# bãbã, bãbãni ## Ma'ana A kusan kullum in ana magana akan kalmar nan bãbã ana nufin mutum ne da aka cirewa mazakuta. A wancan lokacin an yi amfani da kalmar wajen ambaton duk wani jami'in gwabnati, koma da waɗanda basu da wani lahani a jiki. * Yesu ya ce waɗansu bãbãnin haka aka haife su, ƙila sabo da lahani a fannin mazakutarsu, ko kuma sabo da rashin iya yin jima'i. Sauran suka zaɓi yin rayuwa irin ta bãbãni. * A kwanakin cancan baya bãbãni su ne masu yiwa sarki hidima, akan sa su su zama 'yan tsaro akan wurin zaman mata. * Waɗansu bãbãnin kuma manyan jami'ai ne na hukuma, irin su bãbã na Habasha, wanda ya sadu da manzo Filib a jeji. (Hakanan duba: Filib) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 08:27 * Ayyukan Manzanni 08:36 * Ayyukan Manzanni 08:39 * Ishaya 39:7-8 * Irmiya 34:17-19 * Matiyu 19:12