# falmara ## Ma'ana Falmara ko riga mai baki biyu, wata irin riga ce firistocin Isra'ila ke sawa. Tana da haɓa biyu gaba da baya, da aka haɗa a kafaɗu sai haɗa a ɗaure tare da maɗaurin sutura. * Irin wanan falmarar akan yi ta da zane iri ɗaya kuma firistoci kan sa ta. * Falmarar da babban firist ke sawa an yi mata adon zinariya na musamman tana da kalar shunaiya, tsanwa, dakuma ja da ƙyal-ƙyal. * Wanan makarin ƙirji na babban frist an liƙe shi da falmarar, a bayansu kuma an sanya duwatsu masu sheƙi da ake amfani da su domin a tambayi Allah game da nufinsa akan waɗansu al'amura. * Alƙali Gidiyon cikinwawanci ya yi falmarar da ta zinariya sai ta zama abin da Isra'ilawa suka bautawa a matsayin gunki. (Hakanan duba: firist) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sama'ila 02:18-19 * Fitowa 28:4-5 * Hosiya 03:4 * Littafin Alƙalai 08:27 * Lebitikus 08:7