# giciye ## Ma'ana A lokacin Littafi Mai Tsarki, giciye wani itace ne da ake soka shi ƙasa, sa'annan a ratsa wani gungume a kusan karshen samansa. * Lokacin mulkin Romawa, gwamnatin Roma takan kashe masu laifi tawurin tsire su akan giciye a barsu su mutu a nan. * An zargi Yesu akan laifin da bai yi ba Romawa kuwa suka kashe shi akan giciye. * A yi lura cewa wannan kalmar dabam take da "tsallakewa" wanda ma'anar ta ƙetarewa ne zuwa wancan hayin, misali, rafi ko tafki. Shawarwarin Fassara: * Wannan kalma za a iya fassarata tawurin amfani da wasu magana a harshen masu juyi da ya fassara yadda siffar giciye take. * Ayi kokarin bayyana yadda giciye yake wato abu ne da ake kashe mutane a kansa, yi amfani da furci haka, "gungumen kisa" ko "itacen mutuwa." * Yi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin wani Littafi Mai Tsarki na yaren kasar. (Hakanan duba: gicciyewa, Roma) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Korintiyawa 01:17 * Kolosiyawa 02:15 * Galatiyawa 06:12 * Yahaya 19:18 * Luka 09:23 * Luka 23:26 * Matiyu 10:38 * Filibiyawa 02:08