ha_ulb/01-GEN.usfm

2959 lines
193 KiB
Plaintext
Raw Permalink Blame History

This file contains invisible Unicode characters

This file contains invisible Unicode characters that are indistinguishable to humans but may be processed differently by a computer. If you think that this is intentional, you can safely ignore this warning. Use the Escape button to reveal them.

\id GEN
\ide UTF-8
\h Littafin Farawa
\toc1 Littafin Farawa
\toc2 Littafin Farawa
\toc3 gen
\mt Littafin Farawa
\s5
\c 1
\cl Sura 1
\p
\v 1 A cikin farko, Allah ya hallici sammai da duniya.
\v 2 Duniya bata da siffa, sarari ce kawai. Duhu kuma ya rufe dukkan zurfafa. Ruhun Allah kuma yana kewayawa a bisa fuskar ruwaye.
\s5
\v 3 Allah yace, "Bari haske ya kasance, haske kuwa ya kasance."
\v 4 Allah kuma ya ga hasken, ya kuma ƙayatar. Sai ya raba haske da duhu.
\v 5 Allah ya kira haske "yini," duhu kuma ya ce da shi "dare." Wannan shi ne safiya da dare, a rana ta ɗaya.
\s5
\v 6 Allah yace, "Bari a sami fili tsakanin ruwaye, Sai ya rarraba tsakanin ruwaye."
\v 7 Allah yayi tsakani ga ruwayen dake ƙarƙas da kuma ruwayen dake sammai. Haka kuma ya kasance.
\v 8 Allah ya kira tsakanin "sararin sama." Wannan shi ne maraice da safiya, rana ta biyu kenan.
\s5
\v 9 Allah yace, ruwayen dake ƙarƙashin sammai su tattaru wuri ɗaya, kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana," haka kuma ya faru.
\v 10 Allah ya kira sandararriyar ƙasa "duniya," ruwayen da suka tattaru kuma ya kira su "tekuna" ya kuma ga suna da kyau.
\s5
\v 11 Allah yace, "Duniya ta fitar da ciyayi da itatuwa masu fitar da iri da kuma 'ya'ya waɗanda ke cikin 'ya'yan, kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance.
\v 12 Ƙasa ta fitar da ganyayyaki, da itatuwa masu bada iri kowanne bisa ga irinsa, da kuma itatuwa masu bada 'ya'ya dake cikinsu, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau.
\v 13 Wannan ce safiya da maraice, rana ta uku.
\s5
\v 14 Allah yace, "Haske ya kasance a sararin sama domin ya raba tsakanin haske da duhu, su kuma zama alamu na yanayi, domin ranaku da shekaru.
\v 15 Sai su zama haske a sararin sama domin su haskaka duniya." Haka kuwa ya kasance.
\s5
\v 16 Allah yayi manyan haskoki guda biyu, babban hasken yayi mulkin yini, ƙaramin hasken kuma yayi mulkin dare. Ya kuma yi taurari.
\v 17 Allah ya shirya su a sama domin su bada haske ga duniya,
\v 18 su kuma yi mulki kan yini da kuma dare, su kuma raba tsakanin haske da duhu. Allah kuma ya ga yana da kyau.
\v 19 Wannan ce safiya da yammaci, rana ta huɗu.
\s5
\v 20 Allah yace, "Ruwaye su kasance da manyan halittu masu rai, ya kuma bar tsuntsaye suyi ta firiya a saman duniya a sararin sama."
\v 21 Allah ya hallici manyan hallittu na tekuna, da kuma sauran halittu kowanne bisa ga irinsa, da masu tafiya da kuma waɗanda suka cika ruwaye a ko'ina, da kuma dukkan tsuntsaye masu fukafukai, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau.
\s5
\v 22 Allah ya albarkace su, cewa, "Ku ruɓanɓanya, ku hayayyafa, ku cika ruwaye a cikin tekuna. Ya ce tsuntsaye su ruɓanɓanya a duniya."
\v 23 Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta biyar.
\s5
\v 24 Allah yace, "Ƙasa ta bada hallittu masu rai, kowanne bisa ga irinsa, dabbobin gida, masu rarrafe dana daji kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance.
\v 25 Allah kuma ya yi dabbobin duniya kowanne bisa ga irinsu, dabbobin gida kowanne bisa ga irinsa da duk masu jan jiki a ƙasa kowanne bisa ga irinsa. Ya kuma ga suna da kyau.
\s5
\v 26 Allah yace "Bari muyi mutum cikin kamanninmu, bisa surarmu. Su yi mulkin kifaye na tekuna, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da kuma dukkan duniya, da dukkan abu mai rarrafe a bisa duniya."
\v 27 Allah ya hallici mutum cikin kamanninsa. Cikin kamanninsa ya hallice shi. Mace da namiji ya hallice su.
\s5
\v 28 Allah ya albarkace su ya ce da su,"Ku hayayyafa ku kuma ruɓaɓɓanya. Ku cika duniya ku nome ta. Kuyi mulkin kifaye na tekuna da tsuntsayen sama, da kuma duk abu mai rai dake tafiya bisa duniya."
\v 29 Allah yace, "Duba na baka kowanne tsiro dake bada iri wanda yake a fuskar duniya, da dukkan bishiyoyi dake da iri a cikinsu. za su zama abinci a gare ku.
\s5
\v 30 Ga kowacce dabba ta duniya, da kuma dukkan tsuntsaye na sammai, da kowanne abu mai rarrafe a doron duniya, da kuma dukkan halittu masu numfashin rai na baku kowanne irin koren ganye domin abinci." Haka kuma ya kasance.
\v 31 Allah kuma ya ga dukkan abin da ya halitta na da kyau. Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta shida.
\s5
\c 2
\cl Sura 2
\p
\v 1 To an kammala sammai da duniya, da duk abubuwa masu rai da suka cika su.
\v 2 A rana ta bakwai Allah ya kammala aikinsa da ya yi, domin haka sai ya huta a rana ta bakwai daga dukkan aikinsa.
\v 3 Allah ya albarkaci rana ta bakwai ya kuma tsarkaketa, domin a cikinta ya huta daga dukkan aikinsa na halitta da ya yi.
\s5
\v 4 Waɗannan sune al'amuran da suka shafi sammai da duniya, a lokacin da aka hallice su, a ranar da Yahweh ya yi sammai da duniya.
\v 5 Ba wani filin daji kuma a duniya, ba tsire-tsire kuma a cikin filaye, domin Yahweh bai sa a yi ruwa ba tukuna a duniya, kuma ba mutumin da zai nome ƙasa.
\v 6 Amma raɓa ta sauka a ƙasa ta jiƙe dukkan ƙasar.
\s5
\v 7 Yahweh Allah ya halitta mutum daga cikin ƙasa, ya kuma hura masa numfashin rai a cikin kafafen hancinsa, sai mutum ya zama rayayyen taliki.
\v 8 Yahweh ya yi lambun itatuwa a bangon gabas a cikin Aidan, a can ya sa mutumin daya halitta.
\s5
\v 9 Daga cikin ƙasa Yahweh Allah ya sa ko waɗanne irin itatuwa masu ƙayatarwa da abinci su tsiro. Wannan ya haɗa da itacen rai wanda ke a tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.
\v 10 Rafi ya bi ta tsakiyar lambun Aidan domin ya jiƙa lambun. Daga can ne ya rabu ya zama rafuka huɗu.
\s5
\v 11 Sunan na farko shi ne Fishon. Shi ne wanda ya malala a dukkan ƙasar Habila, inda akwai zinariya. Zinariyar wannan ƙasar tana da kyau.
\v 12 Akwai kuma itatuwa masu ƙamshi da kyawawan duwatsu.
\s5
\v 13 Sunan rafi na biyun shi ne Gishon. Wannan shi ne wanda ya malala zuwa Kush.
\v 14 Sunan rafi na ukun shi ne Tigris, wanda ya malala gabashin Asshur. Rafi na huɗu shi ne Yufaretis.
\s5
\v 15 Yahweh Allah ya ɗauki mutumin ya sa shi a lambun Aidin domin ya nome shi ya kula da shi.
\v 16 Yahweh Allah ya umarci mutumin, da cewa, "Daga kowanne irin 'ya'yan itace na cikin lambun kana da 'yancin ci.
\v 17 Amma ba za ka ci daga cikin itace na sanin nagarta da mugunta ba, domin ranar daka ci daga cikinsa, tabbas za ka mutu."
\s5
\v 18 Yahweh Allah yace, "ba shi da kyau mutumin ya zauna shi kaɗai. Zan yi masa mataimakiyar da ta dace da shi."
\v 19 Daga cikin ƙasa ne Yahweh Allah ya siffatta kowacce irin dabba ta saura da kuma tsuntsun sararin sama. Sai ya kawo su wurin mutumin domin ya ga yadda zai kira su. Duk abin da mutumin ya kira kowacce halitta sunanta kenan.
\v 20 Mutumin ya ba dukkan dabbobi suna da kuma dukkan tsuntsayen sararin sama. Amma ga mutumin ba a sami mataimakin da ya dace da shi ba.
\s5
\v 21 Yahweh Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin domin haka mutumin ya yi barci. Yahweh Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya yi mace ya kuma kawo ta ga mutumin
\v 22 Da haƙarƙarin da Yahweh ya ciro daga jikin mutumin, ya yi mace da shi ya kuma kawo ta ga mutumin.
\v 23 Sai mutumin yace, "A wannan lokacin, wannan ƙashi ne na ƙasusuwana, tsoka ce daga tsokata. Za a kira ta 'mace,' saboda daga jikin mutum aka ciro ta."
\s5
\v 24 Domin haka mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, zai zama haɗe da matarsa, kuma za su zama jiki ɗaya.
\v 25 Dukkan su biyu tsirara suke, mijin da matar, amma ba su jin kunya.
\s5
\c 3
\cl Sura 3
\p
\v 1 To maciji ya fi dukkan sauran dabbobin saura da Yahweh yayi wayau. Sai ya ce da macen, "Ko da gaske ne Allah yace ba zaku taɓa ci daga kowanne 'ya'yan itacen dake cikin lambun ba?"
\v 2 Sai matar ta ce da macijin, "Ma iya ci daga cikin itatuwan lambun,
\v 3 amma game da itacen dake tsakiyar lambun, Allah yace, 'Ba zaku ci shi ba, ba kuma zaku taɓa shi ba, in ba haka ba, zaku mutu."'
\s5
\v 4 Sai maciji yace da macen, "Hakika ba zaku mutu ba.
\v 5 Domin Allah ya san cewa a ranar da kuka ci idanunku zasu buɗe, zaku kuma zama kamar Allah, kuna sanin nagarta da mugunta."
\v 6 Da matar ta duba ta ga itacen yana da kyau domin abinci, yana kuma ƙayatar da idanu, kuma itacen abin marmari ne yana sa mutum ya zama mai hikima, sai ta tsinki waɗansu daga cikin 'ya'yan ta ci shi. Sai ta bada waɗansu ga mijinta, shi kuma ya ci.
\s5
\v 7 Idanun dukkan su biyun suka buɗe, sai suka gane tsirara su ke. Sai suka ɗinka ganyayyakin ɓaure suka yi wa kansu sutura.
\v 8 Sai suka ji motsin Yahweh Allah ya na tafiya cikin lambun da sanyin yamma, domin haka mijin da matar suka ɓuya a cikin itatuwan lambun daga fuskar Yahweh Allah.
\s5
\v 9 Sai Yahweh Allah ya kira mutumin yace da shi, "Ina ka ke?"
\v 10 Mutumin yace "Na ji ka a cikin lambun, na kuma ji tsoro, domin tsirara na ke. Domin haka na ɓoye kaina."
\v 11 Allah yace, "Wane ne ya faɗa maka cewa tsirara ka ke? Ko ka ci 'ya'yan itacen da na dokace ka kada ka ci daga cikinsa ne?"
\s5
\v 12 Sai mutumin yace, "Macen daka ba ni ta kasance tare da ni, ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci shi."
\v 13 Yahweh Allah yace da matar, "Me ki ka yi kenan?" Sai macen ta ce, "Maciji ne ya yi mini ƙarya, na kuwa ci."
\s5
\v 14 Yahweh Allah yace da maciji, "Saboda ka yi wannan, kai kaɗai ne la'ananne a cikin dukkan dabbobin saura da dukkan dabbobin sama. A kan cikinka za ka yi tafiya, kuma ƙasa za ka ci dukkan kwanakin ranka.
\v 15 Zan sa magaftaka tsakaninka da matar, da kuma tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje diddigensa."
\s5
\v 16 Ga macen yace, "Zan ninka shan wuyarki sosai a samun 'ya'ya; a cikin shan wuya za ki haifi 'ya'ya. Duk marmarinki zai zama domin mijinki, amma zai yi mulkin ki."
\s5
\v 17 Ga Adamu yace, "Domin ka saurari muryar matarka, ka ci daga cikin itacen da na dokace ka cewa, 'Kada ka ci daga cikinsa,' saboda kai na la'anta ƙasa; ta wurin aiki mai zafi za ka ci daga cikinta dukkan kwanakin ranka.
\v 18 Za ta fitar da ƙaya da sarƙaƙƙiya domin ka, za ka kuma ci tsire-tsiren ƙasar.
\v 19 Ta wurin zufarka za ka ci gurasa, har sai randa ka koma turɓaya, domin daga cikinta aka ciro ka. Domin kai ƙura ne, ƙura kuma za ka koma."
\s5
\v 20 Mutumin ya kira sunan matarsa Hauwa ita ce mahaifiyar dukkan rayayyu.
\v 21 Yahweh Allah ya yi wa Adamu da matarsa sutura ta fatu ya rufe su.
\s5
\v 22 Yahweh Allah yace, "Yanzu mutumin ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, yana sane da mugunta da nagarta. To yanzu ba za mu taɓa barinsa ya sa hannunsa, ya tsinka daga itacen rai ba, ya ci, ya kuma rayu har abada."
\v 23 Saboda haka Yahweh Allah ya fitar da shi daga cikin lambun Aidin, domin ya noma ƙasa wanda daga ita aka ciro shi.
\v 24 To sai Allah ya kori mutumin daga lambun, ya sa kerubim a gabashin lambun Aidin da kuma takobi mai walƙiya dake jujjuyawa ta kowanne fanni, domin su yi tsaron hanya ta zuwa itacen rai.
\s5
\c 4
\cl Sura 4
\p
\v 1 Mutumin ya kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi Kayinu. Ta ce,"Na haifi mutum da taimakon Yahweh."
\v 2 Sai ta sake haifar ɗan'uwansa Habila. Sai Habila ya zama makiyayi, amma Kayinu ya zama manomi.
\s5
\v 3 Sai ya zamana wata rana Kayinu ya kawo wani sashe daga cikin amfanin gonar da ya noma daga ƙasa a matsayin baiko ga Yahweh.
\v 4 Shi kuma Habila, sai ya kawo waɗansu 'ya'yan fari daga cikin garkensa da kuma sashe na kitse. Yahweh ya karɓi Habila da baikonsa,
\v 5 amma Kayinu da baikonsa bai karɓa ba. Domin haka Kayinu ya fusata sosai, ya kuma ɓata fuska.
\s5
\v 6 Yahweh yace da Kayinu, "Meyasa ka yi fushi meyasa fuskarka ta ɓaci haka?
\v 7 In da ka yi abin dake nagari, da ba a karɓe ka ba? Amma in ba ka yi abin dake nagari ba, zunubi na ƙwanƙwasa ƙofa kuma marmarinsa shi ne ya mallake ka, amma dole ne ka yi mulkinsa."
\s5
\v 8 Sai Kayinu ya yi magana da ɗan'uwansa Habila. Sai ya zamana a lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya kashe shi.
\v 9 Daga nan Yahweh yace da Kayinu, "Ina ɗan'uwanka Habila?" Ya ce, "Ban sani ba. Ni makiyayin ɗan'uwana ne?"
\s5
\v 10 Yahweh yace, "Me ka yi kenan? Jinin ɗan'uwanka yana kira na daga ƙasa.
\v 11 Yanzu kai la'ananne ne daga ƙasar da ta buɗe baki ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka.
\v 12 Daga yanzu duk lokacin daka noma ƙasa, ba za ta baka issashen amfaninta ba. Za ka zama mai yawo barkatai a cikin duniya."
\s5
\v 13 Kayinu yace da Yahweh, "Horona ya yi girma fiye da yadda zan iya ɗauka.
\v 14 Hakika ka kore ni waje yau daga wannan ƙasa, zan kuma riƙa ɓuya daga fuskarka. Zan zama mai yawo barkatai a cikin duniya, kuma duk wanda ya same ni zai kashe ni."
\v 15 Yahweh yace da shi, In har wani ya kashe Kayinu za ayi masa ramako har niki bakwai." Daga nan Yahweh ya sa alama a jikin Kayinu, domin in wani ya gan shi kada wannan mutumin ya kai masa hari.
\s5
\v 16 Sai Kayinu ya tafi daga fuskar Yahweh ya zauna a ƙasar Nod, a gabashin Aidin.
\v 17 Kayinu ya kwana da matarsa sai ta yi ciki ta haifi Enok. Ya gina birni ya bashi sunan ɗansa Enok.
\s5
\v 18 Ga Enok sai aka haifa masa Irad. Irad ya zama mahaifin Mehuyawel. Mehuyawel ya zama mahaifin Metushawel. Metushawel ya zama mahaifin
\v 19 Lamek. Lamek ya aura wa kansa mata biyu: sunan ɗayar Ada, ɗayar kuma sunanta Zilla.
\s5
\v 20 Ada ta haifi Yabal. Shi ne mahaifin masu zama a cikin rumfuna waɗanda ke da dabbobi.
\v 21 Ɗan'uwansa shi ne Yubal. Shi ne mahaifin makaɗan molo da algaita.
\v 22 Ita kuma Zilla, ta haifi Tubal Kayinu, shi ne mai samar da kayayyaki na jan ƙarfe. 'Yar'uwar Tubal Kayinu ita ce Na'ama.
\s5
\v 23 Sai Lamek yace da matansa, Ada da Zilla, ku saurari muryata; ku matan Lamek, ku saurari abin da na ce. Domin na kashe mutum saboda ya yi mani rauni, saurayi domin ya ƙuje ni.
\v 24 In an saka wa Kayinu sau bakwai, to za a saka wa Lamek sau saba'in."
\s5
\v 25 Sai Adamu ya sake kwana da matarsa, sai ta sake haifar wani ɗan. Sai ta kira sunansa Set, ta kuma ce, "Allah ya bani wani ɗan a madadin Habila, domin Kayinu ya kashe shi."
\v 26 Aka haifa wa Set ɗa, sai ya kira sunansa Enosh. A wancan lokacin ne mutane suka fara kiran bisa sunan Yahweh.
\s5
\c 5
\cl Sura 5
\p
\v 1 Wannan shi ne lissafin zuriyar Adamu. A ranar da Allah ya hallici mutum, ya yi su a cikin kamanninsa.
\v 2 Namiji da mace ya hallice su. Ya albarkace su ya basu suna mutane a lokacin da ya hallice su.
\s5
\v 3 Da Adamu ya yi shekaru130 sai ya zama mahaifin ɗa a cikin kamanninsa sai ya kira sunansa Set.
\v 4 Bayan Adamu ya haifi Set, ya yi rayuwa tsawon shekaru ɗari takwas. Sai ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa.
\v 5 Adamu ya yi rayuwa har shekaru 930 daga nan ya mutu.
\s5
\v 6 Da Set ya yi shekaru 105, sai ya haifi Enosh.
\v 7 Bayan ya haifi Enosh, ya rayu har tsawon shekaru 807 ya zama mahaifin 'ya'ya maza da mata da yawa.
\v 8 Set ya rayu har shekaru 912 daga nan ya mutu.
\s5
\v 9 Bayan Enosh ya rayu na tsawon shekaru tasa'in, sai ya haifi Kenan.
\v 10 Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya rayu na tsawon shekaru 815. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa.
\v 11 Enosh ya rayu tsawon shekaru 905 daga nan ya mutu.
\s5
\v 12 Da Kenan ya yi shekaru saba'in, sai ya haifi Mahalalel.
\v 13 Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekaru 840. Sai ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\v 14 Kenan ya rayu na tsawon shekaru 910, daga nan ya mutu.
\s5
\v 15 Mahalalel ya rayu shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Yared,
\v 16 Mahalalel yana da shekaru 830. Sai ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata masu yawa.
\v 17 Mahalalel ya rayu na tsawon shekaru 895, daga nan ya mutu.
\s5
\v 18 Da Yared ya yi shekaru 162, sai ya haifi Enok.
\v 19 Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru ɗari takwas. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\v 20 Yared ya rayu na tsawon shekaru 962, daga nan ya mutu.
\s5
\v 21 Da Enok ya yi shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Metusela.
\v 22 Enok ya yi tafiya tare da Allah shekaru ɗari uku daga nan ya haifi Metusela, ya kuma haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\v 23 Enok ya yi shekaru ɗari uku da sittin da biyar.
\v 24 Enok ya yi tafiya tare da Allah, daga bisani ya tafi, domin Allah ya fyauce shi.
\s5
\v 25 Da Metusela ya yi shekaru 187, ya haifi Lamek.
\v 26 Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\v 27 Metusela ya rayu na tsawon shekaru 965 daga nan ya mutu.
\s5
\v 28 Bayan ya yi shekaru182, sai ya haifi ɗa.
\v 29 Sai ya kira sunansa Nuhu, yana cewa, "Wannan zai bamu hutu daga aikinmu daga kuma aikin hannuwanmu mai wuya, da zamu yi saboda Allah ya la'anta ƙasa."
\s5
\v 30 Lamek ya yi shekaru 595 daga nan ya haifi Nuhu. Daga nan ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata.
\v 31 Lamek ya rayu na tsawon shekaru 777, daga nan ya mutu.
\s5
\v 32 Bayan Nuhu ya yi shekaru ɗari biyar, sai ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.
\s5
\c 6
\cl Sura 6
\p
\v 1 Sai ya zamana da mutane suka fara ruɓamɓanya a duniya aka kuma haifa masu 'ya'ya mata,
\v 2 sai 'ya'yan Allah suka ga 'ya'yan mutane na da ban sha'awa. Sai suka auri mata daga cikinsu, dukkan su da suka zaɓa.
\v 3 Yahweh yace "Ruhuna ba zai dawwama a cikin mutum ba har abada, domin su jiki ne. Za su rayu shekaru 120 ne."
\s5
\v 4 A waɗancan kwanakin akwai ƙarfafan mutane sosai, kuma haka ya faru ne bayan 'ya'yan Allah sun auri 'ya'ya mata na mutane, sun kuma sami 'ya'ya tare da su. Waɗannan sune manyan mutanen dã can, mutane masu jaruntaka.
\s5
\v 5 Yahweh ya ga muguntar mutum ta haɓaka a duniya, kuma dukkan tunane-tunanen zuciyarsa kullum mugunta ce.
\v 6 Yahweh ya yi takaicin halitar mutum a duniya, kuma abin ya dame shi a zuciyarsa.
\s5
\v 7 Domin haka Yahweh yace,"Zan shafe mutum wanda na halitta daga fuskar duniya; mutum da manyan dabbobi, da abubuwa masu rarrafe da tsuntsayen sammai, domin na yi takaici dana halicce su."
\v 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a idanun Yahweh.
\s5
\v 9 Waɗannan sune abubuwa game da Nuhu. Nuhu adalin mutum ne, kuma ba shi da abin zargi a cikin mutanen kwanakinsa.
\v 10 Nuhu yayi tafiya tare da Allah. Nuhu ya haifi 'ya'ya uku: Wato Shem da Ham da Yafet.
\s5
\v 11 Duniya ta ƙazanta a gaban Allah, ta kuma cika da hargitsi.
\v 12 Allah ya ga duniya; duba, ta gurɓanta, domin dukkan mutane sun ɓata tafarkinsu a duniya.
\s5
\v 13 Allah yace da Nuhu, Na ga cewa lokacin ƙarshen dukkan hallita ya yi domin duniya ta cika da hargitsi ta wurin su, hakika, zan hallaka su tare da duniya.
\v 14 Ka yi wa kanka jirgi da itacen sida ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka rufe shi ciki da waje.
\v 15 Ga fasalin yadda zaka yi shi: tsawon jirgin kamu ɗari uku, faɗinsa kamu hamsin, bisansa kamu talatin.
\s5
\v 16 Ka yi wa jirgin rufi, ka kuma kammala shi ka dalaye shi daga sama har ƙasa. Ka sa ƙofa ta gefen jirgin, ka yi masa matakala, ƙarama, da ta biyu, da kuma matakala ta uku.
\v 17 Ka saurara, Na kusa kawo ambaliyar ruwa a duniya domin in hallakar da dukkan masu rai dake da numfashi rai dake a ƙarƙashin sama. Duk abin dake a duniya zai mutu.
\s5
\v 18 Amma zan kafa alƙawarina da kai. Zaka shiga cikin jirgin, da kai da 'ya'yanka da matarka da matan 'ya'yanka tare da kai.
\v 19 Da dukkan hallitu masu rai, kowanne iri biyu dole ne kuma ka shigar dasu cikin jirgin, ka ajiye su, su tsira tare da kai, dukkan su namiji da mace.
\s5
\v 20 Da tsuntsaye bisa ga irinsu, da manyan dabbobi bisa ga irinsu, dukkan wani abu mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu, biyu daga cikin kowanne iri daga cikinsu za su zo tare da kai, domin ka tsirar da rayukansu
\v 21 Ka kuma yi wa kanka tanadin kowanne irin abinci na ci ka adana shi, domin ya zamar maka abinci da kuma dominsu."
\v 22 Sai Nuhu ya yi wannan. Bisa yadda Allah ya umarce shi, haka ya yi.
\s5
\c 7
\cl Sura 7
\p
\v 1 Yahweh yace da Nuhu, "Ka zo, da kai da dukkan gidanka, zuwa cikin jirgin, domin na ga kai mai adalci ne a gabana a wannan tsara.
\v 2 Da dukkan dabbobi masu tsarki tare da kai, maza bakwai mata bakwai. Daga dukkan dabbobi marasa tsarki ka ɗauko biyu-biyu.
\v 3 Hakanan daga tsuntsayen sararin sama, ka kawo maza bakwai da mata bakwai daga cikinsu, domin a tanadi irinsu a faɗin duniya.
\s5
\v 4 Domin a rana ta bakwai zan sa a yi ruwa a dukkan duniya har kwana arba'in dare da rana. Zan hallakar da dukkan masu rai dana halitta daga fuskar duniya"
\v 5 Nuhu ya yi dukkan abin da Yahweh ya umarce shi.
\s5
\v 6 Nuhu yana da shekaru ɗari shida a lokacin da aka yi ruwan tsufana a duniya.
\v 7 Da Nuhu, da 'ya'yansa maza, da matarsa, da matan 'ya'yansa maza suka shiga jirgin saboda ruwan tsufana.
\s5
\v 8 Dabbobi masu tsarki da tsuntsaye da duk abu mai rarrafe a ƙasa,
\v 9 biyu-biyu, namiji da mace, suka zo wurin Nuhu suka shiga akwatin, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu.
\v 10 Sai ya zamana bayan kwanaki bakwai, ruwan tsufana ya sauko a duniya.
\s5
\v 11 A shekaru ɗari shida na Nuhu, a wata na biyu, a ranar sha bakwai ga wata, a dai wannan ranar, sai dukkan taskoki na zurfafa suka buɗe suka fashe, sakatun sama suka buɗe,
\v 12 Ruwa ya fara sauka a duniya har kwanaki arba'in dare da rana.
\s5
\v 13 A wannan ranar dai Nuhu da 'ya'yansa, Shem da Ham da Yafet da matar Nuhu, da matan 'ya'yan Nuhu uku na tare da su, suka shiga jirgin.
\v 14 Suka shiga tare da dukkan dabbobin jeji kowanne bisa ga irinsa, da kuma kowacce irin dabba ta gida bisa ga irinta, da kuma duk abu mai rarrafe da kowaɗanne irin tsuntsaye bisa ga irinsu, da dukkan wata hallitta mai fuka-fukai.
\s5
\v 15 Biyu daga dukkan hallitar dake da numfashin rai suka shiga jirgin tare da Nuhu.
\v 16 Dabbobi da dukkan hallitun da suka shiga sun shiga ne kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Yahweh ya kulle ƙofar bayan sun shiga.
\s5
\v 17 Sai ruwan tsufana ya sauko a duniya kwanaki arba'in, ruwan kuma ya ƙaru ya ɗaga akwatin sama da ƙasa.
\v 18 Ruwa ya rufe duniya gaba ɗaya jirgin kuma yana ta lilo a saman ruwa.
\s5
\v 19 Ruwa ya tumbatsa sosai a duniya har ya rufe dukkan duwatsu dake ƙarƙashin sama.
\v 20 Ruwan ya kai har taki shida a bisa duwatsu
\s5
\v 21 Dukkan halittu dake motsi bisa duniya suka mutu; tsuntsaye, da dabbobin gida dana daji, dukkan dabbobi dake da yawa waɗanda ke duniya da kuma dukkan mutane.
\v 22 Da dukkan hallitun dake bisa ƙasa, waɗanda ke da numfashin rai a hancinsu, suka mutu.
\s5
\v 23 Kowanne abu mai rai dake bisa duniya an shafe su, daga mutane ya zuwa manyan dabbobobi, da duk masu rarrafe, ya zuwa tsuntsayen sama. Dukkan su an hallakar da su daga duniya. Sai Nuhu da waɗanda ke tare da shi ne suka rage.
\v 24 Ruwan bai janye daga ƙasa ba har kwanaki ɗari da hamsin.
\s5
\c 8
\cl Sura 8
\p
\v 1 Sai Allah ya yi la'akari da Nuhu, da dukkan dabbobin jeji, da dukkan dabbobin gida dake tare da shi a cikin jirgin ruwan. Allah ya sa iska ta hura a kan ƙasa, sai ruwaye suka fara sauka ƙasa.
\v 2 Maɓuɓɓugai na ƙarƙas da sakatun sama aka rufe su, ruwa kuma ya ɗauke.
\v 3 Ambaliyar ruwa kuma ta kwanta sannu a hankali daga ƙasa, bayan kuma kwanaki ɗari da hamsin, sai ruwa ya yi ƙasa.
\s5
\v 4 Sai jirgin ruwan ya sami sauka a wata na bakwai, a ranar sha bakwai ga wannan watan, a kan duwatsun Ararat.
\v 5 Ruwan ya ci gaba da sauka har wattanni goma. A rana ta farko ta watan, sai ƙonƙolin duwatsu suka bayyana.
\s5
\v 6 Sai ya zamana bayan kwanaki arba'in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin ruwan da ya yi.
\v 7 Ya aiki hankaka ya yi ta kai da komowa har sai da ruwa ya tsane daga duniya.
\s5
\v 8 Daga nan sai ya aiki kurciya ta ga yadda ruwan ya tsane daga ƙasa,
\v 9 amma kurciyar ba ta sami wurin sauka ba, sai ta koma gare shi cikin jirgin ruwan, domin har ya zuwa lokacin ruwa na rufe da ƙasa baki ɗaya. Sai ya miƙa hannunsa ya kamo ta ya shigar da ita cikin jirgin ruwan tare da shi.
\s5
\v 10 Sai ya jira na tsawon ƙarin kwanaki bakwai, sa'an nan sai ya sake aiken kurciyar daga cikin jirgin ruwan.
\v 11 Kurciyar ta koma wurinsa da yamma. Duba! a cikin bakinta ta tsinko sabon ganyen zaitun. Daga nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga ƙasa
\v 12 Sai ya ƙara jira na waɗansu kwanaki bakwai, sai ya sake aiken kurciyar. Ba ta sake komawa wurinsa ba.
\s5
\v 13 Sai ya zamana a shekara ta ɗari shida a farkon shekara, a wata na farko, a ranar farko ta wata, sai dukkan ruwa ya bushe daga dukkan ƙasa. Nuhu ya buɗe rufin jirgin ruwan, ya dudduba ya ga ƙasa ta bushe.
\v 14 A cikin wata na biyu, a ranar ashirin da bakwai ga wata, ƙasa ta bushe.
\s5
\v 15 Sai Allah yace da Nuhu,
\v 16 "Ka fito daga cikin jirgin ruwan da kai da matarka da 'ya'yanka da matan 'ya'yanka tare da kai.
\v 17 Ka kuma kwaso kowacce halitta mai rai dake tare da kai, da tsutsaye, da dabbobi da duk abin da ke rarrafe a doron ƙasa - domin su hayayyafa, su zama babbar runduna ta masu rai a ko'ina a duniya, su hayayyafa, su ruɓamɓanya a cikin duniya."
\s5
\v 18 Sai Nuhu ya fita tare da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa.
\v 19 Da kowacce irin hallitta dake tare da shi da dukkan masu rarrafe da dukkan tsuntsaye da duk wani abu mai motsi bisa duniya, bisa ga irinsu, suka fito daga cikin jirgin ruwan.
\s5
\v 20 Nuhu ya gina bagadi ga Yahweh. Ya ɗauki waɗansu daga cikin dabbobi masu tsarki da tsuntsaye masu tsarki ya miƙa hadaya ta ƙonawa da su akan bagadin.
\v 21 Yahweh ya shaƙi ƙanshin hadayar sai ya ce a cikin zuciyarsa, "Ba zan sake la'anta ƙasa saboda mutum ba, koda yake nufe-nufen mutane a zukatansu mugunta ne tun daga yarantakarsu. Ba zan ƙara hallakar da duk masu rai ba kamar yadda na yi.
\v 22 Muddin duniya tana nan, lokacin iri da lokacin girbi, sanyi, da zafi, bazara da damuna, dare da rana ba za su taɓa ƙarewa ba."
\s5
\c 9
\cl Sura 9
\p
\v 1 Sai Allah ya albarkaci Nuhu da 'ya'yansa, ya ce da su, "Ku ruɓanɓanya ku hayayyafa, ku cika duniya.
\v 2 Tsoronku da tsoratarwarku za ta zama a kan dukkan dabbobi masu rai dake duniya, da kowanne tsuntsu dake sararin sama, da duk wani abu dake motsi bisa ƙasa, da dukkan kifayen teku. An bada su a hannunka.
