# Mai Tsarki ## Ma'ana Kalmar nan "Mai Tsarki" muƙami ne a cikin Littafi Mai Tsarki har kullum kalmar na nufin Allah. * A cikin Tsohon Alƙawari, wannan muƙamin yakan baiyana a "Mai Tsarki na Isra'ila." * A cikin Sabon Alƙawari, shima Yesu ana kiran sa da "Mai Tsarki." * Kalmar nan "mai tsarki" a wani lokaci ana amfani da ita a ambaci mala'ika. Shawarwarin Fassara: * Ma'anar kalmar nan "Mai Tsarki" a sauƙaƙe ita ce a cikin harsunan kamar hausa kan ce "Ɗaya" ko "Allah." * Wannan kalmar za a fassara ta da "Allah, wanda yake mai tsarki" ko "Keɓaɓɓe." * Kalmar nan za'a iya fassara da "Allah, Mai Tsarki na Isra'ila" za'a fassara ta "Allah Mai Tsarki wanda Isra'ila ke bautawa" ko "Mai Tsarki da ke mulkin Isra'ila." * Ya fi kyau a fassara wannan kalmar ta wurin amfani da kalmar "tsarki." (Hakakan duba: tsarki, Allah) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Yahaya 02:20 * 2 Sarakuna 19:22 * Ayyukan Manzanni 02:27 * Ayyukan Manzanni 03:13-14 * Ishaya 05:15-17 * Ishaya 41:14 * Luka 04:33-34