yahweh. Wannan shi ne baiko domin laifi.
\v 6 Kowanne namiji daga cikin fistoci zai iya ci daga wannan baikon. Dole ne a ci shi a wuri mai tsarki domin mafi tsarki ne.
\s5
\v 7 Baiko domin zunubi kamar baiko domin laifi ya ke. Doka guda ce domin su biyun. Za su zama na firist wanda ya ke yin kaffara da su.
\v 8 Firist wanda ya miƙa wa wani baikonsa na ƙonawa zai iya ɗaukar wa kansa fatar wannan baikon.
\s5
\v 9 Kowanne baiko na garin hatsi da aka toya a cikin tanda, da kowanne makamancin baiko da aka dafa a tukunya ko a kaskon tuya zai zama na firist da ya miƙa baikon.
\v 10 Kowanne baiko na garin hatsi, ko busasshe ko kwaɓaɓɓe da mai, za su zama rabon dukkan zuriyar Haruna dai-dai wa dai-da.
\s5
\v 11 Wannan ita ce shari'ar hadayar baye-baye na salama wadda mutane za su miƙa ga Yahweh.
\v 12 Idan wani ya miƙa shi domin ya yi godiya, to dole ya miƙa shi da hadayar waina da aka yi ba a sa gami ba, amma kwãɓe da mai, waina da aka yi ba gami, amma an shafa masu mai, waina da aka yi ta da lallausar gari da aka kwaɓa da mai.
\s5
\v 13 Kuma domin dalilin miƙa godiya, dole ya miƙa baikonsa na salama tare da wainar gurasa da aka yita da gami.
\v 14 Zai miƙa guda ɗaya na kowanne irin waɗannan hadayu ya zama baikon da aka miƙa ga Yahweh. Zai zama rabon firist wanda ya yayyafa jinin baye-baye na salama a kan bagadi.
\s5
\v 15 Mutumin da ke miƙa baiko na salama domin nuna godiya dole ya ci naman baikonsa a ranar yin hadayar. Kada ya bar ragowar har kashegari da safe.
\v 16 Amma idan hadayar baikonsa domin wa'adi ne, ko kuma domin bayarwar yardar rai, dole a ci naman a ranar da ya miƙa hadayar, amma duk abin da ya rage a ciki za a iya cinsa kashegari.
\s5
\v 17 Amma, kowanne ragowar naman hadaya a rana ta uku dole a ƙone shi.
\v 18 Idan aka ci naman hadayar wani na baikon salama a rana ta uku, ba za a karɓa ba, ba kuma za a lisafta shi ga mai miƙa wa ba. Zai zama abin ƙyama, kuma mutumin da ya ci shi zai ɗauki laifin zunubinsa.
\s5
\v 19 Duk naman da ya taɓa abin da ba tsarki ba za a ci shi ba. Dole a ƙona shi. Game da sauran naman, duk wanda ya ke da tsarki zai iya cin shi.
\v 20 Amma fa, mutum marar tsarki wanda ya ci wani nama daga hadayar baiko na salama wanda ya ke na Yahweh ne- wannan mutum dole a datse shi daga mutanensa.
\s5
\v 21 Idan wani mutum ya taɓa wani abu marar tsarki - ko ƙazamtar mutum ne, ko na ƙazamin dabba, ko na wani abu marar tsarki na ban ƙyama, sa'an nan kuma ya ci daga naman hadayar baiko na salama wanda ya ke na Yahweh ne, wannan mutumin dole a datse shi daga mutanensa.'"
\s5
\v 22 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 23 "Yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, 'Ba za ku ci kitsen sã ko na tunkiya ko na akuya ba.
\v 24 Kitsen dabba mushe da ba a yi hadaya da ita ba, ko kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin amfani da su domin wani abu, amma kada ku kuskura ku ci su.
\s5
\v 25 Ko wane ne ya ci kitsen dabbar da mutane zasu iya miƙa ta hadaya ta ƙonawa ga Yahweh, wannan mutumin dole a datse shi daga mutanensa.
\v 26 Ba za ku ci jini ba daɗai a gidajenku, ko daga tsuntsu ya ke ko dabba.
\v 27 Duk wanda ya ci jini, dole a datse wannan mutum daga mutanensa.'"
\s5
\v 28 Sai Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 29 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, 'Wanda duk ya ke miƙa hadayar baiko na salama ga Yahweh dole ya kawo wani sashen hadayar ga Yahweh.
\v 30 Baiko domin Yahweh da za a yi da wuta, mai ita ne zai kawo da hannunsa. Dole ya kawo kitsen tare da ƙirjin, saboda a kaɗa ƙirjin ya zama baiko don kaɗawa a gaban Yahweh.
\s5
\v 31 Dole ne firist ya ƙona kitsen a kan bagadi, amma ƙirjin zai zama na Haruna da zuriyarsa.
\v 32 Dole a bada cinyar ƙafar dama ga firist a matsayin baikon da aka miƙa daga cikin hadayarku ta baye-baye na salama.
\s5
\v 33 Firist, ɗaya daga cikin dangin Haruna, wanda ya miƙa jinin baye-baye na salama da kitsen - shi zai ɗauki cinyar ƙafar dama rabonsa kenan na baikon.
\v 34 Gama na ɗauka daga mutanen Isra'ila, ƙirjin baiko na kaɗawa, da cinya su zama bayarwarsu, an rigaya an ba Haruna firist da 'ya'yansa maza waɗannan su zama rabonsu koyaushe.
\s5
\v 35 Wannan ne rabon Haruna da zuriyarsa daga baye-bayen da aka yi wa Yahweh da wuta, a ranar da Musa ya miƙa su su yi wa Yahweh hidima a cikin aikin firist.
\v 36 Wannan rabon ne da Yahweh ya umarta a ba su daga mutanen Isra'ila, a ranar da ya keɓe firistoci. Kullum zai zama rabonsu har dukkan tsararraki.
\s5
\v 37 Wannan shi ne shari'ar baiko na ƙonawa, da baiko na hatsi, da baiko domin zunubi, da baiko domin laifi, da baiko na keɓewa, da na hadayar baye-baye na salama,
\v 38 wanda Yahweh ya ba da umarnai ga Musa a kan Tsaunin Sinai a ranar da ya umarci mutanen Isra'ila su miƙa hadayunsu ga Yahweh a jejin Sinai.'"
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa'
\v 2 "Ka ɗauki Haruna da 'ya'yansa maza tare da shi, da riguna, da man ƙeɓewa, da bijimi domin baiko na zunubi, da raguna biyu, da kwandon waina marar gami.
\v 3 Ka tara dukkan taron a ƙofar rumfar taruwa."
\s5
\v 4 Sai Musa ya yi yadda Yahweh ya umarce shi, dukkan taron suka tattaru a ƙofar rumfar taruwa.
\v 5 Sai Musa ya cewa taron, "Ga abin da Yahweh ya umarta a yi."
\s5
\v 6 Musa ya kawo Haruna da 'ya'yansa maza ya wanke su da ruwa.
\v 7 Ya sa wa Haruna riga 'yarciki ya ɗaura masa ɗamara a ƙugunsa, ya sa masa taguwa ya kuma sa masa falmara, sa'an nan ya ɗaura masa falmarar da wata ƙasaitacciyar ɗamara mai kyan ɗinki ya zagaya ƙugunsa da ita ya ɗaure.
\s5
\v 8 Ya sa masa ƙyallen ƙirji, a kan ƙyallen kuma ya sa Urim da Tumim.
\v 9 Ya naɗa masa rawani a kansa, a kan rawanin, a goshi, ya kafa masa tasar zinariya, kambi mai tsarki, kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 10 Musa ya ɗauki man ƙeɓewa, ya keɓe rumfar da dukkan abin da ke cikinta ya keɓe su ga Yahweh.
\v 11 Ya yayyafa man a kan bagadi sau bakwai, ya shafe bagadin da dukkan kayan aikinta, da daron wanki da maɗorinta, saboda a keɓe su domin Yahweh.
\s5
\v 12 Ya zuba wasu man keɓewa akan Haruna ya shafe shi don a keɓe shi.
\v 13 Musa ya kawo 'ya'yan Haruna maza ya suturta su da su riguna 'yanciki. Ya ɗaura masu ɗamara kewaye da ƙugunsu ya ɗaura masu rawanin ƙyallen lilin a kawunansu, kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 14 Musa ya kawo bijimin na baiko domin zunubi, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan bijimin da suka kawo saboda baiko domin zunubi.
\v 15 Ya yanka shi, sai ya ɗauki jinin ya sa a kan ƙahonnin bagadin da ɗan yatsansa, ya tsarkake bagadin, ya zuba jinin a ƙarƙashin bagadin, ya keɓe shi ga Yahweh domin ya yi kaffara domin shi.
\s5
\v 16 Ya ɗauki dukkan kitsen da ke kan kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, da ƙodojin biyu da kitsensu, sai Musa ya ƙona su dukka a kan bagadi.
\v 17 Amma bijimin, da fatarsa, da namansa, da kashinsa ya ƙona su a bayan sansani, kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 18 Musa ya miƙa rãgon domin baiko na ƙonawa, kuma Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan rãgon.
\v 19 Ya yanka shi ya yayyafa jininsa a kowanne gefen bagadin.
\s5
\v 20 Ya yanka rãgon gunduwa gunduwa ya ƙona kan da yankakkun naman da kuma kitsen.
\v 21 Ya wanke kayan cikin da ƙafafun da ruwa, ya kuma ƙona rãgon ɗungum a kan bagadi. Baiko ne na ƙonawa mai bada ƙamshi mai daɗi, baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\v 22 Sa'an nan Musa ya miƙa ɗaya ragon, ragon tsarkakewa, Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan rãgon.
\v 23 Sai Haruna ya yanka shi, Musa kuma ya ɗiba daga jinin ya sa su a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun damansa da bisa babban yatsan ƙafarsa ta dama.
\v 24 Ya kawo 'ya'yan Haruna maza, ya sa daga jinin a kan leɓatun kunnuwansu na dama, da kan manyan yatsan hannuwansu na dama, da kan manyan yatsansu na ƙafafun dama. Sa'an nan Musa ya yayyafa jinin a kowanne gefen bagadin.
\s5
\v 25 Ya ɗauki kitsen, kitsen wutsiya, dukkan kitsen da ke bisa kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, da ƙodojin biyu da kitsensu, da cinyar dama.
\v 26 Daga cikin kwandon gurasa da bata da gami da ke gaban Yahweh, ya ɗauki curi guda na marar gami, da curi guda na gurasa da aka shafe ta da mai, da waina guda, sai ya ɗibiya su bisa kitsen da kuma kan cinyar dama.
\v 27 Ya sa su dukka a hannuwan Haruna da kuma hannuwan 'ya'yansa maza kuma ya kaɗa su a gaban Yahweh domin baiko na kaɗawa.
\s5
\v 28 Sa'an nan Musa ya karɓe su daga hannunsu ya ƙona su a kan bagadi domin baiko na ƙonawa. Baiko ne na keɓewa ya kuma bada ƙamshi mai daɗi. Baiko ne da aka yi da wuta ga Yahweh.
\v 29 Musa ya ɗauki ƙirjin ya kaɗa su don su zama baikon kaɗawa ga Yahweh. Wannan shi ne rabon Musa daga rãgon domin naɗa firist, kamar yadda Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 30 Musa ya ɗiba daga man keɓewa da jinin da ke kan bagadi; ya yayyafa su a kan Haruna, da kan rigunansa, da kan 'ya'yansa maza, da kan rigunan 'ya'yansa maza tare da shi. Da haka ne ya keɓe Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu ga Yahweh.
\s5
\v 31 Sai Musa ya cewa Haruna da 'ya'yansa maza, "Ku dafa naman a ƙofar shiga rumfar taruwa, ku ci a can da gurasar da ke cikin kwandon tsarkakewa, kamar yadda na umarta, cewa, 'Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi.'
\v 32 Duk abin da ya rage daga naman da gurasar dole a ƙona.
\v 33 Ba za ku fita daga ƙofar rumfar taruwa ba har kwana bakwai, sai kwanakin naɗinku sun cika. Domin Yahweh zai tsarkake ku kwana bakwai.
\s5
\v 34 Mene ne aka rigaya aka yi yau - Yahweh ya umarta a yi domin a yi maku kaffara.
\v 35 Za ku zauna dare da rana har kwana bakwai a ƙofar rumfar taruwa, ku yi biyayya da umarnin Yahweh, domin kada ku mutu, domin wannan ne aka umarce ni.
\v 36 Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukkan abubuwan da Yahweh ya umarce su ta wurin Musa.
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 A rana ta takwas Musa ya kira Haruna da 'ya'yansa maza da dattawan Isra'ila.
\v 2 Ya cewa Haruna, "Ka ɗauki ɗan maraƙi daga garke domin baiko na zunubi, da rago marar lahani domin baiko na ƙonawa, ka miƙa su a gaban Yahweh.
\s5
\v 3 Dole ka yi wa mutanen Isra'ila magana ka ce, 'Ku ɗauki bunsuru domin baikon zunubi da kuma ɗan maraƙi da ɗan rãgo, dukka biyun bana ɗaya kuma marasa lahani, domin baiko na ƙonawa;
\v 4 kuma ka ɗauki sã da rãgo domin baiko na salama a yi hadaya ga Yahweh, da baiko na garin hatsi cuɗaɗɗe da mai, domin yau Yahweh zai bayyana a gare ku.'"
\v 5 Sai suka kawo dukkan abin da Yahweh ya umarta zuwa rumfar taruwa, sai dukkan taron Isra'ila suka matso suka tsaya a gaban Yahweh.
\s5
\v 6 Sai Musa ya ce, "Wannan shi ne Yahweh ya umarce ku kuyi domin ɗaukakarsa ta bayyana a gare ku,"
\v 7 Musa ya cewa Haruna, "Ka matso kusa da bagadi ka miƙa baikonka domin zunubi da na ƙonawa, ka yi wa kanka kaffara domin mutane kuma, ka kuma miƙa hadaya domin mutane domin a yi masu kaffara kamar yadda Yahweh ya umarta."
\s5
\v 8 Sai Haruna ya tafi kusa da bagadi ya yanka ɗan maraƙin domin baikon zunubi wanda domin kansa ne.
\v 9 'Ya'yan Haruna suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa cikinsa ya sa a ƙahonnin bagadin; sa'an nan ya zuba jinin a gindin bagadin.
\s5
\v 10 Amma, ya ƙona kitsen, da ƙodojin da wanda ya rufe hanta a kan bagadi domin baikon zunubi, kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\v 11 Da naman da fatar ya ƙona su a bayan sansani.
\s5
\v 12 Haruna ya yanka baiko na ƙonawa, 'ya'yansa maza suka bashi jinin, wanda ya warwatsa a kowanne gefen bagadi.
\v 13 Sa'an nan suka miƙa masa baiko na ƙonawa, gunduwa-gunduwa, tare da kan, sai ya ƙona su a kan bagadi.
\v 14 Ya wanke kayan cikin da ƙafafuwan ya ƙona su a kan baiko na ƙonawa a kan bagadi.
\s5
\v 15 Haruna ya miƙa hadayar mutanen - bunsuru, sai ya ɗauke shi domin hadayar zunubansu ya yanka shi; ya miƙa hadayar ne domin zunubi, kamar yadda ya yi da bunsuru na fari.
\v 16 Ya miƙa baiko na ƙonawa ya miƙa kamar yadda Yahweh ya umarta.
\v 17 Ya miƙa baiko na garin hatsi; ya cika tafin hannunsa da ita ya ƙona ta a kan bagadi, tare da baikon ƙonawa na safe.
\s5
\v 18 Ya kuma yanka san da rãgon, hadaya domin baiko na salama, saboda mutanen. 'Ya'yan Haruna maza suka ba shi jinin, wanda ya yayyafa a kowanne gefen bagadi.
\v 19 Amma, suka yanke kitsen bijimin da na rãgon, da kitsen wutsiyar, da kitsen da ya rufe kayan ciki, da ƙodoji, da wanda ya rufe hanta.
\s5
\v 20 Suka ɗauki sassan da aka yanka suka ɗibiyasu a kan ƙirjin, sa'an nan Haruna ya ƙona kitsen a kan bagadi,
\v 21 Haruna ya kaɗa ƙirjin da cinyar ƙafar dama domin baiko na kaɗawa a gaban Yahweh, kamar yadda Musa ya umarta.
\s5
\v 22 Sa'an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa yana fuskantar mutane ya albarkace su; sai ya dawo daga miƙa baiko na zunubi, baiko na ƙonawa, da baiko na salama.
\v 23 Musa da Haruna suka shiga rumfar taruwa, suka sake fitowa kuma suka albarkaci mutanen, sai ɗaukakar Yahweh ta bayyana ga dukkan mutane.
\v 24 Wuta ta fito daga Yahweh ta cinye baikon ƙonawar da kitsen da ke kan bagadin. Da dai dukkan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suka kwanta fuskokinsu a ƙasa.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Sai Nadab, da Abihu 'ya'yan Haruna maza, kowannensu ya ɗauki farantinsa ya sa wuta a ciki, da kuma turare. Sa'an nan suka miƙa haramtacciyar wuta a gaban Yahweh, wanda bai dokace su su miƙa ba.
\v 2 Saboda haka wuta ta fito daga gaban Yahweh ta hallaka su, suka kuwa mutu a gaban Yahweh.