\s5
\v 3 Dukkan wani abu mai motsi dake rayuwa zai zama abinci a gare ku. Na baku koren ganyayyaki, yanzu na ba ku kowanne abu.
\v 4 Amma ba za ku ci naman da jininsa da ransa ke cikinsa ba.
\s5
\v 5 Amma a bisa jininka, da ran dake cikin jininka, zan bukaci diyya. Daga dukkan dabbobi zan bukace ta. Daga hannun kowanne mutum, wato, mutumin da ya aikata kisan kai ga ɗan'uwansa,
\v 6 zan bukaci bada lissafi na wannan mutum. Duk wanda ya zubar da jinin mutum ta wurin mutum za a zubar da jininsa, domin cikin kammanin Allah aka hallici mutum.
\v 7 Ku kuma, ku hayayyafa, ku ruɓanɓanya, ku warwatsu a ko'ina a duniya, ku ruɓanɓanya a cikinta."
\s5
\v 8 Sai Allah ya yi magana da Nuhu da 'ya'yansa dake tare da shi cewa,
\v 9 Amma, "Ka saurara! Zan tabbatar da alƙawarina da ku da zuriyarku dake biye da ku, da kuma
\v 10 dukkan halittu masu rai dake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da kowacce halitta ta duniya dake tare da ku, da kuma duk abin da ya fito daga cikin jirgin, da kuma dukkan halittu masu rai dake duniya.
\s5
\v 11 Na tabbatar da alƙawarina da ku, cewa ba zan ƙara hallakar da dukkan halittu da ruwa ba, ba za a sake yin ruwan da zai hallaka duniya ba."
\v 12 Allah yace, "Wannan ce alamar alƙawarin da nake yi tsakanina da ku da dukkan halittun dake tare da ku, domin kuma dukkan tsararraki masu zuwa:
\v 13 Na sa bakangizona a cikin girgije, zai kuma zama alamar alƙawarina da ku da kuma duniya.
\s5
\v 14 Zai kuma zamana a lokacin da na sauko da girgije a kan duniya aka kuma ga bakangizo a cikin girgijen,
\v 15 to zan tuna da alƙawarina da ku da dukkan halitta mai rai. Ruwaye ba zasu ƙara zama abin hallakarwa ga mutane ba.
\s5
\v 16 Bakangizon zai kasance a cikin girgije, zan kuma gan shi, domin in tuna da alƙawarina madawwami, tsakanin Allah da dukkan halittu masu rai a duniya.
\v 17 "Sai Allah yace da Nuhu, "Wannan ita ce alamar alƙawarin da na tabbatar tsakanina da dukkan masu rai na duniya."
\s5
\v 18 'Ya'ya maza na Nuhu da suka fito daga cikin jirgin sune Shem, Ham, da kuma Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan'ana.
\v 19 Waɗannan guda uku sune 'ya'yan Nuhu, daga waɗannan ne aka sami dukkan mutanen duniya.
\s5
\v 20 Nuhu ne ya fara zama manomi, ya kuma shuka garkar inabi.
\v 21 Sai ya sha waɗansu 'ya'yan inabin, ya kuma bugu. Yana kwance a cikin rumfarsa tsirara.
\s5
\v 22 Sai Ham mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya kuma faɗawa 'yan'uwansa guda biyu a waje.
\v 23 Sai Shem da Yafet suka ɗauki mayafi suka ɗora a kafaɗunsu, suka tafi da baya suka rufe tsiraicin mahaifinsu. Fuskokinsu na fuskantar wani bangon, domin haka ba su ga tsiraicin mahaifinsu ba.
\s5
\v 24 Da Nuhu ya tashi daga mayensa, sai ya gane abin da ɗansa ƙarami ya yi masa.
\v 25 Domin haka ya ce, "Kan'ana zai zama la'annanne. Ya zama baran barorin 'yan'uwansa."
\s5
\v 26 Hakan nan ya ce, "Yahweh Allah na Shem, ya zama da albarka, Kan'ana kuma ya zama baransa.
\v 27 Allah ya faɗaɗa abin mulkin Yafet, ya kuma sa gidansa a cikin rumfunan Shem. Kan'ana kuma ya zama baransa."
\s5
\v 28 Bayan ruwan tsufana, Nuhu ya yi shekaru ɗari uku da hamsin.
\v 29 Dukkan kwanakin Nuhu shekaru ɗari tara ne da hamsin, daga nan ya mutu.
\s5
\c 10
\cl Sura 10
\p
\v 1 Waɗannan sune zuriyar 'ya'yan Nuhu maza, wato Shem da Ham da Yafet. An haifa masu 'ya'ya maza bayan ruwan tsufana.
\s5
\v 2 'Ya'yan Yafet maza sune Gomar, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.
\v 3 'Ya'yan Gomar maza sune Ashkenaz, Rifhat da Togarma.
\v 4 'Ya'yan Yaban maza sune Elisha, Tarshish, Kittim da Dodanim.
\v 5 Daga waɗannan ƙasashe mutane suka watsu suka tafi ƙasashensu, kowanne da nasu harshe bisa ga kabilarsu, da kuma janhuriyunsu.
\s5
\v 6 'Ya'yan Ham maza sune Kush, Mizraim, Fut da Kan'ana.
\v 7 "Ya'yan Kush maza sune Seba, Habila, Sabta, Ra'ama da Sabteka. 'Ya'ya maza na Ra'ama sune Sheba da Dedan.
\s5
\v 8 Kush ya zama maihaifin Nimrod, wanda shi ne ya fara mamaye duniya.
\v 9 Shi riƙaƙƙen maharbi ne a fuskar Yahweh. Wannan ya sa ake cewa "Kamar Nimrod riƙaƙƙen maharbi a fuskar Yahweh."
\v 10 Wurin mulkinsa na farko shi ne Babila, Erek, Akkad, da Kalne a ƙasar Shinar.
\s5
\v 11 Daga cikin ƙasar ya fita zuwa Assiriya ya gina Nineba da Rehobot Ir, Kala,
\v 12 da Resen wadda take a tsakanin Nineba da Kalash. Ita babban birni ce.
\v 13 Mizraim ya zama mahaifin Ludatiyawa, Anamitiyawa, da Lehabiteyawa, Naftuhitawa,
\v 14 Fatrusitiyawa da Kasluhiyatawa (waɗanda daga cikinsu ne Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftoriyawa.
\s5
\v 15 Kan'ana ya zama mahaifin Sidom, ɗansa na fari, da kuma Het,
\v 16 har kuma da Yebusawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
\v 17 Hibiyatawa, da Arkittawa, da Sinitawa,
\v 18 da Arbaditiyawa, da Zemaritiyawa, Hammatiyawa. Bayan haka kabilar Kan'aniyawa ta yaɗu waje.
\s5
\v 19 Kan iyakar Kan'ana tana daga Sidon, wajen Gerar har zuwa Gaza da kuma kamar mutum zai yi wajen Sodom, da Gomara, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
\v 20 Waɗannan sune 'ya'yan Ham bisa ga kabilarsu, da kuma harsunansu, a cikin ƙasarsu, da al'ummarsu.
\s5
\v 21 Hakanan an haifawa Shem 'ya'ya maza, babban ɗan'uwan Yafet. Shem shi ne kãkan dukkan mutanen Eber
\v 22 'Ya'yan Shem maza sune Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da kuma Aram.
\v 23 'Ya'yan Aram maza kuwa sune Uz, Hul, Gezar, da Meshek.
\s5
\v 24 Arfakshad ya zama mahaifin Shela, Shela kuma ya haifi Eber.
\v 25 Eber na da 'ya'ya biyu sunan ɗayan shi ne Feleg, domin a cikin kwanakinsa aka raba duniya. Ɗan'uwansa shi ne Yoktan.
\s5
\v 26 Yoktan ya zama mahaifin Almodad, Shelef, Hazamabi, Yerah,
\v 27 Hadoram, Uzal, Diklah
\v 28 Obal, Abimawel, Sheba,
\v 29 Ofir, Habila, da Yobab. Duk waɗannan 'ya'ya maza ne na Yoktan.
\s5
\v 30 Iyakarsu ta kama daga Mesha, har ya zuwa hanyar Sefhar da tsauni na gabas.
\v 31 Waɗannan sune 'ya'yan Shem maza, bisa ga kabilarsu da harsunansu, a cikin ƙasashensu, bisa ga al'ummarsu.
\s5
\v 32 Waɗannan sune kabilar 'ya'yan Nuhu, bisa ga ƙididdigar asali, ta hanyar janhuriyarsu. Daga waɗannan janhuroriyoyi suka rarrabu suka shiga ko'ina a duniya bayan ruwan tsufana.
\s5
\c 11
\cl Sura 11
\p
\v 1 To dukkan duniya sun yi magana da harshe ɗaya, kalmominsu kuma ɗaya ne.
\v 2 Da suka yi tafiya zuwa gabas a hayin filin Shinar suka zauna a can.
\s5
\v 3 Suka ce da juna, "Zo mu yi tubula mu gasa su sosai." Suka yi aiki da tubali a madadin dutse, katsi kuma a maimakon yunɓu,
\v 4 "Suka ce, "Ku zo, mu gina wa kanmu birni da kuma hasumiya wadda tsawonta zai kai har sararin sama, kuma mu yi wa kanmu suna. In ba mu yi ba, za a warwatsu mu a fuskar duniya dukka."
\s5
\v 5 Sai Yahweh ya zo daga sama domin ya ga birnin da hasumiyar da zuriyar Adamu suka gina.
\v 6 Yahweh yace "Duba su mutane ɗaya ne da harshe ɗaya, kuma sun fara yin wannan! Ba da jimawa ba zasu iya yin duk wani abin da suka yi niyya, ba abin da zai gagare su.
\v 7 Zo, mu sauka mu rikirkitar da harshensu a can, domin kada su fahimci juna."
\s5
\v 8 Sai Yahweh ya warwatsa su daga can zuwa ko'ina a duniya, sai kuma suka dena ginin birnin.
\v 9 Domin haka sunansa ya zama Babila, domin a can ne Yahweh ya rikirkitar da harsunan duniya baki ɗaya, kuma daga can ne Yahweh ya watsa mutane ko'ina a sararin duniya.
\s5
\v 10 Waɗannan sune zuriyar Shem, Shem na da shekaru ɗari, sai ya zama mahaifin Arfakshad shekaru biyu bayan ruwan tsufana.
\v 11 Shem ya rayu har shekaru ɗari biyar bayan ya haifi Arfakshad. Hakanan ya haifi 'ya'ya maza da mata ma su yawa.
\s5
\v 12 Da Arkfashad ya yi shekaru talatin da biyar, sai zama mahaifin Shela.
\v 13 Arkfashad ya rayu na tsawon shekaru 403 bayan ya haifi Shela. Hakanan ya haifi waɗansu sauran 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 14 Da Shelah ya kai shekaru talatin, ya haifi Ebar.
\v 15 Shelah ya rayu har shekaru 403 bayan ya haifi Ebar. Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 16 Da Ebar ya yi shekaru talatin da huɗu sai ya haifi Felag.
\v 17 Ebar ya yi shekaru 430 bayan ya haifi Felag, Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 18 Da Felag ya yi shekaru talatin, sai ya haifi Reu,
\v 19 bayan Felag ya haifi Reu ya rayu har shekaru 209, ya kuma haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 20 Da Reu ya kai shekaru 32 sai ya haifi Serug.
\v 21 Reu ya yi shekaru 207 bayan ya haifi Serug. Hakanan ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 22 Da Serug ya kai shekaru talatin sai ya haifi Nahor.
\v 23 Bayan Serug ya haifi Nahor, ya rayu na tsawon shekaru ɗari biyu sai kuma ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\s5
\v 24 Bayan Nahor ya rayu shekaru ashirin da tara, sai ya zama mahaifin Tera.
\v 25 Nahor ya rayu shekaru 119 bayan ya haifi Tera. Hakanan ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da mata.
\v 26 Bayan Tera ya rayu na tsawon shekaru saba'in sai ya zama mahaifin Abram, da Nahor, da Haran.
\s5
\v 27 To waɗannan sune zuriyar Tera, Tera ya haifi Ibram, Nahor, Haran, Haran kuma ya haifi Lot.
\v 28 Haran ya mutu a fuskar mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa.
\s5
\v 29 Ibram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Ibram Sarai matar Nahor kuma sunanta Milka, 'yar Haran wanda shi ne mahaifin Milka da Iskah.
\v 30 To Sarai bakarariya ce; ba ta da ɗa.
\s5
\v 31 Tera ya ɗauki ɗansa, da Lot ɗan ɗansa Haran, da kuma surukarsa Sarai matar ɗansa Ibram, tare suka bar Ur ta Kaldiyawa, zuwa ƙasar Kan'ana. Amma suka zo Haran suka zauna a can.
\v 32 Tera ya rayu shekaru 205 daga nan ya mutu a Haran.
\s5
\c 12
\cl Sura 12
\p
\v 1 Sai Yahweh yace da Ibram "Ka tashi ka bar ƙasarka da danginka, da kuma ƙasar mahaifinka, zuwa ƙasar da zan nuna maka,
\v 2 zan maishe ka babbar al'umma, zan albarkace ka in kuma sa sunanka ya yi girma, kuma za ka zama albarka.
\v 3 Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, zan kuma la'anta duk wanda ya tozarta ka. Ta wurin ka dukkan al'ummar duniya za ta sami albarka."
\s5
\v 4 To Ibram ya tafi, kamar yadda Yahweh ya faɗa masa ya yi, Lot kuma ya tafi tare da shi. Ibram yana da shekaru saba'in da biyar a lokacin da ya tafi ya bar Haran.
\v 5 Ibram ya ɗauki matarsa Sarai, da Lot ɗan ɗan'uwansa da dukkan mallakarsu da suka tara, da kuma dukkan mutanen da suka samu a Haran. Suka tafi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa isa ƙasar Kan'ana.
\s5
\v 6 Ibram ya wuce ƙasar har zuwa Shekem, zuwa al'ul na Moreh. A wancan lokacin Kan'aniyawa na zaune a ƙasar.
\v 7 Yahweh ya bayyana ga Ibram, ya ce, "Ga zuriyarka Zan ba da wannan ƙasa." Daga nan Ibram ya gina bagadi domin Yahweh, wanda ya bayyana a gare shi.
\s5
\v 8 Daga can ya tafi zuwa ƙasar duwatsu a gabashin Betal, inda ya kafa rumfarsa, ga Betal a yammaci, Ai kuwa a gabashi. A can ya kafa bagadi domin Yahweh, ya kuma yi kira bisa sunan Yahweh.
\v 9 Daga nan Ibram ya ci gaba da tafiya, zuwa wajen Negeb.
\s5
\v 10 A kwai yunwa a cikin ƙasar, don haka Ibram ya gangara zuwa Masar ya zauna domin yunwar ta tsananta sosai a cikin ƙasar.
\v 11 Da ya kusa shiga Masar sai ya ce da matarsa Sarai, "Duba na san ke mace ce kyakkyawa.
\v 12 In Masarawa suka gan ki za su ce, 'Wannan matarsa ce; za su kuma kashe ni, amma za su bar ki da rai.
\v 13 Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin komai ya yi mani dai-dai saboda ke, don a bar ni in rayu saboda ke."
\s5
\v 14 Sai ya zamana bayan Ibram ya shiga cikin Masar, Masarawa suka ga cewa Sarai kyakkyawa ce.
\v 15 'Ya'yan sarki suka gan ta, suka kuma yaba mata a gaban Fir'auna, sai aka ɗauki matar zuwa gidan sarki.
\v 16 FIr'auna ya kyautatawa Ibram saboda ita, ya ba shi tumaki, takarkarai, da jakai maza da mata da bayi maza da mata da kuma raƙuma.
\s5
\v 17 Sai Yahweh ya bugi gidan Fir'auna da annoba mai zafi saboda Sarai matar Ibram.
\v 18 Fir'auna ya kira Ibram ya ce da shi me kenan ka yi mini? Meyasa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ba ce?
\v 19 Meyasa ka ce ita 'yar'uwarka ce; don in ɗauke ta ta zama matata? To yanzu ga matarka nan. Ka ɗauke ta ku tafi."
\v 20 Sai Fir'auna ya bada umarni game da shi daga nan suka sallame shi ya tafi, tare da matarsa da duk abin da yake da shi.
\s5
\c 13
\cl Sura 13
\p
\v 1 Sai Ibram ya bar Masar ya tafi Negeb, shi da matarsa da duk abin da ya mallaka. Lot ya tafi tare da su.
\v 2 Ibram ya wadata sosai ta fannin dabbobi da zinariya da azurfa.
\s5
\v 3 Ya ci gaba da tafiya daga Negeb har zuwa wurin da ya kafa rumfarsa a dã baya, tsakanin Betal da Ai.
\v 4 Ya tafi har zuwa inda ya kafa rumfa a baya. A nan ya fara kiran sunan Yahweh.
\s5
\v 5 To Lot wanda ke tare da Ibram shi ma yana da garke da sauran bisashe da rumfuna.
\v 6 Ƙasar kuma ta yi masu kaɗan, su da mallakarsu domin suna da mallaka da yawa, saboda haka ba su iya tsayawa a wuri ɗaya ba.
\v 7 Hakanan akwai rashin jituwa tsakanin makiyayan dabbobin Ibram da kuma makiyayan dabbobin Lot. Feriziyawa da Kan'aniyawa ne ke zama a wannan ƙasar a wancan lokacin.
\s5
\v 8 Sai Ibram yace da Lot, "bai kamata a sami rashin jituwa tsakanina da kai ba, ko kuma tsakanin makiyayan dabbobina da makiyayan dabbobinka.
\v 9 Fiye ma da haka mu dangi ne, duba ba fili ne nan gabanka ba? Ka zaɓi duk inda kake so, in ka zaɓi hagu, ni sai in zaɓi dama, in ka zaɓi dama ni sai in zaɓi hagu"
\s5
\v 10 Sai Lot ya duba yankin Yodan, ya kuma gan shi kore shar har zuwa yankin Zowar, kamar lambun Yahweh, kamar kuma ƙasar Masar. Haka yake kafin a hallaka Sodom da Gomora.
\v 11 Sai Lot ya zaɓi wannan filin na Yodan ya tafi gabas, dangin suka rabu da juna.
\s5
\v 12 Ibram ya zauna a ƙasar Kan'ana Lot kuma ya zauna a biranen filin ƙasa. Ya kakkafa rumfunansa har zuwa Sodom,
\v 13 To mutanen Sodom miyagu ne sosai, masu yi wa Yahweh zunubi ne.
\s5
\v 14 Yahweh yace da Ibram bayan Lot ya rabu da shi. "Duba daga inda kake tsayuwa zuwa arewa, kudu da gabas da yamma.
\v 15 Dukkan wannan ƙasar da ka ke gani, na bada ita ga zuriyarka har abada.
\s5
\v 16 Zan haɓaka zuriyarka ta zama kamar turɓayar ƙasa, domin in har mutum zai iya ƙirga turɓayar ƙasa to zai iya ƙirga zuriyarka.
\v 17 Tashi ka kewaya faɗin ƙasar da tsawonta, domin zan bada ita gare ka.
\v 18 Sai Ibram ya tashi ya ɗauki rumfarsa ya je ya zauna kusa da itatuwan rimayen Mamre, wanda ke a Hebron. A can ya kafa bagadi domin Yahweh.
\s5
\c 14
\cl Sura 14
\p
\v 1 Sai ya zamana a kwanakin Amrafel, sarkin Shinar, Ariyok sarkin El'asar, Kedorlaoma sarkin Elam, da Tidal sarkin Goyim,
\v 2 suka kai yaƙi kan Bera sarkin Sodom, Birsha, sarkin Gomora, Shinab, sarkin Adma, Shemebar, Sarkin Zeboyim, da sarkin Bela (wato wanda ake kira Zowar).
\s5
\v 3 Waɗancan sarakuna na baya suka taru a kwarin Siddim (wanda kuma ake kira Tekun Gishiri).
\v 4 Suka bautawa Kedorlawoma shekaru sha biyu, amma a shekara tasha uku suka yi tayawe.
\v 5 A shekara ta sha huɗu kuma, da sarakunan dake tare da shi suka zo suka kawo hari kan Rafaim a Ashterot Karnaim, da Zuzim a Ham, na Emim a Shaba Kiriataim,
\v 6 da Horitiyawa a ƙasar duwatsu ta Se'ir, har zuwa El Faran dake kusa da hamada.
\s5
\v 7 Daga nan sai suka juyo suka zo En Mishfat (wadda kuma ake kira Kadesh), suka cinye dukkan ƙasar Amelikawa, da kuma ta Amoriyawa waɗanda ke zama a Hazazon Tamar.
\v 8 Daga nan sai sarkin Sodom, da sarkin Gomora, da sarkin Admah da sarkin Zeboim da sarkin Bela (da ake kira Zowar) suka je suka yi shirin yaƙi
\v 9 găba da Kedorlawomar sarkin Elam, Tidal, sarkin Goim, Amrafel sarkin Shinar, Ariok, sarkin Ellasar; sarakuna huɗu găba da biyar.
\s5
\v 10 To kwarin Siddim ya cika da ramukan yaƙi, da sarakunan Sodom da Gomora suka gudu sai suka faɗa cikinsu a can. Waɗanda suka rage suka gudu kan duwatsu.
\v 11 Domin haka maƙiya suka kwashe dukkan kayayyakin Sodom da Gomora suka tafi abin su
\v 12 Da suka tafi, suka kame Lot, ɗan ɗan'uwan Ibram, wanda ke zama a Sodom tare da dukkan malakarsa.
\s5
\v 13 Wani da ya tsira ya zo ya gaya wa Ibram Ba'ibirane. Yana zama a gefen rimin Mamre Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, Waɗanda dukkansu abokan Ibram ne.
\v 14 To da Ibram ya ji maƙiya sun kame ɗan'uwansa, sai ya jagoranci horarrun mazajensa guda 318 waɗanda aka haifa a gidansa ya bi su har zuwa Dan.
\s5
\v 15 Ya rarrraba mazajensa găba da su a wannan daren ya kai masu hari, ya bi su har zuwa Hoba wadda ta ke arewa da Damaskus.
\v 16 Daga nan ya dawo da dukkan mallakar, ya kuma dawo da ɗan'uwansa Lot da duk kayansa, da mataye da sauran mutane.
\s5
\v 17 Bayan Ibram ya dawo daga yin nasara da Kedorlawoma da sarakunan dake tare da shi, sarkin Sodom ya tafi ya tare shi a kwarin Shabe (Wanda kuma ake kira Kwarin Sarki)
\v 18 Melkizedek, sarkin Salem ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.
\s5
\v 19 Ya albarkace shi cewa, Mai albarka ne Ibram ta wurin Allah Mafi Ɗaukaka, Mahallicin sama da duniya.
\v 20 Albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka, wanda ya bada maƙiyanka a hannunka." Sai Ibram ya ba shi kaso ɗaya bisa goma na komai.
\s5
\v 21 Sarkin Sodom yace da Ibram, "Ka bani mutane, ka ɗauki kayayyakin domin kanka.
\v 22 "Ibram yace da sarkin Sodom, "Na ɗaga hannunna sama zuwa ga Yahweh, Allah Maɗaukaki, Mahallicin sama da duniya,
\v 23 cewa ba zan ɗauki koda tsinkin zare ko takalmi ko dukkan wani abu dake naka ba, domin kada ka ce, 'Na sa Ibram ya azurta,'
\v 24 Ba zan ɗauki komai ba sai abin da matasa samari suka ci da kuma rabon mazajen dake tare da ni. Let Aner, Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu kason."
\s5
\c 15
\cl Sura 15
\p
\v 1 Bayan waɗannan abubuwa sai maganar Yahweh ta zo wurin Ibram a wahayi, cewa, "Ibram kada ka ji tsoro ni ne garkuwarka da kuma babban ladanka."
\v 2 Ibram yace, ya Ubangiji Yahweh, me za ka bani tunda yake har yanzu bani da ɗa. Magajin gidana kuma Eliyazar ne daga Damaskus,"
\v 3 Ibram yace, da yake baka bani zuriya ba, duba, ɗan aikin gida ne ya zama magajina.
\s5
\v 4 Sai ga maganar Yahweh ta zo gare shi, cewa "Ba wannan mutumin ne zai gaje ka ba, amma wanda zai fito daga cikin jikinka ne zai zama magajinka."
\v 5 Daga nan sai ya fito da shi waje ya ce, "Duba sama, ka kuma ƙidaya taurari, in za ka iya ƙirga su. Daga nan ya ce da shi, haka zuriyarka za ta zama."
\s5
\v 6 Ya yi imani da Yahweh, sai ya lisafta masa shi a matsayin adalci.
\v 7 Ya ce da shi, "Ni ne Yahweh, wanda ya fito da kai daga Ur ta Kaldiyawa, domin in baka wannan ƙasar ka gãje ta."
\v 8 Ya ce ya Ubangiji Yahweh, ta yaya zan sani cewa zan gãje ta?"
\s5
\v 9 Daga nan ya ce da shi, "Ka kawo mini bijimi ɗan shekara uku da kuma akuya 'yar shekara uku da kurciya, da tantabara."
\v 10 Ya kawo masa dukkan waɗannan ya kuma datsa su biyu-biyu ya kuma ajiye kowanne tsagi a gefen ɗayan, amma bai raba tsuntsayen ba.
\v 11 Lokacin da tsuntsayen dake yawo suka zo wurin mushen sai Ibram ya kore su.
\s5
\v 12 Daga nan bayan rana ta kusa faɗuwa, Ibram ya yi barci mai nauyi, sai ga wani babban duhu mai ban razana ya sha kan shi.
\v 13 Daga nan Yahweh yace da Ibram, hakika ka san cewa zuriyarka zasu yi baƙunci a ƙasar da ba tasu ba, za a kuma bautar da su, a tsananta musu har tsawon shekaru ɗari huɗu.
\s5
\v 14 Zan hukunta waccan al'ummar da zasu bauta wa, bayan haka kuma zasu fita da mallaka mai yawa.
\v 15 Amma za ka je wurin ubanninka da salama, kuma za a yi maka jana'iza a shekaru ma su kyau.
\v 16 A cikin tsara ta huɗu zasu sake zuwa nan kuma, saboda muguntar Amoriyawa ba ta kai iyakarta ba tukuna."
\s5
\v 17 Da rana ta faɗi dare kuma ya yi, sai ga hayaƙin wuta da kuma harshen wutar tukunya da tartsatsi suka wuce a tsakanin yankin naman.
\v 18 A wannan lokaci Yahweh ya yi yarjejeniya da Ibram cewa ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa tun daga kogin Masar zuwa babban kogin Yuferetis-
\v 19 da Kan'aniyawa da Kanizitawa
\v 20 da Hitiyawa da Feriziyawa da Refatiyawa,
\v 21 da Amoriyawa da Kan'aniyawa da Girgashiyawa da Yebusiyawa."
\s5
\c 16
\cl Sura 16
\p
\v 1 To Sarai, matar Ibram, ba ta haifa masa 'ya'ya ba tukuna, amma tana da baiwa, mutumiyar Masar, sunanta Hajara.
\v 2 To sai Sarai ta ce da Ibram, "Duba Yahweh ya hana mani 'ya'ya, ka je ka kwana da baiwata. Watakila na sami 'ya'ya ta wurinta." Ibram ya saurari muryar Sarai.
\v 3 Bayan Ibram ya yi shekaru goma a Kan'ana ne Sarai ta miƙa baiwarta Hajara ga Ibram a matsayin mata.
\v 4 Sai ya yi tarayya da Hajara ta kuwa yi juna biyu. Da taga ta yi juna biyu sai ta fara duban uwargijiyarta da reni.
\s5
\v 5 Daga nan Sarai ta ce da Ibram, "Wannan kuskuren a kaina saboda kai ne. Na bada baiwata gare ka, kuma bayan ta ga ta yi juna biyu, sai aka sayar da ni a idonta. Bari Ubangiji ya shari'anta tsakanina da kai."
\v 6 Amma Ibram yace da Sarai, "Duba ita baiwarki ce, tana ƙarƙashin ikonki, ki yi mata abin da kike tunanin ya fi kyau," Sai Sarai ta takura mata sosai, sai ta gudu daga gare ta
\s5
\v 7 Sai mala'ikan Yahweh ya same ta a maɓulɓular ruwa a jeji, wannan maɓulɓular dake kan hanya zuwa Shur.
\v 8 Ya ce da ita, Hajara baiwar Sarai daga ina ki ka zo kuma ina za ki? sai ta ce "ina gujewa uwargijiyata ne Sarai."
\s5
\v 9 Mala'ikan Yahweh yace da ita, "Ki koma wurin uwargiyarki, ki miƙa kai ga shugabancinta."
\v 10 Sai mala'ikan Yahweh yace da ita, "Zan ruɓanɓaya zuriyarki sosai, domin su zama da yawa, su wuce ƙirge."
\s5
\v 11 Hakanan mala'ikan Yahweh yace da ita, Duba kina ɗauke da juna biyu na ɗa namiji, kuma za ki kira sunansa Isma'ila, saboda Yahweh ya ji ƙuncinki.
\v 12 Zai zama jakin jeji, zai yi magaftaka da dukkan mutane, dukkan mutane kuma na gãba da shi, zai kuma zauna a ware da 'yan, uwansa."
\s5
\v 13 Sai ta bada wannan sunan ga Yahweh wanda ya yi magana da ita, "Kai Allah ne mai ganina," domin ta ce, "Ko zan ci gaba da gani, bayanda ya gan ni?"
\v 14 Saboda haka ake kiran rijiyar Beyer Lahai Roi; tana nan tsakanin Kadesh da Bered.
\s5
\v 15 Hajara ta haifa wa Ibram ɗa namiji ta ba shi suna Isma'ila.
\v 16 Ibram na da shekaru tamanin da shida a lokacin da Hajara ta haifi Isma'ila.
\s5
\c 17
\cl Sura 17
\p
\v 1 Da Ibram ya kai shekaru tasa'in da tara, lokacin da Yahweh ya bayyana a gare shi ya kuma ce masa, "Ni ne Allah mai iko dukka. Ka yi tafiya a gabana ka zama da rashin laifi.
\v 2 Daga nan zan cika alƙawarina tsakani na da kai, zan kuma kuma ruɓanɓanya ka sosai."
\s5
\v 3 Ibram ya sunkuyar da fuskarsa ƙasa sai Allah ya yi magana da shi cewa,
\v 4 "Ni kam, duba, alƙawarina na tare da kai. Zaka zama uban al'ummai masu yawa.
\v 5 Ba za a ƙara kiran sunanka Ibram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim - domin na zaɓe ka ka zama uban al'ummai masu yawa.
\v 6 Zan sa ka ruɓanɓanya sosai, daga cikinka kuma zan samar da al'ummai, daga cikinka kuma za a sami sarakuna.
\s5
\v 7 Zan kafa alƙawarina tsakanina da kai da kuma zuriyarka dake biye da kai, a dukkan tsararrakinsu domin alƙawari na har abada, in zama Allah a gare ka da kuma zuriyarka dake biye da kai.
\v 8 Zan bada ƙasar da kake zama gare ka da kuma zuriyarka, dukkan ƙasar Kan'ana domin ta zama mallakarka ta har abada, zan kuma zama Allahnsu."
\s5
\v 9 Sai Allah yace wa Ibrahim, "Amma kai dole ka kiyaye alƙawarina, da kai da zuriyarka dake biye da kai a dukkan tsararrakinsu.
\v 10 Wannan shi ne alƙawarina da dole zaka kiyaye, tsakanina da kai da dukkan tsararrakin dake biye da kai:
\v 11 Dole ka yi wa kanka kaciya, kuma wannan nan zai zama alamar alƙawarina da kai.
\s5
\v 12 Kowanne ɗa namiji a cikinku da ya kai shekaru takwas, dole ne a yi masa kaciya, a dukkan tsararrakin mutanenka. Wannan ya haɗa da wanda aka haifa a gidanka, da kuma wanda aka saya da kuɗinka daga kowanne irin bãƙo wanda ba ya cikin zuriyarka.
\v 13 Da wanda aka haifa maka da wanda ka saya dole ne ayi masa kaciya. Da haka alƙawarina zai kasance a jikinka domin zama alƙawari na har abada.
\v 14 Duk wani namiji wanda ba shi da kaciya za a fitar da shi daga cikin mutanensa. Ya karya alƙawarina."
\s5
\v 15 Allah yace da Ibrahim, "Game da Sarai matarka kuma Kada ka ƙara kiranta Sarai. A maimakon Sarai za a kira sunanta Saratu.
\v 16 Zan albarkace ta, kuma za ta zama uwar al'ummai. Sarakunan mutane za su fito daga cikinta."
\s5
\v 17 Daga nan sai Ibrahim ya sunkuyar da fuskarsa ƙasa ya yi dariya, a cikin zuciyarsa ya ce, "Ko za a haifa wa ɗan shekara ɗari ɗa? Ta yaya Saratu wadda ta kai shekaru tasa'in za ta iya haifar ɗa?"
\v 18 Ibrahim yace da Allah, "Ah Isma'ila zai zauna tare da kai!"
\s5
\v 19 Allah yace, "A 'a, amma Saratu matarka za ta haifa maka ɗa, kuma za ka ba shi suna Ishaku. Zan kafa alƙawarina da shi wato alƙawari na har abada da zuriyarsa dake biye da shi.
\v 20 Shi kuma Isma'ila na ji ka. Duba na sa masa albarka, zan kuma ruɓaɓɓanya shi zan wadata shi sosai. Zai zama uban kabilu goma sha biyu. Zan kuma mai da shi babbar al'umma.
\v 21 Amma alƙawarina zan kafa shi da Ishaku, wanda Saratu za ta haifa maka baɗi war haka."
\s5
\v 22 Da ya gama yi masa magana, sai Allah ya rabu da Ibrahim.
\v 23 Sai Ibrahim ya ɗauki Isma'ila ɗansa, da duk waɗanda aka haifa a cikin iyalinsa, da duk waɗanda ya saya da kuɗinsa da dukkan mazaje na mutanensa duk suka yi kaciya a rana ɗaya kamar yadda Allah ya faɗa masa.
\s5
\v 24 Ibrahim yana da shekaru tasa'in da tara lokacin da ya yi kaciya.
\v 25 Ɗansa Isma'ila kuma yana da shekaru sha uku a lokacin da aka yi masa kaciya.
