# iko, hukuma, ikoki ## Ma'ana Wannan kalma "iko" fassararta shi ne karfin bishewa da mallaka da wani mutum yake da shi akan wani mutum daban. * Sarakai da masu sarauta suna da iko akan mutanen da suke mulki. * Kalman nan "mulkoki" yana nufin mutane, gwamnatai, ko ƙungiyoyi da suke da iko kan wasu. * Maigida yana da iko akan barorinsa ko bayi. Iyaye suna da iko akan 'ya'yansu. * Gwamnati tana da iko ko 'yanci ta kafa dokoki da zasu kare 'yan ƙasarta. Shawarwarin Fassara: * Wannan kalma "iko" za a iya fassarata haka, "sarrafa" ko "'yanci" ko "fannin ƙwarewa." * Wani lokaci "iko" zai iya zama da ma'ana haka "ƙarfi." * Sa'ad da aka yi amfani da "masu iko" game da mutane ko ƙungiyoyi dake mulkin mutane, za a iya fasara shi a ce "shugabanni" ko "masu mulki" ko "ikoki." * Wannan faɗar "da ikon kansa" za a iya juya shi a ce "da 'yancin kansa na shugabanci" ko "bisa ga fannin kwarewarsa." * Wannan furci "ƙarƙashin iko" za a iya fassara shi haka, "yana da kamun kai yayi biyayya." ko "yana biyayya da umarnan waɗansu." (Hakanan duba: ɗan ƙasa, umarni, biyayya, iko mai mulki) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Kolosiyawa 02:10 * Esta 09:29 * Farawa 41:35 * Yona 03:6-7 * Luka 12:05 * Luka 20:1-2 * Markus 01:22 * Matiyu 08:09 * Matiyu 28:19 * Titus 03:01