# Ibraniyanci, Ibraniyawa ## Ma'ana "Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane." * Kalmar nan "Ibraniyanci" zata iya zamaharshen da mutanen Ibraniyawa ke magana da shi. Mafi yawa daga cikin sashe na Littafi Mai Tsarki an rubuta shi ne da harshen Ibraniyanci. * A wurare da bam da ban a cikin Littafi Mai Tsarki, ana kiran Ibraniyawa "Yahudawa" ko "Isra'ilawa." Ya fi kyau a mori waɗannan sunaye guda uku a cikin ayoyin, muddin dai an gane cewa wurin na magana ne akan waɗannan mutanen. (Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 26:12-14 * Farawa 39:13-15 * Farawa 40:15 * Farawa 41:12-13 * Yahaya 05:1-4 * Yahaya 19:13 * Yahaya 01:8-10 * Filibiyawa 03:5