# kaffara, yin kaffara ## Ma'ana Kalmar nan "yin kaffara" da "kaffara" ana nuna yadda Allah ya bada hadaya domin biyan hakin zunuban mutane a kuma huce hushin Allah akan zunubi. * A lokacin Tsohon Alƙawari, Allah ya bari a yi kaffara na ɗan gajeren lokaci a yi shi domin zunubin Isra'ilawa ta wurin miƙa jinin hadaya, wanda ya ƙunshi yanka dabba. * Kamar yadda yake a rubuce cikin Sabon Alƙawari, mutuwar Amasihu akan gicciye ita ce kaɗai gaskiya da kuma kaffara ta din din-dindin domin zunubi. * Lokacin da Yesu ya mutu, ya ɗauki hukunci da ya cancanci mutane saboda zunubansu. Ya biya hakin kaffara ta wurin hadayar mutuwarsa. Shawarwarin Fassara: * Kalmar "kaffara" za a iya fassarata da kalma ko furci mai ma'ana haka, "biya domin" ko "tanada abin biya domin" ko "ayi dalilin da za a gafarta zunuban wani" ko "gyara domin laifi da aka aikata." * hanyoyin fassara "kaffara" za su haɗa da waɗannan, "biya" ko "hadaya domin a biya sabili da zunubi" ko "tanada abu domin gaffara." * A tabbatar fassarar wannan kalma bai nuna biyan kuɗi ba. (Hakanan duba: marfi kaffara, yafewa, sasantawa, sulhu, fansa) Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: * Ezekiyel 43:25-27 * Ezekiyel 45:18-20 * Lebitikus 04:20 * Littafin Lissafi 05:08 * Littafin Lissafi 28:22