\s5
\v 3 Sai Musa ya cewa Haruna, "Wannan shi ne Yahweh ya ke magana a kai sa'ad da ya ce, "Zan bayyana tsarkina ga waɗanda suka matso gare ni. Za a ɗaukaka ni a gaban dukkan mutane.'" Haruna bai ce komai ba.
\v 4 Musa ya kira Mishayel da Elzafan, 'ya'ya maza na Uziyel kawun Haruna, ya ce masu, "Ku zo nan ku ɗauki 'yan'uwanku daga cikin sansani daga gaban rumfar taruwa."
\s5
\v 5 Sai suka matso kusa suka ɗauke su, suna saye da rigunansu na firistoci, zuwa bayan sansani, kamar yadda Musa ya umarta.
\v 6 Sai Musa ya ce da Haruna da Eliyazar da kuma Itamar 'ya'yansa maza, "Kada ku bar gashin kanku da tsawo, kada kuma ku kekketa tufafinku, domin kada ku mutu, kuma domin kada Yahweh ya yi fushi da dukkan taro. Amma ku bari 'yan'uwanku wato dukkan gidan Isra'ila, su yi makoki domin waɗanda wutar Yahweh ta babbake.
\v 7 Ba za ku fita daga ƙofar rumfar taruwa ba, ko kuwa ku mutu, gama man shafewa na Yahweh yana kanku." Sai suka aikata bisa ga umarnin Musa.
\s5
\v 8 Yahweh ya yi magana da Haruna, cewa,
\v 9 "Kada ka sha ruwan inabi ko barasa, da kai, da 'ya'yanka maza da ke tare da kai, yayin da kuka shiga rumfar taruwa, domin kada ku mutu. Wannan zai zama tsayayyar ka'ida dukkan tsararrakin mutanenku,
\v 10 domin a faiyace mai tsarki da marar tsarki, tsakanin ƙazamtacce da tsarkakke,
\v 11 domin ka koyar da mutanen Isra'ila dukkan farillan da Yahweh ya umarta ta wurin Musa."
\s5
\v 12 Musa ya yi magana da Haruna da Eliyazar da kuma Itamar, 'ya'yansa maza da suka rage, "Ku ɗauki baiko na hatsi da ya ragu daga baye-bayen Yahweh da aka yi da wuta, ku ci bada gami ba kusa da bagadi, gama mafi tsarki ne.
\v 13 Dole ka ci shi a wuri mai tsarki, domin rabonku ne da kuma rabon 'ya'yanku maza baye-bayen da aka yi wa Yahweh da wuta, gama wannan ne aka umarce ni in faɗa maku.
\s5
\v 14 Ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka miƙa wa Yahweh, dole ku ci a wuri mai tsabta karɓaɓɓe ga Yahweh. Da kai da 'ya'yanka maza da 'ya'yanka mata tare da kai za ku ci waɗannan rabon, gama an bada su domin su zama rabonka da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayu na baye-baye na zumunta na mutanen Isra'ila.
\v 15 Cinyar da aka miƙa da ƙirjin da aka kaɗa, dole ne su kawosu da baye-baye na kitse da aka yi da wuta, domin a kaɗa su a gaban Yahweh. Za su zama naka da na 'ya'yanka maza rabonku ne har abada, kamar yadda Yahweh ya umarta."
\s5
\v 16 Sa'an nan Musa ya tambaya game da bunsurun baiko na zunubi, sai ya ga an ƙone shi kurmus. Saboda haka ya yi fushi da Eliyazar da Itamar, sauran 'ya'ya maza na Haruna; ya ce,
\v 17 "Me ya sa ba ku ci baiko na zunubi a harabar rumfar sujada ba, tunda shike mafi tsarki ne, kuma tun da Yahweh ya bada shi gare ku domin a ɗauke laifin taro, domin a yi masu kaffara a gabansa?
\v 18 Duba, ba a kawo jininsa cikin rumfar sujada ba, yakamata lallai da kun ci shi a harabar rumfar sujada, kamar yadda na umarta."
\s5
\v 19 Sai Haruna ya amsa wa Musa, "Duba, yau sun miƙa baikonsu na zunubi da baiko ta ƙonawa a gaban Yahweh, kuma ga wannan abu ya faru da ni yau. In da na ci baiko na zunubi yau, da zai zama da kyau kenan a idon Yahweh?"
\v 20 Da Musa ya ji wannan, sai ya gamsu.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa,
\v 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana, ka ce, 'Waɗannan su ne masu rai da za ku ci daga cikin dukkan dabbobin da ke a duniya.
\s5
\v 3 Za ku ci kowacce dabba da ke da rababben kofato tana kuma tuƙa.
\v 4 Amma fa, wasu dabbobin suna tuƙa, ko kuma suna da rababbun kofatai, ba za ku ci su ba, dabbobi kamar su raƙumi, domin yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato. Saboda haka raƙumi marar tsarki ne a gare ku.
\s5
\v 5 Haka ma rema, domin tana tuƙa amma ba ta da rababben kofato, ita ma marar tsabta ce a gare ku.
\v 6 Zomo yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato, saboda haka marar tsabta ne a gare ku.
\v 7 Alade, koda shike yana da rababben kofato, ba ya tuƙa, marar tsabta ne a gare ku.
\v 8 Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawakinsu. Marasa tsabta ne a gare ku.
\s5
\v 9 Dabbobin da ke zaune cikin ruwa da za ku ci su ne duk waɗanda ke da ƙege ko kamɓori, ko a cikin teku ko cikin koguna.
\v 10 Amma duk rayayyun hallitu da ba su da ƙege ko kamɓori a cikin teku da koguna, har da ma dukkan masu yawo a ruwa da dukkan hallitu da ke cikin ruwa - dole za su zama abin ƙyama a gare ku.
\s5
\v 11 Tun da ya zama dole ku ƙyamace su, ba za ku ci daga namansu ba; kuma, dole ku ƙyamaci gawawakinsu.
\v 12 Dukkan abin da ba shi da ƙege ko kamɓori a cikin ruwa dole ku ƙyamace su.
\s5
\v 13 Ga tsuntsayen da za ku ji ƙyama kuma ba za ku ci su ba su ne: gaggafa, da ungulu,
\v 14 da shirwa, da kowacce irin mikiya,
\v 15 da kowanne irin hankaka,
\v 16 jimina, da mujiyar dare, da shaho, da kowacce irin shirwa.
\s5
\v 17 Za ku kuma ƙyamaci mujiya, da babba da ƙarama, da zalɓe,
\v 18 da kazar ruwa, da kwasakwasa, da ungulu,
\v 19 da shamuwa, da jinjimi, da burtu, da jemage.
\s5
\v 20 Dukkan ƙwari masu fukafukai da ke tafiya a kan ƙafa huɗu abin ƙyama ne a gare ku.
\v 21 Amma za ku iya cin ƙwari masu tashi suna kuma tafiya a kan ƙafafu huɗu idan ƙafafunsu suna da mahaɗi don tsalle a ƙasa.
\v 22 Za ku iya cin kowacce irin fara, da gara mai fukafukai da gyare, ko fara.
\v 23 Amma duk ƙwari masu tashi masu ƙafa huɗu abin ƙyama ne a gare ku.
\s5
\v 24 Za ku ƙazantu har faɗuwar rana ta wurin waɗannan dabbobi idan kun taɓa mushen ɗaya daga cikinsu.
\v 25 Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawakinsu dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har ya zuwa faɗuwar rana.
\s5
\v 26 Duk dabbar da ke da rababben kofato kuma bata tuƙa zai zama ƙazantacce a gare ku. Duk wanda ya taɓa ta zai ƙazantu.
\v 27 Duk abin da ke tafiya a kan daginsa a cikin dukkan dabbobi da suke tafiya a kan ƙafafu huɗu, ƙazantattu ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu zuwa maraice.
\v 28 Duk wanda ya ɗauki gawarsa dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har ya zuwa maraice. Waɗannan dabbobi za su zama ƙazantattu a gare ku.
\s5
\v 29 Cikin dabbobi masu rarrafe a ƙasa, waɗannan dabbobi za su zama ƙazantattu a gare ku: da murɗiya, da ɓera, da kowanne irin babban ƙadangare,
\v 30 da tsaka, guza, da ƙadangare, da damo da hawainiya..
\s5
\v 31 A cikin dukkan dabbobi masu rarrafe, waɗannan ne dabbobin da za su zama ƙazantattu a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har maraice.
\v 32 Idan waninsu ya mutu ya kuma faɗi a kan wani abu, wannan abin ya ƙazantu, ko an yi shi da itace, ƙyalle, fata, ko tsumma, Ko mene ne shi kuma ko mene ne ake amfani da shi, dole a sa shi cikin ruwa; zai zama ƙazamtacce har maraice. Sa'an nan zai zama tsarkakakke.
\v 33 Duk tukunyar yumɓun da ƙazantacciyar dabbar ta faɗa ciki, duk abin da ke cikin tukunyar ya ƙazanta, dole ku fasa tukunyar.
\s5
\v 34 Duk abinci da za a iya ci amma yana da ruwa a bisansa wannan tukunya ba ta da tsabta. Duk abin sha da ya ke cikin tukunyar ya ƙazantu.
\v 35 Duk abin da mushe ya faɗi a kansa ya ƙazantu; ko tanderu ne ko ƙaramin murhu ne, dole a farfasa su mitsi-mitsi. Ba su da tsarki kuma dole su kasance marasa tsarki a gare ku,
\s5
\v 36 Maɓuɓɓugar ruwa ko daron ɗibar ruwa zai zama da tsabta; amma duk wanda ya taɓa mushensu ya ƙazantu.
\v 37 Idan wani shashen mushen ya faɗa kan iri domin shuka, waɗannan irin yana da tsabta.
\v 38 Amma idan an zuba ruwa akan wannan iri, kuma wani sashe na mushen ya faɗi a kansa, za ya zama ƙazantattu a gare ku.
\s5
\v 39 Idan dabbar da ya kamata ku ci ta mutu, sai shi wanda ya taɓa gawar ya ƙazantu har sai maraice.
\v 40 Duk wanda ya ci wannan mushen dole ya wanke tufafinsa ya ƙazantu har faɗuwar rana. Wanda duk ya ɗauki wannan gawa zai wanke tufafinsa ya ƙazantu har maraice.
\s5
\v 41 Kowacce dabba da ke rarrafe a ƙasa za ku ƙyamace ta; ba za ku ci su ba.
\v 42 Duk abin da ke jan ciki, da duk abin da ke tafiya akan ƙafafu huɗu, ko mai ƙafafu da yawa - dukkan dabbobi masu rarrafe a ƙasa, ba za ku ci waɗannan ba, domin abin da za a ji ƙyama ne.
\s5
\v 43 Ba za ku ƙazantar da kanku da kowacce hallita mai rai wanda ya ke jan ciki ba; ba za ku ƙazantar da kanku da su ba, har da za ku zama marasa tsarki da su.
\v 44 Gama ni ne Yahweh Allahnku. Za ku ƙeɓe kanku da tsarki, saboda haka, kuma ku zama da tsarki, domin ni mai tsarki ne. Ba za ku ƙazantar da kanku da kowacce irin dabbar da ke tafiya a fuskar ƙasa ba.
\v 45 Domin ni ne Yahweh, wanda ya fitar daku daga ƙasar Masar, domin in zama Allahnku. Saboda haka dole ne ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne,
\s5
\v 46 Wannan ita ce dokar da ta shafi dabbobi, da tsuntsaye, da dukkan rayayyun hallitu da ke yawo cikin ruwaye, da kowacce hallita da ke rarrafe a fuskar ƙasa,
\v 47 waɗanda za a sa bambanci tsakanin marasa tsarki da masu tsarki, da tsakanin abubuwa masu rai da za a iya ci, da abubuwa masu rai da ba za a ci su ba.'"
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Yahweh ya cewa Musa,
\v 2 "Ka yi wa mutanen Isra'ila magana, cewa, "Idan mace ta yi ciki ta haifi ɗa namiji, za ta ƙazantu har kwana bakwai, kamar yadda ta ƙazantu a kwanakin watan hailarta.
\v 3 A rana ta takwas dole a yi wa ɗan yaron kaciya.
\s5
\v 4 Sa'an nan tsarkakewar uwar daga zubar jini zai ci gaba har kwana talatin da uku. Ba zata taɓa wani abu mai tsarki ba ko ta shiga harabar haikali har sai kwanakin tsarkakewarta sun cika.
\v 5 Amma idan ta haifi 'ya mace, za ta ƙazantu sati biyu, kamar yadda take kwanakin hailarta. Sa'an nan kwanakin tsarkakewar uwar zai ci gaba har kwana sittin da shida.
\s5
\v 6 Lokacin da kwanakin tsarkakewarta suka cika, domin ɗa na miji ko mace, dole ta kawo ɗan tunkiya bana ɗaya, domin baiko na ƙonawa, da ɗan kurciya ko tattabara domin baiko na zunubi, zuwa ƙofar rumfar taruwa, zuwa ga firist.
\s5
\v 7 Sa'an nan zai miƙa shi a gaban Yahweh ya yi kaffara domin ta, sa'an nan za ta tsarkaka daga zubar jininta. Wannan ita ce doka game da matar da ta haifi ɗa ko ɗiya.
\v 8 Idan ba ta iya ba da tunkiya ba, to sai ta ɗauko kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai biyu, ɗaya domin baikon ƙonawa, ɗayan domin baiko na zunubi, sa'an nan firist zai yi kaffara domin ta; sa'an nan za ta tsarkaka.'"
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da kuma Haruna, ya ce,
\v 2 "Sa'ad da wani yana da kumburi ko ɓamɓaroki ko tabo mai haske a fatar jikinsa, har ya kamu da cuta kuma akwai cutar fata a jikinsa, dole a kawo shi ga Haruna babban firist, ko ga ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza firistoci.
\s5
\v 3 Firist zai dudduba cutar a fatar jikinsa. Idan gashin da ke cikin cutar ya zama fari, kuma idan an ga cutar ta yi zurfi fiye da fatar jiki, to cuta ce mai yaɗuwa. Bayan da firist ya dudduba shi, dole ya furta shi marar tsarki.
\v 4 Idan tabon mai haske a jikinsa fari ne, kuma ba aga cutar ta yi zurfin data zarce fatar jikin ba, kuma idan gashin da ke cikin cutar bai rikiɗa fari ba, to dole firist ya ware wannan mai cutar shi kaɗai har kwana bakwai.
\s5
\v 5 A rana ta bakwai, dole firist ya duba shi idan a ganinsa cutar ba ta ƙara muni ba, in kuma ba ta bazu a cikin fatar ba. Idan ba ta bazu ba, sai dole firist ya ƙara tsare shi wasu kwanaki bakwai kuma.
\v 6 Firist zai sake bincike shi a rana ta bakwai ya ga ko cutar ta yi sauƙi, bata kuma ƙara bazuwa a fatar ba. Idan bata bazu ba, sai firist ya furta shi tsarkakakke. Ƙuraje ne. Dole ya wanke tufafinsa, sai ya tsarkaka.
\s5
\v 7 Amma idan ɓamɓaroki ya yaɗu a cikin fatar bayan ya nuna kansa ga firist domin tsarkakewarsa, sai dole ya sake nuna kansa ga firist kuma.
\v 8 firist zai sake duba shi ya ga ko ɓamɓarokin ya ƙara yaɗuwa a fatar jikin. Idan ya yaɗu, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cutar fata ce mai bazuwa.
\s5
\v 9 Idan cutar fata mai yaɗuwa tana jikin wani, dole a kawo shi wurin firist.
\v 10 Firist zai duba shi ya ga ko akwai farin kumburi a fatar jikinsa, idan gashin ya rikiɗa ya zama fari, ko kuma akwai buɗaɗɗen ƙurji a kumburin.
\v 11 Idan akwai, to lallai akwai riƙaƙƙiyar cutar fata mai yaɗuwa, dole firist ya furta shi marar tsarki. Ba zai ware shi ba kaɗai, gama ya rigaya ya ƙazantu.
\s5
\v 12 Idan cutar ta bazu barkatai a cikin fata kuma ta mamaye duk fatar jikin mutumin daga kansa har zuwa kafafunsa, bisa ga ganin firist,
\v 13 sai dole firist ya dudduba shi domin ya ga ko cutar ta rufe dukkan jikinsa. Idan kuwa haka ne, sai firist dole ya furta cewa mutumin nan mai cutar tsarkakke ne. Idan ta rikiɗa ta zama fari, to tsarkakakke ne.
\v 14 Amma idan akwai buɗaɗɗen ƙurji a kansa, to ya ƙazantu.
\s5
\v 15 Dole firist ya duba miƙin jikin ya furta cewa ya ƙazantu domin miƙin fatar ƙazantacce ne. Cuta ce mai yaɗuwa.
\v 16 Amma idan miƙin fatar ya koma kuma ya zama fari, dole mutumin ya tafi wurin firist.
\v 17 Firist zai dudduba shi ya ga ko fatar ta koma fari. Idan ya koma, sai firist ya furta wannan mutum tsarkakke ne.
\s5
\v 18 Idan mutum yana da maruru a fatar jikinsa amma ya warke,
\v 19 kuma a tabon marurun nan sai ga wani farin kumburi ko fata mai ƙyalli, ja da fari, to fa dole a nuna wa firist.
\v 20 Firist zai dudduba ya ga ko ya shiga cikin fata sosai, kuma idan gashin wurin ya rikiɗa ya zama fari. Idan haka ne, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce ta fata mai saurin yaɗuwa, idan ya girma a inda kumburin ya ke.
