# yin kaciya, kaciya ## Ma'ana Wannan kalma "yin kaciya" yanke loɓar abin fitsarin ɗa namiji ne. Za a iya bikin yin kaciya game da wannan. * Allah ya umarci Ibrahim yayi wa kowanne ɗa na miji a cikin iyalinsa da barorinsa kaciya alamar alƙawarin Allah da shi kenan. * Allah ya umarci zuriyarsa su cigaba da yin haka don kowanne yaron da aka haifa a gida. * Wannan furci "kaciyar zuciya" fasarar shi ne "yankewa" ko "fitar da zunubi daga mutum. * A cikin ruhaniya, "masu kaciya" sune mutane waɗanda Allah ya tsarkake daga zunubi tawurin jinin Yesu kuma sune mutanensa. * Wannan furci "marar kaciya" na nufin waɗanda ba a yi masu kaciyar jiki ba. Zai iya zama kamar misalin waɗanda ba a yi masu kaciyar ruhaniya ba, waɗanda ba su da zumunci da Allah. Shawarwarin Fassara * idan a yaren masu yin fassara akwai al'adar kaciyar maza, kalmar da suke amfani da ita sai ayi amfani da ita a wannan. * Wasu hanyoyin fassara wannan kalma sune, "yanka kewaye" ko "yanka a zagaye" ko "yanke loɓar abin fitsarin maza." * A al'adar da ba a san kaciya ba, zai zama dole a fassara shi a ƙarshen shafin littafi. * A tabbata kalmar da aka yi amfani da ita wajen fassara bai haɗa da mãta ba. Mai yiwuwa ya zama dole a fassara da kalma ko furci da zai haɗa da ma'anar "namiji." (Hakanan duba: Ibrahim, alƙawari) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Farawa 17:11 * Farawa 17:14 * Fitowa 12:48 * Lebitikos 26:41 * Yoshuwa 05:03 * Littafin Alƙalai 15:18 * 2 Sama'ila 01:20 * Irmiya 09:26 * Ezekiyel 32:25 * Ayyukan Manzanni 10:44-45 * Ayyukan Manzanni 11:03 * Ayyukan Manzanni 15:01 * Ayyukan Manzanni 11:03 * Romawa 02:27 * Galatiyawa 05:03 * Afisawa 02:11 * Filibiyawa 03:03 * Kolosiyawa 02:11 * Kolosiyawa 02:13