# Asaf ## Gaskiya Asaf Ba'lebi ne da baiwar waƙa shi ne ya wallafa muryoyi domin zabura ta Sarki Dauda. Shi ma kansa ya rubuta nasa zaburar. * Sarki Dauda ya naɗa Asaf ya zama ɗaya daga cikin mutum uku mawaƙa waɗanda suke bada waƙoƙin sujada a haikali. Wasu waƙoƙin annabtai ne. * Asaf ya tarbiyar da 'ya'yansa suka kuma ɗauki wannan nawaiya, ta kaɗa kayan waƙoƙi da yin annabci cikin haikali. * Wasu kayan kaɗe-kaɗe na waƙoƙi sun haɗa da su, sarewa, garaya, ƙaho, da molaye. * Zabura 50 da 73-83 ance daga Asaf suke. mai yiwuwa waɗansu daga cikin waƙoƙin nan marubutansu daga cikin iyalinsa ne. (Hakanan duba: zuriya, garaya, sarewa, annabi, zabura, ƙaho) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Tarihi 06:39-43 * 2 Tarihi 35:15 * Nehemiya 02:08 * Zabura 050:1-2