\v 26 A wannan ranar aka yi wa Ibrahim da ishaku kaciya a rana ɗaya.
\v 27 Aka yi masa kaciya tare da dukkan mazajensa, da waɗanda aka haifa masa da waɗanda ya saya da kuɗi daga bãƙi.
\s5
\c 18
\cl Sura 18
\p
\v 1 Yahweh ya bayyana ga Ibrahim a gefen itatuwan rimi na Mamre a lokacin da yake zaune a ƙofar rumfa da tsakar rana.
\v 2 Ya duba sama, sai ga mutane uku na tsaye kewaye da shi. Da ya gan su, sai ya ruga daga ga ƙofar rumfar domin ya gamu da su, ya sunkuya ƙasa.
\s5
\v 3 Ya ce, "Ubangiji, in na sami tagomashi a wurin ka, kada ka wuce ka rabu da bawanka.
\v 4 Sai a kawo maku ɗan ruwa, ku wanke ƙafafu, ku kuma shaƙata a ƙarƙashin itace.
\v 5 Sai in kawo maku abinci domin ku sami ƙarfi tun da kun zo wurin bawanku. "Suka amsa, Ka yi kamar yadda ka ce."
\s5
\v 6 Sai Ibrahim ya yi hanzari ya shiga rumfa wurin Saratu, ya ce, "Hanzarto ki samo awo uku na gãri ki cuɗa shi ki yi gurasa."
\v 7 Sai Ibrahim ya ruga garke ya ɗauko ɗan maraƙi ƙosasshe ya ba bayinsa su yi sauri su gyara shi.
\v 8 Ya ɗauki curin da madara da maraƙin da aka gyara ya kai musu ya tsaya a gefensu a lokacin da suke ci.
\s5
\v 9 Suka ce da shi, "Ina Saratu matarka?" Ya amsa, Ta na can, cikin rumfa,"
\v 10 Ya ce, hakika zan komo wurinka baɗi war haka, kuma duba, Saratu matarka za ta sami ɗa." Saratu tana ji a bakin ƙofa cikin rumfa dake bayansa.
\s5
\v 11 To Ibrahim da Saratu sun tsufa, shekarunsu sun yi nisa sosai, Saratu kuma ta wuce lokacin da mata ke iya haifar 'ya'ya.
\v 12 Domin haka Saratu ta yi wa kanta dariya, tana cewa da kanta, "Bayan na tsufa, shugabana kuma ya tsufa, ko zan sami wannan jin daɗin?"
\s5
\v 13 Yahweh yace da Ibrahim, "Meyasa Saratu ta yi dariya ta kuma ce, "Ko hakika zan iya haifar ɗa Yanzu dana tsufa"?
\v 14 Ko akwai abin da ke da wuya ne ga Yahweh? A daidai lokacin dana sa, kamar war haka, zan komo wurinka a shekara mai zuwa Saratu za ta sami ɗa,"
\v 15 Sai Saratu ta yi musu, ta ce "Ban yi dariya ba domin tana jin tsoro. Ya amsa mata ya ce, "A'a, kin yi dariya."
\s5
\v 16 Sai mutanen suka tashi suka tashi suka duba wajen Sodom. Sai Ibrahim ya tafi tare dasu ya raka su a kan hanyarsu.
\v 17 Amma Yahweh yace "Ko zan ɓoye wa Ibrahim abin da zan aikata,
\v 18 da yake Ibrahim zai zama babbar al'umma kuma dukkan al'umman duniya zasu sami albarka ta wurinsa?
\v 19 Domin na zaɓe shi domin ya umarci 'ya'yansa da gidansa dake biye da shi domin su bi tafarkin Yahweh, su aikata adalci da aikin adalci, domin Yahweh ya cika abin da ya faɗa wa Ibrahim zai aikata a gare shi."
\s5
\v 20 Daga nan sai Yahweh yace, "Saboda kukan Sodom da Gomora ya yi yawa, kuma zunubinsu ya haɓaka,
\v 21 Yanzu zan sauka in ga kukan da ake yi a kan su wanda ya zo gare ni, ko hakika sun aikata al'amarin. In ba haka ba zan sani."
\s5
\v 22 To sai mazajen suka juya daga can, suka nufi wajen Sodom, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Yahweh.
\v 23 Sai Ibrahim ya matso ya ce "Ko zaka share adalai tare da mugaye?
\s5
\v 24 In a ce za a sami adalai hamsin a cikin birnin. Ko zaka hallaka shi ba tare da la'akari da adalan nan hamsin ba dake can?
\v 25 Ba zai yiwu ba ka yi haka wato ka kashe adalai tare da miyagu, domin a hori adalai kamar yadda aka hori miyagu. Ba zai yiwu ba mai hukunta duniya ya yi abin da ke dai-dai?"
\v 26 Yahweh yace, "In na sami adalai hamsin a cikin birnin Sodom, to zan kuɓutar da dukkan birnin saboda su."
\s5
\v 27 Ibrahim ya amsa ya ce, "Duba na jawo wa kaina magana da Ubangijina, koda yake ni ƙura ne kawai da toka!
\v 28 To in ace adalan sun gaza hamsin ba mutum biyar? Zaka hallaka birnin saboda rashin biyar?" Daga nan sai ya ce, "Ba zan hallaka shi ba, in na sami mutane arba'in da biyar."
\s5
\v 29 Sai ya sake yi masa magana, ya ce "To a ce za a sami arba'in a can fa?" Ya amsa, "Saboda mutane arba'in ɗin ba zan yi ba."
\v 30 "Ya ce, "Har yanzu dai ina roƙo Ubangiji kada ka yi fushi in na yi magana. To in a ce za a sami talatin a can fa." Ya amsa ba zai yi hakan ba, in a kwai mutane talatin a can."
\v 31 Ya ce "Ga shi na dage in yi magana da Ubangijina! In a ce za a sami ashirin a can fa." Ya amsa "Saboda mutane ashirin ɗin ba zan hallakar da shi ba."
\s5
\v 32 Ya ce, "Ina roƙo kada ka yi fushi, Ubangiji, zan sake faɗin wannan karo na ƙarshe. In a ce za a sami goma fa a can." Sai ya ce, "Ba zan hallaka shi ba saboda mutane goman nan."
\v 33 Sai Yahweh ya tafi a lokacin da ya gama yin magana da Ibrahim, shi kuma Ibrahim ya koma gida.
\s5
\c 19
\cl Sura 19
\p
\v 1 Mala'ikun guda biyu suka zo Sodom da yamma, a lokacin da Lot ke zaune a ƙofar Sodom. Da Lot ya gan su sai ya tashi ya tare su, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa.
\v 2 "Ya ce, "Ya shugabannina, ina roƙon ku daku biyo ta gidan baranku, ku kwana ku wanke ƙafafunku. Da safe sai ku tashi ku yi tafiyarku." Suka amsa, "A'a za mu je mu kwana a kwararo."
\v 3 Amma ya yi ta roƙon su, sai suka tafi tare da shi, suka shiga gidansa. Ya shirya musu abinci ya kuma soya musu gurasa marar gami suka ci.
\s5
\v 4 Amma kafin su kwanta, mazajen birnin, wato mazajen Sodom, suka kewaye gidan, da tsofaffinsu da matasansu, da dukkan mazajen birnin.
\v 5 Suka kira Lot, suka ce da shi, "Ina mutanen da suka zo gidanka yanzu? Fito da su gare mu, domin mu kwana da su."
\s5
\v 6 To sai Lot ya fita wajen ƙofa ya kulle ƙofar a bayansa.
\v 7 Ya ce da su, "Ina roƙon ku 'yan'uwana, kada ku yi aikin mugunta irin wannan.
\v 8 Duba ina da 'ya'ya mata guda biyu da ba su taɓa kwana da maza ba. Ina roƙon ku in kawo muku su, ku yi duk abin da kuka so da su. Amma kada ku yi wa mazajen nan komai, domin suna nan ne a ƙarƙashin kulawata
\s5
\v 9 Suka ce, "Ka tsaya can!" Haka kuma suka ce, "Shi da ya zo baƙunta, yanzu kuma ya zama alƙalinmu! Yanzu za mu ci mutuncika fiye da yadda za mu yi musu." Suka matsa wa Lot da kuma mutanen, suka zo kusa da ƙofar domin su ɓarke ta.
\s5
\v 10 Amma sai mutanen suka miƙa hannuwansu suka shigo da Lot ciki suka kulle ƙofar.
\v 11 Sai bãƙin na Lot suka bugi mutanen da makanta, wato mutanen dake wajen ƙofar gidan, duk da matasansu da tsofaffinsu duk ƙarfinsu ya ƙare a lokacin da suke ƙoƙarin ɓarke ƙofar
\s5
\v 12 Sai mutanen suka ce da Lot, "Ko kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko 'ya'ya maza da mata da duk wanda kake da shi a cikin birnin, ka fitar da su daga birnin nan.
\v 13 Domin mu na gab da hallaka wannan wurin, saboda zargin da ake yi wa birnin a gaban Yahweh ya yi yawa shi ya sa ya aiko mu domin mu hallaka shi."
\s5
\v 14 Sai Lot ya tafi ya yi magana da surukansa, wato mazajen da suka yi alƙawari zasu auri 'ya'yansa mata, ya ce "Ku hanzarta, ku fita daga wannan wurin, domin Yahweh na gab da hallaka birnin." Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi.
\v 15 Da safiya ta yi, mala'ikun suka hanzarta Lot, "Ka fito da kai da matarka da 'ya'yanka mata guda biyu dake a wannan wuri, domin kada a share ku tare a cikin wannan hukunci na birni."
\s5
\v 16 Amma ya yi jinkiri. Sai mazajen suka kama hannuwansa, da hannun matarsa, da hannuwan 'ya'yansa mata guda biyu, saboda Yahweh ya yi masa jinƙai. Suka fitar dasu bayan birnin.
\v 17 Da suka fitar dasu waje, ɗaya daga cikin mazajen ya ce, "Ku tserar da rayukanku! Kada ku waiga baya, ko kuma ku tsaya a wannan filin. Ku gudu kan duwatsu domin kada a hallakar da ku."
\s5
\v 18 Lot yace da su, "A'a shugabannina ina roƙon ku!
\v 19 Baranku ya sami tagomashi a wurinku, kuma kun nuna mini kirki sosai da kuka ceci raina, amma ba zan iya kai wa kan duwatsu ba, masifar za ta same ni, kuma zan mutu.
\v 20 Duba ga wani birni can, ya isa in je can domin tsira, kuma ƙarami ne, ina roƙo ku bar ni in je can in tsira (ba ɗan ƙarami ba ne?), rayuwata kuma za ta cetu."
\s5
\v 21 Ya ce da shi, "Shikenan, na biya maka wannan buƙata, kuma ba zan hallaka birnin da ka faɗa ba.
\v 22 Ka yi hanzari ka gudu can, domin ba zan yi wani abu ba sai ka isa can." Shi ya sa ake kiran wurin Zowar.
\s5
\v 23 Rana ta ɗaga bisa duniya a lokacin da Lot ya isa Zowar.
\v 24 Sai Yahweh ya saukar da ruwan wuta da matsanancin zafi bisa Sodom da Gomora.
\v 25 Ya hallaka waɗannan biranen, da filayen, da duk mazauna biranen da tsire-tsire da suka yi girma a ƙasa.
\s5
\v 26 Amma matar Lot dake bayansa, ta waiwaya baya, sai ta zama umudin gishiri. Ibrahim ya tashi da sassafe ya je wurin da ya tsaya tare da Yahweh.
\v 27 Ya duba wajen Sodom da Gomora da kuma dukkan filayen.
\v 28 Da ya duba sai ya ga hayaƙi na tashi daga filin kamar na hayaƙin matoya.
\s5
\v 29 To lokacin da Allah ya hallakar da biranen da filayen, Allah ya tuna da Ibrahim Ya fitar da Lot daga wannan hallakarwar a lokacin da ya hallaka biranen da Lot ya zauna.
\s5
\v 30 Amma Lot ya fita daga Zowar zuwa duwatsu tare da 'ya'yansa mata guda biyu, domin yana jin tsoron zama a Zowar. Sai ya zauna a cikin kogon dutse, shi da 'ya'yansa mata guda biyu.
\s5
\v 31 Babbar ta ce da ƙaramar, "Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wanda zai kwana damu bisa ga tsarin dukkan duniya.
\v 32 Ki zo, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi ya bugu, sai mu kwana da shi, domin mu wanzar da sunan mahaifinmu."
\v 33 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi ya bugu a wannan daren. Sai babbar ta je ta kwana da mahaifinta, bai ma san lokacin da ta kwanta ba, bai kuma san lokacin da tashi ba.
\s5
\v 34 Washegari Sai babbar ta ce da ƙaramar, "Kin ga, jiya na kwana da mahaifina. Yau kuma sai mu sa shi ya sake buguwa da ruwan inabi, ke kuma sai ki je ki kwana da shi, domin mu wanzar da sunan mahaifinmu."
\v 35 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi ya bugu, sai ƙaramar ta je ta kwana da shi. Bai san lokacin da ta kwanta ba haka kuma bai san lokacin da ta tashi ba.
\s5
\v 36 Ta haka 'ya'yan Lot guda biyu suka yi juna biyu ta wurin mahaifinsu.
\v 37 Ta farin ta haifi ɗa namji ta sa masa suna Mowab. Shi ne ya zama uban Mowabawa a yau.
\v 38 Ita ma ƙaramar 'yar ta haifi ɗa namiji sai ta ba shi suna Ben Ammi. Shi ne ya zama uban mutanen Ammon na yau.
\s5
\c 20
\cl Sura 20
\p
\v 1 Ibrahim ya bar wurin ya gangara zuwa Negeb, ya zauna tsakanin Kadesh da Shur. Shi baƙo ne mazaunin Gerar.
\v 2 Ibrahim yace game kuma da Saratu matarsa, "Ita 'yar'uwata ce" Sai Abimelek sarkin Gerar ya aika mazajensa suka ɗauko Saratu.
\v 3 Amma Allah ya zo wurin Abimelek a mafarki da duhu, ya ce da shi, "Duba kai mataccen mutum ne saboda matar daka ɗauko, domin ita matar mutumin ce."
\s5
\v 4 Abimelek kuma bai kusance ta ba ya ce, "Ubangiji ko zaka kashe har ma al'umma mai adalci? Ashe ba shi da kansa ne ya ce da ni 'ita 'yar'uwataba ce?'
\v 5 Har ma ita da kanta ta faɗa, cewa 'Shi ɗan'uwana ne.' Na yi wannan bisa nagartar zuciyata, da kuma rashin laifofin hannuwana."
\s5
\v 6 Sai Allah yace da shi a cikin mafarki, I nima na sani ka yi haka ne bisa ga nagartar zuciyarka, Ni ma kuma na hana ka yi mini zunubi. Saboda haka ne ban bar ka ka taɓa ta ba.
\v 7 Saboda haka ka mayar wa mutumin matarsa domin shi annabi ne. Zai yi maka addu'a kuma za ka rayu. Amma in ba ka mayar da ita ba, ka sani tabbas kai da dukkan abin da ke naka zaku hallaka."
\s5
\v 8 Abimelek ya tashi da asuba ya kira dukkan bayinsa gare shi. Ya faɗa musu duk waɗanna abubuwa, sai mazajensa suka firgita.
\v 9 Sai Abimelek ya kira Ibrahim yace da shi, "Me kenan ka yi mana? Yaya nayi maka laifi, da ka jawo wa mulkina da ni kaina wannan zunubi? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba."
\s5
\v 10 Abimelek yace da Ibrahim, "Meyasa ka yi wannan abin?"
\v 11 Ibrahim yace, domin na yi tsammanin cewa hakika babu tsoron Allah a wannan wurin, kuma zasu kashe ni saboda matata.'
\v 12 Bayan haka kuma hakika ita 'yar'uwata ce, 'yar mahaifina ce, amma ba 'yar mahaifiyata ba, sai kuma ta zama matata.
\s5
\v 13 Lokacin da Allah ya sa na bar gidan mahaifina in yi tafiya daga wannan wuri zuwa wancan wuri, na ce da ita dole ne ki nuna mini wannan aminci a matsayin matata: A duk inda muka je ki faɗi haka game da ni, "Shi ɗan'uwana ne.""
\v 14 Sai Abimelek ya kwashi tumaki da takarkari da maza da mata na bayi ya bada su ga Ibrahim. Daga nan ya mayar da Saratu, matar Ibrahim a gare shi.
\s5
\v 15 Abimelek yace, "Duba, wannan ƙasar tawa tana gabanka. Ka zauna a duk inda ya yi maka kyau."
\v 16 Ga Saratu kuma ya ce, duba, na ba ɗan'uwanki azurfa dubu. Wannan domin ya shafe duk wani laifi dana yi maku ne a fuskarku dukka, da kuma a gaban kowa da kowa, hakika kun yi abin da ke dai-dai."
\s5
\v 17 Sai Ibrahim ya yi addu'a sai Allah ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata domin su iya haifar 'ya'ya.
\v 18 Domin Yahweh yasa dukkan matan gidan Abimelek su zama marasa haihuwa baki ɗaya, Saboda Saratu matar Ibrahim.
\s5
\c 21
\cl Sura 21
\p
\v 1 Yahweh ya saurari Saratu kamar yadda ya ce zai yi, Yahweh kuwa ya yi wa Saratu kamar yadda ya alƙawarta.
\v 2 Saratu kuwa ta yi juna biyu ta haifa wa Ibrahim ɗa a cikin kwanakin tsufansa, a daidai lokacin da Yahweh ya yi masa magana.
\v 3 Ibrahim kuma ya raɗa wa ɗansa suna, wato wannan ɗa da aka haifa masa, wannan da Saratu ta haifa masa wato Ishaku.
\v 4 Ibrahim ya yi wa ɗansa Ishaku kaciya da yayi kwana takwas, kamar dai yadda Allah ya umarce shi.
\s5
\v 5 Ibrahim na da shekaru ɗari a lokacin da aka haifa masa Ishaku.
\v 6 Saratu ta ce, "Allah ya sa ni dariya, duk wanda ya ji zai yi dariya tare da ni."
\v 7 Wane ne zai ce da Ibrahim cewa Saratu za ta yi masa renon 'ya'ya, kuma duk da haka na haifa masa ɗa a kwanakin tsufansa!"
\s5
\v 8 Yaron ya yi girma aka yaye shi, Ibrahim ya yi babbar liyafa a ranar da aka yaye Ishaku.
\v 9 Saratu ta ga ɗan Hajara Bamasariya, da ta haifa wa Ibrahim, na ba'a.
\s5
\v 10 Saboda haka ta ce da Ibrahim, "Ka kori wannan baiwar matar da ɗanta: domin ɗan wannan baiwar ba zai ci gãdo, tare da ɗana Ishaku ba."
\v 11 Wannan abin ya yi wa Ibrahim zafi a rai saboda ɗansa.
\s5
\v 12 Amma Allah yace da Ibrahim, "Kada ka damu saboda yaron, da kuma saboda wannan matar baiwarka. Ka saurari kalmominta kan duk abin da ta faɗa maka kan wannan al'amari, saboda ta wurin Ishaku ne za a kira zuriyarka.
\v 13 Hakanan zan sa ɗan baiwar matar ya zama al'umma, domin shi zuriyarka ne."
\s5
\v 14 Ibrahim ya ta shi da asuba, ya ɗauki gurasa da goran ruwa, ya ba da shi ga Hajara ya ɗora shi a kafaɗarta. Ya ba ta ɗan ya sallame ta ta tafi. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Beyersheba.
\v 15 Da ruwan da ke cikin goran ruwan ya ƙare, sai ta yashe da ɗan a gindin wasu ciyayi.
\v 16 Sai ta tafi ta zauna can nesa dai-dai harbin kibiya, domin ta ce, "Kada in ga mutuwar ɗana." Da ta zauna daura da shi sai ta ta da murya ta yi kuka.
\s5
\v 17 Allah ya ji kukan ɗan, sai mala'ikan Allah ya kira Hajara daga can sama, ya ce da ita, "Me ke damun ki, Hajara? Kada ki ji tsoro, domin Allah ya ji kukan ɗan a inda yake.
\v 18 Tashi ki ɗauki yaron, ki ƙarfafa shi, domin zan maishe shi babbar al'umma."
\s5
\v 19 Sai Allah ya buɗe idanunta, sai ta ga rijiyar ruwa. ta je ta cika gorar da ruwa, ta ba ɗan ya sha.
\v 20 Allah na tare da ɗan, ya kuma yi girma. Ya yi rayuwa cikin jeji sai ya zama mafarauci.
\v 21 Ya yi rayuwa a jejin Faran, mahaifiyarsa kuma ta aura masa mata daga ƙasar Masar
\s5
\v 22 Sai ya zamana a lokacin da Abimelek da Fikol shugaban sojojinsa ya yi magana da Ibrahim, cewa, "Allah na tare da kai a cikin dukkan al'amuranka.
\v 23 Yanzu sai ka rantse mini cewa ba zaka yi mini ƙarya ba, haka kuma 'ya'yana, da zuriyata. Ka nuna mini da kuma ƙasar da kake zaune a ciki irin wannan alƙawari mai aminci da na nuna gare ka."
\v 24 Ibrahim yace "Na rantse."
\s5
\v 25 Ibrahim kuma ya miƙa kukansa ga Abimelek game da rijiyar ruwa da bayin Abimelek su ka ƙwace daga wurinsa.
\v 26 Abimelek yace "Ban san wanda ya yi wannan abu ba. Ba ka faɗa mini ba tuntuni; Ban ji al'amarin ba sai yau."
\v 27 Sai Ibrahim ya ɗauki tumaki da shanu ya ba Abimelek, su biyun suka yi yarjejeniya.
\s5
\v 28 Sai Ibrahim ya ware raguna bakwai na garken da kansu.
\v 29 Abimelek yace da Ibrahim, "Mene ne ma'anar waɗannan matan tumakin daka shirya su da kansu?"
\v 30 Ya amsa, waɗannan matan tumakin guda bakwai zaka karɓa daga hannuna, domin su zama shaida domina, cewa ni na haƙa wannan rijiya."
\s5
\v 31 Sai ya kira wannan wurin Biyasheba, saboda a can ne dukkan su suka yi rantsuwa.
\v 32 Suka yi yarjejeniya, Daga nan sai Abimelek da Fikol, shugaban sojojinsa, ya koma ƙasar Filistiyawa.
\s5
\v 33 Ibrahim ya dasa itacen sabara a Biyasheba. a can ya yi sujada ga Yahweh, Allah madawwami.
\v 34 Ibrahim ya zauna a matsayin baƙo a ƙasar filistiyawa na kwanaki masu yawa.
\s5
\c 22
\cl Sura 22
\p
\v 1 Sai ya zamana bayan waɗannan abubuwa Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce da shi, "Ibrahim" Ibrahim yace, "Ga ni nan,"
\v 2 Sai Allah yace, "Ka ɗauki ɗanka, tilon ɗanka, wanda kake ƙauna, Ishaku, sai ku je ƙasar Moriya. A can za ka miƙa shi baiko na ƙonawa akan ɗaya daga cikin duwatsun dake can, wanda zan faɗa maka game da shi."
\v 3 Sai Ibrahim ya tashi da asuba ya ɗaura wa jakinsa sirdi, ya kuma ɗauki biyu daga cikin matasan mazajensa tare da shi, haɗe kuma da Ishaku ɗansa. Ya sassari itace domin baiko na ƙonawa, daga nan ya kama hanyarsa zuwa inda Allah ya faɗa masa.
\s5
\v 4 A rana ta uku Ibrahim ya duba sama sai ya hangi wurin daga nesa.
\v 5 Sai Ibrahim yace da matasansa, "Ku tsaya nan da jakin, ni da yaron zamu haura can. Za mu yi sujada daga nan sai mu dawo wurinku."
\v 6 Sai Ibrahim ya ɗauki itace domin hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa Ishaku ɗansa. Sai ya ɗauki wuƙa da wuta a hannunsa; sai kuma suka tafi tare.
\s5
\v 7 Ishaku ya yi magana da Ibrahim mahaifinsa ya ce, "Babana," sai ya ce, "Ga ni nan ɗana." Ya ce, Ga wuta anan da itace, amma ina ɗan ragon baikon ƙonawa?"
\v 8 Ibrahim yace, "Ɗana Allah da kansa zai tanada ɗan rago domin baikon ƙonawa." Sai suka ci gaba da tafiya tare su dukka.
\s5
\v 9 Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, Sai Ibrahim ya gina bagadi a can ya zuba itace a kansa. Sai ya ɗaure ɗansa Ishaku, ya ɗora shi akan bagadin bisa itacen.
\v 10 Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauko wuƙa domin ya yanka ɗansa.
\s5
\v 11 Sai mala'ikan Yahweh ya kira shi daga sama ya ce, "Ibrahim, Ibrahim!" sai ya ce, "Ga ni nan."
\v 12 Ya ce, "Kada ka ɗora hannunka a kan yaron, kar ka yi duk wani abu da zai cutar da shi, domin yanzu na sani kana tsoron Allah, ganin cewa ba ka hana mini ɗanka ba, tilon ɗanka."
\s5
\v 13 Ibrahim ya duba sama, sai ga ɗan rago a sarƙafe da ƙahonsa. Ibrahim ya ɗauki ɗan ragon ya miƙa shi baiko na ƙonawa a maimakon ɗansa.
\v 14 Saboda haka Ibrahim ya kira wurin, "Yahweh zai tanada," haka kuma ake kiran wurin har yau,"A kan tsaunin Yahweh za a tanada shi."
\s5
\v 15 Mala'ikan Yahweh ya kira Ibrahim daga sama a karo na biyu
\v 16 ya ce - wannan shi ne furcin Yahweh - na yi rantsuwa da kaina cewa da yake ka yi wannan abu, ba ka hana ɗanka ba tilon ɗanka,
\v 17 Hakika zan albarkace ka zan kuma ruɓanɓanya zuriyarka kamar taurarin sammai, kamar kuma yashin dake gaɓar teku; zuriyarka kuma zasu mallaki ƙofar maƙiyansu.
\s5
\v 18 Ta wurin tsatsonka za a albarkaci dukkan al'ummar duniya, saboda ka yi biyayya da muryata."
\v 19 Sai Ibrahim ya koma wurin barorinsa, suka tafi Beyarsheba tare sai ya zauna a Beyarsheba.
\s5
\v 20 Ya zamana bayan waɗannan abubuwa sai, aka ce da Ibrahim "Milka ta haifi 'ya'ya, haka kuma ɗan'uwanka Nahor."
\v 21 Su ne Uz ɗansa na fari, Buz shi ne ɗan'uwansa, Kemuwal shi ne mahaifin Aram, da
\v 22 Kesed da Hazo, da Fildash da Yidlaf da Betuwel.
\s5
\v 23 Betuwel ya haifi Rebeka. Waɗannan sune 'ya'ya takwas da Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim.
\v 24 Ƙwarƙwararsa mai suna Reuma ita ma ta haifi Tebah da Gaham Tahash da Ma'aka.
\s5
\c 23
\cl Sura 23
\p
\v 1 Saratu ta rayu tsawon shekaru ɗari da ashirin da bakwai. Waɗannan sune shekarun Saratu.
\v 2 Saratu ta mutu a Kiriyat Arba wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim ya yi makoki da kuka domin Saratu.
\s5
\v 3 Sai Ibrahim ya tashi ya bar wurin da matarsa ta mutu, ya yi magana da 'ya'yan Het, cewa.
\v 4 "Ni bãƙo ne a cikin ku Ina roƙo ku bani mallakar wurin maƙabarta a cikinku domin in bizne matattuna."
\s5
\v 5 Sai 'ya'yan Het suka amsa wa Ibrahim cewa,
\v 6 "Ka saurare mu shugabana. Kai yariman Allah ne a cikin mu. Bizne matattunka a duk inda ka zaɓa a maƙabartunmu, ba wanda zai hana maka maƙabartarsa domin ka bizne matattunka."
\s5
\v 7 Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna wa mutanen ƙasar, ga "ya'yan Het.
\v 8 Ya yi musu magana cewa, "In kun yarda cewa in bizne matacciyata, sai ku saurare ni ku roƙi Ifron ɗan Zohar domi na.
\v 9 Ku tambaye shi ya sayar mini da kogon Makfela, wadda ya mallaka, wadda yake a ƙarshen filinsa. Domin cikakken farashi ya kuma sayar mini da shi a gaban mutane domin ya zama mallakata, da maƙabarta."
\s5
\v 10 Ifron kuma na zaune a cikin 'ya'yan Het, sai Ifron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan 'ya'yan Het maza da kuma duk waɗanda suka zo ƙofar birninsa, cewa,
\v 11 "A'a shugabana, ka saurare ni. Na baka filin da kuma kogon dake cikinsa. Na baka shi a gaban 'ya'yan mutanena maza. Na baka shi domin bizne matacciyarka."
\s5
\v 12 Sai Ibrahim ya sunkuyar da kansa ƙasa a gaban mutanen ƙasar.
\v 13 Ya yi magana da Ifron a kunnen mutanen ƙasar cewa. "Amma in ka amince, inka yarda ka saurareni. Zan biya kuɗin filin. Ka karɓi kuɗi daga wuri na, ni kuma zan bizne mattaciyata a can."
\s5
\v 14 Ifron ya amsa wa Ibrahim, da cewa,
\v 15 "Ina roƙo, ya shugabana, ka saurare ni. Ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu na azurfa, mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka bizne mamaciyarka."
\v 16 Ibrahim ya saurari Ifron, ya auna shekel ɗari huɗu kamar yadda Ifron ya ambata a kunnuwan dukkan 'ya'yan Het maza, mudu ɗari huɗu na zinariya, bisa ga mizanin ma'aunin fatake.
\s5
\v 17 Domin haka filin Ifron dake a Makfela wanda ke gaban Mamre, wato da filin da kogon dake cikinsa, da duk itatuwan dake cikin filin, da dukkan iyakarsa,
\v 18 aka ba Ibrahim tawurin sayarwa a gaban 'ya'yan Het maza, da kuma duk waɗanda suka zo ƙofar birninsa.
\s5
\v 19 Bayan wannan Ibrahim ya bizne Saratu matarsa a cikin kogon filin Makfela, wanda ke gaba da Mamre wato Hebron, a cikin ƙasar Kan'ana.
\v 20 Domin haka da filin da kogon dake cikinsa aka miƙa su ga Ibrahim daga 'ya'yan Het maza domin ya zama maƙabarta.
\s5
\c 24
\cl Sura 24
\p
\v 1 Ya zamana kuma Ibrahim ya tsufa ainun, kuma Yahweh ya albarka ce shi a cikin komai.
\v 2 Sai Ibrahim yace da baransa, wanda ya fi daɗewa da kuma ke kula da komai da ya mallaka, ya ce "Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,
\v 3 zan sa ka ka rantse da Yahweh, Allah na sama da kuma Allah na duniya, cewa ba zaka auro wa ɗana mata daga cikin Kan'aniyawan da nake zama a cikinsu ba.
\v 4 Amma zaka je cikin ƙasata da dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata daga can."
\s5
\v 5 Sai baran yace da shi, "To yaya kenan, in matar ta ce ba za ta biyo ni zuwa wannan ƙasar ba fa? Ko ya zama tilas in mayar da ɗanka zuwa ƙasar da ka baro?"
\v 6 Ibrahim yace da shi, "Ka tabbata cewa ba ka komar da ɗana can ba!
\v 7 Yahweh Allah na sama, wanda ya ɗauko ni daga gidan mahaifina da kuma ƙasar dangina, wanda kuma ya yi mini tabbataccen alƙawari cewa, 'Ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa,' zai aiko mala'ikansa a gabanka, kuma zaka samo wa ɗana mata daga can.
\s5
\v 8 Amma in matar ba ta son ta biyo ka, to ka kuɓuta daga rantsuwata, kada ka komar da ɗana can,"
\v 9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyoyin Ibrahim shugabansa, ya yi masa rantsuwa game da wannan al'amari.
\s5
\v 10 To sai baran ya ɗauki raƙuma goma na shugabansa ya tafi. Haka nan ya ɗauki duk waɗansu kyaututtuka da suka kamata daga wurin shugabansa ya tafi da su yankin Aram Naharaim zuwa birnin Nahor.
\v 11 Ya sa raƙuman suka kwakkwanta a gefen rijiyar ruwa. Da yamma ne daidai lokacin da mata ke fita ɗiban ruwa.
\s5
\v 12 Daga nan sai ya ce, "Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, ka ba ni nasara a yau ka kuma nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim.
\v 13 Duba yanzu ina tsaye a bakin ƙoramar ruwa, kuma 'yan'matan mutanen birnin suna fitowa domin su ɗibi ruwa.
\v 14 Ka sa abin ya kasance kamar haka. In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha; sai kuma ta ce da ni, ka sha, zan kuma shayar da raƙumanka ma; to bari ta zama matar daka nufa ta zama matar bawanka Ishaku. Da haka zan sani cewa ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana."
\s5
\v 15 Sai ya zamana kafin ma ya gama magana sai ga Rebeka ta zo da abin ɗiban ruwanta a kafaɗarta. Rebeka 'yar Betuwel ce ɗan Milka, matar Nahor, ɗan'uwan Ibrahim.
\v 16 Budurwar kyakkyawa ce kuma ba ta ɓata budurcinta ba. Ba mutumin da ya taɓa kwana da ita. Sai ta tafi ƙoramar ta cika abin ɗiban ruwanta, ta hauro.
\s5
\v 17 Sai baran ya yi gudu domin ya gamu da ita ya ce, "Ina roƙo ki sam mani ruwa in ɗan sha daga cikin abin ɗiban ruwanki."
\v 18 Ta ce ya shugabana ka sha sai ta yi sauri ta sauke abin ɗiban ruwan ƙasa a hannunta ta ba shi ya sha.
\s5
\v 19 Bayan ta gama ba shi ya sha, sai ta ce, "Zan ɗebowa raƙumanka ma su sha har sai sun kammala sha."
\v 20 Sai ta yi sauri ta juye abin ɗebo ruwan, ta yi gudu ta sake komawa rijiyar domin ta ɗebo ruwa domin dukkan raƙumansa.
\s5
\v 21 Sai mutumin ya dube ta a natse domin ya gani ko Yahweh ya ba tafiyarsa nasara ko kuwa a'a.
