# albarka, mai albarka, sa albarka ## Ma'ana A sã wa wani mutum ko wani abu "albarka" ma'anar shi ne a sã abu mai kyau da abubuwan amfani su faru ga mutumin nan ko wannan abin da ake săwa albarka. * Ma'anar sã wa wani mutum albarka furta marmarin abu mai kyau da kuma amfani ne ya faru ga mutumin nan. * A lokacin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci mahaifi zai furta ƙaiyadadden albarka akan yaransa. * Sa'ad da mutane suka "albarkaci" Allah ko suka nuna son a albarkaci Allah, wannan ya nuna suna yabon sa. * Wannan kalma "albarka" wani lokaci ana amfani da ita a tsarkake abinci kafin a ci ko domin godiya da kuma yabon Allah domin abincin. Shawarwarin Fassara: * Idan an sã "albarka" za a iya fassara shi ya zama "ayi tanadi mai ɗunbun yawa domin" ko "ayi alheri da tagomashi ga." * "Allah ya kawo babbar albarka ga" za a iya juya shi haka, "Allah ya bada kyawawan abubuwa da yawa ga" ko "Allah yayi tanadi jingim domin" ko "Allah ya sa abubuwa masu kyau su faru." * "An albarkace shi" za a iya juya shi haka "Zai sami babbar riba" ko "zai ɗanɗana abubuwa masu kyau" ko "Allah zai sa ya wadata." * "Mai albarka ne mutumin da" za a iya fasara shi haka "Zai zama da kyau ƙwarai ga mutum wanda." * Furci kamar wannan "albarka ga Ubangiji" za a iya fasarata "Bari a yabi Ubangiji" ko "Yabi Ubangiji" ko "Na yabi Ubangiji." * A lokacin da aka sã wa abinci albarka, za a iya fassara wannan haka, "a gode wa Allah domin abinci" ko "a yabi Allah domin ya basu abinci" ko "a tsarkake abincin ta wurin yabon Allah domin sa. (Hakanan duba: yabo) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Korintiyawa 10:16 * Ayyukan Manzanni 13:34 * Afisawa 01:03 * Farawa 14:20 * Ishaya 44:03 * Yakubu 01:25 * Luka 06:20 * Matiyu 26:26 * Nehemiya 09:05 * Romawa 04:09