# baftisma ## Ma'ana A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "baftisma" za a fassara ta haka "yiwa Kirista wanka a ruwa don a nuna an tsarkake shi daga zunubi an kuma haɗa shi ɗaya da Almasihu. * Banda kuma baftisma ta ruwa, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar "baftismar Ruhu Mai Tsarki" da "baftisma da wuta." * Wannan kalma "baftisma" an sake yin amfani da ita a Littafi Mai tsarki domin a fassara shan matsananciyar wahala. Shawarwarin Fassara: * Kiristoci sun banbanta a ra'ayi game da yadda za a yiwa mutum baftisma da ruwa. Mai yiwuwa zai fi kyau a fassara wannan kalma da yadda za a yi amfani da ruwan kawai. * Zai danganta ga nassin, kalmar "baftisma" za a iya fassara haka "a tsarkake," "a zuba a kan," ko lumawa" a ko (tsomawa) a ciki," "wankewa," ko "tsabtacewa a ruhaniya." A misali, "a yi maka baftisma da ruwa" za a iya fassarawa a matsayin , "tsoma ka cikin ruwa." * Kalmar "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "tsarkakewa," "zubawa," "lumawa," "tsabtacewa," ko "wankewar ruhaniya." * Sa'ad da ake nufin wahala, "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "zamanin matsananciyar wahala" ko "tsabtacewa ta wurin matsananciyar wahala." * A kuma yi la'akari da yadda ake fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki cikin yaren garin ko ƙasar. (Hakanan duba: Yahaya (mai Baftisma), tuba, Ruhu Mai Tsarki) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ayyukan Manzanni 02:38 * Ayyukan Manzanni 08:36 * Ayyukan Manzanni 09:18 * Ayyukan Manzanni 10:48 * Luka 03:16 * Matiyu 03:14 * Matiyu 28:18-19