# ɗaukaka, ɗaukakakke, yin ɗaukaka, aikin ɗaukaka ## Ma'ana Kalmar nan "ɗaukaka babban yabo ne kogirmamawa ga wani. Za ta iya zama ɗora wani ne akan babban muƙami. * A cikin Littafi Mai Tsarki kalmae nan "ɗaukaka" an fi moron ta ne a ɗaukaka Allah. * Sa'ad da mutum ya ɗaukaka kansa, wannan na nufin yana tunanin kansa ta hanyar fahariya, da rashintawali'u. Shawarwarin Fassara: * Hanyoyin da za'a fassara "ɗaukaka" sun haɗa da "babban yabo" ko "yabo mafi girma" ko "girmamawa sosai" ko "kwakwazantawa" ko faɗinmanyan abubuwa game da mutum." * A waɗansu wuraren za'a iya fassara ta ta amfani da kalmomin kirari, wato a yaba wa "mutuma kan babban matsayi"ko yin maganar ƙasaita game da mutum." * "Kada ka ɗaukaka kanka" za'a iya fassara shi da "kada ka ɗauki kanka fiye yadda ya kamata" ko "kada ka yi fahariya da kanka." * "Waɗanda suka ɗaukaka kansu" za'a iya fassara shi da "waɗanda ke tunanin kansu fiye da yadda ya kamata" ko "masu taƙama da kansu." (Hakanan duba: yabo, sujada, ɗaukaka, fahariya, girman kai) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Bitrus 05:5-7 * 2 Sama'ila 22:47 * Ayyukan Manzanni 05:31 * Filibiyawa 02:9-11 * Zabura 018:46