# kira, ana kira, kirayowa, kirayayye ## Ma'ana Waɗannan maganganu "kira" da "ƙwala kira" hanya ce ta faɗin wani abu da ƙãra ga wani mutum wanda baya kusa. Akwai wasu ma'anan da yawa. * A "ƙwala wa wani mutum kira shi ne yin magana da ƙarfi wa wani mutum dake nesa. Za a iya fassara shi neman taimako daga wani, musamman daga Allah. * Yawancin lokaci a Littafi Mai Tsarki, "kira" na da ma'anar "umarni" ko "umarnin a zo" ko roƙon a zo." * Allah yakan kira mutane su zo gare shi su zama mutanensa. Wannan shi ne "kiransu." * Wannan kalma "kirayayye" ana amfani da ita a Littafi Mai Tsarki da ma'anar Allah ya aza ko ya zaɓi mutane su zama 'ya'yansa, su zama bayinsa da masu shelar maganarsa ta ceto ta wurin Yesu. * Wannan kalma kuma ana amfani da ita in za a kira mutum da suna. Misali, "Ana ce da shi Yahaya," ma'ana "Ana ce da shi Yahaya" ko "Sunansa Yahaya." * Idan an ce "ana kiransa da sunan wani" ma'anar shi ne an ba wani mutum sunan wani mutum. Allah ya ce ya kira mutanensa da sunansa. * Ga wani furci daban, "na kira ka da suna" ma'ana Allah ya san sunan mutumin kansa ya kuma zaɓe shi musamman. Shawarwarin Fassara: * Kalman nan "kira" za a iya fassarata haka ' kiran umarni," wato kiran hakika ne kuma da dalili. * Wannan furci "an ƙwala maka kira" za a iya fassarta shi "na roƙe ka taimako" ko "na yi maka addu'a nan da nan." * Sa'ad da LIttafi Mai Tsarki ya ce Allah ya "kiraye" mu mu zama bayinsa, za a iya fassara wannan haka, "an zaɓe mu musamman" ko "ya sa mu" mu zama bayinsa. * "Dole ka kira sunansa" za a iya juya shi zuwa "dole ka raɗa masa suna." * "Ana kiran sunansa" za a iya fassara shi haka, "sunansa" ko "ana kiran sa." * "‌Ƙwala kira" za a iya fassara shi haka "faɗi da ƙarfi" ko "yi ihu" ko " faɗa da murya mai ƙarfi." A tabbata fassarar bata nuna kamar mutumin yana fushi ba. * Wannan furci "kiran ka" za a iya fassara shi zuwa "dalilin ka" ko "nufin Allah domin ka" ko "aikin Allah musamman domin ka." * A "kira bisa sunan Ubangiji" za a iya cewa "nemi Ubangiji ka kuma dogara a gare shi" ko "ka dogara ga Ubangiji ka yi masa biyayya." * Ma'anar "kira domin" shi ne "tilasta" ko "roƙo domin" ko "umarta." * Wannan furci "ana kiran ku da sunana" za a iya fassara shi haka, "na baku sunana, yana nunawa ku nawa ne." * Sa'ad da Allah ya ce, "na kirayeka da suna," za a iya fassara shi haka, "na san sunanka na kuma zaɓe ka." (Hakanan duba: addu'a) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Sarakuna 18:24 * 1 Tasalonikawa 04:07 * 2 Timoti 01:09 * Afisawa 04:01 * Galatiyawa 01:15 * Matiyu 02:15 * Filibiyawa 03:14