\v 22 Bayan raƙuman sun gama shan ruwan, sai mutumin ya ciro zoben zinariya na hanci mai nauyin rabin ma'auni, da ƙarau guda biyu na azurfa na sawa a dantse wanda ya kai nauyin ma'auni goma,
\v 23 sai ya tambaya, "Ke "yar wane ne? Ina roƙon ki ki faɗa mini, ko akwai masauki a gidan mahaifinku da za mu kwana?"
\s5
\v 24 Ta ce da shi, "Ni 'yar Batuwel ce ɗan Milka wanda ta haifawa Nahor."
\v 25 Ta kuma ce da shi muna kuma da ciyawa da abincin dabbobi da kuma ɗaki domin ku kwana."
\s5
\v 26 Sai mutumin ya sunkuya ƙasa ya yi sujada ga Yahweh.
\v 27 Ya ce, "Albarka ta tabbata ga Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, wanda bai yashe da alƙawarinsa mai aminci ba da kuma amincinsa ga shugabana. Ni da kaina Yahweh ya bi da ni kai tsaye zuwa gidan dangin shugabana."
\s5
\v 28 Sai budurwar ta yi gudu ta je ta faɗa wa iyalin gidan mahaifiyarta duk abin da ya faru dangane da waɗannan al'amura.
\v 29 Rebeka kuma tana da ɗan'uwa, sunansa Laban. Sai Laban ya ruga zuwa wurin mutumin wanda ke can kan hanyar ƙoramar.
\v 30 Da ya ga wannnan zobe na hanci da ƙarau na dantse a dantsen 'yar'uwarsa, kuma bayan ya ji duk abin da Rebeka 'yar'uwarsa ta faɗa, "Wannan shi ne abin da mutumin ya ce da ni," sai ya tafi wurin mutumin, sai ga shi a tsaye a gefen raƙuma a wurin ƙoramar.
\s5
\v 31 Sai Laban yace, "Zo, kai mai albarka na Yahweh. Meyasa kake tsayuwa a waje? Na shirya gida da kuma wuri domin raƙuman."
\v 32 Sai mutumin ya zo gidan ya kuma sauke wa raƙuman kaya. Sai aka ba raƙuman ciyawa da abincin dabbobi aka kuma tanadi ruwa domin ya wanke ƙafafunsa da kuma na mutanen dake tare da shi.
\s5
\v 33 Suka kawo masa abinci domin ya ci, amma ya ce, "Ba zan ci ba sai na faɗi abin da zan faɗa. "Sai Laban yace to faɗi abin da zaka faɗa."
\v 34 Ya ce, "Ni baran Ibrahim ne.
\v 35 Yahweh ya albarkaci shugabana sosai ya kuma yi girma sosai. Ya ba shi garkuna da dabbobi da zinariya da azurfa, da bayi maza da mata da raƙuma da jakuna.
\s5
\v 36 Saratu matar shugabana ta haifi ɗa ga shugabana a lokacin da ya tsufa, ya kuma bayar da duk abin da ya mallaka gare shi.
\v 37 Shugabana ya sa na rantse, cewa, 'Ba za ka auro wa ɗana mata daga cikin 'yanmatan Kan'aniyawa ba, waɗanda a ƙasarsu na yi gidana.
\v 38 Maimakon haka dole ka je wajen dangin mahaifina, cikin 'yan'uwana ka samo wa ɗana matar aure.'
\s5
\v 39 Na ce da shugabana, in a ce matar ba zata biyo ni ba fa.'
\v 40 Amma ya ce da ni, Yahweh wanda nayi tafiya a gabansa, zai aiko mala'ikansa ya kasance tare da kai ya kuma baka nasara bisa tafiyarka, domin ka auro wa ɗana mata daga cikin dangina da kuma iyalin mahaifina.
\v 41 Amma zaka kuɓuta daga rantsuwata in ka zo wurin 'yan'uwana in ba su baka ita ba. To zaka kuɓuta daga rantsuwata.'
\s5
\v 42 To da na kawo wurin ƙorama, na ce, 'Ya Yahweh, Allah na shugabana Ibrahim, ina roƙon ka, in har ka so ka ba tafiyata nasara-
\v 43 gani nan a tsaye a bakin ƙorama-ka sa budurwar da ta zo ɗiban ruwa, wato macen da zan ce, "Ina roƙo ki ɗan san mani ruwa in sha daga abin ɗiban ruwanki,"
\v 44 macen da ta ce da ni, "Sha, zan kuma shayar da raƙumanka"_Bari ta zama macen da kai, Yahweh, ka zaɓa domin ɗan shugabana.'
\s5
\v 45 Tun ma kafin in gama magana a cikin zuciyata, sai ga, Rebeka ta zo da abin ɗiban ruwanta a kafaɗarta sai ta gangara ƙoramar ta ɗebo ruwa. Sai na ce da ita, 'Ina roƙo ki bani ruwa in sha.'
\v 46 Sai ta yi sauri ta sauko da abin ɗiban ruwan daga kafaɗarta ta ce, 'Ka sha, zan kuma shayar da raƙumanka.' Sai na sha, ta kuma shayar da raƙuman.
\s5
\v 47 Na tambaye ta cewa, 'Ke 'yar wane ne?' Ta ce, 'Yar Betuwel, ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.' Daga nan sai na sa zoben a hancinta da kuma ƙarau a damtsenta.
\v 48 Sai na sunkuya na yi sujada ga Yahweh, na albarkaci Yahweh Allah na shugabana Ibrahim, wanda ya bishe ni a madaidaiciyar hanya domin in sami 'yar dangin shugabana domin ɗansa.
\s5
\v 49 Yanzu kuma, in kuna shirye ku nuna zumunci mai aminci da amana, ku faɗa mini. Amma in ba haka ba, ku faɗa mini, domin in bi dama ko hagu."
\s5
\v 50 Sai Laban da Betuwel suka amsa suka ce, Al'amarin daga Yahweh ya zo; ba zamu iya ce maka ya yi kyau ko bai yi kyau ba.
\v 51 Duba Rebeka na gabanka. Ɗauke ta ku tafi, domin ta zama matar ɗan shugabanka, kamar yadda Yahweh ya faɗa."
\s5
\v 52 Da baran Ibrahim ya ji maganarsu, sai ya sunkuyar da kansa ƙasa ga Yahweh.
\v 53 Sai baran ya fito da kayayyaki na zinariya da azurfa da sutura ya miƙa su ga Rebeka. Hakanan ya bada kyautai masu daraja ga ɗan'uwanta da kuma mahaifiyarta.
\s5
\v 54 Daga nan shi da mazajen dake tare da shi suka ci, suka sha. Suka kwana har gari ya waye, bayan sun tashi da safe, ya ce "Ku sallame ni zuwa gun shugabana."
\v 55 Ɗan'uwanta da mahaifiyarta suka ce, "Bari budurwar ta ɗan yi waɗansu 'yan kwanaki kamar goma tukuna. Bayan nan za ta iya ta tafi."
\s5
\v 56 Amma ya ce da su kada ku hana ni da yake Yahweh ya sa tafiyata ta yi nasara. Ku sallame ni domin in koma wurin shugabana."
\v 57 Suka ce za mu kira budurwar mu tambaye ta."
\v 58 Sai suka kira Rebeka suka tambaye ta, "Za ki tafi tare da wannan mutumin?" Ta amsa "zan tafi."
\s5
\v 59 Sai suka aika 'yar'uwarsu Rebeka, tare da baranyarta, a cikin tafiyarta tare da baran Ibrahim da mazajensa.
\v 60 Suka albarkaci Rebeka, suka ce da ita, "Yar'uwarmu, muna addu'a ki zama uwar dubun dubbai goma, da ma zuriyarki ta mallaki ƙofar maƙiyansu."
\s5
\v 61 Sai Rebeka ta tashi, ita da barorinta mata suka hau raƙuma, suka bi mutumin. Da haka baran ya ɗauki Rebeka ya yi tafiyarsa.
\v 62 Ya zamana Ishaku na zama a Negeb, ya dawo kenan daga Beyerlahairoi.
\s5
\v 63 Ishaku ya fita domin yin nazari a saura da yammaci. Da ya duba tudu, ya hanga, sai ya ga raƙuma na tafe!
\v 64 Rebeka ta duba, da ta ga Ishaku sai ta diro daga kan raƙumin.
\v 65 Ta ce da baran, "Wane ne wancan dake tafiya a cikin saura domin ya tarbe mu?" Baran yace, "'Shugabana ne." Sai ta ɗauki gyale ta yi lulluɓi.
\s5
\v 66 Baran ya zaiyana wa Ishaku dukkan abin da ya yi.
\v 67 Sai Ishaku ya kawo ta rumfar mahaifiyarsa Saratu ya ɗauki Rebeka, ta zama matarsa, ya kuma ƙaunace ta. Da haka Ishaku ya ta'azantu bayan mutuwar mahaifiyarsa.
\s5
\c 25
\cl Sura 25
\p
\v 1 Sai Ibrahim ya auro wata mata mai suna Ketura.
\v 2 Ta haifa masa Zimra, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak, da Shuwa.
\v 3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Asiriya, da mutanen Letush, da mutanen Leyum.
\v 4 'Ya'yan Midiyan sune Efa, Efer, Hanok, Abida, da Elda'ah. Duk waɗannan sune zuriyar Ketura.
\s5
\v 5 Ibrahim ya mallaka duk abin da yake da shi ga Ishaku.
\v 6 Duk da haka, a lokacin da yake raye ya ba da kyautai ga 'ya'yan ƙwaraƙwaransa ya aika su ƙasar gabas nesa da ɗansa Ishaku.
\s5
\v 7 Waɗannan sune kwanakin shekarun rayuwar Ibrahim da ya yi shekaru, 175.
\v 8 Ibrahim ya yi numfashinsa na ƙarshe ya mutu a cikin kyakkyawan tsufa, tsohon mutum mai cike da kuzari, sai aka tattara shi ga mutanensa.
\s5
\v 9 Ishaku da Isma'ila, 'ya'yansa suka bizne shi a kogon Makfela, a filin Ifron ɗan Zohar Bahitte, wadda ke kusa da Mamre.
\v 10 Wannan filin Ibrahim ya saya daga'ya'yan Het maza. A can aka bizne Ibrahim da matarsa Saratu.
\v 11 Bayan mutuwar Ibrahim Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku, Ishaku ya zauna kusa da Beyer Lahai Roi.
\s5
\v 12 To Waɗannan sune zuriyar Isma'ila ɗan Ibrahim, da Hajara Bamasariya baiwar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
\s5
\v 13 Waɗannan sune sunayen 'ya'yan Isma'ila bisa ga tsarin haihuwarsu: Nebaiyot - shi ne ɗan fari na Isma'ila, da Kedar, da Adbe'el, da Mibsam,
\v 14 da Mishma, da Massa,
\v 15 Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema.
\v 16 Waɗannan su ne 'ya'yan Isma'ila, kuma waɗannan sune sunayensu bisa ƙauyukansu, suna kuma da sarakuna sha biyu bisa ga kabilarsu.
\s5
\v 17 Waɗannan su ne shekarun rayuwar Isma'ila, shekaru, 137 ya yi numfashinsa na ƙarshe sa'an nan ya mutu, sai aka tattara shi ga mutanensa.
\v 18 Sun yi rayuwa daga Habila zuwa Ashur, wadda take kusa da Masar, ɗaya kuma ya nufi Asiriya. Sun yi zaman tankiya da juna.
\s5
\v 19 Waɗannan su ne al'amura game da Ishaku, ɗan Ibrahim: Ibrahim ya haifi Ishaku.
\v 20 Ishaku nada shekaru arba'in a lokacin da ya ɗauki Rebeka a matsayin matarsa, 'yar Betuwel mutumin Aramiya ta Faddan Aram, 'yar'uwar Laban na Aramiya.
\s5
\v 21 Ishaku ya yi addu'a ga Yahweh domin matarsa saboda ba ta da ɗa, Yahweh kuma ya amsa addu'arsa, Rebeka matarsa kuma ta yi juna biyu.
\v 22 'Ya'yan na ta fama tare tun daga cikinta, sai ta ce, "Meyasa wannan ke faruwa da ni?" Ta je ta tambayi Yahweh game da haka.
\s5
\v 23 Yahweh yace da ita, "Al'umma biyu ce a mahaifarki, mutane biyu kuma zasu rabu daga gare ki. Ɗaya jama'ar za ta fi ɗayar ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin."
\s5
\v 24 Da lokacin haihuwarta yayi, sai ta kasance da 'yan biyu a mahaifarta.
\v 25 Na farkon ya fito da gargasa a ko'ina kamar tufafin gashi. Suka kira sunansa Isuwa.
\v 26 Bayan haka, ɗan'uwansa ya fito hannuwansa na riƙe da diddigen Isuwa. Sai aka kira shi Yakubu. Ishaku na da shekaru sittin lokacin da matarsa ta haifa masa su.
\s5
\v 27 Samarin suka yi girma, Isuwa ya zama shahararren mafarauci mai yawo a saura; amma Yakubu mai shiru-shiru ne, wanda ya kashe lokacinsa cikin runfofi.
\v 28 Sai ishaku ya ƙaunaci Isuwa domin yakan ci namomin jejin da ya harbo, amma Rebeka ta ƙaunaci Yakubu.
\s5
\v 29 Yakubu ya shirya ɗan dage-dage. Isuwa ya zo daga saura, ya kuma raunana saboda yunwa.
\v 30 Isuwa yace da Yakubu, "Ka ciyar da ni da dage-dagenka mana. Ina roƙonka ƙarfina ya ƙare!" Shiyasa aka kira sunansa Idom.
\s5
\v 31 Yakubu yace, "Da farko ka sayar mani da matsayinka na ɗan fari tukuna."
\v 32 Isuwa yace, "Duba, Na kusa mutuwa. Wanne amfani ne matsayin ɗan fari ke da shi a gare ni?"
\v 33 Yakubu yace, "Da farko sai ka rantse mani" ta haka Isuwa ya yi rantsuwa kuma ta haka Isuwa ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yakubu.
\v 34 Yakubu ya ba Isuwa dage-dagen wake da gurasa. Ya ci ya sha, daga nan ya tashi ya tafi abinsa. Ta wannan hali Isuwa ya banzantar da matsayinsa na ɗan fari.
\s5
\c 26
\cl Sura 26
\p
\v 1 Sai aka yi yunwa a ƙasar, bayan wacce aka yi ta fari a kwanakin Ibrahim, Ishaku ya tafi wurin Abimelek, sarkin Filistiyawa a Gerar.
\s5
\v 2 Sai Yahweh ya bayyana gare shi ya ce, "Kada ka gangara Masar; ka zauna a ƙasar dana ce ka zauna a ciki.
\v 3 Ka zauna a wannan ƙasar, zan kasance tare da kai, in kuma albarkace ka; domin a gare ka da zuriyarka ne zan bayar da ƙasashen al'ummai, kuma zan cika alƙawarin dana yi wa Ibrahim mahaifinka.
\s5
\v 4 Zan ruɓanɓanya zuriyarka kamar taurarin sama zan kuma bada waɗannan ƙasashe ga zuriyarka. Ta wurin al'ummarka dukkan ai'umman duniya zasu sami albarka.
\v 5 Zan yi wannan domin Ibrahim ya yi biyayya da muryata ya kuma kiyaye dokokina, da farillaina, da shari'una. da ka'idodina."
\s5
\v 6 Don haka Ishaku ya zauna a Gerar.
\v 7 Da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, "Ita 'yar'uwata ce". Ya ji tsoro ya ce, "Ita matata ce," saboda ya yi tunanin cewa, mutanen zasu kashe ni su ɗauke Rebeka domin ita kyakkyawa ce."
\v 8 Bayan Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba ta taga. Sai ya ga Ishaku na shafa Rebeka, matarsa.
\s5
\v 9 Abimelek ya kira Ishaku gare shi ya ce, "Duba hakika ita matarka ce. Don me ka ce, ita 'yar'uwata ce'?" Ishaku yace da shi, "Saboda na yi tsammanin wani zai iya ya kashe ni don ya same ta."
\v 10 Abimelek yace, "Me kenan ka yi mana? Da kuwa wani ya kwana da matarka cikin sauƙi, da kuma ka jawo mana laifi."
\v 11 Sai Abimelek ya gargaɗi mutene ya ce, "Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa hakika za a kashe shi."
\s5
\v 12 Ishaku ya shuka hatsi a waccan ƙasar, ya kuma yi girbi a wannan shekara, ya sami riɓi ɗari, saboda Yahweh ya albarkace shi.
\v 13 Mutumin ya azurta, ya dinga bunƙasa sosai har sai da ya yi girma sosai.
\v 14 Yana da tumakai masu yawa da dabbobi, da iyalai masu yawa. Filistiyawa suka yi kishinsa.
\s5
\v 15 To dukkan rijiyoyin da barorin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin Ibrahim mahaifinsa, Filistiyawa suka cike su da ƙasa.
\v 16 Abimelek yace da Ishaku, "Ka tafi ka ba mu wuri, domin ka fi mu ƙarfi."
\v 17 Sai Ishaku ya bar garin ya koma Kwarin Gerar ya zauna a can.
\s5
\v 18 Haka kuma Ishaku ya tone rijiyoyi na ruwa waɗanda aka haƙa a kwanakin Ibrahim mahaifinsa. Filistiyawa suka ɓata su bayan mutuwar Ibrahim. Ishaku ya kira rijiyoyin da ainihin sunan da mahaifinsa ya kira su.
\s5
\v 19 Bayan barorin Ishaku sun yi tono a cikin kwarin, sai suka sami wata rijiya mai fitar da ruwa a can.
\v 20 Makiyayan Gerar suka yi faɗa da makiyayan Ishaku suka ce, "Wannan ruwan namu ne." Domin haka Ishaku ya kira rijiyar "Esek" wato rikici, saboda sun yi rikici da shi.
\s5
\v 21 Sai suka sake haƙa wata rijiyar, sai suka sake yin rikici akan itama wannan rijiyar, sai ya ba ta suna "Sitnah."
\v 22 Sai ya bar wurin ya ƙara haƙa wata rijiyar, amma ba su yi rikici kan wannan ba. Don haka ya kira ta Rehobot, ya ce, "Yanzu Yahweh ya samar mana masauki, kuma za mu wadata a cikin ƙasar."
\s5
\v 23 Sai Ishaku ya haura daga can zuwa Bayersheba.
\v 24 Yahweh ya bayyana a gare shi a cikin wannan daren ya ce, "Ni ne Allah na Ibrahim mahaifinka. Kada ka ji tsoro, domin ina tare da kai zan kuma albarkace ka in ruɓanɓanya zuriyarka, saboda barana Ibrahim."
\v 25 Ishaku ya gina bagadi ya yi kira bisa sunan Yahweh. A can ya kafa rumfarsa, barorinsa kuma suka haƙa rijiya.
\s5
\v 26 Sai Abimelek ya je wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzat, abokinsa, da Fikol, jagoran sojojinsa.
\v 27 Ishaku yace da su, "Meyasa kuke zuwa gare ni, tun da yake kun ƙi ni, kun kuma kore ni daga wurinku?"
\s5
\v 28 Sai suka ce, "Zahiri mun ga Yahweh na tare da kai. Shi yasa muka ga ya fi kyau a sami rantsuwa tsakaninmu, i, tsakaninmu da kai, To in ka yarda sai mu yi yarjejeniya da kai,
\v 29 cewa ba zaka wahalshe mu ba, kamar yadda muka yi maka muka sallame ka cikin lumana, hakika Yahweh ya albarkace ka."
\s5
\v 30 Sai ishaku ya shirya liyafa domin su, suka ci suka sha.
\v 31 Suka tashi da asuba suka yi rantsuwar alƙawari da juna. Daga nan Ishaku ya sallame su, suka bar shi cikin salama.
\s5
\v 32 A wannan ranar dai barorin Ishaku suka zo suka ba shi labari game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, Mun sami ruwa."
\v 33 Ya kira rijiyar da suna Shiba, shi ya sa a ke kiran wannan birni da suna Bayersheba har ya zuwa yau.
\s5
\v 34 Da Isuwa ya kai shekaru arba'in, ya auri mata mai suna Yudit 'yar Be'eri Bahitte, da kuma Basemat "yar Elon Bahitte.
\v 35 Suka kawo baƙinciki ga Ishaku da Rebeka.
\s5
\c 27
\cl Sura 27
\p
\v 1 Da Ishaku ya tsufa har ta kai ga ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa, babban ɗansa, ya ce da shi, "Ɗana." Ya ce da shi "Ga ni."
\v 2 Ya ce, "Gashi yanzu, na tsufa. Ban kuma san ranar mutuwata ba.
\s5
\v 3 Domin haka, ka ɗauki kwarinka da bakanka da makamanka, ka je daji ka yiwo mini farauta.
\v 4 Ka yi mani dage-dage, irin wanda nake ƙauna, ka kawo shi gare ni domin in ci in albarkace ka kafin in mutu."
\s5
\v 5 Sai Rebeka ta ji lokacin da Ishaku ke magana da Isuwa ɗansa. Isuwa ya tafi daji domin ya yiwo farauta ya kawo.
\v 6 Sai Rebeka ta yi magana da Yakubu ɗanta ta ce, "Duba, na ji mahaifinka ya yi magana da Isuwa ɗan'uwanka. Ya ce,
\v 7 'Ka farauto mani nama ka shirya mani dage-dage domin in ci in albarkace ka a gaban Yahweh kafin mutuwata.'
\s5
\v 8 Yanzu fa ɗana, ka yi biyayya da muryata kamar yadda zan umarce ka.
\v 9 Ka je garke, ka kawo mini "yan awaki guda biyu; zan kuma shirya dage-dage mai daɗi da su domin mahaifinka, kamar yadda yake ƙauna.
\v 10 Zaka kai shi wurin mahaifinka, domin ya ci, ya albarkace ka kafin ya mutu."
\s5
\v 11 Yakubu yace da Rebeka mahaifiyarsa, "Gashi, Isuwa ɗan'uwana gargasa ne, ni kuma sulɓi ne.
\v 12 In mahaifina ya taɓa ni, na kuma zama mayaudari a gare shi. Zan jawo wa kaina la'ana ba albarka ba."
\s5
\v 13 Mahaifiyarsa ta ce da shi, "Ɗana, bari duk wata la'ana ta auko mani. kai dai ka yi biyayya da muryata, ka je ka kawo su wurina."
\v 14 Sai Yakubu ya tafi ya samo 'yan awaki guda biyu ya kawo su ga mahafiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya dage-dage, kamar yadda mahaifinsa ke ƙauna.
\s5
\v 15 Sai Rebeka ta ɗauki tufafin Isuwa babban ɗanta, mafi kyau, wanda ke tare da ita a gida, sai ta sa wa Yakubu, ƙaramin ɗanta.
\v 16 Sai ta sa fatar 'yan awaki a hannunsa da kuma tattausan sashen wuyansa.
\v 17 Sai ta sa dage-dagen mai daɗi da gurasar da ta shirya a hannun ɗanta Yakubu.
\s5
\v 18 Sai Yakubu ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, "Mahaifina." Ya ce,"Ga ni nan; Wane ne kai ɗana?"
\v 19 Yakubu yace da mahaifinsa, "Ni ne Isuwa ɗanka na fari; Na yi kamar yadda ka ce da ni. Yanzu sai ka tashi ka zauna ka ci ɗan dage-dagen, domin ka albarkace ni."
\s5
\v 20 Ishaku yace da ɗansa, "Ɗana yaya aka yi ka samo shi da sauri haka?" Ya ce, "Domin Yahweh Allanka ya kawo su wurina".
\v 21 Ishaku yace da Yakubu, "Ɗana ka matso kusa da ni, domin in taɓa ka, domin in san ko kai ɗana ne."
\s5
\v 22 Yakubu ya matsa ga Ishaku mahaifinsa, Ishaku kuma ya taɓa shi ya ce, "Muyar kamar ta Yakubu ce, amma jikin na
\v 23 Isuwa ne." Ishaku bai iya gane shi ba, domin hannuwansa gargasa ne kamar na hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, domin haka Ishaku ya albarka ce shi.
\s5
\v 24 Ya ce "Kai ne ɗana Isuwa kuwa?" Ya amsa "Ni ne."
\v 25 Ishaku yace, "Kawo abincin wurina, zan ci in kuma albarkace ka. Yakubu ya kawo abincin gare shi. Ishaku ya ci, Yakubu kuma ya kawo masa ruwan inabi, ya kuwa sha.
\s5
\v 26 Sai babansa Ishaku yace da shi, "Ɗana ka zo nan kusa ka sumbace ni."
\v 27 Yakubu ya matso kusa ya sumbace shi' ya sunsuni ƙamshin suturarsa ya albarkace shi. Ya ce, "Duba, ƙamshin ɗana yana kama da ƙamshin ganyayyakin da Yahweh ya sa wa albarka.
\s5
\v 28 Allah ya baka rabo na raɓar sama, rabo na sashin ƙasa mafi dausayi, ya baka hatsi da ruwan Inabi mai yawa.
\s5
\v 29 Mutane da al'ummai kuma su rusuna maka. Ka zama shugaban 'yan'uwanka maza, 'ya'yan mahaifiyarka maza kuma su rusuna maka. Duk kuma wanda ya la'ance ka ya zama la'annanne, duk wanda kuma ya albarkace ka ya zama mai albarka."
\s5
\v 30 Ishaku na gama sa wa Yakubu albarka kenan, bayan ya fita daga wurin mahaifinsa Ishaku, sai ga Isuwa ɗan'uwansa ya shigo daga wurin farautarsa.
\v 31 Shi ma ya shirya dage-dagen, abinci mai daɗi ya kawo shi wurin mahaifinsa. Ya ce da mahaifinsa, "Mahaifina, ka tashi ka ci irin dage-dagen ɗanka, domin ka albarkace ni."
\s5
\v 32 Ishaku mahaifinsa ya ce da shi, "Kai wane ne?" Ya ce, "Ni ne ɗan farinka, Isuwa.
\v 33 Ishaku ya gigice sosai ya ce, "Wane ne ya yiwo farauta ya kawo mani dage-dage? Na ci a gabanin zuwanka, na kuma albarkace shi. Hakika, zai zama da albarka."
\s5
\v 34 Bayan Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, ya yi kuka da baƙinciki matuƙa, ya ce da mahaifinsa, "Ni ma ka albarkace ni mana, mahaifina."
\v 35 Ishaku yace, "Ɗan'uwanka ya zo cikin yaudara ya karɓe albarkarka."
\s5
\v 36 Isuwa yace, "Ashe ba haka ta sa aka ba shi suna Yakubu ba? Domin ya zambace ni sau biyu. Ya karɓe matsayina na ɗan fãri, kuma duba yanzu ya karɓe albarkata." Daga nan ya ce, "Ba ka rage wata albarka domina ba?"
\v 37 Ishaku ya amsa ya ce da Isuwa, "Duba, na maishe shi ya zama shugabanka, kuma na ba shi dukkan 'yan'uwansa maza su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Me kuma zan yi maka, ɗana?"
\s5
\v 38 Isuwa yace da mahaifinsa, "Ko albarka ɗaya ba ka rage mani ba mahaifina? Ka albarkace ni nima mahaifina." Isuwa yayi kuka da ƙarfi.
\s5
\v 39 Ishaku mahaifinsa ya amsa masa cewa, "Duba, wurin da zaka zauna zai zama da nisa daga wadatar duniya, nesa kuma da raɓar sararin sama.
\v 40 Ta wurin takobinka zaka rayu, kuma zaka bautawa ɗan'uwanka. Amma lokacin da kayi tayarwa, zaka kawar da karkiyarsa daga wuyanka."
\s5
\v 41 Isuwa ya ƙi Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya ba shi. Isuwa yace a cikin zuciyarsa, "Kwanakin makokin mahaifina sun kusa wucewa, bayan wannan zan kashe ɗan'uwana Yakubu."
\v 42 Sai aka faɗa wa Rebeka kalmomin da babban ɗanta ya faɗa. Domin haka ta aika a kira Yakubu ƙaramin ɗanta ta ce da shi, "'Duba, ɗan'uwanka na tunanin yadda zai kashe ka.
\s5
\v 43 Saboda haka, ɗana, yanzu sai ka yi biyayya da muryata, ka gudu wurin Laban ɗan'uwana a Haran.
\v 44 Ka zauna tare da shi na ɗan lokaci,
\v 45 har sai fushin ɗan'uwanka ya huce daga gare ka, ya kuma manta abin da kayi masa. Daga nan zan aika a dawo da kai daga can. Don me zan rasa ku dukka a rana ɗaya?
\s5
\v 46 Rebeka ta ce, "Na gaji da rayuwa saboda 'ya'yan Het. In Yakubu ya auri 'yanmata irin waɗannan mataye, waɗansu daga cikin 'yan matan ƙasar, wanne abu ne mai kyau zai zama a rayuwata?"
\s5
\c 28
\cl Sura 28
\p
\v 1 Ishaku ya kira Yakubu, ya albarkace shi, ya kuma dokace shi, "Tilas ba zaka ɗauki mata daga cikin matan Kan'aniyawa ba.
\v 2 Ka tashi, ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan Betuwel mahaifin mahaifiyarka, ka kuma ɗauki mata daga can, ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Laban, ɗan'uwan mahaifiyarka.
\s5
\v 3 Bari Allah mai iko dukka ya albarkace ka, yasa kayi 'ya'ya, ka kuma ruɓanɓanya, yadda zaka zama mutane tururu.
\v 4 Bari ya bada albarkar Ibrahim, gare ka, da zuriyarka a bayanka, domin ka iya gãdon ƙasa inda ka ke zama, wadda Allah ya ba Ibrahim."
\s5
\v 5 Sai Ishaku ya sallami Yakubu, Yakubu ya tafi Faddan Aram, zuwa ga Laban ɗan Betuwel Ba'aramiye, ɗan'uwan Rebeka, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.
\s5
\v 6 Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya albarkaci Yakubu ya kuma sallame shi zuwa Faddan Aram, ya ɗauko mata daga can. Ya kuma ga cewa Ishaku ya albarkace shi ya kuma dokace shi, cewa, "Tilas ba za ka ɗauki mata daga matan Kan'aniyawa ba."
\v 7 Isuwa kuma ya ga cewa Yakubu ya yi biyayya da mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya kuma tafi Faddan Aram.
\s5
\v 8 Isuwa ya ga cewa matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba.
\v 9 Sai ya tafi wurin Isma'ila, ya ɗauko, baya ga matan da yake da su, Mahalat ɗiyar Isma'ila, ɗan Ibrahim, 'yar'uwar Nebayot, ta zama matarsa.
\s5
\v 10 Yakubu ya bar Bayesheba ya tafi zuwa Haran.
\v 11 Ya iso daidai wani wuri ya kuma tsaya wurin dukkan dare, saboda rana ta fãɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun wurin, ya sa ƙarƙashin kansa, ya kuma kwanta a wurin domin ya yi barci.
\s5
\v 12 Ya yi mafarki ya kuma ga hawan bene an kafa bisa duniya. Ƙololuwarsa ta kai cikin sama kuma mala'ikun Allah suna hawa suna sauka a kansa.
\v 13 Duba, Yahweh ya tsaya a bisansa ya kuma ce, "Ni ne Yahweh, Allah na Ibrahim mahaifinka, da Allah na Ishaku. Ƙasar inda kake kwance, zan bayar gare ka ga kuma zuriyarka.
\s5
\v 14 Zuriyarka zasu zama kamar turɓayar ƙasa, kuma zaka bazu nesa zuwa yamma, zuwa gabas, zuwa arewa, zuwa kuma kudu. Ta wurin ka da ta wurin zuriyarka dukkan iyalan duniya zasu yi albarka.
\v 15 Duba, Ina tare da kai, kuma zan kiyaye ka ko'ina ka tafi. Zan sake kawo ka cikin wannan ƙasa; gama ba zan barka ba. Zan yi dukkan abin dana yi alƙawari a gare ka."
\s5
\v 16 Yakubu ya tashi daga barci, ya kuma ce, "Tabbas Yahweh yana wannan wurin, kuma ban sani ba."
\v 17 Ya ji tsoro ya kuma ce, "Wurin nan mai ban tsoro ne! Wannan ba wani wuri ba ne wanda ya wuce gidan Allah. Wannan ƙofar sama ce."
\s5
\v 18 Yakubu ya tashi da sassafe ya kuma ɗauki dutsen da ya sa ƙarƙashin kansa. Ya kafa shi a matsayin ginshiƙi ya kuma zuba mai a kansa.
\v 19 Ya kira sunan wannan wuri Betel, amma asalin sunan wannan birni Luz ne.
\s5
\v 20 Yakubu ya yi wa'adi, cewa, "Idan Allah zai kasance tare da ni ya kuma kiyaye ni a cikin wannan hanya dana ke tafiya, ya kuma ba ni gurasa in ci, da suturar sanya wa,
\v 21 yadda zan dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, daga nan Yahweh zai zama Allah na.
\v 22 Daga nan wannan dutse dana kafa a matsayin ginshiƙi zai zama tsarkakakken dutse. Daga kowanne abin da ka bani, babu shakka zan bayar da kashi ɗaya cikin goma a gare ka."
\s5
\c 29
\cl Sura 29
\p
\v 1 Daga nan Yakubu ya kama tafiyarsa ya zo cikin ƙasar mutanen gabas.
\v 2 Yayin da ya duba, sai ya ga rijiya a saura, kuma, duba, garkunan tumaki uku na kwance a gefen ta. Domin daga wannan rijiyar za su yi wa garkunan ban ruwa, kuma dutsen dake bakin rijiyar ƙato ne.
\v 3 Sa'ad da dukkan garkunan suka taru a nan, makiyayan zasu gangarar da dutsen daga bakin rijiyar su kuma yi wa tumakin ban ruwa, sai kuma su mai da dutsen bakin rijiyar, daidai wurinsa.
\s5
\v 4 Yakubu yace masu, "Yan'uwana, daga ina ku ke?" Suka maida amsa, "Daga Haran muke."
\v 5 Ya ce masu, "Kun san Laban ɗan Nahor?" Suka ce, "Mun san shi."
\v 6 Ya ce masu, "Yana nan lafiya?" Suka ce, "Yana nan lafiya, kuma, duba can, Rahila ɗiyarsa na zuwa tare da tumaki."
