# gafara, yin gafara, gafartacce, halin gafara, jinƙai, wanda aka nuna wa jinƙai ## Ma'ana Yin gafara shi ne kada a riƙe wani da zafi a zuciya duk da yake sun yi abu na cutarwa. "Yin gafara" shi ne gafartawa wani. * Gafartawa wani a mafi yawan lokuta shi ne rashin horon mutum a sakamakon kuskuren da ya aikata. * Kalmar nan akan yi amfani da ita cikin salon magana ta bada ma'anar "sokewa" kamar "soke bashi." * Lokacin da mutane suka furta zunubansu, Allah yakan gafarta musu bisa ga hadayar mutuwar Yesu a kan gicciye. * Yesu ya koya wa almajiransa su gafartawa sauran kamar yadda ya gafarta musu. Kalmar "jinƙai" tana nufin a gafartawa ba tare da bada horo akan zunubin wani ba. * Wanan kalma tana da ma'ana ɗaya da "yin gafara" amma tana ɗauke da ra'ayi na ɗaukan ƙudiri na kai na ƙin horon wani sabo da laifinsa. * A sahi'ance, Alƙali kan iya yin gafara ga mutumin da aka samu da laifi. * Ko da yake munyi laifin zunubi, Yesu ya yi mana jinƙai don kada a hukunta mu da wutar jahannama, bisa mutuwarsa ta hadaya akan gicciye. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "gafara" da "jinƙai" ko "sokewa" ko "saki" ko "rashin jin zafin" (wani) * Kalmar "gafartawa" za'a iya fassara ta da rashin aiyana hukunci akan (wani) akan "ba shi da laifin" wato "nuna halin jinƙai." * Idan harshen na da wata tsararriyar matsaya ta gafara, za'a iya amfani da kalmar a fassara "jinƙai." (Hakanan duba: laifi) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Farawa 50:17 * Littafin Lissafi 14:17-19 * Maimaitawar Shari'a 29:20-21 * Yoshuwa 24:19-20 * 2 Sarakauna 05:17-19 * Zabura 025:11 * Zabura 025:17-19 * Ishaya 55:6-7 * Ishaya 40:2 * Luka 05:21 * Ayyukan Manzanni 08:22 * Afisawa 04:31-32 * Kolosiyawa 03:12-14 * 1 Yahaya 02:12