# wanda aljani ya kama ## Ma'ana Mutumin da aljani ya kama yana da aljani ko kuma mugun ruhun da ke sarrafa shi akan abin da yake tunani ko yi. * A lokuta da yawa mutumin da mugun ruhu ya buge yakan ciwatar da kansa ko kuma sauran mutane domin aljanin yakan sa shi ya yi haka. * Yesu ya warkar da mutane waɗanda aljanu suka kama ta wurin umartar aljanun su fita daga cikinsu. Wannan akan fi yawan kira da "fitar" da aljanu. Shawarwarin Fassara: * Waɗansu hanyoyi da za'a yi fassara wanda aljani ya kama sune sune "mai aljanu" ko "mai bugun aljanu" ko wanda ke da mugun ruhu a cikinsa." (Hakanan duba: aljani) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Markus 01:32 * Matiyu 04:24 * Matiyu 08:16 * Matiyu 08:33