\s5
\v 21 Amma idan firist ya dudduba ya ga ba farin gashi a ciki, kuma zurfin bai zarce fata ba amma ya dushe, dole firist ya ware shi da bam har kwana bakwai.
\v 22 Idan ta bazu ta mamaye fatar, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa.
\v 23 Amma idan fata mai haske ta kassance wuri guda bai bazu ba, to tabon maruru ne, dole kuma firist ya furta shi tsarkakakke.
\s5
\v 24 Idan fata tana da ƙuna kuma wani buɗaɗɗen ƙurji ya fito a wurin da launi jaja-jaja fari-fari ko farin ɗigo,
\v 25 sai firist ya dudduba shi ya ga ko gashin wurin ya zama fari, in kuma zurfinsa ya wuce fata. Idan haka ne, to cuta ce mai yaɗuwa. Ya ɓullo ne akan tabo, dole ne firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa.
\s5
\v 26 Amma idan firist ya dudduba shi ya ga babu farin gashi a wurin, kuma bai zarce fata ba amma ya dushe, sai dole firist ya ware shi shi kaɗai har kwana bakwai.
\v 27 Sa'an nan ɗole firist ya dudduba shi a rana ta bakwai. Idan ya yaɗu ya mamaye fatar, dole firist ya furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa.
\v 28 Idan cutar ta tsaya wuri guda ba ta yaɗu cikin fatar ba amma ta dushe, to kumburi ne daga ƙuna, dole firist ya furta shi tsarkakakke, saboda ba wani abu ba ne, sai dai tabo ne daga ƙuna.
\s5
\v 29 Idan namiji ko mace na da cuta mai yaɗuwa a kã ko a haɓa,
\v 30 sai dole firist ya dudduba mutumin saboda cutar da ke yaɗuwa domin a ga ko ta zarce fatar jikin, idan aka ga gashi ruwan ɗorowa, kuma siriri a cikinsa. Idan akwai shi, to dole firist ya furta shi marar tsarki. Ƙaiƙai ne. Cuta ce mai yaɗuwa a kã ko a haɓa,
\s5
\v 31 Idan firist ya dudduba cuta mai ƙaiƙayi ya ga babu ita ƙarƙashin fata, kuma ba baƙin gashi a ciki, to sai firist ya ware mutumin nan mai cutar ƙaiƙayi shi kaɗai har kwana bakwai.
\s5
\v 32 A rana ta bakwai firist zai duba cutar ya ga ko ta bazu. Idan babu gashi mai kalar ruwan ɗorowa, kuma idan cutar ba ta zarce zurfin fata ba, sai dole a yi masa aski,
\v 33 amma ba za a aske wajen cutar ba, kuma dole firist ya ware mutumin nan mai cutar ƙaiƙayi shi kaɗai kimamin wasu kwana bakwai.
\s5
\v 34 A rana ta bakwai firist zai dudduba cutar ya ga ko ta dena bazuwa a cikin fatar, Idan an ga bata zarce zurfin fata ba, sai dole firist ya furta shi tsarkakakke. Dole mutumin ya wanke tufafinsa, sa'an nan za ya zama tsarkakakke,
\s5
\v 35 Amma idan cutar ƙaiƙayin ta bazu da yawa a cikin fatar bayan firist ya ce ya tsarkaka,
\v 36 sai dole firist ya sake dudduba shi kuma. Idan cutar ta bazu a cikin fatar, firist bai buƙatar ya nemi gashi mai launin rawaya. Mutumin ya kazantu.
\v 37 Amma idan a ganin firist cutar ƙaiƙayi ta dena bazuwa kuma baƙin gashi ya toho a wurin, to cutar ta warke. Ya zama tsarkakakke, dole firist ya furta shi tsarkakakke.
\s5
\v 38 Idan namiji ko mace na da farin tabbuna a fata,
\v 39 sai dole firist ya dudduba mutumin ya ga ko tabbunan ba farare sosai ba ne, wannan ƙuraje ne kawai da suka farfashe a cikin fatar. Shi tsarkakakke ne.
\s5
\v 40 Idan gashin namiji ya zube daga kansa, yana da saiƙo, amma yana da tsarki.
\v 41 Idan gashinsa suka zube daga gaban kansa, idan goshinsa na da saiƙo, shi tsarkakakke ne.
\s5
\v 42 Amma idan akwai wani ƙurji jaja-jaja fari-fari akan saiƙonsa ko goshinsa, wannan cuta ce mai yaɗuwa da ta faso.
\v 43 Saboda haka dole firist ya dudduba shi ya ga ko kumburin cutar inda take a kan saiƙo ko goshinsa ya yi jaja-jaja fari-fari, da kuma kamannin cuta mai yaɗuwa ce a cikin fata.
\v 44 Idan ita ce, to yana da cuta mai yaɗuwa kuma ba shi da tsarki. Tabbas kuma dole ne firist ya furta shi marar tsarki saboda cutarsa da ke a kansa.
\s5
\v 45 Mutumin da ke da cuta mai yaɗuwa dole ya sa yagaggun tufafi, ya bar gashin kai ba gyara, dole kuma ya rufe fuskarsa har hanci yana kira da ƙarfi, 'Marar tsarki, marar tsarki.'
\v 46 Dukkan kwanakin da ya ke da wannan cuta mai yaɗuwa zai kasance marar tsarki. Domin ya ƙazantu da cuta mai yaɗuwa, dole ya zauna shi kaɗai. Dole ya zauna a bayan sansani.
\s5
\v 47 Rigar data ƙazantu da kuturta ko ta ulu ce ko rigar lilin ce,
\v 48 abin da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko lilin, ko fata, ko mene ne dai da aka yi shi daga fata -
\v 49 idan akwai wani kore-kore ko jaja-jajar ƙazanta a taguwar, fatar, da saƙa ko ɗinkakken yadi, ko mene ne dai da aka yi daga fata, to wannan kuturta ce data yaɗu; dole a nuna wa firist.
\s5
\v 50 Dole firist ya dudduba kayan don kuturta; dole ne ya kulle duk abin da ke da kuturta har kwana bakwai.
\v 51 Zai sake duba kuturtar nan a rana ta bakwai. Idan ta bazu a tufar da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko yadin lilin ko fata ko wani abu da aka yi amfani da fata, to wannan kuturta ce mai cutarwa, wannan abu ya ƙazantu.
\v 52 Dole ya ƙona wannan tufar, ko sakakkiya ko ɗinkakkiyar abin da aka yi da ulu ko yadin lilin, ko fata, ko wani abin da aka yi daga fata, dukkan abin da aka sami kuturta mai cutarwa a ciki, gama zai iya kaiwa ga cuta, Dole a ƙona wannan abin ƙurmus.
\s5
\v 53 Idan firist ya dudduba abin ya ga kuturta amma bata bazu cikin tufa ba ko cikin abin da aka ɗinka da yadi ko aka saƙa da ulu ko lilin, ko kayayyakin da aka yi su da fata,
\v 54 sa'an nan zai umarce su su wanke kayan da aka sami kuturta a ciki, dole kuma zai kulle shi wasu kwana bakwai kuma.
\v 55 Sa'an nan firist zai duba abin bayan an wanke wannan kayan mai kuturta. Idan kuturtar bata sauya launin ba, koda shike bata bazu ba, ƙazamtacce ne. Dole a ƙona wannan abin, ko ma a ina kuturtar ta ƙazamtar da shi.
\s5
\v 56 Idan firist ya duba wannan abin, idan kuturtar ta dushe bayan an wanke ta, dole ya yage wannan ƙazantaccen wuri daga tufar ko fatar, ko daga saƙaƙƙe ko ɗinkakken yadi.
\v 57 Idan kuturta ta sake bayyana a taguwar ko a cikin saƙaƙƙe ko ɗinkakken yadi, ko wani abin da aka yi da fata, bazuwa take yi. Dole ku ƙona duk wani abin da ke da kuturta.
\v 58 Riga ko wani abin da aka saƙa ko aka ɗinka daga ulu ko yadin lilin, ko fata, ko wani abin da aka yi da fata - idan kun wanke abin kuma kuturtar ta fita, sai kuma dole ku wanke wannan abin karo na biyu, sa'an nan zai zama da tsarki.
\s5
\v 59 Wannan ita ce shari'a game da kuturta a tufar ulu ko lilin, ko kowanne abin da aka saƙa ko ɗinka daga ulu ko yadin lilin, ko fata ko ko mene ne da aka yi shi da fata, domin ku furta shi mai tsarki ko marar tsarki."
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 2 "Wannan ce shari'a domin mutum mai cuta a ranar tsarkakewarsa. Dole ne a kawo shi ga firist.
\s5
\v 3 Firist zai fita daga cikin zango domin ya dudduba mutumin ya ga ko cutar mai yaɗuwa a fata ta warke.
\v 4 Sa'an nan firist zai bada doka cewa wanda za a tsarkake ya ɗauki tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta, da itacen sida. da jan zare, da ɗaɗɗoya.
\v 5 Firist zai umarce shi ya kashe ɗaya daga cikin tsuntsayen a kan ruwa mai tsabta da ke cikin tukunyar yumɓu.
\s5
\v 6 Firist zai ɗauki tsuntsun mai rai da itacen sida, da jan zare da ɗaɗɗoyar, yatsoma dukkan waɗannan abubuwa, har ma da tsuntsun nan mai rai, a cikin jinin tsuntsun da aka kashe a kan ruwa mai tsabta.
\v 7 Sa'an nan firist zai yayyafa wannan ruwa sau bakwai a kan mutumin da za a tsarkake daga cutar, sa'an nan firist zai furta cewa ya tsarkaka. Sa'an nan firist zai saki tsuntsun mai rai ya yi tafiyarsa jeji.
\s5
\v 8 Mutumin da ake tsarkakewa zai wanke tufafinsa, ya aske dukkan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan zai tsarkaka. Bayan wannan dole ya dawo cikin zango. amma ba zai zauna a cikin rumfarsa ba sai bayan kwana bakwai.
\v 9 A rana ta bakwai dole ya yanke dukkan gashin kansa, kuma dole ya aske gemunsa da girar idonsa. Dole ya aske dukkan gashinsa, kuma dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa; sa'an nan zai zama da tsarki.
\s5
\v 10 A rana ta takwas dole ya ɗauki 'yan raguna biyu marasa lahani, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da kashi uku bisa goma na mudun lallausar gari cuɗaɗɗe da mai domin baiko ta hatsi, da moɗar mai ɗaya.
\v 11 Firist da ya tsarkake shi zai tsaida wanda za a tsarkake, tare da waɗannan abubuwa, a gaban Yahweh a ƙofar rumfar taruwa.
\s5
\v 12 Firist zai ɗauki ɗaya daga cikin 'yan ragunan ya miƙa shi baiko domin laifi, tare da moɗar mai; zai kaɗa su domin baiko na kaɗawa a gaban Yahweh.
\v 13 Dole ya yanka ɗan ragon a inda suke yanka baye-baye na zunubi da baye-baye na ƙonawa, a harabar haikali, domin baiko na zunubi rabon firist ne, haka ma baiko na laifi, domin mafi tsarki ne.
\s5
\v 14 Firist zai ɗauki kaɗan daga cikin jinin baikon domin laifi ya sa shi a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun damansa, da kan babban yatsan ƙafarsa ta dama.
\v 15 Sa'an nan firist zai ɗauki mai daga moɗar ya zuba shi a tafin hannun hagunsa,
\v 16 ya tsoma yatsansa na dama a cikin man da ke tafin hannunsa na hagu, ya yayyafa daga man da yatsansa sau bakwai a gaban Yahweh.
\s5
\v 17 Firist zai sa ragowar man a hannunsa a kan leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a kan babban yatsan hannunsa na dama, da a kan babban yatsan ƙafarsa ta dama. Dole ya sa wannan mai a kan jinin baiko domin laifi.
\v 18 Game da sauran man da ke hannun firist, zai sa shi a kan mutumin da za a tsarkake, firist kuma zai yi kaffara dominsa a gaban Yahweh.
\s5
\v 19 Sa'an nan firist zai miƙa baiko na zunubi ya yi kaffara domin wanda za a tsarkake saboda rashin tsarkinsa, bayan wannan zai yanka baiko na ƙonawa.
\v 20 Sa'an nan firist zai miƙa baiko na ƙonawa da kuma baiko na hatsi a kan bagadi. Firist zai yi kaffara domin wannan mutumin, sa'an nan zai zama da tsarki.
\s5
\v 21 Amma, idan mutumin matalauci ne har ba zai iya ba da waɗannan hadayu ba, to sai ya ɗauki ɗan rago ɗaya domin baiko na laifi saboda a kaɗa shi, a yi kaffara dominsa, da awon garwa na gari mai laushi da aka kwaɓa da mai domin baiko na hatsi, da mai a moɗa,
\v 22 tare da kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu, iyakar dai abin da ya iya samu; tsuntsu ɗaya zai zama na baikon zunubi ɗayan kuma baiko na ƙonawa.
\v 23 A rana ta takwas dole ya kawo su domin tsarkakewarsa ga firist, zuwa ƙofar shiga rumfar taruwa, a gaban Yahweh.
\s5
\v 24 Firist zai ɗauki ragon domin baiko, zai ɗauke shi tare da moɗar man zaitun, sai ya ɗaga su sama sosai sa'ad da ya ke miƙa wa Yahweh.
\v 25 Zai yanka ɗan ragon baiko domin laifi, zai ɗauki ɗan jinin baiko domin laifi ya sa su a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun dama, da kan babban yatsan ƙafar damansa.
\s5
\v 26 Sa'an nan firist zai zuba daga cikin man a tafin hannunsa na hagu,
\v 27 kuma ya yayyafa da ɗan yatsansa na dama daga cikin man da ke tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Yahweh.
\s5
\v 28 Firist zai sa daga man da ke tafin hannunsa a kan leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da kan babban yatsan hannun damansa, da kuma kan babban yatsan ƙafar damansa, a nan wuraren da ya sa jinin baiko domin laifi.
\v 29 Zai sa sauran man da ke hannunsa a kan wanda za a tsarkake, domin a yi kaffara dominsa a gaban Yahweh.
\s5
\v 30 Dole ya miƙa ɗaya daga cikin 'yan kurciyoyin ko 'yan tantabarai, gwargwadon abin da mutumin ya iya samowa -
\v 31 ɗaya domin baikon zunubi ɗaya kuma domin baiko na ƙonawa, tare kuma da baiko na garin hatsi. Sai firist ya yi kaffara domin wanda za a tsarkake a gaban Yahweh.
\v 32 Wannan ita ce doka domin mutumin da ke da cutar fata mai yaɗuwa, wanda ya gaza bayarwa bisa ga ka'idodin baye-baye domin tsarkakewarsa."
\s5
\v 33 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa,
\v 34 "Sa'ad da kuka shiga cikin ƙasar Kan'ana wanda na ba ku ta zama mallakarku, idan na sa kuturta mai yaɗuwa a cikin gida cikin ƙasar mallakarku,
\v 35 sai dole mai wannan gida ya tafi ya faɗa wa firist. Dole ne ya ce, 'Ni a gani na akwai wani abu kamar kuturta a cikin gidana.'
\s5
\v 36 Sa'an nan firist zai umarta a fitar da komai daga cikin gidan kafin ya shiga ya duba ya tabbatar akwai kuturtar, domin kada a ƙazamtar da dukkan abin da ke gidan. Bayan wannan firist zai shiga ya duba cikin gidan.
\v 37 Dole ya dudduba kuturtar ya ga ko tana bangayen gidan, ya duba ko yana da kore-koren launi ko jaja-jaja cikin zurfin bangayen.
\v 38 Idan akwai kuturta a gidan, sai firist ya fita daga gidan ya rufe ƙofar gidan har kwana bakwai.
\s5
\v 39 Sa'an nan firist zai sake dawowa a rana ta bakwai ya dudduba shi domin ya ga ko kuturtar ta bazu a bangayen gidan.
\v 40 Idan ta bazu, sai firist ya umarta a cire duwatsun da aka tarar da kuturta a jefar da su a wuri marar tsabta a bayan birni.
\s5
\v 41 Zai sa a kankare dukkan bangayen cikin gidan, dole kuma a kwashe dukkan ƙazamtattun kayayyakin da aka kankare a kai su can bayan birni a zuba su a wuri marar tsabta.
\v 42 Dole su ɗauki wasu duwatsu su cike gurbin waɗancan duwatsun da aka cire, dole kuma su yi amfani da sabuwar ƙasa su yaɓe gidan.
\s5
\v 43 Idan kuturta ta sake ɓullowa cikin gidan da aka ciccire duwatsun bangayen aka kakankare su aka kuma yi sabon shafe,
\v 44 sai dole firist ya shiga ciki ya dudduba gidan ya ga ko kuturtar ta bazu a cikin gidan. Idan ta bazu, to kuturtar mai cutarwa ce, gidan kuma ya ƙazantu.
\s5
\v 45 Dole ne a rushe gidan nan. Da duwatsun, da katakan, da dukkan shafen cikin gidan dole a kwashe su daga cikin birni zuwa wuri marar tsabta.
\v 46 Bugu da ƙari, duk wanda ya shiga cikin gidan a lokacin da aka kulle gidan zai zama marar tsarki har maraice.
\v 47 Duk wanda ya kwana a cikin gidan dole ya wanke tufafinsa, kuma duk wanda ya ci a cikin gidan dole ya wanke tufafinsa.
