# ranar Ubangiji, ranar Yahweh ## Ma'ana A cikin Tsohon Alƙawari "ranar Yahweh" ana ambatonta ne domin a nuna wani lokaci na musamman da Allah zai hukunta mutane sabo da zunubinsu. * Sabon Alƙawari a yau yana baiyana "ranar Ubangiji" a kan ranar da Yesu zai dawo ya sharianta mutane a ƙarshen lokaci. * Wannan hukunci na ƙarshe da kuma tashi daga matattu ke tafe shima ana ganinsa a kan "ranar Ubangiji." Wannan lokacin zai fara a lokacin da Yesu zai dawo domin ya shari'anta masu zunubi ya kuma kafa mulkinsa na har abada. * Kalmar nan "rana" a wasu lokutan ana moron ta domin a nuna wata rana ko kuma wani "lokaci" ko "taro" wanda ya wuce rana ɗaya. * A wani lokaci kuma ana ganin hukunci akan cewa shi ne "saukar da fushin Allah" a kan waɗanda ba su bada gaskiya ba. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta ga abin da ke rubuce a wurin, waɗansu hanyoyi da za a fassara "ranar Yahweh" za su iya haɗawa da "lokacin da Yahweh zai hukunta masu ƙin sa" ko kuma "lokacin fushin Yahweh." * Waɗansu hanyoyi kuma da za a fassara "ranar Ubangiji" sun haɗa da Ubangiji Yesu zai zo ya yi wa duniya shari'a." (Hakanan duba: rana, ranar hukunci, Ubangiji, tashi daga matattu, Yahweh) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Korintiyawa 05:05 * 1Tassolonikawa 05:02 * 2 Bitirus 03:10 * 2 Tassalonikawa 02:02 * Ayyukan Manzanni 02:20-21 * Filibiyawa 01:9 -11.