# ɗiyar Sihiyona ## Ma'ana "Ɗiyar sihiyona wani salon magane da ke nufin mutanen Isra'ila. An fi amfani da wannan salon maganar a cikin anabce-anabce. * A cikin Tsohon Alƙawari, ana fin yawn yin amfani da sunan "Sihiyona" a matsayin sunan birnin Yerusalem. * Ana amfani da "Sihiyona" da Yerusalem" da nufin ambaton Isra'ila. * Kalmar nan "Ɗiya" ƙauli ne na ƙauna ko tarairaya. Salon magna ne da ke nuna haƙuri da kulawar da Allah ke da su ga mutanensa. Shawarwarin Fassara: * Hanyar yin fassara wananya haɗa da "ɗiyata Isra'ila, daga Sihiyona," ko "mutane daga Sihiyona, waɗanda ke kamar ɗiya a gare ni" ko "Sihiyona, ƙaunatattun mutanena Isra'ila." * Yafi kyau a riƙa moron kalmar "Sihiyona da yake an more ta sosai a cikin Littafi Mai Tsarki. Za a iya ɗan yin rubutu a cikin fassara don a nuna yadda aka mori misalin wata siffa domin a baiyana wata ma'ana ko wani anabci. * Hakanan ya fi kyau ayi ta moron "Ɗiya" a fassarar waɗanan kalmomin muddun dai an fahimce su da kyau. (Hakanan duba: Yerusalem, annabi, Sihiyona) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Irmiya 06: 02 * Yahaya 12:15 * Matiyu 21:05