\s5
\v 48 Idan firist ya shiga domin ya dudduba ya ga ko kuturtar ta yaɗu a cikin gidan bayan an yi wa gidan yaɓe, sa'an nan, idan kuturtar ta tafi, sai ya furta wannan gida tsarkakakke.
\s5
\v 49 Sai dole firist ya ɗauki tsuntsayen biyu domin tsarkake gidan, da itacen sida, da shuɗin zare, da ɗaɗɗoya.
\v 50 Sai ya kashe ɗaya tsuntsun a bisa ruwa mai tsabta cikin tukunyar yumɓu.
\v 51 Zai ɗauki itacen sida, da ɗaɗɗoyar, da shuɗin zaren da kuma tsuntsun mai rai, ya tsoma su cikin jinin ɗaya tsuntsun da aka kashe, cikin ruwan nan mai tsabta, ya yayyafa gidan sau bakwai.
\s5
\v 52 Zai tsarkake gidan da jinin tsuntsun da ruwan nan mai kyau, tare da tsuntsun nan mai rai, da itacen sida, da ɗaɗɗoya, da kuma jan zare.
\v 53 Amma zai bar tsuntsun mai rai ya fita daga cikin birni ya tafi jeji. Ta haka ne dole zai yi kaffara domin gidan, zai kuma zama da tsarki.
\s5
\v 54 Wannan ita ce shari'a domin dukkan irin cutar fata mai yaɗuwa, da abubuwan da ke sa irin wannan cuta, ko ƙaiƙayi,
\v 55 da kuma kuturta a cikin tufafi da cikin gida,
\v 56 da kumburi, da ƙuraje, da kuma tabo,
\v 57 domin a tabbatar da lokacin da makamantan haka ba tsarki ko da tsarki. Wannan ita ce shari'a a kan cututtukan fatar jiki mai yaɗuwa da kuma kuturta.
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa da Haruna, cewa,
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, ka ce masu, "Yayin da kowanne mutum ya ke da ruwan da ke fitowa daga cikin jikinsa, ya zama ƙazantacce.
\v 3 Ƙazantarsa sakamakon wannan cutar ruwan ce. Ko jikinsa yana zubar da ruwan ko ya tsaya, kazantacce ne.
\s5
\v 4 Kowanne gadon da ya kwanta akai zai ƙazantu, duk abin da ya zauna akansa kuma zai ƙazantu.
\v 5 Duk wanda ya taɓa gadonsa dole ya wanke tufafinsa kuma ya yi wanka cikin ruwa, kuma ya ƙazantu har yamma.
\s5
\v 6 Duk wanda ya zauna akan kowanne abin da da mutum mai cutar zubar ruwan nan ya zauna akai, wannan mutum dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa, kuma zai zama marar tsabta har yamma.
\v 7 Duk wanda ya taɓa jikin mai cutar zubar ruwa dole ya wanke tufafinsa kuma ya yi wanka cikin ruwa, ya ƙazantu har yamma.
\s5
\v 8 Idan mutumin nan mai cutar zubar ruwa ya tofa miyau a bisa wani mai tsabta, daga nan wannan mutumin dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka cikin ruwa, kuma ya ƙazantu har yamma tayi.
\v 9 Kowanne sirdi da mai zubar ruwan ya hau kai zai zama ƙazantacce.
\s5
\v 10 Duk wanda ya taɓa kowanne abin da ke ƙarƙashin mutumin zai ƙazantu har yamma, kuma wanda ya ɗauki waɗannan abubuwan dole ya wanke tufafinsa ya yi wanka cikin ruwa; ya ƙazantu har yamma ta yi.
\v 11 Duk wanda mai cutar zubar ruwan ya taɓa ba tare da ya ɗauraye hannuwansa da farko cikin ruwa ba, mutumin da aka taɓa dole ya wanke tufafinsa ya yiwa kansa wanke cikin ruwa, kuma zai zama marar tsabta har yamma ta yi.
\v 12 Kowacce tukunyar yumɓun da mai irin wannan zubar ruwan ya taɓa dole a fasata, kuma kowanne akushin itace dole a ɗauraye shi cikin ruwa.
\s5
\v 13 Sa'ad da shi mai zubar ya tsarkaka daga zubar tasa, daga nan sai ya ƙirgawa kansa kwana bakwai domin tsarkakewarsa; daga nan dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa mai gudu. Daga nan zai tsarkaka.
\v 14 A rana ta takwas dole ya ɗauki "yan kurciyoyi biyu ko 'yan tantabarai guda biyu ya zo gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa; a can dole ya bada tsuntsayen ga firist.
\v 15 Dole firist ɗin ya miƙa su, ɗaya a matsayin hadayar zunubi ɗaya a matsayin ƙonanniyar hadaya, kuma dole firist ya yi kaffara domin sa a gaban Yahweh domin zubarsa.
\s5
\v 16 Idan kowanne mutum yana da fitaccen maniyyi, daga nan dole ya wanke dukkan jikinsa cikin ruwa; zai zama marar tsabta har yamma.
\v 17 Kowacce riga ko tufar fata inda akwai maniyyin dole a wanke ta da ruwa; zata zama marar tsarki har yamma.
\v 18 Idan mace da miji suka kwanta tare kuma akayi canjin maniyyi zuwa gare ta, dole dukkansu su yi wanka cikin ruwa; zasu zama marasa tsarki har yamma.
\s5
\v 19 Idan mace tana haila, rashin tsarkinta zai ci gaba har kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓata zai ƙazantu har yamma ta yi.
\v 20 Kowanne abin data kwanta akai lokacin al'adarta zai zama marar tsarki; kowanne abin data zauna akansa kuma zai zama marar tsarki.
\s5
\v 21 Duk wanda ya taɓa gadonta dole ya wanke tufafinsa kuma ya wanke kansa cikin ruwa; wannan mutumin zai zama marar tsarki har yamma.
\v 22 Duk wanda ya taɓa kowanne abin data zauna a kansa dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa; wannan mutumin zai ƙazantu har yamma.
\v 23 Ko akan gado ko akan kowanne abin da ta zauna akai, idan ya taɓa shi, wannan mutumin zai zama marar tsarki har yamma.
\s5
\v 24 Idan kowanne mutum ya kwana da ita, kuma idan zubar rashin tsarkinta ya taɓa shi, zai zama marar tsarki har kwana bakwai. Kowanne gadon da ta kwanta kai zai zama marar tsarki.
\s5
\v 25 Idan mace tana zubar jini kwanaki da yawa wanda ba cikin kwanakin hailarta bane, ko idan tana zuba fiye da kwanakin hailarta, lokacin dukkan kwanakin zubar rashin tsarkinta, zata zama kamar tana cikin kwanakin hailarta. Marar tsarki ce.
\v 26 Kowanne gadon data kwanta akai dukkan kwanakin zubar jininta zai zama a gareta kamar gadon data kwanta akai lokacin hailarta, kuma duk abin data zauna akai zai ƙazantu, kamar rashin tsarkin ta na haila.
\v 27 Duk wanda ya taɓa kowanne ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai zama marar tsarki; dole ya wanke tufafinsa ya kuma wanke kansa cikin ruwa, kuma ya zama marar tsarki har yamma tayi.
\s5
\v 28 Amma idan ta tsarkaka daga zubar jininta, daga nan sai ta lisafta wa kanta kwanaki bakwai, bayan wannan ta tsarkaka.
\v 29 A rana ta takwas za ta ɗauki 'yan'kurciyoyi guda biyu ko 'yan' tantabarai guda biyu za ta kawo su wurin firist a ƙofar rumfa ta taruwa.
\v 30 Firist zai miƙa tsuntsu ɗaya a matsayin hadaya ta zunubi, ɗayan kuma domin ƙonanniyar hadaya, kuma zai yi kaffara domin ta a gaban Yahweh domin zubar jininta.
\s5
\v 31 Ta haka za ku keɓe mutanen Isra'ila daga ƙazantarsu, domin kada su mutu ta wurin ƙazantarsu, ta wurin ɓata rumfar sujadata, in da nake zama a tsakiyar su.
\s5
\v 32 Waɗannan su ne ka'idodi domin duk wanda ya ke zubar ruwa, domin kowanne mutum da maniyinsa ya fita daga gare shi ya sa shi ya zama marar tsarki,
\v 33 ga kowacce mace da ke haila, da duk wanda ya ke zubar ruwa, ko namiji ko mace, da kuma duk wanda ya kwana da matar da ta ƙazanta.'"
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa -- wannan bayan mutuwar 'ya'yan Haruna guda biyu, lokacin da suka kusato Yahweh kuma suka mutu.
\v 2 Yahweh ya ce da Musa. "Ka yi magana da Haruna ɗan'uwanka ka ce masa kada kowanne lokaci ya riƙa shiga wuri mai tsarki cikin labule, a gaban mazaunin jinƙai wanda ke bisa kan akwatin al̀ƙawari. Idan ya yi haka, zai mutu, saboda ina bayyana cikin girgije a bisa mazaunin jinƙai.
\s5
\v 3 Don haka ga yadda Haruna zai shiga wuri mafi tsarki. Dole ya shiga da ɗan bijimi domin hadaya ta zunubi, da rago domin hadaya ta ƙonawa.
\v 4 Dole ya sanya riga mai tsarki, kuma dole ya sa riga 'yarciki a jikinsa, kuma dole ya sa ɗamarar linin da rawanin linin. Waɗannan su ne riguna masu tsarki. Dole ya wanke jikinsa cikin ruwa daga nan ya shirya kansa da waɗannan rigunan.
\v 5 Dole ya karɓi bunsura biyu daga taron jama'ar Isra'ila a matsayin baikon zunubi da rago ɗaya domin ƙonanniyar hadaya.
\s5
\v 6 Daga nan dole Haruna ya miƙa bijimi domin baikon zunubi, wanda ya ke domin kansa, zai yi kaffara domin kansa da iyalinsa.
\v 7 Daga nan dole ya ɗauki bunsura biyun ya ajiye su gaban Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa.
\s5
\v 8 Daga nan dole Haruna ya jefa ƙuri'a domin bunsuran biyu, ɗaya domin Yahweh, ɗaya a matsayin refataccen bunsuru.
\v 9 Daga nan dole Haruna ya miƙa bunsurun da ƙuri'a ta faɗa wa ga Yahweh, kuma ya miƙa bunsurun a matsayin baikon zunubi.
\v 10 Amma bunsurun da ƙuri'a ta faɗa wa a matsayin refataccen bunsuru dole a kawo shi da rai gaban Yahweh, domin kaffara ta wurin aikar da shi a matsayin refataccen bunsuru cikin jeji.
\s5
\v 11 Daga nan dole Haruna ya miƙa bijimi domin baikon zunubi, wanda zai zama domin kansa. Dole ya yi kafara domin kansa da kuma domin iyalinsa, dole ya yanka bijimi a matsayin baikon zunubi domin kansa.
\s5
\v 12 Dole Haruna ya ɗauki kasko cike da garwashin wuta daga bisa bagadi gaban Yahweh, hannuwansa kuma cike da gyararren garin turare mai ƙanshi, ya kuma kawo waɗannan abubuwan cikin labule.
\v 13 A can dole ya ɗibiya turare akan wuta gaban Yahweh domin hayaƙi daga turaren ya rufe marfin kaffara a bisa dokokin alƙawarin. Dole ya yi haka domin kada ya mutu.
\s5
\v 14 Daga nan dole ya ɗauki jinin bijimi ya yayyafa shi da yatsansa a gaban marfin kaffara. Dole ya yayyafa sauran jinin da yatsansa sau bakwai gaban mazaunin jinƙai.
\s5
\v 15 Sa'an nan dole ya yanka bunsuru domin hadayar zunubi wanda ya ke domin jama'a ya kawo jininsa cikin labule. A can dole ya yi da jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin: Dole ya yayyafa shi a bisa murfin kafara da kuma gaban murfin kafara.
\v 16 Dole ya yi kafara domin wuri mai tsarki saboda ƙazantar ayyukan mutanen Isra'ila, da kuma domin tayarwarsu da dukkan zunubansu. Dole kuma ya yi haka kuma domin rumfar taruwa, inda Yahweh ke zama cikinsu, a gaban ƙazantattun ayyukansu.
\s5
\v 17 Ba wanda zai kasance a rumfar taruwa sa'ad da Haruna ya shiga domin ya yi kaffara cikin wuri mafi tsarki, har lokacin da ya fito ya kuma gama yin kaffara domin kansa da kuma iyalinsa, da kuma dukkan taron Isra'ila.
\v 18 Dole ya fita zuwa bagadin da ke gaban Yahweh domin ya yi kaffara domin sa, kuma dole ya ɗibi jinin bijimi da jinin akuyar ya sa shi a bisan ƙahonnin bagadi ko'ina kewaye.
\v 19 Dole ya yayyafa daga cikin jinin a kai da yatsansa sau bakwai ya tsabtace shi ya keɓe shi ga Yahweh, nesa daga ƙazantar ayyukan mutanen Isra'ila.
\s5
\v 20 Sa'ad da ya gama yin kaffara domin wuri mafi tsarki, rumfar taruwa, da bagadi, dole ya miƙa bunsurun mai rai.
\v 21 Dole Haruna ya ɗibiya hannayensa a kan bunsurun mai ran ya furta dukkan muguntar mutanen Isra'ila, dukkan tayarwarsu, da dukkan zunubansu. Daga nan dole ya sa zunubansu a kan bunsurun ya sallami bunsurun ta wurin kulawar mutumin da ya shirya ya jagoranci bunsurun zuwa cikin jeji.
\v 22 Dole bunsurun ya ɗaukarwa kansa dukkan muguntar mutane zuwa wurin da ba kowa. A can cikin jeji, mutumin zai saki bunsurun ya tafi hakanan.
\s5
\v 23 Daga nan dole Haruna ya koma cikin rumfar taruwa ya tuɓe rigunansa na linin waɗanda ya sa kafin ya shiga wuri mafi tsarki, kuma dole ya bar rigunan can.
\v 24 Dole ya wanke jikinsa a cikin ruwa cikin wuri mai tsarki, ya sa tufafinsa da ya saba; daga nan dole ya fito ya miƙa baikonsa na ƙonawa da baikon ƙonawa domin jama'a, ta haka zai yi kaffara domin kansa kuma domin jama'a.
\s5
\v 25 Dole ya ƙone kitsen baikon zunubi a bisa kan bagadi.
\v 26 Mutumin da ya bar refataccen bunsuru ya tafi dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa; bayan haka, zai iya dawowa cikin sansani.
\s5
\v 27 Bijimi domin baikon zunubi da bunsurun domin baikon zunubi, wanda aka kawo jininsu domin kaffara cikin wuri mai tsarki, dole a ɗauke su waje bayan sansani. A can dole su ƙone fatarsu, namansu, da kashinsu.
\v 28 Mutumin da ya ƙone waɗannan sassan dole ya wanke tufafinsa ya wanke jikinsa cikin ruwa; bayan haka, zai iya dawowa cikin sansani.
\s5
\v 29 Zai zama farilla a gare ku kullum a cikin wata na bakwai, a bisa rana ta goma, dole ku ƙasƙantar da kanku kada ku yi aiki, ko wanda aka haifa ɗan gari ko bãƙo wanda ya ke zama a cikinku.
\v 30 Saboda a ranar nan za ayi kaffara domin ku, a tsarkake ku daga dukkan zunubanku domin ku tsarkaka a gaban Yahweh.
\v 31 Assabat ta musamman ta hutawa domin ku, dole kuma ku ƙasƙantar da kanku kada ku yi wani aiki. Wannan zai zama farilla a gare ku kullum.
\s5
\v 32 Babban firist, wanda za a zuba masa mai a keɓe shi ya zama babban firist a madadin mahaifinsa, dole ya yi wannan kaffarar ya sa tufafin linin, wato, tufafi masu tsarki.
\v 33 Zai yi kaffara domin wuri mafi tsarki; dole ya yi kaffara domin rumfar taruwa da kuma domin bagadi, kuma dole ya yi kaffara domin firistoci kuma domin dukkan taron jama'a.
\s5
\v 34 Wannan zai zama farilla a gare ku koyaushe, a yi kaffara domin mutanen Isra'ila saboda dukkan zunubansu, sau ɗaya a cikin shekara." An yi haka kamar yadda Yahweh ya umarci Musa.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 2 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa, da dukkan mutanen Isra'ila. Ka faɗa masu abin da Yahweh ya umarta:
\v 3 'Duk mutumin da ke daga gidan Isra'ila wanda ya kashe sã, rago ko akuya a cikin sansani, ko wanda ya kashe shi a bayan sansani, domin ya miƙa shi hadaya -
\v 4 idan bai kawo shi a ƙofar rumfar taruwa ya miƙa shi hadaya ga Yahweh a gaban mazaunin sa ba, wannan mutum ya zama da laifin zubar da jini. Ya zubar da jini, wannan mutum dole a datse shi daga cikin jama'arsa.
\s5
\v 5 Dalilin wannan dokar shi ne domin mutanen Isra'ila su kawo hadayunsu ga Yahweh a ƙofar rumfar taruwa, wurin firist domin hadaya a matsayin baikon zumunta ga Yahweh, maimakon baikon hadayun da suke miƙawa a fili.
\v 6 Firist zai yayyafa jinin a bisa bagadin Yahweh a ƙofar rumfar taruwa, zai ƙona kitsen domin ya bada ƙanshi mai daɗi domin Yahweh.
