# laifi, yin laifi ## Ma'ana Kalmar nan "laifi" tana nufin yin wani abu dake na zunubi ko kuma taka doka. * A zama "mai laifi" na nufin ayi wani abu ba bisa tsarin rayuwa ba, wato keta dokar Allah. * Kishiyar kalmar "laifi" ita ce "mara laifi." Shawarwarin Fassara: * Waɗansu harsuna na iya fassara "laifi" da "ladan zunubi" ko kuma "ƙirga zunubai." * Hanyoyin fassara ga "zama mai laifi" sun haɗa da faɗar "kalmar da ta zama laifi" ko kuma "yin wani abu wanda bai dace ba" ko kuma "aikata zunubi." (Hakanan duba: mara laifi, laifi na zuci, hukunci, zunubi) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Fitowa 28: 36-38 * Ishaya 06:7 * Yakubu 02:10-11 * Yahaya 19: 4 * Yona 01:14