\s5
\v 7 Yakubu yace, "Duba, yanzu rana tsaka ne. Lokaci bai yi ba da za a tattara garkuna tare. Kuyi wa tumakin ban ruwa daga nan ku tafi ku kai su kiwo."
\v 8 Suka ce, "Ba za mu iya yi masu banruwa ba har sai dukkan garkunan sun tattaru tare. Daga nan mazan zasu gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, sai kuma mu yi wa tumakin banruwa."
\s5
\v 9 Yayin da Yakubu ke magana tare da su, Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, domin ita ke kiwon su.
\v 10 Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, ɗiyar Laban, ɗan'uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, ɗan'uwan mahaifiyarsa, Yakubu ya zo kusa, ya gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma yi wa garken Laban ɗan'uwan mahaifiyarsa banruwa.
\s5
\v 11 Yakubu ya sumbaci Rahila ya yi kuka da ƙarfi.
\v 12 Yakubu ya gaya wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne, kuma cewa shi ɗan Rebeka ne. Daga nan ta ruga ta gaya wa mahaifinta.
\s5
\v 13 Sa'ad da Laban ya ji labarin Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, ya ruga domin ya same shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kuma kawo shi cikin gidansa. Yakubu ya gaya wa Laban dukkan waɗannan abubuwa.
\v 14 Laban yace masa, "Tabbas kai ƙashina ne da namana." Daga nan Yakubu ya zauna tare da shi har wajen wata ɗaya.
\s5
\v 15 Daga nan Laban ya cewa Yakubu, "Kã bauta mani a banza saboda kai ɗan dangina ne? Gaya mani, mene ne zai zama ladanka?"
\v 16 Yanzu dai Laban na da 'ya'ya mata biyu. Sunan babbar Liya, sunan ƙaramar kuma Rahila.
\v 17 Idanun Liya tausasa ne amma Rahila na da kyakkyawar siffa.
\v 18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, "Zan bauta maka shekaru bakwai domin Rahila, ƙaramar ɗiyarka."
\s5
\v 19 Laban yace, "Gwamma in bayar da ita a gare ka, maimakon in bayar da ita ga wani mutumin. Ka yi zamanka da ni."
\v 20 Sai Yakubu ya yi bauta shekaru bakwai domin Rahila; sai kuma suka yi masa kamar kwanaki kaɗan, domin ƙaunar da yake yi mata.
\s5
\v 21 Daga nan Yakubu ya cewa Laban, "Ka bani matata, domin kwanakina sun kammalu - domin in aure ta!"
\v 22 Sai Laban ya tattara dukkan mutanen wurin ya kuma yi biki.
\s5
\v 23 Da maraice ya yi, Laban ya ɗauki ɗiyarsa Liya ya kuma kawo wa Yakubu, wanda ya kwana da ita.
\v 24 Laban ya ɗauki baiwarsa Zilfa ya ba ɗiyarsa Liya, ta zama baiwarta.
\v 25 Da safe, da ya duba, sai ya ga ashe Liya ce! Yakubu ya cewa Laban, "Mene ne wannan ka yi mani? Ba domin Rahila na bauta maka ba? To me ya sa ka yaudare ni?"
\s5
\v 26 Laban yace, "Ba al'adarmu ba ce mu bayar da ƙaramar ɗiya kafin ta fãrin.
\v 27 Ka kammala satin amarcin wannan ɗiyar, za mu kuma baka ɗayar a sakamakon sake bauta mani na wasu shekarun bakwai."
\s5
\v 28 Yakubu ya yi haka, ya kammala satin Liya. Daga nan Laban ya ba shi Rahila ɗiyarsa a matsayin matarsa.
\v 29 Laban kuma ya bayar da Bilha ga ɗiyarsa Rahila, ta zama baiwarta.
\v 30 Haka kuma Yakubu ya kwana da Rahila, amma ya ƙaunaci Rahila fiye da Liya. Sai Yakubu ya bauta wa Laban na wasu shekaru bakwai.
\s5
\v 31 Yahweh ya ga cewa ba a ƙaunar Liya, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ba ta da ɗa.
\v 32 Liya ta ɗauki ciki ta haifi ɗa, ta kuma kira sunansa Ruben. Domin ta ce, "Saboda Yahweh ya dubi azabata; babu shakka yanzu mijina zai ƙaunace ni."
\s5
\v 33 Daga nan ta sake ɗaukan ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Saboda Yahweh ya ji cewa ba a ƙauna ta, saboda haka ya bani wannan ɗan kuma," ta kuma kira sunansa Simiyon.
\v 34 Daga nan ta sake ɗaukan ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Yanzu a wannan lokacin mijina zai haɗe da ni, saboda na haifa masa 'ya'ya maza uku." Saboda haka a ka kira sunansa Lebi.
\s5
\v 35 Ta sake ɗaukar ciki ta kuma haifar ɗa. Ta ce, "Wannan lokacin zan yabi Yahweh." Saboda haka ta kira sunansa Yahuda; Daga nan ta tsaya da haihuwar 'ya'ya.
\s5
\c 30
\cl Sura 30
\p
\v 1 Da Rahila ta ga cewa ba ta haifa wa Yakubu 'ya'ya ba, sai Rahila ta ji kishin 'yar'uwarta. Ta ce wa Yakubu, "Ba ni 'ya'ya, ko in mutu."
\v 2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna gãba da Rahila. Ya ce, "Ina a madadin Allah ne, wanda ya hana ki samun 'ya'ya?"
\s5
\v 3 Ta ce, "Duba, wannan baiwata ce Bilha. Ka kwana da ita, saboda ta haifi 'ya'ya bisa gwiwoyina, kuma in sami 'ya'ya ta wurin ta."
\v 4 Sai ta bayar da baiwarta Bilha a matsayin mata, Yakubu kuma ya kwana da ita.
\s5
\v 5 Bilha ta ɗauki ciki ta haifa wa Yakubu ɗa.
\v 6 Daga nan Rahila ta ce, "Allah ya baratar da ni, ya kuma ji muryata ya kuma bani ɗa." Domin wannan dalili ta kira sunansa Dan.
\s5
\v 7 Bilha, baiwar Rahila, ta sake ɗaukar ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.
\v 8 Rahila ta ce, "Da kokowa mai girma na yi kokowa da 'yar'uwata na kuma yi nasara." Ta kira sunansa Naftali.
\s5
\v 9 Sa'ad da Liya ta ga cewa ta tsaya da haihuwar 'ya'ya, ta ɗauki Zilfa, baiwarta, ta bayar da ita ga Yakubu a matsayin mata.
\v 10 Zilfa, baiwar Liya, ta haifa wa Yakubu ɗa.
\v 11 Liya ta ce, "Wannan rabo ne!" Sai ta kira sunansa Gad.
\s5
\v 12 Daga nan Zilfa, baiwar Liya, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.
\v 13 Liya ta ce, "Na yi murna! domin 'ya'ya mata zasu kira ni murna." Sai ta kira sunansa Asha.
\s5
\v 14 Ruben ya fita a lokacin yankan alkama ya kuma samo 'ya'yan itacen manta'uwa daga saura. Ya kuma kawo su wurin mahaifiyarsa Liya. Daga nan Rahila ta ce wa Liya, "Ki ba ni daga cikin 'ya'yan itacen manta'uwa na ɗanki."
\v 15 Liya ta ce mata, "Ƙaramin al'amari ne a gare ki, cewa kin ɗauke mani miji? Ki na so yanzu ki ɗauke 'ya'yan manta'uwa na ɗana, kuma?" Rahila ta ce, "To zai kwana dake a daren nan, a matsayin musanya domin 'ya'yan manta uwa na ɗanki."
\s5
\v 16 Yakubu ya dawo daga gona da yamma. Liya ta fita ta same shi ta ce, "Tilas ka kwana da ni a daren nan, domin nayi hayar ka da 'ya'yan manta'uwa na ɗana." Sai Yakubu ya kwana da Liya a wannan daren.
\v 17 Allah ya saurari Liya, ta kuma ɗauki ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.
\v 18 Liya ta ce, "Allah ya bani ladana, saboda na bayar da baiwata ga mijina." Sai ta kira sunansa Issaka.
\s5
\v 19 Liya ta sake ɗaukan ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na shida.
\v 20 Liya ta ce, "Allah ya bani kyauta mai kyau. Yanzu mijina zai girmama ni, saboda na haifa masa 'ya'ya maza shida." Ta kira sunansa Zebulun.
\v 21 Daga baya ta haifi ɗiya ta kuma kira sunanta Dina.
\s5
\v 22 Allah ya tuna da Rahila ya kuma saurare ta. Ya sa ta ɗauki ciki.
\v 23 Ta ɗauki ciki ta haifi ɗa. Ta ce, "Allah ya ɗauke kunyata."
\v 24 Ta kira sunansa Yosef, cewa, "Yahweh ya ƙara mani wani ɗan."
\s5
\v 25 Bayan da Rahila ta haifi Yosef, sai Yakubu yace wa Laban, "Ka sallame ni saboda in tafi nawa gidan da ƙasata.
\v 26 Ka bani matayena da 'ya'yana waɗanda domin su na yi maka bauta, bari kuma in tafi, gama ka san hidimar dana yi maka."
\s5
\v 27 Laban yace masa, "Idan yanzu na sami tagomashi a gaban ka, ka jira, saboda ta wurin amfani da sihiri na gane cewa Yahweh ya albarkace ni saboda kai."
\v 28 Daga nan ya ce, "Ka faɗi ladanka, zan kuma biya su."
\s5
\v 29 Yakubu yace masa, "Ka san dai yadda na bauta maka, da yadda dabbobinka suka kasance tare da ni.
\v 30 Domin 'yan kaɗan kake da su kafin in zo, kuma sun ƙaru a yalwace. Yahweh ya albarkace ka a duk inda na yi aiki. Yanzu yaushe zan samar wa nawa gidan shi ma?"
\s5
\v 31 Sai Laban yace, "Me zan biya ka?" Yakubu yace, "Ba zaka bani komai ba. Idan zaka yi wannan domina, zan sake ciyar da dabbobinka in kiwata su kuma.
\v 32 Bari in ratsa cikin dukkan dabbobinka a yau, zan ware daga cikin su duk wasu tumaki dabbare-dabbare da masu ɗigo, da waɗanda ke baƙaƙe daga cikin tumakin, da masu ɗigo da kyalloli daga cikin awakin. Waɗannan ne zasu zama ladana.
\s5
\v 33 Amincina zai yi shaida game da ni daga bisani, sa'ad da zaka zo ka duba ladana. Duk wadda ba kyalla ba ce ko mai ɗigo daga cikin awaki, da baƙa daga cikin tumaki, duk wadda a ka samu a wurina, a ɗauke shi a matsayin sata."
\v 34 Laban yace, "Na yarda. Bari ya kasance bisa ga maganarka."
\s5
\v 35 A wannan rana Laban ya ware dukkan bunsurai masu zãne da masu ɗigo, da dukkan awaki kyalloli da masu ɗigo, duk wata mai fari a jikinta, da dukkan baƙaƙe daga cikin tumaki, ya kuma bayar da su cikin hannun 'ya'yansa.
\v 36 Laban kuma ya sa tafiya ta kwana uku tsakaninsa da Yakubu. Sai Yakubu ya ci gaba da kiwon sauran dabbobin Laban.
\s5
\v 37 Sai Yakubu ya ɗauko ɗanyun tsabgun auduga, da rassan itacen almond da rassan itacen durumi, ya kuma fera fararen zãne a kan su, ya sanya fararen itatuwan dake cikin ƙiraren su bayyana.
\v 38 Daga nan ya jera ƙiraren da ya feffere a gaban dabbobin, a gaban kwamamen ruwa in da suke zuwa su sha. Suna ɗaukar ciki sa'ad da suka zo shan ruwa.
\s5
\v 39 Dabbobin suka yi ta barbara a gaban ƙiraren; dabbobin kuma suka yi ta haihuwar 'ya'yai masu zãne, da kyalloli, da masu ɗigo.
\v 40 Yakubu ya ware waɗannan 'yan raguna, amma ya sanya sauran su fuskanci dabbobin masu zãne da dukkan baƙaƙen tumaki a garken Laban. Daga nan sai ya ware nasa dabbobin domin kansa kaɗai ba ya kuma haɗa su tare da dabbobin Laban ba.
\s5
\v 41 A duk sa'ad da ƙarfafan tumakin ke barbara, sai Yakubu ya shimfiɗa ƙiraren nan a cikin kwamamen ruwan nan a gaban idanun dabbobin, saboda su ɗauki ciki a tsakiyar ƙiraren.
\v 42 Amma idan dabbobi marasa ƙarfi daga cikin garken suka zo, ba ya sanya ƙiraren a gabansu. Sai ya zama dabbobin marasa ƙarfi na Laban ne, ƙarfafan kuma na Yakubu ne.
\s5
\v 43 Mutumin ya zama wadatacce sosai. Yana da manyan garkuna, bayi mata da bayi maza, da raƙuma da jakuna.
\s5
\c 31
\cl Sura 31
\p
\v 1 Yanzu Yakubu ya ji maganganun 'ya'yan Laban maza, cewa sun ce, "Yakubu ya ɗauke dukkan abin dake na mahaifinmu, kuma daga mallakar mahaifinmu ne ya samo dukkan wannan dukiyar."
\v 2 Yakubu ya kalli yanayin fuskar Laban. Ya ga cewa halinsa zuwa gare shi ya canza.
\v 3 Daga nan Yahweh ya cewa Yakubu, "Ka koma ƙasar ubanninka da danginka, zan kuma kasance tare da kai."
\s5
\v 4 Yakubu ya aika a ka kira Rahila da Liya zuwa saura a garkensa
\v 5 ya kuma ce masu, "Na ga halin mahaifinku zuwa gare ni ya canza, amma Allah na mahaifina yana tare da ni.
\v 6 Kun san cewa da dukkan karfina ne na bautawa mahaifinku.
\s5
\v 7 Mahaifinku ya ruɗe ni ya canza ladana sau goma, amma Allah bai ba shi damar cutar da ni ba.
\v 8 Idan ya ce, "Dabbobin kyalloli zasu zama ladanka,' daga nan dukkan garken suka haifi jarirai kyalloli. Idan ya ce, "Ma su zãne zasu zama ladanka,' daga nan dukkan garken suka haifi 'ya'ya masu zãne.
\v 9 Ta wannan hanya Allah ya ɗauke dabbobin mahaifinku ya kuma bayar da su a gare ni.
\s5
\v 10 Sau ɗaya a lokacin yin barbara, na gani a mafarki cewa bunsuran na barbara da dabbobin. Bunsuran masu zãne ne, da kyalloli, da masu ɗigo.
\v 11 Mala'ikan Allah yace da ni a cikin mafarkin, 'Yakubu.' Na ce, 'Ga ni nan.'
\s5
\v 12 Ya ce, 'Ka ɗaga idanunka ka ga dukkan bunsuran dake barbara da dabbobin. Masu zãne ne, da kyalloli, da masu ɗigo, gama na ga dukkan abin da Laban yake yi maka.
\v 13 Ni ne Allah na Betel, in da ka yi wa ginshiƙi shafewa, in da ka ɗaukar mani wa'adi. Yanzu ka tashi ka bar wannan ƙasar ka kuma koma ƙasar haihuwarka."'
\s5
\v 14 Rahila da Liya suka amsa suka ce masa, "Akwai kuma wani rabo ko gãdo dominmu a gidan mahaifinmu?
\v 15 Ba kamar bãre ya maida mu ba? Gama ya sayar da mu kuma ya lanƙwame kuɗinmu gabaɗaya.
\v 16 Domin dukkan arzikin da Allah ya ɗauke daga wurin mahaifinmu yanzu na mu ne da 'ya'yanmu. To yanzu duk abin da Allah yace maka, sai ka yi."
\s5
\v 17 Daga nan Yakubu ya tashi ya ɗora 'ya'yansa da matayensa bisa raƙumma.
\v 18 Ya kora dukkan dabbobinsa gaba da shi, tare da dukkan kaddarorinsa, har da dabbobin da ya samu a Faddan Aram. Daga nan ya kama tafiya zuwa wurin mahaifinsa Ishaku a cikin ƙasar Kan'ana.
\s5
\v 19 Sa'ad da Laban ya tafi yi wa tumakinsa sausaya, Rahila ta ɗauke allolin gidan mahaifinta.
\v 20 Yakubu shi ma ya ruɗi Laban Ba'aramiye, ta wurin ƙin gaya masa cewa zai tashi.
\v 21 Sai ya tsere da dukkan abin da yake da shi, nan da nan kuma ya wuce ƙetaren Kogi, ya kuma doshi zuwa ƙasar tudu ta Giliyad.
\s5
\v 22 A rana ta uku a ka gaya wa Laban cewa Yakubu ya gudu.
\v 23 Sai ya ɗauki danginsa ya kuma bi shi na tsawon tafiyar kwana bakwai. Ya sha kansa a ƙasar tudu ta Giliyad.
\s5
\v 24 Sai Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye a cikin mafarki da dare ya kuma ce masa, "Ka yi hankali kada kayi magana da Yakubu mai kyau ko marar kyau."
\v 25 Laban ya sha kan Yakubu. Yanzu Yakubu ya kafa rumfarsa a ƙasar tudu. Laban shi ma ya kafa sansani tare da danginsa a ƙasar tudu ta Giliyad.
\s5
\v 26 Laban ya cewa Yakubu, "Mene ne ka yi, da ka ruɗe ni ka kuma ɗauke 'ya'yana mata kamar kamammun yaƙi?
\v 27 Meyasa ka tsere a asirce ka kuma yi mani dabara ba ka kuma gaya mani ba? Da na sallame ka da biki da waƙe-waƙe, tare da tambari da garayu.
\v 28 Ba ka bar ni na yi sumbar sallama ga jikokina da 'ya'yana ba. Yanzu ka aikata wawanci.
\s5
\v 29 A cikin ikona ne in cutar da kai, amma Allah na mahaifinka ya yi magana da ni a daren da ya wuce ya ce, 'Ka yi hankali kada ka yi magana da Yakubu mai kyau ko marar kyau.'
\v 30 Yanzu ka gudu saboda kana marmarin ka koma gidan mahaifinka. Amma me ya sa ka sace allolina?"
\s5
\v 31 Yakubu ya amsa kuma ya ce wa Laban, "Saboda na ji tsoro kuma na yi tunanin za ka karɓe 'ya'yanka mata da ƙarfi daga gare ni sai na gudu a asirce.
\v 32 Duk wanda ya sace allolinka ba zai ci gaba da rayuwa ba. A gaban dangoginmu, ka tantance abin da ke naka tare da ni ka ɗauka." Gama Yakubu bai san cewa Rahila ta sace su ba.
\s5
\v 33 Laban ya shiga cikin rumfar Yakubu, cikin rumfar Liya, da cikin rumfar bayi matan biyu, amma bai gan su ba. Ya fita daga rumfar Liya ya shiga cikin rumfar Rahila.
\s5
\v 34 A she Rahila ta ɗauki allolin gidan, ta sanya su a sirdin raƙumi, ta kuma zauna a bisansu. Laban ya bincike rumfar gabaɗaya, amma bai same su ba.
\v 35 Ta ce wa mahaifinta, "Kada ka ji haushi, shugabana, cewa ba zan iya tashi ba a gabanka, domin ina cikin al'adata." Sai ya bincike amma bai ga allolin gidansa ba.
\s5
\v 36 Yakubu ya husata ya yi gardama da Laban. Ya ce masa, "Mene ne laifi na? Mene ne zunubi na, da ka runtumo ni da zafi?
\v 37 Gama ka duba dukkan mallakata. Me ka samu daga dukkan kayayyakin gidanka? Ka fito da su yanzu a gaban dangoginmu, sai su shar'anta a tsakanin mu biyu.
\s5
\v 38 Shekaru ashirin ina tare da kai. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuma ci wani rago ba daga garkunanka.
\v 39 Abin da bisashe suka yayyage ban kawo maka ba. Maimako, na ɗauki asararsa. Ko yaushe kana sa in biya duk wata dabbar da ta bace, ko wadda a ka sace da rana ko wadda a ka sace da dare.
\v 40 Nan ni ke; da rana zafi na cinye ni, da dare cikin sanyin dusar ƙanƙara; na yi tafiya kuma babu barci.
\s5
\v 41 Waɗannan shekaru ashirin ina cikin gidanka. Na yi maka aiki shekaru sha huɗu domin 'ya'yanka biyu mata, shekaru shida kuma domin dabbobinka. Ka canza ladana sau goma.
\v 42 Idan ba domin Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim, da wanda Ishaku ke tsoro, yana tare da ni ba, tabbas da yanzu ka kore ni hannu wofi. Allah ya dubi tsanantawata da aiki tuƙuru dana yi, ya kuma tsauta ma ka a daren jiya."
\s5
\v 43 Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, "'Ya'yan mata 'ya'yana ne, jikokin jikokina ne, dabbobin kuma dabbobina ne. Dukkan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan iya yi a yau game da waɗannan 'ya'ya matan nawa, ko kuma game da 'ya'yansu da suka haifa?
\v 44 To yanzu, bari mu ɗauki alƙawari, kai da ni, bari kuma ya zama domin shaida tsakanin kai da ni."
\s5
\v 45 Sai Yakubu ya ɗauki dutse ya kuma dasa shi a matsayin ginshiƙi.
\v 46 Yakubu ya cewa danginsa, "Ku tattara duwatsu." Sai suka ɗebo duwatsu suka tattara su.
\v 47 Laban ya kira shi Yagar Saha Duta, amma Yakubu ya kira shi Galid.
\s5
\v 48 Laban yace, "Wannan tarin shaida ne tsakani na da kai a yau." saboda haka a ka kira sunansa Galid.
\v 49 A na kuma kiransa Mizfa, saboda Laban yace, "Bari Yahweh ya duba tsakanin ka da ni, yayin da muka ɓace daga juna.
\v 50 Idan ka wulaƙanta 'ya'yana mata, ko kuma ka auri wasu matan baya ga 'ya'ya na, ko da yake babu wanda ke tare da mu, duba, Allah ne shaida tsakanin ka da ni."
\s5
\v 51 Laban ya cewa Yakubu, "Dubi wannan tarin, ka kuma dubi ginshiƙin, wanda na kafa tsakanin ka da ni.
\v 52 Wannan tarin shaida ne, ginshiƙin kuma shaida ne, cewa ba zan ƙetare gaba da wannan tarin ba zuwa gare ka, kai kuma ba zaka ƙetare gaba da wannan tarin ba da wannan ginshiƙin zuwa gare ni ba, domin cutarwa.
\v 53 Bari Allah na Ibrahim, da allahn Naho, da allolin mahaifinsu, su shar'anta tsakaninmu." Yakubu ya rantse da tsoron mahaifinsa Ishaku.
\s5
\v 54 Yakubu ya miƙa hadaya a bisa tsaunin ya kuma kira danginsa su ci abinci. Suka ci suka zauna tsawon dare a tsaunin.
\v 55 Tun da sassafe Laban ya tashi, ya sumbaci jikokinsa da 'ya'yansa mata ya albarkace su. Daga nan Laban ya tafi ya koma gida.
\s5
\c 32
\cl Sura 32
\p
\v 1 Yakubu shima ya tafi hanyarsa, mala'ikun Allah suka same shi.
\v 2 Sa'ad da Yakubu ya gan su, ya ce, "Wannan sansanin Allah ne." sai ya kira sunan wannan wuri Mahanayim.
\s5
\v 3 Yakubu ya aiki manzanni gaba da shi zuwa ga ɗan'uwansa Isuwa a cikin ƙasar Seyir, a cikin lardin Idom.
\v 4 Ya dokace su, cewa, "Ga abin da zaku cewa shugabana Isuwa: Ga abin da bawanka Yakubu yace: 'Ina zaune tare da Laban, na kuma yi jinkirin dawowata har zuwa yanzu.
\v 5 Ina da shanu, da jakkai, da garkunan tumaki, da awaki, bayi maza da bayi mata. Na aiko da wannan saƙon ga shugabana, domin in sami tagomashi a idanunka."'
\s5
\v 6 Manzannin suka dawo wurin Yakubu suka kuma ce, "Munje wurin ɗan'uwanka Isuwa. Yana zuwa ya same ka, da mutane ɗari huɗu tare da shi."
\v 7 Daga nan Yakubu ya tsorata kuma ya ji haushi. Sai ya raba mutanen dake tare da shi ya yi sansani biyu, da garkunan tumaki, da awaki, da garkunan shanu, da raƙumma.
\v 8 Ya ce, "Idan Isuwa ya zo ga sansani ɗaya ya kawo mana hari, daga nan sansanin da ya rage zasu kuɓuce."
\s5
\v 9 Yakubu yace, "Allah na mahaifina Ibrahim, da Allah na mahaifina Ishaku, Yahweh, wanda ya ce mani, 'Ka koma ga ƙasarka da danginka, zan kuma wadata ka,'
\v 10 Ban cancanci dukkan ayyukanka na alƙawarin aminci ba da dukkan yarda da ka yi domin bawanka ba. Domin da sandana kawai na ƙetare wannan Yodan, yanzu kuma na zama sansanai biyu.
\s5
\v 11 Ina roƙonka ka cece ni daga hannun ɗan'uwana, daga hannun Isuwa, domin ina jin tsoronsa, cewa zai kawo mani hari tare da iyaye matan da 'ya'yan.
\v 12 Amma ka ce, 'Babu shakka zan sa ka wadata. Zan maida zuriyarka kamar rairayin teku, waɗanda ba za a iya lissafawa ba domin yawansu."'
\s5
\v 13 Yakubu ya zauna nan a wannan daren. Ya ɗauki wasu daga cikin abin da yake da su a matsayin kyauta domin Isuwa, ɗan'uwansa:
\v 14 awaki ɗari biyu da bunsuru ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin,
\v 15 raƙuma talatin masu shayarwa da 'ya'yansu, shanu arba'in, bijimai goma, jakkai mata ashirin da jakkai maza goma.
\v 16 Waɗannan ya bayar dasu cikin hannun bayinsa, kowanne garke daban. Ya cewa bayinsa, "Ku tafi gaba da ni, ku sanya tazara tsakanin kowanne garken."
\s5
\v 17 Ya umarci bawa na farko, cewa, "Idan Isuwa ɗan'uwana ya gamu da kai ya tambaye ka, cewa, 'Kai na wane ne? Ina za ka je? Dabbobin wane ne waɗannan da ke gabanka?'
\v 18 Daga nan za ka ce, 'Na bawanka ne Yakubu. Kyauta ce a ka aiko wa shugabana Isuwa. Duba, shi ma yana zuwa bayanmu."'
\s5
\v 19 Yakubu ya sake bada umarnai ga ƙungiya ta biyu, ta uku, da dukkan mutanen da suka bi garkunan. Ya ce, "Zaku faɗi abu iri ɗaya ga Isuwa idan kuka same shi.
\v 20 Tilas kuma ku ce, 'Bawanka Yakubu yana zuwa bayanmu."' Gama ya yi tunani, "Zan tausar da shi da kyaututtukan da nake aikawa da su a gabana. Sai daga baya, sa'ad da zan gan shi, wataƙila zai karɓe ni."
\v 21 Sai kyaututtukan suka tafi gaba da shi. Shi kuwa da kansa ya tsaya a wannan daren a cikin sansani.
\s5
\v 22 Yakubu ya tashi da daddare, ya kuma ɗauki matayensa biyu, da matayensa barori su biyu, da 'ya'yansa maza sha ɗaya. Ya aika da su ƙetaren kududdufin Yabbok.
\v 23 Ta wannan hanyar ya aika da su ƙetaren rafin tare da dukkan mallakarsa.
\s5
\v 24 A ka bar Yakubu shi kaɗai, wani mutum kuwa ya yi kokowa da shi har wayewar gari.
\v 25 Sa'ad da mutumin ya ga cewa ba zai kayar da shi ba, sai ya mazge shi a kwankwaso. Sai kwankwason Yakubu ya goce sa'ad da yake kokowa da shi.
\v 26 Mutumin yace, "Bari in tafi, domin gari yana wayewa." Yakubu yace, "Ba zan bar ka ka tafi ba sai ka albarkace ni."
\s5
\v 27 Mutumin yace masa, "Yayã sunanka?" Yakubu yace, "Yakubu."
\v 28 Mutumin yace, "Ba za a sake kiran sunanka Yakubu ba, amma Isra'ila. Gama ka yi gwagwarmaya tare da Allah tare da mutane ka kuma yi nasara."
\s5
\v 29 Yakubu yace masa, "Ina roƙon ka, ka faɗi mani sunanka." Ya ce, "Meyasa kake tambayar sunana?" Daga nan ya albarkace shi a wurin.
\v 30 Yakubu ya kira sunan wurin Feniyel, gama ya ce, "Na ga Allah fuska da fuska, kuma rayuwata ta kuɓuta."
\s5
\v 31 Rana ta taso bisa Yakubu sa'ad da yake wuce Feniyel. Yana ɗangyashi saboda kwankwasonsa.
\v 32 Shi ya sanya har wa yau mutanen Isra'ila ba su cin jijiyoyin kwankwaso waɗanda suke mahaɗin kwankwaso, saboda mutumin ya yi wa jijiyoyin rauni sa'ad da ya sa kwankwason Yakubu ya goce.
\s5
\c 33
\cl Sura 33
\p
\v 1 Yakubu ya hango, kuma, duba, Isuwa na zuwa, tare da shi kuma mutane ɗari huɗu. Yakubu ya raba 'ya'yan tsakanin Liya, Rahila, da matayen biyu barori.
\v 2 Daga nan ya sanya matayen barori da 'ya'yansu a gaba, a biye kuma Liya da 'ya'yanta, a biye kuma Rahila da Yosef na ƙarshen su dukka.
\v 3 Shi da kansa kuma ya tafi gaba da su. Ya rusuna zuwa ƙasa sau bakwai, har sai da ya zo kusa da ɗan'uwansa.
\s5
\v 4 Isuwa ya rugo ya same shi, ya rungume shi, ya rungumi wuyansa, ya sumbace shi kuma. Daga nan suka yi kuka.
\v 5 Sa'ad da Isuwa ya hanga, sai ya ga matayen da 'ya'yan. Ya ce, "Su wane ne waɗannan mutanen tare da kai?" Yakubu yace, "'Ya'yan da Allah ta wurin alherinsa ya ba bawanka ne."
\s5
\v 6 Daga nan bayi matan suka zo gaba tare da 'ya'yansu, suka kuma rusuna.
\v 7 Sai Liya ita ma da 'ya'yanta suka zo gaba suka rusuna. A ƙarshe kuma Yosef da Rahila suka zo gaba suka rusuna.
\v 8 Isuwa yace, "Mene ne kake nufi da dukkan waɗannan ƙungiyoyi da na tarar?" Yakubu yace, "Domin in sami tagomashi a gaban shugabana ne."
\s5
\v 9 Isuwa yace, "Ina da isassu, ɗan'uwana. Ka ajiye abin da kake da shi domin kanka."
\v 10 Yakubu yace, "A'a, ina roƙon ka, idan na sami tagomashi a idanunka, to ka karɓi kyautata daga hannuna, gama babu shakka, na ga fuskar ka, kuma kamar ganin fuskar Allah ne, kuma ka karɓe ni.
\v 11 Ina roƙon ka ka karɓi kyautata da a ka kawo maka, saboda Allah ya aiwatar da alheri zuwa gare ni, saboda kuma ina da isassu." Haka nan Yakubu ya lallashe shi, Isuwa kuma ya karɓe su.
\s5
\v 12 Daga nan Isuwa yace, "Mu kama hanya. Zan tafi gaba kafin kai."
\v 13 Yakubu yace masa, "Shugabana yasan cewa yaran ƙanana ne, kuma tumakin da garken dabbobin suna renon ƙananansu. Idan a ka kora su da ƙarfi a rana ɗaya, dukkan dabbobin zasu mutu.
\v 14 Ina roƙon ka bari shugabana ya tafi gaba da bawansa. Zan yi tafiya a hankali, bisa ga saurin dabbobin dake a gabana, bisa kuma ga saurin yaran, har sai na zo ga shugabana a Seyir."
\s5
\v 15 Isuwa yace, "Bari in bar maka wasu daga cikin mutane na dake tare da ni." Amma Yakubu yace, "Meyasa zaka yi haka? Bari in sami tagomashi a idanun ubangijina."
\v 16 Sai Isuwa a wannan ranar ya fara tafiya bisa hanyarsa ta komawa Seyir.
\v 17 Yakubu ya tafi Sukkot, ya gina wa kansa gida, ya yi wa dabbobinsa kuma wurin zama. Saboda haka sunan wannan wuri ana kiransa Sukkot.
\s5
\v 18 Sa'ad da Yakubu ya zo daga Faddan Aram, ya isa lafiya a birnin Shekem, wanda ke a cikin ƙasar Kan'ana. Ya kafa sansani kusa da birnin.
\v 19 Daga nan ya sayi filin da ya kafa rumfarsa daga hannun 'ya'yan Hamo, mahaifin Shekem, a kan jimillar azurfa ɗari.
\v 20 A nan ya kafa bagadi, ya kuma kira shi El Elohi Isra'ila.
\s5
\c 34
\cl Sura 34
\p
\v 1 Sai Dinah, ɗiyar Liya wadda ta haifawa Yakubu, ta fita ta tafi wurin 'yanmatan ƙasar.
\v 2 Shekem ɗan Hamo Bahibiye, yariman ƙasar, ya ganta ya kuma cafke ta, ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita.
\v 3 Ya shaƙu da Dinah, ɗiyar Yakubu. Ya ƙaunaci yarinyar, ya kuma yi mata magana mai taushi.
\s5
\v 4 Shekem ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Ka samo mani wannan yarinyar a matsayin mata."
\v 5 Yanzu Yakubu ya ji cewa ya lalata ɗiyarsa Dina. 'Ya'yansa kuma na tare da dabbobinsa a saura, sai Yakubu ya kame bakinsa har sai da su ka zo.
\s5
\v 6 Hamo mahaifin Shekem ya tafi wurin Yakubu domin ya yi magana da shi.