\s5
\v 7 Nan gaba mutanen ba za su ƙara miƙa hadayunsu ga gumakan bunsuru ba, domin sun aikata kamar karuwai. Wannan zai zama farilla ta din-din din a gare su ga dukkan tsararsu.'
\s5
\v 8 Dole ka ce masu, 'Kowanne mutumin Isra'ila, ko kowanne baƙon da ke zaune a cikinsu, wanda ya miƙa baikon ƙonawa ko hadaya
\v 9 kuma bai kawo ta a ƙofar rumfar taruwa domin a miƙa ta ga Yahweh ba, wannan mutumin dole a fitar da shi daga jama'arsa.
\s5
\v 10 Idan wani mutumin gidan Isra'ila, ko wani baƙon da ke zaune a cikin su ya sha kowanne irin jini, zan sa fuskata gãba da wannan mutum da ya sha jini kuma zan datse shi daga cikin jama'arsa.
\v 11 Gama ran dabba yana cikin jininsa. Na bada jininsa gare ku domin ku yi kaffara a bisa bagadi domin rayukanku, saboda jini ne ke yin kaffara, gama jini ke yin kaffara domin rai.
\s5
\v 12 Domin wannan na ce da mutanen Isra'ila ba wani a cikinku da zai ci jini, ko kowanne bãƙo da ke zaune a cikinku ya ci jini.
\v 13 Kowanne mutumin Isra'ila, ko baƙin da ke zaune a cikinsu, wanda ya yi farauta ya kashe dabba ko tsuntsun da za a iya ci, dole wannan mutumin ya zubar da jinin sa'an nan ya rufe jinin da ƙasa.
\s5
\v 14 Gama ran dukkan halitta yana cikin jininta. Shi ya sa na ce da mutanen Isra'ila, "Ba za ku ci jinin kowacce halitta ba, gama ran kowacce halitta yana cikin jininta. Duk wanda ya ci ya zama dole a datse shi."
\s5
\v 15 Kowanne mutumin da ya ci dabbar data mutu ko wadda namomin jeji suka yayyaga, ko mutumin nan haifaffen gida ne ko baƙon da ke zama a cikinku, dole ya wanke tufafinsa ya kuma yi wanka cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har yamma. Sa'an nan zai tsarkaka.
\v 16 Amma idan bai wanke tufafinsa ba ko ya wanke jikinsa ba, daga nan dole ya ɗauki alhakin laifinsa.'"
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Ni ne Yahweh Allahnku.
\v 3 Ba za ku yi abubuwan da mutane ke yi a Masar ba, in da kuka taɓa zama. Ba za ku yi abubuwan da mutane ke yi a Kan'ana ba, ƙasar da nake kai ku. Kada ku bi al'adunsu.
\s5
\v 4 Shari'una su ne za ku yi dole, dokokina kuma su ne za ku kiyaye dole, domin ku yi tafiya cikinsu, saboda ni ne Yahweh Allahnku.
\v 5 Don haka dole ku kiyaye umarnaina da shari'una. Idan mutum ya yi biyayya da su, zai rayu saboda su. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 6 Ba wanda zai kwanta da kowanne dangi na kusa domin ya buɗe tsiraicinsa. Ni ne Yahweh.
\v 7 Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwanciya da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce! Kada ka ƙasƙantar da ita.
\v 8 Kada ka kwana da kowacce matar mahaifinka; kada ka ƙasƙantar da mahaifinka kamar haka.
\s5
\v 9 Kada ka kwana da kowacce 'yar'uwarka, ko ita ɗiyar mahaifinka ce ko ɗiyar mahaifiyarka, ko a gidan ku ta girma ko a wani gida na nesa da kai. Kada ka kwana da 'yan'uwanka mata.
\v 10 Kada ka kwana da ɗiyar ɗanka ko ɗiyar 'yarka. Wannan zai zama abin kunya gare ka.
\v 11 Kada ka kwana da ɗiyar matar mahaifinka, wadda mahaifinka ya haifa. Ita 'yar'uwarka ce, kuma kada ka kwana da ita.
\s5
\v 12 Kada ka kwana da 'yar'uwar mahaifinka, Ita 'yar'uwar mahaifinka ce ta kusa.
\v 13 Kada ka kwana da 'yar'uwar mahaifiyarka. Ita 'yar'uwar mahaifiyarka ce ta kusa.
\v 14 Kada ka ƙasƙantar da ɗan'uwan mahaifinka ta wurin kwana da matarsa. Kada ka yi kusa da ita akan wannan dalili; ita bãbarka ce.
\s5
\v 15 Kada ka kwana da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ce; kada ka kwana da ita.
\v 16 Kada ka kwana da matar ɗan'uwanka; kada ka ƙasƙantar da shi ta wurin yin haka.
\s5
\v 17 Kada ka kwana da mace da ɗiyarta kuma, ko ɗiyar ɗanta ko ɗiyar 'yarta. Su danginta ne na kusa, kwana da su zai zama mugunta.
\v 18 Ba zaka auri 'yar'uwar matarka a matsayin kishiyarta ba kuma ka kwana da ita yayin da matarka ta farko na da rai.
\s5
\v 19 Kada ka kwana da mace a lokacin hailarta. Ba ta da tsarki a wannan lokacin.
\v 20 Kada ka kwana da matar maƙwabcinka kuma ka ƙazantar da kanka da ita ta wannan hanya.
\s5
\v 21 Kada ka bada ko ɗaya daga cikin 'ya'yanka a sa su cikin wuta, domin ka miƙa su hadaya ga Molek, saboda ba za ka tozarta sunan Allahnka ba. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 22 Kada ka kwana da wasu maza kamar yadda ake yi da mace. Wannan zai zama mugunta.
\v 23 Kada ka kwana da kowacce dabba ka kuma ƙazantar da kanka da ita. Ba wata mace da zata kwana da kowacce dabba. Wannan zai zama keta doka.
\s5
\v 24 Kada ka ƙazantar da kanka ta kowanne irin waɗannan hanyoyi, gama ta cikin irin waɗannam hanyoyi ne al'ummai suka ƙazantu, al'umman da na kora daga gaban ku.
\v 25 ƙasar ta ƙazantu, na hukunta zunubansu, ƙasar ta amayar da mazaunanta.
\s5
\v 26 Domin haka, ku, dole ku kiyaye dokokina da umarnaina, kuma ba za ku aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan banƙyama ba, ko haifaffen Ba - Isra'ile ko bãƙon da ke zaune a cikinku.
\v 27 Gama wannan ita ce muguntar da mutanen cikin ƙasar da suka rigaye ku suka aikata, waɗanda suka zauna nan kafin ku, yanzu kuma ƙasar ta ƙazantu.
\v 28 Don haka sai ku yi hankali don kada ƙasar ta amayar da ku bayan da kun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da mutanen da suka rigaye ku.
\s5
\v 29 Duk wanda ya aikata kowanne ɗaya daga cikin abubuwan banƙyamar nan, mutanen da suka yi waɗannan za a datse su daga cikin jama'arsu.
\v 30 Don haka dole ku kiyaye dokata kada ku aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan al'adun mãsu banƙyama waɗanda aka aikata a nan a gaban ku, domin kada ku ƙazantar da kanku ta wurin su. Ni ne Yahweh Allahnku.'"
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa cewa,
\v 2 "Ka yi magana ga dukkan taron jama'ar Isra'ila ka ce masu, "Dole ku zama da tsarki, gama ni Yahweh Allahnku mai tsarki ne.
\v 3 Kowanne dole ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, kuma dole ku kiyaye assabataina. Ni ne Yahweh Allahnku.
\v 4 Kada ku juya ga gumakai marasa amfani, ko ku yi wa kanku alloli na ƙarfe. Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 5 Sa'ad da ka miƙa hadaya ta zumuntar baye-baye ga Yahweh, dole ka miƙa ta yadda za a karɓe ka.
\v 6 Dole a cinye ta a ranar da aka miƙa ta, ko kuma washegari. Idan wani abu ya rage har rana ta uku, dole a ƙone shi da wuta.
\v 7 Idan anci ta ko kaɗan a kan rana ta uku, naman ya zama marar tsarki; ba za a karɓe ta ba,
\v 8 kuma duk wanda ya ci dole ya ɗauki alhakin laifinsa saboda ya ƙazantar da abin da ke mai tsarki na Yahweh, wannan mutum dole a datse shi daga jama'arsa.
\s5
\v 9 Sa'ad da kuka girbe amfanin ƙasarku, ba za ku girbe kusurwowin gonarku dukka ba, ba kuma za ku tattara dukkan amfanin girbin ku ba.
\v 10 Ba za ku tattara kowanne inabi daga garkar inabin ba, ko ku tattara inabin da ya faɗi a ƙasa cikin garkar. Dole ku bar su domin matalauta kuma domin bãƙi. Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 11 Kada ku yi sata. Kada ku yaudari juna.
\v 12 Kada ku rantse da sunana kan ƙarya kuma ku tozarta sunan Allahnku. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 13 Kada ka zalunci makwabcinka ko ka yi masa fashi. Haƙin bawan da aka yi hayarsa kada ya kwana wurinka har safiya.
\v 14 Kada ka la'anta kurma ko ka sa abin tuntuɓe gaban makaho. Maimakon haka, dole ku ji tsoron Allah. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 15 Kada ka aikata rashin gaskiya cikin shari'a. Kada ka nuna tãra ga wani saboda shi talaka ne, kuma kada ka nuna tãra ga wani saboda muhimmancinsa. Maimakon haka, ka shari'anta makwabcinka bisa ga adalci.
\v 16 Kada ka yi tafiyar yawon ɓatanci a cikin mutanenka, amma ka nemi kare ran makwabcinka. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 17 Kada ka ƙi ɗan'uwanka a zuciyarka. Dole ka tsauta wa maƙwabcinka akan gaskiya domin kada zunubinsa ya shafe ka.
\v 18 Kada ka ɗaukar wa kanka fansa ko ka riƙe shi da ƙiyayya gãba da wani cikin mutanenka, amma maimakon haka sai ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 19 Dole ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da wasu irin dabbobi dabam. Kada ku cuɗa iri biyu lokacin da kuke shuka a gonarku. Kada ku sa tufafin da aka yi da ke da haɗe-haɗe iri biyu tare.
\s5
\v 20 Duk wanda ya kwana da yarinyar da take baiwa wadda aka alƙawarta wa miji, amma ba a fanshe ta ba ko 'yanta ta ba, dole a hukunta su. Ba za a kashe su ba saboda ba a 'yanta ta ba.
\v 21 Sai mutumin ya kawo baikon laifinsa ga Yahweh a ƙofar shiga rumfar taruwa - rago domin hadayar laifi.
\v 22 Daga nan firist zai yi kaffara domin sa da rago domin baikon laifi a gaban Yahweh, domin zunubin da ya aikata. Daga nan za a gaffarta masa zunubin da ya yi.
\s5
\v 23 Sa'ad da kuka zo cikin ƙasar kuma kuka dasa ko waɗanne irin itatuwa domin abinci, sai ku maida 'ya'yan itatuwansu haramtattu gare ku har shekaru uku. Ba za ku ci su ba.
\v 24 Amma a cikin shekara ta huɗu dukkan amfaninsu za su zama mãsu tsarki, baikon yabo ga Yahweh.
\v 25 A cikin shekara ta biyar za ku iya cin amfanin, domin kun jira saboda itatuwan su ƙara ba da 'ya'ya da yawa. Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 26 Kada ku ci kowanne irin nama tare da jininsa a cikinsa. Kada ku tuntuɓi ruhohi game da abin da zai faru nan gaba, kada ku nemi ku mulki waɗansu ta wurin manyan ikoki ko duba.
\v 27 Ba za ku aske gashin kanku a kewaye ko ku aske ƙarshen gemunku ba.
\v 28 Kada ku yanke jikinku domin matattu ko ku yi tsaga a jikinku. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 29 Kada ka kunyatar da ɗiyarka ta wurin sa ta karuwanci, ko ƙasar ta faɗa cikin karuwanci ƙasar kuma ta cika da mugunta.
\v 30 Dole ku kiyaye Assabataina ku girmama mazaunina mai tsarki. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 31 Kada ku juya wurin waɗanda suke magana da matattu ko da ruhohi, kada ku neme su, domin za su ƙazantar da ku. Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 32 Dole ku tashi tsaye gaban wanda ya ke da furfura kuma ku gimama kasancewar dattijo. Dole ku ji tsoron Allah. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 33 Idan bãƙo na zaune a wurinku cikin ƙasarku, kada ku cutar da shi.
\v 34 Bãƙon da ke zaune tare da ku dole ya zama kamar haifaffen Ba-Isra'ile wanda ya ke zama a cikin ku, kuma dole ka ƙaunace shi kamar kanka, saboda dã ku bãƙi ne a cikin ƙasar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 35 Kada ku yi awo da ma'aunin ƙarya lokacin auna tsawo, nauyi ko yawa.
\v 36 Dole ku yi amfani da ma'auni, madaidaici, kwanon gaskiya kofi na gaskiya. Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fitar da ku daga ƙasar Masar.
\v 37 Dole ku kiyaye dukkan farillaina da dokokina, kuma ku aikata su. Ni ne Yahweh.'"
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa cewa,
\v 2 "Ka faɗa wa mutanen Isra'ila 'Duk wanda ke daga cikin jama'ar Isra'ila, ko bãƙon da ke zaune a cikin Isra'ila ya miƙa ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga gunkin nan Molek, dole a kashe shi. Dole mutanen cikin ƙasar su jejjefe shi da duwatsu.
\s5
\v 3 Zan kuma sa fuskata gãba da wannan mutumin in kuma datse shi daga cikin mutanensa domin ya miƙa ɗansa ga Molek, domin ya ƙazantar da wurina mai tsarki ya kuma muzanta sunana mai tsarki.
\v 4 Idan jama'ar ƙasar suka kulle idanunsu ga wannan mutumin a lokacin da ya ke miƙa ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, Idan suka ƙi kashe shi,
\v 5 Sa'an nan Ni da kaina zan sa fuskata gãba da wannan mutumin da danginsa, zan kuma datse shi da kuma dukkan wanda ya shiga karuwanci domin ya aikata karuwaci tare da Molek.
\s5
\v 6 Mutum wanda ya juya ga waɗanda suke magana da matattu, ko ga waɗanda ke magana da ruhohi don ya yi karuwanci tare da su, Zan sa fuskata gãba da wannan mutumin; Zan datse shi daga cikin mutanen sa.
\v 7 Don haka ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 8 Dole ku kiyaye umarnaina ku kuma aikata su. Ni ne Yahweh wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka.
\v 9 Duk wanda ya la'anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi. Ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, to ya yi laifi kenan ya kuma cancanci mutuwa.
\s5
\v 10 Mutumin da ya yi zina da matar wani, wato, dukkan wanda ya yi zina da matar maƙwabcinsa - mazinacin da mazinaciyar dole ne a kashe su.
\v 11 Idan mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya buɗe tsiraicin mahaifinsa. Da ɗan da matar mahaifinsa dole a kashe su. Alhakin jininsu na kansu.
\v 12 Idan mutum ya kwana da matar ɗansa, dukkan su dole ne a kashe su, sun aikata abin ƙyama. Masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa.
\s5
\v 13 Idan mutum ya kwana da namiji, yadda ake yi da mace, dukkansu sun aikata mummunan abin ƙyama. Hakika tilas ne a kashe su. Masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa.
\v 14 Idan mutum ya auri mace ya kuma auri mahaifiyarta, wannan mugunta ce. Dole ne a ƙone su, shi da matar dukka, domin ya zama babu mugunta a tsakiyarku.
\s5
\v 15 Idan mutum ya kwana da dabba, dole ne a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar.
\v 16 Idan mace ta kusanci kowacce dabba domin ta kwana da ita, dole ku kashe macen da dabbar. wajibi ne ku kashe su. masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa.
\s5
\v 17 Idan mutum ya kwana da 'yar'uwarsa, ɗiyar mahaifinsa ko ɗiyar mahaifiyarsa, ya kuma buɗe tsiraicinta, ita kuma ta ga tsiraicinsa, abin kunya ne. Dole a datse su daga gaban jama'arsu, saboda ya kwana da ƴar'uwarsa. Dole ya ɗauki alhakin sa.
\v 18 Idan mutum ya kwana da mace a lokacin jinin al'adarta har ya kwana da ita, har ya buɗe jinin da ke gudanowa daga jikinta, maɓulɓular jininta. Da mutumin da matar dole a datse su daga cikin jama'arsu.
\s5
\v 19 Ba za ka kwana da 'yar'uwar mahaifiyarka ba, ko kuma da 'yar'uwar mahaifinka, domin zaka ƙasƙantar da danginka na kusa. Wajibi ne ka ɗauki alhakinka.
\v 20 Idan mutum ya kwana da bãbarsa, ya ƙasƙantar da kawunsa. Za su ɗauki hakkin zunubinsu, za su kuma mutu babu 'ya'ya.
\v 21 Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa sa'ad da ɗan'uwansa ke da rai, wannan ƙasƙanci ne. Ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa, kuma zan ɗauke wa 'ya'yansu duk wata mallaka da suka gada daga iyayensu.
\s5
\v 22 Saboda haka wajibi ne ku kiyaye dukka farillaina da dukkan dokokina; Dole ku yi biyayya da su domin kada ƙasar da Na ke kai ku domin ku zauna a ciki ta amayar da ku daga cikinta.
