# umarta, umarci, umarni ## Ma'ana Wannan kalma "umarci" shi ne a dokaci wani mutum ya yi wani abu. "Umarta" ko "umarni" abin da aka dokaci wani mutum yayi ne. * Koda shike waɗannan kalmomi suna da ma'ana ɗaya, "umarni" yawancin lokaci ana nufin wasu dokokin Allah waɗanda tsararru ne kuma basa sakewa, kamar "Dokoki Goma." * Umarni zai iya zama haka ("Ka girmama iyayenka") ko doka ("Ba zaka yi sata ba"). * Idan aka "karɓi umarni" ma'ana "an bada doka" ko "a bishe da" wani abu ko wani mutum. Shawarwarin Fassara * Zai fi kyau a fassara wannan maganar dabam da, "shari'a." Kuma zai yi kyau a kwatanta fassararsa da "dokoki" da "ka'idodi." * Wasu masu fassara za su fi so su fasara "umarta" da "umarni" da kalma iri guda a yarensu. * Waɗansu za su fi so su yi amfani da wata kalma musamman domin umarni da zai nuna daɗewar, tsararrun umarnai da Allah yayi. (Hakanan duba: umarni, farilla, shari'a, dokoki goma) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Luka 01:06 * Matiyu 01:24 * Matiyu 22:38 * Matiyu 28:20 * Littafin Lissafi 01:17-19 * Romawa 07:7-8