\v 7 'Ya'yan Yakubu suka dawo daga saura sa'ad da suka ji batun al'amarin. Mutanen ransu ya ɓaci. Suka fusata sosai saboda ya kunyatar da Isra'ila ta wurin tilasta kansa bisa ɗiyar Yakubu, domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba.
\s5
\v 8 Hamo ya yi magana da shi, cewa, "Ɗana Shekem na ƙaunar ɗiyarka. Ina roƙon ka. ka bayar da ita a gare shi a matsayin mata.
\v 9 Ku yi auratayya da mu, ku bayar da 'ya'yanku mata a gare mu, ku kuma ɗauki 'ya'yanmu mata domin kanku.
\v 10 Zaku zauna tare da mu, za a buɗe ƙasar kuma a gare ku domin ku zauna ku kuma yi sana'a a ciki, ku kuma mallaki kaddarori."
\s5
\v 11 Shekem yace wa mahaifinta da 'yan'uwanta maza, "Bari in sami tagomashi a idanunku, duk kuma abin da kuka ce mani zan bayar.
\v 12 Ku tambaye ni komai yawan sadakin da kyautar da kuke so, kuma zan bayar da duk abin da kuka ce, amma dai ku bani yarinyar a matsayin mata."
\v 13 'Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da Hamo mahaifinsa tare da zamba, saboda Shekem ya ɓata Dina 'yar'uwarsu.
\s5
\v 14 Suka ce masu, "Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu bayar da 'yar'uwarmu ga duk wani wanda ba shi da kaciya; domin zai zama abin kunya a gare mu.
\v 15 Sai dai a kan wannan matakin kaɗai za mu yarda da ku: Idan zaku zama masu kaciya kamar mu, idan kowanne namiji a cikin ku an yi masa kaciya.
\v 16 Daga nan ne za mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare ku, mu kuma zamu ɗauki 'ya'yanku mata a gare mu, mu kuma zauna daku mu zama mutane ɗaya.
\v 17 Amma idan baku saurare mu ba kuka zama masu kaciya, daga nan zamu ɗauki 'yar'uwarmu kuma za mu tashi."
\s5
\v 18 Maganganunsu suka gamshi Hamo da ɗansa Shekem.
\v 19 Saurayin bai ɓata lokaci ba wurin yin abin da suka ce, saboda yana jin daɗin ɗiyar Yakubu, saboda kuma shi ne taliki mafi daraja a dukkan gidan mahaifinsa.
\s5
\v 20 Hamo da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu suka kuma yi magana da mutanen birninsu, cewa,
\v 21 "Mutanen nan suna zaman salama da mu, bari su zauna cikin ƙasar su kuma yi sana'a a ciki domin, tabbas, ƙasar na da isasshen girma domin su. Bari mu ɗauki 'ya'yansu mata a matsayin matayen aure, bari kuma mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare su.
\s5
\v 22 A wannan matakin kaɗai mutanen za su yarda su zauna da mu kuma mu zama mutane ɗaya. Idan a ka yi wa kowanne namiji a cikin mu kaciya, kamar yarda suke da kaciya.
\v 23 Ba dukkan dabbobinsu da kaddarorinsu - dukkan dabbobinsu zasu zama namu ba? Don haka mu yarda da su, zasu kuma zauna a cikinmu."
\s5
\v 24 Dukkan mutanen birnin suka saurari Hamo da Shekem, ɗansa. Kowanne namiji a ka yi masa kaciya.
\v 25 A rana ta uku, sa'ad da suke cikin zafi tukuna, 'ya'yan Yakubu biyu (Simiyon da Lebi 'yan'uwan Dina), kowannen su ya ɗauki takobinsa suka kuma kai hari ga birnin dake da tabbacin tsaro, suka kuma kashe dukkan mazajen.
\v 26 Suka kashe Hamo da ɗansa Shekem ta kaifin takobi. Suka ɗauke Dina daga gidan Shekem suka yi tafiyar su.
\s5
\v 27 Sauran 'ya'yan Yakubu suka zo wurin gawawwakin suka washe birnin, saboda mutanen sun ɓata 'yar'uwarsu.
\v 28 Suka ɗauki garkunan tumakinsu dana awaki, da garkunan shanunsu, da jakkansu, da duk wani abu dake cikin birnin da gonakin dake kewaye tare da
\v 29 dukkan dukiyarsu. Dukkan 'ya'yayensu da matayensu, suka kame. Suka ma ɗauke kowanne abu dake cikin gidajen.
\s5
\v 30 Yakubu ya cewa Simiyon da Lebi, "Kun kawo mani matsala, domin kun sa in yi ɗoyi ga mazaunan ƙasar, da Kan'aniyawa da Feriziyawa. Ni kima ne a lissafi. Idan suka tattara kansu tare gãba da ni, su kuma kawo ma ni hari, daga nan zan hallaka, ni da gidana."
\v 31 Amma Simiyon da Lebi suka ce, "Ya kamata Shekem ya yi da 'yar'uwarmu kamar karuwa?"
\s5
\c 35
\cl Sura 35
\p
\v 1 Allah ya cewa Yakubu, "Ka tashi, ka nufi sama zuwa Betel, ka kuma zauna a can. Ka ginawa Allah bagadi a wurin, wanda ya bayyana a gare ka sa'ad da kake gujewa Isuwa ɗan'uwanka."
\v 2 Daga nan Yakubu ya cewa gidansa da dukkan waɗanda ke tare da shi, "Ku fitar da bãƙin alloli dake a tsakaninku, ku tsarkake kanku, ku kuma canza suturarku.
\v 3 Daga nan mu bar nan, mu nufi sama zuwa Betel. Zan ginawa Allah bagadi a can, wanda ya amsa mani a ranar ƙuncina, kuma ya kasance tare da ni dukkan inda na nufa."
\s5
\v 4 Sai suka ba Yakubu dukkan bãƙin alloli da suke a hannunsu, da zobban da suke a kunnuwansu. Yakubu ya bizne su a ƙarƙashin rimi dake kusa da Shekem.
\v 5 Yayin da suke tafiya, Allah ya sanya tsoronsu ya fãɗo a bisa biranen dake kewaye da su, domin haka waɗannan mutane ba su runtumi 'ya'yan Yakubu ba.
\s5
\v 6 Sai Yakubu ya iso Luz (wato, Betel), wadda ke cikin ƙasar Kan'ana, shi da dukkan mutanen dake tare da shi.
\v 7 Ya gina bagadi a nan ya kira sunan wurin El Betel, saboda a wurin ne Allah ya bayyana kansa a gare shi, sa'ad da yake gudu daga ɗan'uwansa.
\v 8 Debora, mai kula da Rebeka, ta mutu. A ka bizne ta a gangare daga Betel ƙarƙashin itacen rimi, domin haka ana kiran wurin Allon Bakut.
\s5
\v 9 Sa'ad da Yakubu ya zo daga Faddan Aram, Allah ya sake bayyana a gare shi ya kuma albarkace shi.
\v 10 Allah yace masa, "Sunanka Yakubu, amma ba za a sake kiran sunanka Yakubu ba. Sunanka zai zama Isra'ila ne." Sai Allah ya kira sunansa Isra'ila.
\s5
\v 11 Allah yace masa, "Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka hayayyafa ka kuma ruɓanɓanya. Ƙasa da ƙungiyar ƙasashe zasu fito daga gare ka, kuma sarakuna zasu kasance cikin zuriyarka.
\v 12 Ƙasar dana bayar ga Ibrahim da Ishaku, zan bayar a gare ka. Ga zuriyarka bayanka kuma zan bayar da ƙasar."
\v 13 Allah ya tafi daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.
\s5
\v 14 Yakubu ya kafa ginshiƙi a wurin da Allah ya yi magana da shi, ginshiƙin dutse. Ya zuba baikon sha a bisansa ya kuma zuba mai a kansa.
\v 15 Yakubu ya kira sunan wurin inda Allah ya yi magana da shi, Betel.
\s5
\v 16 Suka kama tafiya daga Betel. Yayin da suke da 'yar tazara daga Efrat, Rahila ta fãra naƙuda. Ta yi naƙuda mai wuya.
\v 17 Yayin da take cikin azabar naƙuda, unguwar zomar ta ce mata, "Kada ki ji tsoro, domin yanzu za ki sami wani ɗan."
\v 18 Yayin da take mutuwa, da numfashinta na mutuwa ta raɗa masa suna Ben-Oni, amma mahaifinsa ya kira shi da suna Benyamin.
\v 19 Rahila ta mutu a ka kuma bizne ta a kan hanyar zuwa Efrat (wato, Betlehem).
\v 20 Yakubu ya kafa ginshiƙi bisa kabarinta. Shi ne shaidar kabarin Rahila har ya zuwa yau.
\s5
\v 21 Isra'ila ya ci gaba da tafiya ya kafa rumfarsa a gaba da hasumiyar tsaron garke.
\v 22 Yayin da Isra'ila ke zaune a wannan ƙasa, Ruben ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra'ila kuma ya ji labari. Yakubu dai na da 'ya'ya maza sha biyu.
\s5
\v 23 'Ya'yansa maza daga Liya su ne Ruben, ɗan fãrin Yakubu, da Simiyon, Lebi, Yahuda, Issaka, da Zebulun.
\v 24 'Ya'yansa maza daga Rahila su ne Yosef da Benyamin.
\v 25 'Ya'yansa maza daga Bilha, baiwar Rahila, sune Dan da Naftali.
\s5
\v 26 'Ya'ya maza na Zilfa, baiwar Liya, su ne Gad da Asha. Dukkan waɗannan 'ya'yan Yakubu ne waɗanda a ka haifa masa a Faddan Aram.
\v 27 Yakubu ya zo wurin Ishaku a Mamri a Kiriyat Arba (ita ce dai Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.
\s5
\v 28 Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin.
\v 29 Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, a ka kuma tattara shi ga kakanninsa, tsohon mutum cike da kwanaki. Isuwa da Yakubu, 'ya'yansa, suka bizne shi.
\s5
\c 36
\cl Sura 36
\p
\v 1 Waɗannan ne zuriyar Isuwa (wanda kuma a ke kira Idom).
\v 2 Isuwa ya ɗauki matayensa daga Kan'aniyawa. Waɗannan ne matayensa: Ada ɗiyar Elon Bahittiye; Oholibama ɗiyar Ana, jikar Zibiyon Bahibbiye;
\v 3 da Bashemat, ɗiyar Isma'il, 'yar'uwar Nebayot.
\s5
\v 4 Ada ta haifi Elifaz da Isuwa, Bashemat kuma ta haifi Ruwel.
\v 5 Oholibama kuma ta haifi Yewish, Yalam da Kora. Waɗannan ne 'ya'yan Isuwa waɗanda a ka haifa masa a ƙasar Kan'ana.
\s5
\v 6 Isuwa ya ɗauki matayensa, da 'ya'yansa maza, da 'ya'yansa mata, da mutanen dake gidansa, da dabbobinsa - dukkan dabbobinsa, da dukkan mallakarsa, wadda ya tattara a ƙasar Kan'ana, ya tafi cikin wata ƙasa nesa da ɗan'uwansa Yakubu.
\v 7 Ya yi haka ne saboda mallakarsu ta yi yawan da ba zasu iya zama tare ba. Ƙasar da suka zauna ba za ta iya ɗaukar su ba saboda yawan dabbobinsu.
\v 8 Sai Isuwa, wanda kuma a ka sa ni da Idom, ya zauna a ƙasar tudu ta Seyir.
\s5
\v 9 Waɗannan ne zuriyar Isuwa, kakan Idomawa a ƙasar tudu ta Seyir.
\v 10 Waɗannan ne sunayen 'ya'ya maza na Isuwa: Elifaz ɗan Ada, matar Isuwa; Ruwel ɗan Bashemat, matar Isuwa.
\v 11 'Ya'ya maza na Elifaz sune Teman, Omar, Zefo, Gatam, da Kenaz.
\v 12 Timna, wata ƙwarƙwarar Elifaz, ɗan Isuwa, ta haifi Amalek. Waɗannan ne jikoki maza na Ada, matar Isuwa.
\s5
\v 13 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Ruwel: Nahat, Zera, Shamma, da Mizza. Waɗannan ne jikoki maza na Bashemat, matar Isuwa.
\v 14 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Oholibama, matar Isuwa, wadda ita ce ɗiyar Ana da jikar Zibiyon. Ta haifa wa Isuwa Yewish, Yalam, da Kora.
\s5
\v 15 Waɗannan ne kabilu a cikin zuriyar Isuwa: Zuriyar Elifaz, ɗan fãrin Isuwa: Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
\v 16 Kora, Gatam, da Amalek. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga Elifaz a ƙasar Idom. Su ne jikoki maza na Ada.
\s5
\v 17 Waɗannan ne dangogi daga Ruwel, ɗan Isuwa: Nahat, Zera, Shamma, Mizza. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga Ruwel a cikin ƙasar Idom. Su ne jikokin Bashemat, matar Isuwa.
\v 18 Waɗannan ne dangogin Oholibama, matar Isuwa: Yewish, Yalam, Kora. Waɗannan ne dangogin da suka fito daga matar Isuwa Oholibama, ɗiyar Ana.
\v 19 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Isuwa (wanda a ka sa ni da Idom), kuma waɗannan ne hakimansu.
\s5
\v 20 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Seyir Bahorite, mazauna ƙasar: Lotan, Shobal, Zibiyon, Ana,
\v 21 Dishon, Eza, da Dishan. Waɗannan ne dangogin Horitiyawa, mazauna Seyir a cikin ƙasar Idom.
\v 22 'Ya'ya maza na Lotan su ne Hori da Heman, kuma Timna 'yar'uwar Lotan ce.
\s5
\v 23 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Shobal: Alban, Manahat, Ebal, Shefo, da Onam.
\v 24 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Zibiyon: Aiya da Ana. Wannan Ana shi ne ya gano maɓulɓular ruwa mai zafi a jeji, yayin da yake kiwon jakkan Zibiyon mahaifinsa.
\s5
\v 25 Waɗannan ne 'ya'yan Ana: Dishon da Oholibama, ɗiyar Ana.
\v 26 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Dishon: Hemdan, Eshban, Itran, da Keran.
\v 27 Waɗannan ne 'ya'ya maza na Eza: Bilhan, Za'aban, da Akan.
\v 28 Waɗannan ne "ya'ya maza na Dishan: Uz da Aran.
\s5
\v 29 Waɗannan ne dangogin Horitiyawa: Lotan, Shobal, Zibiyon, da Ana,
\v 30 Dishon, Eza, Dishan: Waɗannan ne dangogin Horitiyawa, bisa ga dangoginsu da aka lissafa a ƙasar Seyir.
\s5
\v 31 Waɗannan ne sarakunan da suka yi mulki a ƙasar Idom kafin wani sarki ya yi mulki a bisa Isra'ilawa:
\v 32 Bela ɗan Beyor, ya yi mulki a Idom, sunan birninsa kuma Dinhaba ne.
\v 33 Sa'ad da Bela ya mutu, daga nan Yobab ɗan Zera da Bozra, ya yi mulki a gurbinsa.
\s5
\v 34 Sa'ad da Yobab ya mutu, Husham wanda ke daga ƙasar Temanawa, ya yi mulki a gurbinsa.
\v 35 Sa'ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad wanda ya ci Midiyanawa da yaƙi a ƙasar Mowab, ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Abit ne.
\v 36 Sa'ad da Hadad ya mutu, daga nan Samla na Masreka ya yi mulki a gurbinsa.
\s5
\v 37 Sa'ad da Samla ya mutu, daga nan Shawul na Rehobot ta gefen kogi ya yi mulki a gurbinsa.
\v 38 Sa'ad da Shawul ya mutu, daga nan Ba'al Hanan ɗan Akbor ya yi mulki a gurbinsa.
\v 39 Sa'ad da Ba'al-hanan ɗan Akbo, ya mutu, daga nan Hadar ya yi mulki a gurbinsa. Sunan birninsa Fawu ne. Sunan matarsa Mehetabel, ɗiyar Matred, jikar Me Zahab.
\s5
\v 40 Waɗannan ne sunayen shugabannin kabilu daga zuriyar Isuwa, bisa ga dangoginsu da lardunansu, bisa ga sunayensu: Timna, Alba, Yetet,
\v 41 Oholibama, Ela, Finon,
\v 42 Kenaz, Teman, Mibzar,
\v 43 Magdiyel, da Iram. Waɗannan ne shugabannin dangogin Idom, bisa ga mazaunansu a cikin ƙasar da suka mallaka. Wannan ne Isuwa, mahaifin Idomawa.
\s5
\c 37
\cl Sura 37
\p
\v 1 Yakubu ya zauna ƙasar da mahaifinsa ke zama, a cikin ƙasar Kan'ana.
\v 2 Waɗannan ne al'amura game da Yakubu. Yosef, wanda ke saurayi ɗan shekaru sha bakwai, yana kiwon tumaki da awaki tare da 'yan'uwansa. Yana tare da 'ya'yan Bilha da 'ya'yan Zilfa, matan mahaifinsa. Yosef yana kawo labarai marasa daɗi game da su wurin mahaifinsu.
\s5
\v 3 Isra'ila dai yana ƙaunar Yosef fiye da dukkan 'ya'yansa maza saboda shi ɗan tsufansa ne. Ya yi masa wata riga mai kyau.
\v 4 'Yan'uwansa suka ga cewa mahaifinsu na ƙaunarsa fiye da dukkan 'yan'uwansa maza. Suka ƙi jininsa, kuma ba su maganar alheri da shi.
\s5
\v 5 Yosef ya yi wani mafarki, ya kuma gaya wa 'yan'uwansa game da mafarkin. Suka ƙara ƙin jininsa.
\v 6 Yace masu, "Ina roƙon ku da ku saurari wannan mafarkin da na yi.
\s5
\v 7 Duba, muna ta ɗaurin dammunan hatsi a gona, gashi kuwa, sai damina ya tashi ya kuma tsaya a tsaye, sai kuma, dammunanku suka zo a kewaye suka rusuna wa damina."
\v 8 'Yan'uwansa suka ce masa, "Lallai zaka yi sarauta a kanmu? Lallai kuwa zaka yi mulki a kanmu?" Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkansa saboda kuma maganganunsa.
\s5
\v 9 Ya sake yin wani mafarkin ya gaya wa 'yan'uwansa. Yace, "Duba, Na yi wani mafarkin: Rana da wata da taurari sha ɗaya sun rusuna mani."
\v 10 Ya gaya wa mahaifinsa kamar yadda ya gaya wa 'yan'uwansa, mahaifinsa kuma ya tsauta masa. Yace masa, "Wanne irin mafarki ne ka yi haka? Ko hakika mahaifiyarka da Ni da 'yan'uwanka maza za mu zo mu rusuna ƙasa a gare ka?"
\v 11 'Yan'uwansa suka yi kishin sa, amma mahaifinsa ya ajiye al'amarin a rai.
\s5
\v 12 'Yan'uwansa suka tafi kiwon dabbobin mahaifinsu a Shekem.
\v 13 Isra'ila ya cewa Yosef, "Ba 'yan'uwanka na kiwon dabbobin a Shekem ba? Zo, zan kuma aike ka wurin su." Yosef yace masa, "Na shirya."
\v 14 Yace masa, "Ka tafi yanzu, ka duba ko 'yan'uwanka na lafiya ko dabbobin kuma na lafiya, sai ka kawo mani magana." Sai Yakubu ya aike shi daga Kwarin Hebron, Yosef kuma ya tafi Shekem.
\s5
\v 15 Wani mutum ya sami Yosef. Duba, Yosef yana ta gararanba a saura. Mutumin ya tambaye shi, "Me kake nema?"
\v 16 Yosef yace, "Ina neman 'yan'uwana ne. Ka gaya mani, ina roƙon ka, inda suke kiwon dabbobin."
\v 17 Mutumin yace, "Sun bar nan wurin, domin na ji suna cewa, 'Bari mu tafi Dotan."' Yosef ya bi bayan 'yan'uwansa ya kuma same su a Dotan.
\s5
\v 18 Suka hange shi daga nesa, kafin kuma ya iso kusa da su, suka shirya makirci gãba da shi su kashe shi.
\v 19 'Yan'uwansa suka ce wa junansu, "Duba, mai mafarkin nan yana tafe.
\v 20 Ku zo yanzu, saboda haka, bari mu kashe shi mu kuma jefa shi cikin ɗaya daga cikin ramukan. Za mu ce, 'Naman jeji ya cinye shi.' Za mu ga abin da zai fãru da mafarkansa."
\s5
\v 21 Ruben ya ji labari, kuma ya ceto shi daga hannunsu. Ya ce, "Kada mu ɗauki ransa."
\v 22 Ruben yace masu, "Kada ku zubar da jini. Ku jefa shi cikin wannan ramin dake cikin jeji, amma kada ku ɗora hannu a kansa" - domin ya ceto shi daga hannunsu ya maida shi wurin mahaifinsa.
\s5
\v 23 Sai ya kasance da Yosef ya iso wurin 'yan'uwansa, suka tuɓe masa kyakkyawar rigarsa.
\v 24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin ramin. Ramin ba komai a ciki babu ma ruwa a ciki.
\s5
\v 25 Suka zauna, su ci abinci. Suka ɗaga idanuwansu suka duba, kuma, duba, zangon Isma'ilawa na tafe daga Giliyad, tare da raƙummansu ɗauke da kayan yaji da man ƙanshi da kayan ƙanshi. Suna tafiya zasu kai su Masar.
\v 26 Yahuda ya cewa 'yan'uwansa, "Ina ribar da ke ciki idan muka kashe ɗan'uwanmu muka kuma rufe jininsa?
\s5
\v 27 Ku zo, mu sayar da shi ga Isma'ilawa, kada dai mu ɗora hannunmu a kansa. Gama shi ɗan'uwanmu ne, jikinmu." 'Yan'uwansa suka saurare shi.
\v 28 Midiyawan fatake suna wuce wa. 'Yan'uwan Yosef suka jawo shi, suka fito da shi daga rijiyar. Suka sayar da Yosef ga Isma'ilawa a kan azurfa ashirin. Isma'ilawa suka ɗauki Yosef zuwa cikin Masar.
\s5
\v 29 Ruben ya dawo ga ramin, kuma, duba, Yosef ba shi cikin ramin. Ya yage tufafinsa.
\v 30 Ya dawo wurin 'yan'uwansa ya ce, "Yaron ba shi a wurin! Ni kuma, ina zan tafi?"
\s5
\v 31 Suka yanka akuya, daga nan kuma suka ɗauki rigar Yosef suka tsoma a cikin jinin.
\v 32 Sa'an nan suka kawo ta wurin mahaifinsu suka ce, "Mun tsinci wannan. Muna roƙon ka, ka duba ko rigar ɗanka ce ko a'a."
\v 33 Yakubu ya gane ta ya ce, "Rigar ɗana ce. Naman daji ya cinye shi. Babu shakka an yayyaga Yosef gutsu-gutsu."
\s5
\v 34 Yakubu ya yayyage tufafinsa, ya sanya tsummokara a kwankwasonsa. Ya yi makokin ɗansa kwanaki da yawa.
\v 35 Dukkan 'ya'yansa maza da 'ya'yansa mata suka tashi domin su ta'azantar da shi, amma ya ƙi ya ta'azantu. Ya ce, "Tabbas zan gangara zuwa Lahira cikin makoki domin ɗana." Mahaifinsa ya yi kuka domin sa.
\v 36 Midiyawa kuwa suka saida shi a Masar ga Fotifa, wani maƙaddashin Fir'auna, hafsan masu tsaro.
\s5
\c 38
\cl Sura 38
\p
\v 1 Sai ya kasance a wannan lokaci Yahuda ya bar 'yan'uwansa ya je ya zauna da wani Ba'addulmiye, mai suna Hira.
\v 2 Ya haɗu da wa ta ɗiyar wani mutum Bakananiye mai suna Shuwa. Ya aure ta ya kuma kwana da ita.
\s5
\v 3 Ta ɗauki ciki ta sami ɗa, a ka sa masa suna Er.
\v 4 Ta sake ɗaukar ciki ta sami ɗa. Ta kira sunansa Onan.
\v 5 Ta sake samun wani ɗan ta kira sunansa Shela. A Kezib ne wurin da ta haife shi.
\s5
\v 6 Yahuda ya samar wa Er mata, ɗan fãrinsa. Sunanta Tama ne.
\v 7 Er, ɗan fãrin Yahuda, mugu ne a idanun Yahweh. Yahweh ya kashe shi.
\s5
\v 8 Yahuda ya cewa Onan, "Ka kwana da matar ɗan'uwanka. Ka yi aikin ɗan'uwan miji a gare ta, ka samar wa ɗan'uwanka ɗa."
\v 9 Onan ya san cewa ɗan ba zai zama na shi ba. Duk lokacin da ya kwana da matar ɗan'uwansa, sai ya zubar da maniyin a ƙasa domin kada ya samar wa ɗan'uwansa ɗa.
\v 10 Abin nan da ya yi kuwa mugunta ce a idanun Yahweh. Yahweh ya kashe shi shima.
\s5
\v 11 Daga nan Yahuda ya cewa Tama, surukarsa, "Ki yi zaman gwauruwa a gidan mahaifinki har sai Shela, ɗana, ya girma." Gama ya ji tsoro, "Shi ma wataƙila ya mutu, kamar 'yan'uwansa." Tama ta tashi ta kuma koma da zama gidan mahaifinta.
\s5
\v 12 Bayan lokaci mai tsawo, ɗiyar Shuwa, matar Yahuda, ta mutu. Yahuda ya ta'azantu ya kuma tafi wurin sausayar tumakinsa a Timna, shi da abokinsa Hira Ba'addulmiye.
\v 13 Aka gaya wa Tama, "Duba, surukinki zai tafi Timna domin sausayar tumakinsa."
\v 14 Sai ta tuɓe tufafin gwaurancinta ta rufe kanta da gyale ta kuma lulluɓe jikinta. Ta zauna a ƙofar Enayim, wadda ke kan hanyar zuwa Timna. Domin ta ga Shela ya girma, amma ba a bayar da ita ba a gare shi a matsayin mata.
\s5
\v 15 Sa'ad da Yahuda ya ganta ya zaci cewa karuwa ce saboda ta lulluɓe fuskarta.
\v 16 Ya je wurin ta a bakin hanya ya kuma ce, "Zo, ina roƙon ki bari in kwana da ke" - domin bai san cewa surukarsa ba ce - sai kuma ta ce, "Mezaka bani domin ka kwana da ni?"
\s5
\v 17 Ya ce, "Zan aiko maki da 'yar akuya daga garke." Ta ce, "Zaka bani diyya har sai ka aiko da ita?"
\v 18 Ya ce, "Wacce irin diyya zan ba ki?" Ta maida amsa, "Zoben hatiminka da ɗamararka, da sandar dake a hannunka." Ya bayar dasu a gare ta ya kuma kwana da ita, sai ta sami ciki daga gare shi.
\s5
\v 19 Ta tashi ta yi tafiyarta. Ta tuɓe lulluɓinta ta sanya tufafin gwaurancinta.
\v 20 Yahuda ya aika da 'yar akuyar ta hannun abokinsa Ba'addulmiye saboda ya karɓo diyyar daga hannun matar, amma bai same ta ba.
\s5
\v 21 Sai Ba'addulmiyen ya tambayi mutanen dake wurin, "Ina karuwar asiri dake zaune a Enayim a bakin hanya?" Suka ce, "Babu wata karuwar asiri dake zaune a nan."
\v 22 Ya dawo wurin Yahuda yace, "Ban same ta ba. Kuma, mutanen wurin sun ce, 'Babu wata karuwar asiri dake zaune a nan."'
\v 23 Yahuda yace, "Bari ta ajiye abubuwan, domin kada mu sha kunya. Tabbas, na aika da 'yar akuyar nan, amma ba ka same ta ba."
\s5
\v 24 Sai ya kasance bayan wajen wata uku, sai a ka gaya wa Yahuda, "Tama surukarka ta aikata karuwanci, kuma tabbas, ta sami ciki ta haka." Yahuda yace, "Ku kawo ta nan bari a ƙona ta kuma."
\v 25 Sa'ad da aka fito da ita, sai ta aika wa surukinta da saƙo, "Ta wurin mutumin dake da waɗannan nake da ciki." Ta ce, "Ina roƙon ka da ka gano mani waɗannan na waye, zoben tambarin da ɗamarar da sandar."
\v 26 Yahuda ya gane su ya kuma ce, "Ta fi ni adalci, tunda ban bayar da ita ba a matsayin mata ga Shela, ɗana." Bai sake kwana da ita ba kuma.
\s5
\v 27 Sai ya kasance da lokacin haihuwarta ya kai, duba, tagwaye ne ke cikin mahaifarta.
\v 28 Sai ya kasance a lokacin da take haihuwar ɗaya ya fito da hannunsa waje, unguwar zomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura masa a hannu ta kuma ce, "Wannan ne ya fãra fitowa."
\s5
\v 29 Amma daga nan sai ya maida hannunsa, kuma, duba, sai ɗan'uwansa ya fito farko. Unguwar zomar ta ce, "Ya ya ka faso waje!" Sai aka sa masa suna Ferez.
\v 30 Daga nan ɗan'uwansa ya fito, wanda yake da jan zare a hannu, aka kuma sa masa suna Zera.
\s5
\c 39
\cl Sura 39
\p
\v 1 Aka kawo Yosef zuwa Masar. Fotifa, maƙaddashin Fir'auna kuma hafsan masu tsaro kuma Bamasare, ya sawo shi daga Isma'ilawa, waɗanda suka kawo shi nan.
\v 2 Yahweh yana tare da Yosef ya kuma zama wadataccen mutum. Yana zaune cikin gidan ubangidansa Bamasare.
\s5
\v 3 Ubangidansa ya ga cewa Yahweh na tare da shi kuma Yahweh na wadata kowanne abu da ya yi.
\v 4 Yosef ya sami tagomashi a idanunsa. Ya bautawa Fotifa. Fotifa ya maida Yosef shugaban gidansa, da kowanne abu da ya mallaka, ya sanya ƙarƙashin lurarsa.
\s5
\v 5 Sai ya kasance tun lokacin da ya maida shi shugaba bisa gidansa da bisa kowanne abu da ya mallaka, sai Yahweh ya albarkaci gidan Bamasaren saboda Yosef. Albarkar Yahweh tana bisa kowanne abu da Fotifa yake da shi a cikin gida da gona.
\v 6 Fotifa ya sanya kowanne abu da yake da shi a ƙarƙashin lurar Yosef. Ba ya buƙatar ya yi tunani game da komai sai dai kawai abincin da zai ci. Shi dai Yosef kyakkyawa ne gwanin sha'awa kuma.
\s5
\v 7 Sai ya kasance bayan wannan matar ubangidansa ta yi sha'awar Yosef. Ta ce, "Ka kwana da ni."
\v 8 Amma ya ƙi, ya kuma ce wa matar ubangidansa, "Duba, ubangidana ba ya kulawa da abin da nake yi a cikin gidan nan, kuma ya sanya kowanne abu da yake da shi a ƙarƙashin lura ta.
\v 9 Babu wanda ya fi ni girma a cikin gidan nan. Bai hana mani komai ba sai dai ke, saboda ke matarsa ce. Ta yaya daga nan zan yi wannan irin babbar mugunta da zunubi gãba da Allah?"
\s5
\v 10 Ta dinga magana da Yosef rana bayan rana, amma ya ƙi ya kwana da ita ko ya kasance tare da ita.
\v 11 Sai ya kasance wata rana, Yosef ya shiga cikin gidan domin ya yi aikinsa. Babu ko ɗaya daga cikin mutanen gidan dake cikin gidan.
\v 12 Ta kama shi ta tufafinsa ta ce kuma, "Ka kwana da ni." Ya bar tufafinsa a hannunta, ya tsere, ya fita waje kuma.
\s5
\v 13 Sai ya kasance, sa'ad da taga cewa ya bar tufafinsa a cikin hannunta ya kuma tsere waje,
\v 14 sai ta kira mutanen gidanta ta ce masu, "Duba, Fotifa ya kawo Ba'ibraniye ya wulaƙanta mu. Ya shigo wurina ya kwana da ni, na kuwa yi ihu.
\v 15 Sai ya kasance sa'ad da ya ji ina ihu, sai ya bar tufafinsa tare da ni, ya tsere, ya kuma fita waje."
\s5
\v 16 Ta ajiye tufafinsa a kusa da ita har sai da ubangidansa ya zo gida.
\v 17 Ta faɗi masa wannan bayyani, "Ba'ibraniyen nan bawa wanda ka kawo mana, ya shigo domin ya wulaƙanta ni.
\v 18 Sai ya kasance sa'ad da nayi ihu, ya bar tufafinsa tare da ni ya kuma tsere waje."
\s5
\v 19 Sai ya kasance, sa'ad da ya ji bayanin da matarsa ta faɗi masa, "Wannan ne abin da bawanka ya yi mani," sai ya fusata sosai.
\v 20 Ubangidan Yosef ya ɗauke shi ya saka shi cikin kurkuku, wurin da a ke tsaron 'yan kurkukun sarki. Ya na nan a cikin kurkukun.
\s5
\v 21 Amma Yahweh na tare da Yosef ya kuma nuna alƙawarin aminci a gare shi. Ya kuma ba shi tagomashi a idanun shugaban kurkukun.
\v 22 Shugaban kurkukun ya bayar da dukkan 'yan kurkukun dake cikin kurkukun cikin hannun Yosef. Duk abin da suka yi a nan, Yosef ne ke shugabancin sa.
\v 23 Shugaban kurkuku ba ya kulawa da kowanne abu dake cikin hannunsa, saboda Yahweh na tare da shi. Duk abin da ya yi Yahweh na wadatar da shi.
\s5
\c 40
\cl Sura 40
\p
\v 1 Sai ya kasance bayan waɗannan abubuwa, mai riƙon ƙoƙon sha na sarkin Masar da mai toye-toye na sarki suka ɓata wa ubangidansu, sarkin Masar rai.
\v 2 Fir'auna ya ji haushin ofisoshinsa biyu, da shugaban ma su riƙon ƙoƙon sha da shugaban masu toye-toye.
\v 3 Ya sa aka tsare su a cikin gidan shugaban masu tsaro, a cikin wannan kurkuku inda aka tsare Yosef.
\s5
\v 4 Shugaban masu tsaron ya miƙa Yosef a gare su, ya kuma yi masu hidima. Suka ci gaba a tsare na wani lokaci.