\v 23 Ba za ku yi tafiya cikin al'adun al'umman da nake kora daga gabanku ba, domin sun aikata duk waɗannan abubuwan, kuma na ƙyamace su.
\s5
\v 24 Na faɗa maku, "Za ku gãji ƙasarsu; Zan ba ku ita ku mallaketa, ƙasa mai ɓulɓulo da madara da zuma. Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran mutane.
\v 25 Dole ne ku bambanta tsakanin dabbobi masu tsarki da marasa tsarki, da kuma tsakanin tsuntsaye marasa tsarki da masu tsarki. Wajibi ne ku ƙaurace wa ƙazantar da kanku da dabbobi ko tsuntsaye ko da kowacce irin halitta mai rarraffe akan ƙasa, wanda Na keɓe su a matsayin ƙazamtattu daga gare ku.
\s5
\v 26 Dole ne ku zama da tsarki, gama Ni, Yahweh, Mai Tsarki ne, kuma Na keɓe ku daga sauran mutane, saboda ku nawa ne.
\s5
\v 27 Mutum ko matar da ke yin magana da matacce ko suke yin magana da ruhohi dole ne a kashe su. Dole jama'a su jejjefe su da duwatsu. masu laifi ne sun kuma cancanci mutuwa.'"
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Yahweh ya cewa Musa: "Ka yi magana da firistoci, 'ya'ya maza na Haruna, ka ce masu, 'Kada a sami wani a cikinku da zai ƙazantar da kansa da gawar wanda ya mutu daga cikin mutanensa,
\v 2 sai dai idan shi dangi ne na kusa - mahaifiyarsa, mahaifinsa, ɗansa, 'yarsa, ɗan'uwansa,
\v 3 ko 'yar'uwarsa budurwa wadda ya ke rike da ita, tunda ya ke bata da miji - saboda ita yana iya ƙazantar da kansa.
\s5
\v 4 Amma kada ya ƙazantar da kansa saboda waɗansu dangi ta haka ya kuma ɓata kansa.
\v 5 Firistoci ba za su aske kansu ko su aske gefen gemun su, ko su yanka jikkunnansu ba.
\v 6 Dole su zama tsarkaka ga Allahnsu, kada kuma su ƙasƙantar da sunan Allahnsu, gama firistoci ke miƙa hadayun Yahweh na abinci, gurasa ta Allahnsu. Don haka wajibi ne firistoci su zama da tsarki.
\s5
\v 7 Ba za su auri kowacce mace wadda take karuwa ba da wadda aka ɓata, Kuma ba za su auri mace wadda mijinta ya sake ta ba, domin su keɓaɓɓu ne ga Allahnsu.
\v 8 Za ku keɓe shi, domin shi ne mai miƙa gurasa ga Allahnku. Dole ya zama da tsarki gare ku, domin Ni, Yahweh wanda ya tsarkake ku, Mai Tsarki ne.
\v 9 Duk wata ɗiya ta firist da ta ƙazantar da kanta ta wurin zama karuwa ta ƙasƙantar da mahaifinta. Dole a ƙone ta.
\s5
\v 10 Wanda ya ke shi ne babban firist daga cikin "yan'uwansa, wanda aka zuba mai na keɓewa a kansa, wanda kuma aka tsarkake domin ya sa rigar babban firist, ba zai kwance gashin kansa ko ya keta tufafinsa ba.
\v 11 Ba zai je wurin da akwai gawa ba ya kuma ƙazantar da kansa, ko da mataccen mahaifinsa ne ko mahaifiyarsa ce.
\v 12 Babban firist ba zai bar harabar haikali ko ya ƙazantar da haikalin Allahnsa ba, domin an keɓe shi a matsayin babban firist ta wurin man keɓewa na Allahnsa. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 13 Wajibi ne babban firist ya auri budurwa a matsayin matarsa.
\v 14 Ba zai auri gwauruwa, ko sakakkiyar mace, ko mace wadda take karuwa ba. Ba zai auri irin waɗannan matan ba. Zai iya auren budurwa daga cikn jama'arsa,
\v 15 domin kada ya ƙazantar da 'ya'yansa daga cikin jama'arsa, domin Ni ne Yahweh, wanda ya maishe shi tsarkakakke.'"
\s5
\v 16 Yahweh ya yi magana da Musa, ya ce,
\v 17 "Ka yi magana da Haruna ka faɗa masa, 'Dukkan wanda aka samu da wata nakasar jiki cikin zuriyarka a dukkan tsararrakinsu, ba zai matso kusa domin ya miƙa abinci ga Allahnsa ba.
\s5
\v 18 Kowanne mutum da ke da nakasa a jiki kada ya kusanci Yahweh, irin wannan makahon ko mutumin da bai iya tafiya, shi da ya ke da nakasa a jiki ko fuskar,
\v 19 mutumin da ke da nakasa a hannu ko a ƙafa,
\v 20 mutumin da ke da ƙusumbi a bayansa ko shanyayye ko wãda, ko mutumin da ke da hãkiya a idanunsa, ko ya ke da cuta, gyambo, ƙurji, ko rauni a mazakutta.
\v 21 Ba wani mutum daga cikin zuriyar Haruna firist mai nakasa a jikinsa da zai matso kusa domin ya miƙa baye-bayen da ake miƙawa da wuta ga Yahweh. Irin wannan mutumin mai naƙasa a jiki; kada ya zo kusa domin ya miƙa gurasar Allahnsa.
\s5
\v 22 Ya iya cin abincin Allahnsa, ko daga cikin mafi tsarki ko kuma daga cikin mai tsarki.
\v 23 Duk da haka, Ba zai shiga daga cikin labulen ko ya zo kusa da bagadi ba, saboda yana da naƙasa a jikinsa, domin kada ya ƙazantar da tsattsarkan wurina, gama Ni ne Yahweh, wanda ya tsarkake su."'
\v 24 Haka Musa ya faɗawa Haruna waɗannan maganganu, ga 'ya'yansa, da kuma ga dukkan mutanen Isra'ila.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 2 "Ka yi magana da Haruna da 'ya'yansa maza, ka faɗa masu su kiyaye kansu daga kayayyaki masu tsarki na mutanen Isra'ila, waɗanda suka keɓe gare ni. Ba za su ƙasƙantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Yahweh.
\v 3 Ka faɗa masu, 'Idan wani daga cikin zuriyarku cikin dukkan tsararrakinku ya kusanci kayayyaki masu tsarki da jama'ar Isra'ila suka keɓe ga Yahweh, a sa'ad da ya ke marar tsarki, wannan mutumin dole a datse shi daga gabana: Ni ne Yahweh.
\s5
\v 4 Kada wani daga cikin zuriyar Haruna wanda ke da cutar fata, ko mai miki da ke zubar da ruwa daga jikinsa, ya ci ko ɗaya daga waɗannan hadayun da aka miƙa ga Yahweh har sai ya tsarkaka. Dukkan wanda ya taɓa wani abu marar tsarki ta wurin taɓa gawa, ko ta wurin taɓa mutum mai zub da maniyyi,
\v 5 ko kowacce dabba mai rarrafe data ƙazantar da shi, ko kowanne mutum ɗaya maida shi marar tsarki, ko dai kowacce irin ƙazanta ta zama-
\v 6 daga nan firist wanda ya taɓa kowanne abu marar tsarki zai zama marar tsarki har maraice. Ba zai ci duk wani abu mai tsarki ba, har sai ya wanke jikinsa a cikin ruwa.
\s5
\v 7 Sa'ad da rana ta faɗi, zai zama tsarkakakke. Bayan rana ta faɗi ya iya ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa, domin su abincinsa ne.
\v 8 Ba zai ci duk abin da aka same shi matacce ba ko abin da naman jeji ya kashe, wanda ta wurin haka zai ƙazantar da kansa. Ni ne Yahweh.
\v 9 Wajibi ne firistoci su bi umarnaina, domin kada su yi zunubi, su mutu domin muzanta ni. Ni ne Yahweh wanda ke tsarkake su.
\s5
\v 10 Kada wanda ba daga iyalin firist ya ke ba, duk da baƙon da ya sauka a gidan firist ko barorinsa, ya ci duk abin da ya ke tsatstsarka.
\v 11 Amma idan firist ya sayi wani bawa da kuɗinsa, wannan bawan na iya ci daga cikin abin da aka keɓe ga Yahweh. Iyalan gidan firist da kuma bayin da aka haifa a gidansa, za su iya cin waɗannan abubuwan tare da shi.
\s5
\v 12 Idan ɗiyar firist ta auri wani mutum wanda ba firist ba, ba za ta ci ko ɗaya daga cikin baye-bayen gudunmuwa mai tsarki ba.
\v 13 Amma idan ɗiyar firist ɗin gwauruwa ce, ko kuma sakakkiya, kuma idan bata da ɗa, kuma idan ta koma ta zauna a gidan mahaifinta kamar a lokacin ƙuruciyarta, za ta iya ci daga cikin abincin mahaifinta. Amma kada wani wanda ba daga cikin iyalin firist ya ke ba yaci abincin firist.
\s5
\v 14 Idan mutum yaci abinci mai tsarki ba da sani ba, dole ya biya firist abin da ya ci; wajibi ne ya ƙara kashi ɗaya bisa biyar akan abin ya kuma maida wa firist.
\v 15 Mutanen Isra'ila ba za su ƙazantar da abubuwa masu tsarki waɗanda suka ɗaga sama suka miƙa ga Yahweh ba.
\v 16 Su jawowa kansu ɗaukar zunubin da zai sa su yi laifin cin abinci mai tsarki, gama Ni ne Yahweh wanda ya ke tsarkake su."
\s5
\v 17 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 18 "Ka yi magana da Haruna shi da 'ya'yansa maza, da dukkan mutanen Isra'ila. Ka faɗa masu, 'Duk Ba-Israi'le, ko bãƙon da ke zaune cikin Isra'ila, lokacin da suka kawo hadaya- kodai ta cika wa'adi, ko ta bayarwar yadda rai, ko idan sun kawo hadayar ƙonawa ga Yahweh,
\v 19 Idan za ta zama karɓaɓɓiya, dole su miƙa dabba namiji marar aibu daga cikin garken shanu, tumaki, ko awaki.
\s5
\v 20 Amma kada ku miƙa duk wani abu mai aibu. Ba zan karbe su a maimakon ku ba.
\v 21 Kowanne mutum da ya miƙa hadaya ta salama daga cikin garke ko tumaki ga Yahweh don cika wa'adi, ko a matsayin bayarwar yardar rai, dole ta zama marar aibu kafin a karɓe ta. Kada a sami nakasa cikin dabbar.
\s5
\v 22 Ba zaku miƙa mani dabbobi makafi ba, ko guragu, ko naƙasassu, ko masu kirci, ko masu ƙuraje, ko tabbai. Ba za ku miƙa waɗannan ga Yahweh a matsayin hadaya ta ƙonawa a kan bagadi ba.
\v 23 Zaku iya miƙa bayarwar yardar rai da sã, ko da ɗan rago da ke da naƙasa ko ƙanƙane, amma bayarwa irin wannan ba za ta karɓu domin cika wa'adi ba.
\s5
\v 24 Kada ku miƙa wa Yahweh kowacce dabbar da ke da ƙurji, gurzajje, yayyagagge, ko dandaƙaƙƙe ba. Ba za ku yi wannan a cikin ƙasarku ba.
\v 25 Kada kubar baƘo ya miƙa maku gurasa ga Allahnku. Waɗannan dabbobin naƙasassu ne suna kuma da aibu a cikin su, ba za'a karɓe su a madadinku ba."
\s5
\v 26 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 27 "Sa'ad da aka haifi ɗan maraki, ko ɗan tunkiya ko ɗan akuya, dole ya zauna tare da mahaifiyarsa har kwana bakwai. A kwana na takwas, a iya karbar shi a matsayin hadayar ƙonawa da wuta ga Yahweh.
\s5
\v 28 Ba za ku kashe saniya ko tunkiya tare da ƙananunsu, dukka a rana ɗaya ba.
\v 29 Duk sa'ad da kuke miƙa hadaya ta godiya ga Yahweh, dole ku miƙa ta ta karɓaɓɓiyar hanya.
\v 30 Dole ku cinye naman hadayar a ranar da aka miƙa ta. Ba za ku rage komai daga ciki zuwa safiya ba. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 31 Dole ne ku kiyaye dokokina ku kuma aikatasu dukka. Ni ne Yahweh.
\v 32 Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole ne a san ni a matsayin mai tsarki ta wurin jama'ar Isra'ila. Ni ne Yahweh mai tsarkake ku,
\v 33 wanda ya fishsheku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku: Ni ne Yahweh.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Yahweh ya faɗa wa Musa:
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, kace masu, 'waɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwanku ga Yahweh, waɗanda dole ku shaida su a matsayin tattaruwa mai tsarki; su ne bukukuwana na yau da kullum.
\s5
\v 3 Za ku iya yin aiki kwanaki shida, amma rana ta bakwai asabar ce ta cikakken hutu, tattaruwa mai tsarki. Ba za ku yi wani aiki ba domin asabar ce ta Yahweh a cikin dukkan wuraren da kuke zaune.
\s5
\v 4 Waɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwa na Yahweh, tattaruwa mai tsarki da dole ku sanar a ƙayyadaddu lokuttansu:
\v 5 A wata na farko, a rana ta goma sha huɗu ga wata washegari, ranar bukin ƙetarewa ne na Yahweh.
\v 6 A rana ta goma sha biyar ga wannan watan ranar za ta zama ranar bukin gurasa marar gami ga Yahweh. Dole za ku ci gurasa marar gami har tsawon kwana bakwai.
\s5
\v 7 A rana ta farko za ku keɓe kanku domin ku taru wuri ɗaya; ba za ku yi kowanne irin aiki da kuka saba yi ba.
\v 8 Za ku miƙa bayarwar abinci ga Yahweh har kwana bakwai. Kwana na bakwai tattaruwa ce keɓaɓɓiya ga Yahweh, kuma a wannan rana wajibi ne ba za ku yi kowanne aiki da kuka saba yi ba.
\s5
\v 9 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 10 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Lokacin da kuka shiga cikin ƙasar da zan ba ku, Sa'ad da kuka yi girbi, wajibi ne ku kawo dami na nunar fari na hatsin ga firist.
\v 11 Shi zai ɗaga damin hatsin a gaban Yahweh ya kuma miƙa shi gare shi, domin a karɓe shi a maimakon ku. A kwana ɗaya bayan assabacin firist zai ɗaga abin ya kuma gabatar da shi gare ni.
\s5
\v 12 A ranar da kuka ɗaga damin hatsin kuka kuma miƙa shi gare ni, wajibi ne ku miƙa ɗan rago mai shekara ɗaya kuma marar naƙasa hadaya ta ƙonawa ga Yahweh.
\v 13 Hadaya ta gari wajibi ne ta zama kashi biyu bisa goma na lallausan gari da aka gauraya da mai, bayarwar da aka yi da wuta ga Yahweh. Domin ta bada ƙamshi mai daɗi, kuma tare da ita hadaya ta abin sha, awo huɗu na ruwan inabi.
\v 14 Ba za ku ci gurasa, ko gasashshen nama, ko ɗanyen hatsi ba, har sai ranar da kuka kawo sadakar ga Allahnku ta kewayo. Wannan farilla haka zata zama din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku, a cikin dukkan wurin da kuke zaune.
\s5
\v 15 Tun daga kwana ɗaya bayan ranar asabaci-Wannan ce ranar da ku ka kawo damin hatsi a matsayin sadaka ta ɗagawa - ku ƙirga makonni bakwai cikakku.
\v 16 Dole ku ƙirga kwanaki hamsin, wanda zai kasance rana bayan asabar ta bakwai. Wajibi ne ku miƙa bayarwar sabon hatsi ga Yahweh.
\s5
\v 17 Dole ku ɗibo curi biyu daga cikin gidajenku da aka yi da kashi biyu bisa goma na garwa. Wajibi ne a yi su da lallausan gari da aka yi da gami; zasu zama bayarwar nunar fari ta ɗagawa ga Yahweh.
\v 18 Za ku miƙa gurasar tare da 'yan raguna bakwai masu shekara ɗaya marasa aibu, ɗan maraƙi ɗaya, da raguna biyu. Dole su zama hadaya ta ƙonawa ga Yahweh, tare da hadayar garin da hadaya ta sha, bayarwar da aka yi da wuta mai kuma bada ƙanshi ga Yahweh.
\s5
\v 19 Za ku miƙa bunsuru ɗaya domin hadaya ta zunubi, ku kuma miƙa 'yan raguna biyu masu shekara ɗaya hadaya, a matsayin hadaya ta zumunci.
\v 20 Wjibi ne firist ya kaɗa su tare da gurasar nunar fari a gaban Yahweh, ya kuma miƙa su gare shi a matsayin bayarwa tare da 'yan raguna biyu. Za su zama baye-baye masu tsarki na Yahweh domin firist.
\v 21 Dole kayi shaida a wannan ranar. Za'a haɗa taro mai tsarki, kuma kada kuyi aikin da kuka saba yi. Wannan zai zama farilla na din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku a cikin dukkan wuraren da kuke zaune.
\s5
\v 22 Lokacin da kuka girbe amfanin gonarku, baza ku girbe har ƙurewar gonakinku ba, ba kuma za ku yi kalar gonakinku ba. Dole ne ku rage wa matalauta da baƙi su. Ni ne Yahweh Allahnku'".
