# ƙaunatacce, ƙaunatattu ## Ma'ana Wannan kalma "ƙaunatacce" magana ce ta soyayya da yake nuna wanda ake ƙauna da kuma kwarjini ga wani daban. * Kalman nan "ƙaunatacce" ma'anarta shi ne "wani wanda yake ƙaunatacce" ko "(wanda ake) ƙauna." * Allah ya ambaci Yesu "ƙaunataccen ‌Ɗansa ne." * A cikin wasiƙunsu zuwa ga ikilisiyoyin Kirista, yawancin lokaci manzanni sukan ce da 'yan'uwansu masu bada gaskiya "ƙaunatattu." Shawarwarin Fassara: * Wannan kalmar za a iya fassarata a ce "ƙauna" ko "ƙaunataccen nan" ko "wanda an ƙaunace shi" ko "mai daraja." * Idan ana magana akan aboki na kurkusa, za a iya fassara wannan haka "abokina mai daraja" ko "abokina amini." A Turance za a ce, "mai daraja abokina, Bulus" ko "Bulus wanda abokina ne mai daraja." Wasu yare zai fi masu sauƙi su sa shi a wani jerin. * Ayi lura kalmar nan "ƙaunatacce" ta zo ne daga magana game da ƙaunar Allah, wanda ba sai da dalili ba, babu son kai, kuma hadaya ce. (Hakanan duba: ƙauna) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * 1 Korintiyawa 04:14 * 1 Yahaya 03:02 * 1 Yahaya 04:07 * Markus 01:11 * Markus 12:06 * Wahayin Yahaya 20:09 * Romawa 16:08 * Waƙar Suleman 01:14