\v 5 Dukkan su biyu sai suka yi wani mafarki - mai riƙon ƙoƙon sha da mai toye-toye na sarkin Masar waɗanda ke tsare a kurkukun - kowanne mutum ya yi nasa mafarki a dare ɗaya, kuma kowanne mafarkin da tasa fassarar.
\s5
\v 6 Yosef ya zo wurin su da safe ya kuma gan su. Duba, suna cikin baƙinciki.
\v 7 Ya tambayi ofisoshin Fir'auna waɗanda ke tare da shi a tsare a cikin gidan ubangidansa, ya ce, "Meyasa kuke baƙinciki a yau?"
\v 8 Suka ce masa, "Dukkan mu biyu munyi wani mafarki kuma babu wanda ya iya fassara su." Yosef yace masu, "Fassarori ba ta Allah ba ce?" Ku faɗa mani, ina roƙon ku."
\s5
\v 9 Shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ya gaya wa Yosef mafarkinsa. Ya ce masa, "A cikin mafarkina, duba, itacen inabi na gabana.
\v 10 A itacen inabin akwai rassa uku. Suka tsiro, suka yaɗu da 'ya'ya nan da nan inabin kuma suka nuna.
\v 11 Ƙoƙon Fir'auna yana hannuna. Na ɗauki 'ya'yan inabin na matse su cikin ƙoƙon Fir'auna, sai kuma na miƙa ƙoƙon cikin hannun Fir'auna."
\s5
\v 12 Yosef yace masa, "Wannan ce fassarar sa. Rassan uku kwanaki uku ne.
\v 13 A cikin kwanaki uku Fir'auna zai ɗaga kanka ya kuma mai da kai wurin aikinka. Za ka sanya ƙoƙon Fir'auna cikin hannunsa, kamar dai sa'ad da kake mai riƙon ƙoƙon shansa.
\s5
\v 14 Amma ka tuna da ni sa'ad da komai ya tafi lafiya da kai, ina roƙon ka kuma ka nuna mani alheri. Ka ambace ni wurin Fir'auna a fito da ni daga wannan kurkuku.
\v 15 Domin tabbas an sato ni ne daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma banyi wani abu ba da zai sanya su su sani cikin wannan rami ba."
\s5
\v 16 Sa'ad da shugaban masu toye-toye ya ga cewa fassarar ta yi daɗi, ya cewa Yosef, "Ni ma nayi mafarki, kuma, duba, kwanduna uku na gurasa suna bisa kaina.
\v 17 A cikin kwandon na sama akwai kowanne irin kayan toye-toye domin Fir'auna, amma tsuntsaye suka cinye su daga cikin kwandon a bisa kaina."
\s5
\v 18 Yosef ya amsa ya ce, "Wannan ce fassarar sa. Kwandunan uku kwanaki uku ne.
\v 19 A cikin kwanaki uku Fir'auna zai ɗaga kanka daga gare ka zai kuma sarƙafe ka bisa itace. Tsuntsaye kuma zasu cinye namanka daga gare ka."
\s5
\v 20 Sai ya kasance a rana ta uku ranar tunawa da haihuwar Fir'auna ce. Sai ya yi wa dukkan bayinsa biki. Sai ya ɗaga kan shugaban masu riƙon ƙoƙon sha da shugaban masu toye-toye, daga cikin bayinsa.
\v 21 Ya maido da shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ga hidimarsa, ya kuma sake sanya ƙoƙon cikin hannun Fir'auna.
\v 22 Amma ya sargafe shugaban masu toye-toye, kamar yadda Yosef ya yi masu fassara.
\v 23 Duk da haka shugaban masu riƙon ƙoƙon shan bai tuna da Yosef ba, amma ya manta da shi.
\s5
\c 41
\cl Sura 41
\p
\v 1 Sai ya kasance bayan shekaru biyu cur Fir'auna ya yi wani mafarki. Duba, yana tsaye bakin Nilu.
\v 2 Duba, sai ga wasu shanu bakwai sun fito daga Nilu, masu ban sha'awa da ƙiba, suna kuma kiwo a cikin iwa.
\v 3 Duba, ga wasu shanun bakwai sun fito bayan su daga cikin Nilu, marasa ban sha'awa ramammu kuma. Suka tsaya gefen waɗancan shanun a bakin kogin.
\s5
\v 4 Daga nan shanun marasa ban sha'awa ramammu kuma suka cinye shanun masu ban sha'awa da ƙiba. Daga nan Fir'auna ya farka.
\v 5 Daga nan kuma ya sake yin barci ya kuma sake yin mafarki karo na biyu. Duba, kawunan hatsi bakwai sun fito bisa kara ɗaya, cikakku masu kyau kuma.
\v 6 Gashi, kawuna bakwai, ƙanana waɗanda kuma iskar gabas ke kakkaɓewa, suka fito bayan su.
\s5
\v 7 Ƙananan kawunan suka haɗiye kawunan cikakku masu kyau kuma. Fir'auna ya farka, kuma, duba, ashe mafarki ne.
\v 8 Sai ya kasance da safe ruhunsa ya damu. Ya aika aka kira dukkan 'yan dabo da masu hikima na Masar. Fir'auna ya gaya masu mafarkansa, amma babu wani da ya iya fassara su ga Fir'auna.
\s5
\v 9 Daga nan shugaban masu riƙon ƙoƙon sha ya ce wa Fir'auna, "A yau ina tunani game da laifuffukana.
\v 10 Fir'auna ya yi fushi da bayinsa, ya kuma sanya ni cikin tsaro a cikin gidan shugaban masu tsaro, shugaban masu tuya tare da ni.
\v 11 Muka yi mafarki a cikin dare ɗaya, shi da ni. Muka yi mafarki kowanne mutum bisa ga fassarar mafarkinsa.
\s5
\v 12 Tare da mu a can akwai wani saurayin mutum Ba'ibraniye, bawan shugaban masu tsaro. Muka faɗi masa kuma ya fassara mana mafarkanmu. Ya fassara wa kowannen mu bisa ga mafarkinsa.
\v 13 Sai ya kasance kamar yadda ya fassara mana, haka ya faru. Fir'auna ya maido ni bisa aikina, amma ɗayan ya sarƙafe shi."
\s5
\v 14 Daga nan Fir'auna ya aika aka kuma kirawo Yosef. Nan da nan suka fito da shi daga ramin. Ya kuma yi aski, ya canza sutura, ya kuma fito zuwa wurin Fir'auna.
\v 15 Fir'auna ya cewa Yosef, "Na yi mafarki, amma babu mai fassara. Amma na ji labarinka, cewa idan ka ji mafarki kana iya fassara shi."
\v 16 Yosef ya amsawa Fir'auna, cewa, "Ba ni ba ne. Allah zai amsawa Fir'auna da tagomashi."
\s5
\v 17 Fir'auna ya yi magana da Yosef, "A cikin mafarkina, duba, ina tsaye a bakin Nilu.
\v 18 Gashi, shanu bakwai suka fito daga cikin Nilu, masu ƙiba da ban sha'awa, suna kuma kiwo cikin iwa.
\s5
\v 19 Gashi, wasu shanun bakwai suka fito bayan su, marasa ƙarfi, marasa ban sha'awa, ramammu kuma. A cikin dukkan ƙasar Masar ban taɓa ganin wani abin rashin ban sha'awa ba kamar su.
\v 20 Shanun marasa ƙiba da rashin ban sha'awa suka cinye shanun na farko masu ƙiba.
\v 21 Sa'ad da suka cinye su, ba za a ma san cewa sun cinye su ba, domin sun kasance marasa ban sha'awa kamar dã. Daga nan na farka.
\s5
\v 22 Na duba a cikin mafarkina, kuma, duba, kawuna bakwai na hatsi suka fito bisa kara ɗaya, cikakku masu kyau.
\v 23 Gashi kuwa, ƙarin kawuna bakwai - busassu, ƙanana, waɗanda kuma iskar gabas ke kakkaɓewa - suka fito bayansu.
\v 24 Ƙananan kawunan suka haɗiye kawunan bakwai masu kyau. Na faɗi waɗannan mafarkai ga masu dabo, amma babu wani da zai yi bayyanin su a gare ni."
\s5
\v 25 Yosef ya cewa Fir'auna, "Mafarkan Fir'auna ɗaya ne. Abin da Allah ke gaf da aiwatar wa, ya bayyana wa Fir'auna.
\v 26 Shanun masu kyau guda bakwai shekaru bakwai ne, kawunan hatsin bakwai kuma shekaru bakwai ne. Mafarkan iri ɗaya ne.
\s5
\v 27 Shanun bakwai ramammu marasa ban sha'awa da suka fito bayan su shekaru bakwai ne, haka nan kuma kawunan hatsin ƙanana da iskar gabas ke kakkaɓe wa shekaru ne bakwai na yunwa.
\v 28 Wannan batun ne na faɗawa Fir'auna. Abin da Allah ke gaf da aiwatar wa ya bayyana wa Fir'auna.
\v 29 Duba, shekaru bakwai na yalwa zasu zo cikin dukkan ƙasar Masar.
\s5
\v 30 Shekaru bakwai na yunwa zasu zo bayan su, za a kuma manta da dukkan yalwar da aka yi a ƙasar Masar, kuma yunwar za ta lalata ƙasar.
\v 31 Ba za a tuna da yalwar ba a cikin ƙasar saboda yunwar da za ta biyo baya, domin za ta zama da tsanani sosai.
\v 32 Cewa an maimaita wa Fir'auna mafarkin saboda Allah ya tabbatar da al'amarin ne, kuma Allah zai aiwatar ba da daɗewa ba.
\s5
\v 33 Yanzu bari Fir'auna ya nemi wani mutum mai fahimta da hikima, ya kuma ɗora shi bisa ƙasar Masar.
\v 34 Bari Fir'auna ya zaɓi shugabanni bisa ƙasar, bari kuma su ɗauki kashi biyar na dukkan amfanin Masar a cikin shekaru bakwai na yalwa.
\s5
\v 35 Bari su tattara dukkan abincin waɗannan shekaru masu kyau dake zuwa su kuma ajiye hatsi a ƙarƙashin ikon Fir'auna, domin abincin da za a yi amfani da shi a cikin biranen. Su adana shi.
\v 36 Abincin zai zama abin wadatar wa domin ƙasar domin kuma shekaru bakwai na yunwa da zasu kasance a ƙasar Masar. Ta wannan hanyar ƙasar ba zata lalace ba ta wurin yunwar."
\s5
\v 37 Wannan shawara ta yi kyau a idanun Fir'auna da idanun dukkan bayinsa.
\v 38 Fir'auna ya cewa bayinsa, "Za mu iya samun wani mutum kamar wannan, wanda Ruhun Allah ke cikinsa?"
\s5
\v 39 Sai Fir'auna ya cewa Yosef, "Tunda Allah ya nuna maka dukkan waɗannan abubuwa, babu wani mafi fahimta da hikima kamar kai.
\v 40 Zaka kasance bisa gidana, kuma bisa ga maganar ka za a yi mulkin dukkan mutanena. A bisa kursiyi ne kawai zan fi ka girma."
\v 41 Fir'auna ya cewa Yosef, "Duba, na sanya ka bisa dukkan ƙasar Masar."
\s5
\v 42 Fir'auna ya cire zoben hatiminsa daga hannunsa ya sanya a hannun Yosef. Ya yi masa sutura da suturar linin mai laushi, ya kuma sanya sarƙar zinariya a wuyansa.
\v 43 Ya sanya shi ya tuƙa karusarsa ta biyu da ya mallaka. Mutane suka yi sowa a gabansa, "Gwiwa a durƙushe." Fir'auna ya sanya shi bisa dukkan ƙasar Masar.
\s5
\v 44 Fir'auna ya cewa Yosef, "Ni ne Fir'auna, baya gare ka kuma, babu mutumin da zai ɗaga hannunsa ko ƙafarsa a cikin dukkan ƙasar Masar."
\v 45 Fir'auna ya kira Yosef da suna "Zafenat-Faniya." Ya ba shi Asenat, ɗiyar Fotifera firist na On, a matsayin mata. Yosef ya fita bisa ƙasar Masar.
\s5
\v 46 Yosef yana da shekaru talatin sa'ad da ya tsaya a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Yosef ya fita daga gaban Fir'auna, ya kuma tafi cikin dukkan ƙasar Masar.
\v 47 A cikin shekaru bakwai na yalwa ƙasar ta fitar da amfani a yalwace.
\s5
\v 48 Ya tattara dukkan abinci na shekaru bakwai dake cikin ƙasar Masar ya kuma sanya abincin a cikin biranen. Ya sanya a cikin kowanne birni abincin gonakin dake kewaye da shi.
\v 49 Yosef ya ajiye hatsi kamar rairayin teku, da yawan gaske har ya daina ƙirgawa, saboda ya zarce ƙirgawa.
\s5
\v 50 Yosef ya haifi 'ya'ya biyu kafin zuwan shekarun yunwa, waɗanda Asenat, ɗiyar Fotifa firist na On, ta haifa masa.
\v 51 Yosef ya kira sunan ɗan fãrinsa Manasse, domin ya ce, "Allah ya sa na manta da dukkan damuwata da dukkan gidan mahaifina."
\v 52 Ya kira sunan ɗan na biyu Ifraim, domin ya ce, "Allah ya maida ni mai bada 'ya'ya a cikin ƙasar wahalata."
\s5
\v 53 Shekaru bakwai na yalwa da suka kasance a ƙasar Masar suka kawo ƙarshe.
\v 54 Aka fãra shekaru bakwai na yunwa, kamar yadda Yosef ya faɗa. Aka yi yunwa a cikin dukkan ƙasashen, amma a cikin dukkan ƙasar Masar akwai abinci.
\s5
\v 55 Sa'ad da dukkan ƙasar Masar suka fãra yunwa, mutanen suka kira ga Fir'auna da ƙarfi domin abinci. Fir'auna ya cewa dukkan Masarawa, "Ku je wurin Yosef ku kuma yi abin da ya ce."
\v 56 Yunwa tana bisa dukkan fuskar ƙasar. Yosef ya buɗe dukkan gidajen ajiya ya sayar wa da Masarawa. Yunwa ta yi tsanani a ƙasar Masar.
\v 57 Dukkan duniya na zuwa Masar su sayi hatsi daga wurin Yosef, saboda yunwar ta yi tsanani a dukkan duniya.
\s5
\c 42
\cl Sura 42
\p
\v 1 Yanzu Yakubu ya sami sani cewa akwai hatsi a Masar. Ya ce wa 'ya'yansa maza, "Meyasa kuke kallon juna?"
\v 2 Ya ce, "Ku saurara, Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sawo domin mu dagacan domin mu rayu kada kuma mu mutu."
\v 3 'Yan'uwan Yosef goma suka gangara domin su sawo hatsi daga Masar.
\v 4 Amma Benyamin, ɗan'uwan Yosef, Yakubu bai aike shi ba tare da 'yan'uwansa, saboda ya ji tsoron cewa wani bala'i na iya afko masa.
\s5
\v 5 'Ya'yan Isra'ila na cikin waɗanda suka zo saye, domin akwai yunwa a cikin ƙasar Kan'ana.
\v 6 Yanzu dai Yosef shi ne gwamna a ƙasar. Shi ne ke saida wa dukkan mutanen ƙasar. 'Yan'uwan Yosef suka zo suka kuma rusuna masa da fuskokinsu ƙasa.
\s5
\v 7 Yosef ya ga 'yan'uwansa ya kuma gãne su, amma ya ɓadda masu kamarsa ya kuma yi magana da su da zafi. Ya ce masu, "Daga ina kuka fito?" Suka ce, "Daga ƙasar Kan'ana domin mu sayi abinci."
\v 8 Yosef ya gãne 'yan'uwansa, amma su basu gãne shi ba.
\s5
\v 9 Daga nan Yosef ya tuna da mafarkan da ya yi game da su, ya kuma ce masu, "Ku 'yan leƙen asirin ƙasa ne! kun zo ku ga sassan ƙasar da basu da tsaro."
\v 10 Suka ce masa, "A'a, shugabana. Bayinka sun zo sayen abinci ne.
\v 11 Dukkan mu 'ya'yan mutum ɗaya ne. Mu mutane ne masu gaskiya. Bayinka ba 'yan leƙen asirin ƙasa ba ne."
\s5
\v 12 Ya ce masu, "A'a, kun zo ku ga sassan ƙasar da ba su da tsaro."
\v 13 Suka ce, "Mu bayinka 'yan'uwa sha biyu ne, 'ya'yan mutum ɗaya a cikin ƙasar Kan'ana. Duba, ƙaramin mu a yau yana tare da mahaifinmu, ɗayan ɗan'uwan kuma baya da rai."
\s5
\v 14 Yosef yace masu, "Abin da na ce maku ke nan; ku 'yan leƙen asirin ƙasa ne.
\v 15 Ta haka za a gwada ku. Da ran Fir'auna, ba zaku bar nan ba, sai idan ƙaramin ɗan'uwanku ya zo nan.
\v 16 Ku aiki ɗaya daga cikin ku ya je ya zo da ɗan'uwanku. Zaku zauna a kurkuku, domin a gwada maganganunku, ko akwai gaskiya a cikin ku."
\v 17 Ya sa dukkan su a ka kulle su har kwana uku.
\s5
\v 18 A rana ta uku Yosef yace masu, "Ku yi haka kuma ku rayu, domin ina tsoron Allah.
\v 19 Idan ku mutane ne masu gaskiya, bari ɗaya daga cikin 'yan'uwanku a tsare shi a kurkuku, amma ku ku tafi, ku ɗauki hatsi domin yunwar gidajenku.
\v 20 Ku kawo mani ƙaramin ɗan'uwanku domin a tabbatar da maganganunku kuma ba za ku mutu ba." Sai suka yi haka.
\s5
\v 21 Suka cewa juna, "Babu shakka mun yi laifi game da ɗan'uwanmu yadda muka ga ƙuncin ransa sa'ad da ya roƙe mu, amma muka ƙi sauraron sa. Saboda haka wannan ƙunci ya zo bisanmu."
\v 22 Ruben ya amsa masu, "Ban gaya maku ba, 'Kada kuyi zunubi game da saurayin, amma baku saurare ni ba? Yanzu, duba, ana neman jininsa daga hannunmu."
\s5
\v 23 Basu san cewa Yosef ya fahimce su ba, domin akwai mai fassara a tsakanin su.
\v 24 Ya juya daga gare su ya yi kuka. Ya kuma dawo gare su ya yi magana da su. Ya ɗauki Simiyon daga cikin su ya ɗaure shi a gaban idanunsu.
\v 25 Daga nan Yosef ya umarci bayinsa su cika buhunan 'yan'uwansa da hatsi, kuma su maida wa kowa kuɗinsa cikin buhunsa, su kuma basu kayan masarufi domin tafiyarsu. A ka yi haka domin su.
\s5
\v 26 Suka ɗora wa jakunansu hatsi suka kuma yi tafiyar su daga wurin.
\v 27 Yayin da ɗaya daga cikin su ya buɗe buhunsa domin ya ciyar da jakinsa a wurin hutawar su, ya ga kuɗinsa. Duba, suna bakin buhunsa.
\v 28 Ya cewa 'yan'uwansa, "An maida mani kuɗina, ku dube su; suna bakin buhuna." Zukatansu suka nitse, suka kuma juya suna rawar jiki ga junansu, suna cewa, "Mene ne haka da Allah ya yi mana?"
\s5
\v 29 Suka tafi wurin Yakubu, mahaifinsu a cikin ƙasar Kan'ana suka kuma gaya masa dukkan abin da ya faru da su. Suka ce,
\v 30 "Mutumin, ubangijin ƙasar, ya yi magana da mu da zafi ya zaci cewa mu 'yan leƙen asirin ƙasa ne.
\v 31 Muka ce masa, "Mu mutane ne masu gaskiya. Ba 'yan leƙen asirin ƙasa bane.
\v 32 Mu 'yan'uwa ne sha biyu, 'ya'ya maza na mahaifinmu. Ɗaya baya da rai, ƙaramin kuma yau yana tare da mahaifinmu a ƙasar Kan'ana.'
\s5
\v 33 Mutumin, ubangijin ƙasar, ya ce mana, 'Ta haka zan sani cewa ku mutane ne masu gaskiya. Ku bar ɗaya daga cikin 'yan'uwanku tare da ni, ku ɗauki hatsi domin yunwar dake gidajenku, ku kuma yi tafiyarku.
\v 34 Ku kawo ƙaramin ɗan'uwanku wuri na. Daga nan zan sani cewa ku ba 'yan leƙen asirin ƙasa ba ne, amma ku mutane ne masu gaskiya. Daga nan zan saki ɗan'uwanku a gare ku, kuma zaku yi sana'a a ƙasar."'
\s5
\v 35 Sai ya kasance yayin da suka zazzage buhunansu, duba, kowanne mutum jakkar azurfarsa na cikin buhunsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga jakkunan azurfarsu, sai suka tsorata.
\v 36 Yakubu mahaifinsu ya ce masu, "Kun salwantar mani da 'ya'yana. Yosef ba shi da rai, Simiyon kuma ya tafi, kuma zaku ɗauke Benyamin. Waɗannan abubuwa dukka gãba suke da ni."
\s5
\v 37 Ruben ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Kana iya kashe 'ya'yana biyu idan ban maido maka da Benyamin ba. Ka sanya shi cikin hannuwana, kuma zan sake maido maka da shi."
\v 38 Yakubu yace, 'Ɗana ba zai tafi tare da ku ba. Domin ɗan'uwansa ya mutu shi kaɗai kuma ya rage. Idan wani bala'i ya zo masa a hanyar da zaku tafi, daga nan zaku kawo furfurata da baƙinciki zuwa Lahira."
\s5
\c 43
\cl Sura 43
\p
\v 1 Yunwa ta yi tsanani a ƙasar.
\v 2 Sai ya kasance sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce masu, "Ku sake komawa; ku sayo mana ɗan abinci."
\s5
\v 3 Yahuda yace masa, "Mutumin ya yi mana kashedi sosai, 'Ba za ku ga fuskata ba har sai ɗan'uwanku na tare da ku.'
\v 4 Idan ka aika ɗan'uwanmu tare da mu, to za mu gangara mu je mu sayo maka abinci.
\v 5 Amma idan ba ka aika da shi ba, ba za mu tafi ba. Domin mutumin ya ce mana, 'Ba za ku ga fuskata ba har sai ɗan'uwanku na tare da ku."'
\s5
\v 6 Isra'ila yace, "Meyasa kuka yi mani mummunan abu haka ta wurin gaya wa mutumin cewa kuna da wani ɗan'uwan?"
\v 7 Suka ce, "Mutumin ya yi tambaya dalla-dalla game da mu da iyalinmu. Ya ce, 'Mahaifinku yana nan da rai? Kuna da wani ɗan'uwan? Muka amsa masa bisa ga waɗannan tambayoyi. Ta yaya zamu san cewa zai ce, 'Ku kawo ɗan'uwanku nan?"'
\s5
\v 8 Yahuda ya cewa Isra'ila mahaifinsa, "Ka aiki saurayin tare da ni. Zamu tashi mu tafi domin mu rayu kada kuma mu mutu, dukkanmu, da kai, da kuma 'ya'yanmu dukka.
\v 9 Ni zan tsaya domin sa. Zaka riƙe ni hakkinsa. Idan ban dawo maka da shi ba na kuma tsaida shi a gabanka ba, daga nan bari in ɗauki laifin har abada.
\v 10 Domin idan da ba mu yi jinkiri ba, tabbas da yanzu mun dawo karo na biyu.
\s5
\v 11 Mahaifinsu Isar'ila yace masu, "Idan haka abin yake, yanzu kuyi haka. Ku ɗauki mafi kyau daga cikin amfanin ƙasar a cikin jakkunanku. Ku tafi da su kyauta ga mutumin - su man shafawa da zuma, kayan yaji da ƙaro, tsabar 'ya'yan itace dana almond.
\v 12 Ku ɗauki kuɗi ka shi biyu a hannunku. Kuɗaɗen da aka maido maku da aka buɗe buhunanku, ku ɗauka a cikin hannunku. Wataƙila kuskure ne.
\s5
\v 13 Ku ɗauki ɗan'uwanku kuma. Ku tashi ku sake tafiya wurin mutumin.
\v 14 Bari Allah maɗaukaki ya baku jinƙai a gaban mutumin, domin ya sakar maku ɗaya ɗan'uwanku da Benyamin. Idan na rasa 'ya'yana, na rasa su."
\v 15 Mutanen suka ɗauki kyautar, a hannunsu kuma suka ɗauki kuɗi kashi biyu, tare da Benyamin. Suka tashi kuma suka tafi suka gangara zuwa Masar suka je suka tsaya kuma a gaban Yosef.
\s5
\v 16 Sa'ad da Yosef yaga Benyamin tare da su, ya cewa ma'aikacin gidansa, "Ka kawo mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya ta, domin mutanen zasu ci tare da ni da rana."
\v 17 Ma'aikacin ya yi yadda Yosef ya ce. Ya kawo mutanen cikin gidan Yosef.
\s5
\v 18 Mutanen suka tsorata saboda an kawo su cikin gidan Yosef. Suka ce, "Saboda kuɗaɗen da aka maido mana cikin buhunanmu a zuwanmu na farko aka kawo mu ciki, domin ya sami zarafin gãba da mu. Zai iya ɗaure mu ya ɗauke mu a matsayin bayi, ya kuma karɓe jakkunanmu."
\v 19 Suka kusanci ma'aikacin gidan Yosef,
\v 20 suka kuma yi magana da shi a bakin ƙofar gidan, cewa, "Shugabana, mun zo karo na farko sayen abinci.
\s5
\v 21 Sai ya kasance, da muka isa wurin hutawa, sai muka buɗe buhunanmu, kuma, duba, kuɗin kowanne mutum na bakin buhunsa, kuɗaɗenmu kuma nada nauyinsu dai-dai. Mun sake kawo su a hannuwanmu.
\v 22 Mun sake kuma kawo wasu kuɗaɗen domin mu sayi abinci. Ba mu san wanda ya sanya kuɗaɗenmu cikin buhunanmu ba."
\v 23 Ma'aikacin yace, "Salama a gareku, kada ku ji tsoro. Allahnku da Allahn mahaifinku ne ya sanya kuɗaɗenku a buhunanku. Na karɓi kuɗaɗenku." Daga nan ma'aikacin ya fito da Simiyon wurinsu.
\s5
\v 24 Ma'aikacin ya kai mutanen cikin gidan Yosef. Ya basu ruwa, suka kuma wanke ƙafafunsu. Ya ciyar da jakkunansu.
\v 25 Suka shirya kyaututtukan domin zuwan Yosef da rana, domin sun ji cewa zasu ci abinci a nan.
\s5
\v 26 Sa'ad da Yosef ya zo gida, suka kawo kyaututtukan dake hannuwansu cikin gidan, suka kuma rusuna a gabansa har ƙasa.
\v 27 Ya tambayi lafiyarsu ya kuma ce, "Mahaifinku na nan lafiya, tsohon da kuka yi maganar sa? Har yau yana nan da rai?"
\s5
\v 28 Suka ce, "Bawanka mahaifinmu yana nan lafiya lau. Har yau yana nan da rai." Suka kwanta kuma suka rusuna har ƙasa.
\v 29 Sa'ad da ya ɗaga idanunsa ya kalli Benyamin ɗan'uwansa, ɗan mahaifiyarsa, sai ya ce, "Wannan ne ƙaramin ɗan'uwanku da kuka yi mani maganarsa?" Daga nan ya ce, "Allah ya yi maka alheri, ɗana."
\s5
\v 30 Yosef ya yi hanzari ya fita daga ɗakin, saboda ya motsu sosai game da ɗan'uwansa. Ya nemi wurin da zai yi kuka. Ya tafi ɗakinsa ya yi kuka a can.
\v 31 Ya wanke fuskarsa ya kuma fito. Ya kame kansa, ya ce, "A raba abincin."
\s5
\v 32 Bayin suka yi wa Yosef hidima shi kaɗai, suka kuma yi wa 'yan'uwan hidima su kaɗai. Masarawan suka ci tare da shi su kaɗai, saboda Masarawa ba zasu ci abinci tare da Ibraniyawa ba, domin yin haka abin ƙyama ne ga Masarawa.
\v 33 'Yan'uwan suka zauna a gabansa, na farko bisa ga matsayin haihuwarsa, ƙaramin kuma bisa ga samartakarsa. Mutanen suka yi mamaki tare.
\v 34 Yosef ya aika masu kaso daga abincin dake gabansa. Amma kason Benyamin ya yi sau biyar fiye dana 'yan'uwansa. Suka sha suka kuma yi murna tare da shi.
\s5
\c 44
\cl Sura 44
\p
\v 1 Yosef ya umarci ma'aikacin gidansa, ya ce, "Ka cika buhunan mutanen da abinci, iya yadda zasu iya ɗauka, ka kuma maida wa kowannen su kuɗinsa cikin bakin buhunsa.
\v 2 Ka sanya kofina, kofin azurfa, cikin bakin buhun ƙaramin, da kuɗinsa na hatsi." Ma'aikacin ya yi yadda Yosef ya ce.
\s5
\v 3 Da asuba, aka kuma sallami mutanen, su da jakkunansu.
\v 4 Sa'ad da suka fice daga birnin ba su riga sun yi nisa ba, Yosef ya cewa ma'aikacinsa, "Tashi, ka bi bayan mutanen, idan kuma ka sha kansu, ka ce masu, 'Meyasa kuka maida mugunta domin nagarta?
\v 5 Wannan ba kofin da maigidana ke sha bane, kofin da yake amfani da shi domin sihiri? Kun yi mugunta, wannan abin da kuka yi."'
\s5
\v 6 Ma'aikacin ya sha kansu ya kuma faɗi waɗannan maganganu a gare su.
\v 7 Suka ce masa, "Meyasa shugabana yake faɗin waɗannan maganganu haka? Bari ya yi nesa daga bayinka da zasu aikata irin wannan.
\s5
\v 8 Duba, kuɗaɗen da muka samu a bakin buhunanmu, mun sake kawo maka su daga ƙasar Kan'ana. Ta yaya daga nan zamu yi sãtar azurfa ko zinariya daga gidan shugabanmu?
\v 9 Duk wanda aka same shi a wurinsa daga cikin bayinka, bari ya mutu, mu kuma zamu zama bayin shugabana."
\v 10 Ma'aikacin yace, "Yanzu kuma bari ya kasance bisa ga maganganunku. Shi wanda aka sami kofin a wurinsa zai zama bawana, ku kuma sauran zaku fita daga zargi."
\s5
\v 11 Daga nan kowanne mutum ya yi hanzari ya sauko da buhunsa ƙasa, kowanne mutum kuma ya buɗe buhunsa.
\v 12 Ma'aikacin ya bincike. Ya fãra da babban ya kuma ƙarashe da ƙaramin, aka kuma sami kofin a buhun Benyamin.
\v 13 Daga nan suka kece tufafinsu. Kowanne mutum ya ɗora kaya a jakinsa suka kuma dawo cikin birni.
\s5
\v 14 Yahuda da 'yan'uwansa suka zo gidan Yosef. Har yanzu yana nan, suka kuma rusuna a gabansa har ƙasa.
\v 15 Yosef yace masu, "Mene ne kuka yi haka? Ba ku san cewa mutum kamar ni ina aikata sihiri ba?"
\s5
\v 16 Yahuda yace, "Me za mu cewa shugabana? Me za mu faɗa? Ko yaya zamu baratar da kanmu? Allah ya gãno laifin bayinka. Duba, mu bayin shugabana ne, dukkan mu da wanda aka iske kofin a hannunsa." Yosef yace,
\v 17 "Bari yayi nesa da ni da in aikata haka. Mutumin da aka iske kofin a hannunsa, wannan taliki zai zama bawana, amma game da ku sauran, ku tafi cikin salama ga mahaifinku."
\s5
\v 18 Daga nan Yahuda ya matso kusa da shi ya kuma ce, "Shugabana, na roƙe ka bari bawanka ya faɗi magana cikin kunnuwan shugabana, bari kuma fushinka ya yi ƙuna gãba da bawanka, domin kamar dai Fir'auna kake.
\v 19 Shugabana ya tambayi bayinsa, cewa, 'Kuna da mahaifi ko ɗan'uwa?'
\s5
\v 20 Muka cewa shugabana, 'Muna da mahaifi, tsohon mutum, kuma da ɗan tsufansa, ƙarami ne. Amma ɗan'uwansa ya mutu, shi kaɗai kuma ya rage ga mahaifiyarsa, kuma mahaifinsa na ƙaunarsa.'
\v 21 Daga nan ka cewa bayinka, 'Ku kawo shi nan a gare ni domin in gan shi.'
\v 22 Bayan haka, muka cewa shugabana, 'Yaron ba zai iya barin mahaifinsa ba. Domin idan har ya bar mahaifinsa to mahaifinsa zai mutu.'
\s5
\v 23 Daga nan ka cewa bayinka, 'Har sai ƙaramin ɗan'uwanku ya zo tare da ku, ba zaku sake ganin fuskata ba.'
\v 24 Daga nan ya kasance sa'ad da muka tafi wurin bawanka mahaifina, muka faɗi masa maganganun shugabana.
\v 25 Mahaifinmu yace, 'Ku sake komawa, ku sawo mana ɗan abinci.'
\v 26 Daga nan muka ce, 'Ba za mu iya komawa ba. Idan ƙaramin ɗan'uwanmu yana tare da mu, daga nan zamu gangara mu tafi, domin ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba har sai ƙaramin ɗan'uwanmu yana tare da mu.'
\s5
\v 27 Bawanka mahaifina ya ce mana, 'Kun san cewa matata ta haifa mani 'ya'ya maza biyu.
\v 28 Ɗaya daga cikin su ya fita daga gare ni kuma na ce, "Tabbas an yage shi gutsu-gutsu, ban sake ganin sa ba kuma tuni."
\v 29 Yanzu idan kuka sake ɗauke wannan daga gare ni, kuma bala'i ya zo masa, zaku gangarar da furfurata da baƙinciki zuwa Lahira.'