\s5
\v 23 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 24 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka faɗi masu, 'A wata na bakwai, ranar farko ta wannan watan zata zama ranace ta cikakken hutu gare ku, ranar tunawa tare da busa sarewa, da kuma ranar taro mai tsarki.
\v 25 Ba za ku yi wani aiki ba, kuma dole ne ku miƙa hadaya da wuta ga Yahweh."'
\s5
\v 26 Sai Yahweh ya yi magana da Musa, cewa
\v 27 "Yanzu ranar goma ga wannan wata na bakwai ita ce Ranar Kaffara. Za ta kasance tattaruwa mai tsarki, kuma dole ku ƙasƙantar da kanku ku kuma miƙa baiko da wuta ga Yahweh.
\s5
\v 28 Ba za ku yi wani aiki a wannan rana ba gama Ranar Kaffara ce, ku yi kaffara domin kanku a gaban Yahweh Allahnku.
\v 29 Dukkan wanda bai ƙasƙantar da kansa a wannan rana ba dole a datse shi daga cikin mutanensa.
\s5
\v 30 Dukkan wanda ya yi wani aiki a wannan rana, Ni, Yahweh, zan hallakar da shi daga cikin mutanensa.
\v 31 Ba za ku yi kowanne irin aiki a wannan rana ba. Wannan zai zama farilla ta din-din din cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan wuraren da kuke zama.
\v 32 Ranar nan zata zama Assabat ta cikakken hutu gare ku, kuma dole ku ƙasƙantar da kanku a rana ta tara ga watan da maraice. Daga maraice zuwa maraice za ku kiyaye Assabacinku."
\s5
\v 33 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 34 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila, cewa, 'Rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai zata zama ranar bukukuwan bukkoki ga Yahweh. Za ku kiyaye shi har kwanaki bakwai.
\s5
\v 35 Za ku yi tattaruwa mai tsarki a rana ta fari. Ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba.
\v 36 Tsawon kwana bakwai za ku miƙa hadaya ta wurin wuta ga Yahweh. A rana ta takwas za ku yi taro mai tsarki, kuma dole ne ku miƙa hadaya ta wuta ga Yahweh. Wannan babban taro ne, kuma ba za ku yi aikin da kuka saba yi ba.
\s5
\v 37 Waɗannan su ne ƙayyadaddun bukukuwa ga Yahweh, waɗanda zaku shaida a matsayin tattaruwa mai tsarki ku miƙa hadayu na wuta ga Yahweh, bayarwar ƙonawa da kuma bayarwar gari, hadaya da kuma bayarwar abin sha, kowacce a ranar ta.
\v 38 Waɗannan bukukuwa ƙari ne ga Assabar ta Yahweh da kuma kyaututtukanku, dukkan alƙawuranku, da kuma dukkan baye-bayenku na yardar rai da kuka ba Yahweh.
\s5
\v 39 Dangane da bukukuwan bukkoki, a ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, lokacin da kuka gama tattara albarkun ƙasar, Dole ku kiyaye wannan bukukuwa ga Yahweh har kwana bakwai. Ranar farko zata zama ta cikakken hutu, haka rana ta takwas ma zata kasance ranar cikakken hutu.
\s5
\v 40 A rana ta fari za ku ɗauka daga cikin mafi kyau na 'ya'yan itatuwanku, rassan itatuwan dabino, da rassa masu ganyayyaki na itatuwa masu ƙarfi, da ciyayi masu yaɗo daga rafuka, zaku yi murna a gaban Yahweh Allahnku har kwana bakwai.
\v 41 Tsawon kwana bakwai a kowacce shekara, wajibi ne ku yi wannan buki ga Yahweh. Wannan zai zama farilla gare ku cikin dukkan tsararrakin mutanenku a dukkan wuraren da kuke zama. Dole ne ku yi bukin nan a wata na bakwai.
\s5
\v 42 Wajibi ne ku zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Dukkan haifaffen gidan Isra'ila dole ya zauna cikin ƙananan bukkoki tsawon kwana bakwai,
\v 43 domin zuriyarku, daga tsara zuwa tsara, su koyi yadda nasa mutanen Isra'ila suka zauna a cikin irin waɗannan bukkokin lokacin da na jagorance su daga cikin ƙasar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku."'
\v 44 Ta haka fa, Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila ƙayyadaddun bukukuwa ga Yahweh.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 2 "Ka umurci mutanen Isra'ila su kawo maka mai mai tsabta da aka tatso daga zaitun don a riƙa amfani dashi cikin fitilu, domin su yi ta bada haske ba yankewa.
\s5
\v 3 A wajen labulen a gaban akwatin alƙawari cikin rumfar taruwa, wajibi ne ga Haruna daga maraice zuwa safiya, ya sa fitila ta yi ta ci a gaban Yahweh. Wannan zai zama farillanku na din-din din cikin dukkan tsararrakin jama'arku.
\v 4 Dole babban firist ya sa fitilu su yi ta ci a gaban Yahweh, fitilun za su kasance a kan maɗorin da aka yi da zinariya tsantsa.
\s5
\v 5 Ka ɗauki lallausan gari ka yi curin gurasa goma sha biyu dashi. Kowanne curi a yi shi da adadin kashi biyu bisa goma na garwa.
\v 6 Sa'an nan wajibi ne ku jera su a layi biyu, shida a kan kowanne layi, a kan tebur na zinariya mai tsabta a gaban Yahweh.
\s5
\v 7 Wajibi ne ku sa turare mai tsabta a kan kowanne jerin gurasa a maimakon baiko. Wannan turaren za a ƙone shi domin Yahweh.
\v 8 Kowacce Assabar babban firist ya ajiye gurasa a gaban Yahweh a maimakon mutanen Isra'ila, a matsayin alama ta alƙawari na har abada.
\v 9 Wannan bayarwar zata zama domin Haruna da 'ya'yansa maza, kuma za su ci gurasar a wurin da ya ke mai tsarki, domin rabo ne daga baye-baye ga Yahweh da aka miƙa ta wuta."
\s5
\v 10 Ya zama fa ɗan wata mata Ba-isra'iliya, wanda mahaifinsa Ba-masare ne, ya tafi tare da mutanen Isra'ila. Wannan ɗan matar Ba-isra'iliya ya yi faɗa da mutumin Isra'ila a cikin zango.
\v 11 Wannan ɗan matar Ba-isra'iliya ya zagi sunan Yahweh ya kuma la'anta Allah, domin haka jama'a suka kawo shi gaban Musa. Sunan mahaifiyarsa Shelomit, ɗiyar Dibri, daga kabilar Dan.
\v 12 Suka tsare shi a kurkuku har sai sun ji abin da Yahweh da kansa zai furta nufinsa a kansu.
\s5
\v 13 Daga nan Yahweh ya yi magana da Musa, cewa,
\v 14 "Ka ɗauki mutumin da ya la'anta Allah bayan sansani. dukkan wanda ya ji shi dole su ɗibiya hannayensu a kansa, daga nan dukkan taron jama'a su jejjefe shi.
\s5
\v 15 Dole ka bayyanawa mutanen Isra'ila ka ce, "Duk wanda ya la'anci Allahnsa dole ya ɗauki alhakin laifinsa.
\v 16 Shi wanda ya saɓi sunan Yahweh hakika dole a kashe shi. Dukkan taron jama'a dole su jejjefe shi da dutse, ko shi baƙo ne ko haifaffen Ba-Isra'ile. Duk wanda ya yi saɓon sunan Yahweh, dole a kashe shi.
\s5
\v 17 Duk wanda ya bugi wani mutum har ya mutu, lallai dole shi ma a kashe shi.
\v 18 Idan wani ya bugi dabbar wani har ta mutu, dole ya mayar, rai maimakon rai.
\s5
\v 19 Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa rauni, dole ayi masa yadda ya yi wa maƙwabcinsa:
\v 20 tsaga maimakon tsaga, ido domin ido, haƙori domin haƙori. Kamar yadda ya jawo lahani ga mutum, to haka shi ma za'a yi masa.
\v 21 Duk wanda ya kashe dabba dole ya biya, kuma duk wanda ya kashe mutum dole shi ma a kashe shi.
\s5
\v 22 Dole ku kasance da doka iri ɗaya domin baƙo da wanda ya ke haifaffen Ba-Isra'ile, gama Ni ne Yahweh Allahnku.'"
\v 23 Sai Musa ya yi magana da mutanen Isra'ila, mutanen kuma suka fito da mutumin wajen sansani, wanda ya la'anta Yahweh. Suka jejjefe shi da duwatsu. Mutanen Isra'ila suka aiwatar da dokar Yahweh ta hannun Musa.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa akan tsaunin Sinai, cewa,
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, "Sa'ad da kuka zo cikin ƙasa wadda na ba ku, daga nan dole ƙasar za ta kiyaye Assabat domin Yahweh.
\s5
\v 3 Dole ku shuka gonarku shekaru shida, shekaru shida kuma dole ku gyara gonarku ta inabi ku tattara amfaninta.
\v 4 Amma a cikin shekara ta bakwai, dole a kula da Assabat mai saduda ta hutu, Assabat domin Yahweh. Ba za ku shuka gonar ba ko ku gyara gonar inabinku ba.
\s5
\v 5 Ba za ku shirya girbe duk abin da ya tsiro don kansa ba, kuma ba za ku shirya girbin inabin da ya tsiro a kuringar da baku gyara ba. Wannan za ta zama shekara mai saduda ta hutawa domin ƙasar.
\v 6 Duk tsiron da ƙasar da baku aikata ba ta bayar lokacin Assabat na ƙasar zai zama abinci domin ku. Ko, 'ya'yanku maza, da bayinku mata, da bayin da aka yi hayarsu, da baƙi da ke zaune tare da ku za ku iya tattara abinci,
\v 7 dabbobinku kuma da bisashenku za su iya cin amfanin da ƙasar ta bayar.
\s5
\v 8 Dole ku lisafta Assabat guda bakwai na shekaru, wato, bakwai sau shekaru bakwai, wato akwai Assabat bakwai na shekaru, jimilla duka shekaru arba'in da tara ke nan.
\v 9 Sa'an nan za ku busa ƙaho da ƙarfi ko'ina a rana ta goma a watan bakwai. A ranar kaffara dole ku busa ƙaho ko'ina a cikin ƙasarku.
\s5
\v 10 Dole ku keɓe shekara ta hamsin ga Yahweh kuma ayi shelar 'yanci ko'ina a ƙasar ga dukkan mazaunanta. Zata zama ranar mayarwa domin ku, inda kowacce mallaka da bayi dole za su koma wurin iyalinsu.
\s5
\v 11 Shekara ta hamsin zata zama shekarar mayarwa a gare ku. Ba za ku shuka ko shirya girbi. Ko cin duk abin da ya tsiro da kansa ba, kuma ba za ku tattara inabi da ya tsiro a kuringai da baku gyara ba.
\v 12 Gama Shekarar 'Yanci ce, wadda za ta zama mai tsarki domin ku. Dole kuci amfanin da ya tsiro don kansa a gonaki.
\s5
\v 13 Dole ku mayar wa da kowanne mutum mallakarsa a shekarar 'Yanci.
\v 14 Idan ka sayar da gona ga maƙwabcinka ko ka sayi gona a wurin maƙwabcinka, kada ku cuci ko ku zalunci juna.
\s5
\v 15 Idan ka sayi gona daga maƙwabcinka, sai ka yi la'akari da shekaru da amfanin da za a girbe har zuwa shekarar gaba ta 'Yanci. Maƙwabcinka da ke sayar maka da gonar dole ya kula da wannan shi ma.
\v 16 Yawan shekarun har zuwa shekarun 'Yanci zai ƙara tamanin ƙasar, gwargwadon ƙarancin shekarun za a rage tamanin ta, saboda yawan girbin da ƙasar zata bayar domin sabon mai gonar yana alaƙa da yawan shekaru kafin shekarar 'Yanci ta gaba.
\v 17 Ba za ku cuci ko ku zalunci juna ba; maimakon haka dole ku girmama Allahnku, gama Ni ne Yahweh Allahnku.
\s5
\v 18 Domin wannan dole ku kiyaye umarnaina, ku kiyaye dokokina, kuma ku aiwatar da su. Daga nan za ku zauna cikin ƙasar lafiya.
\v 19 ƙasa za ta bada amfaninta, kuma za ku ci ku ƙoshi kuma ku zauna can cikin tsaro.
\s5
\v 20 Za ku iya cewa, "Me zamu ci cikin shekara ta bakwai? Duba, ba dama mu shuka ko mu tattara amfaninmu ba."
\v 21 Zan umarci albarkata ta zo bisanku a cikin shekara ta shida, kuma zata bada isasshen amfani har shekaru uku.
\v 22 Za ku shuka cikin shekara ta takwas kuma ku ci gaba da cin abincin da kuka ajiye a shekarun baya. Har lokacin girbi na shekara ta tara ta zo, za ku ci daga tanajin ajiyar da kuka yi a shekarun baya.
\s5
\v 23 Ba za a sayar da ƙasa ga wani ya zama sabon mai ita ta din-din din ba, saboda ƙasa tawace. Dukkanku bãƙi ne masu zama na ɗan lokaci a ƙasa ta.
\v 24 Dole ku kula da haƙin fansa domin dukkan ƙasar da kuka mallaka; dole ku bari a sake sayen ƙasar ga iyalin daga wanda ya saye ta.
\v 25 Idan ɗan'uwanka Ba-Isra'ile ya zama talaka kuma akan wannan dalili ya sayar da wata mallaka tasa, daga nan danginsa na kusa zai iya zuwa ya fanshi mallakar da ya sayar maka.
\s5
\v 26 Idan mutum ba shi da ɗan'uwa da zai fãnshi mallakarsa, amma idan ya azurta har zai iya fãnsar ta,
\v 27 daga nan zai iya lissafta shekaru tun lokacin da aka sayar da ƙasar sai ya biya sauran ga mutumin da ya sayar wa. Daga nan zai iya dawo wa ga mallakarsa.
\v 28 Amma idan bai iya dawo da ƙasar domin kansa ba, daga nan ƙasar da ya sayar za ta kasance cikin mallakar shi wanda ya saye ta har zuwa lokacin shekarar 'Yanci. A shekarar 'Yanci, ƙasar zata koma ga mutumin da ya sayar da ita, ainihin mai ita kuma zai koma ga mallakarsa.
\s5
\v 29 Idan mutum ya sayar da gidansa a cikin birni mai ganuwa, daga nan zai iya ya fãnshar sa cikin dukkan shekara bayan ya sayar. Gama a cikin cikar shekara yana da 'yancin fãnsa.
\v 30 Idan ba a fãnshi gidan kamin cikar shekara ba, daga nan gidan da ke cikin birni mai ganuwa zai zama mallaka ta din-din din ga wanda ya saya shi da zuriyarsa. Ba za a mayar da shi cikin shekara ta 'Yanci ba.
\s5
\v 31 Amma gidajen ƙauyukan da ba su da gãnuwa kewaye da su za a yi lissafinsu a matsayin filin ƙasa. Za a iya fãnsarsu kuma dole a dawo da su a shekarar 'Yanci.
\v 32 Amma, gidajen da Lebiyawa suka mallaka cikin birane za su iya fãnsarsu a kowanne lokaci.
\s5
\v 33 Idan ɗaya daga cikin Lebiyawa bai fãnshi gidan da ya sayar ba, daga nan gidan da aka sayar a cikin birni a inda ya ke dole a dawo da shi cikin shekarar 'Yanci, gama gidajen biranen Lebiyawa mallakarsu ne a cikin mutanen Isra'ila.
\v 34 Amma filayen da ke kewaye da biranen ba za a sayar da su ba saboda mallakar Lebiyawa ne na din-din din.
\s5
\v 35 Idan ɗan ƙasarku ya zama talaka, yadda ba zai iya biyan buƙatar kansa ba, daga nan dole ka taimake shi kamar yadda za ka taimaki bãƙo ko wani dabam da ke zaune kamar na waje a cikinku.
\v 36 Kada ka caje shi da ruwa ko ka yi ƙoƙarin samun riba daga gare shi ta kowacce hanya, amma ka girmama Allahnka domin ɗan'uwanka ya ci gaba da zama tare da kai.
\v 37 Kada ka bashi bashin kuɗi da ruwa, ko ka sayar masa abinci don samun riba.
\v 38 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, domin in baku ƙasar Kan'ana, kuma in zama Allahnku.
\s5
\v 39 Idan ɗan ƙasarku ya zama talaka har ya sayar da kansa gare ka, kada kasa shi ya yi aiki kamar bawa. Ka kula da shi kamar baran haya.
\v 40 Dole ya zama kamar wanda ya ke zama da kai na ɗan lokaci. Zai yi hidima tare da kai har zuwa shekarar 'Yanci.
\v 41 Daga nan zai tafi daga gare ka, shi da 'ya'yansa tare da shi, zai koma wurin iyalinsa da mallakar kakanninsa.
\s5
\v 42 Gama su bayina ne waɗanda na kawo daga ƙasar Masar. Ba za a sayar da su kamar bayi ba.
\v 43 Kada ku mallake su da tsanani, amma dole ku girmama Allahnku.
\v 44 Ga zancen bayinku maza da mata, waɗanda za ku samu daga al'umman da ke kewaye da ku, za ku iya sayen bayi daga gare su.
\s5
\v 45 Za ku iya sayen bayi daga bãƙin da ke zaune a wurin ku, wato, daga iyalin da ke tare da ku, 'ya'yan da aka haifa cikin ƙasarku. Sun zama mallakarku.
