# almajiri, almajirai ## Ma'ana Kalmar nan almajiri tana nufin mutum ne wanda ya ɗauki dogon lokaci tare da malami, yana koyo daga hali da kuma koyarwar malaminsa. * Mutanen da suka bi Yesu suna koyon da kuma sauraren koyarwarsa da kuma yin biyayya da su ana kiran su "almajirai." * Yahaya mai baftisima shima yana da almajirai. * A lokacin hidimar Yesu akwai almajirai da dama da suka bi shi suka saurari koyarwarsa. * Almajiran Yesu ya zaɓi almajirai goma sha biyu su kasance masu bin sa na kurkusa; waɗannan mutane su aka sani da "manzanni." * Almajiran Yesu sha biyu sun ci gaba da zama "almajiransa" ko "sha biyu." * Gab da tafiyar Yesu sama, ya ummarci almajiransa da su koya wa sauran mutane yadda suma za su zama almajiran Yesu. * Duk wanda ya yi imani da kuma biyayya ga koyarwarsa ana ki ransa almajirin Yesu. Shawarwarin Fassara: * Kalmar almajiri za'a iya amfani da ita a ambaci "mai bi" ko "ɗalibi" ko mai "koyo" ko "makoyi" * A tabbata cewa irin wanan fassarar kalmar ba wai makoyi da ke koyo a aji kawai take nufi ba. * Fassarar irin wanan kalma za ta zama da bambanci dafassarar kalmar "manzo." (Hakanan duba: manzo, imani, Yesu, Yahaya (mai Baftisima), sha biyun) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 06:1 * Ayyukan Manzanni 09:26-27 * Ayyukan Manzanni 11:26 * Ayyukan Manzanni 14:22 * Ayyukan Manzanni 13:23 * Luka 06:40 * Matiyu 11:03 * Matiyu 26:33-35 * Matiyu 27:64