# 'ya'ya, yaro ko yarinya ## Ma'ana A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai. * A cikin Littafi Mai Tsarki, al'majirai da mabiya ana kiransu "'ya'ya." * Sau da yawa wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da it wajen kiran zuriyar mutum akan ce da su 'ya'yansa. * Wannan furci "'ya'yan wani abu" ana nufin halaiyar'ya'yan yadda take. Ga misali: * 'ya'yan haske * 'ya'ya masu biyayya * 'ya'yan shaiɗan * Wannan furci "'ya'ya" zai iya zama game da mutane waɗanda 'ya'yan ruhaniya ne. Misali, "'ya'yan Allah" wato mutanen Allah tawurin bangaskiya cikin Yesu. Shawarwarin Fassara * Wannan kalma "yara" yakamata a fassarata a matsayin "zuriya" sa'ad da ana nufin jikokin mutum ko tattaɓa kunnensa. * Bisa ga yadda zai shiga cikin rubutu "'ya'yan wani abu" za a iya fassara shi haka, "mutane waɗanda ke da halaye kamar" ko "mutane masu yi kamar." * Idan yayiwu, wannan furci "'ya'yan Allah" za a iya juya shi a sauƙaƙe, tunda muhimmin kan magana a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne Allah Ubanmu na sama. Wasu fassarar tare da waɗannan sune, "mutanen Allah" ko "'ya'yan Allah na ruhaniya." * Lokacin da Yesu ya kira almajiransa "yara" wannan ma za a iya fassara shi haka, "aminaina abokai" ko "ƙaunatattun almajiraina." * Wannan furci, 'ya'yan alƙawari" za a iya fassara shi haka, "mutanen da suka karɓi abin da Allah ya alƙawarta masu." (Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Yahaya 02:28 * 3 Yahaya 01:04 * Galatiyawa 04:19 * Farawa 45:11 * Yoshuwa 08:34-35 * Nehemiya 05:05