\v 46 Za ku iya tanada wa 'ya'yanku irin waɗannan bayi su zama gãdo bayan ku, su riƙe su a matsayin mallaka, su kuma za su zama bayi har abada, amma baza ku yi mulkin 'yan'uwanku cikin mutanen Isra'ila da tsanani ba.
\s5
\v 47 Idan bãƙo ko wani da ke zama cikinku na ɗan lokaci ya azurta, ɗan'uwanku kuma Ba-Isra'ile ya talauce ya sayar da kansa ga bãƙon, ko ga wani cikin iyalin bãƙon,
\v 48 bayan da an sayi Ba-Isra'ilenku, za a iya fãnsarsa. Wani daga cikin iyalinsa zai iya fãnsar sa.
\s5
\v 49 Zai iya zama kawun mutumin ko ɗan kawunsa, wanda ya fanshe shi, ko wani wanda ya ke kusa da iyalinsa. Ko, idan ya azurta, zai iya fãnsar kansa.
\v 50 Dole ya yi ciniki da wanda ya saye shi; dole su lisafta shekarun daga shekarar da ya sayar da kansa ga wanda ya saye shi har zuwa shekarar 'Yanci. Farashin da aka fãnshe shi zai zama dai-dai da yawan wanda aka biya baran da akayi hayar sa, zai iya ci gaba da yin aiki har wasu shekaru ga wanda ya sawo shi.
\s5
\v 51 Idan har yanzu akwai sauran shekaru da yawa kafin shekarar 'Yanci, dole ya biya kuɗin domin fãnsarsa bisa ga adadin waɗannan shekaru.
\v 52 Amma idan shekarun sun ragu kaɗan ga shekarar 'Yanci, daga nan dole ya yi ciniki tare da mai sayensa ya nuna yawan shekarun da suka ragu kafin shekarar 'Yanci, kuma dole ya biya domin fãnsarsa bisa ga yawan shekarun.
\s5
\v 53 Dole a kula da shi kamar mutumin da aka yi hayarsa shekara bayan shekara. Dole ku tabbatar ba a tsananta masa da tsanani ba.
\v 54 Idan ba a fãnshe shi ta waɗannan hanyoyi ba, daga nan zai ci gaba da bauta har zuwa shekarar 'Yanci, shi da 'ya'yansa tare da shi.
\v 55 A gare ni mutanen Isra'ila bayi ne. Bayi na ne waɗanda na fisshe su daga ƙăsar Masar. Ni ne Yahweh Allahnku.'"
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 "Ba za ku yi gumakai ba, kuma ba za ku ɗaga sassaƙaƙƙiyar siffa ko keɓaɓɓen ginshiƙin dutse, kuma ba za ku kafa kowacce irin sassaƙaƙƙiyar siffa ta dutse a cikin ƙasarku da za ku durƙusa masa ba, gama ni ne Yahweh Allahnku.
\v 2 Dole ku kiyaye assabataina ku girmama rumfar sujadata. Ni ne Yahweh.
\s5
\v 3 Idan kuka yi tafiya cikin umarnaina kuka kiyaye dokokina kuma kuka yi biyayya da su,
\v 4 daga nan zan ba ku ruwan sama a lokacinsa; ƙasar kuwa zata bada amfaninta, itatuwan gonaki kuma za su bada 'ya'yansu.
\s5
\v 5 Za ku yi ta girbi har lokacin girbin 'ya'yan inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuka. Za ku ci abincinku ku ƙoshi kuma ku zauna lafiya inda kuka yi gida a cikin kasarku.
\v 6 Zan bada salama cikin ƙasar; za ku kwanta ba abin da zai tsoratar da ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar, takobi kuma ba zata ratsa ta ƙasarku ba.
\s5
\v 7 Za ku runtumi maƙiyanku, kuma za su faɗi a gaban ku ta wurin takobi.
\v 8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi ɗari, mutum ɗarinku kuma za su runtumi mutum dubu goma; maƙiyanku za su faɗi a gabanku ta wurin takobi.
\s5
\v 9 Zan dube ku da idon rahama in sa ku hayayyafa in riɓanɓanya ku; zan tabbatar da alƙawarina tare da ku.
\v 10 Za ku ci abinci ku ajiye shi tsawon lokaci. Za ku fitar da abincin da kuka ajiye saboda kuna buƙatar ɗaki domin ku ajiye sabon hatsi.
\s5
\v 11 Zan kafa mazaunina a tsakiyar ku, ba kuwa zan ƙi ku ba.
\v 12 Zan yi tafiya tare da ku in kuma zama Allahnku, kuma za ku zama mutanena.
\v 13 Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, domin kada ku zama bayinsu. Na karya sandunan karkiyarku na sa ku yi tafiya madaidaiciya.
\s5
\v 14 Amma idan ba za ku saurare ni ba, kuma ba za ku yi biyayya da dukkan dokokin nan ba,
\v 15 idan kuma kuka yi watsi da dokokina kuma kuka ƙi umarnaina, domin kada ku yi biyayya da dukkan dokokina, amma kuka karya alƙawarina -
\s5
\v 16 - idan kuka yi waɗannan abubuwa, daga nan nima zan yi wannan a gare ku: Zan sa tsõro a kan ku, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idanunku rayuwa zata zama da wahala. Za ku shuka irinku a banza, amma maƙiyanku ne za su ci amfaninsu.
\v 17 Zan sa fuskata gãba da ku, maƙiyanku za su fi ƙarfinku. Mutanen da suke ƙin ku za su mallake ku. Za ku yi gudu ko da wani bai kore ku ba.
\s5
\v 18 Idan bayan dukkan wannan baku saurare ni ba, daga nan zan ƙara hukunta ku da tsanani sau bakwai domin zunubanku.
\v 19 Zan karya gimanku cikin ikonku. Zan sa sama da ke kanku ta zama kamar ƙarfe ƙasarku kuma kamar tagulla.
\v 20 Ƙarfinku zai zama ba amfani, saboda ƙasarku ba zata bada amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su bada 'ya'yansu ba.
\s5
\v 21 Idan kuka yi tafiya gãba da ni ba ku saurare ni ba, Zan kawo nushi sau bakwai akan ku, bisa ga yawan zunubanku.
\v 22 Zan aiko maku da mugayen namomin jeji gãba da ku, waɗanda za su sace 'ya'yanku, su hallaka dabbobinku, su sa ku zama kaɗan. Hanyoyin kuma za su zama ba masu gilmawa.
\s5
\v 23 Idan baya ga waɗannan duk da haka ba ku karɓi gyara na ba kuka ci gaba da tafiya cikin yin adawa da ni,
\v 24 daga nan ni ma zan yi tafiya cikin yin adawa da ku, kuma Ni da kaina zan hukunta ku sau bakwai saboda zunubanku.
\s5
\v 25 Zan kawo takobi a kanku a kashe ku da ramuwa domin karya alƙawari. Za a tattara ku tare cikin biranenku, can zan aikar da cuta a wurin, za a miƙa ku cikin hannun maƙiyanku.
\v 26 Idan na datse abincin da kuka tanada, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, kuma za su rarraba abincinku bisa ga ma'auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba.
\s5
\v 27 Idan ba ku saurare ni ba duk da waɗannan abubuwan, amma kuka ci gaba da tafiya gãba da ni,
\v 28 daga nan ni ma zanyi tafiya gãba da ku cikin fushi, kuma zan hukunta ku har sau bakwai sosai saboda zunubanku.
\s5
\v 29 Za ku ci naman 'ya'yanku maza; za ku ci naman 'ya'yanku mata.
\v 30 Zan lalatar da wurarenku masu tsayi, in datse bagadan ƙona turarenku, in jefar da gawarwakinku akan gawarwakin gumakanku, kuma ni da kaina zan ji ƙyamar ku.
\s5
\v 31 Zan juyar da biranenku su zama kufai in lalatar da masujadanku. Ba zan ji daɗin ƙamshin baye-bayenku ba.
\v 32 Zan lalatar da ƙasar. Maƙiyanku da ke zaune a ƙasar za su yi mamaki da irin lalatarwar.
\v 33 Zan warwatsaku cikin ƙasashe, kuma zan zare takobina in fafareku. Ƙasarku za a yashe ta, biranenku kuma za su zama kangaye.
\s5
\v 34 Daga nan ƙasar zata ji daɗin hutunta muddin tana kwance yasasshiya kuma ku kuna ƙasashen maƙiyanku. A wannan lokaci, ƙasar zata huta zata ji daɗin hutunta.
\v 35 Muddin ƙasar tana kwance kango, zata huta, zai zama hutun da bata samu ba tare da assabatunku, lokacin da kuka zauna cikinta.
\v 36 Amma ga waɗansun ku da suka ragu cikin ƙasashen maƙiyanku, Zan aikar da tsoro cikin zukatansu yadda motsin kaɗawar ganye cikin guguwa ma zai razanar da ku, za ku sheƙa a guje kamar kuna gujewa takobi. Za ku faɗi, koda ba wanda ke korar ku.
\s5
\v 37 Za ku yi ta karo da juna kamar kuna gujewa daga takobi, kodashike ba mai korar ku. Ba za ku sami ikon tsayawa gaban maƙiyanku ba.
\v 38 Za ku hallaka cikin al'ummai, ƙasar maƙiyanku kanta za ta haɗiye ku.
\v 39 Waɗanda suka ragu a cikinku za su lalace cikin zunubansu, a can cikin ƙasashen maƙiyanku, saboda zunubin kakanninsu kuma za su lalace kamar su.
\s5
\v 40 Duk da haka idan suka furta zunubansu da zunubin kakanninsu, da cin amanar su da suka zama da rashin aminci a gare ni, da tayarwar da suka yi mani --
\v 41 wanda ya sa ni na juya gãba da su na kawo su cikin ƙasar maƙiyansu - idan suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, kuma suka karɓi hukunci domin zunubansu,
\v 42 daga nan zan tuna da alƙawarina da Yakubu, alƙawarina da Ishaku, da kuma alƙawarina tare da Ibrahim; kuma, zan tuna da ƙasar.
\s5
\v 43 Za su yashe da ƙasar, za ta ji daɗin hutunta yayin da take kwance yasasshiya ba tare da su ba. Za su biya alhakin zunubansu saboda su da kansu sun yi watsi da umarnaina suka yi ƙyamar dokokina.
\s5
\v 44 Duk da haka bayan dukkan waɗannan, sa'ad da suke cikin ƙasar maƙiyansu, ba zan ƙi su ba, ko in ƙyamace su domin in hallaka su gaba ɗaya har in karya alƙawarina da su ba, Gama Ni ne Yahweh Allahnsu.
\v 45 Amma saboda su zan tuna da alƙawarina tare da kakanninsu, waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai, domin in zama Allahnsu. Ni ne Yahweh."
\s5
\v 46 Waɗannan dokoki, umarnai da shari'u waɗanda Yahweh ya yi tsakaninsa da mutanen Isra'ila a Tsaunin Sinai ta hannun Musa.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Yahweh ya yi magana da Musa ya ce,
\v 2 "Ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce masu, 'Idan wani ya yi alƙawari na musamman ga Yahweh, yi amfani da waɗannan tamanin.
\s5
\v 3 Darajar misalin abin da za ka biya domin maza daga shekara ashirin zuwa sittin dole ya zama awo hamsin na tagulla, bisa ga awo na wuri mai tsarki.
\v 4 Ga mataye masu shekaru iri ɗaya darajar abin da za a biya dole ya zama awo talatin.
\s5
\v 5 Daga shekara biyar zuwa shekara ashirin darajar abin da za a biya domin maza dole ya zama awo ashirin, mataye kuma awo goma.
\v 6 Daga wata ɗaya zuwa shekara biyar darajar abin da za a biya domin maza dole ya zama awo biyar na tagulla, ga mata awo uku na tagulla.
\s5
\v 7 Daga shekaru sittin zuwa sama ga maza tamanin abin da za a biya dole ya kai awo goma sha biyar, mata kuma awo goma.
\v 8 Amma idan mutumin da ya yi wa'adi ba zai iya biyan tamanin ba, daga nan mutumin da aka bayar dole a kawo shi gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamanin abin da mutumin da ya yi wa'adin zai iya biya bisa ga ƙarfinsa.
\s5
\v 9 Idan wani yana son miƙa hadayar dabba ga Yahweh, kuma idan Yahweh ya karɓe ta, daga nan wannan dabbar za a keɓe ta dominsa.
\v 10 Kada mutumin ya musanya irin wannan dabbar, mai kyau da marar kyau ko marar kyau da mai kyau. Idan ya musanya ko canza dabbar da wata, daga nan dukkan su biyu da aka musanya da wadda aka musanyar za su zama masu tsarki.
\s5
\v 11 Duk da haka, idan abin da mutumin ya yi wa'adi zai ba Yahweh ta zama marar tsarki, don haka Yahweh ba zai karɓe ta ba, daga nan dole mutumin ya kai dabbar wurin firist.
\v 12 Firist zai kimanta tamanin ta, bisa ga darajar dabbar. Duk yadda firist ya kimanta dabbar, haka darajarta zata zama.
\v 13 Idan mai ita yana so ya fãnshe ta, sai ya yi ƙarin kashi biyar na farashin fãnsa.
\s5
\v 14 Idan mutum ya keɓe gidansa a matsayin kyauta mai tsarki ga Yahweh, daga nan sai firist ya kimanta tamaninsa ko da kyau ko ba kyau. Duk yadda firist ya kimanta darajarsa, haka zai zama.
\v 15 Amma idan mai gidan wanda ya keɓe gidan yana so ya ƒãnshe shi, dole ya ƙara kashi ɗaya cikin biyar na tamanin farashin fansa, gidan kuwa zai zama nasa.
\s5
\v 16 Idan mutum ya keɓe wani sãshe na gonarsa, daga nan tamaninta zai zama kimanin dai-dai da yawan irin da ya kamata a shuka - tiyar bãli tamaninta zai zama a bakin shekel hamsin na azurfa.
\s5
\v 17 Idan ya keɓe gonarsa lokacin shekarar 'Yanci, haka tamaninta zai tsaya.
\v 18 Amma idan ya keɓe gonarsa bayan shekarar 'Yanci dole firist ya lisafta yawan tamanin ƙasar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa shekarar 'Yanci, kuma dole a rage tamaninta.
\s5
\v 19 Idan shi mutumin da ya keɓe gonar yana so ya fãnshe ta, daga nan dole ya ƙara kashi biyar na tamanin, kuma sai ta zama ta sa.
\v 20 Idan bai fãnshi gonar ba, ko idan ya rigaya ya sayar da gonar ga wani mutum, ba za ta fãnsu ba faufau.
\v 21 Maimakon haka, idan gonar, an sake ta cikin shekarar 'Yanci, zata zama kyauta mai tsarki ga Yahweh, kamar gonar da aka bayar gaba ɗaya ga Yahweh. Zata zama mallakar firist.
\s5
\v 22 Idan mutum ya keɓe gonar da ya saya, amma wannan gonar bata cikin ƙasar gãdon iyalinsa,
\v 23 daga nan firist zai kimanta tamaninta har zuwa shekarar 'Yanci, daga nan dole mutumin ya biya tamaninta a ranar a matsayin kyauta mai tsarki ga Yahweh.
\s5
\v 24 A cikin shekarar 'Yanci, sai gonar ta koma ga mutumin wanda daga wurinsa aka saye ta, ga ainihin mai gonar.
\v 25 Dukkan kowanne tamani dole ya zama bisa ga nauyin awo na wuri mai tsarki. Ƙaramin awo ashirin da ke matsayin awo ɗaya.
\s5
\v 26 Ba wanda zai keɓe ɗan fãri cikin dabbobi, da shike dama na Yahweh ne; ko sã ko tunkiya, na Yahweh ne.
\v 27 Idan dabbar marar tsarki ce, daga nan mai ita zai iya fãnsar ta bisa ga tamanin, dole ya ƙara kashi biyar akan tamanin. Idan ba'a fãnshi dabbar ba, daga nan sai a sayar da ita bisa ga tamanin da aka sanya.
\s5
\v 28 Amma ba abin da mutum zai bayar ga Yahweh, daga dukkan abin da ya ke da shi, ko mutum ko dabba, ko ƙasar gãdonsa, da za a sayar ko a fãnsar. Duk abin da aka keɓe ya zama mai tsarki na Yahweh.
\v 29 Ba za a biya kuɗin fãnsa ba ga mutumin da aka keɓe domin hallakarwa. Wannan mutumin dole a kashe shi.
\s5
\v 30 Dukkan zakkar ƙasa, ko ta hatsin da aka noma a ƙasa ko 'ya'yan itatuwa, na Yahweh ne. Mai tsarki ne ga Yahweh.
\v 31 Idan mutum ya fãnshi kowanne abu na zakkarsa, dole ya ƙara ɗaya bisa biyar na tamaninta.
\s5
\v 32 Ga kowanne ɗaya bisa goma na makiyaya ko dabbobi, ko mene ne ya wuce ta ƙarƙashin sandar makiyaya, dole a keɓe ɗaya bisa goma ga Yahweh.
\v 33 Kada makiyayin ya nemi mai kyau ko munanan dabbobi, kada ya musanya da wata. Idan har ya canja, daga nan dukkansu da wadda ya canja za su zama tsarkakku ga Yahweh. Ba za a fãnshe su ba.'"
\s5
\v 34 Waɗannan su ne dokokin da Yahweh ya bayar a tsaunin Sinai ga Musa domin mutanen Isra'ila.