# mara bada gaskiya, halin rashin bada gaskiya ## Ma'ana Kalmar nan "mara bada gaskiya" tana nufin a zama da rashin bangaskiya ko a ƙi gaskatawa. * Wanan kalmar an more ta domin a nuna mutane waɗanda ba su yi imani da Allah ba. Ƙarancin imanin ana ganinsa ta wurin mummunar rayuwarsu da suke yi. * Annabi irmiya ya zargi Isra'ila da zama da rashin bada gaskiya ga Allah. * Sun bautawa gumaka suka kuma bi waɗansu al'adu na waɗansu mutane da ba su bautar Allah. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta ga wurin, kalmar nan "marar bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin aminci" ko "marar yin imani" ko "marar biyayya ga Allah" ko marar imani." * Kalmar nan "halin rashin bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin imani" ko "rashin aminci" ko "tayarwa ga Allah." (Hakanan duba: gaskatawa, aminci, rashin biyayya) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ezekiyel 43:6-8 * Ezra 09:1-2 * Irmiya 02:19 * Littafin Misalai 02:22 * Wahayin Yahaya 21:7-8