# Allah ## Ma'ana A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh." * Allah na nan a kullum; ya kasance kafin komai ya kasance kuma zai ci gaba da kasancewa har abada. * Shi ne kaɗai Allah na gaskiya yana kuma da iko akan komai da ke cikin duniya. * Allah cike yake da adalci, mai matuƙar hikima, mai tsarki, marar zunubi, adali, mai jinƙai, da kuma ƙauna. * Shi Allah ne mai riƙe alƙawari, wanda ke cika alƙawarinsa a kullum. * An hallici mutane nedomin su bautawa Allah kuma shi kaɗai za su bautawa. * Allah ya baiyana sunansa da "Yahweh" wanda ke nuna "shi ne" ko "ni ne" ko "Wanda har kullum yana nan." * Hakanan Littafi Mai Tsarki yana koyar da mu game da "allolin" ƙarya waɗanda gumaka ne mara sa rai rai da mutane ke bautawa cikin kuskure. Shawarwarin Fassara: * Hanyoyin da za'a fassara "Allah" za haɗa da "Mahallici" ko "Siffa" ko Mai Iko." * Waɗansu hanyoyin da za'a yi fassarar "Allah" su ne "Mahallici Mai Iko Dukka" ko "Ubangijin Dukkan Hallita" ko "Madawwamin Mahallici." * Yi la'akari da yadda ake kiran Allah a naku harshen da ake fassara. Idan haka ne yana da muhimmanci a tabbatar cewa wanan kalma ta yi daidai da ɗabi'ar Allah na gaskiya da aka ambata a sama. * Harsuna da yawa kan mori babban baƙi na farko a rubuta suna Allah na gaskiya domin bambanta shi da allahn ƙarya. * Wata hanya kuma da zata sa wanan ya zama ikakke ita ce moron wata kalmar domin ambaton "Allah" da kuma "gunki." * Kalmar nan "zan zama Allahnsu za su zama mutanena" za'a iya fassara ta da "Ni Allah zan yi mulki bisa waɗanan mutane za su kuma yi mini sujada." (Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Yahaya 01:7 * 1 Sama'ila 10:7-8 * 1 Timoti 04:10 * Kolosiyawa 01:16 * Maimaitawar Shari'a 29:14-16 * Ezra 03:1-2 * Farawa 01:2 * Hosiya 04:11-12 * Ishaya 36:6-7 * Yakubu 02:20 * Irmiya 05:5 * Yahaya 01:3 * Yoshuwa 03:9-11 * Littafin Makoki 03:43 * Mika 04:5 * Filibiyawa 02:6 * Littafin Misalai 24:12 * Zabura 047:9