23 lines
1.0 KiB
Markdown
23 lines
1.0 KiB
Markdown
# makoki, masu makoki, kuka
|
||
|
||
## Ma'ana
|
||
|
||
Wannan furci "makoki" manufarsa shi ne nuna baƙinciki yawancin lokaci a mutuwar wani mutum.
|
||
|
||
* A cikin al'adu da yawa, makoki ya ƙunshi yin wasu abubuwa a sarari da zai nuna baƙinciki da damuwa.
|
||
* Isra'ilawa da sauran mutane a zamanin dã sukan nuna makokinsu ta wurin kwala ihu da kururuwa. Sukan sa kaya mararsa kintsi da aka yi da tsummokara su kuma baɗa toka a kawunansu.
|
||
* Gwanayen makoki, yawancin lokaci mata ne da ake biyan su, za su saka kururuwa suyi kuka mai zafi daga lokacin mutuwar har bayan an bizne gawar a kabari.
|
||
* Ƙayadadden lokacin makoki kwana bakwai ne, amma zai iya zarcewa har kwana talatin (kamar na Musa da Haruna) ko kwana sabba'in (kamar na Yakubu).
|
||
* Littafi Mai Tsarki ya yi magana da misali akan "makoki" domin zunubi. Ya yi magana akan nuna baƙinciki mai zafi domin zunubi yana kawo wa Allah baƙinciki da kuma mutane.
|
||
|
||
|
||
(Hakanan duba: tsummoki, zunubi)
|
||
|
||
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
|
||
|
||
* 1 Sama'ila15:34-35
|
||
* 2 Sama'ila 01:11
|
||
* Farawa 23:02
|
||
* Luka 07:31-32
|
||
* Matiyu 11:17
|