# kãda mai laifi, kayarwa ## Ma'ana Wannan magana "kãda mai laifi " da "kayarwa" ana nufin sharianta mutum ne domin abin da bai yi dai dai ba. * Yawancin lokaci "kãda mai laifi" ya haɗa da hukunta wannan mutumin domin abin da yayi da ba dai dai ba. * Wani lokaci "kãda wa" yana da ma'ana haka zargin marar laifi ko a sharianta wani da haushi kwarai. * Wannan kalma "kayarwa" ana nufin kãda wa ko zargin wani. Shawarwarin Fassara: * Ya danganta da yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, za a iya fassara wannan kalma haka "shria'antawa tsawa maitsanani" ko "kushe mutum cikin rashin gaskiya." * Wannan furci "kãda shi" za a iya juya shi zuwa "zartar da shari'a cewa wani yana da laifi" ko "a ce dole a hore shi domin zunubinsa." * Wannan kalma "kayarwa" za a iya fassara shi haka "shari'antawa da haushi" ko "a furta wani da laifi" ko "hukunci domin laifi." (Hakanan duba: alƙalai, horo) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Yahaya 03:20 * Ayuba 09:29 * Yahaya 05:24 * Luka 06:37 * Matiyu 12:07 * Littafin Lissafi 17:15-16 * Zabura 034:22 * Romawa 05:16