# cikasawa, cikakkake, yin wani abu ## Ma'ana Kalmar nan "cikasawa" tana nufin kammalawa ko cikasa wani abu da ake sauraro. * Lokacin da aka cika anabci, wanan ya nuna Allah ya sa abin da aka yi anabci ya cika. * Idan mutum ya cika abin da ya yi alƙawari ko wa'adi, wanan na nuna cewa ya cika abin da ya yi alƙawarin yi. * A cika wani aiki na nufin yin abin da ake bukaatar mutum ya yi. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "cikasawa" da "kammalawa" ko "gamawa" ko "iddawa" ko "sa abin ya faru" ko "biyayya" ko "cikasa." * Kalmar nan "an cikasa" za'a iya fassara ta da "abin ya tabbata" ko "ya zama gaskiya" ko "abin da ya faru" ko "abin da ya wakana." * Hanyoyin fassara "cikasawa," kamar a kalmar "cikasa hidamarku," zai haɗa da "kammala" ko "yin" ko "aiwatar" ko hidimta wa sauran mutane kamar yadda Allah ya kira ka ka yi." (Hakanan duba: annabi, Kristi, mai hidima, kira) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sarakuna 02:27 * Ayyukan Manzanni 03:17-18 * Lebitikus 22:17-19 * Luka 04: 21 * Matiyu 01:22-23 * Matiyu 05:17 * Zabura 116:12-15