# Asha ## Gaskiya Asha ɗan Yakubu na takwas ne. Zuriyarsa tana ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila wanda kuma ake kira "Asha." * Mahaifiyar Asha ita ce Zilfa, baranyar La'aitu. * Ma'anar sunansa "farinciki, ko "mai albarka." * Asha kuma sunan yankin ƙasar da aka ba kabilar Asha ne lokacin da Isra'ilawa suka shiga ƙasar alƙawari. (Hakanan duba: Isra'ila, kabulu sha biyu na Isra'ila) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Tarihi 02:1-2 * 1 Sarakuna 04:16 * Ezekiyel 48:1-3 * Farawa 30:13 * Luka 02:36-38