\s5
\v 30 Yanzu, saboda haka, sa'ad dana koma wurin bawanka mahaifina, kuma saurayin baya tare da mu, tun da rayuwarsa ɗaure take da rayuwar yaron,
\v 31 zai kasance, sa'ad da ya ga yaron ba ya tare da mu, zai mutu. Bayinka zasu gangara da furfurar bawanka mahaifinmu da baƙinciki zuwa Lahira.
\v 32 Gama bawanka ya zama wanda ya tsaya domin yaron ga mahaifina na kuma ce, 'Idan ban maido maka da shi ba, daga nan zan ɗauki laifin ga mahaifina har abada."
\s5
\v 33 Saboda haka yanzu, ina roƙon ka bari bawanka ya tsaya a maimakon yaron a matsayin bawan shugabana, bari kuma yaron ya tafi tare da 'yan'uwansa.
\v 34 Gama ta yaya zan tafi wurin mahaifina idan yaron ba ya tare da ni? Ina tsoron in ga mugun abin da zai zo bisa mahaifina."
\s5
\c 45
\cl Sura 45
\p
\v 1 Daga nan Yosef bai iya kame kansa ba a gaban dukkan bayin dake tsaye a gefensa. Ya ce da ƙarfi, "Kowa ya bar ni tilas. "Babu bawan da ya tsaya a gefensa sa'ad da Yosef ya sanar da kansa ga 'yan'uwansa.
\v 2 Ya yi kuka da ƙarfi, Masarawa suka ji, gidan Fir'auna kuma suka sami labari.
\v 3 Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ni ne Yosef. Har yanzu mahaifina nada rai?" 'Yan'uwansa ba su iya amsa masa ba, domin sun gigice a gabansa.
\s5
\v 4 Daga nan Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ku zo kusa da ni, ina roƙon ku." Suka zo kusa da shi. Ya ce, "Ni ne Yosef ɗan'uwanku, wanda kuka sayar zuwa cikin Masar.
\v 5 Kada kuyi baƙinciki ko kuji haushin kanku saboda kun sayar da ni zuwa nan, domin Allah ya aiko ni ne gaba da ku saboda a ceci rai.
\v 6 Domin shekaru biyu kenan yunwa na cikin ƙasar, har yanzu kuma akwai shekaru biyar inda ba za a yi huɗa ko girbi ba.
\s5
\v 7 Allah ya aiko ni gaba da ku domin ya adana ku a matsayin ragowa a duniya, ya kuma ajiye ku da rai ta wurin babbar kuɓutarwa.
\v 8 Saboda haka yanzu ba ku ne kuka aiko ni nan ba amma Allah ne, kuma ya maida ni uba ga Fir'auna, shugaban dukkan gidansa, kuma mai mulki a cikin dukkan ƙasar Masar.
\s5
\v 9 Ku yi hanzari ku tafi wurin mahaifina ku ce masa, 'Wannan ne abin da ɗanka Yosef yace, "Allah ya maida ni shugaban dukkan Masar. Ka gangaro zuwa gare ni, kada ka yi jinkiri.
\v 10 Zaka zauna a ƙasar Goshen, zaka kuma kasance kusa da ni, kai da 'ya'yanka da 'ya'yan 'ya'yanka, da garkunan tumakinka dana awaki da garkunan shanunka, da dukkan abin da kake da shi.
\v 11 Zan biya buƙatunka a can, domin har yanzu akwai shekaru biyar na yunwa, domin kada ku kai ga talaucewa, kai, da gidanka, da dukkan abin da kake da shi."'
\s5
\v 12 Duba, idanunku sun ga ni, da idanun ɗan'uwanku Benyamin, cewa bakina ne ya yi magana da ku.
\v 13 Zaku gayawa mahaifina game da dukkan ɗaukakata a Masar da dukkan abin da kuka gani. Zaku yi hanzari ku kawo mahaifina a nan."
\s5
\v 14 Ya rungume wuyan ɗan'uwansa Benyamin ya kuma yi kuka, Benyamin kuma ya yi kuka a wuyansa.
\v 15 Ya sumbaci dukkan 'yan'uwansa kuma ya yi kuka a kansu. Bayan wannan 'yan'uwansa suka yi magana da shi.
\s5
\v 16 Aka faɗi labarin al'amarin a gidan Fir'auna: "'Yan'uwan Yosef sun zo." Abin ya gamshi Fir'auna da bayinsa sosai.
\v 17 Fir'auna ya cewa Yosef, "Ka cewa 'yan'uwanka, 'Ku yi haka: Ku yi wa dabbobinku kaya ku kuma tafi ƙasar Kan'ana.
\v 18 Ku ɗauko mahaifinku da gidanku dukka ku kuma zo wurina. Zan baku nagartar ƙasar Masar, kuma zaku ci dausayin ƙasar.'
\s5
\v 19 Yanzu an umarce ku, 'Ku yi haka, ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'ya'yanku domin matayenku kuma. Ku kuma ɗauko mahaifinku ku zo.
\v 20 Kada ku damu da mallakokinku, domin nagartar dukkan ƙasar Masar taku ce."'
\s5
\v 21 'Ya'ya maza na Isra'ila suka yi haka. Yosef ya basu kekunan shanu, bisa ga dokar Fir'auna, ya kuma basu guzuri domin tafiyar.
\v 22 Ga dukkan su ya ba kowanne mutum canjin tufafi, amma ga Benyamin ya bayar da azurfa ɗari uku da canjin tufafi biyar.
\v 23 Ya aika wannan domin mahaifinsa: jakuna goma ɗauke da kyawawan abubuwan Masar; da matan jakuna goma ɗauke da hatsi, gurasa, da sauran kayan masarufi domin mahaifinsa domin tafiyar.
\s5
\v 24 Sai ya sallami 'yan'uwansa suka kuma yi tafiyarsu. Ya ce masu, "Ku tabbatar cewa ba ku yi faɗa ba a kan hanya."
\v 25 Suka tafi daga Masar suka zo ƙasar Kan'ana, ga Yakubu mahaifinsu.
\v 26 Suka gaya masa cewa, "Yosef yana nan da rai, kuma shi ne shugaba bisa dukkan ƙasar Masar." Zuciyarsa ta yi mamaki, domin bai gaskata da abin da suka faɗa masa ba.
\s5
\v 27 Suka gaya masa dukkan maganganun Yosef da ya faɗi masu. Sa'ad da Yakubu ya ga kekunan shanun da Yosef ya aiko su da su, ruhun Yakubu mahaifinsu ya farfaɗo.
\v 28 Isra'ila yace, "Ya isa. Yosef ɗana yana nan da rai. Zan tafi in gan shi kafin in mutu."
\s5
\c 46
\cl Sura 46
\p
\v 1 Isra'ila ya kama hanyarsa da dukkan abin da yake da shi, ya kuma tafi Bayersheba. A can ya miƙa hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.
\v 2 Allah ya yi magana da Isra'ila a cikin wahayi da dare, cewa, "Yakubu, Yakubu." Ya ce, "Ga ni nan."
\v 3 Ya ce, "Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron gangarawa zuwa Masar, domin a can zan maida kai babbar al'umma.
\v 4 Zan gangara da kai zuwa cikin Masar, kuma tabbas zan sake hawo da kai kuma Yosef zai rufe idanunka da hannunsa."
\s5
\v 5 Yakubu ya taso daga Bayersheba. 'Ya'yan Isra'ila suka tafi da Yakubu mahaifinsu, 'ya'yansu, da matayensu, a cikin kekunan shanun da Fir'auna ya aiko a ɗauke shi.
\v 6 Suka ɗauki dabbobinsu da mallakarsu da suka tattara a ƙasar Kan'ana. Suka zo cikin Masar, Yakubu da dukkan zuriyarsa tare da shi.
\v 7 Ya taho Masar tare da 'ya'yansa maza da 'ya'yan 'ya'yansa maza, da 'ya'yansa mata da 'ya'yan 'ya'yansa mata, da dukkan zuriyarsa.
\s5
\v 8 Waɗannan ne sunayen 'ya'yan Isra'ila waɗanda suka zo Masar: Yakubu da 'ya'yansa, Ruben, ɗan fãrin Yakubu;
\v 9 'ya'yan Ruben, Hanok, Fallu, Hezron, da Karmi;
\v 10 'ya'yan Simiyon, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar, da Shawul, ɗan Bakan'aniya;
\v 11 'ya'yan Lebi kuma, Gashon, Kohat, da Merari.
\s5
\v 12 'Ya'yan Yahuda su ne Er, Onan, Shela, Ferez, da Zera, (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Ferez su ne Hezron da Hamul.
\v 13 'Ya'yan Issaka su ne Tola, Fuwa, Lob, da Shimron;
\v 14 'ya'yan Zebulun sune Sered, Elon, da Yalil
\v 15 Waɗannan ne 'ya'yan Liya waɗanda ta haifa wa Yakubu a Faddan Aram, tare da ɗiyarsa Dina. Lissafin 'ya'yansa maza da mata talatin da uku.
\s5
\v 16 'Ya'yan Gad su ne Zefon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi, da Areli.
\v 17 'Ya'yan Asha su ne Imna, Ishba, Ishbi, da Beriya; kuma Sera ce 'yar'uwarsu. 'Ya'yan Beriya su ne Heba da Malkiyel
\v 18 Waɗannan ne 'ya'yan Zilfa, wadda Laban ya bayar ga ɗiyarsa Liya. Waɗannan 'ya'ya ta haifa wa Yakubu - sha shida dukka dukkansu.
\s5
\v 19 'Ya'yan Rahila matar Yakubu su ne Yosef da Benyamin.
\v 20 A Masar Asenat ɗiyar Fotifera firist na On, ta haifa wa Yosef Manasse da Ifraim.
\v 21 'Ya'yan Benyamin su ne Bela, Beka, Ashbel, Gera, Na'aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim, da Ard.
\v 22 Waɗannan ne 'ya'yan Rahila da aka haifa wa Yakubu - sha huɗu dukkan su.
\s5
\v 23 Ɗan Dan shi ne Hushim.
\v 24 'Ya'yan Naftali su ne Yaziyel, Guni, Yeza, da Shillem.
\v 25 Waɗannan ne 'ya'yan da Bilha ta haifa wa Yakubu, wadda Laban ya bayar ga Rahila ɗiyarsa - bakwai dukka dukkansu.
\s5
\v 26 Dukkan waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, waɗanda ke zuriyarsa, ba a ƙidaya da matayen 'ya'yan Yakubu ba, su sittin da shida ne dukkansu.
\v 27 Tare da 'ya'yan Yosef maza biyu da aka haifa masa a Masar, yawan iyalinsa da suka tafi Masar su saba'in ne dukkansu.
\s5
\v 28 Yakubu ya aiki Yahuda zuwa ga Yosef saboda ya nuna masa hanya a gabansa ta zuwa Goshen, suka kuma zo ƙasar Goshen.
\v 29 Yosef ya shirya karusarsa ya kuma tafi domin ya sami Isra'ila mahaifinsa a Goshen. Ya gan shi, ya rungumi wuyansa, ya kuma yi kuka na dogon lokaci bisa wuyansa.
\v 30 Isra'ila yace wa Yosef, "Yanzu bari in mutu, tunda na ga fuskarka, cewa kana nan da rai."
\s5
\v 31 Yosef ya cewa 'yan'uwansa da gidan mahaifinsa, "Zan tafi in gaya wa Fir'auna, cewa, "Yan'uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina.
\v 32 Mutanen makiyaya ne, domin suna kiwon dabbobi ne. Sun kawo garkunan tumakinsu dana awakinsu, da garkunan shanunsu, da dukkan abin da suke da shi.'
\s5
\v 33 Zai kasance, sa'ad da Fir'auna zai kira ku ya yi tambaya, 'Mene ne sana'arku?'
\v 34 To zaku ce masa, 'Bayinka masu kiwon dabbobi ne tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yanzu, dukkanmu, da ubanninmu.' Ku yi haka domin ku zauna a ƙasar Goshen, domin kowanne makiyayi haramtacce ne ga Masarawa."
\s5
\c 47
\cl Sura 47
\p
\v 1 Daga nan Yosef ya shiga ya gaya wa Fir'auna, "Mahaifina da 'yan'uwana, da garkunan tumakinsu da na awaki, da garkunan shanunsu, da dukkan abin da ke nasu, sun iso daga ƙasar Kan'ana. Duba, suna ƙasar Goshen."
\v 2 Ya ɗauki biyar daga cikin 'yan'uwansa ya kuma gabatar da su ga Fir'auna.
\s5
\v 3 Fir'auna ya cewa 'yan'uwansa, "Mene ne sana'arku?" Suka cewa Fir'auna, "Bayinka makiyaya ne, kamar kakanninmu."
\v 4 Daga nan suka cewa Fir'auna, "Mun zo ɗan zama ne a ƙasar. Babu makiyaya domin garkunan bayinka, saboda yunwar ta yi tsanani a ƙasar Kan'ana. To yanzu, muna roƙonka bari bayinka su zauna a ƙasar Goshen."
\s5
\v 5 Daga nan Fir'auna ya yi magana da Yosef, ya ce, "Mahaifinka da 'yan'uwanka sun zo wurinka.
\v 6 Ƙasar Masar na gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a lardi mafi kyau, ƙasar Goshen. Idan ka san maza ƙwararru daga cikinsu, ka sanya su kiwon dabbobi na."
\s5
\v 7 Daga nan Yosef ya shigo da Yakubu mahaifinsa ya kuma gabatar da shi ga Fir'auna. Yakubu ya albarkaci Fir'auna.
\v 8 Fir'auna ya cewa Yakubu, "Tsawon rayuwarka nawa?"
\v 9 Yakubu ya cewa Fir'auna, "Shekarun yawace-yawace na ɗari ne da talatin. Shekarun rayuwata kima ne kuma cike da wahala. Ba su kai yawan na kakannina ba."
\v 10 Daga nan Yakubu ya albarkaci Fir'auna ya kuma fita daga gabansa.
\s5
\v 11 Daga nan Yosef ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa. Ya ba su gunduma a ƙasar Masar, yankin ƙasar mafi kyau, a ƙasar Ramesis, kamar yadda Fir'auna ya umarta.
\v 12 Yosef ya wadata abinci domin mahaifinsa, da 'yan'uwansa, da dukkan gidan mahaifinsa, bisa ga lissafin masu dogara da su.
\s5
\v 13 Yanzu dai babu abinci a dukkan ƙasar; domin yunwar ta yi tsanani. Ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka lalace saboda yunwar.
\v 14 Yosef ya tattara dukkan kuɗaɗen dake ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana, ta wurin sayar da hatsi ga mazaunan. Daga nan Yosef ya kawo kuɗaɗen fãdar Fir'auna.
\s5
\v 15 Sa'ad da aka gama kashe dukkan kuɗaɗen dake ƙasashen Masar da Kan'ana, dukkan Masarawa suka zo wurin Yosef suka ce, "Ka bamu abinci! Ya ya zamu mutu a gabanka saboda kuɗaɗenmu sun ƙare?"
\v 16 Yosef yace, "Idan kuɗaɗenku sun ƙare, ku kawo dabbobinku ni zan kuma baku abinci misanya domin dabbobinku."
\v 17 Sai suka kawo dabbobinsu wurin Yosef. Yosef ya basu abinci misanya domin dawakai, domin garkunan tumaki da awaki, domin garkunan shanu, domin kuma jakuna. A wannan shekarar ya ciyar dasu da abinci a misanyar dukkan dabbobinsu.
\s5
\v 18 Sa'ad da shekara ta ƙare, suka zo wurinsa a shekara ta gaba suka kuma ce masa, "Ba zamu ɓoye ba daga shugabanmu cewa kuɗaɗenmu sun tafi, kuma garkunan shanun na shugabanmu ne. Babu abin da ya rage a idanun shugabana, sai jikkunanmu kawai da ƙasarmu.
\v 19 Yaya zamu mutu a gaban idanunka, dukkanmu da ƙasarmu? Ka saye mu da ƙasarmu a musanya domin abinci, mu da ƙasarmu mu zama bayi ga Fir'auna. Ka bamu iri domin mu rayu kada mu mutu, kada kuma ƙasar ta zama kufai."
\s5
\v 20 Saboda haka Yosef ya saye wa Fir'auna dukkan ƙasar Masar. Domin kowanne Bamasare ya sayar da gonarsa, saboda yunwar ta yi tsanani sosai. Ta wannan hanya, ƙasar ta zama ta Fir'auna.
\v 21 Game da mutanen, ya mayar dasu bayi daga ƙarshen kan iyakar Masar zuwa ɗaya ƙarshen.
\v 22 Ƙasar firistoci ce kawai Yosef bai saya ba, saboda ana ba firistocin albashi. Suna ci daga kason da Fir'auna yake ba su. Saboda haka basu sayar da gonarsu ba.
\s5
\v 23 Daga nan Yosef ya cewa mutanen, "Duba, na saye wa Fir'auna ku da ƙasarku. Yanzu ga iri domin ku, zaku kuma noma ƙasar.
\v 24 Da kaka tilas ku bada kaso biyar ga Fir'auna, kashi huɗu kuma zai zama naku, domin iri na gonaki domin kuma abinci domin gidajenku da 'ya'yanku."
\s5
\v 25 Suka ce, "Ka ceci rayukanmu. Bari mu sami tagomashi a idanunka. Zamu zama bayin Fir'auna."
\v 26 Sai Yosef ya maida haka doka mai aiki har wayau a ƙasar Masar, cewa kashi biyar na Fir'auna ne. Ƙasar firistoci ce kawai ba ta zama ta Fir'auna ba.
\s5
\v 27 Saboda haka Isra'ila ya zauna a ƙasar Masar, a ƙasar Goshen. Mutanensa suka sami mallakar wurin. Suka hayayyafa suka ruɓanɓanya sosai.
\v 28 Yakubu ya zauna a ƙasar Masar shekaru sha bakwai, saboda haka shekarun rayuwar Yakubu ɗari da arba'in da bakwai ne.
\s5
\v 29 Sa'ad da lokaci ya kusato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yosef yace masa, "Yanzu idan na sami tagomashi a idanunka, ka sanya hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka kuma nuna mani aminci da yarda. Ina roƙon ka kada ka bizne ni a Masar.
\v 30 Sa'ad da na yi barci da ubannina, zaka ɗauke ni ka fitar da ni daga Masar ka kuma bizne ni a maƙabartar kakannina." Yosef yace, "Zan yi yadda ka ce."
\v 31 Isra'ila yace, "Ka rantse mani," Yosef kuma ya rantse masa. Daga nan Isra'ila ya rusuna a bisa kan gadonsa.
\s5
\c 48
\cl Sura 48
\p
\v 1 Sai ya kasance bayan waɗannan abubuwa, sai wani ya cewa Yosef, "Duba, mahaifinka bai da lafiya." Sai ya ɗauki 'ya'yansa maza biyu tare da shi, Manasse da Ifraim.
\v 2 Sa'ad da aka gaya wa Yakubu, "Duba, ɗanka Yosef ya iso ya ganka," Isra'ila ya ƙoƙarta kuma ya zauna bakin gado.
\s5
\v 3 Yakubu ya cewa Yosef, "Allah maɗaukaki ya bayyana a gare ni a Luz cikin ƙasar Kan'ana.
\v 4 Ya albarkace ni ya kuma ce mani, 'Duba, zan sa ka hayayyafa, ka kuma ruɓanɓanya. Zan maida kai taron al'ummai. Zan bayar da wannan ƙasar ga zuriyarka a matsayin madawwamiyar mallaka.'
\s5
\v 5 Yanzu 'ya'yanka biyu maza, waɗanda aka haifa maka a ƙasar Masar kafin in zo wurinka a Masar, nawa ne. Ifraim da Manasse zasu zama nawa, kamar yadda Ruben da Simiyon suke nawa.
\v 6 'Ya'yan da zaka haifa bayan su zasu zama naka; za a lissafa su ƙarƙashin sunayen 'yan'uwansu a cikin gãdonsu.
\v 7 Amma game da ni, sa'ad dana zo daga Faddan, cikin baƙincikina Rahila ta mutu a ƙasar Kan'ana a kan hanya, yayin da da sauran tazara a isa Ifrat. Na bizne ta a nan a kan hanyar zuwa Ifrat" (wannan ce, Betlehem).
\s5
\v 8 Sa'ad da Isra'ila ya ga 'ya'yan Yosef maza, ya ce, "Na wane ne waɗannan?"
\v 9 Yosef yace wa mahaifinsa, "'Ya'yana ne, waɗanda Allah ya bani a nan." Isra'ila yace, "Kawo su wurina, domin in sa masu albarka."
\v 10 Yanzu dai idanun Isra'ila na kasawa saboda shekarunsa, har baya iya gani. Sai Yosef ya kawo su kusa da shi, kuma ya sumbace su ya kuma rungume su.
\s5
\v 11 Isra'ila ya cewa Yosef, "Banyi tsammanin zan sa ke ganin fuskarka ba, amma Allah ya bar ni inga 'ya'yanka ma."
\v 12 Yosef ya fito da su daga tsakanin guiwoyin Isra'ila, Daga nan kuma ya rusuna da fuskarsa ƙasa.
\v 13 Yosef ya ɗauke su biyun, Ifraim a hannun damansa zuwa hannun hagun Isra'ila, Manasse kuma a hannun hagunsa zuwa hannun damar Isra'ila, ya kuma matso da su kusa da shi.
\s5
\v 14 Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama ya kuma ɗora bisa kan Ifraim, wanda shi ne ƙarami, hannun hagunsa kuma bisa kan Manasse. Ya gitta hannuwansa, domin Manasse shi ne ɗan fãri.
\v 15 Isra'ila ya albarkaci Yosef, yana cewa, "Allah wanda a gabansa ubannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allah wanda ya lura da ni har ya zuwa yau,
\v 16 mala'ikan da ya kiyaye ni daga dukkan bala'i, bari ya albarkaci waɗannan samari. Bari a raɗa sunana a sunansu, da sunan ubannina Ibrahim da Ishaku. Bari su yaɗu su yi tururu a bisa duniya."
\s5
\v 17 Sa'ad da Yosef ya ga cewa mahaifinsa ya ɗora hannunsa na dama bisa kan Ifraim, bai ji daɗi ba. Ya ɗauke hannun mahaifinsa domin ya matsa da shi daga bisa kan Ifraim zuwa bisa kan Manasse.
\v 18 Yosef yace wa mahaifinsa, "Ba haka ba, babana; domin wannan shi ne ɗan fãrin. Ka ɗora hannunka na dama bisa kansa."
\s5
\v 19 Mahaifinsa ya ƙi ya kuma ce, "Na sani, ɗana, Na sani. Shi ma zai zama jama'a, shima kuma zai zama babba. Duk da haka ƙanensa zai fi shi girma, kuma zuriyarsa zasu zama al'ummai tururu."
\v 20 Isra'ila ya albarkace su a wannan rana da waɗannan maganganu, "Mutanen Isra'ila zasu furta albarku da sunayenku suna cewa, 'Bari Allah ya maida ku kamar Ifraim kamar Manasse kuma'." Ta wannan hanya, Isra'ila ya sanya Ifraim gaba da Manasse.
\s5
\v 21 "Isra'ila ya cewa Yosef, "Duba, ina gaf da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku, zai kuma maida ku ƙasar ubanninku.
\v 22 Game da kai, a matsayin wanda aka ɗora sama da 'yan'uwansa, Na baka gangaren tsaunin dana karɓe daga hannun Amoriyawa da takobina da kuma bakana."
\s5
\c 49
\cl Sura 49
\p
\v 1 Daga nan Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya kuma ce: "Ku tattara kanku tare, domin in gaya maku abin da zai faru daku a gaba.
\v 2 Ku tattara kanku ku kuma saurara, ku 'ya'yan Yakubu. Ku saurari Isra'ila, mahaifinku.
\s5
\v 3 Ruben, kai ne ɗan fãrina, ƙarfina, da farkon ƙarfina, ka yi fice wajen jamali, ka kuma yi fice wajen iko.
\v 4 Marar kamewa kamar ruwan dake ambaliya, ba zaka yi muhimmanci ba, saboda ka hau bisa gadon mahaifinka. Daga nan ka gurɓata shi; ka hau bisa gadona.
\s5
\v 5 Simiyon da Lebi 'yan'uwa ne. Makaman ta'addanci ne takubbansu.
\v 6 Ya raina, kada ka zo cikin shawararsu; kada ka shiga cikin taruwarsu, domin zuciyata ta fi haka daraja sosai. Domin cikin fushinsu sun kashe mutane. Saboda annashuwa ne suka turke shanu.
\s5
\v 7 Bari fushinsu ya la'ana, domin mai zafi ne - hasalarsu kuma domin mai tsanani ce. Zan rarraba su a Yakubu in kuma warwatsa su a Isra'ila.
\s5
\v 8 Yahuda, 'yan'uwanka zasu yabe ka. Hannunka zai kasance bisa wuyan maƙiyanka. 'Ya'yan mahaifinka za su rusuna a gabanka.
\s5
\v 9 Yahuda ɗan zaki ne. Ɗana, ka haura daga kamammunka. Ka duƙa, ka rarrafa kamar zaki, kamar zakanya. Wa zai kuskura ya tada kai?
\s5
\v 10 Sandan sarauta ba za ta fita daga Yahuda ba, ko sandar mulki daga tsakanin ƙafafunsa, har sai Shilo ya zo. Al'ummai zasu yi masa biyayya.
\s5
\v 11 Yana ɗaure jakinsa ga kuringar inabinsa, da ɗan jakinsa ga zaɓaɓɓiyar kuringar inabinsa, ya wanke tufafinsa cikin ruwan inabi, da alkyabbarsa cikin jinin inabi.
\v 12 Idanunsa zasu yi duhu kamar ruwan inabi, haƙoransa kuma farare kamar madara.
\s5
\v 13 Zebulun zai zauna a gaɓar teku. Zai zama masaukin jiragen ruwa, kuma kan iyakarsa za ta zarce har zuwa Sidon.
\s5
\v 14 Issaka jaki ne mai ƙarfi, yana zaune a tsakiyar turakun tumaki.
\v 15 Yana ganin wurin hutawa mai kyau da ƙasa mai gamsarwa. Zai sunkuyar da kafaɗarsa domin kaya ya kuma zama bawa domin hidimar.
\s5
\v 16 Dan zai hukunta mutanensa a matsayin ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila.
\v 17 Dan zai zama maciji a gefen hanya, maciji mai dafi a tafarki dake cizon kofaton doki, saboda mahayinsa ya fãɗi ta baya.
\v 18 Ina jiran cetonka, Yahweh.
\s5
\v 19 Gad - mahaya zasu kai masa hari, amma zai kai masu hari ta diddigensu.
\v 20 Abincin Asha zai zama wadatacce, zai kuma bayar da girke-girken sarauta.
\v 21 Naftali sakakkiyar barewa ce; zai haifi kyawawan 'ya'ya.
\s5
\v 22 Yosef mai hayayyafa ne, mai bayar da 'ya'ya ne, mai bayar da 'ya'ya dake gefen ƙorama wanda rassansa ke hawan katanga.
\v 23 Maharba zasu kai masa hari, su kuma harbe shi, su firgita shi.
\s5
\v 24 Amma bakansa zai tsaya dai-dai, kuma hannayensa zasu ƙware saboda hannayen Mai Iko na Yakubu, saboda sunan Makiyayi, Dutsen Isra'ila.
\s5
\v 25 Allah na mahaifinka zai taimakeka kuma Allah Mai Iko Dukka zai albarkace ka da albarkun sararin sama, albarkun zurfafa dake kwance ƙarƙashin ƙasa, da albarkun nonna da mahaifa.
\s5
\v 26 Albarkun mahaifinka sun fi albarkun duwatsun zamanin dã ko abubuwan marmari na tuddan dã. Bari su kasance bisa kan Yosef, har bisa rawanin dake kan yariman 'yan'uwansa.
\s5
\v 27 Benyamin damisa ne mayunwaci. Da safe zai lanƙwame kamammensa, da yamma kuma zai raba ganimarsa."
\s5
\v 28 Waɗannan ne kabilu sha biyu na Isra'ila. Wannan ne abin da mahaifinsu ya ce masu sa'ad da ya albarkace su. Kowannen su ya albarkace shi bisa ga albarkar da ta dace.
\v 29 Daga nan ya umarce su ya ce masu, "Ina gaf da tafiya ga mutanena. Ku bizne ni tare da kakannina a kogon dake cikin gonar Ifron Bahittiye,
\v 30 a cikin kogon dake cikin gonar Makfela, wadda ke kusa da Mamri a ƙasar Kan'ana, gonar da Ibrahim ya saya a matsayin maƙabarta daga hannun Ifron Bahittiye.
\s5
\v 31 A nan ne aka bizne Ibrahim da matarsa Saratu; a nan ne suka bizne Ishaku da matarsa Rebeka; a nan ne kuma na bizne Liya.
\v 32 Gonar da kogon dake cikin ta an saye su ne daga mutanen Het."
\v 33 Da Yakubu ya gama waɗannan umarnai ga 'ya'yansa, ya ja ƙafafunsa cikin gadonsa, ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma tafi wurin mutanensa.
\s5
\c 50
\cl Sura 50
\p
\v 1 Daga nan Yosef ya rikice, ya faɗi bisa fuskar mahaifinsa, ya kuma yi kuka a bisansa, ya kuma sumbace shi.
\v 2 Yosef ya umarci bayinsa masu ilimin magani su nannaɗe mahaifinsa. Masu ilimin maganin suka nannaɗe Isra'ila da maganin hana ruɓewa.
\v 3 Suka ɗauki kwana arba'in, domin wannan ne tsawon lokaci idan an naɗe gawa. Masarawa suka yi masa kuka na kwana saba'in.
\s5
\v 4 Da kwanakin makoki suka cika, Yosef ya yi magana da gidan Fir'auna, cewa, "Idan yanzu na sami tagomashi a idanunku, ina roƙonku ku yi magana da Fir'auna, ku ce,
\v 5 'Mahaifina yasa in yi rantsuwa, cewa, "Duba, ina gaf da mutuwa. Ka bizne ni a kabarin dana gina domin kaina a ƙasar Kan'ana. A can zaka bizne ni." Yanzu bari in haye in tafi, in kuma bizne mahaifina, daga nan kuma zan dawo."'
\v 6 Fir'auna ya amsa, "Ka tafi ka bizne mahaifinka, kamar yadda yasa ka yi rantsuwa."
\s5
\v 7 Yosef ya haye ya tafi bizne mahaifinsa. Dukkan 'yan majalisar Fir'auna suka tafi tare da shi - dattawan gidansa, dukkan manyan masu gari na ƙasar Masar,
\v 8 tare da dukkan gidan Yosef da 'yan'uwansa, da gidan mahaifinsa. Amma 'ya'yansu, da garkunan tumakinsu, dana awaki, da garkunan shanunsu aka bari a ƙasar Goshen.
\v 9 Karusai da mahaya dawaki suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiyar mutane ce sosai.
\s5
\v 10 Sa'ad da suka iso bakin masussukar Atad a ɗayan gefen Yodan, suka yi makoki da babban makoki da baƙinciki mai tsanani. A can Yosef ya yi makokin kwana bakwai domin mahaifinsa.
\v 11 Sa'ad da mazauna ƙasar, Kan'aniyawa, suka ga makokin a masussukar Atad, suka ce, "Wannan taro ne na baƙinciki sosai ga Masarawa." Shi yasa ake kiran wurin da suna Abel Mizrayim, wanda ke tsallaken Yodan.
\s5
\v 12 Daga nan 'ya'yan Yakubu suka yi masa kamar yadda ya umarta.
\v 13 'Ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana suka kuma bizne shi a kogon cikin gonar Makfela, kusa da Mamri. Ibrahim ya sayi kogon tare da gonar a matsayin maƙabarta. Ya saya ne daga Ifron Bahittiye.
\v 14 Bayan da Yosef ya bizne mahaifinsa, sai ya koma cikin ƙasar Masar, shi, tare da 'yan'uwansa, da dukkan waɗanda suka raka shi bizne mahaifinsa.
\s5
\v 15 Sa'ad da 'yan'uwan Yosef suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, suka ce, "To idan Yosef ya riƙe mu da fushi gãba da mu fa, kuma yana so ya yi mana cikakkiyar sakayya domin dukkan muguntar da muka yi masa?"
\v 16 Sai suka umarci kasancewar Yosef, suka ce, "Mahaifinka ya bada umarni kafin ya mutu, cewa,
\v 17 'Ku gaya wa Yosef haka, "Mu na roƙonka ka gafarta laifin 'yan'uwanka da zunubinsu sa'ad da suka yi maka mugunta."' Yanzu muna roƙonka ka gafartawa bayin Allah na mahaifinka. Yosef ya yi kuka sa'ad da suka yi masa magana.
\s5
\v 18 'Yan'uwansa kuma suka zo suka kwanta fuska ƙasa a gabansa. Suka ce, "Duba, mu bayinka ne."
\v 19 Amma Yosef ya amsa masu, "Kada ku ji tsoro. Ina gurbin Allah ne?
\v 20 Game da ku, kun yi niyyar mugunta a gare ni, amma Allah ya yi niyyar alheri ne, saboda a adana rayuwar mutane da yawa, kamar yadda kuka gani a yau.
\v 21 Saboda haka, yanzu kada ku ji tsoro. Zan tanada maku da ƙananan 'ya'yanku." Ya ta'azantar dasu ta wannan hanyar ya kuma yi maganar mutunci ga zukatansu.
\s5
\v 22 Yosef ya zauna a Masar, tare da iyalin mahaifinsa. Ya yi rayuwa shekaru ɗari da goma.
\v 23 Yosef ya ga 'ya'yan Ifraim har zuwa tsara ta uku. Ya kuma ga 'ya'yan Makir ɗan Manasse, waɗanda aka sanya a gwiwoyin Yosef.
\s5
\v 24 Yosef ya cewa 'yan'uwansa, "Ina gaf da mutuwa; amma tabbas Allah zai zo gare ku, ya kuma bida ku hayewa daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse zai ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu."
\v 25 Daga nan Yosef ya sa mutanen Isra'ila suka rantse da alƙawari. Ya ce, "Tabbas Allah zai zo gare ku. A wannan lokacin tilas ku ɗauki ƙasusuwana daga nan."
\v 26 Sai Yosef ya mutu, da shekaru 110. Aka nannaɗe shi da maganin hana ruɓa, kuma aka ajiye shi cikin akwati.